Skip to main content

Darasin Rayuwa - Hausa Novels

🔥 *DARASIN RAYUWA* 🔥

 

Chapter 1

 

Amina, Amina, dattijuwar mata keta faman kwala kira, can saiga ga ta ta fito daga daki, tana mika alamar daga barci ta tashi, kai dan Allah Mama, wana irin kira ne haka, bayan kinsan nace miki, kaina ke ciwo zanje na kwanta, to ai Amina tunda kika ga na taso ki ai kinsan abun zaki min ko, ta fada da alamar ranta ya dan baci, karasowa tayi bakin katuwar bishiyar mangwaro dake tsakiyar tsakar gidan nasu inda Maman ke zaune tana tsinkar zogale, kujera ta janyo ta zauna, to gani, Mama mezan miki, kinga wllh har nazo zan dora sanwa, na duba zan dauki ashana, sai naga ta kare, kuma naje inda muke ajiyewa, ashe ta kare, bamu sani ba, dan Allah tashi kije nan shago ki siyo min rana tayi, kai Mama yanzu dan Allah kamar ni zan wani je siyan ashana a shago, ai sai ki saka a raina ni, haba yar Maman ta, bafa ma haka dake, kin manta alkawain dana miki, indai kina so na cika tofa sai kinje min aiken nan, haushi ne ya kama ni ganin wannan katuwar budurwar ake wa wannan shan kan, kamar irin tabararrun yaran nan yan shekara biyar, tashi tayi, tana mikewa na kuma kare mata kallo cikakkiyar budurwa ce wacce a kalla zatai shekara sha takwas zuwa sha tara, ba gajera bace dan kai tsaye zaka iya kiran ta da doguwa, bata da jiki kuma bazaka kira ta da ramammiya ba, tana da jikin ta dai dai gwargwado, fara ce irin fararan nan tatas, kai in takaita maka dai idan ka ganta sai dai kace masha Allah dan duk inda mai kyau ta kai to takai nan, shiyasa samari ke mata tururuwa danma baban ta mutum ne mai tsatstsauran ra'ayi da akida, yace shi bazai bar yarsa ta fara kula samari ba har sai ta gama karatun ta, amma fa ta bangaren Amina hakan ba haka bane dan irin samarin da take dasu a boye Allah yai yawa dasu, ( kalubale gare mu iyaye), daki ta shige can ta fito sanye da zurmemen hijabi har kasa, wannan dokar Abban tane bai yarda ta fita koda nan da zaure ba ba tare da hijabi ba, kuma a gidan sa ko biki ake ba'a saka mayafi, amma fa a bangaren Amina har rolling tana yi da dan kankanin mayafi ta fita ba tare da sanin mahaifin ta ba, kawo kudin, ta fada lokacin da take kokarin zura takalmi a kafar ta, gashi ki siyo park kawai a ajiye, kafin Abban ki ya siyo amma dan Allah Amina kada ki dade, nasan halin ki kisa Abban ki yazo yana min tashin hankalin nan nasa, karba tayi kawai ta fice daga gidan, Maman ta girgiza kai, Allah ka shirya min wannan yarinya, daga haka ta mike ta wuce cikin kitchen.

  Bayan ta fita ta hadu da kawar ta, Sadiya, yar gari kwana da yawa, tun rannan nake cigiyar ki, kinsan Marwan ya kawo miki sakon ki, ke dalla bari, ai ni rannan ma bala'i ya janyo min a gida, shine kika jini shiru, ina randa ya dauko ni daga gidan ku, ba sai da nace ya barni na tafi ba, amma shima kafirin bawan nan yaki, da wani kan sa kamar na sadaka, suka kwashe da dariya suka tafa, to wllh ina fada miki yana sauke ni bayan layin nan ashe akan idon munafukan unguwar nan, suka kwashe suka fadawa Abba kuma kinsan halin sa, shine fa harda saka min takunkumi, yanzu ma da kika ganni Mama ce ta aike ni, can shagon tace nayi sauri kar ya dawo, Allah ya kyauta, me kika zoyi a layin mu, wllh, Umma ce ta aike ni gidan wata kawar ta a can kasan layin ku, da naso ma na shigo, amma ganin kamar Mama bata so ina zuwa wajen ki yasa na fasa, ke bafa haka bane, muna fukan unguwar nan ne suka sami Abba suka hada masa karya da gaskiya, shine yace wai ya raba mu, amma kinsan ai Mama tana son duk abinda nake so, kinga ma bari nayi sauri na kai mata aiken nan karta fara mita, to Allah dai ya kyauta.

Darasin Rayuwa Part (2)
Aisha Muhammad

Yanzu ya zanyi da mutumin ki, wllh ya fitine ni wai shi ko bacci baya yi, wai na kawo shi gidan ku, baki ta rike rufa min asiri na mutu maza su kaini, ai sai yasa Abba ya kashe ni, to yanzu ya zanyi da shi, kinga kawai ki bashi hakuri, ai an kusa komawa hutu, zamu dinga haduwa duk sanda yake so, to amma ya za'ayi da sakon ki, yanzu da nasan zamu hadu dana taho miki da ita, karki damu, gobe war haka kizo gida ki kawo min Abba baya nan, to Allah ya kaimu, daga haka sukai sallama kowa ya wuce inda zashi, washe gari kuwa bayan azahar suna zaune tare da Mama tana mata tsifar kanta, masha Allah tana da gashi masha Allah gashi ne da ita har gadon baya, gashi da alama zaiyi santsi, gashi baki kirin, Sadiya ce tayi sallama ta shigo oyoyo ta tashi ta tare ta, karasowa tayi ta tsugunna ta gaida Mama, ta amsa tana tambayar ta wajen Maman ta, daga haka Amina taja ta suka shige dakin ta, bayan sun zauna ta fita ta kawo kawo mata ruwa, bayan ta dawo ta ajiye mata sannan itama ta hawo kan katifar ta inda Sadiyan ke zaune, ke sai wani ja min aji kike ki bani mana, jakar ta ta zuge ta dauko wata leda ta mika mata, hannun tasa ta zaro kwalin dake ciki, waya ce kirar kanfanin iphone, sai da ta saki wani karamin ihu, Sadiya tayi saurin toshe mata baki ke dalla zaki tona mana asiri, kai gaskiya kawata nayi babban kamu, nifa ba wani son sa nake ba amma da alama za'aje dashi, budewa sukayi ta tashi ta dauko tsohuwar wayar ta ta bude da niyyar cire sim card din, ke dalla me zakiyi layi zan saka mana, dalla tsaya jakar ta ta bude ta dakko mata sabon layin airtel ta mika mata, yanzu idan kika mayar da main layin ki cikin ta kenan ta koma ko kina gida da ita zakiyi amfani, kuma kinsan ko Mama bazata goya miki baya akan wannan ba, haka ne fa, shegiya kanki fa yana ja, sabon layin ta saka Sadiya ta karba ta kunna masha Allah, Allah ya sanya alkhairi a kashe lafiya, bari kika ga na tafi ki kira mutumin ki, akwai number sa a kan layin, na miki full charge, sai anjima kada Abba ya dawo ya same ni, to bari na raka ki, aa nagode zauna kiji dadin sabuwar waya, aa to bari na raka ki ko bakin get ne, haka suka fito ta leka dakin Mama ta mata sallama sannan ta raka ta ta dawo, tana dawo wa ta wuce ta koma daki aka cigaba da dannne danne a sabuwar waya, har Allah Allah take a Monday tazo su koma school itama ta shiga tana budawa.

     Yau ta kama Monday, kuma yau ne su Amina zasuyi resuming school, da wuri ta shirya dan ba karamin dokin komawa makarantar take ba ko ta samu kafar yawo, karfe takwas saura ta gama shirin ta duk da ba'a kafe timetable ba, bata san karfe nawa suke da lecture ba, amma ita dai ta kagu ta ganta a makaranta, tayi kyau abinta cikin abaya ruwan hanta wacce ta boye mayafin abayar a cikin jaka, ta dauki zubbulelen hijabin ta ta dora akan kwalliyar ta, data kalli kan ta a mudubi sai da tai dariya yanzu dan Allah ace kamar ni na shiga school da wannan  abin ai sai a raina ni, ana cikin haka Sadiya ta kira ta ya yan mata kin shirya, na shirya yanzu zaki ganni, bani minti sha biyar, tana kashe wayar ta dauki jakar ta da takalmi tayi waje bayan ta jefa wayoyin ta a cikin jakar, kitchen ta wuce ta tsiyayo ruwan tea ta tsaya a kitchen din ta shanye dan ma tasan Mama baza ta taba barin ta fita bata karya ba da baza ta sha ba, da sallama ta shiga dakin Abba ta same shi tare da Mama suna zaune suna karyawa, dan sun saba indai yana gida a tare suke cin abinci, shima cikin shirin fita yake, take ta fara addu'a Allah yasa kar yace ta tsaya su tafi ya ajiye ta, haka ta karasa kusa dasu ta zauna, sannan ta shiga gaida su.

Darasin Rayuwa Part (3)
Aisha Muhammad

Suka amsa mata da sakewa, dan ba karamin so suke mata ba kawai dai shi Abba yana dannewa ne sabida fitina irin ta yayan zamani, musamman ma ita da duk kokarin da yake akan ta amma lamarin Aminan sai godiya, uwata badai har kinyi shirin makarantar ba, eh Abba na shirya, to haka zaki fita baki karya ba cewar Mama, yanzu na sha tea a kitchen, kinga badan munyi zamu hadu da Malam Idi ba ai da na tafi dake na sauke ki, babu komai Abba kada ka damu, to shikenan Mamana a kula kada naji kada na gani, kina jina ya fada yana rike da kunnen sa alamar gargadi, inaji Abba to Allah ya miki albarka, Ameen Abba, ya juya gefe ya dauko wallet dinsa ya ciro kudi naira dubu ya mika mata, ta amsa tana masa godiya, Allah ya bada sa'a kiyi abinda ya kaiki, insha Allah Abba, ta mike tana yiwa Mama sallama, itama addu'a ta mata, ta juya ta fice, tana fita ta kama hanyar gidan su Sadiya, a zaure suka hadu, banza kin shanya ni, uwar korafi ai dai gani ko, to muje muje ina a haka kike nufi zan tafi, cikin zauren ta kara shigewa harda tura kofa, ta cire hijabin jikin ta, ta mikawa Sadiya sannan ta ciro dan mayafin abayar ta nada shi akan ta ya kuwa zauna das, ta ninke hijabin sosai ta dannan shi a jaka, sannan suka fito, suna taku dai dai kai kace yayan wani kusan gomnati ne, duk da ita Amina Abban ta yana da rufin asirin sa daidai gwargwado babu abinda suka nema suka rasa ko gidan su ma mai kyau ne sannan yana da motar sa mai kyau ta hawa.

     Bayan sun shiga makaranta sun tarar da yan department din su da yawa, an zo ana ta faman raha, yau din dai dai dai ku ne a department din basu zo ba, kasancewar dogon strick da aka tafi, kowa na dokin zuwa makarantar, suna shiga department din, aka saka ihu, ana mata tafi, ita kuwa sai wani budawa take, tana taku dai dai, waje ta samu da suka zauna, tana bayan ta bibbi mutanen wajen sun gaisa, dan ko kadan bata da girman kai ko wulakanci, idan baka san ta bane, a ganin farko zaka iya mata kallon mai girman kai, sabida irin kirar da Allah ya mata, ta kyau, ga kuma iya kwalliya, da jan aji, nan da nan yawancin mazan dama wasu daga cikin matan wadan da suke good time da ita suka tashi suka koma wajen ta, aka cigaba da hira, dan gwana ce wajen kawo cafta.

   Haka suka gama hirarrakkin su, basu suka bar department din ba, sai da aka kira sallar azahar, nan da nan Amina ta mike, kunga ni dai nayi nan, Sadiya ma ta tashi, bari mu tafi kun san ustaziyar ta mu, ba daga nan ba, wajen kula da sallah, duk suka tuntsire da dariya, wani daga cikin su yace, Allah fili fir'auna a zuci, suka kwashe da dariya, har ta fara tafiya ta juyo ta kalle shi, Allah yasa ba uban wani nakewa sallar ba, daga haka ta juya tayi tafiyar ta, Sadiya ma tabi bayan ta, tana bata hakuri.

   Baki kawai ya saki yana bin inda tabi da kallo, sauran suka saka dariya, kai amma wllh yarinyar nan yar rainin sense ce, kalli fa yanda ta zage ni, amma ko a jikin ta, wllh koda nake jin labarin rashin mutuncin yarinyar nan, ban taba tunanin abun nata yakai haka ba, yanzu ta kalli kama ta ta zaga, yarinyar da nayi kanwa ta uku da ita, cab ai kadan ma ka gani, indai Meena ce, ai wllh bata ki ta ko da Malami ne ya mata ba dai dai ba, akan gaskiyar ta, ta zage shi ba, sai dai a kore ta a makarantar, cewar wata daga cikin matan, take wata kuma tayi caraf tace, kuma kinsan.

Darasin Rayuwa Part (4)
Aisha Muhammad

Kuma kinsan korar Meena a makarantar nan ba karamin abu bane, dan kinsan VC dan Uwan su ne wasu kuma suna cewa dan garin su ne, kuma ma kinsan ana rade radin, son ta yake.

  Dalla Malamai ku mana shiru, mu ina ruwan mu da duk wannan, cewar wanda aka zaga, dariya suka kara saka masa, dan sun san duk haushi ne na yanda aka dizga shi, kuma dama shine bai san Amina ba, bata daukar raini ko kadan, sannan duk rashin mutuncin da take shukawa na kula kulan samari, zuwa ofisoshin Malamai, yawo da kana nan mayafai, duk an santa akan irin wadan nan abubuwan, amma in ka cire wannan duk duk wanda ya mata wata shaida ta iskanci, rashin kamun kai, tofa yayi karya, kuma duk abinda take, lokacin sallah yayi zata bari taje tayi ta akan lokacin ta, an mata wannan shaidar.

  Haka suka tashi a wajen, ana ta cecekuce da masu bin bayan Amina da kuma masu goyawa abokin fadan nata baya, daga nan wasu sukai masallaci wasu kuma cafeteria, wasu kuma ma gida suka nufa, dan dama yau din sun san ba lallai su samu lecture ba, kawai dai dokin makarantar ne yasa suka zo.

   A bangaren su Amina ma daga masallaci, cafeteria suka nufa, dan bata son tafiya gida yanzu, sunyi da Marwan zai zo su hadu, basu dade ba kuwa ya kira ta, yace ya iso, cafeteria tace yazo ya same su, suma fita sukai, suna fita kuwa suka hango motar sa, jira sukai ya karaso, bayan ya fito suka samu waje suka zauna, bayan sun gaisa da Sadiya, ta tashi ta basu waje, nan suka shiga hira, duk yawancin hirar tasu, korafi ne da yake mata, na hana shi zuwa gidan su da takeyi, hakuri ta bashi, tace yayi hakuri ya bari sai ta kammala makaranta, kwana nawa ne, abinda yanzu duka duka bai fi wata biyu ba, badan ma wannan yajin aikin ba, ai da yanzu mun kammala, haka dai tayi ta masa dadin baki har ta samu ya hakura.

    Sai bayan sunje sunyi sallar la'asar sun dawo, yace to zai tafi, idan sun gama abinda suke to su zo kawai ya sauke su a gida, fur taki dan bata son abinda zai janyo mata matsala, kamar kwana ki da aka ganta a motar sa, aka je aka fadawa Abban ta, sai da taga ransa ya baci, sannan tace to suje amma sai dai ya sauke su, a hanya kar ya kai su unguwar su, akan haka suka tafi, suna tafe suna taba hira, har yazo inda zai sauke su, Sadiya ce ta fara fita dan ta barsu suyi sallama, sallama sukai, sannan ya dauko wata yar karamar leda, ya mika mata, taso taki karba, sai da taga ransa ya baci, sannan tasa hannun ta karba, ta masa godiya, da kansa ya fito ya bude masa kofar motar ta fito, sannan ya saka hannu a aljihu ya dauko, sabbin yan dari bibbiyu ya mikawa Sadiya, dan yasan ko ya bawa Aminan baza ta karba ba, dan Amina akwai rashin jin kula kulan samari, amma ko kadan bata da kwadayin abin hannun su, sabida Baban ta akwai tsare gida, babu abinda iyalin sa suka nema suka rasa, dan haka babu abinda wani zai bata da zai burge ta wanda mahaifin ta zai gagara mata shi.

  Godiya Sadiya ta masa, sannan ya tare musu Nafef ya masa kwatancen inda zai kaisu, ya biya kudin, duk da su sun so ya barsu su karasa da kafa tunda babu wani nisa, amma fur yaki, wai baya so sarauniyar sa na tafe maza na kalle masa ita, haka suka shiga shi kuma yaja motar sa.

Darasin Rayuwa Part (5)
Aisha Muhammad

ya bar wajen.
  Kwanci tashi babu wuya a wajen Allah, yau gashi har su Amina suna gab da kammala jarabawar su ta fita, sai shirye shirye suke, ranar nan sun fito daga jarabawa, suna zaune suna duba handout din daya jarabawar da zasuyi anjima, aka kira Sadiya a waya, dagawa tayi, tayi kasa da muryar ta sosai tana wayar, ta dauki wajen awa guda tana wayar, sai bayan ta gama, ta kalli Amina wacce ta cika tayi fam, haba kawas menene kuma abun fishi, tsaki taja, dalla rabu dani, mutum sai shegen fi'ili, idan ba munafurci ba mene na ana magana da kai lafiya, amma ana kiran ka a waya, zaka hau wani kus kus baka son aji me kake fada kamar wani abun munafurci, dafa ta tayi tana dariya, yi hakuri aminiya wllh ba haka bane, wani sabon gaye nayi, kuma wllh da alama babban yaro ne, shiyasa dole sai nima ina iya takuna, ina abu irin na manyan yara, tsaki ta kuma ja, ke dai kika sani, gani Amina yau yan jarabar ne akan ta, bata da niyyar sakkowa yasa ta tuno tana fa da lagon ta, la Meena ai na manta ban baki labari ba, mutumin nan fa, dan uwan AA sa'ad ne, nan da nan kuwa ta jiyo, wane AA Sa'ad din, wanda dai kika sani, producer AA Sa'ad, kice Allah, wllh kuwa dan uwa na jiki sosai ma, dan cousin dinsa ne, kuma a gidan su ma aka rike shi, da sauri ta rungume Sadiya, kai Allah ya mika albarka kawata, ki jita sai kace wata uwa, dalla ni sake ni, ta fada tana ture ta, ai wllh baki isa ba, kema kinsan ko min wulakancin da zaki min bazai dame ni ba.

Dariya tayi, dama tasan Amina da mugun son film da yan film, duk da tasan ko zata mutu mahaifin ta ba zai taba bari tayi film ba, amma da tasan wanda zai mata hanya ta shiga da babu abinda zai hana ta shiga, sai dai idan Abban ta ya kashe ta idan ya samu labari, amma dai zuwa lokacin ko film daya ne ta samu tayi.
Da farinciki ranar ta baro makaranta, koda zasu rabu da Sadiya sai ta bata sakon idan sunyi waya tace aminiyar ta tana gaishe shi, dariya kawai Sadiyan tayi, dan ita har mamaki Amina take bata yanda ta kwallafa rai akan abinda tasan bazai yuwuba.

A yau ne suka kammala jarabawar su ta fita, ko wannen su yana cike da farin ciki, zasuyi graduation party gobe, a wani holl da suka hada kudi suka kama, duk da Amina sanda ta bada kudin ta bayar ne kawai amma a dar dar take dan tasan ma babu yanda za'ai Abban ta ya barta taje, dan za'a kai dare, kawai ta biya ne tana kan neman mafita.

