Skip to main content

Antin Yara - Hausa Novels

🔥 *ANTIN YARA* 🔥


Chapter 1



Had'ad'd'un motocine guda uku ne suke wucewa 406 ne a gaba,se prado a tsakiya, sannan benz a karshe suna tfy a titin GIREI local government.

Daga nesa kuwa wani tsohone kwance akan titi yanata birgima,sega wata budurwa tana rik'e da kwanon abinci da kuma ruwa mai sanyi tana tfy a gefen titi se idonta yakai gun wannan tsohon daya fad'in.
"Da sauri ta ajiye abinci tayi gun wannan tsohon da bisimillah sannan ta d'agoshi tana cewa sannu baba lfy? Meke damunka? Ita kanta tasan bazata samu amsar tambayanta daga gareshiba gashi babu yadda zatayi seta hango motocinnan suna zuwa. Kwantar da tsohon tayi ta mik'e tare da tsayawa akan titi tanata k'ok'arin tsaida motocin amma sam basu da niyan tsayawa. Ganin halin da tsohon yake cikine setak'i matsawa akan titin dole dai 406 d'innan ya tsaya ganin budurwan tak'i kaucewa. Da saurinta ta k'araso gun motan tanata buga glass, d'aya daga ciki ya sauke glass d'in gaba yace ke wace irin...bata bari ya k'arasaba tace dan Allah malam fito ka taimakamin wancan tsohon ya fad'i bansan meke damunshiba. Suka kalli junansu sukace bazamu iyaba, mamaki ya cikata seta rabu dasu taje gun pradon tanata buga glass d'in gaba dana baya. Glass d'in baya aka sauke nidai SAD-NAS idanu na bud'e da kyau dan ganin wani had'ad'd'en saurayi a ciki yana sanye da suit fari tas k'amshine kawai yake tashi. Budurwan ta had'iyi yawu sannan tace bawan Allah pls ka taimaka min wancan tsohon yana neman taimako sannan ni kad'ai bazan iya d'agashi daga kan titiba shiyasa na tsai daku. Cikin mamaki seya cire glas d'in idonshi ya ajiye a gefensa sannan ya bud'e mota ya fito batare daya ce mata komai seyayi mata nuni da hannunshi alaman muje. Da sauri ta wuce gaba yana biye da ita har suka k'arasa gun tsohon,budurwan tace toya ka tsaya kuma d'agashi ka maidashi gefe mana, saurayin yana kallonta har cikin ido yayi magana a hankali yace to ai ke nake jira mu d'agashi tare. Mamaki ya kamata tace yanzu kai a matsayinka NAMIJI bazaka iya d'agashiba harse na taimaka maka? Kai kawai ya d'aga mata alamar EH. Ba musu ta kama tsohon suka d'agashi zuwa gefen titi, saurayin ya lura da cewa farfad'iyace take damun wannan tsoho, dan haka ya koma gun 406 ya karb'i inhela sannan ya dawo ya taimakawa tsohon cikin ikon Allah tsohon ya dawo hayyacinsa sannan saurayin yace sannu baba Allah ya baka lfy sannan ya juya ya koma motarshi. Budurwan tace sannu baba ina zuwa kaji, sannan ta mik'e taje gun pradon ta sake buga glass d'in a hankali lokacin motar tana k'ok'arin tashi. Saurayin ya sake sauke glass tare da cewa me kuma? Budurwan tana murmushi tace nagode da taimakonka. Saurayin yace me alakarki dashi? Tace MUSULUNCI bayan wannan bakomai, saurayin yace dama "you don even know him? Budurwan tace yeah na taimaka mishine saboda yana buk'atan taimakon dan haka nagode Allah ya kiyaye hanya, harta juya ta fara tfy seyace 'yan mata. Na'am tace dashi tare da dawowa gun ta tsaya, yasa glass d'inshi yace nima nagode da kikasa na samu wannan ladan. Budurwan tace karkamin godiya bawan Allah amaimakon godiyan da zaka min, inaso idan ka sami dama toka taimaki mutum UKU kuma suma kace musu su taimaki mutane UKU inaga K'ASARMU zataci gaba tayin hakan se'anjima sannan ta tafi. Kalaman yarinyar sun burgeshi sosai yace da driver'n shi "lets go" nan driver yayi hon se 406 d'in tayi gaba sannan suma suka wuce saurayin yanata bin budurwan da kallo se karkad'ewa tsohon jiki takeyi sannan ta rik'e hannunshi ya mik'e yana cewa nagode sosai yarinya Allah ya miki albarka. Budurwan tace ameen baba, amma banason godiyan nafiso idan ka samu dama a rayuwarka toka taimaki mutum UKU kuma suma kace musu su taimakawa mutane UKU. Tsohon yace to shikena yarinya ya sunanki? Tace sunana MARYAM amma amfi sanina da AUNTY'N YARA,seta d'auki abincinta ta tafi yanata binta da kallo.
Shi kuwa wannan saurayin kalaman MARYAM kawai yaketa mishi yawo a kwakwalwanshi.
Suna cikin tfyane seya hango wasu mutane UKU suna bin wata yarinya a guje se kuka takeyi. Yace da driver tsaya, bayan driver ya tsayane seya cire farin suit nashi da glass d'insa ya fita da sauri ya fara bin bayan mutanennan da gudu harya cafko biyu. Jin hakan yasa yarinyar tsayawa tana cewa bawan Allah ka taimakamin wai fyad'e zasumin. Duka ya fara musu kamar ba gobe suna bashi hakuri, yace baku da tausayi sam,yanzu ku zakuso ayiwa k'anwarku fyad'e? Sukace a'a kayi hakuri bazamu sakeba, yace ina fata zaku gyara halinku inba hakaba wataran se anyiwa k'annenku koma 'ya'yan cikinku. Jikinsu yayi sanyi sukace kayi hakuri kema kiyi hakuri daga yau mun dena kuma mungode. Saurayin yace karkumin godiya,amaimakon godiyar da zakumin inaso arayuwa idan kun samu dama toku taimaki mutane UKU2 suma kuma kucemusu su taimakawa wasu mutane UKUN ya juya ya kalli yarinyar yace harda kema sannan ya tafi sunata binshi da kallo sukacewa yarinyar muje zamu rakaki har gida, dad'i taji sannan suka tafi.
Shi kuwa ya koma mota yasha ruwan FARO mai sanyi sannan ya goge takalminshi tare dasa suit da glass nashi sannan driver yaja mota se gida.
Suna isa saurayin ya fito ya shiga ciki. Wata kyakkyawar budurwace ta fito daga d'aki tana sanye da wandon jeans fari da kuma black top mai hannu d'aya kanta ba d'ankwali ta baza gashinta tana danna TAP ahannunta daga ganinta kasan k'anwar wannan saurayinne dan kamannin harya b'aci. Murmushi takeyi tare da cewa "The Prince! "The Captain!! "And d Bro MANOSH!!! Daga ina ka fito hakane dukka dawo a gajiye bro MANOSH? Suit d'inshi yake cirewa yanacewa "pls not now MIHER" Bari na watsa ruwa se inzo kinji? Alright tace dashi sannan ya wuce side d'inshi ita kuwa MIHER ta zauna tanata buga game d'inta. Sallama taji, ta masa batare data kalli kosu wayeba, tap d'in hannunta taji an karb'e seta d'ago kai da murna sosai tace "The 6 Emms" (M) yaushe kuka shigo k'asar without alartn me? dariya sukayi mata amma banda d'aya daga cikinsu, MIHER tace bro MARWAN miskilancin ya tashi kenan? Marwan yace ke ina MANOSH, tace yana ciki,duk suka wuce sukabar MAJID yana rik'e da TAP d'in yace bana hanaki irirn wannan shigarba? Tace am sorry luv aidan ina gidane kuma bansan kun dawoba wlh amma promise daga yau bazan sakeba tana murmushi. Shima murmushin yayi yace to shikenan kije kisa himar ina jiranki a side d'in PRICE, ok luv ina zuwa me za'a kawo muku? Karki damu a k'oshe muke ruwa kawai muke buk'ata kuma zamu samu agun bro naki dan haka ki huta my luv yana mata murmushi sannan ya bata TAP d'in ya wuce itama ta shige ciki dansa hima...
Palon manosh suka wuce kai tsaye suka baje akan kujerunsa masu kyau ga laushi. Muhammad ya kunna musu TV tare da d'ansa volume ta yadda manosh zaisan akwai mutane a palon,ball suke kallo suna hira. Manosh ya fito sanye da shets fara da kuma bak'in jeans,mamakine ya kamashi su kiwa dariya sukasa tare da cewa the prince captain manosh. Karasawa yayi ya zauna kusada muhsin da marwan yace gaskya bakuda kirki wlh,ashe kuna hanya shine har marwan kana cemin wayankane ba charg,marwan yai mirmushi yace muhsin ne yace karmu gaya maka,muhsin yace haba dude haka zakamin kuma,dariya sukasa dukkansu manosh yace to ina tsarabana naganku empty hand. Majid yace babu ya ibada ya hanya kawai se tambayan tsaraba,gaskya bakada kirki,manosh yace wannan tambayan ai mata kad'ai akeyiwa dan sune sakaltattu amma kana namiji dan kaje UMRAH harse anyi maka wani sannu,muhammad yace sosai kuwa ai haka ya dace,manosh yace toku rik'e tsarabanku indai hakane nasan marwan zai bani. Marwan yace ni ibada kawai naje ba sayan tsaraba ba my friend,muhsin ya mik'e ya d'auko ruwan sanyi yasha sannan yace to nidai zanje hira,kuda bakuda kowa sekuyita hiranku da kallon ball,harzai wuce manosh ya janyoshi yace wlh baka isaba nima na samu matar aure had'add'iya kuwa tamafi MIHER d'inka dan haka ka dena wani cika baki,ba majid kad'aiba dukkansu suka juya suna mishi kallon mamaki,domin duk cikinsu manosh ne kawai tun tashinsu bai tab'a ganin wata 'ya mace yace yana soba koda wasa. Muhsin yace "wow dude" gaskya zanso inga mai wannan SA'AN yau kaine da budurwa kodai wasa kakeyi? Manosh ya bisu da kallo dan dukkansu idonsu a kanshi yake suna jiran jin mezaice,yace wlh yauna had'u da wata yarinya bafulatana nitsatsiya gata tason taimakon wanda bata saniba sedai k'aramace,amma wlh ta burgeni sosai kuma kunsan wani abu dayasa na damu da ita "we luk alike dudes" zanso ku ganta she's so sweet. Majid yace harka tab'ata kenan,bugun wasa yakaiwa majid yace kai d'an iskanefa a hakanma wai k'anwata kake so shine kake min wannan maganan,majid yace to ai naji kace she's so sweet ne shine ban kane ba,manosh yace eh ina nufin voice nata yadda kasan mutum in yana mura kasan muryanshi yana canjawa,to amma nata yayi dad'i sosai kuma ba muran takeyiba natural voice nata kenan,bari dai in tak'aice muku kunsan dai muryan RANI dabanyake a cikin sauran matan indians da suke FILM,to haka dai itama yarinyan amma nata yafi na RANI dad'i idan tana magana bazakaso ta gamaba wlh nd.....marwan yace enoght me sunanta? Manosh yace nidai bansan sunantaba but zan dinga kiranta da MY APPLE. Ajiyar zuciya suka sauk'e muhammad yace gaskya zanso in ganta ko zan samu k'awarta nima,manosh yace ai wannan ne nakeso in samamishi k'awarta dan naga ya kusa ya tsufa baiti aureba,marwan yayi murmushi yace kai baka tsufaba seni,muhsin yace gara dai kam ka taimakawa marwan dan tunda FADILA ta rasu ta barshi gabad'aya bana gane mishi. Majid yace kuka sani kozai bitane ku kyaleshi kawai,duka marwan zaikawa majid se yayi sauri wucewa gun k'ofa yana cewa to ai gaskyane nidai na tafi gun luv d'ina prince ina tayaka murna dolene muje nemo soyayyar APPLE namu,manosh yace gaskya na baka k'anwata koba'ayi tambayana nariga dana baka ita. Dariya suka sa sannan majid ya tifa gun MIHER,su kuwa sukaita hira nada'an wani lokaci sannan suka fito kowanne ya shiga motarsa ya tafi.
Miher tace bro manosh k'awata tana sonyin magana da kai amma kuma idan kun had'u seta kasa saboda kunya. Manosh yace wata k'awarkin kenan,tace LUBNA nama bro kaima kasan banida da k'awar data kaita duk duniya,manosh yace to to ai bata cika maceba kenan tunda tana tsoron na miji,miher tace bafa tsoro takejiba kunyane da kuma tunanin disgin da zaka mata,manosh yayi murmushi tare dajan hancin miher yace wani irin disgi kuma luvlyn sis,tace bro SONKA fa takeyi wlh amma takasa gaya maka nace ta bari in sanar dakai amma tak'i tace wai ita zata sanar dakai kuma wlh bazata iyaba pls bro ka amin....shiii sis karki k'arasa pls kedai ki bari tunda bata sakiba harse lokacin dataga ya dace seta sanar dani kinji,miher tace hakan ya nuna kaima kana sonta kenan? Manosh yace nop ina dai sonta a matsayin k'anwan abokina kin gane yana mata murmushi,miher tace dat why nake so ku fahimci juna tunda k'anwar marwan ne. Manosh yace zomuje palo mu zauna,bayan sun shiga sun zaunane yace miher akwai abinda baki saniba inaso ki nutsu ki saurareni kuma bance ki gayawa kowa,miher tace haba bro kasan akwai sirri mai karfi a tsakaninmu kuma babu wanda yake sani se mutum d'aya,manosh yace wa kenan? Tace zuciyana mana tana dariya wanda yake kara mata kyau,shima dariyan yayi yace to kina jina
Ita dai LUBNA ba k'anwar marwan na jini bane, iyayen marwan suna son bby girl tun farkon aurensu tunma ba'a haifemuba,se Allah ya basu d'a namiji marwan kenan,sunyi farin ciki sosai kuma ke kanki kinsan yadda suke sonshi,amma ita mahaifiyarshi tanata so ta haifi mace gashi kuma bata sake haihuwaba shine sukaje gidanmarayu suka d'auko lubna tun tana jaririya suka riketa tamkar 'yar cikinsu. Mamaki sosai mihertayi dajin wannan lbrn da bro manosh ya bata,tace bro da gaske kake?murmushi yayi yace na tab'a miki karyane,tace wlh abun yaban mamaki amma to itama lubnan batasan da hakaba ko? Manosh yace bata saniba amma duk iyayenmu sun sani damuma,shiyasa banaso kiyinunakin sani kema. Miher tace to amma shine dalilin da yasa baka sonta kenan,manosh yace bahakabane sis yana jnkumatunta yace ai lubna yarinyar kirkice gata kyakkyawa duk namijin daya ganta zai sota amma kuma nid'in ban shirya neman mace bane yanzu shiyasa,ya kare maganar yana murmushi tare da barin palon ya d'auko key'n motansa ya fito yana cewa me,zan sayo miki sis,binshi kawai take da kallo tace bro ina zakaje kuma,yace gurin OGA na zanje yana nemana daga nan kuma zanje a rage min gashin kaina dan yana damuna sosai,miher tace pls kar'a rage dewa domin gashin yana maka kyau ai adai gyara maka shi,to luvlyn sis byee,itama hannun ta d'aga mishi guards d'insa sun mik'e da sauri yace no ni kad'ai zanfita karku damu,ok sukace dashi sannan mai gadi ya bud'e gate ya fita.
Auntyn yara har an gama abincinne,eh baba an gama ya rana ya kasuwan? Alhamdulillah yau na samu ciniki sosai se hamdala,murmushi tayi tace to madallah baba kaci abincin idan anzo saya se in sayar,to 'yar baba nagode ya maman naki,lfyanta k'alau tace in gaidaka,yace to ina amsawa yau kind'an dad'e yar baba,tace wlh baba wlh mutum ne farfad'iya ta kamasa akan titi ya fad'i shiyasa kaga na dad'e, yace Allah sarki 'yar baba Allah ya rayamin ke Allah ya miki albarka,Allah yasa kiyi kyakkyawan karshe a rayuwarki. Tace ameen baba harda kai da mama da dukkan 'yan'uwa musulmai. Tun daga nesa ta fara jin muryan yaran makaranta sunata cewa oyoyo auntyn yara2,da sauri ta fito daga cikin gidan FLOWER tana murmushi tare da tafa hannun tana cewa oyoyo kannen aunty suka rungumeta dukkansu yaran amma banda d'aya, seda suka gama oyoyon sannan d'aya yaron yace sannu auntyn yara,tace sannun Abdallah nah ya makarantan,yace alhamdulillah sannan ya gaida baban auntyn nasu,yaran sukace aunty mutafi gida to, tace to baba ka gamane? Babanta yace na gama kuje yana murmushi,suka mishi sallama tare da addu'an Allah ya kawo kasu mai albarka suka tafi.
Dad'i yakeji a ransada samun 'ya kamar maryam gashi tana da marrin jini kowa yana sonta manya da yara...
Maryam ko kuma ince auntyn yara suna tfy suna hira da yara se bata lbrn makaranta sukeyi ita kuwa tanata dariya dayake ita d'in akwai fara'a ga kowa. Abdallah yace auntyn yara wai yaushe uncle ibrahim zai dawone,tace yadai kusa akwai wani abune,yace kawai dai naga nauyin ya miki yawane,tayi murmushi ta e aiba komai koda ya dawoma ai aiki zai kama tunda bautar k'asa ya tafi,abdallah yace har inaso in girma da wuri kodon indinga taimakawa kamar ke,dariya tayi tace insha Allah burinka zai cika abdallah. Haka dai suketa hira da yaran unguwansu suna tafiya jama'an dake wucewa sunata d'agawa auntyn yara hannu tare da gaisuwa maza da mata kowa ya santa a garin girei.
Maryam ita kad'aice agun iyayenta suna sonta sosai fiye da ransu gashi sunyi sa'an yarinya tunda ta taso da son mutane take musamman yara k'anana kowa nata duk gireim ana alfahari da ita tun tana primary ita take zuwa na d'aya har secondary kuma ko'a islamiyama haka gata da murya mai dad'i musamman idan tana karatun Qur'an kyaututtuka sosai garin girei ta samu dukta dalilin maryam har gasan Alqur'ani mai girma tana zuwa state state kuma ita take zuwa na d'aya kona biyu ta hakanne takai iyayenta makka da kyautar kujeran da take samu agun MUSABAK'A,dayake ta samu kujeran sau dewa dan haka aminan mahaifintama dukta basu kyautar su uku kuma itama taje amma sam bata hakorin makka ba. Maryam tana da son yara sosai, dan haka take koyar dasu acikin gidansu bayan yaran sun dawo daga makara,duk fanni arabic da boko tana koyar dasu daidai iyawarta,dan tana da ilimi sosai. Ayanzu dai sun gama secondary suna jiran result kenan, yaranma suna sonta sosai dan tana kula dasu sosai komai k'azartar yaro bata kyamarsa gashi ta iya sayomusu abin wasannin musamman balobalo da ice cream na dela kananan nan,indai ta shiga gari toseta sayo musu shiyasama bata rabuwa da katon din biski da su sweet a d'akinta.
Wannan daliline yasa ake kiranta da auntyn yara babba da yaro dan yanzu ba'ama ganeta da maryam sedai kace AUNTY'N YARA,itama tana jin dad'in sunan da ake kiranta dashi. K'awayenta su hud'u ne kuma kansu a had'e yake dukkansu, rashida muh'd,amina babale,zahida abba,da kuma samira jauro. Sune k'awayen maryam tare suka gama makaranta kuma duk y'an girein ne,abdalla shine k'anin rashi muh'd yarone mai hankali da nutsuwa ga son addini kuma yana da ilimi sosai yaron yana da shiga rai sosai shiyasa duk cikin yaran maryam tafi sonshi,saboda mahaifinsu baya raye suda mamansu kawai suke zama uncle ibrahim shine babban yayansu.
Bayan sallan la'asar baban maryam ya dawo gida,daga maryam har mamanta sunyi amakin ganinsa,yace kuna mamaki ko wlh flower dai kad'an ya rage duk an saye yanzuma cikin JIMETA zan shiga in sayo wasu. Maryam tace baba yanzu duk sun k'are,yace wlh addu'arkuce ta d'azu ta karb'u kinsan bakin yara wani mutumine yayi sabon gida kuma yana so ya shuka flower shine ya sayi fiye da rabi,sukace Alhamdulillah baba ka kawo inje tunda nima nasan gurin kaika huta a gida,yace to 'yar baba gashi.
Nan da nan maryam ta shirya cikin after dress bak'i ta d'auki pos d'inta tace sena dawo,sukace to Allah ya kare tace ameen sannan ta wuce titi tana isa kuwa ta samu mota se jimeta.
Koda ta isa kekenape ta hau ta k'arasa gurin, amma sai mai keke yace bashi da canji,tace toya zamuyi kenan tana ta waige waige seta hango manosh yana rabawa masu bara sakadan 200 sabbi gal,ta kalli mai nape tace malam dan Allah kayi hakuri bari inje can in nemo canji,yace to bakomai. Nan ta nufi gurin manosh yanata raba musu kud'i tayi sallama tare da cewa bawan Allah,d'agowa yayi da sauri danjin muryan Apple ya kalleta batare dayin maganaba,tace sannu dai dan Allah canji zaka taimakamin dashi, ya kalli k'udin hannunta dubu d'aya,amma seyace wannan dai sadaka nake rabawa sannan banida wani canjin,tace to dan Allah ko 200 d'inne ka bani gashi ka rike 1000 d'in zan biya mai keke ne. Juyawa yayi yana kallon napen seyace rik'e dubun seya mik'a mata 200 d'in,tace nagode sannan taje tabiya mai nape ya bata canjin 150 seta dawo tace to kayi hakuri bari na shiga gun flower'nnan sena baka kud'inka,yace to se tayi saurin wucewa ciki yanata binta da kallo. Da yake sun santa tana shiga dama sun h'ada komai tunda babanta ya sanar dasu a waya dama. Bayan su gaisa se d'aya yace tokije ki nemo mota mana, tace akwai motoci anan muje kawai,suka bita dashi taga wani mota tace girei zaka kaini da wannan flowers d'in. Manosh yana ganin haka yama drivernshi waya take yazo da HILOX fara,yace kaje ka kaso flowers d'in can kasa a mota, har an fara sawa seya zo yace oga yace oga yace asa miki a mota,tace waye kuma oga,yace gashican shine mai gurinnan gabad'aya. Shuru tayi suka kwashe suka zuba dukka a hilox d'in setacewa mai motan data tsayar dan allah malam kayi hakuri,yace bakomai yarinya karki damu,tace nagode sannan ta k'arasa gurin manosh tace dama kaine mai nan gurin? Eh yace da ita tare da cewa kuje a kaiki gida koh,tace nagode sosai ga 200 d'inka,yace karkimin godiya,arayuwa idan kin samu dama toki taimaki mutane uku,suma kuma kice musu su taimaki wasu ukun ya k'are maganan yana murmushi,dad'i taji sosai har cikin ranta tana binshi da kallo harya shiga motarsa ya tafi. Gun hilox d'in ta nufa driver ya bud'e mata ta shiga ya rufe tace nagode sannan suka kama hanya yace ina zan kaiki,tace girei,yace ok sannan yaja suka tafi tana mai farin cikin jin kalaman manosh. Suna cikin tfy wayan driver yayi k'ara ya d'auka tare da cewa hello sir,se kuma yace eh nan girei ne sannan yace ok sir seya saka wayan a aljihunsa har suka k'arasa kofan gidan flower'n babanta sannan tace anan zamu tsaya,yace ok tare da tsayawa,dama babanta yana jiranta a shagonsa,drivern ya gaida baban maryam sannan suka kwashe flowern tare. Maryam da babanta sukayi godiya sannan ya tafi. Maryam taba babanta lbrn komai tun ranar da suka had'u da manosh,babanta yace to Allah ya saka mishi da alkhairi tace ameen sannan suka gyara ko ina sannan suka wuce gida.
Manosh yake tambayr drivernshi kaga gidansu? Yace no,sir a shop d'in babanta tace in tsaya shiyasa,inane shop d'in,nan yayiwa manosh kwatance,manosh yace gud shikenan kana iya tfy. Shima side d'insa ya wuce amma bata palonsu mum nashi ba ta d'ayan gefen yaje ya watsa ruwa ya kwanta yana tunanin apple.
Ita kuwa maryam tun bayan rabuwansu taketa tunanin had'uwansu na yau,taji dad'i sosai dataga yana bada sadakannan,gashi handsome guy musamman brawn eye nashi,sedai ta lura baya sonyin dariya sam.
Manosh ne a palo da mum nashi da kuma miher yana cewa mum jibi zan tafi ABUJA saboda aikana da oganmu yayi kuma zan kai 1week kafin na dawo,mum tace to Allah ya taimaka Allah yakare,yace ameen se miher tajiyo wayanta na k'ara a cikin d'aki da sairi ta mik'e manosh yana binta da kallo yace mum dama akwai wata yarinya dana ganine shine nake so asani a addu'a in alkhairine to Alah ya tabbatar,dad'i sosai mum taji tace to Alhamdulillah gaskya naji dad'i sosai Allahya tabbatar da alkhairi lallai mahaifinka zaiyi farin ciki dajin hakan. Manosh yace amin mum nagode nizan fita,tace to Allah ya kare,yace amin sannan ya fice tare da gads nashi basu tsaya ko inaba se hospital d'inda muhammad yake aiki. A office ya samu muhammad bayan sun gaisa yace yane ina zakaje haka,manosh yace inaso kumin rakiyane gun surukina,dariya muh'd yayi yace da wuri haka,manosh yace banbi takan marwanba dan nasan bayi da lokaci a yanzu shine kake min tsiya,muh'd yace ai nima aiki nakeyi sedai ka nemo naji nasan "he's free",manosh yace wlh zan maka rashin mutunci ka tashi mana,tofa price da zafinka irin na sojoji muje kar tsumin naka ya tashi yanzu ka sani tsallen kwad'o,dariya manosh yayi sannan muh'd yace bari nayiwa nurse d'incan magana zan sameka a waje. Bayan muh'd ya fitone yace to kana nufin inbar motana kenan,manosh yace eh sannan suka wuce NNPC suka d'auki muhsin dan shine accounta general agun yake aiki. Mota uku ce se kuma majid suka d'auka a gida amma banda marwan shi banker ne sam babu lokaci, dan haka suka sallami mota d'aya suka tafi da guda 2.
Shidai wannan driver'n dayakai maryam shine yake musu jagoro har suka isa,cikin sa'a kuwa shagon a bud'e yake maryam ce a ciki tanata fesawa flowers d'in ruwa tana sanye da toyobo himar milk colour dogone har k'asa kuma mai hannu bakama iya ganin kayan da yake jikinta. Da sauri ta fito dan a tunaninta flower aka zo saya,ahankali suke fitowa majid ne ya fara fitowa tare dayin sallama sannan suma suka fito da irin sarin indian nan na maza jajaye se binsu da kallo takeyi harta hango manosh wana shi farin sarine a jikinsa duk wanda ya gansu dole su burgeshi. D'an murmushi kad'an tayi tare da amsa sallamar majid tace sannunku,majid yace yawwa,setace ina kwananku,suka amsa lfy amma manosh bai amsaba kallonta kawai yakeyi,bayan sun gaisane tace lfy dai ko,muhsin yace lfy lau munzo sayan flower ne,tace flower kuma ai naga kuna tare damai sayarwan,muh'd yace eh hakane amma mu naki mukeso,murmushi tayi wanda yake k'ara mata kyau batare datace komaiba,majid yace zan iya sanin sunanki dan nidai sunana majid,tace ni kuma sunana MARYAM amma auntyn yara akekirana,majid yace wow maryam babban suna,muhsin yace lallai yanzu mun zama 7 emms kenan,bata gane maganan muhsinba amma setayi shuru,muhammad yace meyasa ake kiranki da auntyn yara,tace yarane suka samin sunan,majid yace alamu ya nuna kina son yara kenan,murmushi tayi tace eh,majid yace munzo gurin mahaifinkine,tace ok yaje gida amma inaga yana hanyan zuwa nan. Muhsin yace nidai sunana muhsin,wannan kuma muh'd seya nuna manosh dayake tsaye yana waya da miher tana cewa wato bro shine ka tafi ko sallama babuko,yace wannankuma sedai ya gaya miki da bakinsa,murmushi tayi tace lallai fa dukknku "emms" muhsin yace eh shiyasa nace yanzumun zama 7 emms kenan akwai d'ayanmu shi bai samu zuwaba sannan akwai k'anwarmu ita M ce. Dariya tayi wanda ya baiyana fararen hakwaranta tace masha Allah,manosh ya gama waya yana binta da kallo yace ni ai bata gaisheniba bare in gaya mata sunana,kanta ta kawar gefe tana mirmushi tace ina kwana,yace seda na rok'a,shuru tayi ta rasa me zatace,majid yace tunda dai ta gaisheka ai shikenan,yace to lfy ya kike,tace fy lau kodai zaku k'arasa ne naga har yanzu bai dawoba wata k'ila akan yanya kuke,muhammad yace ta ina gidan yake,tace hanyan nan dai zaku mik'e duk wanda kuka gani a hanya ku tambayeshi gidansu auntyn yara za'a nuna muku,majid yace to mun gode amma ke kad'ai anan bakya tsoro,tace tsoro kuma aiba komai tana murmushi,muhsin yace to maryam auntyn yara bari muje idan muna dawowa zan sayi flower'n,dariya tayi tace to sekun dawo sannan suka shige motan shi kuwa manosh ya matso kusa da ita yana kallonta,kunya sosai taji tace kai bazaka tafi bane,yace zan tafi amma inaso in miki tambaya kafin in tafi,tace to ina jinka amma kanta na kallon wani gurn,yace akwai wanda yayi sallama agidanku akankine? Shuru tayi tare da kallonshi cikin kunya tace a'a amma ban saniba ko tagun babana,ahankali yake maganan yace akwai wanda yake zuwa gunkine? Tayi saurin mayar da kanta gefe tace a'a,murmushi yayi yace Alhamdulillah nagode AUNT semun juyo,shuru tayi batace komaiba ya wuce ya shiga mota suka tafi tanata binsu da kallo tana jin farin ciki a ranta kome dalili oho.
Har k'ofar gidan aka kaisu tare dayin sallama da Alhaji muh'd ATTAH. Ya fito yaga dai bak'ine dan baisansuba,da sauri suka sunkuya dan gaishesa,amma dayake mahaifinnata mai ilimin addinene seyace a'a a'a karku sunkuyamin wlh ku mik'e dan Allah,dad'i sosai sukaji azuciyarsu kuwa sukace lallai akwai SUNNAH agidannan,bayan sun mik'e yace to bisimillah ku shigo,suna biye dashi a baya har palonshi,inda ya musu nuni da kujera suka zauna sannan suka gaggaisa. Mahaifin maryam yace sedai ban ganekuba wlh, wani yarone ya shigo da sallama tare da kawo musu FARO WATER mai sanyi yana ajiyewa tare dayin gaisuwa ya fita. Muhammad yace eh baba abokinmune yazo neman izini akan maryam, baba yace Allahu Akbar ayya kuma sam maryam bata gaya min zaku zoba wlh,muh'd yace eh gaskya ita kanta bata sanmuba muna dai ganintane se mukayi tambaya akanta shine shine mukazo amma dai sun tab'a had'uwa dashi abokinmu. Baba yace Allah sarki toba damuwa an muku izini zaku iya zuwa a nan kuke ne? Muh'd yace eh muna nan a cikin jimeta tare da iyayenmu, ni sunana muh'd wannan majid,wannan muhsin sannan abokinmu kuma muh'd manosh. Baba yace to alhamdulillah bakomai Allah ya tabbatar da alkhairi,suka amsa da amin baba mun gode sosai, sannan ya tashi ya shiga cikin gida gun maman maryam ya gaya mata cewa tazo su gaisa,himar tasa baba yana gaba ta tsuguna daga waje shikuwa baba ya shiga cikin palon yace ga mahaifiyarta ku gaisa,sunkuyar da kai sukayi k'asa dukkansu sukace ina kwana mama,tace lfy kun zo lf,sukace lfy lau,tace to madallah sannunku da zuwa,sukace sannu mama sanna ta shige ciki bayare dasun gantaba. Majid da muhsin suka d'auki ruwan sukace to baba mu zamu tafi,baba yace to madallah mun gode sosai Allah ya kiyaye hanya kugaida gida,suka ce amin baba sannan suka fito baba ya bisu har kofar gida sannan ya koma ciki. Ajiyar zuciya manosh ya sauke suka kalleshi suna murmushi angon maryam,dariya yayi sannan yace majid kira mana yaran can mana,take sukazo muhsin ya bud'e but d'in mota yara suka dinga shiga da kayayyaki gidansu maryam. Bayan sun gamane baba ya fito yace haba ku kuwa harda d'awainiya haka to Allah ya saka da alkhairi mungode,sukace bakomai baba sannan baba ya koma gida,yaran kuwa kud'i majid ya rarraba musu naira d'ari d'ari sabbi se godiya sukeyi da murna sannan suka tafi.
Auntyn yara kuwa shuru taga baba bai dawoba bare kuma su majid,can seta hango motarsu na zuwa. Bayan sun isone se muhsin ya fito yace to ina flower nawa,tace wanne kake so,ya nuna wani yace wancan,anitse taje ta kawo mishi,yace nawane,tace 500 ne,yace to abani guda 2,nan ta sake kawo mishi,daidai lokacin suma suka fito,se muhsin ya karb'a tare da bata 1000,ta karb'a tace tona gode da ciniki,yace bakomainima na gode da sayarwa,dariya tayi,muh'd yace mun godefa auntyn yara ko kuma ince auntynmu mu zamu wuce toh,tace bakomai to Allah ya kiyaye hanya,sukace ameen se muhsin ya mik'awa manosh flower d'aya ya karb'a yana kallon muhsin d'in,sannan ya mik'awa maryam d'ayan amma bata karb'aba tace ya kuma kake bani,yace ka'rbi se in gaya miki,bamusu ta k'arba yace to dukkanku inaso ku shinshini flower'n sannan ya shige mota suka barsu su biyu rik'e da flower. Manosh yakai hancinsa kan flower'n uana kallonta kefa,murmushi tayi tare dakai flower'n kusa da hancinta tace nidai banji komaiba,manosh yace toni naji,tace me kenan,yace sosayyarki tare da ajiye mata flower'n yana murmushi yace ina wayarki? Agefenta ya hango INFINIX HOTNOTE ya d'auka yasa number'nshi yayi flashing wayanshi sannan ya ajiue mata wayan yace sekin jini AUNT. Murmushi kawai takeyi tana rik'e da flowern,suka sauke glass d'in motan tare da cewa byee AUNT, murmushi sosai takeyi tace tona gode,kamar had'in baki sukace karki mana godiya,idan kin samu hali ki taimaki mutum UKU suma kuma kice su taimakawa wasu UKUN,suna mata murmushi sosai itama haka,shi kuwa manosh hannu ya d'aga mata batasan lokacin data d'aga masa nataba suka tafi.

ANTIN YARA.
2----10
.
Maryam ta tsincin kanta dabin motansu da kallo tana murmushi tare da ajiye flowern hannunta tace kenan neman izini sukaje gurin baba akai?
Manosh kuwa murmushi da jin dad'i kawai yakeyi su majid sunata yaba kyawu da nutsuwa irinna maryam,muhsin yace gaskya abokina kayi sa'a dan wlh ganin maryam yafi jinta. Muh'd yace sosai kuwa muma dai Allah yasa mu samu k'awayenta,dariya manosh yayi daidai nan wayansa ta fara ringing,majid yace kodai maryam d'ince,manosh yace haba kai kuwa meka d'auketa kenan 'yar gaggawa? Majid yace no nidai banceba,manosh yasa wayan a kunne tareda cewa hello abokina ya akayine,marwan yace lbr zaku bani mana mun samu karb'uwa kuwa,manosh yayi dariya yace kaida ka sani kuma,marwan yace aaah "congrats dude" kadai samomin friend nata ko,dariya sukayi dayake suna iya jiyo abinda marwan yake cewa,muhsin yace muma da mukaje bamu samuba bare kuma kai,dariya marwan yayi yace to ai abin rabone,muh'd yace sosai to har yanzu dai rabon namu bai rantseba tukunna kaga majid dayake d'an iskane se dariya yake mana waishi ai yana da miher,marwan yace rabu dashi ba laifinshibane captain ne ya b'atashi ai tunda yace ya bashi miher tun da wuri,any way se kun iso ya banji muhsin bane,muhsin yace abokina aure kawai nakeso nima shiyasa ka jini silent,dariya sukeyi sannan marwan ya katse wayar yana dariya.
Mahaifin maryam seda ya rabawa makwabta abin alkhairin dasu manosh suka kai,sannan ya rabawa yaran da suka shiga da kayan sannan ya koma shop d'inna.
"Maryam tace sannu baba,yace sannu 'yar baba bak'in da sukazone yasa banzo da wuriba sunzo neman izinine akanki. Shuru maryam tayi dan kunya daya kamata tace baba zan iya tfy gida,yace eh jeki,sannan ta bashi kud'in cinikin seta tafi tana mai jin kunya.
Koda ta isa gida mahaifiyarta ta gaya mata komai tare da alkhairin da suka kawo. Murmushi kawai tayi tana bin kayan da kallo,wayar tace ta soma ringing,koda ta duba number'n manosh ne seta tashi ta shige d'akinta tare da d'aukan wayan tace assalamu alaikum,wa'alaikumus salam AUNT,murmushi tayi dan tasan shine setace na'am kun isa lfy,yace lfy lau ya muka barki,tace lfy mun godefa Allah ya saka da alkhairi,yace amin,tace inasu majid,yace duk sun wuce gurin aiki dama akan aikinsu na tattarosu,tace eyyah,yace bazaki tambayeni sunanaba,murmushi tayi tace to ina sauraro,yace a'a ai baki tambayeniba,shuru tayi tana murmushi a hankali,manosh ya sake kiran sunanta AUNT,tace na'am ina sauraon sunanka,yace sunana maryam,dariya tayi wanda shima ya sashi dariyan sannan yace eh mana,tace maryam ai sunan mata ne bana mazaba,yace sunana muh'd manosh mu biyune agun iyayenmu nida k'anwata miher,sannan ni SOJA ne amma friends d'ina suna kirana da prince wannan shine lbrna a tak'aice. Dariya sosai maryam tayi dan yadda yayi bayaninshi da sauri sauri tace masha Allah yanzu kai d'in soja ne,yace banyi kama da sojaba ko,tace gaskya kam,yayi murmushi yace to ai k'aramin sojane ni ba babba ba shiyasa,murmushi tayi kawai batace komaiba,yace aunt ya kikayi shuru kona dameki ne,tace a'a bakomai,yace to kefa,tace sunana maruam ni kad'aice agun iyayena na gama secondary skul muna jiran result,manosh yace ok to Allah yasa muga alkhairi,tace ameen,yace suwaye friends naki na kusa, tace rashida muh'd,amina babale,samira jauro da zahida abba,ya e duk a girei suke,tace rashida da sameera suna gireizahida tana jimeta,amina kuma tana yola. Yace ok kuma ku 5 kenan,tace eh,yace to duk ki gaishe min dasu pls,tace zasuji nagode,yace ok byee,tace byee tare da katse wayan ta sauke wani ajiyar zuciya tana murmushi.
Miher taji dai bro manosh yana waya kuma tasan da mace yakeyi,abin ya dameta sosai seta kira LUBNA a awaya tace k'awata gaskya kina sanya dewa kuma wlh na hango matsala,lubna tace kamar ya matsala,miher tace ina tunanin bro manosh ya fad'a soyayya da wata dan kamar naji suna waya ya kamata kiyi mishi magana yanzu gaskya kar asamu matsala. Hankalin lubna ya tashi tace da gaske kikeyi miher,miher tace wlh kuwa,lubna tace pls miher ki tambayi majid tunda saurayinkine pls kinsan babu yadda zanyi in tuntub'i bro marwqn da irin wannan zancen amma tunda ke budurwan majid ne pls miher,miher tace bakomai zan tambayeshi amma dukda haka "you have to do somethin friend" lubna tace sosai ma kuwa zanyi nagode byee.
Bayan sun gama wayane lubna ta ciza baki tace ina wlh bazai tab'a yuwaba,duk wanda tayi k'ok'arin shiga tsakanina da manosh wlh sena d'auki mummunan mataki a kanta ko 'yar gidan uban wayece ita.
Yaune manosh zai tafi abuja yana sanye da kakin sojojinshi yayi matuk'ar kyau ya fito da 'ayar k'aramar kit d'inshi a hannu ga kuma bindiga a aljihunsa yace mum zan wuce a mana addu'a,tace to Allah ya kare ka kula da ibada sannan kaji tsoron Allah aduk inda kake,miher da take gefe tace mum kullum sekin gaya mishi haka aiya zauna a kanshi,tace to ai addu'ace kuma d'an adam azijine,manosh yace amin mum rabu da ita yarantace,miher tace wlh bro niba yarinya bace "am a big gal"dariya sukayi suka rakoshi har waje driver yaja suka tafi air port. A hanyane ya kira maryam yace aunt kin tashi lfy,tace lfy lau ya mutanen gida,yace lfyansu lau yanzu na barosu ina hanya zan tafi abuja sannan zanyi 1week kafin in dawo karkiga shuru banzoba,tace ok Allah ya kiyaye hanya Allah kuma ya bada sa'an tfy,yace ameen aunt thankyou so much,tace wlcum,yace ki kulamin da kanki kinji,tace to nagode,yace ok byee sannan ya katse wayar.
Ita kuwa maryam seta tsinci kanta dason sake ganinshi dan ad'an lokaci kad'an da had'uwansu amma se taji tana sonshi sosai a ranta,dan tunda take babu wanda ya tab'a zuwa yace yana sonta sedai taji yara suna cewa aunty ai wane yace mana kece matarshi ko kuma wane yace mana ke zai aura, amma babu wanda ya tab'a sallama a gidansu se manosh.
Lubna ce kwance a d'akinta daya sha kayan duniya tana tambayan miher a waya toya ake cikine,miher tace wlh da gaskene amma nima majid yak'i gayamin mum ne na tambaya take cemin wai ai har sunje neman izini a girei yarinyar take. Ran lubna se tafasa yakeyi tace shikenan nagode,miher tace bro manosh yayi tfy yau kuma zai jima dan haka ki shirya yana dawowa sekizo,tace insha Allah miher nagode sannan sukayi sallama.
Hankalin lubna in yayi dubu ya tashi setace wlh dolene in fara shige shige gun malamai dan samo kan manosh kota halin k'ak'a koma wacece wannan yarinyar zan ganta ai kuma zanga dame tafini,kyaune ko gashi ko hasken fata ko kuma dukiya koma dai menene zakici ubanki wlh tunda kika shiga tsakanina da masoyina.
Manosh yana isa ya kira mum nashi sannan ya kira maryam,yace aunt na iso lfy,kunya taji sosai dan bata kirashiba tace to Alhamdulillah,yace baki damu danibako aunt,gashi ko kirana bakiyiba,tace am sorry bahaka bane,yace to menene,tace kayi hakuri zan gyara,dad'i yaji sosai yace toba komai I LUV U,kunya taji tayi shuru tana jinsa,ya kira sunan aunt,tace na'am,yace bakiji abinda nace bane,tace "me too" tare da katse wayan dan kunya dataji, shi kuwa dariya yakeyi yanaji sonta na k'aruwa a ransa...
Auntyn yarane take koya musu karatu a cikin gidansu dan har black bord babanta ya mata dan koyar da yara,gidan nasu d'an daidaine ba wani gidan masu hali bane,amma dai koda yaushe gidan tass yake. Tsakar gidan flour ne na silinti se'a shinfid'a katuwar taburma ana karatu.
Marwan ne a hanya zuwa girei duba abokinsa da bayaida lfy,ya kira manosh a waya amma yayita ringing bai d'aukaba. Bayan yaje sund'an tab'a hirane se yayi mishi sallama ya kama hanyan koma,kiran salla yaji muryan k'aramin yaro nan danan imani ya k'ara ratsa marwan yace kai bari dai na k'arasa kawai nayi la'asar tunda an kira. Har gun masallacin ya isa ya paka motarshi ta gefe seya hango wani yara,ya k'ara gun masallacin yayimasa sallama yaron ya amsa tare da cewa salla zakayi,marwan yace eh wanene ya kira sallah yanzu,yaron yace nine,marwan yace masha Allah amma kana da murya mai dad'i menene sunanka,yace sunana ABDALLAH,marwan yace suna mai dad'i gaskya inaso mu kulla abota dakai,abdallah yace to shikenan ya sunanka,yace marwan,abdallah yace kaima sunanka da dad'i ga buta kayi alwala a nan girei kake,yace a'a ina jimetane,abdallah yace ayyah nikam anan girei nake kagama gidanmu can ba nisa,marwan yace to ashe zan dinga zuwa kana koyamin k'ira'a,dariya abdallah yayi yace sedai kaje gun Auntyn yara ta koya maka itace malamata,yace waye kuma Auntyn yara,abdallah yace itace malamata kokuma ince malamar yaran unguwannan harma dana nesa.
Marwan yace bari dai muyi sallah ko semuyi hira,yace to sega yara sun fito daga gidansu maryam mata sun wuce gida maza kuma sun nufi masallaci. Kowannen sallama yayiwa 'yan masallacin sanan suka hauyin alwala,marwan yana ta ganinsu abun ya burgeshi sosai.
"Bayan an idar ne marwan yace da abdal muje can muyi hira se in tafi. Bayan sun k'arasane yace ina jinka kagani na mijine kuma babba kanaga auntyn yaran zata koya min karatun, yace a'a kam kayi girma sedai in zaka dinga zuwa masallacinnan daga magrib zuwa isha kullum ana karatu da kuma litattafai masu yawa. Dad'in hirannasu sosai marwan yakeji yace to yaran can da suka fito daga gidancan fa kodai koyarwa ake acan,yace eh auntyn yara ce mai koyarwa bayan azahar zuwa la'asar,biyanta akeyi,abdallah yace a'a fisabilillah dai ai auntyn yara kowa natane kuma kowa ya santa babba da yaro babu wanda zai iya gaya maka halinta don ta cika goma cip cip. Dariya sosai marwan yayi yace matar aurece,abdallah yace a'a budurwace kuma kuma kasan me,marwan yace a'a,abdallah yace auntyn yara macece mai tarin ilimin addini dana boko gata da son mutane sam bata da kyamar d'an adam aduk yadda ta ganshi,kuma tana son taimakon dan adam,gata kyakkyawa sosai amma kuma 'yar karamace.
Dariya sosai marwan yayi yace kai abdallah duk ita kad'ai kodai ka kara da nakane,yace wlh da gaske ko inkirata ku gaisa ne,marwan yace a'a kace mata me?abdallah yace ince mata tazo abokina yana so su gaisa,marwan yace zata fito,yace eh zata fito bari inje.
Maryam tana sanye da aldoguwar riga jah ta nad'a gyalen akanta tana k'okarin fitowa,se abdallah yayi sallama ta amsa tare da cewa abdalla rashida fa ta shirya kuwa,abdallah yace wlh ban saniba zaku fitane,tace eh zamuje jimeta duba zahida ba lfy,yace to muje dama gunki nazo zaku gaisa da abokina. Mamaki ya kama maryam tace aboki kuma,yace eh,tace to muje se suka fito a tare.
Marwan ya zubawa budurwan kallo har suka k'araso tayi mishi sallama ya amsa sannan suka gaisa,tace to abdallah mun gaisa nizan wuce,abdllah yace to ai shima jimeta zaije abokina ka sauketa dan Allah. Marwan yace tobakomai abokina auntyn yara muje,batayi mamakin jin sunata a bakin marwanba,se tace a'a wlh da wata k'awata zamu tafi yanzuma gidansu zanbi kafin mu wuce,abdallah yace abokina yayatace bari naje na kirata yana juyawa sema ga rashidan tahowa,yace kama ganta,murmushi maryam tayi tace daga yin aboki se kuma a d'aura mishi nauyi,abdallah yace to ai hanyanku d'aya,marwan yace sosai kuwa kuma ai zan samu lada ko,abdallah yace kwarai lokacin rashida ta iso suka gaisa sannan abdallah yayi mishi sallama har ya juy se kuma yace abokina bani numbern wayanka,marwan yana fad'a mishi shi kuwa yana sawa a wayansa sannan yace nagode sena kiraka,marwan yace tonagode sena sake zuwa.
Rashida ta kaftawa maryam ido akan ta zauna a gaba,badan tasoba hakata zauna ita kuma rashida tana baya suka tafi. Koda suka fara tfy babu wanda yayi magana acikinsu,se marwan yace auntyn yara ina zakuje a cikin jimeta,tace gurin NTA ,yace ok gaskya abdallah yarone mai hankali yaron ya shiga raina sosai wlh,maryam tace mungode,yace yace inzo zaki dinga koyamin karatu,tayi murmushi tace toba damuwa seka zo,marwan ya d'auki wayanshi yace hello Majid yane,majid yace ka dawone,yace na kusa isowa dai,yace ok idan ka shigo kamin waya,marwan yace ok sannan ya katse wayan.
Babu wanda ya k'ara cewa komai har suka iso har gidan,sannan suka fito tare da cewa mun gode fa,yace bakomai wlh kozan dawo in maidakune,maryam tace a'a za'a mai damu mungode sosai,yace to shikenan nima na gode.
Har seda suka shige gidan sannan yabar gurin yanata yaba kyau da nutsuwan maryam da kuma halaiyarta da abdallah ya gaya mishi.
Hira sosai sukayi da zahida sunata nishad'i gwanin sha'awa,zahida tace samira tacemin sunje mubi ko,maryam tace eh wlh se gobe zasu dawo, zahida tace ku tashi muje YAKUBU SHOPPING LPAZA zan sayi always da kuma kayan ado sun k'are,rashida tace ashe dai kin warke to muje kar muyi dare.
"Shopping sukayi dukkansu d'an daidai sedai maryam tayiwa yaranta tsaraba. Harsunzo fita se maryam taga key wata ya fad'i daga cikin bag nata batare data saniba, da sauri ta d'auka ta bita hargun motar k'irar HENESI tace 'yar'uwa kin yarda key d'inki,yarinyar ta juya suka had'a ido ta karb'a tare da cewa ayya nagode sosai kuma kinga keyn motatace wlh bansan ya fad'iba nagode sosai,maryam tace karkimin godiya 'yar'uwa inaso kema ki taimaki mutane uku a rayuwarki sannan suma kice su taimaki wasu ukun,murmushi tayi tace to shikenan ya sunanki,tace sunana maryam,tace eyyah ni kuma sunana LUBNA,tace ok sannu lubna se anjuma,lubna tace dan Allah bani number ki mana,nan taba maryam wayanta tasa mata number sannan tayi flashin,maryam tace zanyi saving lubna ko,lubna tace eh nagode sannan ta wuce gunsu zahida suka tafi.

