 |
*💫TSANTSAN SO.💫* |
*Ep One.*
*💫TSANTSAN SO.💫*
*The Pure Love.*
*LAFAZI WRITER'S ASSOCIATION.*
___________________
*~Paid book 500₦~*
```_-_❣️Life with Destiny, Struggle, Inclination, Merciless, suffering, Excruciation, and Negate Pure Love.❣️_```
_________
*Tsokaci...🧏*
*Khadeejarth Sabi'u Yahyah Kaduna (Nainarh KD.) Ina Godiya ga Ubangiji da ya bani ikon kammala Novel nawa SARAUNIYAR KYAU (👑Queen Of Beauty. 👑) Gashi ya nufa mun sake haɗuwa a wannan labari Tsantsan So (❣️Pure Love. ❣️) Allah Ubangiji ya ikon rubuta abin da yake daidai cikin wannan labarin kuma abin da zai amfana al'umma baki ɗaya.*
*Labarin Tsantsan So ƙirƙirarren labari ne da ya kafu bisa salon da Marubuciyar ta ƙirƙira sannan Paid Book ne (500₦ Only) But Akwai Free Page's Sai dai ba zasuyi yawa ba.*
___________
*Gargaɗi...✖️✖️*
*Marubuciyar bata yarda da kowa da ya canza ma ta salon labari ba ko ta wata si ga ba. A kiyaye sannan a girmama juna Dan Allah.*
_________
*Tunatar wa...😊*
*Ana rubutu ne domin ci gaban al'umma, domin masu wani hali ko wata ɗabi'a da bai dace ba. Da su gane cewa basa kan hanya ta daidai kuma da fatan su gyara halayen nasu. Kuma domin samun nasara a rayuwar al'umma. Muna fata sanadin rubutu al'umma da yawa su ƙaru kuma su canza daga halayensu da basu dace ba. Allah Ubangiji ya bamu ikon rubuta abin da yake daidai Jinjina ga Marubuta na Duniya Gaba ɗaya...🙏📚✍️✊📚*
__________
*Daga Alƙalamin Nainarh KD✍️*
*👑From The Writer Of The Queen Of Beauty.👑✊*
*Dedicated To Princess Teemarh [Star Lady.]💋*
*Ep_One.*
"Ita ce fa wannan Budurwar jikar Mai martaba Sarkin mu da tazo daga ƙasar waje kwanaki biyu da suka wuce."
Ya yi maganar wa abokin nasa da ya yi masa tambayar gaba ɗayan su kowanne yana kuma hangame baki wurin kallon kyakyawar fuskarta da kuma haɗaɗɗiyar surar da Ubangiji ya azurtata da shi.
Outfit dake jikinta normally Jean's ne sai kuma Riga Top white ta ɗaure rigar sanyi a ƙugunta ƙafafunta sanye da Boots irin na fita training na safe ga dukkan alamu daga training take. A hankali take lumshe kyawawan idanunta yayin da take ƙara buɗe su. Hannu takai tana gyara gashin kanta da ya leƙo tana ci gaba da faɗi cikin daddaɗar Muryarta mai daɗin saurare.
"Tabbas ba son gaskiya yake miki ba shawara anan ita ce ki rabu da shi Allah ya haɗa kowa da rabon sa."
Ta ƙari sa maganar sannan ta gyara Bicycle nata tana faɗin.
"Ohya Teema zo mu wuce."
"'Yar uwa na gode sosai da shawara kuma in Allah ya yarda na rabu da shi har abada, dama tun tuni nake zargin ba tsakani da Allah yake ƙaunata ba."
Kallon Yarinyar tayi ta ce.
"Ina miki fatan haɗuwa da wanda ya fisa kuma mai ƙaunar ki da gaskiya domin akasarin mazan yanzu ba tsakani da Allah suke tare da mace ba sai dan cika wasu burika nasu, sai dai matan basa ganewa domin ruɗin Duniya rufe musu ido yake yi. Nayi farin ciki da ke kika fahimci hakan."
"Wannan gaskiya kika faɗa 'yar uwa domin kaso 80 na samarin yanzu ba tsakani da Allah suke tare da Budurwa ba sai dan cika wani buri nasu cikin su kuwa harda wannan tur da Irin wannan Rayuwar."
Tayi maganar tana nuni da saurayin nata cike da tsanarsa domin yau ya nuna ma ta Asalin kalansa.
"Toh tun da an gama komai kowa sai ya watse ko. Su Labib ɗan gayu harda Kai ne a hangame baki to a gyara dai kafin ƙuda ya shige."
Budurwar da ta kira da Teema tayi maganar tana kallon gaba ɗaya mutanen wurin da suka tattaru ana kallon abin da ke faruwa. Sannan ta hau Bicycle ɗin kana ta fara tafiya da su suka bar wurin.
"HHhH Lallai ma wannan Teema ko yaushe bakin ta ya buɗe da zata dubeka ta gaya maka magana, amma fa kaima ka bani Dariya Kawai daga ganin wannan kyakyawar Baturiyar Budurwar da tazo Garin nan sai ka nema ka kasa controlling kanka kodai.."
Katsesa ya yi da faɗin.
"Kodai Mene karma ka fara wannan tunanin domin kafi kowa sanin Hazel ita ce kaɗai a zuciyar Labib ko dai ka manta ne?."
Ɓoye dariya Abokin nasa ya yi suna ci gaba da tafiya ya ce.
"A'a kam ban manta ba Aikuwa ga ta can ma mutuniyar taka sai ka ƙari sa kuyi irin gaisuwar taku da kuka saba Kullum."
Ya yi maganar yana masa nuni da ita da take tsaye daga can cikin jama'a 'yan kallo, ganin kowa ya watse ne, yasa ta gyara Book's ɗin dake a hannunta ta rungume su a chest nata sannan ta fara tafiya a hankali cikin nutsuwa kamar yadda ta saba tana kare fuskarta daga hasken Rana da ta fara ɓullo wa kaɗan.
Da sauri ya ƙari sa saitin ta kamar yadda ya saba a kullum sannan ya ciro handkerchief daga trouser pocket nasa kana ya fara tafiya yana goge gumi idanunsa na kallon ƙasa.
Yau ma kamar kullum karo da taji tayi da mutum ne yasa cikin sauri ta ɗa go kanta domin ganin ko wanene.
"I'm so sorry Bro sauri nake yi na tafi school domin nayi late sosai shiyasa nayi karo da kai, ba tare da na sani ba, amma ina mai baka haƙuri."
Tayi maganar silently tana sauke idanunta ƙasa daga kallon sa domin ta fara gajiya da karo da suke yi a Kullum kuma ita ke basa haƙuri har hakan ya sa ta fara insulting wani abu kamar dai...
"Oh ni Labibu naga alama fa kamar ba son ganin na biyo hanyar nan kike ba Kullum ke ke nan cikin tafiya idanun ki na kallon sama wasu lokutan kuma ƙasa sannan duk ƙoƙarin guje miki kar muyi Collision da nake yi a banza domin Kullum sai mun buga karo an ya kuwa?..."
Ya yi Maganar yana ɗan Murmushi tare da nuna ta da yatsa.
"I'm so sorry ba wai da wata manufa ba ce kaji late nayi Shiyasa nake sauri har mukayi karo amma ina mai baka haƙuri."
"Tohm shikenan babu damuwa na haƙura amma da sharaɗi."
Cikin sauri ta katse sa da tambayar.
"Menene sharaɗin Bro Ina jin ka Please?."
"Okay ba yanzu ba, idan gobe kika kuma karo dani shi ne zan faɗa sharaɗin. Kiyi kokari kar gobe mu kuma yin karo a hanya."
"Toh na gode."
Ta faɗa tana raɓa wa ta gefansa sannan ta wuce.
_______________________________
Duk irin kira da ya yi ma layin ba'a ɗauka kuma tana ringing bai san dalilin ba yaji ya shiga damuwa na rashin amsa Call nasa da Arissa barayi ba. Gyara training Bicycle nasa ya yi sannan ya ɗauki hanya domin zuwa gida.
____________________________
"Am Teema kike ko?."
"E Anty haka sunan nawa yake Teema sai dai an fi sanina da kuma kirana da Teema Silent."
"Okay."
Ta furta tana shan kwanar hanyar da zata kaita har gidan mai Martaba Sarki. Sannan ta ci gaba faɗin.
"Am yanayin Garin naku ya burgeni sosai, ina ga zuwa da yamma, zaki rakani domin yawatawa domin na zagaye garin na bawa ido na haƙƙinsa."
Ɓoye dariya Teema tayi ba tare da ta ce komai ba.
"Kamar dariya kikeyi ko?."
"E, mana Anty ai Dariya maganar ki ta bani, keda kikazo daga ƙasar America shi ne kike cewa wannan Garin namu ya burgeki, shi ne abin ya bani Dariya."
"Allah Sarki. Ai America daban haka ma nan ma daban ko wanne da irin shauƙi da nakejin kaina idan na kasance a ciki, kinga kamar nan yana tunamin da Yarinta na ne can kuma a can na tashi na girma nasan kaina."
"Anty ke nan ai duk da haka America ta daban ce kowa dake nan burinsa ke nan zuwa America ciki kuwa har dani. Wai ma Anty menene Sunan ki ne ma nifa ban sani ba?."
"Okay kina da Burin zuwa America ke nan. Tohm Ubangiji ya cika miki Burin na ki."
"Ameen ya Allah."
Teema ta amsa tana dariya cike da farin ciki.
"To Anty baki faɗa min Sunan ba nima ban sani ba kuma ance tun shekaran jiya kike a Garin nan amma ban samu na haɗu dake ba sai yau da yake bana fitowa ne kwana biyu saboda jikin Mamana ya tsananta shiyasa ba kullum nake fitowa gidan Sarki domin aiki ba. Kwatsam kuma yau da Asuba da naje shi ne na haɗu dake har Hajiya Bilkisu Uwar gidan mai Martaba Sarki take cewa na rakoki training na safe da kuke zuwa irin naku na Turawa."
Murmushi tayi kaɗan domin maganar Yarinyar ya bata dariya sai dai da yake ita ɗin ma'abociya wurin yin Murmushi ne yasa tayi kaɗan tana faɗin.
"Teema ko lallai kina da taɗi. Har na fara insulting kiran ki da Teema Silent da kikace ana yi."
"HHhH Anty ke nan Allah bani da surutu ko hayaniya Kawai kece da jinin mu ya haɗu shiyasa ma nake miki surutun."
Zata yi magana bayan shigarsu Babban gate na Gidan daidai lokacin wasu tsalatsalan motoci na alfarma guda uku suka shiga gidan daidai parking lot suka yi parking sannan mutanen ciki suka fara fitowa bayan wasu mintoci da yin parking ɗin.
"Oh Allah kamar a mafarki Mommy Asfiya Uncle Junayd ga kuma Hamrarh da Amrarh wayyo nayi farin ciki sosai ashe kuma kuna hanya?."
Tayi maganar tana ƙari sa wurin sannan tayi hugging nasu ɗaya bayan ɗaya fuskokin kowannen su ɗauke da fara'a Budurwar ɗaya cikin Biyu da ta kira da Hamrarh da Amrarh ta amsa ma ta da faɗin.
"Sameera Adila Dina wow yaushe rabo gaskiya nayi missing naki sosai sosai fa."
Murmushi tayi tana kamo hannunta ta ce.
"Ai Hamrarh nima nayi kewarki sosai sisterna an daɗe ba'a haɗu ba. Ina fatan kun ƙari so lafiya Uncle Judge Barka da Hanya."
Ta ƙarishe maganar tana komawa ga Uncle ɗin nata tana kuma hugging nasa fuskarta ɗauke da Murmushi. Yayin da Teema tayi tsuru a gefe tana kallon su cike da sha'awa sosai suka burgeta.
" 'Yan Gayu kunji daɗin ku."
Ta faɗa ƙasa ƙasa tana Dariya.
"Nayi fushi ma tunda an manta dani."
"Oh sorry sorry Mommyna ta kaina ina zan manta dake Mahaifiyata guda ina fatan kun ƙariso lafiya mu shiga daga ciki Please."
Tayi maganar tana Karisa wa wurin Amrarh sannan ta riƙe ma ta keken da take zaune akai Irin na guragu waɗanda basa tafiya. Suna gaisawa da Amrarh ɗin da yake Bata da son hayaniya shiyasa bata ce komai ba, lokacin da suke gaisawa. Sannan suka nufa cikin katafaren gidan mai Martaba Sarki Muhammad Raees.
Miss Asfiya ta ce.
"Aina ɗauka 'yan shekarun da muka yi Bama haɗuwa har kin Manta dani ne da kuwa kin ga fushina a yau."
Saita zaman Bicycle ɗin tayi a cikin katafaren parking lot na gani na faɗa dake cikin gidan gefan wurin da take tana jin tana bata amsa.
"Sameera Adila Dina..."
Ta maimaita Sunan sosai ya yi ma ta daɗi kuma taji sunan ya dace da ita musamman da ta lura tana da kirki.
_______________________
"Althaf yi sauri ka tafi anjima zamu haɗu ga Yayana nan zuwa, Bye."
Sauri sauri ta gyara tsayuwar da nutsuwar ta ba tare da ta amsa sallamar da ya yi ma ta ba. Sannan ta nufe sa.
"Lah Yayana har ka dawo ke nan daga training ɗin?."
A nazarce ya kalleta ya shafa kanta tare da murmushi ya ce.
"Na dawo Cutie daga ina kike haka da safiyar nan?."
Sai da gaban ta ya faɗi jin tambayar da ya yi ma ta. A tunaninta ya hangota tare da Althaf ne. Da kyar ta daure ta ce.
"Ah Yayana daga Tahfiz mana ko ka manta yau Friday ne Akwai Tahfiz na Safe."
"Okay. Na tuna ina fatan kun yi karatu mai yawa kuma kin fahimci komai na karatun?."
"E, Yayana idan ma naji na manta wani wuri ai ina da kai zata koyamin na sani."
Ta faɗa tana Dariya da ya bayyana Dimples nata. Kyakykywa ce sosai Yarinyar sannan ba zata haura shekaru Goma sha shida zuwa sha bakwai ba.
"Good Girl baki da matsala yanzu mu shiga daga cikin gida ki bani Labarin abin da ya faru a Tahfiz ɗin."
"Tohm Yayana baka da matsala."
Ta faɗa tana sauke ajiyar zuciya kaɗan tare da furzar da iska na farin cikin bai hangota da Althaf ba. Suka shiga gidan...
_-_*Like Share Comment and vote 🙏💖 _-_*
____________________________________________
*_-_ For any and more information_-_*
*My WhatsApp Countact (08081129487 Or 07085212808)_-_*
*💫TSANTSAN SO.💫*
*The Pure Love.*
*~Paid 500~*
*What'sapp Countact*
* 07085212808*
*Daga Alƙalamin Nainarh KD*
*The Writer Of Queen Of Beauty👑✍️.*
*Dedicated To Princess Teemarh [Star Lady.]💋*
*Ep_Two.*
"Ke! Ke! Mamana menene kika dawo yi anan gidan ko har kin gama aikin naki ne wai ma bakiji irin kalamin da nayi Miki kafin ki tafi ba ne da zaki dawo mana gida Yanzu da safiyar nan?."
Shiru tayi tana daga tsaye tsakiyar gidan nasu da ko arzikin siminti na ƙasa babu hatta ga jikin bangon gidan yaɓe ne na jar ƙasa, ban da kyaf kyafta ido babu abin da take yi tare da turo baki ba tare da ta ce komai ba, tana ji ya cika gaba da sababin, idan da sabo ta saba da irin halin Mahaifin nata na shegen son abin Duniya.
Sai da ya gama surfa ma ta tsiya son ransa tana tsayen yayin da Mahaifiyarta ke daga gefe ta zuba ugan tagumi ba ta ce komai ba, domin tasan tana furta wani abun kanta zai dawo. Har sai da ya gaji dan kansa sannan ya yi shiru, sai kuma cikin sassauta Murya ya fara faɗin.
"Mamana kin gama aikin naki ne a gidan Sarkin da kika dawo da wuri haka?."
"E, Baba na gama ne shiyasa na dawo kuma wannan Baturiyar da a ka ce tazo daga America ta ce zan rakata domin ta zagaye Garin nan. Yauwa Sunan ta ma Samira.. e haka ne amma sunan guda uku a haɗe ko kuma mai daɗi na manta sauran."
"Yauwa Ɗiyar albarka yanzu abin da nakeso dake shi ne ki ci gaba da maƙale ma ta ko'ina zata je cikin garin nan kuna tare kinji Mamana?."
Ya ƙari sa maganar cikin sakin Dariya haƙoransa da suka dafe tsaban cin goro suka bayyana.
Da mamaki ta ce.
"Saboda me ke nan Baba me yasa zan maƙale ma ta ɗin ko'ina muna tare?."
"Kajimin mara yawon Yarinya mana, yo idan kina maƙale ma ta ko'ina kuma kina yawan bata labarin mu da irin talauci da muke fama da shi kika sani ko sanadin haka ta tausayamin ko Hakimi a bani. Ke Yarinya ce ba zaki gane komai ba koda nayi miki bayani"
Fashewa Teema tayi da dariya har da buga ƙafa jin ta inda ya ɓullo wato Hakimi cabb.
"Tohm Babu in sha Allah zan yi iyakar ƙoƙarina kan hakan."
Ta faɗa tana saita kanta ganin wani mugun kallo da yake bin ta da shi.
Cikin zuciyarta kuwa faɗi take.
"Chabbb lallai ma wannan Baban yo Ina ga ko Dogare ma ba za'a baka ba balle kuma Hakimi."
"Yauwa 'yar albarka wannan ita ce mai Sunan Mamana in miki na turawa suka ce that's my daughter."😅
Ya faɗa cikin washe baki Ganin bakinta na motsi ne ya ce.
"Mene ne abin da kike cewa."
Da sauri ta ce.
"A'a Baba cewa nayi Allah ya taimaka daga Hakimi ka zama har Sarkin garin nan ma."
"Ja'ira Kawai."
Ya furta yana sa kai ya fice daga gidan.
"Mama kinji wannan mijin naki wai Hakimi Lallai ma."
"Fateema ke nan ki dena biye masa ma fa."
"HHhH Mama ai kawai kallon sa nake. Amma ya jikin naki?."
Ta tambaye ta cike da kulawa.
___________________________________________
*CAIRO INTERNATIONAL AIRPORT.*
Tana tsaye daga harabar airport ɗin daura da wurin da a kayi da rubutu jikin allo mai launin ruwan ɗaurawa da manyan baƙi NEW ARRIVALS.
Hannu takai tare da cire Glasses dake idanunta tana kare fuskarta daga hasken Rana. Sannan ta ƙari sa wurin iyayen ta da suke tsaye kowannen su fuskarsa ɗauke da farin ciki na kammala karatun ta da dawowarta garesu. A tare tayi hugging nasu cike da farin ciki take faɗin yadda tayi missing nasu.
"Baby Ambrah Yarinyata kin kammala karatun ki cikin Nasara gashi kin dawo gare mu sosai nayi farin ciki da kasancewar hakan."
Murmushi tayi kaɗan tana faɗin.
"Abhie na! finally am back and nayi kewarku sosai sai dai bai kai rabin yadda nayi kewar Bro Taufan nawa ba, idanuna babu abin da suke da muradin gani a halin yanzu fa ce su yi karo da kyakyawar fuskarsa, sai naji gaba ɗaya na ƙosa mu tafi gida na huta sannan na shirye na wuce kai tsaye zuwa gidan General Tajudeen Ozan domin nayi arba da sahibina."
"Yanzu dai ba wannan ba tukunna finally you are back saboda haka mu shiga Mota Domin zuwa gida koma menene ya biyo baya."
"Okay, Oum na."
Ambrah ta faɗa sannan gaba ɗaya suka shishshiga cikin motocin nasu suka bar Airport ɗin tare da Guards kai tsaye har suka ƙari sa zuwa gidan katafaren gidan Prof... Yusuf El_ Mustapha ke nan shararren mai dukiya na ƙin ƙarawa kaf Yankin Egypt da kewaye kuma tsohon professor ne a Babban University dake Cairo. Matarsa ɗaya tal wato Dr Aadnah Taj Ozan sun kasance yarinyar su ɗaya tilo Ubangiji ya azurtasu da ita wato Ambrah Yusuf El_ Mustapha shekarunta Ashirin da ɗaya ta kammala karatun ta a ƙasar Jamus ɓangaren tattalin arziƙi.
Prof... Yusuf El_ Mustapha da Matarsa Dr Aadnah Taj Ozan sun kasance suna masifar son wannan tilon Ɗiyar tasu Ambrah kyakyawar Balarabiyar Budurwa mai ji ƙuruciya ga kyau ga kuma Dukiya suna son ta fiye da komai na Rayuwa domin ita ce ma Rayuwar tasu Yayin da gaba ɗaya tunanin Ambrah da Soyayyarta ta ɗaura a kan Taufan jika wurin General Tajudeen Ozan sannan kuma Mahaifinsa Ali Taj Ozan Yaya ne a wurin Mahaifiyar ita Ambrah ɗin. Ambrah tana matuƙar son Taufan fiye da komai domin har karatun ma da kyar ta tafi wata ƙasar ta zauna ba tare da tana a kusa da shi ba. Finally gata ta dawo kuma Brother Taufan nata har yanzu yana ran ta. Bata da wani Buri sai ganin kyakyawar fuskarsa da shi kansa.
Domin
"Wai kuwa baka ganin akwai ƙura a ƙasa Ambrah ta dawo gashi Taufan baya ƙasar ma gaba ɗaya ni tsoro ma nake a kan abin da zai iya biyo baya."
Ajiyar zuciya ya sauke jin maganar ta sannan ya kamota ta zauna kusa da shi gefan Bed ɗin. Tabbas gaskiya ta faɗa akwai ƙura idan Ambrah ta fahimci Taufan fa baya nan.
"Nasan da duka waɗan nan sai dai ina ga kin manta wata ɗaya kacal ya rage Shekara ta cika da hakan yake nuni da Taufan ya kusa dawowa ke nan."
Da sauri ta kallesa fuskarta na wadatuwa da ƙayataccen Murmushi sam ta manta ma sai yanzu da ya faɗa.
"Kin ga yanzu sai mu san yadda zamuyi da Ambrah har nan da one Month before Taufan ya dawo musha shagali biki irin wanda ba'a taɓa yi a Cairo ba kuma ba za'a taɓa kalansa ba."
Shiru tayi Murmushin dake fuskarta bai ɗauke ba sai dai tana nazarin wannan lamarin ba tajin koda Taufan ya dawo zai amince da Ambrah matsayin Future wife tasa domin tsayin lokacin nan a matsayin Ƙanwar sa Kawai yake kallon ta ba da wani matsayin da ya wuce wannan ba.
General Tajudeen Ozan ya kasance tsohon soja ne kuma haifaffen ƙasar Egypt Mazaunin Cairo yana da mata ɗaya Dr Shazam Taj Ozan. Yaransu Biyu a Duniya Ali Taj Ozan shi ne Babba yana da yara Biyu Taufan sai kuma Arissa da suke kira Cutie. Matarsa mai suna Aamalah ta rasu shekara ɗaya baya sanadin ciwon Cancer matakin ƙarshe. Sai kuma Dr Aadnah Taj Ozan da ta biyo Mahaifiyarsu ita kuma 'Ya ɗaya tilo gare ta wato Ambrah. Tun lokacin da Aamalah Matar Ali Taj Ozan ta rasu ya bar Cairo ya koma New York da zama yayin da Yaran sa biyu ƙaddara tayi silar rabuwa tsakanin su, sun yi nesa da shi domin cika wasiyyar da mahaifiyar su Aamalah ta bari.
*WANNAN KE NAN...*
____________
*JOS NIGERIA.*
Cikin wani madaidaicin gida na masu rufin Asiri ginin bulon siminti da ya sha fenti ciki da waje ƙaramar ƙofar gate ne da Gidan sannan ɗakuna huɗu ne cikin Gidan sai kuma ban ɗaki dake gefe sannan sai ɗakin girki sai ɗakin a je tarkace sannan sai rijiya dake can gefe cikin Gidan.
Hajiya Sumayya Dattijuwar mace mai kimanin shekaru sittin da ɗauriya tana daga zaune saman tabarma yayin da Mijinta Alhaji Muhammad Ali da aka fi sani da Nakowa yake daga kwance saman tabarman a gefanta ya lumshe ido yana tunanin Rayuwa. Radio dake rataye saman wani dogon katako tana faman aiki yayin da gaba ɗaya hankalin Hajiya Sumayya yake a kan Radio ɗin tana sauraren shirin Duniya Tumbin Giwa.
"Assalamu Alaikum."
Suka yi sallama a tare lokacin da suke shiga gidan sannan suka ƙari sa wurin kakannin nasu. Fuska ɗauke da murmushi bayan sun amsa musu sallama Arissa ta ce.
"Heyyy Kakus ana ta fama ke nan da Radio kin bar ɗan tsohon mijinki da tunani an ya kuwa kina kula mana da Grandfa yadda ya kamata na fara zargin wani abu fa."🙃
"E, a haka ɗin yake maƙale dani ni ɗaya babu ƙari ki gama sa idon ki mijina yafi ƙarfin ki da jar fatar ki a wurin."
Dariya Arissa tayi yayin da take ƙoƙarin shiga wani madaidaicin ɗaki ta ce.
"Kakus ke nan bani na kar zomon ba ai menene ma zan yi da wannan tsohon kedai da kikaga zaki iya sai a ɗaura niyya. My Yaya T.A ko ya kace?."
Tayi maganar tana mayar da kallon ta kan Yayan nata kuma farin cikin ta.
"A'a ai kun fi kusa babu mai shiga tsakanin ku domin ko an shiga ma kunya za'a kwasa."
Ya yi maganar cikin sassanyar Muryarsa mai daɗin saurare kuma a taƙaice, kyakyawar fuskarsa ɗauke da Murmushi kaɗan da bai bayyana haƙoran sa ba.
Dariya tayi sannan ta shige ciki.
"Fatan kun shigo lafiya?."
Hajiya Kakus ta faɗa tana mayar da kallon ta kansa.
"Alhamdulillah."
Ya furta yana gyara zama so yake ya mayar da hankalinsa wurin sauraren Radion duk ba ra'ayin sa ke nan ba amma zama da waɗan nan Dattijawan Biyu ya saka ya fara. Sai dai ganin kamar da magana a bakin kakannin nasa ne yasa shi nutsuwa tare da mayar da gaba ɗaya hankalinsa gare su musamman ma Alhaji Nakowa.
"Lokaci yana ja cikin lokaci ƙanƙani shekara ɗaya tana neman zagayowa da hakan ke nuni da lokaci ya kusa a ƙiyasina bai fi nan da kwanaki ashirin da Takwas ba komai zai faru kuma ya ƙare."
Shiru ya yi domin shi ba mutum ne mai son yawan surutu ko hayaniya ba. Yana sauraren maganganun da suke fitowa daga bakin kakan nasa wato Alhaji Muhammad Nakowa da ya kasance Asalin ɗan Garin Jos ne gaba da baya matar sa ɗaya ita ce Hajiya Sumayya sai 'yar su ɗaya tilo Aamalah da ƙaddara tayi sanadin rabuwar su shekaru masu yawa Baya sanadin karatu da ta tafi ƙasar waje....
__________________________________________
"Anty dama na dawo ne domin na rakaki zagaye Garin kamar yadda kika buƙata."
Teema ta faɗa tana kallon Samira Adila Dina Baturiyar baƙuwar tasu kuma kyakyawar gaske, kwanaki biyu da suka gabata ta shigo Garin ta sauko cikin masarautar Garin Gidan Sarkin Garin wato Muhammad Raees sarki mai adalci ga Al'ummar sa matan sa uku Hajiya Bilkisu ita ce ta farko tana da yara uku Junayd Muhammad Raees mahaifin Hamrarh da Amrarh kuma sanannen Alƙali ne mai gaskiya a Aikin sa matar sa ɗaya Miss Asfiya kyakykywar bafulatana da kyawunta ya zamo silar afkuwar ƙadarori da dama cikin Rayuwar su sanadin haka wani baƙin sirri da babu wanda ya san da shi ya mamaye Ahalin. Dr Salma ita ce ta biyu cikin yaran Hajiya Bilkisu sannan sai Alhaji Nawaz da yake zaune a garin tare da Iyalansa yaran sa maza biyu Ustaad Arkan da kuma Althaf.
Sai matar Sarki ta Biyu Hajiya Safiyya Yaranta Biyu, Canal Nubaid dake zaune a Lagos da iyalansa sai kuma Barrister Aeshah da take Auren wani ɗan kasuwa kuma ɗan kwangila bata taɓa haihuwa ba kuma suna zaune ne a birnin tarayya Abuja. Sannan sai matar Sarki ta uku Hajiya Asiya ɗa ɗaya tilo gare ta sannan ya daɗe da rasuwa shekaru masu ɗan yawa Baya.
Kamar yadda aka saba duk ƙarshen Shekara a gidan mai Martaba Sarki Muhammad Raees gaba ɗaya yaran nasa masu Aure a ƙasashen waje da wasu States ɗin gaba ɗaya kowa yake hallara da iyalan sa a gidan domin gudanar da hutun anan. To haka ma wannan ƙarshen Shekara ta kasance gaba ɗaya Yaran Sarki da Iyalansa sun kasance sun zo daga mabanbantan States da suke kuma tare da iyalan su domin gudanar da hutu anan kamar yadda aka saba sai dai wannan shekarar da ban mamaki lamarin ya kasance sanadin zuwan bazata da Samira Adila Dina ɗiya wurin Sulaiman Mutallab Raees tayi kowa ya yi mamaki da zuwanta duba da Irin abubuwan da suka faruwa a Baya. Sai dai kuma sun yi farin ciki da tazo sai dai ba tare da iyayenta tazo ba. Mahaifiyarta ta kasance Haifaffiyar ƙasar Turkey ce kuma acan suke zaune a halin yanzu. Samira tazo Nigeria ne ba tare da sanin iyayenta ba...