Ranar ba ita ta koma gida ba sai ana kiran sallar magriba, da sanda ta shiga gidan duk da tana kyautata zaton Abba yana masallaci, sai da ta fara lekawa ta hango Mama a zaune akan kujera yar tsugunno tana alwala, sannan hankalin ta ya kwanta tasan Abba ya tafi masallaci, da sallama ta karasa shiga cikin gidan, Mama dake alwala ta dago ta kalle ta tana amsa sallamar, Mama sannu da gida, yauwa sannu a gantala, sunan da Maman ke kiranta mafi yawancin lokuta, idan ta tafi wani waje ta dade.

Darasin Rayuwa Part (6)
Aisha Muhammad

Fuska ta tabe kamar wata karamar yarinya, kai dan Allah Mama daga shigowa ta ko sannu baki min ba, amma kin fara min fada, bayan kinsan yau ranar farinciki na ce, ko ki bari ki fara min murna ma, amma baki ba kin fara min fada, baki kawai Maman ta saki tana kallon ta, to sannu uwa ta, da kika hauni da irin wannan fadan, duka na zaki yi, baki ta turo, ni yaushe nace zan dake ki, Allah ya baki hakuri, baki kawai Maman ta tabe, Allah ya shirye ki, daga haka ta juya ta cigaba da alwalar ta.

Daki ta wuce ta cire kayan jikin ta, sannan ta fito daure da towel ta doro hijabi a kai, ta fito ta debi ruwa ta wuce bayi, wanka tayi bayan ta fito ta tsaya ta daura alwala sannan ta wuce daki.

Har ta gama duk abinda take a dakin ta fito ta nufi falon Mama, bata ji motsin shigowar Abba ba, bayan ta shiga falon ta tarar da Maman ta na zaune tana kallo, da sallama ta shiga, daga amsuwa Maman bata ko dago ido ta kalle ta ba, hakan ya tabbatar mata da fushi Maman take da ita, duk da tasan fushin Maman akan ta baya tsaho dan bata iya jure fushi da diyar tata, amma duk da sanin hakan itama baza ta iya samun sukuni ba, alhalin Maman tata tana fushi da ita, wajen ta nufa tana zuwa ta fada jikin ta, kawai ta fashe da kukan shagwaba, ture ta Maman ta fara, ke mene haka, ba ke bace kike fushi dani, to wllh yau bazan daga ki ba, sai kince kin yafe min, bata san sanda dariya ta kufce mata ba, ita kanta tasan yarinyar tata yar dirama ce, duk irin laifin da tayi maka tasan yanda zata saka ka dole ka manta ka kula ta, bata bar ta ba sai da ta tabbatar ta manta da wani zancen fushi.

Sannan tace wai Abba bai dawo bane, naji banji shigowar sa ba, wllh Abban ki dazun nan bayan la'asar yau ya dawo da wuri, wai Kawun ki Bala ne bashi da lafiya, shine fa ya tafi, Allah sarki Kawu Bala, me ya same shi, wllh ban sani ba, dayake tinda ya tafi nake kiran shi amma ban same shi ba, kinsan garin nan babu network, haka ne Allah ya dawo da shi lafiya, shi kuma Kawun Allah ya bashi lafiya, Ameen.

Tashi tayi taje ta zubo abinci, tare ta hado musu da Mama dan tasan bai kai ace taci ba, haka suka zauna suna ci suna hira, wayar Mama tayi ringing, Amina ce ta tashi ta dauko mata a caji, Mama Abba ne fa, da sauri ta mika mata wayar, ta daga, bayan sun gaisa ta tambaya shi ya mai jikin, yace da sauki, amma gaskiya yana jin jiki, sai dai ku taya shi da addu'a, to Allah ya bashi lafiya, ameen, shiyasa nace bari na fada muku, gaskiya, gobe ma bana tunanin zan dawo, zan dan tsaya naga abinda ya kamata ayi, to Abban Amina, mai zai hana a taho da shi nan a kaishi asibiti, hmm kema kinsan bazasu yarda ba, to Allah ya bashi lafiya, ameen, sai anjima bana jin ki sosai kinsan network din garin nan, nima nayi ta kiran ka ai bata shiga, ka masa sannu, Allah ya sauwake, Ameen, Amina na gaishe ka, ina amsawa, gobe idan na kira ma gaisa yanzu network din babu kyau, daga haka suka kashe wayar.

Mama ya jikin nashi, da sauki dai amma Abban ki yace jikin nashi babu dadi, wllh shiyasa ma yace, bazai dawo gobe ba, sai ya tsaya yaga ya jikin nasa yayi tukunna, to Allah ya bashi lafiya, Ameen, yau kuma an kammala makaranta, abinda zan fada miki Amina shine, ki nutsu ki san abinda kikeyi, a yanzu abinda ya rage miki shine ki fito da miji kuma mu aurar dake.

Darasin Rayuwa Part (7)
Aisha Muhammad

 Muma mu sauke nauyin da Allah ya dora mana akan ki, nasan ko mahaifin ki idan Allah ya dawo dashi lafiya, abinda zai fada miki shine ki fito da miji, shiyasa na fara sanar dake, idan ma babu to sai kiyi hanzarin zabar shi a cikin tarin samarin da kike kulawa, dan babu abinda bamu sani ba, muna da labarin duk abinda kikeyi.

Shiru tayi gaba daya jikin ta yayi sanyi, amma duk da haka ko kadan zuciyar ta bata rissina ba akan kudirin ta, amma zata kwantar da kai ta samu ta samu abinda take so, insha Allah Mama zan duba, kuma insha Allah daga yanzu baza ku kara kuka da ni ba, Allah yasa, Allah kuma ya miki albarka, Ameen Mama na nagode, daga nan suka shiga hirar duniya, sai da aka kira isha'i sannan suka tashi suka tafi gabatar da sallah.

Bayan sun idar sun dawo, Amina ta zauna tayi zugum, duk hirar da Mama ta ke mata bata wani maida hankalin ta akai, sai da Mama ta gaji tace, Amina lafiya kuwa, tayi figigit ta kalle ta, lafiya Mama me kika gani, Amina nifa na haife ki, nasan idan kina cikin walwala da kuma akasin haka, shiru tayi bata ce komai ba, meya faru, idan baki fadan damuwar ki ba kina da wanda zaki fadawa, kai ta girgiza, to ina sauraren ki, wllh Mama ina tsoron baza ki amince bane, fada min mene ne, idan na amincewa ne ai zan amince, dama a makaranta ne aka shirya walimar kammala makaranta, za'ayi gobe a makarantar, shine nake tunanin bazaki barni naje ba, akan wannan ne har kike damuwa, to ai ba niba ko Abban ki, idan yana nan bana tunanin zai hana ki, zuwa murnar kammala makarantar ki, abu na rana daya kuma a cikin makaranta ai babu wata damuwa, halin ki ne kawai bana so, Amina kin tabbata a cikin makarantar ne, kai Mama wato ni makaryaciya ce ko, Allah a cikin makaranta ne, to Allah ya kaimu, goben idan munyi waya da Abban ki zan sanar masa, ince ko dai baza a kai dare ba, gaskiya za'a iya kaiwa magariba, dan kinga baza'a fara ba ma sai bayan la'asar, to Allah ya kaimu, amma gaskiya Amina kar ki wuce magaribar kinga zaki iya ja min matsala a wajen Abban ki, dan idan ma zan fada masa bazan ce za'a kai har magariba ba, dan kinsan bazai yarda ba, kinyi sa'a ma baya nan, tashi tayi ta rungume ta, na gode Mama na, Allah ya barmin ku, Ameen, Allah kuma ya shirya mana ke, dariya tayi to ameen, ni na rasa abinda nake yi da kullum ake magana akai na, hmmm Allah ya kyauta, tashi muje mu kwanta, kinga har goma saura, to Allah ya bamu alkhairi, Ameen, kowa ya tashi yayi dakin sa.

Tana shiga dakin ta, ta samu missed call din Marwan da yawa a wayar ta, kiran sa tayi, tana shiga kuwa kamar yana jira, ya katse ya kira ta, bayan sun gaisa yake sanar da ita zaiyi tafiya gobe da safe, tare da Daddyn sa dan haka yake bata hakurin bazai samu zuwa wajen partyn nasu ba, bata so haka ba sabida, ko babu komai Marwan akwai karewa mutum yawa, dan gaye ne na gaske ga kyau ga iya wanka, ga kuma uwa uba yayan banki, sun hadu da kuruciya, kuma idan da yana nan, bata da matsala, dan tasan shi zai kai su a mutunce, kuma ya dawo da su a dalleliyar mota, amma ya ta iya, ta samu Sadiya kuma su sake sabon lale, waya sukai mai tsaho, har saida yaji ta fara bacci bacci sannan ya kyale ta sukai sallama ya kashe wayar.

Darasin Rayuwa Part (8)
Aisha Muhammad

Kashe gari, da wuri Amina ta tashi, ta shiga taya Mama ayyukan gida, bayan sun kammala komai, suka zauna suka karya, sannan Amina ta tashi ta shirya tace da Mama zata je lalle nan bayan gidan su, daga nan kuma zata biya wankin kai, a dawo lafiya Maman ta mata tare da gargadin dadewa, idan kuma tayi abinda bata so to fa wllh zata hana ta zuwa wajen walimar, dariya tayi bama za'ai haka ba, Mama na, haka ta fita bayan Maman ta mata a dawo lafiya.

Tana fita ta kira Sadiya suka hadu suka wuce wani katon wajen gyaran jiki, anan akai musu lallen da kuma gyaran kai, Aminan ta biya, dan a jiya kudi sosai Marwan ya tura mata a account, wai gudummawar sa, gift din ta kuma sai ya dawo.

Sai bayan azahar aka kammala musu, suka fito suka hau nafef suka nufi gida, a hanya suka rabu, kowacce tayi gida, bayan sun tsara ana yin sallar la'asar zasu hadu, su tafi wajen makeup, dan karfe shida za'a fara, har dinkin da zasu saka Sadiya ce ta kai musu wajen telan ta, ya musu, yana wajen ta sai zasu tafi makeup zata taho musu dashi.

Da sallama ta shiga gida ta tarar da Mama ta idan da sallar azahar tana zaune akan sallayar tana cin abinci, bayan ta amsa, ta karaso inda Maman take, zubewa tayi a wajen, wash Allah, wllh na gaji, ai ke kika saka kanki, kawai dan walimar kammala makaranta ace wai sai anyi wani lalle dasu gyaran kai, haka fa akeyi Mama ku dan ba lokacin ku bane, Allah ya kyauta, ki tashi kiyi sallah kije ki zuba abinci ki ci, nayi sallah, abincin dai zanci, yanzu Mama ko kice lallen nawa yayi kyau, yayi kyau mana, gaskiya yarinyar nan ta samu sana'a, dariya tayi, wllh kuwa, daga ta nufi kitchen tana dariya a ranta, na yanda ta rainawa Maman hankali.

Sai da tayi sallar la'asar, sannan ta shiga ta kara yin wanka ta fito ta shirya cikin atamfar ta a cikin kayan sallar ta ta bara, dinkin doguwar riga, ta daura dan kwalin ta gwanin sha'awa tayi kyau masha Allah, da gyale ta fito a hannun ta, Mama ta daga ido ta kalle ta, ina zaki da wannan, kai Mama yau fa walimar kammala makarantar mu, kowa zaiyi kwalliya ta kece raini, kawai ni sai a ganni da wani zurmemen hijabi, ai sai a min dariya, Allah kawai tunda Allah yasa Abba baya nan kawai ki barni nima na fito kamar sauran yan mata, dariya Maman tayi, kin ganki, ni tunda nake da mahaifin ki, ban taba masa karyar wani abu ba, sai akan ki, gashi sai kiyi ta saka ni ina masa karairayi ma ba karya ba, ni dai Allah ya kawo miki miji na gari mu aurar da ke mu huta, baki ta tabe, wai ke Mama daga anyi magana sai ki fara wani zancen aure aure, naga du dudu guda nawa nake, ni wllh har yanzu ban isa wani aure ba, kawai ku bari, Allah ya kawo min aiki, ko kuma abinyi, ke har wane abinyi zaki iya keda bakya son sana'a, dariya tayi akwai kuwa, kedai kawai ki taya ni da addu'a Allah ya cika min burina, baki ta tabe to ameen, yauwa ko ke fa, amma daga anyi magana sai zancen wani aure, Allah dai ya shirya ki, amma ai duk darajar diya mace gidan mijin ta, kinga nidai Mama idan na biye take wllh makara zanyi, sai na dawo, Allah ya tsare kar ayi dare.

Darasin Rayuwa Part (9)
Aisha Muhammad

Tana fita kiran Sadiya na shigowa wayar ta, tana dauka tace gani fa na fito, nima na fito, mu hadu a bakin titi, tana zuwa titin kuwa ta hango Sadiya tana tsaye tana jiran ta, karasawa tayi, kinyi kyaufa baby kamar ma kar a miki kwalliyar, basaja ne, kinsan Mama ta dauka a haka zani wajen, kinsan fa ce mata nayi walima ce, suka tuntsire da dariya, wllh baki da kyau, Meena, hmmm iyayen namu ne sai da haka, su basa gane an wuce irin wannan lokacin na takurawa yara ba, Allah dai ya shirye ki, ameen tace tana tare musu nafef, shagon kwalliyar suka kwatanta masa, sukai ciniki, sannan suka shiga yaja.

Bayan an gama musu kwalli, Sadiya ta kira wani saurayin ta dama sunyi shi zai kai su wajen, basu dauki wani lokaci ba kuwa ya iso, waya ya mata suka fito, mota ce dashi ba wata mai kyau ba shiyasa ma bata wani son kula shi sosai, sai dai idan tana da bukata kamar dai yanzu, amma shi kuma baya zuciya har so yake yaji ta kira shi tace tana bukatar wani abu, sabida Allah ya jarabce shi da mugun son Sadiya sai dai ita kuma ko kadan bai mata ba, baya cikin irin tsarin mazan da take so.

Bayan ya kaisu wajen Amina ta fita ta bar ta a motar ko zasu dan samu su zanta, ai tana fitowa, itama Sadiyan ta biyo bayan ta, rada ta mata a kunne, haba Sadiya meye hakan, wulanci fa babu kyau, kiga yanda mutumin nan yake nan nan da ke amma sai faman wulakanci kike masa bayan mutumin nan yana miki amfani, dan Allah ki tsaya kuyi yar sallama, mana, haka dai ta samu taja ra'ayin ta ta tsaya, ita kuma ta koma can jikin wata mota ta tsaya tana jiran ta.

Basu wani dade ba sukai sallama ya tafi, inda Aminan ke tsaya ta karasa ta same ta, ke wllh mutumin nan dan rainin hankali ne, kiga fa yasan inda ya kawo ni, amma babu wata kyauta balle wani dan gift, a haka kuma kike so na sakar masa fuska, dan Allah kiga Marwan ba zai samu zuwa bama, amma nawa ya tura miki a account, kuma harda alkawarin gift idan ya dawo, ai ke dai wllh kin dace, dan ma kin tsaya shirme, ai idan nice ke, wllh gabatar da shi zanyi a wajen Abba musamman yanzu da kika kammala karatun ki, gayen komai ya hada, gashi babu rowa, yanzu dan Allah ki kalli, wannan Hafiz din dana hadu dashi, gashi dai da alama suna da kudin, sai dai wllh hannun jarirai ne dashi, ko kadan bashi da kyauta, dariya ta sa ke Sadiya wllh baki da kirki, abinda du dudu yaushe kuka hadu, ki bari ki gani mana, hmm ke dai kawai ki bari, wllh badan ke ba, ni da tuni ma na shata masa layi, kinga wajen nan fa da alama ya fara cika, mu samu muma mu shiga, daga haka suka yi hanyar shiga cikin hall din.

Sanda suka shiga wuri ya cika, ana ta faman kade kade, waje suka samu suka zauna, bayan sun dan gaggaisa da na kusa dasu, ansha rawa, anyi liki, daga baya kuma aka fara gabatar da abinci, anci an sha, masha Allah taro yayi taro, sai dai addu'ar Allah ya kawo abinyi, ai Amina bata ankara ba, sai da aka tashi taro, taga karfe goma da rabi, hankalin ta ba karamin tashi yayi ba, ga missed call nan daga Mama babu adadi, innalillahi kawai ta fara mai maitawa, duk da ba wai tana wani tsoron Maman bane, amma ta aikata abinda bata taba aikatawa ba.

Darasin Rayuwa Part (10)
Aisha Muhammad

Sadiya na shiga uku, karfe goma da rabi fa, wllh gaskiya mun shagala da yawa, sai muzo mu tafi ko, naga baki wani damu ba, kinsan kuwa me nace miki, fast ten fa, eh mana, to ya kike so nayi, ni damuwa ta ma, Allah yasa mu samu abin hawa, ita Amina haushi ma Sadiya ta bata, da irin halin ko in kula din da ta nuna, dan tasan ita a gidan su hakan ba komai bane,haka ta tashi jiki a sanyaye tayi hanyar fita, babu wanda ta tsaya yiwa sallama.

Ai kuwa suna fita hankalin Amina ya kara tashi, dan kafa har ta fara daukewa a wajen, sai tsurarun motocin dake wucewa, babu ma alamar wani abu wai shi nafef, innalillahi Amina ta fara kira, kamar zata fashe da kuka, Sadiya kuwa dariya ma ta bata, dan ita har mamaki take yanda hankalin Aminan ya tashi, ko da yake ba abun mamaki bane, duba da yanayin gidan su Aminan, ba fita ta fiya sosai ba, dan ma Aminan bata ji, tana satar fita.

Haka suka dinga tattaki, akan titin suna fatan su samu abin hawa, kawai sun hau kan wani titi, suka ji mota a bayan su, juyawar da zasuyi suka ga yan sanda a motar, su da alama masu patrol ne, tsaida su suka yi, suka sha gaban su, a wannan gabar hatta Sadiya sai da hantar cikin ta ta kada, bare kuma uwar gayya Amina, tuni ta fara kuka, ganin suna diddirowa daga mota, tambayoyi suka fara musu, daga ina kuke, inda inda suka fara, Sadiya ce ma mai dan karfin halin, ita ta samu dakyar ta sanar dasu daga partyn kammala makarantar su suke, amma basu yarda ba, suna zargin yan good evening ne.

Tuni ogan su yace a saka su a mota, suna ji suna gani haka aka tasa kyeyar su, suka shiga mota, aka tafi dasu, dana sani babu adadi sunyi shi, musamman Amina da ita karya tayiwa mahaifiyar ta, kuka take kawai tana neman yafiyar Allah, dan tasan hakkin mahaifiyar ta ne ya kama ta, dan a yanzu Allah kadai yasan irin halin tashin hankalin da take ciki, sannan yanzu zuwa safiya, wannan abin tasan har mahaifin ta sai ya sani, ita bata damu da abinda zai mata ba, amma tana tsoron irin matsalar da zasu samu da mahaifiyar ta, kuma ta dalilin ta, kai ta rike tana kuka, kaico na wllh ban kyauta wa kaina ba.

A haka har suka isa police station, tunda suke dukan su basu taba zuwa police station ba sai yau, innalillahi Allah ka yafe mana, ta furta a fili, suna zuwa shiga sukayi kicibus da DPO din devision din zai fita, sara masa yan sandan da suke tare sukayi, me wadan nan sukayi, ya tambaya, wllh yallabai a titi muka kama su, muna kyautata zaton yan good evening ne, ai kafin yace wani wani abu Amina ta fara kururuwa, wllh mu ba yan iska bane, dan girman Allah yallabai ka taimake mu, dan darajar iyayen ka.