 ANTIN YARA 11-30
.
Azumi yanata tafiya,abdallah se samun kayan sallah yakeyi agun jama'a. Dan shine mai kiran sallah a masallaci gashi da shiga rai. Ranan manosh manosh da marwan sunje girei se marwan yace aboki abdallah zoka gaisa da abokina wanda zai auri auntyn yara.
Abdallah yazo suka gaisa cikin fara'a yace dama kaine kake neman auntynah,manosh yace eh nine,abdallah yace to Allah ka rik'eta da amana karka cutar da ita dan Allah dan ance soja suna dukan matansu. Dariya sosai su manosh sukayi sannanya rik'o hannun abdallah yace har abada abdallah,karka sa ranni zan wulak'anta maryam domin ina k'aunarta fiye da yadda nake k'aunar kaika kuma wlh bacika baki nake makaba kaji? Abdallah yace alhamdulillah naji dad'i sosai Allah ya tabbatar muku da alkhairi,sukace ameen,sannan yace auntyn yara ta aikeni bari aje aje na dawo,sukace to seka dawo sannan ya tafi.
Abdallah yaje gunda uncle ibrahim yake da friends nashi yamusu slm tare da gaisuwa sannan yace yah ibrahim gurinka nazo an aikoni,ibrahim yace to ina jinka,se kuma abdallan yayi shuru,ganin shurunne ibrahim ya mik'e yace to muje gefe ka kaya mun.
Bayan sun koma gefene abdallah yace yah ibrahim auntyn yara ce ta aikoni gunka,dad'i sosai ibrahim yaji da akace auntyn yara yana sonji menene aikan. Abdallah yace tace wai tayita kiran number'nka amma yak'i tafiya,wai inzo ince maka tayi bak'i kuma tana so gu gaisa dasu. Ibrahim yace bak'i wani iri maza ko mata?abdallah yace maza wanda yake nemanta da kuma aunty rashida. K'irjin ibrahim ya buga sosai yace abdallah dama zance danaji da gaskene kenan akan auntyn yara? Abdallah yace eh yaya hakane tare da sunkuyar da kansa k'asa yana tusayin yayan nashi don shi kad'ai yasan irin k'aunar auntyn yara da yakeyi amma dayake bai gama karatunshiba shiyasama baiyiwa mahaifinta magana akaiba yafiso seya gama komai na karatunshi. Ibrahim yace kaje ina zuwa,sannan abdallah ya tafi jikinshi a sanyaye.
Ibrahim ya kunna wayanshi ya kira number'n maryam ringing d'aya ta d'aunka tare da salma,wani irin dad'i yaji har cikin ranshi dajin daddad'ar muryanta. Yace aunty wai kina nemana,murmushi tayi tace eh na kira wayanka ban samuba,yace wlh na kashene saka makon damuna da akayi,tace eyyah,yace ganinan ina zuwa ki basu hakuri kinji,tace laa bakomai wlh sunanan a waje dama gurinka kawai sukazo. Yace tonagode da mutuntani da kikayi aunty se anjuma,tace bakomai aikafi haka a guna uncle ibrahima nima nagode.
Koda ya ajiye wayan shi kad'ai yasan meyakeji a cikin ranshi game da maryam.
Ya k'arasa gumsu da sallama suka gaisa sosai kuma cikin fara'a dama shi ibrahim na kowane kamar dai maryam d'in. Hira sukayi sosai kamar sun dad'e da sanin juna,yayi musu tambayoyi suka bashi amsan gaskya domin wani abunba manosh b'oyewa yakeyi,sam bayaso asan mahaifinshi mai arzikine. Haka sukaitayidai har suka gama sannan suka sallama ibrahim ya wuce gida,se manosh ya kira maryam a waya yace aunt pls ki fito in ganki zamu wuce,tace har gun gaisa kenan zaku tafi,yace eh wlh ibrahim yana da kirki sosai wlh gaskya naji dad'in had'uwa dashi,dad'i taji da aka yabi ibrahim tace nagode nidai bazan fitoba aiba gurina kazoba,ya marairaice murya yace pls aunt kinga marwan yanata min dariya ai gara shi tunda rashi bata nan hankalinsa a kwance "pls come aou aunt"kodon fita kunya a idon marwan don wlh yau idan muka koma shimenan ya samu abun tsokana harsu majid sesunji. Dariya tayi tare da katse wayar d'inkin atamface a jikinta na fitet gaun seta sa himar iya gwinwanta ta fito.
Tunda ya hangota yake murmushi tare da k'are mata kallo harta iso gunsu tana murmushi,marwan yace ai wlh banso ki fito har addu'a nakeyi a raina amma se gashi kin fito meyasa aunt,mirmushi tayi tace saboda banaso ku mishi dariya,manosh yace "thankyou aunt"tare da kaiwa marwan bugu a bayansa yayi saurin shigewa mota gurin tuk'i ya rufe kofar maryam tanata dariya. Manosh ya dawo da kallonshi kan maryam yace wato har kin fara min yanga ko,tace aiba yana bane dama gun uncle ibrahim kukazo ba gunmuba,yace eh amma dai ai kinsan zanso in gaki ko,tace to ai gashi ka ganni kuma ni zan wuce gida,yace nidai ban sallamekiba tukunna,tace to sallameni,murmushi yayi wanda ya k'ara mishi kyau tana kallonshi shi kuwa wani gurin yake kallo daban. Tace wlh ka dingayin mirmushi yana k'ara maka kyau,dad'i yaji sosai yace wauace ki kalleni,mirmushi tayi tace ni ban kallekaba kawai dai na fad'a makane,yace kin kalleni mana kuma ai ke kika sani na fara murmushi sosai wlh,tace ahakan,yace "yes" ki tambayi miher zata gaya miki ni gaskya bancikayin fara'aba, yace hmmm to gaskya nidai ka dinga yi kaji,yace ai inayi kuma danke.
Tace to shikenan zan wuce,yace meyasa kikemin hakane aunt kodon kinga ina sonki sosaine shiyasa kike min haka,tace a'a wlh aiba guna kazoba kuma ai min gaisa,yace to shikenan mun tafi,tace kayi fushi kenan,yace a'a banyiba kawai dai zamu tafine,kallonshi takeyi amma sam yak'i kallonta kuma yana tsaye yana fiskantarta,tace toshikenan Allah ya kiyaye hanya,yace ameen sannan ta juya ta shiga gida,mota ya bud'e yashiga marwan yaja suka tafi.
Manosh ya saba idan suka bar girei seya kira maryam a hanya,amma yau sam sebai kirataba abun yad'an dameta tace to kodai fushi yayine? Har bayan 2hrs bai kiraba,kuma a wannan lokacin tasan suna gida,marwan ne ya kirata yace aunt mun iso gida lfy,tace alhamdulillah tona gode sosai,yace bakomai wlh mune da godiya sannan sukayi sallama.
Har bayan isha manosh bai kira maryam se taji taba kyauta mishiba dan tasan fushi yayi dukda dai basu tab'a samun matsalaba se yau. Har 9:00pm seta d'auki wayanta ta kirashi yanata ringing harya d'auke,zata sake kira kenan setaga call d'inshi,ta d'auka cikin sanyin murya tace hello
Shuru yayi baice komaiba
Ta sake cewa hello
Nanma shuru yak'i yayi magana, tace hello manosh,
Karon farko data kira sunanshi kenan,seyaji dad'i har cikin ranshi amma baice komaiba,ta sake cewa "manosh pls talk 2me" yace me kike so nace miki aunt? Tace wai fushi kakeyi danine, shuru yayi uanajin daddad'ar muryanta,ta sake cewa "manosh am talking to you" yace inace ni kike kora agaban marwan ko? Wani iri taji a ranta dan yadda yayi maganan batasan lokacin datace "am so sorry manosh i din't main to hurt you pls?" Nanma shuru yayi,ta sake cewa manosh wai bazaka min magana bane kuma kanajina? Yace "yes" take jikinta yayi sanyi tace manosh am sorry pls,nanma shuru yayi seta katse wayan. Hankalinta ya tashi sosai tayi dana sanin yimasa hakan.
Har 10pm manosh bai sake kirantaba,seta tsinci kanta cikin damuwa sosai sam ta kasa sakewa,dan tana son manosh sosai acikin ranta. K'arar shigowar texs tayi a wayanta da sauri ta d'auka ta bud'e taga
_Am sorry too apple_
_I love you so much_
_Nd i will call you leta_
_Am talking with my dad now okey,manosh loves you so verry much apple_.
Maryam tana gama karanta texs d'in taji dad'i sosai a ranta tayi murmushi tana mai k'ara jin sonshi na ratsa jikinta,tace i love you too peach tare da rufe idanunta tana murmushi.....
.
Seda manosh suka gama magana da dad nashi,sannan ya koma d'aki ya kira maryam har gurin 11:00pm. Maryam har tayi bacci,ta jiyo wayanta na k'ara da d'auka tare da sawa a kunnenta amma idonta a rufe yake tace hello,cikin muryan bacci, yace "apple am sorry for waking you up"tace "don worry manosh am fine"muryanta ya kashe mishi jiki gabad'aya atake yaji inama tana kusa dashine.
Sakeyin k'asa da muryanshi yayi yace "are you sure" tace "yeah am fine"ai manosh aiseya fara juyi akan gadonshi yace "no apple you have to sleep"zan kiraki da asuba kinji,tace "okey good night" yace sweet dreams apple,murmushi kawai ta mishi tare da katse wayar. Manosh ya sauke ajiyar zuciya yace "ooh my apple"Allah ya nunamin ranar da zan mallakeki a matsayin matata,da wannan tunanin bacci ya kwasheshi.
Wannan karon manosh baiyi tfy ba,har akayi nisa da azumi sannan suka kaiwa 'yan matansu kayan sallah a d'inke kuma masu tsada,da kuma redimate ga fashions ga takalma da jaka da turare komai dai suka had'o musu kowa da irin nashi,sannan sukayiwa iyayensu,harta abdallah seda manosh da marwan suka mishi kayan sallah.
Almajirai sam basa so azumi ya k'are,gashi indai a girene to kusan rabinsu sunsan maryam. Daidai da sabulun wanki ko omo haka zatayita raba musu 1/1 tace suyi wanki dashi,dan haka suna sonta sosai.
Azumi ya k'are yau gobe sallah se murna akeyi su maryam ansha kitso gata da gashi amma sam ita tafi so tayi kitso akan tabar kanta haka,su rashida kuwa wanke kai kawai sukayi amma zahida kitso tayi da ameena babale,su samirane yan wanke kai,gashi suna lalle gayu dai sosai sukayi.
Manosh bai samu zuwa rananba dan haka maryam tayi *cake* mai dad'i kuma had'ad'd'e dama duk sallah tanayi. Mhaifinta kuwa drinks ya sayo kala kala dan yasan 'yar tashi da jama'a bugu da k'ari suna son maryam sona hak'ik'a zai iya kashe duk dukiyarsa dan farin cikin maryam,shiyasa ma idan ka shiga d'akin maryam wlh bazaka tab'a zatan cewa a cikin gidansu d'akinta yakeba dan yadda mahaifinta ya gyara mata shi,gurin zuba littattafaima na musammanne,ga computer komai dai se wanda ya gani.
Yau take sallah kowa se murna su maryam suka shirya shirya tafiya *idi* anko suka sha ita da rashida da samira da himar nasu neavy blue toyobo dogaye har k'asa masu hannu sunyi ado sosai se k'amshi sukeyi. Mama tazo tace to maryam kinyi bak'o a waje,tace bako kima mama,tace eh,da sauri ta mik'e ta fita kawai setaga drivern manosh ne da *406* ash wai yazo ya kaisu masallaci. Mamaki ya kama maryam tace wlh kaje kawai masallacin fa babu nisa da k'afa zamu tafi,yace a'a madam idan na koma fad'a zaimin kiyi hakuri. Shuru tayi tace to ina zuwa,nan ta koma ta sanar da mamanta,mamanta tace to maryam kuje kawai tunda haryazo, haka suka fito abdallah ne a gaban motan su kuwa ukun suna baya sunata salati zikiri har suka isa, sannan yayi pakin a gefe shima yaje akayi sallah.
*Allahu Akbar Allah ka k'ara dauwamar damu a musulunci ameen*
Bayan an idarne sukaita hotuna a wayansu,ai se suka hango uncle ibrahim da friends nashi nan suka wuce aka gaisa sannan sukayi pictures da uncle ibrahim da kuma friends nashi yana tsaye kusa da maryam hotunan sunyi kyau sosai,shima driver se d'aukansu yakeyi a tap batare da sun saniba,amma sam bai d'auki su ibrahim ba.
Bayan sun gama ne sukayi sallama sannan suka zo gun drivern ya maidasu gida. *cake din* maryam ta zuba mishi a kula tare da soyayyen naman kaza da kuma ruwan faro mai sanyi ta bashi,karb'a yayi tare da godiya ya tafi.
Bayan tfyanshine ta kira manosh tace mun godefa,yace bamun b'ataba meyasa kika kirani,tace godiya na kira in maka sannan kuma....yace sannan kuma me, tace inaso ka kawo min *miher* anjuma mu yini,yace coman kike bani kenan,tace *no captain* alfarma nake nema,yace nak'i bazan kawotaba,tace haba mana pls ka kawota,yace nak'i d'in,tace to shikenan ni zanzo gurinta anjuma,murmushi yayi yace zan turo azo a d'aukeki sannan ya katse wayar ya sake kiranta.
Ta d'auka tace bana bukata dama zamuje gun zahidane se mu wuce gurin ameena. Yace wa kika tambaya babu inda zakije,tace saboda da me,yace ra'ayinane hakan,shuru tayi tace to shikenan ka kawomin miher dan tace seka yadda kafin take fita wani girin pls ka barta,yace sekin ce *am sorry peach* dariya tayi tace menayi to,yace nidai na gaya miki,tace ok am sorry peach,murmushi yayi yace tosekin fad'a da muryana,tace ni mace kai miji ai muryanmu dabanbanci bazan iya ba,yace to bazata zoba,tace pls mana captain,yace wlh sekinyi muryana, nan dai ta gyara muryanta wai a dole zatayi irin nashi,ai tun bata k'arasaba take dariya shima haka take ta katse wayar tanata dariya shima hakanne muhsin yace ku kamashi muje gun malam mahmud yayi mishi ruk'iyya inaga yad'an samu matsala ne,daroya sosai manosh yakeyi harya shiga gida,mum da miher se binshi da kallo sukeyi,miher tace the prince lfya kuwa,yace wlh maryam ce take haukatani uama manta mum nashi tana palon,ai take ya seta kanshi yace mum dama kina nan ne,yad'an sosa k'eya,tace nidai inaso akawomin maryam d'innan inga mai sunana kuma sirikata,miher tace dama yau nake so inje in bro ya yadda zuwa jibi kuma se inje mu taho tare.
Manosh yace a'a ki bari dai jibin se driver ya kaiki ku taho tare,miher bata so hakanba amma tasan manosh magana d'aya yakeyi dan haka ta sanar da maryam cewa baza samu zuwaba se jibi,maryam bataji dad'iba dan batayi zaton manosh zaik'iba.
Da yamma su manosh sukaje gaisuwa gun surukansu tun daga gun mahaifin ameena suka fara har na zahida sannan suka wuce gire mota 3 masu zafi.
Kyakkyawan k'arb'a aka musu dama ansan da zuwansu. Koda sukaje gidansu rashida da samira sannan suka wuce batare dasunyi hira da 'yan matanba.
Bayan sun komane ya kira maryam se fushi takeyi waidan ya hana miher zuwa. Babu irin rarrashin dabai mataba amma tak'i tanata fushi. Yace am sorry apple zan kawota jibi da kaina kinji,tace banso indai kai zaka kawota bazaniko inaba,yace to shikenan bazan zoba zan kiraki anjuma pls zan d'auki wani kiran kinji,tabace komaiba ta katse wayan shi kuwa ya d'auki wayan oganshi.
Kamar yadda manosh yace yau miher ta shirya driver ya kaita gun maryam,mirna sosai maryam tayi bayan sun gaisa da mamane se suka wuce d'akinta,ita kanta miher d'akin ya burgeta dukda dai ita 'yar masu akwai ne. Hira sukayi kad'an maryam ta cikawa miher ciki da abin mak'ulashe sannan tace bari in yiwa mama sallama semu tafi dan in dawo da wuri koh,tare suka mik'e sukai mata sallama tace a gaishesu sannan suka tafi.
After dress ce red a jikin maryam tayi kyau sosai taga sun tsaya a wani katafaren gida. Koda aka bud'e gate se taga ashe cikin yafi wajen had'uwa,bayan sun k'arasane taketa ganin flawers kala kala masu kyau sosai. Miher tana rik'e da hannunta se gaisheta gards din sukeyi har suka k'arasa palo, me zata gani...hoton miher da manosh ne da kuma iyayensu,jikinta yayi sanyi tanata fad'in *innalillahi wa'inna ilaihirraji'un* tabbas maryam bazata tab'a mance fiskan wannan mutumin da take tunanin shine mahaifin manosh ba,acikin ranta kuwa tace wlh bazan tab'a b'oyewaba koda hakan zaisa in rabu da manosh peach d'inaba. Miher tace yanaga kina ta kallon hotonmu da iyayenmu nadai fi bro manosh kyau,murmushin kawai tayi tace nidai bance komaiba,miher ta kaita d'aya palon sannan ta zauna tace ina zuwa bari na kira mum sannan ta wuce wani kofa,ita kuwa tana zaune kanta a sunkuye tana tunani.
.
Mum da miher sun fito a tare kan maryam a sunkuye, tayi saurin durqusawa qasa ta gaishe da mum din manosh cikin fara'a da sakewa sosae mum ta amsa mata gaisuwa tare da tambayanta ya mutanen gidan, sun dae gaisa sosae amma kan maryam a sunkuye yake. Mum tace ki saki jikinki fa , nan kaman gida ne haka dae sukaci gaba da hira mum ta kama hanya ta tafi ta barsu ita da miher. Miher ta kawo mata kayan maqolashe kala kala, maryam bata iya cin komai ba in banda ruwa da tasha. Suka dan yi hira kadan daedae lokacin dad din manosh ya shigo yana kiran miher da sauri tace naam dad, sannan ta fita taje wurin dad dinta, yace ke da wa kuka shigo?? Tace nida wanda bro manosh zae aura ne. Tazo gaida mom ne nan dae tace dad bari tazo ta gaishe ka, tayi sauri ta koma taje ta kira mrym da sauri ta fito kanta a sunkuye ta durqusa har qasa ta gaishe da dad shima ba laifi cikin fara'a ya amsa. Koda suka gaisa ya wuce dakinshi ita kuwa maryam tana kallonsa a nitse ta sake tabbatarwa wannan shine mutumin da nan da bazata taba mantawa dashi ba a rayuwarta.
Jiki sanyaye ta koma falo suka zauna dae, ita kanta miher ta lura da sauyi daga gareta amma bata ce mata komai ba. Maryam ta dan zauna na kusan 30 mins tace to gaskiya zata tafi saboda batason dare yayi miher tace bazaki tafi ynxu ba dole se bro manosh ya dawo dan shine zai maida ke gida maryam tace aa ni bamuyi haka dashi ba dan allah ki tashi ni zan koma gida. Miher taga dae da gaske takeyi dan haka ta kira bro manosh a waya ta sanar dashi bada jimawa ba yazo daedae lokacinda suka fito tayi sallama wa mum zata tafi, mum ta hada mata goma ta arziki ta rako ta har kofar falo sannan ta juya , shi ko dad daman ya riga da ya fice. Ko da ta iso wurin mota tana tsaye shi ko manosh ya danno shi da marwan kallonta yakeyi tun daga sama har qasa saboda kayan ya bala'in mata kyau murmushi kawae takeyi tare da gaishe da marwan bayan sun gaisa ne manosh ya matso kusa da ita yace wato bazaki gaishe ni ba kenan?? Shuru tayi batace mishi komai ba tace nidae ka kaini gida yace ae ba ni na kawo ki ba wanda ta kawo ki saeta maida ke,maryam ta maida kallonta gun marwan tace marwan kaji abinda yace ko,marwan yace rabu dashi muje in maidake,duka manosh ya kaiwa marwan tare da cewa ina ruwanka acikin hidimata,marwan yace da ruwana mana aunt muje in kaiki gida kinji tare da dannan keyn mota ya bud'e mata gaba ta shiga ta zauna sannan manosh ya karb'e keyn a hannun marwan yace zaka zauna a baya kenan,marwan yace eh ba matsala,maryam tayi mirmushi yayinda miher tasa mata goma na arzikin da mum ta had'ota dashi sukai sallama manosh yaja mota suka tafi.
Tunda suka fara tfy manosh da marwan ne suketa hira itakam tayi shuru tana ta tunani a ranta. Manosh ya lura cewa akwai sauyi tattare da ita,yace kira sunanta a hankali apple,juyowa tayi suka had'a ido sannan ta mayar da kanta gefe,shuru yari bai sake cewa komaiba har suka iso girei,marwan yace jirani abokina bari naje gun rash a tsatstsaye yanzu zan dawo.
Bayan marwan ya tafine su kuwa suna zaune a cikin mota manosh yace apple meyake damunki? Murmushi tayi tace bakomai,yace no apple karmu fara haka dake pls ki gayamin dan nasan akwai wani abu,tace gaskya naji dad'in yadda aka karb'eni a gidanku mum naka tana sona sosai nagode sosai tana murmushi tare da kallon kyawawan idanunsa,shima idanun nata yake kallon yayi da yakejin shaid'an yana zugashi da cewa kayi kissing nata manosh,maryam taga kallon da yake mata ya fara wuce gona da iri dan haka tayi saurin kawar da kanta tare da cewa zan shiga gida. Manosh ya dawo hayyacinsa yace bakomai apple kin cancanci a k'aunaceki domin kina da halayya na gari masu kyau daban sha'awa,dad'i taji tace ai kaima haka,dan azamanin yanzu da kyar asamu namijin da baya iya tab'a koda hannun budurwansa shiyasa kullum nake k'ara sonka manosh nasan cewa kana min so na gaskyane kuma mai tsafta. Jikinshi yayi sanyi dajin kalaman maryam,yayi hamdala a cikin zuciyarsa yace Allah nagode maka danafi k'arfin shaid'an a wannan lokacin Allah ka k'ara kareni akan sha'awar da nakeyiwa maryam ameen. Ta katseshi da cewa ya naga kayi shuru,yace bakomai kawai bana so ki tafine harse marwan ya dawo,murmushi tayi tace toshikenan kamin hira,yace kedai zaki min,tace ni nawa sun k'are ai,yace to mata biyu nake sofa in aura dake da kuma wata kin amince? Murmushi tayi tace eh na amince mana ai halal ne kana iya yin hud'uma,dariya sosai manosh yakeyi,wanda yake burge maryam dan manosh ya had'u wlh sedai sam bai fiye yin dariyaba wanda ta lura hakanma dan itace yakeyi se kuma dasu marwan ko miher. Manosh ya tsargu da irin kallonsa da maryam takeyi yayi sauri tsayawa da dariyan nashi yace "apple why are looking at me like that?" Kunya sosai taji dan batama san ya akai taketa kallonshi hakaba,kuma aduk lokacin take kallonshi sha'awarta tane kawai yake kamashi. Maryam tace ina son ganinka aduk lokacin da kake dariya dan kanamin kyau sosai manosh,jiyayi kamar ya rungumeta dan yadda yake ji,amma seya daure yayi d'an murmushi tare da d'aukan wayarsa ya kira marwan yace ganinan zuwa mutafi sannan ya katse wayar maryam tana kallonshi,shi kuwa bai sake kallontaba hannayenshi suna kan siterin mota yace apple am goying,mamaki taji amma setace tonagode Allah ya kiyaye hanya yare da bud'e kofar mota ta fita se nanne shima ya fito tare da d'aukan abubuwan da mum ta bata yake mata har zauren gidansu ya ajiye.
Tace nagode tana murmushi,kallonta yayi batare dayayi murmushi yace *minfu miyatti* sannan ya wuce motarshi ya shiga yaja yana mata bye,ita kuwa murmushi kawai take mishi daga k'arshe ta d'aga masa hannu sannan ta wuce gida.
Maman maryam tayi farin ciki sosai dajin yadda aka k'arb'i maryam hannu bibbiyu,ga kuma zannuwa da less masu tsada ga sarka da turare da mum din manosh ta bata.
Maryam ta koma d'aki tana kwance se kuma ta tashi ta bid'e kit nata ta d'auko memori tasa a wayarta ta sake tabbatar da cewa lallai wannan shine mahaifin manosh,hawayene suka fara zuba a idanunta se taji wayanta na k'ara,koda ta duba *peach &cream* ne seta d'auka tare da share hawayenta tace hello,manosh yace apple mun tafi,tace to Allah kare nagode,yace ameen *i luv u* murmushi tayi tare da cewa *she luvs u 2* dad'i yaji yace thankyou apple,tace always *peach* wayyo Allah manosh kamar zaiyi hauka yana mirmushi ya katse wayar yatana lumshe ido,marwan yace bari in karb'eka dan naga kamar ka gaji,dariya sukayi dukkansu sannan manosh ya fizgi motar kamar zasu fire sama,marwan yace a'a mudaije a hankali kaga dukkanmu tuzuraire hhhhhh
Maryam kuwa wasu zazzafan hawayene suke zub'o mata tinda ta ajiye wayar. Tace inason sosai manosh,yanzu ya zanyi kenan? Wayarta ta d'auka ta kira uncle ibrahim bayan sun gaisa tace dam inaso miyi magane in baka cikin mutane,yace ok bari na kiraki.
Bayan ya katsene ya sake kiranta yace yes aunty ina jinki,tace ka tuna da wannan vedion dana tura maka a wayarka,yace ai devio d'aya kika tab'a turamin na wanda ya buge mahaifina ko? Hawaye ya sake zubowa a fiskarta tace eh shi,yace eh har yanzu yana wayana ai,tace bakowa bane wannan mutumin illa mahaifin manosh yah ibrahim. What! Mahaifin manosh kikace,tace eh shine na tabbatar da hakanne yau danaje gaida mahaifiyarshi yah ibrahim bazan iya b'oye makaba dannima mahaifinka mahaifinane sannan mun dad'e muna nemanshi se gashi kuma ashe shine mahaifin manosh,kukane yaci karfin maryam take ta katse wayar. Hankalin ibrahim ya tashi sosai ya rasa meyake mishi dad'i musamman dayaji maryam tana kuka,don ya dad'e dasa son maryam a ranshi tun mahaifinshi yana raye ya sanar dashi,amma se mahaifinshi yace karka damu ibrahim ka gama karatunka tukunnan maryam 'yace aguna nima zafin samun kwarin gwuiwa idan ka gama karatu ka samu aiki se inyiwa mahaifinta magana tunda amininane. Hakan yasa ibrahim ya hakura yabar abin a ranshi amma kash *muna namu Allah yana nashi* hankalin ibrahim atashe ya wuce gidansu maryam.....
.
Uncle ibrahim yana isa yayi sallama,maryam ta fito tare da amsa sallamar,tunda ganin fiskarta ya tabbatar tayi kuka. Kallonta yakeyi mai cike da kauna,yace ina mama,miryarta k'asa ba tare data kalleshiba tace tana d'aki. Ibrahim yace aunty meyasaki kuka,shuru tati ta kasa cewa komai,ya sake cewa aunty pls banaso in sake ganin hawaye a fiskarki wlh na yafewa mahaifin camtain amma saboda kece kawai wlh dabadan keba danayi k'aransa,aunty kin wuce duk yadda kike tunani aguna sannan babanki ya rik'emu kamar uba tun bayan rasuwan mahifinmu dan haka ki wantar da hankalinki kinji wlh komai ya wuce zan samu baba anjuma muyi maganan.
"Maryam ta d'ago da kanta tana kallonshi tace nagode sosai yah ibrahim,basan dame zan biyakaba a duniyannan Allah yabar zumunci. Murmushi yayi mata tare da cewa ameen aunty pls kicire komai a ranki karki nunawa captain wani canji sannan karki sanar dashi kinji,to tace dashi yace to ai seki murmushi dan fishi bai kamacekiba,dariya takeyi wanda yake kara mishi kaunarta a ranshi nan sauyin kallon da yake mata ya canja,wanda ita ita da kanta ta lura da hakan,take jikinta yayi sanyi,shi kuwa juyawa yayi ya tafi batare daya sake cewa komaiba.
Tunani sosai maryam ta shiga akan yanayin yah ibrahim tace kodai sona yakeyi to? Kai a'a da sona yakeyi aida ya dad'e da fad'a kawai dan kila dan kokarinane yasa yake sona haka amma kuma meyasa yakemin wannan kallon da manosh yake min sannan ya tafi babu sallama?
Wayanta ta d'auka ta kirashi bugu d'aua ya kayse ya kirata ta d'auka da sanyin murya tace yah ibrahim katafi babu ko sallama? Yace am sorry aunty bazan iya tsayawa inaci gaba da kallonki bane,tace todai ai semuyi sallama koh kamar dai yadda muka saba. Murmushi yayi yace tokiyi hakuri aunty nayi laifi,murmushin ta mayar mashi tace ba komai ya wuce dama shiyasa na sake kiranka. Yace tona gode aunty ina so in miki wata tambaya pls ki gayamin karkiji kunyana,tace to inaji, "you love camtain right?" Shuru tayi dan bata tab'a tunanin jin wannan tambayan daga garesaba,yace aunty kinyi shuru,tace yah ibrahim yana da wani haline mara kyau kodai kasan wani abu mara kyaune game dashi? Yace "aunty" namiki tambaya kimin tambaya,cikin sanyin murya tace yah ibrahim bazan iya b'oye maka komai a duniyannan ba "yes ina sonshi" amma wlh idan yana da wani aibu kagayamun ko kuma baba,tunda dama ai nace kayi bin ike akanshi. Ibrahim yace hakane aunty wlh bayi da wani aibu ko hali mara kyau kawai dai na tambayekine,tace tomeyasa kamin tambayan? Yace yanzu nayi laifi kenan,yace bakayiba nima ina so ka gayamin me dadilin tambayan? Yace idan muka sake had'uwa zan gayamiki yayinda nake kallon fiskarki kinji,tace toshikenan nagode,yace ok bye sannan ya katse.
Maryam dai da tunanin maganansu ta kwana a rai kuma daahi ta tashi.
Rashida ce taje gun maryam,lokacin tana zaune a gaban *computer* tana sanye da blue jeans da kuma jan top mai dogon hannu ta nad'e kanta da *light brown* gyale k'arami,rashida tace kai amma kinyi kyau a kayannan bari in miki *picture* ai kuwa maryam tayi dariya fararen hakwaranta suka bayyana rash ta dauka tare da cewa gaskya ki turawa captain wannan pic din dan yayi kyau sosai wlh. Murmushi maryam tayi tare da kab'ar wayan rash tana ganin pic din, nan suka koma kan k'aramin gadonta tana shirya books nata rashida se d'aukata takeyi,maryam tace ke ya isama mana.
Dariya rash tayi sannan suka fara hira nanne maryam take gaya mata cewa mahaifin manosh ne ya buge mahaifinta kumata gayawa yah ibrahim,hankalin rashida ya tashi sosai ta mik'e tsaye tace mahaifin manosh fa kikace,maryam tace eh wlh wlh shine kinsan jiya naje gaida mum nashi acan naganshi. Rashida tace wlh bazai yuba,ya rabani da mahaifina shikenan aahe manosh bai sami mahaifi nagari wlh tunda har zai iya yin kissa sannan kuma ya gudu mugu mara imani wlh Allah ya isa mana. Maryam tace dan kiyi hakuri rash kidena fad'a haka,rash tace ai wlh ba mutumin kirki bane tunda haka yake Allah yasa camtain karya d'auko halinsa dan wlh indai halinsu d'aya to ina tausaya miki maryam. Maryam tanata bata hakuri amma ina rash se kuka takeyi harta fara cewa to yanzu kinsan hakan tome kuke ciki da captaim maryam? Maryam tace kamar ya rash? Rash tace har yanzu kina son captain, maryam tace rash wani irin magane haka kuma pls kiyi hakuri ki nitsu pls,rash tace in nutsu,hakan ya nuna har yanzu kina tare da captain kenan maryam mahaifina fa mahaifinkine,kuma har zaki iya ci gaba da soyayya da d'ansa,lallai nagode danke mahaifin na raye shiyasa keto marwan d'inma daga yau bani bashi tunda shi abokin manosh ne koma ince amininsa dan haka kema daga yau *bani bake maryam* tana kaiwa nan ta ta fice tanata kuka sosai.
Mamakine sosai ya kama maryam dajin kalaman rash,dan tunda suka taso ko musu bai tab'a shiga tsakaninsuba kowa ya sansu kuma yasan shak'uwarsu sannan maryam tana son rash sosai fiye da sauran k'awayenta dan haka se abin ya dameta sosai, dama mamanta ta tafi angiwa dan haka ta rufe gida tabi bayan rash.
Kuka sosai rash takeyi itama mamanta bata gida dan yare suka fita da maman rash d'in sunje barkan haihuwa. Maryam tace haba rash yau har zaki iya furta cewa *bake bani* akan manosh,rash nasan ina son manosh amma wlh soyayyar da nake miki yafi wanda nakeyiwa manosh,domin shi zan iya rabuwa dashi amma ke na d'aukeki tamkar k'anwatace da muke ciki d'aya meyasa zakice haka dan Allah? idan rash jajur dan kuka tace wlh karyane maryam dakam nasan kina sona amma banda yanzu dan haka ki fita kibar mana gidanmu ki fita bana bukatan in sake ganinki dake da kowa nakima ki fita anan da k'arfi ta hank'e maryam har waje se jinta tayi ta mannu da mutum ta bayanta. Da sauri ta goge hawayen idonta tare da juyowa se sukayi ido hud'u da yah ibrahim take hawaye yaci gaba da gangarowa a fiskanta ta juya tana kallon rashida da tsoro ya gama kamata dan ganin yah ibrahim datayi.
Wucewa maryam zatayi da kukanta se yah ibrahim yayi saurin rik'o hannunta yace auntyn kiyi hakuri meya had'aku? Karon farko kenan danamiji ya rike hannu maryam bata iya cewa komaiba se kokarin fisgan hannunta takeyi agun yah ibrahim tace dan Allah ka sakeni yah ibrahim zan tafi gida,yace no aunty dan Allah ki tsaya yana rike da hannunta ya juya rai a b'ace yana kallon k'anwarshi rash yace ke meya faru,jiki na rawa ta gaya mishi,ya e shine yau da hannunki harkin iya hankad'e maryam rash? Ina ruwanki azan,yana rik'e da hannun maryam harya isa gun rash *belt* d'in jikinshi ya zaro rash ta fara kuka tare da cewa dan Allah yah ibrahim kayi hakuri wlh bazan sakeba.
Rash ta tsorata sosai dan tasan halinshi sarai, kukda dai bai tab'a dukantaba tunda take. Maryam tayi saurin shiga tsakaninsu tana hawaye tace dan Allah ya ibrahim karka dake pls,tsawa ibrahim ya dakawa maryam wanda dukkansu seda suka tsorata yace aunty ki matsa! Rash ta rike maryam sosai tana bashi hakuri. Maryam tace kayi hakuri yah ibrahim amma sedai ka dakemu dukkanmu tana kuka sosai.
Jikinshi yayi sanyi dan yadda yaga maryam take kuka haka ya sake *belt* din a k'asa rash kuwa da gudu ta fita ta wuce d'akin mamanta ta kulle da key. Maryam ma tazo zata wuce amma seya tareta,kuka takeyi tace yah ibrahim zan tafi gida,yace *aunty am sorry pls akan abinda rash tamiki*,maryam batace komaiba tace pls kaban hanya in wuce,yace sekin share hawayenki,bai jira me zataceba yasa hannunsa yana share mata,tayi saurin kawar da kanta gefe tare da buge hannunsa daga kan fiskanta,amma ina seya sake mayarwa tare da rik'e hannunta yace pls aunty ki dena kuka wlh har cikin raina nake jin kukanki sabo da yadda nake *k'aunarki tunda dad'ewa*. Da sauri maryam ta d'ago da kanta suna kallon junansu sosai har cikin ido,hakan ya sake rikitar da ibrahim sosai aise ya tsinci kanshi da fara matso da fiskarshi dedai nata da niyan kissing nata. Idanunta ta zaro tare da bigeshi gefe tayi saurin barin d'akin da gudu ta wuce gida,shi kuwa wani ajiyar zuciya ya sauke huuuuuh! tare da nadaman abinda yake son aikatawa...
.
Maryam tana komawa gida ta wuce d'akinta dama mamanta bata dawoba,ta kwanta tana kuka sakamakon tunawa da kalmomin rash agare. Dan bata tab'a zaton cewa wani abu zai shiga tsakaninsuba.
Wayartace ta fara ringing kodata duba se taga manosh ne,haka tak'i d'aunkan call d'n nashi har sau 3.
Bayan azahar ya sake kiranta seta d'auka hello,yace apple ina kiga shiga haka,tace sorry bacci nakeyi dan kaina da yake ciwo,ya kake yasu mama,yace eyyah sorry apple ya jikin naki,tace da sauki sosai,yace zanzo da yamma kinji,tace to nagode sekazo.
Dab la'asar manosh yazo abdallah yana kiran sallah,alwala yayi yayi sallah sannan suka zauna hira da abdallah inda yake tambayarshi ina marwan,makosh yace yana gun aiki,nan dai sukai ta hiransu manosh se dariya yakeyi seda aka watse sannan maryam ta fito babu ko fara'a a fiskanta.
Ta k'arasa da sallama,suka amsa sannan abdallah yace auntyn yara yanaganki haka babu ko murmushi, tace bakomai abdallah banajin dad'ine,yace sannu Allah ya baki lfy,tace ameen sannan ya kalli manosh yace toni zan tafi seka sake zuwa,manosh yace to bari na baka sako,yace to,sannan manosh ya bud'e motarshi ya fito da leda da gani kayayyaki ne a ciki yan kanti ya mik'awa abdallah. Abdallah ya karb'a yace wazan kaiwa?manosh yace nakane na baka kyauta,godiya sosai abdallah yayi yace auntyn yara ki tayani godiya,mirmushi tayi tace mungode Allah ya saka da alkhairi suka amsa da ameen sannan abdallah ya tafi.
Maryam tace ko zamu shiga cikin gidane,yace yau kuma,tace eh ko kuma muje zaure in shinfid'a maka taburma wlh bana jin dad'ine,manosh yace amma kinje hospital ne,tace banjeba dan ko su mama basu saniba,yace tomeyasa,tace babu komai,kallonta yakeyi tun daga sama har k'asa sannan ya d'auki wayarsa ya kira muh'd ya gaya masa cewa inda hali yazo girei ya duba apple nashi sannan ya katse wayar tare da cewa to muje zauren karki fad'i min anan,murmushi tayi sannan ta wuce gaba shi kuwa ya fito da sayayyan fruits daya mata da sauran abubuwan kwad'ayi yabi bayanta lokacin taje d'auko taburma da karamin carpet ta shinfid'a mishi carpet din ita kuwa ta zauna a taburman.
Sam tak'i kallon manosh dukda dai tana son ganinsa dan yau red top ne a jikinsa da black jeans se kamshi yakeyi. Shi kuwa kallonta yakeyi sosai,can dai tace meyasa ka kira muh'd ai naaha magani,shuru yayi kamar baijitaba yana ci gaba da kallonta,da taga yayi shuru seta d'ago da kai tana kallonshi suna kallon juna,murmushi tayi tace nika dena min irin wannan kallon bana so,yace tobase ki hananiba,mik'ewa tayi taje ta yanko mishi kankanan daya kawo mata dasu apple ga greves dadai sauransu tayi jerensu a tirai kamar fiskan manosh sannan taje ta ajiye mishi ta yadda zai gane fiskanshi tayi drawing. Mamaki sosai yayi yanata kallon drawing d'in danya burgeshi sosai harya bashi sha'awan ci,amma kuma bayaso ya b'ata drawing d'in,kawai setaga ya d'ako wayanshi yanata d'aukan pic din friut d'in.
Bayan ya gamane yace fiskan waye kenan wannan,tace na wanda zaisha,dariya yayi wanda ya k'ara mata sonshi azuciyarta,yace haka fiskana yake kenan? Tace eh amma dai fiskanka yafi wannan kyawun gani. Dad'i sosai yaji amma baice mata komaiba,wayansane ya fara ringing ya d'auka ok bari na fito. Kallonta yayi yace bari muh'd ya shigo kuma ki tabbata kin gayamishi abinda yake damunki kinji ko, mamaki sosai tayi har mh'd yazo kenan,tace to sanna ya fita suka shigo tare.
Muh'd yayi sallama ta amsa sannan suka zauna tace ina wuni,yace lfy lau aunty ya jiki ashe bakiji dad'i ba,tace eh amma da sauki,manosh yace ba wani sauki wlh dairewa kawai takeyi danko a gida basu saniba. Muh'd yace haba aunty pls kidena wasa da rashin lfyanki karki sawa kanki ciwo kinji,mirmushi tayi tace kainane fa dama kuma nasha paracetamol,manosh yace towayace kisha? Murmushi tayi tare da kallonshi cikin zolaya sannan ta taahi ta wuce gida. Manosh yanata binta da kallo,muh'd yace haba prince irin wannan kallo haka,manosh yace wlh bata da lfy daga ganinta daurewa kawai takeyi pls ka gwadata sosai. Muh'd yace "calm down dude" zata samu lfy insha Allah. Faro mai sanyi ta kawo musu sannan ta zauna,muh'd yace mungode amma wannan fiskan yamin kyau kamar fiskana. Dariya sukayi dukkansu,manosh yace a'a kaje can samira ta maka naka wannan fiskan nawane kuma bazaka ciba,dariya mh'd yayi tare da d'aukan inibi d'aya yasa a bakinsa yace shikenan zanen ya b'aci. Manosh yace gaskya baka kyautaba,memakon ka jira in fara sha kafin kasha,mikewa maryam tayi ta sake d'auko inibi tazo ta mayar inda mh'd ya cire sannan tace shikenan magana ya k'are.
Dariya sukayi sannan manosh ya far sha cikin nutsuwa take satar kallonshi,dan bai tab'a cin wani abu suna tareba se yau.
Muh'd yace nagode aunty gaskya abin ya burgeni nima zance samira ta dinga min. Manosh yace copy copy,murmushi sukayi sanna muh'd yace aunty meke damunki ne? Tace wlh ciwon kaine kawai,k'irjinta yana mata ciwo amma sam tana jin kunyan cewa harda k'irjinta. Muh'd yayita tambayoyinta tana bashi amsa sannan yace ok ina zuwa bari inje inzo,manosh yace akwai wani damuwane,yace no bakomai sena dawo sannan ya tafi.
"Manosh yace kin tabbata abinda kike ji kenan?"
"Tace eh kanta na kallon wani gefen"
"Manosh yace apple bana so ki b'oyemin komai imma kina jin kunyan muh'd toki gayamin tunda baya nan"
Maryam taga bazata iya b'oyewaba dan yadda take jin k'irjinta,setace da k'irjina yana min ciwo sosai.
"Kallonta yakeyi cikin damuwa,dan yana lura da yanayinta yasan tana jin ciwo tadai k'i fad'ane kawai.
"Sunanta ya kira a hankali yace apple?
Kanta ta d'ago ta kalleshi har idonta yayi jah tace na'am tare da sunkuyar da kanta,yace se kuma inane yake miki ciwon? Tace shikenan....bata gama k'arasawaba taji cikinta ya kame kamar an soka mata wani abu,innalillahi wa'inna ilaihirraji'un taketa nanatawa a zuciyarta.
Manosh yace ya kikayi shuru,tace bakomai ina zuwa,bata jira mezaiceba ta mik'e ta wuce gida yana binta da kallo. Koda ta k'arasa gun mamanta ta wuce a d'aki ta cire doguwar himar nata ta fad'a kan gado tana cewa mama cikina ya kameni sosai yana min ciwo. Hankalin maman ya taahi sosai tayi kanta tana mata sannu tare da tofa mata addu'oi,tace bak'on ya tafine? Cikin jin ciwo take magana tare da kame cikinta tace basu tafiba suna zaure.
Mama ta rasa yadda zatayi seta d'auki wayanta ta kira baban maryam ta gaya mishi komai,shima hankalinsa a tashe ya kira number yah ibrahim yace lallai yaje gida.
Bada b'ata lokaciba yah ibrahim yazo a zaure sukaci karo da manosh. Su gaisa sannan yace ina maryam d'in? Manosh dabaisan komaiba yace ta shiga ciki,yah ibrahim yace kasan bata da lfy,yace eh na sani harma abokina ya dubata yanzu. Kan yah ibrahim ya d'aure seyace bari in shiga ciki dai dan yanzu babanta ya kirani yake cemin bata da lfy sosai cikinta na ciwo,a razane manosh ya mik'e yace ciki kuma,tacewa yanzu kenan ko,ibrahim yace eh sannan ya wuce ciki akabar manosh cikin damuwa sosai.
Maryam se juyi takeyi tana addu'oi,har ya ibrahim yayi sallama,mama ta fito tace bari na fito da ita sannan ta koma tasawa maryam himar,shi kuwa yah ibrahim da sauri ya kira rash a waya yace tazo yanzunnan kuma cikin shiri.
Bada b'ata lokaciba sega muhammad yazo sakamakon wayan da manosh yayi mishi. A tare sukazo da rash ta gaishesu sannan ta wuce ciki,maryam ta fara hangowa babu yadda take mama tana rik'e da ita ita maeyam bata iya ko mik'ewa tana sunkuye kuma rik'e da cikinta.
Da sauri rash ta k'arasa ta riketa sosai tana mata sannu. Hankali mama a tashe tace gaskya zan biku muje asibitin nan dan hankalina zaifi kwanciya,waya tama baban maryam,sannan ibrahim yaje ya sanar dasu manosh komai,se manosh yaba ibrahim keyn motanshi yace ya d'auki su mama a ciki shi kuma zasu tafi da muh'd. Haka kuwa akayi su manosh suka tafi shida muh'd sannan ibrahim ya bud'e musu motar, da sauri abdallah yazo dan yadda yaga mama da rashida suna rik'e da auntyn yara,baice komaiba ya karasa yace lfy mama,tace wlh maryam ce ba lfy zamuje asibiti. Subhanallah nima zan biku, ibrahim yace shiga baga to,abdallah ya shige gaba su mama kuwa suna baya suka kama hanyan jimeta.
Asibitin da muh'd yake aiki sukaje, aka wuce da ita kai tsaye. Ae a lokacinne manosh da muh'd suka gaida mama sannan muh'd ya wuce duba maryam.
"Yana shiga rashida ta fito ta wuce gunsu mama,shi kuwa manosh kunya sosai ya kamashi gaahi k'ananan kayane a jikinshi,nan ya kira su majid cikin k'ank'anin lokaci suka zo dukkansu ukun.
Marwan majid da muhsin sukaje suka gaida mama sannan suka gaisa da ibrahim. Rashida tana gefe ita da abdallah sannan marwan ya k'araso suka gaisa ranta a b'ace,amma seya d'auka kodan rashin lfyan maryam ne.
Muh'd ya fito su manosh suka k'arasa da sauri donjin meke damunta harda yah ibrahim d'in da abdallah. Mama da rash kuwa suna tsaye a gefe guda.
Muh'd yace *ulcer* kawai babu wani abu, kuma dole zata zauna a asibiti dan se'an k'ara mata ruwa har leda biyar. Sannan yayi mata allura yanzu dan har tayi bacci ma, ibrahim yace to mun gode kayi duk wani abunda ya dace pls yanzu medame ake buk'ata? Muh'd yace haba aiba komai wlh already nasa mata ruwan karka damu babu wani abu da ake buk'ata kudai tayamu da addu'a kawai. Godiya sosai ibrahim yayi sannan yace bari naje na sanar da mama dan hankalinta a tashe yake,muh'd yace muje inyi mata bayani.
Bayani sosai muh'd yayiwa mama tare da cewa ta kwantar da hankalinta maryam zata samu lfy insha Allah. Godiya mama tayitayi sannan ya tafi gunsu manosh.
Manosh yace zan iya ganinta,majid yace jeka ka kanga inba hakaba ai bazamu gane hankalinkaba ad'an lokaci kad'an kashi harka fita hayyacinka kamar ba sojaba, dariya sukayi baima kulasuba ya wuce d'akin tana kwance babu himar a jikinta se atamfa d'inkin doguwar riga daga sama ya bada shape amma k'asan a bud'e yake. Karon farko kenan da manosh yaga maryam babu himar ajikinta,mara ce sosai gata 'yar karama bata da jiki sam,amma k'irjinta a cike suke. Bai k'arasaba ya janyo k'ofar ya koma gunsu majid yace muje ko,dan muma mamanta damar shiga, haka sukayi musu sallama suka wuce yacewa ibrahim ya rik'e key din motarsa dan zirga zirga,amma sam ibrahim yak'i seda ya bashi key din,shi kuwa manosh ya karb'a suka tafi.
Auna tfya mama da rash suka wuce d'akin da maryam take harda ibrahim da abdallah.
Tausayin maryam ya kama rsah sosai tayi dana sanin gaya mata kallomin jiyan dukda dai tasan bashine silan rashin lfyanba amma tana k'aunar maryam a ranta sosai.
Manosh kuwa ya gayawa mum nashi da kuma miher,sannan yacewa dad nashi yana so ya bashi kyautar mota guda d'aya dan zaibawa su maryam ne dan abinda ya faru yau,da baijeba kenan se sunyita neman motan hawa. Dad d'in manosh business man ne sosai kuma yanda gidan saida motocin,sannan yana k'aunar manosh sosai,dan haka yace manosh yaje ya d'auki duk motar da yake buk'ata. Godiya sosai manosh yayi dama suna hira da abdallah sosai kuma abdallah ya gaya mishi motar da maryam take so saosai a ranta shine *307 red* dan haka ya wuce yaje ya d'auko mata red d'in kuwa guda d'ayan kenan ya rage aka rubuta sunan maryam akan takardun da komai sannan yazo dashi gida ya nunawa mum da miher sukaita murna tare da addu'oi yace bari ya watsa ruwa sesu tafi shida miher...

