Skip to main content

MATACCIYAR RAYUWA - HAUSA NOVELS

🔥 *MATACCIYAR RAYUWA* 🔥

Chapter 1

KANO "SANI ABACHA INDOOR STADIUM
Rufaffen dakin taron na sani abacha da akafi sani indoor
Cike yake da manyan mutane kama daga yan kasuwa, zuwa
manyan malama'i da sarakai da ma sauran jama’a.
Daga can gefe jerin dalibai ne mata kowanne cikin shiga ta mutumci da daraja, kusan dukkaninsu hijabai ne da su masu yalwa wad'anda . suka kai musu har kasa.
Daga can Bangaren maza suma suna cikin . shiga ta mutumci, yau ne ake shirin fidda gwarzon shekara akan musabaKar karatun alkur’ ani ta qasa wanda Kano ce keda masaukin baqi a wannan karon. “ ‘ ‘ . * ' . Ta Bangaren maza aka fara, in da gwaraza guda uku a ajin gasar karsh‘e suka yi karatunsu aka fidda gwarzo. ' ‘
' . Sai aka'komo ajinmata, mutum biyu sun fito sun yi karatunsu sai daliba ta qarshe FALMATA waccc ta fito daga jihar Maiduguri ta fito ta fara karatunta, muryar'ta da qira anta da yadda take bai wa kowane harafi haqqinsa ya sanya dakin ya dauki shiru tamkar babu kowacce
halitta a cikinsa.
Malamin da ke musu gyara ya yi tsai yana sauraron karatun dalibar wanda ya kasa zakulo gyara a cikinsa har ta kammala, aka dauki kabbara cike da mamakin baiwar da Allah Yai mata.
Ya dago kanshi ya yi mata kallo d'aya, wanda. ya haddasa masa abubuwa da dama, sannan ya maida kanshi gefe. Gaba daya jikin‘sa ya mutu murus ya samu kansa cikin rashin kuzari, sai dai muryar dalibar tana yi masa amsa kuwwa acikin kunnuwansa. ' ~
Haka nan dai ya daure ya yi ta ‘yanmaza ya ci gaba da abin da ya zaunar da shi a gurin.
" Kallon da ya yiwa Fahnata, anyi sa’a ita ma , a lokacin shi ta ke kallo, don haka
daurewa tayi ta karaSa gurin zamanta kusa da y‘ar uwarta Yagana. '
Ta dan yi qasa da murya tana fadin, “Yagana malamin nan mai darasi bai burge ki ba don Allah? Komai nasa cikin nutsuwa yake yin shi k0?”
Yagana-ta yi dariya tana fadin, “Yau kuma kin yi karo da namijin da‘ya burgeki kenan, ina ce kece kike cewa, me ye abin burgewa ga namiji kuma, sanda na taba ce miki Yaya Sani yana burgc ni?”
Ta ja bakinta ta gumtse don tasan Yagana ba
zata raga mata ba, sai dai ta kasa daina kallon malamin mai darasi, Wanda tun lokacin bai kuma kallon inda ta ke ba.
Har. aka tashi daga taron hankalinta yana kansa, ta rasa irin murnar da zata yi idan har ta zamo ta daya a cikin matan Nigeria, amma sanda aka sanar da ita sai tagaza murnar yadda ya dace, har saida ya zamana, Yagana da malamansu da sauran d‘aliban makarantarsu sun fita murna. Ita ce ta zo ta daya daga bangaren mata, yayin da Abdul-ra’uf
wanda “ya fito 'daga jihar Kano yazo na daya a. Bangarcn maza.
An raba musu kyaututtuka har da kujerun Makka, shugaban kasa da gwamnoni ma sun cika su da kyauta har da su mota da tsabar kudi, amma wannan duk bai sanya Falmata murba sosai ba.
Yagana ta dan zungure ta tana fadin, “Na ga kamar ba kya murna, bayan burinki ya cika kin zamo ta daya, kin san Abba da Inna za su yi murna matuka da hakan fa”. ‘
Ta yi yaketa sunkuyar da kanta qasa tana cewa, “Nayi murba mana, me kika gani Yagané?”
Yagana tayi dariya kawai, amma ta fara gano inda qawar tata ta sanya a gaba.
Sun kammala komai ana shirye-shirycn tafiya gida, Falmata taso shiga cikin garin kano gidan wasu ‘yan uwansu da 'akayi mata kwance, amma malamansu sun hana su matsawa k0 nan da ' can.
Ta isa gurin malaminsu Gwani Muhammad . ta durkusa kanta yana qasa cikin ladabi ta ce, “Malam zaka iya bani-dama na je cikin gari gurin wasu ‘yan uwanmu na dawo yanzu da wuri?” “Salon ki bata, ki jawa. mutane 'tashin hankali?”
Ta'd‘aga kai da sauri, don‘ganin me yin maganar. Gabanta ya yanke ,ya fadi malam mai darasi ne da yazo gurin kufa-da haka. .
Gwani Muhammad yayi murmushi yana fadin “Kinji dai abin da shehi-yacc ki koma cikin ‘yan uwanki mun kusa daukar hanyar gida”.
Ta mike jikinta da sanyi ta koma gurin su Yagana ta cikin nikabinta ta kc qara kallon malam mai darasu, sai hira suke yi da Gwani Muhammad suna dariya.. Tana kallonshi ya wuce hannaunsa riqe da babbar robar swan water
“Falmata Gwani Abbagana”. Taji an kwala mata kira. ta waiga da sauri sai ta ga Alubura ce da suka taho tare. Alaburu ta kamo hannunta tana fadin zo kiji
Suka nufi can gefc suka tsaya, Alabura ta. dage nikabin fuskarta tana fadin “Kin caba Falmata, kinji yadda malamin can mai darasi ke batunki, ya ce kin burge shi matuKa, ina ma nina sami wannan matsayin, kin zamo tauraruwar
Elkanemi Bara’imul Iman, ina miki murna ta”. -‘Dage nikabita itama tayi cikin maganganun na malam mai darasu tafi yi mata dadi, ta kwantar da wuya tace“Kin ga ai yana da kirki k0?” Wa?”Alabura ta tambaya da hanzari.
Ta gano kwaBar da take son yi don haka da sauri tace GWani Muhammad mana” ..
" Alabura ta_dan_saki fuska, tace, “Au? Nayi zaton‘ malamin kike nufl..,Ni kuwa da zai aure ni da
na yarda”. Falmata tace, .“Ina son mutum mai ilimi k0 ke bai burgc ki ba nc? ’
. Alabura ta yi dariya, tace, “Kema da maza basu burgeki ya burge ki balle ni? Ni fa banda ina jin kunya'da na' rubuta masa ‘yar takarda kafin mu tafi”.
_Yagana ta Karaso gurin tana fadin, ‘qulmar
me ake yi ne? An gama shirya' komai ku zo mu wucc” .
** ** **
Taso ko sallama yazo ya yiwa malamansu kota
Qara kallonsa, amma abin ya faskara, tadinga
waige waige ko Allah zau sanya ta ganshi. amma
har motarsu ta tashi babu alamunsa.
Sanda motarsu ta d‘auki hanyar garinsu ta
lumshe idanunta cikc da takaici tana tunaninsa, tana jin yadda abokan tafiyarta keta surutunsu ba su damu da ita ba, koda yake ko ba don haka ba ma basu sanyata cikin surutunsu tunda sun san ita ba . surutun ta iya irin nasu ba, sau da dama idan ka ji ta yi magana to tabbatar abu mai muhimminci zata fad‘a, ko hirar akeyi ma sai dai ta yi murmushi idan abin murmushin yazo Sun yi nisa a tafiya, masu magana har sun ‘ gaji sun yi bacci, amma Falmata idonta biyu tunanin malam mai darasu ya h‘anata runtsawa, ga shi tasan babu wani abu da zai qara kawota Kano , balle ta sanya ran rara ganinsa, duk da ta sha jin a'na cewa, suna da ‘yan uwa a Kano amma koda wasa ba a taBa cewa za a kai su ba, don haka koda ta ji a nan za su yi musabaka ta qarshe a Kano ta dami mahaifiyarta akan ta yi mata kwatancen gidan ‘yan uwansu a Kano idan ta sami dama taje, amma bata sami damar hakan ba.
MAIDUGURI ‘
Malam Abbagana‘yana zaune bisa kujera mai cin mutum uku a cikin Kayataccen falonsa mai girma da fadi, wanda ya sha kujeru na zamani.
Daga jikin bango Tv ce irin ta zamani plasma, da qaramar'video da receiver a bisa dan wani tcbur na ‘ tangaran baki.
‘Dakin malale yake da jan kafet ta mai taushin tsiya,‘ can daga kusurwar' gabas babbar drower ce cike da littattafan addini kala-kala, da kaga dakin kasan na shahararren malami ne, kuma mai arziki. ‘
Hajiya Iyami ta shigo dauke da faranti wanda ke shaqeda tufa ta shigo da sallama, mace mai kwarji da cikar kamala wa’cce ba zata wuce ‘ ' shckaru arba’ in ba. Ta nufi mai gidan nata cike da farin ciki, ta zauna kusa da shi gami da Janyo wani tebur na glass ta dora yankakkiyar tuffar.
' Hankalinsa yana 'kan talabijin wacce yake kallon Saudi 2, ya. waigo 'yana qoqarin rage maganar 'da' linzamin rage magana (remote control)
‘ “Yaya kin gaya wa Falmata saqon nawa -kuwa?”
Ta dan yi murmushi, “Kai ma kasan dole na isar da sakonka, ita ma dokin haduwar taku ta keyi, don fa jiya'ma ni na hanata zuwa gurinka nace dare, ya yi a bar wa yau kuma, amma da tun daren zaka ganta .
Ya yi dariya yana fadin,‘ “Ai dole ta yi murna, kin san fa yanzu itace zata wakilci matan
Nigeria a gasar musabuqa ta kasa, wacce nake kyautata zaton a Saudia za ayi, Allah Ya shi mata albarka, ta gado gida,itama nasan .duk cikin diyoyina mata tafi kowa qokari, amma sai a dinga jin haushi don ina nuna mata. kulawa da ba ta kyautuka. Shin zan yarda na bai wa masu zubda min daraja gida kyauta ne
Ya qarasa maganar muryarsa amo takaici ya bayyana qarara akan fuskarsa. .
Iyami ta dan kwantar da murya, .tana fadin, “Malam ban son kana fadin haka ya’yan nan duk Allah ne'Ya ba ka, akan me zaka dinga nuna kafi , son wani Bangare? Su da kake ganin suna yin abin da bai dace ba ai addu’a ya kamata kAnayi musu ba~ kyara ba, tunda kaga iyayensu sun kasa yarda da gaskiya, bayan tana bayyane..."
“Addu’ a ta nawa Iyami? Ai ke shaida ce, amma yaran nan sun yi kunnen uwar shegu da tarbiyyar daba basu, wai ace diyoyina ke zuwa, tadin dare, kamar ni da ake girmamawa a garin nan wa ’adinsu ya kusa cika, sati hud‘u ya rage duk wacce ba ta kawo miji ba cikin almajiraina zan samo mata wallahi...
Maganar tashi ta katse saboda :shigowar Falmata, wacce ke sanye da doguwar riga har qasa da karamin hijabi ma’abociyar nutsuwa da sanyin
jiki Ya maida hankalinsa garcta, yana amsa sallamar cike da fara’a.
“Yauwa diyata, shigo ga guri zauna”.
Ya nuna mata kusa da Kafafunsa.
Ta isa fuskarta cike da farin ciki, 'ta durkusa cikc da ladabi tana fadin, “Abba ina wuni?”
‘ “Lafiya lau diyar Abba, ko na ce mutanen Kano ko?” . ' Ta Kara sunkuyar da kai cike da kunya, ya yi dariya yana fadin, “Yau dai duk abinki sai kin ba ni labarin tafiyar nan da abubuwan da kika gani a ,hanya” . . Hajja Iyami tabe fuska, “Lallai zaka . kwana a nan kana jira, yarinya kamar ba a yanka 'mata fatar baki ba, sai dai ta yi ta yaKe maka hakora kamar me tallan makilin, wallahi idan zaka ' wuni da yarinyar nan a daki ba zata ce maka uffan ba, Abba”.
Ya yi dariya yana fadin, “To me ye amfanin surutu ratata? Ai a nan ake samun rarar zance, ni daman tsokanarta nake yi,'ai malaminsu ya ba ni labarin komai, da duk alkhairin da ta samo. Yanzu sai ki sanar da ni abin da kike so nayi miki auta, domin kin faranta min, kin qara daga martabar gidana a idon duniya, kuma na Kara alfahari da
haihuwarki kamar kullum Falmata, Allah Ya yi miki albarka, ina jiranki ki sanar da ni abin da kike so, uhum!”
Ta Kara duqar da kanta tana wasa da yatsun hannunta, ta dai daure tace “Abba ni ba na bukatar komai, sai dai ka mini addu’ar biy’an bukata kawai”.
‘Suka kalli juna da mamaki, sannan suka kalli diyar tasu, Abban ya daure yace . “To sai ki gaya mini buqatar taki na biya miki mana, ko a gurin Allah kike nema Falmata‘?”
Ta daga kai alamar eh, abin da ya sanya shi shiga damuwa, yace, “Falmata ba zaki iya sanar da ni abin da ke damunki ba, nasan ki da zurfin ciki, ko wani abu‘ yan uwanki ke miki ne‘?”
Ta daga kai da sauri, ganin yadda hankalin mahaifin nata ya tashi, tace, “Abba babu komai wallahi,dama zan yi addu’, a ne don na roki Allah cikawa da imani, kasan ba ni da matsala da kowa Abba ” .
Ya yi ajiyar zuciya, hankalinsa ya kwanta ya yi dan murmushi, “To shi kenan zan rubuta miki, kin ji k0? Amma idan wani abu yana darnunki ki sanar dani kinji ko? Tashi kije. Allah Ya shi miki albarka”.
Ta tashi ta nufi waje, ya kalli Hajja Iyami yace “Me kika fahimta da Falmata? Kamar tana da
damuwa fa”.
Ta tabe baki, “Kana son wahalar da kanka
ta ya ya za a gane damuwar Falmata? Kullum a haka ta kefa. .”. ‘
_ Ya yi dariya, yana fadin, “Kai ni dai da an sani da ba,a haifar mini Falmata a ta fari ba, duk anbi a _ tsangwame ta haka? Idan tana da matsala ma ai ba z‘ata iya sanar da ke ba da kin ganta sai ki kama wani
ciccin magani kamar za a yi dambc da ke.
Suka yi dariya su duka biyun a tare.
. Kai tsayc 'Falmata dakinta ta wuce ta fada , gadonta ta kwanta, .idonta yana kan silin ta kasa. mantawa da suffar malam mai darasu, k0 bacci ta ke mafarkinsa ta ke. Idan tana ido biyu kuma ya
'dinga yi mata gizo. '
Shin idan ta yi addu’a a-kansa ta yi laifi ne? Mutum mai ilimi da daraja irin haka ai kowace mace zata so shi matuka. Tabbas idan ba ta same shi ba ta yi asarar mutum mai alkharii', ba tasan meye so ba, tunda ba ta taBa yiwa wani ba, sai dai ita a yi mata, amma da alamu abinda takeji a kansa shi ne so, shifa? shin yasan so k0 bai sani ba? ‘Shin matansa nawa ma, diyoyinsa nawa?
Gabanta ya yanke ya fadi, tasan abu ne mai.......
Hmmm me zai faru?
Bari mu dakata a nan mu tara domin ci gaba da sauraron wannan qayataccen littafin.