*WANNAN KE NAN KAƊAN DAGA CIKIN LABARIN TSANTSAN SO.!*
*WITH FULL OF...*
```_-_Life with Destiny, Struggle, Inclination, Merciless, suffering, Excruciation, and Negate Pure Love._```
____________________________________________
*Present Day....*
Kallon Teema Samira tayi da kyar ta gane maganar nata domin ba sosai takejin harshen Hausa ba. Tayi ƙoƙari sosai ma da ta iya harshen domin ba'a cikin masu magana da harshen ta taso ba.
"Oh sorry Ina ga zagayen Garin nan zamu barshi sai zuwa Gobe fa domin yau kam ina tare da 'Yan uwana musamman ma Hamrarh da Amrarh."
"Tohm Anty Allah ya kaimu Goben."
Teema ta faɗa tare da ƙoƙarin fita daga katafaren palon domin ji take ta tsargu ganin Irin kyawawan mutanen dake ciki maza da mata duka jikokin mai martaba sai dai bataji duk kyansu duka sun kai kyan wannan Baturiyar wato Samira.
"Ina zakije kuma Teema?."
Juyawa tayi ta kalle da murmushi ta ce.
"Zan koma gida ne domin Mamana tana can tana jirana Allah ya kaimu Goben in sha Allah da wuri zan zo."
Teema ta faɗa silently domin ita ɗin mace ce mara son hayaniya shiyasa ma inkiyarta yake Teema silent.
"Okay Bye ki gaida su Mama."
Samira ta faɗa tana mayar da kallon ta kan 'yan uwan nata da suke cike da Palon bayan Teema amsa sannan ta fita daga Palon sauri sauri.
_______________
*HAZEL POV.*
Dawowarta daga school ke nan a gajiye ta shiga gidan nasu na ginin bulo da ko arziƙin fenti bai samu ba. Granny ta hango zaune daga tsakiyar gidan tana faman Aikin wanke tumatur dake cikin bokiti da alama sun fara lallacewa ne take cire masu kyau daga ciki.
"Granny sannu da aiki."
"Yauwa Sannu kin dawo lafiya."
"Lafiya qalau Father bai dawo daga Church ba ke nan?."
Hazel ta tambaya tana a je littatafan karatun ta saman wani dogon table daga cikin baranda na gidan.
"Bai shigo ba tukunna ina ga ayyuka ne suka riƙe sa."
"Okay, bari na shiga ciki na watsa ruwa sannan na dawo na tayaki."
Hazel ta faɗa tana shiga cikin ɗakin ta, ta sauya kaya sannan ta fito ta ɗiba ruwa a baho ta shiga wanka lokaci ƙanƙani ta gama sannan ta shirya cikin t-shirt mai garejen hannu da wando mai faɗi baƙi na shan iska sannan ta saka hular Bat ta rufe dogon gashin kanta. Fitowa tayi ta kama ma Granny suka ci gaba tsince masu kyau daga cikin tumaturan...
_*Nainarh KD ✍️_*
_-_*Like Share Comment and vote 🙏💖 _-_*
____________________________________________
*_-_ For any and more information_-_*
*My WhatsApp Countact (08081129487 or 07085212808)_-_*
*💫TSANTSAN SO.💫*
*The Pure Love.*
*Daga Alƙalamin Nainarh KD.*
*The Writer Of Queen Of Beauty👑✍️.*
*Dedicated To Princess Teemarh [Star Lady.]💋*
*Ep_Three.*
*Around 9:30am.*
Fitowa tayi jikinta sanye da Doguwar rigar yadi da alama Bacci ta tashi duba da yadda take jan doguwar hamma tare da miƙa.
Sauke idanunta tayi a kan mutanen Gidan da suka kasu kashi kashi tsakiyar gidan manyan su da Yaransu kowa yana gudanar da harkar gaban sa kama daga Kishiyar Baabarta wato Inna Sahura dake fama da yara maza da mata masu siyan koko da ƙosai ita tana toya ƙosan yayin da Ɗiyar ta mace Zahrah take faman zuba kokon wa masu siya, kamar kullum tana sababi ita ta gaji wa ya mutu wa ya tashi, Inna Sahura na jin ta sai dai ba tace komai ba, domin koda tayi maganar ba fasa sababin zatayi ba.
"Allah ya yi kin tashi ke nan har kin sama fitowa?."
Inna Lami dake gaban kaskon waina da take yi na siyarwa ta faɗa ba tare da ta kalle ta ba.
"E, Inna Lami na farga ya Ayyukan?."
Ta amsa ta tana zama saman kujerar tsugunno gaban kaskon wainar.
Amsa ma ta Inna Lami tayi da faɗin.
"Ayyukan Alhamdulillah kam gashi fa Allah ya yi dare gari ya waye mun ɗaura daga in da aka tsaya jiya."
Murmushi tayi kaɗan. Inna Lami ke nan babu ruwanta. Buɗe baki tayi domin sake wata maganar sai dai kasa faɗin komai tayi gaba ɗaya tsiyar jikinta na mimmiƙe wa idanunta akan ƙannin ta da suke gudanar da wasan felin felin daga can gefe na gidan da yake babba ne sosai.
"Ke! Aminatu menene kike haka ne wai shin bakyajin zafi ne kike saka yatsar ki kina jan layin felin felin?."
Da mamaki suka kalle ta gaba ɗaya har da Inna Lami sai dai ba ta ce komai ba.
Washe baki Yarinyar mai Kimanin shekaru goma sha biyu da ta kira da Aminatu tayi tana faɗin.
"Lah Anty Aaqilah Babu wani zafi fa, Humm ai na saba ma, ban sama ƙusa da zan ja layin ba ne shiyasa nake ja da ƙumbana."
Shiru tayi ba tare da ta ce komai ba. Har lokacin tsigar jikinta bai koma ya kwanta ba. Ji take kamar ita ke jan layin. Dama haka take ita.
"Allah mai iko wato wasan ma ba za'a bari yara suyi cikin walwala ba, yo zafin Mai zataji kuma abu da ta riga da ta saba, oh ni Sahura yau nake ganin iyayi ana wuri."
Bata kula ta ba kamar yadda taso domin tasan neman magana ce irin na Sahura ba'a saka da ita ba ta kwashe.
"Zahrah naji labarin Kun rabu da wannan mayen saurayin naki Sule yake ko wa, garin ya ya hakan ta kasance kuma na ganki garau ba'a asibiti ba, is it cewa fa kikayi ba zaki taɓa iya rabuwa da shi ba, idan hakan ma ta kasance a gadon asibiti zaki ƙare?."
Tayi maganar tare da gimtse dariya, dara daran idanunta akan Zahrah kamar yadda kowa da yasan irin Soyayya dake tsakanin ta da Saurayin nata Sule kuma rana tsaka ta ce sun rabu.
"Uhum menene ma zance Anty Aaqilah, ina gaya Miki wannan mutumin ɗan akuya ne bani yake so ba jiki na yakeso ni kuma makauniyar soyayya da nake masa ta hana na gane Hakan sai jiya Jikar Mai Sarki wannan Baturiyar dana baki labarin tazo garin nan kwanaki uku da suka wuce, ta ganar dani bisa hanya ta daidai ta nusar da ni jikina yakeso bani ba."
Tunda Zahrah ta fara maganar Mamanta Inna Sahura ta saki baki, kunne, hanci duka tana kallon 'Yar tata da mamaki har sai da taga takai aya sannan ta laylayo wani ashar ta kutuntumo ta ce.
"Kayyasa to da izinin uban wa kika rabu dashi sannan akan me, ba ce miki nayi ki ƙara jan shi a jiki ba kici arziƙi ki barsa a inda yake."
"Kai Inna Sahura kin jiki kuma wannan bunsurun zanso, mutumin da bashi da aiki sai yawo da 'yan iska kuma fa har bin matan banza yake yi, ni ban ma san ya aka yi na fara son shi ba, sai dai na gode Allah da na gane gaskiya na koma hanya madaidaiciya tun wuri, sannan da kike maganar naci arziƙi na bar sa a inda yake, ina arziƙin anan kina da labarin har kamashi aka taɓayi shi da su Bello sun shiga gidan Alhaji Nawaz zasuyi sata, kalar wannan kikeson 'yar ki ta aura har su haifo miki jikoki, ba ma wannan ba yanzu fa a gaban ki nake faɗin ba sona yake tsakani da Allah ba jikina yakeso kuma..."
Katseta Inna Sahura tayi cikin borin kunya da kumbar baki cike da rashin gaskiya, masu iya magana suka ce, da hauka ake naɗe tabarmar kunya aikuwar hakan ta fara.
"Ce ce ce ai naji ko to ya isa hakan tun da kun rabu shikenan ban san sake jin komai kuma haba."
Tayi maganar tana zazzare ido lokaci guda wani gudawa na taso ma ta tsaban tsoro na abin da zai je ya dawo saƙe saƙen mafita takeyi cikin ranta.
"Oho dai ke kika sani zakiyi bayani ne sai ma ya damƙe ki ki basa kuɗaɗen sa da kika dinga amsa da Sunan zaki aura masa ni ayi dai mu gani."
"Zaharatu."!!
Sahura ta ja sunan nata muryar ta na shaƙewa jin abin da take faɗa.
"Atoh gaskiya na faɗa."
Zahrah ta faɗa tana mayar da kallon ta kan Aaqilah da hayaniyar nasu ya ishe ta, ta miƙe cikin tafiyarta tana bubbuɗawa uwa Namiji ta nufa ƙofa ba tare da ta ce da kowa komai ba.
"Anty Aaqilah ina zaki tafi haka da sassafiyar nan naga ko Hijabi baki saka ba bare mayafi kefa mace ce."
Dakatawa tayi da tafiyar daidai kyauren gidan ta juya gaba ɗayan ta lokaci guda tana sauke dara daran idanunta akan ta.
"Ke! Yaushe raini ya fara shiga tsakanin mu da kikemin irin wannan tambayar, a je ni kikayi ko kin fini sanin abin da yake daidai da akasin sa ne?."
Cikin jan ido tayi maganar lokaci guda yanayin ta ya sauya ba kamar farko ba da alama an tunzuro mutanen kanta.
"Kai Anty Aaqilah ni ba haka nake nufi ba, to Allah ya baki haƙuri, dama gani nayi an yi ruwa kuma..."
Zahrah tayi Shiru baki a sake bata ƙari sa ba ganin wacca take maganar da ita ta daɗe ta ficewa abin ta daga gidan ba tare da ta kuma sauraren ta ba.
"Allah ya ƙara wai ke 'yar iya har wani wa'azi ki naji daɗi da ta gwale ki."
Naseeba Ƙanwar ta ta faɗa tana Dariyar sheƙiyanci.
"Munafuka ina Wasa dake ne?, zan ci kaza kazan ki anan wurin tohm..."
Zahrah ta laylayo uwar ashar Naseeba kuwa ta ce.
"Ba dai ni ba sai dai ke."
Nan suka fara sana'ar tasu dama sun saba sai dai ba'a haɗu ba saƙo da saƙo.
SAMIRA ADILA DINA (SAM POV)
Sakamakon Ruwan Sama da aka raba daren jiya ana yi ne yasa yau gaba ɗaya garin aka tashi da wani irin yanayi mai burgeni luf luf garin yake ga wata irin ni'imtacciyar iska wadatacciya da ta gauraye ko'ina tana kaɗawa kaɗan kaɗan yanayi na damina garin ya yi lumi lumi, mutane jifa jifa ne suke wucewa cikin yankin da suke tafiya ita da ƙawar tata da tayi a Garin duk da ta girme ma ta a shekaru nesa ba kusa ba, domin akalla ba'a kasara ba, zata iya bata shekaru huɗu zuwa Biyar.
Samira tana daga saman Keken ta ƙarama na hawa irin na training na safe, Teema tana tsaye gefan ta suna tafiya a hankali Teema tana ci gaba da bata Labarin yadda garin nasu yake.
Idanunta ya sauka akan wani dogon ƙarfe na service da ma'aikata suke faman aikin saka masa wani abu kamar drum haka dai a wurin ta da alama Service ɗin ba'a daɗe da saka shi ba, ko kuma har yanzu ana sakawan ne duba da yadda ba tsayi ya yi ba.
"S.K."
Ta furta sunan da aka rubuta jikin wani allo da aka kafe shi gefen hanya daura da ginin service ɗin.
"S.K shi ne sunan kamfanin da suka ɗauki nauyin saka mana service ɗin ba tare da sun Buƙaci komai daga garemu ba."
Teema ta faɗa tana Murmushi domin tasan tambayar da zata ma ta ke nan.
"Wow kice ba Gwamnati bane ta ɗauki nauyi kamar yadda nayi hasashe."
Teema tayi dariya jin abin da ta faɗa.
"Anty Sam ke nan badai Gwamnatin wannan lokaci da muke ciki ba da wannan zamanin da kowa kansa ya sani ba, babu ruwan kowa da kowa."
Teema ta faɗa Samira ta buɗe baki domin magana. Sai dai ba ta iya cewa komai ba. Ta zaro ido tana kallon wasu garɗa garɗan samari majiya ƙarfi sai dai raguwan sigari ne da ganin su, sun tare musu hanya suna sakin wani shu'umin Murmushi.
"Sule kaine menene yasa kuka tare mana hanya ku bamu hanya mu wuce menene haka?."
Teema tayi maganar a fusace tana kallon Sule da yaran da ya yi hayan su ta gane su gaba ɗaya yaran Bello (Shegen Kaya ) ne wato shugaban su haka Sunan sa yake sanannen Tantirin Matashin Saurayi ne mara aikin yi sai sace sace da daba, kowa cikin garin tsoron yake da mutanen sa kuma Sule yana ɗaya daga cikin mutanen nasa na hannun dama ma.
"Su waye su kin san su ne kike musu magana?.
Samira ta tambaya tana ja da baya sakamakon damƙa da ɗaya daga cikin mutanen yakai ma ta tayi baya ta sakar masa Bicycle ɗin tana zaro ido, ƙirjin ta da ya tsokale masa ido yaso damƙowa duk da kuwa ba hango su yake ba domin sanye take da Sagittarius shirt mai gajeren hannu sai skinny jeans kamar kullum ta ɗaure ƙugunta da rigar sanyi ta scorpio, ƙafar ta sanye da Boot shoe irin na ma ta kuma na training dogon gashin kanta mai launin baƙi rabi da kuma coffee Brown da tayi style ɗin in cute punytail ya leƙo daga cikin Baseball Cap da ta saka, ya sauka har gadon bayanta da alama tsayin sa ya yi yawa.
Ko kafin Teema ta bata amsar tambayar Sule da yake a fusace ya sheƙe da wata uwar dariya ta Bosawa kafin ya tamke fuskarsa lokaci guda kamar ba shi ne mai dariya lokcin ba ya ce.
"Oh really da gaske baki gane ko wane ne ni ba mutumin da kika raba da abar ƙaunarsa Zahrah a jiya."
Ajiyar zuciya ta sauke ita sai yanzu ta fara ganeshi.
"Menene yasa ka tare mu?.''
Teema ta tambaya a fusace tana ɓalla nasa harara cike da tsiwa, fuskarta ko alamun tsoron sa babu.
"Ke yarinya ki lafamin badan ke nazo nan ba dan wannan mai jan kunnen nazo wato uwar ɗakin naki saboda haka ki matsa gefe bakya ciki agenda na, idan kuma zaki shiga ga fili ga mai doki mai ya rage?."
"Sukuwa "
Teema ta faɗa sannan ta ci gaba da faɗin.
"Ku bamu hanya mu wuce tun kafin nayi muku ihun gwartaye gaba ɗaya...."
Bata kai ga ƙari sa faɗar abin da tayi niyya ba jin ta da ganin ta ya gushe na wani lokaci sakamakon wani bahagon mari da ɗaya daga cikin garɗa garɗan samarin ya zuba ma ta.
"Kan uban can Dan uban uwarki su waye gwartayen tsohuwar kika ga na danne ko wa da zaki kirani da gwarto?."
"Allah ya isa ban yafe ba mugu Azzalumi kuma Anty Samira tafi ƙarfin ku dukkan ku babu wanda ya isa ya yi ma ta wani abun kaf cikin ku mugaye."
Teema ta faɗa cikin ƙarfin hali tana dafe da kuncinta da shedan yatsun sa biyar ya bayyana saman fuskarta daidai wurin marin, domin ta fara sarewa da lamarin tasan su ciki da waje zasuyi sama da hakan ma da suka faɗa, sai dai zata tsaya iya ƙarfin ta da jajircewar ta wurin ganin basuyi ma Adila abin da suka ƙudurta ba.
Hannu ɗayan yakai a fusace zai ƙara kifa ma ta mari ta ɗayan side ɗin face ɗin nata gefen wurin da wanda suka kira da Toro ya fara marinta.
Teema ta rumshe ido tana jiran ta inda marin zai tsirga ta. Sai dai jin shiru da tayi ne tare da ihun da Samira ta kurma yasa ta buɗe idon ta a hankali. Zaro ido tayi waje ganin Buloo da ya kai ma ta mari zube a ƙasa riƙe da karyayyen hannunsa yana cije baki da rumtse ido.
"Shashasha ashe ma kai ɗin ragon banza ne daga saka maka hannu ka zube ƙasa ƙaramin ɗan iska kawai."
Aaqilah ta faɗa tana juyawa ta mayar da kallon ta kan Teema da take matsayin ƙanwarta uwa ɗaya uba kowa da nashi sannan ta mayar da kallon ta kan Samira. Sule ya yi amfani da damar juyawan da tayi ya dage iya ƙarfin sa ya raɗa ma ta sandar hannunsa irin tasu ta Fulani mai kauri da girma a kai.
Tangal tangal tayi zata zube a ƙasa tayi saurin cijewa tare da juyawa tana kallon sa cikin layi domin ko a bazata yakai ma ta dukan kuma ta baya da hakan yasa ba kaɗan ba dukan ya shigeta sai dai tsaban taurin zuciya irin nata yasa ko'a fuska taƙi nuna zafin da taji ta daure ta cije.
"Matsoracin banza, kai ta baya kake kai farmakin saboda kasan kai ragone da ka sani kayi ta gaba mana ƙidahumi."
Tayi maganar tana tangal tangal zata faɗi Samira da gaba ɗaya jikinta babu inda baya rawa tayi saurin tarota, yayin da shi kuwa Sule a fusace cikin jin haushin maganar ta ya kuma ɗa ga sandar zai buga musu gaba ɗaya.
Sai dai duk yadda yaso ya yi gaba da sandar ya kasa.
A hankali ya juya da jajayen idanun sa ya sauke su domin ganin wani isasshen ne ya riƙe masa sanda suka yi four eyes da mutumin da ba zai taɓa mantawa da shi ba a Rayuwar sa... To a kan me ma zai manta da mutumin da ya kusan fasa masa ido da naushi Kawai Ranar haɗuwar su ta farko, nan da nan jikinsa ya fara rawa kamar yadda bakinsa yake yi, so yake ya yi magana sai dai tsaban tsoro ya hanasa faɗin komai, ya mayar da kallon sa kansu Buloo da Toro yana bin su da kallon su kawo masa ɗauki sai dai tun kafin su gama fahimtar abin da yake nufi yaji wani irin bahagon naushi da aka maka masa a hanci da ya haddasa masa zubewa a wurin hancinsa yana zubar da jini na haɓo da ya yi masa, ganin abin da ya faru da shi ne yasa Buloo da Toro cika wandon su da iska ba tare da sun bari ya dawo kansu ba.
"Wato baka dandara da dukkan mutuwa da nayi maka ba wancan haɗuwar, yanzu kazo ka tare yaran mutane kuma mata saboda kai bunsuru ne kuma matsoraci, zaka basu haƙuri sannan ka ɓacemin daga gani ko kuwa sai na fasa maka ɗayan idon da duka?."
Jiki na rawa tsaban tsoro Sule ya kalle su tare da bawa Samira haƙuri bai jira amsawarta ba ya ruga a 360 har yana tuntuɓe ko waigen baya baya yi har ya ɓace da ganin su.
"Ƙaramin ɗan tururi kawai."
Ya faɗa tare da jan qwafa sannan ya juya da kallon sa garesu a karo na farko.
Taimakawa Aaqilah ta miƙe tsaye tana dafe kai Samira tayi.
"Kiyi haƙuri saboda ni ce ya yi miki hakan."
"No, ba saboda ke ba ne akwai tsamar dake tsakanina da shi dama, karki damu fa zamu jame ne zai gane ya daki Aaqilah Tantiriya hummm ƙaramin mara kunya na rantse da assamadu sai Sule ya raina kansa."
Ita dai Samira bata kuma faɗin komai ba, ta ɗa ga keken ta riƙe da hannu guda da sauri ta ƙari sa wurin sa ganin ya yi nisa zai bar wurin bayan ya ɗauki Keken sa da take kamar nata na training ta mafi nata tsada da komai.
"Am bakaji ba, na ce ba?."
"Menene ko akwai wata matsalar ne?."
Ya tambaya bayan sun dakata da tafiyar da suka fara shida Ƙanwarsa Arissa dama tare suke.
"No ba wani abu ba ne dama godiya zan maka bisa ceton Rayuwata da kayi hannun wancan mutumin. Na gode sunana Samira Adila Dina ana kira da Sam."
Ta faɗa tana miƙa masa Right hand nata alamun su gaisa ya bita da kallo yana maimaita Sunan a Ransa.
"Samira Adila Dina."
Sannan ya kalla hannun da take miƙe masa. Ganin haka yasa ta faɗin.
"Zamu iya zama abokai?."
Da ido Arissa tayi masa alama da ya bata hannun nasa su gaisa shima, domin tasan halin Yayan nata.
"Am Taufan Ali."
Ya faɗa a taƙaice. Cikin kamilalliyar Muryarsa da ɓacin rai ya dakusar da zaƙin ta.
"Wow pleasure to meet you Dear "
Ta faɗa daidai lokacin da hannunsa ya haɗe da nata domin gaisawa daidai lokacin kuma wurin gaba ɗaya ya bada wani haske na tartsarin wuta da yafi kama dana lantarki sakamakon gocewa da abu mai kama da drum da ɗin ya yi daga hannunsa ma'aikacin service ɗin, hakan ya yi silar hasken da ya haske wurin lokaci guda yayin da drum ɗin ya yo ƙasa gadan gadan ya tunkari saitin da Samira take a tsaye. Lura da hakan da Taufan ya yi ne yasa cikin zafin nama ya janyo ta da niyyar matsar da ita, ita kuwa ta taho gaba ɗaya ta rinjaye sa gaba ɗaya suka zube saman Bicycle nata da ya goje daga Hannunta.
Ita ce ta fara faɗi kafin ya biyo ta, ko kafin tayi wani motsi ta lura da drum ɗin gadan gadan kansu ya nufo, cikin zafin nama ba tare da ta san lokacin da hakan ta kasance ba, ta mirgina gefe tare da janyo sa suka fara gungure a tudu da kwari na wurin cikin taɓo. Yayin da Drum ɗin ya faɗa ƙasa gefe daban.
Wata nannauyar ajiyar zuciya gaba ɗaya suka sauke ganin wannan lamarin da ya faru.
"Ash Kai na."!
Ta faɗa tana rumshe ido da alama wurin gunguren ta bige kan ta ne.
"Menene ya sama kan naki iyee Adila?."
Ya faɗa da ɗan ƙarfi kuma a kiɗime yana Miƙewa tsaye ganin ta rufe idanunta tun bayan da ta ce kanta.
"Yayana suma fa tayi mu kaita Asibiti ina ga Kanta ne ya bugu."
Ya juya ya kalla Arissa da tayi Maganar.
"E, mu kaita can ɗin zai fi da alama buguwa tayi daga baya a nemo Familyn ta, ba an ce a gidan Sarki take ba?."
Aaqilah ta faɗa, sai dai babu wanda ya iya bata amsa. Taufan ya kin kime Samira.
Aaqilah taja tsaki lokacin da ya saka Samira a Napep da Teema ta tare. Tabi jikinta da kallo.
"Shashashan banza Dan Allah dubi yadda ya saka duk na ɓata kayana?."
Ta kuma jan tsaki.
"Sai dai ba komai bashi yaci zamu jame ne a gaban Sule ka kuka da kanka.''
Ta faɗa tana ciccijewa ita dole ranta ya ɓaci sannan ta bar wurin domin sun daɗe da ɓacewa ganinta. Sai dai kyakyawar fuskarsa Bata Dena ma ta gizo a ido ba haka ma kamilalliyar Muryarsa mai cike da nutsuwa cikinta daɗin sauraro kamar ana busa sarewa a ganinta. Tun da take a Garin wannan shi ne karon ta na farko da ta haɗu da shi duk da tana jin labarin sa sosai bakin Mutanen garin Especially 'yan matan da dayawa suka ma ce akan son sa, wanda ba komai ne sila ba sai tsantsan kyau da Ubangiji ya azurtasa dashi kyakyawa ne na gaba gaba idan ana lissafin masu kyau da hakan ya daɗa hura wutan kaunar sa zuciyoyin mata da yawa Bama iya waɗan da suke a ƙauyen ba, shi dai bai ma san sunayi ba domin ko tsawon watanni goma sha ɗaya da ya yi a Garin bai taɓa yin koda aboki ba sai watanni huɗu baya da ya haɗu da Labib har suke 'yar magana sama sama shima sai sun haɗu kuma kafin su haɗun a daɗe sosai.
________
*Tofah Mene ne yake faru ne, wai shin son Taufan Aaqilah take yi ko ya ya?.*
*Ga Samira Adila Dina ta suna wai shin akwai ciwo da take fama da shi basu basu sani ba ne??.*
*Shin Sule zai haƙura kuwa???.*
*By: Nainarh KD ✍️*
*_-_ For any and more information_-_*
*My WhatsApp Countact (08081129487 or 07085212808)_-_*
*~_Paid Book Don't Miss It._~*
_*~👑N.K.D.S. Writer's.👑📚✍️~*_
_Proudly Present_
*💫TSANTSAN SO.💫*
*The Pure Love.*
_❣️Destiny, Struggle, Inclination, Merciless, suffering, Excruciation, and Negate Pure Love.❣️_
*Dedicated To Princess Teemarh [Star Lady.]💋*
~_From The Pen Of Nainarh KD Writer Of Sarauniyar Kyau And Aneeserh (Innocent Girl.)_~
_Wannan Page naki ne Fatima Abdullahi Kano (Autar Marubuta) Fatan Alkhairi 😘_
*Ep_Four.*
_HAZEL POV_
Yau ma kamar kullum ta shirya tsaf cikin uniform nata na school tayi sallama da Granny ta fito domin tun sassafiya Mahaifinta wato Astrid David da ake sama laƙabi da Father kuma da yawan mutane haka suka sanshi a garin kuma ake kiransa, sakamakon shi ɗin Babba ne kuma wanda ake ji da shi cikin Babban church guda ɗaya tal dake Garin, yanzu haka ma can ya yi sammakon zuwa domin meeting suke yi na bikin Christmas da ya matso.
Tana tafiya kamar ko yaushe silently da ita littatafan ta rungume a chest ɗin ta ta karyo kwana ta shiga layin da kai tsaye zai sadata da school nasu da masarautar RAEES ke daura da ita masarauta ma girman gaske da ɗin bin tarihi.
Wani ƙaramin ɗan kwikwiyon kare ne da yazo wucewa ta sai tin ta ya ja hankalin ta.
Aikuwar da sauri ta ƙari sa wurin sa tare da tsugunawa ta ɗauke sa tana ƙare masa kallo. Saman laɓɓanta ta karanta harufan da aka rubuta jikin wani abu dake jikin doguwar sarƙe dake ɗaure a wuyan ƙaramin kwikwiyon.
"My H."
Ta karanta rubutun tana Miƙewa tsaye, waige waige ta fara ko zata hangi mamallkakin karen sai dai sakamakon yanayin garin da yake luf luf anyi ruwa mutane ɗay ɗay kune ke wucewa ta yankin.
Ta sauke ajiyar zuciya ganin bataga kowa ba, tana shafa kwikwiyon da ya lafe a hannunta lokaci kaɗan taji son kwikwiyon ya mamaye ruhinta.
"My H, ni dai banga kowa ba, saboda haka na sama kwikwiyon daga yau Sunan ki little H."
Hazel ta faɗa tana kallon kwikwiyon cike da farin ciki dan ta fahimci mace ce. Gyara littatafan ta tayi sannan ta fara tafiya hannunta riƙe da kwikwiyon da tayi ma laƙabi da Little H.
Labib ya fito daga maɓoyarsa yana Murmushi.
"Yes tarkona ya kama, da alama tanason kwikwiyon sosai."
Ya faɗa tare da fara tafiya sauri sauri har ya cimma ta, suna jerawa tare bai kalleta ba ya ce.
"Am bakiji ba, wannan kwikwiyon nawa ne fitowa ta yi daga gida ban sani ba, na fito ina neman ta. Allah ya taimaka ashe kece kika gansa, na gode sosai bani ita mu koma gida kar sanyi ya ma ta illa."
Dam...! Shi ne sautin bugun da ƙirjin Hazel ya bada lokacin da ta gama jin abin da yake faɗa. Tayi rau rau da ido kamar zatayi kuka ta ce.