 ANTIN YARA Page 31-40
.
miher tayi shiga na alfarma,daidai nan lubna ta kirata a waya tana tambayanta ya maganan zuwa tambayane nasu bro manosh,nan miher take gaya mata cewa ai maryam bata da lfy tana hospital d'in su bro muh'd yanzu hakama ina jiran prince ya fitone mu tafi.
Lubna tace eyyah Allah ya bata lfy,a ranta kuwa tace Allah yasama ta mutu.
Koda wasa lubna bata gayawa miher cewa tasan maryam ba,kuma bata yiwa miher tambayoyi akan maryam d'in sam,dan gudun zargi.
Manosh ya fito cikin shigar indians da blue sari na maza yayi kyau sosai,ya mik'awa mihaer key d'in *benz* nashi yace taje zai bita a baya. Mirna sosai tayi yau bro manosh yabarta tayi driving da kanta. Tana gaba yana binta a baya da *307*din apple nashi.
*Atiku abubakar mall* suka nufa inda manosh ya kashe kud'i sosai harta flaks seda suka saya mata da cups su plate dukdai wani abu da zasu buk'ata a hospital haka mihar tayi ta d'auka, se kallonsu akeyi don yadda sukayi kyau shi kuwa captain ko dariya bayayi se amsa waya da yakeyi. Mihar tana biye dashi bayan sun biya kud'ine suka tafi tana gaba yana binta a baya har,suka isa hospital d'in.
Lokacin yah ibrahim da abdallah sun koma girei domin suyiwa maman rashida bayani kuma tayi abinci dasu. Manosh yacewa miher ta shiga idan maman maryam bata d'akin tozai shigo,ai kuwa seta shiga da sallama da kuma kayayyaki sosai a hannunta har rashida ta tayata da wasu,sannan ta sake komawa ta kwaso sauran nanma seda rash ta tayata sannan suka gaisa maryam tana bacci har yanzu,mihar tace yamai jiki,rash tace da sauki wlh,tace Allah ya sauwaka mama fa? Tace mama sun fita da baba amma inaga sun kusa dawowa.
Da sauri mihar ta fita taje ta sanar da bro manosh,kafin su shigo maryam ta farka tana cewa mama zansha ruwa,dama yah ibrahim yad'an sayo abin tab'awa kad'an dan haka rash ta mik'a mata ruwan tasha sosai sannan ta koma ta kwanta rash tana mata sannu da jiki,tace yawwa.
Manosh da mihar suka shigo da sallama,kunya sosai maryam taji tace rash mik'amin himar d'ina,da sauri tad'an rataye matashi a k'irjinta sannan suka k'araso.
Rash suka gaisa da manosh yace ya mai jikin,tace da sauki yace to Allah ya bata lfy tace ameen sannan rash tace mihar mud'an basu guri ko,tare suka tashi suka fita sannan yazo ya zauna akan kujeran da yake kusa da gadonta yana kallonta. Kunya sosai taji ta dai daure ta tashi ta zauna tare da gyara rufe jikinta tace ina wuni,kallonta kakeyi tare dajin k'aunarta yana ratsashi yace lfy apple ya jiki,tace da sauk'i.
Yace wato dama kina jin jiki shine kika cemin kaine yake miki ciwo ko,mirmushi tayi tace amma ai da sauki yanzu. Yace drip d'in harya k'are ne? Tace eh yace se bayan isha za'a samin wani,yace ok Allah ya baki lfy apple,tace ameen tare dajin kunyanshi sosai danba himar a jikinta dukda dai ta rufe jikinta amma yana iya hango kananan kitson dake kanta gata da bak'in gashi.
Ya maida kallonsa kan wayanshi yace ina wayanki,nan ta mik'a mishi ya karb'a ba tare daya kalletaba ya shiga galary, pic d'in da rashida tayi mata da kayan daya saya matane ya gani pic d'in sun mishi kyau sosai atake ya turasu zuwa wayanshi sannan yasa mata credit na 3k seya mik'a mata yace kimin kyau a hotonnan ya nuna mata wayanshi.
Murmushi tayi tace nagode meyasa ka tura baka sanar daniba,yace tokiyi hakuri bazan sakeba. Batace komaiba se kuma tace nagodefa da d'awainiya Allah ya saka da alkhairi,shuru yayi kamar baiji metaceba yana ta dannan wayanshi.
Ita kuwa se kallonshi takeyi dan yadda yayi kyau sosai. Batate daya kalletaba yace apple nifa bana so ayita kallona,kinya sosai taji dan tasan bai kalletaba,tace nifa ban kallekaba,yace kin kalleni mana aina ganki,tace ta ina kenan yace ta idona mana, dariya tayi tana ci gaba da kallonshi se wayanshi yayi k'ara ya d'auka yadai miher,tace bro mum da dad nata sun dawo dayake sunsan kana ciki se basu shigoba,yace ok tnx sannan ya katse wayar tate da mik'ewa tsaye yana kallonta. Itama shi take kallo tace ina zakaje,yace zan tafi in barki ki huta mana,kawai jin bakinta tayi tace mishi pls karka tafi yanzu,yace meyasa bakya so in tafi,tace haka kawai,ka zauna kamin hira.
Ba musu ya koma ya zauna yaci gaba da danna wayanshi yana magana batare daya kalleta yace su mama sun dawone kuma suna waje shiyasa nake so in tafi dama ina son inga baba. Tace to ai bakomai suma bazasu shigoba inhar sunsan kana ciki,yace eh hakanne yasa zan tafi ai. Yanayin manosh yana burgeta sosai da wasu irin abubuwansa,sam seyaso kallonta kafin ya kalletan,sannan kamar bakoda yaushe yake son magana ba. Shuru tayi tanata kallonshi sosai tana yaba kyansa a ranta,seyace tunanin me kikeyi apple,shuru tayi,yace pls ki dinga cin abinci sosai sannan ki dena cin yaji dan abdallah yacemin kina cin yaji sosai. Mamaki tayi sosai,tace yaushe kukayi hira dashi haka,yace ina ruwanki,tayi murmushi tace to zan dena insha Allah tunda yana nemar yimin illa. Manosh ya mik'e yace apple am goying amma zanyi missing naki wlh yau bazamuyi hiraba kenan tunda mama tananan bazan iya kiran wayankiba amma zan dawo safe kinji, tace to nagode sosai. Yace Allah ya baki lfy tace ameen sannan ya nufi kofar fita,harzai bud'e kofa tace eeem....tsayawa yayi cak tare da juyowa yace yes akwai wani abu ne,mirmushi ta mishi tace bakomai seda safe,shima murmushin ya mata tare da cewa idan akwai ki gayamin,tace akwai abinda nake so amma zanyi maka texsn,yace ok ina jira sannan ya fita.
Manosh ya gaida mama cikin girmamawa sannan ya gaida da baba tare da cewa dama yana son magana dashi,daidai nan yah ibrahim yazo da abinci sosai a kwando suka gaisa sannan ya wuce.
Miher da rash suka shiga da mama sega yah ibrahim,miher ta gaishesa sannan ya ajiye abincin tare da cewa aunty ya jikin dai,tace da sauki sosai,yace to Allah ya baki lfy tace ameen sannan ya fita gunsu baba inda suke magana da manosh. Godiya sosai baba ya dingayi tare da cewa ibrahim kagafa mota ya kawowa maryam wannan kyauta yayi girma dewa wlh dukda dai kace mahaifinkane yayi mana mun gode sosai,nanma ibrahim yayi godiya sosai,sannan yaje ya kira mama itama baba ya gaya mata godiya,sosai sukayi wanda baizai misaltuba,manosh yaji dad'i sosai a ranshi sannan ibrahim ya rakashi hargun motarshi sukayi sallama,sannan ya kira miher a waya,nan ta musu sallama tace zasu da mum nata da safe,rash ce ta rakata har wajen mota sannan suka tafi.
Koda baba ya gayawa maryam kyautar da manosh yayi mata da taimakon babanshi mamaki sosai tayi,babanta ya nuna mata takardun motan dukda sunanta a jiki,dan kunya bata iya cewa komaiba anata tayata murna sannan baba yace zasu tafi shida ibrahim seya tuk'a motar maryam d'in shi kuwa baba yahau nashi suka tafi ibrahim yanata mamaki.
Manosh yayiwa maryam texs kamar haka
_am still waiting my apple_
_akan abunda kike so_
Koda maryam ta karanta setaji a yanzu kam bazata iya cewa komai se tace
_Allah ya saka da alkhairi_
_wannan kyauta yayi girma dewa my peach banajin zan iya sake tambayar wani abu_
Bayan manosh ya karantane seya ce
_pls apple kigayamin indai kina so inyi farin ciki dan ina k'aunarki sosai apple nd i can do anything just for you sweetheart_
dad'i sosai maryam taji sannan ta sake tura mishi
_ba wani abu bane illa flower_ _i love you nd i love flowers so verry much peach_
Koda ya gama karantawa murmushi yayi yace indai wannan ne sekin gaji dashi dan lambunsa guda zanyi a gidanmu my apple,da haka yayi bacci.
Washe gari da safe ya shirya seda ya tambayi maryam tace su baba sunzo sun koma,ita da mama da rash ne,yace ok ganinan zuwa tace to sekazo.
Koda manosh yazo cikin kakin sojojinshi yake se kallonshi yakeyi,office muh'd ya wuce yace yadai abokina ya wifey nane da jiki,muh'd uace tofa tu ba'a baka ba,kar dai harka shirya kenan se tafya,manosh yace wlh kuwa driver yana waje daga nan airport zamu wuce,muh'd yace ok jeka ka fito se in rakaka,manosh ya wuce d'akin da sallama dama mama ta fita tunda maryam tace manosh yazo taje can d'aya d'akin gun wasu matan da y'arsu ba lfy suma.
Manosh ya shigo kenan rash ta mik'e tare da gaisheshi sannan ta fita,ita kuwa maryam flowers d'in kawai take bi da kallo da kuma yadda yayi kyau a kakin sojojin. Akan kujeran ya zauna suka gaisa seya ajiye mata flowern a gefenta,da sauri ta d'auka tana murmushi tare da shinshinawa taji wani k'amshi mai dad'i wanda yasa ta limshe idanunta tace _thankyou so much captain_,murmishi yayi yana kallonta yadda take ta murna da ganin flowers d'in,itama shi take kallo yare da d'auko *ring*mai kyau na maza ta mik'a mishi batare datace komaiba. Hannun yasa ya karb'a tare da cewa thankyou apple naji dad'i sosai,yasa a yatsan hannunshi tare da pecking d'in yatsan nashi yana mata murmushi tare da cewa ya jikin,tace naji sauk'i sosai wlh,manosh yace alhamdulillah zuwa gobe za'a sallameku insha Allah nizanyi tfy kuma zankai 1week kafin in dawo su dad zasuje gun baba dan asa mana rana kinji?
Sam maryam bataso tfyan manosh ba haka kurun tad'an canja fiska,shi kanshi ya lura da hakan seya sauya muryanshi yace "apple r u aokey?" Tace yes am fine ina zakaje? Yace zanje kaduna ne,karki damu kinji zan dawo insha Allah addu'arki nake buk'ata apple,kallonshi takeyi tare da tausayin kanta tace Allah ya kare min kai,yace ameen suna kallon junansu ciki so sannan tayi saurin kawar da kanta gefe tana kallon flower daya kawo mata,manosh bazai iya jurewaba dan haka ya mik'e tare da cewa nizan tafi apple ga wannan,ya ajiye mata kud'i a gefen gadonta sannan ya nufi kofar fita. Har yakai gun k'ofan kanta na kallon flowern,seya juyo yana kallonta sam taqi kallonsa har ya gama kallonta sannan yaja k'ofa ya fita harzai kulle kenan seta d'aga kanta suka had'a ido cikin tausayin junansu yace _i love you so much apple_
_tace i love you too manosh_
Harda d'an kwalla a idonta sannan yaja kofar da sauri ya rufe,ita kuwa hawayene suka zubo mata kona menen oho....
.
Hankalin maman maryam ya kasa kwanciya,seta kira baban maryam a waya tana tambayanshi ko maryam ta iso? Baba yace a'a bata isoba,hankalinta ya sake tashi tace malam yaci ace ta iso ai,shi kanshi hankalinsa ba'a kwance yakeba,amma seyayita kwantar mata da hankali da daddad'an kalamai yana cewa kinsan fa maryam da taimako da kuma tausayi,zaiyu wani abinne ya tsaida ita a hanya amma bari nabi sawunta.
Mahaifin maryam ya rufe shop nashi yabi hanya ai ko seyaga almajirai sunata d'iban abinci a k'asa kuma ya tabbatar da cewa wannan kulan abincinshine. Wayansa ya d'auka ya kira matarshi ya tambayeta cewa me kika dafa minne yau,tace shinkafa da miyace mai had'e da wake,katse wayan yayi ya kama fad'in *innalillahi wa'inna ilaihirraji'un* tare da duduba guraren kozai hango maryam amma sam se *rivom* nata daya hango wanda shida kanshi ya sayo matashi.
Hankalinshi ya tashi sosai,ya kira number'n maryam yanata ringing amma ba'a d'aukaba har kusan sau biyar. Haka ya wuce gida a rud'e inda ya had'u da yah ibrahim da abokanshi suka gaisheshi ya amsa amma suna ganinshi sunan akwai abinda ke faruwa,ibrahim yace baba lfy kuwa,yace lfy lau ka biyoni gida.
Haka suka juya abokanshi suna tsaye daga waje su kuwa suka wuce gida. Mama tana jin sallama ta fito tare da cewa malam lfy,nan ibrahim ya gaisheta sannan baba ya gaya musu duk abinda ya gani a hanya sannan yayita kiran number'n maryam shuru. Addu'a suketayi dukkansu tare da tunanin to ina maryam take?
Ibrahim ya kira rashida da sameera a waya suka ce mishi sam maryam bata zoba,ya sake kiran zahida da amina suma sukace bata zoba,nan ya wuce gidan hajiya iya nanma batanan,koda hajiya iya taji lbrn hankalinta a tashe harda kukanta dan yadda take son maryam a ranta.
Nan tayi lullub'i ta wuce gidansu maryam inda mahaifiyarta taketa addu'a tare da kwalla a idonta. Duk wanda yaji yasan ba lfy bane domin maryam bata tab'a yin hakaba,ga kuma rivom da mahaifinta ya gani agun yasan lallai akwai matsala sosai.
Bayan anyi sallan azahar ne mahaifin maryam yayi bayani a masallahi akan a tayasu da addu'a. Duk wanda yaji seyayi addu'a dan base na gaya muku daliliba.
Cikin k'ank'anin lokaci magana ya baza ko ina a garin girei. Ibrahim ya kira manosh a waya amma yanata ringing bai d'agaba,hakan yasa ya kira number'n marwan bugu d'aya ya d'auka bayan sun gaisane yake ce mishi manosh fa,domin yayita kiranshi amma bai d'aukaba,marwan yace wlh ni ina office ne maybe baya kusane. Ibrahim yace ok dama wlh maryam ce aketa nema tun d'azu taje kaiwa mahaifinta abinci har yanzu shuru babu ita babu lbr,ahanya akaga kulan abincin a zubar a k'asa sannan an tsinci rivom d'inta har haryanzu babu wani lbr.
*innalillahi wa'inna ilaihirraji'un* marwan yaketa nanatawa tare da mik'ewa yayi gun manajer'nsu bayan sunyi magana marwan ya d'auki motarsa se gida.
Miher ya gani a tsakar gida zata fita,nan dai suka gaisa yace ina prince,tace yana bacci bayajin dad'i kanshi yana ciwo. Marwan yace ok sannan ya wuce d'akin miher tanata binshi da kallo dayya taganshi tasan ba lfy,haka kawai taji ta fasa tfyan dan tana so taji menene da sauri tabi bayan marwan ta lab'e daga bakin kofa inda taji marwan yana cewa "dude" "dude" ahankali manosh ya bud'e ido yana mamakin ganin marwan a wannan lokacin. Marwan yace sorry na tashe ya jikin,yace alhamdulillah lfy? Marwan yace ka kashe wayar kane,manosh yace no a silent nasa dan ind'anyi bacci wlh ya akayi,marwan yace "dude" akwai matsala baga'a apple ba tun 11:40am yanzu gashi har 3:20pm,kuma duk inda ake tunanin tana zuwa anje bata nan sannan........da sauri manosh ya mik'e tare da d'aukan wayanshi yaga miss call din baban maryam dana ibrahim dadai wasu daban,number'n apple ya kira yanata ringing amma sam bata d'agawa. Kamar zaiyi kuka ya sake kiran wayan yanata cewa "pls apple pick d call okey" where are you apple,wurgi yayi da wayan seda screen d'inshi ya pashe ya shige toilet da wuri,shi kuwa marwan ya d'auko wayan amma ina ba'a ganin komai taci screen.
Manosh ya fito ya shirya suka fita ko mum nashi bai sallamaba,daya ga miher yace miher maryam ta kiraki?miher da jikinta yayi,sanyi tace a'a,yace kiyita kiran numbern ta sannan ki gayawa mum cewa ba'aga maryamba nina fita.
Hawaye miher ta fara dan yadda taga bro nata ya hargitse a lokaci d'aya.
Basu wuce ko inaba se girei,inda suka isa har parlon mahaifinta yana zaune da mutanen unguwa,sukayi sallama tare da gaisuwa sannan manosh ya farayiwa baba tambayoyi kamar ba surukinsaba,shi kanshi baba yasan manosh a rikice yake,manosh yana gama jin komai ya musu sallama suka wuce gurin yayita dube dube amma baiga komaima. Abokinsa *faruq* ya kira wanda yake aiki a *mtn office* yace faruq matar da zaura an d'auketa wayanta a kunne yake inaso kabin min line nata pls insan a ina take da sauri dan Allah. Da sauri faruq ya fara neman line na maryam amma baiga komaiba da tana inda babu netwrk,nan ya sake duba kira na k'arshe daya shiga wayarta ba'a d'aukaba yaga lokacin tana *gurore* sannan yanzu baya iya ganin inda suke. Faruq ya kira manosh yace captain d'azu kaine ka kirata last kuma ya shiga lokacin tana gurore. "Whats! Gurore fa kace faruq? Faruq yace tabbas captain karka damu zanci gaba dabin line d'in inga suna inda ba netwrk ne.
Katse wayan manosh yayi yace ina tausaya musu wlh tunban kamasu kowaye yayi miki wannan aikin "he will pay for it wlh" dan bazan barshiba. Marwan yace muje gida mu shirya manosh,manosh yace no karka damu ka koma kawai yanzu motarmu zaizo zamu bi bayansu,marwan yace ok "dude but pls becarefull,daidai nan motan sojojin ya iso wani ya fito daga gaba manosh ya shiga sannan shi ya shiga baya suka tafi,sega majid yazo suka wuce girei gun iyayen maryam,koda marwan ya gaya musu inda maryam take mamaki sosai sukayi,mahaifiyarta kuwa kuka sosai takeyi,makota sunata bata hakuri.
Abdallah yana zaune a masallaci tare da samari da sauran yara anata karatun qur'an amma abdallah hawayene kawai yakebin fiskanshi.
K'awayentama duk sunzo sunata kuka
Manosh ya kira muhsin yace pls zan tura maka pic na apple kai gidan TV da radio dake adamawa dukka duk wanda yaba da wani bayani akwai babban kyauta ageshi,mihsin yace ok "dude" pls ka kwantar da hankalinka insha Allah za'a sameta cikin k'oshin lfy,manosh yace Allah ya amshi addu'anmu tnx "dude" sannan ya katse wayan.
Maryam ta fara bud'e idanunta tare dayin addu'a harta gama bud'esu dukka tana k'arewa d'akin da take kallo. Katiface kawai a d'akin da wani zanin gado se tsami yakeyi ga akwati da tarin taba wiwi dasu totolin sune kawai a wannan d'akin. Nan danan taji gabanta ya fad'i tanata addu'a tare da mik'ewa ta murd'a kofan amma setaji a kulle yake,nan ta tuna da wayanta datasashi cikin pants nata tun lokacin da suka bige mata abincin babanta. Da sauri tasa hannunta akan pants d'in cikin ikon Allah taji har yanzu wayan yana jikinta,hamdala tayiwa Allah sannan ta ciroshi da wuri dama a silent yake,kodata duba missed calls babu adadi a cikin,da sauri ta kashe wayan gabad'aya dan ganin 7:00pm ne ko sallan azahar batayiba. Kofan data gani ta bud'e taga toilet ne amma babu kyan gani sam a cike yake da k'azanta,hancin
ta ta d'aure da d'ankwalinta ta shiga da yake akwai ruwa ga kuma morning fresh da izal nan da nan ta wanke shi tas sannan tayi alwala wayanta yana cikin pants nata ta shinfid'a d'ankwalinta tayita biyan sallolinta.
Tana cikin yin sallanne se taji ana bud'e kofan tare da shigowa. Daga jin muryanshi kasan d'an giyane,yana cewa daga zuwanki har kin fara mana kashi ko kashi kin bud'emu da wari kota ina,koda yake shinkafa da wake kuka dafa a gidanku yau shiyasa,ga abinci nan idan kin gama sallan sekici,bayan ya ajiyene ya d'auki kwalin sigari sannan ya tafi.
Bayan maryam ta idar da sallolintane tare,dayin addu'in neman tsari sannan ta dubi abincin daga gani a resturant aka sayo,amma sam bata ciba seta tashi tasa sakatan d'adkin ta ciki sannan tashiga toilet ta kunna wayanta tare da kiran number'n mahaifinta bai d'aukaba dan yana tlband'aki,dan haka ta sake kiran mahaifiyarta bugu d'aya ta d'auka tare da cewa maryam,maryam tana magana a hankali tace na'am mama sannan,ta fara kuka tana cewa mama ya kuke ku kwantar da hankalinku ina halin lfy amma bansan a ina nakeba...bata k'arasaba taga call d'in manosh,tace mama zan sake kiranki bari inyi magana da manosh,to maryam Allah ya kareki zan sake kiranki bayan kunyi wayan kiyi k'ok'ari kozaki gane inda kike dan azo a taimaka miki su waye suka d'aukeki? Maryam tace wlh mama har yanzu bansan komaiba ina kullene a wani d'aki banga kowaba har yanzu. *innalillahi wa'inna ilaihir raji'un*suketa nanatawa ita da mamanta suna hawaye amma ita maryam daurewa takeyi kar ajita tana waya azo a karb'e.
Banyan maryam sun gama hira da mamane se call d'in manosh ya shigo. Da sauri ta d'auka tare da cewa hello peach,wani sanyi yaji har cikin ranshi yace apple ina fata basu miki komaiba,cikin muryan kuka tace eh bakomai amma ina jin tsoro sosai dan ga dukkan alamu mutanen bana garibane domin kayan shaye shaye ne cike a d'akin kota ina peach,hankalin manosh ya sake tashi sosai yace ki b'oye wayan apple zan kiraki anjuma i love you aunt ki kula da kanki pls zanyi k'ok'arin gano inda kike kinji? Ok Allah ya taimaka peach bansan inda nakeba bare in gaya maka,pls aunt ki dena kuka "i will soon come to you" nasan inda kike already,ina nake pls ka gayamin,calm down apple kina *numan* ne nima yanzu haka muna numan d'in zanzo inda kike yanzu ki b'oye wayanki zan kiraki anjuma okey? Ok thankyou,i luv apple,i luv u too byeee...
.
33-34 da sauri maryam ta share kwallanta dan kar azo a ganta. Manosh kuwa wani iri yaji a ranshi sam baiso ya bartaba amma babu yadda zaiyi,awaje ya samu muh'd sukayi sallama ya sake jaddada mishi cewa ya kula mishi da apple shidasu majid.
Manosh ya isa kd lfy,yana isa maryam ya fara kira,taji dad'i sosai suka d'an tab'a hira sannan sukayi sallama.
Hajiya iya dake zaune a gefen maryam tace surukin nawa kenan shine ba'a tab'a kawo minshiba,dariya maryam tayi tace saurin me kikeyi hajiya ai dole zaizo ya gaisheki dan kece babbar k'awa.
Dariya sukayi dukkansu maman rashida tace to maryam mudai zamu wuce Allah ya baki lfy,tace ameen mama nagode. Hajiya tace ni wannan mota naki semun rabata gaskya,ya zaiyi ya kawo miki bai kawomin,rash da maman maryam sunata dariya,maryam tace karki damu wai yasan ke baki da k'afane bazaki iya tuk'iba kinga ni se inyi ta kaiki duk inda zakije ko? Nanma dai dariyan akayi daidai lokacin samira zahida da ameena suka shigo da sallama.
Bayan an gaisane su maman rash suka fita inda yah ibrahim ya mayar dasu a motar maryam.
Maryam da k'awayenta se hira sukeyi tare da tayata murnan samun mota. Sosai maryam take samun jama'a harda malaman islamiyyansu se zuwa gaisheta akeyi dayake ita mai jama'a ne sosai. Daga masu kawo mata fruits se masu bata kud'i,su kansu doctors da nurses d'in sunata mamaki har tambaya sukeyi wai maryam d'innan 'yar wayece a garinnan dan yadda jama'a suke sintiri agunta. Shi kanshi dr muh'd yaji mamaki sosai,dan haka ya kira manosh yace gaskyaka samu mata wlh ka rik'eta da kyau sannan mu dami su dad akan ayi maganan aurennan da wurifa. Dad'i sosai manosh yaji yace insha Allah.
Maryam ta samu sauk'i sosai koma ince ta warke. Da yamma miher da mum nata sukazo inda miher ce tayi driving nasu gwanin sha'awa.
Lokacin maryam ta idar da sallan la'asar kenan tana addu'oi setaji bud'e kofa tare da sallama,mamantane ta amsa musu dan rash ta koma gida.
Koda maryam ta idar,kunya sosai taji da ganin mum d'in manosh. Kanta a sunkuye tace sannu da zuwa,mum tace yawwa maryam sannu ya jiki,maryam tace da sauki ina wuni,tace lfy lau ya kika k'ara ji da jikinki,tace da sauki,mum tace to Allah ya k'ara lfy Allah kuma ya yaye miki,maryam tace ameen gabad'ayansu sannan mum ta zauna kusa da maman maryam akan carpet dake shinfid'e a k'asa,ita kuwa miher ta zauna a gefen maryam tana zolayarta matar bro kin samu lfy se kuma magan aurenku da bro,ahankili tayi maganar cikin zolaya tana dariya.
Maryam data kasa sakewa dan kunyan mum murmushi kawai takeyi,miher tace wlh ki dena jin kunyan mum dan bata da matsala sam wlh garama ki saki jikinki bro yace in kawo miki wannan,flower ne d'an k'arami maiban sha'awa,amma maryam taqi karb'a dan kunya,miher se dariya takeyi tace idan bakya so shikenan se in gaya mishi yanzunnan,muntsinin miher tayi ta cinyarta batare dasu mum sun ganiba. Daroya sosai miher takeyi tace shikenan nifa wasa nakeyi kar anjuma inji kin cijeni,mirmushi sosai maryam tayi tajin kalmar miher amma sam taqi tayi magana,mum ma ta lura da cewa maryam a takure take dan haka tace miher mu tafi ko donmu barta ta huta. Murmushi maryam tayi miher ta mik'e,maryam tace mun gode Allah ya kare,mum tace ameen sannan tayi gaba itada maman maryam. Ai suna fita maryam ta karb'e flowern tace wlh sena had'aki da captain kinata sani magana bayan kinsan bazan iyaba ko,miher tayi dariya tace nima ai zan gayamishi harda muntsinin da kika min,dariya sukasa dukkansu sannan tace miher mungode sosai ku bakwa gajiya da d'awaiyinane pls bana buk'atar wani abu kuma dan Allah ya isa haka mana,miher tace dani kikeyine,kallonta maryam ta tsayayi tace ni kike mannawa hauka ko,miher tace "am sorry our wifey" ban isa in manna miki haukaba wlh amma wlh mum bazata tab'a yarda inzo dubaki empty hand bane nizan tafi nabar mum tana jirana zamuzo gobe nida *my majid* kafin a sallameki *apple* tate dajan lallausar kumatun maryam. Dariya sosai maryam takeyi yayinda miher ta fita da sauri tana mata byee,ita kuwa murmushi takeyi tare da cewa tonagode Allah ya kiyaye hanya.
Maman maryam ta bud'e ledojin kayan tea ne manyan gwangwanaye da kuma fruits. Mama ta kalli maryam tace sude basa gajiya wlh,mamansu tana da kirki wlh gata da sauk'in kai kamar ba matar mai kud'iba kuma naga soyayyarta akanki sosai wlh. Maryam tayi murmushi tace wlh mama hakama miher tana sona sosai wlh gaskya ba laifi Allah yasa su d'aure a haka,mama tace ameen sannan sukaci gaba da hiransu irinna *uwa da 'ya*.
Yau aka sallami maryam,babantane ya d'aukesu a motarshi inda sukaitawa dr muh'd godiya, cikin girmamawa yace wlh bakomai baba Allah ya bata lfy,suka amsa da ameen sannan maryam tace nagode fa sosai da k'ok'arinku Allah yabar zumunci,murmishi yamata tare da cewa ameen aunty bakomai semunzo girei,tace wlh na hutar daku hakama yayi wlh sannan ta tafi yana musu Allah ya kiyaye.
A girei ma tinda maryam ta dawo zuwa ake ana gaisheya.
Bayan kwana biyu ne miher tazo da drivernsu da kula sabuwa babba a hannunta peppe chikeen ne a shike. Murna sosai maryam tayi da daginta suna d'an tab'a hira sannan ta mik'e tace zan tafi dan akwai inda zanje wlh sannan ta bud'e zip na jakanta ta ciro flower tace inji camtain. Murmishi maryam tayi tace nagode bari in wanke kulan ki tafi dashi,mihe tace no wlh danke kawai na sayi kulan dan haka shima nakine. Gidiya sosai maryam tayi tare da rakota har waje sukayi sallama.
Bayan tfyantane samira da rsha sukazo sukaita hira,maryam ta d'ibo musu kazan sunaci suna hira inda maryam take sanar dasu cewa gobe za'azo tambayarsu.
Washe gari da misalin 10:00am na safe iyayen manosh dasu marwan sukazo girei domin tambayan auren 'ya'yansu. Dama baban maryam yasan da zuwansu dan haka shima ya nemo mahaifin samira da kuma 'yan unguwa dan shine uban maryam da rashida dukka.
Koda sukaga mahaifin manosh masu ji mamakiba dan yah ibrahim ya musu bayanin komai kuma yace ya yafe harma da maman rash,amma baban maryam yace dole za'a sanar dashi kodon yasan yayi kissa kuma *azumi sitti* yahau kansa.
Zuwan manya sukayi da iyaue su majid,dan seda sukayi tambayan zahida da amina sannan sukazo girei.
Karb'a na musamman aka musu inda aka gaggaisa kuma aka fahimci juna ansa aure nanda 3month.
Bayan an gamane sukayi godiya sannan suka tafi.
Bayan sun koma gidane mahaifin maryam ya kira mahaifin manosh yace dama inaso muyi wata magana mai muhimmancine akan wani bawan Allah daka tab'a bugewa akan hanya girei shekaru biyu da suka shige,idan baka mantaba akwai wata yarinya dataketa bin motarka a wannan lokacin tana kuka. Jikin mahaifin manosh yayi sanyi dan baizai tab'ance wannan rananba.
Baban maryam yace to wannan mutumin bakowabane illa mahaifin rashida wanda marwan yake neman aurenta,tun daga wannan lokacin daga bugeshi ko minti goma bai k'araba Allah yayi mishi rasuwa. A wannan lokacin akwai wanda ya ganka shine da kukazo girei yace lallai kaine wannan mutum, yanzuma na gaya maka hakanne dan kasan cewa azumi yahau kanka,sannan yana da kyau ka nemi gafarar iyalansa,wanda ya gankan bakowa bane illa d'an cikinsa wanda yazo ya gaisheku mai suna ibrahim wato yayan rashidan kenan,amma sunce sun yafe har abada sun d'auki kadda.
Mahaifin manosh ya sauke ajiyar zuciya yace nagode sosai alhaji Allah yabar zumunci,kuma wlh naji dad'i sosai da yadda kamin magana a sirrance Allah ya saka da alkhai kuma insha Allah gobe zanzo gun iyalan marigayin,wlh tun wannan lokacin nima bani da sukuni kuma na koma girein na tambayi wani matashi akan wani da aka buge da mota nan ya tabbatar min da cewa Allah yayi mishi rasuwa,wlh tun daga wannan lokacin na kamu da hawan jini kuma nayi azumina sittin,sannan nayi aike zuwa ga iyalan wannan mutumin a wannan lokacinma sedai na hana abayyana sunan,kuma nasan nayi kuskure sosai wanda hakan shiyasa na gyara halayyata da dama alhaji nagode sosai kuma insha Allah gobe inanan zuwa girei da safe.
Mahaifin maryam ya tuna da randa akazo da abinci da kaya da kuma kud'i har *dubu d'ari uku* wai a baiwa iyalan marigayi,kuma sunyita tambaya daga gun waye aiken yazo amma sam basu samu amsaba.
Kamar yadda mahaifin manosh ya fad'a da safe yaje shida mahaifin marwan da kuma drivernsu,inda suka samu mahaifin maryam a gida dan baije ko inaba tunda yasan da zuwansu. Shiya musu jagora har cikingidansu yah ibharim suka gaida da iyalinsa sannan suka bada hakuri tare da musu gaisuwan rashin. Suka amsa tare da cewa cewa ai kwananshine ya k'are dan haka bakomai sun yafe wlh,godiya sosai mahaifin manosh yayi tare da musu alkhairai sosai sannan kuka fito tare da yah ibrahim yana rakasau da baban maryam.
Bayan fitowansune mahaifin manosh yake tambayan ibrahim akan aikin da yakeyi,nan ibrahim ya gaya masa cewa bai dad'e da gaba NYSC nashiba yana jirane tukunna,nan mahaifin manosh ya bashi *card*nashi yace ya same ran monday.godiya sosai ibrahim yayi dan yasan kawai aiki za'a bashi.
Lokaci yanata tafiya angwaye se himma suke bayarwa wajen aikin ginin gidajensu da zasu tare da amarensu. Manosh kusan kullum seyaje girei tun bayan dawowarshi,ranan suna hira yake tambayar apple wani irin gida take so,dadai tak'i gaya mishi,amma da taga zai b'ata rai tace ita dai ranta nason gidan sama,sannan ya kasance *milk da d'an army green*. Murmushi manosh yayi yace shikenan nagode. Itama murmushin tayi tace amma pls karka takura kanka danni kai nake so ba gidaba dan haka kakyi komai d'an daidai pls,dad'i sosai yaji yace shikenan apple zanyi d'an daidai *mata 4* dariya sosai tayi tace bakomai tunda dai nice *uwar gida*
Soyayyarsu abun burgewa wlh domin mai tsafta ce.
Maryam ce zata kaiwa babanta abincin a shop nashi tana cikin tfy se wata bak'ar mota ta tsaya,da sauri suka fito maryam bata zata gurinta zasu nufoba kaiwai suka big'e abincin hannunta ya zube a k'asa,kan tace wani abu sunsa mata hanki a hanshi mai d'auke da magani take ta mance inda take sukayi saurin jefata cikin mota suka fizgi motar a guje. Adaidai wannan lokacin iyayen maryam sukaji gabansu ya fad'i atare suka hau fad'i *Hasbunallahu wani'imal wakim* suketa nanatawa...
Hankalin manosh a taahe ya kalli d'aya daga cikin sojojin yace ina tausayawa duk wanda yayiwa maryam haka wlh.
Miher ce zaune ita da mum nata a palo suna jimamin abinda ya fari da maryam se wayanta ya fara k'ara da sauri ta d'aga tare da cewa hello lubna,lubna tace miher ya gida naji bro marwan yana cewa anyi kidnaping maryam d'in da bro manosh zai aura? Miher tace wlh kuwa lubna,lubna tace subbahanalillah yanzu su waye sukayi wannan aikin,miher tace wlh har yanzu dai shuru tukunna amma ansan inda maryam d'in take yanzu haka,lubna tace haba alhamdulillah a ina aka sameta,miher tace bawai an sametabane fa,andai gano inda take a *numan ne*. Lubna tace har numan aka kaita kai Allah ya tona asirinsu zanzo gobe insh Allah,to sekinzo nagode.
Koda lubna ta ajiye wayan miher se ta kira wani tace hello *saddam* ya akayi har su bro suka gane cewa maryam tana numan,aikinka baiyiba saddam domin yanzu haka su captain suna numan dan haka kuyi gaggawan d'agata daga numan ku k'ara gaba da ita zan tiro maka da kud'i yanzu a account naka saddam idan asirinmu ya toni zansha wuya agun bro marwan wlh seya kusan kasheni pls indai da gaske kana sona tokayi wani abu plss saddam. Murmushi yace karki b'ata bakinki bbynah, yanzu zamubar adamawan ma kwatakwata karki damu sweetheart zan nuna miki cewa da gaske nake k'aunarki bari na nemo wani abokina,lubna taji sanyi a ranta tace nagode sena jika.
Maryam kuwa dama ta kashe wayan gabad'aya tasa a cikin pant nata. Yadda aka ajiye mata abincin haka sukazo suka samu,yace wato bakici abincin bako,bai jira jin abinda zata ceba ya toshe mata baki da hanci da wani hankachif fari take ta mance inda take seya d'auketa cak se mota suka kama hanya,cikin ikon Allah kuwa ba'a tsaidasuba har suka bar numan.
Tfy sukeyi hankalinsu a kwance suna dariyan mugunta yana cewa *captain manosh* zanga iya kwarewarka kafin in shiga hannunka kuwa sena gama lalata budurwan naka tukunna dan nasan idan na shiga hannunka tofa tawa ta k'are shiyasa nima zanyi abinda nakeso tunda dama banida iyaye se kawai in bisu bayan na shana hhhhhhh...
Manosh se kiran line na maryam yakeyi amma shuru, seyayi tunanin kodai tana tare da mutanenne shiyasa bata bud'e wayanba. Nan dai yace bari yad'an k'ara jira. Anan ne muhsin ya kirashi yace "dude" na raba hotunanta kota ina yanzu haka ma ana haskawa a gidan *TV GOTEL* , *NTA* da kuma *ATV* duk anta haska hotunanta,manosh yace nagode abokina pls kuyita tayamu da addu'a sannan kuyita bada sadaka Allah ya bamu sa'an gano inda take,muhsin yace ka kwantar da hankalinka abokina insha Allah zamuga maryam cikin k'oshin lfy dan maryam tana da halayya masu kyau.
Iyaye maryam kuwa hankalinsu yad'an dawo jikinsu da sukaji lfyarta k'adau amma dai har'a yanzu suna cikin tashin hankali sosai. Duk girei seda akaji zance sace maryam auntyn yara,dan haka aketa addu'oi babba da yaro kai harta almajirai idan sukaji lbrn tofa suna komawa gun malaminsu suka gaya mishi,yace musu kwarai yaji a radio dan haka kota ina addu'oi maryam take samu.
Hajiya iya kuwa tafi kowa tashin hankali ana zaton,ko menene dalili oho? Kuka takeyi safe da dare tare da addu'an Allah ya baiyana maryam.
K'awayen maryam sun zama abin tausayi musamman rashida data tina kalmomin data dinga gayawa maryam ranan,dan haka ta dinga kuka tare da kewar aminiyarta. Hakama abdallah ya shiga wani hali sosai dan ganin maryam yakeyi kamar yarsa da cike ciki d'aya,yah ibrahim nema yake lallashinsa dan kowa yasan irin k'aunar da take tsakaninsu hakama ita maryam d'in tana ji da abdallah fiye da,sauran yaran.
Manosh baiga kiran maryam ba har 12:00pm dan haka yasan cewa akwai matsala,kuma shi yasan babu wadda ya gayawa cewa maryam tana numan daga iyayenshi se iyayen maryam se kuma friends nashi,dan haka abin ya dameshi sosai gashi faruq yace mishi wayan maryam a kashe yake bazai iya gane inda takeba dole se wayanta yana kunne.
Da misalin 2 na dare suka isa wani jeji tare dabi cikin jejin daba kowa se wani d'an k'aramin gini daba'a k'arasashiba nan suka tsaya suka fitar da 'yan kayayyakin da suka taho dashi suka dai kimtsa gurin se suka kwantar da ita akan bargo sannan suka zauna a gefe.
Saddam ya kira lubna yace hello bbynah mun iso lfy,tace sannu da hanya a inakuke yanzu? Yace muna jihar bauchi cikin gefe da *jejin yankari* ido lubna ta zaro tace har bauchi,yace yes bazasu tab'a tunanin zamuzo bauchiba,dad'i taji har cikin ranta tace nagode bbynah aikinka ya gyaru,murmushi yayimata yana busa sigarinshi yace bbynah gaskya bazan kyale yarinyarnanba dolene sena tab'ata fa,hankalin lubna ya tashi tace no bbynah kafa cemin ni kad'ai ce yarinyar da kake so taya za'ayi kashe min haka kuma,wato dama kana cin amanata kenan ko? Saddam yace wlh ba haka bane bby shikenan wlh bazan mata komaiba amma kinsan ked'in kince dole semunyi aure kafin muyi wani harka kuma gaskya ni a matse nake wlh,lubna ta murgud'a baki tace karka damu idan mun gama wannan aikin zakasha mamaki da irin gift d'in dazan baka wlh bbynah,nan saddam yaji dad'i yace okey my luv shikenan sekin jini,tace ok but pls karka mata komai indai har kana sona,yace wlh bazan mata komaiba karki damu bbynah.
Maryam bata farkaba har asuba,ta jita ak'asa nan ta tashi da sauri tana addu'oi tare da k'arewa gurin kallo setaji hawaye a fiskan,kukan tane ya tashi mutum guda d'aya da yake kwance daga gefe dan sauran kam duk sun shiga gari neman abinci.
A gigin baccin yazo inda take yace ke 'yanmata yane? Kallonshi takeyi tare da cewa bawan Allah inane nan kuma? Yace nan jihar bauchine ta gefen jejin yankari. *innalillahi wa'inna ilaihirraji'un* maryam taketa fad'i sannan tace karfe nawane yanzu? Ya duba wayanshi yace 5:30am,tace ina zan samu ruwa nayi sallah,nan ya d'auko pure water ya mik'a mata tare da ciro bindiga a aljihunsa yace kinga wannan,wlh idan kikayi wani kuskure sena pasa kanki dashi,jikinta na rawa tace to alwala kawai zanyi inyi sallah.
Komawa yayi ya kwanta ita kuwa jiki na rawa ta koma gefe tana alwala. Bayan nan ta koma cikin ginin tare da lekashi taga dai bacci na damunshi sosai,dan haka ta ciro wayanta ta kunna tare da da turawa manosh texs sannan ta kashe wayar tahau yin sallah.
Manosh daya kasayin bacci yana zaune a mota a numan seyaji texs ya shigo wayanshi,da sauri ya duba
_hello peach,sun d'aukeni daga numan zuwa jejin gefen yankari dake jihar bauchi gurin babu kyan gani a tsakiyar jeji muke cikin wani kango da babu ko rufi asaman pls peach do something ka kulamin da iyayena plss da kuma abdallah nah byeee_.....
Manosh ji yayi kamar zaiyi hauka dan yadda yakejin k'irjinji yana tafasa. Kwana d'aya kawai amma dukya fita hayyacinsa haka ya juya ya koma girei ya dad'a baiwa iyayen maryam hak'uri tare da kwantar musu da hankali,sannan yasa aka kira mishi abdallah yace kayi hakuri abdallah maryam tana cikin jarabawane amma komai zai wuce ina tabbatar maka da cewa auntynka zata dawo insha Allah kuma dukda halin da take ciki sam bata mance da kaiba tace ingaisheka abdallah. Rungume manosh abdallah yayi yana zubda kwalla shima manosh daurewa kawai yayi sannan ya kalli yah ibrahim yace ka kula dashi dan sak'on maryam kenan akanshi.
Manosh ya shige mota ya wucegida a galabaice,toilet ya shige ya watsa ruwa sannan ya fito yasa jaket maroon da black yana k'ok'arin fitowa sega mum nashi da miher,nan ya koma lallausar gadonshi *milk colour* yad'an jingina yana kallonsu.
Kuka miher ta farayi tare da ciro wayanta ta d'aukeshi hoto taje har kusa dashi tace kalli yadda ka zama fa bro, kwallan idonshi ya share tare da kamo hannun miher yace karki damu zan koma normal ne bayan na samo apple d'ina. Mum tanata kallonsu tare da tausayawa d'an nata tace Allah ya baka sa'a *son*, yace ameen mom nina tafi sena dawo,har waje miher ta bishi tanata kuka harya tafi....
.
Bayan maryam ta idar da sallah ne taketa hamman yunwa,dan tunda ta baro gida bata sake cin abinciba se ruwa data sha,gata da *ulcer*.
Lek'owa tayi taga har yanzu bacci yakeyi,dan haka taje inda yake tanata crwa 'bawan Allah脳2' ahankali ya bud'e ido tare da tasowa ya zauna! Kallon juna suka tsayayi domin sun tabbata akwai inda suka tab'a had'u dukkansu d'in. Can maryam ta tuna shine mutumin da mota ta tab'a bigeshi a hanya harta taimaka mishi yahau mashine aka kaishi hospital tabbas shine wannan. Wani sanyi taji a ranta tare dayin mirmushi tace bawan Allah dama kaine ka rabani da iyayena? Shuru yayi yana kallonta cikin mamaki yace dama kece yarinyar da aka d'auke? Kallonshi ta tsaya yi tana mamaki tare da cewa aka d'auke ko kuka d'auke bawan Allah.
Bayansa yaketa waigawa sannan ya mik'e tsaye cikin hanzari yace banina d'aukekiba abokin aikinane,maganar gaskya nidai ba mutumin kirki bane wannan ranan da muka had'u dakema sata naje nayi aketa bina tare da fasamin jiki,dak'ar nasamu na gudu shine na b'ullo ta girei har muka had'u dake kuma na miki k'arya kika tausaya min tare da taimakona.
Maryam tayi shuru tana sauraranshi tace to bawan Allah dan Allah ka gayamin abu guda d'aya wanene yasa a kamoni? Shiru yayi yace bazan gaya mikiba sedai in taimakeki in baki wayana ki kira duk wanda kike buk'ata indar har kinaga za'a iya taimaka miki,shuru maryam tayi tace to ai nabar wayata a gida ban kuma san numbern kowaba sena iyayena da k'awayena.
Shuru yayi nad'an lokaci sannan yace toki gayamin numbern iyayenki,nan ta gaya mishi numbern babanta yasa ya kirashi,bugu d'aya ya d'auka lokacin suna tare da dad d'in manosh yaje yi musu jaje. Maryam tace baba nice yanzu haka ina jihar bauchi cikin jejin dake gefen yankari,baba yace to wannan numberfa? Tace baba karka damu lfyata lau babu abinda ya sameni sedai ina jin yunwa sosai har k'irjina ya fara min ciwo,subhanallah maryam haka suka barki da yunwa dan basu da imani tun jiya? Baba sunban abinci amma bazan iya cibane ka gaida mama kuma dan Allah karka kira numbern nan domin na d'aya daga cikinsune ya taimakamin idan ka kira suka gane zasu kasheshi. Hankalin mahaifinta a tashe yace shikenan maryam na fahimceki amma dan Allah ki daure kici abinda suka baki kodan lfyarki,to baba ya mama take,lfy lau karki damu damu maryam ki kula da kanki,insha Allah zaki dawo garemu da izinin Allah,Allah ya amshi addu'ar mahaifina na gode....bata k'arasa maganarba ta katse saboda kuka daya ci karfinta.
Mahaifin maryam hankalinsa a tashe ya kira manosh ya gaya mishi komai,manosh yace karka damu baba insha Allah zata dawo kudai tayamu da addu'a.
Shi kuwa bawan Allah kallon maryam yakeyi tare dajin tausayinta ya bud'e ledanshi ya d'auko *maltina da biskits* d'aya ya bata ta karb'a tare dayin godiya,yace bakomai ki koma inda kike dan nasan sun kusa dawowa zanyi iya k'okarina dan in taimakeki ki dena damuwa kinji? To nagode sannan ta koma taje ta zauna tare da bud'e malt d'in da biskits tana sha.
Wayarta ta bud'e sega texs d'in manosh dana miher,na miher ta fara bud'ewa inda taga hoton manosh sanye da maroon jaket,ita kanta maryam tasan manosh ya shiga wani hali daga ganin hoton nashi,sannan ta karanta texs nata kamar haka
_slm 2u my aunt_
_bansan mezance mikiba aunt,amma ina cikin damuwa sosai musamman yadda naga bro manosh ya zama kamar bashiba dan rashinki_. _Aunt munanan munata addu'a Allah ya d'auraki akansu,kinga dai yadda bro nah ya zama wlh tun jiya baici komaiba har yabar gida yanzu_. _ina sonki wifeynmu,pls koda empty rexs ne ki aiko min dan inji sanyi a raina_. Yours miher....
Koda maryam ta karanta setaji kwalla ya zuba mata,nan ta tura mata da
_thankyou so much sis,nagode sosai da kulawarki,kuma nayi farin cikin ganin pic d'in peach,dan yasani farinciki sosai wlh_. *nagode*
Koda taga texs d'in manosh batayi reply ba se kawai ta kirashi. Katsewa yayi ya kirata ta d'auka tare da cewa *captain*, sanyi yaji har cikin ranshi yace yes apple a wani hali kike yanzu? Karka damu ina halin lfy,sedai nayi fushi dakai,meyasa mena miki apple? Saboda kabar cikinka da yunwa rabonka da abinci tun breakfast d'in safe meyasa hakan peach? Am sorry apple amma kema ai bakici komaiba,eh amma yanzu haka ina shan malt da biskits,naga pic naka yanzu miher ta turo min peach a jiya kawai amma ka canja. Yadda yaji muryanta kamar zatayi kuka yacewa sojan da yake driving tsaya anan ka karb'o min malt da biskits,sannan yace "apple am goying to eat now okey" pls banaso kisa damuwa aranki muna hanyan bauchi kinji? Murmushi tayi tace "thankyou peach" cikin sanyin murya. Sunanta ya kira a hankali *aunt*, cikin muryan kuka tace uhmm,yace pls stop it apple i will soon come to u okey? Har yanzu kukan takeyi "tace okey i have to peach byee...
Bayan ta katse wayanne ya had'iye tausayinta a wuyanshi daidai lokacin aka kawo malt da biskit d'in ya bud'e ya fara sha,bayan ya gamane ya karb'i driving d'in gudu yakeyi kamar zai tashi sama..
Can kuwa koda maryam ta ajiye wayan da sairi ta kashe ta mayar pant d'inta dan taji zuwan mota.
Saddam ne tare da sauran abokanshi 3 suka dawo,wannan d'ayan da suka bari yana kwance ya mik'e yare da cewa ya kuka dad'e ne haka? Saddam yace wlh bari kawai,ta tashi kuwa,eh ta tashi tayi sallah,saddam yace gaskyafa ni a matse nake wlh dan haka kawai zan sauke gajiyata akanta wlh,d'ayan yace haba saddam karkayi haka pls da safiyannan idanma hakane ai gara ka bari se dare kai kanka zakafi jin nishani idan duhu yayi. Saddam yace hakanefa,to gaskya dole na koma cikin gari in nemo wata dan wlh a matse sosai nake kasan abunka da sabo,yana kaiwa nan yaje ya duba maryam tana rakub'e a gefe tana kuka. Dariya sosai saddam yayi yace garama ki dena wannan kukan domin anjuma zakiyi wanda ya fishi sauti hhhhhhhh
Hankalin maryam ya sake tashi domin taji hiransu. Abinci wani ya kawo mata ya e gashi kici ko fine girl,ko kallonshi batayiba ya ajiue ya k'ara gaba.
Tana jin motarsu ya tashi ya tafi ta lek'o taga duk sun tafi seshi wannan bawan Allah. Wayarta ta kunna ta nemi layin manosh amma sam baya shiga,ta tabbatar da suna hanyane dan haka taje tayi alwala tare dayin sallan walaha tayi addu'oi sosai sannan ta sake gwada numbern manosh har yanzu dai shuru yak'i shiga,haka ta koma gefe tana zaune tanata karatun qur'an a cikin zuciyanta har azahar tayi.
Maryam tanayin alwala yazo yace amma ki gayamin sunan k'awayenki mana,tace lfy? Yace lfy lau,nan dai ta dinga kiransu harta gama yace babu wasu da kike tunanin sun tsaneki? Tace gaskya babu,yace to shikenan jeki kiyi sallah.
Bayan ta idarne seta bud'e wayanta cikin ikon Allah call d'in manosh ya shigo,da sauri ta d'auka tace hello,yace peach kina dai lfy ko? Tace lfy lau manosh kuna ina,pls kazo da sauri domin suna da niyan aikata wani abu a kaina pls..karki damu apple inanan a inda kike yanzu zanzo gareki,mik'ewa tayi da sauri tare da jujjuyawa tana kallon jejin tace ina kake peach?...
Wayan hannunta ya karb'a tare da kashe wayar gabad'aya yana binta tana komawa da baya tana cewa dan Allah kayi hakuri. Ran saddam a b'ace yace wato dama da waya a hannunki ko,to wlh bazaki b'ata min aikiba sedai in kasheki in kashe banza. Bindiga ya d'au zai harb'eta d'aya mutumin yace haba saddam kar kayi haka mana mace zaka kashe kuma k'aramar yarinya,kawai muyi gaggawan barin nan d'in shine mafita,domin yarinyar data saka aikin itace take baiwa masu binciken address d'in inda muke dan a kamaka ka fita daga rayuwarta for good. Kan saddam ya d'aure sosai yace kana nufin *LUBNA AHMAD* tana min wasa da hankali ,yace kwarai kuwa.
Mamaki ya cika maryam ta nanata sunan a cikin ranta *lubna ahmad*? Kawai seta d'iba da gudu ta barsu atunaninta ai su manosh sun iso inda take. Bindiga saddam ya d'aga tare da harbinta ai kuwa seya sameta a saman hannunta kusa da kafad'arta,ihu sosai maryam ta saka tareda fad'uwa k'asa tana kuka. Saddam zai kara mata se d'ayan ya bige bindigan yace meyasa hakane saddam wai kasheta zakayine? Sauran ukun ne sukazo da mota sukace kuzo mu sampe sojoji sunji k'aran bindiga zasuzo kuma,d'ayan yace bari in d'auko yarinyar dan bazamu barta a hakaba ai. Da gudu saddam yahau mottafi suka tafi suka barshi,gashi sam baiga maryam a inda ta fad'iba kamar wanda ta b'ace. Yanata tsaidasu saddam amma sam sunk'i tsayawa sema harbinsa dasukayi a k'afa ta yadda bazai iya guduba. Ai kuwa segasu manosh da gudu ya k'araso yana cewa apple, apple na iso ina kike? Kan mutumin ya nufa tare da d'agoshi yace ina maryam! Take mutumin ya fara b'ari dan yasan shikenan kashinsa ya bushe tunda ya shiga hannun *sojoji*, yace *sir* wlh ban saniba acan ta fad'i nima ita nake nema...

 ANTIN YARA Page 41-50
.
Hajiya khadija ce zaune agidansu maryam tanata kuka,maman maryam se hak'uri take bata,tace yanzu fisabilillahi me maryam tayi haka dahar za'a d'auketa a rabata da iyayenta,se kuma ta sake fashewa da kuka mamace taketa bata hak'uri.
Auntyn yara ta dubi tsohon dade rik'e da hannunta yana tab'a inda aka harb'etan da hannayensa,cikin ikon Allah sam bataji zafiba. Se alokacin da take kallon tsohonne seta tuna cewa wannan shine wannana tsoho mai farfad'iyan data tab'a taimakawa lokacin daya fad'i akan titi rananne farkon had'uwanta da *peach* shiyasa bata bance fiskanshiba sam. Murmushi tayi tace baba,yace na'an maryam kin ganeni ashe,tace sosaima kuwa meya kawoka nan bab ya jikinka? Murmushi yayi yace jiki da sauk'i maryam tun bayan rabuwana dake na taimakawa mutane hud'u yanzu kece ta biyar,tace eyyah baba Allah ya saka da alkhairi,dama a nan jihar bauchi kakene? A'a a jihar adamawa nake ca *hong* ayyah baba a hong kake dama toya akayi kazo nan? Maryam saboda ke nazo danaga kina cikin damuwa kuma dama nace kece mutum ta biyar dazan taimakawa shiyasa nazo. Har zatayi magana ya katseta da cewa maryam ki saurari abinda zan gayamiki da kyau,tace to baba ina jinka amma akwai wanda ya kamata mu had'u dashi nasan kuma sun iso yanzu gashi sun karb'e wayana nasan zaiyita nemana baba. Yaga dai ta damu sosai seyace karki damu zan kaiki har inda suke kiban hankalinki anan maryam,tace to baba ina jinka yare da kallon hannunta daya d'aure mata bayan wasu abubuwa dayayi wanda basan meneneba.
Baba ya kalli maryam yace nasan zaki gayawa mutane cewa *lubna ce* tasa akayi miki haka ko? Tace eh baba,yace to karki gayawa kowa maryam,cikin mamaki tace meyasa amma dolene in gayawa iyayena ai,baba yace harta iyayennaki kada ki gaya musu komai kuma bana so ki tabbayeni dalili indai har kin yadda dani kinsan bazan cutar dakeba to rashin gayawa kowa shine afi akhairi a gareki maryam. Mamaki sosai ya baiyana a fiskar maryam tace to baba idan ban fad'a an d'auki matakiba ai zata sake bin wata hanyan,yace bazata sakeba maryam maganar gaskya niba mutum bane kamar ke maryam ni alja....bai k'arasaba maryam ta tsorata sosai tare da mik'ewa tana komawa dabaya dukda dai tasan batasan kota inda zatabiba. Baba ya mik'e yace maryam karkiji tsorona ki d'aukeni kamar kina tare da mahaifinkine,dan Allah karki sanar da kowa cewa lubna ce ta miki haka kigayawa kowa cewa su saddam ne,sannan yanzu haka bawan Allah can yana can hannu sojojin zasu gana kece zaki iya dakatar dasu tawajen gayamusu cewa shi bayida hannu taimakonki yake da niyanyi shine suka miki rauni kinji maryam? Cikin rawan jiki dama tunda taji shiba mutum bane taketa add'ua,setace to baba dan Allah inaso in koma gida,yace ba gidaba maryam karki rud'e ki nitsu kinji,kibi wannan hanyan gabanki zaki samesu nina tafi.
Yana kaiwa nan ya b'ace,gudu maryam tasa tare da kiran sunan manosh...!
Kamar daga sama manosh yaji muryanta ta gefensu da sauri ya juya ya nufin gun da gudu yana apple, "where are you?" Can ya hangota tanata gudu tana juya bayanta har suka iso gun juna.
Kallon juna suka tsayayi yayinda take ta waige waige,manosh ya lura da cewa bata cikin hayyacinta sam. Sunanta ya kira aunt? Da sauri ta juyo se'a sannan ne ta dawo hayyacinta nan ta tsaya kallonshi cikin so da kuma tausayin yadda taga ya zama. Sunanshi ta kira tare da murmushi tace manosh,shima murmushin yayi tare da k'are mata kallo da wuri yakai hannunshi gurin hannunta da aka harbeta sannan ya juya yana kallonta cikin tuhuma. Ita kanta tasan dalilin kallon nan tace wani bawan allah na hango shine yayi saurin d'aukeni ya kuma taimakamin sosai shinema ya d'aure min hannun. Manosh yace yarone ko tsoho? Har cikin ido take kallonshi ta kuma gane me yakenufi wato yana kishi wani ya tab'a jikinta kenan. Tace tsohone manosh kamar mahaifina yake kuma wlh ba wani tab'a jikina sosai yayiba abun nashi daban al'ajabi kuma sam bana jin wani ciwo yanzu,murmushi yayi mata dan yasan sam maryam bazata mishi k'aryaba ya yadda da ita har cikin zuciyarshi.
Matsowa yayi kusa da ita gab kad'anne a tsakaninsu kunya sosai taji sannan ya mata kwarjini sosai ta yadda bazata iya had'a ido dashiba. Hannunshi ya mik'a mata mana'a tazo su tafi,amma sam tak'i bada hannunta tanata jan himar nata da d'ayan hannun. Murmushi yayi yace Alhamdulillah "i'm so happy to see you apple" kanta a sunkuye tace "me too" sannan ya d'auki wayanshi ya kira babanta yace baba mun sameta lfyanta k'alau gatanan yanzu zau taho,maryam ta karb'i wayan tana kallonshi tare dayin dariya tasa a kunnenta tace hello baba,yace alhamdulillah 'yar baba Allah ya amsa addu'armu barka 'yata,mirmushi tayi wanda yaji dad'i sosai tace baba ina mama,nan mama ta karb'i wayan tace maryam Alhamdulillah bari naje kichin na dafa miki abinci 'yar albarka,dariya tayi tace ina sonki mamat semun dawo na kuma gode sosai da addu'oinku.
Bayan ta gamane ya kira miher da mum nashi nanma suka gaisa sannan ya kira su marwan suka sakegaisawa daidai lokacin suka iso gun otansu manosh d'in.
Maryam ta hango bawan Allah yana ta zubar da jini a k'afanshi yayinda wani yake gyara mishi k'afa. Da sauri tace peach me kuka mishi haka,wlh sam bayi da laifi kokad'an dan shinema wadda yake kiran baba a waya,sannan taimakona yakeyi sam bayida hannu a ciki dan Allah ku rabu dashi,manosh yace apple pls karkisa baki a ciki,tace pls manosh ka saurareni wlh..ya isa apple,yana da hannu mana tunda ya biyosu kuma ai shima yasan da zance sacekin inhar da gaske yakeyi meyasa bai sanar da 'yan sandaba. Shiru maryam tayi dan yadda taga ran manosh ya b'aci cikin k'ank'anin lokaci da sauri tabar gun ta koma jikin motarsu tana zubda kwallah.
Manosh yabi bayanta tare da bud'e mata gaban motan yace shiga mu tafi,ba musu ta shiga ta zauna daga tsakiya tana ci gaba da kukanta wanda babu sauti hawaye awai kake hangowa yana zuba. Hankalinsa ya tashi nan ya shigo gaban shima yana zaune tagun k'ofa driver a ya shiga maryam tana tsakiyansu sannan sauran suka tattaro tarkacen su saddam da wannan mutumin a bayan motan suka kama hanyan.
Maryam ta share kwallanta kanta a sunkuye dan gabad'aya a takure take. Manosh yace da driver idan kaga wani shop ka tsaya agun,yace ok sir.
Maryam ya kalla yace apple me zakici,tace ni banason komai,yasan cewa fushi tayi yace dolene kici wani abu dan kina jin yunwa sosai,tace ni banajin yunwa muje kawai,nan driver ya tsaya suka fita shida manosh nad'an wasu lokuta sannan suka dawo amma drivern bai shigo motaba.
"Anosh yace apple karb'a kici,tayi kamar bata jishiba,ya sake cewa bana so mu fara haka dake pls apple ki barni inyi aikina inyaso zan barshi daga baya amma ba yanzuba kinji? Ko kallonshi batayiba tace amma nace maka babu hannunshi fa,yace yes aunt i know bincike kawai zanyi akan wanda yasasu kuma shi yasan kowanene,tace nima na sani ai saddam sunanshi kafin kuzo suka gudu,yace eh saddam dinma akwai wanda ya sashi ai,tace pls peach indai kana sona to kawai kabar maganan tunda Allah yasa nadawo nina yafe wlh,murmushi yayi yace ok apple eat first okey,tace nifa bazanci komaiba seka janye,yace tona janye karb'i apple d'in kici pls,karb'a tayi yana mata murmushi sannan shima ya fara cin nashi ita kuwa sam ta kasa ci tana rike dashi. Ta lura da cewa yana kallonta dan haka tace nifa bazan iya cin komai ayanzuba senaje gida,bakinshi ya matso dashi daidai kunnenta yace "kinaso inyi fushi dake koh?" Kunya taji tace wlh bazan iya cin komaiba kayi hakuri,shuru yayi bai sake ce mata komaiba sunata tfy har suka iso *yola*.
Dad'i sosai maryam taji suka wuce da bawan Allah can barac nasu inda ya mik'awa manosh wayan maryam yave lokacin da take wayane ya karb'e wayan,bayan ya ajiye wayan shine na d'auke. Manosh ya karb'a sannan yazo suka wuce girei itadai maryam tanata tausayawa mutumin can dasuka kama,ahanyane manosh ya bata wayanta,tanata godiya tace a ina ka samo dan ai wayan tana hannun saddam ne,nan yagaya mata komai daidai lokacin suka iso k'ofar gidansu maryam a girei...
.
k'ofan gidansu maryam a cike yake da jama'a kowa yana jiran dawowar auntyn yara,koda akaga motan sojoji ya tsaya da sauri aka nufo motar anata hamdalah da mata murna sosai,musamman abdallah hannu ya d'aga sama yanayiwa Allah godiya.
Su manosh suna tsaye daga waje yanaganawa da jama'a,ita kuwa ta wuce gida dasu rash da sameera daidai sauran jama'a. Maryam ta rungume mahaifiyarta tana murmushi bayan nan ta zauna bada lbrn abinda ya faru amma sam tace batasan bayasa a mata hakanba,nan dai kowa yayita tofa albarkacin bakinsa. Can akajiyo hayani a waje nan take kowa ya fito,yarane da almajirai suketa tsalle da wak'a.
_Alhamdulillah auntyn yara ta dawo,ta bayya,Allah mungode maka daka dawo mana da auntyn mu lfy lau_.
Hahahah sunatayi manosh ya nufin gurin se zuba musu kud'i yaketayi yara se k'ara murya sukeyi suna d'iban kud'i yah ibrahim ne yazo ya koresu yace toya isa haka mungode kowa ya wuce gida,nan suka watse suna murna. Dariya manosh da ibrahim sukayi sanan suka wuce gunsu baba suna magana,maryam ta wuce band'aki tayi wanka tare da d'auro alwala tazo tayi sallolinta sannan taci abinci sosai dan dama tana jin yunwa.
Bayan ta koshine tace mama da sauran wani abincinne zan zubawa manosh a kula ne,mama tace eh akwai,nan taje ta had'o a kula ta kawowa maryam tace gashi,godiya tayi tare da mik'ewa taje palon babanta tare da sallama suna zaune da yah ibrahim da kuma abokinsa soja wato yusuf maryam ta ajiye musu abinci sannan ta koma ta d'auko plate da kuwa ruwan sanyi tare da exotic d'in da hajiya khadija ta kawo musu.
Bayan ta fitane yah ibrahim ya zuba musu ba laifi kuwa sunci sosai sannan sukace zasu tafi. Maman maryam tazo suka gaisa sannan ta musu godiya,manosh ya kira maryam ya sanar da ita cewa zasu tafi ta kwanta ta huta,godiya sosai ta mishi yare da jajdada mishi cewa karya cutar da bawan Alla can,murmushi yace yace "yes my princess"tambayoyi kawai zai amsamin nayi miki alk'awarin bazan cutar dashiba matuk'ar zai amsamin tambayoyin da nake buk'ata agunshi. Dad'i taji sosai tace yaushe zaka sake zuwa? Yace se jibi akwai wani abune,tace yes ina son *flower* murmushi yayi yace angama aunt gobe mum da miher zasuzo zan aikota dame kuma kike so? Tace da *peach d'inah*,dariya yayi itama haka sannan suka tafi. Yah ibrahim ya shigo gida sunata hira dasu rash daga k'arshe suka tafi.....
Washe gari da safesartuday ne,dan haka su marwan suka da safe sukayiwa maryam barka sannan suka d'anyi hira suka tafi. Da misalin 11:00am mum d'in manosh da miher sukazo nanma dai suka zauna kad'an,miher dasu maryam sunata hira a d'akinsu yayinda ta mik'a mata flowern da bro nata ya bayar akawowa marya,dad'i sosai taji tare da lumshe ido su miher da rash se dariya sukeyi mata suna zolayarta. Awa d'aya su miher sukayi sannan suka tafi sesu zahida da amina sukazo,bak'idai sosai suketa zuwa da abin arziki babu wanda yake zuwa empty.
Hajiya iya ce zaune a gaban maryam tanata kuka tana rungume da maryam,maryam da mamanta duk kansu ya
d'aure da irin kukan hajiya iya. Amma se suka d'auka kodon k'aunarda takeyiwa maryam ne.
Saddam ne zaune a d'akinsa ya kira lubna a waya yace kina ina,tace ina gida me nakeji wai maryam ta koma gida? Yace kizo mu had'u dan muyi magana,tace ok amma bazan fito da motaba zanzo yanzu semu had'u,yace ok.
Babu wani b'ata lokaci lubna ta shirya cikin after dress black tahau nape se daidai gate d'in gg ta kira saddam a waya tace ina daidai gg,yace wlh motata tayi pashi bamma bar gida ko zaki k'arasone semu fito tare,bata soba dai amma dan bataso asirinta ya taunu setace to gashi kayiwa mai napen kwatance. Nan suka d'auki hanya har inda saddam ya kwatanta musu,se kuwa gashi ya fito daga d'akinsu yazo yabiya mata kud'in dan ita batada canji.
Bayan mai nape ya tafine saddam yace ki shigo mana kar wani wanda ya sanki ya ganki anan kinga se'a ganki kamar mutumiyar banza,haka tabishi a baya suka shiga sannan ya kulle k'ofan ta key,lubna data zauna aiseta mik'e tare da cewa ya kuma ka rufe kofan saddam? Take ya canja ido yace ashe ki muguwace munafuka ban saniba,kece kike gayawa maryam inda muke kaita dan azo a kamani in fita daga rayuwarki ko lubna,hakazakim
in,wlh to bazan barki hakaba sena lalata miki rayuwarki kafin in bada kaina. Kuka lubna ta farayi tace haba saddam wlh bansan komai akan abinda kake fad'aba taya za'ayi in kira lubna kuma,dan Allah karkamin haka saddam wlh karyane duk wanda ya gayamaka karya yakeyi wlh,nan dai lubna ta rikice ta fara kuka. Shuru sadda yayi yace kiyi hakuri lubna na d'auka koda gaskene wlh,bakomai share hawayenki mu tafi domin yanzu ni suke nema abokina ya yaudareni wlh amma zanyi maganinshi baisan wayenibane shiyasa,juice ya zuba mata da sauri ta karb'a tasha batare dayin wani tunaniba ta shanye tas dama datajin k'ishi. Shi kuwa saddam wayo ya mata dan kartayi kuka ta tona mishi asiri dan haka ya juba magani a ciki ai kuwa take lubna ta fara fita hayyacinta,saddam kuwa ya tashi ya fara cire kayan jikinshi tas tana iya ganinsa bakomai a jikin,nan hankalinta ya tashi tana k'okarin tashi amma ina seta fad'a kan katifarshi kamar macacciya,da sauri ya rabata da kayan jikinta tas se lashe baki yakeyi kamar tsohon maye,yahau shafeta tare da wani irin gigicewa da ganin kyakkyawar suranta. Cikin k'ank'anin lokaci ya rabata da budurcinta gashi ya kwashi romo sosai danshi a tunaninshi an dad'e da sanin lubna saboda irin shigan dayaga takeyi. Bayan ya gamsune yayi saurin watsa ruwa ya shirya tare da kwashe kud'ad'en dake jakarta ya d'auki akwatinsa ya gudu da motarshi.
Koda lubna ta dawo hayyacinta kuka sosai takeyi tare da tsinewa saddam albarka tana tuna yanzu shikenan ya gama b'ata mata rayuwa ya zatayi kenan? Miher ce kawai ta fad'o mata arai harta d'auki wayarta zata kirata kuma seta tuna cewa koda yaushe miher suna tare da majid kuma tasan dole miher zata fad'a wanda idan bro marwan yaji shikenan nata ya k'are. Kuka sosai lubna takeyi gashi jikinta duk jini haka ta rasa yadda zatayi kawai se maryam ta fad'o mata a rai data tuna da abinda wani tsoho ya gaya mata akan maryam,ai kawai seta kira maryam.
Lokacin su maryam sun shigo jimeta dasu yah ibrahim dasu sameera,mamaki tayi sosai da ganin kiran lubna,seta d'auka hello,lubna cikin miryan kuka take magana hello maryam dan Allah ki gafarce akan abinda na miki nasan kinsan komai amma dan Allah ki rufamin asiri dan yanzu hakama Allah ya saka miki akan abinda na miki maryam sadda ya cuceni yamin fyad'e bazan iya kiran kowaba seke,saboda abunda wani tsoho ya gayamin dan Allah maryam ki taimaka kizo saddam ya gudu yanzu haka ina d'akinsane a bayan gg idan aka sani za'a kasheni a gida musamman bro marwan maryam dan Allah ki rufamin asiri. Shuru maryam tayi ta kasa cewa komai,kuma batasan ya za'yi tabar su rash taje ita kad'aiba. Nan tace ok inazuwa tare da kashe wayar, tace yah ibrahim dan Allah ku saukeni anan ku shiga kasuwan rash idan naje na gama zan gaya muku inda nake sumu tafi,yah ibrahim yace to shikenan sannan ta sauka tahau nape se bayan gg,nan dai ta kira lubna tayi musu kwatance suka k'arasa har gun sannan ta sallameshi ya tafi,ta sake kiran lubna nan taji k'aran wayan a kofar gabanta,da sallama ta shiga taga lubna a kwance cikin jini,tsorata sosai tayi tare da dasa key a kofan tana ta addu'a,ta k'arasa ta taimaka mata ta mik'e ta rakata toilet dake kicin d'akin sannan ta tsaya daga bakin kofa tana mamakin abinda ya faru.
Wayartace tayi k'ara ta d'auka hellow peach,yace apple nah kina ina,k'irjinta ya buga tace ina jimeta munzo sayayyane dasu yah ibrahim idan muka gama zan sake kiranka muna cikin kasuwane,yace ok badamuwa,tace ina kake? Yace muna kan aiki yanzu zamuje inda saddam yake zaune ne mu kamashi,tace a ina kuka sameshi peach,yace wai yana bayan gg yanzu haka muna hanyane,tsoro ya kama maryam tace to shikenan sena kiraka,yace ok byee. Maryam tace lubna fito su manosh suna hanyan zuwa nan domin sun samu lbrn cewa saddam yana nan karsuzo su tarar damu anan gashi na mishi karyam idan ya samemu anan tofa ina cikin tahin hankali,lubna take zawo ya kamata haka tayitayi a toilet d'in tana kuka,ita kuwa maryam se kallon windo takeyi tare da k'ara rufe ko ina a d'akin,daidai lubna ta fito tasa kayanta da sauri jikinta se b'ari yakeyi tausayinta ya kama maryam har seda tayi kwalla,seta d'aga zanin gadon taje ta wanke da ruwa tazo ta bazashi akan gadon sannan maryam ta kwashe mata wayanta da sauran kayan makeup nata tasa a bag na lubnan suka yunk'uro zasu fita kenan sega motar su manosh,aida sauri suka wuce toilet sunata addu'a ita kuka lubna zawone ya sake kamata haka tayitayi tana hawaye sosai dan yadda take tsoron bro marwan barema kuma aji cewa an mata fyad'e ne hmmmm...
.
Tsayawar mutar sukaji,ba lubna kad'aiba ba harta maryam a tsorace take,gashi tayiwa manosh karyan cewa tana kasuwa kuma yanzu idan ya ganta a d'akin saddam kimarta zai ragu a idonsa addu'anma dakyar take iyayi,ita kuwa lubna idan ka gantama dole kayi kwalla dan tausayinta. Muryan manosh sukajiyo yana cewa ya kuma naga padlock a k'ofan,hakan yana nufin saddam ya sake tserewa kenan?yusuf yace ai mu b'alla kofan kawai k'ila sawa yayi a rufeshi ta baya dan muyi tunanin bayanan.
Maryam da lubna aise suka tsure suna *innalillahi wa inna ilaihirraji'un* jikinsu se rawa yakeyi. Bawan Allah ne yace duk yadda akayi saddam guduwa yayi baya ciki domin banga motarshiba lallai yasan za'azo nemanshi shiyasa ya gudu,manosh yace ina kenan kake tunanin zai tafi?yace numan zai koma inda yakai maryam,wanine yazo wucewa manosh yace kai ina wanda yake zama anan?mutumin yace d'azu ya fita da kayansa dewa ya zuba a mota da gudu yabar nan. Manosh yace muje yusuf,nan danan sukabi bayan saddam gudu sosai manosh yakeyi da mota.
Basu maryam kad'aiba,harta ni *sad-nas* seda nace *alhamdulillah* wani irin ajiyar zuciya maryam ta sauke tare da k'arayin godiya wa ALLAH sannan suka fito. Lubna tace kwad'o fa naji sunce ansa ajikin k'ofan to taya za'ayi mufita kenan,maryam ma abun ya bata mamaki tace towaya mana kwad'o kenan?
Gwada bud'e kofar tayi cikin mamaki taga kofan ya bud'u,kallon juna sukatsayiyi ita da lubna dukkansu mamakine ya bayya a fuskarsu,maryam tace shikenan gaskya muyi hanzarin barin nan,dan nima su yah ibrahim suna jirana. Lubna ta rik'o hannunta tace kije maryam niki barni anan dan bazan koma gidaba wlh bro marwan zai kasheni. Maryam tace ki dena fad'a haka lubna aiba a son ranki bane fyad'e aka miki kawai ki fad'a musu gaskya,lubana tace wlh na gwammace insha wani abun in mutu amma sam nikam bazan iya komawa gidaba maryam bazaki ganebane,ba'asan ina da alak'a da saddamba,idan kuma aka sani to za'amin kallon mutumiyar banza za'ace dama mun saba iskanci dashine baza'a tab'a uarda fyad'e yaminba wlh nan ta fashe da kuka sosai..
Tausayinta ya kama maryam tace toke meya had'aki dashi lubna?
Lubna tace wlh kawai yaketa bibiyata waishi yana sona,ni kuma danaga 'yan shaye shayene se tsoro ya kamani dan kar sumin wani abu shiyasa na tsaya muka dai gaisa duk dan mu rabu lfy,so dewa idan maza suna takuramin saddam shine mai taimakona dayake anganshi ana tsoronshi dan ansan zai iyayin kissa ma indai a kainane,kuma babu wanda yasanshi a gidanmu hakan ya bani daman sakewa dashi dan taimakona da yakeyi,nima ina mishi kyautan kud'i sosai amma sam baya so sabodashi wai sona yakeyi muyi aure shinefa naketa binsa a hankali danmu rabu lfy. Lokacin dana tabbatar da kece macen da price manosh yake k'auna se kishi ya kamani saboda yadda na dad'e ina k'aunarsa shinefa na biya saddam kud'i harda kukata na gaya mishi k'arya tare da b'ataki agunshi,shi kuwa yace seyayi maganinki shine ya d'aukeki dukda taimakona amma gashi gashi tun ina duniya Allah yayi miki sakayya maryam dan Allah kiyi hakuri ki yafemin.
Maryam ma kwalla takeyi dan yadda lubna ta bata tausayi,rungume juna sukayi lubna tanata kwalla ga azaba da takeji a jikinta. Dukkansu se suka tsinci kansu cikin nishad'i alokacin da suke rungume da junansu,harta kukan da lubna takeyi seta denashi wanda basan dalilin tsayawanshiba. Maryam ta saketa tace karki damu lubna nayafe miki har cikin ziciyata wlh fatana shine Allah yasa kar saddam ya ambaci sunanki idan an kamashi,idan kina da number'n shi kiyi sauri ki kirashi. Haka kuwa akayi number biyu duk a kashe suke seta sake kiran d'ayan liyin cikin sa'a ta shiga,ya d'auka tare da cewa hello my luv kiyi hakuri da abinda na miki kece kika tunzurani alokacin danaga kyakkyawan suranki kuwa sena sake haukacewa naji bazan iya kyalekiba,wlh dama d'aukeki nayi muka tafi kawai muci gaba da zamammu dan gaskya baiwarki daban bby kin had'u sosai. Zazzafar hawayene suke zubowa daga idanunta tace saddam ka cuceni ka cuci rayuwata wlh bazan tab'a yafe makaba mugu azzalimi d'an iska Allah ya tona asirinka...kuka ma tsanani ta fashe dashi,shi kuwa saddam se dariya yakeyi tare da cewa Allah sarki lubna bby kiyi hakuri kinji,koda an kamani nayi miki alk'awarin bazan tab'a anbatar sunanki a cikiba koda kuwa kasheni za'ayi tunda dama bani da iyaye shikenan nima sena bisu,ki kwantar da hankalinki kuma ki goge nanmaba a wayanki karki sake kirana dannima yanzu zan yarda sim d'in ne ki kula da kanki kuma ki yafemin my luv byeee.
Kukan taci gabadayi,maryam ta rungumeta tanata rarrashinta. Aduk lokacin da maryam ta rungumeta setaji wani sanyi a ranta har bata so maryam ta saketa wlh,maryam tace lubna ya isa haka miyi mubar nan muje gida ki gayawa mahaifiyar komai karki b'oye mata,lubna tace wlh bazan iyaba maryam sedai inbar garinnan inje wani gurin,maryam tace ina kuma zakije bayan ga iyayenki anan lubna dolene mahaifiyarki ta sani wannan ba maganene da zamuyi shuru akaiba,saboda idan asirinmu bai tonu yau ba,tofa tuabbas zai tonu watara wanda hakan zaifi miki ciwo da zafi ina nufin kamar idan kikayi aure dolene mijin daya aureki zansan cewa keba budurwa bace wanda hakan zaija miki babban matsala wlh,amma idan kika gayawa mahaifiyar komai zaizo da sauki insha Allah.
Lubna dai tak'i yadda da shawaran maryam,haka maryam ta gaji ta rabu da ita tace to shikenan Allah yasa karki d'auki ciki lubna,dan inhar kin d'auki ciki tofa nida kaina zanje har gidanku in gayawa iyauenki komai bazan b'oyeba,amma inhar baki da ciki toni na cire hannuna akai sedai kiyi k'okari ki dinga shiga cikin ruwan zafi safe da yamma insan samunema ki nemi ganyen magarya ki tafasashi da jan kanwa kina zama a ciki insha ALLAH zaki had'e amma fa bazaki koma kamar budurwaba sedai kuma zaki had'u sosai. Lubna taji dad'i sosai tace nagode sosai maryam gaskya keta dabance wlh nagode sosai,maryam tayi murmushi tace karki min godiya lubna,amaimakon godiyan da zakimin,inaso idan kin samu dama toki taimaki mutum uku suma kuma kice su taimakawa wasu ukun. Murmushi lubna tayi tare da sake rungume junansu suna masu matuk'ar farin ciki dukkansu.
Ahankali suka fito babu kowa agun dan haka sukayi sauri suka k'araso bakin titi suka suka sami nape se gidansu lubna.
Suna tafya lubna daga gani kasan tfyarta ya canja dukda dagewa da takeyi dan kar'a gane amma dole duk wanda ya ganta zesan akwai wani abu. Sun isa palo inda taga mahaifiyarta na zaune tana kallo,sallamarsu shiya juyo da fiskanta gunsu...
Maryam tace hajiya khadeeja,hajiya khadeeja tace maryam tare da mik'ewa ta rungumeta sema a lokacin ta lura da lubna a gefe data tsaya tana kallonsu. Mum d'in lubna ta saki maryam tare da k'are musu kallo dukkansu,suma kallonta sukeyi dan sun tsorata sosai da irin kallon da take musu. Maryam tace hajiya dama lubna 'yarkice,kuma kece mum d'in marwan? Hajiya jikinta a sanyaye tace eh nice dama kunsan junane keda lubna? Tace a'a ta had'u da tsautsayine machine ne ya bugeta ni kuma ina sayya lokacin senaji ta fad'o ta jikina,to dai naga ta k'asa mik'ewa shine na rakota gida. Mum d'in lubna tace subhanalillah tare da zuwa gun lubna tanata dudduba jikinta tana mata sannu to Allah ya kare na gaba yanzu inane yake miki ciwo? Lubna tace k'afatace mum da k'yar nake takawa,tace sannu ai dole muje a duba miki kafan agun masu duban kafa koma kinyi targad'e waya sani. Shuru lubna tayi yayinda mum ta zaunar da ita tace sannu maryam ki zauna bari in kawo miki abun sha,ashe kuma haka ya faru,maryam tace eh wlh,mum tace to Allah ya kare na gaba Allah ya toni asirinsu,maryam ta kalli lubna tace ameen sannan mum ta wuce.
Maryam tace nizan tafi idan kinga period naki seki gaya min,koma dai me ake ciki zamuyi waya dan yanzu kin zama k'awata lubna,murmushi tayi tace nagode maryam kin zama kamar 'yar'uwata na jini wlh bazan tab'a mantawa dakeba,wlh a tsorace nake har yanzu,maryam tace ki dena tsoro mudai jira tukunna nayi miki alk'awarin zanyita tayaki da addu'a Allah ya bamu mafita akan wannan lamarin,lubna tace ameen. Sega mum ta shigo da abin tab'awa kad'an maryam taci tace nizan tafi hajiya nagode sosai da hidimar da kikayi a gidanmu,mum tace bakomai maryam kigaida mutanen gidan dukka,tace zasuji,mum tace bari insa driver ya maidake,tace a'a wlh dasu yah ibrahim mukazo idan mun gama zaidawo ya d'aukemu yanzu kasuwan zan koma,tace eh to bari drivern ya maidake kasuwan,tace to hajiya nagode sannan ta kalli lubna tace to Allah ya sauwaka ya kiyaye nagaba,lubna tace ameen nagode.
Mum d'in lubna ta rakata hargun mota sannan suka tafi. Hankalin mum d'in lubna a tashe tare da tunani mai zurfi a cikin ranta ta shige gun lubna tana mata sannu.
Maryam se taji dad'i sosai a ranta tace dama hajiyace mahaifiyar marwan da lubna,gaskya sunyi sa'an iyaye domin hajiya khadija macece mai kirki sosai sannan tason maryam ita. Wayan maryam ne ya far k'ara ta duba taga samira ce,tace hello samira kuyi hakuri ganinan na kusa isowa,samira tace okey. Bayan ta ajiyene call d'in manosh ya shigo ta d'auka tare dayin sallama,ya amsa sannan yace Alhamdulillah apple mun kama saddam,k'irjinta ya buga sosai tace haba peach,yace wlh kuwa yana can gurin horo,tace tokun saki wannan mutumin,yace karki damu bazan cutar dashiba,gobe zan sakeshi insah Allah,tace to nagode sosai Allah ya saka da alkhairi,yace ameen apple kin gama sayayyanne? Tace eh nagama amma yah ibrahimma ya shigo jimetan kawai zamu koma tare,yace ok toshikenan ki gaishesu senazo kinji,tace yaushe zakazo,yace sedai zuwa gobe insha Allah,tace har gobe kwana d'aya fa kenan ban gankaba,dad'i yaji data nuna damuwarta agareshi,yace kinaso inzone,tace eh amma bakomai yau da goben duk d'ayane,yace to lnagode zanzo gobe da safe kinji,tace Allah ya kaimu,yace ameen aunt ki gayamin wani abu,tace *i luv u* tare da katse wayar dan kunya dataji. Dariya yaketayi tare da sauke wani ajiyar zuciya yace *i luv u 2 apple* yusuf yace tofa ai bata jikaba sedai ka sake kiranta,manosh yayi murmushi yace waya gayamaka taji mana,dariya sukayi tare da wucewa..
Maryam tayiwa drivern godiya ta tafi gunsu rash tayi d'an sayayya kad'an sannan suka kira yah ibrahim yazo suka wuce gida a motar da manosh ya sayawa maryam.
Kowa gida ya wuce maryam taje ta watsa ruwa tare da alwala tayi sallah tayi addu'oi sosai. Abdallah ne ya shigo sunata hira da auntyn shi har magrif sannan ya tafi masallaci.
Anata zuwa yiwa maryam da iyayenta barka harda malamai manya. Koda yaushe suna waya da lubna tana tambayarta akan shiga ruwa zafi,tace eh tana shiga sosai dan yanzu kamma tfya normal takeyi. Dad'i sosai maryam taji kuma sam bata gayawa kowa komai akan lubna,hakama shi saddam duk azabar da ake gana mishi yace shine kawai yayi ra'ayin sace maryam wabu wanda ya sashi,hakan yasa suka kaishi gidan yari aka kulleshi acan,shi kuwa d'ayan tuni an sakeshi har gidansu maryam yazo yayita mata godiya tare da tabbatar mata da cewa daga yau ya zama mutumin kirki ya dena d'aukan abun tsakaninshi da mutane sedai taimako. Dad'i maryam taji sosai tare dayiwa Allah godiya...
***
Bayan wata d'aya lubna taga period nata yazo kamar dai yadda ta saba. Murna sosai tayi tare dayiwa Allah godiya sannan ta kira maryam ta gaya mata komai, murna sosai itama tayi tace shikenan lubna nagode,lubna tace nice da godiya damuwa d'ayane yanzu shine idan nayi aure,maryam tace inga kawai ki gayawa mahaifiyarki danki samu mafita,lubna tace sam bazata fad'aba,maryam tace to shikenan duk yadda ake ciki zamuyi waya se'anjuma.
Maryam tana kwance a d'akinta wajen 10:pm seta kira yah ibrahim a waya,yayi mamakin ganin kiranta amma seya d'auka yace hello aunty lfy dai koh?
Tace lfy lau kayi hakuri na tasheka,yace bakomai akwai wani abune? Tace dama shawara nake nema agunka akan wani abu daya dameni wanda bazan iya gayawa koda mahaifiyata bane bare kuma wasu amma haka kawai naji zuciyata ta raya min cewa na gaya maka yah ibrahim. Yace to aunty ina sauraronki,tace yah ibrahim wata baiwar Allah ne ta had'u da jarabawa kuma se muka had'u da ita a wannan lokacin da abun ya sameta.
Nan dai maryam ta kwashe lbrn da lubna ta bata tun farkon had'uwansu da saddam har zuwa fyad'en daya mata ta gaya mishi tas sedai bata gayami ko wacece yarinyarba kuma bata gayamishi abunda lubna da saddam suka mataba kawai dai lbrn shak'uwar saddam da lubna ta bashi batare data gaya mishi sunayensuba.
Shuru ibrahim yayi dan yama rasa mezaice,yace amma meyasa tak'i sanar da iyayenta,aunty wannan babban maganace wanda dole se manyanta sunsan dashi,dan haka kigaya mata ta cire wani tsoro a ranta ta sanar da iyayenta tunda ba laifinta bane wannan shine kawai shawaran da zakibata.
Maryam tace yah ibrahim wlh nayi iyakan k'ok'arina dan in fahimtar da ita amma seta nunamin cewa garata gudu koma ta kashe kanta akan ta sanar dasu. Yah ibrahim yace aunty wanene wannan yarinyar? Tace kayi hakuri yah ibrahim bazan iya gaya makaba domin nayi mata alk'arin zan b'oye sirrinta. Shuru yayi yace to aunty gaskya shawaran da zan iya bata kenan dan shine kad'ai mafita agareta. Maryam tayi shuru tace yah ibrahim zan gayamaka kowacece amma inhar zaka taimaketa,yace wace irin taimako kuma ni zanyi mata aunty? Maryam ta gyara murya tace yah ibrahim taimakon da nakeso kamin shine ka amince zaka aureta.
Shuru yayi tare dayin murmushi yace in auretafa kikace aunty? Tace kwarai yah ibrahim,a rayuwata babu wanda nake k'auna da burin ya zamanto mijina irinka yah ibrahim,jira nakeyi ka dawo daga bautar k'asa se'in sanar dasu baba, amma muna namu Allah yana nashi segashi su manosh sunje gun baba batare dana saniba sun nemi izini kuma baba ya amince musu,hakan yasa na amincewa manosh na kuma cigaba da addu'a wanda hakan yasa naji ina son manosh har cikin raina kai kuwa na maka matsayin " *soulmate*" d'ina, yah ibrahim wlh kaina fara so a raina kuma har gobe kai *soulmate* d'inane...
Maryam bata k'arasa maganaba ta fara kwallah,yah ibrahim kuwa wani zazzafar k'aunarta yake shigansa,yace aunty kidena pls ya isa haka kinji? Tace yah ibrahim dan Allah ka amincewa buk'atata wlh yarinyar tanada hankali gata fara ce kyakkyawace sosai bugu da k'ari zaka ilmartar da ita sosai tafannin addininmu. Yace shikenan aunty na amince koda mummunace ita tunda dai ke kika zab'amin ita na yarda zan aureta kidena kuka kinji aunty, "i will do anything just for you aunty" shikenan? Bazan iya misalta muku farincikin da maryam ta shigaba,bata san lokacin datace "i love you so much uncle" dad'i yaji yace to wacece ita yarinyar? Tace sunanta lubna k'anwar marwan ne wanda zai auri rashida. Mamaki sosai yayi yace to shikenan ki kwanta kiyi bacci zanzo da safe kinji,tace to nagode sosai seda safe...
.
Washe gari da safe yah ibrahim yaje suka gaisa da mama sannan sukayi hira sosai da aunty harta bashi number lubna dan dama tun a jiyan ta sanar da lubna komai,dukda dai lubna taji kunya sosai,amma setaga koba komai ai asirinta zai rufu tunda shi yah ibrahim yasan halin da ake ciki kuma ya amince zai aureta a hakan.
Lokaci yanata tfy,ibrahim da lubna suna waya sosai dan ta turo mishi da pic nata ta whatsapp shima kuma ya tura mata amma bai tab'a zuwa gidansuba. Koda yaga pic d'in lubna mamaki sosai yasha dan kawai seyaji k'aunarta na k'aruwa a cikin ranshi tare da addi'an da yakeyi akanta. Itma lubna ta yaba sosai dan yah ibrahim ba irin mazan da mata zasu k'ishi bane.
Hakanan suketa soyayyarsu,wanda har abdallah yasan lubna suna gaisawa sosai.
Ita kiwa maryam seta tsinci kanta cikin farin ciki da kwanciyan hankali mara misaltuwa.
Ranan taje jimeta aike tana cikin keke nape seta hango manosh tsaye da wata budurwa wanda sam bataga fiskartaba saboda yana tsayene dab gabanta. Kuma ta tabbatar da cewa manosh ne dan taga motarshi sannan kuma ga marwan a gefe yana tsaye rai abace,se taga manosh ya bud'ewa budurwa kofar motarshi na baya harta shiga se kuma ta sake fitowa ya bud'e mata gaba ta shiga. Maryam ta kira number manosh dan tabbatarwa,ai kuwa seta ya d'auka tare da cewa hello,tace ya kake,yace lfy lau zan kiraki anjuma kinji,tace meyasa kana wani abune? Yace eh kiyi hakuri zan kira kinji,tace ok sannan ta kashe wayar tanata binsu da kallo setaga shima ya shiga mazaunin driver yaja suka tafi yayinda marwan yake tsaye agun rai a b'ace.
Hankalin maryam ta tashi sosai ta rasa meke mata dad'i,tace wato dama da manosh yake cemin mata 2 ko 4 zaiyi kenan yana neman wata...?