MATACCIYAR RAYUWA
CHAPTER 2
wahala acc wannan kamilallan mutumin ba shi da mata hud‘u, sai ta ji idonta ya ciko da kwalla, gabanta ya hau bugawa.
Tabbas ta hadu da mugun ciwo da ta sani da ba ta je Kano ba, ta sha ayyanawa idan ta zo ta daya a gasar musabaka ta gama cika burinta na duniya, sai dai ta roki cikawa da imani, sai dai a yanzu ta yadda burikan dan Adam ba sa cika harya koma ga Allah, amma dai zata tsananta addu’a idan ta je makaranta ma zata Kara tambayar malaminsu wata addu’ar .
ELKANAMI BARA'IMUL IMAN
Falmata ce tafe da Yagana sun taso daga makarantar islamiyya ta Elkanemi Bara’imul Iman suna rike da kur’anai.
Yagana ta dan daki kafad’ar Falmata tana fadin “Ya Ustaziyya', duk kin zama shiru kwana biyu na kasa gane kanki tunda muka dawo daga Kano fa kika koma haka, k0 kina tunanin malam mai darasu ne?”
Falmata ta tsaya da sauri tana kallon Yagana, gabanta yana faduwa, don Yagana ta gama gano laqonta, amma sai ta danne tace. “Yaushe na gaya miki haka?”
Yagana ta. yi dariya tana fadin, “aiba sai _
kin gayn min ba. yanayinki kawai ya isa ya gaya min, Koba dazun naji kina tambayar gwani Sale ya ba ki addu'ur biyan buqatu ba?" Tana maganar tana dariyu.
Fulmata ta yi wuki-wuki amma me sai tayi gaba da sauri cikeda borin kunya, tana fadin, “Haka kuma kika koma? Tabbas kin wuce sanina”.
Yagana ta bita da gudu tana dariya, tana cewa. “Tuba nake mu bar maganar Malam mai darasu, mu koma wata. Yaushe ya dace mu shiga islamic Techcology ne, mu amso resue dinmu? Na gaya miki Malam Bukar ya kirani ya sanar dani results dinmu ya fito,amma kinqi kice komai, na rasa gane kanki, ko aure kike so ne yanzu kin fasa karatun?"
Ta waigo ta harari 'Yagana da keta babbaka dariya, don tasan iskanci kawai ta ke mata. Yagana ta ci gaba da dariya tana fadin “A to meye laifin wanda ,yace yana sonka? Ni fa ban ga aibun Malam Bukar ba Falmata, Allah da gaske nake ya dace ki ba shi dama".
Ta shige gidansu da sauri dai-dai sanda suka zo qofar gidan, don idan akwai maganar da ta tsana ba ta wuce ta malam Bukar ba. Yagana taci gaba da dariya kafin ta wuce ta nufi gidansu dake makwabtaka da nasu Falmalan Sai dai gidans‘u bai kai qeruwar nasu Falmam ba.
A harabar gidan Falmata ta ci karo da Yakwari ana ta gyara damarar bel da alama wani guri zata. Falmata ta bita da kallo cike da mamaki, sanda ta ga ta zaro doguwar riga (after dress) ta dora akai, wato sai taje zata_cire, wai wannan diyar babban malamin dake fad’a a ji ke irin wannan shigar.
Caraf suka yi ido biyu da Yakwari tasan kwanan zancen, don haka sai ta nufi cikin gidan da sauri. Amma tuni Yakwari ta sha gabanta tana wata girgiza, ta nunata da yatsa.
“Munafuka, algunguma, na ga kina wani kallona, to wallahi koda wasa na ji wannan magana a gurin Abba ki kuka da kanki, domin nasan hali, an yi gadon gulma da mugun abu ta ko’ina, mtssss Taja tsaki gami da wucewa ta barta a nan tsaye
Falmata ta girgiza kai cike da takaici a ranta, tana fadin “Allah dai Ya shirya, sai na rasa dadin me sukeji a zubarwa da gidan nan qima”.
Ta kada kai ta shige cikin gidan tana tuno maganganun Yagana tana murmUShi.
ELKANEMI COLLAGF. OF ISLAMIC TECNOLOGY
A hankali motar ta yi parking, Yagana da Falmata suka fito daga gidan baya cikin shigar
mutumci. Yagana tana sanye da dogon hijab iya gwiwa, ta sanya shadda a ciki, yayin da Falmata ke cikin shigarta ta gado, wato doguwar riga har qasa ‘yar Maroco, ta nannade kanta da gyalen rigar irin nadin Larabawa, da medicated glass a idonta don -tana _da matsalar ido, idan ta ga rana ta kalla sai ta sanya shi k0 idan zata yi karatu. Har sun dan yi gaba direban ya fito yana fadin “ Malama Falmata zan jiraki ne k0 .kuma zuwa zanyinadawo?” ..
“Ka Jiramu mana, ai ba Jimawa zamu yiba”.
cewar falmata.
Yagana ta. kalle ta tana qunshe da dariya, don tasan dole ta sanyata shigowa makarantar, sai da ta hadata da mamansu ma sannan ta yarda suka shigo. .*
Tace“Anya ya jira mu? Gwara dai ya je ya dawo
A qule Falmata tace “Eh, da yake kwana zamu yi k0, kin 'san Allah zan komawata cikin mota Allah kuwa”.
' “A ’a, bani na kar zomon ba, rataya aka bani Wuce mu je”.
Suka wuce cikin nutsuwa suna tafe Yagana
*na zuba, yayin da Falmata ke binta da eh ko a‘a
Ko rirgiza kai da take ita ba ma’abociyar ?zance bace
Ran Falmata ya yi wasai ganin harsun kusa kammala abin da zasu yi ba su hadu da Malam Bukar ba, wanda shi kuma Allah Ya doro masa qaunarta kamar 'ya hadiye zuciya ya huta Ita kuma k0 miskala zarratin ba ta qaunarshi sam baya ranta, ta tsani k0 had‘uwa suyi.
Sun kammala komai sun fito cike da murna domin sakamakon nasu ya yi kyau matuka, suna da damar neman gurbin karatu a jami’a.
Suna gab da isa inda motarsu take suka jiyo ana kwala musu kira,‘ sarai Falmata ta ji shi, kuma ta gane k0 waye-don haka ta qara sauri, sai da Yagana tace
“Kina ji Malam Bukar yana kiran mu; ki tsaya bai dacemu wofintar da kiran malaminmu ba k0?” ‘ . .
Da wann‘an dabarar ta shawo kanta ta tsaya, amma gaba daya ranta ya cunkushe ta rasa irin Kin da take yiwa malam Sadik, shi dai ba muni ne da shi ba balle munin hali, ammn tunda ya ambata yana sonta ta ji bata ko kaunar ganinsa. A can baya takan girmama shi matuka, don yana cikin malaman‘da tafi qauna. da‘ngane da aikinsu, am‘man tun suna gab da zasu fara jarabawar WAEC da ya bayyana mata abin da ke ransa ta ji tana jin haushinsa har
takanqi halartar darasinsa da yake musu na share fagen jarabawa.
Shi kam ya kasa fushi don sone yake mata na gaskiya, mai kuma zafinnan da nukurkusar zuciya, irin son da komai zaka yiwa mutum ba ya jin haushi bare ya daina ganin wanda yakeson“ da qima.
Ya iso inda suke yana haki saboda saurin da ya yi, gaba daya hankalinsa yana kan Falmata, wacce ta sha kunu matuKa kamar an aiko matada -sakon mutuwa. '
' Suka .yi cirko-cirko su dukkansu kamar .zakaru aka rasa wahda zaice da dan uwansa wani 'abu.
Yagana ce ta yi saurin durqusawa tana fadin, “Malam ina wuni” .
Abin da ya sanya ita ma Falmata ta yi saurin durqusawa ke nan tace “Ina wuni”.
Da ’sakin fuska ya amsa, bakinsa yaqi rufuwa saboda murnar ganin Falmata.
Yana kallon idonta yake fadin, “Yagana babu daidaia 'me ya kawo gaba ace har ku shigo makarantar nan amma ku kasa nemana mu gaisa, kamar na yi "wani laifi
Yagana ta kalli idon Falmata don tasan da ita yake, ta ce “Ka yi haquri Malam, da yake
dircba yana jiranmu ne shi ya sanya muke ta sauri”.
Ya matsa gaban Falmata don ya kula bata da niyyar yin magana, yace Hajja Falmata, rannan ina ta turo saqo shiru babu amsa, ni na kasa gane laifin da nayi miki Falmata”.
Ta sunkuyar da kai, shiru tayi ta kasa cewa komai. Yagana kuwa sai tayi saurin barin gurin ta nufi motar, ta bi Yagana da kallo cike da takaici kamar ta bita da gudu, amma tasan ba zata iya yiwa Malaminsu haka ba, don haka ta ci gaba da tsayuwa tana wasa da zara-zaran yatsun hannunta.
“Uhm! Ke nake saurare, idan akwai wani laifi da na yi miki ki sanar dani, domin dan Adam ajizi ne tana iya yiwuwa na aikata wani laifi ne wanda ni a gare ni nake ganin ba laifn bane”.
Cikin qosawa da zancen shi, Tace “Nifa malam babu abin da ka yi min, kawai dai, uhm... uhm...” Ta kasa qarasa abin da ke ran nata.
Ya kwantar da kai cike da tausayin kansa, yacc, “Kawai dai me? ko kina nufin kawai dai sona ne ba kyayi?”
Ta daga kanta da sauri suka hada idanu, ganin yanayin da ya shiga duk sai ya ba ta tausayi. tayi saurin kawar da kanta gefe tana fadin. '
“Ni fa ba haka nake nufi ba Malam". .
“To me kike nufi Falmata? A tunanina
soyayya bata zama qiyayya, haka kawai Allah Ya jarrabeni da matuqar sonki, shin wanda yace yana sonka ya yi laifi? Haba Falmata MENE NE LAIFIN ZUCIYA don ta ga abu tana so? Ki kalle ni da kyau kin sani ‘yan mata nawa ke sona a makarantar nan, amma ni kuma ke Allah ya dora mini sonki, ke kuma kina wulakanta ni. Don Allah ki tausaya min mana Falmata, ko ba ki san zafi da radadin so banc?”
Matukar tausayinsa ya kamata, amma kuma ba ta jin k0 digon sonsa guda daya a cikin zuciyarta, tabbas acan baya ba ta tausayinsa k0 miskala zarratin, don tana ganin zakewa ce kawai irin tasa. Sai dai a ‘yan kwanakin nan da ita ma ta gamu da irin ciwon da ya harbe shi ta ke tausaya masa, domin ta fuskanci zafi da radadin so ba abu ne mai sauKi ba.
Cikin kwantar da kai, tace da shi.
“Malam ka gama mu zamu wuce dircba yana jiranmu”. ‘
Wani abu mai ciwo ya tsaya masa a makogwaro, wato duk abi‘n da ya fadi a banza ma ke nan? Amma dai fushin fari ba nashi bane dole ya bi komai a sannu yana ganin watakila zaici ‘riba a gaba, don haka ya karkata kai yana fadin.
“Shi kenan Falmata. kuje kawai. amma don
Allah idan na kira a dinga daga wayata, kin ji k0?”
Ta daga masa kai alamar to, sannan ta wuce da sauri tana ajiyar zuciya. Tana jinta kamar akan qaya take daman.
Ya bita da kallo yana girgiza kai, a ransa kuwa addu’a yake Allah Ya, sanya Falmata matarsa ce uwar ‘ya’yansa, domin Allah Ya jarrabe shi da sonta matuka.
. .............
Kai tsaye ta wuce sashinsu ta shige dakinta ta sillo wanka, ta fita cikin wata doguwar riga mai yankakkcn hannu, kanta da ya sha kitso qanana irin na bare-b‘arin usuli ta sanya' hula mai kyau irin ta mata. Kai tsaye kicin ta wuce ta fara zubo abinci a cikin faranti ta nufi falo.
Ta tarar da mahaifiyarta zaune akan kujera tana kallon tasoshin Larabawa, ta isa kusa da ita tana fadin.
“Hajja, sannu da gida”.
Mahaifiyar tata ta dan kalle ta, sannan tace “Yauwa, har kin dawo? Ina sakamakon naku? Allah dai ya sanya ya yi kyau”.
Ta yi dariya tace “Yana daki, yunwa ce ta
gigita ni har na manta ban dauko ba. Bari na dauko miki shi..."
“A’a, gama cin abincinki tukuna, abin da ba guduwa zai yi b,,,,,
Ta sami guri ta zauna bisa kujera ta fara cin 'abincin nata tana kallon film din da Babar tata ke kallo a tashat MBC 4, ita dai tana son fina-finan Larabawa ita da Abbansu, k0 don suna jin Larabcin nc? Oho! '
Hajja Iyami ta kalli diyarta tana fadin, “Kece ‘yar sarkin son zuwa Kano, to yau dai Allah Ya kawo Hajiya Mariya, sai hankali ya kwanta k0?”
Wani irin dadi ya cikata kamar ta shide ta dire farantin abincin tana fadin, “Kai Hajja, da gaske? Kai amma na ji dadi, kin san na so zuwa gidanta sanda mukaje, amma malaminmu ya hanani, bari naje na gaisheta. Tana ina?” Duk dadi ya cika ta.
Hajja .Iyami,ta kalleta cikc da mamakin yadda take zakwadi duk ta wani gigice ta rasa irin son da takeyiwa Kano haka. Tayi dan murmushi tana fadin
“Ina zaton tana can sashen Abbanku, ki bari ta shigo nan mana sai ku gaisa”.
Ta yi dan jim, sannan tace“Don Allah Hajja ki kyale ni naje na ganta, ina son mutanen Kano ko dan ni yadda ake ba ni labarinsu?”
Uwar tabw baki tana cewa, “Sai kin dawo, amma dai ki shiga a hankali kar ki bugeta garin wannan rawar kan naki”.
Ta yi dariya gami da nufar dakinta ta d‘auko qammin hijab dinta ta nufi sashin mahaifm nata.
Sai dai me? Sanda ta isa tana gab da shiga ta jiyo alamun kuka da magana, ta tsaya turus cike da tsoro, don ba ta raba daya biyu muryar bakuwar da tazo ce Hajiya Mariya ke kukan, ta yi kamar ta juya ta koma, amma abin da take fadin ya dauke mata hankali.
Gaba daya hankalin Malam Abbagana ya tashi jin kukan da Hajiya Mariya ta ke yi.
Ita kam kukan shibe mafita a gunta, cikin kukan ta ke fadin.
“Yanzu Abba don qasa ta rufe idon malam sai ace ba mu da wani mai tsaya mini akan lamarin yaron nan, mutum idan ka kalle shi kamar mutumin kirki, amma sai ,kayan haushi, yana zaune da yarinya _tsawon shekaru tana juya shi ita ba haihuwa take yi ba, balle ace rabo ne rabon dai wahala, ku kuma kun zuba 'mini ido? Sau nawa nake sanyawa ya yi aure sai komai ya kankama sai ta rushé maganar?”
“A’ a Mariya, banda zargi abu ne mai muni a addininmu, tunda kin sani zato zunubi ne k0 da ya
Kasance gaskiya ne”.
“Wallahi mallam babu zargi a cikin wannan batu, da kanta take aiko min da wai na daina asarar kudina shi da aure sai dai a lahira idan har ana yi, k0 kuma ba ta raye. Gwara na tsine masa na bar wa duniya don ita na haifawa”.
“Subhanallahi, abin har ya kai ga haka? Lallai ta yi nisa, ki yi hakuri, ki kwantar da hankalinki insha Allahu ni da kaina zan yi maganin abin, ki daina zaton don malam ba shi da rai zamu zubawa iyalansa ido suna watangaririya, ban san matsalar Muktari ta. kai haka -ba, amma ki sha kuruminki, ki daina' qokarin yi-‘masa baki, insha 'Allahu za -a warware komai, ba dai aure kike son ya yi ba? Sai dai ki yi imani da Allah Shi ne mai bayar da da, ba wai zamu yi masa aure ba ne don matar tasa ba ta haihuwa ba ne, sai dai muna son nuna mata ba -ta isa 'ta ja da ikon Allah ba. Shi kuma ya sami nutsuwa da sauki a rayuwarsa, domin irin wadannan matantashin hankali ne matuqa, kedai ki dage ki yi ta addu’a.
Idan kin koma kuma kada ki gaya masa yadda muka yi da ke, idan na kammala shirina zan neme ki a waya na sanar dake shi kuma zab kira shi mu yi maganar, amma don Allah ki daina ambaton tsinuwa, tunda ita din ai ba gyara take yi sai dai qara lalata abu”.
“Na godc Malam Abba daman nasan kai kadai ne zaka iya share mini hawayena”.
“Babu komai, Allah dai Ya shige mana gaba, kuma ina tunanin cikin yaran gidan nan zan samar masa matar auren, zan yi istihara dai nu“ gani”. '
Falmata dake labe ta dafe qirji cike da tsoro da faduwar gaba, sai taji kamar ita za aba wa Muntarin da akc fadi lallai da an kashe ta, ita da ta gama burin ta bi Hajiyan Kano ta yi ta binciken masoyinta, k0 ta samu ta dace yace yana sonta, gaba daya Sai murnarta ta koma ciki, ta ma fasa shiga don kada tsautsayi ya fada kanta, don haka ta juya sumi-sumi tabar gurin.
. Harta nufi sashinsu sai kuma ta tuna abin da zata ceda Hajjanta ya hanata shiga, sai ta Wuce kai tsaye ta yi wajeta nufi gidan su Yagana.
Sai da aka yi sallar magriba sannan ta dawo gidan. Tana shiga mahaifiyar tata ta hauta da fada.
“Ina kika shiga keda kika ce za ki je ku gaisa da Hajiya Mariya, ta shigo tun d‘azun tana nemanki?”
Ta kwantar da Kai, tace, “Hajja na nufi dakin na ji suna hira da Abba, to don kada na katse musu hirar tasu ya sanya na wuce gidan su Yagana”.
Ta yi ajiyar zuciya, “Ai shi kenan, sai kije tana wajen Hajja Kaltum ku gaisa”.
Ba kamar dazu ba da take cike da muma ta fice,mahaifiyar°tata ta bi ta da kallo tana saka wani abu a ranta.
Ta d’an jima kofar sashin Hajj: Kaltmn. ~ saunan ta daure ta shiga da sallama. ‘
Hajiya Mairo ce ta fara waigowa, sai ta saki murmushi tana fadin, “Duk yadda aka yi wannan . ce Falmata k0?”
' Hajja Kaltu‘m ta saki murmushi, tace “Yaya kika gane ta?” '
Ita ma ta yi murmushin, ta ce, “Ai kamar haka Abba ya auro Iyami tana ‘yar kucilarta su Yakolo suna ta mita da tashin hankali kamar a kanta aka fara yi musu kishiya”. .
Hajja Kaltum ta yi dariya, tana fadin. “Yakolo ke nan, sai addu’a " .
Falmata ta shiga ta durkusa gaban Hajiya Mariya tuna fadin, “Hajiya ina wuni?”
“Lafiya lau, ya ya karatu Falmata?”
“Alhamdu lillahi’.
Hajiya Mariya ta dubeta tana fadin.
“Ashe haka ku ka sha Kano ba a kawo mana ko
ziyara ba Falmata? Sai yaushe za, azo mana, ko sai an kammala karatu?"
Gaban Falmata ya yanke ya fadi, amma sai ta kasa cewa komai, sai duqar da kai take, tana yaqen dole.
Hajja Kaltum cw tace, “Ai ba ki ga takaicin da ta sha ba, ta kuma kammala karatunta, kin san tun bayan su Zanna da Sani ba a samu mai koqarin Falmata a gidan nan ba, kin san tana cikin wadanda zasu wakilci Nigeria a gasar karatun qur’ani ta duniya, jibi za su tafi ma”.
“Kai masha Allah; ai yarinyar da gani akwai nutsuwa”. har Hajiya Mariya tana kallon Falmata cike da sha’awa; a ranta tana addu’ar Allah Ya sanya malam Abba ya zabarwa Mukhtari ita, domin diyoyin Yakolo ma ba su da wani banbanci da matar tasa, amma dai ba zata yi azarbabin magana ba, za dai ta yi ta addu’a kawai a zuciyarta idan rabonsu ce Allah sai Ya ba su ita.
Haka nan ta tashi ta bar dakin sumi-sumi cike da kunya da faduwar gaba, don jin yadda Hajiya Mariya ke ta zuzuta halinta.
Bayan ta fita, Hajiya Mariya ta dubi Hajja Kaltum ta ce, “Hajja Kaltum me ya sanya Yakolo ta yi sakaci da tarbiyyar yaranta haka, kinga dana shiga sashinta wani irin kallo da suka dinga mini
kamar sun ga kashi, sai da tace su gaida ni fa sannan suka gaishe ni da shigarsu kamar ba diyoyin me fada aji ba babban malami . Ita kuwa ‘yar kadifire Basma sai wani harare-harare ta ke yi ‘yar kora, ashe har yau halin nan dai nasu yana nan, ‘ babu abin da suka sauya?”
Hajja Kaltum ta tube baki, ta ce, “Kema dai Hajiya Mariya ai an ce idan kun jima baa kaga mutum ba in kun had‘u tambaye shi wani abun ba halinsa ba yakolo bata tunanin abinda zaije yazo bayan ita ya dace tafi kowa taka tsan-tsan ita da Allah Ya bai wa ‘ya’ya mata amma ta watsar da duk tarbiyyar da Abba ke basu, ita kam Basma ai batadakaico tunda batada kuda agidan ko?Idan kin ~yi magana tace an tsane ta ita da ‘ya'yanta, kinga k0su Bulama na hana su yiwa 'ya’yanta fada domin tace sun tsanesu saidai nata su hanasu , gidan matansu kuwa babu abinda suke yi sai hada gulma a-zo nan ayi ta dambarwa, wani lokacin ki ji wai bar da dambe, to me ya yi zafi lamarin dai sai addu’a
ai”. Gaba daya sai jikin Hajiya Mariya yayi,sanyi tabbas idan tunanin Abban ya fada kan diyoyin Hajja Yakolo an yi badi babu rai kenan k0 ace b, a rabu da Bukar ba an haifi Habu. Amman sai wata dabara ta fad‘o mata ta gyara zama tace
Hmm yanzufa aka fara.
#SULAIMAN_BOMBOY
.
MATACCIYAR RAYUWA
CHAPTER 3
Tace“Ni kuwa Hajja Kaltum k0 Falmata nada alkawari a kanta na aurc ne? Don yarinya mai kyau ce da nutsuwa irin wannan ba zata rasa manema ba”.
Hajja Kaltum tace“Lallai na ga alamar kin
' yaba da nutsuwar diyar tawa, kin ganta nan miskila ce mai zurfin ciki, da tsananin hakuri taki bai wa.
kowa fuska yazo, bare har a tsaida magana ita ko irin rawar kan nan ta yaran zamani sam Falmata ba ta da ita”.
'Hajiya -Mariya ta girgiza kai cike da gamsuwa, a ranta ta fara zabga addu’a.’
***
. 'Washe gari Hajiya Mariya ta harhada kayanta zata wuce Kano, Falmata kam a gurinta zamu iya cewa ga Koshi ga kuma kwana da yunwa. 'Tana son-zuwanta Kano don kuwa ranar da zasu‘ tafi musabaka‘ kasa bacci tayi don doki amma tana
tsoron kada taje a lika mata Muntarin Hajiya 'MarYam don haka ta toge akan zata je idan sun dawo daga musabakarsu ta duniya.
Bayan tafiyarta, Abbagana ' ya tattara matansa da ‘yanmatan gidan hudu na hajja Yakolo ‘sai Falmata ta biyar, uku daga cikinsu sun girme mata, wato Yakura da Salima da Zubaida, sai kuma Zahra da suke sa,a‘nni don kwanaki ne
tsakaninsu, duk‘ diyoyin Hajja Yakolo ne
Yaran duk suna qasa kamar gaske sun sha hijabai, yayin da iyayen ke sama.
Malam Abbagana ya gyara zama, sannan ya ce, “Kamar yadda na gaya muku (ya nuna iyayen mata) abinda ke tafe da hajiya Mariya shi ne maganar a nemarwa danta Muntari aure, kowa cikinku yasan Muntari, yasan alaqar dake tsakanina da mahaifnsa, don haka na yanke shawarar sanya shi cikin alkawarin da . nayi na aurar daku. Ke Falmata da keda Zahra da babu ku amma na shigo da ku yanzu, don ba zan kuma yarda wata mace taci gaba da karatu a gidan nan ba bayan ta kammala secondary ba, domin na yi akan Yakura da Salima da Zubaida ban ji dadi ba. Don haka ku ma kuna cikin wadanda zan aurar bana”.
Gaban Falmata ya yanke ya fadi, ta duqar da kai idanunta suka ciko da kwalla, wannan shine tashin hankalin da ba a sanya maka rana. ita kam Hajja Yakolo cika ta yi fam ta batse kamar zata fashe don a ganinta an tsani ‘ya’yanta ne, don matane su kamar yadda Hajja Basma ke zuga ta kullum,
Amma dai wargi ma ai guri yake sa'mu, sai dai tayi kumburin nata bata isa tace ko qala ba.
Bai kula du yadda Haijja Yakolo ke cika tana
batsewa ba, ya ci gaba da bayaninsa.
Yace“Don haka qofa a bude take daga nan zuwa sati guda, duk wacce keda Wanda ta ke so ta sanar ‘ wa da Hajja Kaltum, k0 ta same ni kai tsaye, idan wannan satin ya cika baku kawo ba, to kuwa zan sanar da Wanda raina 'ya shiryawa ya shirya ya 'kawo sadakinsa, wannan ita ce qarshen maganata daku
Hankalin ‘yanmatan gaba daya ya tashi, don sun san duk cikin samarin nasu babu na aure; ‘yan Iove you ne kawai, Zahra ce me dan dama-dama a cikinsu ta kwantar da murya ta ce
“Abba ina da magana ni”. '
Ya dube ta da kulawa, yace “,Uhm Zahra’u ina jinki” .
Gaba daya suka tsareta da ido musamman Hajja Yakolo da take tunanin matsiyacin saurayinta zata ambata, sai harararta take yi kamar idonta Zai fadi, amma ko kallon inda taje ba tayi ba. .
Ta Kara gyara zama, tace, “Abba ni dama
tun tuni Muhammadu Ligari keta ce mini na tambayo ka za su turo iyayensu, sai nace ya yi hakuri, yanzu na sanar masa kenan?”
Fuskarsa ta fadada da fara’ a, yace, “Masha Allah, kinga irin abin da nake so kenan, ki gaya masa ya turo kinji k0 Zahra?”
Dadi ya cikata kamar ta taka rawa don dadi, yayin da Hajja Yakolo kejin kamar ta hadiye zuciyarta ta mutu don takaici. .
Haka nan aka tashi daga taron kowa da abin da yake saqawa a cikin ransa.
Suna isa daki Hajja Yakolo ta dirarwa Zahra.
“Banza, sakarya, ke barazanar Abba ce ta rude ki da har kika ambata za ki auri matsiyacin yaron nan Ligari? Me na sama yaci balle ya bai wa na qasa? Yaron da ke koyarwa a makarantar islamiyya, dame kike tunanin zai iya riqe ki? K0 kin manta ké ko‘ diyar waye? Ki fito daga wannan babban gidan ki kuma Kare a dan matsiyata dan gargajiya? To wallahi ki sake tunani, sam ban laminci hakan ba”.
Ta dukar da kai tana fadin, “Ki yi hakuri Umma, amma ni dai shi nake so, ai arziki nufin Allah ne, da Abba Ya ba ni wani da ban sani ba kuma bana so,' ai gawara shi”. .
“Kc tafi can, rufc mini baki. Ai k0 da Abbanku'zai bada ku ba zai bada ku ga fakirai ba. Nasan zai zaba cikin dalibansa masu arziqi ne, ana nuna miki Gabas kina runtse idanuwa, sakarya”. Cewar Hajja Basma.
Yakura ta taBe baki tare da cewa, “Ku kuke wani damuwa da ita, ta je ta yi ta yi, idan dai rayuwar talauci dadi Ce zata ji, ni fa naji takaicin' qarfa-Karfar. da ake shirin yi mana, yanzu kamar mu da muke karatu a jami’, a ace za a bada mu? Cabdijan wallahi da an cue mu, kuma fa Abba zai iya bada mu ga wadannan daliban nasa masu dangalallun wanduna' wad’anda ba su san rayuwa ba, amma dai kamin satin nan dole nasan abin yi”.
“Yanzu Umma babu taimakon da zaki yi mana don Allah?” Zubaida ta fada hankalinta a tashe. ‘ ’
Hajja Basma' ta amShe, “Ni kuwa zan so ace yaron nan ‘dan gidan Hajiya Mariya a dakinki za a zaBar masa mata, domin k0 babu komai ai suna da bala’in kudi; kuma dai ai ba-shi da makusa ko ya ya kika gani Yakolo?”
Hajja yakolo ta yi dan‘jim, sannan tace, “daya ambaci wannan maganar naji dama cikin ‘ya’yan dakina za a baiwa, amma nasan son rai irin na malam wata qila waccan banzar munafukar yarinyar zai ba wa shi”.
“Cabdijan, mu kuma zama zamu yi mu zuba musu ido? Ai wallahi tashi zamu yi tsaye mu bi malamai da bokaye har ya fada dakinki, wannan itace damar da zamuyi amfani da ita ta qarshe don idan
muka bari wannan damar ta fada dakin Iyami zamu sha haushi, ta dinga wannan kwambon da fadin ran taga kamar da gasken tafi kowa, k0 ya ya kika gani?”
Hajja Yakolo tace “Tabbas wannan haka yake, dole mu shirya zan kira Malam Tanimu a waya anjima na ji yadda zamu yi da shi, to da wa kika ga yafi dacewa a yi aikin da sunanta...?”
“Dani!” Yakura ta yi saurin amshewa.
Zubaida 'ta kalle ta, “Candijan sannunki, , wallahi ba ki isa ba, sai dai a saka sunana”.
Salma tacc, ‘.‘Eh da yake ni ba mutum ba ce ba, ko Yasin sai dai kowa ya rasa haka kawai”. Ta yi tsaki ta doki cinya.’ , '
Nan fa rigima ta harke kowacce tana son ace da ita ce za ayi aikin tunda an kwadaita musu Muktari, kuma dai sun sanshi duk da ya jima dai rabonsu da shi, amma sun san shi dan gayu ne mai ilimi kuma. Zahra dai tana gefe cike da takaicin halayyar ‘yan uwa da iyaycnnata, idan tace zata nusar da su kuma a yi kanta kamar za a cinye ta, don haka dole ta zuba musu ido kawai.
Can Hajja Yakolo tace, “Kinga banzayc ku rufe mini baki, ni k0 kan wa ya fada duk daya ne, zan bada sunanku can duka dai, shi ke nan magana ta wuce.
Duk da haka basu daina Kananan maganganu ba, kowacce tana ganin ita yafi dacewa ace ta sami Muktari.
Ita kam Falmata kai tsaye dakinta ta wuce cike da tsananin tashin hankali, ta shiga uku ita kam, don tana ganin gwara kowa da ita, da ace ba ta hadu da Malam mai darasu ba ma da abin zai zo mata da sauki, amma haduwa' da shi ya sanya ba ta jin har abada zata kuma son wani namiji. Shi kuma ga-shi bai san tana yi ba, wai kunu a wani gida.
Matuqar tausayin kanta' ya cikata har ta fara kuka, lallai CiWon so masifa ne, shin k0 kiran malaminsu-zata yi Gwani Muhammad ta sanar da shi gaskiyar «abin da-ke ranta,’ ta kuma roke shi alfarmar ya'rok‘ar'mata Malam mai darasu k0 zai amince ya so ta? Amma tana ganin’ hakan da kamar wuya.
Ta tashi .-ta fara sintiri a dakima idonta yana zubda haWaye
K0 a makarantar islamiyya da yamma ana musu karatu kasa fahimtar komai ta yi har sanda aka biyo layi kowa ya biya sai ta yi duru-duru cike da fargaba don ba ta ji abin da aka biya bama balle har ta maimaita
Gwani Muhammad ya tsare ta da ido yana fadin, “Falmata ina hankalinki ya tafi ne, tunda aka
fara karatu na kula dake sam hankalinki yana wani guri, me ke damunki ne?” '
Ta dukar da kai idanunta sun ciko da kwalla kamar ta gaya masa abin daje damunta, ganin yadda ‘yan ajinsu suka zuba mata ido ya sanya ta yi saurin waskewa, tace
“Ka yi hakuri Malam, ba xab kuma ba”.
Sannan aka ci gaba da karatu, amma dai har aka kammala ta kasa samun nutsuwarta.
Sanda aka tashi suna tafc a hanya Yagana tadube ta da kulawa ta ce, “Kamar akwai abin da ke damunki Falmata, duk da dai nasan kina da zurfin ciki ba komai kike son fad‘awa kowa ba. Ina fatan zaki sanar dani, domin lamarin na yau babba ne _ tunda har ya gaza boyuwa a ranki kamar yadda
kika saba” Falmata ta sanya gefen hijab dinta tana goge hawayen daje gangaro mata cikin muryar: kuka ta fara magana.
“Tabbas ina cikin damuwa Yagana...”
Ta kwashe duk abin da ya faru ta sanar mata. * .
“To ke meye abin damuwa? Kin sha ce mini kina mamakin yadda su Yakwari ke Batawa Abbanku rai, kin yi alkawarin har abada ba zaki Saba masa ba. kuma ga shi ya baku lokaci yace
kowa ya kawo wanda yakc so, idan kina ganin kina tsoron zabin Abban meZai hana ki sanar da shi kina da mai sonki..”.
Ta kalle ta da mamaki, “Me sona kuma Wayc me son nawa Yagana
Ta dan yi murmushi tace “Ai masu sonki suna da yawa, kinga Malam Bukar ma ai yana cikinsu” .
‘Taja tsaki ta wucc da sauri tana fadin, “Ke idan ana maganar arziki sai ki dinga soko ta tsiya, kinga tafiyata”.
Ta bita da sauri, “Wallahi ba maganar wasa bace nasan ke ranki yana kan malam mai darasu, mutumin da bai san kina yi ba, watakila ya ma manta dake, kuma ko a hanya kuka hadu bai sanki ba, bai san wace ce ke ba, don haka gwara ki nutsu' ki koma cikin hankalinki, kin san Malam Bukar, kin san halinsa, da ki tsaya Abba ya aura miki . wanda ba ki sanshi ba, shin tsoho ne ko yaro ne, mummuna, mai mugun hali ne? Duk ba ki sani ba, a ganina gwara ki auri wanda kika sani tunda ance ita qiyayyar mace tana da lokaci. Amma idan kinga za ki iya bayyanawa wanda kikeso halin da kike ciki, na yi miki alkawarin raka ki ko’ina ne domin cinma burin ranki”.
Falmata ta dan tsaya jugum tayi sanyi
qalau, cikin alamun kuka take magana.
“Wacc mace mai mutumci kika taba ganin ta yi haka a wannan zamanin? Zamanin da ake gayawa maza ‘ana sonsu ya wuce, wato zamanin Annabawa da sahabbai da tabi’ai, domin su har abada ba zasu wulakanta ki k0 su tozarta ki ba. A wannan zam’anin namijin yaje gidanku yace yana sonki ya auro ki, yana wulakanta ki ma balle ace kece kika furta masa kina sonsa? Ba zan‘ iya ba, ina ga dai zan haqura na sanar da Abba Malam Bukar, ki taya ni addu’a Allah Ya sanya hakan shi ne alkhairi, kuma maslaha a rayuwa,ta amecn”.
Yagana ta dinga kallonta da tausayawa, tabbas qawar tata tana cikin tsaka mai wuya, sai dai ta tayata addu’a Allah Ya fiddata, a haka suka rabu kowacce zuciyarta babu dadi
Falmata ba ta taBa zaton irin wannan lokacin zaizo a gare ta da ta jima tana nema, wato ace ga ta zata wakilci duniya gasar karatun kur’ani, sannan kuma ace tana cikin damuwa ba, haka ranar ma ta wuni a daki babu walwala, duk da mahaifiyarta tasan diyar tata miskila ce_amma ta kula tun jiya da mahaifinsu ya yi maganar nan ta Kara tsangwamar kanta da damuwa, don haka ta nufi dakinta kai tsaye
A zaune ta tarar da ita akan sallaya da
alkur’ani a hannunta tana karatu cikin sanyayyar muryarta da kira’arta mai dadin saurare. Ta shiga cikin dakin ta zauna gefen gadonta.
Tana ganin babar tata ta shigo tasan muhimmin abu ne ya kawota, don haka tana kaiwa qarshcn ayar da ta keyi, ta yi sadakallahul azim,‘ta yi shaida a inda ta tsaya ta ajiye alkur’anin ta fuskanci mahaifiyar tata tace
“Hajja barka da gida”. '
Mahaifiyae tata tace, “Yauwa barkanki, nazo mu yi wata muhimmiyar magana”. Ce
Ta sake nutsawa ta duqar da kanta qasa tana sauraran mahaifiyar tata.
“Shin akwai wani da kike sone, k0 kuma kuka yi alkawarin yin aurc?”
Muryar mahaifiyar tata ta daki kunnenta, gabanta ya hau bugawa, ba tayi zaton abin da ya kawo Hajjan tata kenan ba.
Amma sai ta dake ta girgiza kai alamar, a’a. Hajja Iyami ta ce “Kinga budw baki zaki yi kiyi mini magana, bana son wannan karatun kurmayen naki”. '
Ta Kara takurewa cike da kunya, tace “Hajia babu kowa”. .
“To amma don mahaifinki ya yi miki maganar zai aurar da ke ga almajiransa kika tada
hankalinki har da su qin cin abinci, eye Ta dago kanta idonta ya ciko da kwalla, tace, “Hajja wallahi ba haka bane ba”.
,to menwne? Ai ina kula da ke tun jiyan, a tunanina kece ya dace a fara koyi da biyayyar da zaki yi wa mahaifinki, saboda yabonki da yake yi kullum. Don Allah Falmata kada ki watsa mini kasa a idona, kiyi ta addu’a kawai, sannan ki zama mai biyayya ga mahaifinki, sai ki ga Allah Ya sanya miki albarka kinji ko?”
Ta daga kai tana fadin, “To Hajja, insha ' Allah ba zan ba ki kunya ba, ki dai ci gaba da yi mini addu’ar da kike min”.
“Insha Allahu, Allah Ya yi miki albarka”.
Tana kaiwa nan ta tashi ta Fice. Falmata ta bita da kallo
Ranta yana zafi, shin wane irin ciwo ne Allah Ya dora mata haka ne‘? Kuka yana so yazo mata,.amma tana hana shi ta dauko alkur’ani taci gaba da karatunta, muryarta rana rawa tana hawayc gwanin ban tausayi.
' Daren ranar kam baccinta qalilan ne, domin kwana ta yi tana addu’ar Allah Ya zaBa mata abin da zai zama alkhairi a gere ta, da rayuwarta gaba daya‘ don haka da safe sai ta tashi wasai, ta dinga shiri cikin” nutsuwa har zuwa lokacin da mahaifinta ya aiko mata ya shirya
Suka yi sallama da mahaifiyarta da sauran yan UWanta suka fice a motarshi Su Hajia Yakolo da Basma ana ta zumbura baki. ' ~ Haija Basma ta ce.“Ni fa ban yarda Saudia za ta gasar duniya ba, an yi ne kawai don a aba mu haushi, ubanta ne kawai zai ,kaita ta huta zai wani layance mama”.
Hajja Yakolo tace “Ai shi munafunci dodo ne, mai shi ya keci Muna nan Allah zai mana sakayya wallahi”.
A can makarantar islamiyyar tasu ta Elkanemi bara’imul iman suka hadu da babban Yayanta, Yaya Bulama dan gidan Hajja Kaltum, domin a tsarin tafiyar dole ita sai ta tafi da muharraminta tunda doguwar tafiya ceda za, a yi kwanaki, da yakeshi ma Yaya Bulama tsohon gwani ne na shekaru ashirin da daya da suka wuce, shi ne ya daukowa Nigeria lambar farko a duniya, don haka yasan komai akan tafiyar.
A nan Elkanemi Bara’imul Imana din suka rabu da Abba yana ta yi mata addu’a. Falmata kam tunda suka kebe da Yagana hankalinta ya kwanta, domin har da Yaganar za, a tafi, domin itace tazo ta uku a Jihar Barno. tun kafin a tafi ta qosa gaba daya, sai Alabura da tazo ta biyu, amma ita makarantarsu daban, don haka wannan karon ma dasu za a tafi
Suna nan sauran suka kammala zuwa har da Alabura, don haka aka dunguma aka wuce Maiduguri International Airpor ta inda daga can za su daga Kasar Saudia.
SAUDI AREBIA KING ABDUL’AZIZ AIRPORT
An sauke su a babban hotel din DARTA PVHID, tun daga airport suke ta kalle kalle, domin wannan shi ne karonsu na farko da suka taBa fita kasar waje kowanne ya rike mamakinsa a cikin ransa.
Sa’i dai da suka isa masauki suka dinga dariya da maida yadda aka yi, musamman sanda ’ suka keBe a guri daya.
Kwanakinsu uku aka fara gabatar da musabakar, dukkanin kasashen musulmi sun hallara a gurin, irin su Saudian kanta, su Misra, Iraq, Fakistan da dai sauransu
An fara gabatar da musabaqar cikin kwanciyar hankali da kowa yana fatan ya zamo na daya a ransa.
Ita kam Falmata kusan kullum sai taje dakin Allah mai tsarki ta yi ta salloli da addu’o’i, har zuwa wannan lokacin ta gaza mantawa da malam mai darasu . amma ta sani zata iya auren kowa ta zauna da shi bisa biyayyah da girmamawa, sai dai sonta guda daya yana ga bawan Allan nan Kuma tana samun nutsuwa a ranta duk sanda ta ziyarci dakin Allah, don haka duk sanda bata kai ziyarar ba sai taji ta babu dadi
An dinga gabatar da musabakar daki-daki har zuwa sanda aka zo kashi na karshe, wani abin alfahari da farin ciki a gurin duk wani dan Nigeria da dangin Falmata, domin har wannan lokacin tana kan gaba ba ta yin baya.
Ana saura kwana guda a gabatar da kaso na qarshe wanda ya rage ita da wata qalibar qasar Saudian, 'tawa'gar manyan malamai ta iso daga Kasar Nigeria cike da alfahari da jin dadin qokarin da daliban nasu suka yi.
Shi kam Abdul a mataki na biyun qarshe ya tsaya, wanda idan aka fiddo gwarzo na daya na biyu shine zai zamo na iki.
Gwani Muhammad me ya kirasu a waya su isa can masaukinsu, domin su gana da malaman da suka iso. Doguwar riga ce a jikin Falmata, mai tattara daga qirji, mai qaramin hannu, don haka ta dora bakar silk din doguwar abaya mai yalwa. Ta nade kanta da irin nadin nata na Larabawa da silifas na fata mai kyau a qafarta. Kusan su ma duk dogayen bakaken rigunan suka sanya kamar
baqaken larabawa, suka nufi masaukin nasu.
Da sallama suka shiga kan Falmata da ma sauran d‘aliban yana qasa, har suka isa inda aka nuna musu su zauna
Malamai suka fara jawabinsu da qarfafa gwiwa da yabo matuka, bakin Gwani Muhammad da Yaya Bulama yaqi rufuwa don dadi, har bayanin Ya dura akan shehi na qarshe
Da zolaya ya ce “Ina ce an barki kin je Kano din kin gano ‘yan uwan naki?”
‘ Ko cikin bacci ta ji wannan muryar zata shaidata, don haka ta d‘aga kanta da sauri qirjinta yana wani irin bugu, Yagana ta kula da yanayinta.
Suka had‘a ido da Malam mai darasu karo na farko da suka yi kallon-kallo, ta yi saurin duqar da
' kanta qasa cike da kunya tana dariya.
Gaba daya farin ciki ya cika ta, fuskarta ta kasa boye hakan, sai fararen haqoranta ke kyalli, lotsawar kumatunta (dimple) na dan qara haskaka fuskarta
Ya ci gaba da jawabinsa duk da shi ma ya dan shiga wani hali, domin tun a wancan karon muryarta ta girgiza shi, balle yau da yaga fuskarta. Cikin ransa yake fadin “Tsarki ya tabbata ga ubangijin da yayi wannan kyakkya
war halittar’
"Kin zame mana d‘alibar da zamu yi alfahari da ita....
Sulaiman Bomboy.