"Wayyo Dan uwa ka barmin mana please ina son ta sosai fa."
Ya yi Murmushin gefan fuska da bai bari ta lura ba, sannan ya ɗan tamke fuska ya ce.
"Akan me zan baki shi bayan ce miki nayi ita ɗin mallaki nane?."
"Am so sorry gata nan ka cinye idan ana ci."
Ta faɗa a fusace tare da cilla masa kwikwiyon jin yana ƙoƙarin buga ma ta tsawa abin da ba'a taɓa ba, duk tsawon zaman ta da kakarta Granny ko dungurinta bata taɓayi ba, balle uwa uba Father da ko kukan ta bai son ji. Duk soyayyar da take ma kwikwiyon ta haƙura akan dai ya yi ma ta tsawa.
Labib ya yi kasaƙe yana bin bayan ta da kallo hannunsa riƙe da kwikwiyon da ta wullo masa ya yi saurin cafewa.
"Tofa wai fushi tayi nan?."
Ya tambaya kansa, ganin babu mai basa amsa, yasa shi saurin ƙari sawa wurin ta har tayi nisa.
"Koda yake na lura kina son ta gata nan dake tafi dacewa."
Ya faɗa yana miƙa ma ta. Batayi fushi ba kamar yadda ya yi zato. Ta washe baki tare da Juyowa ta kallesa ita sai yanzu ma ganesa ashe Mutum jiya ne kuma ta lura yana yawan bin hanyar nan da take bi wurin zuwa school sannan suna yawan karo ba tare da sun sani ba.
"Da gaske na gode sosai kuwa."
Ta faɗa, tana yunƙurin karɓar kwikwiyon a hannunsa.
Ya ja baya da sauri. Ta zuba masa ivy eyes ɗin ta domin jin abin da zai ce.
"Kafin na baki karyata yana da kyau muyi Deal dake."
"Okay Tohm Ina sauraren ka."
Ta faɗa cike da ɗan ƙosawa.
"Koda yake zan faɗa miki Deal ɗin daga baya yanzu dai gata nan ki kulamin da My H kamar kwai idan wani abu ya same ta kamar ni ya sama ita ce ni, ni ne ita."
"Kaji dashi dai badai ka bani ita ba."
Ta faɗa ƙasan ranta, a fili kuwa cewa tayi.
"Tohm na gode."
Ta faɗa tare da karɓar kwikwiyon daga hannunsa.
Ya yi Murmushi.
"Zan shiga makaranta."
"Okay take care."
Tayi Murmushi kaɗan ba ta ce komai ba, ta shige ciki hannunta riƙe da kwikwiyon har ta ƙari sa izuwa class ɗin su S.S.3,A science yau ne Ranar da zasu zana Final paper na kammala school ɗin.
Fuskar sa ɗauke da murmushi sai da ya tabbatar da shigarta school ɗin sannan ya kara wayarsa a kunne bayan ya lalubo lambar Abokinsa Taufan ya danna kira.
Sallama ya yi bayan an yi picking, ya yi Shiru domin jin abin da zai faɗa ta ɗayan ɓangaren.
"Wai kana ina ne haka naji hayaniya?. Asibiti.! Okay na fahimta, idan ka dawo sai mu haɗu a can ɗin."
Ya katse kiran tare da nufar hanya ya bar wurin.
_____________
_Aaqilah POV_
"Daga ina kike haka jikin ki gaba ɗaya duk taɓo, faɗi kikayi a taɓon da girman ki, ina hijabin ki, ko haka kika fito ganɗai ganɗai dake babu ko lulluɓi?."
Mamanta ta jero ma ta tambayoyin lokaci guda tana tsareta da ido.
"Mtsww, wai Mama mai kika mayar dani ne Yarinya ko me, sannan Mene ne aibin shigata a haka, banason zafi shiyasa na fito haka sannan...."
Katseta tayi a fusace.
"Sannan me yanzu Tantirancin naki yakai ki kalla tsaban idona ina faɗa kina faɗa, lallai ne na fahimta, kiyi gaggautawar ficemin daga gida yanzu yanzu tun kafin raina ya fara ɓaci shashashar banza."
Mama ta faɗa a fusace daga ƙasan zuciyarta a karye take ayyana wa take.
Shikenan an gama ita an lalata ma ta rayuwar 'ya. Ji take bazata taɓa yafe wa Lami da Salame ba har abada domin sun cutar da ita.
"Wow dama wannan ranar nake jira ashe kin yarda ni Tantiriya ce, wai Aikuwa tantiranci salo salo zan fito da, sannan ki kwantar da hankalin ki zan fice Miki daga gida ba zama ya kawo ni ba, dama labari na samu bakyajin daɗi sai dai na lura ma kin warke zan tafi."
"Da yafi dai Umma ta gaida Aysha."
Aaqilah tayi Murmushin takaici tana juyawa daidai lokacin ita kuma Teema ta shigo gidan da sallama. Turus taja ta tsaya baki sake.
"Wannan kallon fa nifa banason gulma Mene ne ya faru har kin dawo daga Asibitin ne ya jikin nata?."
Aaqilah ta faɗa a dake tana zuba ma ta coals eyes nata da ɓacin rai ya fara rinar dasu.
"E, na dawo ne na faɗa ma Gidan Sarki abin yake faruwa, dama acan take, tana lafiya likita ya ce ba Babban abu ba ne kawai ta tsorata ne ta yi. Anty Aaqilah Mene ne yake faru ne wai, mai ya haɗaki da Mama nake jiyo muryoyin ku tun daga waje?."
"Ban sani ba gulma awiya kawai, abin da na tambaye ki daban amsar da kike bani daban, sannan ki shirya zanzo anjima ki rakani na ganta. Koda yake barshi ma na fasa sai gobe."
Ta faɗa ba tare da ta jira abin da Teema zata kuma faɗa ba ta raɓa ta gefanta ta fice daga gidan gaba ɗaya.
"Mama.."!
Teema ta kira Sunan Mahaifiyar nasu da tabi Ɗiyar tata Aaqilah da kallo tana ma ta fatan shiriya daga wannan murɗaɗɗen halin nata.
"Mene ne ya faru naji ta ce asibiti, kiyimin Bayani illa tayima wata ko me?."
Maman ta tambaya tana ɗan fito da ido da alama a tsorace take tun lokacin da aka ambaci asibiti.
"Mama ke nan, ba wani abu tayi ba, kawai akasi aka samu."
Teema ta faɗa sannan ta bawa Mahaifiyar tasu labarin duka abin da ya faru daga farko har zuwa yanzu.
Mama taja salati cike da tarabbabi sai dai ta kasa faɗin komai.
______
_Aaqilah kuwa._
Da fitarta kai tsaye Gidan mahaifinta ta koma da Babu nisa sosai da gidan da Mahaifiyarta ke aure bai fi gidaje huɗu zuwa Biyar ba tsakani.
Hayaniya ce ke fitowa daga cikin gidan da alama mutanen gidan sun fara sana'ar tasu.
"Mtsww Baba dai ya mutu ya bar ma mutanen Duniya ala ƙaƙai ko menene yake faruwa kuma yanzu oho."
Ta ƙari sa zancen zucin tana shiga gidan. Karo taji tayi da mutum. Sai dai bata damu da sanin ko wanene ba tasa kai zata shata ta gabansa ta wuce.
"Ke daga gidan uban wa kike a haka babu ko mayafi?."
Ta kalle sa ɗere re sama da ƙasa kai tsaye ta basa amsa da.
"Daga gidan uban ka mana."
A fusace ya kai Hannu da niyya kifa ma ta mari. Ta tsaya ƙyam tana jira.
Inna Lami tayi saurin riƙo ta ta janyo ta tana faɗin.
"Haba Umaru wai Yaushe zaka dena biyewa wannan Yarinyar Aaqilah ne kullum naga zubar da girman ka, baka tsoron ta raina ka?."
A fusace ya juya ya kalle Mahaifiyar tasu ya ce.
"Haba Inna Lami kina ji dai zagina tayi ni ɗin sa'an tane ko me?."
Ya faɗa Muryarsa na kakkarwa da alama Ransa ya ɓaci sosai.
"Kayi haƙuri to, ke kuma Aaqilah ki dena kalan wannan ki basa haƙuri yanzu komai ya wuce."
Tayi Murmushin rainin wayo ta kalla Inna Lami ƙere re.
"Wai wannan abin zan bawa haƙurin never wallahi."
Ta faɗa tana gaba ta shige cikin Gidan tana watsawa Inna Sahura da ta dataka daga cacar baki da suke yi ita da Yaran gidan kamar sa'o'inta wata uwar harara mai cike da ma'anoni.
"Kizo ki zubamin waina ta idan kuma ta ƙare ne a ga Ruwan Bala'i, kai kuma kayi sauri kaje ka kaima wannan kucakar matar taka waina da ta aikoka amsa tun kafin ta biyo ka mijin ta ce kawai."
Huci Umaru yake tsaban takaici yasa kai ya fice daga gidan hannunsa riƙe da kular waina da aka zubawa matar sa.
"Aaqilah kinsan abin da kikeyi bai dace ba ko, ke fa Mace ce ki sani gidan wani zakije yana da kyau ki gyara hali tun kafin lokaci ya ƙure miki."
Aaqilah taja tsuka kaɗan shikenan kuma zata fara nasihar nata.
Inna Lami bata damu da ƙin kulata da Aaqilah tayi ba domin inda sabo ta saba ta ci gaba da ma ta nasiha akan rayuwa can ƙasan zuciyarta kuwa wani irin nadama ne na Rayuwar ta ta baya ta takeji, ta sani tana da saka hannu cikin halin da Aaqilah ta tsinci kanta a rayuwa sai dai yanzu tayi nadama ta ƙudurce a ranta zata tara kuɗi na cinikin wainar ta domin zuwa a karya baƙin Asiri da aka ma Aaqilah tun Ranar da ta fito Duniya....
*~_Paid Book Don't Miss It_~*
______
~N.K.D.S Writer's Team~
1: Nainarh KD
_Heartie Of The N.k.d.s_
2: Kainaat
_Queen Of The N.k.d.s_
3: Dodo Zaynab
_Dodo's Of The N.k.d.s_
4: Salma Ahmad Isah
_Salmani'ans Of The N.k.d.s_
_*~👑N.K.D.S. Writer's.👑📚✍️~*_
_Proudly Present_
*💫TSANTSAN SO.💫*
*The Pure Love.*
_BY_
_Nainarh KD✍️_
*Dedicated To Princess Teemarh [Star Lady.]💋*
*Ep_Five.*
_Hazel Kuwa._
Tun bayan shigarta class ɗin su tsawon mintuna ashirin tana zaune bata ce da kowa komai ba haka ma babu wanda ya kulata, domin a ganinsu ita ɗin 'yar girman kai ce ita ba kowa ba sai shegen jama'a jijji da kai ga miskilanci shi ya sa bata shiga harkar kowa kuma kowa baya shiga nata.
Tana nan zaune tana shafa kwikwiyon cike son sa. Arissa ƙawarta da suke zaune benji ɗaya ta shigo class ɗin ta ƙari sa ta zauna tana a je littatafan ta saman desk.
"Barka da ƙari sowa amma fa yau kin makara sosai."
Arissa ta sauke ajiyar zuciya tana kallon kwikwiyon dake hannun ƙawarta ta Hazel ta ce.
"Kedai bari kawai wani abu ne ya tsayar dani, kina lafiya?."
"Lafiya Qlau. Wani abu ne ke nan?."
Hazel ta tambaya tana kallon ta.
Ba tare da ɓata lokaci ba Arissa ta kwashe dukkan abin ya faru lokacin da suka haɗu da su Teema ta faɗa ma ta.
Hazel ta ce.
"Allah Sarki yanzu haka tana can Hospital ɗin ke nan ya jikin nata?."
"E tana can, lafiya Qlau, domin Doctor ya ce ba wani abu ba ne Kawai firgici ne ta shiga da alama this is the first time na Rayuwarta da ta shiga kalan wannan halin.''
"Ayya."
Shi ne kawai abin da Hazel ta faɗa da yake surutu bai dameta ba ita ma Arissa ta san hakan.
"Althaf fa kuna haɗuwa kuwa kwana biyu?."
Arissa ta kalla Hazel da ta jefo ma ta tambayar tayi Murmushi ta ce.
"Sama sama dai wai kuwa ma kin san cewa jiya saura ƙiris Yayana ya ganni da shi?."
Hazel ta zaro ivy eyes ɗin ta ce.
"Wani Yayan naki ke nan?."
"Hummm ina da wani Yaya da ya wuce Taufan Ali ne?."
Hazel tayi Murmushi kaɗan karo na farko sannan ta ce.
"Sorry na sha'afa ne sam kin san wannan Yayan naki baya shiga harkar kowa shiyasa ma nake mantawa da shi idan ba na ganku tare ba ko kuma nazo gidan ku."
"Hummm."
Kawai Arissa ta faɗa suka canza topic ɗin. Fira suke kaɗan kaɗan kafin su shiga Exam Class.
_________
_Taufan Ali POV_
Cikin tafiya da suke tare da sanyin idaniyar sa abar ƙaunarsa Ƙanwar sa Arissa da ya ɗauko ta daga Tahfiz na safe da ta tafi duk da kuwa yanayin da aka tashi a garin an sha ruwa daren jiya amma haka ta nace sai ta tafi Islamiyya domin suna dab da sauka ne bata son komai ya wuce ta, wannan dalilin ya sa Yayan nata Taufan ya rakota makarantar sannan ya jira har aka tashesu sannan suka kamo hanyar gida tana riƙe da Alkur'ani mai girma shi kuma yana riƙe da ƙaramar kekensa ta training, suna tafiya suna fira kaɗan kaɗan suka hangi Teema Ƙawar Arissa ɗin ita da wata kyakkyawar Budurwa tsaye ga kuma wasu Samari uku gefe sai kuma wata Budurwa da ke tangal tangal zata faɗi bayan buga ma ta sanda da ɗaya daga cikin samarin ya yi.
Arissa ce ta roƙe shi da ya daure ta taimaka musu don ganin yadda ya yi kamar bai gansu ba tasan dalili amma haka ta nace har sai da ya shiga aka yi da shi sannan ne komai da ya faru ya biyo baya.
Bayan ƙari sawa da ita Hospital da suka yi ne bayan Likitoci sun rufu akan ta, bayan wani lokaci Doctor ya fito yake faɗa musu su kwantar da hankulansu ba wani Babban abu ba ne kawai firgici ne ya sameta jin haka yasa Taufan sauke ɓoyayyar ajiyar zuciya da bai san kona Mene ne ba, sannan ya umarci Teema da ta wuce ta faɗawa Familyn Samira abin da yake faruwa, nan ne ma take faɗa masa a gidan Sarki take. Bai ce komai ba yaja hannun Ƙanwar sa Arissa suka fito daga Hospital ɗin gaba ɗaya har da Teema domin bai ga amfanin ci gaba da zaman su ba don Doctor ma ya ce ta sama Bacci.
A hanya ne wayar Abokin sa Labib ya shigo masa. Umarni ya yi ma Teema da Arissa da su wuce gida ya bata Training Bicycle ɗin sa ta wuce masa da ita gida yayin da shi kuma kai tsaye ya wuce zuwa wurin da suka saba haɗuwa da Labib ɗin dama sauran Abokansu samarin unguwa. Yayin da Arissa ta wuce gida kai tsaye ta shirya sauri sauri ta wuce school domin ta makara bayan ta bawa kakannin nasu labarin abin da ya faru har yaja ma ta tseko.
"Mutumina sai yanzu ka ƙari so ke nan?."
Labib ya faɗa yana dariya ya miƙawa Taufan hannu suka yi misabaha ya ci gaba magana bayan sun zauna.
"Mutumina shawararka tayi aiki fa finally zan sama muradin zuciyata cikin sauƙi Hazel annurin Rayuwar Labib..."
Ya faɗa yana lumshe ido tare da jan Sunan daga ji zaka fahimci ba ƙaramin so yake ma Hazel ɗin tasa ba.
Abokansu suka kwashe da dariya, Taufan ya yi Murmushi kaɗan, nan suka ci gaba fira da mafi yawanci Labib keyi ba'a kan komai ba sai Hazel ɗin sa, yana faɗa musu Irin TSANTSAN SO da yake ma ta, inda sabo yaci ace sun saba da wannan surutun nasa akan Hazel da bata san yana yi ba ma, domin da sun zauna zaman Majalisa bashi da aiki sai maganar Hazel ɗin sa duk da kuwa yasan cewa ita ɗin ba musulma ba ce, Bama wannan ba, wayar gari aka yi aka gansu a garin ita da mahaifinta da Kakarta ba'asan daga ina suke ba shekaru uku baya ke nan, da yake Sarki Muhammad Raees mai adalci ne bayan gabatar da dukkanin bincike akan su ya fahimci ba zasu cutar masa da al'umma ba ya basu matsuguni cikin Garin....
_____
_Around 9:10pm_
_Arissa_
Kamar yadda suka saba kuma ya zame musu jiki ita da Yayan nata kuma Babban Amininta yau ma suna zaune ne tsakiyar gidan suna shan iska, Arissa tana daga saman tabarma zaune ita da Kakus da gaba ɗaya hankalinta yake kan Radio da take saurare suna taɓa fira jifa jifa da Mijinta Nakowa, Arissa ta kalla Yayan nata Taufan dake zaune gefe saman Plastic Chair yana shafa wayarsa cikin nutsuwa sannan ta ce.
"Ni kuwa Yayana ka koma Asibitin ne?."
"Asibiti kuma?."
Ya tambaya da alamun bai mene abin da take nufi ba. Ko da ya gane to basarwa ya yi.
"E, na ɗauka ka koma duba jikin nata ne."
"A'a."
Ya faɗa a gajarce.
Tayi Murmushi.
"Okay Tohm Gobe da safe ina so naje na ganta Dan Allah zaka rakani?."
Ta tambaya tana marairaicewa.
Akwai abin da yake yi gashi ta addabesa ta surutun ta hakan yasa shi amsa ma ta da faɗin.
"Okay "
A taƙaice.
"Na gode Yayana."
Ta faɗa duk da tasan ta wuya ya kuma wata maganar.
_________
*_Hayy Gharb, Zamalek, Cairo_*
_Around 11:30am_
_Ambrah POV_
A hankali take taka katafaren matattakalan Benen da ya haɗu iya haɗuwa gaba ɗaya ƙamshinta ya mamaye katafaren palon. Strapless Dress ne jikinta Doguwar Gown da ta wuce gwiwarta kaɗan sai Jodhpurs trouser da ya matseta a jikinta, ta yane kanta da veil mai kyau da dacewa, ƙafafuwan ta sanye Cikin wasu arnun strappy shoes black color tana riƙe da handbag nata neck ɗin ta kuwa maƙale da festoon necklaces, fuskarta wadace da make-up ba ƙaramin kyau tayi ba domin kyakyawa ce sosai tana tafiya cike da gadara ta ƙari sa saukowa Downstairs ɗin, har ga Allah bata lura da Iyayenta dake daga can side ɗin Dining suna Breakfast ba, take ƙoƙarin sa kai zata fice daga Palon tana karkaɗa car Key's ɗin ta.
"Baby Ambrah Ina ne zaki tafi da sassafiyar nan haka?."
Ta dakata daga ƙoƙarin fita daga Palon da take yi sannan ta juya ta kalle ta fara'ar da ta kasa ɓoyuwa daga fuskarta ta ce.
"Wurin Brother Taufan ɗina mana."
Ta bawa Oum ɗin nata amsa.
Gaban Oum ya faɗi ta kalla Mijinta tana masa nuni da ido na ya ce wani abu.
"Am Ambrah zo nan ɗiyata kiji."
Ya faɗa yana yafitota da hannu.
"A'a Abhie ko mene ne ka faɗa daga nan ina sauraren ka domin yau na rantse banga mai hanani fita daga gidan nan ba domin zuwa ganin sanyin ruhina."
Tsawa Oum ta daka ma ta.
"Ambrah kina cikin hankalinki kuwa Abhie naki kike faɗawa haka?."
Cuno baki Ambrah tayi tana rau rau da ido cikin dasashiyyar murya Irin na mai shirin kuka ta ce.
"Haba Oum ya ya kuke so nayi da rayuwata ne tun shekaran jiya na dawo ƙasar nan nayi nayi ku barni naje naga Brother Taufan da sauran Family amma kun hanani ban san me kuke nufi ba kuma kunsan wani matsayi yake da shi a Zuciyata."
Ta ƙari sa zancen cikin karyewar murya tana share kwalla.
Gaba ɗaya jikinsu ya yi sanyi Tabbas su sheda ne akan kalar sun da Ambrah take ma Taufan tun tana ƙaramar Yarinya.
Dr Aadnah taja ajiyar zuciya tana tattaro dukkanin nutsuwarta ta mayar kan Tilon Ɗiyar tasu sannan ta ce.
"Please Ambrah ƙari so nan akwai abin da zan faɗa miki kinji Babyna."
Ambrah ba tare da tace komai ba ta fara taku har ta ƙari sa wurin Dining ɗin ta zauna gefan Mahaifinta Prof Yusuf El Mustapha tana cuno baki ita dole an ɓara ranta.
"Uncle ɗin ki baya wannan ƙasar a halin yanzu yana can New York har su Taufan suna can akwai wani dalili na zuwan nasu amma ina mai tabbatar miki nan da One Month gaba ɗayansu zasu dawo daga nan kinga sai ayi magana akan auren ku ko?."
Ta ƙari sa maganar wa ɗiyar ta ta cike da alhini na abin da zata faɗa.
A firgice Ambrah ta miƙe tsaye cike da tashin hankali ta ce.
"What..! New York Oum kuma Dukkannin su Oh My God amma me yasa baki faɗa min ba, ai dana wuce can kai tsaye kawai da ban dawo nan ƙasar ba."
Gaba ɗaya suka kalle ta da tsaban mamaki na kalamin dake fitowa daga bakinta...
* * *
Fitowarsa ke nan daga Bathroom yana sharce ruwan dake ɗiga daga jikinsa da alama wanka ya yi ya hangota zaune gefan Bed ta zabga uban tagumi hannu bibbiyu. Da sauri ya ƙari sa wurin tare da tambayar mene ne yake faruwa ne ta shiga wannan yanayin. Ta kallesa ta ce.
"Prof an ya kuwa akwai Alkhairi a wannan lamarin gani nake wannan makaucin son da Ambrah Ɗiyata ɗaya tilo take ma Taufan Yaro wurin Yayana Ali Taj Ozan kamar tayi yawa gani nake shi baya ma ta son da take masa tunda har ya iya barin ƙasar da take ba ko waiwaye, nifa na fara karaya da wannan lamarin ka duba fa yadda take kuka ɗazu baji ba gani."
Ta ƙari sa maganar cike da rauni. Ya yi Shiru yana nazari tare da matsota jikinsa yana lallashi.
"Aadnah."
Ya kira Sunanta. Ta amsa sannan ya ci gaba da faɗin.
"Tabbas gaskiya kika faɗa son da Ambrah take ma Taufan yafi wanda shi yake ma ta idan yana matan ke nan, saka kanki a damuwa ba shi ne zai kawo mafita a lamarin ba fa ce ki bisu da addu'a kawai, sannan ina tunanin baki manta cewa bawai da gangar ya tafi ya koma wata ƙasar ya shantake ba, wasiyyar Mahaifiyarsa da ta bar masa yake ƙoƙarin ganin ya cika, kuma in sha Allah komai ya wuce dama Deal ɗin na shekara guda ne, kuma cikin iznin Ubangiji cikin wannan shekara ɗayan kwanaki kaɗan ne Kawai suka rage, a shawara ki daure ki ci gaba da lallashin Ɗiyar ki har Ubangiji ya yi dawowarsu lafiya shi da ƙanwar tasa sannan muga mene ne abin da zai biyo baya kinji Doctor na?."
Ta sauke ajiyar zuciya tana gyaɗa masa kai cike da gamsuwa da baya nansa ta ce.
"Shikenan babu damuwa in sha Allah zan yi ƙoƙari wurin yin hakan."
Ya yi Murmushi.
"Yauwa ko kefa, kawai kinje kina sakamin kanki cikin damuwa da bata miki kyau sam."
Tayi Murmushi ita ma kaɗan.
Nan dai suka ci gaba tattaunawa akan Babban lamarin dake gaban su na dawowar Taufan tare da Arissa da kuma yadda zasu runkaresa da maganar aurensa sa da suke son haɗawa Ambrah.
______
_Ni kam bana ce komai ba a halin yanzu 🌚_
👑Nainarh KD ✍️👑
https://whatsapp.com/channel/0029VaEZtE15a2429vfcpf20
*KUYI FOLLOWING WHAT'SAPP CHANNEL NAWA DOMIN SAMUN TSANTSAR SO TUN DAGA PAGE 1 ZUWA INDA AKA TSAYA, MASU NEMAN LITTAFIN ANEESERH MA ZAKU IYA FOLLOWING DOMIN SAMUN DAGA FARKO SHIMA ZUWA INDA AKA TSAYA.*
*🌹👑The Pure Love.🌹👑*
_A yadda bincike ya nuna a ƙa'idar Adabin Hausa. Tsantsar so ne, ba wai Tsantsan so ba. Saboda haka sunan labarin Tsantsar so. Ina fata zaku fahimta.🙏💖_
____________
_*~👑N.K.D.S. Writer's.👑📚✍️~*_
*_The Nainarh KD_*
_Proudly Present_
*_❣️TSANTSAR SO❣️_*
*Dedicated To Princess Teemarh [Star Lady.]💋*
*Ep_Six $ Seventh.*
*_Jos Nigeria_*
_Specialist Hospital Jos_
"Ƙarba mana please ki daure kisha ko kaɗan ne, kinji Sister kinga fa bakici komai ba tun safe har yanzu. Haka ma jiya da kyar aka samu kika saka wani abu a bakin ki."
Hamrarh ta faɗa daga tsayen da take bakin gadon da Samira take kwance sai dai an ɗa go da ita kaɗan ba'a kwance take ba, ta jingina bayan ta da abin da aka saka domin ta jingina jikinta.
Gefe tayi da fuskarta alamar dai ba zata sha abin da Hamrarh ke miƙa ma ta ba.
"Kin gani ko Mumma gashi dai a gaban ku nayi nayi amma taƙi tasha gashi taƙi cin komai."
Hamrarh ta faɗa cike da damuwa tana mayar da kallon ta kan mutanen dake zagaye da Babban Room ɗin gaba ɗaya Familyn Raees sannan ta sauke idanunta akan Mahaifiyar tasu tana zama saman ming chair dake gefan Gadon da Samira take a kai.
Lumshe kyawawan idanunta tayi a hankali ba tare da ta ce komai ba. Wannan lokaci ya yi daidai da turo ƙofar Room ɗin da aka yi Arissa suka shigo ita da Taufan bakunan su ɗauke da sallama. Samira tanaji mutanen Room suna amsa sallama da aka yi bayan an shigo sai dai hakan bai saka ta buɗe idanun nata ba, sai ma nutsuwa da tayi tana shaƙar wani daddaɗan ƙamshi mai sanya nutsuwa da ya kaima ƙofofin hancinta ziyara, ji tayi kamar ta san ƙamshin kamar ta taɓa jin kalar kamshin, sai dai a'ina?. Abin da ta kasa tunawa ke nan.
"Taji sauƙi Alhamdulillah sai dai ƙafafuwan ta ne da suka bugu ne, da ba'a lura ba sai daga baya su ne kawai matsalar amma da tun tuni an sallame mu. Gashi taƙi taci komai."
Hamrarh ta faɗa idanunta akan Handsome Guy ɗin da ya shigo Room ɗin lokaci guda ƙamshin sa ya cika ko'ina yana tare da wata Cutie Girl da tafi zaton ƙawansa ce, Bayan Arissa ta tambaya lafiyar Samira ɗin domin duk a zaton su Bacci take yi ba idanunta biyu ba, da kallon yadda Hamrarh ta ƙarishe maganar zaka fahimci a fusace take da Samira domin kuwa ba ƙaramin haushi ta bata ba.
"Buɗe bakin ki."
Shi ne Kawai abin da taji an faɗa cikin wata kalar sassanyar kamilalliyar murya mai daɗin saurare ta buɗe kyawawan dara daran idanunta tare da zaro su gaba ɗaya cike da mamaki na ganin sa zaune saman Gadon daga gefanta hannunsa riƙe da Cup da Hamrarh take ƙoƙarin tasha abin da yake ciki da ita kanta batasan ko mene ne ba amma taƙi, tsaban mamakin ganinsa ne yasa ta buɗe baki ba tare da tayi shawara da zuciyarta ba. Aikuwa ga mamakin ta ya hara bakin nata da Cup ɗin sannan ne ta fahimci kakkaurar tea ne a cikin bayan ta karɓa kaɗan, ta lumshe ido tare da buɗewa tana kuma kurɓa bayan ta shanye ya kuma bata a baki.