 ANTIN YARA Page 51 . Da wannan tunanin ta koma girei,bayan ta ajiye aiken da mamanta tamatane seta wuce d'aki ta kwanta har yanzu manosh bai kirataba ita kuwa ta kasa hakura seta kirashi. Hello apple kiyi hakuri wlh am busyne shiyasa ban sake kirankiba,tace busyn me kenan,yace ki bari kawai hidiman dewa pls kimin hakuri zan kira pls,tace bakomai se'anjuma,yace ok tnx luv u,shuru tayi tare da katse wayar. Abin ya d'an dami manosh amma dayake yana da abinyi sosai sebai sake kirantaba. Har la'asar bai kiraba,ita kuwa maryam abin yana cinta sosai a rai,manosh bai kirataba harse bayan magrib yace da ita am so sorry apple zanzo bayan sallan isha kinji,shuru tayi mishi,ya sake nanata tace sekazo tare da katse wayar,sake kiranta yayi ta d'auka batare datayi magana ba,yace apple are you okey? Tace ues am fine,yace amma naji muryanki wani iri,tace bakomai sekazo... Abun ya dami manosh sosai dan haka suna idar da sallan isha suka taho shida muh'd da marwan. Kamar kullum muh'd da marwan sun tafi k'ofan gidansu rash da mota shi kuwa manosh suna zauren gidansu maryam inda ta shinfid'a mishi k'aramin carpet tare da kawo mishi fruit kamar yadda ta saba dantasan yana son fruit sosai shiyasama bata rabuwa dashi a gida. Manosh yaga canji sosai tattare da ita hakan yasa ya ajiye wayarsa a gefe ya maida kallonshi gareta,ita kuwa kanta na kallon cikin gidansu kyakkyawar gefen fiskanta yake kallo tare da b'akin takalmin dayayiwa kafarta kyau yace apple lfy kuwa,tace lfy lau batare data kalleahiba. Yace toyana ganki haka kodai bakya jin dad'i ne,tace a'a lfyta k'alau,yace tomeyasa tunda nazo yau baki kalleniba kuma gashi sam baki sakeba kamar namiki laifi? Juyowa tayi suna kallon juna har cikin ido sannan tace kwarai kuwa kamar ka sani,seta sake mayar da kanta gefe, murmushi yayi yace pls apple ki bari fushin bai karb'ekiba wlh tomenayi nikuma yau? Ta sake kallonshi da kyau sannan ta juya,murmushin ya sakeyi yace kidena min wannan kallon kina bani tsoro wlh,shuru tayi batace komaiba,yace wai dagaske kike yine aunt,to pls ki gayamin laifina so that in nemi yafiyarki kinji,tace bakomai zan shiga gidane, yace ok to jeki mana yau harse kin nemi izinin shiga gida? Tace ina nufin zanje in kwanta bacci nakeji,shuru yayi yana kallonta cikin mamaki seyace ok badamuwa bari inji kosu marwan sun gama,nanya kira marwan tare da sawa a handsfree yace ya kun gamane mu wuce? Marwan yace kaji gayennan fa danka gama muma semu gama,manosh yayi murmushi yace bahakabane bata jin dad'ine shiyasa,amma shikenan bari na shiga masallaci nima inji karatu idan kun gama seku tab'ani,marwan yace ok ka gaisheta pls,yace zataji. Manosh ya kalleta yace apple zan tafi kije kiyi baccin kinji,mik'ewa tayi batare datace komaiba zata shige yace tsaya ki tafi da carpet d'in. Cak kuwa ta tsaya ya nad'e tare da d'aura mata tiran friut d'in danko d'aya bai shaba yau,tausayinshi ya kama maryam se kuma bataji dad'in abinda ta mishiba,matsowa yayi kusa da ita inda suke jin kamshin turaren junansu yace gashi,friut d'in ta kalla sannan ta kalli idonshi wanda shima idon nata nake kallo cike da tausayi ta kawar da kanta gefe tare da karb'a ta wuce da sauri batare datace mishi komaiba yanata binta da kallo harta tafi sannan shima ya fito ya shiga masallaci amma shi kad'ai yasan abinda yake damunshi hakama ita maryam d'in koda ta shiga gida friut d'in tasa a gaba tanata kallo tare dajin kwalla yana zuba a fiskanta. 9:30pm su marwan sukayi hon wa manosh wanda har ita maryam taji hon d'in kuma tasan sune zasu wuce,sam bataji dad'in abinda tayiwa manosh ba. Manosh yace musu yau sam banganewa apple ba,akwai wani abu amma tak'i gayamin. Muh'd yace kodai jikintane to,manosh yace sam bahakabane akwai dai wani abu daban dan sam tak'i sakemin yau kamar wanda nayi mata wani laifi kuma tak'i cewa komai. Abin ya d'aure musu kai sosai haka suka koma gida yayita kiran wayanta amma sam tak'i d'agawa yayi texs shima shuru bata amsa mishiba hakan ya tabbatar mishi da cewa fushi takeyi dashi. Washe gari tun asuba yake kiran numberta amma tak'i d'auka abin ya dameshi sosai dan sam jiya bai samu yayi bacci gashi kuwa yau zaiyi tfya zaije lagos ama 2days kawai zaiyi,haka yayi sallama dasu mum da marwan sannan ya tafi. Koda yaushe seya kira number apple amma sam bata d'auka daga karshema ta rufe wayan nata gabad'aya. Abun yayiwa manosh ciwo sosai,bayan abunda ta mishi ranan shi baiyi fushiba,bai kuma san laifin daya mataba dan haka shima yasa a ranshi cewa bari dai yad'an kyaleta na 2days maybe kafinnan zata huce. Da magariba maryam ta bud'e wayanta amma ga mamaki bataga texs d'in manosh ko d'ayaba. Hakan yasa tad'an damu kad'an tanata zaman jira har bayan isha shuru. Manosh dai bai sake kiran maryam ba harya gama 2days nashi a lagos ya dawo gari. Kuma so da yawa idan suna tare dasu rashida yakan kirasu su gaisa amma sam ya dena kiranta,hakan yasa ta damu sosai kuma tana matuk'ar son ganinshi. Yau wenesday bikinsu manosh saura 9days kawai,abun ya dami maryam sosai tanata tunani aranta. Bayan ta idar da sallan azaharne sega wani yaro yazo yace auntyn yara ana kiranki a waje,tace wanene,yace wanda yake zuwa gurinkine,nan taji dad'i a ranta dajin cewa manosh ne, tace to jeka kace ina zuwa. Atamfa tasa d'inkin riga da siket tare da himar kalan atamfar peach colour tayi kyau sosai. Tunda take fitowa yake kallonta harta k'araso da sallamarta,ua amsa tare da cewa kin kyauta apple da kika maidani haka,fiskanta a had'e tace kaima ai ka kyauta. Yace menayi,kalonshi tayi har cikin ido tace bansaniba,yace ni kikema wannan kallon ko, wlh appale idan kika shiga hannuna ko hmmm. Kunya sosai taji tare dayin mirmushi tace ina wuni,lfy ya mama,lfyanta k'alau,ya rashin kirkinki,tace muna fama dukkanmu,mirmushi yayi yana danna wayanshi. Tace ka fara ko,nifa bana so mun magana kana tab'a waya,kallonta yakeyi harda dakewanta,wayan nashi ya d'ago yace kalli nan,juyowa tayi tana kallonshi inda ya nuna mata wayan,mamaki sosai tayi da ganin pic nata akan wayan lalli kuwa wato dama d'auka hoto kakeyiko,murmushi yayi yayinda pic nata suketa wuce akan screen nashi kala kala,mamaki sosai tayi wato duk lokacin da suke tare pic yaketa mata yana k'are mata kallo. Katseta yayidan ya sauke wayanshi k'asa yace tun randa mukazo shop din baba nakeda pic naki har ranan yau. So duk lokacin da nake tare dake muna hira ina kallon ki a wayana,tace oh shiyasa ni kake cemin in dena kallonka ko,yace eh mana ni bana so ana kallonane shiyasa,murmushi tayi tace ina miher,yace oho ban saniba,tace haka kace ko,yace eh nima yau na dawo daga lagos kwanana biyu acan dana dawo ban sameta a gidaba taje gun k'awarta. Maryam tace baka gari? Yace yes ai kece kika cazamin kai shiyasa nima na tafi,kuma nayi iyakan k'okarin in sanar dake kink'i picking call nawa bansan wani irin laifi nayimikiba. Tace lallai ka kyauta,yace wlh bani da laifi apple kece da laifi dan haka kibani hak'uri,murmushi tayi tace bashakka kuwa ai kamin laifine shiyasa,yace to amma idan na miki laifi bazaki gayaminba apple sedai kiyita wulak'antani dan kinsan ina sonki ko? Tace hmm su so manya,kallonta yakeyi sosai yace bakiyardaba kenan,tace dakam ina sane da wannan son,amma ayanzu kam bansaniba konice ko kuma ita. Kallon juna sukeyi yace me kikace apple? Tace eh aikaji abinda nace. Yace pls ki gayamin ban ganeba,tace wata yarinyace na ganku da ita ranan kana tsaye dab da ita marwan yana gefe,harka bud'e mata k'ofa kuka tafi kuka bar marwan agun,kuma na kiraka alokacin amma sam kaki kirana da sunan daka saba gayamin sema cemin kayi wai zaka kirani anjuma shine baka kiraniba harse bayan magrib shine kukazo kaida muh'd da marwan. Tabbas manosh ya gane komai dan haka ya shiga yin dariya sosai kamar bashiba,yace kardai kicemin shine dalilin dayasa kika min wannan horon,shuru tayi tana kallonshi rai ab'ace shi kuwa dariya sosai yakeyi yace haba aunt gaskya bakimin adalciba dama ashe kina da kishi apple,dariya sosai manosh yakeyi wanda hakan ya tfyar da hankalin maryam ta tsaya kallonshi tana murmushi,dariyanshi yana mugun kasheta dan wani kyau na musamman yakeyi,manosh ya lura da irin kallonsa da takeyi wanda ita kanta basan tanayiba,hakan yasa ya dena dariya shima ya tsaya kallonta tare da juyawa yaga ba mutanen sam a inda isuke,hakan yasa yace mata zonan aunt,se yanzu ta dawo saiti tace nak'i,yace pls ki matso apple,tace meyasa,yace toki dena pls kallona banso saboda kina tafiyarmin da hankali aduk lokacin da kike kallona wlh. Shuru tayi tare da kallon wani girin gabad'aya kunya ya kamata shima ya lura da hakan dan haka ya kira marwan a waya yace abokina gani agun aunt,marwan yace kace komai ya daidaita kenan?manosh yayi murmushi yace zai daidaita dai kasan meyasa take fushi dani,marwan yace seka fad'a menen wai? Yace randa dad ya aikemu muka fito se muka tsaya a gefen gidan man su muhsin. Marwan yayi dariya yace kardai ince taganka kaida lubna lokacin da nake mata fad'a? Dariya manosh yayi yace to wlh fushin da takeyi dani kenan waita d'auka budirwatace. Dariya sosai sukeyi marwan yace haba aunt har kina sa ran abokina zai iya hango wata bayan ke,murmushi tayi tana sauraronsu,marwan yace wlh lubna ce k'anwata kuma laifi tayi yasa nake k'okarin hukuntata shine abokina ya shiga tsakaninmu yace muje mu maidata gida,danace bazan jeba suje shine yace da lubna tota dawo gaba ta zauna se suka tafi ni kuwa ina jiranshi yadawo wannan shine gaskya aunt,ai wlh ki kwantar da hankalinki mu sam iyayenmu zamu gada mata d'aya kawai is okay,manosh yace a'a nidai 2 zanyi dan nama gaya mata kuma tsarin gidanama na mata biyune,nagode daka wankeni marwan sena shigo,yace ok a gaisheta,manosh yace zataji amma gaskya na canja mata suna daga *apple zuwa jealousynah*, ba marwan kad'aiba harda ita maryam dariya sosai tayi wanda harshi marwan yana jiyowa. Bayan sun gama dariyanne manosh yace *jealousynah* ina so mufitane bazamu jimaba kije ki sanar da mama kinji? Tace nifa bana son wannan sunan,yace okay apple,murmushi sukayi tare tace inane zamuje? Yace cikin jimeta amma yanzu zamu dawo kinji,tace to bari inje in gayamata,ok yace da ita sega abdallah yazo gunshi. Mama tace to maryam ki kula da kanki ki kuma ji tsoron Allah aduk inda kike,tace to mama nagode sannan tafito. Tace nagayamata,yace ok muje harda abdallah,nan abdallah ya bud'e mata gaba yace auntynah kishiga,murmushi tayi tace kaidai ka shiga nizan zauna a baya,haka kuwa akayi suka kama hanyan jimeta,shi kuwa manosh wayansa ya d'auka yayiwa maryama texs nan ta duba kamar haka tagani. _Hi my jealousy_ _I love you so verry much_ _Kuma ki dena wahalar dani pls,saboda ni manosh nakine ke kad'ai batare da kowaba,kwanaki kad'an suka rage in mallakeki apple jealousynah_. Murmushi sosai taketayi bayan ta gama karantawa,shi kuwa yanata kallonta ta mirrow yana tayata murmushin. Tun daga nesa abdallah yake gango wani had'add'en gida mai penti cream da kuma d'an army green yace gaskya gidancan ya had'u,manosh yace ko,abdallah yace sosai wlh koba hakaba aunty? Maryam ta kalli gidan tace hakane k'anin aunty. Daidai gidan manosh ya tsaya,dama maigadi yana baiwa flower ruwa ata wajen gate dinne,da sauri ya ciro remote a aljihunsa ya danna se gate d'in ta bud'u sannan suka shige ciki,daga maryam har abdallah bud'e ido sukayi sosai suna kallo . Bayan sun fitone manosh ya rik'o hannun abdallah kamar wani yaro k'arami yace muje d'an gaban goshin aunty. Murmushi abdallah da maryam sukayi,ya kalli apple yace muje _jealousy_ tare da mata gwalo ya kashe mata ido d'aya wanda ya bata dariya tana biye dasu. K'ofa ya bud'e suka shiga palon farko babbane sosai wanda yasha wll peper army green mai tsadan gaske da labule ga kujeru da standart AC,can gefe kuwa daining ne shima komai army green ne harda frdje d'in. Akwai d'aki babba komai white ne a ciki,se kuma d'ayan d'akin blue amma bakomai daga gani kasan d'akin boys masu zuwane. Se katon kichine da store wanda farin tiles ne kota ina ansa gas da frezer ne kawai. Abdallah ya kalli aunty yace abokina white d'akinnan na wayene,yace nawa ne,blue d'in kuma na yaran aunty maza masu zuwa nan gaba,hhhh abdallah yayi dariya ita kuwa kunyane ya kamata. Sama suke hawa wanda palo 2 ne a saman,dama da hagu,na dama shine na manosh komai *milk colour ne* na hagu kuwa na maryam ne komai *peach colour ne*. Woooo! zanso ace kunga gidannan,kowannesu da daining nashi colourn palonshi,sannan a palourn maryam akwai wani ki hine da store komai light blue ne sedai bayi da girma kamar kichin d'in k'asa. Agefen maryam akwai d'akinta da toilet a ciki,daga gefe kuma d'akin bbynsu mace ce mai ziwa bayan sunyi aure ba'asa komaiba dai amma wall peper pink ne. Se kuma d'akin baki da toilet a ciki. A palon manosh kuwa dainingne se kuma d'akinsa da toilet. Gaskya tsarin gidan ya burgeni mu samman idan ka haura sama, palour 2ne a gefenka ga peach ga kuma cream. Manosh ya nuna musu ko ina tare da musu bayani. Abdallah ya dad'e yana addu'a a cikin gidan sannan ya yabawa manosh da irin k'okarin dayayi a wannan gidan nashi,dan base na fad'a. Drinks masu sanyi ya d'auko musu daga frdje,mamaki sukayi lokacin daya bud'e fridje d'in a cike yake da drinks da kuma faro water. Maryam dai taki shan komai,abdallah ne yasha abinshi shida manosh,yace nifa banga d'aki naba,manosh yace d'akinka uana daga gefen flour ata waje,yace yawwa bari naje na duba,manosh yace to muma gamu fitowa. Shuru maryam tayi gashi palourn yad'au sanyi,dan tun shigowarsu ya kunna AC. Tashi yayi daga inda yake zaune ya dawo inda take yace tashi muje ki zauna a palo na kafin mu tafi dan nacewa su marwan sekin fara zama akan kujerun kafin su zauna. Ba musu ta mik'e suka k'arasa a 3seta ya zauna,ita kuwa a 2,yace tashi ki dawo nan,sam tak'i tace a'a nanma na zauna ai,yace pls apple kizo zan mana pic ne anan,amma sam kunya ya hanata tashi,haka ya yashi yace inda take ya zauna batare da jikinsu ya had'uba ya musu pic. Thankyou yace da ita tare da nuna mata pic d'in,murmushi tayi tare da karb'an wayan dan sunyi kyau sosai,yace amma fa kin fini kyau dan haka zanyi deleting,tace a hakan pls ka barshi wlh kama fini kyau,yace to shikenan tare da mik'ewansu a tare. Kallon juna suka tsayayi,take ta kawar da kanta gefe tace gida yayi kyau sosai Allah yasa mu shigo a sa'a Allah kuma ya k'ara arziki ya karemu daga dukkan....hannunsa taji acikin nata yasa ta kasa k'arasawa,shi kuwa yace ameen aunt. Hannunta take k'ok'arin gwacewa daya lura da hakan seya sake mata hannun yace sorry apple haka kawai naji cewa in rik'e hannunki,kanta ta d'ago suna kallon juna atsarge tace muje,murmushi yayi tare da cewa to muje,gaba tayi yana biye da ita a baya,sedaya kashe komai sannan ya fito harta fita waje. Sunanta ya kira aunt,juyowa tayi tare da kallonshi,yace zo muje gida flower naki,da murna taje suka bi gefe sam takasa b'oue farincikinta sebin flower d'in takeyi da fararen hannunta hakwaranta tas a waje shikuwa se pic yake mata batare data saniba. Can kuma ta hango wani guri mai kama da swiming pool,amma kuma taganshi a rufe da wani glass kana iya ganin cikinsa,sosai taji dad'i tare da kallonshi tana murmushi,gwalo yayi mata da harshensa tare da dannan gefen pool d'in seya bud'u. Sam ta kasa boye murnanta tace thankyou so much peach,mirmishi yakeyi tare dajin dadin yadda yaga tana farinci seyaji dad'i sosai har cikin zuciyarshi yace Always my jealousy. Yake ta b'ata rai tare da mik'ewa tayi hanyan komawa gun mota,da sauri harda gudunshi yasha gabanta tare da had'a hannayenshi gu d'aya yace _pardon me apple_, k'itayi zata wuce ta gefenshi se yayi saurin rik'o yatsan hannunta guda 2 yace inyi tsallen kwad'o? D'aga kanta tayi alaman eh,aiba b'ata lokaci ya saki yatsunta yahau yin tsallen kwad'on se dariya takeyi sannan tace ya isa haka shikenan har a yanzu dariyan takeyi,shi kuwa se kallonta yakeyi yana mirmushi. Daidai nan abdallah yazo yace gaskya d'akina yayi kyau sosai nagode,manosh yace bakomai d'an aunty kafi haka aguna. Abdalla yace naga swiming pool amma na ganshi a rufe kuma na kasa bud'ewa,manosh yace na rufene saboda bana so kowa ya fara shiga se auntynka,amma muje in bud'e maka tunda ta tab'a ruwa,murmushi abdallah yayi suka tafi acan manosh yayi ta mishi pic sannan sukayi tare,maryam taga shuru yasa ta lek'asu taga se selfi sukeyi,abdallah yace auntyna kizo muyi tare,amma sam tak'i,dole abdallah yasa taje manosh yanata d'aukansu sannan suka kama hanyan komawa girei bayan sayayyan da sukayi a shop. Godiya sosai abdallah yayi dan kayayyaki masu tsada manosh ya sake saya mishi. Maryam ma ta tayashi godiyan sannan sukayi sallama ya tafi ita kuwa taje tanata baiwa maman lbrn gidan manosh. Dad'i sosai mamaji tare dayin addu'a. Washe gari alhamis su miher harsun fara shirye shiryen biki lubna ce mai tayata. Su rash sukace sam su dole ayi biki amma maryam tace babu abunda zatayi. Bayan isha abdallah yazo sunata hira da maryam yace wlh aunty kaina ciwo yake min kid'an kamamin mana,nan ta kama mishi kan da addu'a har mama tana cewa toga paracetamol d'an aunty ka daure kasha,yace a'a kamun da aunty taminma naji dad'i seda safe,aunty tace to Allah ya sauwaka yace ameen. Da asuba yau jumma'a bayan an idar da sallan asuba,abdallah yayita karatun qur'ani mai girma da daddad'an muryansa mai k'arawa mai sauraro imani. Yakai 1hr yanayi sannan akayi wa'azi aka watse,gidansu maryam ya shigo suka gaisa tace kaji karatunka na yanzu a wayata nayi recording,mirmushi yayi yace kai aunty keda ma naki yafi nawa shine kiketa tara muryana a wayarki,tace eh har gobe kiran sallanka yana cikin wayan manosh,dariya yayi yace Allah yabarmin ke auntyna,tace ameen nima Allah yabar min kai,babane ya shigo yace abdallah ya jikin dai,yace ai naji sauk'i baba,baba yace Allah ya kara lfy,yace ameen. Seyace aunty naji su aunty rashida sunce zasuyi biki sosai ina fata dai banda ke ko? Tace eh bandanikam walima kawai su captain zasuyi,yace kin kyauta aunty irin wannan karatun zanyi a wannan ranan Allah ya kaimu lokacin kawai aunty,tace ameen sannan ya fita. 8:40am mama tazo d'akin maryam tana cewa maryam yau kuma kece mai baccin safe,toki tashi maryam *innalillahi wa'inna ilaihirraji'un* da sauri ta farka tace mama lfy,mama tace maryam yau kuma munyi rashin ABDALLAH seta fashe da kuka tare da rik'e maryam gam. Maganan kamar a mafarki tajishi,amma yadda taga mamanta ta riketa ta kuka tasan cewa ba mafarkibane gaskyane, *innalillahi wainna ilaihirraji'un*itama take furtawa tare da kallon mamanta tace wani abdallan kenan mama kina nufin abdallah nah? Da sauri ta mik'e bata jira amsar mamaba ta zurma himar nata tayi waje. Jama'an data gani a wajene tun daga bakin masallaci har k'ofar gidansu abdallah yasa ta k'ara fashewa da kuka tana wuce mutane batare datasan cewa wandon sleeping dress bane a jikinta,harta k'araso k'ofar gidan dakyar ta samu hanya ta shige ciki. Kukan rash ta fara jiyowa dana mamansu,rash ta mik'e ta rungumeta tana cewa shikenan abdalla yatafi yabarmu maryam innalillahi wa'inna ilaihirraji'un.... zama sukayi sunta kuka sosai,hiransu na d'azu kawai taketa tunowa a zuciyarta da kuma dariya yayita sasu ita da manosh lokacin da sukaje ganin gida,nan ta sake fashewa da kuka tana cewa ashe daman bankwana muketayi dakai d'an aunty,innalillahi wa'inna ilaihirraji'un suketa nanatawa tare da cewa Allah ya jik'anka abdallah yasa ka huta. Yah ibrahim ne da friends nashi seke fitowa da gawan abdallah bayan sun gama mishi sutura. Koda suka fito daga d'akin ya ibrahim kuka sosai jama'a keyi,da sauri maryam ta d'ago da kanta ai kuwa setaga gawan a hannunsu suna zuwa gun mama dashi,tunda yah ibrahim ya had'a ido da aunty seyaji hawaye yazo mishi ido amma ya daure ita kuwa kuka sosai sukeyi ita da rash. Mama ta matso tayita mishi addu'a,rasha da maryam ma suka matso se kuma baban maryam d'in tunda shine matsayin ubansu dukkansu. Haka aka d'auki gawan aka fita dashi yayinda jama'a suketa kuka akai mishi sallah,batare da b'ata lokaciba aka kaishi gidansa na gaskya hardasu manosh wato "the 5 emms" dan yah ibrahim ya tura musu texs d'in rasuwan k'aninshi abdallah kuma d'an autansu. Yah ibrahim ya kasa barin kabarin se hawaye yakeyi akan kabarin,friends nashine taredasu marwan suka d'agashi jiki sanyaye suka dawo gida inda aka zauna kab'ar gaisuwa. Hmmm!rayuwa kenan,yau kaine gobe bakaibane. Kuduba dai kuga irin mutuwar da abdallah yayi,ran friday,kuma koda yabar gidansu maryam ya wuce gida hira sosai sukeyi da mama da yah ibrahim rash kam tuni ta koma bacci dan ko wani sallama basuyiba,in banda gaisuwa daya mata na safiya tace ya jikin,yace wlh na samu lfy. Koda suka gama hira dasu yah ibrahim alwala yayi yayi sallah sannan yace mama tea zansha,ta had'a mishi yasha ya ajiye cup d'in yaci gaba da addu'oinshi bayan nan seya kwanta akan sallayan a d'akin yah ibrahim dama tare suke kwana,tofa kwanciyan kenan dabai tashiba. Yah ibrahim kuwa yana gum mama suna hira,bayan sun gamane ya dawo d'akin yace abdallah a k'asa kuma,tashi ka kwanta akan kafifar mana,shuru bai tashiba,kuma kowa yasan abdallah sam bayida nauyin bacci,hakan yasa ibrahim tab'ashi amma seyaji baya numfashi. Salati ya kamayi tare da girgiza abdallah amma babu abdallah ayau ya rigamu zuwa gidan da duk wani musulmi seyaje dazanar lokacinmu yayi. Allahu akbar,Allah yasa muyi irin rasuwan abdallah ameen. Ana zaune agun makoki kowa juki yayi sanyi,idan aka tuna da karatunshi na asuba cikin suratul muh'd. Kai jama'a duniya ba komai bace wlh,Allah ya gafarta mana kurakurenmu ameen. Manosh se kallon hotunanshi yakeyi a wayanshi yana tsaye tagun pool ya d'aga yatsan hannunshi d'aya wato ALLAH WAHID. kwalla manosh yaji a idonshi amma sam yaqi zubar dasu,dan bayaso azabtar da abdallah,domin shi kuka ga mamaci azabace ake k'arawa mamacin. Jama'a sosai abdallah ya samu kowa alkhairai kawai kakeji abakinsa akan abdallah,hakan yasa yah ibrahim farinciki sosai,domin shaidar duniya itace zata bika har lahiranka. 11:00am su manosh suka shiga cikin gidansu rash,inda suke zaune a rana suka shigo da yah ibrahim sukayiwa mama gaisuwa dakuma rash harma da maryam,dan dole agaida maryam saboda indai kasan abdallah tofa dole kasan maryam dan kowa shaidane akan k'aunar da take tsakaninsu. Rash da maryam basu iya amsa gaisuwanba banda kuka da sukeyi har'yanzu,haka suka fice tare dayiwa baban maryam gaisuwa sannan suka tafi. Haka dai akayita zuwa gaisuwa mutane ma'a magana. Yau monday yaune uku dan haka su manosh da iyayensu sukazo hardasu dad,akayi addu'an sannan sukayi musu gaisuwa suka wuce. Da hantsi su mum d'in manosh danasu marwan harda miher da lubna sukazo gaisuwa. Kukan da rash takeyi yasa duksuma suketayi. Miher tace ina yah ibrahim muyi mishi gaisuwa,samira ce ta kirashi yazo suka gaisa harda lubna,tausayinshi ya kamata setaji sabon k'aunarshi yana shiganta a hankali saboda wannan shine ranar farko da suka fara ganin junaeye to eye,dukda dai dama tayi mishi gaisuwa a waya kuma tagayamishi cewa zasuzo ranan uku. Yace mun gode sosai Allah ya bada lada,sukace ameen sannan ya gaida mum nasu ya fita waje. Rayiwa kenan yau wenesday bikin su maryam saura 2dys kawai. Manosh ya kira maryam a waya haryau kuka takeyi,yace pls apple kiyi hakuri kibar kukan,batace mishi komaiba se dan Allah ina neman alfarma a d'aga bikinmu se zuwa wani lokaci pls? Shuru yayi yace ok apple zanyiwa baba magana kinji,tace nagode sannan ta katse wayar. Manosh ya sami mahaifinshi da zance amma se mahaifinshi yace munyi maganan da iyayensu amma sunce baza'a d'agaba tunda an sanar,sannan mamacin bazai dawoba sedai idan akwai wani biki da zakuyi to duk kuyi canceling nashi saboda rasuwan. Manosh yace to dad mungode sannan ya tafi tare da sake kiran apple ya gaya mata,aise fashe da kuka sosai wanda ya d'aga mishi hankali da sauri ya katse wayan cike da damuwa ya kira marwan suna magana,marwan yace eh wlh ibrahim ma cewa yayi kawai ayi bikin baza'a d'agaba kuma wlh nima naso a d'aga. Manosh yace to yaushe zamuje girei,marwan yace anjuma ba,manosh yace dama ba'yi musu jeren kichineba kud'in nake son bawa apple ta sayi kayan kichine sannan suje suyi jere amma yanzu komai ya tsaya kenan,marwan yace sedai muba su mum kawai su k'arasa mana dan kaga ba time yanzu gaskya. Haka kuwa akayi a ranan mum da 'yan'uwansu sukayi sayayyan kayan kichine abin se wanda ya gani aka shirya komai tas zuwa 8:pm suka gama komai aka rufe gidan. Ran alhamis da safe bayan an gama yiwa miher lalle tasa driver yakai mai zanen lallen har girei dan ayiwasu maryam rash da samira. Dayake tana sauri nan danan ta musu ta gama zuwa azahar ta gama musu,maryam tace nawane kud'inki,mai lallen tace an riga da'an biyani zan koma,nan driver ya maidata gidansu miher aka biyata kud'ade masu yawa aka kaita gun zahida da amina ma ta musu. Bayan la'sar angwaye sukazo harda yusuf angon amina. Amare suka fito amma sam babu wata walwala a fiskarsu,angwayen basu damuba dan sunso a d'aga auren amma sam ank'i. Bayan sun gaisane kowanne yaja fefe da matarsa suna magana,yayinda majid da muhsin da yusuf suke gu d'aya da yah ibrahim suna magana. Manosh yace apple,shiru tayi dan sam setaji bata son auren. Yace babu wani abu da kike buk'ata,tace babu komai tare da kwalla a idanunta,ledan hannunsa ya mik'a mata dan dole ta karb'a yace kije gida zamu tafi muma amma pls kibar wannan kukan,batace komaiba ta wuce gida batare data musu sallama ba. Manosh jikinsa a sanyaye yace wlh ibrahim aurennan da d'agashi akayi se nan da 2month,gabad'ansu baso sukeyiba wlh mutuwar abdallah kamar yau akayi suke jinta a jikinsu,muma kuma haka wlh,muhsin yace wlh kuwa. Ibrahim yace haka Allah yayi karku damu Allah yayi mishi rahama,suka amsa da ameen sannan suka tafi. Bayan isha manosh ya kira apple,tace kayi hakuri pls da abinda nake maka ba laifina bane,yace don't worry apple am okay with everything kinji,wlh naso abar auren amma hakan baiyuba,tace hakane nagode,yace kidena min godiya apple am sorry for d lost of our abdallah,shuru tayi hakan ya tabbatar mishi da cewa kuka takeyi,yace apple are you okey? Tace "yeah am fine" cikin muryan kuka tace peach gobene fa abdallah zaiyi karatu a walima,ashe fad'a kawai yakeyi...manosh yace pls stop it apple,babu abinda zai canja zauyi walimar kuma karatun abdallah zamu saurara agun insha Allah. Tace thankyou so much peach,yace "anything for apple" _i love you so much_,tace me too. Dad'i yaji yace ki huta kinji gud nyt,tace thankyou. Lubce agun doctor da safiyar friday taje ayi mata gwajin jini ko tana d'auke da H I V. Amma sam babu komai Allah ya kareta,murna sosai tayi tare dayiwa Allah godiya,bayan ta kira yah ibrahim ta gaya mishi komaine,seta kira maryam ma. Murna sosai maryam tayi tace shikenan barka lubna,tace nagode maryam bazan manta dakeba sannan ina tayaki murnan zama matar bro manosh,maryam cikin hawaye tace nagode. Bayan sallan juma'a aka d'aura auren masoya 6 a babban masallacin jumma'a dake jimeta,inda angwaye sukasa jallabiya ash da lullub'i irin na larabawa,sunyi kyau sosai kuma suna cikin wani ni'ima mara misaltuwa amma dukda haka manosh da marwan akwai damuwan rashin abdallah sossi a fiskansu,bare kuma da suka san halin da matansu suke ciki a yanzu haka kuka sosai sukeyi an kasa rarashinsu dan ansanma bajin rarrashin zasuyiba dan haka akabarsu suyi mai isarsu... . Hankalin manosh ya kasa kwanciya seya sake kiran maryam,daidai lokacin da yapendo ladi tayita mata nasiha har tayi shuru sannan ta barta. Wayan ta d'auka tare dayi sallama,yace aunt ina fata kin dena yin kukan,tace eh,yace gud pls kiyi hak'uri komai ya wuce da akwai yadda zanyi inganki yanzu dana zo,tace bakomai,yace inatayamu kasancewa miji da mata yau,murmushi tayi tace nima haka,dad'i sosai yaji yace gaskya an cika sosai dayake kuma jumma'a mun samu jama'a harda wanda ba'a gayyacesuba,mirmushi tayi tace to Alhamdulillah ina gaida angwaye,yace apple,tace na'am,yace i luv u apple,wani iri taji yadda yayi maganan tace me too. Yace semunzo anjuma ko akwai abinda kike bukata,tace eh akwai yace menene,tace flower,murmushi yayi yace zan kawo miki anjuma idan nazo d'aukan matata,tace da kanka,yace yes ba matatabace,tace eh amma ai da manya zamu,zauna a motan,yace a'a nidai dagani seke,dariya tayi tace a'a nidai manya nafiso,ok bakya son inkaiki ko,toshikenan nibazan zobama nayi fushi. Tace haba fushi kuma dani,yace yes se anjuma bari mu gaisa da friends na dad,tace ok pls karka manta da flowernah,yace indai bazan manta dakeba to hakama flowern,murmushi tayi shima haka sannan sukayi sallama. Nasiha sosai akayiwa amare harma da angwaye musamman manosh ance dole yabar maryam taci gaba da karatunta,yace dukya amince harda sa hannu kuma ya rubuta cewa maryam itace matarsa ta farko kuma ta karshe babu k'arin aure tare dasa hannunsa dana mahaifinsa akabawa babanta takardan da kuma malamanta se kuma iyayen manosh d'in. Da dare bayan sallan isha aka had'a walima ta maza agu d'aya, inda akasa karatun abdallah ne kawai yake tashi agun ga malamai da angwaye da abokai dadai jama'a sosai,masu kuka sunata kukansu,harda su maryam dan angwayen sun kirasu a waya donsu saurari walimar. Karatun abdallah yakai awa daya sannan malam balalau yayi musu wa'azi sosai tare dayiwa abdalla addu'oi akaci abinci maiji da lfy aka sha aka k'oshi sannan aka rufe taro da addu'a. Bayan an d'an watsene aka fara shirin zuwa d'aukan amare. Nidai bazan iya irga motocin da sukazo d'aukan maryam rashida da kuma samiraba,dan tun daga titin daya shigo unguwansu maryam wata *holmare*acike yace tun daga k'arshen layinsu har kan titi,wasu motocinmma emty suka koma. Ko wacce amarya da manya aka had'ata wanda yapendo ladi itace k'anwar mama maryam,se kuma goggo hafsatu itace k'anwar baban maryam,dayake maryam mai jama'ace hakaaka wuce da kowace amaryam katafaren gidanta tare da jama'anta. Masha Allah kawai kakeji kota ina ana yaba gidajen amaren,tare da wanke ido suna kallo. Abokin manosh ne yayi musu jagora har sama inda d'akin maryam yake,shi kuwa manosh ango yana tajin farinciki sosai a ranshi yau ya mallaki maryam apple nashi se godiya yakeyiwa Allah. Maryam tana zaune a gadonta na alfarma ita kanta tana cikin farinciki sesai akwai damuwan rashin abdallah wanda har a yanzu kuka takeyi data tuna zuwansu gidan tare. Bayan anga gida anyi san barka masu cire kauyanci sunyita fama se dariya akeyi masu d'aukan pic sun d'auki ko ina a gidan,gefen manosh ne kawai basuje dan a rufe yakema. Haka aka sake maidasu girei se mutane kad'anne kawai a gidan amaren,sayayya angwaye sukayiwa amare da kuma wanda suka rakosu nan aka kawo musu,inda abokin manosh yace wannan wai na amaryarmuce,wata ta karb'a tare dayin murmushi tace to amarya tagode sannan ya tafi ita kuwa taje ta kaiwa maryam a d'akinta. Koda maryam ta bud'e amincine a take away ga kuma nama mai zafi da drinks,dama yunwa takeji dan haka ta taci sosai tayi hamdala gashi naman yayi mata dad'i. 11:00pm manosh ya kira number maryam ta d'auka lokacin su yapendo sunyi bacci dukkansu a d'aya d'akin bak'in da kuma palonta,ita kad'ai ce a d'akinta se friends nata 2 koma ince 'yan'uwanta yaran yapendonta da kuma goggonta sune mazaunin k'awayenta. Ta d'auka tare da cewa hello,yace apple kinyi bacci ne,tace zanyi dai,yace su goggo fa,tace duk sunyi bacci,yace ke kad'aice idonki biyu? Ta juya ta kalli nafisa da hadiza da suke kwance a k'asan kafet suna waya da mashinshinansu,tace eh sedai kawayena biyu sune idonsu biyu,yace ok ina son ganinki pls,tace to kana ina,yace ina d'akina na k'asa,tace to ina zuwa tare da katse wayar. Nafisa da hadiza sukace wato bazai iya hakura mu tafiba gobe ko,kunnuwansu maryam taja tace kawai danyace inje shine har kuke fassara wani abu,to Allah ya shiryeku ta wuce a hankali dan kar su yapendo suji,su hadiza kuwa se dariya suke mata suna binta da kallon tsokana. Da sallama ta shiga,ya amsa yana zaune akan gadonsa da kayan ball masu dogon hannu. Tana tsaye tace gani,kallonta yakeyi tun daga k'asa har sama,dan rigan baccine a jikinta riga da wando dogo kuma himar nata har k'asa ya sauka sedai yana iya hango kayan jikin. Kunya taji sosai kanta na agefe,yace bazaki k'arasobane,ahankali tace daga bakin gadon ta zauna tare da cewa gani,yace fruits nakeso ki yankamin pls aunt,murmushi tayi tace to ina suke,yace nakai miki kichine,tace ok tare da mik'ewa ta ta fita cikin jin kunya shi kuwa yanata binta da kallo. Kichine ya burgeta sosai,da irin abubuwan dake ciki,tirai k'arami ta d'auko ta goge da karamin towel data gani an jerasu dewa sannan ta d'auki wuk'a ta yanka mishisu kamar yadda ta saba sedai yau batayi zanen fiskanshi dasuba ta wanke hannu takai mishi tare da sallama. Lokacin yana gyara gashin kansa seya juyo tare da k'arasawa gunta ya karb'eta yana kallon friuts d'in ba amar yadda ta saba mishi,kallon juna sukayi a tare suna rik'e da tirai d'in,kunya taji se tayi saurin kawar da kanta gefe tana murmushi,yace rik'e kayanki nibazan shaba tunda bakyaso inshane,rik'e tirai d'in tayi tace kayi hakuri bawai hakabane,yace banci abincibafa friuys d'in kawai nafibuk'a kumani wannan yamin kad'an,murmushi tayi tare da juyawa ta fice,shima murmushin yakeyi yana kallonta. Bayan 2minit ta dawo ta ajiye mishi akan stul d'in mirrow shi tana kallon fiskanshi,se murmushi yakeyi dan kuwa tayi zanen fiskanshi da friuts d'in abin yana birgeshi sosai. Kallonta yayi tana tsaye bata zaunaba,hannunt a ya kamo yace bazaki zaunabane,tace eh zan komane,yace ina kenan? Tace d'aki,yace bazakije ko inaba anan zaki kwana,k'irjinta ya buga tace a'a nidai zan tafi sakeni dan Allah,ai kuwa seya janyota ta fad'o jikinsa kan cinyarsa,hannayenta tasa ta rufe fiskanta dan kunya dataji,murmushi yakeyi tare dashan fruits nashi baice da ita komaiba. Kunya sosai taji,gashi ta kasa tashi kuma tak'i bud'e fiskanta tana zaune kan ciyarsa,setaji yasa hannunshi akanta ya manna kanta da k'irjinsa yace idan bacci kikeji tokiyi baccinki ajikina kinji,tmaryam kamar ta nitsi dan kunya aranta tace qato dama manosh ya iya soyayya haka,tace wlh inaso in koma d'akine,bana so su yapendo susan nafito,yace saboda me,aiko sun sanima bazasuce miki komaiba sunsan na zama mijinki yanzu. Tace dan Allah ka barni in tafi,yace tosekin bud'e fiskarki,ba musu ta cire hannayenta amma tak'i su had'a ido,shidai friut kawai yaketasha bayama kallonta sam,hakan ya bata daman satan kallonshi,murmushi yakeyi da sauri ta sunkuyar da kanta,yace aibase kinyi satan kallonaba kiyita kallona bakomai na zama naki yanzu,kunya taji tace pls ina so in tafi kayi hakuri,yace zaki tafi amma sena gama shan friut,shuru tayi tare da juyawa tana kallon friut d'in wanda ko rabi baiyiba,kanta ta d'ago tana kallonshi tana ganin yadda friut d'in yake wucewa a mak'ogoronshi,d ariya yayi tare da sunkuyo da kanshi suna kallon juna,tayi saurin kawar da kanta shikuwa yace meyasa kike son kallonane apple nifa banso wlh,ita dai batasan meyasa bayaso tadinga kallonshiba,tace to kabarni in tafi bacci nakejifa,yace ainagaya miki sena gama kozaki kwanta akan gadon inna gama se'in rakaki,tace a'a dan tanajin dad'in turarenshi sosai kuma bataso ta kwanta kar bacci ya d'auketa. Manosh yaci gaba dashan friut tana satan kallonshi a hankali,fiskanta taji ya rik'o batayi zatoba yace banace miki banason kina kallonaba, tace bazan sakeba,yace b'ude bakinki in baki kankana,tace nakoshi,yace idan baki shaba anan zaki kwanafa,ido ta d'ago tana kallonshi,yace yes am serious apple,ba musu ya d'auko yankakken apple yasa a bakinshi sannan ya rik'o fiskanta suna kallon juna,kunya taji kuma babu yadda zatayi wani irin kallo mai kashe jiki yake mata hakan yasa ta nutsu,ya kawo bakinsa mai d'auke da apple d'in daidai saitin bakinta wanda ita kanta basan lokacin data bud'e bakinta d'an kad'an yasa mata apple d'in yana gutsuransa ahankali ita kuwa rufe idanunta tayi tana jinshi saura kad'an abakinta seya cire bakinshi yana kallonta idanunta a rufe dan kunya da wani yanayi da takeji,idanunta ya tsunbata tare da kwantar da kanta a k'irjinsa yayi magana cikin wani irin murya yace kici sauran kinji,ba musu ta faraci idonta a rufe,sedata cinye tace" zan tafi" cikin wani murya mai shigan jiki,yace bazaki tafiba sena gama kiyi hakuri kinji,shiru tayi bata sake d'ago da kantaba tana kwance a k'irjinsa harya gama,seyace nagama to muje in rakaki? Kanta kawai ta d'aga alamun eh,yace to d'ago fiskanki,sam ta kasa,hannunsa yasa ya d'agota yana kallon fiskanta tare da tambayarta meyafaru apple,tace bakomai kamar zatayi kuka,kwantar da ita yayi akan gadon tare da mik'ewa ya kashe wutan d'akin,ya dawo gunta tare da kwanciya akanta ya rungumeta sosai,kuka ta fara tace dan Allah ka barni in tafi,yace apple ki dena kuka bazan miki komaiba kibarni a hakan "for some minit pls" apple ya k'arasa maganar akunnenta. Shuru tayi amma k'irjinta se bugawa yakeyi gashi yayi mata nauyi kafad'arsa take bugawa ahankali tana cewa peach pls cikin muryan shagwab'a,bakinsa kawai taji acikin nata yana kissing nata,ahankali itama ta fara kissing nashi se k'ara matseta yakeyi wanda shi kanshi yakejin tausayin. Jikinta taji ya jik'e yayinda take jin yadda abu yake fitowa daga jikin manosh,tsoro taji sosai,se bayan 2minit ya saki bakinta tare da barin jikinta ya kwanta a gefe yana sauke numfashi,da sauri maryam ta mik'e zata gudu yayi k'ok'arin kamo hannunta amma hartakai gun kofa,mik'ewa yayi ya cafkota tare da rungumeta sosai yace "thankyou apple" kiyi hakuri kinji,batace komaiba,seyayi peacking kunnenta yace i luv u apple,tace i luvu too,sake matseta yayi sosai sannan ya saketa tareda bud'e kofan yana rik'e da hannunta hargun steps sannan yace mata gud nyt,kai tad'aga mishi sannan ta hau sama dasauri yana binta da kallon sannan shima ya wuce d'aki ya shiga toilet yin wanka. Maryam taga harsu nafisa sunyi bacci,dan haka ta wuce toilet ta gama komai sannan ta fito ta mayar da kayan data ciren don karsu nafisa su mata tsiya da safe,sannan ta kwanta tana tuna abinda ya faru tsakaninta da manosh tace wato yanzu harya gamsu kenan a hakan tunda dai gashi yafitar da maniyi? Hmmm se kuma taji dad'i aranta tace wato dai ya iya soyayya amma shine kamar ba ruwanshi,murmushi tayi aranta tace i love you so much peach,da haka bacci ya d'auketa.............