MATACCIYAR RAYUWA
CHAPTER 4
Alfahari dake har abada, ko da ace anan kika tsaya wato gurbi na biyu, balle ma muna fatan ki zamo garzuwar duniya gaba daya, ki kwantar da hankalinki ki sanya a ranki ko kin ci k0 baki ciba ' baki da kaico sai lada domin ba caca bace aikin Allah ne, Allah Ya yi muku albarka ameen”."
Duk bayaninsa yafi na kowanne yi mata dadi, ba wai don yafisu iya kalamai ba, a’a don dai shi ranta ke ganin yafi din.
Har aka basu.umarnin su tafi ba ta sani ba, sai da Yagana‘ ta dan zungureta sannan ta farga' suka fice.
Koda suka isa daki bakinta yaqi rufuwa, kowa zai iya ganewa farin cikita yafi na kullum,
‘Yagana kam bata buqatar fashin baqi Alabura ce ma ta ishe ta da magana kamar zata tsage mata kunne
“Anya kuwa Malam mai darasu bai Kyasa ba? Nifa ina ganin yarinyar nan kin tafi da imanin Malam Muhammad mai darasu , kai ina ma nice, kin ga wani kallo da yake yi miki?
Hmm Kin san Allah bani da sha’awar auran ustazan nan amman irin yau Kin gansu tsaf-tsaf babu abin da za a nuna musu na wayewar rayuwa, ga bokon .ga arabic din. Dan gemunsa cas bai fiye tsayi ba. ga kwantaccen saje, ya kuma iya tsara kwalliya kamar za shi gasar shigar gargajiya ta Afn‘ca”.
Suka dinga dubanta da mamaki, Yagana tace, “Kc Alabura har kika iya tsayawa kika yi masa wannan kallon kurullan yanzu?”
Alabura tace, “Ke rufa mini asin', babu wani kallon kurilla a kallo biyu na gano hakan”
Suka fashe da dariya gaba dayansu, Falmata na fadin,"‘To ai-kallo daya ne ya halatta ba biyu ba, Alabura”.
Ta ce, “Uhmm Allah dai Ya yafe mana, amma mutumin ya hadu Allah kuwa, idan kika matsa zai ambata miki yana sonki, don irinsu suna da wuyar sha’ ani wallahi, amma idan mace ta kama su a hannu ta dace, wallahi”.
Yagana ta dan daki kafad‘arta tace“Kawata k0 dai shi ne sintirin da ake ta yi harami babu dare babu rana?” Tana dariya.
Falmata ta yi shiru ba ta amsa mata ba, don ba ta son fasa sirrin zuciyarta, tafi son ta barwa ranta sirrinta zaifi mata sauqi fuye da komai, musamman ma gudun muguwar fassara.
Ta gallowa Yagana harara ta rasa mai ya sanya duk abin da ta yi take ganota nan da nan. Koda yake Allah Ya baiwa Yagana wani irin kaifaffar kwakwalwa da duk abin da ka yi sai ta gane ka, ta nufi gado ta fada don ba zata iya da
halin Yagana ba.
Suka dinga tiqa mata dariya harta qulu ta lumshe idanuwanta wai bacci take amma tunanin malamin ta ke ashe sunansa Muhammad ma, wato m’ai darasun lakani ne da ya maye sunan nasa na gaskiya ke nan? Sai ta ke suffanta kamanninsa kamar yadda Alabura kefadi, sai ta ga tabbas haka din ne, ta tsinci kanta. da addu’ ar Allah ya sanya Malam mai darasu yana cikin qaddarorin da Allah Ya tsaro mata.
Ita kam ta kuma samun Kwarin gwiwa, k0 ba komai tana son.ta sanya Malam mai datasu farin ciki tunda tasan yana gurin, don haka ma kusan kwana ta yi tana roqon Allah ya ba ta nasara.
RABITAH ISLAMIC WORLD LEAKUE. ~
Yankin filin da ake taron gasar musabaqar
na Saudia mai suna a sama yayi cikar kwari. Malamai, larabawa da bakar fata kw jere a mazauninsu na alkalanci, bandakalmomin larabci babu abin da ke fitowa daga-gurin, sai sanyayyen Kamshin turaren almiski da ya gauraye gurin
Falmata tana can inda aka tanada domin su. Bayan an yi addu’a aka fara gabatar da musabukar kamar yanda aka saba, Hanna ‘yar qasar Saudia aka fara kira ta yi karatunta cikin qira, ar hafsi,
wacce ta karade gaba saya dakin taron da ya yi tsit, har ta kammala ta amsa duk tambayoyin da aka yi mata. ' . ' . Daga nan aka koma kan Falmata ta yi karatunta cikin sanyayyar muryarta mai cike da kwarjini, har ta kammala ba a yi mata k0 gyara daya ba. Sai Ayush da ta yi nata karatun, wacce ita ce ta qarshe daga nan alkalan gasar suka dukufa fidda sakamako.
Daga qarshen musabakar Alkalan gasar sun tabbatar da sunanta a wacce ta zo ta daya, wato gwarzuwar duniya' ke nan a Bangaren mata. Yayin da Hamia tazo ta biyu daga Saudia, sai Ayush da tazo ta uku daga Misra, a Bangaren maza kuma Saudia ce ta fidda gwarzon shekara.
' Sun koma masaukinsu cike da kyaututtuka da yabo, dadi ya cika ta don tasan zuciyar malamanta da Malam mai darasu ta yi haske da farin ciki. Abbanta ne ya fara kiranta ya yi mata murna da sanya mata albarka, sannan ‘yan uwanta ma'za 'suka dinga kiranta suna yaba mata, arziki naduniya kam ta same shi darajar karatun alkur’ani har sai take ganin tafi kowa farin ciki.
Tunda suka fito daga babban d‘akin taron musabakar RABITAH ISLAMIC WORLD LEAKUE
ta dinga rarraba ido ko zata hangi malam
mai darasu, amman bata ganshi ba, har suka isa masaukinsu, hakan ya dan taba ranta sai dai ta dake. '
Har suka fara haramar komawa Nigeria bata kuma ganinsa ba, sai daga baya neta ke jin Ya wuce Jami’atul Madina shi da wani Malami, don za su gudanar da wasu ayyuka, su daga, baya za su taho gida.
Ranta ya d‘an sosu har sai da ta makale a bandaki ta yi kuka, domin ko babu komai ta so tayi masa kallon karshe, don tasan idan ta koma gida babu wani bata lokaci za a aurar da ita ga wanda ba ta sani ba ta kuma tabbatarwa da ranta da baya sonta, baijin komai game da ita magana ko sashen Alabura da Yagana ba gaskiya bane, da gaskiya ne da bai tafi bai neme ta ba, da k0 sallama ya tsaya su yi, k0 ya yi 'mata jinjina kamar yadda sauran malaman suke yi mata. Wasu ma har da kyaututtuka suka ba ta.
Dole k0 ta so k0 ta ki ta cire shi daga ranta, shi ne samun maslahar rayuwarta,
. Haka nan suka tarkata suka dawo gida Nigeria kowa yana cike da farin ciki, ita kam yake ne yafi yawa a fuskami, sai dai ba kowa ke gane hakan ba tunda miskila ce ita.
NIGERIA
Shugaban kasar Nigeria ma sai da ya shirya babban taro da aka bai wasu Falmata kyaututtuka, bakin mahaifinta da ‘yan uwanta yaqi rufuwa. Falmata tazame musu diyar da zasu yi alfahari da ita duniYa da lahira;
_Wani abu da ya fiyiwa Falmata dadi shi ne daukar‘ nauyin karatunta' da kasar Saudia ta yi na jami‘a har Zuwa sanda za ta kammala. Wannan -‘abin' ya yi mata dadi, sai dai mahaifin nata yace, sai idan 'tayi aure mijinta ya amince sai ta tafi saboda'haka murnarta .ta koma ciki, don tana ganin
‘ zata iya amfan'da wannan damar ta karatunta a ' Jami’atul Madina, tunda malam mai darasu yana da alaqa dacan 'din
Kwanakinta uku da' dawowa mahaifin nasu ya kuma tarasu gabanta yana faduwa ta isa dakin. Kowa ya hallara tana shiga su Yakura da Hajja Yakolo suka dinga yi mata wani kallo na banza, domin suna takaicin irin abin arzikin da ta samu‘, kuma Abban 'ba shi da wata magana sai tata a gidan. Ta sami guri ta rakube cikc da fargaba.
Abbagana ya gyara zama sannan ya fara magana. ' .
“Kamar yadda nake ta fada, ina cikin matukar farin ciki na abin da Falmata tayi, domin
ta kuma samowa wannan gida daraja da d‘aukaka ba kamar yadda sauran ke neman zubar mini da darajar gida ba.
Wannan abu ya sanya mutane da dama sun nuna sha’ awar na basu auren Falmata, ciki kuwa har da sarakai da attajirai da ace kuma hakan kukayi koyi da hali irin nata bazan yi ta baku lokacin fito da miji yana shudewa ba idan baku manta ba a can baya na sanya muku watanni suka shude ba ku cika umarnina ba, na kuma baku sati daya wanda dalilin tafiyar Falmata musabaka ya Kara sanya lokacin ya tashi har izuwa wata guda, amma a banza kuna ganin kamar wasa
nake. Sai dai kun fi kowa sanina babu wasa cikin . '
' lamarina, don haka a yau ne nake son sanar daku ranar juma ’a mai zuwa za a daura muku aure da mazajen da na tanadar muku!.
Gaba daya hankalinsu ya tashi, zuciyar Hajja Yakolo tsai hanqoro ta keyi tamkar zata fashe, gani take kawai an shirya haka ne domin a tozartata a idon duniya. .
Cikin zafin rai tace “Gaskiya Abba idan aka yi haka ba a yi min adalci ba, ai kai kanka ba ayi maka irin wannan auran ba, kai da kazo a wancan zamanin ma balle wannan zamanin. Kawai dai ana son a wulaqanta mini ‘ya’ya ne
Allah Ya ba ni ‘ya’ya mata, ai na jima da gano ba kaunar ‘ya’yan nan kake yi ba, kafi son maza, na ga ai ba ni na baiwa kaina ba...” Sai ta fashe da kuka. . '
Ran su Yakura da Zubaida ya yi. sanyi, gwara ta kwatar musu ‘yancinsu ko saji dadi
Shi kam yake ya yi, wanda ake kira yafi kuka ciwo, sannan ya fara magana.
“Tsakanina dake za a sami wanda bai qaunarsu, don ni dai nasan Allah Shi ke bada mace da namiji, ya‘ragega dan Adam ya yi musu irin tarbiyyar da ta dace, domin tarbiyya ke nuna da na gari ba jinsi ba. Tunda aka haifi yaran nan nayi ‘qoqarin ba su nagartacciyar tarbiyya da ilimin da ake yayi : a wannan zamanin, domin su sami nagartacciyar rayuwa, amma sai da kika yi kutunkutun din da kika lalata musu tarbiyya har suke kallona a dan qauye wanda bai san rayuwa ba, suke ganin rayuwar Bature ita ce ta dace da su, har ya zamana samarin da suke tarawa marasa tarbiyya da na kore'su kika ce ina korarwa ‘ya’yanki samari, don suna da farin jini. Yanzu kin gano abin da nake guje musu ko‘.’
Samarin arziki sunga na banza sunqi zuwa. yayin da na banza suka gaza amfana muku komai, sai dai magana ta ta qarshe ki sani umami ne nake
yiwa ‘ya’yana, idan idonki zai iya gani to, idan ba zai iya kalla ba qofa a bude ta kc, don bazan iya lamintar abin da na laminta a kanki a baya ba”.
Ta kuma rushewa da kuka tana shirin yin magana ya daga mata hannu, yaci gaba da magana.
“Ke Zubaida akwai malam Mu’azzamu, limamin masallacin juma’a ne kamar yadda kika sani, shi ne mijinki don sadakinsa zai iso da daddaren yau. Ke kuma Yakura Alhaji Isa mai sumunti ne mijinki. Ke kuma Salima Hassan dalibin nan nawa da yazo daga Sokoti ne mijinki. 'Kekuma Falmata Muntari dan abokina Abbas shi
ne mijinki insha Allahu..
. “Wallahi wannan son kai ne, ta ya ya za a baiwa Falmata Muntari? Ai a dakina ya dace a yi
, masa mata idan dai gaskiya ne” . Hajja Yakolo ta
katse shi a harzuke tana ci gaba da kuka. Su ma
‘ya’yan nata duk 'sai suka saka kukan.
‘ Hajja Iyami ta kwantar da murya, tace “Malam idan kana ganin hakan zai zama rigima ka bai wa Yakura ko Salimar Muntarin mana,ita Falmata k0 wa ka bata ai zata yi murna da godiya ne.
Falmata kam ta yi wuki-wuki tana ganin duk wanda aka ba ta ita babu wani gwara, su suka wani damu da Muntarin Kano, ita da za a yarda ai
da an cire ta daga wannan tsarin auren, amma tasan ba ta isa ta ja da maganar mahaifinta ba, don haka taja bakinta ta tsuke tana jiran hukuncin da za a yi. Abbagana ya harzuka matuKa ya kalli Iyami, yace “Kina ji ba wai na taraku na nemi shawararku bane, a’a, umarni no make bayarwa kowa ya tashi ya ba ni guri, sai ku sanar da ‘yan ‘ uwanku ranar jumna’a'daurin auren ‘ya’yanku, saura kwanaki takwas ke nan”. ' Haka nan suka tashi kowa da abin da yake sakawa a cikin ransa. '. .
A dakin hajja~ Yakolo, Hajja Basma keta ' ‘ qara ingizata wanda da ace tana da hankali da ta gane domin duk abinta ba ta cewa uffan gaban Abbah, wai dole ita nan mai kirki, ya riga ya ganota amma sai ya kyaleta yake kallonta kawai.
“Wallahi wannan shiryayya ce don cuta, ace duk an hada‘ yan dakinki datarkace, sam da sake’? . inji Hajja Basma
Yakura ta dago jan ido tana cewa, “To wai ni Momy_ina aikin da kika ce malam ya yi aka ba mu magani da turare muka yita dirka, amma ace maganar nan ta tashi daga kanmu?” , '
Hajja yakolo tayi saurin amshewa, “Ya zama asara, ai na jima ina aiki akan uban nan naku amma a banza, tun ba kawoku duniya ba nake neman
fada ta hanyar malamai da bokaye, sai dai tamkar ina shuka dusa, na ma rasa yadda zan yi da rayuwata”. Ta qarasa maganar cike da tsananin takaici.
_ Zubaida ta amshe, “Ni kam guduwa zan yi, gwara na bi duniya idan ya huce na dawo, don wallahi ba zan yarda kamarni mai digiri a hada ni aure da wani wawan almajiri ba, ba zai yiwu ba”.
“Keki kiyayi kanki, wallahi malam ya yi miki aikin shashatau ki zama mara hankali da dai ace kin jawo masa wannan abin kunyar, ki shiga taitayinki wallahi, kuma kina tunanin idan kika qi yarda da auren nan zai kuma yarda ki zauna masa a gidansa ne? Akul na kuma jin wannan maganar, ku dai ' barni da shi, akwai‘ wani hatsabibin boka dake' tsafi, gobe zanje na same shi, komai zai zamo daidai dole ma kuwa”. Yakolo ta qarasa tana hura hanci.
Wannan ya sanya sauran yaran suka dan kwantar da hankalinsu, don sun san Babar tasu Boss ce. . ,
ita kam Falmata abin ya tsaya mata a ranta, sai dai ba ta son mahaifiyarta ta fuskanci hakan, don haka dole ta fito babban falonsu ta tattara qannenta tana ta koya musu karatun Alqur’ani mai girma, hakan ne ya dan sanyaya ranta. Can da aka
jima ta tambayi mahaifiyar tata ta shiga gidan su Yagana.
Ta bata izinin shigar domin ita kanta tana tausayin diyar tata, ta riga ta gano ba ta maraba da wannan auran, amma tsananin biyayya ya sanya taqi nunawa koda akan fuskarta.
' Sanda ta isa gidan su Yagana suna kebewa a dakinta ta fashe, da kuka mai ciwo, hankalin Yagana ya tashi matuka, ta dafe Kirji tana fadin
“Subhanallahi, Falmata me ya yi zafi haka? Don Allah ki kwantar da hankalinki, nasan dai ba zaiwuce maganar malam mail darasu da kuma auren da Abba ke shirin yi ba” .‘
Ta dago kai idonta jajur ta ce “Na rasa yadda zan yi da raina Yagana, addu’ ar da Abba da Gwani Muhammad suke ba ni duk na yi amma kullum son mutumin nan kuma karuwa yake yi a raina, babu kuma abin da yafi mini ciwo illa za, a aurar da nine ga, mutumin da bai son auran, fa shi da bashi da lokacin wata diya mace ma bayan matarsa da ta mallake shi. Yarizu kina zaton akwai wani jin dadi da kwanciyar hankali a auran irin wadannan mutanen’.’ Tabbas Abba ya yi shirin auren na huce dani, Wanda nasan karshensa kuma wulakanci da dana-sani ne, dama na amince tun farko na fara Sauraran Malam Bukar da duk hakan ba ta faru da ni ba. Ni kam na ga ta kaina a rayuwata”.
Tausayinta ya cika Yagana domin ta bata labarin abin da ya hanata bin Hajiya Mariya Kano, wato ta yi gudun gara ta fada gidan Zago kenan, amma ya ya ta iya? Haka nan ta dinga lallashinta har ta dan kwantar mata da hankali tana fadin.
“Nasan Allah Ya amsa addu’arki, domin bakinki mai albarka ne, bakin da ya saba karatun littafi mai girma Allah ba zai wofintar da shi ba. Nasan wallahi Allah Ya amshi du’a’inki, sai dai ba mu sani ba a duniya zai cika miki shi, k0 kuma zai sanya miki cikin mizaninki na can ne wanda nasan sai kinfi farin biki idan kika riske shin ' Kece fa kece mini wannan duniya wani ',d‘an taqi ce mara dorewa, k0 kin manta hadisin ma’aiki , duniya kurku ce ta mumini, kuma aljana ce ta fasiki, don haka ki kwantar da hankalinki, ki dauki duk batun aurenki da Muntari a matsayin ibada, wacce zaki yi fatan ta kai ki aljana, ki yi kuma ta addu’a Allah Ya musanya miki halinsa da na matar tasa sa su zama masu alkhairi”.
Da wannan ta dan sami nutsuwa da sassauci a cikin ranta har suka ci gaba da hirarsu. .
Sai da ta ga magriba ta doso sannan ta yi haramar komowa gida. Gidansu yana kallon gidan su Yagana, ita kam iyayenta ba su da shi don
karatunta ita da sauran ‘yan uwanta duk Abbagana ke daukar nauyu. KUSan rabin hidimar gidansu ma shi neke yi, sai dai Yagana ba ta fiye shiga gidan su ba sosai saboda wulakancin su Yakura, domin su ba su harka da diyan talakawa, ita kuwa Falmata babu ruwanta tunda ta taso suka shadu da Yagana ba ta taba jin wani fifiko ko dana digon kwayar zarra a ranta game da ita ba, wannan ya sanya mahaifiyar Yagana ke matuqar sonta da yaba mata.
Shakuwarsu' ta kai ko d‘ankwali Malam Abbagana inzai dinkawa Falmata sai ya hada da Yagana, hatta Hajja Iyami ma, domin ita kanta ta 'yaba da tarbiyyar Yaganar kusan babar Yagana Hajja Fatime ma kawarta ce,'ko muce aminiyarta.
Tana shiga harabar gidan nasu can daga qofar sashin da zai sadaka da sashin Abbansu ta hango su Yakura da Zubaida suna ta haqa rami. Tasa musu ido cike da tsananin mamaki, tana kallonsu har zuwa sanda suka zaro wani abu daga cikin _laffayar Zubaida suka sanya a ramin suka maida da sauri suka rufe, har da dandabéwa. Ita kuwa tsananin mamaki ya sanya ta kasa motsawa har suka kammala.
Sanda suka hangota tana kallonsu sai da Suka firgita matuka, amma da yake zuciyar ta taurare sai suka dake suka nufota da saurinsu, ganin
ta dauke kai tana shirin Shigewa Kofar da zata sadaka da ainihin gidan.
Zubaida ce ta fara magana, “Magulmata makwanzama masu zuwa lahira da kokon dambu, . wallahi mukaji wannan maganar a bakin wani sai kin gwammace kida da karatu, munafuka”.
Yakura ta amsh “Kc ba ki ga har wani rawar kai ta ke ba, don ita an mata kyakkyawan zabii, to yarinya bar murna karenki ya kama zaki, mu nan zamu yi maganinku, banzaye”.
Ita dai ta wuce da saurinta ta nufi sashinsu, ~ domin ta riga ta saba da wannan halin nasu, tunda ta taso tana yarinya ta ke shan wahalarsu da shegen . ‘yan ubanci, da ace dane ma sai sun hada mata da
‘ duka. '
" tana isa sashinsu ta wuce dakinta, ta dauro ' 'alwala ta jima gurin sallah tana gayawa Allah, amma kuma _dai ta gaza samun nutsuwa tana ganin kamar wani abu zai iya samun Abban nasu. Ta kuma yarda duk abin da ya sami Abban nasu da kamashonta a ciki, tunda dai ta gani, amma kuma tana tsoron sanar da wani don tafi kowa sanin ’halin masifar Hajja Yakolo da ‘ya’yanta, sai ma ta lauya abin ya koma kansu. Tana mamakin butulci irin na su Yakura, duk irin hidimar da mahaifinsu yake yi musu, amma har su yarda su cutar da shi.
Ta gaza jure abin da ke cin ranta, don haka ta mike da saurinta ta nufi dakin mahaifiyarta, ta tadda ita tana linke kaya tana sanyawa cikin sif, ta shiga da sallama.
Mahaifiyar tata ta daga kai tana kallonta, tana nazarin yanayinta, ta gano tana cikin damuwa amma sai ta dake ta ce
' “Ya aka yi na ganki haka Falmata?”
Ta sami gefcn' gado ta zauna kanta yana kasa, tace “Hajja wani abu na gani yanzu da bazan iya hakuri da shi ba” .
Mahaifiyar tata ta bar linke kayan ta zauna gefen gadon ta tattara hankalinta a kanta domin tasa‘n duk abin da ya sanya diyarta magantuwa ba qarami bane domin itaidai bata gulma duk abin da zaku yi a gabanta sai taga dama zata daga kai mata kalle ku balle har tasan kana yi taje ta gayawa wani, domin kuwa duk irin cin zarafin da ‘yan‘ uwanta ke mata ba ta taBa gaya mata ba, sai dai idan ita ta gani da idonta.
Falmata ta kwashe duk abin da ta gani ta sanarwa mahaif'iyar tata, ta dora da cewa, “Hajja ina tsoron kada su cutar da Abba, nasan akan maganar Muntari ce dai”.
Hajja lyami ta yi murmushi, tace, “Kada ki damu an jima ana ruwa qasa tana shanyewa.