Kowa dake Room ɗin ya saki baki cike da al'ajabi na ganin yadda Samira take shan Tea ɗin a hannunsa, take Miss Asfiya da Yaranta da sauran mutane suke kira da Momma yayin da wasu suke kiran ta da Miss Asfiya ta saka ayar tambaya tsakanin Samira da wannan Handsome da ya shigo da abin mamaki garesu, Arissa tayi Murmushi tana lura da yadda idanun mutumin nata Althaf suke a kanta yana ta ƙoƙarin ganin sun haɗa ido sai dai taƙi basa damar hakan, tana daga zaune gefen Ambrah dake zaune cikin kujerar ta na guragu sakamakon da wannan lalura na rashin ƙafa aka haife ta, akwai ƙafafun sai dai likitoci sun tabbatar da ba zata iya taka su ba sakamakon dannesu da aka yi tun tana ciki, twin's ne su ita da Hamrarh sai dai basa kama sam domin ita Hamrarh irin matan nan ne 'yan duma duma bata da tsayi sosai sai dai ba gajeruwa ba ce, kuma fara ce hasken ta mai silkin ja akwai ta da dara daran idanu, yayin da Amrarh ta kasance doguwa ce ita duk da kuwa ba tafiya take ba kuma siririya ce mai sanyin hali fara ce ita sosai domin hasken ta bai silka da ja ba, sam ɗabi'un su basu zo ɗaya da biyunin ta Hamrarh ba.
"Sannu."
Ya faɗa yana kallon ta kaɗan cikin kamilalliyar Muryarsa da ta sanya ta cikin nutsuwa a lokacin.
"Yauwa Sannu."
Ta amsa.
"Mene ne yasa ƙika ƙi cin komai bayan kinsan hakan Hatsari ne ga lafiyarki?."
Ta dubesa jin tambayar da ya yi ma ta, sai dai maimakon ta basa amsa, sai ita ma ta jefo masa nata tambayar da faɗin.
"Kana lafiya babu abin da ya sameka?."
Bai bata amsa ba saima kallon ta da ya yi kaɗan cikin sakanni biyu sannan ya kawar da idanunsa daga gare ta yana sakin ɓoyayyiyar Murmushin da shi kaɗai yasan ya yi abin sa.
"Sorry ka ceci Rayuwata ban maka godiya ba, saboda wannan lamarin da ya biyo baya ya kasance, na gode."
Cikin daddaɗar Muryarta mai kamar sarewa tayi maganar kuma a hankali domin ko Hamrarh da bayan Taufan babu wanda yake kusa da Samira cikin mutanen dake Room ɗin bata ji abin da ta faɗa ba.
Miƙewa ya yi a nutse yana kallon agogo da yake ɗaure a tsintsinyar hannunsa. Samira ta bisa da kallo ganin ya ƙari sa wurin Arkan ɗa wurin Uncle Nawaz da suke kira da Ustaad suka yi misabaha kamar yadda suka yi lokacin da ya shigo Room ɗin, sannan suka yi ma mutanen Room ɗin sallama tare da ficewa daga Room ɗin. Mutumin nata da Arkan sai kuma wata Cutie da take da tabbacin ƙanwarsa ce duba da yadda suke kama. Ta kuma lumshe ido tana jin yadda Hamrarh take ma ta tsiya ta hanyar faɗin.
"Oho Owkay na fahimta Tabbas kuwa ashe shi ya sa."
Banza tayi da ita don kuwa sarai ta fahimci abin da take nufi. Muryar Barrister Aeshah Ɗiya ta Biyu wurin Umma Safiya Matar Sarki Muhammad Raees ta Biyu da yara Biyu kawai gareta tare da mai martaba, Canal Nubaid shi ne Babba sannan sai Aeshah da ta kasance Barrister ce babba tana Auren wani Tantirin Matashin sanannen mai Dukiya lamba ɗaya sunan sa Sartaj Khamis Taj ana masa laƙabi da S.K Taj suna zaune a garin Abuja bata taɓa haihuwa ba.
"Adila kina lafiya kuwa?."
"Lafiya Qlau Anty Aeshah mai kika gani?."
Samira ta amsa ma ta bayan ta buɗe idanunta karo na farko a taƙin da tayi Murmushi kaɗan.
"No, tun da kina lafiya shikenan. Kai Althaf sai kuyi magana da Doctor akan sallama domin naga ƙafafuwan nata ba wani damuwa ba ne sosai kawai sai ta ci gaba da amfani da crutches kafin komai ya daidaita."
Althaf da tun shigowar hasken ruhinsa wato Arissa ya susuce da kallon ta har fitar su, yaja dogon numfashi kamar wanda ya sha gudu, ganin yadda mutanen Room ɗin suka zuba masa ido ne, yasa cikin sosa ƙeya ya nufa hanyar fita yana amsawa Barrister Aeshah da faɗin.
"Okay Sis B.B." (Big Barrister)
___
A Ranar wuraren ƙarfe Biyar Na marece Doctor da yake kula da Samira ya yi Discharging nasu domin kuwa Matsalar ƙafarta nata ba wani mai yawa bane sun bata crutches da zata ci gaba da amfani da shi kafin ƙafarta ta ta koma normal, kanta ma da ta Bugu tun washe gari ya dena ma ta zafin da yake ma ta. Sun koma can Masarautar Raees an ci gaba da kula da ita 'yan uwa suna zuwa du ba ta danma kusan yawancin su suna nan a masarautar sakamakon hutun ƙarshen Shekara da suka zo kamar yadda aka saba. Duk wannan lamarin da ake ciki, Samira taƙi bari a sanar da iyayenta, da Mai martaba Muhammad Raees ya tambaye hujja, sai cewa tayi hankalinsu ne zai tashi idan suka sama labari kuma da wuya wata shekarar su bari ta sake zuwa ita kuma tsakani da Allah tanason zuwa Nigeria kodan ta haɗu da 'yan uwanta dangin Mahaifinta sai dai Iyayenta ba son zuwanta suke ba, daga cikin dalilan ta na neman a ɓoyewa iyayenta zancen shi ne basu san Nigeria tazo ba, ƙarya tayi musu da cewa zataje Dubai Bikin School mate nata shi ne ta gudo Nigeria babu wanda yasan wannan gaskiyar sai ita da Ubangijinta.
_Kwanaki Biyu Gaba_
Alhamdulillah kam domin a halin yanzu ƙafar Samira ta fara warkewa sai dai still bata dena amfani da crutches ba Doctor ya ce ta ci gaba zuwa wani lokaci a ga abin da hali ya yi. Tun bayan komawar ta Masarautar bata kuma fitowa wajen masarautar ba, duk kuwa da son fitowa da take yi.
Daga ɓangaren Hazel kuwa sun kammala Secondary school saboda haka bata fita sosai a halin yanzu haɗuwa da Labib yana ma ta wuyar duk da kuwa da Irin son su haɗu da yake yi ba dare ba Rana idanunsa na kan ƙofar gidansu ko zai ga fitowarta sai dai Shiru.
Daga can Zamalek dake Cairo cikin Egypt kuwa Ambrah duk yadda taso da iyayenta na su barta ta tafi New York ɗin domin ganin masoyinta kuma Ɗan uwanta Taufan abu ya cutura domin duk ta inda ta ɓullo musu sun ƙi yarda har hakan ya ɗarsa kokwanto a zuciyarta game da lamarin ta fara tunanin an ya kuwa iyayenta babu abin da suke ɓoye ma ta, Gashi ko waya sun ƙi bari tayi da Taufan ɗin ta, ta dai kira Daddynsa wato Ali Taj Ozan sun gaisa daga haka babu wanda ta kuma kira domin ita Arissa bata da waya dama shi kuma Masoyin nata layin nasa ma gaba ɗaya baya shiga.
Sosai Ambrah ta shiga damuwa na wannan lamari.
Fitowarta ke nan daga Bathroom tayi wanka ta hango tsadadiyar wayarta dake saman Bed daga gefe tana ruri alamun shigowar kira, ta ƙari sa da sauri domin picking sai dai tun kafin ta ɗa ga kiran ya katse, ta sauke numfashi mai nauyi ganin sunan mai kiran.
"Dole yau na fita kota halin ƙa ƙa."
Ta faɗa a fili tana furzar da iska.
Nan da nan cikin ƙanƙanin lokaci ta shirya cikin wasu arnun dress. Body wrap gown iya gwiwa mai adon stones Mai kyalli daga gaba sannan mai igiya da wurin Bottles sai coffed trouser mai launin kore mai haske ya matseta tsam yana da yanka yanka kamar irin crazy ɗin nan ta gyara gashin kanta ya yi kyau tayi make-up saffa saffa sannan ta ɗauki Heeled Boots Shoes Black ta saka ta dubi kanta a mirror tayi Murmushi sannan ta ɗauki wata Abaya ta ɗaura saman Dress na jikinta ta ɗauki jakarta da wayarta ta fito bayan ta saka ƙaramin lufaya ta yane kanta da shi.
Sauri sauri gudu gudu take taka Benen lokacin da take saukowa Sannan bayan ta ƙari sa saukowa Down ta ƙari sa wurin iyayen ta suke zaune a Palo da alama fira suke yi ta rungumo su gaba ɗaya a tare tana Murmushi tare da manna musu sumba a goshi da yake tare suke zaune saman Sofa.
"Hey Abhie and Oum Morning ya kuke zan fice ƙawayena suna jirana ina nan dawowa ba daɗewa zan yi ba nayi alƙawari."
Lokacin da ta ƙari she maganar har ta fice daga Palon ba tare da jiran ta bakinsu ba, suka bita da kallo kawai.
Wata tsadadiyar mota Lexus LS500 Black color ta shiga sannan ta kunna ta fita daga gidan.
Da isarta wurin da ya fi kama da Hotel bayan ta shiga ciki tayi parking wurin da ya kamata daga cikin motar ta tsaya ta cire Abaya da ta saka tare da lufayan sannan ta saka kettle brim hat Mai launin baƙi da ratsi ratsin kore ta fito daga motar sannan ta shiga cikin kai tsaye ta wuce zuwa Ɗaki mai lambar da aka faɗa ma ta ta cikin wayar dake kare a kunnen ta, bayan ta shiga ta rufo ƙofar garam.🌚
Tsawon awanni biyu ta share tana cikin sannan ta fito kai tsaye ta fito daga hotel ɗin ta biya Boutique tayi siyayya Daga nan ta wuce Wurin ƙawarta tun ta Yarinta Atyaf ta daɗe sosai gidan su Atyaf daga bisani zuwa lokacin yamma tayi liƙis ta wuce gida a gajiye.
___
_Jos Nigeria_
_Samira Adila Dina (SAM POV)_
"Sannu fa kece Aaqilah da aka ce kinzo wurina ke nan."
Samira tayi maganar tana kallon Budurwar da suke tare da Teema suna zaune ne cikin wani keɓantaccen Palo. Tana Bedroom nata data sauka wata hadima take faɗa ma ta Teema sun zo wurinta ita da wata sunanta Aaqilah shi ne da jin haka Samira ta ce a kaisu Palon baƙi dake ɓangaren sannan ta fito daga Bedroom ɗin ta, ta wuce palon da Ganin Budurwar ta saki Murmushi sannan bayan ta zauna ta faɗa maganar da tayi.
Bata jira Aaqilah ta amsa ma ta ba fuskarta wadace da murmushi ta ci gaba da faɗin.
"Dama ina so nayi miki godiya na ceton mu nida Teema da kikayi, har kika so samun rauni saboda hakan ina mai baki haƙuri."
Aaqilah ta kalleta karo na farko taji ta burgeta ganin yadda take maganar ta Babu girman kai a tare da ita ko kaɗan balle alamun wulaƙanci tunda har take ma ta godiya da bata haƙuri.
Taja Ajiyar zuciya a nutse ta ce.
"No Karki wani damu dan yiwa kai ne tun washe gari na Ranar da abin ya faru ma naso nazo Asibitin na dubaki Allah bai nufa ba sai yau."
"Allah Sarki bakomai hakan ma na gode."
Samira ta faɗa.
Yayin da Teema ta zubawa Aaqilah ido cike da mamaki jin yadda tayi Maganar a yanzu babu wannan ciccijewa da take yi kuma a nutse tayi maganar.
Aaqilah ta watsa ma ta harara, sannan ta miƙe tsaye tana faɗin.
"Bari na wuce gida, ke Teema zaki tafi ne ko kina nan?."
Tayi Maganar tana sauke coals eyes nata akan Teema.
"E, nima komawa zan yi ai yamma tayi sai dai gobe nazo aiki."
"Badai tafiya zakuyi ba yanzu yanzu?."
Samira ta faɗa tana Miƙewa tare da Gyara crutches ɗin.
"E tafiya zamuyi Anty Samira Allah ya baki lafiya."
Teema ta amsa ma ta.
"Okay na gode amma kafin nan please kinsan gidan da wannan Handsome Guy ɗin yake shi da ƙanwarsa?."
Teema ta dakata da tafiyar da suka fara ta juya tana kallon Samira jin abin da faɗa.
"E Anty ai nan kusa ne ma Babu nisa."
Teema ta faɗa domin ta gane ko wa Samira take nufi.
"Okay inaso zaki rakani ne yanzu."
"Okay babu damuwa ai."
Teema ta amsa.
Samira tayi Murmushi sannan Teema ta taimaka ma ta wurin kama ma ta ta gyara sandar crutches ɗin nata dama Doguwar Gown ce a jikinta sai veil da ta yafa ba tare da ta rufe dogon gashin kanta da tayi style nasa in ponytail da hula ba, tayi rolling kanta da veil ɗin.
Fitowa suka yi su uku tare da Aaqilah ɗin da zata wuce Samira da Teema kuma su wuce gidansu Arissa...
______
# _👑Nainarh KD✍️👑_
*_The Nainarh KD_*
_Proudly Present_
*Ep_Eight.*
*❣️ TSANTSAR SO.❣️*
*The Pure Love.*
_❣️Destiny, Struggle, Inclination, Merciless, suffering, Excruciation, and Negate Pure Love.❣️_
~_From The Pen Of Nainarh KD Writer Of Sarauniyar Kyau And Aneeserh (Innocent Girl.)_~
*Dedicated To Princess Teemarh [Star Lady.]💋*
A hankali ta juya ta kalla Teema dake zaune gefe da ita saman tabarma da aka shimfiɗa musu lokacin da suka ƙari so gidan, tayi Murmushi kaɗan tana kuma bin gidan da kallo, maganar da taji an yi ne yasa ta juya domin ganin mai maganar.
"Lah Anty Samira kece a gidan namu lale lale."
Tayi Murmushi ganin wannan cutie Girl ɗin ne da har zuwa yanzu batasan sunanta ba, buɗe baki tayi zatayi magana Kakus ta riga ta da faɗin.
"Allah mai iko daga shigowa babu sallama balle gaisuwa kin zo kin cika mana kunne da ihu."
Arissa tayi Murmushi bayan ta ƙari sa wurin su ta zauna daga saman tabarman ba tare da ta kalle Kakus ba ta ce.
"Uhum ai nayi sallama kece kawai baki ji ba. Ina wuni Anty Samira ya ƙarfin jikin naki ya ƙafar?."
"Alhamdulillah naji sauƙi kina lafiya?."
Samira ta amsa ma ta sannan ita ma tana tambayar ta.
"Lafiya Qlau wallahi bari na cire hijabin nan Nazo muyi fira.".
Arissa ta faɗa tana tashi tsaye ta cire Hijabin islamiyya da ta dawo dake jikinta sannan ta kai Alkur'ani mai girma Ɗaki ta a je, ta fito tana faɗin.
"Teema yau baki tafi Tahfiz na yamma ba ina fata lafiya?."
Teema taja ajiyar zuciya ta ce.
"Kedai Arissa bari kawai Hadda ne ban wani mayar da hankali na iya ba, shi ya sa ma ban je ba domin kuwa nasan yadda zata ƙare ni da Malam Mahmoud karon ba zai mana kyau ba."
Ta ƙarishe maganar tana dariya ita ma Arissa Dariya take yi domin kuwa sarai tasan Teema da irin show da ake kwasa tsakaninta da malamin ajin nasu wato Malam Mahmoud.
"Ki dage dai nasan baki manta muna gab da yin sauka ba ki daure ki mayar da hankali."
Arissa ta faɗa.
Teema ta amsa da. "Shikenan in sha Allah zan gwada."
"Sannun ku bayin Allah na barku zaune ina tuƙa tuwo ke Arissa zo ta nan ki tayani kawo ma baƙi tuwo miyar kuɓewa nasan dai ba zasu ƙi ci ba."
Amsawa Arissa tayi tana Miƙewa tsaye yayin da Samira ta bita da kallo Teema kuwa ta ɗauki Ruwan dake gabansu wanda shigowar su gidan Kakus ta kawo musu bayan sun ma ta Bayanin godiya suka zo yima wanda ya taimaki Samira godiya acewarsu, har take faɗa musu baya nan sannan ta ce su zauna susha ko ruwa ne sun kwaso tafiya shi ne ta shimfiɗa musu tabarma ba tare da gardama ba suka zauna.
"Anty Samira ga fa tuwo raɓa raɓa Allah ya sa kin san shi?."
Arissa ta faɗa lokacin da ta ƙari so wurin sannan ta a je kwano da tuwo ke ciki sai kuma wata roba daban miyar kuɓewa ɗanya yaji haɗi sai ƙamshi take fitarwa a ciki.
"Nasan shi mana sai dai ban taɓa ci ba, amma me yasa kika ce ko zan iya ci?."
Samira ta jefowa Arissa da ta zauna gefan su bayan ta a je musu tuwon tambayar tana kallon ta.
"Ah bakomai kawai saboda naji ance daga ƙasar waje kika zo ne shi ya sa."
Arissa ta bata amsa tana dariya.
"Allah Sarki ai Mommyna tana yiwa Daddyna domin yanaso sai dai ban taɓa ci ba ita kam tana ci sosai."
"Ikon Allah."
Arissa ta faɗa. Tana shirin sake magana Kakus ta riga ta da faɗin.
"Ku Dena biyewa wannan kuji tuwon ku kunji domin kam ita bata ci sam 'yar gayu ce na lura so take ta hanaku ci."
Samira da Teema suka yi Murmushi tuni Teema ta janyo kwanon tuwon gaban ta, Arissa da ta miƙa musu ruwa da roba da zasu wanke Hannu ta ce.
"HHhH Kakus shagali kishi kike dai banacin tuwo balle nayi saurin tsufa kina kishi kar ɗan mijin naki ya susuce."
Ta faɗa tana dariya.
"Ja'ira Kawai."
Cewar Kakus tana ɓallawa Arissa harara na wasa.
Samira ta yi Murmushi tana ganin Drama da ake kwasa tsakanin cutie ɗin da taji Teema ta kira da Arissa da kuma Dattijuwar da take da tabbacin Kakar Arissa ɗin ce.
"Anty Samira kici mana."
Cewar Arissa tana kallon yadda Samira ta zubawa kwanon tuwon ido tana kokwanton ci.
"Yanzu kam a ƙoshe nake amma nayi alƙawari idan na dawo next time zan zage naci na ƙoshi."
Suka yi dariya gaba ɗaya har da ita.
Suna ɗan taɓa fira sama sama da mafi yawa Arissa ce take yi da ita Kakus nata Samira Sai dai ta bisu da ido, yayin da Teema ta zage ta buɗe ciki taci tuwo ta ƙoshi domin kuwa ba ƙaramin daɗi ya yi ma ta ba dama tayi missing tuwon Kakus sosai domin rabon ta da gidan an kwana biyu.
Bayan Teema ta kammala ta wanke Hannu suka miƙe da niyyar tafiya suka yi musu sallama sannan suka fito domin tafiya.
Idanunta suna kallon ƙasa daidai lokacin da suka fito daga gidan taji ta yi karo da Mutum ga wani daddaɗan ƙamshi da ya ziyarce ilahirin ƙofofin hancinta.
Ta sauke ajiyar zuciya ɓoyayyiya tana ɗa go softly Blue eyes nata masu matuƙar shaining tare da ɗaukar hankali ta sauke su saman kyakyawar fuskarsa mai cike da tarin annuri da haiba, sam batayi tunanin da shi tayi karo ba sanadin haɗuwar da idanunsu suka yi ya haddasa ma ta jin Damm bugu da ƙirjin ta ya yi. Ta lura da yadda ya waro ido yana bin ta da kallon mamaki sai dai tayi mamaki jin bai ce da ita komai ba koda yake duba da yanayinsa na kamala kallon farko zaka masa ka fahimci baya daga cikin waɗan nan mutanen masu hayaniya balle kuma surutu, ta sauke ajiyar zuciya a karo na ba a dadi tare da faɗin.
"Barka dama kuwa kai nake nema."
Ta faɗa idanunta akan sa fuskarsa ta nuna tsantsan mamaki bata bari ya ce komai ba ta ci gaba da cewa.
"A wancan lokacin sanadin wannan gunguren da muka yi ƙafa ta ta gurɗe shi ne sanadin da nake riƙe da crutches yanzu kuma dama kai nayi ƙoƙarin ceta har hakan ta sameni saboda haka kai ne kake da alhakin kula dani har ƙafar tawa ta warke, abin nufi shi ne kaso hamsin na lokacin ka zai koma kana kula dani da su ne har ƙafa ta ta warke duk da Doctor ya ce ba daɗe zatayi sosai ba warke ba ina fata ba zaka min mummanar fahimta ba daga gobe Deal ɗin namu zai fara."
Shiru Taufan ya yi ya harɗe hannu bibbiyu a ƙirji cike da mamaki yake bin ta da kallo sai dai ya kasa furta komai tsaban al'ajabi.
Samira tayi Murmushi tare da yin gifgif da ido ta ce.
"Zan tafi gida yanzu Gobe mu haɗu anan misalin ƙarfe Biyar na marece zuwa lokacin nake so na ɗan yawata cikin garin nan kuma Kaga yadda ƙafata take saboda haka kaga sai mu tafi tare."
"Okay."
Ya tsinci kansa da faɗin hakan a gajarce.
Tayi Murmushi sannan ta riƙe hannun Teema suka yi gaba. Arissa dake tsaye gefe babu wanda yasan da wanzuwar ta a Wurin ta tuntsire da dariya da ya saka Taufan da ya yi nisa a Duniyar al'ajabin Samira ya juyo ya kalleta.
"Mene ne kuma kike ma Dariya?."
Ya tambaya yana ɓata fuska.
"A'a ba komai kawai dai mamaki nake yi yadda ka kasa koda magana ne a gaban Anty Samira sai ma amsa ma ta umarnin da kayi kamar yaro da uban gidan sa."
"Umarni kuma?."
Ya tambaya da mamaki.
"E mana Yayana haka nake nufi ai yadda Anty Samira tayi maganar kuma baka mata ja'inja ba kowa ya gani kai tsaye zai ce umarni ta baka."
"To kaska uwar surutu naji mu shiga daga ciki."
Ya faɗa tare da riƙe hannunta suka shiga cikin Gidan yana shafa stubble short hair style na fuskarsa.
*_Samira Sam kuwa_*
Suna tafe babu um bare um um har suka ƙari sa masarautar Raees a tafiyar da suke yi a ƙasa domin ba wani nisa ba ne na azo a gani tsakanin gidan su Arissa da masarautar. Aka buɗe musu gate suka shiga ciki suna gafda da shiga Apartment ɗin da aka warewa 'yan matan kuma suke zaune ita da Hamrarh da Amrarh da sauran 'yan matan dangin Raees a ciki ta dubi Teema ta ce.
"Mene ne abin da kika sani game da Arissa da Yayanta kuma mene ne sunansa. I mean Tarihin su kuma Kinga ai ban san sunan su ba."
Tayi maganar tana kallon Teema.
Teema tayi Shiru kamar mai nazari sannan ta ce.
"E, to abin da na sani dangane dasu dai kaɗan ne kuma Sanadin Arissa ce da muke Class ɗaya da ita a Tahfiz. Abin da na sani shi ne kuwa. Shi dai sunan sa Taufan Arissa tana kiransa da Yayana ita kuma kamar yadda kika sani Sunanta Arissa wasu suna kiranta da Cutie domin kyau da Ubangiji ya halicce ta da shi, Alhaji Muhammad Ali Nakowa da Matarsa Hajiya Sumayya da Arissa take kira da Kakus muma muka kama. Aamalah ita ce kaɗai 'ya a wurin Muhammad Ali Nakowa da Matarsa Sumayya. Yayin da Taufan da kuma Arissa suke 'ya 'ya a wurin ta magana dai jikokin Kakus da Alhaji Nakowa."
"Ikon Allah amma me yasa suke zaune tare da Kakannin su na wurin uwa kuma Mahaifin su fa da ita mahaifiyar tasu Aamalah?."
Samira ta tambaya cikin sauri.
"E, to abin da na sani dai shi ne Aamalah ta tafi ƙasar Egypt domin karatu na University bata dawo ba sai da yaro da kuma wasu Larabawa kuma sojoji ne wai tayi Aure a can ne kuma ta haihu shi ne a lokacin Alhaji Nakowa da Matarsa ransu ya yi mugun ɓaci na abin da Aamalah tayi Aure ba tare da ta sanar da kowa ba har suka ƙi kulata daga ƙarshe ma suka koreta. Daga nan ba'a sake jin labari akan ta ba. Sai shekara ɗaya da ta wuce Arissa da Yayanta suka zo nan ƙasar wurin Kakannin nasu nan ne suke basu labarin sun zo ne su zauna da su tsawon shekara ɗaya daga nan zasuyi musu bayanin dalilin dawowarsu garesu ba tare da Mahaifiyarsu ba. Wannan shi ne abin da zan iya ce Miki na sani Dangane da Arissa da Yayanta nima dai a wurin Mamana nakejin wasu abubuwan."
Samira tayi Shiru cike da mamaki tana nazarin wannan labarin da Teema ta bata.
Daidai lokacin kuma suka ƙari sa bakin entrance na Apartment ɗin shiga ciki suka yi da sallama Aikuwa Samira tayi kyakykywan gani.
____
https://whatsapp.com/channel/0029VaEZtE15a2429vfcpf20
*KUYI FOLLOWING WHAT'SAPP CHANNEL NAWA DOMIN SAMUN TSANTSAR SO TUN DAGA PAGE 1 ZUWA INDA AKA TSAYA, MASU NEMAN LITTAFIN ANEESERH MA ZAKU IYA FOLLOWING DOMIN SAMUN DAGA FARKO SHIMA ZUWA INDA AKA TSAYA.*
____
# Khadeejarth Sabi'u Yahyah
*Ep_Nine $ Ten.*
*💫 TSANTSAR SO.💫*
*The Pure Love.*
*Daga Alƙalamin Nainarh KD Nkd's.🤞*
*Dedicated To Princess Teemarh [Star Lady.]💋*
_This page is honestly dedicated to Anty Aysha JB Amincin Allah ya kai miki Ubangiji ya ƙara kaifin basira da zaƙin hannu.🙏💖_
______
_Samira Adila Dina - Means= Extraordinary woman of just faith_
_____
"Anty Khairiyya kece a garin saukar yaushe?."
Samira ta faɗa cike da mamakin ganin Khairiyya Matar Canal Nubaid da tayi, ke nan dai zuwa suka yi babu sanarda wa.
Kyakyawar Matar da ba zata haure shekaru Ashirin da Takwas ba ta juyo fuskarta ɗauke da murmushi tana kallon Samira da ta ƙari so wurin ba tare da jiran Komai ba tayi hugging na ta cike da farin cikin ganin ta.
"Dina ke nan dubeki kamar wata Yarinya ƙarama zaki ɓallani fa."
Samira ta zauna saman Sofa tana faɗin.
"Ba dole ba duka a cikin farin cikin ganin ki ne ai, ina fata dai kun iso lafiya, ina Babyna take?."
Sai da Khairiyya ta zauna sannan cike da al'ajabi idanunta akan Samira ba tare da amsa maganar da tayi ma ta ba ta ce.
"Ikon Allah ke kuma mene ne ya sameki haka na ganki da crutches Hatsari kika yi ne?."
Samira ta dubi crutches ɗin da ta a je gefe bayan ta zauna sannan ta dube Teema dake tsaye gefe ta ce.
"Teema jeki gida kawai sai gobe ki gaida Mama."
"Tohm Anty Samira Allah ya tashe mu lafiya."
Teema ta amsa tare da fita daga Palon.
"Ba wai Hatsari nayi ba kawai dai tsautsayi ne da baya wuce Ranar sa amma Doctor ya ce ba daɗe wa zan yi a hakan ba."
Samira ta faɗa bayan ta amsawa Teema.
"Ayya, Allah ya kare gaba. Amma dai Madam Sarah bata sani ba ne ko, i wonder ma ya aka yi ta bari kikazo Nigeria."
Karo na biyu Samira ta murmushi har haƙoran ta farare ƙanana da su suka bayyana tuna Wacece Mahaifiyarta da kuma irin kyakyawar tsana da tayi ma Nigeria ba a dalilin komai bayyana ne ba.
"Hummm Anty Khairiyya ke nan a tunanin ki Mom zata bari nazo Nigeria ke nan bayan na faɗa ma ta nan zan zo, ai daga ita har Dad ce musu nayi Dubai zan tafi bikin wata School mate nawa shi ya sa suka bar ni, Direct ni kuma nayo nan."
Samira ta faɗa hakan tana Dariyar sheƙiyanci.
"Ya Allahu mai yadda ya so, Sannu fa Dina da ƙoƙari yanzu bakya tsoron su sani?."
"E, to ban yi tunani akan wannan ba tukunna sai dai abin da na sani shi ne bani da kalmar kare kaina wurin su especially ma Momna a duk lokacin da suka gane ina a Nigeria duk da banajin cewa nayi wani rashin kyautawa domin kuwa wurin Dangin Mahaifina nazo ban san mene ne dalilin da ya sa ita Mom bata son su ba kuma Dad yake biye ma ta kuma nima basaso nake shiga cikin Dangin Mahaifina sosai."
Samira takai zancen tana sauke ajiyar zuciya kai daga jin yadda tayi maganar kasan ba ƙaramin taɓa ma ta zuciya tayi ba. Yayin da Khairiyya ta zuba tagumi hannu bibbiyu tana sauraren ta, tabbas ta fahimci Samira kuma sosai ta bata tausayi. Ta buɗe baki domin magana. Hamrarh ta shigo palon hannunta riƙe da Baby Ɗiyar Khairiyya tana faɗin.