 ANTIN YARA Page 52-55
.
Washe gari da asuba maryam ta tashi tayi wanka tare dayin alwala tazo tayi sallah sannan ta zauna shafa mai ta shirya tsap cikin maroon less daya mata bala'in kyau sannan taje suka gaisa dasu yapendo.
Hadiza da nafisa sukace amma dai jiya acan kika kwana yau da asuba kika dawo nan ko? Murmushi takeyi tare dace musu eh acan na kwana. Dariya sukayi sukace ehen dan har mukayi bacci baki dawo gaskya akwai aiki da captain d'innan naki,maryam tace bafa nason sa ido kun dameni wlh bari inmishi waya azo a maidaku kawai,dariya sukayi dukkansu tare da cewa base anzo kaimubama,zamu tafi da kanmu.
Nafisa tace bari inje naji ana kirana,da sauri ta fito taga abokin angone,bayan sun gaisane yace dan Allah kiyiwa amaryanmu magana captain yana kiranta wayanta a kashe,tace ok tareda komawa tace hmm wannan angonka wai kije ki bashi na safe ya kira wayarki a kashe,dariua maryam tayi tare da dukan nafisa tace wlh kina da aiki yanzu badama ya kirani seda wani abu?tace eh mana tome zai niki aidai ya hak'ura semun bar gidan. Maryam ta d'auki farin gyalenta mai kauri ta yafa tace kanki akeji 'yar sa ido sannan ta fita.
Ahankali take sauka daga saman,amma bata hangoshi a palonba,tace kodai yauma a d'akin yake? Daga bayanta taji yace apple,juyowa tayi ta ganshi sanye da kakin sojojinsa yana zaune kan daining. Ta k'ara inda yaja mata kujera ta zauna tare da cewa ina kwana,yace lfy kin yashi lfy tace lfy lau,yace yasu yapendo dasu hadiza,tace duk lfyansu lau.
Kallonshi takeyi da alamun tambaya ganinshi sanye da kaki,murmushi ya mata yace yadai,tace zakaje wani gurinne,ya rik'o hannunta yana wasa dashi da hannunsa masu laushi gashi sunyi sanyi yace eh zan fitane amma zuwa azahar zan dawo. Tace lfy dai ko,yace lfy lau sema alkhairi idan na dawo zakiji komai kinji,tace toh Allah ya taimaka Allah yasa ka fita a sa'a,yace ameeen thankyou sannan ya mik'e tsaye itama ya mik'ar da ita tare da rungumeta tsam,tace dan Allah ka bari idan wani ya shigofa,yace babu wanda zai shigama ki saki jikinki kinji,jin hakan yasa ta sake sosai a jikinsa tanajin k'amshi jikinsa.
D'agowa yayi yace kardai har kin fara bacci,mirmushi tayi tace bacci kuma anan,yace eh mana gashi naji kin sake kamar kin samu gado,kunya sosai taji tare da k'ok'arin janye jikinta amma sam yak'i,tace toni ka barni tunda har tsokanata kakeyi,yace nifa wasa nake miki,murmushi tayi tace to muje,ya saketa tare da cewa ina kenan,suna kallon junansu,taace muje ku gaisa dasu yapendo kafin ka tafi,yace apple a hakan tare da nuna jikinshi,tace eh mana aiba komai,yace wlh dai bazan iyaba tare da rik'o hannunta suka wuce d'akinshi.
Agado ya zaunar da ita tare da mik'a mata flower mai kyau yace naso in baki jiya amma sena mance har kika tafi,tayi murmushi tace thankyou tarr da sashi a hanshinta tana jin kamshinsa,yace bari in canja kaya idan naje muka gaisa se inzo inmaida kakin ko,tace to tare da mik'ewa zata fita yace ina zakije,tace zanje in sanar dasu zaka shigone,yace a'a kijirani mu tafi tare dawo ki zauna,bata soba amma haka taje ta zauna,shi kuwa wall drop ya bud'e ya d'auko jallabiyarsa fara tas mai adon glod sannan ya cire kayansa daga shi se boxer da singilet,sam maryam tak'i kallonsa harya saka jallabiyar yasa turare,inda taji kamshi seta juyo dan taga turaren nan suka had'a ido shi kanshi ya lura da abinda take kallo sannan ta juya,zuwa yayi har inda take yace kinason turarenne? Kai ta d'aga mishi alaman eh,murmushi yayi tare da bud'e gun ajiye turarensa ya d'auko mata guda d'aya a cikin kwalinsa yazo ya bata,murna tayi tare da cewa nagode,yace bakomai tashi muje,mik'ewa tayi kuma yana tsaye a gabanta da turarensa a hannunshi,yace bari in fesa miki nawa tunda a bud'e yake,to tace dashi sannan yahau fese mata harda cire lullub'inta da hannunshi yayita fesa mata yana k'arewa kirjinta kallo,kunya sosai tajitace aiyi haka,yace kin tabbata tace eh,nan ya ajiye turaren batare dayaje ko inaba sannan ya d'auki gyalenta ya yafa mata kamar yadda tayi,kallon juna sukeyi suna murmushi tace nagode,yace nima nagode sannan ya d'auki takalminsa yace muje yana rik'e da hannunta suka k'arasa gun steps. Anan ya tsaya ita kuwa ta haura yanata kallonta taje ta sanar musu sannan ta dawo tace mishi bismillah,yace ok sannan yaa rike da ita a kafad'a har suka isa gun k'ofa shinefa ya saketa tayi saurin wucewa d'akinta shi kuwa ya tsuguna yana gaishesu.
.
Maryam tana shiga ta ajiye turaren da kuma flower tana mai murmushi,hadiza tace tofa hmmm wato seda kika sakeyin wanka acan harda turare,tace eh d'in banafa nason sa ido ni inadai yazama mijina tofa ku kiyayeni kuma kar wanda ya bud'e turarennan bare kuma ku tab'amin flower yara sesa ido kuka iya tana murgud'a musu baki ta fice sunata binta da kallo.
D'akinsa ta shiga da sallam harya maida kakin sojojinsa,seya ganta da tea a hannunta da kuma bread ga blueband duk a tirei tasasu ta ajiye tace kasha kafin ka fita.
Hakan yayi mishi dad'i sosai data nuna kulawarta akansa,shi kuwa manosh baya shan tea mai madara amma dayake ta had'o bayaso yak'i sha haka ya zauna ta mik'a mishi cup d'in take yaji zuciyarsa tana tashi da madaran dayaji,yannunsa yasa a kirjinsa,tace lfy,yace zuciyanane yake tashi wlh,tace toko in had'o maka lipton kawai,yace wannan kuma fa,tace nise insha,yace ok sannan ta fita taje ta had'o ta kawo nishi. Ya karb'a tare da cewa thankyou yasha kuwa sosai tanata kallon yadda yake cin abinchi abin birgewa,kunnenta yaja yace banace miki banaso kallo ba,hannunta tasa akan nashi tace kayi hakuri nifa bakai nake kalloba,seya saki kunne yace nayi karya kenan,tace a'a haka yaci gaba tanata kallonshi harya gama. Sannan yace tokisha,tace zansha amma ba'a nanba,yace toshikenan nizan tafi,ta mik'e tace to Allah ya dado da kai lfy,yace ameen sannan ya mik'a mata kud'i yace karb'i wannan maybe zaki aiken wani abu kasuwa kodai wata buk'ata,tace wlh a'a bana buk'atan komai kuma akwai kud'i a hannuna sosai wlh,yace sam seta karb'a take ta b'ata rai tace ni wlh bana so wlh akwai kud'i a hannuna mai yawa,yace nawane,tace 70k,yace apple kin tabbata,tace wlh kuwa,yace toshikenan gadai kud'i anan ya nuna mata walldrop nashi yace idan kina da buk'ansu kina iya d'auka koma nawa kinji jealousy nah,nan ta b'ata rai yayi saurin rungumeta yace am sorry sunanne kawai yazomin a baki yanzu sorry my luv,shuru tayi,yace haba apple yanga zakiminne to shikenan na fasa fita mukwanta muyi bacci,ido ta zaro tare da cewa na hakura wlh,dariya yayi yace dama kina da idanu manya haka,kunya taji tace muje karkayi late,yace ok tare dasa takalminsa se kallonshi takeyi tanajin dad'i tare da godewa Allah,d'agowa yayi yace apple pls bana son yawan kallo kinji,itadai abin yana bata mamakiyi kuma taga da gaske yake,tace meyasa to? Yace idan na dawo zan gaya miki,tace to tare daci gaba da kallonshi,rungumeta yayi tare da tsotsar lips nata sannan ya saketa yace idan na dawo zan naidasu yapendo kinji,tace to sannan ya tafi ita kuwa ta d'auki tirai ta fice ta dawo ta gyara mashi ko'ina sannan ta rufo kofan ta taho da key d'in d'aki.
Lubna ce agun miher tanata kuka tace yanzu shikenan wanda zuciyata take k'auna ya zama mijin wata,kuka sosai takeyi miher amarya se bata hakuri takeyi tace haba lubna tunfa jiya kike abu d'aya,kiyi hakuri kibarwa Allah komai idan bro manosh mijinkine tofa dole seya aureki.
Lubna ta bud'e jajauen idanunta tace pls kidena zolayata nafasan irin k'aunar da captain yakeyiwa maryam,baya iya 5minit baiji muryantaba kuma bro marwan yacewa mum wlh manosh yayi alk'awarin cewa maryam ita kad'aice manosh yake kauna duk fad'i duniya. Miher tace hakane amma ai komai yana gun Allah ne bagun bro manosh,lubna dai sam tak'i se kuka takeyi tare dajin haushin maryam kuma ayanzu.
.
Azuciyarta tace wlh dabadan saddam ya cuceniba dasena auri manosh kota wace hanyace danni shi kad'ai nake so,ibrahim kawai dan dai asirina zai rufune badan ina sonshiba wlh,kai amma maryam kinyi sa'an samun miji kamar bro manosh,mik'ewa tayi ta shige toilet tanata kuka sannan ta wanke fiskanta ta fito miher sebinta da kallo takeyi tare dajin tausayinta gashi duk sunyi aure banda ita.
Abinci lafiyayya aka kaiwasu maryam daga gidansu manosh,na safe daban na rana ma daban.
Tunda manosh ya fita bai kira maryam ba se 3:37pm yace da ita albishirinki,tace goro,yace fari ko ja,tace fari tas kamar fiskarka. Murmushi yayi yace toshikenan ganinan dawowa nafiso inga fiskarki lokacin da nake sanar dake,murmushi tayi tace to seka iso.
Zuwa 4pm manosh ya iso gida,wayanta ya kira taje d'aki ta sameshi,ya cire kayanshi harya shiga wanka,kayan nashi ta nad'e ta mayar walldrop,sannan ta fito mishi da wanda zaisa. Tana zaune ya fito da towel a west nashi,sam tak'i d'agowa har seda yasa data fito mishi dashi yace nagode,tace dame,yace da fito min da kayan sawana,murmushi tayi tace kaci abincine? Yace nachi wlh acan akoshe nake apple "thanks for d care" zama yayi kusa da ita yace juyo kina kallona,ba musu ta fiskance,yace k'iran da akamin bana koai bane sena k'arin girma daga captain manosh zuwa asistan major,kallonsa tayi har cikin ido cikin mamaki tace kad'in,yace wlh kuwa, rungumeshi tayi sosai sedaya fad'i akan gadon. Kunya taji tayi saurin tashi tace kayi hakuri murnane yamin yawa,alhamdulillah Allah ya tayaka rik'o akan gaskya da adalci peach nah,yace ameen my luv tare da kissing d'in hannunta yace su yapendo sun shirya,tace eh tun d'azu,yace ok muje bari abokina yaje ya musu magana,tace to tare da komawa d'akinta.
Bayan isarta da 5minit abokin yayi sallama yace hadiza wai kufito muje inkun gama,tace to sannan ta gayawa su yapendo suka shirya tsaf suka fito,nan maryam ta fara kuka dataga zasu tafi a barta ita kad'ai. Su nafisa kuwa se zolayarta sukeyi haka suka tafi aka barta ita kad'ai agidan tanata kuka.
Manosh bai dawoba harse bayan magrib abokanshi suka rakoshi lokacin maryam tana karatun qur'an yashigo d'akinta da sallamarshi......
.
Gidan majid duk an watse amma banda lubna,tanata kuka tana jiran shigowan majid. Bayan ya shigone yaga motarta,yana shiga yaga se kuka takeyi,yace sis lfy kike kuwa meya faru? Nan miher ta bashi lbrn duk abinda yake damunta game da bro manosh. Shuru majid yayi tare da tausayawa lubna,yace amma sis kinsan kina sonshine shine koni baki tab'a gayaminba,idan bazaki iya gayawa marwan ba aini seki gayamin ko muhsin ko muh'd,gaskya ina tausaya niki sosai dan wlh lokaci ya k'ire yanzu tunda kinga manosh yayi aure,sannan kwata kwata captain bayi da ra'ayin yin mata biyu a rayuwarsa dan yana kaunar aunt fiye da tunani wlh sannan koda marwan d'in kika gayawa nasan hakuri zai baki danmune shaida akan irin k'aunar da manosh yakeyiwa aunt. Banaji ance ibrahim brothern su rash yana nemankiba,ai shima mutumin kirkine sis dukmun yaba da halinsa wlh ga addini zakiji dad'i sosai agunshi,amatsayina ya brothernki shawaran dazan baki shine kiyi hakuri ki cire captain a ranki dan wlh wahala kawai zakisha bazai yaddaba,dama ace ace baiyi aure bane toyariga dayayi aure sis.
Lubna cikin muryan kuma tace pls bro majid kayiwa daddy magana wlh ni shikad'ai nake so dan Allah ka taimakamin,tausayinta ya kama majid sosai yace kiyi hakuri sis amma gaskya nake gaya miki idan kikaci gaba dasashi a ranki to wlh zakisha wahalane kawai gara kiyi hakuri kici gaba da addu'a. Wayan manosh ne yashigo majid ya d'auka hello abokina yane,yace lfy lau ina k'anwata,yace gatanan,nan majid ya mik'awa miher ta karb'a tate dacewa hello bro,yace yakike,tace lfy ina aunt,yace gata zakuyi magana,nan maryam tace hello amarya,miher tayi dariya tace amare dai,tace ina ango majid,tace gashinan,maryam tace ok yadawo gida kenan shima,tace eh,maryam tayi murmushi tace toshikenan seda safe,miher tace to Allah ya bamu alkhairi sannan ta mik'awa majid,yace ango shikenan,manosh yace aunt ce tace waina dawo gida da wuri bayan ku baku komaba,shine na kiraka danta tabbatar da cewa kana gida,dariya majid yayi yace a isarmin da gaisuwa,yace tana jinka ai seda safe yace okey.
Majid yace lubna muje in maidake gida se driver ya dawo dani dan bazan barki kiyi driving a hakaba,cikin kuka ta mik'e suka tafi.
Manosh ne zaune kusa da maryam a d'akinta yace meyasa kikayi shuru agaban friends nawa? Tace tomezance aidai na musu godiya bayan sun gama jawabin ko,murmushi yayi yace to kici kazan mana,tace nifa ak'oshe nake,yace niban uardaba kici,tace wlh nak'oshi bazan ciba. Yace kinaso mu b'ata ko,ta e Allah peach akoshe nake,yace to shikenan nima bazanciba.
Kazan ta bud'e tasa musu a plate tace to bismillah seta d'auki k'oda taci,sannan shima yaci amma itakam bata sake cin komaiba se ruwa datasha.
Dama tunda yaje raka friends nashi ta shirya tasa rigan bacci dogo iya gwiwanta ya tsaya se hula dayake kanta mara nauyi,shi kuwa 3quater ce kawai ajikinsa jikinshi babu komai,hakan yasa takejin kunyanshi da kuma tsoronshi.
Bayan ya gamane seya shiga toilet nata da sauri ta kwace komai takai kichine tanata sauri ta dawo karya fito daga toilet amma setaga harma ya kwanta kuma yasa riga k'arami a jikinsa yayinda ya rufe rabin jikinsa da bargo.
Dad'i taji aranta tace Allah yasama bacci ya d'aukeka dan tsoronshi takeji sosai yaud'in. Ahankali ta kwanta gefe tare dajan bargon itama ta rufe dukkan jikinta dan d'akin yayi sanyi,sunkai kusan 10minit shuru kamar wanda sukayi bacci amma kuma idonsu biyu,juyowa yayi yana ganinta yayi magana batare daya kira sunantaba yace dawuta kike bacci ne,amsa tabashi batare data juyoba tace a'a,tashi yayi ya kashe wutan sannan ya koma ya kwanta. Bayan tayi addu'ointane ta tofe ko ina sannan tayi niyanyin bacci,shuru babu wanda yace komai har kusan 1hr,itadai maryam tanata mamakinshi sam baice suyi nafila ba,dan haka tayi niyan yin bacci abinta se taji yace wai bacci zakiyine,eh tace dashi,setaji yace bacci kikazoyi? Tambayar yayi mata wani iri amma setayi shuru kamar batajishiba,ya sake cewa dake nake *maryam*bacci kikazoyi gidanna,mamakine sosai ya kamata dajin irin kalaman manosh,gashima yau ya kira da sunan mum nashi kai tsayae wanda sam bai tab'a kiranta dashiba tunda suke.
Batada amsan da zata bashi dan haka tayi shuru tana jiran mezai k'ara cewa.
Sunanta ya kira a tsawace maryam! Ina miki magana kinajina,take tsoro ya kamata tayi saurin cewa naga kamar bacci kakeji shiyasa,yace aikin banza tare da tashi ya d'auki wayanshi yabar mata d'akin zuwa nashi d'akin. Maryam ta tashi ta kunna wutan d'akin tana mamakin abinda ya faru yanzu kamar a mafarki take gani. Wani zuciya yace ta tashi ta bishi,wani zuciyan kuma yace mata kwanta abinki,haka takasa kashe wutan ta kwanta tanata tunanin abun aranta daganan bacci ya d'auketa ba ita ta farkaba se asuba.
Koda maryam ta farka bataga manosh ba,hakan ya tabbatar mata da cewa bai dawoba kenan a d'akinsa ya kwana. Mikewa tayi tayi alwala tayi sallah tare dayin addu'ointa sannan ta wuce d'akinshi dake sama ta shiga da sallama,yana kwance akan sallaya inda yayi sallah,harma ya fara bacci seya farka tare da amsa sallamarta idanunshi sunyi jah. Tunda taganshi tasan cewa baiyi bacciba jiya,sunkuyawa tayi har k'ara tace ina kwana,yace lfy kin tashi lfy,tace lfy lau yanaga idanunka sunyi jah haka,yace bacci nakeji sosai apple kuma na gaji wlh ban ganewa jikin nawaba,tace subhanallahi bakayi bacci jiyabane? Jajayen idanunsa ya d'ago yana kallonta yace bakin barni nikad'aiba kink'i kizo,mamaki sosai tayi tace muna kwancefa ka tashi ka fito peach kodai fushi kake dani dan nak'i cin kazan jiya,yace a'a taimakamin inhau gado pls apple,kallonsa takeyi kamar dai bugegge haka ta rikoshi ya kwanta tare da janyota jikinshi ya rungumeta yace i luve apple,wani sanyi taji a ranta ta kwanta lub ajikinshi.
Shuru taji alamun bacci yayi,ahankali ta d'ago da kanta setaga yayi bacci,mamaki abun yabata tace tomeya hana peach yin bacci jiya,abun ya d'aure mata kai sosai setayi yunk'urin tashi,amma sam ya k'ank'ameta da hannayenshi daya had'asu a bayanta,idan tayi yunk'urin tashi seyace pls apple let sleep okay? Tace okay peach amma na takuraka ai a hakan bari mu gyara kwanciya,sam yaqi hakata kwanta harseda baccin nashi yayi nisa sannan tajanye jikinta tare da rufeshi tanata k'are mishi kallo sannan ta fita zuwa d'aki itama baccin tayi bayanta gama tunani.
Manosh bai farkaba har se azahar,maryam ta damu sosai da irin baccinshi. Har aka kawo musu abincin safe dana rana duk yana bacci. Yana tashi yayi toilet yayi wanka tare da alwala yayi sallah ya shirya cikin kananan kaya ya fito,abincine jere akan daining na palourn shi amma seya wuce d'akin apple inda take kwance akan gadonta,shigowarshi yasata mik'ewa ya qare mata hannayenshi da sauri taje ta rungumeshi tana murmushi shima haka,yace kiyi hakuri apple inata bacci nabarki ke kad'ai yaushe kika tashi,tace tun lokacin dakayi bacci,yace wato kinmin wayoko,murmushi tayi tace muje kaci abinci mum ta aiko mana tun safe ga kuma naranama. D'aukanta yayi cak yayinda kunya ya kamata shi kuwa ko'ajikinshi har suka isa daining sannan ya ajiyeta akan cinyarsa ita kuwa ta zuba musu abinci tare da spoon 2,tana bashi yana bata abin sha'awa take ta mance abinda ya faru jiya sunci abinci sosai sannan sukasha fruit,ya sake d'aukanta se d'akinta can suka kwanta akan gado ita kuwa tana kwance a jikinsa.
Yace apple meya faru jiyane,tace bakomai,yace ya akayi banci amarcinabane,kunya taji sosai batace komaiba,ahankali ya fara shafata ita kuwa tsoro ta faraji,yace menene apple,tace babu,yace akwai mana gashi jikinki yana rawa,kina jin tsorone,kaita d'aga alamun eh,yace kidena tsoro bazan miki komaiba kinji? Shuru tayi tanajin yadda yake tab'ata,yawu ya had'iya tare da cewa yau kam ai zanci amarcina ko apple,kaita girgiza alamun a'a,murmushi yayi yace haba apple d'ina meyasa,cikin wata irin murya tace inajin tsoro,matseta yayi ajikinshi tare dayin k'asa da muryanshi yace kidena tsoro bakomai kinji,batace komaiba yace apple dakenakeyi,nidai banso,yace toni ai inaso apple bakya tausayinane,akunnenta yayi maganar a hankali qanda ya sake kashe mata jiki ta lume sosai ajikinshi,shi kuwa rikicewa yayi dosai aise yahau kissing nata tun tanajin kunya harta sake.
Da dare kuwa manosh yana d'akinshi sam baizo gun maryamba. Ita kuwa tayita jiran shigowarshi amma shuru har 9:30pm,kuma bataso takai kanta dan haka ta kwanta har tayi bacci baizoba aeda taji kiran sallah seta farka tare da mamaki yauma manosh a d'akinshi ya kwana kenan,abun ya fara damunta yanzu kam,bayan tayi sallah ne taje taga yana bacci tare da jallabiyarshi a jikinshi da alamu tunda yayi sallah ya koma bacci. Hakan yasa ta koma d'aki tanata tunani,gashi su samira sunbata lbrn yadda sukasha wuya agun mazajensu,dukdadai basu gaya mata komaiba amma tasan duk sunci amarcinsu inbanda rash da take period nata.
Hakadai manosh da maryam suka kasance har tsawon 3days batare da wani abu ya shiga tsakaninsuba.
Yaune kwana na hud'u kamar kullum maryam tace bari dai taje ta duba meyasa manosh baya zuwa da dare seda rana yayita romancing nata.
Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un ta fad'a tare da k'arasawa inda yake kwance yana juyi tare da rik'e cikinsa da hannayensa. Maryam ta rik'oshi tana hawaye peach lfy,meke damunka,hannunta tasa adaidai nashi tace cikinkane,cikin wata irin murya yace apple tashi ki tafi d'aki,tace meyasa zan tafi d'aki bayan gashi kanafa da ciwon ciki,ita a tunaninta dan yaga tanajin tsoronshine baya so ya kusanceta harya ja mishi ciwon cikin. Cikin kuka tare dajin tausayinshi tace peach dan Allah kayi hakuri wlh daga yau nadena jin tsoronka bansan ina cutar dakai har hakaba pls kayafemin.
Yace apple pls ki tashi ki fita! Cikin tsawa wanda sedata razata amma sam tak'i barinsa se kuka da takeyi tana tofa mishi addu'a a cikin nashi sannan ta cire rigan baccinta daga ita se wandon tace peach kayi hakuri wlh nadena daga yau,jinta a jikinshi kuma yaji babu riga yasashi tasowa idanunsa kamar atarugu yana kallonta rai b'ace,take tsoro ya kamata tace peach miye kuma haka kake min irin wannan kwallon,wuyanta ya kamo yana cewa wato ke gaki mara kunya 'yar iska ko,take maryam ta fara tari da kuma kuka tana magana da kyar tana cewa pea..ch menay..i ma..kane zaka kashe..nine.wuyana pea...ch sannan taci gaba da tari,flower gefen gadonshi ta d'auka ta buga mishi awuya sannan ya saketa da sauri ta gudu zuwa d'akinta tana kuka tare da sauke numfashi tana mamakin manosh,tabbas manosh yaba cikin hayyacinsa,riga ta d'auko a walldrop tasa setaji yanata buga k'ofa yana cewa ki bud'e kofannan *maryam* tsoro sosai taji da yadda yake buga kofan,toilet ta shiga tayi alwala tazo tayi sallah raka'a 2 ta zaunayin addu'a sosai.
Manosh ta jiyo yana cewa wlh idan kika yadda na bud'e kofannan tofa gawanki za'afitar. Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un taketa yi tare da addu'uoi. Yah ibrahim ne kawai ya fad'o mata arai,nan ta d'auki waya ta kirashi lokacin 10:5pm bugu d'aya ya d'auka baice komaiba tace yah ibrahim dan Allah kazo yanzu,akwai matsala amma pls karka gayawasu mama komai,hankalinshi atashe dajin yadda take kuka yayi saurin zuwa gun babanta yace abashi aron mota yanzu zai dawo,batare da b'ata lokaciba baba ya bashi keyn hondansa,dan motar maryam kam tun ran biki yakai mata shi gida.
15minit sega ibrahim a gate d'in gidan manosh,amma maigadi ya hanashi wucewa seda ya kira maryam ta waya ya had'asu kafin yabar ibrahim ya shigo da saurin. Jin tsayuwar mota yasa manosh yadawo daidai, take ya fara cewa apple meyasameki ,meyasa kike kuka bud'emin kofan kinji apple, ita kanta taji sauyin mura tattare dashi, mamakine ya kamata amma sam tak'i bud'e mishi. Bugun kofan falon k'asane yasa manosh barin gurin yaje ya bud'e kawai seyaga yah ibrahim ne a tsaye suna kallon juna cikeda mamaki,manosh baisan babu riga ajikinsaba sedayaga irin kallon da ibrahim yake mishi sannan yalura da jikinsa dagashi se boxers.....
.
Bismillah yace da ibrahim,cikin jin kunya ya wuce sama domin sa kaya. Ibrahim ya zauna yana jiran fitowan maryam.
Bayan manosh ya sako jallabiyane yaje kofan d'akin maryam saboda kukanta dayakeji,take hankalinsa ya tashi yanta cewa apple pls apen d door,ahankali ta bud'e tana rakub'e ajikin kofa sanye da doguwar riga da kuma gyalenshi. Rungumeta yayi sosai dan ganinta wani iri,ita kuwa sam takasa sake jikinta se fama kwacewa takeyi,manosh ya lura da hakan yace apple meke faruwane meyasa kike kuka,kallonshi ta tsayayi cike da hawaye tace bakaivabe ka shak'eni kace zaka kasheni dak'ar na kwaci kaina agunka dubi wuya kaga yadda kamin peach mena maka hakane, kallon wuyanta yake ga alamun hannun mutum kuma yayi jah shatin hannun ya zauna a wuyanta sosai.
Hannu manosh yakai yana tab'a tare da cewa apple ni kuma,yaushe na miki hakan,kallonshi ta tsayayi cikin mama da kuma tsoro tace ka matsamin zanje gun yah ibrahim,se anan ya tuna da yah ibrahim yazo,tace nina kira yah ibrahim a waya nace yazo dan ka biyo har nan kashe idan ka shigo kasheni zaki nikuma ina jin tsoro shine na kirashi. Rungumeta yayi yana magana cikin nadama yace apple wlh bansan komai akan abunda kike gayaminba pls apple kiyi hakuri karki gayayawa ibrahim komai,yaushe akayi airen har za'a fara jinmu,pls apple wlh niban miki komaiba taya za'ayi in miki haka kuma? Itadai gabad'a bata gane mishiba dan haka tace to muje gun yah ibrahim,yace kimin alkawarin bazaki fad'a,shuru tayi tace muje bakomai,nan suka firo a tare tana sauka k'asa tayi gudu taje inda ya ibrahim yake ta zauna kusa dashi tare dayin kuka tace yah ibrahim ka d'aukeni mu tafi gida wlh kasheni zaiyi kaga abinda yaminfa.
Afusa ibrahim ya mik'e dan yasan maryam bazata tab'a mishi karyaba,yace captain meke faruwane,metayi haka da irin wannan shatin dake wuyanta? Manosh ya juya a sanyaye yana kallon maryam yace haba apple yanzu haka zakimin,wlh ibrahim niban mata komaiba meyasa kikamin haka apple? Maryam tana kuka tace wlh yah ibrahim shine,sedana buga mishi flower a wuyansa sannan ya sakeni wlh kaine peach babu yadda za'ayi inyi maka karya wlh yah ibrahim cewa yayi zai kasheni kuma wlh banyi ishi komaiba. Manosh kamar zaiyi kuka se rantsuwa yakeyiwa ibrahim yace shi wlh baiyi mata komaiba,ibrahim yace yanzu maganan waye zan kama acikinkune kaina ya d'aure wlh. Maryam tace yah ibrahim na tab'a maka karya,kuma menene ribana idan nayiwa mijina karya,wlh Allah shine ya shakeni tare dayin wasu maganganu wlh yah ibrahim ba karya nake mishiba. Manosh yayi shuru danya rasa mema zaice,ibrahim ya kira marwan a waya yace kazo ina gidan manosh yanzu pls. Marwan ya kalli rash da take kwance ajikinshi yace kiyi hakuri zanje gun ibrahim in dawo kin,tace pls karka dad'e dan tsoro nakeji,yace bazan dad'eba my darling sannan ya shirya ya tafi.
Cikin k'ankanin lokaci ya iso cike da tunanin komeya faru ibrahim ya kirashi kuma gidan captain.
Da sallama ya shigo tunda yaga maryam kusa da ibrahim yasan akwai matsala,bayan ya zaunane yace captain,manosh yace yane,sannan suka gaisa da yah ibrahim.
Yah ibrahim yace marwan wani abune ya d'aure min kai sosai gaskya shiyasa na kiraka ko zamu samu mafita,marwan yace okey meya faru yana kallon maryam kanta a sunkuye,ibrahim ya gaya mishi,mamakine bayyane a idon marwan yace gaskya kozaka kwana kana gayamin bazan tab'a yadda abokina zaiyiwa aunty hakaba saboda mune shaida akan irin k'aunar da yake mata taya kuma za'ace manosh ya shak'eta da sunan zai kasheta a wani dalili? Ibrahim yace kamar yadda ka yarda da manosh ka kuma san halinshi,tonima haka na yarda da aunty na kuma san halinta bazata tab'amin karyaba wlh,sannan idan ka dubi wuyanta zaga shaidan abinda take fad'a,kuma lokacin dana shigo da kuma yanayin danaga captain ya tabbatar min acewa akwai matsala,kodai manosh yana da wata matsala ko kuma wani abu da baya so? Marwan yace gaskya bayi da wata matsala ko damuwa,abu d'ayane muka san baya so shine mace tayita kallonshi sam bayason haka. Ibrahim yace bayasan mace ta kalleshi,to saboda me? Marwan yace shidai haka nashi tsarin yake kuma komu bamusan dalilinba kawai dai yace mana shi kawai baya sone. Ibrahim yace to aunty kodai kallonshi kiketayi,dariya abin yabaiwa marwan yace to idan aunty ta kalleshi kuma seya shaketa? Ibrahim yace eh mana tunda dama baya so,marwan yace amma kuma harda aunty gaskya dai ban ganeba abokina meke faruwane? Wani irin mugun kallo manosh yakeyiwa maryam wanda tsoro ya kamata tace yah ibrahim kaga kallon da yakemin ko,wlh ni bazan zaunaba zan bika mu koma gida dan idan kun tafi kasheni zaiyi wlh...bata k'arasaba manosh yayi kanta tare da sake shak'eta yana cewa wlh bazaiyuba baki isaba wlh! Ibrahim da marwan suka mik'e domin tsaidashi,amma ina sun kasa ita kuwa maryam se tari takeyi suna kallon juna da manosh wanda babu alamun tausayi a fiskanci gashi su marwan sun kasa karb'armaryam a hannunshi kuma da hannu d'aya ya shaketa. Marwan yace manosh meke damunkane me kuma haka,aunty cefa saketa mana dama ashe gaskiya zaka kasheta kenan? Yace eh kasheta zanyi dan wlh baki isaba maryam kinyi kad'an,maryam ta fara fita hayyacinta tana magana dakyar tana cewa yah ibrahim zai kashenifa. Ibrahim yace marwan matsa baya,ba musu marwan ya matsa dan abin yabasu tsoro,ran yah ibrahim a bace ya bige hannun manosh da dukkan karfinsa take manosh ya fad'i akan carpet,ita kuwa maryam bayan ya ibrahim ta koma tare da rik'e mishi riga tana tari tace yah ibrahim kaganiko,wlh bazan zauna dashiba,tausayinta ya kamasu dukkansu,da sauri marwan ya d'auki wayanshi ya kira dad d'in manosh yace dad kazo gidan manosh akwai babban matsala. Shi kuwa ya ibrahim zaunar da maryam yayi akan kujera ya nufi kan manosh yanata karatun qur'an danya fahimci cewa balaifin manosh bane tun lokacin da yaga irin kallon da manosh yakeyiwa maryam kafin ya nufi kanta. Maryam dai kuka kawai takeyi marwan yace mata sannu,shi kuwa ibrahim karatu kawai yakeyi da k'ira'a irinta abdallah,hakan yasan maryam tsananta kukanta sosai fiye dana dah. Take manosh ya fara magana yana cewa wlh ibrahim idan ka shiga hannuna zakasha wuya,ni kake yiwa haka ko,wlh to maryam zatasha wuya aguna tunda ni kake wahalarwa,ibrahim dai baya ko sauraronshi karatu kawai yakeyi yayinda maryam ta tsaya dayin kukanta suna mamaki ita da marwan cewa dama manosh yana da aljanune kenan?
Sallamar dad da mum ne ya juyo da maryam da marwan,shi dai yah ibrahim karatu kawai yakeyi yayinda manosh yaketa surutai.
Maryam ta sunkuya k'asa ta gaishesu kanta a sunkuye suka amsa dad ya nufi gunsu manosh,ita kuwa mum mamakine ya shikata da abinda ta gani,yau manosh d'antane da aljanu?
daidai nan manosh yace kayi hakuri ibrahim zanyi magana wlh zanyi magana ka dena k'onani dan naga bakada imani ko kad'an,ibrahim yace kai kana da imanine,me manosh yayi maka haka kake k'okarin kashe matarsa? Yace nifa ka dena dangantani da naniji ni macece,ibrahim yace macece ke? Tace eh tunda na fara ganin manosh naji ina sonshi saboda kyawunsa yamin,toh tun a wannan lokacin na shiga tsakaninsa da duk wata macen dake fad'in duniyannan wanda bazaiji mace tamishibama bare har yace yana sonta,dukda dai baya wasa da ibadanshi amma senayi nasara akanshi,se rana d'aya ya had'u da wannan makiran wai ita maryam,ibrahim yace karki sake ce mata makira domin zan k'ona gabad'aya,tace saboda kana sonta kenan,meyasa ka bari akayi aurensu da manosh d'ina to tunda dai itace yarinyar daka dad'e kana kauna? Kunya sosai ibrahim yaji,yace ki dena min wannan shirmen ki gayamin abinda yasa kika shigo rayuwarsu,tace tunda ya had'u da maryam ya fad'a mata ra'ayinshi akanta,abin yamin zafi nayi iya k'okarina in cutar da maryam d'in kuma amma shegiya na kasa samun nasara akanta,ibrahim yace ta Allah batakiba tafi karfinkine shiyasa. Hhhh tayi dariya tace wlh batafi karfinaba ina tarata ne kawai,nice nake hana manosh kallon ko wace mace,shiyasa nasashi tsanan kallo,duk wata mace da zata dinga kallonshi tise nasa tsanan hakan agareshi,itama maryam d'in batajine ai amma soda yawa ina gaya mata cewa bana son kallon da takemin amma taqi,tunda akayi auren banbar manosh yaje kusa da maryamba,duk lokacin dayayi yunk'urin zuwa se'in rikitashi inyita bashi wahala,sena tabbata yaji jiki sannan nake barinsa idan ya farka da asuba kuma garau yake se kuma wata daren,dan bana barin yazo d'akinta sam itace take zuwa gaisheshi da safe,shine yau ta ibi kafafunta taje gunshi daidai lokacin da nake bashi wahala,yayi iyakar kokarin yaga ya hanata karasowa inda yake,amma dayake ita d'in mai taurin kaine sedata k'araso dan taga halin da yake ciki,shine na shike jikinsa nake son kasheta domin in rabata dashi..
Jikin kowa a palon yayi sanyi tare dajin mamakin abinda aljanan take cewa.
Ibrahim yace to ina gargad'inki daki fita daga jikinsa kona k'onaki,tace wlh bazan fita ibrahim ina tausayinka wlh,yace baki fitabako,nan yaci gaba da karatu se ihu takeyi tana cewa kayi hakuri wlh zan fita amma tabbas zan dawo wannan alkawarine kuma wlh bazan kyale maryam ba,danya d'auki son duniya ya d'aura mata wanda hakan yana k'ona min rai sosai,ibrahim yace toke akwai aure a tsakanin ku damu ne,tace eh nida manosh kam wlh akwai aure a tsakaninmu,ibrahim yace menene sunanki? Tace sunana SHUKRA,yace to shukra ina miki gargad'i na karshe ki fita a rayuwarsu idan ba hakaba zakisha wuya,tace lallaima yah ibrahim wlh kona fita zan dawo kuma idan ka rabani na masoyina senayi maganinka,yace kiyi koma menene sannan yaci gaba da karatu babu sassauci,ihu takeyi tana cewa wlh zan fita kayi hakuri ibrahim mugu zan fita wlh, aisam bai saurareta yanata karatu se kawai akaji manosh yayita attishawa,dukda haka ibrahim bai tsayaba seda yayi sosai sanan yayi hamdala ya koma gefe ya zauna.
Tare da gaisawa dasu dad,se godiya suke mishi harda marwan da jikin yayi sanyi. Wayan ibrahim ne yayi k'ara ya duba yaga baban maryamne ya d'auka hello baba,baba yace ibrahim lfy baka dawoba mamanka ta damu an kiraka shuru,yace lfy lau baba yanzu zan dawo insha Allah,yace to Allah ya kare,yace ameen sannan ya katse yaga time har 11:20pm. Yace toni zan koma sedai inda hali kar'a barsu sukad'ai agidan,dad yace mungode sosai ibrahim badamu semu tafi gida dukkanmu inyaso zuwa gobe sesu dawo,ibrahim yace to nagode aunty kiyi hakuri kinji komai yawuce insha Allah,cikin sanyin murya tace nagode Allah ya kiyaye hanya,yace ameen sannan suka fita shida marwan ya rakashi.
Mum tace sannu maryam aima kinyi k'okari wlh jeki ki had'o nuku kayanu koda kala d'ayane semu tafi ko,tace to tare da mik'ewa shi kuwa dad yanata kallon d'ansa cike dajin tausayinshi wanda har yanzu bacci yakeyi bai farkaba. Marwan ya shigo daidai lokacin maryam ta fito da kit se dad ya tashi manosh kuwa yana farkawa yagansu ciki da mamakin ganinsa kwance a k'asa kumaga marwan,mum tace son muje gida,yace mum lfy,tace lfy lau ga dad naka a bayanka,juyowa yayi da sauri ya kalli dad tare dajin kunya ya gaisheshi,se dad ya mike yace zamuje gidan dakai da maryam gobe seku dawo,mamaki sosai manosh yayi amma bazai iya cewa komaiba se toh. Maryam ya hango rik'e da kit a hannunta kanta a sunkuye marwan yajawoshi yace muje.
Marwan yayi musu sallama ya wuce gida,manosh yace dad bari nakaimu,bamusu dad ya bashi key d'in tare da shiga gaba,mum da maryam akuma suna baya ahaka suka isa gida.
Koda suka isa se mum tace kuje side naka seda safe,daga shi har maryam kunya sosai sukaji tare da wuce.
Suna shiga ya rufe ko ina,ya juyo suna kallon juna da maryam,murmushi tamishi shima haka tare da rungumeta yace apple kiyi hakuri kinji,bansan dalilin dayasa su dad sukajeba kuma sukace muzo nan,amma gobe zan tambayeahi kinji,murmushi tayi tare da d'agowa suna kallon juna tace kanaso in dinga kallonka? Yace eh mana,sedai fa aduk lokacin da kike kallona fita hayyacina nakeyi,tace wannan karon babu abinda zai faru inane d'akinka,yace mujene,kai ta d'aga mishi aise ya d'auketa kamar bby ita da kit d'in dukka ae d'akinshi,akan gado ya ajiyeta tare da karb'an kit d'in ya ajiye a gefe yace namance wayaya wlh ni kwata kwata banganebama,tace karka damu wayanka yana cikin kit d'innan na d'auko mana komai,yace yaushe marwan yaje gidanmu,tace tare dasu mum yazo nina kirasu nace ina tsoron gidanmu,shine sukazo d'aukanmu. Kallon maryam yakeyi tare dajin mamakinta harzaiyi magana se tace pls peach nifa amaryace koka manta,inaso in watsa ruwa,inda take yazo tare da rungumeta yace i luv apple,tace i luv u too peach,sannan ya cire jallabiyanshi dagashi se boxer tayi saurin juya mishi baya ahankali ya cire mata doguwar rigan se wandon sleeping dress nata kawai,kunya sosai taji tayi saurin kare k'irjinta da hannayenta dare da rufe idanunta. Juyo da ita yayi a hankali yana kallonta,batare data bud'e idoba tace inaso inyi wankane cikin wata irin murya,d'aukanta yayi cak se toilet shida kanshi yayi mata wanka tanajin yadda yake gogeta da sosonshi cikin wani irin salo,ita kuwa idonta arufe tana jin kunya.
Seda ya wanketa sannan ya dawo da ita d'aki yayi pecking idonta yace bari inje inyi nima kinji,shuru tayi batace komaiba ya wuce toilet.
Da sauri goge jikinta tasa rigar bacci dogo har kasa,sannan ta d'auki wayanta ta kira yah ibrahim,bugu d'aya ya d'auka yace hello aunty,murmushi tayi tace yah ibrahim ka koma lfy,yace lfy lau harma na kwanta,ya captain,tace lfyanshi mun gode sosai yah ibrahim,yace bakomai aunty seda safe ko,tace to sannan ya katse wayar yana maijin kaunarta har cikin ranshi sam baiyi bacciba....
.
Bayan manosh ya fito daga wanka ne,tace peach ka kira marwan kaji ya isa lfy,wayanshi ta mik'a mishi ya kirashi,marwan yace lfy lau wlh harma na kwanta,manosh yake toseda safe,yace yawwa.
Kayan baccinsa ta bashi yasa tare da fesa turare sannan yamatso har inda take kwance ya mannata da jikinshi yace apple bamuci amarcinmubafa kina sane,shuru tayi kamar bata jishiba seya janyota jikinshi yana mata wasu salo na soyayya tace dan Allah ka bari ba'a gidannu mukebafa ni ina kunyan su mum. Yace aibazasu jimuba,tsakaninmu dad'an nisa,tace nidai pls kayi hakuri semun koma gida,haka ya hakura suka kwanta amma suna manne da junansu kamar zasu had'i juna.
Washe gari mum ta kirashi inda suka zauna da dad ya gaya mishi duk abinda ya faru jiya,mamaki sosai manosh yayi sannan dad yaci gaba da mishi nasiha yana cewa nasan baka wasa da ibada manosh amma ka k'ara himma,gidiya sosai yayi sannan ya tafi musu da abin karyawa. Maryam tayi kyau tana zaune yazo da abinci ya zuba musu sukaci suka koshi se yaketa kallonta,yace apple abinda ya faru kenan dama,kai ta d'aga mishi,ya matso ya runguneta yace kiyi hakuri kinji,tace bakomai wlh aiba laifinkabane komai ya wuce. Manosh yaso su kma amma mum tace sam su bari se magariba,haka suka kasance a cikin d'aki har dare bayan sunyi salla se driver ya maidasu da kulan abincinsu.
Seda suka gama komai yace tazo suyi sallan nafila,bayan sun idarne ya wuce kan gado ita kuwa ta mik'e ta cire himar tare da zanin jikinta dayake rigan baccin daya d'auko mata guntune sosai iya cinya.
Tana cier zani tayi sauri kashe wuta ta kwanta a gefe,dariya yayi yace kunyata kikeji,shuru tayi batace komaiba in banda tsoronshi daya cika mata zuciya. Ahankali yake mata wasanni har suka shagala sannan captain ya hankad'oni waje anan bakin k'ofa na tsinci kaina bana iya jin komai se kukan maryam.
Tun tanayi a hankali na dauriya harta kasa hakura,se kusan 11pm kafin na samu dama shiga ciki lokacin manosh ya kunna wuta yana rungume da ita ta baya yana bata hakuri,ita kuwa ko motsibatayi in banda kuka. Toilet ya wuce ya wanke jikinsa sannan ya dawo ya kwanta a bayanta ciki dajin tausayinta. Wutan naga ya sake kashewa zuwa iri 2:30am naji kukan maryam se dad'uwa yakeyi shi kuwa captain numfashinsa kawai kakeji. 3am na samu ganin maryam kwance babu yadda take dan wuya datasha agun captai. Bayan ya fito daga toilet yaje ya wanketa tas,sannan ya shiryata, kan gadon nasu kuwa babu jini ko kad'an akai,ita kanta maryam tayi mamakin rashin ganin jinin,dan yadda tasha azaba. Shi kuwa captain se washe baki yakeyi ya same maryam daidai gata masha Allah zanzan ya jita yadda ake buk'ata
Sorry apple,am very sorry akay? Shuru tayi tare da matsawa daga jikinshi wai ita a dole tana fushi dashi,murmushi yayi yace haba aunt wlh balaifina bane pls karkiyi fushi dani,cikin muryan ban tausayi tace amma kanaji inata baka hakuri koka saurareni,dariya abun ya bashi yace to ai bana jinkine apple amma kinsan ai bazan miki hakaba ko jealousynah,murmushi tayi tace ka tafi d'akinka ka barni,yace haba apple am sorry bazan sakeba kinji,lumui ta kwanta ajikinshi ya matseta sosai a haka sukayi bacci
Bayan sunyi sallan asubane yace bari na fita kozan sami chemis a bud'e in nemo miki magani jikinki yayi zafi sosai,tace to peach karka dad'e pls,yace bazan dad'eba aunt tare da manna mata kiss sannan ya tafi.
Duk chemis d'in a rufe suke dan haka ya kira muh'd yace bari nazo na karb'i magani agunka mana apple na fama da zazzab'i wlh,dariya muh'd yayi yace ai dama ina tausayin aunty randa ta shiga hannuka,dariya manosh yayi tare da katse wayar ya isa gidansa.
Magani muh'd ya had'a mishi yana dariya kai kuwa baka mata a hankali bane,koda yake ashe kaid'in sojane komai da zafin nama akeyinshi,duka manosh yakai mishi yace ashe kaima majid ya b'ataka ban saniba,muh'd ya gudu gefe tare da kiran marwan a waya yace marwan ganiga captain yayiwa aunty bad-bad shine yazo neman magani,ai da duka manosh ya biyoshi,shi kuwa muh'd yayi saurin shigewa gate d'in gidansa ya rufe yana dariya,shima manosh dariyan yakeyi ya shiga mota ya wuce tare da d'aukan kiran marwan yace 'yansa ido me kuma zaka gayamin,marwan yace idan ka isa gida kashewa aunty ina mata sannu,dariya manosh yayi yace zan had'u daku,marwan yace nidai ka isar min da sakona bari in gayawa muhsin. Ai kuwa nan danan muhsin ya kira manosh yace haba captain ba sauk'i sam kodai bakaga aunty namu 'yar chukula bace,manosh yace wlh karka sake ce mata 'yar chukula dan wlh idoce ita chukulan amma a ciki ba haka abin yakeba,dariya sosai muhsin yayi yace naji kaje neman magani dama kai baka tanadi maganiba bayan kasan yadda kake,manosh yace d'an isa karku sake kirana ya katse yana dariya. Yasan cewa majid zai kirashi dan haka yayi saurin kiran majid yace kaikuma mezaka cemin? Majid yayi dariya yace nidai kawai kabar aunty se bayan 3days kafinnan ta samu lfy sosai dan idan ka sake afka mata yau tofa dole muje asibiti jinya,manosh yace kaifa iskancin naka daban ne amma zan rama d'an iska wayasan wuyan da sis miher tasha agunka,majid yace duk wuyar da zatasha dai bazaikai na matar sojaba dai hhhhhhhhh,manosh yace zaci ubaka wlh majid idan muka had'u zaka gane,majid yana dariya yace ai bazama mu had'uba jibi zanyi tafiya nida my luv,manosh yace ai zaka dawo d'an iska ai gara kowa dakai wlh,majid yace captain ba suki Allah sarki aunty walh ina tausayinta hhhhh.
Da dariya sosai manosh ya shigo d'aki tare da rungume maryam yace in hada miki tea? Tace a'a ruwa kawai zata sha,nan ya bata tasha da maganin sannan suka kwanta bacci.
11:30am suka farka inda ya wuce yayi musu wanka suka shirya sanna ya had'a musu tea da bread ta soya musu egg suka sha tana jin kunyanshi sosai.
Shi kanshi ya lura da haka bayan sun gama ya d'auketa se d'akinshi can suka koma suka kwanta yana mata hira mai dad'i ita kuwa se dariya takeyi cikin k'ank'anin lokacin ta sake dashi sosai sukaci gaba da soyayyarsu.
Mum ce ta kira maryam suka gaisa take tambayarta babu wata matsala dai ko,maryam tace bakomai wlh,tace to shikenan Allah ya muku albarka tace ameen tare da kallon manosh tana dariya.
Manosh da friends nashi suka shirya sukaje yiwa surukansu gidiyan aure kamar yadda akeyi,sannan ya bada kud'i sosai dan a k'ara fad'ad'a masallacin unguwansu ya kuma bada kud'i a gyara musu gidan.
Godiya sosai maryam tayi tare sadu zahida dan duk sun yiwa iyayensu hidima sosai. Ya ibrahim kuwa girma dad d'in manosh ya k'ara mishi a companinsa dake kaduna wanda aka bashi asistan director a gurin. Kud'i sosai yake samu cikin k'ank'anin lokaci ya sayi mota EODbarka na musam maryam da rash sukaje sukayi mishi,murna sosai mama tayi da ganin yadda maryam ta k'ara kyau, itama maryam dad'i taji sosai da ganin yadda aka gyra musu gidansu,rash ta shigo tana tayi musu hotuna,inda maryam take sanye da green atamfa tasha ado tare da coffee bag a hannunta. Da yamma mazajensu sukazo d'aukansu, inda suke koyawa matansu driving,sannan result ya fito duk aka sasu a FUTY YOLA inda dukkansu suke level one.
Hmmm sosayya sosai suke zubawa junansu,inda duk suke d'auke da ciki amma na marya dabanne dan wahala sosai takesha.
Lubna kuwa taga ba sarki se Allah dan haka tatsai da zuciyanta kawai agun yah ibrahim musamman lokacin da bro marwan ya kirata yace lallai ta cire son manosh a ranta dan manosh baya ganin kowa se maryam,sannan yace mata ibrahim mutumin kirkine ga addini wanda duk wani uba ko yaya zaiso ace 'yarsa ko k'anwansa ta auri miji irin yah ibrahim. Hakanne yasa lubna saduda tabashi dukkan soyayyarta,inda suke soyayyarsu mai tsafta sosai.
Ciwon maryam se gaba gaba yakeyi,abun harya fara damun kowa,tunba yah ibrahim da iyayen manosh bare sunsan abinda shukra tace,amma dukda hakan se suka barshi akan laulayin cikine,hakadai taketa fama ga laulayi ga zuwa makaranta ga kuma kula da peach.
Hajiya hadiza mahaifiyar lubna da kuma hajiya iya kullum idan suka had'u banda kuka da nadama babu abinda sukeyi.
*********
Kwanci tashi su maryam har sunyi hutu,se abin yad'an mata sauki kad'an. Mum da mamanta kusan kullum suna hanya zuwa dubata,kuma sam har yau yah ibrahim bai gayawa kowa abinda ya faru,iya tsakaninsu kawai sukabar zance. Cikin maryam yafi nasu rash girma da kuma yawan watanni,ranan tana yankawa manosh fruit kawai seta zube a k'asa,dab kuwa lokacin manosh yazo gida,ai da sauri ya d'auketa se hospital d'insu muh'd, tun azahar akace musu haihuwace amma har magriba tanata fama. Hankalin mama da hajiya iya ya tashi sosai dama tunda manosh ya kira baba yace ga maryam sunzo haihuwa se yah ibrahim ya kaisu hospital d'in. Addu'a maryam taketa samu kota ina,mama kuka kuka takeyi dan bazata tab'a mance haihuwan maryam ba wanda bata cikin hayyacintama ta haifi maryam d'in. Hajiya iyace taketa kuka tana rarrashi mama,maryam bata haihuba har 2 na dare,anan akace jinin jikinta yayi kad'an dole asa mata wani,yah ibrahim kamar zaice a d'ibi nashi dayake yanaba mutane sosai jininshi. Amma seyayi shuru manosh ne yabada nashi aka sama mata.
Ana kiran sallan asuba maryam ta haihu amma sam bata iya gane kosu waye akanta. Kukan bby ne yasa kowa yasan maryam ta haihu,dan manosh yaso ya kwana a hospital d'in amma dan kunyan su mama yasa ya tafi gida sam ya kasa bacci 4am cib yazo hospital d'in yana dawowa daga masallaci yaji kukan bby,hamdala yayi tare dajin farin ciki aransahi.
Mata biyune suke kula da bbyn, d'aya ta fito tace dasu maryam ta sauka lfy an sami 'yan biyu. Manosh ya kasa b'oye murnanshi yace maryam fa,lfyanta k'alau dai ko,tace eh lfyanta k'alau sedai tasha wahala sosai dan haka tana buk'an hutu yanzuma ruwa nasa mata,hamdala kowa yakeyi muh'd yace bari na shiga na dubata,lokacin an rufeta bbys kuwa an shiryasu tsaf,dama ba kaya d'aya aka rik'oba.
Suka fito da yara kyawawa kamar iyayensu,manosh yace zan iya shiga inga maryam,sukace eh kaje,da sauri ya wuce baima kalli jariranba,inda mama da hajiya iya suka k'arb'esu. Manosh yana shiga ya rungumeta tana bacci,muh'd yace kwantar da hankalinka idan ta farka garau zata tashi insha Allah,ina taya baban twins murna,murmushi yayi yace nagode sannan suka fita danta samu bacci sosai.
Boy ne da kuma byy kyawawan gaske,manosh da muh'd suka karb'esu tare da murna.
Daidai sega yah ibrahim yazo tare dasu mum d'in manosh. Murna sosai akayi kowa se cewa yake masha Allah. Kinya yasa manosh barin gurin ya kira mai shiryawa bbys nashi d'aki yace matata ta haifi wtins mace dana miji dan haka ka shirya gobe sekazo a gyara musu d'aki.yana ajiyewa yayita kiran abokan arziki yana shaida musu haihuwan maryam kowa se tayashi murna yakeyi,kafi 8am hospital ya shiga da friends nasu ga kuma su rash da miher.
Gefe d'aya hajiya iya ta koma tanata kuka tare da cewa ohh Allah,meyake shirin faruwane dani,kodai lokaci yayne dazan fasa wannan kwan kowa ya sani..
.
maryam bata farkaba har se azahar,koda bud'e ido mum d'in manosh ce da mamanta zaune suna mata sannu maryam,kunya sosai taji dan tasan cewa ta haihu.
Mum ta kira manosh a waya tace to "son" maisunana ta farka seka kwntar da hankalinka kaci wani abun ko,mirmushi yayi tare da cewa thankyou mum ina zuwa yanzu.
Maman maryam tace Allah ya gagara cin abinci ko,mum tace wlh yaqi sam duk ya rud'e, kunya sosai maryam taji,mum d'in manosh ta had'a mata malt da peakmilk aka bata tasha sannan aka bata nama mai zafi sannan suka bata guri danta sake.
Yah ibrahim ne ya shigo da mamanshi,murmushi takeyi tace yah ibrahim,yace na'am sannu ya jiki,tace da sauk'i ciki dajin kunyarsa,yace Allah ya baki lfy ya kuma raya mana twins,tace ameen a ranta,afili kuma tace nagode,sannan suka gaisa da maman rash inda ta ajiye mata tuwon shinkafa da kuma kunun gyad'a mai zafi.
Haka dai akaita shigowa su k'awayenta da kuma abokan manosh musamman muh'd dayake shine doc d'inta.
Manosh baizo hospital ba se 3:10pm shida maigidanshi,bayan sun gaisa dasu mum ne seya mishi jagora har d'akin marya. Tana kwance tana d'an hutawa kamar yadda doc yace abarta ta huta dan tana buk'atan hutun.
Da sallama suka shiga,manosh yayi saurin d'aukan himar nata yasa mata tare da kashe mata ido d'aya sannan yace yallab'ai bismillah,cikin mamaki maryam taga babban mutum ya shigo,sunkuyar da kanta tayi tace ina wuni,yace lfy lau mmn twins mun samu k'aruwa,tace hmm tana murmushi,yace toh Allah ya raya manasu tafarkin addinin musulunci, tace ameen mungode,yace amma babu wani problem ai ko,manosh yace yes bakomai amma dai doc yace tana buk'atan hutu sosai inga zamu kai jibi kafin a sallamemu,oganshi yace ok to Allah ya bata lfy,manosh yace ameen "sir ga bbys d'in,nan suka k'arasa suka d'aukesu shima manosh se yanzu ya k'are musu kallo se wani farinciki yakeyi wanda oganshi se kallonshi yakeyi,yace gaskya dole kayita smiling irin wannan kyauta da Allah ya maka gaskya se godiya,manosh yayi dariya yace "thankyou sir" yace boy zai zama soja kenan shima,dariya sukayi dukkansu harda maryam,sannan yayi musu sallama manosh ya rakashi gun mota inda driver yake jiranshi sannan ya dawo gun apple nashi.
Da gudu ya rungumeta ita ta sake langwamewa a jikinshi ta matseshi sosai tana cewa i luv u peach,yace ai wasane apple,nene nake k'aunarki kamar zanyi hauka wlh peack mai zafi ya manna mata yace thankyou so much apple,kai ta d'ago tana kallonshi mai d'auke da alaman tambaya,yace yes saboda kinyi k'ok'ari gashi kinsha wahala sosai wlh "im sorry for what i did to u apple" tace me kenan? Yace (dana shigeki mana) amma dai munga riban hakan tunda gashi mun samu yara har 2 a lokaci d'aya, ya rad'a mata akunnenta.
Dariya sosai takeyi shima haka,slm sukaji tayi saurin janye jikinta daga nashi,shi kuwa bai matsaba dan yasan dai basu mama bane. Miher ce ta shigo tana murmushi tave eyye maman twins kamar bake kika haifesuba,manosh yace karki yarda kowa yagansu yasan itata haifesu kidena hura mata kai dan yanzu kam ta tsufa saura inyo mata amarya,wani irin kallo ta watsawa manosh tare da cewa wlh peach kaga bana sofa,dariya sukayi shida miher ya tashi yana cewa jealousy tare da d'aukan boy d'in dan miher ta d'auki girl. Tace peach matso dashi nan pls,ba musu yakai mata tanata k'are mishi kallo tace mai kama da bbnshi,miher tace wannan kuma mai kama da mmntaba,dariya sukayi yace wani suna kike so aba girl d'in? Tace boy d'infa,yace a'a banda boy ke kizab'a sunan girl ni kuma inzab'a na boy,tace to ayiwa su mum da mama da ni kakwara,miher tace lallaikam nima na amince shikenan maryam ta haifi maryam,hhhhh sukayi dariya,manosh yace thanks naji dad'in hakan kuma na amince,amma wani suna aza'a kirata dashi? Maryam tace *Alfiyya*, miher tace "wooo! what a nice name" gaskya sunan yamin dad'i,maryam tace nagode,manosh yace thankyou *mom alfiyya*, miher tace bro boy kuma zakayiwa majid takwarane ko,hhhh sukayi dariya,yace kunji mara kunya ko,hhhh sannan ya mik'e yace se nan da 3days zakuji sunan boy nah.
Bayan manosh ya fita miher ta zauna sunata hira tare da shirin yadda suna zai kasance.
Hajiya iya ta shigo tanata murna tana cewa sannu da zuwa mai gida da kuma kishiya,hhhh maryam tace bakya kishi,tace banayi tunda na samu sabon mai gida. Hakadai akaita hira koda yaushe mum d'in manosh tana hanyan zuwa duba jikokinta musamman datasan takwara aka mata ita da mmn maryam dan duk sunansu d'ayane.
Yau kwana uku da haihu aka sallami maryam,gidan mijinta aka maidata inda yapendo ladi take zaune da kuma nafisa itace mai girki.
Manosh ya sanar da apple sunan yaro "ABDALLAH" dad'i sosai taji mara misaltuwa,dan duk tunaninta zaiyi wa mahaifinsane takwara. Rungumeshi tayi sosai tana murna harda kwalla,dan har azuciyarta tanada niyan yiwa abdallah takwara amma sam bata san ran yanzu bane. Hawayen ya share mata yace bana so ki sake kukan rashin abdallah apple danga abdallanki ya dawo.murmushi tayi tace nagode sosai peach,kai dabanne acikin sauran mazaje shiyasa akoda yaushe nake k'arayin godiya wa Allah daya bani miji kamarka,peach ina maka k'aunar dabasan iyakacinsa,fata akoda yaushe shine Allah yabarni dakai har' aljanna. Rungumeta yayi sosai danjin dad'an kalamanta masu kwantar da hankali da kuma shiga rai,har seda ya kwantar da ita akan gadonsa sunata kissing junansu,dakyar ta kwaci kanta ta gudu d'aki tana mishi gwalo shikuwa murmushi kawai yakeyi tare dajin k'aunarta na ratsa jijin jikinsa.
D'akin alfiyya komai pink ne kamar yadda kuka sani,shi kuwa abdallah blue,basena na tsaya yin bayanin yadda d'akin zai kasanceba,saboda ku masu karatu kunsan wanene manosh kua kunsan abunda zaiyi.
Yau suna harta motanta 307 sayarwa manosh yayi ya saya mata benz sabudal.
Kar kuga yadda akayi wani decorection agidan,'yan makarantansu su maryam kowa se kallo dasan barka,idan kanajin ruwan kud'i tofa anyi ambaliyansa agun maryam da yaranta, ranan gidan a cike yake da 'yan media se d'auka akeyi, gift kuwa maryam ta samu hardana hauka.
NOKIA manosh ya saya guda 100 irin masu tosh d'innan wanda a yanzu kusan 8k suke haka yasa aka k'era mishi ya raba a suna,banda sauran tarkacen da akayi wanda bazasu irguba. Idan ka kuna wayan sunan abdallah da alfiyyane yake bayyana maimakon kaga NOKIA,hmmm naso ace *fans* kunje sunan zaku wanke ido taass.