Daya daga cikin police din da suka zo dasu ne ya daka mata tsawa, dalla Malama rufe mana baki, idan ba yaran banza bane ku meya fito daku daga gidajen iyayen ku a wannan daren, kuma kun sha uwar kwalliya haka, tunda DPO ya dora idon sa akan Amina ya kasa daukewa, kallon su ya karayi sosai, kawai ya rafka salati, ku meya fito daku a wannan daren, wato dai ku baza ku bar iyayen ku su huta ba ko, yallabai ka san su ne, hmm yaran neighbor na ne, wllh basa ji haka iyayen suke fama dasu, Allah ya shirya cewar police din, ku wuce muje mota, ya daka musu tsawa.

Darasin Rayuwa Part (11)
Aisha Muhammad

Duk da ran Amina ya baci da yanda mutumin da tunda take bata taba ganin sa ba ma yake mata kazafi har yana buga mata tsawa kamar wani uban ta, hakan bai hana ta bin bayan shi da sauri ba, dan ko babu komai ya cece su, dan tasan matsawar ta kwana a wajen nan, to ikon Allah ne kawai zai hana mahaifin ta samun labari, tasan kuma muddin hakan ta kasance kashin ta ya bushe, sannan ba abin mamaki bane idan hakan ya janyowa mahaifiyar ta gagarumar matsala wacce zata iya saka auren ta rawa, idan kuwa hakan ta faru bataiwa kan ta adalci ba, kuma itama tasan Allah bazai bar ta ba.

Da wannan tunanin suka isa bakin motar tasa, yana bude motar Sadiya tayi saurin shigewa baya, dan ita yanda mutumin nan ya zage yana zazzaga musu masifa tsoro ma yake bata, haka Amina babu yanda ta iya ta shiga gidan gaba, dan kota sha giyar wake tasan basu isa su shige baya su kame ba su barshi a gaba kamar wani driver su, dan taga babu alamun wasa a fuskar shi, yana shiga yaja motar suka harba titi.

Sai da suka hau hanya sosai sannan ya tambaye su wace unguwa suke, hada baki sukai wajen fada masa dan kana ganin yanda suka takure a cikin motar kasan sun shiga taitayin su, motar tayi shiru babu motsin wanda kake ji, babu zato ya jeho musu tambayar daga ina kuke, muryar sa babu alamun wasa, cikin inda inda suka fara masa bayani, sai da suka kammala sannan ya shiga musu fada mai hade da nasiha, duk tsiwa irin ta Amina yau bakin nan yayi lubus, cike da ladabi, suke amsa masa tare da alkawarin insha Allah baza su sake ba.

Suna shiga unguwar su sukace sun gode ya sauke su daga nan ma zasu karasa, yace lallai sai sun nuna masa gidajen su sannan zai yarda dasu, haka suka dinga nuna masa hanya har suka isa gidan su Sadiya, sauka tayi bayan tayi masa godiya tare da addu'ar gamawa lafiya, yace babu komai abinda zasu masa kawai su tabbatar basu kara aikata makamancin irin wannan ba, alkawari suka masa, bai ja motar ba har sai da yaga ta shige gidan sannan yaja suka wuce gidan su Amina, itama bayan ya ajiye ta bai tafi ba saida yaga ta buga gidan an bude mata ta shiga sannan yaja motar sa ya tafi.

Mama na ganin ita ce, ta wuce ciki abinta, bata tsaya bi ta kanta ba, rufe kofar tayi sannan tabi bayan ta, tasan ba karamin fushi Mama take da ita ba, a falo ta same ta kwance akan kujera, ta juya baya kamar me bacci, a hankali ta shiga dakin tana bin bango kamar barauniya, gaban kujerar da Maman ke kwance taje ta durkusa akan gwuiwoyin ta, nasan na aikata miki babban laifi, wanda ya wuce na furta miki kalmar hakuri amma bani da wata kalmar da ta fita, dan girman Allah Mama dan darajar iyayen ki, kiyi hakuri ki yafe min, nayi miki alkawairin bazan sake aikata duk abinda kuka hane ni da shi ba.

Banza Maman ta mata kamar ma bata jin ta, dan Allah Mama kiyi hakuri wllh yau Allah ya hukunta ni da kansa, naga iftila'i, da badan Allah ya rufa mana asiri ba ya turo mana bawan sa daya taimake mu ba da yau sai nayi kwanan cell, da sauri Maman ta juyo ta kalle ta, tana maimaitawa cell fa kikace, kai ta synkuyar, cell Mama, kuma a dalilin saba muku.

Darasin Rayuwa Part (12)
Aisha Muhammad

Dan Allah kiyi hakuri ki yafe min, tashi Maman tayi ta zauna, meya jawo kikai dare haka, ganin Maman ta fara saukowa ta samu dama ta zaiyane mata duk abinda ya faru, abinka da uwa nan da nan tausayin diyar tata ya kama ta, duk da tayi kokarin boyewa hakan akan fuskar ta, dan ta nuna mata kuskuren ta, dan ita kanta tasan yarinyar tata bata jin magana ko kadan, sai dai tana taya ta da addu'ar Allah ya shirya ta, ya kuma bata miji na gari su aurar da ita, wala'alla idan aka mata aure ta nutsu, nan ta same ta da fada, ta inda ta shiga bata nan take fita ba, sai da ta mata tas, tana ta faman kuka, zaka rantse da Allah da gaske tayi nadama, bazata kara aikata laifi ba, sai dai ita kanta Maman tasan sai dai kuma aljanun fitinar tata basu motsa ba.

Sai da ta mata fada sosai sannan kuma ta saki ta koma nasiha, saida taga jikin ta yayi sanyi sosai sannan ta barta tace ta tashi taje ta kwanta idan kuma tana bukatar abinci taje ta diba a kitchen, ta koshi tace, amma ta kasa tashi a wajen sai da Maman ta gaji tace lafiya wai, ai gani nayi kamar har yanzu fushi kike dani ne Mama, tsaki taja sannan tace idan ban hakura ba na ma kula iskar ki, to Mama kice kin yafe min, ganin dai bata da niyyar kyale ta, tace na yafe miki Allah ya yafe mu, amin Mama na gode, daga haka ta mike ta mata sai da safe, bata amsa ba ta wuce, dama tasan za'ai haka, ai abin ma yazo mata da sauki ba kamar yanda tayi tsammani ba, amma tasan Maman tata bata da riko, zuwa safiya zata watsar, da wannan tunanin ta kammala duk wasu al'adun ta na kafin tayi bacci, sannan ta kwanta bayan tayi addu'ar bacci.

Gari na wayewa ta fito ta kama aikin gida, abinda bata saba ba, dama tunda tayi sallar asuba bata koma ba, dan tana neman shiri ne da Maman tata, dan haka duk abinda tasan tana so zata yi shi, har dakin Abban ta ta shiga ta gyaro dan a yau suke saka ran dawowar shi, dan yace jikin Kawu Balan da sauki, kuma asibitin nan garin da suka je sun tura su asibitin shika na Zariya, sai yazo gida tukunna sun dan shirya dan asibiti sai da kudi, idan suka gama shirin su sai yaje su tafi.

Kafin Mama ta fito gida ya dau harami, sanda ta fito gidan yasha gyara ko ina sai kanshi yake, murmushi kawai tayi ta girgiza kai, dan tasan badan Allah Amina zata tashi da sanyi safiya haka ba ta hau aiki sai dan tana neman shiri, a zuciyar ta tace Allah ya shirya mana ke Amina.

Kitchen ta nufa dan anan take jiyo motsin ta, aiko ta same ta tana hada musu abin kari, tana ganin Maman tayi saurin zuwa ta taugunna, Mama ina kwana, lafiya lau Amina irin wannan aiki haka da sassafen nan, murmushi tayi kawai, to Allah yayi albarka yasa a dore, Amin, shiga tayi suka karasa hada abin karin kumallon tare, bayan sun kammala suka wuce falon Mama, anan suka karya suna dan taba hira, wacce yawancin ta akan dawowar Abba ne.

Bayan sun kammala Amina ta tashi Mama bari naje na watsa ruwa na dan kwanta kafin a dora girki, ya dai kamata, dan kinsha aiki, Allah yayi albarka, ameen, ta juya ta fita, itama Maman waya ta dauka ta kira Abban Aminan taji karfe nawa zai taho.

Darasin Rayuwa Part (13)
Aisha Muhammad

Ba ita ta tashi ba, sai ana kiran sallar azahar, mika tayi tayi salati, sannan ta janyo wayar ta, kai har karfe biyu saura, da sauri ta mike ta dauki hular ta ta saka akan ta, fitowa tayi waje, bata samu Mama a tsakar gida ba, hakan yasa tayi hanyar kitchen dan tana jin motsi a ciki, tana zuwa ta sami Maman tana maida sanwar dambu, cikin tukunya, har tayi hawa na farko tana maida na biyu, sannu da aiki Mama, meyasa baki tashe ni ba, ai naga baccin ya dauke ki da karfi shiyasa na barki, yanzu nake shirin dama idan na gama maida dambun nan naje na taso ki, dan naji an fara kiran sallah, wllh kuwa, kunyi waya da Abba kuwa, eh yace insha Allah la'asar a gida zata masa, shiyasa ma na tarki dambu, dan kinsan Abban ki da son dambu, gaskiya kam, akwai abinda zan taya ki ne, aa na ma gama nima yanzu zan fito nayi sallah kafin ya turara, nima bari naje nayi alwala, eh idan kin idar sai kizo ki tace min wancan zobon, to Mama.

Tana idar da sallah tazo ta dauki zobon ta tace sannan ta zauna ta fara hada shi, har Mama ta idar da sallah tazo ta same ta, suka gama hada shi, sannan ta dauka ta kai tasaka a fridge, ta dawo, ta tarar Maman ta sauke dambun tana zubawa a flask din Abba, bayan ta zuba masa kuma ta dauki kula ta kwashe sauran, tray ta dauko ta dora flask din da plate cokali da duk abinda tasan zai bukata, ita kuma Amina ta dauka ta kai falon Abban, bayan ta dawo, Mama tace bari naje nayi wanka Amina ke kuma sai ki karasa gyara wajen, to Mama.

Wanka tayi ta dauro alwala, sannan ta fito ta shirya, kwalliya tayi sosai kamar zata je biki ko suna, hakan dama ya zamar mata al'adar ta, matsawar mai gidan nata yayi tafiya, koda kuwa ta kwana daya ce idan zai dawo sai ta shiryawa dawowar tasa, ta ko wane bangare kama daga kan gyaran gidan abinci da kuma uwa uba kwalliyar ta, duk da ta saba da masa kwalliya a kowane yammaci kafin dawowar sa daga aiki, amma idan yayi tafiya, abin yana fin na ko yaushe, idan kaga yanda Maman ke kula da lamuran mai gidan nata zaka ce yara ne sabon aure, wanda dama hakan shine abinda ya dace da ko wace mace, dan ita mace bata taba tsufa a wajen mai gidan ta koda kuwa ta kai shekara dari, matsawar zata gyara to kullum zata kasance sabuwa a wajen mai gidan ta, mu tashi mu farka mata, ki cire lalaci da kyuiya a zaman auren ki, shine zaki ci riba, har a dinga cewa kin asirce mijin ki, wanda babu ko daya, kissa kadai ta isa ta gyara miki gidan ki, idan kika hada da addu'a ba sai kinje wajen wani kato yasaki kin kauce hanya ba kuma kin bata kudin ki akan abinda zai miki jagora zuwa wutar jahannama, a ranar gobe kiyama, Allah ya kiyashe mu, ameen.

Tana gama shiryawa taji sallamar sa a tsakar gida, fitowa tayi da sauri, ta tarar da shi da Amina tana masa sannu da zuwa, itama karasawa tayi ta masa sannu da zuwan, Amina ce ta karbi kayan da ya shigo da su a hannun sa, hanyar dakin sa ya nufa Mama ta rufa masa baya, Amina kuwa tabarma ta dauko ta shimfida a tsakar gidan, dan tasan nan zai fito ya ci abinci, kayan abincin ta dauko ta jere masa kamar yanda Maman takeyi, sannan ta nemi waje ta zauna tana dan danna wayar ta.

Darasin Rayuwa Part (14)
Aisha Muhammad

Bata dade da zama ba suka fito tare da Mama, yayi wanka ya sauya kaya zuwa marasa nauyi na zaman gida, sannu da aiki Aminatu, murmushi tayi yauwa Abba sannu da hanya, waje ya samu ya zauna sannan ta kara gaida shi sosai ta tambaye shi me jiki, yace da sauki, Mama kuma ta zuba masa abincin ya fara ci yana zuba santi, su kuwa sai dariya suke, idan ka gansu sai sun baka sha'awa.

Sai bayan ya gama ya tambayi Amina game da maganar kammala makaranta, ta amsa masa da komai Alhmdllh sai hamdala, yanzu sai jiran fitowar result, to Allah ya taimaka, sai magana ta gaba, wllh Amina bazan dauki shashancin ki ba, na gaji da irin dauko min magana da kike a unguwa, koda ina can ma sai da na dinga samun labarin ki, dan haka yanzu dai kin kammala makaranta dan haka a cikin yaran da kike kulawa ki zabo daya wanda kika san zan iya aminta da shi, ba irin wadan nan shashashan yaran ba, masu ido a tsakar ka, dan ina samun labari wasu lokutan ma ido na ke gane min, irin yaran da kike kulawa, dan haka na gaji gara na aurar dake kafin kifi karfi na.

Tunda ya fara magana Amina ke sharar kwalla kamar ta Allah, kina wani sharar kwalla kamar wacce akayiwa karya, ni dai na gama magana, wllh idan baki kawo ba ma, to ni zan nema miki, kuma wllh kada kiyi tunanin zan ja lokaci, kinsan dai ke daya da Allah ya bani bazan gagara aurar dake ba, aduk lokacin dana so, Allah ya min wannan rufin asirin, dan haka kiyi kina sani.

Daga haka ya mike, bari na leka mu gaisa da makwafta, na sanar dasu na dawo, Allah ya tsare cewar Mama, yana fita Amina ta fada cinyar Mama ta fara rusa kuka harda birgima, ni wllh bazan yi aure yanzu ba, kuma Allah bazan auri wanda bana so ba, ture ta Maman tayi, dalla ni daga ni, da kinsan bakya son auren amma kike kule kulen samari, ai ni wllh wannan hukuncin da Abban ki ya yanke ya min dai dai, ai dama naga alamar ba kauna ta kike ba, au Allah, eh wllh indai akan wannan ne kije bana kaunar taki, daga haka ta mike ta bar mata wajen, tana fadin nidai shawarar da zan baki idan kinga dama ki fito da wanda kike so tun wuri dan kinsan dai Abban ki baya magana biyu, daga haka tayi shigewar ta daki ta barta a wajen tana ta rafzar kuka kai kace cemata akai uwar ta ta mutu.

Sai da tayi mai isar ta taga dai babu sarki sai Allah sannan ta tashi ta shige dakin ta, wayar ta ta janyo ta kira Sadiya dan babu damar fita, tasan Abba yana kofar gida, tana dagawa ta fashe mata da kuka, Meena lafiya, ina fa lafiya kina jin Abba daga dawowar sa wai na fito da miji aure zai min ko kuma shi ya zaba min, tsaki Sadiya tayi, kefa banza ce yanzu akan wannan kika kira ni kina irin wannan kukan, har kin sa gaba na ya fadi, au wannan ba abun damuwa bane, kwarai ma kuwa, dan ni yanzu ma nake niyyar kiran ki.

Darasin Rayuwa Part (15)
Aisha Muhammad

Meya faru, wllh dazu Hafiz ya kira ni muna hira nake bashi labarin yanda kike mutuwar son yin film da yan film, shine yace idan kina son shiga babu wata matsala zai hada ki da A A Sa'ad, kuma kinsan indai ya hada ku kamar burin ki ya gama cika ne, ai Amina bata san sanda tayi wani tsalle ba, saura kiris ma ta kurma ihun murna, sai kuma ta farga a gida take, yanzu zaki ga Mama ta leko tana tambayar ba'asi.

Dan girman Allah kawata da gaske kike, kinsan bazan miki wasa akan wannan ba, Allah da gaske nake, wayyo Allah kawata nagode nagode, haka ta ringa jero mata godiya, duk ta gigice, sai da Sadiya tace to wai duk wannan murna haka, ki bari kiga komai ya tabbata mana, hmm ai kema kinsan dole nayi murna, yanzu dai yaushe yace zai hada mun, yace baya nan amma dai baya tunanin zai wuce satin nan, yana dawowa zai masa magana, duk yanda yace zakiji, to shike nan Allah ya nuna mana nagode, kinji ki sai wani rawar kafa kike, yanzu kinsan fa su Abba baza su barki ba, ke dan Allah rufe min wannan bakin naki, ai kema kinsan mutuwa ce kadai zata iya dakatar dani daga cikar burina, kinga kin fara halin naki, ke dai kawai malama ki addu'a, ce miki nayi bana yi, zaki fara rashin mutuncin naki ko, to wllh sai nace na fasa miki hanyar, aa baza ai haka ba yi hakuri kawas, kyaji da shi, ni sai anjima, ina da abinyi.

Tuni bayan sun gama waya Amina ta shige walwalar ta, gaba daya maganar Abba ta fita a kanta ta daina damun ta, har Mama sai da tayi mamakin yanda Aminan ta ware haka da wuri, amma sai tayi tunanin ko dai ta hakura ne, zatai auren tunda dama dai a irin tarin samarin da take kulawa babu yanda za'ai ace babu wanda take so, ita dai addu'a ta cigaba da mata Allah ya zaba mata abinda yafi zama Alkhairi.

A daren ranar bayan sallah isha'i, muna zaune dukan mu a tsakar gida muna hira, aka aiko ana sallama da Abba, ya fita, ya dan jima sannan ya shigo, daki ya kira Mama, da alama magana ce akan bakon nashi, daga nan itama ta mike ta shige daki ta fara sana'ar tata ta waya da samari barkatai.

Bayan kwana biyu, da safe bayan Abba ya kammala shirin sa na fita ya saka Mama ta kira Amina, bayan taje ta zauna, yake sanar da ita, ta shirya anjima da yamma zatayi bako, gabanta ya yanke ya fadi, amma dai ta dake, ya cigaba, da kansa yazo neman auren ki ba nina tallata masa ke ba, dan hasali ma ban san shi ba, sai bayan shekaranjiya da yazo, kuma nasaka an min duk binciken da ya kamata ace nayi, kuma Alhmdllh ban same shi da wani aibu ba, dan haka na bashi izinin yazo ku fahimci juna, bance zan miki auren dole ba, amma dai a matsayi na na mahaifin ki addini ya bani damar na zaba miki mijin da zai iya kulawa dake, dan haka na baku dama ku dai dai ta, amma hakan baya na nufin zan yarda da a dauki tsahon lokaci ba, dan haka kiyi tunani kiyi abinda ya dace, dan dai indai kina da hankali kinsan baza mu zaba miki abinda zai cutar dake ba.