"Wannan 'ya batasan abin arziƙi ba sam, daga reno sai uban ihu take ma mutane duk ta hana mu sukuni ni ban ma san lokacin da ta fara ƙiuya har haka ba."
Ta ƙarishe maganar daidai lokacin da ta shigo ta ƙari sa ta miƙawa Khairiyya 'yar sannan ta zauna saman 1 sieter gefan Samira da take zaune saman 2 sieter.
Samira ta mike tana faɗin.
"Anty Khairiyya bari na shiga daga ciki zan watsa ruwa. Sister Hamrarh Barka da Rana."
"Barka dai Adila ta ya kike ya yau ɗin ya kuma ƙarfin jikin?."
"Alhamdulillah Sister na."
Samira ta amsa tana murmushi na jin daɗin irin caring da Hamrarh take bata shi ya sa take son ta kuma suka fi shaƙuwa sosai sai dai shaƙuwar da suka yi da Hamrarh bai kai kwatankwacin yadda suka shaƙu da Amrarh ba domin kuwa ita Amrarh a can Turkiya ta taso hannun Mahaifin Adila saboda yanayin halittar ta ana nema ma ta magani domin kwararrun Likitoci na Duniya sun tabbatar da cewa zata iya samun waraka daga rashin tafiya da ƙafafuwan ta da take fama dasu, shi ya sa tun tana Yarinya ta taso wurin Chief Sulaiman Mutallab Raees Mahaifin Samira, daga baya ne ta dawo Nigeria wurin Mahaifiyar su Miss Asfiya Matar Judge Junayd Muhammad Raees da suke da yara uku kacal tare kuma Triples ne maza biyu mace ɗaya, Hamrarh da Amrarh ba judge Junayd ne ya haifesu ba mahaifin su daban kuma ya rasu da daɗewa. Akwai wani sarƙaƙiya mai ban mamaki cikin labarin Miss Asfiya da yadda aka yi ta haifa Yaranta na farko twin's mata Hamrarh da Amrarh.
Direct haɗaɗɗen bedroom ɗin ta Samira ta wuce yayin da a palo Khairiyya suka ci gaba da fira ita da Hamrarh suna jiran Samira ta shirya ta fito su wuce shashen matar sarki ta farko Hajiya Bilkisu da suke kira da Ammie domin kowa da kowa duk suna can ana ta fira ita ma Khairiyya wurin Samira tazo cikin Apartment ɗin kuma ta tarar ba ta nan, shi ne tana ƙoƙarin fitowa daga Palon suka haɗu da Samira ɗin.
_SAMIRA SAM KUWA_
Akalla takai kusan mintuna bakwai cikin Bathroom tana wanka sannan ta fito ɗaure da towel white color ga ƙarami a hannunta tana goge doguwar sumar kanta mai two color kuma a haka aka haife ta sai faman sheƙi take zubawa.
Samira Adila Dina dai wata kyakyawar matashiyar budurwa ce da a ƙiyasi shekarunta ba zasu haura goma sha tara ba. Doguwa ce dirarra mai kyan diri da a turance ake kira da Hourglass Shape irin wanda mata masu zarra ne kawai suke da shi domin kuwa yafi coca cola shape kyau da kyau da kuma burgewa ga kyawawan mata da suka amsa sunan su kyawawa.
Fara ce mai masifar kyau na ƙin ƙarawa idanunta masu Shape na Almond kuwa dara dara ne gasu farare kyawawan gaske tabarakallah gata da wani cute mouth ɗan daidai kuma ɗan ƙarami domin kuwa da wuya idan mutum ya yi ƙoƙarin zura yatsun sa uku su shige ciki, hancinta dogo da shi ma sha Allah ga tsini sai dai bashi da irin tsinin nan da ya wuce kima daidai yake kuma yana daidai ne da yanayin Diamond Beauty face nata da a koda yaushe take ɗauke da murmushi saman ta. Samira irin mutanen nan ne da ake kira masu farin jini domin kuwa koda baka son ta kana haɗuwa da ita zakaji kana masifar son zama da ita koda kuwa so ɗin ba na Soyayya ba. A halayya Samira ta kasance bata da girman kai ko kaɗan sannan bata zama kusa da masu shi, tana da kirki daidai ita amma fa tana da saurin fushi, shagwaɓaɓɓiya ce ta ƙin ƙarawa, tana son mutane sosai kuma tana da ilimin boko dana addini wadatacce domin kuwa sosai iyayenta suka yi ƙoƙari wurin ganin sun ɗaura Rayuwarta bisa turba ta daidai basu ruɗata da kyalekyalen Duniya ba kuma arziƙi da jin daɗi da ta taso ta tarrar iyayenta da su bai saka tana banbance kanta da kowa ba wai taji tafi kowa sam wannan baya daga cikin halayyar Samira Sulaiman Mutallab Raees. Mom nata tana kiranta da Adila a wasu lokutan kuma Mira yayin da Daddynta yake kiranta da Dina sauran mutane kuma suka haɗe sunayen gaba ɗaya ya bada Samira Adila Dina wasu da haka suke kiran ta wasu kuma da Samira wasu da Adila wasu kuma da Dina har masu kiranta da Mira da Sam ma duka akwai domin kuwa Jarumar tamu tana da jama'a.
_BRIEF EXPLANATION KE NA AKAN SAMIRA. KU KASANCE CIKIN WAƊAN DA ZA'AYI TAFIYA NA WANNAN LABARI DA YAZO DA SALO NA MUSAMMAN DOMIN SANIN IRIN DARUSSAN DAKE CIKI_
______________________________________✍️The Nainarh KD Nkd's Ce👑
_____________________
Cikin ƙan ƙanin lokaci ta shirya cikin Capricorn shirt pink da wando High waisted flare Jeans Black sai hula turban da ta saka sannan ta saka flat shoes make-up dama already saffa saffa tayi, tayi kyau sosai kamar a wanke hannu a taɓa sannan a zura cikin jaka kana a ruga 360.🤪
Direct palo ta fito tana baza ƙamshi sai dai babu Hamrarh da Khairiyya da ta bari hakan yasa ta gyara sandar crutches ɗin ta kana ta fito daga Apartment ɗin gaba ɗaya ta wuce sashen uwar gidan mai Martaba Fulani Bilkisu....
_HAZEL POV_
Cikin waɗan nan kwanaki biyar na Rayuwar da suka gabata ta wuce su tare da wani irin shaƙuwa da ya fara shiga tsakanin ta da Labib sakamakon yawan nacinsa a gare ta yasa tun bata kulasa har ta fara sauraren sa da kuma yawan kyautata ma ta da yake ƙoƙarin yi koda yaushe ba tare da gajiyawa ba ko kyashi duk da sanin cewa ba addininsu ɗaya ba da ya yi, dama ita zuciya haka take tanason mai kyautata ma ta a koda yaushe hakan ya sa Hazel ta saka Labib cikin zuciya a ɓangare na mutane masu matuƙar muhimmanci a wurin ta ban da mahaifinta Father da Kakarta Granny Za'a iya cewa Labib shi ne mutum na uku da yake da muhimmanci wurin Hazel duk da cewa mahaifiyar tana ta raye amma bata ɗauke hakan da wani muhimmanci ba sam, domin ta taso ko fuskar mahaifiyar ta bata taɓa gani ba sai a hoto gani a hoton ma sau ɗaya kacal ta taɓa yi sam bata damu sanin wani hali mahaifiyar ta take a halin yanzu ba hasalima tayi matuƙar tsanar mahaifiyarta a Rayuwarta....
____
Granny cikin ɓacin rai ta kalla Hazel dake zaune gefanta tana kallon Wayarta ƙirar Infinix Smart 6 da Father Mahaifinta ya bata tun bayan kammala Secondary school da tayi sannan ta ce.
"Yake Hazel wai Mene ne kike nufi da kika kawo mana wannan baƙin mutumin da ya fita yanzu cikin Gidan nan me kike nufi wai da gaske ne abin da nake ji cikin gari yana yawo wai kina Soyayya da wannan Ɗan musulman?."
Hazel ta ɗa go ivy eyes na ta a daƙile take bin Granny ɗin nata da kallo karo na farko a Rayuwarta da tayi ma wanda ya girme ma ta irin wannan kallon.
"E, tabbas gaskiya ne maganar da kike ji a gari na muna Soyayya Ni da Labib kuma ina tabbatar Miki da aure zamuyi kwanan nan kiji da kunnen ki kuma shi ba baƙi ba ne domin kuwa kyakyawa ne duk da ba fari ba ne amma a hakan nakeson abina domin yana da kyakyawar zuciya kuma da kike maganar Ɗan Musulmai ai naga matan mu zasu iya auren mazan su, sai dai matan su ne Bazai yiwu su aure mazan mu ba."
Hazel ta faɗa a fusace tare da Miƙewa zata bar wurin ita kanta mamakin irin baƙaƙen kalamin da ta watsawa Granny ɗin nata take yi duk da kuwa da cewa ita taja.
Fashewa Granny tayi da kuka daidai lokacin da Father ya shigo gidan. Cikin fa ce hanci kuma da ƙarfi yadda Hazel zataji ta ce.
"Lallai Hazel kin bani mamaki kuma ki sani ina mai tabbatar miki ba zaki taɓa Auren wannan Ɗan musulman ba idan ma hakan ta kasance sai dai idan bana raye ne cikin wannan Duniyar."
Da ƙarfi kuma cikin fusata Hazel ta banko ƙofar ɗakin ta bayan ta shiga, ji kake garam gam gagam...! Har sai da ƙarar ya tsorata Granny dama kuma hakan Hazel takeso. Sai dai duk da hakan bai saka Granny ta dakata ba sai ma juyawa da tayi ta duba Father ta ce.
"Astrid kana dai ganin abin da wannan ja'irar Ɗiyar taka tayimin. Ina tsoron Tarihi ya maimaita kan sa Wallahi."
Ta faɗa a fusace tana watsa masa harara.
Nan da nan Father ya fara haɗa uban gumi duk da iskan dake kaɗawa jin kalamin mahaifiyar tasa. Hakuri ya fara bata domin ban da hakan bai san mene ne ya kamata ya yi ba, sai dai Granny taƙi sauraren sa sai ma ci gaba da sababi da tayi. Yayin da shi kuma ya yi Shiru cikin rashin abin yi domin kuwa bai san lokacin da ya yi sake har Hazel ta sake da mutane haka ba har suka fara Soyayya da wani kuma Ɗan musulmai sai dai bai ɗaura laifin hakan akan kowa ba sai a kansa gefe kuma yana tabbatar da maganar Mahaifiyar tasa Granny da ta ce tarihi zai maimaita kansa. Aikuwa Indai hakan ta kasance yana cikin wani hali mara misaltawa domin kuwa ƙiri ƙiri yake Ganin cewa reshe ne zai juye da mujiya. Babu abin da yake rayawa a Ransa fa ce na yadda zai yi ma tufkar hanci cikin sauri sauri...
___
*LABIB LAHAM POV.*
Labib ainihin Sunansa Labib Laham Asalin 'Yan Kaduna State ne iyayensa gaba da baya. Su uku ne wurin iyayen su Labeer shi ne Babba Engineer ne sai kuma Lipika mai bi masa ita kuma sannan sai Labib Auta.
Shekaru biyu da suka wuce yazo Jos yana zaune ne wurin wata Iyami Dangin Mahaifiyarsa ce Dangi na nesa sosai ma tunda yazo bai koma gida ba sai jifa jifa yake zuwa Kaduna State ya yi musu kwanaki ya dawo Jos domin anan ne yake Aiki kuma sanin hakan ne yasa iyayen sa basu taɓa masa magana akan hakan ba duk da hakan yana damun su sai dai basu da yadda zasu yi saboda irin aikin da Yaron nasu ya zaɓawa kansa na sirri fatan Nasara kawai suke bin sa da shi.
______
*AAQILAH OMAR POV.*
Koda isarta gida tasha mamakin garin Dawowar Inna Lami daga anguwa da ta faɗa ma ta ta tafi kuma ce ma ta tayi a can zata kwana. Ba ta ce komai ba tasa kai zata nufa ɗakin 'yan matan gidan da nan ne suke zaune ita da Zahrah da sauran 'yan matan gidan, dama sallama baya daga cikin ɗabi'un ta, hasalima ta manta yadda ake yi domin rabon da tayi ita kanta ta manta, abu mai kyau da ta san take iya yi a halin yanzu shi ne kawai gaisuwa shima Dan bata da yadda zatayi ne da ta yaki ce shi shima.
"Umm Aaqilah Dan Allah ki shiga Ɗakina yanzu akwai maganar da nakeso zamuyi dake ne."
Inna Lami ta faɗa cikin sanyin murya tana nufar Hanyar ɗakin ta yayin da Aaqilah tayi kamar ba zata ba sai kuma ya tafi.
"Wato Aaqilah dama bakomai ba ne dalilin da ya sa na kiraki fa ce akan wata magana mai muhimmanci da nakeso na faɗa miki duk da ban san yadda zaki ɗauke ta ba, amma ya zama dole na faɗa miki saboda hakan shi ne kawai mafita a halin yanzu."
Inna Lami ta faɗa bayan ta zauna saman tabarma a ɗakin nata. Ba ta bari Aaqilah ta ce komai ba duk da kuwa bata jin zatace wani abun ta ci gaba da cewa.
"A shekarun baya Malam Umaru wato Mahaifin ki, matan sa Biyu ni ce ta farko da aka yi mana auren haɗi kuma Auren saurayi da budurwa, sannan sai Sahura ta Biyu, sai kuma Mahaifiyar ki da ta shigo gidan nan matsayin mata ta uku wurin Malam Umaru.
A baya kafin Mijin mu Malam Umaru ya Auro Dije mahaifiyar ki sam ni da Sahura bama zaman lafiya kona misƙala zarratin domin kuwa kullum makwabta cikin rabamu faɗa suke yi masifar yau daban ta gobe daban haka Mahaifin ku malam Umaru mutumin kirki kuma mijin mu maragayi ya ci gaba da haƙurin zama da mu har Allah ya nufa ya Auro Mahaifiyar ki.
A lokacin ne kuma muka yi wani abu shi ne muka haɗe kan mu ni da Sahura kamar ba mu ba muna zaman lafiya a fili yayin da na ciki ke ciki kowa da mummanar ƙudurinsa. Watannin Mahaifiyar ki Biyu a gidan nan ta sama ciki da dalilin hakan shi ne Babban abu na farko da ya kawo haɗin kai da bana tsakani da Allah ba ne, tsakani na da Sahura muka haɗa kai muna matuƙar jizgunawa Mahaifiyar ki da uƙubobi kala kala kuma muna ma ta bazara akan muddin Malam ya sani sai mun kasheta tare da ɗan cikin ta, babu irin zalunci da mugunta da bamuyi ma Mahaifiyar ki ba daga ƙarshe ma boka muka samu muka tafi wurin sa da mummanar ƙudurinmu na hallaka Dije mahaifiyar ki da abin da yake cikinta, sai dai boka ya yi mana ɓakar ishara da faɗin babu wani asiri ko tsafi da zai yi tasiri akan ta domin kuwa bata wasa da ibada sam musamman azkhar hankalin mu ya tashi sosai da jin hakan domin kuwa boka ya tabbatar mana da mace Dije zata haifa. Abin da Malam Umaru yake mafarkin samu ke nan wato ɗiya mace domin yaran mu duka maza ne a wancan lokacin. Jin hakan ne ya sa ba tare da tunanin komai ba muka saka boka ya yi mana wani baƙin aiki akan Yarinyar dake cikin mahaifar Dije wato ke na ya ɗai ɗai ta rayuwar ki, ki taso bakya sauraren kowa kuma bakya ganin kowa da Gashi kuma ki kasance muguwar sheɗaniya da Sanadin hakan har Malam Umaru ya tsine miki kibi Duniya.
A lokacin Tabbas kishi ya rufe mana ido mun aikata abin da har mu mutu Ubangiji bazai taɓa yafe mana ba.
Domin kuwa kamar yadda mukaso haka Boka ya gudanar da aikinsa bayan haihuwarki masifa kala kala ta fara samun malam Umaru kullum babu zaman lafiya tsakanin sa da Dije yayin da ke kuma sheɗanun aljanun da aka turo suke tare dake suke sakawa kike aikata sheɗanci da rashin mutunci ga kuma rashin girmama mutane tun tasowar ki daga ƙarshe ma sanadin haka Dije ta rabu da Malam Umaru.
Sosai muka yi farin ciki da hakan domin kuwa bazan manta ba har ruwa a ƙasa Sahura ta zuba ta sha tsaban farin ciki..."
Tun da ta fara magana Aaqilah tayi shiru tana sauraren ta tsaban mamaki, kaɗuwa, ruɗani, al'ajabi tare da tashin hankali ya hanata faɗin komai har sai da taji tayi Shiru sannan ne ta sama damar faɗin.
"Yanzu da kika tsare ni kike faɗa min Sirrin ku Mene ne abin da hakan yake nufi?."
Aaqilah ta jefo ma ta tambayar ba tare da ta kalleta ba.
Inna Lami tayi Murmushi mai ciwo na nadama mara amfani ta ce.
______
*Labib shin mene ne aikin da ya kawo shi garin Jos ne?.🤔*
*Hazel sannu da ƙoƙari kam.🌚*
*Inna Lami Aikuwa ke da Inna Sahura baku kyautawa rayuwarku ba sam.*
*Turƙashi...!*
*Reader's kunji fa. Ko ya ya zata kaya???.*
*Ku sani ba'ayi komai ba cikin labarin har yanzu... Muje zuwa...!🔥*
_______
*KUYI FOLLOWING WHAT'SAPP CHANNEL NAWA DOMIN SAMUN TSANTSAR SO TUN DAGA PAGE 1 ZUWA INDA AKA TSAYA, MASU NEMAN LITTAFIN ANEESERH MA ZAKU IYA FOLLOWING DOMIN SAMUN DAGA FARKO SHIMA ZUWA INDA AKA TSAYA.*
*Ep_Eleven.*
*💫 TSANTSAR SO.💫*
*❣️The Pure Love.❣️*
Nainarh KD ✍️
*Dedicated To Princess Teemarh [Star Lady.]💋*
_Taufan means= A strong storm._
____
"Tabbas nasan na aikata kuskure masu yawa a Rayuwata ta baya sai dai a halin yanzu na tuba kuma ina ƙoƙarin ganin cewa na gyara koda kaɗan ne daga cikin kusakuren da son zuciya tare da sharrin shaiɗan suka saka na aikata. Sai dai kuma bakin Alƙalami ya riga ya bushe a halin yanzu bani da wata sauran mafita fa ce na sameki na faɗa Miki gaskiyar komai wata ƙila idan mutuwa ta tazo na mutu cikin salama domin kuwa nasan nawa ta riga da ta ƙare..."
"Wai Mene ne kike nufi ne Inna Lami nifa sam ban fahimci abin da kike nufi ba kin sakani a gaba kina wasu surutai kamar bakya a cikin hayyacinki.
Aaqilah ta faɗa tana taɓe baki domin a irin mugayen abubuwan da Inna Lami ta faɗa ma ta ta aikata kuma yanzu take ma ta wannan hawayen na munafurci a wurin ta shi ya sa ko tausayi ba ta bata ba.
"A yau na shirya na tafi wurin Bokan da muka saka ya yi mana aikin a wancan lokacin da nufin ya ƙarya komai da ya yi ki dawo hayyacinki sai dai mummanar labarin da na tarar shi ne ya yi matuƙar ɗa gamin hankali sosai kuma ya sakani a ruɗani sannan tsoron Allah ya kuma shiga ta na kuma tabbatar wa da Duniya da abin da ke cikin ta ba'a bakin komai muke ba. Allah ya yi ma Bokan da ya yi wannan baƙin aikin rasuwa shekaru biyu baya Gashi bayan shi babu wani mai iya karya baƙin Asirin sai dai wata ƙudurar ta Ubangiji."
Wani irin tsoro ne da tsananin firgici na jin kalaman Inna Lami suka jefa Zahrah dake tsaye bakin ƙofar ɗakin laɓe tana sauraren Komai domin tun lokacin da Inna Lami ta ce Aaqilah ta same ta a ɗaki haka kawai taji bata yarda da Inna Lami ba dalilin haka ya sa ta tsaya laɓe bakin ƙofar gashi ta jiyo abin da ya girme ma tunaninta. Ban da zufa babu uwar abin da take haɗawa duk tayi sharkaf da gumi ta rasa ma ya zata yi da Rayuwarta, tayi da ta sanin tsayawa bakin ƙofar har taji wannan BAƘIN SIRRI (BY Jiddarh S Mapi) ya fi cikin kwando.
Ɗakin su ta shiga ta kasa zaune ta kasa tsaye. Jin alamun motsin za'a shigo ne ya sa tayi saurin zama gefan katifa tana ƙoƙarin gyara nutsuwar ta.
Aaqilah ta shigo cikin wani irin ɓacin rai da Zahrah bata taɓa ganin ta ciki ba. Direct ta nufa Ghana Most Go da kayanta ke ciki. Ta fara kici kicin fito da kayan daga cikin.
‘‘Anty Aaqilah ina ne zaki tafi haka naga kina haɗa kaya?.’’
Ta tambaya cike da tsoro da kuma tausayin 'yar uwan nata da basa zama inuwa ɗaya ganin yadda take fito da kayan tana zubawa cikin wata madaidaiciyar trolley.
"Barin Gidan zan yi domin ba zan iya ci gaba da kwana a cikin ba har abada kuwa.’’
"Saboda me Anty Aaqilah wani abun ne ya faru?."
Zahrah ta tambaya da kyar cikin matsanancin tashin hankali tana ƙoƙarin ɓoye hawayen dake barazanar zubo ma ta.
"Zahrah..! Ki Dena pretending domin nasan kin saurare komai sannan kin san komai sannan ina mai gargaɗin ki da Babbar murya akan kada kowa ya san wannan maganar, idan kuma ba haka ba.."
Ta kaɗa kai tare da taunar harshen ta. Ta fi ce daga ɗakin riƙe da trolley da ta zuba wasu daga cikin kayanta. Zahrah ta bita da kallo baki sake cike da Tsantsar Mamaki.
Aaqilah kuwa bata kula kowa ba, tun bayan fitowarta daga ɗakin riƙe da trolley Direct hanyar waje fa nufa ta fi ce daga Gidan tana fita kuwa taci Sa'a ta haɗu da wani Ɗan Unguwan Lawal da Machine ɗin sa irin ta ‘yan acaɓa. Tare sa tayi tare da masa kwatancen gidan da zai kaita. Sannan ta hau Machine ɗin suka tafi. Zahrah da ta biyo bayan ta ta koma gida da sauri tana hawaye tun da take bata taɓa jin tausayin ‘yar uwan nata ba kalar yau a yanzu, da yake Inna Sahura Mahaifiyar Zahrah ɗin bata nan cikin gidan domin ta fita gidan sha'ani. Inna Lami kuwa kuka sosai take yi cikin ɗakin ta kukan data sani da nadama mara amfani.
_Aaqilah Kuwa._
Gidan Kakansu mahaifiyar mahaifinsu ta saka Lawal ya wuce da ita, koda isarta ta tarar da wani kayan takaici da ɓacin rai domin kuwa tarar da Kakar tasu tayi cikin hali na ciwo gashi ɗakin nata ita kaɗai matan Gidan su biyu matan Yayan Mahaifin su Aaqilah ɗin ma basa nan a gidan suna makwabtan su ana biki.
Tayi bayan gari caɓa caɓa ga ɗakin da yake wani uban wari kamar ba mutum ke Rayuwa ciki ba. Cike da Tsantsar takaici Aaqilah ta a je trolley na kayanta gefe sannan ta zage ta fara gyara Kakar tata sai da ta fara wanke ta sannan tayi ma ta wanka ta naɗo ta a zane kamar ƙaramar Yarinya ta fito da ita nan da nan ta sauya ma ta kaya sannan cikin ƙanƙanin lokaci ta gyara ɗakin fes kamar ba shi ba ƙamshi ya cika ko'ina domin kuwa Aaqilah tana da tsabta sosai kuma ta tsana ƙazanta shi ya sa ko yanzu da zata taho kamar ta sani turaren ta ta taho. Bayan shafe tsawon lokaci tana gyaran ɗakin ne bayan ta kammala gaba ɗaya ta dawo madaidaicin Palon gidan mai matsakaicin kyau ta danna wata wayar tarho dake gefe ta danna kira ta layin da gaba ɗaya yake haɗe ne da layukan yaran Kakar nasu sannan ta sanar da announcement ga kowa na cewar gobe kowa ya da kowa ya hallara gidan Alhaji Sale wato gidan da Kakar tasu take zaune ta sanar da cewa akwai taro na gaggawa kuma ana buƙatar kowa ya hallara kwansu da kwarkwatan su....
___
*Samira Adila Dina (SAM POV.)*
*Around 8:37pm.*
"Assalamu Alaikum Barka da dare Ɗan uwa shin zan iya zama?."
Ta faɗa bayan tayi sallama lokacin da ta ƙari so wurin. Althaf dake zaune ya kalleta bayan ya amsa ma ta ta zauna daga gefansa saman ɗaya daga cikin haɗaɗɗun kujerun dake zagaye da wurin hutawan da yake daga wani sashe na masarautar wurin.
"Kamar dai tunanin wani abun ne ya ɗauke wa Ɗan uwa hankali har ya yi tsit haka nan?."
Ta faɗa tana jingine bayan ta jikin kujerar da take kai wacca take fuskantar wacca Althaf yake zaune.
"E, to wani abu dai kamar hakan sai dai tunanin Cutie na shi ne yaja hankalin har haka."
"Wow cutie is it your cat?."
Ya juya ya kalleta ta zuba masa ido tana danne dariya.
"No, ba mage ba ce mutum ce kuma mace sannan Budurwa ta da Soyayyarta yake neman yimin illa a zuciya duk da cewa bani da matsala da ita domin da daɗewa mun fahimci juna duk cewa ban bayyana ma ta ina son ta ba."
Gyara zama Samira tayi da kyau tana dubansa ta ce.
"Amma wace mace ce mai zarra hakan?."
"Arissa ce mana sanyin idaniyata."
"Arissa. Arissa.."
Ta maimaita Sunan tana ƙoƙarin tuna Inda ta sani tsawon sakanni talatin sannan ta kalle sa da sauri ta ce.
"Badai Arissa dana sani ba wata fara hasken ta mai haɗe da ja Cutie da ita mai yawan fara'a sannan tana da Yaya is Like Taufan Teema ta cemin sunan sa ko, wani Dogo haka kyakyawa na gaske mara hayaniya."
"Yes ita fa wacca suka zo Hospital wurin ki ita da Yayan nata, e Taufan sunansa Abokin Arkan ne kinsan shi ma ɗin ba mai yawan surutu ba ne wata ƙila shi ya sa suka kasance abokai."
"Okay na fahimta amma mene ne ka sani dangane da ita Arissa ɗin kuma Tsawon yaushe kuke tare sannan matsalar naka da waye bayan kace Yarinyar Kum fahimci juna da ita. Kodai saboda baka faɗa ma ta kanason ta ba ne shi ya saka ka tunani?."
Althaf ya yi Murmushi mai alamomi biyu, takaici, ban Tausayi.
"Tun Watanni Goma baya na haɗu da ita lokacin ko Hausa ba sosai ta iya ba."
Ya yi Murmushi tuna lokacin da ya fara haɗuwa da Arissa sannan ya ci gaba.
"Ban san komai akan ta ba sai dai ina so na sani amma ban san wa zan tambaya ba ita kuma taƙi faɗa min. Sannan damuwata sun kasu kashi biyu ne, na farko shi ne Umma (ma'ana mahaifiyar su) so take ta haɗani da Husna Ɗiyar ƙawarta ni kuma sam yarinyar bata burgeni ta cika rawar kai, sai na biyu shi ne, Arissa ta faɗa min nan da wasu ‘yan kwanaki zan nemeta na rasa domin zasu koma ƙasar su ta faɗa min ba'a Nigeria suke ba Kawai daga haka bata kuma cemin komai ba, wannan shi ne abin da ke damuna a yanzu."
Samira taja ajiyar zuciya tana kallon gefe guda sannan ta juyo da kallon ta gare sa ta ce.
"Yanzu abin da zaka farayi shi ne ka tuntuɓe ita Arissa ɗin ta faɗa maka ainihin Labarin ta idan zata iya sannan maganar auren ka da Husna da Umma take son haɗawa zan yi iya ƙoƙarina wurin ganin hakan bai faru ba tun da bakason Yarinyar ni kuma farin cikin Ɗan uwa na shi ne a gabana."
Ta ƙarishe tana murmushi shi ma Althaf dariya yake yi. Suka ci gaba da fira cike da Nishaɗi iskar damina tana kaɗasu, suna nan zaune sai ga Canal Nubaid nan ya ƙari so Aikuwa fira ta dawo sabuwa domin kuwa ba ƙaramin shaƙuwa ba ce tsakanin Samira da Uncle ɗin nata Nubaid da ya kasance Canal ne na sojoji Matarsa ɗaya Khairiyya ‘ya ɗaya garesu Baby watannin ta biyar kacal a Duniya.
Misalin ƙarfe Biyar na marece washe gari ke nan. Zuwa lokacin kowa da kowa na Dangi na nesa dana kusa sun hallara Gidan Alhaji Sale sai gidan ya zama kamar ana sha'ani domin ba laifi suna da yawa kam.