 ANTIN YARA Page 56-60
.
Kula sosai suka samu daga maryam har yaran. Inda aka tura manosh k'asar waje kuma zaikai 3 to 4 kafin ya dawo. Haka ya shirya ya tafi danba yadda ya iya.
Yana can miher,zahida da rash suka haihu. Manosh baya gari akayi suna,suma kunsan ba bayaba,shagali sosai akayi.
Satinda manosh zai dawo satin samira da amina suka haihu,manosh yana gari akayi suna. Hmmm abundai ba sauk'i.
Bayan dawowan manosh ne yapendo ta koma amma nafisa tana nan daga gidan take zuwa makaranta,dan manosh ya rok'a abar nafisa tad'an zauna kafin twins suyi kwari. Ita dai nafisa bata soba,dan haka maryam taketa mata dariya tana tsokanarta, nafisa tace seki barni da yara kije kuyi soyewa da mijinkiko wlh na kusa tafiya. Hhhhhhhh maryam tayi dariya tace tome aikinki babu inda zakije se lokacin aurenki yayi kuma wlh ki tabbata kina kula mana da yaranmu idanma biyanki kikeso muyi to zamuyi amma kar in sake ji kina kirana idan peach nah yana gida saboda kina takura mana wlh. Harara nafisa takewa maryam tare da d'aukan teadyn alfiyya ta jefi maryam dashi, da sauri ta fita da gudu inda sukaci karo da manosh yayi saurin rungumeta tace peach kaga nafisa ko,d'aukanta yayi cak se d'aki yace muje karma ki sake komawa sedai in twins suna buk'atan nono. Kiss ta manna mishi tare da cewa yawwa angon maryam shiyasa nake k'ara sonka,daga nan kuma suka wuce duniyartasu.
Ayau ake auren yah ibrahim da lubna,programs sosai lubna tayi su maryam sune k'awaye su manosh kuwa abokai kuma yayyu.
Zanso kuga bikin abin sha'awa da birgewa babu wasu k'awaye iya zallah sune kawai,sedai shi yah ibrahim yanada friends sosai. Mahaifin lubna shiya gina musu gida mai kyau acikin jimeta,inda akayi harda d'akin mamansa daga gefe.
Dukda dai yah ibrahim yasan halinda lubna take ciki,amma dukda haka a had'e yajita sosai saboda gyara datasha sosai,kuma da taimakon Allah tunda fyad'e ne bawai dasonta bane, zaman lfya sosai sukeyi hankali kwance,zumunci mai k'arfi yashiga tsakaninsu kamar 'yan'uwa.
*****
3years
Lokaci babu wuya yanzu su abdallah sunada shekara uku,ga wayo shiyasama akasa a skul dukkansu.
Yau sartuday sukaje girei gun kakarsu zasu kwana d'aya sunbar manosh shi kad'ai agida.
Alfiyya ita dai se shigan turawa kawai take so adinga mata,shi kuwa manosh cewa yayi abarta tunda k'aramace idan ta fara girma se'a dena sayowa,maryam batasoba amma haka ta hakura. Farin rigane a jikin alfiyya tare da wani dogon takalmi se kuma hula inda gashinta ya rufe mata fiska dan tsawo,dan tafi maryam gashi gashin manosh suka d'auko,sunaji da yaran sosai akama mutane suna son yaran musamman alfiyya. Haka ta ishe maryam waisam tayi mata hoto dan idan baban maryam angonta ya dawo zata nuna mishi,dariya maryam da mmnta sukayi sannan ta d'auketa.
Ayau akayi hutun first term,inda manosh ya kashi su alfiyaya kaisu gun mum sunyi 2weeks,daga can kuma sesu wuce gun maman maryam a girei.
Gida daga maryam se manosh,tana zaune a d'akin alfiya tanata k'arewa d'akin kallo duk kewarsu ya kamata gashi manosh bai dawo da ruwaba yau har 9:30pm sannan taji shigowar motarshi, da sauri ta fito tana sanye da gajeren wandon manosh da kuma wani shets nashi fari dama ya kasa mishi dan haka tasa ya mata kyau sosai ta tsaya ajikin k'ofan shigowa daga gefe,yana shogowa da sallama tace kamashi nan! Tsorata sosai yayi ita kuwa kayayyakin hannunsa ta karb'a ta wuce da gudu tana mishi dariya tare da cewa soja dajin tsoro,gaskya kaba dani wlh peach tanata dariya tare dayi mishi gwalo ta wuce sama.
Ahankali ya k'arasa saman yana mana kallon,zaki gane kuranki. Bayan ta ajiye komaine,tazo da gudu ta haye bayanshi tana cewa
_aga aga_ _aga tsoja dajin tsoro aganshi hhhhh_
Ai kuwa daya cirota yayi daga bayanshi bai ajiyeta ko inba se d'akinshi yana cewa nine matsoracinko,tace sosaima kuwa ka cika babban matsoraci,ta fad'a tare da mishi galo,shi kuwa kallonta kawai yakeyi yace wayace miki kisa min kayana,tace ai yanzu kam sun zama nawa tunda sun kasa maka,bakaga yadda suka min kyau fiyema dakaiba. Shi kanshi yasan sunyi mata kyau sosai amma seyace sam basu miki kyauba kuma ki cire min kaya dan bance na bakiba,ta marairaice tace haba bby nah,yace waye bby'n?ta nunashi da yatsan hannunta batare datayi maganaba,manosh yayi murmushi yace wlh na wuce bby tunda har na samo abdallahda alfiya,hhhhhh maryam tayi dariya tace to babban mutum naji,amfa ka sani bakai kad'ai ka samosubayace ni kad'aine mana saboda lokacin dana samosu ai bakya cikin hayyacinki kuka kawai kike kinsan me kike cewa? Ta girgiza kai sunayiwa juna murmushi,yace cewa kike _pls peach kayi hakuri wlh dazafifa,baka tausayinane kanaji ina maka magana,dan Allah ka tausayamin peach kasanfa ni k'aramace_
Dariya sosai maryam takeyi shi kuwa yana kallonta yace wlh kuwa haka kika dinga cewa,ita kuwa maryam yanayin yadda yayi maganane waishi adole yana kwaikwayon muryanta shiyabata dariya.
Janyota yayi tare da cire mata kayan jikinta itama ta tub'e masa nashi suka wuce toilet sunata cud'ar junansu sannan suka fito tana manne a jikinsa.
Bayan sunyi shirin baccine se suka wuce daining sukaci abinci yasha fruit yana cewa wlh nayi missing d'in honeys d'ina sosai fa,maryam tayi murmushi tace to ai hakuri zamuyi kamar gobene sekaga har hutun ya k'are. Yace ina kullum zanje inyita ganinsu mana hira,tace nifa,yace zan kiraki a waya se'in had'aku.
Haka dai sukaita hira har suka kammala sannan suka wuce d'aki,kwanciya yayi akan gadon sannan ya janyota tare da kashe wutar.
Wato idan manosh da maryam suna luv seka d'auka yau ne farkon amarcinsu saboda wata ni'ima na musamman da Allah yayiwa maryam,sam ita bata shan wani maganin mata koma wani irine daya wuce fruit,shima bawai dan yayi mata maganiba sedan kawai ita tana son fruit,kuma se Allah ya had'ata da wanda yafita son fruits.
Akullum satin manosh akanta dabanne,bayan sun samu gamsuwa sosaine yake ce mata gaskya aunty Allah yayi miki wata baiwa ko kuma ince halitta wanda bakowace mace bace take dashiba,yace wlh apple aduk lokacin dana kusanceki banda irin ni'imar dani kad'ai nasan dad'inki to wlh koda yaushe senaji wani farinciki mara misaltuwa a tare dani,sannan zazzafar k'aunarkice take shiga jikina tun daga tafin kafata har tsakiyar kaina pls apple gayamin sirrin.
Dad'i sosai taji wanda bazata iya b'oyewaba tace wlh bakomai sedai ince Alhadulillah kuma zanci gaba dayiwa Allah gofiya yasa in d'aure haka har abada,dan banida wata buri irin inga koda yaushe kana samu gamsuwa dani 1000% peach,yace kin wuce 1000% apple aguna babu wata adadin dazan iya dangantaki dashi sedai incigaba dayiwa Allah godiya daya bani wannan kyautar apple d'in nawa 'yar baiwa. Sanyi taji har cikin ranta tare da sake shigewa jikinsa tana juyi irinna sake taso da shawa'a, ai kuwa sannu a hankali manosh ya rikid'e yashiga sarrafa yar bbynsa son ranshi gata 'yar k'arama mara nauyi,dama kuma kunsan ance siraran mata daban suke.
Idan manosh yana tare da maryam tofa nuna mata yake shekarunsu dai-daine,shiya ita kanta maryam take gamsuwan da koda yaushe tana buk'atan su kasance a tare. Kai soyayya tayi a rayuwa.
Washe gari maryam ta hana manosh fita kwata-kwata,babu yadda baiyi da itaba danya rarrasheta ta hak'ura amma sam taqi wai ita dai dole seya zauna suyini suna luv ko Allah zai karb'i addu'ansu ta sake samun wani ciki.
Haka ya zauna da apple a gida tare da sanar da kowa cewa bayajin dad'ine,ai kuwa gaisu aketa zuwa gida,wannan na fita wannan zai shigo,manosh dai dariya kawai yakeyiwa maryam. Tace to wlh babu wanda zai sake ganinka duk kace musu kayi bacci batajira mezaiceba ta shagwab'e tare da fara kai hannunta cikin wandonshi,ai tuni suka haura sama anata abu d'aya,seda suka gaji sosai dukkansu sannan suka kwanta bacci har azahar.
Byan sun idar da sallah ne sukaci abinci sannan suka koma bacci suna farkawa ya janyota jikinshi akadai suketa abu d'aya,sannan sukayi wanka da sallan la'asar se tace zauna in baka lbr,ba musu ya zauna tana kwanshe a jikinsa tana mishi hiran zamanin annabawa,kawai setaji yana cewa apple tashi kinji,tace meyasa,yace pls apple,da sauri ta tashi aisetaga idonshi sunyi jah sosai,tace lfy peach meya shiga maka idon haka mugani,bakinta takai zata hura mishi idon,setaji yace aisekiyi kuwa nidai yanzu muna miki bankwana.........
Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un3 maryam taketa maimaitawa tare da tab'a inna manosh yake kwance amma sam bata ganin komai agun se pillow, addu'a maryam ta farayi tana kuka amma sam har yanzu bata ganin manosh a d'akin daga ita se gado da pillow.
Kukata farayi tana cewa peach,ina kake pls peach kadena me kuma haka,waje ta fito ta nufi d'akinta amma bayanan,ta duba ko'ina dai acikin gidan kozata ganshi,dukda dai ita tasan suna tare dashi a d'akinshi batare daya sauka daga gadonba tanemeshi ta rasa.
Ai take maryam ta rikice tare da tsorata ta d'auki wayanta ta kira yah ibrahim tace hello yah ibrahim akwai matsala babba wannan karon na nemi manosh sama da k'asa na rasashi kuma yanzu muna tare dashi anan wlh b'acewa yayi.. yah ibrahim kansa ya d'aure sosai yace aunty b'acewa kuma kamar yaya,tace wlh duk yadda akayi SHUKRAH CE itace ta d'aukemin mijina yah ibrahim wlh itace..ai se yanzu ibrahim ya gano abinda maryam take nufi,yace kiyi hakuri aunty ganinan zuwa sannan ya katse wayan ya kira mahaifin maryam ya gaya mishi abinda maryam ta gaya mishi,dukdai wanda yaji se kanshi ya d'aure,dukda dai su yah ibrahim kam sunsan komai,amma kuma mamakinsu shine yaza'ayi shukrah ta d'auke manosh lokaci d'aya kuma ace b'acewa,ibrahim yace lallai akwai aiki sosai tausayin aunty kawai yafarayi tunma baigantaba a halin yanzu,tana zaune a inda suke itada manosh tana cewa peach dan Allah ka fito ganinan ina jiranka pls peach.
Wayanta ta d'auka ta kiran mum d'in manosh tana kuka ta gaya mata komai,rikicewa mum tayi tare da fad'in alhaji karma ka fita akwai matsala,yanzu maryam ta kirani wai manosh ya b'ace yanzu a d'aki batare daya tashi yaje wani guba b'acewa kawai yayi yau ni maryam wannan wani irin abune kuma.
Cikin 1hr gidan manosh ya cika da iyaye da kuma abokai. Kuka kawai maryam taketa rusawa,tun daga gate ake fara tambayan mai gadi koyaga fitar manosh,yace ai oga yana cikin gida yau sam bai fito ko tsak'ar gidaba.
Haka suka karasa ciki,maryam taje ta rungume mamanta tana cewa mama manosh wlh banganshi. Su marwan da ibrahim da kansu suka wuce ko ina agidan suka duba amma sam babu manosh,gashi maryam ta tabbatar musu da cewa tana zaune ajikin kalmarsa na karshe yanata cewa apple tashi,ganin jan da idonshi yayine tace barita hura masa dan ita atunaninta abune ya shiga mishi ido,takai baki kenan setaji yace aise kiyi.
Tunda lbr ya sami dad d'in manosh ya samo malamin sunna ya gaya mishi komai tun daga farko har karshe,yah ibrahim yace ina wayanshi aunty,tace duk a d'aki yake amma babu yanzu,majid yayi saurin kiran wayan ai kuwa se waya ta fara ringing,a hands free yasa ta yadda kowa zaiji.
Muryan mace tanata dariyan mugunta wanda kowa hankalinsa ya koma gun wayan,majid yace hello abokina,tace hhhh abokinka kuma,wannan matar abokinkace ai. Ibrahim ya karb'e yace wace matar kenan,dariya tayi sosai tare da cewa ohh yah ibrahim barkanmu da sake ganawa ka manta abinda na gaya maka,nace zan dawo kuma gashi na dawo ai auntyn ta gama more rayuwarta dashi kuma na hakura na barsu,dan haka nima yabzu lokacina kabawa aunty hakuri sannan karku b'atawa kanku lokaci dan wlh manosh bazai dawoba domin shi nawane yanzu! Ta k'arasa maganar cikin tsawa.
Ibrahim yace amma shukra ke acikin aljanunma kafira ce wawiya,kiyi gaggawan dawo da manosh idan ba hakaba mukuma zamu klarb'o manosh da ikon Allah. Dariyan nugunta tayi tace wlh kana burgeni sosai yah ibrahim da karfin halinka da kuma jarumtarka,lokacin dana d'auke manosh wlh kai kawai na fara tunowa,da ace kai zuciyata takeso ta tuni na d'aukeka. Yace karya kikeyi wlh yanzu ina kika kai manosh,tace yananan kacewa maryam garama ta kwantar da hankalinta dan duk k'aunarshi da takeyi tofa a bayan nawa yake,sannan ta dena wannan kukan kasan dama lfy bata ishetaba,kukaita manyan hospital zasu saboda akwai babban ciwo da yake amunta,karkuyi wasa har ciwon yayi nisa *k'odarta guda d'aya yana da matsala* idan baka yaddaba kuma kuje ayi mata gwaji,ba kuma nina samata ba,nadai gaya mukune dan ku d'auki mataki da wuri sannan ku sama mata wani mijin tayi aure dan wlh manosh bazai dawoba,daga k'arshe ina baku hakuri iyayen manosh kaunarsa nakeyi sosai shiyasa na muku haka kuma babau abinda zai sameshi,yah ibrahim seka sake jina dan kai kad'ai kawai zanyi magana dashi ma'assalam!
Koda aka sake kiran wayan se akajita a rufe,duk wanda ke parlour jikinshi a mace anma rasa me za'ayi akai. Malam yace ku kwantar da hankalinku tabbas zata dawo dashi da yardan Allah muyita addu'a zansan yadda zamuyi,domin hakan na faruwa sosai ta wasu k'asashen,maganar k'arshe itace lallai aje ayiwa maryam gwaji domin zai iya yuwa maganar shukran gaskyane, dama bata da lfya ne? Mahaifin maryam yace eh tun bayan haihuwanta take fama kuma ance mana dai babu komai,dad d'in marwan yace to ai se'a shirya zuwa kano muji,baban maryam yace badamuwa zamu je,dan wani lokacin aljanu suna iya fad'in daidai,sannan karku damu insha Allah muh'd zai dawo domin na tab'a had'uwa da wasu wanda abin ya faru irin haka,kuma matar tadawo sedai ta d'auki kusan watan shidda kafin suka dawo da ita da kuma lfy lau.
Haka dai baban maryam da wan malamin da dad d'in manosh ya kira sukaita kwantarwa mutane da hankali hardai suka samu sukuni a ransu,sannan akace maryam ta shirya su tafi gida da iyayenta,zuwa gobe za'a musu komai suwuce kano,yah ibrahim yace nima zanje,haka aka watse kowa dai jiki sanyaye, maryam kuwa batasanma me take cikiba sam tak'i yarda tace babu inda zataje manosh zaidawo d'aki bazai sametaba,tausayinta ya kamasu mum d'in manosh ta rungumeta tanata rarrashinta itama kukan takeyi har suka k'arasa gun mota dakyar ta shiga motan mamanta tana cewa kiyi hakuri maryam jarabawace kuma insha Allah zakici wannan wannan jarabawan ki daure kiyita addu'a. Dama yah ibrahim ne yaje ya d'aukosu baban maryam,dan haka shiya d'aukesu ya mayar dasu mama da maryam sun zaune a baya, hmmmm akwai aiki........
.
Hajiya khadija tana tsaye a palo se faman rusa kuka takeyi tana kiran lubna,amma ina lubna ta d'auki bag da gyalenta ta fito da sauri tana hawaye ta nufi gun mota,inda hajiya khadija taketa faman kiranta amma ina aguje ta figi mota se girei.
Hajiya khajida ta kira hajiya iya ta gaya mata komai,hankalin hajiya iya ya tashi sosai dama kuma ranan batajin dad'in jikinta sam. Sallamar maryam ce yasa hajiya iya tayi saurin katse wayan tace maryam yanzu seda kikazo dubani dukda irin halin da kike ciki? Maryam tayi murmushin k'arfin hali tace haba hajiya ai rashin lfy ya wuce komai ya jikin naki? Tace da sauk'i yasu hajiyan,maryam tace lfy lau sannan ta marairaice murya tace hajiya kusan *sati uku* fa kenan babu lbrn manosh d'ina gaskya banajin zan iya ci gaba da rayuwa indai har na rasashi har abada,tacigaba da cewa hajiya ina son manosh fiye da tunaninku ko a wani hali yake ciki se Allah
Hajiya tayita rarrashinta da kalamai masu sanyaya zuciya dukda dai ita maryam ji take kamar ana sake sata kukane hakan yasa ta mik'e ta wuce cikin d'akin hajiya ta shige toilet domin wanke fiskanta,ita kuwa hajiya sebinta da kallo takeyi cike da tausayawa da kuma laifin datayiwa maryam da iyayenta wanda a yanzu taketa d'an dana sani da kuma tunanin abinda zai biyo baya yanzu da hajiya khadija tace luvna tasan komai gashi ta fita tana kuka ba'asan ina ta nufaba.
Kamar daga sama hajiya iya taga lubna ta shigo rai a b'ace ko sallama babu ta fara zagin hajiya iya zagi marasa dad'in ji. Hakan yasan maryam ta fito da sauri har tana tuntub'e,tsakanin lubna da hajiya iya ta shiga tana cewa lfyanki kuwa lubna,wani irin rashin hankaline wannan me kuma ya kawoki nan dahar zakizo kina mata irin wannan rashin mutunci? Lubna batama san waya shiga tsakaninsu da hajiya iyaba saboda yadda ranta ya b'aci cewa take kinji kunya wlh tsufanki bai amfaneki da komaiba se tsuta dacin amana wlh kunya nakeji wai ace ke kakatace...lubna bata kai ayaba taji wawan mari da maryam ta sake mata a fiska tace baki da hankaline wai lubna kin santane? Kuma meta miki haka dazaki mata wannan cin fiska sekace wanda bata da tarbiya?
Se a wannan lokacin lubna ta lura da cewa ashe hasanantace maryam jininta,hawaye masu zafi suke kwaranyowa daga fiskanta cikin sanyi murya tace maryam lfy lau kuma nasan me nakeyi hajiya iya ta cuceni ta cuci rayuwata kuma wlh har abada bazan tab'a yafe mataba tir da mai hali irin naki wlh kinji kunya kuma ki sani randa kowa zaiji wannan abun rananne kowa zai d'aukeki a matsayin tsohuwar banza kokuma ince tsoffin banza wlh kunji kunya kun cuci mahaifina sannan kin cuci d'an cikinki tunda shima baisan komai akaiba muguwar tsohuwa... mari maryam ta sake bata tace lubna ki fita kibar gidannan dan bazaiyu in barki kiyita hauka ba da alamun tab'in hankali a tattare dake,waya ta d'auka ta kira yah ibrahim take gaya mishi irin cin fiskan da lubna takeyiwa hajiya wanda har a wannan lokacin zagin takeyi shi kansa yah ibrahim yana jiyo muryarta da munanan kalaman da take gayawa hajiya iya. Ita kuwa hajiya iya kuka sosai takeyi tare da kasa had'a ido da dukkanninsu saboda tasan bata da gaskya,ita kuwa maryam rungume hajiya iya tayi tana rarrashinta tare da cewa lubna kibar gidannan baki san cewa bata da lfy bane? Lubna tace ai dole tayi rashin lfy,sakayya ne ta fara gani tun a duniya akan abinda ta aikata natabbata idan kika san abinda wannan tsohuwar banzan tayi wlh sekin tsaneta har abada,maryam wannan tsohuwar basonki takeyiba domin ita ta rusa miki farincikinki muguwace ta k'arshe shiyasa take kyautata miki sosai dan abinda ta aikata miki amma kinji kunya wlh tsohuwar banz....mari mai kyau marwan ya d'auke lubna dashi wanda har yah ibrahim seda ya tausaya mata bare kuma maryam da hajiya iya.
Yah ibrahim yace haba marwan irin wannan marin,yayi saurin kamo matarshi ya rungume ita kuwa lubna dukda tsoron marwan da takeyi amma sam a wannan lokacin seta nemi tsoron ta rasa bare kuma yanzu da tasan shiba yayanta bane,tace ko kasheni zakayi wlh bazan dena zagin tsohuwar banzan nanba maciya amana wlh kinji kunya,sannan kuma karka sake marina dan baka da wani iko akaina ina fatan ka gane me nake nufi,tunda kakarkace sekaje gareta amma dole maryam zata bar gidannan,da gudu taje ta janyo maryam daga jikin hajiya kaka tace zomu tafi *aunty* ki rabu da tsohuwarnan datasan bata da gaskya ai gashi tayi shuru bata cewa komai se kukan nadama da takeyi wlh kin cucemu kuma nikam bazan tab'a yafewaba.
Mamakine ya kama marwan sosai shidai yasan lubna tana tsoronshi sannan bata da rashin kunya amma yadda yaga ta dage tana kuka tana magana hakan yasa jikinshi yayi sanyi yaje gun kakanshi hajiya iya yanata rarrashinta,maryam da yah ibrahim ma mamaki abun ya basu,maryam ta fisge hannunta tace koma me hajiya iya tamiki bata cancanci haka daga garekiba lubna tafa haifi mahaifinki tunta naji kince kakarkuce,lubna tace kakar bro marwan dai amma banda ni kizo mutafi *aunty* bazaki gane komaiba a yanzu kuma banaso ki gane komai saboda bayida amfani a yanzu muje my luv kakyi k'ok'ari asamu a fitar da *aunty* waje ayimata aiki wannan shine burina na farko na biyu kuma Allah ya bayyana mana captain,tsantsan farin ciki maryam ta rungume lubna tana hawaye saboda an sosa mata inda yake mata k'aik'ayi. Wani irin dad'i sosai lubna taji lokacin da suka rungume juna da jinin jikinta,tana maganan zuci tana cewa ancuceni da aka rabani dake 'yar'uwata bazan iya gaya miki komai ayanzuba saboda damuwan da kike ciki,sannan dukka cewa hajiya khadija ba mahaifiyata bace ina sonta sosai har cikin raina saboda k'auna data nunamin wanda ko d'an cikinta bro marwan albarka,sun nunamin gata na k'arshe hakan yasa bazan gaya miki komai yanzuba dan naji tace ko daddy nama baisan da zancenba to amma yaya hakan ya faru kenan ya za'ace daddy baisan cewa niba 'yarsa bace? Yah ibrahim ne ya katse lubba da zancen zuci da takeyi idanunta rufe tana kance a kafad'ar maryam.
Afirgice ta d'ago da kanta tana kallon maryam,mamakine ya kama maryam d'in daduk wanda yake tsaye agun. Lubna ta wayance tace muje na rakaki gida *aunty* dan kema baki da lfy muje ki kwanta ki huta my luv muje,yah ibrahim yace kaka dan Allah kiyi hak'uri bari na kaisu gida zan dawo,maryam zatayiwa kaka magana kenan se lubna ta janyota da k'arfi tace muje nikam dan idan ina gidannan tofa abin bazai mana kyauba nan gaba,haka maryam ta bita a baya kamar wata wawiya se cikin motan yah ibrahim.
Yah ibrahim yace meyake damunkine my luv,mum naku ta kirani tana tambayana kokinzo gida nace mata a'a,munyita kiran numbernki bakya d'auka kuma mum tace mana rai a b'ace kika bar gida kina kuka shine tasa marwan yaje ko ina ya nemo mata ke hankalinta ya tashi sosai wlh waime yake faruwane my luv,kuma menene hajiya iya tayi miki haka? lubna dake zaune a baya itada maryam seta rushe da kuka tace wlh an cuceni my luv kuma bazan tab'a yafewaba,gara cutan da saddam yamin so dubu akan wannan cutan da akamin wlh, kuka sosai takeyi kamar ranta zai fita wanda yasa hankalin yah ibrahim da maryam tashi sosai tare da mamakin jin kalaman lubna. Maryam ta janyota jikinta tanata rarrashi har suka iso gidansu maryam,dukkansu suka wuce cikin gidan inda yah ibrahim ya wuce palon baba su kuwa suka wuce d'akin maryam,wani sanyi da ni'ima lubna ta tsinci kanta a ciki,maryam tace barina dubo mama ina zuwa,lubna tace to.
Fitan maryam kenan wayanta ya fara ringing,lubna tana dubawa taga *PEACH & CREAM* ai da gudu ta fito ta nufi d'akin mamansu tana cewa hello,ai kawai setaji muryan manosh yace apple, da gudu da murna take kiran aunty ga bro manosh...,

 ANTIN YARA Page 61-65
.
koda suka isa gida maryam kuka kawai takeyi,su abdallah kuwa suna gidansu mum dan ba'ama zo dasuba.
Iyayen maryam sun tausaya mata sosai,musamman yah ibrahim,ahankal
i aka fara shirye shiryen tfyansu kano domin aduba lfyar maryam kamar yadda shukrah tagaya musu,mama da yah ibrahim da kuma muh'd ne suka tafi kano inda dad d'in manosh yabiya musu kud'in jirgi se aminu kano.
Kamar da wasa doctor ahmad babban dr ne wanda kowa yasani, ya iya aikinsa sosai batare da b'ata lokaciba cikin 2days akayiwa maryam duk wani gwajegwaje daya dace,maganan shukrah dai ya tabbata domin k'odan maryam kusan dukma sun samu matsala wanda dolene se'an mata sabon dashe,ma'ana se'an sa mata wani k'odan.
Hankalin mama ya tashi sosai,tanata hawaye,yah ibrahim da muh'd ne suke rarrashinta tare da kwantar mata da hankali,kwanansu biyar suka koma yola.
Mamaki sosai akayi dajin matsalar maryam,mahaifinta yace zai fitar da ita zuwa *india* domin ayi mata aiki,amma sam maryam tak'i tace ita babu inda zataje se manosh ya dawo.
Su marwan sunyi iyakan k'ok'arinsu zuwa masallatai da kuma malaman sunna akan abinda ya sami amininsu manosh,sun raba kud'ad'e sosai kota ina zuwaga marasa k'arfi domin atayasu da addu'a Allah ya baiyana manosh.
Addu'oi sosai aketayi ba dare ba rana, kusan kullum ake kiran number manosh amma sam baya shiga yau kusan sati kenan.
Abdallah da alfiya kuwa tunda akace musu daddynsu yayi tafiyane shikenan suka yadda tunda dama yanayin tfya yayi 2to3month ma baidawoba,dan haka sam basu damuba.
Ahankali mahaifin manosh yake shirye shiryen tfyansu maryam india batare da sanin mahaifin maryam ba.
Idan kaga maryam da miher dole ka tausaya musu sun rame sunyi wani iri,barema maryam da damuwan yayi mata yawa kuma dama kunsan batada auki.
Miher tana son bro nata wanda kowa yasan da hakan,shiyasa majid yake iya k'ok'arinsa domin kwantar mata da hankali,hakama maryam kullum nasiha iyayenta suke mata da kuma yah ibrahim dasam baya son ganinta cikin damuwa,hakan yasa zaibada k'odanshi guda d'aya asawa maryam,amma sam koda aka gwada baiyi daidaiba.
K'awayen maryam gabad'aya sun zama abin tausayi domin ganin irin halin da maryam take ciki,rashida tace da marwan ita aje a gwadata idan har a'a iya sawa maryam k'odanta to wlh ta bayar da guda d'aya tunda zasu iya rayuwa da d'ad'd'aya, marwan yace karki dau luv zamu samo mafita amma ina tausayin aunty sosai wlh,friend na manoh dukkansu basa iya kocin abinci saboda rashin abokinsu,kowa yasan irin shak'uwar da take tsakaninsu.
Mahaifiyar manosh kuwa ta zama Allah sarki domin sun d'auki son duniya sun d'aurawa manosh dayake shine d'ansu na fari.
Kuma duk wanda yasan manosh ko kuma wata alak'a dake tsak'aninsu tofa dole ya shiga damuwa. Cikin sati biyu lbrn manosh ya baza ko ina dayake sojane mai kwazo ga kuma taimakon marasa k'arfi,sam bayida kyama kamar dai matarsa wato *auntyn yara*.
Lubna ce kwance a gidansu tana cewa mum nata gaskya mum lokaci yayi daya kamata in taimakawa maryam akan taimako da rufin asirin data min,mum zanje inba maryam k'odata guda d'aya,bazan iya bari anemo k'odan wani dabamu saninshiba asawa maryam.
Hajiya khadija tace lubna lfyarki kuwa bana so ki sake sa bakinki cikin maganannan,kuma wace irin taimako maryam tayi miki haka? Lubna cikin muryan kuka tace mum kinsan me,ada bani da wata mak'iya irin maryam saboda yadda nake k'aunar bro manosh araina,babu wanda yasan hakan dagani se miher naso in sanar dashi amma dayake shiba mijina bane senaji cewa ya samu mata a girei,nayi bak'in cikin hakan sosai tunma bansan wacece yake nemaba,ranan muka had'u da maryam da kuma friends nata a yakubu shopping plaza na yarda keyn motata batare dana saniba ta biyoni ta bani anan ne muka san juna da maryam harna karb'i numbernta. Mum daga bayane na san cewa maryam itace yarinyar da bro manosh yake so,tun daga lokacin tsanarta ya shiga zuciyata nayi niyan d'aukan mataki sosai dan in raba maryam da bro manosh. Lubna tayi shuru tana kuka sosai cikin tausayawa tace mum kinsan me? Nice nasa akayi kidnaping maryam lokacin da aka kusayin aurensu,nasa akayi nesa da ita yayinda nake samun duk wata lbr agun miher wanda ita kanta basan inada hannuba,tun daga numan nasan aka sakeyin nesa da ita mum zuwa jejin yankari dake jihar bauchi,amma dayake Allah ba azzalumin bawansa bane dukda cewa ita maryam tasan cewa nine nasa ayi mata hakan amma sam tak'i gayawa ko iyayenta da suka haifeta ta b'oye zancen cikin ranta domin bataso asamu matsala tsakanin familynmu da kuma familyn su bro manosh saboda tasan irin shak'uwa da soyayya dake tsakanin bro marwan da kuma bro manosh hakan yasa tayi shuru tabar komai aranta mum.
Marwan yana tsaye abakin k'ofa ya kasa shigowa yana sauraron lbrn da lubna take baiwa mum nasu,wanda mamakine sosai abaiyane a fiskarsa.
Lubna taci gaba da cewa mum bayan maryam ta dawo gidane,shi wanda na basu aikin yace inje muyi magana domin maryam tasan komai kuma k'ila zata tauna musu asiri,tsoron kar sunana ya fito dan yadda nake tsoro bro marwan yasa ranan na fita naje can inda saddam yake ya bayan GG..kuka lubna ta fashe dashi tace mum koda naje juice ya siyaya mana nidashi,ban kawo komai a rainaba saboda k'ishin danakeji a wannan lokacin kawai sena canye wannan juice d'in,shikenan ban sake sanin inda nakeba kodana farka senaji jikina wani iri mum saddam ya cuceni yamin fyad'e....
Mum ta kama salati tare da kwalla a idanunta itama lubna haka tace naso na kira miher amma senayi tunanin bazata rufamin asiriba dole za'a sani,shine na kira maryam ban b'oye mata komaiba na gaya mata komai,kinsan me mum hankalin maryam ya tashi sosai take tazo inda nake mum ta taimakamin ta kimtsa kaina hawayene cike a idanunta tare da tausayawa,muna tare da ita su bro manosh sukazo gun nida maryam muna ciki d'akin ab'oye a toilet munata addu'a saboda maryam tayiwa bro manosh k'aryan cewa tana cikin kasuwa suna sayayya se kuma gashi yazo inda muke a d'akin saddam,hankalin maryam ya tashi sosai badan komaiba sedan jinin dake kan katifar saddam kuma gashi ni babu yadda nake alokacin jikina rawa kawai yakeyi. Cikin ikon Allah mukaji suna cewa saddam ya gudu kenan tunda gashi harda kwad'o ajikin kofan,kuma wlh mum babu wanda ya kullemu ta waje,seda suka tafi muma muka fito da sauri shine maryam ta kawoni har gida tayi miki k'aryan cewa bigeni akayi da mota naji ciwo a k'afa,kuma mum maryam itace ta had'ani da ibrahim wanda yake matsayin yayanta,bata b'oye mishi komai akan batun fyad'en da aka minba ta gaya mishi komai,tare da neman amincewarsa akan ya aureni,k'aunar da ibrahim yakeyiwa maryam ne yasa ya aureni badon yana sonaba,kuma wlh mum koda na rana d'aya ibrahim bai tab'a nuna kyamarsa akainaba se kauna da kulawa na musamman kuma har gobe babu wanda yasan da wannan zance fyad'e dagani se maryam da ibrahim duk maryam tayi hakanne don ta rufamin asiri mum da kuma k'aunar da take min,gaskya mum maryam macece wanda ba'a samun irinsu a zamanin yanzu,ina ganin k'aunarta aduk lokacin da muka had'a ido da ita.
Dan haka zan iya yiwa maryam komai koda hakan zaisa in rasa rayuwatane to lallai zanbawa maryam k'odata guda d'aya watak'il zan iya biyanta da alkhairan datamin arayuwa......
Ba mum kad'aiba harta marwan dake tsaye a waje ya shigo rai a b'ace,take lubna ta gudu bayan mum dan yadda ta ganshi tasan sarai yaji komai dan haka ta fara kuka sosai tana cewa waiyo mum dan Allah karki bari ya dakeni wlh ina da ciki mum,bro marwan dan Allah kayi hakuri.
Mum tace karka tab'ata marwan nace ka kyaleta! Cak marwan ya tsaya yana kaima lubna sakon harara yace baga irintananba mum,daga taimako gashi ta b'ata mana suna tayi abin kunya,ke bari kiji ingaya miki dabadan cikin dake jikinkiba wlh yau dase na kusan karyaki wawiya mara hankali dole kibar mana gidanmu dan dama ke 'yar tsuntuwace ni kad'ai iyayena suka haifeni tsintattiyar mage kawai ya fita rai a b'ace ya fisgi mota.
Daga lubna har mum kuka sukeyi lubna tana bin mum da kallo mai d'auke da tambaya tace mum menaji bro marwan yake cewa? Wainiba 'yarku bace? Tsuntoni kukayi hakane mum? Mum da kuka yaci karfinta tace hakane lubna keba 'yarmu bace.
Lubna ta tsaya da kukanta tace tosu waye iyayena mum,a ina kuka samoni mum,meyasa kuka b'oyemin mum? Mum cikin kuka ta rik'o hannun lubna tace shi kanshi dad naku baisan iyayenkiba lubna domin ce mishi nayi na tsuntokine,lubna keba 'yar kowa bace se 'yar Alhaji muh'd atta. Zaro ido lubna tayi tace wanne kenan mum? Mum ta rungumeta tace wanda dai kika sani mahaifin maryam *auntyn yara* ku 'yan biyune lubna maryam itace babba sannan ke uwarku d'aya ubanku d'aya da ita lubna ki gafarceni dan Allah,cikin mamaki lubna ta janye jikinta tace taya hakan ya faru kenan mum? Kina nufin kowa yasan hakan kenan? Mum tace babu wanda ya sani dagani se hajiya iya kakarki lubna. Kuka sosai lubna takeyi tare da barin palon da gudu......
Da sauri auntyn yara ta waigo donjin me lubna take cewa,kai se sukayi gwaru akansu atare sukakai hannu goshinsu don sunji zafi dukkansu.
Maryam ta karb'i wayan hannunta tare da cewa sannu lubna ita lubna sannu take mata suna masu kallon junansu cike da murmushi,maryam tabar d'akin da sauri ta koma d'akinta tare dasa wayan a kunnenta tace cikin zumud'i tace *hello peach*, muryan manosh yace apple ya kike yasu abdallah,lfyanmu lau peach nah ina ka shiga ka barmu da tashin hankali da kewa,yace kiyi hakuri apple yanzuma na kirakine dan in gaya miki cewa ki mance dani a rayuwarki kwatakwata kamar baki tab'a had'uwa daniba domin bazan sake dawowa garekuba apple ki cireni a zuciyarki su abdallah kuwa ki gaya musu cewa na mutu kuma mamaci baya dawowa ta yadda zasu manceni daga k'arshe kuma ki samu miji wanda kike ganin zai rik'e min su alfiya ki aura koda d'aya daga cikin abokainane wannan shine dalilin dayasa na kiraki kinji apple,ya k'arashe maganan cikin murya maiban tausayi.
Ita kuwa maryam tunda taji abinda ya fara fad'a taketa zubda hawaye harya k'arasa. Jin tayi shurune ya sake kiran sunanta apple pls am sorry,na zab'i hakanne dan in cetoki daga sharrin shukrah bawai don wani abuba...bai k'arasa maganaba naryam ta katseshi da cewa ya isheni haka peach bana son sakejin komai daga gareka indai akan wannan magananne mubarta kawai,yanzu ka gayamin ya yake a ina kake me kuma shukrah tayi maka haka peach? Yadda manosh yaji muryan apple bashi yasan tana cikin tashin hankali,yace karki damu da sanin halin da nake ciki apple dama abinda na kira in gaya miki kenan ina miki bankwana ta karshe.
Da sauri da kuma ihu tace pls peach karka katse wayannan ka saurari abinda zance maka,ina cikin wani hali sosai peach na rashin lfy,k'odata gabad'aya sun b'aci dole se an min dashe,yanzu haka ana shirye shiryen fita dani india ne dan haka ka saurareni wata k'ila maganata dakai na k'arshe kenan zaiyu idan najema bazan dawoba dan haka inaso ka yafemin dukkan wasu abubuwa dana maka na rashin sani,sannan ina so ka sani har inbar duniya babu wani d'a na miji dazan iya zama dashi bayan kai kuma har inbar duniya bazan dena yin addu'a Allah ya d'auraka akan shukrah daduk wani abu mai cutarwa ameen,inaji ajikina cewa zaka dawo garemu peach,sedai bana tunanin zaka sameni sedai iyayenka da kuma yaranmu peach dan Allah ka kula min dasu domin kune farin cikina daga k'arshe ina k'aunarka k'auna ta hak'ik'a wanda baya k'arewa _i love you so much peach_, alfarma d'aya zan nema agunka shine inji kalmar soyayyata abakinka pls...?
Kwalla sosai manosh yakeyi idanunshi kamar attarugu,amma ina bazai iya gaya mata kalmar so ko d'ayaba,dan haka yace ina miki fatan alkhairi apple se anjuma......
Kuka sosai maryam ta fashe dashi tana cewa peach dan Allah karka barni ka tsaya ka gayamin cewa kana sona dan Allah my captain,kuka sosai takeyi tana kallon wayan. Mama da lubna da suke tsaye akanta tun ihunta na farko sune suka rik'eta sunta rarrashi dan sunji dukkan hiran maryam da manosh d'in.
Yah ibrahim da babane suka shigo dajin muryan kukan maryam suna tambaya ko lfya? Nan lubna ta gaya musu komai,inda mamaki ya kamasu sosai. Yah ibrahim yayita kiran numbern amma sam baya shiga,maryam dai se kuka takeyi tana ta surutai kamar wanda ta zare tana cewa baba manosh yace in samu miji inyi aure yana nufin ya sakeni kenan baba,menayi mishi dazai min haka baba,nagaya mishi halin da nake ciki amma koya kula baba,innalillahi wa'inna ilaihirraji'un. Lubna tana rungume da yarta itama kuka takeyi sosai,sam bata son ganin naryam cikin damuwa musamman ma datasan cewa yartace uwarsu d'aya. Hakadai ranan lubna bata koma gidantaba shi ibrahim d'inne ya koma saboda mahaifiyarsa ita kad'aice se mai musu girki. Daga baba har mama abin ya basu mamaki ganin yadda lubna takeyida maryam,bayan iyayenta sun rarrashetane se suka barsu a d'aki ita da lubna.
Yah ibrahim kuwa tunani iri iri yakeyi a zuciyarshi,ga kuma damuwan halin dayaga maryam aciki yau ya tausaya mata sosai harma yake tunanin inama dashine ya aureta da shikenan maryam bata da damuwa sam,amma ina haka Allah yake tsarawa kowa rayauwarsa. Wayarsa ce tayi k'ara number manish ne,mamaki yayi sosai tare da d'auka da sauri yace slm,wslm yaji muryan manosh,basu gaisaba manosh yace na kirane don inji cewa dagaskene za'a fitar da aunt india? Ibrahim yace eh hakane,manosh yace to shikenan idan kun dawo ka sama mata miji ka aurar da ita dan nikam bazan dawo garekuba na zab'i in zauna anan domin ceton apple zan iya jure komai ibrahim shiyasa nafiso ace kaika auri aunt ba waniba pls ka auri aunt nasan zaka kula da ita kamarni. Ibrahim yace mekake fad'ane captain insha Allah zaka dawo kuma kadena sa ran cewa wani abu zai same aunty babu abinda zai sameta da yardan Allah zaka dawo kushi gaba da zamanku munata addu'a kuma shukrah setasha wahala wlh muguwa...tsawa maikyau ibrahim yaji akunnensa ana cewa wlh k'arya kake ibrahim wahala kam sedai auntyn yara amma badai niba,kuma zanga yadda zaku karb'o my manosh daga hannuna dama kai kad'aine mai taka min birki kuma ina so kasan cewa my manosh yabarku kenan har abada bazaku sake ganinshiba,sannan ka gayawa mahaifin maryam ya kiyayeni wlh su dena b'ata lokacinsu waisu suna so suga bayana to wlh idan bai dena shiga gonataba sena tozarta maryam d'in da kuke ji da ita. Hhhhh ibrahim yayi dariya yace dama ashe kece shukrah,kece kika ari muryan captain kike so ki b'ata tsakaninsu da aunty,to Allah ya tona asirinki muguwa,ina so kisan cewa aunty tafi k'arfinki shiyasa har yanzu kika kasa mata komai shine kika b'ullo mata tasan muryan mijinta koh,tota Allah ba takiba wannan kad'ai bai isheki shukrah,komai kikayi seya warware hakan yana nufin bazaki tab'a samun nasara akanmu bane kuma mahaifintama yafi k'arfinki hatta shi captain yafi karfinki wlh kawai dai jarabawace Allah ya sauko mishi dashi kuma insha Allah zamuci wannana jarabawan muzuba dake shukrah *QUR'AN* yana sama da komai acikin duniyan kuma dashi zamu karb'o captain agurinki idan kuma kin isa toki hanamu d'aukoshi daga gareki kawai lokaci muke jira kekanki kisan duk duniya babu wanda captain zai bud'ewa zuciyarshi ta shiga ta zauna se *aunty* . Haushi da takaici yasa shukrah katse wayar
Yah ibrahim ya tsinci kanshi dayin murmushin tare dajin dad'in sanin cewa ba manosh bane yayi magana da aunty shukrah ce. Take ya kira baba a waya ya gaya mashi komai,baba baiyi mamakiba dan yasan babu abinda aljanu basayi, take yaje ya sanar dasu maryam dan hankalinta ya kwanta.
Ai kuwa dad'i sosai taji tare dayin add'ua Allah ya kare mata mijinta ya kuma dawo dashi garesu.
Marwan kuwa yana kwance ne kawai amma yakasa bacci dan irin abubuwan dayaji yau da kuma gani. Tun bayan barin su lubna gidan yaketa tambayar hajiya iya kakarsa meke faruwane danshi kansa yasan akwai wani abu dayasa lubna tayi mata hakan amma sam hajiya iya tak'i cemishi komai se kukan nadama da taketayi babu sassaushi. Haka marwan ya gaji ya tafi gida gun mum nasu,koda ya gayawa mum nasu abinda lubna tayiwa hajiya iya sam mum batayi mamakiba,shima marwan d'in ya lura da yanayin mum d'in nashi wanda yasashi tambayar mum nasu yace wai meke faruwane mum nakasa fahimtar komai tabbas akwai wani abu dayake faruwa mum dan Allah ki gayamin.
Marwan ya kamota suka zauna yana share mata kwalla.
Mum ta dubi marwan tace zan gaya maka marwan amma sekamin alk'awarin bazaka bari mahaifinka ya d'auki mummunan mataki akainaba, cikin rashin fahimta marwan yace banganeba mum?
Mum tace marwan dad naka yana k'aunarka fiye da komai a duniya,idan yasan abinda na'aikata tonasan zamana dashi yazo k'arshe, kaine zaka iya hanashi rabuwa dani d'ana saboda k'aunarka da yakeyi.
Marwan ya sauke ajiyar zuciya yace namiki alk'awari mum har abada bazan bari ku rabu da dad ba. Mum tace nagode marwan, sannan ta fara bawa marwan lbr kamar haka...
.
marwan ya rasa mema zaicewa mum nashi,dan tsabar yadda jijinshi yayi sanyi kamar k'ank'ara. Cikin sanyi murya yace mum danasan abinda kika aikata kenan daban miki alk'awarin dana d'auka mikiba,amma koba komai ke mahaifiyata babu abinda zan iyayi ko kuma ince miki,sedai kiyi hakuri amma sam abinda kukayi baidaceba sam wlh mum abin babu dad'i ji. Matsowa yayi kusa da ita yana kwalla kamar yadda takeyi yace mum kidena kuka inaso kimance da cewa kin bani wannan lbrn,ki d'auka cewa har yanzu sirrine kamar yadda kuka rufeshi keda hajiya iya,dan gaskya mum nibansan ne nake cikiba a yanzu haka. Komin dad'ewa gaskya zai fito wanda bansan yazan tsinci kainaba a wannan lokacin da kowa zaisan me mahaifiyata da kakata suka aikata.
Jiki babu kwari ya mik'i zai fita tayi saurin kamoshi tace dan Allah kaban mafita ya d'ana. Mum wlh babu wata mafita danasan zan baki akan wannan lamarin domin baki bani wani ilimi akan hakanba lokacin da kuka bani tarbiya keda dad. Mum tace nasan ban kyautaba shiyasa nake neman nafita marwan? Marwan yace mafita shine kisami dad ki gaya mishi komai tun kafin lubna tatona muku asiri mum.
Bayan fitan marwan ne mum taketa kukan dana sanin akan abinda suka aikata. Shikuwa marwan gida ya koma da zazzab'i mai k'arfi daya rufeshi,seda rashida ta kira dr muh'd a waya yazo gida yayi masa allura da kuma magunguna inda suke mishi sannu. Sam marwan ya kasa had'a ido da abokan nashi saboda tun a yanzu kunyansu yakeji bare kuma ace gaskya ta bayya kowa yaji.
"Lubna ce kwance tana bacci ad'akin maryam hankalinta kwance,ita kuwa maryam se mamakin kulawar da lubna tayi da ita takeyi acikin zuciyarta tare dajin sonta a ranta. Wayan lubna ce yake k'ara koda maryam ta duba setaga yah ibrahim ne,daidai nan lubna ta farka tare dasa wayan a kunne tace hello,yace kin tashi lfy yasu aunty,tace lfyansu lau ya mama,yace tana lfy ina hanyan zuwa d'aukanki da fatan kin shirya? Ta murza ido tare da kallon maryam tace wlh yanzu na tashi ko wanka banyiba kabari se anjuma kad'an pls...? Yace ok naji amma ki tabbata kin shirya dan zamubi gidan marwan mu gaisheshi bayida lfy tun jiya zazzab'i mai k'arfine ta rufeshi wlh. Subhanallah!tobari kawai na shirya nan da 1hr sekazo.
Maryam ta kalli lubna tace lfy? Lubna tace bro marwan ne ba lfy zazzb'i sosai,maryam tunda nake ban tab'aganin rashin lfyanshiba bro marwan yana sona sosai har cikin ranshi dukda zafinshi amma akan gaskya yake komai nashi i respect him so much aunty,maryam tace eyyah nima barina shirya muje tare inyaso zanbi gunsu miher zuwa yamma sena dawo.
Maryam ta gama shiri tsaf,ita kuwa lubna tana zaune tana k'are mata kallo,maryam tace naga kina zaune,lubna tace eh bazan maida kayan jikinabane shiyasa dan sunyi datti. Maryam ta gane me take nufi hakan yasa ta d'auko mata zanin da manosh ya saya mata tunda ta d'inka bata tab'a sawaba ta batashi tace ga wannan kisa,godiya sosai tayi ai kuwa nan danan ta mik'e tasa sun mata kyau sosai ajikinta ta juyo tace aunty nagode kayan sun amshi jikinki sosai wlh harda rungume maryam,azuciyar
ta tace nagode sosai 'yar'uwata jinin jikina.
Mama ta shigo tace todai sekunci abinci kafin ku tafi,bamusu sukaci amma maryam kad'an taci dan dama tunda aka nemi manosh aka rasa tadena cin abinci. Ita kanta mama lubna tana burgeta kome dalili oho,ita kuwa lubna sakewa sosai tayi dasu ko'ajikinta dukda ta lura da cewa suna mamakin yadda ta sake dasu tazama kamar 'yargida.
Gun motan yah ibrahim suka nufa bayan sun gaisa suka shige maryam ce a baya suna tfy ta hango manosh daga nesa. Peach ta kira sunanshi cikin mamaki wanda yasa yah ibrahim tsaida mota da sauri suka had'a baki tare da cewa ina yake? Tayi musu nuni da hannu zuwa inda yake tsaye ajikin wata black car. Mamaki sosai sukayi dan tabbas shine tsaye sanye da kakin sojojinsa ya hard'e hannaye yana duba agogon hannunsa bisaga dukkan alamu wani yake jira...
.
Marwan auren so da k'auna mukayi da dad naka kuma shi shi d'an wan mahaifinane auren dangi aka mana nida dad naka.
Tun ina 'yan'mata Allah ya d'oramin son yara musamman mata,kowa yasan da haka a dangi. Bayan munyi aure da mahaifinka ne kusan 2yrs kafin na samu cikinka,bazan iya gaya maka burin da muka d'auka akan wannan cikinba,dan muna ta fatan Allah yasa mace zan haifa,amma se yazama kaine marwan na haifa,hakan baisa na fidda ran haifan maceba.
"Marawan har kakai 12yrs ban sake sake samun cikiba,babu irin damuwa da tashin hankali da bamu shigaba harta dangi,dayake ansan yadda nake son mace,gashi dangi kam kowa namiji yake haifa ba mace ko d'aya. Hajiya iya mahaifiyar dad naka tana sona sona tamkar 'yar cikinta sam bata son ta ganni cikin damuwa,har zamuje gidan marayu d'aukan yarinya,amma se mahaifin dad naka wato wan mahaifina yace a'a bai aminceba,hakan yasa muka hakura har wata rana naje girei gun hajiya iya yini...
"Muna zaune se aka zo da sallama wai wata mata tana nak'uda kuma ta galabaita sosai gashi duk mak'otan sunce bazasu iyaba sedai a nemo tsofi,sakamakon mijinta baya kusa,kuma yana fama da kansa ana tunanin idan an kaita asibitima kud'i za'a nema lokacin kuwa kowama yana fama da abinda zaicine. Hakan yasa nida hajiya iya mukaje gun wannan mata mai nak'udan wanda batama san inda takeba ta zama abin tausayi bata cikin haiyacinta sam.
Munfi awa muna kanta cikin ikon Allah ta haifi bby girl kyakkyawa,kwalla ne ya zubo a idona dan ji nayi kamar in gudu da jaririyar,muna cikin murnan kenan sega wani kai ya fito ashe dai 'yan biyune dukkansu mata,murna sosai mukayi nida hajiya iya muna cewa ashe 'yan biyune shiyasa ta wahala haka.
Tofa shine hajiya iya tace dama mijin natan baida hali kuma gashi har yara biyu,dan haka tace in tafi da d'aya tunda babu kowa a waje,duk wanda suke jiran haihuwan harsun gaji sun tafi saboda sunga bata haihuba. Ni kuwa banyi tunanin komaiba saboda yadda nake son mace,a d'ankwalina na nad'e jaririyan nasata cikin himar na koma gidan hajiya iya,acan na mata wanka da komai na koma gun hajiya na d'auki kayan jaririya d'aya dayake sund'an sayi kayan kad'an,na koma na sama mata.
Ita kuwa hajiya iya tayiwa jariya da uwar wanka ta kimtsasu saf,amma har'a lokacin uwar jaririyan bata farfad'owa harse bayan awa biyu,koda taga abinda ta haifa murna sosai tayitayi tare dayiwa hajiya iya godiya.
"Bayan hajiya iya ta dawo gidane,tace maza in tafi da jaririyar gida kar asirinmu ya tonu,tsoro ya kamani nace tome zan gayawa dad naka? Tace zata mishi bayanin cewa an sami jaririyar ne a hanya aka ajiyeta kuma kowa na tsoron d'auka saboda yadda duniya ta canja,shine ita ta d'auka mana tunda tasan muna son 'ya mace. Dayake lokacinma dad naka yana umrah shine komai yazo da sauk'i kuma haka muka gayawa kowa na dangi da kuma abokan arziki harda kuma....
Hajiya khadija ta tsaya anan da lbrnta tana kuka,marwan kuwa jikinsa yayi sanyi yama rasa me zaice mata saboda shidai asaninsa wannan abunda mum nashi da kakarsa sukayi sata kenan satan jaririya. Mum ta lura da yanayin marwa tayi saurin rik'o hannunsa cikin muryan kuka tace marwan karka manta kamin alk'awarin zaka taimakeni amma tun yanzu naga rashin jin dad'i afiskanka,marwan karkace komai ka saurari ci gaban lbrn..
Haka na rik'e jaririyannan na samata sunan hajiya iya muna kiranta da *LUBNA* gata sosai ta samu agun mahaifinka,kuma dukkanmu muna sonta tsakani da Allah..marwan ya katse mum nashi da cewa naji mum kuma na fahimta,yanzu lubna 'yar gidan wayene,su wanene iyayenta a ina suke? Mum tana kuka sosai tace marwan iyayen lubna sunan a raye kuma acikin girei sannan 'yartama tana raye dan lubnan itace k'arama. Marwan ya mik'e tsaye yace mum baku kyauta ko kad'an wlh,wannan abinda kuka aikata bansan me zance akaiba kun kyauce sosai wlh kun raba yarinya da iyayenta da 'yar'uwanta yanzu idan maganannan ya fito waje duniya sukaji mum ya kike so inyi da raina,sunanefa zai b'aci mum ace mahaifiyata ta aikata hakan mum,da wani ido zan dubi jama'a musamman abokaina mum? Kwallane yake zuba daga idanun marwan yace a ina suke? Mum ta mik'e ta kasa dena kuka tace marwan se yanzu nake nadaman abunda na aika busa son zuciyata.
Marwan yace no mum,dukda tarbiyan da kuba lubna kiga dai abinda ta aikatawa *aunty* yanzu da asirinta ya tonu a lokacin da dawani ido zan kalli princ mum,kinsan yadda nake son manosh kinfi kowa sanin shak'uwarmu dashi da kauna dake tsakaninnu ashe ankama lubna ce tayiwa aubty haka daya zanyi,kumafa kiga ita *auanty* ne ta had'a lubna da miji nagari irin ibrahim,mum kinsan yadda ibrahim yake son aunty,wlh daya san lubna ce tayiwa aunty haka wlh bazai tab'a bariba,amma kuma duk wannan bai isaba kika yaudaremu dukkanmu dangi akan tsintota kukayi alhali bahaka maganan takeba haba mum... yanzu waye mahaifin lubna ki gayamin mum?
Cikin nuryan kuka sosai tace bakowa bane *illa mahaifin maryam aunty'n yara* marwan aunty itace twin sister'n lubna ita ta fara zuwa duniya kafin lubna,ta k'are maganan tana zama a k'asa kamar kayan wanki. What! Marwan ya tambaya da k'arfi da fiskan mamaki tare da juyawa yana kallon mum nashi kamar yaga dodo yana fad'in *innalillahi wa'inna ilaihir raji'un*,ita kuwa mum kuka kawai takeyi tana rik'e da hannun d'an nata...
.
Da sauri yah ibrahim ya tsaida motarsa suka fito dukkansu suka nufi gun da *manosh* yake tsaye,cikin mama maryam ta rik'o hannushi tace peach? Ahankali ya juyo yana kallonta kamar wawa,yah ibrahim yace aunty sakeshi...ai bai k'arasa maganaba seka wata kyakkyawar budurwa ta fito daga wani shago kawai ta d'auke maryam da mari tana cewa ke wace irin shashashace dazaki rik'emin miji?
Ai kafin yah ibrahim yayi magana lubna ma tayi saurin d'auke budurwan da mari tace ai shashashun suna dewa wawiya jaka ke har kinkai a tab'a mijinki,yah ibrahim ne ya shiga tsakaninsu yanayiwa lubna fad'a,ita kuwa maryam sam bataji marinba tamaida hankalinta gun manosh da yake tsaye yanata kallonta baya ko kyafta idonsa. Ahankali ta sake dawowa gefensa tana mai zubda kwalla tace *peach* jikina yana bani cewa kaine dan Allah kacemin wani abu. Kawai setaji yace baiwar Allah banine wanda kike tunaniba,sunana *muawiya* sannan wannan matatace. Kuka mai k'arfi maryam ta fashe dashi tare dabarin gurin aguje zata koma mota nan sukayi kicimus da majid,kallon juna sukeyi har cikin ido tanata hawaye tace majid dan Allah ka k'are mishi kallo wancan ba captain bane duba kakinsafa dan Allah kazo muje nasan zaka iya ganeshi tunda tare kuka taso.
Da sauri majid ya karasa lokacin fad'a sosai akeyi tsakanin lubna da wannan budurwan tace cewa kisa maganata a ranki cewa senayi maganinki,lubna tace ta Allah ba takiba banza mara hankali da kyar yah ibrahim ya janyo lubna ya kaita mota gun maryam se faman kuka takeyi lubna ta zauna a gefenta tana rarrashinta. Majid yaje dabda manosh ya tsaya yana k'are masa kallo tun daga k'asa har sama,shima manosh d'in kallonsa yakeyi kamar dai yadda yayiwa maryam,majid yace *dude kaine*? Budurwan tace yau naga ikon Allah waiku wasu irin mutanene haka,kawai kunzo kun damemu kunat....tsawa mai kyau majid ya daka mata kimin shuru badake nakeyiba! Take ran budurwan ya b'aci idanunta sukayi jah jazur kamar attarugu tayi saurin rik'e hannun manosh tace kadaiga yadda akacimin mutunci amma ka kasa sewa komaiko,shikenan mutafi dan idan nacigaba da zama anan to lallai mutanen dake yankinnan kam zasu shiga cikin matsala. Yah ibrahim da majid suka kalli juna sukace matsala kuma? Daidai nan maryam ta fito daga mota da gudu tana cewa yah ibrahim wlh peach d'inane shine gashi yana min bye bye. Koda yah ibrahim da majid suka maida kallonsu ga manosh da budurwan se sukaga wayam,babu su kuma babu motarsu.
Mutanen dake gurin kowa kafa menaci ban bakaba kusan rabi duk sun gudu,su kansu yah ibrahim sun tsorata sosai,majid yace ina suka shiga? Maryam cikin muryan kuka tace wlh manosh ne yah ibrahim wannan duk aikin shukrah ce wlh sune lokacin da take magana kaida majid kuna kallon junanku se manosh ya juyo yana kallon inda seting motarmu take shine ya d'aga min hannu yanamin bye daga nan kuma suka b'ace yah ibrahim dan Allah kace tadawo min da mijina inda manosh ya tsaya nan maryam taje ta zauna agun daya ajiye kafafunsa tanata kuka,lubna da yah ibrahim ne suka d'agota dakyar suka kaita mota shima majid ya shiga nashi suka koma girei gidansu maryam.
Koda baban maryam ya samu lbrn abin shuru kawai yayi danya rasa mezaice,mama kuwa tanata rarrashin maryam tare da cewa lubna kekuwa meyasa kika rama mata marin?yanzu gashi kin mari aljana idan kuma ta d'auki matakifa gaskya bana son wani ya cutu ata dalilin maryam. Lubna tace mama zan iya bada rayuwa indai akan maryam ne kuma matuk'ar ina raye tofa sedai ad'auki raina bazan tab'a bari a cutar da itaba wlh har abada anyina farko kuma anyi na k'arshe wlh Allah ya isa bazan tab'a yafewa Allah ya isa mama....tanata kuka wanda hankalin kowa yadawo gun lubna se zagi da fad'e-fad'e takeyi wanda babu wanda yafahimci abinda take nufi se ita kad'ai.
Maryam ce ta kamota tace lubna ki nutsu mana meyakawo zagi kuma nan lfyanki kuwa? Tace lfyata kalau aunty wlh an zalinceni kuma bazan yafeba Allah ya isa! Da k'arfi ta k'arasa maganan,nan dai hankalin kowa ya tashi akace gaskya akwai matsala,yah ibrahim ya kamota,takisam ta mannu ajikin maryam tanata kuka. Majid yace gaskya akwai matsala kodai shukrah ce ta maidata hakan? Hankalin kowa ya tashi domin kowama abinda yake tunani kenan.
Maryam ta rungumeta tace a'a majid shukrah bata isa ta mata komaiba lubna dan Allah ki bari kicemin lfyarki kalau kinji,lubna ta d'ago da kanta tana kallon maryam tace lfyta kalau aunty babu abinda yake damuna se abu d'aya,maryam tace menene wannan abun? Lubna kamar zatayi magana se kuma ta fasa domin yadda take k'aunar hajiya kadija aranta bataso ta tona mata asiri,nan ta sake fashewa da kuka tace kigafarce aunty bazan iya fad'aba sannan ta mik'e da sauri ta koma d'akinsu tanata kuka mai k'arfi,su kuwa aka barsu da kallon labule,kowa hankalinsa atashe kuma tunaninsu shine kodai shukrah ce tayimata wani abu akan marin data mata?
Bayan sun gama magananne yah ibrahim yace aunty kiramin lubna tazo mutafi,bamusu maryam ta mike jiki sanyaye tanata tunanin had'uwansu da manosh yanzu,tace dama rungumesa nayi lokacin dana ganshi,wayyo Allah peach Allah ya dawomin dakai ya mijina uban yarana i luv u so much peach dan Allah ka dawo garemu. Maryam bata sammata shigo d'akinba kuma ita ta d'auka cewa acikin zuciyarta take wannan maganan bata cewa lubna tajiba. Lubna ta dakata da kukanta tace kiyi hakuri aunty insha Allah bro manosh zai dawo gareki shukrah bata isatayi komaiba wlh,itama kuma lokaci da zaidawone baiyiba kidena kuka pls aunty dukda dai nasan yadda kikeji amma bana so inganki cikin damuwa pls kiyi hakuri mucigaba da addu'a kinji aunty? Rungume juna sukayi sunata kuka sannan maryam tace yah ibrahim yana kiranki wai kije ku tafi kuma dan Allah kugaida marwan kice nima zanzo ko zuwa gobe insha Allah. Lubna dai bata soba amma babu yadda ta iya seta mike ta shiga palon baba rai ab'ace tace baba mama se'anjuma sannan ta fita waje tanata kuka,mamakinta ya sake kamasu dukkansu haka dai suka fito suka tafi tanata kuka.
Tun a hanya ibrahim yake tambayarta dalilin kukanta amma sam tamak'i kulashi har suka iso gidan marwan. Nanma da kukan ta shiga gidan amma tad'an tsagaita sukadai gaisa da rashida sannan tagaida bro marwan yanata k'are mata kallo ita kuwa sam tak'i kallonsa. Rashida tace lubna yanaga idanunki sunyi jah haka? Lubna tace bakomai,yah ibrahim ne yabasu lbrn abinda ya faru,ahankali marwan ya mik'e zaune yace kunga manosh? Ibrahim ya tabbatar mishi da zance,mamaki sosai sukayi dukkansu,rashida tace Allah sarki maryam Allah ne kad'ai yasan yadda takeji acikin ranta yanzu haka,dabadan rashin lfyarkaba danaje na d'ebemata kewa dan nasan tana cikin damuwa da tunani musamman ma yau data ganshi dan tana matuk'ar k'aunar captain sosai,hawayene yakebin idanun rashida,ita kuwa lubna fita tayi da gudu tana kuka bata tsaya ko inaba se cikin mota. Da sauri rashida tabi bayanta tana tambayarta ko lfya? Shi kuwa yah ibrahim lamarin ya fara damunsa sosai. Marwan yace ibrahim ina neman wata alfarma agurinka akan lubna,dan Allah duk wani abu da zata maka kayi hakuri kamata uzuri ninasan irin k'aunar da lubna takeyiwa aunty. Ibrahim yace bakomai wlh zamu tafi,haka dai sukayi sallama suka tafi rashida dai bataji komai daga gun lubna ba.
Yah ibrahim ne da lubna kwance akan gado yana cewa haba y luv yau kwana nawa kenan rabonda wani abu ya shiga tsakanina dake? Tace to ai period nakeyi shiyasa,yace amma fa kwananki uku kenan da gama period d'in nabarki ranan jiya kuma agidansu aunty kika kwana sannan kuma yau kicemin bakya mode? Cikin sanyin murya tace dan Allah kayi hakuri wlh damuwace tamin yawa bazaka tab'a gane kainaba shiyasa nake baka hakuri idan kuma ka yarda zaka gamsu kai kad'ai shikenan bisimillah nidai bazaka samu tallafinaba yau. Ibrahim baiji dad'in kalamantaba gashi yanada bukatarta hakan yasa ya daure ya juya yayi kwanciyarsa.
Shurun dataji yayine yasa tasan cewa fushi yayi,ahankali take kiran sunanshi my luv dan Allah kayi hakuri karkayi fushi kamin uzuri tunda ban tab'a maka hakanba se yanzu banaso kayi fushi domin bana son tsinuwan Allah ya tabbata akaina kaji my luv tana rungume da bayansa ajikinta. Yace naji amma ki sakeni dan kina kara tayarmun da hankaline,bamusu ta sakeshi tare dayin godiya se wayansa ta fara ringing. Da sauri ya da'uka dan ganin mahaifin manosh ne mai kiranshi,bayan sun gaisane yake sanar dashi cewa tafiyansu india ran monday ne shida baba mama da maryam da kuma lubna,yah ibrahim yayi godiya sosai sanan ya ajiye wayar ya juyo yana kallon lubna yace tfyarmu ran monday amma banda ke,ta marairaice tace habamana my luv najifa lokacin dayacemaka da lubna saboda yasan kila zaku wuce 4month kuma dama ka'ida ba'ason miji yabar matarsa har tsawon watanni hud'u,yace to aike babu amfani zuwanki tunda kina hanani hakkina, dasauri ta rungumoshi tana dariya tace wlh nadena amma pls karka barni my luv kaga ai zan taya mama kula da aunty ko? Shima murmushi yayi sannan ya matseta ajikinshi suka fara sarrafa junansu kamar zasu had'iye junansu....
.
Bayan yah ibrahim da lubna sun samu cikakkiyar gamsuwa da junansune suka wuce toilet bayan sun tsabtace jikinsu ne se suka sake shirin kwanciya amma duk sun kasa bacci babu abinda yake musu yawo a kwakwalwa se b'acewar manosh da shukrah da sukagani d'azu agaban idanunsu kamar a fimlm.
Wannan abu ya dami mutane dewa sosai harta wanda abin ya faru aaban idanunsu sun kasa yadda da hakan ya faru dan gani sukeyi kamar amafarki. Hakan yasa akakai lbrn gidan *radio gotel* wanda basusan da faruwan abun bama tofa gashi yanzu sunji agidan radio magadai ya baza ko ina agarin *Adamawa*. Hakan yasa majid yaje gidan *TV GOTEL* akayi hira dashi inda yake cewa aabansa akayi komai ba kuma tatsuniya bace gaskyane domin abokinsune wanda kusan kowa ya sanshi tunda sojane mai kwazo sosai. Hakan yasa akayita rok'on jama'a cewa sutaimaka a addu'a akan b'acewan captain manosh,kokuwa d'aukeshi da aljana tayi tsawon wata uku kenan harda kwanakima. Wanda matarsa itace maryam muh'd attah wanda akafi sani da AUNTY'N YARA mahaddaciyar qur'ani, cikin kwanaki biyu ko ina se faman rok'on ALLAH aeyi akan manosh da kuma duk 'yan'uwa musumai da irin hakan ya shafa,domin idan idan ka shiga damuwa tofa karkayiwa kanka addu'a batare dakasa 'yan'uwankaba.
Maryam kuwa tun wannan lokacin ta sake shiga matsanancin damuwa fiye danada. ita kuwu lubna yah ibrahim yayi iyakan k'ok'arinsa dan yaji ta bakinta saboda canji dayagani tattare da ita musamman akan aunty, amma sam ta'i gaya mishi komai dan batamasan ta ina zata faraba.
Ana saura kwana uku tafiyansu aunty india,sega hajiya khadija agidan hajiya iya. Koda hajiya iya ta ganta seta fashe da kuka itama ma hajiya khadijan kukan takeyi,bayan sun gama koke kokensune hajiya khadija tace da hajiya iya dan Allah hajiya muyi k'ok'arin fad'an gaskya tunkafin su auntyn yara subar k'asar watak'ilama tfyarsu kenan bazamu sake had'uwa kuma gaskya bazan so hakanba yazama dole mufasa wannan dad'ad'd'an kwan kowama yaji warinta ban damu da abinda zai biyo bayaba nidai mu sauke wannan zunubin da muka d'aukawa kanmu. Hajiya iya tace shikenan khadija karki damu nina haddasa komai kuma zan wankeki da yardan Allah....garakam! Gara kugayawa duniya abinda kuka aikata kaka,konima zan samu lfy,juyowa sukayi sukaga marwan tsaye akansu ranshi a b'ace yake magana yanacewa wlh baki kyautaba kaka kinso kanki dewa awannan lamarin natabbata koda daddy zai zauna bashi da d'a aduniya bazai tab'a yarda da wannan abinba wannan aiba sonshi kikeba hajiya danba haa ake son mutumba,hajiya iya cikin muryan kuka tace jikana marwan bason mahaifinkane yasa nayi hakanba sedan son da nakeyiwa mahaifiyarka da kuma toshewar kwakwawa irin nawa. Marwan yace babu toshewar kwakwalwa anan kaka,domin wannan abun da kikayi se mutum mai wankakken kwakwalwane zai iya aikatashi kawaidai son zuciyane irin naki da kuma rashin tausayi,kaka matar dabasan yanda akayi ta haihubama dan tsabar azabar datasha kiduba yadda ake kwatanta rad'ad'in haihuwa wanda kema kinsan hakan tunda kin haifa amma shine kika sace mata yarinya haba kaka! Wani irin shaid'anune suka shiga kanki awannan loacin!? Mum ce ta mik'e tace marwan kayi ahankali kakarkacefa duk lalacewa. Afusace yace tabbas kakatace shiyasa nake gyara mata kuskurenta mum ba lubna da iyayenta kad'ai kuka cutaba hardani da dad! Gabad'aya kun gama b'ata mana suna mum,kuna tunanin zaku gayamusu gaskya suyi hakuri abar maganan to mum sauran jama'an garifa?? Shikenanfa sunanmu yab'aci kun cucemu kuma wannan sunan bazai tab'a gyaruwaba domin yariga dayazama tabo! Kuka sosai marwan yakeyi tare da juyawa hanyan waje yace nizanyi tfy yau nida rashida se bayan wata d'aya zamu dawo kigafarceni mum...
Hawaye yakasa tsayawa daga idanunsu dukkansu sunabinsa da kallo harya fita.
Mum tasan halin d'anta marwan sarai,sam bayason zalinci,gashi dama rashin amininsa manosh yafi komai d'aga mishi hankali,yanzu kuma gashi tasake k'ara mishi damuwa wanda har yasashi rashin lfy kuma gashi yatafi ya barta.
Rashida ce zaune ita da aunty tana gayamata irin sauyi sosai da take gani agun marwan,ko hakkin aurenta ya denabata kwata-kwata,sannan bayason duk wani magana dazata gayamishi seyace dan Allah kirabu dani. Aunty tace kiyi hakuri rash,watakila yanada damuwane kuma kinsan maza idan har sunada damuwa tofa basa buk'atar *sex* domin shi sex jindad'i da kwanciyar hankali shine ke kawosa wanda ba mijinki ne kad'aiba duk mazan duniya haka suke. Dan haka kiyi hakuri *kimishi uzuri pls?* Sannan kikai kukanki gun Allah,Allah ya daidaita al'amurorin mijikin su koma yadda suke insha Allah komai zai daidaita,kuma banaso ki sake gayamin duk wani hali dakike ciki keda mijinki domin babu wanda zai miki maganin damuwanki se ALLAH.
Rash taji dad'in kalaman maryam har cikin ranta kuma taji sanyi azuciyarta,sannan tabbas itama se yanzu take danasanin gayawa maryam sirrinta da mijinta tunda wannanma shine karo na farko dasuka fara samun matsala itadashi. Sallamar marwanne ya tsaidasu suka fito zuwa palon baba.
Marwan yace aunty zamu tafi,dan Allah ki k'ara hakuri mucigaba da addu'a insha Allah captain zai dawo garemu musammanma gun apple d'inshi da kuma abdallah alfiya. Murmushi sosai tayi dan tasan yanaso yasata farincikine,tace insha Allah kuma nagode sosai Allah ya kiyaye hanya akulamin da k'awata sosai pls,murmushi yayi na k'arfin hali yace baki da matsala indai wannanne aunty. Rash tana murmushi ta mik'e tare dacewa barinaje na d'auko jakata.
Bayan fitar tane marwan ya sunkuyar da kanshi k'asa yace aunty dan Allah kiyi hakuri da abinda zakiji bayan tfyarmu,aunty banaso ki tambayeni komai zakiji komai bayan mun tafi,kuma dan Allah kiyafi wanda suke da hannu cikin abin badanniba sedan ALLAH,shiyasa zanyi wannan tfyn saboda inaga yin hakan zaimin d'an sauk'i araina,sannan banaso kigayawa kowa abinda na gayamiki ayanzu,ki rik'eshi amatsayin irin sirrin da kika rikewa *lubna* abaya. Yana kaiwa nan ya mik'e yafita waje ita kuwa jikinta gabad'aya yayi sanyi dai-dai nan rashida ta shigo tace to aunty semunyi waya kenan,ta daure tace to Allah ya tsare Allah ya dawo daku lfy,rash tace ameen sannan suka fito waje rash ta shiga mota marwan yaja dasauri suka tafi inda akabar aunty atsaye jiki babu kwari maganganun marwan ne suketa mata yawo a kwawalwar ta...
.
Jiki sanyaye aunty ta koma cikin gida dama mama bata nan,dan haka ta wuce d'akinta ta kwanta tana tuno kalaman marwan. Tace me yake nufi da wad'annan kalaman nashi? Kuma me yake nufi da sirrin dana b'oyewa lubna? Kardai na fyad'en da saddam yayi mata? Towaya gaya mishi indai hakane? Duk wannan tambayoyin ita kad'ai takeyiwa kanta bayan tasan bata da amsoshinsu.
Hakan yasa tayi shuru tanata tunani,daga bisani aka kira sallah ta mik'e taje tayi alwala tayi sallah tare da addu'oi sosai kamar yadda ta saba musamman akan *peach* d'inta,sannan tayi akan maganganun marwan cewa Allah yasa taji alkhairi.
Yau asabar mum d'in manosh tazi duba aunty tare dasu abdallah da alfiya. Sunyi murna sosai da ganin juna dan sund'an juma basu had'uba,sakamakon mum d'in manos datace subar aunty ta huta sedai akan kawosu suyi kwana biyu. Sunyi kyau sosai se k'ara girma sukeyi. Abdallah yace mum wai yaushe daddy zaidawone gaskya ya dad'e sosai ni ina son ganinshi ya d'aukeni muje yawo inga sauran abokansa sojoji da wannan ogan nashi yana da kirki sosai domin yana sona,rananma yazo gidan su mum din dad yayi mana sayayya sosai kaya masu kyau yace dad namu yakusa dawowa amma gashi har yanzu shuru. Aunty ta rungume d'anta ko ince sanyi idaniyanta domin jinshi take kamar abdallah marigayi,tace kad'an k'ara hakuri kad'an kaji aiyukane suka mishi yawa amma ya kusa dawowa kaji? Alfiya kuwa fushi takeyi waisam se an kira mata dad nata sun gaisa tunda ya tafi basuyi wayaba kulum rikicinta kenan,hakan yasa aunty ta kira muhsin sakamakon yakan kwaikwayi muryan manosh wani lokaci,bayan ya d'auka da hello aunty,kawai setaji hawaye yana bin idanunta amma seta daure tace hello daddyn abdallah da alfiya,jikinshi yayi sanyi kuma yasan cewa su abdallahne suka sata kiran babansu domin sun tab'ayin hakan agaban jama'a bayan sunbar gurinne dad din manosh yace se'a dinga had'asu da muhsin ta waya tunda muryansu kusan d'ayane.
Muhsin bai iya cewa komai se tausayinta daya kamashi,tace dama ashe bakayin waya dasu abdallah ko,gaskya yanzu dai ga alfiya se fushi takeyi barina bata. Da murna ta karb'a tace daddy,kwallane ya zubo daga idanun muhsin amma seya daure yace sweetynah yakike,tace lfy lau daddy inaka shiga haka kaki dawowa nidai gasky muna so kadawo domin mu koma gidanmu da mummy kuma kaga gidansu mummyn daddy basu da swiming pool kuma inaso inyi wanka,dariya sosai muhsin yayi yace karki damu nanda wata d'aya zan dawo kinji,kidai inaso idan kikayi sallah kice Allah ya dawomin da daddyna lfy kinji,tace idan nayi zaka dawo? Yace da wurima kuwa,ai kuwa setayi murmushi tace da kana kusa dani dase mun tafa daddy,yace yanzuma zamu tafa mutafaaa,ahanka
li ta ajiye hannunta akan screen shima haka kamar suna kallon juna setayi dariya tace *i luv u daddy* yace *i luv u too my swthrt* sannan yace ina abdallah,tace gashi can yayi fushi wai bazaiyi magana dakaiba sedai ka dawo kuje yawo a mota,yace kie mishi yayi hakuri ya karb'i wayan,tace daddy yaqi ga mummy,yace to kicewa abdallah ina gaisheshi kuma shima yayimin addu'a zan sayo mishi mota karami wanda zaku shiga ku biyu kuma ina sonshi kinji? Tace to daddy mungode byee. Bayan alfiya ta mik'awa mummyntane setace to daddy kafa dawo dawuri dan kaga abdallah yana fushi dakai ka dinga kira ta wayan mum seku gaisa,yace insha Allah aunty,tace nagode se anjuma.
Muhsin ya sauke ajiyar zuciya tare da tausayamusu dukkansu,se kuma ya shiga tunanin lokacin da suke hira dukkansu suna cewa captain kam ai dole ya k'ara aure,seyace musu wlh apple na ita kadai ta isheshi,kuma ko wani irin rayuwa ko hali zata tsinci kanta nan gaba koda kuwa zata zama batada matancin kwata-kwata to wallahi ita kawai nakeso ba wani abuba,guys ina k'aunar apple yadda bakwa tsammani fatana mukasance tare da ita har a lahira, basan wani irin k'auna nake mataba bansan taya zan fahimtar daku akan k'aunar da nake mataba, ama dai nasan cewa bazan iya rayuwa babu *aunty ba wlh* shiyasa fatana idan mutuwa zata d'auki d'aya daga cikinmu tota d'aukemu atare da apple d'ina.
Bayan muhsin ya gama wannan tunaninne se hawaye yazo masa ido,yace Allah sarki abokina Allah yabayyana mana kai ameen.
Su alfiya yini sukayi dan sunzo yiwa aunry bye ne akan tfyarta india,sun kuma mata addu'a kamar dai yadda mum d'in manosh tagaya musu. Dakyar abdallah ya yarda yabi mum,saboda yace shisam zaibi mum nashi india yanata kuka dakyar suka tafi. Bayan tfyansu ne aunty taketa faman nata kukan inada mamanta taketa rarrashinta tare a mata nasiha kamr yadda ta saba,aunty tace mama ina iyakan k'ok'arin ganin cewa na dena,amma sam bana iyawa mama taya za'axe aljani ya d'auke d'an adam ne tayaaaa seta fashe da kuka,inda maman nata take cewa haba maryam,karki fad'i haka mana,maryam d'ina nasanta da ilimi da d'aukan kaddara maikyau ko mara kyau,dan haka kicigaba da addu'a Allah yana tare damu maryam koai zai daidaita insha Allah kiyi k'ok'ari kici wannan jarabawan maryam kinji? Tace to mama nagode da kika tunatardani amma nina kewar captain mama wlh inaso inganshi mama koda so d'ayane,itama mama seta tsinci kanta cikin hawaye sakamakon tausayin 'yarta. Amma ahakan tayita gayamata kalamai masu sanyaya zuciya harta dena kukan.
Yaune lahadi su maryam sun gaa shiri tsaf hakama su yah ibrahim da lubna.
Dama baba ya sanar dasu yah ibrahim da kuma umma mamansa cewa suzo akwai magana kamar yadda hajiya iya ta sanar dashi.
Hakama d'an nata wato mahaifin marwan harma da dad d'in manosh dayake aminaine duk aka taru agidansu *auntyn' yara* inda lubna take zaune kusada aunty tana kallon hajiya khadija da kuma hajiya iya dan taga ta ina zasu fara.
Mum d'in marwan dai kanta a sunkuye ta kasa sakewa sam dan batasan mezai biyo bayaba,duk dai ana zaune a palon baban maryam kowa kuma ya damu yasan dalilin wannan taron. Sallaman muhsin da majid da kuma muhammad ne ya katse su,bayan sun samu guri sun zauna ne aka fara gaishe gaishe,koda muhsin yace aunty ina wuni,seta amsa cikin muryan kuka saboda ta tuno da mijinta,kowa kuma yasan dalilin hakan,lubna ce tayita rarrashinta sannan hajiya iya ta d'ago kanta idonta jajur,kowa ya d'auka akan b'atan manosh ne zatayi magana,inbanda lubna datasan dalilin taron. Hajiya ta fara magana kamar hakaaaaaa...
.
"Bakomai yasa na had'a wannan taroba sedan wata magana mai girma ko kuma ince na taramu ananne saboda in tonawa kaina asiri akan abinda na aika".
Hawayene yasa hajiya iya tsayawa tana mai goge kwalla,inda d'an nata wato mahaifin narwan ya shiga damuwa. Hajiya iya tacigaba da magana cikin muryan kuka ta kwashe lbr tun daga farko har k'arshe kamar yadda mahaifiyar arwan ta bashi lbr dalla-dalla. Tun bata k'arasaba kowa ya kama fad'in innalillahi wa'inna ilaihirraji'un",hajiya iya tace dan Allah kuyi hakuri karkuce komai harsenaga.
Taci gaba da cewa nasan zakuji wani iri kilama bazaku yaddaba sakamakon yadda na muku bayanin amma wannan shine gaskyan lamari. Dan Allah kugafarceni kuyafemin wannan laifi mai girma dana aikatashi cikin jahilci da kuma sonkai irin nawa.....
Tunda hajiya iya ta fara magana idon aunry yake zubar da kwalla kamar pampo har kuma yanzu,nanne take tunanin kodai mafarki takeyine,amma sam ba mafarkibane wannan gaskyane,amma kuma anya abinda hajiya iya ta fad'a gaskyane? Lubna ce ta katse maryam da maganan zuci da takeyi,tace aunty kida shakku akan abinda ta fad'a domin babu k'arya ko kad'an aciki fase gaskya zallah. Shine dalilin dayasa naje gidanta nake gaya mata maganganu ranan,sakamakon bazan iya gayawa kowa abinda mahaifiyata da kuma kakata suka aikataba shiyasa na rik'e abun a raina dan banaso sunansu ya b'aci dukda dai nagane gaskyan amma hajiya khadija ta rik'e tamkar 'yar cikinta hakan yasa nayi shuru ban gayawa kowaba,sannan wannan shine dalilin dayasa bro marwan ya k'irk'iro da tfyarsa wanda ko aminansa basu san dalilin wannan tfyanba saboda kunyan abinda familynsa suka aikata baisan ta yadda zai fiskanci mutaneba.......
Aunty ce tasa hannunta akan bakin lubna tana kwallah sosai idanunta sunyi jah,ta kalli hajiya khadija da hajiya iya sannan tace hajiya shin dagaskene...? Atare suka d'aga kai ma'ana ehh gaskyace" hajiya khadija ta k'ara da cewa maryam nasan bamu cancanci yafiyaba amma dan Allah kuyi hakuri wannan shine dalilin dayasa muke k'aunarki sosai aranmu nida hajiya iya,shine dalilin dayasa bamaso ace yau munganki cikin kinci dan musan bamu kyauta mikiba dan Allah alhaji kuyi hakuri mun yadda da duk wani hukunci da zaku yanke mana amma fatanmu shine kusan gaskya akan cewa lubna 'yar cikunkuce k'anwa ga maryam.....
Su baba dai kasa cewa komai sukayi hakama su dad d'in manosh. Shi kuwa dad d'in marwan jiyake kamar ya tsaga k'asa ya shiga dan kunyan abinda mahaifiyarsa da kuma matarsa suka aikata,ga kuma 'ya'yan cikinsa su majid,"oooh" wannan abin kunya dame yayi kama?