Harya gama magana kanta yana kasa, bazaka iya gane a wane hali take ciki ba, sai da yace mata ta tashi taje, sannan ta mike ta fita, tana shiga daki ta dauki waya ta kira Sadiya, hello Sadiya wai me ake ciki ne, har yanzu Hafiz din bai kira ki ba, bai kira ba, meya faru naji ki a hargitse, ba dole kiji ni haka ba, Abba ne yake neman dora min jarfa, ke fa yar iska ce Abban kike fadawa haka, ke dalla kina mayar da abu wasa, wai fa Abba ne ya kira ni wai ya min miji, anjima ma zai zo, dariya Sadiya ta kyalkyale da ita, ke wannan abin wasa ne wai, dalla Malama idan baza ki taimake ni ba, ni sai na kashe waya ta, yi hakuri kinji, wasa nake, ai ni kece kika bani dariyar, wai an miki miji, kamar kwaila, kinga ni fa idan ba mafita zaki kawo min ba, na kashe waya ta, kina kona min kati, yi hakuri, kinga to ke me kika ce musu, bance komai ba.

Darasin Rayuwa Part (16)
Aisha Muhammad

kenan kin amince da auren, Allah ya kiyaye, yauwa ta waje na.

Kinsan abinda za'ayi, aa sai kin fada, ki jira yazo kiga ma wane iri ne ma tukunna, sannan da wane irin taku yazo, sannan daga nan sai musan a layin da zamu saka shi, koba haka ba, kai amma wllh Sady kanki yana ja fa, to ni din ance miki ta wasa ce, kinga kuma muna addu'a insha Allah baza a wuce satin nan ba, zamuji daga Hafiz, insha Allah, na gode kawata, kinga sai anjima, wanka zan je nayi, dariya tayi, kodai zaki je ki fara tarbar bakon ki ne, mutsts taja wani wawan tsaki, ta kashe wayar.

Bayan sallar la'asar Abba ya kira Mama a waya yace, Aminan ta shirya, gashi nan yaron ya kira shi ya sanar dashi yazo, yana waje, a bude masa sittinroom dinsa, su zauna a ciki, da to ta amsa masa, duk da tasan babu wani shiri da Amina nan tayi, babu yanda batayi da ita ba akan ta dan shirya masa wani abu, amma fur taki, haka ta hakura ta kyale ta, yarinyar makwaftan su Shamsiyya da aka aiko ta kawo mata naman suna, da akayi a makwaftan su, ta tsayar, bayan ta shiga ta bude sittinroom din ta ciki, ta saka mata ruwa da sobo da bata rabuwa da shi a cikin fridge a akan tray, tasa takai masa sittinroom din, sannan tace dan Allah idan ta fita tace da bako a waje ya shiga sittinroom din, to yarinyar tace, ta fita da farincikin yar alawar da Maman ta bata.

Bayan yarinyar ta fita, sannan ta leka dakin Aminan, ta same ta a kwance abinta tana danna waya, sannu hakima sai ki tashi kije tunda na gama miki aiki, dan nasan kina jina, saura idan kinje shima ki masa wani bakin halin da zai kore shi, daga haka ta juya ta bar mata dakin, da kallo tabi Maman ganin yanda ta zage take mata fada akan wani banza, ta lura da gaske fa suke dan indai akan maganar aure ne ko kadan Maman bata mata da wasa ko kuma bin bayan ta, har ma kamar so take tafi Abban zafi, lallai ba kadan ba Maman ke so taga tayi aure ba, murmushi kawai tayi, lallai da zata iya da ta amince ko dan ta sanya farinci a zukatan iyayen nata, sai dai cab ko a mafarki bazai ma taba yuwuwa ba.

Mikewa tayi ta dauki hijabin ta na sallah ta zurma ta fito ko arzikin dan goge fuska bai samu ba, tana fitowa taga Mama zaune daga kofar dakin ta akan kujera yar tsugunno, ta zubawa kofar dakin ta ido, abin ma dariya yaso bata, tana karasa fitowa kuwa Maman tayi caraf tace, amma dai Amina Allah ya shirya ki, to me kuma na yi ni sarkin yan laifi, bana yi a yaba ai bakiyi na yabawar bane, yanzu dan Allah ki kasa goga koda yar hoda ce a fuskar ki, kai dan Allah Mama, idan kuma da na dade kice na Dade, nayi azamar fitowa nan ma kuma nayi laifi, shiru Maman ta mata ta saka kafa ta fice.

A zaune ta same shi a daya daga cikin kujerun falon, sallama tayi masa a ciki, yaji ta kasancewar babu motsin komai a wajen, amsa mata yayi yana mata murmushi, ko arzikin kallo bai samu ba, dan a cewar ta bata bukatar ganin fuskar sa, waje ta samu ta zauna ta dora kafa daya kan daya, tana ta cin magani.

Darasin Rayuwa Part (17)
Aisha Muhammad

Shi dariya ma taso bashi, baza mu gaisa bane Hajiya Amina, jin muryar kamar ta santa yasa ta dago kai ta kalle shi, da yatsa ta nuna shi, cikin tsananin mamaki, kai ne, murmushi yayi, nine kinyi mamakin gani na ko, kai kawai ta iya girgiza masa, meya kawo ka gidan mu, nifa Abba na ne yace zanyi bako, ai nine bakon, bani kika so gani ba, sai ta samu kanta da girgiza masa kai, dan wani irin kwarjini mutumin yake dashi, sannan uwa uba taimakon daya taba musu, komai iskancin ta tasan yafi karfin ta wulakanta shi.

Naga alama dai gimbiyar tawa akwai mulki, ni bari na gaishe ki, ina wuni, kunya ce ta kama ta, tayi saurin ce masa ina wuni har tana dan rufe fuskar ta da gefen hijabin ta, wai ita kunya, niko nace anya kuwa Aminatu, amsa mata yayi, yana tambayar ta ya mutanan gida, lafiya ta amsa masa, yarinyar data kawo min ruwa kanwar ki ce, aa yarinyar makwaftan mu ce, Allah sarki, ina kawar ki, tana nan kalau, abokiyar fitina ko, baki ta turo ba munce mun dai na ba, Allah yasa, shiyasa ma zanyi maza na dauke ki na kai ki gida na na killace, kai ta sunkuyar, bata ce komai ba, koya kika gani, ko ban miki ba, ki fada min, bana son boye boye, nan ma shiru tayi, lallai naga alama mutuniyar tawa akwai kunya, dariya tayi a ranta, ita kanta tana mamakin kanta yanda gaba daya tayi laushi, tab har Amina ce take jin kunyar wani yau, lallai wannan mutumin na daban ne.

Muna ta magana baki tambayi ko suna na ba, ko bakya son sani ne, kai ta girgiza, to shikenan zan fada miki ko baki tamabaya ba, amma gaskiya nidai a dinga bude baki ana min magana, kar kisa hankali na ya tashi, nace ko ba'ayi na'am dani ba, murmushi tayi, hakane mana, to ni dai suna na, Ahmad Muhammad mandawari, ni haifaffen cikin gari ne, iyaye na mu biyar suka haifa, hudu mata ni kadai ne namiji, yayyena biyu kanne na biyu, mahaifin mu Allah yai masa rasuwa shekaru biyu da suka wuce, Allah ya jikan sa, tace, yace ameen, nayi tundaga primary na har zuwa secondary na anan, sannan nayi degree na a A.B.U Zaria, daga nan kuma nayi applying police, kuma na samu, in takaice miki, yanzu haka nakai mukamin DPO, ina da mata da yarinya guda daya, kallon ta yayi, yayi dariya har gaban ki ya fadi, ko, kallon sa tayi sabida me, nasan Ku mana mata bakwa son kishiya, a ranta haushi ma taji, dan Allah kaji shi, kamar ma ce masa nayi zan aure shi, har yake wani zancen kishiya, a zahiri kuma murmushi tayi kawai.

To a takaice dai kinji dan kadan daga abin da ya shafe ni, akwai kuma wani abu da kike son sani, kai ta girgiza masa aa, to shike nan, ni bari nazo na tafi, kar kice wannan ya fiya takura, kinsan bana son na ishe ki, yar dariya tayi, baka sha ko ruwa ba, na gode, ina azumi ne, Allah ya bada lada, ameen yace yana mikewa baza ki min rakiya ba, shiru tayi, to ki gaida kawar ki, idan kun hadu, idan kuma kin shiga ki gaida Mama, zata ji, tace ya juya ya fita, ita kuma ta mike ta kulle sittinroom din, sannan tayi cikin gida, sanda ta shiga Mama bata tsakar gida, dakin ta ta wuce ta cire hijabin jikin ta, ta fito domin daura alwala.

Darasin Rayuwa Part (18)
Aisha Muhammad

Yau kwanan Ahmad uku da zuwa gidan su Amina bai kuma zuwa ba, sai dai yana kiran ta a waya su gaisa, dan a wancan zuwan da yayi ya karbi number ta, a yau yake sanar da ita zai zo suyi sallama dan zaiyi tafiya, an tura shi wani aiki abuja, yana dawowa zai turo iyayen sa ayi magana, a ranta tace, dawa badai da ni ba wllh, a zahiri kuma tace sai yazo.

Ya kuwa zo sukai sallama har suka gaisa da Abba yake sanar dashi insha Allah yana dawo wa zai turo magabatan sa, dadi sosai Abba yaji, dan ya yaba da yaron sosai, duk da Mama tunda taji yana da mata, take dari dari da abun dan gaskiya a son samun ta bata son Amina tayi aure gidan mai mata, ko Dan sanin halin yar tata, amma idan hakan shine alkhairin bata da ja, sai dai ta taya ta da addu'a.

Kashegari kuwa ya kama Monday da safe ya kira ta ya sanar da ita ya tafi, ta masa addu'a Allah ya tsare ta masa ya kashe wayar, akan idan sun isa zai kira ya sanar da ita, bayan sun gama waya Sadiya ta kira take sanar da ita, jiya Hafiz ya kira ta yake sanar da ita, ya yiwa A A Sa'ad maganar kuma ya basu appointment ranar alhamis karfe hudu na yamma, nan da nan Amina ta hau murna, ke da Allah tsaya, akwai matsal fa, matsala tame, tun jiya da daddaren na kira ki, amma wayar ki a kashe shiyasa yau da wuri na kira ki, ina jin ki, ta fada cikin zakuwa, yace sai dai muje mu same shi a Abuja, to ta yaya kike tunanin za'a barmu mu tafi har Abuja, gara ma ni, idan nayiwa Umman mu karya nace bikin kawar mu ake ba ni kadai zan tafi ba, zata iya bari na, amma ke fa, gaskiya akwai kura, amma dai kinsan bazan taba barin wannan damar ba, dole zan samo mafita, ai akwai sauran lokaci, kuma jibi su Abba zasu tafi Zariya kai Kawu bala gashin kashi, kinga Mama ce kawai zan san yanda zanyi da ita, to ina sauraren ki, kuma kinsan akwai maganar kudin mota da dan abinda zamu rike ko, ina sane wannan ba matsala bane, Allah yasa, daga haka suka yanke wayar.

Wunin ranar haka Amina tayi shi, sukuku bata da wata walwala, Mama tayi tambayar duniyar nan akan abinda yake damun ta, amma sai tace mata babu komai, har Maman ta fara zargin kodai ta fara son Ahmad ne, tafiyar da yayi ce take damun ta, bata son tsiyar da take kullawa ba.

Kwana biyu da tafiyar Ahmad yana kiran ta lokaci lokaci, idan taga dama ta dauka idan kuma bata ga dama ba taki dagawa, badai ta masa wulakanci, amma shi kan sa yasan ba wani yin sa take ba, a yau din kuma tayi dai dai da ranar da Abba zai tafi su taho da Kawu Bala su wuce Zariya, Amina sai faman murna take, dan a yau take so ta aiwatar da plan din ta, dan gobe sammako zasuyi, dan su samu su isa dan abinka da abin hawan haya.

Bayan Abba ya gama shirin sa ya tafi, ita ta masa rakiya har bakin mota, ya kara mata nasiya da jan kunne, a ranta cewa take kayi ka gama, a zahiri kuma tana ta amsa masa cike da biyayyya, yana tafiya ta dawo gida ta shige dakin ta,
ta dannawa Sadiya kira, tana dauka, tace mata ke ya tafi, zata iya zuwa yanzu, to Sadiyan ta ce mata ta kashe wayar.

Darasin Rayuwa Part (19)
Aisha Muhammad

Ba'afi mimti goma ba wata budurwa ta kwada sallama a tsakar gidan nasu, Mama dake zaune akan tabarma tana jin rediyo ta dago tana amsa mata sallamar, yarinya dake sanye da katon hijabi har kasa ta karaso cikin nutsuwa kana ganin ta kaga kamilalliyar yarinya da ta fito daga gidan tarbiyya, ta karaso gaban tabarmar da Maman ke zaune ta russuna har kasa, ta gaida Maman, ta amsa mata da sakewa, Amina tana nan kuwa, ai kafin Mama ta bata amsa Amina ta fito daga daki da saurin ta, wa nake ji kamar Farida Abbas, dariya yarinyar tayi, nice Amina na biyo ki tunda baki da kirki, inda suke ta matso, ta kama hannun ta yi hakuri kawata, sannan ta juya ga Mama, Mama wannan sunan ta Farida kawata sosai a makaranta, da yake baban su baya barin su fita sosai shiyasa baki san ta ba, amma ta zo gidan nan wajen sau biyu bakya nan, kawata ce sosai.

Allah sarki ai da kyau, sannu kinji ya mutanan gida, lafiya lau, ta fada tana sunkuyar da kai, Amina kai ta daki mana ki zo ki kai mata ruwa, to Mama taso muje Farida, suka shige daki, Mama ta bisu da kallon sha'awa, irin kawayen da take son ganin diyar tata dasu kenan ba irin waccen mai ido a tsakar kan ba, wai Sadiya, bayan Amina tazo ta dauko mata ruwa da sobo, suka zauna hira bata dade sosai ba, suka fito tare da Amina, Mama ta kalle su, ba dai har zata tafi ba, wllh Mama tafiya zatayi, ashe wai bikin ta ma ake, yau ne Kamu gobe yini da daurin aure, ta bada kati a kawo min, ni kuma ba'a kawo min ba, shine kinga ta biyo ni wai taga lafiya, Allah sarki Allah ya sanya Alkhairi ya baku zaman lafiya.

Shiru ta danyi, har saida Maman tace lafiya dai ko, hmmm wllh Mama kingan ta nan, ta dai fada miki da bakin ta, nace mata baza ki bari ba amma ita ta dage, shine nace ta fada miki da kanta, ya akayi yata, cewar Mama, wllh Mama kinga dama gobe ne daurin auren kuma jigawa za'a kai ni, ance ana yin azahar za'a tafi, idan anje can za'a karasa bikin shine akace na zabi kawayen da za'a tafi dasu shine nace dan Allah ki bar Amina taje.

Baki Maman ta rike babbar magana, a gaskiya yata bazan miki wannan alkawarin ba, da dai baban ta yana nan sai ta tambaye shi, to yayi tafiya kuma kinga dai bai kamata na barta tafiya har wani garin ba tare da sanin mahaifin ta ba, dan haka gaskiya kiyi hakuri, na miki alkawarin insha Allah, goben zata zo da wuri ayi komai da ita idan kun tafi sai ta dawo gida, to shike nan Mama hakan ma nagode, babu komai ki gaida gida Allah ya sanya Alkhairi, suka juya suka fita duk da Amina bata so haka ba, taso a bar ta taje, amma duk da haka, ta sami opportunity na fita gobe da wuri.

Suna fita suka hadu da Sadiya, yaya an dace, ina fa amma dai an dan samu wata damar, nan ta kwashe duk yanda sukayi da Mama ta fada mata, to amma ba tace ana tafiya ki dawo ba, kuma fa kinsan dole ne sai mun kwana, bazai yuwu muje mu dawo a ranar ba, na sani, to ba dai fitar ce wahala ba, ai idan na riga na fita dawowa kuma sai na kammala komai, Amina nifa kin fara bani tsoro, wllh ko ni da nayi wa Umma karyar biki a jigawa ta barni tsoro  nake ji, amma ke ko a jikin ki, kinga kanki ake ji, ni vari na shiga gida kar taga na dade, juyawa tayi ta shige gida.

Darasin Rayuwa Part (20)
Aisha Muhammad

Tana shiga ta dauki waya ta kira Marwan, yana dagawa korafi ya fara mata, wllh baby na gaji da wulakancin da kike min, zaka fara korafin naka, kaga ni albishir ma na Kira na maka, Abba yace na turo, kaji ka da azarbabi, to ba haka bane, yaushe ma Abban ya sanka balle yace ka turo, to ai laifin ki ne, amma ni kinga a gidan mu babu wanda bai san ki ba, kayi hakuri nan kusa ba yan gidan mu ba har ta dangi da abokan arzikin mu sai sun sanka, Allah yasa, Ameen, to dai yanzu yaushe zamu hadu, kinga fa tunda na dawo ban ganki ba kullum sai ja min rai kike, kice yau kice gobe, to ai ni baka tsaya ma kaji albishir din da zan maka ba, ka bige da korafi, afuwan ina jin ki, Abba yace na fito da wanda nake so, nan da abinda bai fi wata daya ba, bai San ma ni tuni na riga DA na fitar ba.

Wani ihu yayi a cikin wayar kice na shiryo yau na taho gaisuwar sirikai, kai haba kaji ka da gaggawa, to Abban ma baya nan, yayi tafiya, kuma nima tafiyar zanyi gobe sai na dawo tukunna zan gabatar masa da kai, ina zakije, wllh bikin wata kawar mu ake a Abuja, kuma kasan dai baza'a bar ni ba, yanzu ma sai karya nayi, dan haka dai na fada maka gaskiya, abinda yasa na Kira ka bani da kudin mota, kuma ni da Sadiya zamu tafi, kuma itama bata da kudin.

Wannan ne wani abin damuwa kawai ku shirya na mana booking flight sai mu tafi na raka Ku, tunda nima akwai abinda zai kaini Abujan amma ni sai jibi zan tafi, amma tunda zakije gobe ai sai mu tafi, ai ba girman ki bane tafiya har Abuja a mota, motar ma ta haya, cab ai kuwa sai dai girman nawa ya zube dan kuwa bazan hau jirgi ba, kasan yanda nake tsoron jirgi, kuma tafiyar ma da babu yardar iyaye na salon muje muyi hatsari, ko gawa ta baza'a gani ba, wllh ban yarda ba, kawai ka bamu kudin mota mu tafi, hakan ma mun gode.

To shike nan tunda ke matsoraciya ce, amma dai gaskiya bazan barki ki tafi a motar haya ba, sai dai kawai mu tafi har ni din a mota ta, ban takura ka ba, babu komai girman ki ne, to nagode, karfe nawa zamu tafi, dan ina so mu isa da wuri, dan a goben ma akwai event din da za'ayi, babu komai ki fadi karfe nawa kike so mu tafi, shiru tayi can tace kamar karfe goma yayi, yayi babu matsala, Allah ya kaimu, Ameen nagode, da haka sukai sallama ta kashe wayar.

Tana kashewa ta kira Sadiya ta fada mata duk yanda sukayi da Marwan din, sosai Sadiya taji dadi, har tana mata tsiyar wai ta musu bakin cikin hawa jirgi, eh naji dai hanyar lafiya a bita da shekara, shikenan dai sai goben saura ki mana wannan halin nauyin naki, ke Allah bazanyi ba, Allah yasa daga nan sukai sallama.

Washe gari da wuri Amina ta tashi shiga taya Mama aiyukan gida, kan kace me sun kammala gyara gidan sun hada abin kari, suka zauna suka karya, suna gamawa Amina tace Mama bari na tashi nayi wanka na shirya, kallon ta Mama tayi, haba koda naji, ai ni na manta zaki fita shiyasa kike wannan rawar kafar ni dai nasan haka kawai Amina baza ki tashi tun sassafe ki hau taya ni aiki ba, kai Mama wai ke bakya taba min shedar kirki ne, aa to ni me nace, Allah dai ya shirya ki, yauwa ko kefa Mama Ameen dai, daga haka ta mike ta fice dauke da kayan kwanukan da suka karya.