Ta ɓangaren Arissa da Althaf kuwa zaune suke a wurin da suka saba haɗuwa shi da ita fira suke yi kaɗan kaɗan Althaf ya jefo ma ta tambaya akan sanin ko ita wacece gaba ɗaya. Arissa tayi shiru da alama tunani take yi akan ta faɗa masa ko kuwa dai.
"Althaf tabbas na yarda da kai saboda kai ɗin mutumin kirki ne wannan dalilin ne yasa zan baka labarina da babu wanda na taɓa faɗa ma sai dai kai da zaka sani yanzu."
Ta faɗa tana kallon sa sannan tayi shiru tana nazarin ta inda zata fara yayin da ya zuba ma ta ido cikin wannan taƙin Arissa ta fara bawa Althaf gaba ɗaya labari akan Rayuwarta da irin gwagwarmayar da suka sha ita da Yayan ta mai ƙaunarta da son farin cikin ta wato Taufan. Tun da ta fara bata dakata ba har sai da takai aya zuwa lokacin Althaf ko kwakwkwaran motsi ya kasayi cike da al'ajabi, ruɗani, mamaki yake bin ta da kallo, yaba Tsantsar jarunta irin na Taufan yake yi lallai ya cika ɗa kuma ɗan uwa na gari domin a yadda Arissa ta basa labarin ya yi matuƙar yabawa ƙoƙarin da Taufan ya yi.
____
*Ko mene ne abin da Samira zatayi?.*
*Shin Mene ne labarin da Arissa ta bawa Althaf wani irin gwagwarmaya suka fuskanta a rayuwarsu?.*
*Wani mataki Aaqilah zata ɗauka da ta haɗa taron family na gaggawa, shin zata tonawa Inna Lami ita da Sahura Asiri ne??.*
*Ku kasance masu bibiyar wannan labarin domin yanzu aka fara har yanzu ba'a fara komai ba chakwakiyoyi ma suna gaba.*
___
# Khadeejarth Sabi'u Yahyah
# Nainarh KD
# 08081129487 Or 07085212808.
# Nkd's ce ✍️💖🌹👑
_____________________
*Ep_Twelve.*
👑🌹 TSANTSAR SO.
*Pure Love.💖*
*_©Nainarh KD....✍️_*
*Dedicated To Princess Teemarh [Star Lady.]💋*
_Aaqilah Means = Beautiful radiant light_
______
💞Wukar fiddar giwa ba kaifi gare ta ba sai girma💞
______
_AAQILAH POV_
"Kamar yadda kuka sani ana shirya taron Ahali ne bayan an saka rana da lokaci. Sai dai wannan karon lokaci guda gaba ɗaya kuka sama kira domin taro na gaggawa gashi kuma gaba ɗaya kun hallara har da waɗan da ba'ayi tsammanin ganin su ba ko nace ba'a ganinsu a wurin sai yau cikin nufar Ubangiji sun hallara."
Ta ɗan daka tana kallon gaba ɗaya mutanen dake zazzaune wasu saman kujeru daga cikin babban baranda da aka sassaka kujeru sannan aka shimfiɗa tabarmu da wasu suke zaune. Ita tana dage tsaye ne hannunta riƙe da loudspeaker ya yin da hankulan gaba ɗaya mutanen yake a kanta.
"Ba da ɓata lokaci ba zan yi bayanin dalilin haɗa wannan taron Ahalin na gaggawa badan komai ba ne sai dan na nusar da ku wani kuskure da kuka aikata ko nace kuke aikatawa jiya na shigo wannan gida domin nayi kwanaki duk da hakan ba daɓi'ata ba ne bin gidajen 'yan uwa. Sai dai da isowa ta na tarar da abin da ya yi mugun bani mamaki kuma ya sosa rai na sosai."
Ta basu labarin irin halin da ta tarar da Kakar ta ta ciki da take Matsayin mahaifiya wurin gaba ɗaya manyan mutanen wurin sannan ta ɗaura da faɗin.
"Ku sani cewa Mahaifiya fa ta wuce duk inda ake tunani, Mahaifiya ba abin yarwa ba ce, amma ku duba ku Yaranta mata huɗu ne waɗan da kuke gidajen auren ku amma kun wofin tar da ita gefe ku sani ba ko wani abu ba ne za'ace Umma uwani da Umma Rayya zasu ke ma ta (tana nufin matan Alhaji Sale da Kakar tasu take gidan sa).
Wai shin kun manta cewa kuma kun haifa yaran ne Bakwa fata yaran ku suyi muku biyayya ko idan kun mutu su dinga bibiyarku da addu'a duka kun manta da waɗan nan abubuwan ne kuka wofin tar da wannan Dattijuwar Baiwar Allah haka sai kace ba sanadin ta kuka zo Duniyar ba. Kuyi haƙuri nasan dole maganganuna zasu ɓatawa wasun ku duba da cewa Matsayin iyaye kuke wurina amma ƙoƙarin nusar da ku kuskuren ku kawai nake yi. Domin ita Mahaifiya aljanna ce ta duniya, dukkanin wani gata da yalwar da zaka samu a duniya matuƙar baka da mahaifiya a raye, to haƙiƙa ba zaka ji daɗin wannan wadatar ba kamar ace Mahaifiyar ka tana raye, kullum kada ka dinga mantawa da ita cikin Addu'o'in ka na yau da kullum domin haƙiƙa ba zaka sami me maye maka gurbin ta ba, domin ita ce ta salwantar da dukkanin wani jin daɗinta don kawai kai kaji daɗin rayuwarka. Na roƙe ƙu da ku taimaka ku dawo da hankulanku akan mahaifiyar ku ita da take raye domin tana matuƙar buƙatar kulawar ku, kuyi ma ta biyayya ku kyautata ma ta ga dukkan abin da bai fi ƙarfin ku ba, ku sani wasu neman mahaifiyar suke yi amma bata nan garesu wasu rasuwa tayi wasu kuma ƙaddara ce ta rabasu."
Tun da Aaqilah ta fara maganar babu wanda ya iya furta komai cikin mutanen wurin mazan su da matan su ta burge wasu yayin da ta ɓatawa wasu a ganinsu ita har Wacece zata tarasu tana musu wani wa'azi ta fara gyara kanta da ɗabi'unta mana.
Murmushi kawai Hajiya Umma take yi cike da alfahari take kallon Aaqilah sam bata san Yarinyar ba domin ba son shiga Dangi take yi ba, tun da kuwa ta yi aure ita kanta zata iya ƙirga adadin biki ko suna na Dangin da ta taɓa zuwa kusan shekaru talatin da Aurenta. Ta dubi Umma Rayya dake gefanta ƙasa ƙasa ta ce.
"Wai kuwa Rayya wannan wace yarinya ce haka na lura tana da hankali da kuma nutsuwa."
Rayya da bita da kallon mamaki ganin yau Hajiya Umma ita ke yaba wata watan ma kuma Aaqilah, ta tabbatar Hajiya Umma batasan wacece Aaqilah ba shi ya sa take tambaya koda yake ma taya ya zata sani bayan ba shiga mutane take ba.
"Aaqilah ce ɗiyar maragayi Malam Umaru mai rasuwa."
Hajiya Umma ta zaro ido cike da mamaki jin abin da Rayya ta faɗa wai dama wannan ita ce Aaqilah da take jin labarin ta bakin Mutanen gari da Dangi ikon Allah amma ta shiryu ne daga irin halayenta marasa ɗa'a da take samun labari akai ko ya ya?. Wannan ce Kawai tambayar da Hajiya Umma take yiwa kanta babu mai bata amsa.
Sosai Aaqilah ta yi ma iyayen nata wankin Babban bargo (bawai cin mutunci ba, a'a cikin hikima da tausasan kalami take nusar da su kusakuren su na wofin tar da Mahaifiyarsu da suka yi abin da ya zama Ruwan dare a wannan al'umma tamu sai dai fatan Ubangiji ya sa mudace kawai) Ita kanta Aaqilah har mamakin kanta take yi yadda ta saki jiki ana wa'azi kamar wata ta Allah. 😂
(Abin da Aaqilah da Inna Lami basu sani ba shi ne babu abin da zai karya wannan Asiri sai Ranar da ɗaya daga cikin su wato Inna Lami ko Inna Sahura ta faɗa wa ita Aaqilah ɗin gaskiya sannan Asirin zai fara karyewa a hankali a hankali ba kuma lokaci ɗaya ba, so wata ƙila Asirin ya fara karyewa ne)🙀
Ta daɗe ta yi kafin daga bisani kowa ya fara tofa albarkacin bakinsa daga ƙarshe taron ya watse.
Da sallama ɗauke a bakinta ta shiga Ɗakin. Zama tayi bayan ya amsa ma ta dama tun tuni sun gaisa hakan ya sa ba tare da ɓata lokaci ba ta fara faɗin.
"Dama Yaya Sale wata magana ce nake tafe da ita da ta shafi Aaqilah."
Ta faɗa cike da ladabi ga Yayan nasu Namiji ɗaya tilo da ya yi saura dama su Biyu ne maza to Malam Umaru ya rasu saura shi ɗaya sai kuma ƙanninsa mata huɗu har da ita Hajiya Umma ɗin duk da ba Mahaifiyar su Alhaji Sale ce ba ta haifeta tun tana Yarinya ta rasa Iyayenta Mahaifin ta ƙanin Mahaifiyar su Alhaji Sale ɗin ce hakan ya sa ta karɓe ta ta ci gaba da kula da ita ta taso cikin yaran ta kuma ta haɗe da su tamkar ciki ɗaya suka fito bayan ta yi Aure ne ma da yake Ɗan Adam haka yake mai manta Alkhairi da bin ruɗin Duniya da sheɗan tun bayan tayi Aure ta rage shiga Dangin ta sosai ta rage kula kowa ko sha'ani a ke yi bata damu da ta je ba domin a ganinta tafi kowa tun da mai Dukiya take Aure kuma ɗan Sarki Muhammad Raees guda wato Alhaji Nawaz Yaransu huɗu Babban shi ne Arkan Soja ne sai Althaf bai daɗe da kammala karatun sa ba sannan sai mata Biyu ɗaya tana aure a can Jigawa State ɗayan kuma karatu take.
Alhaji Sale ya nusa tare da gyara zama yana mayar da gaba ɗaya hankalinsa a kan ta ya ce.
"To Aaqilah kuma Allah ya sa dai ba maganganun ta na ɗazu ba ne suka ɓata miki sai dai a ganina Yarinyar tana kan gaskiya duk da cewa ga kalarta ana ma ta wani kallo daban saboda ɗabi'unta amma Yarinyar kirki ce ni na tabbatar da hakan ji nake da'ace zata amince tabbas babu abin da zai hana na haɗa Aurenta da Yaron wurina Bello."😳
Ya kai zancen yana sakin Murmushi domin koba komai ai ɗiyar ɗan uwan sa ce ita duk da cewa ya san wane ne yaron nasa Bello sai dai kallon da ake masa sam ba haka yake ba.
Cikin sauri Hajiya Umma ta ce.
"A'a Wallahi Yaya ai Bama sai an yi hakan ba domin kuwa da kallon ta nayiwa Arkan na wurina riƙo yanzu haka ma akan maganar ne na taho wurin ka domin banaso a ɗauki lokaci so nake ka bani dama tun da kaima uba ne a wurin ta ina so na haɗa Aurenta da Arkan Indai ka amince haka ita ma ta amince."
Alhaji Sale ya yi Shiru da alama zancen nata yake tunani akai. Sannan ya yi 'yar Dariya kaɗan.
"Hajiya Umma ke nan ta yara duk da bakyason mu Sosai amma kinason yaran mu, to shikenan ni dai ta ɓangarena babu wata damuwa domin Arkan da Bello duka ɗaya suke a wurina, yanzu abin da za'ayi gaba shi ne tuntuɓar yaran sannan a haɗa su ma'ana su gana idan sun amince da junansu shikenan babu damuwa Allah Ubangiji ya sanya Alkhairi, sai dai kafin nan yana da kyau kiyi shawara da mijin ki sai ita Khadijatu mahaifiyar Aaqilah ɗin yana da kyau ita ma ta sani."
"E, wannan gaskiya ne Yaya Tohm shikenan in sha Allah gobe zan je gidan ita mahaifiyar Aaqilah ɗin domin mu tattauna akan lamarin kuma in sha Allah yau zamuyi maganar da Alhaji."
"Ma sha Allah Allah ya kaimu."
"Ameen."
Ta amsa, nan suka ci gaba da fira akan lamarin ta daɗe kafin ta fito ta fara shirin komawa gidan ta.
______
_SAMIRA ADILA (SAM POV)_
Tana shirin fita daga Palon ta hango Althaf shi da Arissa suna ƙoƙarin Shigowa hakan ne yasa ta koma ta zauna.
"Tun da mun shigo ba zaki saki jiki ba ko so kike ta ji babu daɗi ne dana san haka zaki koma ai da ban tambaye ki komai akan labarin ki ba."
Ya faɗa ba tare da ya kalleta ba.
"Sorry Yah Althaf kawai tuna rayuwata ce ya sakani kuka kuma nasan zan yi kewar ka."
"Ba nace Wannan Yah ɗin ya fita daga bakin ki ba ni ba Yayan ki ba ne Althaf sunana."
Ta yi Murmushi dama da gangar ta faɗa tana sane bayason tana Kiransa da Yah Althaf ɗin.
"Lah Anty Samira wai dama kece wato shi ne Yah Althaf ka ƙi faɗa min wurin Sister na zamu so ko?."
Ta faɗa lokacin da suka ƙari sa wurin suka zazzauna. Jefa ma ta wata uwar Harara ya yi bai ce Komai.
"To Ɗan lelen Hajiya Fulani wannan hararar fa sai kace zaka faso idanun waje?."
Samira ta faɗa tana ɗan darawa.
"Ki barni da ita Kawai sister ko yaushe ma ta sanki da take kiran ki da Sistern ta oho."
"HHh ai ina ga nafi ka alaƙa da ita ma."
"Kai ke a wa ke nan, Idan baki sani ba bari ki sani Samira ƙanwa ta ce ta jiki."
"Oho dai ni kuma ai surukata zata zama."
Arissa ta faɗa ƙasa ƙasa.
"Mai kika ce?."
"A'a ban ce komai ba."
Ta faɗa tana dariya tare da mayar da Kallon ta kan Samira dake bin su da kallo tana murmushi Arissa ta ce.
"Ina wuni Anty Samira ya ƙarfin jikin har kun dawo ke nan?."
"Lafiya Alhamdulillah daga ina ke nan?."
"Daga wurin da kikace Yayana zai dinga rakaki Kullum mana kuna zagaye gari har kiji sauƙi ai jiya ina jin komai lokacin da kike faɗa masa."
Samira ta zaro ido tana murmushi ita fa sam ta manta ma wallahi.
"Lallai kam Arissa ai wasa nake masa fa, haba sai kace wata mara hankali taimakon da ya yi min ma ai ya wadatar kawai jiyan na faɗa ne da wasa."
"Allah Sarki."
Arissa ta faɗa sam bataji daɗi ba taso ace da gaske Samira take yi, tun da har Yayanta ya yarda wata ƙila ai daga nan abin da take mafarki tsakanin Yayan nata da Samira ɗin ya tabbata gaskiya, sai dai ya ta iya dole ta kyale zancen tun da Samira ta ce wasa take yi.
Fira suka ci gaba yi su ukun Althaf da Arissa sai kuma Samira da jifa take sako musu baki a zancen nasu. Domin hankalinta ya fi karkata akan Wayarta dake hannunta tana sarrafa ta.
Suna nan zaune can sai ga Khairiyya ita da wata kyakkyawar Mata gefanta sun shigo suna taɓa fira.
"Barrister Aeshah ko?."
Arissa ta tambaya Althaf da yake zaune kujarar da take kusa da nata, ƙasa ƙasa tayi masa tambayar.
"E, ita ce a'ina kika santa?."
Ya tambaye ta lokacin da su Barrister Aeshah ɗin suke gaisawa da Samira har suke tambayar jikin nata dama ita suka zo dubawa da yake Barrister Aeshah da Khairiyya ƙawaye ne sosai domin sanadin ƙawancen nasu ne har Khairiyya take zuwa wurin Aeshah ɗin har Allah ya haɗa ta da Canal Nubaid suka fara Soyayya kafin daga bisani suka yi Aure.
"Kawai a TV nake ganinta idan muna kallon labarai gaskiya kyakyawa ce sosai kuma tana da kyan zuciya domin ita ɗin Barrister ce mai gaskiya a kan aikin ta Mutuniyar kirki."
Althaf ya murmusa cike da alfahari shi ma kansa kyawawan halayen Barrister Aeshah suna matuƙar burgesa babu ruwanta bata da girman kai ga kirki kowa nata ne. Yana shirin magana yaji Muryar Khairiyya tana faɗin.
"Althaf Ɗan lelen Hajiya Fulani dama kai ne anan ke nan wannnan cutie ɗin kuma Wacece kodai ita ce Cutie Arissa ɗin taka da kake bani labari?."
Ta faɗa lokacin da suka zauna gefan Samira da take kan 3 sieter gaba ɗaya suka zuba masa ido, Arissa kuwa tayi ƙasa da kanta cike da kunya ta ce.
"Ina wuni fatan na sameku lafiya?."
"Lafiya Qlau Alhamdulillah kece Arissa ɗin dai da gaske ke nan finally dai yau mun haɗu."
Suka amsa ma ta da murmushi Barrister Aeshah ɗin ce ta ci gaba da faɗin hakan.
Arissa dai Murmushi take yi ba ta ce komai ba.
Sosa ƙeya Althaf ya yi ya ce.
"Ita ce Arissa da nake gaya muku ɗin fa fatan dai matar tawa to be tayi muku?."
Gaba ɗaya Murmushi suka yi cike da farin ciki.
"Wow ma sha Allah Aikuwa gata cutie da ita kamar ɗiyar larabawa tabarakallah gaskiya tayi ɗari bisa ɗari."
"Yauwa Anty Barrister na gode sosai. Sis saura ke shin Arissa ta tayi Miki ko kuwa?..."
Ya faɗa ba tare da ya kalla Arissa da ta saki baki tana bin sa da kallon mamaki ba sai ma mayar da hankalinsa kan Khairiyya da ya yi.
"Kai kai Ai Arissa ɗin nan ita ce ƙarshe Indai wurin haɗuwa ne fa kyau komai ya yi daidai kuma ga dukkan alamu zatayi biyayya."
Gaba ɗaya suka saka dariya jin abin da Khairiyya ta ce. Harda Arissa sai da ta murmusa.
"Yauwa Sister kema godiya nake, Mira saura ke."
Ya yi maganar yana mayar da kallon sa akan Samira.
"Ikon Allah wai ita Anty Samira har sunaye nawa gare ta ne?."
Arissa ta faɗa a ranta, a fili kuwa ta mayar da kallon ta kan Samira ɗin domin jin mene ne abin da zata ce.
"Gaskiya kun dace sosai na tayaka murna da ka sama wannan Kyakykywar matsayin matar ka to be ina muku fatan Alkhairi."
Arissa ta kuma zaro ido cike da kaɗuwa da jin abin da Samira ita ma ta faɗa, ita fa ta fara shiga confusing fa wai Mene ne abin da Althaf yake nufi ne?. Ta tambaya kanta, sai dai kafin ta gama lalubo amsar da zata ba kanta ta tsinkayi muryar sa da sauri ta dubesa sai taga baya saman sofa da yake kai, tayi saurin kallon wurin da ta jiyo Muryarsa. Ta kuma zaro ido tana Miƙewa tsaye da sauri ganin Althaf tsugunne saman gwawowin sa ya yi kneel down kamar mai neman gafara, ko kafin ta gama tantance abin da take gani taji Muryarsa yana faɗin.
"Arissa kiyi haƙuri dana kasa sanar dake Sirrin dake Zuciyata sai yanzu a wannan lokacin, Arissa ina matuƙar ƙaunar ki na bayyana miki hakan ne a gaban mutanen da nafi shaƙuwa da su bawai don yaudara a gare ki ba kuma bazan tilasta sai kin soni ba, Please Arissa i you winning to marry me?..."!
Hannu takai cike da mamaki tana toshe baki domin batayi tunanin hakan ba sam. Kasa ce da shi komai tayi sai idanu da ta zuba masa suna kallon tsakiyar idanun juna, yayin da mutanen palon suke bin su da kallo suna jiran amsar Arissa har Hamrarh da ta turo Amrarh a keke suka shigo Wurin babu wanda ya lura da su.
"Althaf kai ne mutum na farko da yake kula dani da damuwa ta bayan Yayana kai ne ka ke tare da ni ko wani irin hali nake farin ciki ko damuwa koda yaushe burin ka shi ne ka ganni cikin farin ciki ina walwala kamar kowa baka taɓa kyamata ta ba, ni kuwa Althaf mene ne abin da zan yi bayan damƙa ma ka zuciyata tabbas kai kaɗai ne Namijin da ka dace da Rayuwata kuma nake fata ka zama Miji na gari gareni sannan uba na gari ga Yaran da zamu haifa. Sai dai abu ɗaya Althaf kamar yadda ka sani rayuwata akwai banbanci da kalar taka Rayuwar ka san Wacece ni a halin yanzu ka kuma san Tarihi na. Tabbas kai ɗin na musamman ne ina ƙaunar ka nima."
Ta faɗa yayin da takai left hand nata tana sha re wasu siraran hawaye da suka zubo ma ta. Yayin da Right ɗin tuni ta miƙa masa aikuwa ya zura ma ta wani Ring na Diamond mai matuƙar tsada da kyau na gasken gaske a hannun.
Gaba ɗaya Palon tafi ya ɗauka tafi raf raf cike da burgewa abin kamar irin a series film ɗin nan ya kasance.
"Wow very Amazing Althaf da Budurwa no wonder kake kakkaucewa Haneefa ashe Akwai sarauniyar zuciyarka."
Hamrarh ta faɗa lokacin da suka ƙari sa wurin da yake Haneefa ɗin ƙawarta ce ta nuna tanason Althaf shi kuma yaƙi bata fuska harta haƙura.
"Kyakykywa kuwa Sannu da ƙoƙarin sace mana zuciyar Ɗan uwa koda yaushe bashi da aiki sai Labarin ki, finally dai yau gamu mun haɗu."
Ƙasa Arissa tayi da kanta cike da kunya ba tare da ta ce komai ba tana murmushi domin kuwa Ranar yau jin ta take yi ta musamman a Rayuwarta Ranar da Althaf ya bayyana ma ta soyayyar sa gare ta.
"Kardai a takuwa surukata ehe kinji dawo nan kusa dani ma domin Hamrarh ta cika takura."
Khairiyya ta faɗa tana Dariya suma gaba ɗaya Dariyar suka saka barin ma Althaf washe baki yake kamar gonar auduga.
Fira suka ci gaba sai dai Arissa taƙi sakin jikinta kamar farko sai can Althaf ya rakata ta koma gida dan ma gidan nasu babu nisa da masarautar.
______
_AMBRAH POV_
*NEWARK LIBERTY AIRPORT (EWR) NEW YORK.*
Ta yi shu'umin murmushi ganin Oumun nata tayi picking call da tayi ma ta tun bayan fitowarta daga harabar airport ɗin lokacin da jirgin su ya sauka ta kunna wayar nata dake kashe sannan ta canza layi zuwa na kasar dama already tana da shi.
"Hello Oum Ya kike ina fata kun tashi lafiya dama na kira ki ne na faɗa Miki cewa ina New York yanzu haka saboda haka karku ɓata lokaci wurin nema na, tun da kinƙi faɗa min gaskiya a kan wurin da Masoyina yake shi ya sa nayi gaban kaina na taho sannan sanin kanki ne ban san ko'ina ba ki turomin da address na Gidan Uncle Ali Taj ta message sannan Please ki turomin kuɗaɗe domin na hannuna sun yi kaɗan ba zasu isheni ba Bye."
Ta faɗa tare da katse kiran ba ta bari ta ce komai ba.
Ta ɓangaren Dr Aadnah kuwa a zabure ta miƙe tsaye cike da tashin hankali gefe guda na zuciyarta na tafarfasa akan wannan rashin tarbiyya na Ambrah kasa faɗin komai tayi har Ambrah ta katse kiran kawai sai tabi wayan da kallo baki sake.
"Lafiya kuwa Mene ne ya faru lokaci guda kika sauya?."
Kamar wata wacca bata a hayyacinta ta juya tana Kallon mijin nata da ya yi ma ta tambayar.
"Mene ne ma bai faru ba uhum Prof yanzu rashin tarbiyyan Ambrah har ya kai ta tafi zuwa wata ƙasar ba tare da mun sani ba kuma har ta kirani tana bani umarni kamar wata 'yar cikin ta."
Shiru ya yi cike da ɓacin rai na abin da Ambrah ɗin ta yi gaba ɗaya Yarinyar tasu ta sauya daga halayenta tun dawowarta daga karatu.
"Kayi Shiru bakace komai ba?."
Ta faɗa tana fashe masa da kuka. Da sauri ya janyo ta zuwa jikinsa yana lallashi ya ce.
"Kiyi haƙuri kinji Ambrah bata kyauta ba sai dai taja ma kanta wannan mahaukaciyar zuciyar ta ta da take tunzurata tana waɗan nan abubuwan lallai zan ɗauki mummunar hukunci akan ta kuma ba zai ma kowa daɗi ba domin kuwa muddun ina numfashi da raina bazan taɓa bari Ambrah ta aura Taufan ba koda kuwa shi ne ya ce yana sonta balle kuma bana tunanin hakan Aure Tsakanin Ambrah da Taufan babu har abada domin basu dace da juna ba kwata kwata...."!
A fusace kuma a zafafe ya ƙarishe maganar domin kuwa yau Ambrah ta kai sa bango.
_Ambrah kuwa_
Taxi ta tara sannan ta shiga ba'a jima ba message ya shigo wayar tana dubawa tayi taga address ne Oumun nata ta turo ma ta, tayi Murmushin gefan baki. "Oum ke nan wato kina ta jamin rai a tunanin ki zan tsaya bayan irin marmarin son ganin Taufan da nake yi ina masa wani Irin makahon Tsantsar so da bana jin kira."
*157 West 57th street, Manhattan.*
Fitowa tayi daga Taxi ɗin da yake ba kuɗi ne a hannunta ba yasa tayi ma mai taxi ɗin transfer. Jan ye Butterfly Sun Glasses dake idanunta tayi tana ƙare wa wani makeken gida mai masifar kyau da take tsaye gabansa kallo ko ba'a faɗa ba tasan nan ne gidan da Uncle ɗin nata yake. Ta sauke Ajiyar zuciya daidai lokacin da wasu mahaukatan tsalatsalan motoci na alfarma masu masifar kyau da tsada suka fito guda shida a jere daga cikin Gidan bayan an wangale makeken gate ɗin tabi motocin da kallo ko kafin tayi wani yunƙuri gaba ɗaya motocin suka tsaya da alama umarnin hakan aka basu. Mota ta uku ce ƙirar Bentley Mulsanne white color ɗaya daga cikin securities ya ƙari sa ya buɗe ta, a hankali ƙafafuwan sa dake sanye cikin wasu tsadaddun takalma wholecuts baƙaƙe da Safa ita ma baƙa daga ciki ya zura su kafin daga bisani gangar jikinsa gaba ɗaya ya biyo baya Dogo Kyakyawan gaske Matashin Dattijon mai kammala da cikar haiba ga kwarjini yana sanye cikin wani dakakken Suit Marron color.
Sakin baki Ambrah tayi tana kallon sa kafin daga bisani ta ƙari sa wurin sa da sauri tare da Hugging ɗin sa cike da farin ciki ta ce.
"Uncle Taj..."
Ya bubbuga bayan ta a hankali yana sakin ƙayataccen Murmushin da shi kansa ya manta rabon sa da ya yi.
"Ambrah Mene ne abin da ya kawo ki nan New York babu sanarwa sannan ita ma Dr Aadnah ɗin bata faɗa min ba?."
Ya yi ma ta tambayar lokacin da suke zaune a katafaren palo na gidan da kai tsaye za'a iya kiransa da Aljanar daula na Duniya. Bayan awanni Biyu da zuwanta ke nan zuwa yanzu har tayi wanka ta shirya cikin wata Doguwar English Gown Marron mai adon stones ta saka hular Gown ɗin.
Gabanta ne ya faɗi jin irin tambayar da ya yi ma ta. Sanin wane ne shi da kuma halinsa na rashin son wasa ne bawai kuma dan bashi da kirki ba yasa ta saita kanta ta ce.
"Dama Surprising naku naso nayi shi ya sa ka ganni ba tare da sanarwa ba, amma Uncle Taj ina Arissa da Yaya Taufan ɗin suke ne naga tun da nazo ban gan su ba?."
Ta ƙarishe maganar tana ɗan dube dube a palon a tunaninta ko zata gansu. Yayin da ya yi shiru yana bin ta da kallon cike da nazari.....
_________
*Jos, Nigeria.*
"Inna-lilahi Inna-lilahi-wa-inna-illahir-raji'un wayyo Allah na wannan wacca kalar Rayuwa ce da rashin tsoron Allah ya yi yawa cikinta wayyo ni Khadijatu amma dai su Lami sun cuceni cuta ta har abada."
Kuka sosai Mamansu Aaqilah take yi kanta har ciwo yake yi cike da tashin hankali tun lokacin da Zahrah ta gama bata Labarin dukkanin abin da taci Inna Lami tana faɗa wa Aaqilah.
Ita ma Zahrah kukan take yi tayi datasanin faɗa wa Mamansu Aaqilah gaskiya da tayi ganin yadda take kuka kamar wata ƙaramar Yarinya.