 ANTIN YARA Page 66-70
.
"Maryam tanakuka ta kalli iyayenta inda kansu yake sunkuye dan basusan me zasuceba,musamman baba,yana ganin girman hajiya iya sosai,bazai iya yin komai akaiba illa yafiya. Maryam tagane komai akan halin da iyayenta suka shiga,hakan yasa ta matso kusa da iyayenta inda kowa yake binta da kallo,tace baba mama,nidai har abada馃槹hawaye sosai takeyi,inda hajiya iya taji zuciyarta na bugawa sosai,maryam tace nayafe musu har abada baba,kuma ina sake baku hakuri akan kuyafe musu,lallai marwan yayimin wani magana kafin ya tafi ya kuma nemi yafiyanmu tun kafin inji wannan lbrn,seyanzune nagane meyakenufin da wannan kalaman nashi,sannan yanzu haka bamu san wani hali suke cikiba baba,dan lokacin da marwan yabar k'ofar gidannan gabad'aya baya cikin hayyacinsa,dan Allah baba kayafesu kaida mama domin ceto rayuwar marwan da rashida danko numbernsu baya shiga,seyanzu na gano dalilin ciwon marwan baba dan Allah baba ka yafe musu..... tana kaiwa nan ta mik'e zuwa d'akinsu tana kuka ita kuwa lubna kallonsu takeyi cikin tausayawa,tace baba kayi hakuri a yafe musu kodon rik'eni dasuka babu kyama babu wulakantawa se d'inbin soyayya da suka nuna min fiye da d'ansu bro marwan,ta sake juyawa ta kalli dad d'in marwan tace daddy har gobe bazan dena kiranka da sunan daddyba,haka kuma kema mummy ina k'aunarku har gobe,nagodewa Allah daya had'ani da 'yar'uwata dukda kun rabamu,kuma cikin k'ankain lokaci nayi koyi da halayenta nagari,daddy samun 'yar'uwa kamar aunty abin alfaharine agareni. Yau zan gayawa kowa abinda baku saniba,daddy nayiwa aunty mugunta har halakata naso nayi sakamakon son zuciya irin na hajiya iya,lokacin da aka nei aunty aka rasa nice nasa akayi kidnaping nata har zuwa jejin yankari,amma cikin ikon Allah aunty ta dawo gida lfy,kuma ita tasan cewa nice nasa a saceta saboda kar ayi aurensu da bro manosh dan k'aunarshi danakeyi acikin raina. Amma hakan baiyuba kuma tak'ita gayawa kowa abinda ya faru harda iyayenta ta b'oye musu saboda bata so ta b'ata tsakanin iyayenu da kuma aminantakar dake tsakanin bro manosh da bro marwan,haka kuma wanda nasa aikin ya yaudareni ya b'ata min rayuwata ta hanyar yimin fyd'e wanda duk alhakin auntyne ya kamani,shiyasa ban gayawa kowaba se ita auntyn,saboda ina tsoron fad'a muku agida daddy,sannan aunty itace kawai wanda ta fad'o min araina wannan lokacin,bayan na kirata nagaya mata komaine,sam batasa komai a rantaba tazo har inda na mata kwatance itata staftaceni ta rufamin asiri ta hanyar had'i aure da yah ibrahim dan tasan zai rufamin asiri zai kuma zauna dani zuciya d'aya.....
Lubna ta tsaya anan tana shehshek'an kuka inda hajiya khadima taketana kai har kusan duk wanda yake palon seda yayi kwalla dajin lbrn da lubna take bayarwa.
" lubna tace wannan sirri dana gaya muku yau babu wanda yasan dashi dagani se aunty,koshi yah ibrahim d'in baisan komai akan sace auntyba,amma dai yasan abinda saddam yamin ya kuma amince ya aureni. Nabaku lbrn nanne badan komaiba sedan innuwa hajiya iya da mummy cewa Allah yasa mana k'aunar junanmu tunba yauba nida aunty,sedai shaid'an yayi tasiri akaina har nake neman halakata dan soyayya,amma duk kukuka janyo hakan,dabaku rabamuba da tare zamu tashi inji jina kusa dani...kin cuceni hajiya kun tarwatsa min rayutawa nidai bazan tab'a yafewaba wlh.. mama ce ta kamota tana rufe mata baki tareda goge kwallan idanunta tace lubna ya isa haka tashi kije gun 'yar'uwanki kinji? Bamusu ta mik'e ta fita nata kuka,su yah ibrahim ma fita waje sukayi dukkansu 4 sukayi zugum a waje babu wanda ya iya cewa komai acikinsu....
"Jirginsu marwan ya sauka a abuja, inda suka sauka a hilton. Tun da marwan ya fita bai dawoba rashida ta shiga damuwa gashi wayarsu duk ya karb'e ya cire sim.
Saukowa tayi dama da kud'i a hannunta sosai,taje ta sayo k'aramin waya da sabon sim mma tama rasa waye zata kira,hakan yasa tafara kuka ko abinci bataciba.
Marwan kuwa tunda ya fita da motan wani abokinsa da yake aiki acan din yaketa tfy,baima san ina yake zuwa. Gabad'aya hanklinsa atashe yake,halinda ake ciki yanzu agida yola,sannan ko wani hukunci dad nashi zai yanke akan mum oho,yanzu abokansa sunsan komai,gashi babu lbrn aminsa dazai iya gayawa damuwarsa wato manosh. Kuka yakeyi sosai kamar k'aramin yaro,baya ko kallon gabanshi hakan yasa wata mota k'ok'arin kaucewa marwan amma sam yagagara saboda yadda marwan yake sake dososhi,se alokacin hankalin marwan ya dawo jikinsa ya fara fad'in innalillahi wa'inna ilaihirraji'un ya kauce da sauri tare da tsyawa a gefe shima wancan din ya tsaya yana zagin marwan,shi kuwa se hakuri yakebashi amma sam se faman masifa yakeyiwa marwan,dak'ar dai ya hakura ya tafi. Shi kuwa marwan zama yayi acikin mota yana zubda kwalla.....
"dad d'in marwan yakasa cewa komai sabida bayida abin fad'a akan mahaifiyarsa". Mahaifin manosh ne yacewa mahaifin maryam dan Allah alhaji kuyi hakuri da abunda muka aikata muku,dukda dai mahaifiyarmuce dukkanmu tunda ta haifemu" amma tabbas sunyi kuskure mafi girma arayuwa,babu da wani abu da zamu iyace cewa sedai muyita baku hakuri daku yafemana sannan 'yarku dama tadawo hannunku tunda tana auren d'anka ibrahim. Za'a iya sanar da dangi amma ataimaka ab'oyewa mutanen waje. Mahaifin maryam yace bakomai alhaji wannan yawuce,sedai fatan Allah yasa mukiyaye gaba,Allah yasa wannan ya,zama darasi akan wasu,saboda munbarwa Allah komai wlh nafe duniya da lahira,amma fa idan da wanine aka mishi haka tofa bazai yafeba,sannan dole se hukima ta shiga shicin zance wanda hakan zai iya janyo wata babban rigima tsakanin familys harma yakai gidan yari.
Amma alhamdulillah yazo gidan sauki tunda duk gashi Allah ya had'a zuri'a a tsakaninmu" bazamu iya cewa komaiba se Allah ya kare nagaba,sannan nagode da kulamin da yarinyata da kukayi,nagane manufar hajiya iya da kuma dalilinta.
Sedai ba haka ya kama a bullowa lamarinba,ita a tunaninta lokacin ina fama da talauci ta yadda bazan iya rik'e koda yarinya d'ayaba,se kuma gashi Allah yabani kyauta biyu a lokaci guda,tofa musani Allah baya d'aurawa bawa abinda bazai iyaba,tunda shiyabani su toshizai bani hanyar da zan renosu,alokacin bani dashi,yanzu kuma ina iya rike mutanen daba jininabama,kamar yadda kuka rikemin lubna. Bakomai hajiya Allah ya yafemu gabad'aya. Har k'asa hajiya iya ta sauko tana kuka tare dayin godiya,hakama mahaifiyar maryam tace tayafe bakomai. Nanne dad d'in manosh yayi magana kansan a sunkuye dan kunya,yace mungode sosai alhaji Allah yabar zumunci,wani lokacin mata basu da tunani,duk abinda zuciyarsu ta rayamusu shi kawai sukebi tabare dasunyi shawara da kwakwalwarsuba,aduk lokacin da zuciya ya raya maka abu maikyau ko mara kyau tofa ana so mutum yayi shawara da kwakwalwarsa domin zuciya zata kaika ta baroka,yanzu kai dakayi hakuri wlh inda wanine bazai hakura,kuma kaduba abinda lubna tayiwa maryam,da maryam ta fad'a awannan lokacin toda abu ya lalace tun daga wannan lokacin se daga baya kuma za'aji kunya,kuma dukkune sanadin faruwar hakan. Hajiya da girmanki amma ki aikata irin wannan abu haka babu dad'inji,sannan kuka b'oyemin akan tsintota akayi wannan wani irin tunanine haka? da wani akayiwa hakan da sunanmu ya gama b'aci,yanzu haka kunyan had'a ido dasu nakeyi wlh mungode sosai Alhaji zamu tafi,yana kaiwa nan ya fito suka biyoshi a baya,bai k'arasa gun motaba ya yanke jiki zai fad'i da sauri su majid suka tallafoshi aka sashi cikin mota ida muhammad yaketa faman dubashi yace ai jininsane yahau sosai. Subhanallah ake ambato agun,da sauri suka shige se jimeta inda akayi hospital dashi.
Dad d'in marwan baida hawan jini sam,amma yau gashi dr yace hawan jinine ya kamashi sosai.
'Ya'yan nashi sunyi iyakan k'ok'arinsu agun dan kula da mahaifin abokinsu.
"Shi kuwa mahaifin manosh,yana cikin damuwa wanda har yake jin ciwon kai mai zafi,amma haka ya daure yana nan akan abokinsa.
"Su maryam kuwa fitowa sukayi daga d'aki sukazo gun hajiya iya kamar yadda babansu ya umarcesu.
Dan tun lokacin dataji abinda ya sami d'an nata shikenan aka rasa gane kanta. Hakuri aketa bata,itama hajiya khadijan sam ta kasa sakewa,hakan yasa tace zata komar da hajiya iya gidansu can na jimeta tunda akwai masu girki,ita zata tafi asibiti gun mijinta.
Haka aka rakosu har waje suka tafi. Maryam sebin motar nasu da kallo takeyi har sukayi nisa sannan lubna ta kamo hannunta tace aunty kidenasa damuwa aranki pls komai ya wuce kamata yayi ace kina murnan samun k'anwa.
Jiki sanyaye ta juyo suna kallon junansu tace lubna,bakya jin komai gameda abunda ya sami daddynkine? Lubna tace daddyn bro marwan dai. Maryam ta dafa kafad'arta tace lubna har gobe har jibi shima daddynkine sannan inaso ki nuna damuwarki sosai akanshi kamar yadda kike nunawa akaina inhar kinasona da gaske. Jikin lubna yayi sanyi ta wuce gida tasa himar nata har k'asa tace mama baba zanje duba daddy,babu wanda ya hanata,seda tazo dabda maryam tace zanjene saboda ke saboda kuma shi daddy bayi da laifi sansan zanjene dan bro marwan bayanan,nasan koba komai zan d'ebemasa kewa.
"Maryam tanata bin lubna da kallo harta dena kallonta zata shiga gida kenan setaji ana kiran sallan la'asar,koda ta juyo dan ganin mai kiran sallan seta wannan tsohonne dai wanda ta taimakawa a farkon littafin...
"Marwan ahankali yake tfy harya isa gun abokinshi yace kaini masaukina.
Bamusu ya kaishi batare dayace mishi komaiba,saboda yadda yaga marwan yasan bazai samu kowace amsa daga bakinshiba.
"Bayan ya saukeshine marwan ya fita yace nagode,abokinsa yace yaushe zanzo to?" Dan numberka kona kira bana samu. Marwan yace zan kiraka sannan ya shige.
Rashida tanata safa da marwa setaji nocking,da sauri taje ta bud'e kofa taga marwan atsaye kansa a sunkuye dukya galabaita yayi wani iri kamar maiyin azumi. Hakan ya tabbatar mata da cewa baici komaima,kallonta yakeyi cikin tausayi ga kwalla dasuke yawo a idanunsa. Tausayinshi ya kamata,ta rungumeshi sam ajikinta tana kuka tana cewa waime yake faruwane luv,dan Allah ka sanar dani bana son yadda nake ganinka ahakannan pls luv, baice da ita komaiba se kwallan da yake zubarwa,ahankali ta cire masa kayan jikinsa itama haa ta jashi zuwa toilet inda ya zama kamar jariri haka ta wankeshi tas sanan itama ta wanke jikinta ya d'auki towel itama haka suka fito a tare,yasa kaya tasake janshi wuza gun cin abinci amma sam yakici da k'yar tasashi yaci kadan sannan ya koma gado ya kwanta.
Bayan ta gama komaine tazo inda yake tana tsunbatan sassan jijinsa a hankali tana kallonshi har cikin ido. Shi kuwa sam hankalinsa baya jikinsa,lips nashi ta far kissing ahankali cikin nutsuwa,shi kuwa idanunsa arufe yana jin yadda take mishi,kamar a mafarki yaji muryan manosh yana cewa marwannnnn
Azabure,ya mik'e rash tace lfy luv,yace my luv manosh naji yakirani wlh ahine. Rash ta mik'e tace manosh fa kace,to a ina yake? Allah yasa dagaskene luv dabanda zaikai aunty farinciki maza muje muduba,bamusu yanufi k'ofa ita kuwa tasa himar ta fito,se juye juye sukeyi suna duba kofofin d'akinan ko zasuga fitowarsa koma suji muryanshi.
Can yasakejin marwannn,ai kuwa yana juyawa seyaga manosh yana k'ok'arin fitowa daga wani d'aki amma sam j'afarshi baya motsi kaman an manda da superglue. Da gudu suka k'arasa gun,amma ina take kofan ta kulle kanta. Bugawa marwan yakeyi kamar zai b'alla kofan amma ina,sunan manosh yaketa kira yanacewa prince gani ka bud'e kofan pls kaida waye? Shuru babu amsa,seyaga k'ofa ta bud'u da kanta,dasuka shiga shiga amma babu alaman mutane acikin d'akin.
Marwan yace ina bazai yuba wannan duk sharrin shukrah ce,duk yadda akayi suna nan,lallai bazan bar nanba senagano captain,nan suka zauna sunata addu'oi,ita kuwa rash tsone ya kamata sosai dan tabbas itama taga manosh da idanunta...
" aunty kuwa koda tsohonnan ya idar da kiran sallah,gunshi ta k'arasa tace baba,murmushi yayi mata yace inatayaki murnan samun 'yar'uwarki. Murmushi tayi mai had'e da tsoro tace nagode,nakuma tuna da abinda ka gayamin a yanzunnan. Yace masha Allah maryam zan tafi,tace baba dan Allah mijinafa,kokasan inda shukrah takai min shi? Dan Allah baba kataima. Baba yace wacece shukrah? Jikin maryam yayi sanyi tace baba aljanace ita,ta rabani da mijina tsawon kusan wata hud'u kenan ba'asan inda yakeba.
Baba yace ta ita maryam bansan komaiba akan wannan kimana tausayamiki sosai,Allah ya bayyana miki shi,kuci gaba da addu'a maryam babu wani abu dazai gagara,sannan kisa a ranki cewa Allah zai dawo miki da mijinki,karki dogara da wani kinji? Jikinta sanyaye tace to baba nagode tare da kwalla a idanunta. Ahankali tabar gun masallacin tayi hanyar komawa gida saboda mutane sun fara zuwa sallah,kan ta karasa kofar gida ta juya amsam bataga baba ba,kuma babu alamarsa tagurin. Mamaki,sosai tayi tayi da gudu ta shiga gida tana kuka ,hankalin iyayenta a tashe suke tambayanta ko lfy,tace gamo tayi da aljani. Iyayen suka tsaya kallon junansu,mahaifinta yace maryam wani irin gamo? Nan maryam ta basu lbr tun daga farkon had'uwansu da baba stohonnan har kuma taimakon daya mata a jejin yankari lokacin da saddam ya harbeta da bindiga a hannu da kuma abinda tsohon ya gaya mata akan lubna.
Mamaki sosai iyayen sukayi,babanta yace maryam anya kuwa lfyanki lau? Tace wlh baba lfyta lau yanzuma shinagani shine wanda kukaji muryanshi ya kira sallah. Baba yace ajani ya kira sallah kuma maryam? Tace eh wlh baba nasan bazaku yaddaba amma wlh shida kanshi yagayamin shiba mutum bane aljanine. Baba yace to Allah ya karemu dadukkan 'yan'uwa musulmai,suka amsa da ameen sannan ya fita zuwa masallaci yanata kalle kalle tare da tambayan jama'a ina wanda ya kira sallah yanzu? Wanine yace tun d'azu yabi tacan,baba yace shibazai tsaya yayi sallan bane? Yaro yace oho mishi tsohone kodai zaije ya dawone oho mishi. Haka dai su baba suka idar da sallah amma wannan wannan tsohon bai dawoba,baba kuwa ya jinkirta yanata karatun qur'an a masallaci harya isar amma baiga kowaba haka ya wuce gida. Lokacin suna cin abincine se maryam tace baba har yanzu lubna shuru kodai sun wuce gidane itada yah ibrahim,mama tace kirasu kiji,bamusu ta d'auki wayarta ta kira lubna,cikin nuryan kuka lubna ta d'auka tace aunty zan dawo anjuma kad'an,maryam tace ya jikinnashi? Lubna tace da sauki yana bacci,maryam tace yanaji muryanki kina kuka lubna? Lubna ta share kwalla tace aunty daddy ya saki mummy. Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un.......
.
Sakifa kikace lubna,tace eh sannan ta katse wayar.
"Maryam ta kalli iyayenta tace baba wai daddyn marwan ya saki hajiya khadija" duk basuji dad'in lamarinba,amma babu abinda zasu iyayi akai haka suka gama cin abinci suka wuce dan k'arasa shirye shiryensu.
Kusan 10:00pm yah ibrahim ya kawo lubna gida,idan suka dad'e suna magana da baba kafin ya tafi.
Ranan dai basuyi wani baccin kirkiba dan gobe zasuyi tfy.
Maryam kuwa tama rasa meke mata d'ad'i.
"Washe gari da safe mahaifin maryam ya sanar da tfyan da zasuyi a masallaci don yiwa maryam aiki,sannan kuma yasake rokon jama'a ayita addu'a wa surukinsa wato manosh Allah ya bayyanashi. Addu'a sosai aka musu awannan lokacinma.
Da misalin 9:10am yah ibrahim yazo ya kwashesu a mota inda suka wuce hospital suka gaida mahaifin marwan sannan suka wuce airpot. 10:20am jirginsu ya tashi abuja,suna sauka dama komai ya zama ready yah ibrahim ya gama komai suka wuce suna zaune zaman jiran tfya india.
Marwan kuwa suyita addu'a har rashida ta fara bacci,shine ya d'agata yakaita d'aki ya kwantar da ita sannan ya koma yayita zama harya gaji sannan ya dawo shima hakadai suka wayi gari.
"Bayan sunyi breafast ne marwan ya sake komawa d'akin amma bakoai aciki" mamaki sosai yakeyi abu kamar a drama?" Rash ce ta biyoshi hakadai suka sake dawowa d'akinsu inda take ce mishi itata sayi waya kuma tayita kiran numbern 'yan gida baya shiga dan haka ya bata numbern su majid,sam marwan yak'i yama karb'e wayan. Nan rash tayi fushi tace waime kake nufine kakawoni nan ka ajiyeni babu wani bayani jiya haka ka fita ka barni bakaika dawoba seda lokaci ya kure waima ina kajene marwan?
Cikin mamaki yake kallonta yau sunanshi ta kira kai tsaye. Yace luv yau nine kuma marwan? Sannan zargina kike kome dakike min wannan tambayoyin? Tace eh zarginka nakeyi saboda abirkice ka dawo jiya kamar wani bugagge idan ka gaji da zama danine nikam kamaidani gidanmu gabad'aya kacanja kadena bani hakkina idan ka sau matan banza awaje toka sallameni intafi gidanmu nan ta fashe da kuka. Shi kuwa marwan maganganun nata sun mishi zafi sosai gashi dama yana da damuwa,baice da ita komai yafita yabar mata d'akin tanata kuka.
Shukrah waike wani irin muguwace haka? Hahahha lallai kam manosh ka samu baki,wlh indai bazan samekaba tofa sedai in hallakaka itama maryam d'in ta rasaka tunda kai taurinkai kakeji dashi,danka samu na sake maka bakinka ko,tokamin bankwana manosh semun had'u a kiyama.........
.....
Ihu mai k'arfi manosh yasa,awannan lokacin kuwa su yah ibrahim zasu tafi dama wayoyinsu akashe yake. Juyowa yayi yana kallon aunty se faman kuka takeyi tana tsaye,gunta yazo shida lubna sukace lfy aunty muje mana? Kuka ta fashe dashi tace sam bazatajeba ta fasa,mutanen gun suka tsaya suna kallonsu,da k'yar mahaifinta yashawo kanta ta yarda se waige waige takeyi har suka wuce tana kwalla.
Yah ibrahim ma kwallan yakeyi dan yana mugun tausayawa aunty sosai. Haka suka wuce cikin jirgi tana tsakiyan mamanta da kuma lubna jirgi ya tashi..
Rash kuwa tayi kuka harta gode Allah can sekashi ya dawo tanata had'a kayanta ciki kit. Kallonta yakeyi tare da tambayar ina zakije? Ko kulashi batayiba ta gama komai tazo wucewa seya kamo hannunta ya matseta a jikinshi yana cewa haba luv meyake damunkine,meyasa bazakin uzuribane yanzu har zaki iya tfya kibarni? Tace shiyafi komai sauk'i wlh. Yace luv bakigane bane ina cikin damuwa dan Allah kimin uzuri pls my luv,rungumeta yayi tsam yace inada bukatarki atare dani kece zaki kwantar min da hankali amma kuma shine kike gayamin maganganu kike k'ok'arin tfya kibarni? Pls luv kiyi hakuri i luv you so much. Hawayene kebin idanunta inda tace i luv you too bazan tab'a barinkaba kaine kab'ata min rai ai. Yace kiyi hakuri pls kinji,tace yawuce tana murmushi inda suke kallon junansu daga nan ta fara kissing nashi shima haka har suka sulale akan gado hmmmm.
Manosh ne kwance a k'asa baya cikin hayyacinsa se muryan wani mutum da yakeji yana cewa manosh bud'e idanunka ka kalli jirginsu matarka ya tashi,amma ina manosh bazai iyayin komaiba a wannan lokacin. Mutumin yace manosh gacan aunty cikin jirgi daure ka mata fatan Allah ya kiyaye hanya. Shuru kakeji kamar gawa, ni kuwa *sad-naa* kallonsu nake kamar a tv babu halinna in gane inda suke,haka dai nayita cija baki ina zubda kwalla tare da kallon jirginsu aunty harna dena hangoshi. Ganin hakan yasa mutumin ya d'auki manosh kamar an d'auke wuta haka na dena kallonsu,sena koma hilton gunsu marwan inda suke manne da junansu a cikin bargo,gadukkan alamu dai marwan yana biyan bashin kwanakin da suka wuce ne hahahaha!
"Mutuminnan bai tsaya ko inaba se gidan manosh,dahar zai shige sekuma ya tuna da cewa ai babu kowa a cikin gidan inbada mai gadi. Hakan yasa ya baina a daidai bakin gate rik'e da manosh a hannusa kamar dai yadda ake rik'e jarirai. Mai gadi yaji ana buga gate,kuma sam mutumin baikaima hannunsa kusa da gate ba. Da sauri yazo yana cewa wayene gidan babu kowa seni kadai mekuma kuke sone...? Mai gidansa yagani wato captain manosh a hannu wani tsohon mutum,Alhamdulillah maigadi ya furta yana kwallan farinciki tare da cewa Allah majirok'o bayinsa alhamdulillah....
.
maigadi yakasa rufe baki,ya kuma rasa mezaiyi a wannan lokacin.
"Tsohon yace bamu taburma mana, bamusu maigadi yaje ya d'auko carpet nashi mai kyau wanda aka kawo mishi tsaranban makka ya shinfid'a cikin rawan jiki yace bisimillah.
Tsoho ya zauna tare da kwantar da manosh yace ahanya na sameshi kwance babu yadda yake,bayan na d'aukosane nake tambayarsa inda yake waye mahaifinsa shine dai ban samu amsaba,kawai senaga hotonsa a gurare da dama an manna,shine na tambayi jama'a suka kwatantamin gidansa tare da nuna farin cikinsu.
"Mai gadi Allahu Akbar"
"Tsohon yace nidai zan tafi dan akan hanya nake nabar iyalita tana jirana can"
Maigadi yace dan Allah kad'an jira barina sanar da iyayensa,amma sam tsohon yaqi yace shidan Allah yayi badan asan yayiba dan haka ya tafi amma inaso ka gayawa matarsa ina tayata murna,kace mata inji baba.
Koda tsoho ya fito lokacin maigadi yana kiran numbern aunty amma sam baya shiga.
Hakan yasa ya kira numbern dad d'in manosh bugu d'aya kuwa ya d'auka tare da cewa kana lfy,maigadi yace lfy lau alhaji se alkahiri yauga oga yanzunnan wani mutum ya kawoshi a stintarshi yayi kwance a k'asa,gashinan...dad d'in manosh ya katseshi da cewa kana nufin d'an manosh? Maigadi yace shidai alhaji gashinan amma baya halin lfy. Subhanallah ganinan.....
Dad yana ajiye waya yayita Hamdala yana godiya wa ALLAH tare da d'aga hannayensa sama da sauri ya kira malam da kuma aminansa da duk dai nakusa dashi. Kowa yaji lbr se godiyawa Allah.
"Mahaifin majid ne ya kira majid suna hospital akan dad d'in marwan" koda suka sami lbrn murna da farin ciki baya misaltuwa. Shikansa dad d'in marwan dukda dai jikin nashi yayi tsanani amma sedayayi murmushi tare dayi godiya wa Allah ya kalli abokan d'an nasa dukyaga suna burin ganin aminunsa daga idanunsu ya gane hakan.
Anitse ya tashi ya zauna yace karku damu muhsin kuje kuga abokinku aina samu lfy ku isarmin da gaisuwata agareshi kafin nazo. Bamusu suka fati cikin d'oki inda yake ta binsu da kallo
Manosh kwance maigadi yayita yayyafa mishi ruwa amma sam ko motsawa baiyiba daidai nan motoci suketa hon abakin gates yayi saurin bud'ewa suka shihshigo.
"Daga dad d'in manosh har abokansa bansan suwaye suke mararin ganinsaba harda gudunsu suka k'arasa gun. Majid ne ya karb'i key yabud'e gidan muhsin da muhammad kuwa suka d'auki manosh se cikin palo inda duk gurin yayi k'ura.
Akan kujera suka kwantar dashi kamar gawa baya ko motsi.
Kowa ya tsaya kallo manosh inda kowa yake zance zuci akan yadda suka ganshi.
Muhammad ya gwadashi ya tabbatar da cewa yana da rai,hakan yasa akayita masa addu'oi ana tofawa a ruwa ana yayyafa mishi,shi kuwa malamin man habbatus sauda dadai sauran had'in su man juda yaketa shafa mishi ajiki.
"Aikuwa segashi ya fara motsawa ahankali amma idanunsa a rufe yake motsawa da dukkan jikinsa"
Murmushi abokansa suka farayi tare dacigaba da addu'an"
Mahaifinsama addu'a yaketa mishi, shi kuwa malami mai ruk'yya se karatu yakeyi.
"Ahankali manosh ya fara bud'e idanunsa yana rufesu hardai ya bud'e garau inda yakebin kowa dake palon da kallo d'aya bayan d'ayan harya gama sannan yace ruwa zansa. Malam ya bashi ruwan addu'an muhammad ya tallafosa aka bashi ruwan ya shanye tas yace ak'ara mishi,hakan yasa aka gane lallai ya dawo hayyacinsa saboda manosh yana son shan ruwa sosai kobayajin k'ishi. Bayan an k'ara mishine yace zaisha fruit,hakan yasa akan yana jin yunwa.
Cikin mintuna goma mahjid yafita nemo fruit ya dawo ya wuce kichine ya d'auki plate da wuk'a yadai yanka yadda zai iya sannan ya dawo ajiye agaban manosh inda yaketa binsu da kallo kamar bai sansuba.
"Majid yace ga fruit d'in"
"Ido manosh yasa akan fruit d'in" bayan wasu dak'ik'ai seya girgiza kai alamun bazai shaba.
Muhsin yace kasha mana abokina nasanka da son fruit fa.
Manosh ya girgiza kai yace ba irin wannan nake shaba. Majid yace kamar yah? Wanne kake sha to?
Kafin manosh yayi magana muh'd ya tuna da irin fruit da aunty take mishi seyace kana nufin irin wanda aunty take maka?
Da sauri ya d'aga kai yana kallon muh'd cikin alamun tambaya? Muh'd yace eh na aunty kake so koh mai irin fiskarka??
Ihu mai karfi manosh yasa wanda dukkansu seda suka tsorata harda malamin. Manosh yacigaba da ihu yana cewa nooooh! Dad shukrah ce wlh tacuceni tagama dani dad ya rik'o dad nashi da k'arfi yana kuka.
Dad yace son saurara mune anan babu shukrah ka saurareni kaji? Ahankali ya nutsu yace "dudes?"
Nanne abokansa suja san cewa yana cikin hayyacinsa sunda ya kirasu da wannan sunan *dude*" murmushi sukayi tare da rungumeshi sukace Alhamdulillah Allah mun gode maka _we are so happy to see "dude_"
"Murmushin k'arfin hali yayi yace _thankyou_, sannan ya kalli dad nashi yace dad mum fa? Yace suna hanya itada driver dasu abdallah,murmushi manosh yayi yace ina dad d'in marwan? Tare da juyowa da sauri ya sake kallon su majid yace ina marwan? Shuru sukayi dan suma tunda ya tafi suketa nemansa basusan inda yajeba tunda numbernshi baya shiga kuma bai kira kowaba har yanzu.
Manosh ya sake maimaita tambayarsa ina marwan? Muhsin yace kaima kasan da yana gari da tare zakaganmu yayi tfya ne.
Manosh yace ok dad nashi fa? Dad yace yana asibiti bayida lfy,subhanallah harda asibi dad,meyake damunsa to? Dad yace my son kana da buk'atan hutu dan haka muje gida idanka huta zakaji komai. To yace da dad d'in nashi yana kallon su muhsin da alamun tambayan *ina aunt?*馃槵 sukuwa dake sun gane abinda yake tambaya,bayaso dad nashi yajine saboda yana kunyan dad nashi. Se suka ce yawwa gasu mum sun iso,ai abdallah da alfiya suna ganin dad nasu suka ruga aguje suka haye jikinsa ya rungumesu yana sauke ajiyan zuciya kad'an-kad'an.
Mum kuwa da umma mahaifiyar yah ibrahim hawayen farin cikine ya lullub'esu sunkasa cewa komai se murmushin farinciki.
"Manosh yace mum umma ina yininku,sukace lfy manosh barka Alhamdulillah Allah ya dawo mana dakai,kunyansu yakeji sosai bai iya sake cewa komaiba sesu alfiya dasuketa damunsa da surutu. Mum tace kuzo nan bayida lfy kubarshi idan ya huta sekuyi hiran,abdalla yace yaudai da ddynmu zamu kwana,mum tace tabbas kuwa amma sekun barshi ya huta,da kyar majid ya lallab'esu suka koma gun mum inda malam yace to Alhamdulillah inaga shikenan ai nizan tafi.
"Dad da malam ne waje suna tattaunawa inda malam ya bashi magani yace manosh ya dinga shafawa a jikinsa,sannan ya samu hutu kuma a dinga mishi karatu koyayi da kansa. Godiya sosai dad yamishi yabashi abun sadaka amma sam malam yak'i karb'a yayi tafiyarsa.
Maigadine yazo da wuri yace alhaji ogan ya tashi? Dad yace eh Alhamdulillah yana halin lfy,maigaji yaji dad'i sosai yace to masha Allah zan iya shigowa? Dad yace eh bisimillah.
Tare suka shigo yagaida ogansa,cikin fara'a manosh ya amsa sannan yatafi yana farinciki sosai.
Iyayensu majid sukayi addu'oi sosai sannan suka tafi inda dad ya rakasu. Alfiya da abdallah kuwa gurin wasan lilonsu suka wuce se wasa sukeyi.
Bayan fitan su dad ne manosh yacewa majid ina miher ne? Majid yace taje suna k'awarta ta haihu,tun d'azu nake neman numbernta dan in sanar da ita amma baya shiga"
Manosh zaiyi magana kenan seka dad ya shigo yace toku tashi mutafi gida,ba musu suka tashi tare da tallafawa manosh ya tashi tare da k'arewa gidan kallo ko ina yayi kura sosai.
Haka suka tafi inda muhsin ya d'augo abdallah a sama yana cewa wlh nikam agidanmu zan kwana,muhsin yace bakaga gidan yayi k'ura bane aidole se anzo anyi share share.
Manosh suna tfya atare hargun mota inda ya shiga motarsu majid yana rik'e da alfiya a ciyarsa yana gyara mata gashi seyace rad'a mata cewa _ina mummynkine dasu babanta_? Alfiya kuwa tabashi amsa da k'arfi ta yadda kowa zaiji tace tayi tfy ai bata gayamaka bane?
"Kunya sosai yaji dansu dad sunjisu"
"Hakan yasa yayi shuru har seda motansu dad dasu mum yayi gaba sannan nasu manosh d'in inda shida abokansane kawai se kuma su abdalla dansuki binsu mum sunce gurin daddynsu zasuje"
Se yanzune manosh ya juya da sauri yacewa muhsin kai wai ina *aunt* ne babu wanda yacemin komai,kunyansu dad ne yahanani tambayarta wlh _where is my wife_ muhammad dake driving yace ba alfiya ta baka amsaba,tayi tfy wlh,majid yace tfya mai nisama kuwa,muhsin yace akallah zatakai 3month kan ta dawo ba. Kallonsu manosh ya tsayayi d'aya bayan d'ayan yace wai meyasa kukemin hakane bawasa nakeyibafa kunsani ina apple d'ina? Abdallah yace daddy apple ta tafi *india* batada lfyne shine suka tafi ita da mama da baba da kuma uncle ibrahim da aunty lubna duk suka tafi....

