![]() |
🔥 *LAILA MAJNUN* 🔥 |
Nasan kun daɗe kuna jin Labaran Soyayya Amma na Tabbata baku taɓa cin karo da irin wannan ba....
Su waye majnun da lailah?
Wani mutumne da aka yi a daular banu umaiyya abisa zancemafi. Sunansa shine "Qais Bn Mulawwah" daga "kabilar Banu Amir",
Qais balaraben Æ™auyene, ya taso tare da ’yar gidan kawunsa mai suna "LAILA BNT MAHDI IBN SA'D" Amfi sanin Laila da sunan "Laila Aamiriya", tare suka taso tun suna yara suna kiwon dabobi har suka girma, suka fita daga sahun yara suka kai munzalin balaga.
A Yayin da alamun nuna balaga da cikar budurci suka gama bayyana ajikin Laila sai "Qais" ya ruÉ—e soyayyarsa gare ta, hankalinsa ya dugunzuma ya tashi.
Domin a wannan lokacin ne "Qais" ya Lura da irin kyawun dirin da Allah ya yiwa abokiyarsa "Laila", akullum soyayyar Laila sai kara tashin gwauron zabi take yi a cikin zuciyar "Qais", a cikin wannan yanayine "Qais" ya shiga rera mata canzan soyayya kala-kala babu dare babu rana hakance tasa Mahdi mahaifin "Laila" ya nemi da "Qais" ya fito dan maganar aure, saboda nuna soyayya da fuskar saida Qais ya bayar da raƙuma hoton a gidansu "Laila" a matsayin kudin aure.
Ana haka sai ga wani mutum da ake kira "WIRD BN MUHAMMAD" wani dan hamsha hakkin attajiri ne daga cikin ‘ya’yayen masarautar “Banu Umaiyya”, katsahan yayi ido hudu da "Laila" a wata rana a cikin wani Lambu tana kiwon dabobinta.
Daga wannan rana Soyayyar "Laila" ta hana Wird yayi bacci a wannan dare!
Cikin yan kadan Iyayen "Wird" sukasauka a gidan su "Laila" dan neman aurenta ga É—ansu "Wird".
A wannan rana da Iyayan "Wird" suka je ga mahaifin "Laila" sai da suka ajiye masa Manyan Rara gema guda ɗari (100) a kamar ƙara aure, wato ribi biyu akan abinda "Qais" ya bayar!
Daga nan yakin ya mallakiwa mahaifin Laila, domin kuwa yayi irin mugun abin kunyar nan na nuna kwadai da son abin duniya.
Bayan haka ne Mahaifin "Laila" ya kira'yarsa "Laila" cikin É—aki yanai mata damubar cewar ga mai kudi É—an masu mulki shi zai aurawa ita!
Babbar Magana! Laila ta yara da maganar mahaifinta a karon farko, amma sai ya yi mata barazanar zai yanka ta idan har bata amince da auren "Wird" ba!
Kwatsam sai aka wayi gari "Qais" ya ji gari ya rike da kace nace din an yiwa masoyiyarsa "Laila" aure, da "Wird".
Chapter 2
Nasan da yawan ku zaku bayyanar wuraren Muryar Hausa24 ko Wanne irin hali "Qais" zai kasance a wannan ranar?
Tun daga wannan lokacin bacci yayi hijira daga idonsa, farin ciki ya gagari zuciyarsa, damuwa bakin ciki ciki gami da bacin Rai da damuwa, zubar da hawaye babu dare babu rana, suka kasance tare da "Qais" a Hotuna na din-din-din!
Wake-waken soyayya sune zancensa, bashi da abokin hira sai wa lamarin da yake yiwa "laila" ga kadan daga irin abinda yake cewa:
zuwa ga Allah nake kai kukan son "laila" kamar yadda maraya yake kai kukan maraicinsa zuwa ga Allah.
Mara yanda da kafasa ta karye gashi kuma dangi sun gujeshe "Lallai" rasa iyaye abune mai girman gaske.
Haka "Qais" da aka yiwa lakabi da "Majnunu lailah" yake bin kwararo kwararo da saman manyan launi da bakin ruwa da cikin furanni yana rerawa Laila wadannan baituka masu motsa zuciya bai gushe ba harsai da akayi masa laÆ™abi da “majnunu laila".!
Duk da cewa itama Laila tana motsa son
"Qais" (majnun) amma kuma hakan baya hanata ta wahalar dashi, a wasu yara ma harda yi masa wulaÆ™anci, baya ga yin amfani da mallakeshi da tayi Waredi dashi, dama haka sha’anin mata yake shi yasa majnun awani baiti yace:
“Nace da wani babban malami da na gamu dashi a maka, dan Allah ka bani labarin wacce take cutar dani, ndabere da take jiji da kai (saboda ina sonta) shin hakan da take ba laifi bane?”
Sai Malamin ya fadawa "Qais" cewa "Wallahi da sannu azaba zata shafe ta kuma a duniya ma saita hadu da bala’i”.
Daga nan "Qais" yace, sai na kasaka idona
sai da hawaye ya zubo cikin sauri ya jiƙa min
aljihun rigata, sai nace, Allah yafe mata laifinta duk da yake a duniya dan kadanne samunta.
"Qais" ko Laila Majnun Bai gusheba a cikin wannan hali har sai da ya samu taɓin hankali.
Domin ya kasance idan yaga yara suna wasan Æ™asa yakan zauna tare dasu ya taro kasa ya rinqa gina gida irin wanda yara suke yi da kasa yana cewa cikin waÆ™a: “abokaina kuzo kuga gidana nida laila”....!
A yayinda al-amari ya wahala sai mutane suka baiwa mahaifin "Majnun" wato "Qais" shawara da ya daukeshi ya kaishi ka’aba (ÆŠakin Allah) ya umarce shi da ya ro dan wasa Allah ya cire masa son Laila!
Amma saboda tsananin soyayya a yayin da suka je tsarin ka’aba sai mahaifinsa yace masa: kama tufafin ka’aba ka roki Allah ya cire maka son Laila...
Chapter 3
Sai Majnun ya kama yace: “Allah na tuba gareka daga dukkan laifi, amma bazan tuba daga son da nake yiwa "Laila" ba.
A taƙaice haka "majnun" ya rayu cikin wannan yanayi na abin tausayi! Ita kuwa "Laila" tuni wanda ya aureta ya bi ta daga
kasar Saudiyya ga baki filin zuwa kasar Iraqi.
Haka itama ta rayu cikin wannan yanayin
abinka da ‘ya mace mai rauni sai da rashin ganin "Qais" ya kunna mata ciwon zuciya .
Daga nan ita ma ta kamu da ciwon zuciya saboda tsananin soyayyar "Qais Majnun"!
Tana cikin wannan hali ne na rashin ganin masoyinta Allah ya karbi rayuwarta!
A lokacin da "Majnun" yaji labarinta sai da
yaje har da Iraqi ya nemi inda take, da inda aka binne ta, a ƙaƙƙarfan mabartar da aka binne "laila" a dai-dai gindin kabarinta ya tare.!
Bashi da aiki sai kuka da makamashin soyayya agareta.
Wata rana da safe sai masu ciwon suka hangoshi (Qais-Majnun) ya kifa cikinsa akan kabarinta, ko da aka zo akaduba sai aka tarar Allah ya yi masa cikawa!
Allahu akbar
Wannan shine Qarshen hikayar "LAILA MAJNUN" kunjifa yadda akeyin soyayya ruwa-ruwan ta.