Darasin Rayuwa Part (21)
Aisha Muhammad

Bayan ta gama shirin ta ta fito, dakin Mama ta leka, Mama na shirya, to Allah ya tsare, dari biyar ta mika mata gashi kiyi kudin mota, sannan wannan dubu dayan kuma kya bawa amaryar, dan nikam wllh yarinyar ta kwanta min, to Mama an gode Allah ya kara budi, ameen kada kiyi dare Amina, dan ma fada ta aikin banza ce idan kika so aikatawa, ai kin ganki Mama kefa kike riga kiyi min baki tun kafin na fita, shiyasa idan na fita ake samun matsala, hmmm kyaji dashi, ni Allah ya tsare, Ameen tace ta juya tana dariya ko kefa Mama na, uwa ta ta kaina, banza Maman ta mata tana jin ta har ta fice a gidan.

Tana fita ta kira Marwan tace masa ta fito, cewa yayi ta jira shi a gidan su Sadiya, shima gashi nan yanzu zai fito, Sadiya ta kira tace mata gatanan ta shirya, ce mata tayi ta shirya su take jira, bata dade da zuwa gidan su Sadiyan ba ya kira ta yace su fito ya iso, haka suka fito Umman Sadiya ta musu Allah ya tsare dan ita duk a tunanin ta zasuje bikin kawar su a jigawa.

Bayan sun dauki hanya sun ma yi nisa sosai dan sun wuce Kaduna ma, mota ta lalace musu a wani kauye, dakyar suka samu wajen gyara, dan har sai da sukai sallar la'asar a garin kafin su samu a gyara motar, sannan suka dauki hanya suka cigaba da tafiya, Sadiya kuwa tana ganin biyar na yamma tayi ta kashe wayar ta, dan tasan yanzu Mama zata fara kiran ta.

Basu suka isa garin Abuja ba sai bayan sallar isha'i, suna shiga garin ya nemi waje yayi parking, to Alhmdllh Allah ya kawo mu, amma dai kunga yanzu dare yayi, da zaku bi ta tawa da kun hakura, na kaiku gidan kanwa ta ku kwana sai Allah ya kaimu gobe da sassafe sai ku nemi unguwar da zakuje ko ni da kaina sai na kaiku, kallon juna sukai, Sadiya ta mata magana kasa kasa, kinga Amina kawai mu amince, kinga dai yanzu lokacin da A A ya bamu ya riga da ya wuce, sai dai mu bari sai gobe, tunda ko dazu da mukai waya da Hafiz cewa yayi sai dai zuwa gobe, dan gaskiya lokaci ya wuce ba zai samu ganin mu ba a yau, kuma kinga ko Hafiz mu kai wa waya yazo ya dauke mu bashi da inda zai kaimu sai dai fa Hotel, kuma kinga dai ai ba mutuncin mu bane, kinga tunda ga gidan matar aure ai yafi mana, koya kika gani, haka ne kuma, kawai Marwan ka kaimu can din idan baza mu takura ta ba, kai haba kada ku damu babu wani abu, mungode, daga nan yaja motar suka harba titi.

Kofar get din wani madaidaicin gida yayi parking, ya danna horn, nan da nan mai gadin yazo ya bude masa, suka gaisa da mai gadin sannan yaje yayi parking, sai da ya kashe motar sannan ya fito ya zagayo ta inda Amina take ya bude mata kofar, ta fito Sadiya ma ta budewa kanta ta fito, hanyar da zata sada ka da falon gidan ya nufa, suma suka rufa masa baya, nocking ya fara yi, sannan ya tura kofar ya shiga, suka dan tsaya a bayan sa, sai da ya juyo ya musu nuni da su shigo mana, sannan suka bi bayan sa, Amina sai wani sissinke kai take wai ita tazo gidan sirikai, dariya kawai yayi daya fahimci inda ta dosa.

Darasin Rayuwa Part (22)
Aisha Muhammad

Kujera ya nuna musu suka zauna, sannan yayi hanyar wani corridor, zuwa can ya dawo dauke da ruwa da lemo a tray ya ajiye musu, bisimillah fa, ku fara shan ruwa, tana sallah ne yanzu zata fito, ni bari naje na dawo yanzu kufa saki jikin ku, bata da matsala, aa ina kuma zaka daga zuwan ka, motar nan zan kai yanzu nan akwai gareji nan kusa, su duba min ita kafin zuwa safiya, dan wannan gyaran da aka min baiyi ba kawai dai na lallaba ne, to sai ka dawo, yauwa, ya fice ya ja musu kofa.

Ruwan suka dan sha kadan, suka zauna jiran fitowar matar gidan, amma shiru kake ji babu alamar motsin mutum ma a cikin gidan, sun haura awa guda suna zaune amma shiru, har dai abin ya fara Isar su, gashi sun dauko bashin sallah suna so su samu su rama, ga gajiya ga kuma yunwa, amma matar nan ta shanya su, Amina har ta fara kulewa, tayi niyyar dauko waya ta kira Marwan bata ga jakar ta ba, Kai sadiya kar dai na bar jaka ta a motar shi gashi waya ta tana ciki Amma naga kamar kin shigo da ita, to ki kira shi da waya ta mana ba tana hannunki ba, to ai da kika bani a cikin jakar na saka ta, Yau mun ga iKon Allah ai sai mu zauna mu jira su, hmmm shiru tayi kawai.
Suna zaune jigum sai da suka kara wajen minti talatin, gaba daya ransu ya gama baci, kinga Sadiya tashi mu tafi ni bana son wulakanci kawai ki kira mana Hafiz yazo ya dauke mu, to da wacce wayar zan kira Hafiz din yanzu fa muka gama maganar.

Kiyi hakuri yanzu kawai abinda za'ai mu tashi mu duba idan munga toilet muyi alwala muzo muyi sallah, ko kuma muje kofar dakin matar gidan mu buga mata, ai kuwa sai dai ke kije dan wllh ni idan naje ta fito sai na fada mata ba dadi sai dai tace baza mu kwanar mata a gida ba.
Dariya Sadiya tayi, bama za'ai haka ba, bari ni naje, tashi tayi ta nufi corridor din da suka ga dazu Marwan din ya bi, daki ta gani guda daya yana kallo ta.

Darasin Rayuwa Part (23)
Aisha Muhammad

Nocking tayi a hankali, shiru har ta gaji Amina da taji shiru ta biyo bayan ta, kinga Sadiya muje waje kawai ko aron waya ne muyi ki kira mana Hafiz yazo ya tafi damu, dan nifa gidan nan ya fara bani tsoro.

Gaskiya ina tunanin fa yayi bacci, kinga fa  yanzu nasan goma ta wuce, gaskiya kam, yanzu mene ne abunyi, wllh ban sani ba, dan nifa tsoro ma na fara ji, anya kuwa Amina akwai mutane a gidan nan, tunda muka shigo kinji motsi kuwa, aa mun shiga uku Sadiya, kinga ba wannan ba tashi muje mu bude dakin nan sai mu fita daga kokonto, haka ne kam.

Kofar dakin sukaje suka kara bugawa, babu alamun za'a bude, hannu suka saka suka murza handle din suka bude kofar, kankame juna sukayi, rike da bakin su gudun kada su kwarma ihu, dan ba karamin tsorata sukai ba da sukai arba da tarin mata a dakin yagal yagal cikin wani mawuyacin hali, duk sun kanjame sun lalace, kallon kallo suka tsaya sunayi tsakanin su da matan, duk da su matan ko kadan basuyi mamakin ganin su ba, dan sun saba kusan kullum ne sai an kawo bakin fuska, kuma kusan kullum sai an debi wasu an tafi dasu, dan haka basuyi mamakin ganin su Aminan ba.

Wata daga cikin matan ce tace dasu sannun ku bayin Allah, ku saki jikin ku muma mutane ne kamar ku, dan naga kamar kun tsorata da ganin mu, kai suka shiga girgiza mata, tasowa tayi ta zo ta kama hannun su taje ta zaunar dasu, meya kawo wajen nan duk da nasan bazai wuce tsautsayi ba kamar yanda ya kawo kowannen mu a nan.

Nan suka kwashe duk yanda akai har suka tsinci kan su a wajen, fada sosai matar ta musu dan ta girme musu sosai, sannan suma suka dinga basu labarin yanda akai suka zo wajen, yawancin su Marwan ne ya yaudare su da soyayya, da yake kuma yan matan yanzu Allah ya musu kwadayi shiyasa baya shan wahala wajen yaudarar su, ashe safarar mutane yake, yana siyar dasu, duk sunce daga randa ya kawo ki bakya kara ganin sa, sai dai a kowane sati, ana zuwa a debi wasu daga cikin su, a tafi dasu, wasu ana dawo dasu wasu kuma shike nan sun tafi kenan.

Wasu suna siyar dasu ne, a kasashen waje, aje a maida su kamar bayi, wasu kuma ana kaisu kasashen waje ne a saida su su dinga karuwanci suna kawo musu kudi, da dai sauran su, gaba daya dai a cikin har kokin babu ta arziki.

Darasin Rayuwa Part (24)
Aisha Muhammad

Kafin akai karshen labarin gaba daya daga Amina har Sadiya sun sha jinin jikin su, gaba daya ma hawaye ya kafe a idon su, sai faman hada gumi suke, sun rasa ta cewa, nan wannan matar ta cigaba, dan haka kawai sai dai ku cigaba da addu'a, dan ko ni nan da kuka ganni ba karamin dadewa nayi a gidan ba, dan da daddare suka sato ni, albarkacin addu'a yasa har na kawo yanzu babu abin da suka min, dan sunce wai nayi tsufa basu kula haka nake ba da babu abinda zasuyi dani, shiyasa suka barni anan, nike musu duk wani aikace aikace a cikin gidan.

Sadiya ce ta samu zarafin amsawa, amma Amina zaune kawai take ta zuba wani uban tagumi, tunani take ko yanzu wane hali Mama take ciki ganin har dare yayi haka bata dawo ba, ai dole ita ta samu matsala, irin tashin hankalin da take jefa iyayen ta a ciki.

A ranta ta kuri aniyar kota halin kaka bazata taba bari a siyar da ita kamar wata dabba ko baiwa ba, dole ne ma kota halin kaka tasan yanda za'ai su bar gidan nan, dan gara su kashe ta idan sun kama ta tana niyyar guduwa, ko babu komai ta rataya a wuyan su, duk wani laifi nata su zasu biya shi, akan ta zauna ta kare rayuwar ta da hakkin iyayen ta yana bibiyar ta.

Can ta nisa tace, dan Allah baba akwai inda zamu samu ruwa zamuyi sallah, akwai mana ai muma duka muna sallar, ku shiga bayi gashi nan ta fada tana musu nuni da kofar bandakin dake cikin dakin, Amina sarkin tsafta saida ta kusa yin amai, sabida tsabar kazantar dake cikin bandakin, dakyar suka samu sukayi alwalar suka fito. Falon suka fita suka shimfita dankwalayen su suka tada sallah.

Sai da suka gama biyan bashin sallar da ake bin su sannan suka yi isha'i, bayan sun idan ko wannen su ya gama kwararo addu'ar kubuta, suka shafa, sannan suka juya suka fuskanci juna, Amina tace wai Sadiya menene mafita, babu wata mafita illa mu cigaba da addu'a har Allah ya kawo mana mafita, au kina nufin mu zauna mu nade hannu har wadan nan azzaluman su sai da mu, to wllh idan ke zaki tsaya to ni bazan zauna ba, kota yaya ne sai na gudu, baki Sadiya ta rike, Amina baki da hankali bakiji ba matar nan tana fada mana duk wacce tayi kokarin guduwa kashe ta suke bayan sun lalata mata rayuwa, to ni dai kam gaskiya ban shirya mutuwa ba.

Darasin Rayuwa Part (25)
Aisha Muhammad

Amma dai wllh ke dai Sadiya banza ce yanzu ke daki mutu gara ki kare rayuwar ki a baiwa ko kuma karuwa, to ni dai kam a ciki babu wanda na shirya zama, kuma ga hakkin iyaye na indai bazan samu naje na roki gafarar su ba kuma na gyara rayuwata ba, to wllh gara na mutu, baki Sadiya ta rike tana kallon ta, sannu sayyada Amina, yau kece kike zancen ki mutu, lallai kinga masifa, amma wllh daki zancen wani ki gyara rayuwar ki, wannan kan ban yarda ba ki dai fadawa wani, dan nikam a halin ki babu irin wanda ban sani ba, sau dubu kike tuba kuma ki koma ruwa sau dubun nan.

Dalla Malama rufemin baki idan bazaki fadi Alkhairi ba to kiyi shiru, haka manzon Allah yace, kuma wai ke bakya ma duba condition din da muke ciki sai wasu magan ganun banza da wofi kike, Allah ya baki hakuri nidai gaskiya na fada, to ba'a son gaskiyar ki rike kayar ki, ni dai kinga kiyi hakuri, meye mafita, dan nima ai bawai ina son zaman nan din bane, kifa tuna nima nabar Umma na da yan kanne na, kuma a kaina suka dora duk wani hope nasu, na kammala karatun nan na samu aiki na taimaka musu.

Yanzu abinda za'ayi, ba sunce duk dare suna zuwa ba, eh, to da wannan damar zamuyi amfani mu samu mu gudu, ta yaya kenan, su kansu wadan nan matan na ciki dabara zami musu, baza mu bari su san zamu gudu ba, sabida gudun matsala, kai Amina amma ba gara mu taimake su ba, mu gudu gaba daya, to sannu yar agaji, ai ke sai ki tsaya ki taimake sun amma ni kam guduwa zanyi kowa tasa ta fishshe shi, wllh babu shegen da zan taimaka, Allah ya shirye ki Amina, ameen.

Duk yanda zamuyi kada mu bari bacci ya dauke mu har sai sauran sunyi bacci, ba tace sai sunyi bacci suke zuwa ba, eh, to idan muka tabbatar sunyi bacci, sai mu fito, da farko zamu fara lalata makunnin kwan lantarkin dake falon, sannan sai mu samu wani lungun mu labe, koda ta bayan labule ne, duk da babu wani wajen buya me kyau a falon amma Allah zamu roka shi zai boye mu, idan suka nemi kunna wuta taki, to zasuyi amfani ne da fitilar wayar su, ita kuma bata da wadaccen hasken da zasu iya saurin ganin mu, idan suka shige ciki, mu kuma dama a shirye muke sai kawai mu fice, daga nan kuma idan muka samu muka fitan maga yanda zamuyi, to shike nan tashi mu koma kar suga mun dade.

Da wannan shawarar suka koma dakin suka kwanta, dan dama sun tarar da sauran sun riga da sun kwanta, kokari sukayi tayi wajen ganin bacci barawo bai dauke su ba, dan duk irin tashin hankalin da suke ciki bazai hana bacci daukan su ba idan basuyi da gaske ba, dan shi kowa ya shaida gwanin iya sata ne.

Darasin Rayuwa Part (26)
Aisha Muhammad

Can da suka tabbatar zuwa sannan kowa yayi bacci, da daya daya suka zame suka fita falo, suna zuwa da karfi da yaji suka balle makunni kwan lantarkin,har saida Aminan ta yanke a hannu, amma ko zafi bata ji ba, dan tashin hankalin da take ciki ya girmi wannan yankan, take kuwa wutar falon ta dauke, da lalube suka nemi can bayan labule ta jikin kofar fita daga falon suka buya.

 Basu dade a wajen ba kuwa sukaji, karar bude get din gidan, karar mota sukaji, zuwa can kuma sukaji an kashe motar an fara yowa wajen kofar falon, kara lafewa sukayi a jikin bango, wata uwar zufa na karyo musu, can sukaji an saka mukullin an bude kofar, ji sukayi kamar zasu saki fitsari a wando, basa iya ganin wadan da suka shigo amma tabbas sun san ba mutum daya bane, aa waya kashe wutar falon nan daya daga ciki ya fada.

Oh haska ka kunna mana, waya daya ya daga cikin su ya dauko ya kunna fitila, ayya kaga ashe wajen ne ya lalace Amma Kuma kaga kamar Wanda aka balle shi da karfi, amma muje kawai zuwa safiya a gyara, cikin wannan corridor suka nufa, Amina addu'a kawai take Allah yasa kada su kulle kofar, ai kuwa addu'ar ta ta karbu, dan basu kulle da mukulli ba, turawa kawai sukai.

Ai kuwa suna shiga Amina ta kamo hannun Sadiya suka nufi bakin kofar, suna fitowa sukaji motsin tahowar wani, da gudu suka koma, har saida ta bugu da bango, taji mugun zafi amma ya ta iya, haka dole ta daure ta hadiye abinta, yadan ji motsi kamar motsi ya haska bai ga komai ba, kawai ya wuce, yana tunanin kunnen sa ne, mukullin ya zare a jikin kofar ashe shi ya dawo dauka, sun manta.

Yana komawa su Amina najin bude kofar sa ta dakin, suka kara fitowa da sauri, a hankali suka murda handle din, ai kuwa kofar ta bada wata kara, kurrrrr, wayyo zo kuga idanun Amina kamar zasu fado tsabar tsoro, Allah dai ya taimake su ba'a jiyo ba, suna fitowa, sukaga haske gal a harabar gidan, da sauri taja hannun Sadiya sukayi baya, kada mai gadi ya gano su.

Wajen katanga suka nufa duk da ita kanta Amina tasan babu ta yanda za'ai ta iya haura Katanga, Allah da ikon sa suna isa jikin katangar suka ga tarin block irin wadan da suke saura idan an gama gini, an tare su a jikin katangar, kallon juna sukayi da Sadiya, Sadiya kinga ikon Allah ko, Allah ne yake taimakon mu, hakane kam, muyi sauri bamu da lokacin batawa.

Kakkamawa sukayi suka haye saman block din, daga nan kuma suka dane katangar, sai fa ana wata ga wata, sun manta da idan sun samu sun hau to dira fa, kallo tsahon wajen sukayi, Sadiya mun shiga uku, yanzu ya zamuyi, haka zamu dira, mu dira ina, wllh idan na dira wajen nan ta tabbata sai na karye, to idan kuma baki dira ba, sai ki tsaya ki mutu, ai kafin su karasa magana, suka jiyo, mutanen nan suna tambayar mai gadi ko yaga fitar su, take cikin su ya bada wani sauti, kulululu.

Darasin Rayuwa Part (27)
Aisha Muhammad

Ai kan kace me tuni Sadiya ta zura jikin ta ta dira, Amina ma jikin ta ta zura, amma ta kasa ta dira, Sadiya tayi tayi ta diro ta ki, sai da ta fake ta kawai ta jawo kafar ta, aikuwa ta fado mata a ka, wayyo ta bude baki zata kurma ihu, Amina tayi sauri ta danne mata baki.

Haka suka tashi suna dingishi, suka nitsa cikin unguwar basu san inda suke saka kai ba, suna cikin tafiyar nan sukaji alamun tahowar mutane, haka suka Kara sauri har suna hadawa da gudu duk da yanda gaba daya jikin su ke musu azaba, sabida dirar da sukai, har wani wajen ma sun kukkuje.

Suna cikin gudu, dan har sun fara karaya, kwatsam suka ji karar tahowar mota, ai kuwa mai motar ya dalle su da fitilar motar, daga masa hannu suka shiga yi, suna kuka, kamar zai wuce su sai kuma yayi parking, da gudu suka karasa bakin motar, suna rokon sa dan Allah ya taimake su, daga ina kuke haka da wannan daren, wllh wasu ne suka sace mu, gasu nan sun biyo mu, dan Allah ka taimake mu kar su kama mu.