.
MATACCIYAR RAYUWA
CHAPTER 5


Tace da asirin Yakolo zai ci malam da tuni babu sauran Burbushinsa a duniya, domin tana wata iein matacciyar rayuwa ne da babu imani da Allah a cikinta. Da mai ganewa ce da ta gane don ba na mantawa akwai shekarun da aka yi data dinga daga kadarorinta tana saidawa tana bin ‘yan tsubbu. Da malam ya gane hakan, sai ya ware wasu kudi kullum yake bamu, idan yaje ya bata sai yace ga wannan nasan ba za a rasa zagayawa ba, amma don Allah a daina saida kayan jere ai sai . dakin ya yi mini fadi. '
Ni da Yaya Kaltum ba ki ga abin arzikin da muka tara ba. don da su ma na sayi gidajen da ake mini haya da su, ita kuwa da Basma ko tsinke ba su ajiye ba suka dinga bin malamai har zuwa sanda ya gaji ya daina bai wa kowa.
Ki sani Allah Ya tsare shi da yawan addu’o’insa, naasan babu wani abu da zai faru da shi, sai dai kedin tunda nasan su ba sa daukar komai da sauki, don haka sai ki dage da addu’a kamar yadda kika saba. Zan kuma tadda malam din akan maganar Muntari, amma bazan nuna masa wannan Ba, da kansa zakiga ya gano, kada kuma ki gayawa kowa, ki kwantar da hankalinki kinji k0”.
Ta daga kai alamar, “Toh”. Sannan ta tashi ta koma dakinta taji dan sanyi a ranta da kalaman
mahaifiyar tata. Ita kam Hajja Iyami daga nan dakin hajja
Kaltum ta wuce ta roqi alfarma tayi mata jagora gurin Malam din ta_ taya ta rokon arziki, ba ta yi musu ba suka wuce tare.
Yana zaune yana kallon tasoshin Larabawa hannunsa da carbi yana lazimi, suka shiga da sallama ya ajiye carbin yana amsawa, fuskarsa a sake yake fadin
“Tunda naga uwargida da amarya sun hadu kai nasan cutata aka zo tabbas” .
Suka zauna Hajja Kaltum tace“Haba malam babu wani ”batun cuta sai gaskiya, muna fatan zaka fahimci =abin da ke tafe damu”.
Ya. gyara zama ya kalle su da cikakkiyar nutsuwa, yace ina jinku”.
Hajja Iyami ta gyara murya, sannan tace, “Malam akan maganar Muntari ne, kasan Hajja Yakolo ta jima tana mitar ana mata rashin adalci a gidan ,nan, yanzu kuma Allah kadai yasan yadda zata dauki wannan maganar. Shine nake ganin mezai hana ka hakura ka baiwa Muntarin wata daga cikin‘ yan dakima a huta?”
Hajja Kaltum ta amshe jiya zan wuce Yakolo kamar zata bangajeni tana ta surutai kalakala, wai tasan n’ice na. zuga ka, ban dai kulata ba.
don haka ka duba maganar Iyami ayi mata abin da akeso a sami lafiya”.
Ya qankance ido cike da fushi yace “Saboda ita ce wa? Wani abu da. baku sani ba, yadda kuke tsoro da shakkar Yakolo ko kusa ni bana yi, shin wai me kuka dauki yakolo ne, eyeh? To ku tsaya ku ji, wallahi idan har' Yakolo ba zata bi abin da nake so ba ita ma bara! isa na bi abin da take so ba, domin ni ke aurenta ba. ita ce ke aurena ba.
Ya kuma dace a yau nayi muku bayanin dalilin zuwan Hajiya Mariya gidan nan tazo ne akan matsalar Muntari da iyalinshi, ba zuwa kuke ba ita ma ba zuwa take ba, shi ya sanya" ba ku san halin da suke ciki ba. Ni kaina sai a waya muke magana da ita, sai dai idan na shiga Kano na kan dan biya mu , gaggaisa a tsaitsaye, sanda ta zo ta sanar dani duk halin da ake ciki, don haka nayi niyyar aura masa mace mai nagarta, wacce nake fatan ta zama fitila a rayuwarsa. Ta ya ya zan aura masa ‘ya’yan Yakolo da ba su da maraba da irin tarbiyyar matar tashi? Ku sani Yakolo babu irin abin da ba tayi akan maganar nan ba, dazu har abu ta sanya ‘ya’yanta suka binne min asiri a qofar dakina wai ita a tunaninta sai ta tursasani. Ta kasa gane ta kashe
rayuwarta data ‘ya’yanta, na zuba mata idanu,
don nasan dole wata rana duniya zata zame mata makaranta. K0 inn raye ko qasa ta rufe idanuna zata gane abinsa nake nusar da ita.
, Kuma wallahi na shirya daukar-mummunan mataki a kanta wannan karon muddin ta daure“ ma yaran nan gindi suka~bani kunya. Ku kyale ta kawai, kuma daina sanyata a lissafinku idan Allah Ya had‘aka zama da mutum ne babu yadda zakayi ‘dashi sai addu‘a”.
Dole haka suka haqura da buqatarsu domin yafisu hujja, sai dai suna gudun bala'in Yakolo, don ma tana shakkar malam da ‘ya’yan Hajja Kaltum dinda iskancin da zata dinga yi a gidan sai ‘ Allah ~ ~. Sanda suka zo fita sai suka ci karo da Hajj Yakolo a bakin qofa a tsaye tana ta cika tana batsewa, da alama ta taji duk abin da suke fadi, don sanda suka nufo sashin nasa Basma ta gansu ta falla‘ da gudu ta gaya. mata shibe tazo ta labe tana jin komai.
Ba su kallce taba suka wuce domin dai halinta sai dai'su bai wa wani labari.
Ta yi tsaki. tarceda cewa. “Ai munafurci dodo ne mai shi yake ci, kuma a gidan nan bana neman‘ gindin zama gurin kowa da duwawuna nake Zaune‘ ehe! Kuma mu zuba da mutum dan halak ka fasa Ba su kulata ba suka wuce abinsu, don sun san ' san hali‘ babu fashi, wannan ya sake qularda ita, tasanya hannu a baka cike da takaici tana cizon yatsa, duk dumbin kudin data kashe sun tashi a banza, amma tabbas fa ba zata haqura ba sai taga inda ya turema buzu nadi
YA DACE MUJI ‘ SU WAYE WADANNAN IYALAN
Malam zakariya tsohon' malami’ ne mai matuqar tarihin malunta a garin Barno, a cikin matansa ne ya auro Hajiya Fatima daga Kanon dabo wacce‘ itace ta haifi Malam Abdullahi mahaifiin Abbagana, shima. kansa. Malam Abdullahi ya taso da irin gadon gidansu na malumtar saidai ya dan hada da karatun zamani hakan yasa koda ya sami dansa tilo Abbagana wanda yaci sunan mahaifinsa, yabashi ilimin-zamani da dana addini saidai na addinin yafi yawa don har qasar Misra abbagana-ya-tafi neman ilimi kasancewa tun yana dan shekara goma ‘shabiyar ya sauke qur,’ani. dom! haka sauran littafan addini sai suka zame masa masu sauqi.
Ya jima‘ a qasar Misra yana karatu har ya fara koyarwa a can yana kuma aiki da wani
kamfanin hada takalma.
A can Misra suka hadu da Malam Abbas Wanda ya kasance mahaifi Muntari, da farko abota ce ta hada su, sai daga baya suka gano suna da ' alaqa ta wajen kakanninsu, domin kakar Abbagana da kakan Malam Abbas abokan wasa ne abotar tasu ta yi girma har ya zamana k0 ina suna tare, sai suka fara turo kaya Nigeria ana saida musu suna sarar wasu‘kayan suna kaiwa can, ga kuma koyarwa da suke yi, wannan ya sanya basu yi sha’awar dawowa ba, sai da Kyar aka yakito su, shi daman Abbagana yana da baiko da Kaltum, don haka yana dawowa aka sha shagalin _.biki, su Abbas su ne manyan abokan ango.
Allah Ya albarkaci Kaltun da haihuwa a shekara guda daya da auran nasu, inda aka samu
~Abdullahi, .wato Bulama, a lokacin harkar
kasuwancinsu da maluntarsu ta yi nisa, don kowa sai da ya bude makarantar kansa ta haddar qur,’ani '. a garinsu, banda koyarwa da suke a makarantun gwamnati.
Shi ma Abbas ya yi aure da matarsa Binta a nan garinsu kano suka tare, amma suna yawan ziyartar juna, shi kam Abbagana mai son ‘ya’ya k0 don shi kadai iyayensa keda shi har suka koma ga
Allah, don haka kullum yake fadin sai ya yi mata
hudu. Haihuwar Kaltum shida duk ‘yan maza ya fara neman auren Yakolo wacce ta yi masa lambu lambu.
Farkon auran nasu bai gano halinta ba saboda yadda ta dinga kulla masa makirci da uwarr ‘ya’yansa har ma da ‘ya’yan, Kaltum ta shiga matsala a wannan lokacin, ta dinga addu’a tana gayawa Allah har Allah ya tonawa Yakolo asiri, tun daga wannan lokacin ya ganota komai zata yi a banza, tsawon shekaru biyu tana gidan ko Batan wata ba ta taba yi. ba, wannan ya daga mata hankali ta fara bin bokaye da malaman tsubbu akan sai ta haihun dole. Cikin shekararta ta goma ta samu ciki, amma ita a ganinta asirinta ne ya bata, domin ance mata wai kishiyarta. ce ta toshe mata bakin mahaifa. Sanda cikin ya isa haihuwa ta haifi mace, ba ta so hakan ba, ta so ace ita ma namiji ta haifa saboda sanya rai da gado, shi' kuwa maigidan ya yi murna don anyi masa haihuwa har takwas duk maza, don haka ya dinga dokin. macen, wannan ya dan wankewa Yakolo rai.
_ Sanda ta kuma samun wani cikin ta dinga bin bokaye akan ta hafi namiji, nan ma Allah Ya nuna mata Shi ke bayarwa, ta kuma haifar mace har sau biyu, dole ta haqura da bin bokayen. Sai dai kwatsam sai ga maganar auran Basma da
Abbagana, da shi kansa Abbas Wanda ya yi aure na biyu ya auri Mariya, kusan tare suka yi auran da na Yakolo amma ita haihuwa tayi tuni danta Muntari ya yi wayo, shi kam daga kanta bai qara ba.,
Farkon zuwan Basma gidan ta shiga da izza da gatsali da gadara don diyar mai kudi ce don haka suka fara gwabzawa da Yakolo, ba sa shan inuwa daya, don haka Basma ta so Shigewa Hajja Kaltum amma da ta kula da yanayin rawar kan yarinyar taqi sakar mata fuska, sai dai daga sanda ‘ ta yi shekara a gidan ba ta yi ko batan wata ba, hankalinta ita ma ya fara tashi, ta dinga shige-shige amma a banza har ta kwashi shekaru biyar a gidan.
Da farko Abbagana ya dauki son duniya da kulawa ya dora akan diyoyin 'Yakolo mata, komai zai shigo musu, duk fitar da zai yi sai ya siyo musu gwala-gwalai, ga kayan kwalliya kala-kala, amma ganin tana tabara yaran da .nuna musu kishin yayyensu maza qarara take sanyawa su yi musu rashin kunya, hakan ya sanya ya fara daure musu fuska, don yana da zafi bai son "ya yansa su lalace, wannan ya sanya Yakolo ta fara mita wai an tsani ‘ya ’yanta don duk mata ne.
Gwala-gwalan da yakesai musu ma duk sai Ya daina, don ya kula kasuwarsu takeci tana bin _ malamai da kudin
A sannan ne suka fara hada kai da Yakolo tana gayawa Basma sai ta mike tsaye, don ita kanta sai da ta yi shckaru goma a gidan anayi mata gori, k0 da ta samu ciki ya lalace, kuma tasan Hajja Kaltum ce don haka idan ba ta tashi tsaye ba zata zama ‘yar kallo a gidan, don haka ta fara rakata gurin malamai. ,
Saidai abanza amma suka gaza hakuri,har maigidan ya kula da halin da suka shiga, ya fara yi musu nasiha, amma sai suke ganin kawai Hajja Kaltum ce ta mallake shi, ga yadda yaje yiwa ‘ya’yanta hidima, manyan suna waje karatu daga wadanda suke qasar Sudan, sai masu Misra, sai masu Jami’atul‘ Madina, karatu suke yi sosai, don kusan shakaru uku a jere daga gidansa ake fidda gwanin shekara, wann‘an ma ya tsayawa Yakolo da Basma a ransu saboda kyauta ya dinga yi musu ta bajinta.
Wata musabaqar karatun qur,’ani da aka yi yana cikin alkalan musabakar, Allah Ya hada shi da Iyami, wacce ta zo ta daya ga jaharsu ta Maiduguri, bai yi wasa ba ya nufi gurin iyayenta da ncman aurcnta. Babu mutumin da zaiqi yarda ya hada zuri’a da Abbagana domin Allah Ya ba shi ilimi, ga dukiya ga kuma hali na gari. Ita kanta Iyamin duk da a haife ya haife ta ba ta wani jaba ta ji tana sonshi aka sha biki
Ina wuta Yakolo da Basma su jefa Iyami, musamman da aka kawota suka ganta ‘yar yarinyarda ta fisu komai. Sai dai ba basu isa su cutar da ita ba. don tuni ya gina qaton gidanshi kowacce da sashinta da na ‘ya’yanta babu ruwan wata da wata, saBanin tsohon gidan nasu da dakunan nasu suke a jere, don haka sai ka so zaka ga wani ma. Hakanne ya yi musu katanga da Iyami, amma duk da haka suna yin duk wani abu da zasu quntata mata, sai dai basa gabanta.
Kuma cikin ikon Allah watan da aka kawota ta sami ciki da yake tana da laulayi kowa sai da ya sani.
A wannan. karon Basma tafi kowa shiga damuwa ganin an kawo wata a bayanta zata haihu ita ba ta ajiye ko kwai ba, sun yi duk yadda zasuyi amma sai da Allah Ya kawo Falmata wacce ta fad‘o a hannun Hajja Kaltum, domin tana fara ciwon ta sanya masu hidimta mata suka sanarwa da Haija Kaitum domin ta taimaka mata domin kuwa ita ce mace ta gari a gidan.
Falmata ta taso yarinya mai kyau da haquri, ga shiga zuci ga ladabi da biyayya, don haka yayyenta maza ke bala’in sonta, duk inda suka je sai sun dawo mata da tsaraba niqi-niki. sabanin ‘ya’yan Yakolo da kowa ya tsana saboda rashin kunya da fadin rai. Tun suna qanana suke kyarar masu aikin gidan nasu.
Tun daga kan Falmata ba _ a cika shekara biyu ba sai Iyami ta haihu, kuma duk maza take haifa, abin yake yiwa Yakolo da Basma ciwo ke nan, don haihuwar Yakolo bakwai, amma duk mata, sai ta ke ganin ya ya wata zatazo a banza ace tana ta haifar maza!!!!!! Allah dai Shi ke badawa, ita kam Basma ta nemi duk wani asiri a banza daga Karshe ta koma ganin likitoci suka tabbatar mata da lafiyarta qalau, illa dai haihuwace da ba a yiwa Allah dole, sai lokacin da Ya ga dama zai bada.
Kasancewar ‘yan uwan Falmata duk maza ne ya sanya ha tajin dadin wasa dasu, sai ta tafi dakin Yakolo gurin ‘yan uwan nata, amma da kuka zata koma sashinsu, Zahra,u ce kusan sa’arta, ko taje bangaren nasu itace mai dan janta a jiki suyi wasa amman daga qarshe saida mahaifiyar tata ta hanata, ita kuwa falmata azabace ta sanyata daina shiga sashin yakolon don banda Allah yayi da kwananta a gaba da tuni sun kasheta
don har shinkafar bera sun taba zuba mata cikin abinci aka kaita asibiti ranga ranga aka sakota da kyar wannan ya sanya mahaifiyarta ta dinga kulleta a daki ,
Shi kuwa Malam Abbagana cewa ya yi, duk wacce ta aikata wannab aikin bai yafe mata ba,
Allah Ya isa tsakan’insa da ita.
K0 a jikinsu domin ba su san darajar kansu ba. balle har su san munin Allah Ya isan da aka yi musu ba, 'tun tana da shekaru bakwai ta fara ciyo gasar karatun izifi biyu a islamiyyarsu, wannan ya sanya Babanta sonta matuka, domin yana bakin. cikin daukacin ‘ya’yan Yakolo su baga bokon ba, balle a islamiyyar, sai shegen girman kan tsiya da masifa, nan suka fiauki.
Yagana ce kawarta a cikin layinsu, tun daga islamiyya har zuwa wasan yara na unguwa tare suk‘e yi, sai dai idan ta shigo gidan suka ci karo da Yakura k0 Zubaida k0 Salima sai sun daketa, wannan ya sanya ta daina shiga gidan, sai dai ita Falmata taje gidansu.
' Abin da yake bai wa Hajja-Yakolo da Hajja Basma haushi bai wuce ganin Hajja Iyami da tazo a bayansu tana ta haihuwa ba, suka dinga yin duk yadda zasu iya amma a banza sai don saida ta yi goma sha ‘biyu, Falmata' ta farko, sai qannenta maza tara, sannan aka haifi mata biyu, wannan abu yana yi musu ciwo, don dai babu yadda za su yi ne da yin Allah, da zasu gane da sun daina asiri tunda baiyi tasirin komai ba.
Hidimar biki kam an farata da gaske, cikin amaren nan guda biyar Zahra ce kadai mai murna, domin itace aka bata wanda take so, duk da mahaifiyarta taso hanawa amma babu yadda zata yi dole ta hakura ta kyale ta.
Falmata kam ba zaka gane bacin ranta ba, domin tana ta walwalarta, sai dai duk wanda ya santa ya san ta rame matuqa, sai qashin wuya, daman ita aba ba auki ba.
Saura kwana biyar daurin aure Malam Abbagana ya kirawo wayar Muntari ya ce, lallai yazo ranar juma’a yana son ganinsa. Yana kuma son ya yi sallar juma’ a a Maiduguri, don haka ya hayo jirgi cike da damuwa muntari yake tambayar lafiya?
Ya cc masa kalau, ya dai tabbatar yazo din. Sun rabu akan zai zo ranar juma’a aka ci gaba da hidima.
Tabbas da ace auren sobe da ‘ya’yan nan sunfi kowa murna, domin mahaifinsu ya yi musu kaya na gani na fada daga Dubai ya yi odar komi. hatta kayan sanyawa sai da ya yiwa kowacce saitin jakunkuna biyu-biyu, don shi sadaki kawai zai amsa. duk wata bidi’a yace idan matarka taje gidanka ka yi mata.
Yakura kam mijinta-mai arziqi ne Alhaji Isa
mai sumunti, sai dai matansa biyu ‘yan bala’i ne kamar wuta, tunda aka fara maganar auran suke rigima, ga shi da zagada-zagadan‘ ya’ ya, shi kam murna yake yi, domin yasan "ya yan Malam Abbagana babu na banza, duk kyawawa ne auren . kyau zai yi
Anje anyi jere a manyan dakunanta guda “uku“. sai dai ‘yan jeran kansu sun san an kawata gidan dai-dai ita.
Zubaida kam nata babban malami ne don haka gidansa gida nena tarbiyya da tsantsani, dole ta ajiye duk wannan gayun da iya yin nata na Turawa, domin gidansa ba a fita da rana sai dare, sannan ba,a karamar shiga, don ko da aka je jere ma yace musu duk wani abu da ya kama na hoto ne su koma da shi ba a sanya hoto a gidansa, matansa uku ne ita ce ta hudu.
Ita kam Salima ita ce mai dan gwara-gwara, domin ita Hassan dalibin babanta ne saurayi ne fil, kasuwanci ne ya kai shi Maiduguri yake zuwa gurin lecture din malam har suka zama daga cikin ‘yan kwamitin masallacin gidan.
. Don haka shi gidan haya ya kama mai daki hudu, da wata amarya a ciki da take da dakuna biYU, shi ma ya amshi biyun, don haka kayama da Yawa sai da aka koma da su gida.
Zahra din dai da 'ake raina mijinta tafi kowa morewa, domin ya kammala ginin gidansa tsaf, gwanin sha,awa aka jere mata komai ba ta da wata matsala ita kam auran soyayya zata yi.
Falmata kam an ajiye kayanta, domin ita sai mijin nata ya zo sannan za,aji inda zai ajiyeta, don haka jeranta ya rage. '
Duk labarin da yake zuwa kunnen Yakolo daga bakin Hajja Basma ba labari ne mai kyau ba, ita da‘ ya ’yanta sun tashi hankalinsu matuka banda taji yace muddin ta zuga diyarta ko daya ce ta bashi kunya akan wannan aurcn to itama a bakin aurenta, da cewa zata yi duk su gudu, sai dai ya ya suka iya? Haka dole suka hakura.
Su kam danginsu . sun cika gida suna ta sha_’aninsu cike da farin ciki, ‘ domin daman zamansu Yakura kamar akan ransu suke saboda yaran ba su da'kunya ko cikin dangin ba su da farin jini ba su da wani kataBus. .
Anti Shafa’atu matar_ Yaya Bulama ce ta tsare Falmata mai gudun gyaran jiki domin mai gyara guda mahaifinsu ya dauka. Zahra ce kadai ke zama a yi mata gyaran hankali kwance, sai da Anti Shafar ta tsare Falmata sannan ta yarda. Ai kuwa gyaran kwanaki uku kacal aka yi mata sai gashi ta fito tana ta kyalli da sheqi sai kamshi ke tashi a
jikinta da ta gilma ka.
Da yake an sha sanarwar daurin auren masalaccin juma’ ar ya cika dankam! Da mutane, ana tsaka da huduba Mukhtar ya iso cikin shiga ta alfarma kamar yasan abin da za a yi, ya sami guri ya zauna yana sauraren huduba har aka kammala, kafin a tayar da sallah ya turawa malam saqon ya iso, don haka ana idar da sallah kafin a daura aure ya sanya aka nemo masa shi suka keBe can waje, tunda shi daman babu shi cikin daurin auren, sai anzo kan Falmata inda zai amshi wakilcin Mukhtar.
A can gefe suka kebe, Mukhtar ya durkusa yana gaida Malam cikin biyayya, Malam Abbagana ya amsa da farin ciki, sannan ya dora da cewa.
“Kasan dalilin da ya -sanya na ce ina nemanka kuwa?”
Cikin girgiza kai yace “Ai nasan nayi laifi Malam, na jima ban zo mun gaisa ba, don za a yi shekaru biyu ko uku ma. Ina fatan za a yi mini afuwa?” .
Malam ya yi murmushi yace “Ai wannan mai sauki ne, tunda ina zuwa Kanon ina kuma tambayarka ace kana nan qalau. Wani muhimmin abu ne ya taso, wanda har ya kawo mahaifiyarka garin nan, tana zubar da hawaye a kanka, kasan Zubar hawayen mahaifi matsala ne babba a
Hmm wai me kuke tunanin zai faru ne? Ya mukhtar zaiji idan har yaji wannan Albishir din na bazata ? shin zaima amince da wannan auren ko kuwa?
Mai zai faru idan har matarsa taji wannan danyen labarin?
Wai anya falmata zama ta soshi kuwa?
Mu tara domin ci gaba da sauraron wannan qayataccen littafin.