 ANTIN YARA Page 71-80 (The end)
.
Isarsu manosh hospital dad d'in marwan yana
bacci.
"Amma dole ya farka,dan abdallah sedaya
tasheshi yana cewa bappa tashi ga daddyna ya
dawo"
Da sauri ya farka,inda ya nuna farincikinsa
sosai tare da mik'owa manosh hannusa ya
janyoshi har zuwa inda yake yana rik'e da
hannunsa yace d'ana nayi matuk'ar farincikin
ganinka sosai wlh Allah mungode naka.
Manosh yace nagode daddy ya jikin,yace da
sauki sannan ya tsuguna ya gaida hajiya
khadija dake zaune akan carpet. Tunda
yafurta cewa yasake amma sam tak'i tfya
saboda rashin lfyan dayake cikin kusan babu
wanda zai kula dashi shiyasa ta zauna. Itama
ta nuna farincikinta sosai da dawowar
manosh,haka dai sukaita hira sosai sannan
sukai sallama inda manosh yace mishi zai
dawo zuwa bayan isha.
"Koda suka fita gidan *tv gotel* dake hanyan
hayin gada ta hanyar gire suka tafi"
Ma'ana gidan tv da radio na *alhaji atiku
abubakar* da kowa ya saninshi. Shiga sukayi
inda akaso jinta bakin manosh kasancewan
ko'ina anji lbrn b'atansa kuma ansan cewa
aljanace ta d'aukeshi.
"Nan dai manosh ya fara bada lbr kamar
haka...
Lokacin muna zaune da matata *aunty'n
yara*, dan ranan sam ban fita aikiba munata
hira. Kawai senaga wata mace tana kirana da
cewa lokacin tfyanmu yayi dan haka inzo mu
tafi,sam nayi banza da ita,seta naga tana
k'ok'arin cutar da aunty da wani abu wanda
bansan meneneshiba,ganin hakan yasa
nacewa aunty ta kwauce amma tak'i saboda
batasan dalilin fad'in hakanba.
Nikuma babu yadda zanyi dantafi
karfina,hakan yasa namik'a mata hannuna
shine bansake sani komaiba se bayan wasu
lokaci dana b'ude idona sena ganni a wani
gida na alfarma wanda babu alaman k'ofa
bare window.
Bayan na gama bin gun da kallone sena maida
kallona gun ita wanda nake gani.
Cemin tayi barka da farkawa mekake son ci?
Nace mata babu komai inane kuma nan? Tayi
murmushi tace dani masauk'ina kenan anan
zancigaba da zama har muyi aire da ita. Nace
mata aini ina da aure,tace wacece matar
nawa? Amma sam nakasa tunawa da komai
akaina bare har in kira sunan wani nawa.
Ganin hakanne yasa tayi dariya tare da zuwa
inda nake tashafi kaina tace my manosh
karka damu kakuma kwantar da hankalinka
dan kazama nawa nima na zama naka yanzu
kaji? Dan haka gayamin mezakaci?
Kaina girgiza mata nace bana son komai inaso
ta maidani inda ta d'aukoni,amma setace
ainazo kenan bazan sake komawaba saboda
na baro wannan duniyan mutanen nan
duniyansu na aljanu nake.
Ban iyawa cewa komaiba itama kuma haka
har lokacin sallah yayi wato magrib. Ita da
kanta tazo tacemin lokacin sallah yayi tayimin
nuni da wani gun acikin inda muke wanda
bazai wuce taku shiddaba tace dani toilet ne
idan inada buk'aka. Mamaki sosai naji dan
nidai ganin gurin nayi kamar irin kumbo
ind'in aka jera masu kama da gwala-gwalai se
shek'i sukeyi,ban iya hakuri nanufi gurin
ahankali,ajikin kumbon naga wani guri kamar
alaman kofa ce amma kuma baida girma sosai
danko kainama bazai shigaba bare kuma
nikaina.
Gurin k'ofa nad'an sa hannuna senaga kofar
nata girma kamar di ana bud'e gate mai taya
haka wannan k'ofar ta bud'e inda idanuna
suka makance da wasu irin abubuwa
burgewa dana gani aciki,bansan lokacin dana
shigaba. Nakusan 1hr ina kalle-kalle kafin
yayi alwala nasake sa hannuna agun seya
bud'u.
"Tana tsaye tana kallona tare dayin murmushi
tayimin nuni da sallaya mai kyau naje nayi
sallah ta agun. Bayan na idarne nake
tambayanta ita tayi sallan ne? Tace dani
batayiba kuma bazatayi harsena amince zan
aureta idan ba hakaba kuwa bazata k'arayin
sallahba.
Cikin sauri nace mata na amince zan
aureta,tace tofa lallai inda gaskene sena tara
da ita kafin ta yarda.
Nace mata addina ya haramta hakan bazan
iya aikatawaba, tace toshikenan muje amana
aure,nan naji zuciyata tak'i amincewa da
dahan,nace mata bazaiyuba,idan zaki
bautawa Allah tofa kiyi dan tsoronsa amma
badan son da kike minba,dan haka inhar
kinaso in aureki dagaske tofa sekin koma ga
Allah da zuciya d'aya.
Tacemin zatayi tunani akan hakan,tofa
wannan tunanin nata yakai kusan wata d'aya
bata gamashiba. Kuma kullum irin abincin
dana sabaci takebani,da farko wani abinci
takawomin wanda bansanshi,amma sena k'i
nace mata bansanshiba nafison irin wanda na
saba ci tace min a ina kenan? Amma sam na
kasa bata amsam dan bansaniba bana iya tuna
komai na kaina. Murmushi tayi taje ta
kawomin abinci irin wanda na saba ci,koda ci
abinci senaji irin girkin mum d'inace,da sauri
na kalleta harzanyi magana,seta katseni da
cewa irin abincin mum d'inkako,nace mata
eh ina mamakin kaina,tace karka damu
natane acan naje nad'ibo maka dan nasan
bazaka iya cin namuba kuma banaso karame.
Nidai inada niyan tambayanta akan mumdin
nawa,ban sake tunawaba kuma.
"Kullum haka muka kasance har tsawon wata
guda kuma bata salla. Idan zanyi baccima irin
wannan kumbonne dai aciki gadona na
alfarma yake da kayan sawa,komaida akwai.
Bayan wata guda tacemin ta'amince dan haka
ta fara salla,amma bata yadda muyi tare sedai
kowa yayi nashi,sannan bansan a inda take
kwanaba sesai kawai inganta aduk lokacin da
nake da buk'atar ganinta kawai zan ganta
kusa dani.
Ranan take cemin zata nunamin wani abu
amma sena tsunbaceta,sam nak'i senaga
hoton aunty agunta,idanuna na bud'e sosai
ina kallon fiskan amma nakasa gane
wacece,harzan karbi hoton seta b'oye tace
dani idan kana so kasake gani dole seka
tsunbaceni,nikuwa nak'i,se kuma nagane
cewa auntyce,sannan na tuna komai nawa
awanan lokacin,da sauri na juyo gareta nace
wannan auntyce ai matatace apple nawane
meyasa kika rabani da dangina kimaidani
kinji? Murmushi tayi tace bazan maidakaba
kamadena b'ata bainka. Har zai sake magana
setace ka tsunbaceni zan maidake,babu yadda
na iya haka na tsunbaci bakinta cikin rawar
jiki.
Tun daga wannan lokacin ban sake gane
komaiba jinta kawai nakeyi acikin jikina,tana
cewa kayi hakuri my manosh,wayan aunty ta
kira tanata magana da ita amazaunin
nine,wanda babu yadda na'iya bare
inkaryatata cewa banike magana jikina ta
shiga tun lokacin danayi kissing nata.
Haka kuma ta sake kiran ibrahim amma cikin
ion Allah shiseya gane cewa banine ke
maganaba,itace.
Taji haushi sosai,dan cewa tayi seta had'akar
da rayuwan aunty,shima batai nasaraba
saboda irin addu'oin jama'a dasuketayi min.
Dan kanta ta bar jikina inda naji ta janye
leb'enta daga nawa ta zauna afusace.
Inda yake a matsayin d'akin kwanciyana na
nufa na kwanta ina haki.
Hakadai muka kasance wataran sena tuna da
dangina,amma na k'ank'anin lokacine kuma
na sake mancewa kenan se kuma wani
lokacin harna shafe wata kusan uku a
haka,kuma bana ganinta sosai kamar da. Idan
na tambayeta ina take zuwa se tacein
mutanenka ne suka sani agaba dan haka bani
da zama nima. Ma'ana dai addu'oin kune
'yan'uwana dan wataran gabad'aya
kwakwalwarta toshewa yakeyi kamar ba itaba
gabad'aya seta canja kamanni tayita ihu tana
wasu irin abubuwa wanda bana iya jure
kallonsu sedai ingudu zuwa d'akina inyi
kwanciyata harsena dena jinta. Saboda
dazaran nashige makwancina tofa bana iyajin
komai datakeyi,watarana tace min inzo zata
maidani gida amma sena rungumeta,bamusu
na rungumeta tak'e tace inrufe idona,bayan a
rufe idonane nad'an mintina setace in bu'de.
Kodana bud'e sebangantaba kawai dai
naganni a wani shop tsaye ajikin mota se
dubata nakeyi da idanuna ina ganin
kayanjikina da kuma agogon hannuna wanda
bansan ya akai nagansu ajikinaba.
Kawai senaga aunty dasu ibrahim sunzo
suketamin magana amma sam nakasa ganesu
sebinsu da ido nakeyi musamman aunty.
Haka dai har suka fara fad'a duk bansan
meya had'asuba danna d'auka duniyar tasuce
muke har yanzu.
Sedata rik'e hannunane tace min ind'awa
aunty hannu tayi min nuni da
hannunta,shine kuwa nayi yadda ta gayamin
sannan tace inyi sauri in rufe ido,kawai sena
gammu a nasu duniyar inda tamin masauki.
Bayan mun nitsune kuma sena tuno da komai
sakamakon b'acewar motanu a idon mutane
wanda kowa ya tsorata sekace a film. Dalilin
hakanne masu yimin addu'a suka sake
yawaita tundaga ranan ban sake mance
komaiba game dani harta kaimu wani guri
wanda har yanzu bansan ina bane gurin
nakasa gane gurin... manosh ya tsaya daba
lbrnsa anan saboda razana dayayi yace
muhsin wlh nagana marwan. Tabbas naga
marwan da rashida awannan gurin kuma
suma sun ganni danhar na kirashi ama sam
tak'i ta barni muhad'u daga karshema bansan
inda takainiba sedana bud'e idonane naganta
tana kuka tana cewa wlh bazai yuba my
manosh, bazantab'a yarda a rabani dakaiba
idan bazan kasance tare dakaiba to wlh
auntyma sedai tarasaka.........
_inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un_ manosh
ya furta lokacin dayazo nan da lbrnsane ya
tuna da abinda shukrah ta zuba mishi akan
dick nashi wanda yayi sanadiyar sumewansa
tare dayi ihu mai karfin gaske. Da sauri
manosh yasa hannunsa akan dick nashi yaji
dai yananan,sanan ya kalli mai d'aukansa
yace da wannan nake godiya ga dukkan
'yan'uwa musulmai Allah yasaka muku da
gidan aljannah aminnn.....
Manosh yace what!??
Muh'am kugayamin meke damun aunt!
Muhsin yace haba abokina katsu mana kasan
dai dolene bazamub'oye maka komaiba amma
yana da kyau ka huta.
Majid yace kana nufin zai samu sukunine
batare dayasan inda aunty takeba,abokina
aunty bata da lfy shine aka fitar da ita waje
domin duba lfyarta dakyau.
"Kafin manosh ya sake musu tambaya muhsin
yayi saurin cewa karka d'aga hankalinka
rashinkane yasata cikin damuwa harta kamu
da ciwon...muh'd yayi saurin cewa ciwon
mantuwa.
Manosh dai bai gamsu da bayanin nasuba se
kallon tuhuma yake musu d'aya bayan d'aya
wayar muh'd ya ciro daga aljihun gaban
rigansa yayi dailing numbern aunt amma sam
baya tfy,hakan yasa ya kira mum nashi ta
d'auka tare da cewa hello,manosh yace mum
nine wai ina aint ne?"
Mum tayi ajiyar zuciya tace son karka damu
aunt tana lfy sun tafi indiane domin duba
lfyarta,kayi hakuri zakaji komai agida
gaji,barka da dawowan my son. Murmushin
karfin hali yayi yace to mum,sannan ya ajiye
wayan inda alfiya tace daddy ina ka tafi ka
barmune kullum idan muje gire gun mummy
kuka kawai takeyi waidan baka dawoba.
"Murmishi yayi yace tobaganinadawob
a,kigayamin medame mummy take gayamiki
dabanan?"
Alfiya tace ai suna dewa,abdallah dake gun
muhsin a baya yace toba se ki gayamishi
wanda tafi gaya manaba,tace ina ruwanka
aini aka tambaya bakaiba,daddy cewa takeyi
munyi kewankako,semuce mata eh,setayi
hawaye tace mana itama tana kewarka sosai
amma karmu damu kakusa dawowa
muyitayin maka addu'a Allah ya dawo dakai
lfy,Allah ya kareka daga sharri duk wani abu
mai cutarwa afad'in duniyannan semu
karanta maka *qulhuwallahu ahad da falad da
nass* sannan muyi maka addu'oi wani
addu'anma bamu iyaba mummyce takeyi
munace ameen. Abdallah yace wlh nidai na
iya daddy alfiyace bata iyaba setayita yin
jagwalgwale wai ishcibisshaa setace ameeen.
Ba manosh kad'aiba dukkansu seda sukayi
dariya,inda alfiya tace wlh daddy ka'arya
yakeyi na'iya kuma idan mummy ta dawo a
tambayetama. Manosh yace ainasan duk kun
iua,amma alfiya kinsan abdallah yayankine
ko,tace eh tare da d'aga kanta sama,yace to
bakyau k'anwa tacewa yayanta yana k'arya
kinji? Tace to daddy nadena bazan
sakeba,yace yawwa maisanyi na yana mata
dariya,tace mutafaaa daddy,ai kuwa seya
mika mata hannu suka tafa,sannan ya juya ya
dunk'ulawa abdallah hannu suka buga duk
suna jin dad'i tare dajin k'aunar yaran nashi
yana sake shiga jikinsa musammanma
dayasan apple nashi batanan.
Muhsin yace saukeni anan muh'd zanje gidan
radio goyel domin musanar da al'umma cewa
captain ya dawo sannan muyi musu godiya
kuje zanzo na sameku. Sukace ok sannan
sukaci gaba da tfy hankalin manosh duk baya
kansu yana can tunanin apple nashi saboda
bala'in missing nata dayayi gashi kuma koda
tanananma baisan ya abun zai kasanceba.
Majid yace wai lfyanka ko prince,tunanin me
kakeyine haka munata magana?"
Manosh yace me kukace,wai ina marwan
yajene? Muh'd yace wlh bamu saniba dan
numbernsa bata shiga sam. Manosh yace
kamar yafa? Majid yace pls kabar duk wani
magana semunje gida zakaji komai. Babu
wanda ya sake cewa komai har suka isa gida
Tun daga gate suka fara hango mutane
dasuka yiwa manosh barka har suka
shige,masu gadi da sauran mutanen sukazo
gun da sauri sunayiwa dad d'in manosh barka
tare da gaishe da manosh,ba laifi ya sake
sukayi musabaha daduk jama'an yana rik'e da
alfiya a hannusa sannan suka wuce gefenshi
dake gidansu nan yace da alfiya taje gun
mum zaiyi wanka,ba musu suka tafi itada
abdallah seya wuce toilet. K'arewa kansa kallo
yadingayi sannan yayi wanka ya fito ya shirya
yayi sallolin da baiyi wato azahar da la'asar.
Bayan ya idarne ya fito sanye da jallabiya,dan
yana da kaya kad'an a gidan nasu.
Abinci aka kawo musu suka ci amma sam
dukda yadda manosh yake son fruit yak'isha
seya koma kan kujera ya zauna tare kiran
abdallah da alfiya ya ajiuesu akan cinyarsa.
Daidai nan miher ta shigo da gudunta ta
rungume manosh tana kuka"
Wani sanyi yaji aranshi dan base nagaya
muku irin son da yake tsakanin yaya da
k'anwannanba. Manosh yace haba kuma
miuena kukan tunda ga bro naki ke kad'ai ya
dawo,murmushi tayi tace Allah sarki bro
manosh darabon bazan mutuba ashe zan
ganka,yace haba sis kidena fad'an haka mana
inba kinaso inyi kukaba,take ta share hawaye
tana rik'e da hannusa tace yaya ina suka
ajiyeka dan Allah?
Yace miher ba yanzuba dan Allah kimin
bayanin akan aunty bazan iya jiran bayanin
su dad ba,kekad'aice zaki gayamin komai.
Nan take tace bro Allah sarki aunty taga
jarabawa iri iri wlh idan kaganta dole ka
rausaya mata danma tana da tawakkali. Bro
aunty tana da matsalan *kidney* dukka biyu
nata sun lalace ce bro anje mata dashe
k'odane bro abinda ya kaisu kenan broo...seta
fashe da kuka, mik'ewa manosh yayi yace
what!!?
Dashe fa kikace nawa za'a dasa mata badai na
ibrahim ba!? Miher ta tsorata dan yadda taga
hankalin yayanta ya taahi,itama mik'ewa tayi
tace karkasa damuwa aranka na *lubna* za'a
samata. Manosh ya juya yana kallon miher
cikin tuhuma yace lubna kuma? Tomeyasa
sena lubna? Meyasa aka tafimin da matata
batare dana saniba meyasa!?
Abdallah da alfiya se suka fara kuka dan
ganin yadda daddynsu ya sauya cikin
k'ank'anin lokaci.
Muh'd ya mik'e yace miher shiga dasu
abdallah gun mum,bamusu ta kamosu sunata
kuka kafin su fita manosh yace miher ina
marwan rai ab'ace? Tace yaya bro marwan
bamusan inda ya tafiba dad nashima yana
kwance a hoapital din su bro muh'd.
Majid yace my luv jeki ciki dasu pls.
Bayan ta tafine majid yace za'a sawa aunty
kidney'n lubna sabida su sisters kuma twince
ita da aunty,akwai sirri babba wanda hajiya
iya kakan marwan da kuma mum d'in
marwan suka b'oye wanda se yanzu muka
sani,tuk kafin mu sani ashe shi marwan mum
nashi tagaya mishi lbrn shine silar rashin
lfyanshi daga bisani kuma yayi tfy wanda
komuma bamusan inda yakeba har yau.
Mamakine bayyane k'arara a fiskan manish ji
yake kamar a mafarki kallonsu kawai yakeyi
inda dukkansu suka rasa abunyi kowa da
abinda yake tunawa aranshi. Sallamar muhsin
ne ya katsesu, yace lfy kuwa naganku haka?
Manosh yace mekuje nufi da wannan lbrn ne
nakasa fahimtar komaifa,meya samu dad din
marwan kuma? Sukace hawan jini,sannan
dagaskene aunty da lubna ciki d'aya sukafito
duk yaran alhaji muh'd atta ne...
Wayan muh'd manosh ya karb'a ya kira
numbern oganshi sau biyu kafin ya d'aga yace
hello sir manosh ne. Ogan yace what! Manosh
kana ina? Yace sir ina gida pls sir visa nake
so ka taimaka in samu zanje india. Sir yace
manosh yanzu haka akwai wanda zai tafi
india jibi amadadinka,amma bazan iyabakaba
saboda kana bukatan hutu ina nan zuwa
gidanku... manosh yace no sir pls aunty tana
cikin wani hali sir natabbata tanada bukatana
acan,yace manosh _i know everything but you
need to rest gaskya_yaushe ka dawo? Yace
yanzu sir,pls sir i'm alright wlh just help
me,ogansa yace ina zuwa gidanku yanzu.
Manosh ya shiga d'aki ya cire jallabiyan
jikinsa yasa kananan kaya ya fito yace dasu
muhsin muje hospital muga dad d'in
marwan,muh'd yace no manosh ka zauna
mutane biyu suje gunshi amma kai ana
buk'atanka anan,yace ina bazai yuba ai yanzu
zamu dawo idan kuma bazakujeba toni na
tafi.
Sunsan dagaske yakeyi dan haka suka fito
inda dad yake waje suna zantawa da wasu
malamai. Manosh ya nufi gunsu suka gaisa
sannan yace dad zanje duba daddyn marwan
yanzu zamu dawo,dad bazai iya hanashiba
dan yasan yadda marwan da manosh
suke,yace kuje pls majid ku dawo da
wuri,yace insha Allah dad sannan suka juya
zasu tafi muhsin ne mai driving.
.
Abdallah ne ya fito yanata kuka wai zaibi
daddynshi,daga mirrow manosh ya hangoshi
dan haka muhsin ya tsaya muh'd yace zomuje
abdallah.
Acinyar babanshi ya zauna idan uban ya
rungumeshi yana hawaye yana cewa insha
Allah zan tafi india zanje gurin mummynka
abdallah nasan tana buk'atana akisa da ita,ya
Allah kakaremin matata Allah ka bata lfy yana
hawaye akan d'ansa abdallah su majid suka
amsa da ameeen ya rabbi...
Sannan ya sake cewa ina sake neman wata
alfarma agareku jama'a dakusa matata acikin
addu'oinku domin an fita da ita waje domin
yimata aiki fatanmu shine Allah yasa ayi
aikin a sa'a ameeen nagode. Da sauri abdallah
yace nima zanyi jawabin,akace mezakace to?
Yace Allah yabawa mummyna lfy,Allah
yabarta tare da daddynah har mutuwa
ameeen...
Dariya akayi tare da amsawa da ameen
sannan manosh ya d'aga d'ansa sama suka
fito waje yana cewa baka so in kawo muku
aunty amarya kenan?
Abdallah take ya b'ata rai yace bana so.
Muhsin yace yanzuma kuwa gurin amaryan
zamuje kafin mu wuce gida,abdallah yace
tosedai idan bana nan dan bazan tab'a yadda
daddy yaje wani gun babuniba kuma itama
amaryan zata gane kurenta ciwonta anyi
kuma zance mata sam bana kaunarta nida
alfiya.
Hakadai suketa hira har suka iso gida. Ai
kuwa se suka sami maigidan manosh harya
iso dan dama sun zauna suna kallon bayanin
da manosh yakeyine a gudan TV GOTEL
wanda akeyi kai tsaye,hakama gudan radio.
Duk wanda yaji lbrn se san barka,hatta
almajirai saboda aunty itana kowane.
Bayan awanni biyu maigidan manosh ya tafi
inda akace manosh bazaijeba ya zauna ya
samu lfy sosai.
Wanda shi kuwa sam baiji dad'in hukuncin
da aka yankeba.
Rashida zaune da marwan suna cin
abinci,tace yaudai dan Allh kabani wayata
inkira jama'a kodan asan inda muke. Anitse
yasa hannu a aljihunsa ya fito da wayansa ya
kunna. Texs ne wanda babu adadi sukaita
shigowa,sam bai bud'e ko d'ayaba yayi saurin
kiran number'n mum nashi,lokacin ta idar da
sallan la'ar kenan a hospital da sauri ta
d'auka tare da cewa hello mum,wani sanyi
taji a ranta tace marwan inaka shiga haka
anti neman numbernka amma shuru kaida
rashidan fatan dai kunanan cikin koshin lfy?
Shi kanshi yayi missing na mum nashi yace
lfy lfyanmu lau mum ya kuke,tace lfy k'alau
ina kuka shigane haka? Yace muna nan a
abuja mum. Tace Allah sarki marwan kayi
hakuri ka dawo gida dan Allah domin komai
ya wuce yanzu,marwan yace to mum zamu
dawo ya dad,mum bansan me zan fara cewa
dad ba gabad'aya tsoron kiransa nakeyi wlh.
Mum tace marwan karkaji tsoro domin
daddynka yana buk'atanka ayanzu yana
kwance a asibiti yana fama da jinya abokanka
suketa fad'i tashi akanshi mahaifinka nada
buk'atan ganinka marwan dan haka kayi
gaggawan dawowa sannan kuma...innalillahi
mum meke damun dad? Marwan kaidai ka
dawo gida cikin sauri,badamuwa
mun,ganinan akan hanya insha Allah kigaida
dad d'in.
Marwan yana katse wayan ya tashi
hankalinsa dukya koma gun dad nashi ba
shiri ya shirya suka fito. Abokinsane ya musu
hanya suka samu jirgin karfe biyar se yola.
Suna isowa kusan 6 ya tara musu adaidaita
sawu suka shige ya sauka a hospital yacewa
mai nape ya wuce da rashida gida taje tayi
abinci sannan tazo da mota.
Mahaifin manish da kuma mahaifiyarsa agun
dad d'in marwan sunje dubashi ana zaune
ana hira se sukaji sallaman marwan.
Wani ajiyar zuciya dad d'in marwan ya sauke
lokacin dayaga d'an nasa ya rame sosai kamar
wanda yayi ciwo. Bayan yayi musu sallamane
ya wuce gunda mahaifinsa yake kwance ya
tsuguna tare da rik'e hannunsa yace sannu
dad,ya jikinnaka,dan Allah dad kayi hakuri
karka ce komai,kawai nayi abinda nake
tunanin shine mafita agareni shiyasa,amma
dan Allah kayafemin?
Dad nashi ya shafi kansa yace bazance
komaiba marwan,domin bakayi laifiba hakan
da kayi shine daidai domin na fahimceka
d'ana Allah ya maka albarka,sanyi marwan
yaji a ranshi yayi nurmushi tare da cewa
ameeen dad nagode,toya jikinka? Dad yace
nayi sauki ai yanzu dana ganka kusa dani,ko
kuma ince tun dawowan abokinka na fara
samun lfy,abokanka sunyi k'okari dani sosai
sedai muce Allah ya saka musu da alkhairi
Allah ya masu masu musu suma, aka amsa da
ameen. Amma zuciyar marwan tana nanata
abinda mahaifinsa ya fad'a wai tun bayan
dawowan abokinka,yace dad prince ya
dawone? Yace eh ya dawo yau kwanansa
d'aya kenan da dawowa. Tsantsan farinciki
marwan baisan sanda ya rungume
mahaifinsaba yana cewa Allah sarki abokina
Alhamdulillah,ina yake dad? Dad d'in manosh
yace suna can gida. Sallamar dr muh'd ne ya
katse su,shima ya tsaya kallon marwan cikin
mamaki yace dama zaka dawo ashe? To ai ka
koma domin bana bukatar dawowanka.
Marwan yace haba dr kuyi min uzuri dan
Allah,muh'd ya mik'awa dad maganinsa
sannan ya kalli marwan yace uzurifa kace? Ai
babu wani sauran uzuri kuma domin kanuna
mana cewa bamuda muhimmanci agurinka
har zaka iya mana haka. Dad d'in manosh
yace yanzu dai tunda ya dawo kuma yasan
yayi laifi toku mishi uzuri. Muh'd yace dad
gaskya semunyi zama danba haka kukeba run
yaranta amma gashi alokaci d'aya ya canja
mana tsarinmu dan haka dole semunyi zama
shima yasan hakan.
Babu wanda ya sake cewa komai haka
marwan ya gaidasu dukkansu sannan ya nemi
gafaran mahaifiyarsa sannan suka fito shida
muh'd inda suka wuce office nashi yana cewa
waime hakane muh'd? Amma ai a tunanina
ban d'auka zakumin hakaba tunda kunji
dalilin yin hakan nawa. Muh'd yace sosai
munji dalilinka amma kuma ai abinda kayi
bashine mafitaba kuma kanuna mana cewa
mu abin baishafemuba kenan sekai kad'ai.
Marwan zaiyi magana muh'd yace nazo bawa
dad maganinsane dan haka zan koma idan
mun had'u dukkanmu semuyi magana.
Marwan yace shikenan muje ka saukeni
agida,tare suka fito suka shiga motan muh'd
amma babu wanda yace komai har suka iso
gidan marwan ya fita shima muh'd ya wuce
gidansu manosh inda suketa hira.
Bayan marwan yayi wanka yaci abincine suka
sake fitowa shida rash suka kawowa dad
abinci. Se marwan yace zaibar rash a hospital
d'in bariyaje gunsu manosh ya dawo.
Suna hira amma hankalin manosh gabad'aya
yana india saboda har yanzu su yah ibrahim
basu kira kowaba.
Slm marwan ya fad'a tare da k'arasawa ciki
inda suka amsa salamarsa suna kallonshi
cikin mamaki dan sam muh'd baigayamusu
cewa marwan ya dawoba. Abdallah yanadaga
jijin babanshi yace oyoyo uncle marwan
sannu da dawowa,marwan ya k'arasa gun
manosh cike da murmushi manosh ya mik'e
suka rungume juna suna farinciki abdallah se
kallonsu yakeyi yace daddy dama manyama
suna rungumar junansune? Dariya sosai
manosh yayi tare da sake marwan yace
sosaima kuwa musamman idan sun dad'e
basu had'uba. Marwanma dariya yakeyi
sannan ya d'aga abdallah sama yace ina
alfiya? Yace tayi bacci tun d'azu ko sallan
isha batayiba,marwan yace haba to idan ta
tashi gobe ka tabbata tayi gashi? Abdallah
yace insha Allah zatayi,marwan ya ajiyeshi
yace jeka ka kawo min abin tab'awa kaji? Da
sauri abdallah ya fita sannan ya mik'awa
sauran hannu suka gaisa harda muh'd.
Yace koku had'a fiskokinku koku sake dai ina
cikin farin cikin dawowar prince,saboda haka
bazan biye mukuba sannan kuyi hakuri
kumin uzuri akan abinda nayi muku... babu
wanda yace dashi komai acikinsu,se manosh
da yake binsu muh'd da kallo dan yaga duk
sunyi shuru suna danna wayoyinsu.
Murmushi manosh yayi yace waito me kuma
hakan magana yake muku fa? Muhsin yace
dan Allah malam babu ruwanka aciki kawai
kayi shuru,manosh yace kamar inyi shuru
bayan kunyi shuru kowannenku yana danna
waya hakuri yakebaku tunda yasan yayi laifi
aise ku mishi uzuri. Muh'd yace idan kaine
hakan ya faru dakai mezakayi a wannan
lokacin dakasan komai? Manosh yace gaskya
kusan yadda marwan yayi nima hakan
zanyi,amma dai bazaiyu ace na b'oye nukuba
tunda mun zama d'aya babu wata boyayya a
tsakaninmu ai koma akan menene,amma pls
ubar maganan haka ya isa kawai marwan
baka kyautaba da abinda kamusu semu kiyaye
gaba inaga maganan ta k'are. Muhsin yace
bata k'areba prince wannan wulak'ancine ai
amintakarmu yazama bayi da ma'ana kenan
wai har ace bamusan inda d'aya daga cikinnu
yakeba wannan abun kunyane wlh laifikam
kayi "dude" kawai dai abar maganar haka
nan. Marwan yace nasan nayi laifin ai
shiyasa nake so mufahimci juna ai,majid ya
mik'e yace to nidai prince kacewa miher ta
taimaka tazo mu tafi dan yau bazan barta ta
kwana agidaba jiyama da kyar nayi bacci wlh.
Muh'd yace kaikuma ana magana ka
tashi,majid yace eh ai maganan naku bata
shafenibane shiyasa domin nibamma san
waya shigo nanba. Bugu manosh yakaiwa
majid ta yadda ya isa hargun marwan harya
bugeshi,marwan yace me hakane wai baka
ganine? Majid yace eh aikasan ni
makahone,dariya manosh da marwan sukasa
inda majid yakaiwa marwan duka yace wlh
sa'a kaci d'an iska albarkacin dad baida
lfyane kawai zamu d'agama kafa dabadan
hakaba wlh dase kaci kwakwa-kwakwa kamar
yadda mukayiwa captain a baya...
Hahahaha sukasa dariya dukkansu,manosh
yace ai wlh kune kuka dena kulani amma
muna waya da marwan ab'oye lokacin.
Muhsin yana dariya yana kallon marwan yace
to ashe kaine d'an iskan daka karya mana
doka tun'a wancan lokacinma
bamusaniba,dariya sukeyiwa junansu sosai
inda inda manosh yake kallon muh'd yace
kodai in fad'i nakane abokina? Muh'd yace
ohonka idanka tonama ai kanka ka tonawa...
hakadai suketa hira cikin hara da dariya. Can
se wayar marwan ta fara ringing,kodaya duba
numbern waje yagani hakan yasa yayi saurin
amsawa yace hello,muryan yah ibrahim yaji
yace marwan,marwan yace yane mutanen
india kun isa lfy? Yace lfy lau wlh yawanci
numbernku baya tfy kaima da kyar na sameka
wlh ka dawo daga tfyarnaka ne? Marwan yace
eh wlh yau na dawo yasu mama ya aunty da
lubna? Ibrahim yace suna lfy lau wlh
auntynema bata jin dad'i wlh zazzab'i
taketayi tunda muka bar nigeria wlh.
Subhanallah ya jikinnata to? Yace da sauki
inasu muh'd,yace kowa lfy kun samu masauki
mai kyau ko? Yah ibrahim yace alhamdulillah
wlh,manosh yace banishi mugaisa pls?
Ibrahim yaji kamar muryan manosh,shi kuwa
marwan baisan cewa babu wanda sukayi
waya da 'yan india ba shine mutum na farko.
Manosh ya karb'i wayan yace hello yah
ibrahim,ibrahim ya kira sunanshi cikin
mamaki yace manosh dakai nake magane?
Manosh yayi mirmushi yace nine wlh ya kun
isa lfy ina apple d'ina? Yah ibrahim yaji
dad'in aranshi yace Alhamdulillah bari na
kaimata kozata ji sauk'i gaskya nayi
farincikin jinka captain Allah abin godia.
Shima manosh dad'in yajin a ransa mara
misaltuwa yanata so yaji muryan apple
nashi,yah ibrahim yayi sallama a d'akin da
aunty take kwance lubna ko sallah ko takeyi
mama da baba kuwa suna can d'akinsu ko
kuma ince masaukinsu yah ibrahim lfy kaketa
sauri haka? Yace barima in had'a da gudu
aunty kashi zakuyi magana,batare datasan
wayeba ta karb'a dan atunaninta ma dad d'in
manosh ne.
"Tace Assalamu alaikum"
wani sautin saukan numfashi taji"sannan
akace "wa'alaikumus salam _my one nd only
apple_.
Wayan ta cire daga kunnenta tana karewa
wayan kallo sannan ta sake mayarwa
kunnenta tace peach...? Sautin sauk'an kiss
kawai taji akunnenta har cikin ranta taji wani
ni'ima mara misaltuwa take ta fara hawayen
farin ciki tace peach kaine kodai mafarki
nakeyi? Manosh ya mik'e daga inda ya zauna
kusada marwan ya shige d'akinsa su kuwa
sebinshi da kallo sukeyi suna taya abokinsu
murnan jin muryan matarsa...
.
"Peach yanaji kayi shuru?"
"Apple how are u"
"Ya jikinki my luv?"
Alhamdulillah peach kaine dagaske?"
"Nine apple,Allah ya dawo dani tare da
taimakon addu'oinku agareni."
"Murmushi tayi tace yaushe zakazo india
peach,ina shaik'in son ganinka my luv"
Karki damu *aunt* zanzo insha Allah kema
kinsan nafiki son inganki ko?" Dan haka
inaso ki kwantar da hankalinki yanzu haka
k'ok'arin da naketayi kenan wlh.
Dariya tayi maicike dajin dad'i tace kai
Alhamdulillah Allah abungodiya peach nayi
matuk'ar farinciki wlh Allah,ina fata dai kana
lfy?"
"Dariya yayi tare da cewa i'm fine aunt
kikwantar da hankalinki lfyata lau
jealousynah." Ya k'are maganar yana mata
dariya
Itama dariyar tayi tace ka fara koh?
"Apple yasu mama da fatan duk kuna lfy,ina
kuma sisterna lubna?"
Shuru tayi nad'an lokaci sannan tace kowa
lfya sis lubna ma tanata murnan dawowarka
gata tadameni waisedai in bata wayan,amma
bazan bataba dan nima bangaji dajinkaba
tukun."
"Manosh yayi dariya yace toki
gaishesu,sannan kicewa sis lubna kawai
nagaisheta yanzu bana son jin kowa se apple
d'ina,dan haka tayi hakiri senazo magaisa."
Dad'i aunty taji,farin ciki ya kasa k'auracewa
fiskanta tama mance da yah ibrahim yana
tsaye agefe se shagab'a da kalaman soyayya
kala-kala suke jefan junansu dashi abin ban
sha'awa...
Marwan yana duba account nashi seyaga 0.00
"Yace lallai captain wato seda ka tabbatar
wayan ta gama amfani kafin ka dawomin da
ita koh?"
Manosh yace sorry luv ne yayi nisa nama
d'auka ko muna tarene ashe awaya muke.
Dariya suka sa dukkansu muhsin yace shiyasa
naga kamar ma seda kayi wanka kafin ka fito.
Hahhhhhh!
"Washe gari aka sallami dad d'in marwan
dayake ya samu lfy.
Gida aka wuce dashi inda mahaifin manosh
da sauran 'yan'uwa suka bashi hakuri akan
ya maida matarsa wato hajiya khadija
mahaifiyar marwan
"Cikin saukin kai kuwa ya maidata inda
marwan yaketa murna."
Sedai hajiya iya tana kwance ba lfy,tunda
abun ya faru itama take jinya kad'an kad'an
dan tak'i barima asan bata da lfyan se yanzu
da ciwon yacigaba sosai.
Hakadai aketa faman jinya dan dad d'in
marwan ya d'aukota daga girei ya dawo da ita
gidansa inda take samun kyakkyawan kulawa
daga gun mum d'in marwan.
"Manosh kuwa anata kan masa magani akan
abinda ya sameshi gameda lfyanjikinsa akan
abinda shukrah ta mishi."
Maganin *islamic* ake mishi wanda yake
wanka da kuma shafa wasu mai da aka
harhad'a dan jinnu,shine yake shafawa akan
mazantakarsa dan dama sam kamar ya dena
aiki.
"Wata rana manosh yana bacci seya
tsincikanshi dayin mafarkin shida aunt kuma
suna tarayya irin na ma'aurata acikin
mafarkin nashi"
Kodaya farka kuwa,seyaga dagaske ya b'ata
jikinsa wanda dole seyayi wanka."
"Yawansa ya d'auko a gefen gado ya kira
apple"
Da sauri ta daga tare da cewa peach?"
Muryansa mai d'auke da sha'awarta yayi
maganan cikin yanayi na kashe jikin mai
sauraro yace "apple"
Seda ta had'i yawu sannan tace na'am ina
kwana?"
"Lfy keda waye agurin?"
"Nida lubna ne"
"Ina so inyi magana dakene"
Ta kalli lubna sannan ta mik'e zuwa toilet
dan babu inda zataje tunda a hospital suke."
"Tace ina sauraronka lfy?"
"Apple ina cikin jin yunwarki domin yau da
mafarkinki na farka kuma koda na tashi
senaga harna b'ata jikina pls do some for me
apple."
"Murmushi tayi tare da cewa Alhamdulillah
peach,insha Allah ka samu lfya kenan" yace
no apple pls try something"
"Hhhh peach da... ya katseta da pls *aunt?"*
"Jikinta ya mutu tace ok...
Hmmm! Kunnuwana sun kasa d'aukan abinda
*aunty* takeyiwa *prince manosh*, daga
wayan aunty nake iya jiyo muryan manosh
yanata tsanbatu,ita kuwa cewa take ya isa
haka peach.
"Manosh yace no apple no."
"Yeah karka min asara dewa mana,kabar min
sauran domin nima ina jin k'ishinsu sosai."
Hhhhhhh! Manosh yayi dariya yare da cewa
*ok* my luv,thankyou so much luv u.
Koda taji ya katse wayar seta hau yin dariya
tace eyyah peach kasamu lfy Allah nagode
maka...
"Koda aunty ta fito daga toilet seta lubna tsaye
tana nunata da yatsa tana cewa wato hakane
koh?"
"Tofa lallai bazai yuba,domin inanan koda
yazo babu abunda zai wakana harse malamai
sunyi sharhi akan airenku tunda kusan
*4month* kenan bakwa tare dan haka se an
sake sabon aure."
"Maryam taja kunne lubna tace ba'aso
k'ananan yara sunayiwa manya lab'e."
Bayan maryam ta wucene akabar lubna da ido
tanabin aunty da kallon mamaki,ita kuwa
aunty wayanta ta rungume a k'irji tace _"oh
my peach,i missed you more"_ tare da rufe
idanunta tana mirmushi tana kad'a kanta
ahankali... lubna kuwa se ta bud'e idanu tana
kallon ikon Allah...
Komai na tfyar manosh ya kammala.
"Kowa sako yake basa zuwaga aunty dasu yah
ibrahim"
Sak'on addu'a kala-kala yanata godiya
aminansane suka rakashi har abuja,bayan ya
tafine sukuma suka dawo yola.
"Saukar manosh a india kenan yayiwa wani
abokinsa *hakim* waya,batare da b'ata
lokaciba hakim yazo ya d'aukesa basu wuce
ko'inaba gidan hakim,bayan yayi wanka ne
sam yak'i cin abinci ruwa kawai yasha yace
shida apple nashi zaici abinci insha Allah.
"Tafe suke shida hakim har hospital
d'in,dama acan shi hakim yake aiki,kuma
tunda manosh ya dawo ya nemi number'n
hakim ya gaya masa komai, dan haka hakim
ya nemi su yah ibrahim kuma kullum seya zo
dubasu,yah ibrahim dasu baba dai sunsan
cewa hakim abokin manosh ne saboda ya
gayamusu,amma aunty da lubna basu saniba.
"Isarsu hospital d'in suka had'u da ibrahim
nan suka rungume juna da manosh,suna ta
murna sannan nufi gunsu baba.
Manosh ya gaishesu cikin girmamawa sannan
suka d'anyi hira kad'an se yah ibrahim yace
muje gacan d'akinda su aunty suke fitowana
dai sunata bacci dukkansu.
"Da sallama suka k'arasa,amma duk suna
bacci abinsu"
Daga gefen gadon auntyne ya hango pix
nashida ita dasu badallah sunyi kyau sosai.
Murmushi yayi tare da sauke ajiyar zuciya
Ahankali ya k'arasa inda take kwance sanye
da pakistan red riga da wando baisanta
dashiba yasan tabbas a nan india suka saya
na lubna blue amma duk tsarin iri d'ayane.
Sam ya kasa dena kallonta dan yadda yaga ta
k'ara kyau sosai,aranshi yace garin ya
karb'eki apple.
"Ahankali ya ibrahim yaje inda lubna ke
kwance yamata magana a kunne yace(my
tashi manosh ya k'araso)
Kamar jira take ai kuwa seta bud'e ido taga
yah ibrahim yana mata murmushi,sannan ta
dubi sauran dr hakim se kawai taga bro
manosh yana shafe gegen fiskan aunty da
yatsan hannunshi ahankali.
Ai da sauri ta tashi tare da murna tace "bro
manosh?"
Ahankali ya juyo yana kallonta yana
murmushi wanda yake k'ara mishi kyau yace
na'am *sis lub*
"Ai kamar a mafarki aunty tajiyo muryan
peach, kafin ta bud'e ido hakim yayi sairin
janye manosh shiya tsaya a inda aunty take
kwance,shi kuwa manosh ya b'uya a bayan
hakim."
Koda aunty ta bud'e ido setaga yah ibrahim
ne da dr se kuma lubna"
Amma sam tana jin wani irin k'amshin turare
wanda ta tabbatar agun peach nata kawai
take jinshi.
"Yah ibrahim yace aunty doctor ne yazo
dubaki"
"Tace yah ibrahim kamar naji an kira sunan
peach yanzu"
"Lubna tace sedai a mafarki k'ila kikaji, se
kuma tayi murmushi tare dayiwa aunty'n
alama da kanta wato yana bayan doctor
hakim"
" take aunty ta gane manufar lubna dan haka
ta tashi da sauri tasa silipas nata tayiyo bayan
doctor hakim da sauri shima manosh ya fito
ya rungume matarshi tsam ak'irjinsa itama
haka ta k'ank'ameshi tana mai farinciki
azuciyarta da fili,su kuwa dariya sukasa inda
hakim ya koma gefe d'aya ya tsaya sunata
kallonsu inda manosh ya rufe idanunsa luf
yana juyata a hankali.
"Ganin hakan yasa yah ibrahim kamo hannun
lubna batare dayai maganaba suka fito waje
dukkansu domin subawa amaryam da ango
guri...?
"Aunty tayi saurin d'ago da kanta tana
k'arewa peach nata kallo cike da farinciki
afiskarta."
"Shikuwa sake kwantar da kanta yayi
ak'irjinsa yana cewa "please apple let me be
okey?" Murmushi tayi tare da sake nitsewa
sosai ajikinsa tana addu'a acikin ranta."
"Sund'auki lokaci sosai ahakan sannan tace "i
luv u peach" "i luv u sooo much!"
"Ahankali ya d'agota suna kallon junansu
cikie da shauk'in juna yace "d'ume avi?"
Idanunta suka kawo kwalla tace "miyid'ima
gorko am."
Kwallan daya cike mata ido yakebi da kallo
tare da rik'o fiskarta da hannayensa biyu yace
"sake fad'amin kalaman masoyiyata" fiskanta
abin tausayi tace "ina sonka peach,k'auna ta
hak'ika" ahankali hawayen suka fara
kwaranyowa daga idanunta,amma dukda
haka bata d'auke idanunta daga kallonsaba."
"Harshensa yakai gun hawayen yake lashesu
cikin wani irin salo na k'auna"
"Ita kuwa mannuwa sosai tayi dashi tana
shafe bayansa da k'ananan hannuta."
"Manosh ya sake kallonta har cikin ido yana
murmushi yace "pls say it again apple"
"Murmushi tayi tare da lakace mishi dogon
hancinsa da yatsan hannunta sannan tace "i
maryam muh'd attah, luvs d prince d captain
nd my sweet peach manosh soo verry much
more...!"
Hhhhhhhh!
"Manosh yayi dariya tare da d'agata sama
dama kunsan bata da auki sosai,dan haka se
juyi yake da ita acikin d'akin yana cewa "you
are d best among d bests my heart." Akoda
yaushe godewa Allah nake dayabani ke
amatsayin matata ta duniya da kuma gidan
aljannah insha Allah."
"Allah ya barmu tare apple"
"Tace ameen peach"
"Ya sake cewa Allah yasa mubar duniya tare
rana d'aya lokacima d'aya"
"Ta sake cewa ameen"
"Yace Allah yara mana yaranmu ya albarkaci
rayuwarsu bayan ranmu"
"Aunty tace ameen"
"Yace Allah ya biya iyayenmu da gidan
aljannah"
"Tace ameen ya Allah"
"Yace Allah kabiyawa 'yan'uwa musulmai
buk'atunsu na alkhairi duniya da lahira,Allah
wanda basu da lfya Allah ka basu lfy,Allah ka
gafarta mana zunubammu wanda muka sani
da wanda bamu saniba, Allah ka d'aukaka
musulunci tare da musulmai, ka k'ask'antar
da kafurci tare da kafurai Albarkacin fiyayyen
halitta Annabi Muhammad (S A W)...
"Manosh da aunty'n suka amsa da
ameeen,nima sadnas nace ameeen,kufa masu
karutu?"
"Manosh ya sauke aunty ahankali tare da
matse tsam ajikinsa yace "i miss you 3much
apple."
"Tace me too"
"Fiskarta ya rik'o yana mata wani irin kallo
mai kashe jiki da brawn eye nashi.
"Kunya ta tsinci kanta aciki"
"Shikuwa seya d'aura harcensa akan saman
idonta yana yawo dashi harkan hancinta"
Koda yazo nan seya kira sunanta "aunt?"
Kaita d'ago anitse suka had'a ido
dashi,harcensa yasa akan lips nata ya lashesu
cikin wani irin salo."
Yad'an juma ahakan sannan ya fara tsotsesu
kamar wanda ya samu zuma"
"Itama seta farayin yadda taji yake mata
idanunta a rufe.
"Asannu suka fara kissing d'in junansu kamar
bazasu sake junansuba,duk sun gama shiga
wani hali kusan 10minit."
"Nocking lubna taketayi amma sam basuma
jiba"
"Tahad'a da sallama shuru."
Aiseta sake sallama da karfi tare da bud'e
k'ofan ta shigo.
"Aunty dai taji shigowar mutum,amma sam
manosh yakasa barinta taga wayene"
"Se tsotson abarsa yakeyi kamar "kare yasamu
nama"
Ganin haka yasa lubna yin murmushi
ahankali ta fita tare da rufe kofan ta yadda
bazasujiba."
"Manosh ya saki bakin apple yace koma
wayene ai sunsan abinda zai faru bayan
had'uwata dake,dan haka ad'aga mana kafa
na 3hrs."
"Ido aunty ta zaro tace 3hrs fa kace peach?"
"Yace yes! Yana d'aga mata gira tare da sake
maida bakinsu ya had'e guri d'aya suka
d'aura daga inda suka tsaya."
"Uhmm! Abun ba sauk'i fah."
Lubna tana tsaye abakin kofa tama rasa ya
zatayi,domin dama doctors ne zasu shigo gun
aunty shine yah ibrahim yace lubna taje ta
sanar dasu,se kuma gashi ta fito tana tsaye
abakin kofan."
'Ya ibrahim ya kirata,tace ina zuwa"
"D'akin ta sake shiga da sallama,amma
wannan karon setaga aunty kwance ajikin
manosh inda shi yake kwance akan gado
amma bakomai sukeyiba fase kissing d'in
juna."
"Da sauri ya rufe kofan tare da bubbugawa da
hannunta tana cewa aunty ga doctors zasu
shigo dubaki."
"Ai cikin sauri aunty tabar jikin manosh tare
da kamo hannunsa wai ita adole zata d'agoshi
daga kan gadon.
"Ai kawai seya janyota ta sake fad'owa jikinsa
yayinda shi kuwa yake mata dariya yace
kinajin zaki diya d'aganine?" Tace pls peach
kaji fa doctors suna waje,kuma nasan hardasu
mama da baba za'a shigo yanzu hakafa suna
tsayene awaje wlh kunya nakeji pls katashi."
"Bashiri manosh ya tashi tare da gyara jikinsa
da sauri-sauri,ita kuwa aunty se dariya take
mishi harya k'arasa bakin k'ofa kafin ya juyo
yana kallonta tare da d'aga mata gira d'aya ya
kuma kashe mata ido sannan ya fita."
"Manosh yana fita yaga lubna akofar
d'akin,makzewa yayi yace ah *sis lub* yaushe
kikazo?"
"Murmushi tayi tace awa d'aya da suka
wuce."
"Manosh ya sosa gashin kansan sannan yace
bisimillah tana ciki sannan ya wuce da sauri
ita kuwa tanata binsa da kallo tana dariya ta
shige d'akin."
"Shuru aunty tayi tana kallon lubna"
"Lubna kuwa taje kusa da ita ta zauna tana
tace uhumm abun dai ba sauk'i sam."
"Aunty taja kunnenta tace tokema meya
kawoki a irin wannan lokacin?"
"Lubna tace ganin k'ok'op"
"To ai kingani koh?"
"Lubna tace sosaima kuwa"
"Aunty tayi dariya tace wayyo Allah, luv yayi
arayuwa wlh tare da rungume lubna daga
zaune."
"Lubna tace sosaima kuwa luv yayi
kam,amma kuma kudai bansan me kuka
aikataba dan babu aure a tsakaninku tunda
4month kenan bakwa tare, kuma ance idan
mata da miji basuyi tarayyaba har sawon
4month tofa babu aure se'an sake."
"Aunty ta gyara zama tace Allah malama
lubna?"
"Lubna tace sosaima kuwa,kuma gashi ku
bayan kiss ma harda runguman juna,dan
haka dole idan malamai sunzo maida aurenku
to zan gayamusu harda abunda nagani domin
suyi muku sharhi akai."
"Hhhhhhhhhh!"
"Aunty tayi dariya,tace to malama lubna babu
wani aure daza'a sake atsakanina da peach
domin kuwa aurenmu yananan babu abinda
ya sameshi."
"Shi kuwa kiss da duk wani abu da kika gani
munyi sharhinsa shine d'unbin lada da muka
samu, sannan wannan idon naki maison
ganin k'ok'op wataran seya makance."馃槣
"Hhhhhh! Sukasa dariya dukkansu daidai nan
kuma dictor suka shigo dasu manosh."
*.......*
"Bayan sati d'aya dayiwa aunty dashe k'odan
'yar'uwarta lubna kenan yanzu.
"Cikin ikon Allah anyi aikin cikin nasara
sedai muce Alhamdulillah." Domin aiki yayi
kyau kuma dukkanninsu suna cikin k'oshin
lfy,ga kulawa na musamman da suke samu
daga gun mazajensu da kuma iyayensu kai
harma da doctors d'in."
"Manosh ne zaune da apple nashi tana
kishingid'e ajikinsa yana bata tea baki"
"Yace Allah yabaku lfy apple,nima insamu in
sauke nauyin daya dad'e akaina."
"Murmushi tayi tace ameen peach d'ina wlh
har tausayi kake bani,wata kusa hud'u bama
tare gashi kuma yanzu an k'ara mana wasu
watannin. Ina tausaya maka peach amma idan
kana ganin zaka takura to wlh na amince
maka daka k'ara aure domin ka samu biyan
buk'atanka dan nasan ku maza bakwa iya
jurewa kamar mu mata.....
"Manosh yace haba apple banaso kina sa irin
wannan tunanin aranki pls,nasan cewa
maganarki gaskyane bakowani namijibane zai
iya jurewa,wasu sekiga sun fad'a neman
matan banza wasu kuma auren suke k'arawa
saboda gujewa sab'on Allah, amma
Alhamdulillah kuyita tayamu da addu'a Allah
ya karemu daga sharrin shaid'an domin yana
tasiri akan kowa sedai wanda Allah ya kare."
"Dad'i sosai taji har cikin ranta,tace insha
Allah sweetheartnah."
"Yace amma dagaske zaki yarda in k'ara
aure?" Tace ina k'aunarka matuk'ar k'auna
peach,sannan kishi halittace daga jikin ko
wace mace sedai nawata yafi nawata. Dan
haka daka fad'a halin neman matan banzan
awaje wlh gara ka k'ara aure yafimin,cikakki
yar k'auna da mata zata nunawa miji kenan
shine ta cetoshi daga dukkan wani hanyan
sab'on Allah." Wannan shine k'aunar da nake
maka,sam bana so kaucewa hanya "Ya mijina"
koda kuwa wani irin hali zan shiga indai
zaka kasance cikin farin ciki to nikam
Alhamdulillah."
Allahu akbar! 'Yan'uwana anya akwai sauran
mata irin aunty kuwa.?
"Manosh ya rasa mai zaicewa aunty domin taji
dad'i kamar yadda yakeji ayanzu."
"Kanta ya dafa yace yah Allah kasakawa
matata maryam da gidan aljanna,aljanna na
firdaus,ya Allah kabawa mazajen baya
dabasuyi aureba mata nagari kamar matata
maryam masu ilimin addini musulunci
ameen."
'Ya'uwana mata gu koma ga Allah,mu
rungumi aurenmu da hannu bibbiyu da
gaskya da amana,koda mijinki yana cutar
dake karki fasa yimishi biyayya,domin idan
kina kina masa komai dan Allah,shi kuwa
yana k'untata miki,tofa kisani shi Allah yana
farinciki dake. Allahu akbar,nasan babu
wacce bazataso ace Allah yana farin ciki da
itaba,indai Allah zaiyi farin ciki dani,tofa
koda yanka namana mijina yakeyi bazan
damuba."
"Mukoma islamiyya musamo ilimi mai albarka
mai amfani,muzamanto masuyiwa mazajenmu
biyayya da addu'a maikyau koda ko sun
zalincemune,mucire son duniya
aranmu,mudena fifita duniya sama da
lahira,domin ita duniya aronta aka bamu bata
da tabbas kokad'an,amma lahira fa...?"
**********
"Watansu aunty uku da sati biyu a india aka
sallamesu domin sun samu lfy sosai."
"Kasuwa suka shiga sukaita sayayya tare
dasake k'arewa garin india kallo.
"Ahankali suka gama duk wata
shirinsu,manosh yace apple waime zakiyi da
wannan robobinne?"
"Peach zankaiwa almajiran unguwanmu
tsarabane domin dewa daga cikinsu basu da
roban bara, kuma naga suna da sauk'i ne
robobin shiyasa na saya."
"Eyyah my apple,Allah yabiyaki da gidan
aljanna"
"Tare dakai sweetheart"
"Mama da baba ma sunyi kyau
sosai,sannan,sunyiwa umma wato mahaifiyar
yah ibrahim tsaraba na musamman domin yah
ibrahim yabasu kud'i.
"Hakama kuma manosh,kud'i sosai yabasu
har baba yana k'in karb'a."
"Da kwana biyu su aunty sukabar k'asar india
zuwa gida nigeri."
"International airpot na abuja suka
sauka,bayan wasu awanni kuma suka sake
hawa wani jirgin zuwa yola."
"Dama gidan manosh tunda ya tafi yabar koma
na gyaran gidan agun aminansa,dan haka
komai tsab yake an gyara sosai,hakama ya
ibrahim an sharemusu ko ina tas isowarsu
kawai ake jira."
"6:10pm jirginsu manosh ya sauka a yola,inda
aminansa suke jiran isowarsu wanda har da
abdallah sukaje tarosu a airpot."
"koda abdallah yaga iyayensa murna ya
dingayi babu sassauci yaje da gudu ya
rungume aunty yana cewa " sannuku da
dawowa baban mummy,mahaifin maryam
yace sannu abdallah ina alfiya?"
"Tana gida tana kuka waiseta biyomu"
abdallah ya saki aunty ya rungume manosh
sannan yaje gun mama se kuma yah ibrahim
dukya bisu da oyoyo." Bayan su marwan sun
gaisa da iyayen maryam ne se kuma aka gaisa
bakid'aya sannan aka wuce gidan dad d'in
manosh dan acan aka musu abinci na
musamman.
"Anci ansha anyi hira sosai inda maman
maryam take gun mum d'in manosh da hajiya
khadija mun d'in marwan da kuma umman
yah ibrahim se hajiya iya.
"An had'u anata hira, su dad ma suna can
nasu gefen,hakama su manosh suna can
gefensa,inda su aunty kuma suna had'e
dukkansu ad'akin miher su rash se murna
akeyi aunty ta dawo,su samira amina da
zahida anata shewa abun sha'awa nima
sadnas ba'a barni abaya...
"Kusan 9:00pm su manosh suka maidasu
mama girei"
"Bayan sun dawone aka maida yah ibrahim
dasu umma,dad d'in marwan kuwa ya d'ibi
su hajiya iya da matarsa.
"Daga k'arshe aminaima kowannesu ya d'auki
matarsa cike da tsarabobinsu kowa yawuce
gidansa cike da farin ciki aranshi."
"Manosh da aunty da yaransu sune suke
hon,cikin hanzari maigadi yabud'e gate tare
da nuna farincikinsa na dawowarsu."
"Ya k'arasa suka gaisa sannan yayi saurin
bud'e musu kofa tare da shigar musu da
kayansu ciki.
"Abdallah da alfiya se murna suke sun dawo
gidansu."
"Har kusan 11:00pm kafin sukai bacci,manosh
ne yakaisu zuwa d'akunansu tare da musu
addu'a sannan yazo gun aunty. Cak ya
d'auketa se toilet,dariya aunty takeyi tana
cewa "haba peach saukeni nifa basu alfiya
bane."
"Injiwa?" Ai baki da maraba dasu,kinsan fa
akwai nauyi mai tarin yawa daya dad'e a
kafad'una "hakanne yasa nace zan miki
wanka ta yadda bazaki b'ata mana lokaciba."
"Hhhh to pls dai atausayamin peach"
"Karki damu aunt, zan lallab'aki kamar
sabuwar jaririya" peck mai zafi ta manna
mishi akan idonsa tace "i luv u peach"
"I luv u more apple..."
"Haka sukai wankansu sannan suka fito yana
rik'e da ita sukai shirin bacci ko kuma ince
shirin......
*Alhamdulillah*