Shiru yayi yana kare musu kallo taya ya zan yarda daku, wllh Allah mu ba macuta bane, wllh gaskiya muke fada maka, kallon su ya kara yi, gaskiya ne da alama sun sha walaha, kofar baya ya bude musu, ku shiga muje, ai kafin ya gama rufe bakin sa sun fada motar sun rufo masa kofar, juyawa yayi ya canja hanya bai bi ta inda suka ce an biyo su ba.

Har suka isa gidan sa baice musu komai ba, sai bayan sun isa gidan kuma suka fara shan jinin jikin su, ganin irin girman gidan da kyan sa, kuma gashi bai tambaye su inda zasu ba kawai ya kawo su gidan sa, haka babu yanda suka iya suka fito bayan yayi parking ya basu umarnin su fito, dan babu alamar wasa a fuskar mutumin, gashi siffar sa kadai ta isa ta firgita ka, dan wani katon Alhaji ne baki da jajayen ido, ga katon tumbu, fuskar sa babu alamun rahama a tattare da ita.

Haka ya tasa su a gaba har cikin katon falon gidan, wani daki ya bude yace musu su shiga, da kakkausar muryar sa mai amo abin dai babu dadin ji, da gudu gudu suka shige dakin, ya rufe su yayi gaba abin sa, kallon juna sukayi da Sadiya, mun shiga uku Sadiya, ba'a rabu da bukar ba an haifi habu, mun kuma kawo kanmu mahallaka, ke dai bari ai nima sai bayan mun shiga motar sannan na fara nadama, da wannan daren kawai mu tsayar da mota mu shiga bamu san waye a ciki ba, mun fita daga wata masifar mu kara fadawa, wllh da mun sani cigaba mukai da gudun mu, watakila Allah ya tseratar da mu, hmmm ke dai bari aidai ta riga ta faru sai dai a kiyayi gaba.

Haka suka takure waje daya ga uban sanyi da yake damun su gashi babu komai a cikin dakin sai malalen tiles da yabi ko ina na cikin dakin, har jikin bango, hakan ya karawa dakin sanyi, hawaye ne ya zirarowa Amina a fuskar ta, yanzu badan rashin jin maganar taba, da yanzu tana nan a dakin ta kan dan gadon ta, tana rufe da bargon ta, cikin rufin asirin ta, amma yanzu kalli masifar da ta jefa kanta a ciki, Allah na tuba ka yafe min ka fitar damu a cikin wannan hali, nayi alkawarin gyara halaye na, na zama mutuniyar kirki yarinyar da iyayen ta zaauyi alfahari da ita, Allah mun tuba Allah ka kubutar damu, Sadiya taji tace Ameen, ashe bata sani ba a sarari take magana.

Darasin Rayuwa Part (28)
Aisha Muhammad

Haka suka kwana cikin wannan azabar, kiran sallar farko kuwa a kunnen su, kofar da suka gani a cikin dakin wacce suke kyautata zaton bandaki ne suka tura, ai kuwa bandakin ne, alwala sukayo suka fito, anan kan tiles din suka tada sallah, suna idarwa basu kai ma ga yin addu'a ba sukaji an turo kofar dakin, take hankalin su ya tashi, suka kankame juna, wannan Alhajin ne dai ya turo kofar ya shigo, babu ko sallama yace ku tashi mu tafi, haka nan babu musu suka mike, dan yanzu kam basu da ta cewa, suyi magana ya Nada musu na jaki.

Dan haka salin alin suka tashi rike da hannun juna suka bi bayan sa, wajen motoci yaje wata hillox ya bude musu, da ido ya musu alamar su shiga, haka babu musu suka shiga bakin su dauke da addu'a, shima shiga yayi ya kunna ta, mai gadi ya bude masa get suka fice daga gidan.

Tafiya mai nisa sukayi, suka shiga wata unguwa da alamar sabuwar unguwa ce, dan duk gine gine ne sabbi da wadan da aka gama wasu kuma ana kan aiki, sai kuma filaye, kofar get din wani gida yayi horn mai gadin yazo ya bude, gidan kato ne sosai, amma ba'a kammala ginin sa ba, wajen da aka tanada danyin parking yaje ya faka motar, ya fito sannan ya bude musu bai ce musu uffan ba amma dai sun san yana nufin su fito, fitowar sukai, dan sun san ko kadan babu abinda gaddama zata haifar musu a wajen nan face wahala, dan basu da mataimaki sai Allah.

Cikin gidan ya nufa dasu, wani falo suka shiga, suka tarar da wasu mutane guda uku a zazzaune akan kujerun falon, hannu ya basu suka gaggaisa, daya daga cikin su yace, aa kace kai harda wata tsaraba kake tafe da sanyin safiyar nan, gaskiya shugaba zaiyi farinciki da kai, dariya yayi, wllh nima tsintar dami nayi a Kala, suka kece da dariya, ai kuwa kayi babbar sa'a dan kwana biyu babu harka, ba karamin farin ciki shugaba zaiyi da kai ba, watakila ma ka sami wata babbar kyauta, to Allah yasa, zama yayi, ya kwalawa wani kira a cikin gidan, can kuwa sai ga wani garjejen kato ya shigo falon, wata irin gaisuwa ya masa, hannu kawai ya daga masa, sannan ya masa nuni damu.

Inda muke rakube a jikin bangon falon ya nufo, kamar kaji haka ya kama mu yana ja a kasa muna ihu, ya wuce damu wani daki, yana bude kofar ya jefa mu ya maida kofar ya rufe, wasu mata ne suma su biyu a cikin dakin, amma fa idan baka musu kallon tsanaki ba baza ka gane mata bane, dan kawunan su kwal suke babu alamar gashi an aske shi tas, waje muka samu muka sulale muka zauna manne da juna, muna kallon kallo tsakanin mu dasu.

Daya daga cikin su ce ta ce mana sannun ku, Amina ce tace yauwa, dan Allah bayin Allah ina ne nan, Allah masani dan yanda baku san komai akan wajen nan ba muma hakan take a wajen mu, dan yanda aka kawo ku muma haka aka kawo mu, innalillahi, Allah mun tuba Allah ya yafe mana ka kubutar damu, duka suka amsa da ameen.

Zaman shiru ne ya cigaba da gudana a cikin dakin, zuwa can aka bude kofar, wani garjejen bakin kato babu riga ya shigo ya tasa keyar su Amina ya fita dasu suna ihu, wani daki ya kaisu ya angiza kyeyar su ciki, wani mutum ne a cikin dakin ya ja Sadiya da karfin tsiya ya dora ta akan wata kujera, Amina rasa abinyi ma tayi, hawaye ne kawai yake bin kuncin ta, ganin yanda da gatan su da komai amma ana musu abu kamar wasu dabbobi.

Darasin Rayuwa Part (29)
Aisha Muhammad

Aska mutumin ya dauko da almakashi ya fara yanke gashin kan Sadiya, ganin haka Amina bata san sanda ta kurma uban ihu ba, amma ko a jikin sa haka ya gama rage masa tsaho, ya dakko aska ya fara taltale mata kan, yana gama mata ya janyo ta kasa, har tana bigewa, amma kota kanta baibi ba ya janyo Amina tana ihu tana fusgewa amma ko a jikin sa, daya dora ta a kujerar yaga zata kawo masa matsala sai ya janyo wani belt a jikin kujerar ya daure ta dashi, dama da alama an tanade shi ne sabida irin su.

Haka Amina tana ji tana gani duk uban ihun da take bai saka mutumin nan ya saurara ba har sai da ya aske wannan uwar sumar da take gwalli da ita kawaye na koda ta, kuka kam Amina tasha shi harda majina, dan har aka gama tana kuka, muryar ta har ta dashe fuskar nan ta hadu ta cabe da hawaye da majina, haka bayan ya gama ya tasa keyar su har dakin da suke Amina sai faman rafsa kuka take, ita kuwa Sadiya dama tun tuni ta fawwala wa Allah tayi hakuri, tasan komai ya same su, su suka jawowa kansu dan haka basu da kaico.

Zaune suke sun rafka uban tagumi, aka turo kofar dakin wannan dai mutumin ne wanda ya kawo su dakin, ya shigo da wata roba kamar ta almajirai, a gaban su ya dangwarar da robar, abinci ne a ciki, kwadon gari babu alamar mai a cikin sa, sai dan gishiri, haka ya ajiye musu ya fice, dukan su kan robar sukayo kamar shazumamu yaga suga, dan gaba dayan su yunwa ce a cikin, dan ko su Aminan ma rabon su da abinci tun wanda Marwan ya siya musu a hanyar su ta zuwa.

Amina kuwa ko kallon kwanon batayi ba, sai da Sadiya ta taba ta, Amina kizo muci, bana ci ta fada ciki ciki, haba Amina zaki fara wannan gardamar taki ko, to wllh ki tuna ba'a gida kike ba, kuma kinsan rabon mu da abinci tun jiya da rana, kuma keda kanki kikace bakya son ki mutu yanzu dan haka gara ma kizo muci, matsowa tayi tana hawaye, dan abinda Sadiya ta fada ba karamin fami ya mata ba, da tace yanzu fa ba'a gida take ba, tunawa tayi da yanda a gida dan kankanin abu za'a mata, ta dauki fushi, tace kuma bazata ci abinci ba, haka Mama zata saka ta a gaba da lallashi, wani lokacin ma da kanta take bata a baki, duniya ke nan, shiyasa wanda bai bi iyayen sa ba ya shiga uku, dan tun daga duniya Allah zai fara hukunta shi.

Tana dannan garin nan tana kuka, idan ka kalle ta sai ka ji tausayin ta, Amina yar gayu, yau itace a haka kai yasha tankwal, har wani kyalli yake, gaba daya ta canja kamanni, babu yanda za'ai idan baka mata kyakykyawan sani ba ka ganta take ka gane ta, gaba daya daga jiya zuwa yau ta gama fita kamannin ta, tun kafin a mata askin balle kuma yanzu.

Nan da nan suka lashe dan kwadon garin dan dama gaba dayan su a yunwace suke, wannan kuma dama ba yawa ne dashi ba, gefe duk suka koma suka zauna, kowa da abinda yake sakawa a ransa, Amina kuwa babu abinda take hange irin hanyar da zasu bi su tsere, ita kuwa Sadiya tuntuni, ta fawwalawa Allah ta gama saddakarwa tasu ta kare, dan haka addu'a kawai take Allah ya yafe musu.

Darasin Rayuwa Part (30)
Aisha Muhammad

A haka har duhu ya fara yi, dan basa sanin lokaci ko sallah kawai suna kintatar lokaci ne suyi, kuma alwala ma sai dai suyi taimama, idan kuma kina da bukata ko fitsari, sai dai ki buga kofa, za'a zo a raka ki, wanda ya raka kin yana tsaye kiyi ku dawo, tare, idan kuma a kai rashin sa'a suka shigo suka ga kana sallah, kaci na jaki.

Suna zaune babu jimawa da sukayi sallar isha'i aka turo kofar, wannan dai katon ne, wadan nan mutum biyun da suka zo suka tarar a dakin, yazo yaja, suna kuka suna masa magiya, amma ko a jikin sa, haka ya tafi, dasu, dan ko idon mutanen nan ka kalla kasan babu digon imani.

Bayan sun fita Sadiya ta rushe da kuka, mun shiga uku Amina, yanzu muma muna ji muna gani za'a zo kan mu, aje a kashe mu, dan ko ba'a fada mana me za'a mana ba muma muna sani, gidan nan gidan masu yankan kai ne, yanzu muma haka za'a yanke kawunan mu, shiyasa ma da kike ta faman kukan an yanke miki gashi, kikaga ni nama hakura, to menene gashi, karshe ma kawunan namu duka za'a yanke.

Ke kina da mugun baki, nasan duk inda iyayen mu suke kuma duk yanda muka bata musu rai, nasan baza su fasa mana addu'a ba, kuma addu'ar iyaye bata faduwa kuma muma muna yi, dan haka ina da yakinin Allah zai fitar damu, kada mu fitar da rai, ba'a fidda rai daga rahamar ubagiji, haka ne kam Allah ka kawo mana dauki, ameen.

Har bacci ya fara daukan su ba'a dawo da wandannan matan ba hakan ya tabbatar musu shike nan an kashe su, hakan ya kara saka cikin su ya duri ruwa, a wannan daren bacci barawo ma bai dauke su ba, can cikin dare suna zaune suna tufka da warwara, dabara ta fadowa Amina, tace Sadiya tashi, na tuno wata dabara, akan ka zauna kana ji kana gani, a kashe ka gara ka tabuka wani abun ko yaya yake, idan ka taimaki kan ka sai Allah ma ya taimake ka.

Hakane me kika tuno, kinga yanzu zan buga kofa nace ina da bukata, kinga kema ai kinje fitsari dazu, ta bayan gidan da bandakin, kuma naga katangar wajen bata da tsaho sosai.

idan muka tafi, naga basa rufe kofar da key kuma kinga dare ne babu motsin kowa a gidan, ke kuma sai ki fito, kina fita, ta jikin window zaki ga hanya, itama hanyar zata maida ke wajen bandakin ne, idan kika je ni kuma nasan abinda zanyi, zamu hadu a wajen ta bayan bandakin, kinga sai mu haura mu fita, naga katangar bata da wani tsaho.

Ke kuma Amina a ina kika san duk wannan, kula nake yi, ance miki haka kawai nake ta cewa ina da bukata, ana raka ni, to ina karewa gidan kallo ne, dan ko dazu, da nace ciki na ne ya baci, ai karya nake, muna zuwa na masa dabara, saida ya dan zagaya baya ya bani waje, shine na leko bayan, naga wannan dayar hanyar, kai Amina baki da kyau, hmmm kinga yanzu bani da lokacin wasa.

Darasin Rayuwa Part (31)
Aisha Muhammad

Tashi tayi taje ta kwankwasa kofar, a lokacin har ya fara bacci, dan haka sai da ta buga sosai sannan yaji ya taso ya bude mata, idon sa cike da bacci ya daka mata tsawar menene, ban daki nake so naje, tace masa, tsaki yayi kai wannan yarinya akwai fitina, gaba daya ta fitine shi, tunda tazo ta hana shi ya huta, shi ba abin yaki raka ta ba, a yanda yake ganin idon yarinyar nan a tsatstsaye zata iya tayi shi a inda suke, koda zai saka ta ta gyara dai yasan sai ya tsaya a kanta, kuma dai ta cuce shi.

Haka ya tasa kyeyar ta suka tafi yana tafe yana dungure ta yana mita, har suka isa bandakin, tana shiga, ya zaga baya kan wani dakali, dan dazu ma data shiga babu arziki sai da yabar wajen, dan wani irin fatattaka da take irin na masu gudawa yasa dole ya koma can baya ya zauna kan wani dakali har sai da tace ta gama sannan ya tashi suka tafi, to yanzun ma can yaje ya zauna, bai san dazun ma da bakin ta ta dinga yi dan dole tasan zai bar wajen.

Bangaren Sadiya ma tana tsaye tana jiran ta tabbatar sun fita fita, da ta dauki wani lokaci ta tabbata zuwa sannan ta tura kofar a hankali ta leko kamar wata barauniya, babu kowa sadaf sadaf take tafiya kar taje akwai wani a cikin gidan ya ji motsi ya fito, tana taku a hankali, bayan gidan ta zagaya kamar yanda Amina ta kwatanta Mata, ai kuwa sai gata ta bayan bandakin, a jikin katangar ta hango Amina tana tsaye daga jikin katangar tana jiran ta.

Karasawa tayi, ta fara fadan ta bata musu lokaci, kokarin kama katangar suka farayi, da kyar da sudin goshi suka samu suka dane katangar, amma fa duk sun daddauje hannun su, haka suka daure wannan zafin, suka zauna sosai akan katangar, sannan suka fara kokarin dira, nan fa ake yin ta, dan ta wajen yafi zurfi, wajen babu ciko shiyasa ya zama kamar rami, Amina ce tayi ta maza ta daddage ta rufe ido ta dira, ai tana dirar nan bata san sanda ta kurma wani uban ihu ba, dan ba karamin zafi taji a kafar ta ba, ta dauka ma ta karye.

Wannan ihu da tayi shi yajawo hankalin wannan mai tsaro nasu, ya taso yayo inda ya jiyo ihun, Sadiya ya hango dare dare akan Katanga, ai tun kafin ya karaso Sadiya ta fara hawaye, ai kuwa yana zuwa hannu kawai yasa babu ko digon tausayi ya janyo ta kasa, ta fado da baki, nan da nan bakin ta ya fashe ya hau jini, amma ko a jikin sa, haka ya juya ya fita yaje ya janyo Amina a kasa kamar wata dabba, fatar ta na daddaujewa, tana kuka amma ko a jikin sa, wajen da ya bar Sadiya ya dawo.

amma bai ganta ba, juyawar da zaiyi ya hango ta da gudu tayi hanyar komawa dakin.

Dariya yayi, yarinya kin kyautawa kan ki dan dana zo na same ki kema haka zan ja ki a kasa, jikin ki ya fada miki, haka ya cigaba da jan Amina a kasa har ya je kofar dakin ya bude ya jefa ta ciki, sannan ya kulle dakin da mukulli ya koma yana mitar wahalar da suka bashi.

Darasin Rayuwa Part (32)
Aisha Muhammad

Dukkan su kwanciya sukai suna maida numfashin wahala, ga wata masifaffiyar yunwa da take sakadar su a ciki, dan dama wannan dan Abincin da ake basu sau daya a rana babu abinda zai musu, yanzu Amina menene mafita cewar Sadiya, bansani ba Sadiya wllh kwakwalwa ta ta toshe, sai dai mu cigaba da gayawa Allah shi yasan yanda zaiyi damu.

Haka suka kwana cikin wannan mawuyacin halin, da gari ya waye, suna jin yanda mutane suke ta dan kai kawo a cikin gidan, daga bakin kofar suka ji, wannan mai gadin nasu yana bawa wani labarin abinda ya faru jiya, dayan yace ai dama da alama yaran nan basa ji musamman wannan yar farar ko idon ta ka kalla kasan bata ji, Allah ma yasa yau da daddare za'a gama musu aiki, badan haka ba sai su bamu matsala.

Alhmdllh dan wllh nima tsoron da nake ji kenan, ai nan da nan cikin su ya bada kulululu, tuni gumi ya fara karyo musu, gaba daya suka fita hayyacin su, innalillahi Allah gare ka muke kuma gare ka zamu koma, Allah ka kawo mana dauki badan halin mu ba, haka suka dinga kwararo addu'oi muryoyin su na rawa, gaba daya sun gama karaya.

Suna cikin wannan halin aka turo kofar, ai Amina sabida tsabar tsorata bata san sanda fitsari ya zubo mata ba, me kawo musu abinci ne ya shigo ya dangwarar musu da kwanon abincin, kamar yanda ya saba ya juya ya fita, duk da irin yinwar da suke ji ada, yanzu sai suka neme ta suka rasa, dan haka ko inda abincin yake ma basu kalla ba.

Suna nan dai zaune har sukai sallar azahar basu samu mafita ba, sai dai basu daina kaiwa Allah kukan su ba, dan sun san shi buwayi ne gagara misali, cikin ikon sa sai ya kawo musu hanyar kubuta, koda kuwa an kai lokacin da za'a kashe sun, da wannan tunanin suka sami dan karfin gwuiwa, har suka samu suka tashi sukai taimama suka yi sallar azahar, haka da suka ga yunwa na neman halaka su, suka janyo kwanon garin nan suka hau ci duk da yanda ya kara bushewa.
 