MATACCIYAR RAYUWA
CHAPTER 6
rayuwar da, don haka na yanke shawarar cetoka, domin tace gwara ta tsine maka gaba daya tasan wai duniya ta haifawa kai...”
. Ya daga kai cikin firgici yana kallon Malam Abbagana tare da cewa.
“Subhanallahi, meye ya yi zafi har haka, wallahi ko da bata kawo ni gurinka ba, zan yi duk abin da tace, nasan ba zai wuce akan maganar neman aure ba, ba ta taBa umartata da na nemi aure na'qiyi 'ba, sai dai idan auren ya kusa sai a samu matsala daga Bangaren wadanda nake nema, sai take ganin laifina ne amma don Allah a taimake ni a taya ni lallaBata malam”.
Ya girgiza kai cike da gamsuwa da bayanin Mukhtar din, sannan yace.
“Ai komai yazo Karshe, daga wannan karon burinta zai cika kai ma kuma nake fatan hakan ya zamo sanadin wanke duk wani laifi a gurinta Domin a yanzu za a daura maka aure da qanwarka Falmata na kammala shirin komai...”
, A karo na biyu ya sake daga kansa sai dai wannan karon firgicinsa yafi na dazun bayyana, yace
“Malam aure kuma?”
Malam Abbagana ya tsare shi da ido yana fadin, “k0 ba ka so ne? Ko kuma zargin da Mariya
ke maka na matarka ta mallakeka ya tabbata ke nan?”
Cikin rawar murya yace “Wallahi ba haka bane malam... am... am... am”.
Duk jikinsa ya kama rawa ya hada gumi kamar wanda ya hadiyi Kunama.
Malam ya yi dariya yace “amma kuma me? Kuma sakaci 'da addu’a sai an yi magana ku dinga kiran kunfi mu ilimi da komai, amman bakuda tsarin komai matanku su dinga juyaku, yanzu ba zai zama abin kunya ba ace babban’ mutum kamarka dake koyarwa wasu'tarbiyya mahaifiyarsa na kuka da shi ba? Ka tashi kajw naji an fara addu’ ar daurin aure, idan mun kammala zan nemeka mu wuce can gida tare". ‘
Haka ya mike kamae wanda kwai ya fashewa a ciki, sai ya keJin kamar an kwance wani babban qulli a cikin ransa. ya dinga jin zuciyarsa tana haske yana son yati farin ciki, amma wani tsoro da fargaba suna hanawa. Haka nan ya koma gefe yana sauraron addu'ar daurin auren har aka daura na Yakura da Zuhaida da Sakina gami da Zahra’u.. Yanajin an fara addu‘ar nashi gabansa . ya fara faduwa, sai yaji kamar ya kwasa da gudu yace ya fasa, amma rauyin malam bazai barshi ya iya aikata hakan ba mutumin da yake matsayin uba a gurinshi bazai iya kunyatashi cikin dubban jama,arnan ba shin ya zaiyi da fa,,,la yasan ko zai ko zai kwana yana mata bayani bazata taba yarda ba
Ya dafe kai yan fadin ya salam a cikin zuciyarshi daidai lokacin da aka shafa fatihar qarshe falmata ta zama matarshi fakat
Yana kallo anata raba goro da alewa mutane nata amsa suna addu,a da sanya Albarka shidai zaune yake yana kallonsu cikin wani irin yanayi da bazai iya fassarashi ba har malam ya qaraso gabanshi dasu bulama da sani abinda yafi bashi mamaki bai wuce ganin yayyensa da suke uba daya ba su auwa kabir harda muhammadu da saminu
Kai harda wasu abokan mahaifin nasa ma
Hakanan ya dinga yaqe ya isa suna gaggaisawa
Dasu,,,, babban wansa malam auwal ne yace barka yau dai munci goron auren qaninmu saurab suka fashe sa daria suna fadin lallai kam domin sunyi Alqawarin sun daina nema masa aure don sun neman masa aure yafi sau goma
Amman ana fasawa kullum da abinda zai bullo sabo yau dai Allah ya fatila Alqadarin fatila
Abin da ya qara bashi mamaki bai wuce ganin ‘yan uwanshi mata har da mahaifiyarsa a gidan ba ana ta sabgar biki, wato kowa dai yasan da maganar bikin, -shi da. Fatila ne kawai ba su sani ba ké nan? ' _
Ya hango mahaifiyarsa sai aiki ta keyi cike da farin ciki da nishadi, malam Abbagana ne yace masa, “Ka shiga ku gaisa, sannan ka wuce babban falon baki zan sanya a turo maka amaryar ku gaisa” . .
Ya wuce yana amsawa da, “Toh” . Tunda
suka shigo hankalin da. yawan matan ya yi kansa Hajja Basma ta bazama ta yi dakin Hajja Yakolo, can uwar daki tatarar da ita da gulma, tace mata. . «Fita kiga 'cutar da aka yi miki kina nan ' sankame a daki, Muntari ne ya shigo gaba d‘aya ya haske .-gidan nan kamar wani farin wata sha kallo dan daren goma-sha hud‘u”. ,
Ba ta ma kula da mutanen da suka cika dakin ba domin idanunta sun rufe tsabar gulma da hassada dake nuqurqusar zuciyarta, don ma dai duk ‘yan uwan Yakolon ne a d‘akin. '
Ita ma Hajja Yakolo babu ko tunani, ta bi ta suka nufi waje suka tsaya daga bakzin qofar sashinsu suna hangensa yana gaisawa da mutane fuskarsa kamar gonar auduga. Tabbas ya yi kyau.
mutum mai cike da kamala da kwarjini, kowace mace zata so ace ya zama surukinta.
Bayan ya gama gaggaisawa ya nufi inda aka ce ya je ya zauna, daman tuni Malam ya yiwa Hajja Iyami waya ya ce a tura Falmata can babban falon baki mijinta ya zasu gana.
Hajja Iyami da kanta ta nufi dakin Falmata inda yake cike da qawayenta irin su Yagana, Alabura da sauransu. Ita kam amaryar tana can kuryar gado ta tuge gwaggwaron da aka sanya mata ta nade kamar mara lafiya, ‘yanmata tun suna tsokanarta har suka koma tausayinta ganin yadda ta koma abar tausayi.
Hajja Iyami ta shiga da 'sallama, da sauri Falmata ta mike tana goge hawayen dake idonta tana fadin, “Lah! Hajja yanzu nake cewa bari na je na gaisa da su Anti Jamila”.
Ta taBe baki, “Ke dai kika sani kuma, ga mijinki can ya shigo yana babban falon baqi, kije ku gaisa, sannan kuma idan kinje ki nuna masa ba kya sonshi har ya gano ya sanar da Malam”. Tana kaiwa nan ta juya ta fice.
Falmata ta yi tagumi idonta ya kuma cikowa da kwalla, ji take yi kamar ta dora hannu aka ta fasa ihu ko taji dadi amma haka nan ta tashi sumi sumi ta dauko wata lafiyayyar lafayya ta fara nade
jikinta da ita, ‘yanmatan suka bita da kallo, Yagana ce ta daure ta yi magana. " '
“Gaskiya idan kika yi haka ba ki kyauta ba, . kwalliyar da akafi bukatar ango ya gani sama da kowa zaki rufe? Don' Allah ki cire laffayar ki dora gwaggwaron ki tafi haka”.
Ta zoBara baki gaba tana fadin, “Wallahi sai ki sanya na ciré lafayyan ma na maka zumbudeden gyale k0 hijabi, ai wanda kake so shi kake yiwa kwalliya, don' ka burge shi. Taso muje ki rakani ma don Allah”. '
. Yagana‘ ta riKe baki cike da zolaya, tana fadin “Rufa min asiri, wace ni shiga tsakanin
ma,’aurata na sani ko zai yi sirri da matarsa, ko ya
kika ce‘ Alabura?” .
Suka sheke da dariya gami da tafawa.
Ta kawo iya wuya don haka ba takuma ce musu ko qala ba ta fice da sauri suka .bita da dariya, Alabura tana fadin
“A.dai saki jiki har a samo mana baby”
Suka kuma kwashewa da dariyarsu, ita dai ba ta kula su ba ta wuce abinta.
Ta jima a bakin qofar falon tana tunanin ta yadda zata shiga, shin wane irin miji aka bata, fari ne ko baqi ne, Gabanta ya dinga faduwa, sai da tayi addu’a ta shafa sannan ta shiga
Da sallama. . _ . Kansa yana can gcfe ya amsa sallamar, ita kam kanta a durkushe ta shiga dakin ta sami guri ta zauna. . ,Ta kasa dago kai ta kalle shi, cikin sanyin nuryarta wadda dama haka take, ”sai kuma Karin kukan da ta sha jiya da daddare da ya Kara narkar da muryar tata ta koma kalar tausayi sosai, tace . “Ina wuni‘?” Muryarta ta ja hankalinsa matuka, ya waigo da sauri yana dubanta. ' Gabansa ya yanke ya fadi, zuciyarsa ta shiga wasu-wasi, bakinsa. 'yana rawa ya ambaci sunanta ' da wata irin rikitacciyar murya. .
“Falmata, daman kece mata‘ta?”
Ta daga kai da sauri ita ma domin'ko, a cikin mafarki ta ji wannan muryar sai ta bude idanuwanta, k0 da tayi sallama ma ya amsa mata
sai da tayi tunanin kamar ta san muryar, daurewa kawai tayi ta tsananta ba amma yanzu da taji ya ambaci sunanta ta tabbatarwa kanta wanda take zargin ne ya haye muhallin farin ciki da ya cikata, anya kuwa ba mafarki nakeyi ba‘? Ta ayyana hakan ,a ranta. Malam Muhammud mai darasu shi ne daman mijinta '? Shine Muntarin da ake ta fadi? Meya sanya ba,a taba ce mata shine ba Bnkinta yana rawa tqce
“Malam daman kaine Muntari? Kaibe dan gidan Inna Mar‘wa?“
Ya d‘aga mata kai, “Tabbas nine nine danta ashe kece matata falmata,, Kai har naji sanyi ‘ cikin raina wallahi, da ina tsoron wacecc aka had‘ani da ita auren da ban shirya ba, amma ina ganin kece naji sanyi da farin ciki sun mamaye dukkan illahin‘n jikina“. '
Ba tasan lokacin da bakinta ya kufce tace “Daman kana sona kai ma?"
Sai tayi saurin rufe fuskarta tatuna irin baram baramar ‘da tayi. ,
Yayi murmushi cike da jin dadi yace “Kina tunanin akwai mutumin da zai ganki yaji baya sonki ne Falmata?” ‘ Ta qara Boye fuska tsakanin cinyoyinta tana dariya, ta rasa inda zata sanya ranta taji dadi don farin ciki, duk ta dimauce ta ma rasa me ya dace ta yi, amma dai cikin ranta sai godiya take yiwa Allah da Ya nuna mata wannan rana mai tarin albarka mai kuma kundin tarihin da baya goguwa.
Ya dinga janta da hira kunya ta hanata sakin jiki da shi, har dai ya mike yace
“Bari naje guein su Abba kada su jini ’ shiru
idan anjima kafin mu wuce masaukinmu zan kuma dawowa mu yi hira, sai dai ina fatan ba za,a kuma yimin irin wannan kunyar tayanzuba,kinsanni fa mijinki ne yanzu k0?”
Ta daga kai alamar, “Eh”.
“Shi ke nan, sai na dawo”. Ya nufi qofar
‘ Ta daga kai tana kallonsa, wani irin nishadi 'da jin dadi suka durar mata. ta mike da sauri cike da doki ta nufi dakinta. '
Tana isa ta rungume Yagana tana dariya, tace, “Alhamdulillah, na godewa Allah da ya nuna min wannan rana Yagana”.
Cikin dariyar ita ma Yagana tace “Lallai wannan ango ya shigo da Yaseen a gidan nan, cikin ‘yan mintina qalilan har ‘ya same ki haka?”
Ta sake yin dariya mai nuna farin cikinta a sarari, tace “Wai kin san waye mijina kuwa Yagana? Malam ne fa?”
Da mamaki Yagana tace “Malam? Wanna ke nan, kina nufin Malam Bukar ne mijin naki?”
“Bafa shiba, malam mai darasu fa, ashe shi me dan gidan Inna Mariya, ashe shi ne Muntari? Su Muntari suke ce masa, kai Alhamdu lillah ashe Allah Ya .amshi addu’,ata nima zan yi auren farin ciki, auren tinqaho, auren kece raini, auren da kowacce mace taje fatan tayi irinsa? Ashe dai ni
ma zan more miji a rayuwata, wanda zai zamo abin alfaharina?”
Ita kanta Yaganar farin ciki ya cikata, ta rungume Falmata a j ikinta suna ta murna, Alabura ma ta cika da murna, domin ita ma tasan waye malam 'mai darasu. ' .
Sai ga amaryar ta ware laffaya ta maida gwaggwaro ta dora har da qara gyara fuska, tace da Yagana.
“Ku bikin na farin ciki ne, bari naje mu gaisa da ‘yan uwa wallahi”.
Suka dinga tsokanarta tana dariya ta fice, nan aka dinga hotuna da daukar bidiyo da ita, tayi 'kyau'kamar ka sureta ka gudu; ita da Zahra kam sunfi kowa murna,‘ sai kawa da komowa suke su Yakura kam ana cikin d’aki kamar za a dige don kuka
Abin da tayi din kuwa ya burge kowa, musamman mahaifiyarta da Hajja Kaltum, su sun yi zaton tsabar biyayya ce ta sanyata farin ciki! ba su san dawan 'garin ba, ba su san harda son angon nata na gaskiya ba tunda ta ganshi. .
Tunda yamma aka fara shirye-shiryen kai amare gidajcnsu. Falmata tana ta kiciniyar shiryawa rakiya, tunda ita ba a tsaida ranar tarewartaba. Hajja Yakolo kam kamar zata hadiyi zuciya ta mutu don takaici, su Yakura kam sai kuka ake yi
idanuwa sun yi luhu-luhu.
Sai ga Falmata an shiga wanka da ruwan turare, ta fito ta tsara kwalliya sai kamshi ta ke zabgawa kamar ita kanta ce turaren, aka kashe dauri gwanin sha’awa, Hajja Iyami ta dinga kallonta da sha’awa, diyar tata ta yi kyau matuka kamar ka saceta ka gudu.
Sai daime? Suna gab da tafiya kai amare don har ta shiga mota taji wayarta ta fara qara, abin da ya bata mamaki bai wuce ganin bakuwar lamba ba, ta yi kamar ta share amma dai sai ta daga taji k0 waye.
Daga sallamarsa ta game mai maganar duk jikinta ya yi wani irin sanyi, kamar an tsinke mata Iaka. Ta dan saci kallon Yagana da ta zuba mata idanu.
Cikin kwantar da murya yace, “Ina fatan baki cikin tawagar ‘yan kai amaryan nan da suke jeren gwano
Taji dumm!!! Ta dan dake tace “Har dani mana gamu har mub shiga mota
Ya sha kunu kamar tana gabansa, yace “To da iznin wa kika futa? Kin dai san nike da iko dake k0?"
Tayi yake, a ranta tana fadin, “Ikon Allah
Sai kace wanda ke wani son auren
Kaida ka samu komai a sanga ta fadi a ranta amman a fili sai tace,“Tuba nakeyi namanta ban tambayaba”.
Yace,“Aikuwa baki isaba ,saidai wani lokacin. Ki fito gani inajiranki a falon baqi”.
Gaba daya jikinm yayi sanyi, ranta ya Baci, yaddataci burin kai amarennan ace yayi mata bakin ciki? Amma gaskiya bai kyauta mata ba...
Maganarshi ta katse mata dogon tunaninta. “KO sai kinje ne?” ~
Da sauri tace “Lah Gani nan zuwa fa”.
Ta kashe wayar tana kumbura baki gaba. ta kalli Yagana.
“Kinji mutuminnan zaitakuramin wai yana falon baqi naje shikenan yanzu ba za,akai amare dani ba
Idonta ya ciko da kwalla don takaici.
Yagana tana son yin dariya, amma ta dake tana fadin, “Ai aikin lada zakuje kiyi, mEye na takaici kuma?” ‘
Wani abu ya kuma tsaya mata kamar ta mangare Yagana, kawai saita fice daga motar, Yagana ta shake da dariya har da tafa hannu‘ ta ‘ galla mata harara ta wundo tana fadin “Wallahi
zamu hadu sai kin sani, Allah”, Ta shiga falon ta kumbura ta yi fam! Kamar
zata fashe dakyar ta iya yin sallama, kanta yana qasa tace “Ina wuni?”
Ya tsare ta da ido, tunda ta shigo yake Karewa surarta kallo, sai yanzu ya gano ainihin kyawunta, da yake ba Hijab kuma babu abaya k0 laffaya a jikinta, gyale ne ta yafa.
Doguwa ce sambal! Sai dai tana da kugu ‘da shap, tana kuma da tarin dukiyar fulani, sune kedan sanya a ga cikar idonta, tana da doguwar fuska siririya mai d‘auke da dogon hanci da qaramin baki, amma IeBenta baqi ne irin na barebari. Idanuwanta manya ne masu kamar an diga musu zaiba don kyau, tana da yalwar gashin gira da saje, wanda hakan ke nuna yawan gashinta na kai. Sai dai baka ce amma irin bakin nan mai walqiya, tana da hujen hanci irin na bare-barin asali, ma’abociyar kananan kitso ce koba a yi maka bayani ba kasan babarbara ce Falmata.’
Ya dan yi yaKe yana fad‘in “Sai na ga kamar na batawa amaryar tawa rai k0?”
Ta dago da sauri tana qokarin boye fushinta ta hanyar Kakalo dariya, tace “Kai‘ba haka bane, ban yi dai zaton yanzu zaka shigo bane
Ya karkata kai yana qara Shakar Kamshin da take fitarwa sannan yace “Amma nace miki zanzo muyi sallama k0? K0 baki son mu fahimci juna ne Falmata?”
Ta narke masa cikin shagwaBa take fadin, “Ni fa ba haka ba ne, ka yi hakuri”.
. Ya yi dariya yacc, “Shi kenan gaya mini, samari nawa na kasa? Don dai budurwa mai kyau da ilimi irinki nasan ba zata rasa samari ba”.
Ta Boye kai cikin cinyarta tana dariya, sai taji wani irin farin ciki ya cikata.
Ya yi dariya ya kwanta jikin kujera, sai wani nishadi yake ji, zai iya cewa tunda yake a rayuwarsa bai taba shiga irin wannan yanayin ba, na tsananin shauki da soyayya ba.
Tunda safe ya ga Falmata kuma a matsayin matarsa ya gaza sukuni, gaba daya yaji sonta ya cika ransa, tabbas tun ranar da yaga yarinyar yaji ta burge shi, komai nata ya yi masa, amma saboda takunkumin da aka makalawa zuciyarsa sai ya ji ya kasa fassara komai a zuciyarsa game da ita, illa ya yarda kawai tana burge shi, sai dai daga safiyar da . ya ganta zuwa yanzu ya amincewa ransa yana son Falmata, duk da sau da 'dama idan ya ambaci so a ransa yakan ji gabansa na faduwa.
Ya daure ya tattaro nutsuwarsa yace, “Falmata ya kike mini rowar kanki ne‘? Don Allah ki dago fuskarki na kalla na more, kinga gobe da safe mu zamu wuce Kano, ga shi ni da ganinki sai
randa na dawo. Sai dai na dinga jin muryarki ta waya, ko da yake ai rowar lamba ma aka yi mini, sai gurin Abba na amsa”. Ta dan dago amma ta kasa hada ido da shi,
tace, “To ai ba ka tambaya bane shi yasa”.
Yace “haka ne, ba ni wayar taki na gani”.
Ta tashi ta mika masa ta dan durkusa da hannuwa biyu. Ya kurawa hannayenta ido wanda suka sha jan lalle, qamshinta ya cika shi, sai ya ji kamar ya janyota jikinsa ya rungume, amma dai ya dake ya amsa, ya fara bincikawa. Daya bayan daya ya dinga tambayar sunayen wadanda ke kan wayar yana goge wadanda bai gamsu da bayanin da ta yi ' masa ba. ‘ ' Sanda yazo kan Malam, Bukar ya ga ta sanya, my teacher B, ya kurawa sunan ido nan da ‘nan kamanninsa suka sauya zuwa matukar kishi,
amma ya dake yace “Falmata wakika taba so a rayuwarki? Wa kuma kika fara so?” Yadda ya tsareta da ido ya sanya gabanta ' bugawa, da zata iya, cewa zata yi ‘kai na fara so, kai kuma na taba so’, amma ba zata iya ba, don haka ta yi shirun tana wasa da yatsun hannunta. . Ya yi yake mai ciwo, yace “Da gaske kin taSa son teacher B k0?”
Ta daga kai da sauri don ta gano abin da yake nufi,amma ta kasa magana, ya kuma goge lambar malam Bukar yana fadin
“K0 shi kike so ya rasaki, a yanzu ni ya dace ki fara so, tun ranar da na fara jin muryarki na ji wani abu a raina, balle ranar dana fara ganin fuskarki, don haka na tabbatar na fishi sonki”.
Wani haushi ya tokare wuyanta, kuji don Allah wannan shi ne ta baya ta rago, ta ya ya zata yarda yana sonta, mai ya sanya bai furta yana sonta ba a wancan lokacin? Da ace an aurar da ita ga wani ba shi ba. fa? Shi bai san yadda Malam Bukar ke sonta ba, don dai ita Allah bai dora mata sonsa ba k0 dai-dai da kwayar zarra ba.
“Kin' yi shiru Falmata kin barni ina ta magana, koda yake an fara gaya mini halinki wai miskila ce ke k0?”
Ta girgiza kai da sauri tana fadin, “Bafa haka bane, wanda ya yi min bahaguwar fahimta kawai ke zaton haka”.
Ya yi dariya yace “Idan ba haka bane to ya ya ne? Ni ma ana~cewa miskili ne, amma na kasa yin miskilancin nawa a gabanki, ko don ina sonki ne? Kai wannan mutumin da bada kunya yake ita kam duk kunya ta cikata, domin bata saba jin
Hmm falmata da malam mai darasu sun samu abinda sukeso,,,,,,,,,
.
MATACCIYAR RAYUWA
CHAPTER 7
irin wannan kalaman daga bakin wani ba, don bata taba tsayawa da wani saurayi ba balle har ya dinga gaya mata irin wadannan kalaman.
Tana jiyo hayaniyar ‘yan kai amarya sun dawo, amma shi ba shi da niyyar tafiya, ya tsareta da surutu, duk sai ta ke jin kamar ba wannan dan uztaz din malam mai darasun ba, sai daya kula dare yaja sannan ya mike tsaye yana fadin
“Toni Falmata zan wuce sai yaushe kenan?” ,
Ta kara qasa da kanta cikin sanyin murya, tace, “Sai ranar da ka dawo ke nan, yaushe zaka dawo?”
Ya yi dariya, “Au kina son na dawo kusa kenan To kwantar da hankalinki, ina zuwa zan fara shirye-shiryen inda zaki zauna, don haka idan na _ dawo daje zan wuce, zoki amshi wayarki”.
Ta daga kai tana kallonsa yana tsaye, kirjinta ya tsananta bugawa, suffarsa da Alabura ta taBa suf‘fantawa ta fara dawo mata, ashe ita Alabura ba ta fassara shi dai-dai ba ma. Ta mike ta nufe shi ta mika hannuwanta biyu ya Kara matsowa kusa da ita, duk tsawonta ya shallaketa a tsawo, ta yi kamar ta ja da baya saboda yadda take jinsa kamar zai shige mata, amma ta gaza. Ta mika hannun kuma Yaqi bata wayar sai kallon‘ta kawai yakeyi.
Bata tabajin kunya irin ta yai ba tayi shirin komawa ta zauna taji ya riqe hannunta.
“Wai ba zamu yi sallama bane miji da mata nefa mu?" Cikin wata irin rikitacciyar murya yake maganar.
Sai ta kuma rudewa tayi qasa da kanta, sai kawai taji ya jata jikinsa tayi wata irin ajiyar zuciya sanda ta isa qirjinsa, sai dai kunya ta kuma rufe ta.
Yayi dan murmushi ya janyeta jin yadda jikinta ke rawa, ya sumbaci kuncinta sannan ya kamo hannunta ya sanya mata wayar tata cikin sanyin murya kamar ba daga bakinsa maganar take . fitowa ba, yace“i love you Falmata, ki kula da ‘kanki kafin na dawo, kinji k0?”
Da kyarta iya daga kai alamar, “toh. Tana kallonsa ta Kasan idonta ya fice daga falon, ta koma ta zauna jabar a kujera ta dafe kai tana maida numfashi dai-dai, ta lumshe idanuwa cike da tsananin farin ciki, ita kuwa wace mace ce ta kai ta sa’a a duniyar nan a yanzu?
Ta jima a nan sannan ta tashi ta nufi sashinsu kai tsaye dakinta ta wuce ta dauro alwala ta yi sallar isha’i da shafa’i da wutiri, sannan ta yi tilawar da ta saba duk dare da karatun alma,’asum dinta, sannan ta sanya kayan bacci ta haye gadonta.
Sai data kasa barci sbd dadi da farin ciki ta kamo filo ta rungume tanajin kamar muntari ne shin ashe daman haka soyayyah take
Kamshin turarebsa ya dinga mata yawo akai tabbas ta yarda da tayi sa,ar miji
A haka kamar bazai iya soyayyah ba sai maganar ya gana ta fado mata data tabayi wata rana
Ke falmata ki rabu da uztazan nan sunfi kowa iya soyayyah suda suke koyi da sunna soyayyah mai tsafta sukeyi ai inason auren irinsu tunda naga haka wani kawuna yakema antynmu soyayyah yake nuna mata kamar ya lasheta in gaya mikj yayansu biyar amman tare suke wanka Allah, saida na gano hakan
Ta lumshe idanu tamkar a sannan take kwance a qirjin nasa ranar kam tayi barci mai dadi sa nutsuwa
Shima abangarensa wani irin abu yakeji game da falmata wanda tunda yake bai tabajin hakan akan wata diya mace b a sai ita
Gaba daya yan kwanakinnan ya manta da wata fatila son falmata ya cika masa zuciya
Da safe kafin su wuce kanoma saida ya kirata a waya suka gaisa tare dayin hira sama sama sannan suka rabu akan idan ya isa kano zai sake kiranta
KANO TA DABO CI GARI
Tunda ya dira a biRNin Kano ya ji Qirjinsa ya . cika da Qunci, kai tsaye gidansa ya wuce, bayan ya dauko motarsa a gidansu inda suka fara yada zango, wanda ke unguwar Rijiyar Zaki, babban gida ne da ya. sha gini irin na zamani. Maigadi ya wangale masa babbar qofar ya shiga da motar tasa ya sami guri ya ajiye motar, sannan ya kashe ya nufi cikin gida. ' ' .
Hajiya Fatila manyan mata masu duniya, . tana zaune a kayataccen falonsu tana kallon tashoshin Turawa, tana sanye da wani dogon wando da riga mai fadi, tana son irin wannan shigar duk da bata fiye yi mata kyau ba, domin irin . gajerun matan nan ne masu kiba, fara tas kamar ka tsagata jini ya fito, amma kuma ba ta da shap balle hips"; bayanta kuma a shafe yake had‘e da mazaunanta, wannan ya sanya Kananan kaya ba sa mata kyau,-domin suna fito mata da ainihin surarta.
‘Yar gayu ceta karshen zamani, don haka kullum zaka tarar da ita fes-fes ko da daga bacci kuma ta tashi. Tsananin kissa da son da take yiwa mijinta ke sanya ba ya ganin laifinta, don idan ta ganshi kamar zata yi masa sujjada don biyayya, komai yace bata qetarewa, amma kuma yana
bala’in shakkarta, bai isa ya yi maganar wata mace a gabanta ba koda kuwa mahaitiyarsa ce saboda yadda take kishinsa ta neme shi ta kuma samu.
Tana Jin shigowarsa ta mike da sauri-sauri, gudu-gudu ta nufe shi, ya ajiye jakarsa ta matafiya (brief case) ya bude hannayensa ta shige da sauri har da ajiyar zuciya, ta ce
‘ “Hubby i miss you, kamar na yi tsuntsuwa na Bika don dai nasan taro ne na ustazai irinku”. ‘ Ya yi dariya cike da farin ciki domin idan yana gabanta mantawa yake da komai. Ya ce, “Nima sai da naji kamar na dawo na dauke ki, musamman da aka zubo mini abinci na ji ba irin naki ba neba Wani irin sanyin dadi ya cikata, ta yi wata irin wawuyar dariya, tana fadin
“Bari muje ka watsa ruwa ko kaji dadin jikinka ai kun sha hanya”.
Ta dauki jakar suka wucé sashinsa tana rungume a kirjinsa, ta raka shi har bandakin sannan ta kullo shi ta dawo.
Kai tsaye gurin jakarsa ta wuce ta zugéta ta fara binciken da ta saba, amma ba ta ga wani abu ba, don haka tamaida kowane kaya mazauninsa. Ta yi kamar ta dauko wayarsa ta fara bincika amma
sai taga gwara ta fara zuwa ta kammala zuzzuba
abin da zata zuba cikin abincinsa da ruwan lemonsa.
Tana fita kuwa wayar ta kama kara yana daga bandakin gabansa ya dinga faduwa, don yasan kiran Falmata ne don ya sanya mata kiranta na daban, don haka ya hanzarta ya fito lokacin sau uku ta kira. Ya dauki wayar da sauri tare da sauke ajiyar zuciya, ya duba ga sako ya shigo kamar uku.
malam ina fatan kun isa gida lafiya don yanzu inna tayi kirana taje kunje gida ina kirar wayar taka inajin baka kusa
MATARKA FALMATA
Da 'sauri' ya . fara gage saqon gabansa yana fad‘uwa, sam ya manta baiyi hiding din lambarta ba sai sanda yaso zai kirata da kansa. Yana yin hidding din kuwa Fatila ta shigo babu k0 sallama.
Jikinsa yana rawa ya wayance, “Ina kika shiga wayata tana ta qara?” Da mamaki akan ’fuskarta tace, “Haba nifa nace saurin naka ya yi yawa, wayeya kiraka ne?” . Yana qokarin nemo dauriya yace, “Wani abokin kasuwanci nane Mr. Josep”. Ta zauna a gefen gado tana kallonsa bata kawo komai a ranta ba. “A binci yana jiranka, k0 sai kA dawo daga masallaci don naji kamar kiran. sallar magriba
Ko Da sauri yace, “Bari dai na dawo din".
Ya kama sanya kayansa da sauri ya fice yana riqe da wayoyinsa a hannu.
Bayan ya dawo daga masallaci shaf ya manta bai kira Falmata kamar yadda ya qudirta ba, sai da yaga sabuwar lamba ta shigo sanda suna tsaka da cin abinci, sannan ya tuna. Gaba d‘aya ya nude, yana son ya datse kiran yana kuma tsoron kada ta gano shi, don haka ya kara wayar a kunnensa, gami da yin sallama. Abinda ya yi niyyar yi shi ne da zarar ya fara jiyo muryarta zai' fara cewa, “Hello... hello bana jinka, waye ne?” Amma sai ya ji ba muryar mace bace muryar namiji ce sai daga baya ya gano Gwani Muhammad ne, sai ya saki jiki suka kama hira sosai. Sai dai sanda ya soko masa maganar yaushe Falmata zata tare, sai ya yi duru duru yam fadin
“Zan sanar da kai idan 'lokaci ya yi, wasu abubuwa ne suka sha min kai”.
Bata fahimci abin da yake nufi ba don haka ko a jikinta, har suka kammala hirar ya kashe wayar.
Ta tsare shi da ido bayan ya gama, tana fadin“Naji kana kiran Gwani Muhammad, waye shi kuma?”
Yayi dariya yana qoqarin kai loma bakinsa yace shugaban wata makarantane a maiduguri ta islamiyyah wadanda sukazo kano musabaqa kwanaki
Ta girgiza kai cike da gamsuwa ta haushi da hira saidai shi hankalinsa gaba daya yana wajen falmata da akwai yaddah zaiyi da yayi kiranta
A bangaren falmata kuw taji haushi matuqa somin ta tabbata daga lokacin data kirashi zuwa yanzu yaga kiranta da kuma saqonta amman ya kasa ko biyota ko yana gaban matar tasa ne da akace ta mallake shi!?
Sai yanzu ta tuna da labarin matar tashi
Wannan page din half yayi damage kuyi haquri
Gaba daya wunin ranar ta kasa sakewa, ranta a jagule yake kowa ya kalleta yasan tana cikin Bacin rai matuka, don haka kusan a daki ma ta wuni.
Ta yi shirin kwanciya da wuri yau don k0 abinci ta gaza ci, ta ji wayarta tana kara Daga sautin kid‘an ta gane mai kimn, wani irin farin ciki ya mamayeta amma saita dake taki dauka tayi alkawarin saita raman itama don haka haryakira wayar kusan sau biyar bata d‘auka ba
Shi kam daga Bangarensa duk sai ya damu, tabbas yasan fushi tayi,toshi ya zaiyidaransa ne Dole ya hakura ya tura mata sakon ban hakuri, aransa yana mamakin miskilanci irin nata. Haka ya shiga gidan duk ransa a jagule kamar ya fasakuka.
Yana shiga Fatila ta zuba masa idanu cike da kulawa take fadin, “Hubby na kamar kana da matsalafa tundaka iso nakula dabakacikin kazar kazar dinka kamar can baya”.
Ya yi yake, yana fadin, “Kin fara halin naki k0? Sai kace ‘yar jarida, kawai ina ga gajiyar hanya ce, amma ni babu abin dake damuna”.
Ita ma tayi yaken, amma cikin ranta ba ta yarda ba, yadda yake kaffa-kaffa da wayarsa tunda ya dawo ma ya sanyata shakku, balIe da suka zauna
hira sai ta dinga kulawa lokuta da dama yakan yi shiru yana tunani, sai tayi magana sannan zai wayance.
A Bangaren Falmata kuwa, tana jin kiranshi har ya yi ya gama, tana son ta nuna masa irin ciwon da taji ita ma, domin sai‘da ta zubda hawaye don tana matuqar girmama kanta da datajarta ta ya mace, batason duk wani abu dazaiyi kamada wulakanci k0 cin fuska Jin shigowar sakonsa ya sanya ta dauko da sauri ta fara karantawa, ga abin da ya ce
Haba amaryata fushi haka da sauri kin kira bana kusa amman ayi haquri ki sani dukkan wani motsi kina raina a gobe zan fara nemar mana inda ya dace mu zauna domin muji sadin soyayyarmu babu sanya ido saida safe MMMD
Sai taji ranta ya yi dan sanyi, sannan ta lalubo ma,’anar kalmar da ya qare da ita, wato MMMD, ‘ta yi tsam tana tunani, karshe ta yi hasashen yana nufin Mijinki Muhammad Mukhtar mai Darasu, ba shakka abin da yake nufi kenan. sai ta tsinci kanta da jin haushin kanta da taqi daga wayarsa k0 sautin muryarsa taji.
Yacc, “Sai da safe”. Wato ba zai iya kiranta ba kada matarshi ta kama shi? Tabbas ta yarda yana
matukar tsoron matarsa, kamar yadda ake cewa.
************************
Washcgari tunda sassafe ya nufi daya daga, cikin gidajensa, wadanda yake gini na nan Janbulo, anyi sa’a daman an kusakammala gininsa, don haka tunda asuba dama yaturawa ma’,aikatan sakon sufito,acanma yataddasu,sukadinga gaishe shi da girmamawa.
Ya amsa kamar yadda ya saba, sannan ya basu umarnin yana son a kammala ginin nan cikin sati biyu, duk abin da ake bukata sun sanar da shi a ' shigo da shi yau.
Shugabansu ya' lissafa komai yana rubutawa a takarda, sai da ya kammala rubuta komai, sannan ya wuce kamfanoni komai za su shigo musu da shi.
Daga nan ofis dinsa ya wuce na School of arabic studies wato Legal, domin shi ne mataimakin shugaban makarantar. Sai da ya nutsu 'sannan ya fara neman layin Falmata. Daman taba zaune ta kurawa wayar ido tana ta kallon agogo har wajen sha biyu bai kirata ba, tana tunanin k0 har lokacin yana gida ne.
Can kuwa sai ga kiransa, ta dauki wayar da sauri gami da ajiyar zuciya. Cikin sanyin muryarta ta yi masa sallama, ya lumshe ido tare da kwanciya
Cikin kujera sabodn yadda zakin muryar ta ya ratsashi, cikin kwantar da murya yace.
“Na yi zaton k0 har yanzu baki huce ba, Fatimatul Zahra, ashe haka kike da miskilanci, kin sake yin damarar rigima?”
Ta yi dariya kasa-kasa cike da jin dadi, tacw Kayi haquri, ban ji...”
Yace “A‘a, kada ki mini karya, ke malama cefa ke dai kawai kinramako? Ina fatan hakanya sanya zuciyarki ta huce” .
Ta yi ‘yar dariya, “Mutumin nan yana burgeta, akwai shi da iya kalamai da saurin karantar mutum. Ya katse mata tunaninta.
“To meye labari? Jiya kin yi mafarkina kuwa?”
Dariya kawai ta keyi, kunya ta hanata cewa komai. Shi kuma dariyar tata ke qara kashe masa dukkan ilahirin sassan jikinsa, domin ji yake kamar tana busa masa sarewa.
Sun jima suna hira a cikin hirar tasu ne yake
fada mata abin da ke ransa. “Fatimatul Zahra ina sonki fahimci wani abu, Fatila matata tanada tsananin kishi da rigima, don haka na yanke shawarar bin komai a sannu domin kin san yadda aka yi auran nan. to har zuwa
Yanzu ban sanar da ita ba, nafison sai komai ya
dai-daita tukunna, don haka idan ina gida ba zan dinga kiranki ba, kema ina fatan zaki kiyaye lokuttan da kika kula ina gida, k0 wani abu ne ya .taso gwara ki mini message zan gani, kinji k0?”
Ta yi shiru cike da takaici, gaba daya farin cikin da take ciki ya gushe wacce irin mace ce da shi haka da yake shakkarta?
Jin ta yi shiru ya sanya yace “Yaya na ji kinyishiru?Komaganar batayimikidadib
ane? Bana son nayi miki Karya ne, nafison ki gane k0 waye ni Fatimatul Zahra”.
Cikin kwantar da murya tace, '“Lah babu komai fa, duk sanda ka kirawo dai shi kenan, ' amma Abba yace na tambaye ka k0 wai ka sanya ranar tariyar, domin ya sanar da masu rakoni din. ”
Gabansa ya dan buga, amma ya dake, yace, “Kada ki damn, idan na kammala shiri zan sanar da shi, amma fa kafin lokacin dole zan shigo na ganki, don kina ta mini fatalwa a raina”
Ta yi dariya, a ranta tana fadin, kamar da gaske. Haka nan ya dinga janta da hira har ta saki
jikinta dai.
Hajiya Fatila kam duk ta tsargu da yadda yake wani dari-dari da wayarshi, duk da ta bincike wayar gaba daya ba ta ga wani abu da ya yi kama da na mace ba, domin a number falmata Malam Jafar 2 ya sanya, sunan wani amininsa, duk da yayi
Hidden din lambar sai sanda zai buga mata yake
cirewa, don kada ta yi gangancin kiransa ma suna
Tare, wannan ya sanya bata dago ba, da ace wani
sabon sunan ya sanya ko na namiji ne sai ta kira taji wanda zai dauka, sannan hankalinta yake kwanciya.
Rashin kwanciyar hankalin nata ya sanya ta kira wata kawarta Karima, wacce suke cewa iyana
Diyana irin tsinannun kawayen nan ne wadanda babu Allah a gabansu, ba za a ce itace ta koyawa Fatila bin bokaye ba, domin ita ma kusan a nono tasha, sai dai ta taka muhimmiyar rawa
wajen kara dulmiyar da ita.
Hamshakiya Hajiya Diyana tana zaune akan kujera tana kallon tasoshin Turawa, kiran qawarta
ya shigo a wayarta da hamzari ta dauka tana dariya, Babu ko sallama ta hau zance
“Hajiyata ya ya aka yibe? Na manta shaf ban kiraki ba, tun bayan dawowar oga, wai na dan
barki ne ku sha kola, kin more ne?"
Fatila taja tsaki tana fadin, “Ki kyale ni da
shan kola din nan, ki shirya gobe zamu je gurin Burbushe domin na kula akwai wani abu a zuciyar Mukhtar da yake boyc mini. Ina tsoron kada
maganar mahaifiyarsa' ta tabbata, kin san , maganarmu ta karshe ta rantse mini, wai ko ina tsafi da kan jaki sai d‘anta ya yi aure. To ban sani ba ko aiki ta farayi akansaba. Jikina yana bani wani abu yana' shirin faruwa, gwara muje gurin Burbushe mai gani har hanji ya sanar dabi abin dake shirin faruwa”.
Diyana tace “Kin yi gaskiya tawan, ai ba na son abu da sanya, ba irin wannan sanyar ce ta
Kwari Helin ba? tana kallo yanzu Wata ta aure mata miji, wai kuma har da haihuwa, mtssss!” Taja tsaki, “Idan ni ce da tuni na shaketa ai ta tafi barzahu.. ”
“Ki daina tunanin idan kece ma, domin ni ba zan yarda ta shigo ba balle har lissafina ya qaeu bama, shi da mace sai dai a kabari, don ko na mutu ya yi karya ya kalli wata da sunan so, ni kad‘ai ce abar son Mukhtar”.
Diyana ta fashe da dariya; “Ina son irin haka, shi yasa kullum nake sonki wallahi qawalli, qarfe nawa za mu shiga gurin nasa goben?”
“Ai da safe dole zamu shiga, don kada mu tadda layi k0?”
Da wannan suka yi sallama.
Shi kam gogan aikin gida yake bilhakki‘ don haka ko da ya tashi yau ma da sassafe ya fice
hakan kuwa ya yi mata dai-dai, don haka ta zari mota sai gidan Diyana suka nufi gurin Boka Burbushe.
Da wani ne wanda bai saba irin Batansu ba da zaiji tsoron shiga surkukin dajin da suka shiga, amma su ko a jikinsu, sun saba. Haka nan suka dage zannuwansu suka dinga tsallake bishiyoyin Kaya da ciyayi suka kutsa surkukin dajin. Can cikin daji cikin wata bukka mai kama da ta aljanu yake zaune, ruwa da iska ba sa sauya masa gurin zama.
Suka shiga da ihu kamar yadda ka’ idar gurin nasa ta ke suka sami guri suka tsugunna, jikinsu yana kyarma kamar sun ga wani mayunwacin zaki. Diyana ce ta so yin magana, amma ya dakatar da ita yana dariya mai ban tsoro, muninsa ya sake fitowa domin Katone mai Kira irin ta Samudawa da qaton kai da ciki, ga shi bakikkirin amma komai nasa kato ne. '
Kana ga hancinsa da ya kusa mamaye fuskar tasa, zuwa idanunsa da kamar za su zazzago bare bakinsa mai kama da kofar gari. Bai taba wanka ba, domin yana cikin alkawarinsa da aljanun da suke taimakonsa akan karyar tasa, don haka kullum idan ka shiga bukkar tasa zaka ji kamar an kashe mushe don wari, balle gashinsa baya aski.....

MATACCIYAR RAYUWA

BOOK1 THEND QARSHE

Ta mike ,sai takejin kamar faduwa zatayi saboda azabar ciwon data keji.