Lallashin ta take yi sosai tare da ban baki sai dai da alama kamar hankalin ta ba'a jikinta yake ba wani irin tausayin 'yar nata Aaqilah ne ya far ma zuciyarta lokaci guda.
___
Ta ɓangaren Hajiya Umma kuwa a Ranar da dare bayan ta koma Gida ta sama Mijinta Alhaji Nawaz da maganar bayan ɗan lokaci da ya ɗauka yana tunani ta samu da kyar ta shawo kansa ya amince Aikuwa cike da farin ciki ta shiga yi masa godiya. Washe gari wuraren ƙarfe sha biyu na Rana tsadadiyar motar ta ƙirar Hyundai Black color tayi parking a bakin ƙofar Gidan da Mamansu Aaqilah take Aure. Ba tare da ɓata lokaci ba ta fito daga motar tana baza ƙamshi sanye cikin wata tsadadiyar Lace white color Mai ratsi ratsin gold da kuma adon stones ta yafa mayafi hannunta riƙe da tsadadiyar jakarta idan ka kalleta ka rantse ba tafi shekaru talatin da Biyar ba tsaban yadda hutu da jin daɗi ya sama muhalli a jikinta. Da sallama ta shiga gidan Mamansu Aaqilah da Teema da suke zaune saman tabarma suna gyara shinkafa ga Zahrah zaune gefansu suna ɗan taɓa fira duk da yadda Mamansu Aaqilah ɗin take jin ta kamar ba ta da lafiya tun bayan faɗa mata maganar da ya yi matuƙar tasar ma ta da hankali da Zahrah tayi a jiya a halin yanzu burin ta bai wuce ganin ɗiyarta Aaqilah ta dawo gare ta ba sannan kuma su fara nema ma ta maganin da zai karya baƙin Asirin dake tare da ita. Amsawa suka yi a tare suna mimmiƙewa tsaye cike da Mamakin ganin Hajiya Umma matar da kafin a ganta sai an yanki ticket.
"Maraba lale lale marhaban Sannun ki da zuwa Hajiya Umma ce fatan kin ƙari so lafiya?."
Mamansu Aaqilah ta faɗa lokacin da Hajiya Umma ta ƙari sa ta zauna saman tabarman bayan ta amsa gaisuwar da su Teema da Zahrah da ta tare a gidan suka yi ma ta.
Sannan suka gaisa da Mamansu Aaqilah nan dai take faɗa ma ta da magana mai muhimmanci tazo jin haka yasa Mamansu Aaqilah ta ce su shiga daga cikin ɗaki to, babu musu Hajiya Umma ta amince suka shiga ciki suka bar su Teema suna ci gaba da gyaran shinkafa da suke yi....
________________________✍️🔥🔥🔥🔥💋💋💋💋
# Khadeejarth Sabi'u Yahyah
₳.₭.₳
# Nainarh KD ✍️👑
https://chat.whatsapp.com/EbOQsBuVulF6V1iYl9WASE
*KUYI FOLLOWING WHAT'SAPP CHANNEL NAWA DOMIN SAMUN TSANTSAR SO TUN DAGA PAGE 1 ZUWA INDA AKA TSAYA, MASU NEMAN LITTAFIN ANEESERH MA ZAKU IYA FOLLOWING DOMIN SAMUN DAGA FARKO SHIMA ZUWA INDA AKA TSAYA.*
________________________✍️🔥🔥🔥🔥💋💋💋💋
*Ep_Thirteenth.*
🌹💖TSANTSAN SO.
*💞💞 Pure Love.*
*©The Nainarh KD...✍️👑*
*Dedicated To Princess Teemarh [Star Lady.]💋*
_____
Arissa Means= Beautiful name💖
______
🌹Wuyar noma kunyar fari🌹
_____
"Zan iya ganin lafiyar ƙafarta ta ki?."
Ya faɗa yana juyo da kallon sa a gare ta. Da sauri ta yi gefe da ƙafar nata gabanta na faɗuwa ta zaro ido ta ce.
"A'a wallahi ka barshi kawai ai da sauƙi ma Doctor ya ce bada jimawa ba zan warke."
Zuba ma ta ido ya yi yana kallon ta ba tare da ya ce komai ba domin shi ɗin ba mutum ne mai yawan surutu ba ita ma ta fara fahimtar hakan. Ta murmusa tana tuna haɗuwar bazata da suka yi ɗazu ta fito ita da Teema da take taimaka ma ta suna tafiya cikin garin sun yo ta bakin ruwa shi ne fa ta hangosa zaune saman wata doguwar kujera irin ta bakin ruwa nan, maganar da ya yi ne bayan ya miƙe ya dakatar da ita daga Duniyar tunani da ta fara lulawa.
"Zan wuce gida nasan yanzu haka Arissa tana jirana."
Miƙe wa tayi tana riƙe sandar crutches ɗin ta ce.
"Tohm shikenan mu tafi tare da ma kaga Teema da muke tare ta tafi gida."
Bai ce da ita komai ba ya fara takawa, tayi Murmushi da sauri tabi bayansa tana faɗin.
"Sorry ka jirani mana bakaga irin tafiyar tawa ba sai da bi a sannu."
Jerawa suka yi suna tafiyar babu um bare um um. Jin shirun ya yi yawa ne kuma a yadda ta fara fahimtar ɗabi'unsa ba maganar zai yi ba yasa ta yi gyaran Murya tana faɗin.
"Wai kai baka magana ne?."
"Mene ne nake yi yanzu?."
Shima ya tambaye ta.
"A'a ina nufin baka da hayaniya i Like it zamu iya zama abokai ai koda yake ma mun riga mun zama sai dai har yanzu baka faɗa min sunan ka baz ni kuma na faɗa maka nawa."
"Taufan Ali it's my name, and I don't like we be friends."
Samira ta kuma murmusa wa ita fa wallahi Muryarsa daɗi take ma ta shi ya sa take ƙaƙale ƙaƙalen fira da shi.
"Wow nice name and nice to meet you Mister gentle handsome but mene ne dalilin ka da ya baka sha'awar mu zama abokai?."
"Oh sunan nawa ke nan Gentle handsome?."
Ya yi ma ta tambayar yana kawar da tambayar da ita tayi masa.
"E, mana gani nayi da hakan ka dace." Ita ma ta basa amsa a gajarce.
Tafiya suka ci gaba a hankali Samira tana jansa da fira wasu ya bata amsa wasu ya shareta sai dai bakinta yaƙi shiru kamar wacca dama can surutun ya dame ta ne, duk inda suka wuce sai an bisu da kallo da yake bakin ruwan gefan gari ne shi ya sa akwai 'yar tafiya kaɗan kafin a ƙari so zuwa gidan Sarki Muhammad Raees.
*Teema Silent POV*
Da hanzari ta a je butar Hannunta bayan fitowarta daga Ban ɗaki data shiga, hanyar fita daga gidan ta nufa sai dai Muryar Mamansu da taji tana kiranta ne ya sa ta juyo tana amsawa.
"Ke ina zaki tafi haka?."
"Na'am Mama wurin Anty Samira zan koma nasan tana jirana kuma Mama wai sai kace Ni ɗin 'yar fari ce da bakyason kirana da Teema sai dai Ke, ita kuma Anty Aaqilah da take 'yar fari sai ki kirata da Ita."
Teema ta faɗa tana gwaɓe fuska.
"Oh oh oh ni Khadijatu wannnan Samira ai ko Ƙanwa ta ce ƙarshe ke nan aikin ki ke nan Samira ina kika fito Samira. Ina zaki Samira."
Teema tayi dariya.
"Wato dai Mama ba zaki kulani da magana ta ta ƙarshe ba ke nan."
"Ke ki kiyaye ni fa maza kije gidan Alhaji Sale wurin ita kice da ita ta zo gobe ina son ganinta kinji kuma bance ki daɗe ba."
"Tohm Mama bari na shiga ɗaki na canza Hijabi tukunna na tafi."
Teema ta amsa tana shiga ɗakinsu ta sauya Hijab sannan ta fito.
"Un go Wannan ki hau abin hawa kiyi sauri ki dawo."
Karɓan kuɗin da Mama take miƙa ma ta Teema tayi zatayi magana Zahrah ta shigo gidan da sallama ɗauke a bakinta.
"Wa'alaiki Salam oyo yoyo Anty Zahrah gwara da Allah ya sa kikazo kinga sai mu tafi tare ma."
Teema ta faɗa cike da murna.
"Ina ke nan zamu tafi taren?."
Zahrah ta tambaya bayan sun gaisa da Mama.
"Mama ce ta aike ni Gidan Kawu Sale wurin Anty Aaqilah please muje ki rakani?."
"Tohm shikenan muje."
Zahrah ta amsa, sallama suka yi ma Mama sannan suka fita basu daɗe da fita ba suka tare mai a daidaita cikin ƙan ƙanin lokaci ya kai su can unguwar.
"Allah ya sa ma tana gidan dai."
Teema ta faɗa daidai lokacin da suke ƙoƙarin shiga cikin gidan bata ƙari sa ba taji tayi karo da Mutum tana ɗagowa suka haɗa ido da Bello ya zuba ma ta jajayen idanunsa gabanta ne ya faɗi amma ta daure ta ce.
"Lah Yayah Bello kaine ashe kana nan?."
Ta faɗa tana kallon sa.
"Teema kike ko Ƙanwar Aaqilah?."
Ya tambaye ta, da sauri ta amsa masa da faɗin.
"E, ni ce."
"Oho to sannun ki."
Ya faɗa yana raɓa wa ta gefanta ya fi ce. Ita kuwa ta bisa da kallo tana murmushi.
"Ke Teema mene ne kuma haka kardai ace son wannan mutum kike?."
Zahrah ta tambaya tana zaro ido.
"A'a kam nima har yanzu ban tabbatar ba sai dai abin dana sani shi ne kawai yana matuƙar burgeni."
"Lallai Teema na lura kin fara zarewa fa yanzu ko akai aka ɗaura Miki Bello ai babu abin da zakiyi da shi."
Zahrah ta faɗa cike da takaici sanin ko wanene Bello da tayi.
"Hummm Anty Zahrah ke nan ki sani shi so baya ji baya gani, amma fa ni ba cewa nayi ina son sa ba kawai burgeni yake yi."
"Chabbb Allah ya kyauta to. Amma wallahi Teema duk da cewa shi ɗin Ɗan uwa ne a wurina bana miki sha'awan aurensa haba mana."
"Kedai Anty Zahrah mu bar maganar tun da har nace ba son sa nake ba shikenan magana ta ƙare."
"Oho dai ke kika sani."
Zahrah ta faɗa cike da takaicin Teema ɗin suka shiga cikin Gidan.
"Ah Bahbah kaine a garin Yaushe ka dawo ke nan aikuwa yanzu muka haɗu da Mutuniyar taka."
Bello ya faɗa lokacin da ya ƙari sa majalisar su na Samari irin sa marasa aikin yi.
"Kaidai bari kawai Bahbah gani nayi ƙurar ta lafa tun da har Sarki bai neme ni ba, na taɓa jikarsa da nayi shi ya sa na jamo amma wacece Mutuniyar tawa?."
Dariya Bello ya yi yana dafa Sule ɗin ya ce.
"Matsoracin kaya ai ba Sarki zakaji tsoro ba a halin yanzu Aaqilah ce domin kuwa kasan ba zata kyaleka ba na abin da kayi ma ta sannan Zahrah nake nufi mana Mutuniyar taka."
Ya mutsa baƙar fuskarsa ya yi yana faɗin.
"Bahbah kyale ni da zancen wannan Zahrah domin tafi ƙarfina so nayi na ɗan kwashi rabona sai dai na gano ba 'yar Duniya ba ce shi ya na fita harkar ta."
_____
"Hazel kamar akwai abin da yake damun ki ko?."
Arissa ta faɗa tana kallon Hazel da tayi Shiru kamar mai tunani suna tsaye ne ƙofar gidansu Hazel Arissa ta kawo ma ta ziyara da yake yanzu ba school suke zuwa ba shi ya sa haɗuwar take musu matuƙar wuya gashi sun saba da juna.
_____
*_Kamar yadda na faɗa muku Tsantsar so is Paid Book 500₦ ne kacal wacca ta shirya biya ta tuntuɓe ni ta wannan lambar 08148330075 via WhatsApp Only. Sannan Free Page's suna dab da ƙarewa kuyi ƙoƙarin ganin wannan tafiyar daku zata kasance 🔥❣️_*
___
*_Muddun bana ganin comments tohm next page will be delayed. 😁_*
*Ep_Fourteen $ Fifteenth.*
*The Last Of Free Page's.🙌*
💖🌹TSANTSAN SO.
*❣️The Pure Love.*
*© Nainarh KD...✍️*
*Dedicated To Princess Teemarh [Star Lady.]💋*
____
Arkan Means = The solid pillar of life.💖
________
💞Wanka da gari baya maganin yunwa💞
______
*Around 8:10pm.*
"Yah Arkan kai ne a wannan lokacin haka ina fata dai lafiya?."
Samira ta faɗa lokacin da ta ƙari sa daidai bakin ƙofar da zata sadata da Apartment nasu ta hango Arkan ɗin tsaye kamar yana jiran wani ko wata.
"Ah Mira daga ina haka?. Ƙari so mana dama wurin ki nazo akwai maganar da nakeso muyi dake yanzu idan babu damuwa?."
Ya yi maganar fuskarsa ɗauke da ƙayataccen Murmushi na musamman da ya bawa Samira mamaki domin ita a iya sanin ta da kuma yadda su Hamrarh da ma ƙannin sa suke faɗa sam Yah Arkan bashi da fara'a ga yawan muguntar sa da suke faɗa sai dai ita duk bata san da hakan ba domin bayi ma ta yake ba koda yake ma a'ina zai ganta?.
"E, wallahi daga ɓangaren Fulanin Sarki nake shi ne fa na hango ka, Tohm shikenan babu damuwa ga wuri can sai mu zauna daga can ai."
Ta basa amsa tana Kallon sa kamar yadda shi ma yake kallon ta da alama maganar da zai ma ta na musamman ne, ƙari sawa suka yi wurin da wasu ƙayatattun kujeru na zama suke da aka zagaye su daga can gefe na wurin tsakiyar su kuma madaidaicin table ne na ɗaura abubuwa Like cups of water e.t.s.
Akalla sun shafe kusan mintuna bakwai da zama shi bai ce da ita komai ba, haka ita ma batayi magana ba sai ma wasa da zara zaran yatsun hannunta da take yi. Gyaran Murya da taji ya yi ne ya sa ta ɗa go a nutse ta kallesa yana faɗin.
"Mira ki bani aron hankalin ki Dan Allah akwai magana muhimmanci da nakeso zamu yi yanzu, zan iya samun aron lokacin ki mai tsada da nutsuwar ki da yafi komai burgeni?."
Da sauri ta ce.
"E, mana Yah Arkan ka faɗa koma Mene ne ina sauraren ka."
Ta faɗa hakan tana sauke idanunta ƙasa daga kallon sa domin haka kawai taji gaban ta na faɗi tun bai faɗa abin yake son faɗi ba. Yayin da shi kuwa ya yi Shiru da alama yana nazari ne akan ta inda zai fara, ajiyar zuciya ya sauke a hankali cikin kamilalliyar Muryarsa ya fara magana nutsatsitsya kamar haka.
"Mira ban san ya zaki ɗauka maganar da zan faɗa miki yanzu ba, amma Dan Allah ina so kiyi min kyakyawar fahimta akan maganar da zan faɗa miki yanzu kinji?."
Shiru ya yi bai kuma bari ta ce komai ba ya ci gaba.
"Mira Ina son ki, ba yanzu ba, ba kuma shekara ɗaya baya ba, abin da na sani shi ne kina burgeni sosai kuma kina daga cikin irin matan da nake da muradi a rayuwata tun kina ƙaramar Yarinya nake fama da ɗawainiyar soyayyar ki, ba zan takuraki akan sai kin so ni ba, amma zan baki iya duk adadin lokaci da kike buƙata domin kiyi tunani akan lamarin."
Duk da cewa cikin nutsuwa irin tasa da kuma kamilalliyar Muryarsa yake ma ta maganar, amma hakan bai hana Samira haɗa uban gumi ba tana sauraren sa yayin da zuciyarta take tattaro ma ta wane ne Arkan da kuma irin alaƙar dake tsakanin su an ya kuwa?...
*After Some Minutes.*
Tuƙi yake yi Sannu a hankali zuciyarsa fal tunani akan shin Samira Mira ɗin sa zata amince da shi ta karɓa Soyayyar sa ko kuwa?. Tun da ya faɗa ma ta Sirrin dake Zuciyarsa kuma ta daɗe tana naƙarƙasarsa bai bayyana ma ta ba sai a yau, gashi a yau ɗin ma bai da tabbaci akan zata amince da shi As a future husband da zasu rayu tare har mutawa. Bai san iya adadin lokacin da ya ɗauka yana tunane tunane ba har lokacin da ya isa katafaren gidan Alhaji Nawaz mahaifinsa sannan ne bayan ya shiga ya ƙari sa parking lot ya faka motar a wurin da ya dace, sannan ya fito cikin nutsuwa yake tafiyar yana kiran Allah a zuciyarsa kamar koda yaushe. Tsararren part na mahaifiyarsa ya nufa kai tsaye domin tsawon yau basu gaisa da ita ba, bata nan a palo sai ƙanwarsa da yake shi Althaf kusan gaba ɗaya rayuwarsa a can Masarauta yake gudanarwa wurin Fulani Bilkisu tun yana Yaro bayan an kaisa ya ye. Kai tsaye Up ya nufa yana taka Staircase's ɗin in twins fuskarsa ɗauke da murmushi domin so yake ya faɗa wa mahaifiyar tasa babban albishir a yau na cewa yana daf da kawo ma ta Future wife tasa da ta daɗe tana masa naci akan ya yi aure duk da cewa Samira bata basa amsa ba sai dai bayajin cewa Samira zata ƙi sa wannan ne Babban gwarin giwar Arkan.
Wadatacciyar sallama ɗauke a bakinsa ya shiga Bedroom ɗin bayan ya kwankwasa ta basa izinin shiga daga ciki. Zaune ya hangota daga gefe saman Royal Bed nata tana folding Hijab da alama sallah ta idar.
"Umma Barka da dare fatan na sameku lafiya?."
Ya faɗa bayan ya ƙari sa ya manna ma ta sumba a goshi sannan ya zauna daga ƙasa saman Sallaya da tayi Sallah akan ta bata riga ta nan na ɗe ba.
"Alhamdulillah Ustaad ka baro su lafiya ya Samira da jiki?."
"Duk suna lafiya Umma ta sun ce ma a gaishe ki ita ma Samira ɗin tana lafiya Alhamdulillah."
"Madallah."
Shiru ne ya biyo baya, kafin daga bisani ta katse Shirun ta Hanyar faɗin.
"Ustaad nayi maka laifi fa ban sanar da kai ba."
Dariya ya yi a nutse kamar yadda yake komai nasa a nutse shi ya sa Umman tasu ma take kiransa da Ustaad tun yana ƙarami daga haka kuma kowa ya kama.
"Laifi kuma Umma ta wani kalan laifi ke nan?."
Hajiya Umma ta murmusa tana basa amsa da faɗin.
"Aure zan maka babban abin da kaƙi jini ke nan kuma bakwa haɗa hanya shi ya sa nace nayi maka laifi."
"Aure kuma Ummata seriously?."
Ya faɗa a ɗan daburce ba wai kuma don maganar nata ya rikitasa ko saka masa faɗu war gaba ba. Coz this is not the first time da Umma zata ce zata masa aure kuma wasa take yi ita da kanta take faɗan hakan daga baya. So shi ya sa ma bai ɗauka wannan maganar nata serious ba.
"Yeah Ustaad da gaske nake in sha Allah nan da sati biyu masu zuwa za'a ɗaura auren ka da Aaqilah domin mun gama magana da kowa har an tsayar da lokaci dama kai ne baka sani ba gashi yanzu na sanarda kai ina fata babu wata matsala ko?."
"Matsala babba ma kuwa Ummata mene ne dalilin ki na yimin haka ba tare da sanina ba Why Umma Why?.."!
Abin da yake iya furta wa ke nan a ƙasar Zuciyarsa. Yayin da a fili kuwa cewa ya yi.
"Duk abin da kika yi nasan ba kinyi ba ne domin ki Cutar dani sai ma domin tsananin ƙaunar da kike yimin. Bakomai Umma Allah ya kaimu lokacin kuma ya bamu zaman lafiya."
Ya faɗa yana Miƙewa tsaye domin a wannan lokacin shi kansa bai san inda ya kamata ya a je ƙwaƙwalwar sa ba da take barazanar tarwatse wa, zuciyarsa kuwa kamar zata buga tsaban tashin hankali da magungunan Umman tasa ta saka sa. Tun da yake bai taɓa yi ma ta musu ba akan komai kuma bayaji zai taɓa ma ta musu akan wani abun ita ɗin mahaifiyarsa ce Komai tayi daidai ne.
Sam Hajiya Umma bata lura da irin halin da ɗan nata ya shiga ba saboda farin ciki na amincewa da ya yi duk da cewa sanin kanta ne ba musu zai ma ta ba.
"Yauwa Baka jiba nace gobe ka shirya zaka ce ku gana da ita Yarinyar."
Har ya kai bakin ƙofa ya tsinkayi Muryarta tana faɗin hakan.
"A'a Umma ba ma sai mun gana ba, na yarda dake ba zaki taɓa haɗani da abin da zai cutar dani ba Allah Ubangiji ya bamu zaman lafiya kawai."
Cike da alfahari Hajiya Umma take kallon yaron nata sannan ta amsa da. "Ameen ya hayyu ya qayyum. Ustaad Allah ya maka albarka ya kuma baka yara da zasuyi maka biyayya fiye da yadda kake yimin."
Da Ameen kawai ya amsa yana ficewa daga Bedroom ɗin domin ji yake kamar ya yi hauka. Shi kansa bai san lokacin da ya ƙari sa part ɗin sa ba. Kai tsaye Bathroom ya shiga ya sakar ma kansa shower Mai sanyi a hakan da yake domin a halin yanzu bai san ma ta inda zai fara ba domin Umma ta rushe masa gaba ɗaya tsarin sa dole ne ma ya kira Taufan domin ya basa shawara akan wannan lamarin...
_____
*SAMIRA SAM POV.*
Sheshsheƙar kuka da taji ne ya sa tayi saurin nufar hanyar Bedroom ɗin da ta jiyo sheshsheƙar yana fitowa ta can. Tun bayan rabuwar su da Arkan rasa abin da ya kamata tayi a wancan lokaci tayi, shi ya sa kai tsaye ta yo part da Madam Asfiya ta sauka domin tana da tabbacin Hamrarh da Amrarh suna can. To bayan isowarta ne babu kowa Palon hakan ya saka ta tsaya tana jiran wanda zai fito shi ne fa ta jiyo sheshsheƙar kuka.
"Subhanallah Mom Asfiya mene ne yake faru wa ne?."
Ta faɗa cikin tashin hankali hango Madam Asfiya ɗin da tayi ta kifa kai tana risgar kuka.
A firgice ta ɗa go kyawawan idanunta tana kallon Samira da ta ƙari so cikin tashin hankali tana tambayar abin da ya saka ta kuka.
"Adila Mene ne ya kawoki nan, dama ban rufe ƙofar ba?."
Da sauri Samira jin abin da Madam Asfiya ɗin ta faɗa ta amsa ma ta da cewa.
"Ni ce Mom Asfiya nazo wurin Sister Hamrarh ne shi ne na tarar bata nan. Sheshsheƙar kuka da naji ne ya sa nazo nan Bedroom ɗin kuma abin mamaki naga kece mai kukan Dan Allah Mom Asfiya ki faɗa min mene ne yake faru wa da har kike kuka a wannan lokaci da girman ki hankalina a tashe yake wallahi."
Samira ta ƙarishe maganar cike da damuwa tana kallon Madam Asfiya ɗin da hawaye ya kasa dena ma ta kwarara daga kyawawan idanunta.
"HHhH Samira Mene ne ma bai faru ba dani cikin ƙasƙantacciyar Rayuwata mai cike da zallar zalunci?.... Ba zaki gane komai ba koda nayi miki bayani."
"A'a Mom Asfiya Karki ce hakan ki yarda dani ki faɗa min damuwar in sha Allah ba zakiyi nadama Ba, kuma Bi'iznillah zan tayaki da addu'a koda ba zan iya taimaka miki da komai da zai yi silar gusar da damuwarki ba."
Samira ta yi saurin tarar Madam Asfiya da faɗin hakan domin da jin yadda tayi dariya mai cike da ma'anoni kala kala. Takaici, damuwa, baƙin ciki, tsaka mai wuya tasan lamarin ba ƙaramin ba ne.
Shiru Madam Asfiya tayi tana kallon Samira tasan Samira kyakyawar yarinya ce mai kyan hali da hankali shi ya sa take burgeta. Tunani take yi akan ta faɗa ma ta damuwarta ko kuwa?. Yayin da gefe guda na zuciyarta ya fara tariyo ma ta gaba ɗaya rayuwarta na baya mai cike da baƙin ciki son zuciya zalunci danasani....
*Flash Back...*
"A Yankin Jos cikin ƙasar Najeriya akwai wani a dalin sarki Sunansa Muhammad Raees yana da mata uku ta farko sunanta Bilkisu yaranta uku sai ta biyu Safiya yaranta biyu sannan ta ukun sunanta Asiya yaronta ɗaya Sunansa Ghazi Raees tun tasowar Ghazi ya kasance yaro ne Azzalumi cikin yara 'yan uwansa bashi da Burin komai sama da ganin hawaye ana kuka koma akan mene ne kuma da wannan mummanar ɗabi'a ya taso yana da wasu mugayen halaye murɗaɗɗu da babu mai iya ja da shi ga mugunta a cikinsa sai dai ba'a iya masa komai domin uwarsa Fulani Asiya ta ɗauki son Duniya ta ɗaura akan wannan yaro nata haka ma mai martaba sarki Muhammad Raees sam basa ganin laifin Ghazi akan komai da zai aikatawa domin a ganinsu ƙuruciya ce wata Rana zai Dena sai dai abin nasa tun ana tunanin ƙuruciyar ce zai bari wata Rana har ya fara girma muna nan halayen nasa suna daɗa girmama gaba ɗaya ya addabi Mutanen gari da baƙaƙen halayensa domin ba ƙaramin abu bane a wurinsa ya kama Yarinya ƙarama ya keta alfarmarta kuma a zaune daram babu mai iya masa koda kallon banza saboda ana tsoronsa da halin sa. Tabbas Sarki Muhammad Raees ya san yaron sa Ghazi bashi da ɗabi'a mai kyau amma sam bashi da labarin Irin muna nan halayen Ghazi domin babu mai iya faɗa masa kowa tsoron Ghazi da Mahaifiyarsa Asiya yake sannan..."
Cikin sauri kyakyawar bafulatanar matashiyar budurwa da bazata haure shekaru goma sha uku ba a wancan lokaci ta dakatar da matar da take basu labarin tun bayan Ƙari sowarsu garin domin gudun hijira suka yi suna neman gidan Sarki don a taimaka musu ita da Mahaifiyarta da Mahaifinta da yayyin ta da ƙannin ta.
"Kaɗo dakata miye dalilin ki na bamu wannan labarin?."
Ta faɗa cikin dakusashiyar Hausar ta da sai da tayi da gaske sannan ta iya faɗo ta.
Matar tayi Murmushi tana cewa.
"Na faɗa muku wannan labarin ne saboda kusan ina ne inda kuke a halin yanzu gari ne da ya ke cike fal da baƙin zalunci kuma ganin ke kyakyawa ce da kyan ki yake da matuƙar ɗaukar hankali ya saka na faɗa muku saboda kuyi taka tsantsan."
Ta faɗa tare da yin gaba abin ta. Suka bita da kallon mamaki gaba ɗaya. Da kyar dai suka samu aka nuna musu Gidan Sarkin Garin Aikuwa koda suka ƙari sa suka yi masa bayanin zuwan su garin gudun hijira da basa labarin irin ta'asa da 'yan ta'adda suka yi musu a rugagen su sosai mai martaba da mutanen sa suka tausaya musu nan ba da ɓata lokaci ba mai martaba ya saka a ka basu ɓangare na musamman cikin masarautar abin da ya bawa Kowa mamaki ke nan.
A lokacin da hakan ta kasance Ghazi baya garin kwata kwata. Satin su Biyu a Garin suna zaune a musarautar cikin kwanciyar hankali a tunaninsu shikenan duk wani tashin hankali ya kau tun da sun sama matsu guni da muhalli mai kyau kuma cikin Masarauta a killa ce.
"Kayyasa wani mai ƙarar kwana ne ya shigo mini sashe na babu mahalukin da ya isa ya shigo bai fita da rauni ba."
A yadda farin Kyakykywar matashin Saurayin mai kyan ɗan maciji kai da ka gansa ka ga riƙaƙen jan wuya kuma mugun Tantirin ya yi maganar cikin la yi da alama a make yake baya a cikin hayyacinsa sai da 'yan hanjin cikin Asfiya suka kaɗa domin wanke wanke take ya shigo killataccen shashen kuma da alama bai lura da ita ba gaba ɗaya jikinta babu inda baya rawa saboda tsoro nan da nan labarin da wannan matar da suka gamu da ita ta basu ya fara ma ta yawo a kwanyar ta sam ta gaza motsi balle har ta gudu gashi wurin saƙo ne tana daga ciki shi yana bakin wurin ya yi bake bake gashi ƙaton gaske kamar bijimin sa.