Suna nan zaune har akayi sallar la'asar, can sukaji ana kokarin bude kofar da mukulli, Allah cikin ikon sa, take wata dabara ta fadowa Amina, hannun Sadiya ta kamo suka koma daga bayan kofar suka tsaya, ana bude kofar wanda ya bude ya fara shigowa, Amina ta daddage ta tattaro duk wani karfi da Allah ya bata, ta hankada mutumin da kofar da yake jiki bai riga ya gama barin jikin kofar ba, ai kuwa yayi kara yayi baya, ya gangara kasa da yake dakin da suken yana akan tudu ne.

Da gudu suka fito suka tsallake shi, yana kwance rike da kai wanda ya fashe sakamakon buge shi da kofar tayi a goshi, ga kofar ta karfe, yana ihu, da gudu suka zagaya ta bayan gidan, suna zuwa sukaga motar ruwa ta kawo, an gama juyewa kenan mai motar suna magana da mai gadi, lallabawa sukayi basu gansu ba, suka shige bayan motar inda aka dora tankin ruwan, kwanciya sukai a jikin tankin suka manne da jikin tankin yanda babu yanda za'ai a gano su.

Darasin Rayuwa Part (33)
Aisha Muhammad

Suna jin sanda mai gadin suke sallama da mutumin yana cewa kamar magana nake ji ana Kira na a ciki bari naje na duba, sallama sukai mutumin ya shiga motar ya tayar mai gadin ya bude masa get, suna jin sanda mai gadin nasu yake ta faman kiran mai gadin get din, shi kuma ce masa yake gani nan zuwa, har suka fice a get din aka maida get din aka rufe.

Wata nannauyar ajiyar zuciya suka sauke a tare, suna addu'ar Allah yasa karshen wahalar ke nan, sun danyi tafiya ba mai nisa ba sukaji motar ta tsaya, gaban su ne ya yanke ya fadi, driver sukaji ya fito ya bude gaban motar, ya dan dade yana dubawa, sai kuma daga baya sukaji ya bude motar har suna addu'ar Allah yasa ta gyaru, sai sukaji yana waya, da alama dai yana neman mai gyara ne, can sukaji yace, to shike nan bari na kara dubawa idan bai yi ba, saina tsallaka din na kira wani.

Suna jin sanda ya fito ya rufe motar, ya koma gaban ya cigaba da yan tabe taben sa, bai dauki lokaci ba sukaji ya rufe, ya bar wajen lekowa Amina tayi taga ya dauki hanya yayi can, lekowar tata tayi dai dai da juyowar sa, a wani mugun sukwane ta koma ta kwanta tana maida numfashi, Allah ya musu gyadar doguwa da bai gansu ba.

Basu kara kokarin koda motsin kirki ba har sai da suka tabbatar ya bar wajen, Amina ce ta fara mikewa ta tabo Sadiya, tashi Sadiya tayi, Amina na kallon ta, ke Sadiya kin ganki kuwa, kinyi wani fututu dake sabida tsabar tsoro bama kisan inda kike saka kanki ba, tsaki Sadiya tayi aike kin sani, kinga ni bani da lokacin kula ki, idan zaki taho mu tafi ki taho idan kuma ke zaman wancan wajen bai ishe ki ba sai ki zauna, ta fada tana sauka daga kan motar.

Sakkowa itama Amina ta yi, tabi bayan Sadiyan, har sun fara tafiya, Sadiya taga Amina ta koma sa sauri, ina kuma zaki, ke ina zuwa, haba Amina wai so kike ki janyo mana bala'i ne ina kuma zaki, ke dallah can ki jira ni, waya zan dauko mana, da gudun ta kuwa ta koma jikin motar, taje ta leka ta window motar, dan ya riga da ya kulle motar, dakyar kuwa hannun ta ya kai ta dauko yar karamar wayar sa dake kan sit din motar.

Har suna hadawa da gudu suka samu suka bar cikin layin, hankalin su bai dan fara kwanciya ba har sai da suka ga sun fita daga arear gaba daya, sannan suka dan sassauta suka fara tafiya a dan nutse, duk da duk wanda suka hadu dashi sai ya kalle su, dan idan ka musu kallon farko zaka dauka mahaukata ne, sabida tsabar yanda suka maguzu gaba daya sun fita hayyacin su, gashi gaba daya sun canja kamanni sakamakon askin da aka musu, dan ma inda Allah ya taimake su, a gidan da Marwan ya fara kaisu, da zasuyi sallah sun dauki hijabai a cikin kayan su suka saka, kuma dasu suka gudu daga gidan, kuma yanzu ma da zasu gudu, basu dade da yin sallah ba, shiyasa yana jikin su basu cire ba.

Sai da suka tabbatar sunyi nisa da wannan arear gaba daya sannan suka samu jikin wata bishiya suka tsaya, Amina tace to Sadiya ga wannan wayar, kinga dai ai ta inda aka hau ta nan ake sauka, dan haka yanzu ki kira Hafiz ki fada masa inda muke yazo ya dauke mu, ya bamu kudin mota, dan insha Allah ni dai yau a gida zan kwana, karbar wayar tayi, dan dama itama abinda yake ranta kenan.

Darasin Rayuwa Part (34)
Aisha Muhammad

Wayar ta karba ta zuba number Hafiz wacce ta gama haddace ta a kwakwalwar ta, dan tun haduwar ta da Hafiz ya kwanta Mata a rai, dan haka komai nasa tana daukan shi da muhimmanci, shiyasa ko daga bacci ta tashi, zata iya karanto maka number Hafiz, sai da tayi ringing ta gama bai daga ba, kana ganin fuakokin su, kasan sun shiga damuwa, bai daga ba saida ta kira sau uku, shima a na ukun tana gab da tsinkewa ya daga, gaba dayan su suka sauke ajiyar zuciya.

Sallama ta masa, shima cikin zumudi ya amsa mata yana jero mata tambayar Sadiya ina kika shige, kin jefa ni a cikin tashin hankalin, babu inda ban neme ki ba, amma sam na kasa samun ki, kukan da ya ji tana yi ne yasa shi, tsagaita korafin da ya ke Mata, Sadiya kamar fa kuka naji kina yi, kukan ta ne ya karu, tama kasa masa magana, shi kuma gaba daya ya rude, Amina ce ta karbi wayar ganin Sadiyan baza ta iya masa bayani.

Sallama ta masa, bai amsa ba, yace yauwa Amina ashe ma kuna tare, dan Allah ki min bayani mai ya sami Sadiya, kaga Hafiz a yanzu bamu da lokacin maka bayani, kawai abinda muke so yanzu kazo ka dauke mu, daga baya zaka ji komai, to yanzu kuna ina, kuna Tasha ne, aa muna wata unguwa dai bamu san sunan unguwar ba, sai dai mu tambaya, to ku tambaya ina jira.

Sai da Amina ta tambayi yara sama da biyar suna rugawa da gudu, da alama ma tsoron ta suke ji, sai daga baya ta samu wani dattijo, shine ya fada mata sunan unguwar da kuma layin, sannan ta masa godiya ta koma inda ta bar Sadiya tana ta faman rafzar kuka, kiran Hafiz din ta kara yi, ta sanar dashi, yace mata insha Allah gashi na zuwa, dama daga wanka ya fito, yanzu zai zo, godiya ta masa ta kashe wayar, tana mamakin kanta wai yau, ita Amina ke yiwa namiji godiya dan kawai ya mata wannan taimakon, wanda ita a baya, babu namijin da ya taba Mata abu ta gode masa idan ba mahaifin ta ba, duk abinda namiji zai mata tana cewa ta kai ne girman ta ne dole ne ma a mata, kai rayuwa Allah ka yafe mana.

Basu dauki lokaci mai tsaho ba kuwa Hafiz ya karaso, ai kuwa shima bai gane su ba, har saida suka masa bayanin Kansu sannan ya gane su, dan dama bai taba ganin su a zahiri ba sai dai a waya, mota ya bude musu suka shiga, har lokacin Sadiya kuka take, Amina ta gaji da bata hakuri ta kyale ta.

Sai suka hau hanya sannan Amina ta fara bashi labarin halin da suka tsinci kansu a ciki, ya tausaya musu matuka.

Darasin Rayuwa Part (35)
Aisha Muhammad

Dan dama a yanda ya gansu yana kage da ya ji abinda ya same su, sai dai baya son suga kamar yana musu kwakwkwafi shiyasa bai tambaye su ba, shi kansa da yaji abinda ya faru dasu, sai da ya zargi kan sa dan yana ganin kamar shi ya jefa su a halin da suka tsinci kansu, hakuri ya fara basu, Amina tace haba Hafiz ai ba laifin ka bane, mu bamu da hankali ne tunda ba dole ka mana kace muzo ba, hasali ma, mu muka nemi hakan a wajen ka, dan haka wllh ka daina zargin kan ka.

Murmushi kawai yayi, yace Allah ya kiyaye gaba, duka suka amsa da ameen, Sadiya ya kalla, ya dai Madam kin gama kukan, murmushi tayi tana rufe fuskar ta, sannan ya juya ya kalli Amina, yaya kawar mu yanzu ai kawai sai mu wuce wajen A A Sa'ad ko, ai tun kafin ya kai karshen maganar sa, Amina ta tari numfashin sa, Allah ya kiyaye, ai ni da dan film ma yanzu munyi hannun riga bare wani film.

Allah ya tsare ni, ai ni yanzu ba Aminan da kuka sani a baya bace, wllh yanzu na tuba, ni yanzu ina komawa gida ma aure zanyi na huta, dariya suka kyalkyale da ita har Sadiya mai kuka, a haba Meena me akai da maza, da dai kin bari na kai ku kun gana da A A, hmm kunga kan ku ake ji, ni dai yanzu daga nan sai Tasha, aa wllh ai kuwa wllh ba ki isa ba, kafin nazo ma sai da na muku booking daki a hotel.

Yanzu muje ku samu ku watsa ruwa, a samo muku kaya ku canja, sannan ku samu ku Dan ci wani abu, dan duk wanda ya ganku ya san kuna tare da yunwa, cab aa wllh duk mun gode, dan fa ni nan daka ganni na dai na yarda da kowa, idan ba iyaye na ba, dan haka kawai ka kaimu Tasha mu hau mota, to ai Malama Amina kin manta da abu daya, ko baza ku tsaya kuyi duk wannan ba, ai kwa tsaya kuyi report akan mutanen da suka sace ku.

Cab wllh na yafe, ni dai na bar su da Allah, kaga fa Hafiz wllh yau duk wani iya kwalo kwalon ka, baka isa kamin wayo ba, idan har kaki amince wa da ka kai mu tasha to wllh kaima zan fara zargin ka, kuma wllh zan iya maka ihu yanzun nan, juyowa yayi yana kallon ta, aa kar ki janyo min jafa'i, Sadiya naga alama wannan kawar taki yar jarfa ce, bari na mata abinda take so, kada ta tara min mutane, hmmm kawai Sadiya tace, dan bakin ta tun tuni yayi laushi, ai kadan ma ka gani, indai Meena ce.

Kan motar ya juya ya nufi kaisu tasha, basu dade da fara tafiya ba, aka kira number Hafiz, dauka yayi ya kara a kunnen shi, bai ce komai ba, dan bai san number ba, bakuwar number ya gani, sai bayan ya daga sannan ya dauki murya, Ashe kai ne, naga number ne da kamar ma bazan dauka ba, amma da yake ina tare da Madam ne kasan ko yaya aka Kira ka baka daga ba, yanzu zasu zargi wani abu.

Ka shigo garin ne, au amma shine baka nemeni ba sai yau, OK ashe yauma badan matsala ba bazaka Kira ni ba, to shike nan kama yi sa'a ina kan titin, bari na karaso, bayan ya kashe wayar ya juya ya kalli Sadiya, wani course mate dina ne, rannan mu kai waya yace zai shigo Abuja idan yazo zai neme ni, shine kinga ashe har ya gama abinda yake zai tafi, bai neme ni ba, sai da matsala ta same shi, matsalar me, wai motar sa ce ta lalace, a kan titin nan, kuma kamar yaji gidan mu yana ta wajen shine fa ya kira ni, wai ko zan hada shi da mai gyara.

Darasin Rayuwa Part (36)
Aisha Muhammad

Yar dariya tayi Allah ya kyauta kawai ta ce, ai kuwa basuyi tafiya mai nisa ba suka hango mota anyi parking dinta a gefen titi, gefen ta suma sukayi parking, sannan ya kira shi a waya, gani na iso,kai ne a gaban mu, a mota, ok, bari nazo, ya fada yana kashe wayar, Amina har ta fara mitar ita fa kar ya bata musu lokaci, maganar ta harde mata a baki lokacin da tayi tozali da wanda take cikin motar, ya fito yana nufo motar su, kara ta kwalla, wanda hakan yaja hankalin Sadiya gare ta, ganin wajen da Aminan take nunawa yasa Sadiyan itama kallon wajen, take itama ta nemi kwala kara, tayi saurin kamo rigar Hafiz wanda ya riga ya fita ihun da Aminan ta kwala ne ma ya saka shi dawo wa yana mata kallon tuhuma.

Hafiz kada ka fita kazo mu gudu, wllh shine wannan, shine, wai shine wa, Marwan shine wanda ya fara sato mu, dan Allah Hafiz ka shigo mu gudu, karasa maganar ta yayi dai dai da karasowar Marwan bakin motar yaji abinda take fada sannan yayi tozali dasu.

Hafiz ne ya juya yana masa kallon tuhuma, Marwan kar dai abinda nake ji gaskiya ne, dama mutumin banza ne kai ban sani ba, amma dai Allah wadaran halin ka, kuma wllh bazan barka ka sha a banza ba, yanzun nan zan kira maka police su tafi da kai, ya fada yana dauko wayar sa da niyyar kiran police din.

Basu ankara ba sukaga ya zaro bindiga daga aljihun shi, ya saita Hafiz da ita, ihu suka saka, ya buga musu tsawa, sannan ya ce musu maza maza su fito yanzu su shiga motar sa idan basa son ya harbe Hafiz din, kuka suka kara fashewa da shi, Hafiz yace dasu kada su kuskura su fito a motar, su dauki waya su kira police, ai bamu da number suka fada cikin kuka, kai ya rike yana jin jina rashin wayo irin nasu, dama fa ya fada ne kawai dan shi Marwan din ai bai san basu da shi ba, hakan zai iya sakawa ya rabu dasu yayi ta kansa, amma gashi sun bata masa aiki.

Dariya Marwan din yayi, haba Hafiz da wai ni zaka tsorata, hhhhh, baka san tun muna makaranta overall nake dauka ba, tsawa ya kuma buga musu, wanda yasa su fitowa da gudu daga cikin motar, suna kuka wiwi suna rokon sa akan ya rabu dasu, amma ko alamar tausayawa babu a kwayar idon sa.

Haka ya tasa keyar su har bakin motar sa, ya bude musu, suna shirin shiga, kawai Allah ya kawo motar police zata wuce, suna ganin abinda yake faruwa, suka fara kokarin yin parking, shi kuma Marwan ganin haka kawai, ya saka bindigar ya harbi Hafiz dan yana ganin gaba daya shine ya lalata masa shiri ya bata masa lokaci, sannan ya juya da gudu da niyyar shigewa motar sa ya gudu, bai kara bi ta kan su Amina ba.

Su kuma police din ganin yana neman tsere musu yasa daya daga cikin su daga bindiga da niyyar ya harbe shi a kafa, kawai ya kauce Harbin ya same shi a kahon zuci, take kuwa ya fadi yana zubar da jini, ihu su Amina suka kara saki dama gashi basu gama farfadowa daga tashin hankalin Hafiz dake kwance a gaban su ba, rai a hannun Allah, kawai suka tsinci Marwan ma a zube a gaban su.

Darasin Rayuwa Part (37)
Aisha Muhammad

Amina da tayi wata shidewa daga nan bata kara sanin inda kanta yake ba, ita dai kawai ta farka ta tsinci kanta a gadon asibiti, ga Sadiya zaune a gaban gadon, kamar mutummutumi, bata uhm bata uhmuhm, sai faman sharar kwalla take wata na bin wata.

Tana farkawa Sadiya, Sadiya, Hafiz ya mutu ko, kai ta girgiza mata, aa bai mutu ba Amina, an samu nasarar cire masa bullet din, yana nan cikin koshin lafiya, to meya saka ki kuka, ba dole nai kuka ba Amina dubi fa halin da muka tsinci kan mu a ciki, kallan mu kamar marasa gata, badan ma Allah ya rufe mana asiri ya kawo mana, Ahmad ba da yaya zamuyi.

Wane Ahmad din tayi saurin tambaya, tana zare ido, Ahmad dai Ahmad din ki wanda ya taimake mu waccen ranar, mai ya kawo shi kuma, ai a cikin wannan motar police din da suka taimake mu ashe har dashi a ciki, dama ba yace miki zai je Abuja, ba, eh haka ne, na shiga uku Sadiya, shike nan dama Ahmad din shine sauran hope dina, idan na koma gida su Abba suka yafe min zance ya fito kawai na aure shi na huta, to gashi shima ya same ni a wannan halin, kuma sanadiyyar rashin ji na, kina tunanin zai iya aure na.

Kai dan Allah Amina ki bar wannan maganar mana, yaya muna cikin wannan halin kina wani zancen aure ki bari ma mana muje gidan a fara yafe mana, sannan kya sako zancen aure, ke dai Amina baza ki taba yin hankali bane, ki san abinda ya dace.

Ta bude baki zatai magana aka turo kofar dakin, hakan yasa dole taja bakin ta tayi shiru, Ahmad ne ya shigo dakin, bakin sa dauke da sallama, Amina ji tayi kamar kasa ta tsage ta shige dan kunya, badan ya riga yaga idon ta a bude ba, har sun hada ido da wllh baccin karya zatai, kujerar dake fuskantar Sadiya yaja ya zauna, Sadiya ce ta fara gaishe shi, ya amsa babu yabo babu fallasa.

Daga haka tayi tsalam ta mike zata fice, har ta kai bakin kofa taji muryar sa, mai cike da kamala da kuma laushi, alamar bai da hayaniya, kamar ba jami'in tsoro ba, yace dawo ki zauna, sum sum ta dawo inda ta tashi ta zauna, tana fiki fiki da ido, juyawa yayi ya kalli Amina, tun kafin yayi magana ta, fara gaida shi, itama amsa matan yayi babu yabo babu fallasa kamar dai yanda yayiwa Sadiya.

Shiru ne ya ratsa dakin na wani tsahon lokaci, meya kawo ku Abuja, ya jeho musu tambayar babu tsammani, ciki aka rasa mai amsa masa tambayar, har saida ya kara maimaita musu, sannan Sadiya cikin inda inda ta fara magana, wllh tsautsayi ne, amma wllh munyi nadama, har abada baza mu kara aikata wani abu makamancin wannan ba, kai wllh gaba daya ma mun daina yin abinda aka hana mu, baza mu kara aikata komai ba sai da yardar iyayen mu.

Shiru kawai yayi ya zuba mata ido, tana magana tana kuka sannan yana hangen tsananin nadama da dana sani a cikin idanun su, tun sanda suka hadu, mamaki yake na me yaran nan suka aikata, amma koma menene tabbas babba ne, gaskiya Allah yayiwa yaran nan rashin ji, iyayen su na fama dasu, kalli randa ya fara haduwa dasu, daya musu nasiha nuna masa sukayi sun tuba bazasu kara ba, kuma harga Allah a lokacin ya dauka da gaske baza su Kara ba, amma yanzu kalli ma a inda ya gansu.