Saida gari yayi shaar sannan ya tashi daga kan sallayar ya nufi gadon, saidai daya daga bargon sai yaga a yadda ya barta haka taje Da sauri yace “Subhanallahi, Fatima ba kiyi sallah ba kenan?”
Fuskarta tana Boye cikin filo, muryarta da alamun kuka, ta ce, “bazan iya tashi bane
Ya daga kai da sauri yana fadin “Subhanallahi, yi hakuri ina sauri kada jam’i ya wuce ni, bari ki gani”.
Saiya nufi bandaki da sauri yayi sa'a heater din bandakin tana aiki,don haka da wuri ya hada mata ruwan wanka cikin baho ya koma dakin.
Cak! Ya dauke ta kamar wata ‘yar jaririya, kunya ta sanya ta kasa bude idanunta. Yau dai Malam ya gama tsiya, domin batun kunya ta qare, shi neya sille ‘yar amaryar tasa, wani farin ciki yana Kara cika masa zuciya, k0 yaqi k0 yaso Falmata ta banbanta da sauran mata K0 kusa ba zai iya ajiyesu aji daya da Fatila ba domin daga kirar jiki har ta baiwa ta fita. Bai taba samun kansa cikin halin daya samu a daren jiya ba don ma dai yana tausayin Falmatan ganin ta daure, amma bai kyaleta don ya gamsu Tabbas yasan
kyautar Allah ce kawai a gare shi Falmata.
Sai da ya dawo da ita d‘aki sannan ya fice yana fadin Ki shirya kafin na gama had‘o miki abin da zakici”. . .
Ita dai ta kasa k0 iya daga kanta balle ta kalle shi, domin tsananin kunyarsa ta keji, to daman ya ya lafiyar Kura balle ta yi hauka?
Ba wani abu mai nauyi ya shirya musu ba, wainar kwai ce da shayi da biredi, amma duk da haka ita kam mamaki takeyi yadda akayi duk ya iya komai. Mutum mai daraja kamarsa bai cancanci ya dinga wannan aikin ba-a ganinta. Sanda ya kai abincin a gabanta kasa k0 da loma d‘aya ta yi, ya yi dariya yana fadin'.
“Fatima nayi zaton 'kunyar raguwa zata yi, tunda yanzu mun zama daya. Amma sai ta kuma karuwa, don Allah ki rage kunyar nan kada ki dinga cutar da nifa”.
Ta kasa dai motsawa, sai da ta ga‘ya mike yana fadin “Bari dai na baki a bakinki”. Sannan ta fara matsowa da sauri ya dinga yi mata dariya yana tsokanarta. .
Gaba daya kuma hankalinta ya yi 'gida tana jin nauyin yadda zata iya hada ido da Anti, Allah ma Ya taimaketa ba a gidansu ya daukota ba, da abin kunyar sai yafi haka. Shi da kansa godiya
yake yiwa Allah da Ya sanya daga gidan Bulama ya daukota, domin da daga gidan sune bai isa ya kusanceta ba, dole ya maidata a daren nan koda kuwa abin da yakeji din zai kashe Shi domin zai ji kunyar idon Abba ace ya kwana gida daya da Falmata bata tare a gidansa ba.
Amma tsananin kunya ya sanya ta kasa gaya masa amman tsananin kunya ya sanya ta kasa gaya masa abinda ke ranta yace mata, “Kinga ki kwantar da hankalinki, Yaya Bulama tun jiya na sanar -da shi . kina gurina, kuma a nan zamu kwana. Yanzu ma mun yi waya da shi yanzu Antinki zata zo, don ba zan maidake baki gama jinya ba, dole sai kin warke sumul, babu wanda yasan muna tare bayan su”.
Ta daga kai da sauri cike da fargaba, suna hada ido ta yi saurin maida kanta tace, “Gwara dai mu tafi gidan don Allah malam...”
Ya yi dariya, “Yarinya kuma ai sai kiyi, sai kin warke zan maida ke gida, gwara ma ki saki ranki, kuma ki daina ce min malam din nan fa tunda ai ni ba malaminki bane Gwani Ahmad ne malaminki k0? Ni sai dai kice min DL k0?”
Dariya, da kunya suka kamata, ta Boye kanta cikin filo. Karae wayarsa ce ta katse musu hirar ya daga da sauri yana fadin “Kin karaso ne?”.
Shi ne ya je ya bude babbar qofar Anti Shafa ta shigo da motarta ta sami guri ta yi fakin, sannan suka shiga tare, shi kam k0 a jikinsa, namiji kc nan duk halinsu daya. Ita ce ma ta dan dinga jin nauyinsa.
Falmata kuwa na jin sallamarta ta janyo bargo ta kudundune kanta, don ba zata iya hada ido da Antin tata ba. Anti ta shiga daga ciki ta zauna gefen gado tana murmushi ganin ta kudundune har kanta, k0 iska ba ta Shaka.
Malam Mukhtar kam tsayuwa ya yi daga bakin kofa ya harde hannaye a kirji yana fadin
“Kin ganta nan, ni ban taba ganin mace mai kunyarta ba, haka kawai ta sanya mai jego fitowa ba ta shirya ba” .
Anti Shafa ta yi dariya tana fadin “Malam ai kasan qanwar tawa special ce, dole tayi kunya k0?”
Yace “Ai shi ke nan, bari na baku guri k0 ta gaya miki abunda ke damunta, tunda ni nayinayi taKi magana”.
Sai ya juya ya fice ransa fcs! Kamar an yi masa albishir da gidan aljanna.
Anti Shafa ta yi dariya tana fadin, “To ai sai ki bude fuskarki, wanda kike jin kunyar ya fice”.
Maimakon ta bude sai ta kuma
Bai jira jin amsarta ba, ya fice da saurinsa.
Anti Shafa tace “Kinga ki gaya mini sauri nake yi, na baro babyna fa a gida”.
Ta mike da sauri tana fadin, “Allah Sarki Shahid boy dina, dama kin taho da shi”.
Ta marairaice murya tana kwantar da kai, “Ni dai' Anti ki ce kawai dani za ki tafi don Allah, babu fa abin da ke mini ciwo sai jikina fa”.
Ta mike, “Shi kenan haka ake so ai, nasan malam mai ilimi ne daman, ba zai miki yadda za ki ji ciwo ba. Kada maki sanya rai za ki bini, domin sun gama magana da yayanki sai gata ma zai maida ke can gidan...”
Ta waro ido waje “Gata Anti? Don Allah ki tadi dani, wallahi...” Sai ta yi narai-narai idonta ya ciko da kwallah, don ba zata iya fadin abin da ta keson fadin ba.
Anti Shafa ta koma ta zauna ta dafa kafadarta,tace “Falmata ki nutsu ki nemo wa kanki soyayya a gurin mijinki, kin san bake kadai bace, kina da kishiya, mutumin da ya tsallake matarsa wacce ake ta rade raden bata da imani, k0 kallon mace bai isa yayi ba, har yazo ya kusance ki ai kin san kin karya alkadarinta, don haka ya rage naki ki kuma nemo gurin zama daram a cikin zuciyarshi, ki kwantar da hankalinki baBu wanda yasan kuna tare, kuma bazan gayawa kowa ba, ina
sane na baki abin da zaki qara rikita shi, domin mu tabbatar mun karya alkadarin Fatila da qaryarta, kin san gidan Anti Kubra yayarsa ta sauka, ta sanar dani komai, ki yi hakuri har zuwa gatan kin ji k0?”
Jikinta yayi sanyi ta daga kai alamar toh kawai, taci gaba da magana bayan ta dauko wani kulli daga cikin jakarta.
“Ga wannan ki dinga sha da madara, wannan kuma a ruwan zafi za ki dinga sanyawa kina zama, zai rage miki radadi ki daure ki samo mana boy don Allah, damin mu 'karya camin din Fatila”.
Kunyar tata ta 'dawo ta fada gadon ta kudundune tana dariya, Anti Shafa ta nufi Kofa tana cewa, “Shi kenan, sai gatan. Ki kula da kanki sosai, ki kuma bai wa mijinki hadin kai”.
Har ta ficc bata iya dago kanta ba tana dariya dai, amma maganganun Antin nata sun yi tasiri a ranta, sai taji dama ta tambaye ta wace ce Fatilan da yadda take, domin tun sanda taji kadan daga halinta a bakin surukarta ta tsoronta, wato don ta tabbata ke nan.
:::::::::::::;;;;;;;;;;;;::::
Cikin kwanakin nan da suka yi ta more
soyayyar mijinta, ita kuma ta bashi hadin kai matuka, tabbas Mukhtar mutum ne mai tsananin iya gwadawa mace soyayya, sai dai yana da buqata da yawa, don haka sai ya zame .mata kamar cingam. Tun tana yakice shi tana tsoro har ta saki jiki.
Sai da suka yi kwanaki biyar sannan ya fara shirin kai ta, shi ma din ba don ya so ba, sai don ya koma gida ya fara shirye shiryen tarewarta, kuma ba ya son a gane suna tare.
Sanda ya fara tattara kayan da ya-sissiyo mata cikin wata akwati, sai taji duk hankalinta ya tashi, tana zaune tsakiyar gado ta yi tagumi tana kallonsa. Wani irin sonsa yana kara shigarta, Malam Muntari mutum ne mai kwarjini da cikar kamala, dole ya sacc zuciyar kowa, dogo ne sosai, yana da kiba, amma ba sosai ba.
Yafi kama da yanayin Fulani, wato kamannin mahaifiyarsa, don haka ya kasance fari tas, mai dogon hanci. Gcmunsa kamu-daya ne da saje abin da ke burge ta ba a yin awa biyu sai taje gemun d‘an kuwa da madubi daga aljihunsa ya kama gcmun ya taje, yadda gemun ke shan gyara dole ya yi sheki da sulBi, gwanin sha’awa, ita kam bata taBa ganin mutumin da gemu ya yi masa kyau kamar Mukhtari ba.
Har ya gama shirya kayan sannan ya juyo ya
kalleta yaba murmushi ya nufeta ya hau gadon ya janye hannayenta yana dariya, da fadin
“Ya dace fa mu tashi muyi tsere k0?”
. Ta kalle shi da sauri, “Tsere kuma mal...” Sai ta yi shiru ganin irin kallon da yakeYi mata, sai ta fashe da dariya, “To yaya”.
“Kinga tashi na maida ke gida, nima zan dinga ce miki Malama k0 Anti shike nan mun yi duro k0?” ' .
Ta Iangwabe kai, “Ka yi hakuri na daina”.
Ya mike yana daukar jakar, “Taso mu tafi,
ina son na shiga cikin gari kafin na wuce gobe amma dai ina son na rage wannan tunanin, Mukhtan' naki ne, mijinki nefa, ina komawa zan sanya a yi fenti nan da kwanaki hudu za ki tare insha Allahu”.
Haka nan ta mike jikinta sanyi kalau, sai take jin kamar kada ta bar gidan, dama za a biyota da kayan jeranta acetayi zamanta anan.
A mota ma shi ne ke kokarin yin magana, to daman ya ya lafiyar Kura bare tayi hauka, daman ba ma,’abociya maganar bace, balle a yanzu da take cike da alhinin rabuwa da masoyinta.
Bai shiga gidan Yaya Bulama ba ya ajiyeta yace zaije ya dawo. Haka nan ta shiga gidan, jikinta duk ya yi
Sanyi. Anti Shafa tana falo a zaune ta jiyo sallamarta, ta mike da gudu ta tarota tana fadin, “0yoyo maman baby, kin dawo‘?"
Ta rufe fuska tana dariya, tace, “Ni fa ba, haka bane don Allah Anti ki daina fada, babu komai fa”.
Anti Shafa ta yi da'riya, ‘Ai na sani shiga to maza ki hada kayanki, Abba sai fada yakeyi wai kin zo kin yi zamanki ba tare da an nemi izinin mijinki ba, ban gaya masa kuna tare da shi ba. Maza shirya direba ya kai ki a qarasa soyewar a gidan Abban". '
Ta falla daki da gudu cike da kunya tana dariya. Ba ta‘so tafiya ba don tana jin dadin zama da Shafa'atu wadda ta maye mata gurbin ‘yan uwa mata, tunda su ‘yan uwan nata ba sa qaunarta, don haka duk wata damuwarta daga Anti Shafan sai yagana sune abokan shawararta.
Har ta isa gida tana cike da alhini na rabuwa da masoyinta, tana tafe a hanya ta tura masa da sakon ta koma gida idan ya tashi a can 'zai-same ta.
Tunda ta shiga mahaifiyarta ta kula tana cikin damuwa, amma da yake tasan halin abarta ba tace mata komai ba, bayan amsa gaisuwarta. Ta nufi dakinta tana shiga ta jiyo hayaniyar Yagana a falon. Tayi dariya tana kokarin cire kayanta, ta
shiga ta watsa ruwa.
Yagana ta fada dakin da sauri ta tsaya tana yi mata wani kallo taba dariya, tana fadin, “Kai amaryar malam kin ga yadda kika koma kuwa? Kin yi wani bulbul, lallai gidan Anti Shafa ya amshe ki k0 dai can zamu maida ke ne? Amma fa k0 malam ba zai ganki ba”.
Ta galla mata harara tana wucewa cikin bandakin, Yagana ta yi dariya tana fadin, “Bari na duba kayan na ga irin tsarabar da aka kawo mana kawas” .
Kusan tare suka wuni, tunda suka shiga kicin, Falmata ta fara shirya girlki, Yagana ta fara tsokanarta tana 'dariya, “Lallai' kice malam yana garin, shi ya sanya na ga kin yi wani sharrr daje, iye amaryar ba?”
'Ita dai dariya kawai take yi. Sai da aka yi kiran sallar magruba, sannan Yagana ta koma gidansu akan zata dawo su gaisa da malam din.
Shi kam Dr. Mukhtar tun gab da magriba ya iso gidan, sai dai ya tsaya a masallaci ya yi salla, tukunna suka wuce falon Abba tare, aka dinga kawo abinci kala-kala, shi kam bai saki ciki ya ci ba don yasan gimbiyar tasa tana shirya masa dabge. sai da ya yi sallar isha’i sannan ya sami shiga gurinta.
Sanda suka had‘u kamar ta yi tsalle ta rungume shi don murna, kullum kara burgeta yake yi, saboda ya iya tsara kwalliya, wata dakakkiyar shadda ce a jikinsa riga da wando, sai ya sanya irin rigar nan ta sarakai a ciki, sannan ya dora malummalum akai, kansa ya sha hula zanna-bular da ta zauna das a kan nashi. Gcmun nan nasa sai walkiya yakeyi, ya sha mai da gyara, fuskarsa ma’,abociyar haske da annuri, sai haske ta keyi. Ita ma taci kwalliya cikin sauka dinkin atamfa super, sai dai rigar ba ta cika tsayi ba, yau ma dai an yi sa,’a dan karamin gyal‘e ne ta yafa, koda yake ai ta fara rage jin kunyar tasa. Kamshinta gaba daya ya cika dakin, kai tsaye gurinta ya nufa sanda ta Shigo, sai ta yi sauri ta zauna ta durkusa don ta gano abin da yake shirin yi, cikin sanyayyar muryarta tace.
“Ina wuni?”
Ya zauna yana dariya, “Lafiya lau, wato nan gidan Abba ne ba za a dan gwada mini love din ba k0?” Ta yi dariya tana boye fuskarta, domin dai ya riga ya gama ganota. Sun sha hirarsu ta soyayya, rigima ba ta tashi ba sai da ya tashi yin sallama, ta yi narai-narai da ido sai ga kwallah, wani irin tausayinta mai tsanani ya kama shi. Tabbas ya riga ya gano irin dumbin son da take masa tuntuni
cikin kwayar idonta, don haka tsam ya tashi ya nufe ta. Yayi mata irin rikon da yake mata kamar: ‘yar mage cikin kunnenta yake fadin
“Meye na kukan? Inace nan da sati guda insha Allah kina gidana? Ki kwantar da hankalinki kinjiko Fatina? Ko kinaso nima nayikukanne?”
Da saurita girgizakai alamar a’a, wannan shagwaBar ke qara ruda shi, zuciyarsa ta dinga kissima masa abubuwa da dama, can cikin kwanyarsa ya jiyo ta tana fadin
“Ammadai basau daya zaka dingakirana ba k0?”
Yayi dariya don ya gano kumallon matan ne ya motsa, amma irin kishinta m‘a yana burge shi, yace, “Kiyi haquri zan dinga kimnki duk sanda na ‘ sami lokaci, na miki alkawarin na daina kiranki sau daya, kedai ki kwantar da hankalinki kinj i k0?”
Ta kuma daga masa kai, da kyar suka rabu, shi kam banda gidan surukansa ne da ya nunawa matarsa irin son da yake mata, da kuma yadda yae jin kaunarta. Sai take jin ita ma kamar ta bishi, banda tana jin kunyar abin da-zai biyo baya da ta bishi, ta kuma taya shi kwana.
A d‘akinta kasa bacci ta yi, sai juyi take a gado tana tuno malam dinta da dumbin soyayyarsa I gare ta, malam ya iya soyayya mai ratsa
zuciya, daga qarshc dai miqewa tayi ta fada toilet ta dauro alwala ta dawo ta dinga nafilfili da lazimi da yake gwana ce a gurin yi. . Shima kusan hakane takasance dashi, gaba daya Falmata ta dagula masa lissafi, harya ji ba shi da wani samin shakka akan sonta. Ya kuma shirya tunkarar Fatila da maganar kai tsaye don zai iya rabuwa da kowa ma akan Falmatn, domin sai
yanzu ya gane meye so, ya kuma san son gaskiya yake,,,, Kai Falmata daita tsaya aranshi. Da safe kafin ya tafi saida sukasha hirar soyayya a waya kamar wancan lokacin, don tunda suka kammala lazimin asuba suke abu daya wato hira.
Sai dai yau gidan nasu Falmata da rigima aka tashi, domin tun daman jiya Malam Mukhtar yake gayawa Abban Falmatan nan da kwanaki bakwai iyayensa zasuzo domin tafiya da Falmatan. Ammn kada a tafi da komai saboda kada jigilar kayan yayi yawa, shi zaiyu mata komai. ‘ Abba yace a,a bai yarda ba yanason daidai shima yayima diyarsa wani abu amman dai zasu bari sai anje can kanon saisu siyi komie domin kuwa tafiya da kauan kam jigila ne
Da safe bayan ya karya ya tara matan nasa yana sanar dasu shawarar daya yanke kamar haka , “
“Jiya mijin Falmata ya sanar dani nan da kwanaki shida zai turo ‘yan uwansa su daukar masa matarsa, yace ba ya son komai domin idan akace za,ayi jigilar kayan akwai wahala ni na yarda da shawararshi, amma na nuna masa ina son ita ma na yi mata komai kamar yadda na yiwa ‘yan uwanta. Don haka idan zaku tafi ke Hajja Kaltum zan ba ki kudin komai ki siya mata a can Kano. Wadannan kayan kuma na zance da mahaifin Yagana su turo su diba, domin dai ba mu da sauran ‘yanmata da zamu sa ran a ajiye mawa k0 ya ya kuka gani?”
Tunda ya fara maganar Hajja Yakolo da Hajja Basma suka hade rai, domin tun jiya da suka ji Mukhtat yazo hankalinsu ya tashi musamman ‘da suka ga bai bar gidan ba sai can wajen sha biyun .dare. Sun san sun gama dai-daita kansu ke nan. ' '
Hajja Yakolo ce tayi tsagal tana fadin, “Gaskiya malam wannan zalunci ne, kudin da zaka kashe a sayi wasu kayan ai ba su kai yawan kudin da za akai kayan Kano ba, idan dai ba wata dabara ce aka fito da ita ba domin a ware diyar gwal ba, mu kam ba mu yarda ba ko Basma?” Ta kalli Basma wadda tayi saurin daga kai tana cewa.
“Ni a su wa? Ai mu ‘yan kallo ne, harka ce ta masu ‘ya’ya. Amma dai kowa yasan wannan salo
ne na a raba kan yara dai”.
Yayi dariya, idan da sabo ai ya saba da halin matan nasa, ya sake gyara zama yace “Ai ba maganar kashe kudin kawai ake miki ba, maganar wahalar kai kayan daga ni har shi Muntarin ai ba mu da takaicin kudi. Kuma don kudi nane duk abin da zakuce ba zai dame ni ba, domin duk ‘ya’yana daya na dauke su, tunda ni na haifi abina”.
Ya mike tsaye, “Ni 'ina da gurin zuwa, sai anjimanku”. Ya nufi kofa da saurinsa. '
Hajja Yakolo ta mike ta yiwa sauran kallon banza tana fadin, “Oho dai, duk munafurcin dodo Na mai shi ne, kuma a yi mu gani idan tusa zata hura wuta”. Sai taja wani dogon tsaki ta wuce Hajja Basma ‘yar koro tana biye da ita, su kam sauran abin dariya ma ya ba su.
A can d‘aki bayan sun kule Hajja Yakolo ta yi tagumi tana fadin, “Ai ni daman nasan da gayya aka shirya wannan auran, domin ki duba tun washegarin da aka kai su Yakura suke min waya suna kuka, banda Zahra wacce ta sami gidan zama mai kyau? Ai ke kinje kin gani, ita kuma Falmam har wani shiri ake mata, kina kallon yadda mijin nata ke bin iyayen nata kamar zai musu sujjada, to wallahi bazan yarda ba, duk dan da ya hana uwarsa
bacci shi ma kuwa ba zai runtsa ba, dole nayi duk Wani abu da zan ga bayan auren nan, muddin ina raye Falmata ba zata taba tarewa a gidan Muntari ba, balle har su sami abin da suke so”. ,
Hajja Basma tace, “Ahaf! Ai daman kallonki nake yi, haka kawai kin zauna kina kwasar bakin ciki da arziqin kanki da komai, gwama ki mike ki nemarwa ‘ya ’yanki da ke kanki ‘yanci wallahi. Ni da ace ina da‘ ya ’ya ai da bazan yarda a
yi min wannan cin kashin ba”. Ta dinga zuga Hajja Yakolo tana hawa har
ta yanke shawarar ziyartar bokanta a gobe don yayi mata maganin abin.

Hmmmmmm to masu iya magana dai sukace sannu sannu bata hana zuwa mun kammala littafi na daya
Admin yace, “Allah Ka shirya, Ka raba mu da matacciyar rayuwa”).

Mu hadu a na biyu.

MATACCIYAR RAYUWA

BOOK2

CHAPTER 10

A KANO
Ya isa Kano cikin sa’a da kwanciyar hankali, yana isa ya yiwa Falmata waya yace ya isa lafiya. Kamar ta doka tsalle don murna, ta dinga yi wa Allah godiya da ya kai mata masoyinta kuma mijinta gida laflya.
Gidansa ya wuce kai tsaye, maigadi ya bude masa Kofa yana masa sannu da zuwa. Ya amsa ya wuce ya ajiye motar gurin da yake ajiyeta. ~ .
Fatila kam an ci kwalliya kamar za a filin rawa, domin tasanda zuwan nashi, sai dai bai shiga gidan ba gurin maigadin nasa ya amshi buta ya daura alwala jin tayar da sallar magruba a masallacin: layin nasu, ya nufi masallacin da sauri.
Tun da ya dawo ta baibaye shi da iya yi da kissarta, wadda ke hana shi ganin aibunta. Ba ta d‘aga murya a gabansa balle ta yi fad‘a, ga shi kullum cikin yabon iyayensa da girmamasu take a gabansa, don haka idan ‘yan uwansa ko mahaifiyarsa suna korafi akanta, sai ya ga kawai don ba ta haihuwa ne suka tsangwame ta.
Yana cin abinci tana ta ba shi labarai kala-kala yana dariya, domin ta kula yau cike yake da farin ciki. Amma a can Kasan zuciyarsa .yana tunanin ta yadda zai gaya mata maganar Falmata, don bai san yadda zata dauki maganar ba, har suka kwanta bacci yana dari-darin yadda zai sanar da ita.
Washegari da safe sun sha hirarsu da Falmata a office dinsa ta wayarsa, yau dai ya yi niyyar gaya wa Fatila duk yadda zata dauka kuwa.
-Daga OflS kai tsaye gidansu ya wuce, bayan sun gaisa da sauran abokiyar zaman mahaifiyarsa ya wuce d‘akinta; tana zaune tana kallon tashoshin Larabawa ya shiga da sallama. Ta daga kai ta dube shi fuskarta a sake ba kamar yadda ta ke daure masa ba can baya. Ya sami guri ya zauna bayan ya durkusa ya gaishe ta.
Cikin farin ciki ta ce, “Mutancn Maiduguri yaushe ka dawo ne? Tafiya babu sallama sai Isyaku ke gaya mini ka tafi Maiduguri da nake jajenka kwana biyu, yaya' ka baro su lafiya k0?”
Ya sosa Keya yana dariya, cike da kunya yace, “Lafiya lau suke, sunce a gaishe ku ma”.
. “To, muna amsawa. Har yanzu ba ka yi maganar tariyar Falmatan bafa”.
Ya gyara zama sannan yace, “Abin da ya kawo ni kenan, na sanar da su ranar asabar za,a je d‘aukarta, sai ku zabi wadanda zasu zan'turo da motoci idan kun gama kimtsawa” .
Dadi ya cikata, tace, “Hakan ya yi kyau, a nan gidan naka zata zauna ne ko kuma ka tanadar mata gurin zama ne?”
“A’a, a gidana da nake gini na can Janbulo zata zauna, 'ai an kammala aikin ma, sai da na fara biyowa can sannan na yo nan, fenti kawai za a yi gobe insha Allahu”.
“To ai shi ke nan, Allah Ya sanya albarka, amma kuma kasan ba ka yi mata kayan lefe ba, tunda auren babu shiri aka yi shi, yaya za ayi ke nan?”
Cikin ladabi yace, “Ina sane, gobe wai da zan je gidan Hajiya Safiya na ba ta kudin ta siyo duk abin da ta ga ya dace, ranar da zata tare a tafi da kayan, ina ga ai hakan ya yi k0?”
Ta cc, “Eh, ya yi Allah dai Ya kawo su laflya, amma ya ya maganar matarka, ka gaya mata kuwa?”
Gabansa ya yanke ya fadi,.damuwa ta bayyana karara akan fuskarsa, amma sai ya dan dake ya ce, “A’ a, sai yau dai nake son sanar da ita insha Allahu”.
Ta taBe baki, “Kai dai ka jiyo, amma ka sani bazan yarda a maida Falmata bora ba, dole ne ka tsaida adalci a tsakaninsu muddin kana son a zauna lafiya” .
.Da sanyin murya ya‘ce, “Insha Allahu ba zaki ji komai ba sai alkhairi”. Ya mike tsaye, “Bari na wuce gida na ga magriba tana kawo kai”.
“To ka gaida mutanen gidan, Allah Ya tsare". ‘ ; .. Ya amsa da .amin, sanda yake kokarin ficewa. Hajiya Mariya ta yi jagale cike da fargaba, tasan halin Fatila da uwarta za su iya yin komai akan Falmata, amma dai ta Allah ba tasu ba. Ta san Falmata ba ta sakaci da addu’a,
duk abin da suka tura mata insha Allahu Allah
zai kare ta. Da wannan tunanin ta sami nutsuwa.
Sanda ya koma gida Fatila ba ta nan, ta tafi gidansu, don yau za a kawo kayan auren kanwarta Raliya don haka bayan ya watsa ruwa kai tsaye masallaci ya nufa. Har ya dawo ba ta dawo ba, da yake shi din ba bakon zafi ba ne, sai ya shiga kicin da kansa don ya nemarwa kansa abin da zai ci, indomie ya dafa da kwai, ya dawo falon yana ci yana kallo.
Gaba daya kewar falmata da sonta suka taso masa, ya dinga murmushi shi kadai yana son yanayin shagwaBarta da sanyinta, don haka ya ga gwara ya kirawota k0 ya samu sanyi a cikin ransa, babu wani jinkiri ya kirata.
Cikin siririyar muryarta ta yi sallama, jikinsa ya yi wani yarr ya haye doguwar kujera ya kwanta yana amsawa cike da nishadi a lokaci guda kuma yana rage sautin talabijin.
Daga can Bangaren tace, “Malam yayata ba ta kusa ne k0? Na ga yanzu lokacinta ne ba nawa ba”.
Ya yi dariya, yana fadin, “Au har kin raba muku lokaci? To yanzu ya za, ayi gashi
kishirwarki ta sanya na shiga lokacinta. Ina jin kamar na yi tsuntsu nazo kusa dake, na rungumi' wannan tattausan jikin naki. na sumbaci dan karamin bakinki mai kama da atafa". .
Ta yi dariya cike da nishadi da jin dadi, tana cewa,_“Ni fa kunya nakeji, ka daina fadin haka mama”.
Yace Au? Kunya k0? Ina ma ina kusa daje da kinga abin da zan miki karamar kunya ma wai me kikEyi ne yanzu Fatimatuna?”
Ta sake yin dariya tana kallon dakin nata, tace, “Da dai lazimi nake yi. Yanzu kuma ina sauraron muryarka ne mai dadi
Ya yi dariya, “lye? Lallai yarinyar nan kin fara fitowa. To bakya tunanina kenan k0?”
. “Ina yi mana, .ai kewarka ta sanya na kama karatu da lazimi ma".
Ya kuma yin dariya yana jin dadin kalamanta masu kama da busar sarewa, shaf ya sha’afa ya ma manta a inda yake, balle har ya yi tunanin abin da zaije yazo Ya dan lumshc ido yace
“To kin yi kokari, sauranki abu daya yanzu, kice ina sonka Mukhtat’, kinga sai na yi bacci cikin dadin rai k0?”
Ta kama dariya cike da kunya, don ba zata iya fada ba. Ya ce Uhm, ina jinki k0...” Kamar an ce ya bude idonsa, sai ganin Fatila ya yi a kansa tana huci kamar mayunwacin Zaki, gabansa ya fadi gaba daya ya dimauce. Da sauri yace da Falmata“Shi kenan, zan kiraki an jima”. Bai jira jin abin da zata ce ba, ya kashe wayar. Mamaki ya cika falmata jin muryarsa gaba daya ta sauya, sai tunanin Fatila ya fado mata, k0 ita ce ta zo gurin ne? Tabbas idan dai saboda it ya kidime haka tana da aiki ja a gabanta, domin bashakka yana tsananin tsoronta. Ta zame ta kwanta jikinta ya yi sanyi qalau Shi kuwa ta maza ya yi, yace“Yaushe kika dawo banji shigowarki ba?” . ldanunta sun rune zuwa jawur, kamar Jan gauta. Tace, “Eh daman yaushe zaka san na dawo kana iskanci a waya, yanzu Mukhtar ba ka ji tsoron Allah ba kake magana da mace haka, kana cikin gidanka na aure, kowa yana kallonka kamar kamili, ashe kana can kana watsewarka da ‘yan mata...” . ‘
“Ke Fatila, kisan maganar da bakinki zai dinga fadi”. Ya katseta cikin tsawa kamar zai tsaga falon. Ya ci gaba, “Ta yaya zaki dinga gaya min irin wadannan maganganun masu zafi haka, kin sanni ba tun yau ba, babu matar da zan iya yiwa wadannan kalaman idan ba halaliyata ba, haba...”
Ta waro ido waje cike da tsoro, gabanta yana bugawa da sauri-sauri, tace “Ban gane abin da kake nufi ba Mukhtar, kana son ka ce min ita wadda kake yiwa wayar halak dinka ce? Yaushe ka fara bada fatawar son rai ban sani ba?”
Hawaye ya fara zarya a idonta, wani irin .masifaffen kishi ya tokare kirjinta, har da kyar ta ke zaro numfashinta, da ace wani neya ba ta labarin ya ganshi yana waya da wata lallai da ta karyatawa zatayi
Cikin karfin hali yace, “Ba wai fatawa Ce ta karya ba, sai dai ina son ki yi hakuri ki
fahimta,' wacce nake waya da ita Falmata matata ce kamar yadda kike matata”.
“ What? Kada ka gaya min zancen banza wanda hankali ba zai dauka ba, kana son ka ce min bayan ni kana da wata matar? Shin cikin bacci aka daura muku aure, k0 kuma a duniyar wata ka aure ta? Ka dawo hayyacinka Mukhtar ka gane abin da kake fada don Allah”. Gaba daya jikinta rawa yake yi.
Babu tsoro yanzu a idonsa, ya ce, “A duniyarmu ta mutane aka daura mana aure ba a duniyar wata k0 a mafarki ba. Sanda na tafi Maiduguri ziyarar aikin da na gaya miki, a sannan aka daura mini aure da Falmata diyar Abbana gana abokin mahaifina, ki yi hakuri ni kaina ban san da maganar auren ba, sai da naje aka ce an daura mini aure, a yau dama na yi niyyar gaya miki
Ganin bata ko Kifta ba ya sanya yayi zaton ko ta saduda ne, sai dai bai san shirun tsiya ta yi ba, ya matsa kusa da ita da zummar kamata ya rarrafa, sai dai yana taBata ta yi baya luuu ta fadi a sume.
Da sauri' ya durkusa a gabanta yana kiran sunanta, amma ina ko motsi ba ta yi , tuni ya mike ya nufo firij ya dauko swan water mai sanyi ya yayyafa mata.
, Ta yi wata sassanyar ajiyar zuciya, sannan ta bude idonta ta mike zaune a firgice tana kallonsa, don ta yi zaton mafarki ta keyi, tace masa, “Hubby wani mummunan mafarki na yi yanzu, kai mafarki babu kyau, wai ka yi aure a Maiduguri, da gaske ne k0?”
Ya yi shiru ya ma rasa abin da zaice, bai taba ganin mace mai shegen kishin Fatila ba. Ganin ya yi shiru sai ta hango gyalenta da jakarta da takalminta da ta dawo da su daga unguwa, hakan ya tabbatar mata da lallai ba mafarki take yi ba gaske ne, sai kawai ta fashe da kuka tana fadin.
“Da gaske ka yi aure a Maiduguri, tabbas ka cuce ni, ka ci amana ta, ka tabbatar na gama zama da kai, ,tabbas kai munafuki macuci azzalumi". '
Ta mike ta yi dakinta kamar mahaukaciya, ya mike da sauri ya bita yana
fadin, “Fatila ki saurare ni na gaya miki yadda aka yi auren nan, nima ba da son raina na yi ba”.
Amma ina bata k0 waigo~ ba, ta banko kofar dakin nata har da sanya makulli. Ya yi tsaki cike da takaici, sannan ya wuce dakinsa yana fatan Allah Ya sanya abin ya tsaya iyakacin nan.
Ita kam tana shiga daki tama rasa me zata yi, sai ta koma tsige kayan jikinta tana wurgi dasu kamar mahaukaciya, sai da tayi tumBur sannan ta kama zunduma ihu a dakin ita kadai tana zagaye dakin, hannunta bisa kanta. Sai can dabarar kiran mahaifiyarta ta fado mata, ta janyo wani zani ta daura sannan ta fara neman layin. wayar hajiya Kumatu mahaifiyarta.
Bugu daya Hajiyar ta d‘auka, tana fadin “Hello Fatila ya ya aka yi, har kin isa gida?”
Maimakon ta yi magana sai kawai ta ci gaba da ihu a waya tana kuka, hankalin Hajiya Kumatu ya tashi, ta mike tsaye a rude tana fadin, “Kc Fatila gaya min meke faruwa ne,
kin bugo waya kina mini ihu, k0 mijin naki ne ya rasu?”
Da kyar ta dan tsaida kuka tana fadin “Momy ai gwara ace mini mutuwa ya yi sai nafi jin sauqi da a sanar dani wannan mummunan labarin, wai fa aure ya yi ban sani ba...”
“Aure kuma kan uban can, da gaske kike yi Fatila k0 kuma labarin karya aka zo aka gaya miki? Ni fa bana son kina dinga .yarda da wadannan labaran na karya, ai kin san an ce mama shi da aure k0 bayan ranki har abada k0?”
Ta Kara fashewa da kuka tana fadin“Shi fa da kansa ya gaya mini ba labari aka ba ni ba, samunsa na yi yana hirar soyayya ma da matar tasa, kin san Mukhtar ba ya karya, ina ga tsinanniyar babar nan tasa ce ta hada wannan tuggun, tunda daman tace komai tsafina wai sai ta yiwa danta aure. To burinta ya cika Mommy na shiga uku, ina raye a gaban idona Mukhtar ke hirar soyayya da wata mace ai gwara ace na haukace na huta ma ni...”
Kuka ta keyi kamar ranta zai fita daga jikinta. '
Ita kanta Hajiya Kumatun ta shiga matukar mamaki, to ya ya aka yi hakan ta faru, ko.da wasa ba ta ji maganar a layin ba, ga shi layinsu daya da gidan su Mukhtar din, to ko dai ba a sanya rana bane? Da kyar ta dan daure ta ce
“Kinga ki kwantar da hankalinki, sun yi nasarar daura masa aure da wata, amma na rantse da Allah basu isa ta tare a gidansa ba, balle har wata mu’amalar aure ta shiga tsakaninsu ba, da kanshi zai zo ya gaya miki ya sake ta muddin ina raye, idan kin ga Mukhtar ya zauna da wata mace sai dai idan bana numfashi ne a duniya, k0 ba na numfashi fatalwarmu ba zata kyale shi ya zauna lafiya ba".
Cikin kuka tace“Anya kuwa Momy ba cutarmu bokayen nan keyi ba, washegarin ' sanda ya dawo fa sai da naje gurin Barbushe na sanar da shi sauyin da yazo da shi, yace mini babu komai, har ya ba ni wasu magunguna na ' yi amfani da su, ashe tuni an daura auren ma ba tare da saninmu ba, ni fa abin har ya fara ba ni haushi da takaici fa”.
Cikin kwantar da murya ta ce, “Kiji wani zanccn banza, ba don aikin nasu yana yin .kyau ba, da kin-isa ki aure shi ma balle har ki zauna a wannan gidan, ko kin manta da yadda aka yi auren ne ki daina fadin wannan maganar ma, ai daman dole a semi akasi kuma ba kin ce ‘yar Maiduguri diyar abokin babansa bace? Ai suma ba haka zasu zauna ba, ai nasan malam Abba Gana shegen malami ne, dole sai mun tashi tsaye, ki dai tanadi kudi, gobe zamu koma gurin Barbushe din”.
Da kyar ta samu ta lallaba= diyar tata ta daina kuka, sai dai suna gama wayar ta kirawo kawarta Diyana. Ita kam ruwan ashar ta dinga 'zubawa kamar famfo, ta kuma ce ita ma akwai wani' boka sai sunje gurinshi, dole da ita za a yi tafiyar.
Sai a sannan ta sami dan sauki a cikin zuciyarta, har ta kwanta a gado, sai dai kusan daren nan ba ta runtsa ba, ta Kagu gari ya waye ta nufi gurin bokayenta.
Shi kuwa bawan Allah malam Mukhtar jira yake gari ya waye ya kuma zuwa ya lallasheta, don a ransa bai taBa kawowa Fatila
tana bin bokaye da malamai ba saboda yadda ya yarda da ita.
Don haka da safe yana kammala shiryawa ya nufi dakinta, abin daya -ba shi mamaki bai wuce ganinta tayi wanka ta shirya ba, duk da ba tayi wani make up ba amma bai yi zaton k0 wanka zata iya yi ba, Ya dan ji sanyi a cikin ransa, domin hakan yana nuna masa ta dan sauko ke nan.
Ya isa ya zauna gefen gadon ya kwantar ‘ da kanshi ya shiga lallashinta, kamar zai zubda hawaye. Ta yi shiru kamar ta bari din, amma «cikin zuciyarta tafasa kawai ta keyi, ji take kamar ta shake shi ta kashe shi ta huta ma, ji ta ke yi ta tsaneshi matuka, amma dai ta taushi kanta ba ta tanka masa ba, burinta ya fita ita ma ta fice kawai.
Ya jima yana surutunsa, sannam ya ficc jikinsa sanyi kalau, domin ta ba shi tausayi ainun, ganin yanda ta zabge dare daya.
Tana jin tashin motarsa ta yagi gyalenta da jakarta ta fice ita ma. Yana fita daga gidan ta nufi motarta ta shiga ita ma ta rufa masa baya
zuciyarta tana tukuki kamar zata faso Kirjinta ta fito.
A can gidan mahaifiyarta ta yada zango, ta tadda ta a shirye don haka ta mike kawai ta zari jaka, a kofar gida suka ci karo da Diyana adaidaita sahu ya sauketa suka dunguma suka wuce neman duniyarsu.
Shi kam bawan Allah Doctor Muktar daga nan gida kai tsaye ofis dinsa ya wuce, karfe biyu dai-dai ya tashi daga aiki ya wuce gidan yayarsa Hajiya Safiya. A kofar gida ya yi mata waya .ya isa, murna kamar ta goya shi domin da duk_ ‘yan 'uwansa haushinsa suke ji akan rashin Kara aure, amma yanzu tunda ya yi aure suka sama masa lafiya.
Bayan sun gaisa ta kalle shi tana dariya, tana fadin, “Ango kasha kamshi, dube ka sai wani kyallin goshi kake yi”.
Ya tura hularsa keya yana sosa goshinsa, yana dariya, babu abin da yake burge shi a yanzu illa a yi masa zancen Falmata, yana jinta matuka a cikin ruhinsa.
Hajiya Sahura ta dora da cewar, “Jiya Abba ya yi kirana, yake sanar dani maganar