"Iyeee tsuntsu daga sama gasashe Yarinya da alama baƙar ƙaddarar kice ta kawoki nan babu shakka yau zan kwashi Gara..."
Cikin la yi da alama ya fara fita ma daga hayyacinsa yake maganar yayin da yake tunkarar ta gadan gadan tana ja da baya ihu ta kurma tana ƙoƙarin rugawa da gudu domin ceton kanta daga gare sa. Ya yi saurin fisgota tayo baya hakan ya yi sanadiyar farkewar rigar jikinta gaba ɗaya nan take dukiyar Fulanin ta ya bayyana abin da suka kuma tsokale masa ido ke nan cikin zafin nama tayi ƙasa tana ƙare ƙirjinta. Kifa ma ta wani bahagon mari ya yi da ya yi sanadin ɗauke war jin ta da ganinta gaba ɗaya na wuccin gadi kuma gefan bakinta ya fashe ta ƙara kurma wani azababben ihu na wahala a karo na biyu, cikin zafin nama ya kuma kifa ma ta mahaukatan maruka sun fi Biyar gefe da gefenta sannan ya saka hannunsa ya rufe Bakinta da ƙarfin gaske don mugunta. Sannan ya fara kici kicin raba ta da kayan jikinta a wannan lokaci Baiwar Allah Asfiya tana ji tana gani wannan baƙin mugu ya keta alfarmarta cikin tsananin zalunci da mugunta babu ko ɗigon imani ya yi ma ta kaca kaca bai duba wani hali take ciki ba da Yarintarta ya sa kai ya yi gaba a binsa bayan ya gama yi ma ta cin mutunci gunin ban tausayi wa'iyazubillah....
A lokacin ko ɗa ga 'yar yatsar ta bata iya yi domin ta suma tafi so hamsin tana farfaɗo wa dan kanta saboda tsananin Azaba. Cikin wannan mummanar hali Mahaifiyarta tazo ta same ta Aikuwa a take a wurin ta yanke jiki ta faɗi sumammiya. Bayan gano ainihin abin da ya faru da Asfiya iyayenta sun yi kuka sosai da baƙin ciki na wannan baƙin tabo da Ghazi ya yi ma ɗiyarsu sai dai gudun abin da zai je ya dawo suka so ɓoye zancen suka fawwalawa Allah komai sai dai fafur ɗaya daga cikin yayyin Asfiya yaƙi amincewa da wannan baƙin zalunci da aka yi ma Ƙanwar tasa. Yana Hawaye Asfiya tana turjewa tana Hawaye da kuka haka ma iyayensu amma bai damu ba haka ya janyo Asfiya tun daga sashen da suke zaune har zuwa tsakiyar fadar Sarki Muhammad Raees aka yi sa'a kuma wanda aka zo domin sa yana hakimce cikin fadar kamar bai aikata komai ba a jiya da marece....
Ba tare da ɓata lokaci ba ya yi ma sarki bayanin abin da Ghazi ya yiwa ƙanwarsa ran mai martaba ya ɓaci sosai don kuwa ko musawa Ghazi bai yi ba a tunanin sa ai mahaifin nasa Sarki zai goya bayansa kamar koda yaushe sai dai a wannan karon abin da mai martaba ya yi ya matuƙar bawa kowa mamaki domin kuwa bayan tabbatar da gaskiya akan zancen wasu daga cikin ɗirka ɗirkan fadawan sa majiya ƙarfi ya bawa umarni suka kama Ghazi suka fitar da shi daga cikin fadar domin mai martaba cewa ya yi za'a yanke masa mummanar hukunci kuma dole ya aura Asfiya sosai Iyayen Asfiya suka yi farin ciki da hakan ta kasance domin a ganinsu gobarar titi ne a Jos, ɓa gas ta samu koba komai zasu haɗa jini da masarautar. Suna gab da fita dashi daga cikin fadar ya fakaice idanunsu ya kufce daga riƙon da suka yi masa kafin su yi wani yunƙuri cikin zafin nama ya ƙari sa tsakiyar fadar saitin wurin da wasu kaifafan takofai suke ya zaro ɗaya gadan gadan ya nufa Asfiya domin hallaka ta. domin a ganinsa saboda wannan ƙasƙantacciyar Baiwar mara galihu da ya yi ma fyaɗe mai martaba ya saka a ka ci mutuncin sa haka. Iya ƙarfin sa ya dage zai kai ma ta sara. Aikuwa Yayan ya yi saurin turata gefe ta faɗi wannan kaifaffiyar takofin dake hannun Ghazi ta samesa a tsakiyar kansa nan da nan ya faɗi yana zubar da jini kamar an buɗe famfo ko kafin ayi wani yunƙuri tuni rai ya yi halinsa. Wannan abu da ya faru ne ya kuma hasala mai martaba ganin ɗan sa na cikin sa ya yi kisan kai a gabansa. Aikuwa cikin zafin rai a Ranar ya yanke wa Ghazi hukunci kisa bayan kwanaki uku da za'a ɗauka ana gana masa mummanar azaba. Yayin da ya saka Asfiya da ko motsin kirki bata iya yi aka kaita cikin masarautar wurin uwar gida Fulani Bilkisu. Iyayenta kuwa sosai suke kuka kuma sun yi nadama na bayyana wannan lamari gashi a banza sun rasa Babban ɗan su ita ma Asfiya rai a hannun Allah.
Kwanakin Asfiya biyu a ɓangaren Fulani Bilkisu tana kula da ita yadda ya kamata a Ranar ne kuma wata ɓakar ƙaddara ta faru cikin Rayuwar Asfiya ta rasa kowa nata iyayenta ƙannin ta yayyin ta gaba ɗayan su Sakamakon gobara da ta tashi a sashen da suke ba tare da sanin su ba domin cikin dare wannan lamari ya kasance. Washe gari na Ranar kuma aka yi ma Ghazi hukunci da aka yanke masa na rataya.
*BAYA TA HAIHUWA....*
Ba'a fi watanni biyu da faruwar hakan ba a lokacin ne kuma ciki ya bayyana a jikin Asfiya bata gama farfaɗo wa daga rasa gaba ɗaya danginta da tayi ba zuwa lokacin gaba ɗaya Rayuwarta ta koma yi ne a ɓangaren Fulani Bilkisu domin ita da mai martaba sun zame ma ta Iyaye da ta rasa. Sai dai bayyanar wannan mummanar labari a gare ta ba ƙaramin tayar ma ta da hankali ya yi ba taci kuka sosai kamar ranta zai fita sanin cewa cikin dake jikinta ta Hanyar keta alfarmarta aka samu kuma uban cikin baya Duniyar ya yi ƙasƙantacciyar mutuwa sanadiyyar munanan halayen sa ita kuwa mene zata faɗa wa abin cikin nata bayan ta haifesu?. Duk yadda Asfiya taso ganin wannan ciki na jikinta ya fita ba tare da kowa ya sani ba abu ya cutura domin tana ji tana gani cikin yake ƙara girma na ban mamaki a kullum har ta shiga watan haihuwa a lokacin ba ƙaramin azaba da wahala ta sha ba kafin haife cikin nan domin sumanta yafi Hamsin tana farfaɗo wa dan kanta daga ƙarshe dai cikin ƙudirar Allah ta haifo 'yan biyu duka mata sai dai ɗaya tazo duniya ƙafafuwan bata iya tafiya da su sam kuma likitoci sun tabbatar wurin haihuwar ta ne ta samu wannan matsalar ba'a gane matsalar Bama sai dai suka fara girma suka kai minzalin tafiya. Hamrarh da Amrarh shi ne sunayen da mai martaba da kansa ya laƙaba musu. Kuma aka ci gaba da basu kulawa da ya dace yara kyawawa da su kowa tausayin su yake ji musamman idan aka tuna ta hanyar da suka zo Duniya sai dai an a je hakan a matsayin shi ne tasu ƙaddarar da ga su har mahaifiyar tasu. Shekarun yaran uku a Duniya mai martaba ya yanke wani hukunci da ya bawa Kowa mamaki hukuncin kuwa shi ne aurawa yaron sa Junayd Baiwar Allah Asfiya da ya yi ne bayan sanin cewa shi Junayd ɗin bai taɓa Aure ba. Wannan abu ba ƙaramin farin ciki ya saka wasu ba yayin da wasu suke ganin ba'ayi ma Junayd adalci ba musanman da ya kasance Nawaz ƙiri ƙiri ya nuna yanason Asfiya shi da yake da mata amma mai martaba bai basa ita ba ya ba Junayd yaron Bilkisu. Kasancewar gaba ɗaya yaran Fulani Bilkisu sun taso ne cikin tarbiyya da kuma biyayya ga na gaba da su musamman ma mahaifinsu mai martaba wannan dalilin ne ya saka Junayd bai yi musu ba sam akan wannan hukunci da Mai martaba ya yi bayan ɗaura Auren da satikai Biyu ya ɗauke Asfiya da yaranta suka koma Babban birnin tarayya da zama domin a can ne yafi gudanar da rabin Rayuwarsa kasancewar sa Alƙali ne shi can Abuja suka ci gaba da gudanar da Rayuwarsu yana riƙe da Hamrarh da Amrarh tsakani da Allah tamkar shi ne real mahaifinsu bai taɓa yi musu koda kallo a matsayin ba shi ne mahaifin su ba kuma tsawon waɗan nan shekaru Asfiya bata taɓa haihuwa ba a tare da Judge Junayd Muhammad Raees kuma bai taɓa nuna damuwa akan hakan ba domin a ganinsa lokaci ne bai yi ba kuma Allah bai manta da su ba. Bai ma taɓa tunanin ƙara Aure ba haka suka kasance a taƙaice....
*Present...*
Wani irin gumi ne na tashin hankali yake ketowa Hamrarh gaba ɗaya jikinta babu inda baya rawa tsaban tashin hankali na jin wannan labari da Mom nasu take bawa Samira dama tana gabda shiga Bedroom ɗin Mom ɗin nasu ne domin tayi ma ta sai da safe zata koma Apartment ɗin su shi ne fa ɓakar ƙaddarar ta ta saka kunnen ta suka jiyo ma ta wannan mummanar labari na Asalin ta wai dama duk irin matsanancin ƙauna da kulawa da wannan mutumin da suke yiwa kallon mahaifi a gare su yake basu dama ba shi ne ya haifesu ba. Inna-lilahi ji take gwara ma ta mutu ta huta da wannan baƙar ƙaddara haka shikenan taƙama da take yi da isa da gadara cikin ƙawayenta na cewa Chief Judge na ƙasa shi ne mahaifi a gare ta ashe zan ce ba haka yake ba. Da sauri ta fice daga Palon ba tare da kuma jiran abin da zasu ci gaba tattaunawa ba.
Samira kuwa..
Gaba ɗaya ƙwaƙwalwarta ta kasa samun killataccen wuri da zata a je wannan labari da Mom Asfiya ta bata dama haka ainihin lamarin ya kasance wannan ne dalilin da ya saka basu taɓa ganin dangin Mom Asfiya ba kuma bata ma magana akan su wai kuma da gaske Uncle Judge ba shi ne mahaifin su Hamrarh da Amrarh ba rasa wanene zata tausayawa cikin su tayi shin Uncle Judge zata tausayawa ko kuwa Hamrarh da Amrarh ko Mahaifiyarsu Mom Asfiya jiki a saluɓe take ba Mom Asfiya Baki akan ta yi haƙuri ta dena wannan kuka sai da ta tabbatar ta dena sannan ta miƙe jiki babu laka zata bar Bedroom ɗin Mom Asfiya ta riƙo hannunta da sauri Samira ta juyo tana kallon ta. ta sha re hawaye ta ce. "Mira kiyimin alƙawari babu wanda zai san wannan labarin da na baki?."
"Nayi miki Alƙawari Mom Asfiya in sha Allah da bakina bazan sanarda kowa wannan labari ba."
Samira ta amsa ma ta sannan tayi ma ta sallama ta fi ce daga part ɗin gaba ɗaya Direct Apartment nasu ta koma kai tsaye ta wuce Bathroom wanka tayi ta fito chest ɗin ta ɗaure da towel ga ƙarami tana goge sumar kanta da shi. Cikin ƙanƙanin lokaci ta shirya cikin sleeping dress sannan bayan ta kammala komai na al'ada da ta saba before ta kwanta ne ta zaune gefan Bed hannunta riƙe da wayarta ta dannawa Mahaifinta kira ba tare da tunani akan Komai ba. Murmushi tayi bayan ya yi picking call ta gaisheta suka gaisa sannan cikin nutsuwa ta ci gaba da cewa.
"Am so sorry Dad nayi muku ƙarya nace zan tafi bikin shi ne nazo Nigeria."
Shiru ya yi daga can ɓangaren yana sauraren ta. Jin bai ce komai ba ne yasa ta ci gaba da cewa.
"Sai dai ban yi nadamar zuwa ba domin kuwa na sama ƙarin ilimi akan rayuwa kuma nasan abin da ya shige min duhu. Dan Allah Dad zan iya sanin ainihin tarihin masarautar Raees a bakinka please Dad karka tambaya dalili.''
Yana kishingiɗe ne amma jin kalaman ta na ƙarshe bai san lokacin da ya miƙe tsaye ba yana faɗin.
"Adila ban damu da ƙarya da kikayi min har kika taho Nigeria ba, amma me yasa kikeson sanin tarihin masarautar Raees?."
"Please Dad ba wani abu ba ne fa kawai dai ina son sani ne idan babu damuwa?."
Ta yi saurin faɗar hakan da fatan ya faɗa ma ta Komai domin lamarin zai fi zuwa ma ta a yadda take so komai zai zo ma ta da sauƙi na daga binciken ta.
"Adila ki kula da kanki in sha Allah nan da five days zamu taho Nigeria ɗin ni da Mom naki idan na zo zaki san komai."
"Da gaske Dad kai da Mom zakuzo?."
"In sha Allah."
Ya bata amsa.
"Tohm shikenan Dad zan jira zuwan ku."
Canza firar ya yi suka ci gaba da wani daban sun daɗe suna wayan kafin daga bisani suka yi Sallama zuciyar Chief Sulaiman Mutallab Raees cike fal da tunane tunane daban daban akan dalilin Samira na son jin ainihin labari akan masarautar Raees....
Hamrarh kuwa...
Da fitowarta kai tsaye sashen matar Sarki ta uku ta nufa wato Fulani Asiya zuciyarta fal da tunane tunane ta ƙari sa shashen kaɗan daga ciki kuwa shi ne bai wuce na tuno yadda matar take matuƙar son su da nuna musu kulawa ba, wai dama dalilin ke nan ita ce ainihin Kakarsu bawai Fulani Bilkisu ba kamar yadda suka yi zato kuma suka taso tunaninsu a hakan yake...
"Hamrarhtu kece yau da ƙafar ki a shashena ah maraba lale lale marhaban da zuwa ga wuri zauna Shalele."
Gaba ɗaya wannan maganganun Fulani Asiya ce da take kishingiɗe amma ganin Hamrarh ta miƙe jiki na rawa tana ma ta Barka da zuwa cike da matsanancin murna.
Zama kawai Hamrarh tayi tana ƙarewa Fulani Asiya kallo kai tsaye ta ce.
"Wai da gaske ne da gaske mummunar labarin dana samu a yau na cewa Ghazi wato ɗan ki matacce shi ne uban mu ni da Amrarh?."
Wani irin mugun Bugu ƙirjin Fulani Asiya ya yi jin tambayar da Hamrarh tayi ma ta amma ta daure ta ce.
"Hamrarhtu wannan wani magana kike faɗa haka wanene ya faɗa Miki wannan maganar mai kama da ƙanzon kurege?."
"No ba musu nake buƙata muyi dake ba Just tell me the real truth kawai da gaske Ghazi shi ne uban mu ni da Amrarh ko a'a?."
Cikin rawar jiki dana Murya Hawaye na fara ambaliya a saman suntuma suntuman Kumatunta Hajiya Asiya ta amsawa Hamrarh da cewa.
"Tabbas Hamrarhtu haka zancen yake ku ɗin nan jikokina ne ba wai jikokin Bilkisu ba kuma ɗa na Ghazi shi ne uban ku na ainihi ba wancan Junaydun ba."
Miƙewa Hamrarh tayi domin taji kuma ta tabbatar da abin da ya kawo ta. Ba tare da ta kuma cewa komai ba ta kama Hanyar ficewa daga sashen. Fulani Asiya tana kwaɗa ma ta kira amma ko waigowa batayi ba saboda tsananin yadda zuciyarta take tafarfasa. Sai da Fulani Asiya ta tabbatar da fitar Hamrarh ta saki shu'umin murmushi tana goge hawaye ayyana wa take yi a zuciyarta Tabbas lokaci ya yi da zata nunawa kowa ainihin kalarta zata fara ɗaukar fansa bisa abin da aka yi ma ta ita da maragayin yaronta dole ne ta ɗauki fansa da mummanar hukunci da bazai yiwa kowa daɗi ba kuma akan mijinta mai martaba zata fara ɗaukar fansar nata domin kan mai uba da wabi zatayi mutuwar Ghazi yaronta ɗaya tilo ya dawo ma ta sabo....
______
*HAZEL POV....*
*Around 2:00am.*
Ta shirya cikin wasu fararen kaya Doguwar riga ta baje dogon gashin kanta mawadaci har gadon bayanta gashi baƙin ƙirin da shi ta saka farar toka ta shafe gaba ɗaya fuskarta. Dariya Kawai take yi lokacin da taga kanta a madubi duk wannan abun tanayi ne domin ta tsorata Granny don ta bari ta Aura muradin zuciyarta Labib kuma duka hakan shawarar Arissa ce domin ita ce ta kawo ma ta Doguwar Rigar ma. Cikin wannan talatainin tsohon daren ko tsoro babu ta fito daga ɗakinta a haka da take kai tsaye ta nufa ɗakin Granny. Ta tura ƙofar a hankali ta buɗe sannan ta shiga daga ciki hango Granny ta yi baje tana kwasar bacci. Dariya tayi ta kashe hasken ɗakin sannan ya ƙari sa wurin ta tsaya kan Granny tunani take yi akan ta inda zata fara nan da nan wani abu ya zo kanta. Doguwar sandar dake Hannunta ta fara zungurin Granny da shi a hankali ba yadda zataji zafi ba don ta farka ne Aikuwa Granny ta fara mutsu mutsu zata farka tana buɗe idanunta masu cike da bacci tayi kyakyawar gani domin fatalwa take gani ƙiri ƙiri a gaban ta daburce wa tayi ta rasa mene ne ya kamata tayi gaba ɗaya jikinta ya ɗauki rawa cike da tsoro saura kaɗan fitsari ya zubo ma ta. Dariya Hazel take ɓoyewa ganin yadda Granny duk tabi ta daburce magana ta fara cikin lauya murya zuwa mai kama da ta fatalwa ɗin kamar yadda Granny take tunanin ita ce gaban ta. "Wato kece fil Adama da kike ƙoƙarin raba masoya har kike cewa sai dai idan bayan ranki ne aure zai gudana tsakanin Jikar ki da Ɗan Musulmai ko to tun da haka ne mun zo ne mu ɗauki ran naki domin su yi Aurensu tun da kince muddun kina raye hakan ba zai taɓa faruwa ba."
Cikin matsanancin tsoro da tashin hankali har tana sakin fitsari da ya matsi mararta Granny tayi saurin cewa.
"Ni a wa ni ɗin banza a banza na rantse da jikata hazel bazan taɓa hanata Auren Ɗan Musulmai ba dama kawai na faɗa ne da wasa amma ni a wa da zan hana ta abin da take so kuyi min rai ku kyaleni ban shirya mutuwa yanzu ba."
Dariya ne yaso suɓucewa Hazel jin maganganun Granny wato tsofai tsofai da ita wai bata shirya mutuwa yanzu ba. Ta daure ta ci gaba da tsorata Granny har sai da ta bata Tausayi sannan ta saka tayi ma ta Alƙawarin zata bari jikarta Hazel ta aura ɗan Musulmai kana Hazel ta saka Granny tayi Baccin dole sannan ta samu ta lallaɓa ta fito daga ɗakin kai tsaye ta koma ɗakinta cike da farin ciki ta sauya kaya sannan ta wanke fuskarta ta kwanta abin ta ranta ƙal..... Aikuwa washe gari da safe tayi mamakin ganin Granny ta sameta tana bata haƙuri kuma ta sanar da ita ta amince ta aura Ɗan Musulman cike da farin ciki Hazel ta amsa ma ta tana ɓoye dariya sannan ta koma ɗakin ta kira Labib cike da farin ciki take sanar da shi Granny ta amince da shi matsayin Mijinta ya nuna ma ta farin cikinsa sosai nan dai suka ci gaba da fira kafin daga bisani suka yi sallama Hazel ta shirya domin zuwa gidansu Arissa ta bata labarin komai.....
*BAYAN KWANAKI BIYU...*
Cikin Dariya irin ta sheƙiyanci ya kuma cewa.
"Wai da gaske kake?. Kai amma fa friend na tausaya maka ka bari idan muka haɗu zamu tattauna akan lamarin."
Ta ɓangaren Arkan da yake sauraren Taufan bayan Arkan ya gama basa labarin irin matsanancin hali da yake ciki yanzu yana ji Taufan yana masa Dariyar sheƙiyanci amma ya daure ya amsa ma sa da faɗin. "Shikenan friend mu haɗu anjima kawai.." Amsa ma sa Taufan ya yi sannan suka yi sallama.
"Dama kana Dariya Kamar hakan?."
Samira da take zaune gefansa ta tambaya da mamaki tana zuba ma sa ido cike da burgewa.
"Dama Akwai wanda baya dariya ne?."
"E, mana ai ni na ɗauka bakayi sai dai murmushi."
"Yana yi ne kawai kuma da dalili."
"Tohm shin zan iya sanin dalilin?."
"E to akan wani abokina ne yake tsaka mai wuya."
"Kamar ya ya ke nan shi ne kuma kake masa Dariya?."
Samira ta kuma tambaya da sauri.
"Kin cika surutu fa."
"Sorry Gentle handsome."
Ta faɗa tana murmusa wa. Kallon ta ya yi ƙasa ƙasa ya ce. "See you your face. Tsakar Mai wuya da yake ciki akan Soyayya ne sai da ya bayyana wa wata Soyayyarsa a gare ta bayan ya koma gida mahaifiyarsa take sanarda shi tayi masa mata kuma saura two weeks bikin domin an gama Komai. Shi ne fa dalilin da nake masa Dariyar bayan ya bani labari."
"Ayya Allah Sarki lamari na Soyayya gaskiya na tausaya masa Sosai amma yanzu wani hukunci ya yanke akan lamarin. Ina nufin zai yi ma Mahaifiyar sa biyayya ya aura zaɓin ta ko kuwa dai zai bi son zuciyarsa ya bijirewa mahaifiyarsa ya aura wacca yake so?."
"E to abin da zamu tattauna da shi ke nan bayan mun haɗu ɗin amma a ganin ki mene ne ya kamata ya yi?."
Samira ta saita nutsuwarta.
"Bin Iyaye dai bin Allah ne Tohm idan ni ce a situation da yake ciki yanzu. Kawai zan yi haƙuri da komai nayi ma mahaifiyata biyayya ne domin masu iya magana suka ce abin da Babba ya hango yaro koda ya hau bishiyar Rimi bazai hango ba kuma kaga ai idan mutum yana buƙatar albarka a Rayuwarsa dole sai ya yi ma iyayensa biyayya wannan shi ne."
Nutsuwa Taufan ya yi yana sauraren Samira karo na farko ta burgesa kuma maganganun ta sun tuno masa da Rayuwarsa na baya da irin sadaukarwa da ya yi. Jiki a saluɓe ya miƙe tsaye yana faɗin.
"Tohm shikenan koma Mene ne zan wuce yanzu kuma zan bashi shawara da ya kamata mun gode da tunatar wa."
Miƙewa Samira ita ma take ƙoƙarin yi amma ganin wani ƙaton maciji daga gefanta bata san lokacin da ta data tsalle tayi wurgi da sandar crutches da take basaja da ita ba ta ɗafalfale Taufan cike da tsoro yayin da Taufan ya bita da Kallon mamaki Ganin ta daka tsalle ba tare da ta faɗi ba kuma wai ƙafarta da ciwo an ya kuwa?...
Da gudu wasu yara suka ƙari so wurin suna dariya suka ɗauke macijin ashe na roba ne suke wasa da shi.
Zaro ido Samira tayi cike da kunya tana janye jikinta daga kyakyawar Rungumar da tayi ma Taufan shi kuwa da kallo kawai ya bita.
"Wannan kallon fa sorry fa dama Kawai ina jin daɗin kasancewa a tare da kai ne wannan dalilin ne yasa bayan ƙafa ta ta warke ban sanarwa kowa ba."
Ta faɗa cike da kunya tana gefe da kai. Murmushi kawai ya yi yana Girgiza kai ya yi gaba abin sa da sauri ta bisa tana faɗin.
"Baka ce komai ba Mr Gentle handsome so nake mu zama abokai fa."
Juyowa ya yi yana kallon ta kamar yadda ita ma ta zuba masa kyawawan softly Blue eyes nata.
"Ai tun tuni mu abokai ne."
Ya faɗa yana ci gaba tafiyarsa. Da sauri ta kuma bin sa tana Dariya. Suka ci gaba da tafiya a tare tana jansa da fira.
LABIB....
"Aunty Lubna Ina tunanin lokaci fa ya yi da ya kamata Hazel ta san komai ina nufin lokaci ya yi da zaki bayyana wa Hazel matsayin ki a gare ta."
Shiru ya yi yana sauraren abin da ta ke faɗa ta ɓangaren Aunty Lubna sannan ya sauke ajiyar zuciya ya ce.
"Wow haka nakeson ji tun tuni Allah ya kawoki lafiya."
Kashe kiran ya yi bayan sun gana tattaunawa zuciyarsa fal tunane tunane....
****
Wani irin shaƙuwa ta ban mamaki take ƙoƙarin shiga tsakanin Samira da Taufan domin kuwa kullum suna tare a bakin ruwa tun bayan gano cewa ta daɗe da warkewa da ya yi. Ta ɓangare Samira Sosai take jin wasu feelings akan Taufan da batasan ko mene ne dalili ba. Ta gama yanke wa ranta zata sama abokin shawaranta wato Althaf domin su tattauna akan lamarin kuma dama tanaso su haɗu domin tanason sanin labarin Taufan da Arissa ta basa.
Ita gaba ɗaya ma ta manta da abin da yake tsakanin ta da Arkan na son ta da ya ce yanayi ma ta kuma yana jiran amsa domin kuwa tun a wancan Ranar basu sake haɗuwa ba sakamakon abubuwa da suka sha masa kai. Ta ɓangaren Mr Gentle handsome Taufan kuwa bama ce ga ainihin abin da yake zuciyarsa dan gane da Samira ba. Daga can New York kuwa kwanakin Ambrah huɗu sai da tasan yadda tayi Uncle Ali Taj ya bata Labarin komai kuma ya faɗa ma ta gaskiya na abin da yake faruwa sannan ya faɗa ma ta a wurin da Taufan da Arissa suke a halin yanzu. Tayi kuka sosai lokacin da ya gama bata Labarin. Aikuwa washe gari bata bari ya sani ba ta tattara kayanta ta yi Airport kai tsaye ta hau Jirgin Nigeria sai saƙon hakan ta bar masa a paper, bata ji bata gani zuciyarta fal marmarin ganin Taufan ɗin ta......
*END OF BOOK 1....😁*
_____
1. Mene ne abin da Fulani Asiya take nufi ne da kalamin ta wacca kalar fansa take nufin zata ɗauka?.
2. Wai shin Arkan zai haƙura da Samira ya Aura Aaqilah da har yanzu bai san ta ba.
3. Shin ita Aaqilah ɗin zata yarda ta Aure sa duk da cewa ita ma ɗin batasan ko wanene shi ba?.
4. Mene Samira take nufi ne kuma Mene ne dalilin ta na ɓoye warkewar da tayi sannan wani kalan bincike zatayi a cikin Masarautar.
5. Shin Chief Sulaiman Mutallab Raees zai faɗa wa Samira ainihin Tarihin masarautar Raees idan ta sani mai zatayi akan hakan?.
6. Mene ne abin da Hamrarh zatayi?.
7. Miss Asfiya Mene ne yake damunta har ya saka ta kuka?.
8. Mene ne zai faru bayan Ambrah ta baro New York ta taho Nigeria?.
9. Shin da gaske Taufan da Arissa su ne mutanen da Ambrah take nema mene ne labarin su?.
10. Da gaske Mahaifin Ambrah bazai taɓa bari ta Aura Taufan ba.
11. Wacece Matar da LABIB yake waya da ita kuma wacca iriyar alaƙa ce tsakaninta da Hazel wanene LABIB shi kansa?......🔥🌹💖
*Duka amsoshin waɗan nan lodi lodin tambayoyin suna nan cikin BOOK 2 na Tsantsar So And Book 2 is Paid Book kamar yadda na faɗa muku ɗari Biyar ne kacal (500₦ Only).*
*Sister Karki bari wannan tafiyar ta kasance ba tare dake ba. Ta wannan lambar zaku iya samuna via WhatsApp Only (08081129487) sannan ga masu tambaya akan zamu karɓa katin waya?. E, Tabbas zamu iya amsa kudai kawai ku tuntuɓe ni ta lambata domin samun ƙarin bayani kuma in sha Allah on Friday zamu shiga Paid book waɗan da suka yi Payment.*
*© Nainarh KD...✍️🔥*