Darasin Rayuwa Part (38)
Aisha Muhammad

Cikin hikima da kwantar da murya ya dinga tambayar ta, har ta masa bayanin komai yanda akai suka zo Abuja da kuma duk abubuwan da suka faru dasu, ta karasa cikin kuka sosai, tana fadin amma wllh mun tuba baza mu kara ba, munyi nadama, dan Allah ka taimake mu ka taya mu rokar mana iyayen mu su yafe mana.

Har zuciyar sa ya tausaya musu, amma sai dai ya kudiri a niyyar sai ya gwarza su tukunna ya tabbatar da sunyi hankali, bata rai yayi sosai, ya hade girar sama da kasa, ai ni na zare hannu na a lamarin ku, tunda bakwajin magana, babu ruwana, aiki ne ya kawo ni garin nan, kuma na gama dan haka a yau zan juya babu abinda ya min zafi da Ku.

Gaba dayan su suka hada baki, dan Allah ka taimake mu kayi hakuri wllh mun tuba, ina ai duk wanda ya tuba dan wuya ba lada, yanzu ma wahala kuka gani, amma yanzu da zamu koma gida a gama muku fada a hakura, bana shakkar sai kun koma halin ku, dan ni abinda ya faru tsakanin mu kadai ya ishe ni shaidar halin ku, dan haka babu ruwana.

Haka suka dinga rokon sa, Amina har kamo kafar sa tayi da sukaga da gaske ya tashi zai tafi ya barsu a garin nan, sai da yaga ya gwarza su sosai sun shiga hankalin su, sannan ya koma ya zauna yana cin magani, umarni ya basu kowacce ta koma ta zauna, amma suka ki, duk suka zo suka gurfana a gaban sa, kamar masu naiman gafara, idan wani ya shigo dakin a lokacin sai yaci dariya, dan shi kanshi daurewa yake dan kar yayi dariya, suga damar sa.

Haka ya maze ya shiga musu fada sosai kamar uban su, daga baya kuma ya juya ya koma nasiha, sai da yaga gaba daya jikin su yayi sanyi, sannan ya kyale su, yace maza su tashi suyi wanka zai fita ya siyo musu kaya, yana dawowa zasu tafi, duk da magariba ta gabato, haka zasu tafi dan baya so ya kara kwana a garin.

Da to suka amsa, ya mike ya fita, su kuma suka tashi, Sadiya ce ta fara shiga tayi wanka ta maida kayan jikin ta, sannan ta dauro alwala ta fito Amina ma shiga tayi tayi wankan tayi alwala ta fito suka tada sallah, suna idarwa Ahmad ya dawo nocking yayi Sadiya taje ta bude, leda ya mika mata yace suyi sauri sannan ya koma ta rufe kofar, ta dawo ciki.

Dogayen riguna ne a ciki guda biyu sai abinci takeaway biyu, kayan suka fara dauka suka sa, sannan suka dauki abincin suka ci a gaggauce, basu ma iya ci da yawa ba sabida yanda yunwa ta gama cinye su, suna gamawa suka tashi suka fito, suna fitowa suka same shi a zaune a reception, inda yake suka karasa suna sum sum da kai.

Mikewa yayi yace muje, bayan sa suka bi, har sukaje kofar wani daki, nocking yayi aka basu izinin shiga, ya tura kofar ya shiga suma suka rufa masa baya, wasu mata ne guda biyu a zaune a dakin, sai kuma Hafiz dake kwance akan gadon, fuskar sa tayi fayau kamar wanda ya dade yana jinya, sun tausaya masa sosai, ganin irin halin daya tsinci kansa a ciki dalilin su, gaida matan sukayi suka musu ya jiki, sannan Ahmad yace su fita waje su jira shi.

Darasin Rayuwa Part (39)
Aisha Muhammad

Bayan sun fita shima ya yiwa matan sallama wanda da alamar daya daga cikin su itace mahaifiyar Hafiz din, kada ku damu Hajiya, likita ya tabbatar mana da insha Allah babu damuwa an shawo kan matsalar, dan haka zuwa safiya ma zai iya farkawa, idan ya farka, dan Allah ga number ta a kira ni, na kara masa sannu, to shike nan, officer mun gode Allah ya kiyaye hanya ya kaika lafiya, ameen nagode Hajiya, daga haka ya juya ya fita.

Daga nan direct tashar mota suka wuce dan abokan tafiyar sa tun tuni suka tafi, basu suka isa gida ba sai wajen sha biyu na dare, rasa inda zai kaisu ma yayi, dan a wannan lokacin bai kamata ya tunkari iyayen su dasu ba, kuma zai kaisu gida ne, bayan yana so ya aure ta, za a iya mata zargin rashin tarbiyya.

Daga baya kawai ya yanke hukuncin kama musu hotel duk da bai so haka ba, amma bashi da wata mafita, dole yaje ya kama musu daki, sai da ya tabbatar sun shiga sannan ya musu sallama tare da gargadin kada su yarda su fita sai yazo da safe, godiya suka masa, bai tsaya sauraren su ba ya juya yayi tafiyar sa.

Su kuma duk da a yau sun samu makwanci mai kyau, amma sun gagara bacci sabida fargaba da tsoron abinda zasu tarar gobe a gida, daga baya ma kawai suka tashi sukayo alwala suka fara nafila suna kai kukan su wajen Allah, akan ya kawo musu komai da sauki, ya sanyaya zukatan iyayen su.

Gari na wayewa aka kawo musu breakfast har daki, basu wani iya ci ba, sabida zulumi, bayan sun gama suka yi wanka suka zauna zaman jiran Ahmad, bashi yazo ba har sai da sukai sallar azahar, Amina har ta fara kulewa, zata fara halin nata, Sadiya ta kwabe ta, aa fa Amina kinga ki tausasa zuciyar ki, kada kiyi abinda bawan Allah nan zaiyi fushi yace ya cire hannun sa akan mu, to ya cire mana uban mu ne shi, aa fa aa fa, nan dai Sadiya tayi ta kwakwkwafar ta har ta samu ta sakko.

Bayan sunyi sallar azahar suna zaune suna jiran tsammani, suka ji nocking, Sadiya ce taje ta bude, tana ganin shine ta dawo ciki ta bashi hanya, ya shigo, bai shigo din ba, sai ce mata da yayi, ku fito mu tafi, daga haka ya juya ya bar wajen, komawa tayi ta fadawa Amina yace su fito, tashi sukai jiki a sabule suka fito, ko wannen su zuciyar sa na lugude.

A reception suka same shi a zaune da waya a kunnen sa da alama waya yake, kusa dashi suka karasa, suna zuwa ya yanke wayar da yake ya mike, Sadiya ce ta mika masa mukullin dakin, ya karba ya karasa bakin kantar hotel din ya basu, sannan yazo ya wuce suka rufa masa baya.

Basu sami damar gaida shi ba har sai da suka shiga mota sannan suka hada baki wajen gaishe shi, ya amsa musu a dakile, gaba daya Amina ta gama zuwa wuya dashi, sai dai babu yanda zatai, dole ta kwantar da kai tunda tana nema a wajen sa, kuma ma tayi alkawarin ta bar duk wani hali nata na rashin ji, tayi alkawarin zama yarinyar kirki, dan haka dole ta fara kokarin kwatantawa tun yanzu, amma badan haka ba, ai wllh da shima bai fara kokarin raina mata hankali ba, kawai ya gode Allah Amina ta canja, tayi kwafa a cikin zuciyar ta.

Darasin Rayuwa Part (40)
Aisha Muhammad

Bata ankara ba taji yayi parking, tana dagowa sai da hantar cikin ta ta kada cikin ta ya bada kulululu da tayi arba da Abban ta ya fito daga gida yana gyara hannun riga da alama alwala yayi zai je masallaci, ko kwakwkwaran motsi ta kasa tayi, tana bin sa da kallo har ya wuce su ya shige masallacin dake dab da gidan su.

Gaba dayan su an rasa wanda zaiyi yunkurin fita, har sai da ya gaji yace dasu, malamai ku fita ku shiga ko, masallaci zan shiga kada na makara, haka dai babu yanda zasuyi, suka fita sum sum, kamar wadan da kwai ya fashewa a ciki, yana kallon su kamar zai fashe da dariya, ya dai maze, a ransa yace dan Allah kalle su kamar na Allah, zuciya fal fitina.

Har aka idar da sallah basu iya shiga gidan ba, a rakube ya same su jikin motar tasa sun makale kamar wasu marasa gaskiya, har zai musu magana, ya hango Abba ya fito daga masallaci, suna gaisawa da wani mutum, karasawa yayi ya gaida Abban, cikin fara'a da sakin fuska Abban ya amsa masa, sannan yayi gaba yana masa iso cikin gidan, ya wuce abinsa kamar ma bai ga su Amina ba.

Abban yana shiga ya karaso inda suke, yana guntse dariyar da take cin sa, ai sai ku tashi mu shiga ko, haka babu yanda suka iya suka bi bayan sa, da sallama suka shiga gidan suna bin sa kamar makaho da dan jagora, ko kadan sun ki yarda su fito fili sai faman mannewa suke a bayan sa.

Manyan tabarmi ne guda biyu a shimfide a tsakar gidan, Abba ne zaune da Kawu Bala sai Mama, da Liman din unguwar wanda ya kasance makwafcin su, sai Umman Sadiya da wata yayar ta, da alama dai an san da zuwan nasu, ashe abinda basu sani ba, da safe da Ahmad ya tashi gidan su Sadiya ya fara wucewa yayi sallama da Maman ta, da yake mahaifin ta ya dade da rasuwa.

Bayan ta fito ya fara gabatar mata da kansa a matsayin dan sanda sannan yazo ne akan yarinyar ta Sadiya, bayani ya fara mata, kafin ya fara mata wani bayani tace tana zuwa, ciki ta shiga bata jima ba suka fito tare da wata mata, da alama yayar ta ce, nan dai ya fara musu bayani, ran Umman ya baci, tace dan Allah ya barta bata neman ta taje duniya zata koya mata hankali.

Dakyar suka hadu da wannan yaya tata suka samu suka shawo kan su, sannan ya roki alfarmar, suzo suje gidan su Amina yana so ya kawo su nan, su hadu su musu fada da nasiha, sannan a hadu wajen bawa mahaifin Amina hakuri dan taga alamar babu wasa a tattare da mutumin sannan ko yar tasa yaga yanda take tsoro da fargabar haduwa dashi.

Da Umman Sadiya taso taki amincewa daga baya dai yar uwar ta ta shawo kan ta sannan ta amince, ya dauke su a motar sa har gidan su Amina, to anan ne fa aka sha fama da mahaifin ta yaki amincewa dan yace shifa ya manta yana da wata ya, taje can ta nemi wasu iyayen amma basu ba, idan kuma mahifiyar ta tace zata bi yar ta to ga hanya nan, bai rike ta ba.

Darasin Rayuwa Part (41)
Aisha Muhammad

Babu yanda basu yi da shi ba, har Kawu Bala ma yayi yayi amma yaki daga baya ma fushi yayi yace ya nuna masa Amina ba yar sa bace, amma fur yaki yarda, dama taurin kan Amina wani lokacin yan uwan Abban kan ce na mahaifin ta ne, daga baya ma tashi yayi ya bar musu wajen, dabara ce ta fadowa Mama, tace a kira Liman yana matukar girmamma shi da kuma jin maganar sa.

Hakan kuwa akayi, Ahmad da kansa yaje yayi sallama da Liman ya masa bayanin komai, Liman ma bai ji dadin hukuncin da Abban ya yanke ba, ace ka kori yar ka wannan ai ba dai dai bane, muje gidan, haka Liman ya biyo shi, aka kira Abba nan fa ta inda ya shiga bata nan yake fita ba, ya zage ya masa fada irin na girma da yake idan bai haifi Abban ba tofa tabbas zai girme masa ba kadan ba.

Sannan daga baya ya juya ya koma nasiha, har saida yaga jikin Abba yayi sanyi, yace amma dan Allah Malam a min wata alfarma, muna sauraran ka, a gaskiya abinda yarinyar nan ta min ya bakanta min rai, dan haka gaskiya bazan yarda ta dawo mu cigaba da zama da ita a cikin gidan nan ba, dan ni na haifi Amina nafi kowa sanin halin ta, wllh ina mai tabbatar muku Amina bazata fasa abinda na hana ta ba, ni kuma wllh idan ta Kara min kuskure guda daya zan iya tsine mata, subhanallah duk suka hada baki wajen fada, aa bama za'ai haka ba, yanzu meye kake so.

Yauwa na yarda Amina ta dawo gidan nan amma bisa sharadi daya, baza ta kara min sama da wata daya a cikin gida ba, ta fito da miji na mata aure ko nima zan huta, nan da nan, Ahmad yayi tsalam, ummhh wato Abba a gafarce ni ba wai na tari numfashin ka ba ne, amma ina ganin indai wannan ne babu matsala, ni zan auri Amina koda nan da sati daya ne idan ka bani dama, take da Liman da Kawu Bala suka yi kabbara.

Shike nan ma komai yazo ta gidan sauki, kai dai yaro Allah yayi maka albarka, ameen duk suka amsa dashi, Liman yace amma wani hanzari ba gudu ba, babu yanda za'ai kace wai wata daya, kadai yi hakuri ya turo iyayen sa daga nan kuma duk yanda abu ya kaya kuma sai ayi shi, Allah ubangiji, ya kara shiryar mana da zuri'a kowa ya amsa da Amin.

Tashi Liman yayi bari ni zan shiga gida, idan an zo da yaran sai a min magana, to min gode Malam Allah ya kara girma, Mama ji tayi kamar an wanke mata duk wannan bacin ran da ya ke damun ta, wannan kenan.

shiyasa sanda su Amina suka shigo suka same su a zazzaune suna jiran isowar su ne, Liman ma basu lura da wucewar sa bane da yake hankalin su baya jikin su, amma sanda suna kofar gida ya wuce ya shigo gidan nasu.

Sallama Ahmad ya kara musu sannan ya nemi waje ya zauna, suma sulalewa sukai suka zauna a kasa daga gefe suka tsakure, kana ganin su kaga marasa gaskiya, gaishe su Ahmad ya sake yi suka amsa masa da kulawa, su Amina ma murya a can kasa suna sunne kai suka gaishe su, amma daga Abba zuwa kan Mama da Umman Sadiya babu wanda ya amsa, kowa yana kallon su aka dai kyale su, dan an san bacin rai ne kawai, amma zasu sakko, dan tsakanin da da mahaifin sai Allah.

Fada aka shiga musu tare da nasiha, wannan yayi ya bawa wannan ya karba har aka zo kan Liman, shima ya musu nashi fadan tare da nasiha mai ratsa jiki wacce ba iya su Amina ba dukkannin wanda ke wajen sai da nasihar ta shige shi, har yasa iyayen nasu kara sakkowa daga fushin da suke yi dasu, sannan daga baya Liman da kan sa ya sallami su Amina yace su tashi su shiga daga ciki.

Darasin Rayuwa Part (42)
Part din Karshe
The Last Part
Aisha Muhammad

Bayan shigar su, ne Liman ya kara samun dama ya kuma yiwa iyayen nasiha, akan yanda ya kamata idan yaron ka baya jin magana ka tafiyar dashi, kamata yayi ka kara janyo shi a jiki maimakon janje shi da zaka nayi a jikin ka, hakan ne zai bashi damar fadawa wata hanya da daga baya zaka kasa tafiyar dashi, wanda kai da kanka ka jefa shi a cikin wannan hanyar, sabida da ka jashi a jiki ka maida shi abokin ka da bai samu damar zuwa waje ba ma balle ya aikata abinda zaka zo kana ya za kai, da haka ya kara jan hankalin iyaye da suyi kokari wajen mayar da yaran su abokan su, hakan ne zai bawa yaran ka damar kasancewa da Kai a ko da yaushe, dan haka duk wata shawara tasu kafin su fara tunkarar wani da ita ku zasu fara tunkara da ita, kuma sai ku san ta hanyar da zaku bi wajen hana su abin idan ya saba da naku tsarin ko na addini, Allah kasa mu dace.

Da wannan Liman ya rufe musu taron da addu'a tare da ban hakuri ga iyayen, ya musu sallama, godiya dukkan nin su suka masa dan ba karamin dadi da kuma nusar dasu abinda suka manta nasihar tasa ta musu ba, fita yayi yana kara addu'ar shiriya ga yaran.

Suma su Umman Sadiya mikewa sukayi suka musu sallama aka kira Sadiya suka tafi, ya rage daga Abba sai Kawu Bala da Mama, dan shima Ahmad tare suka fita da su Sadiya, kiran Amina Kawu Bala yayi, nan suka kuma saka ta gaba da nasiha da jan hankali, akan yiwa iyaye biyayya, sosai suka kara mata fada tare da nasiha, kuma da alama abinda ake fadan yana shiga kunnen ta, dan gaba daya kana ganin ta kasan tayi nadama.

Bayan sun gama ne itama ta samu damar rokar gafara akan duk abinda ta taba musu, nan suka ce dama su basu taba rike ta a rai ba, duk abinda suke mata suna yi ne dan barazana, amma a zuciyar su kullum addu'ar shiriya suke mata, nan ta musu godiya, tare da alkawarin ta amince su zaba mata miji kuma ta musu alkawarin ko waye suka zaba mata zata musu biyayya, sosai suka ji dadin furucin ta, suka ce insha Allah kuwa baza su mata zaben tumun dare ba.

Bayan wata uku, mata ne makil cike da gidan su Amina sai faman guda ake da shewe shewe, ga akwatina nan a gaban su, saiti biyu ko wanne, me hudu, kuma cike da kaya na gani na fada, sai dubawa ake ana san barka.

Wata kanwar Mama ce ta zo shiga dakin Maman tayi kicibus da su Amina ita da Sadiya a bakin kofa suna leke, baki ta rike tana sallallami, yanzu dan Allah yaran nan me kuke so ku maida kanku babu kunya dama yau ana kawo lefen ki amma anyi anyi dake ki bar gidan nan kin ki, shine yanzu ki bari ma masu kawo kayan su tafi kin kasa hakuri sai kin labe bayan labule kina leke, to Allah ya shirye ku, marasa kunya, su dai kus sukai har ta gama mitar ta ta bar dakin.

Tana fita suka saka dariya, suka tafa, Sadiya tace ke kawata wllh kinyi goshi irin wannan uban kaya haka, gaskiya Ahmad yayi kokari, ya can canci yabo, nima dai Allah yasa Hafiz ya fitar da ni kunya haka, kema kinsan zaiyi, shida zai yi auren fari, sannan kuma gashi dan Abuja, ta fada da sigar zolaya, dariya sukayi dukan su suka tafa, daga nan Amina ta dauki waya ta kira Ahmad wai ta masa godiya tare da jinjinar ban girma, babu yanda Sadiya batayi ba ta hana ta, amma fur taki hanuwa, daga baya itama ta kyale ta, tace ai wannan Ahmad zai yi kallon rawar Kai.

Tammat bi hamdullah, anan muka kawo karshen littafin mu mai suna DARASIN RAYUWA, muna fata sakon da muke son isarwa ga al'umma ya je, Allah ya kara shirya mana zuri'a.

Wannan labari kagaggen labari ne, ba muyi dan wata ko wani ba, idan labarin yayi karo da wani bangare na rayuwar ka, muna masu baku hakuri, abinda muka rubuta ba dai dai ba Allah ubangiji ya yafe mana.

Bissalam.