Fatila fa taqi yarda da kaddara shin me kuke tunanin zai iya biyo baya oya a buga sharhi.
.
MATACCIYAR RAYUWA

CHAPTER 11

Dauko amarya mu kam gaskiya' an .sha damu, ai' munYi zaton sai mun kara' cashewaa a~ Kano
Yayi ‘dariya, gamida fadin ‘Haba Hajiya; don akin daurema bidi’a gindi, ni .yanzu maganar kayan da za,a ‘hadawa Fatima ne ma ya kawo ni, tunda anyi abin cikin gaggawa kamar nawa» kikaga ya dace a kashene?

’ta kumayin dariyaa cike da farin ciki, wai ,yau Mukhtar ne ‘ke maganar 'zai ’ hadawa wata' kayan aure; mutumin da ada idan kamai maganar mace kamar ka watsa mishi garwashin wutane lallai idan da rai da rabo‘
Tace kaga kamata .yayi mu rubuta duk abinda za,a 'siya sannan-a 'lissafa k0?”
"‘Ya. katseta,‘ ‘Kai Hajiya yaushe za a yi haka kawai' ki kimtaci abinda kike ganin zai isa,
Basai a karo daga bayaba ko

Tayi dan jimm kana tace to ai shi kenan
Inaga dubu dari uku zasu isa a hada daidai na talaka
Ya karkace ya zaro kudi na cikin Aljihunsa na gefw sa gefe bandir din yan dubu dubu yana fadin, “Daman dubu dari biyar na taho da shi, idan sun isa shi kenan, idan ba su isa ba sai ki sanar dani ki sanya duk abin da ya dace Yayata, kin san amaryar ‘yar gayu ce”. .
Ta yi dariya har da shewa, “Lallai wannan amarya taci fas, ashe da ranmu zamu ga wannan rana Mukhtar? T o Allah Ya nuna ' mama ranar da zamu ga ‘yan ‘ya’yanka suna yawo akan qasa, amin”.
Ya dan hade rai, don bai son yanda suka tsangwami Fatila akan rashin haihuwa, shi gani yake don ba ta haihuwa me ya sanya suka sanyata a gaba, ya mike yana dariya qasa-kasa, “Ku kuma kun j i matsalarku kenan Hajiya, bari na wuce ni, sai na ji ki a waya”.
Ta mike ita ma tana fadin, ‘Ahaf, ai an taBo ‘yar gwal din taka ka mike mana, ni kam Allah 'Ya fidda Falmata daga sharrin Fatila, don nasan ba zata dauki abin a kaddara ba”.
‘ Ya yi gaba yana fadin, “Ni dai kinga tafiyata, Allah Ya huci zuciyarki”.
Ta yi dariya sanda ya gama fita tana fadin, “Oho dai k0 a yau ka rabu da Falmata mun nunawa Fatila iyakarta, muguwa kawai”.
Daga nan gidan kai tsaye gidansa ya wuce, sai dai abin da ya ba shi mamaki bai wuce ganin Fatila bata nan ba, ransa ya baci matuka, to ina ta tafi ba tare da ta tambaye shi ba? Ya fara neman layukan wayarta, lokacin tana durkushe gaban boka Barbushe kamar zata yi masa sujjada don biyayya, tana jin kiransa ta dan tsorata ta kalli bokan ya kalle ta yace
“Shi ne yake kiran wayar taki k0?”
Da sauri ta ce, “Eh shi ne boka, watakila yaje gida bai ganni ba ne, ni sam na manta na tambaye shi ma saboda Bacin rai, cewar zan fita unguwa”.
Bokan ya fashe da dariya yana fadin, “Ai haka ake so,ai duk wani abu da zaki saBa masa ake son ki dinga yi, idan har kina tambayarsa idan zaki fita to aikinmu zai iya karyewa, na ‘ gaya miki mijinki malami ne da yake yawan karya mana aikinmu, don haka sai kina taimakon shaidanu da basu‘ gudunmawa akan duk wani abu da suke so, kamar satar fita da -yawan labe, da daukar duk kudacdensa, duk wani abu da zai dinga sanya shi Bacin rai dai. domin sai ransa ya baci sannan zasu samu
damar aiwatar da ayyukansu akan shi, kin gane k0?" Ya fadi yana zare idanu.
Da sauri ta cc, “Eh boka”.
. Ya kara kallonta, “Ki dauko wayar ki kasheta yanzu, idan kin koma kada ki ba shi _ hakuri, kuma duk yanda zaki yi ki takale shi ku yi fada, muddin ransa ya baci to ki tabbatar a daren yau aikinmu zai fara tasiri a kansa. Ga wannan kuma” .
Ya mika mata wata kankana wacce ta sha wani irin zane da rubuce-rubuce duk an huhhudata yana ci gaba da fadin.
“Ki je ki binne a kasa, ki tabbatar ramin ya kai kamar kamu goma, ki kuma tabbatar kin binne cikin makabarta da daddare, idan ta kwana kikoma ki gano yanda ta zama, sai ki sanar dani. Ga wadannan layun ki watsa su a kanta, amma fa kada ki manta inda kika binne kin ji k0?”
Da sauri tace, “Insha Allah...”
“Ke... Ke ya ya zaki fara karya mana aiki? Kada na kuma jin irin wannan kalmomin a bakinki, ai dasu ne yake karya mana aiki shi
“To boka, yanzu me za mu baka ne?” Hajiya Kumatu ta tambaya tana daga gefe a tsugunne, ita da Diyana manyan mata.
--. Ya kalle su ya bushe da dariya, sannan yace, “Ai dole sai dodo ya sha jini, don haka muna bukatar jini, sannan na gaya mata duk ranar litinin da juma’a ba zata yi sallah ba, kuma babu sallar safe da ta isha’i, duk ranar da ta kuskura ta yisu to aiki ya lalace kenan”. .
Hajiya Kumatu ta kara kwantar da kai tana fadin, “To ai boka kasan bamu san inda zamu samo jinin ba, sai dai mu baka abin da za a biya yara su samo a taimake mu boka Barbushe jikan Tsanburbura”.
Ya gyada kai yana wani muzurai, yace, _“Shi kenan, ku bada dubu dari da hamsin...”
Jikin Fatila yana rawa ta zuge jakarta ta zaro kudin ta mika masa. Ya amshe ya watsa bayansa cikin wasu layu kamar marasa amfani.
Da haka suka bar gurin nashi, shi kuwa yana can gida ya kufula, domin a rayuwarsa bai son matarsa ta dinga yawo mara kai, idan akwai abin da yake hada shi fada da Fatila bai wuce
yawonta ba, duk sai ya damu ya kasa yin
komai, saida yaji shigowar sako a waya ne ma sannan ya tuna da Falmata
Yana dubawa kuwa‘ yar halak din itace, da sauri ya kirawota.
Tun daga jin sallamarta hankalinsa ya kwanta, ya lumshe ido wani sanyi yana kwarara a ransa.
Ba ta shigo gidan ba sai gab da sallar magariba, yana falo a zaune ya cika fam kamar zai fashe, sai dai abin da ya kara kular da shi bai wuce ganin ta zo ta shige ba tare da ta k0 kalli inda yake ba. Bai yi niyyar kulata ba, domin yana da matukar hakuri, me yasa ya kyale ta, sai dai wannan rainin wayon da ta yi masa ya hasala shi matuka, ya mike rai a bace yana fadin.
“ke malama daga ina kike, kuma kina ganina kika wani share ni, bayan kin fi kowa sanin zunubin da yake cikin satar fita?”
Ta kalle shi sama da kasa domin ta kular da shi, tace, “Bani da lokacin magana da kai, ka ji k0?”
Ya kuma kufula, sai dai can tunanin abin da ya yi mata jiya na game da auren
Falmata ya fado masa, don haka sai ya sanyawa zuciyarsa sanyi ya koma kujera ya zauna ya dafe kai.
. Sam ba haka ta so ba, domin hasalarshi yana cikin shirinsu na farko, amma ba ta karaya ba taci gaba da magana.
“Kuma fita ma yanzu na fara yin'ta, idan mutum ya isa ya yi maganin abin mana”.
Ya daga idonsa yana kallonta, yana ta tausar zuciyarsa da yi mata uzuri domin kishin Fatila yasan zai iya sanyata yin komai, sai ma ya kwantar da kai yana fadin.
“Fatila ki kula da nauyin da yake kanki, bani ne na dora miki ba, Allah ne Ya dora miki, amma tunda haka kika zaba shi ke nan...” Yana kaiwa nan ya mike da sauri ya nufi hanyar waje domin an fara kiraye-kirayen sallar magriba.
Hankalinta ya tashi matuka don yana neman karya mata aiki , sai ta nufi dakinta da sauri, babu batun sallah dama. Diyana ta fara kira, bakinta na rawa tace.
“Diyana nazo na tarar da shi a falo da farko kamar zai biye min na bata masa rai, amma in gaya miki daga karshe sai ya koma
lallashina, kin san halinsa da shegen hakuri kamar wanda kecin naman damo, yaya zan yi ne yanzu?”
Diyana taja tsaku cike da takaici, tace
“Ke fa banza ce, ke yanzu har sai an gaya miki abin da zaki yi? Kawai ki shiga dakinsa ki nemi kayansa da yafi so ki yayyaga su da reza ki watsar tsakar falon naku, sannan ki fasa talabijin da rediyo ki watsar a falon, sai ki dauko jakarki ki bar gidan a haka, nasan duk iyakacin hakurinsa dole ne ransa ya Baci, dole zai nufi dakinki da zummar yi miki masifa ya tadda ba kyanan, nasan zai kwana ransa a Bace sai kuma shaidanun aljanunmu su kwana aiki a kansa, a daren sai muje mu binne kankanar kiyi zamanki har gobe a gidan da zummar yaji kika yi, idan muka je muka ga yanda ta koma sai ki sanar da tsinannen sai ya sanar da mu abin da zai faru kuma a gaba, amma dole sai mun tashi tsaye tunda kinga yace yarinyar nan ita take .a_ tsaye don har tafi Mukhtar dinma addu’o’i na kariya”. _
Fatila tace, “Lallai kam haka ne, bari naje na fara aikata abin da kika ce din ma”.
Ta kashe wayar ta nufi dakin Mukhtar. Wasu yadikansa da ya siyo daga Dubai da mai ruwan madara da fari kal kudinsu ya .kai kusan dubu hamsin-hamsin, ga shi an yi musu wani dinkin hannu‘mai kyau. A can baya babu abin da ta keso illa ta ga ya sanya wadannan kayan don yana komawa kamar'wani Saraki, shi ma kansa yana son kayan matuka, su ta yayyanka gutsi-gutsi ta watsar a falon, ta faffasa duk plasma T.B da ke gidan da sauran kayan kallon ta bar su barbaje a falon ta nufi dakinta ta hada kaya cikin jakarta tau wucewarta abinta.
Shi kam bai dawo ba sai da ya yi har da sallar isha’in sannan ya nufo gidan. Ya jima cikin .raka’,arsa ta karshe yana addu’ar neman zaman lafiya a gidansa da iyalinsa.
-Sai dai me? Yana shiga gidan ba tare da sani ba ya taka glass wanda ya shige kafarsa ya rike Kafar da sauri yana fadin.
“Subhanallah”.
Sa- alokacin idonsa ya kai kan barnar da ke cikin falon, gaba daya ”sai ya tsaya cak kamar an dasa shi, yana karewa dakin kallo.
Wani irin Bacin rai ya baibaye shi, domin cikin ‘yan sakwanni kwakwalwarsa ta sanar da shi abin daje faruwa, ya maida takalminsa ya nufi cikin dakin da sauri, kai tsaye gurin kayansa da ta yayyanka ya wuce.
Ya daga kayan zuciyarsa tana kuna bai san sanda ya nufi dakinta kai tsaye ba. Tabbas mai hakuri bai iya fushi ba dama, sai dai me? Dakin nata a datse ya ganshi alamun bata nan. Ya Kara tura kofar don ya tabbatar, ransa ya kuma Baci ya nufi dakinsa kai tsaye, ya yi zaune bakin gado tallafe da kumatu, ransa yana suya.
Wace irin mace ce Fatila? Shin kishi hauka ne da har zai sanya ta yaga masa kayansa ta fita ba da izininsa ba? Ya kyale ta shi ne kuma ta yayyaga masa kayansa har da yi masa rotsen kayan kallo?
Tabbas dole ta gane kurenta a wannan lokacin', idan ma yaji tayi yayi' alkawarin ba zaije bikonta ba sam, idan ta gaji da yajin ta dawo don kanta.
Haka nan ya kwanta ransa yana suya, k0
abinci-bai sami arzikin ci ba ya kwanta. Can
dabarar kiran Falmata ta fado masa sai dai yayi rashin sa’,a wayar tata a kashe take, don haka dole ya hakura.
A can Bangarensu kuwa Diyana ta yanke shawarar gidan Haj. Kumatu zasu kwana, ta . yiwa maigidanta karyar Kaduna zata gaisuwa, haka ta tsallake ta barshi da ‘ya’yanta biyu domin su je su binne abin da boka .ya basu. Karfe dayan dare suka fice suka nufi makabarta basu ji tsoron Allah ba, balle aljannun dake yawonsu a daren ba.
_ , Can gefen makabartar suka haka rami
suka binne kankanar da sauran layun suka yi shaida yanda .zasu gane gurin, sannan suka : juya gida.

***************************************
Koda gari ya waye. kai tsaye gurin masu aiki ya nufa ya tadda su har sun fara fentin gidan, daga nan ya wuce ofls dinsa kai tsaye, sai da rana 'ta d'aga sannan ya kirawo layin Falmata. ~Ya yi sa’,ar samunta kuwa, donhaka suka shiga hira mai dadi, sai dai a Bangarensa gabansa sai yawan faduwa yake yi.Haka suka
yi sallama ya hada tagumi ransa yana zafi ya san abin da Fatila ta yi masa ke damunsa, duk da yana son ya ga ya manta da abin amma ya kasa. «. Sai yamma Iikis ya bar ofls dinsa kai tsaye gidansu ya nufa, ya tadda gidan a cike ana ta kallon kayan da Hajiya Safiya ta hado, kaya ne na gani na kowa sai sanya albarka yake yi
sai da suka matsa masa sannan ya dan kalli kayan, duk da ba sanin kayan mata ya yi ba, kayan sun burge shi, daga gani kuma an kaso kudi masu dama. Ya kalli yayar tashi yana fadin.
“Nawa ne kuma cikon Hajiya?”
Ta yi dariya ta ce.
“Cikon babu yawa, su ma don an sai mata awarwaro na gwal ne, dubu ashirin da tara ne, amma ka barsu shi ne gudunmawata”.
. Ya ji dadi matuka, yace
“To an gode, bari na wuce gida”.
Mahaifiyar shi ta tare shi da maganar Fatila, tana fadin, “Ina fatan ka gaya wa matar taka k0?”
Gabansa ya fadi, Bacin ransa ya dawo, don ko sunanta bai son yaji an ambata, amma dai sai ya dake yace
“Eh na sanar da ita Hajiya”.
“To ai shi ke nan, ni dai na gaya maka ka dinga neman magungunan tsarin jiki, kana takama kai malami ne amma ilimin zamani ya lalata ku, bakwa nemawa kanku tsarin komai, kada ka yi tunanin don kana mahaddaci asiri ba zai kamaka ba, yafi kama irinku masu sakaci ma”. Cikin ladabi yace Insha Allahu zan kiyaye”. .
A ransa kuwa mamakin yanda_ suka dauki Fatila yake yi, yaushe zata yi masa wani asiri, su ba su san irun son da take masa ba, banda wannan maganar ta Falmata ta ratso ma shi zai ce bata taba bata masa rai ba, kullum takan yi duk wani abu da zai faranta masa ransa ne, amma dai dole ya bisu da to don a zauna laflya. Da haka ya wuce ya bar gidan.
Baiwar Allah Falmata tunda almuru ya kawo kai ta ji ranta yana baci, zuciyarta tana ta tafasa, ga wani irin faduwa da gabanta ke yi, da
yake ita din malama ce sai kawai ta dauko qur’ani ta fara karantawa har aka yi sallar magriba.
., Shi ma can yaji duk abin da falmatan keji, amma sai ya dauka a Bacin ran abin da Fatila ta yi masa ne, don haka kai tsaye wata majalissar abokansa lakcarori ya wuce, can gefen Gwauron Dutse suke zama, duk da har lokacin ran nasa a bace yake sai ya dan ji dadin hirar, ya yi kokarin boye abin dake damunsa suka yi ta hirarsu anan suka yi jam’in sallar isha’i, sai wajen takwas suka watse kowa ya kama gabansa, shi kam sai da ya biya gidan sayar da abinci ya sayi na taflya ya sanya a motarsa sannan ya wuce gida.
Amma da ya isa gidan sai ya kasa ci, ya dinga juye-juyen tashoshi Arab yana son kiran Falmata ya ji muryarta, amma kuma zuciyarsa taqi ba shi hadin kai, sai yake jin zafinta a ransa matuka. A nan falon bacci ya dauke shi ba tare da ya shirya ba.
Su kam shedanu wajen karfe daya na dare kamar jiya suka kara komawa inda suka
binne abin nan suka kuma tonawa, gabansu ya
fadi ganin ba su ga komai ba, ga shi dai sun tabbatar nan ne suka binne, sai alamar kwallaye na Kankanar, amma ko fatar babu. Suka dinga kallon juna a tsorace amma sun kasa magana, sai da suka isa cikin mota sannan suka iya yin magana. Fatila ce ta fara magana
“Momy kada ace aikin nan ya lalace dana shiga uku na kuwa”.
Hajiya Kumatu ta yi dan qarfin hali ta ce.
“Anya? Mu dai kirawo wayarshi muji”.
Da sauri ta kirawo layin nasa, bugu biyu ya dauka, bakinta yana rawa tayi masa bayanin abin dake faruwa, maimakon ya yi magana sai taji ya fashe da dariya. Gabanta ya ci gaba da faduwa, sai zare ido ta ke yi. Su kuma sun zura mata nasu idanun cike da tsoro da fargaba, sai da ya yi 'dariya son ransa sannan yace.
“Yarinya ki godewa aljani Ifritu domin aikinsa ya yi kyau ina mai miki albishir da yanda kankanar nan tabi kasa babu ko alamunta, to haka maganar auren mijinki tabi ruwa har abada ba zai kuma maganarta ba, kin yi nasara, saura kici gaba da yiwa Aljani biYayya akan abin da ya d‘ora ki".
'Ta yi wata ajiyar zuciya, sanda take kashe wayar, cikin rige-rige suke tambayarta abin da yace. Bakinta kamar gonar auduga tace, “Momy yace mini yanda kankanar nan tabi kasa haka maganar aurcn nan ta bi ruwa”.
“Kai amma naji dadi yau zan yi barci har da minshari”.
Farin ciki ya cika musu zuciya, suka nufi hanyar gida cike da farin ciki suna maida yanda aka yi. Hajiya Kumatu ke fadin.
“To bari kwana biyu mu Kara komawa ya yi mana wani aikin, wanda ko da an yi masa irin wannan auren take a nan zai saki matar ma, tunda ita tsinanniyar uwar tasa mun kasa samun galaba a kanta, koda yake ai ba ta dame mu ba, gwara ma a yi komai ba da son ranta ba, don ina son ta yi ta hadiyar bakin ciki har ranar da zata koma kabarinta, ai mu duk wanda ya Ci tuwo da mu miya ya sha wallahi”.
Tunda Mukhtar ya farka da asuba yake jin zuciyarsa sakayau kamar an sauke masa wani abu. sai dai kuma da soyayyar Fatila ta cikata, har yake jin kamar idan bai je inda taje ba komai zai iya faruwa da shi Cikin hanzari

Tofa wai meke shirin faruwane?????? 

MATACCIYAR RAYUWA
CHAPTER 12
ya dinga shiri ba ya jin k0 offices zai iya zuwa ba tare da ya je yaga Fatila ba, ga shi tun asuba yake neman wayoyima amma duk suna kulle
Karfe bakwai da rabi ya fice. Kamar daga sama suka fara jiyo horn sinsa, da yake gidan babu maigadi sai dai a bude wa mutum, Fatila cikin doki ta ke fadin.
“Momy wallahi horn din motar Mukhtar ne, jeki kuma ki gani, ga shi bana son ya ga gazawata da naje na bude masa, da an san zai zo ma ai da da wuri zamu bude kofar ma”.
' Hajiya Kumatu ta mike da sauri ta nufi kofar ta bude, ai kuwa sai ga motar Mukhtar, ba tace masa kanzil ba ta koma cikin gidan, shi kuma ya sami guri ya yi parkmg ya fito ya nufi , gidan gabansa yana ta faduwa.
Ya jima jikin kofar yana bugawa sannan Fatilan ta zo ta bude, ta wani kalle shi a sheke kamar ba ta yi 'murna da zuwan nasa ba, shi kuwa wani sanyi ya ji a cikin ransa, sai ya ji kamar ya rungume ta don dadi. Ya kalle ta yana dariya.
“To a bani hanya na wuce k0?"
“Ka wuce ina? Ai nan gidanmu me ba naku ba
Ya yi dariya, “To masu gida, ai nan sai dai kice gidan Momy ne, gidanki yana can Rijiyar Zaki k0?”
Ta kwaBe baki ta koma cikin falon.
_ “Wace ni, gidan Mukhtar dai mijin . Falmata, ni komai na ya gama zama a gidan”.
Jin ta ambaci sunan Falmata sai ya ji kamar an watsa masa wuta gaba daya ransa ya Baci, domin tunda gari ya waye ya ji babu abin da ya tsana a duniya sama da ita, ko sunanta bai son ya jima balle ya ganta da idonsa. .
Ganin yanda ya sake gumtse fuska daga ambaton sunan Falmata ya faranta mata rai, ta tabbatar lallai aikinta ya yi kyau.
Ya sami guri ya zauna ita kuwa ciki ta yi shigewarta, ya bita da kallo kamar ya kamota yake ji. Kusan minti goma sannan 'Hajiya Kumatu ta iso falon ya gaishe ta a mutunce yana wani sunne kai.
Ta dube shi da kulawa, tana fadin, “Sai kuma ga Fatila a gida, idan gajiya ka yi da
aurenta ai sai ka kawota da kanka kamar yadda kazo ka aure ta”.
Ya dinga rantse-rantse da neman ya kare kanshi. Ta dinga yi masa yawo da hankali domin ta ga yanda aikin nasu ya yi da shi. Da kyar ta hakura tace bari ta kirwo masa Fatilan ya ji idan za ta koma.
Gabansa ya dinga faduwa, sai ga shi
yana'ta addu’ar Allah Ya sanya ta koma din, kada ta ce ta rabu da shi, da kuwa ya ga ta kanshi lallai. ' Sanda ta fito ta dube shi shekeke ta ce, “Gaskiya Mukhtar babu inda za ni, domin na riga na yankewa kaina shawarar sai dai ka zaba tsakanina da matarka, domin ban yarda zan iya hada ka da wata ba”. ~
Ya Kara kidimewa, yana fadin, “Haba Fatila, kina tunanin gaki zan iya kallon wata ne? Ni wannan aure daman ba da sanina aka yi shi ba, yanzu kuma ina tabbatar miki da ko
sunan yarinyar ba na kaunar na ji, don haka ki kwantar da hankalinki, duk yanda zan yi zan rabu da yarinyar nan...”
Kukanta ya katse masa maganar cikin kuka take fadin,“‘Ai dai kowa yasan Allah ke bada haihuwa, don kawai bana haihuwa sai danginka su tsangwame ni, to ni kam na gaji gwara kawai ka sauwake mini” .
Jikinsa har rawa yake yi, ya matsa kusa da ita yana fadin, “Don Allah ki yi hakuri, na miki alkawarin zan zauna dake a duk yanda kike, shin sun san waye mai laifin ne a tsakaninmu? Ki kwantar da hankalinki, ke nake so, zan kuma rabu da yarinyar nan cikin ruwan sanyi insha Allahu”.
Wani irin .dadi ya cikata, amma duk da haka sai da ta ja shi sosai, daga Karshe dai ya lallaBata suka. shirya, .wai Hajiya Kumatu ce ke musu nasiha su yi haquri da juna, shi dai da ya samu ya dauki matarsa ya ji dadi kome ye ma zai biyo baya karami ne.
A hanya suna tafe wayar shugaban masu ginin gidan nasa ta shigo. Ya d‘aga a hankaii, ta tsare shi da ido gabanta yana faduwa don ba ta san ko wayar waye zai amsa ba, cikin ladabi yace
“Alhaji mun kusa kammala aikin nan, sai dai fenti da alama ba zai isa a yi a can bayan gidan ba, k0 zaka zo ka gani ka karo?”
Ya kalli Fatila da tayi saurin dauke kanta, sannan yace.
“Ai kawai ku bar aikin nan, domin na fasa amfani da gidan ma, ka zo anjima gida ka same ni da makullan gidan sai na baku cikon kudinku
' Mamaki ya kama shugaban masu ginin, domin ya ga yanda ya .azalzali su kammala aikin domin a gobe ne za a kawo masa amaryar amma kuma ya ce haka, anan ya daure ya ce, “Alhaji ai..
Ya katse shi da sauri, “Ka ga ka yi abin da na sanya ka kawai, bana son wani tsari, sai anjima”.
Ya kashe wayar da sauri ya kalli Fatila da ta hade girar sama da ta kasa yana fadin.
“Masu gyaran gidan da yarinyar can zata zauna ne da, suka sanar dani kayan wai sun kare, nace musu su kawo mini makullan na fasa .
Ta taBe baki a ranta maganar tayi mata mugun dadi, amma bata son ta nuna masa a fuska, sai da ya kai ta gida sannan ya nufi otis dinsa. Yana isa kiran wayar mahaifiyarsa ya shigo. Da sauri ya dauka yana gaishe ta, ta amsa cike da kulawa, sannan ta dora da cewar.
“Maganar tafiyar nan, jiya na yi zaton zaka shigo da daddare, k0 yau da safe shiru, kasan gwara a tanadi komai a hannu koka tanadi motocin da za a yi tafiyar ne?"
Baya son a yi masa duk wata maganar da ta danganci Falmata, amma don kada ta gane halin da yaké ciki ya sanya yace
“Eh to, daman dai aikin gidan ne ba a gama ba, ina tantamar anya kuwa goben za,a je daukota din kuwa, k0 za, a daga ranar har in gama kammala gyaran gidan ne?“
Mamaki ya kama mahaifiyar tasa, amma dai tayi kokarin Boye zargin dake ranta, tace, “Amma me ya sanya ba ka sanar da mu ba tun jiyan ka ga harna aikawa mutane kuma duk kowa ya shirya tafiyar‘ shin ka gayawa iyayen Falmatan ma? Nasan suma can suna ta shirinsu",
Ya kwantar da kai yana fadin. . “Ki yi hakuri Hajiya, ni kaina banyi zaton za a sami akasin haka ba'. “To ka kirawo mahaifin nata ka sanar da shi, don kada suyi ta jiranmu Ya sosa keya yana fadin, .ki tainaka mana .kiyi masa bayani domin nauyinsa nakeji
Ta yi jim tana tantamar kada zarginta ya tabbata, amma dai sai ta ce, “Shi kenan zan kirawo shi din, kai kuma ka maida kai a kammala cikin satin nan”._
. Cike da farin ciki kamar an yi masa‘ albishir da gidan aljanna yace, “To Hajiya, na gode.
Da haka suka yi sallama, a take a nan ta .kirawo wayar Malam Abba Gana ta yi masa . bayani. Bai ji komai a ransa ba, yace “To Allah Ya nuna mana' sanda za a kammala, idan
an kammala din ' ' ’ . saiya sanar dani, sai a sanar dasu ranar da zasu zo dun
Suka yi sallama a mutunce, ya tattaro matan nasa yana sanar dasu maganar daga
tarewar Falmata. Yakolo da Basma suka kalli juna suka yi murmushia
Hajja Kaltum da mahaifiyar Falmata kam . ba su kawo komai a ransu ba 'suka ce dai Allah Ya kai mu lokacin kawai.
Falmata tana daki duk ranta babu dadi, domin tun jiya take sanya ran kiran wayar Mukhtar amma shiru, ga shi yau ma har gari ya Waye bai nemeta ba, haka nan ta daure ta tura masa sajo, don ance jiki da jini amma shiru bai ba ta amsa ba, bai kuma kirawota ba, hakan ya sosa mata rai, sai kuma ga labarin daga tariyar tata yazo kwatsam. '
Ta dan firgita da jin hakan, amma sai ta daure ta danne abin da ya dace ta tambaya bai wuce sai yaushe zata tare din ba yanzu, amma kuma kunya ba zata hana ta tambaya din ba.
Haka nan ta hakura ta ci gaba da zurawa wayarta ido ko Mukhtar zai kirawota ya gaya mata dalilin daga tariyar da aka yi.
Fatila kam an sami abin da ake so, don haka ta qara fito da salo da kissa kala-kala na
mallake maigidan nata.
Shi kam k0 tuno Falmata ba ya yi, duk sanda ta turo sako kuwa sai yaji wani takaici a ransa, bai iya dubawa ba sai ya goge kawai.
A haka kwanaki suka ja har sati guda,. mahaifiyarsa ma ta gaji da zura masa ido, don ’haka ta yanke shawar tuntuBarsa da maganar.
Falmata kam ta rude ta fita daga hayyacinta, zaman daki ya kuma auranta, tabbas son Mukhtar ya zame mata tashin hankali, ba ta san laifin da ta yi masa da ya zaBi wulakantata irin haka ba, domin ta yi masa sako yafi guda hamsin babu amsa, balle ta sanya ran zai kirata;
Yau tana gado ta nannade kanta son mijinta ke yawo a ranta, ga Yagana da ke dan debe mata kewa ta sami admission a jami’ar Maiduguri, ta fara zuwa makaranta, don haka ba koda yaushe take zuwa gurinta ba.
Ta dauko wayarta tana dubawa zuciyarta tana sanar da ita kawai ta kirawo shi taji dalilin da ya sanya yayi mata haka, wata zuciyar kuma tana gargadinta kada yana gida. Hawaye ya dinga biyo kumatunta, tama rasa abin da ya dace ta yi.
Can kawai sai ta yi shahada ta fara kiran layin. Bugu daya ta dauka, lokacin yana gida yana ta aiki bisa konfuta yana tura sakonni .akan 'wata tafiya da zasu yi anjima da daddare .. zuwa Sudan. Fatila tana gefensa ana ta zuba iya yi ta ji wayarsa ta fara kira, da sauri ta dauka, number ce babu suna don haka ta kara a kunnenta.
Ita kam Falmata jin an daga tayi wata ajiyar zuciya da hanzari ta manta k0 sallama ma bata yi ba, tace.
“Malam kana lafiya? Me nayi maka ka
shareni haka?” . ' “Wai wace ce ke magana ne? Kawai daga bugo waya sai ki kama surutu ratata ba tare da kin san k0 da wa kike magana ba, wace cc ke ne?”
Fatila ce ta ke maganar cikin Bacin rai, wani irin kishi yana yunkuro mata kamar zata mutu domin jin muryar Falmata kadai masifa ne a gurinta.
Jikin Falmata ya kama kyarma, domin daga ji babu tambaya matarshi ce da yake tsoro
kamar mutuwarsa. Da kyar ta daure tace “Nice Falmata, ki ba ni shi don Allah...”
“An Ki aba ki shi din” Ta katseta da zafin rai, ta ci gaba., “Banda ke Jaka ce tunda . kika ga ya share ki ai baya yi ne, meye kuma ‘na nacin kiran wayar tasa? Malama ki sama mama lafiya kinji k0, yanda kuka san yanda kuka yi kuka daura auran sai kusan yanda zaku yi ku warware, domin mijinaba ya neman matar shige”.
Wani irin abu mai zafi ya dinga yiwa Falmata yawo a ranta, daga can tana jiyo muryar Mukhtar yana fadin, “Wai keda wa kike fada ne Fatila?”
Ba ta tsaya jin amsar da zata ba shi ba ta kashe wayar tata, ta fada gado ta kuma sakin kuka domin dai ta kula a gabansa ne matarsa ke mata wannan cin zarafin, kuma lafiyarsa kalau kawai tsabagen wulakanci ne ya sanya ya
watsar da ita da rayuwarta.
rayuwarta? Tabbas ita son da take masa bana ' wani abu ba ne sai don Allah, yanzu yaya zata yi da ranta idan har Mukhtar ya barta ta shiga .uku, don sai yanzu ne ma take sonsa, take kuma son kasancewa tare da shi.
Soyayyarsu ta kwanaki ta dinga bijiro mata, ta toshe kai cikin filo tana kuka, tabbas tasan ciwon son Mukhtar ne zai kashe ta.
Kamar daga sama ta dinga jiyo ana kiran sunanta. Ta daga kai dasauri don ganin mai maganar, Yagana ce, sai ta fada jikin Yaganar tana kuka. Cikin tashin hankali Yagana ke tambayarta abin da ya faru.
Cikin kuka ta ce, “Yagana Mukhtar ba sona yake yi ba, wani abu yake bukata ashE a jikina tunda ya samu kuma shi ke nan ya watsar dani, yaya zan yi da raina? Ki taimake ni don Allah”. '
Hankalin Yagana ya tashi, amma dai ta daure tace, “Kinga kwantar da hankalinki ki sanar da mi abin da ya faru, ni shaida ce tabbas mijinki yana sonki, sai dai idan wani abu ne ya sanya ya yi miki abin da kike zargi, ki yi hakuri ki sanar da ni".
Ba ta Boye mata komai ba tun daga sakon da take tura masa har abin da Fatila ta yi mata yau.
Jikin Yagana ya yi sanyi, lallai da wa‘ta a Kasa, amma don kada ta kuma tayarwa kawar tata hankali ya sanya ta dake tace
“Amma kin ba ni mamaki, ke yanzu har zaki yarda da kaidin mace, ai wallahi gwara kisan yanda zaki zauna da mijinki, domin kishi ba a yinsa da wasa, kuma bana raba d'aya biyu duk abin da ya yi miki da sanya hannunta...”
Ta waro ido waje, tana fadin, “Kina nufin ita ce ta ke sanya shi yayi min?”
“Ki jiki, ai ba sai ta sanya ya yi miki ba za. a iya binsa ta karkashin kasa, kina jin fa abin da ake fadi akan matar tasa, kin san ba zata dauki lamarin da wasa ba, shawarar da zan baki ki mike da addu’a, idan ba haka ba kina ji kina gani malam Mukhtar zai kubuce miki, domin da alamu babu imani a tattare da matar tashi”.
Ta yi shiru tana sauraron maganganun Yagana cike da mamaki, can ta daure tace, “Wai Yagana kina nufin mutum kamar malam
sai a yi masa asiri ya kama shi, ki tuna irin
iliminsa na addini fa, mutumin da ke koyar da wasu ace an yi masa asiri kuma Yagana, ni fa ina ganin kawai daman biyan bukatarshi yake nema a gurina, kuma ya samu me zai zauna kuma ya yi min?”
“Kinji wautar taki ba, to Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wassalam ma anyi masa sannan ya kama shi balle wani malam, kuma ki sani irinsu asirin ma yafi cinsu, domin su gani suke kamar ba za a iya yi musu asirin ba, kina jin abin da ake fadi shi bai yarda matar tasa tana asiri ba ma, to ba sai ka yarda da abu ba sannan zaka dauki mataki akai ba, kuma da yawan malamai zaki ga Allah Yana jarabtarsu da shaidanun mata, har ki ga mutane suna ‘ mamakin yanda aka haihu a ragaya, ke dai ki dage da‘ addu’a kawai, amma tabbas malam yana sonki”. '
Maganganun Yagana sun dam karfafa mata gwiwarta, har ta rage zargin da take masa, ta kuma yi alkawan'n ganin bayan mai son raba ta da mijinta insha Allahu.
Hajiya Mariya kam ta kulu iyakacin kuluwa burinta Allah ya kawo shi yau, komai dare sai sun jeya nuna mata gidan taga me ya rage a gidan da yaketa yi mata yawo da hankali ne haka?
Tabbas zarginta ya fara zama gaskiya. domin ta kula yanzu ko maganar Falmata ba ya kaunar a yi masa, sai ka ga ya kama wani kwana-kwana, yau kam za ayi ta ta kare.
Sai dai me? Wajen isha’i ta jiyo kiran wayarsa, ta daga ranta a bace da kyar ta amsa gaisuwarshi, ya kwantar da murya yana fadin.
“Ki yi hakuri wallahi wata tafiya ce ta kama ni da gaggawa zuwa Sudan, yanzu haka muna filin jirgi nan da minti biyar jirginmu zai tashi, na so na shigo amma babu lokaci, don Allah kiyi haKuri”.
A kule tace“To idan ban yi hakuri ba Baba ya zan yi da kai? Tunda dai kai ka zama dan kanka yanzu yaushe zaku dawo kenan?”
Ya kalli abokan tafiyar tasa dake hawa
jirgi, ya ce, “Eh to, ba zance ga kwanakin da zamu yi ba, domin wani aiki ne na gaggawa ya taso amma dai bana jin zamu kai sati guda ma”.
Ta cc, “Shi ke nan, Allah Ya dawo da ku lafiya, amma ina fatan ka bar sallahun karashe aikin gidan nan k0?”
Ya ji wata irin faduwan gaba, ita dai Hajiya ba ta da magana sai ta tariyar nan, amma sai ya dake yace mata.
“Eh sun kusan kammalawa, ranar dana dawo washegari za a je a daukota, ki sanar da masu tafiyar su zama cikin shiri”.
' Wannan ya dan faranta ranta, har suka yi sallama cikin kwanciyar hankali.
*****************************
Abu kamar wasa karamar‘ ‘magana ta zama babba, domin tafiyar da aka ce ba za a kai sati daya ba sai ga shi an share wata guda‘ cur.
Falmata tafi kowa shiga damuwa, duk da iyayenta sun dan'fara damuwa amma tafi su, domin ko waya bai kira wani yace ga dalilin da ya hana shi zuwa ba, sai Hajiya Mariyan ce ke sanar dasu tafiyar da ya yi.
Ita kam kunyar duniya ta ishe ta, don tana gudun kada auren nan ya lalace a haka ta
Hmmm naga alamun mukhtar dinnan shima dan duniya ne da.
.
MATACCIYAR RAYUWA
CHAPTER 13
cuci yarinya, idan abin ya fad‘o mata har kwalla ta ke yi.
Falmata kam abu wasa-wasa tana dan ciwon kai da zazzaBi sai ga ciwo ya kwantar da ita magashiyan, mahaifiyarta ke fadan wai idan harta sanya namiji a ranta zata mutu a banza.
Ita kam kuka kawai take yi don ita kadai tasan abin da ta keji a. ranta game da Mukhtar, ga kuma azabar ciwo, su Hajja Yakolo kuwa murba ake ta yi da shewa, domin bokayensu sun tabbatar musu da a haka auren zai lalace, ba zata taba tarewa ba.
Abba Gana ya shiga damuwa musamman sanda aka ce masa Falmata babu lafiya, dama kwana biyu da ba taje gaishe shi ba duk ya damu, da kansa ya-nufi dakin nata, lokacin tana ta kelaya amai kamar ‘yan hanjinta zasu yo waje, mahaifiyarta tana tsaye a kanta cike da tashin hankali.
Kallo daya ya yi mata ya Kara shiga damuwa, cikin sauri yake fadin.
Subhanallahi Falmata ashe haka jikin naki yayi zafi
Ya maida dubansa ga mahaifiyarta yana ci gaba da fadin.
“Garin yaya kukayi sakaci har jikin nata ya yi haka Iyami?”
Ta dan kwaBe fuska tana fadin, “Ni fa na yi zaton kawai tunanin mijinta ta sanya a ranta ban yi zaton ciwon na gaske bane
Ya dan hasala yana fadin, “To idan ta yi tunanin mijin nata ai 'ba ta yi laifi babe k0 kin manta yau wata uku kenan da daura mata aure, duk ‘yan uwanta sun tare ita kuwa tana zaune, ai dole ta yi tunani da kika ga haka ai dacewa ya yi ki lallasheta ba wai ki tsangwame ta ba k0?”
Ta kwantar da kai tana fadin, “Tabbas na yi laifi, a yi hakuri malam”.
Ya dan sassauta murya yana fadin, “Shi kenan maza shiryata mu kai ta asibiti kada ciwon zuciya ya kamata a banza... Koda yake bari na yiwa Dr. Ibrahim waya idan ba shi da aiki yazo ya dubata”.
Ya zaro waya ' daga aljihunsa ya fara neman wayar Dr. Ibrahim, dai-dai lokacin da mahaifiyar tata ke gyara gurin da ta Bata.
Minti talatin Dr. Ibrahim ya shigo gidan, Malam din da kansa ya yi masa iso har dakin Falmata ya yi mata ‘yan tambayoyin da suka dace. Ya ce maza taje ta yo fnsari ta kawo masa. Bayan ya auna fitsarin ya yi mata allura da magunguna, sannan ya koma ya duba fitsarin ya yi rubutu bisa wata ‘yar farar takarda, ya nufi falon da Malam da Hajja Iyami ke zaune suna jiran sakamakon ciwon nata.
Dai-dai lokacin da Hajja Busma da Yakolo suka karaso dakin, tsegumi me ya kawo su. domin sun ga shigowar Dr. Ibrahim sun san babu lafiya ke nan, murna ta cika su, Hajja Yakolo ke fadin, “Allah Ya sanya ciwon zuciya ya kamata kowa ya huta, ai sai muga Karshen diyar so k0?”
Suka yi dariya suka tafa, sannan suka nufi sashin domin su ga kwaf, da sallama suka shigo fuskokinsu da damuwar Karya, Hajja Basma ce ta fara magana.
“Malam waye babu lafiya, yanzu take fada mana wai Dr. Ibrahim yazo ya shiga sashin Iyami, waye babu lafiya?”
Ya kalle su ganin yanayin da fuskokinsu suka nuna ya dauka har cikin ransu haka abin yake, don haka ya fara kora musu bayanin abin da ya faru. Hajja Iyami kam ba ta so hakan ba, domin tasan ba don Allah suka shigo ba,
munafurci ne ya shigo da su Yana tsaka da bayanin Dr Ibrahim ya
shigo dauke da takardar a hannunsa.
Malam ya mike da sauri ya tare shi yana fadin, “Yaya dai likita ba wani abu ne yaso taba zuciyarta ba k0?”
Likitan ya mika masa -‘yar takardar yana 'fadin, “Malam ai abin murba ne, babu wani ciwo a tattarc da ita, illa laulayin da mata suka
saba yi... “Laulayi? Kada dai kace ciki ne da ita?”
Hajja Basma ta katse shi da sauri. . ..
Dr. Ibrahim ya juyo ya kalleta da 'mamaki, domin yasan Falmata matar aure ce. tunda shi ma yana daya daga cikin wadanda suka shaida d‘aurin ‘auren amma sai ya gaza cewa komai ganin malam ya daka mata wata
uwar harara.
Ya kalli malam din yana fadin “Akaramakallah, ni zan wuce,Allah ya bamu alkhairi” .
Malam ya sanya hannu a aljihu yana zaro kudi yana fadin, “A’a malam Ibrahim tsaya ka amshi wannan ka zuba k0 da mai ne cikin
motarka”. Bai waigo ba yace, “A’a ka barshi kawai
malam, a yi mana addu’a”. Ya fice da sauri. Duk da hankalin Malam din a tashe yake bai hana shi daurewa ba ya‘hau Hajja Basma da fada, “Dake ake magana k0 dani? Wato rashin tarbiyyar sai kin nuna shi a ko’ina k0? To ku wuce ku bar; gurinnan. Suka wuce sumi-sumi kowacce tana cike .da mamaki da murna, sun dai san Falmata ba ta tare .ba, kuma mijinta bai taba daukarta sun je wani guri ba. Kai koma shine ya dauke ta suka jewani guri har ya yi mata ciki ai anyi abin ' kunya, 'balle suna da tabbacin ba cikinsa ba ne, sai gasu kowacce tana addu’a a ranta wai Allah ya sa cikin ya zama na shcge ne, in yaso suga karyar tarbiyyar da kullum ake kirawa Falmata,
su ‘ya’yansu da kullum ake kira marasa tarbiyya ba su kwaso abin kunya ba.
Suna fita Hajja Iyami ta fashe da kuka gami da faduwa ta bar cikin kujera tana fadin, “Na shiga uku ni Iyami, wane labari ne nake ji 'haka mai muni . da daga hankali? ~Amma Falmata.ta cuce ni, ashe duk tarbiyyar dana bai wa yarinyar nan zata iya cutata taje tayo-abin kimya?” .
Malam Abba Gana yace, “kin ji ki da 'wata maganar banza, kina tunanin Falmata zata iya cikin,shege ,ne? Duk fadin zuri’ata nasan Allah ba zai jarrabe ni da wannan mummunan abin ba, domin na kiyaye dokokin Allah, na tsarkake zuciyata, Allah ba zai taBa jarabtata da wamnnan mugun abu ba insha Allahu, muje gurinta muji abin da zata ce
Duk da hankalinta ya dan kwanta da kalamin mijinta, amma gabanta bai daina
faduwa ba har lokacin da suka isa dakin
Falmata. ...
Tana kwance bacci ya fara daukarta, da kakkausar murya mahaifiyarta ta yi kiran sunanta abin da ya sanya hankalima mugun
tashi ta bud‘e idon ta babu shiri, ganinsu su biyu ya kuma fadar mata da gaba ta mike da hanzari, sai dai kafin ta kai ga cewa wani abu hajja Iyami ta rigata. da“Uban waye ya yi miKi ciki Falmata...” Falmata dafe da kirji cike da tashin hankali tana fadin, “Ciki kuma Hajja a jikina?” “To karya zan miki amma. kin cuce ni Falmata...” Sai ta fashe da kuka, Malam ya daga mata hannu yana fadin.
“Kada ki Kara cewa komai Iyami”: Sannan ya nufi gefcn gadon da Falmata take kwacce ta waro ido waje a gigice kamar zata fasa ihu ya zauna ya kwantar da murya cikin ran shi yaje fadin.
“Falmata na baki tarbiyya mai kyau nasan ba zaki bani kunya ba ki gaya mim . gaskiya. Cikin jikinki na waye?"
Sai ta fashe da kuka ta kama rantsuwa, “Wallahi Abba ban taba bin wani namiji ba, nasan yanda kuke fadin illar ‘zina ka kawo kur’ani na dafa, idan na taba bin wani namiji Allah Ya tsine..."
Ya daga mata hannu, “Ya isa, nasan daman ba zaki taba bin wani namiji ba, ba kuma za ki bishi ba har abada, sai dai ina son ki gaya mini gaskiya, k0 kin taBa zuwa wata unguwa da Mukhtar ne?”
' Ta yi duru-duru da idonta, wannan shine _ ga koshi ga kuma kwana da yunwa, da kunya tace da iyayenta ta bishi, amma kuma fadin hakan ne zai wanke ta, taci gaba da kuka ta kasa magana. Abin da ya kuma tayarwa da mahaifiyarta hankali ke nan, da ace su Hajja Basma basu ~ji ba.ma da sauki, har su san yanda zasu yi .da Cikin, kamar daga sama ta jiyo muryarsa yana ci gaba da lallashin diyar tasu, abin da ke Kara kular da ita, ita kam da zai kyale ta ta rufeta da duka tafu fadin yanda akayi
“Ki yi tunani a nutse, tun daga sanda aka daura muku aure har kawo yau, k0 kin taba fita, ko kebewa da shi, ki kwantar da hankalinki ki gaya mini, Mukhtar mijinki ne da duniya ta shaida, babu wani wanda zai zarge ki akan komai, kin ji k0 Falmata?” Cikin rarrashi yake maganar.
Ta dan tsaida kukan tace, “Sanda ina gidan Yaya Bulama lokacin Anti Shafa ta haihu, yazo yace na raka shi gidan su zai gyara, har Anti Shafa ya tambaya tace muje kuma...” Ta kasa karasa maganar saboda kunya._
Malam din ya yi wata ajiyar zuciya yana fadin, “Masha Allah kin dai tabbatar da hakan k0, kuma Shafa ce shaidarki k0?”
Ta daga kai da sauri alamar eh.
Malam ya dubi' Hajja Iyami, ya ce, “Ki kirawo mini lambar Shafa’ atun mana” .
Da sauri ta nufi dakinta ta dauko wayarta ta dawo, ta fara neman layin wayar Shafa’ atu, ta yi sa’a bugu daya ta shiga ta mikawa malam
din. 'Daga can Bangaren Shafa’atun ke fadin;
“Hajja ina kwana, ya ya yara?” Malam din ya katse ta yana fadin, “Ba Iyami bace nine Abba. Na bugo ne na yi miki
wata tambaya”. Sai Shafa ta Kara nutsuwa tana gaishe
shi, ya amsa sannan ya dora da cewar, “Sanda Falmata tazo gidanki, wai mijinta yazo ya dauke ta 'har sunje gidansa k0? Ki gaya mini gaskiya Shafa’atu, domin ina cikin tashin hankali ne yanzu”.
Tuni Shafa ta gano abin da ke faruwa. Tunda dai ita din ba yarinya bace ba, daman tun kwanaki ta kula da Fa’mata na da ciki, sai dai ba ta son ta gaya mata ne hankalinta ya tashi, tafi so sai ta tare a gidan mijinta da ake ta sanya rana kullum ana dagawa. Da sauri tace
“Tabbas haka ne, Mukhtar yazo ya dauke ta a nan gidan da zummar zata taya shi ’ gyaran gidansa, har dare ya yi suka kwana a can, k0 yayanta ma ya sani ai”.
Malam din yace, “Masha Allahu, shike nan, na gode Shafa’atu, sai an jima”.
Ya kashe wayar. ya kalli Hajja Iyami, “Kin ji abin da nake gaya miki, kafin ka fara aiwatar da komai kayi bincike, kin dai ji da kunnenki k0?”
Ta yi ajiyar zuciya hankalinta ya fara kwanciya, da yake wayar a hannu bude ta ke, ya maida hankalinsa ga Falmata dake kuka, ya ce, “Kinga daina kuka, nasan ba zaki taba aikata abin da ba dai-dai ba bane ba, bari na
kirawo Muktarin”. Ya fara neman layin
' Mukhtar. Yana ofis dinsa yana tsaka da‘aiki,
kwanansa daya da dawowa daga tafiyar da yayi Sudan kiran malam ya shigo wayarsa, kunya mai tsanani ta kama shi. ga shi ba zai iya kin daukar wayar ba, don haka ya dauka hannunsa yana raWa, cike da kunya ya gaishe da malam din. . Babu wani sauyi a muryarsa ya amsa, ya dira da cewar, “Malam Mukhtar, daman
matarka ce babu lafiya har likita yazo ya dubata, yace tana da juna biyu shine na bugo na sanar da kai, k0 kaima ka sani ne?”
Kunya ta sake kama shi, ya kasa cewa kOmai har sai da malam Abba Gana ya sake
maimaita masa tambayar da fadin.
“Shin k0 ba cikinka bane Mukhtar? Ka sanar dani: gaskiya”
Nan da nan ya dawo hayyacinsa. da sauri yace, Malam ayi hakuri tabbas cikina ne. 'nayi kuskure ne kada aga laifinta, nine mai laifin, .amma babu makawa nine mutum na
farko data taba sani a rayuwarta”.
Hankalin malam ya kwanta ya yi wata .
wawuyar ajiyar zuciya yana fadin.
“Masha Allahu, kada ka damu, ai " ' Falmata matarka ce komai kayi babu mai ,,
tambayarka, ai daura aure shi ne gaba da
komai, ka dai yi kokari ka kammala gidan ta tare ta haihu a dakinta, ka ji k0?”
Da sauru' yace, “Insha Allah malam, a kara yin hakuri dai. Ita ma a bata hakuri zan shigo cikin satin nan insha Allahu”.
Da haka suka yi sallama ya kalli Iyami ’
da hankalinta ya kwanta, wani irin farin ciki ya rufe ta, ya ce.
“Kin ga abin da nake gaya miki k0? To ki kula da ita”. Ya maida dubansa ga Falmata da kunya ta hanata daga kanta, cikin farin ciki yake fadin.
“Ki kwantar da hankalinki ki daina kuka,
ba ki yi wani abin kunya ba, zan Kara neman " mahaifiyarsa mu yi magana sosai, Allah Ya yi .,
miki albarka ameen” .
Ya sa kai ya fice, hajja Iyami tayi dan Jim kamar zata ce wani abu sai kuma ta fasa tabi malam din da sauri.
A falo ta tadda shi yana shirin ficewa tace, “Abba ina da magana”.
Ya tsaya gami da juyowa, ta karaso kusa ‘ da shi da ladabi a muryarta, tace
“Ya dace a sanar dasu Hajja Basma halin da ake ciki, domin kada a sauyawa maganar fahimta”.
Ya girgiza kai yana fadin, “Wannan haka yake, zan tura a kirawo su yanzu, ki taddani a sashina kema, amma ki fara bata magunguna ta sha”.
Ta amsa da toh, sannan ta koma dakin da Falmata ta ke, ita kam Falmata cikin kunya da nauyi ta amshi magungunan ta sha, bayan fitar mahaifiyarta ta koma gado ta kwanta, amma ta gaza lallashin kanta, tausayin kanta da rayuwarta ya cikata ta yaya ta yi sakaci har wannan abu ya auku a kanta? Ta toshe kanta cikin filo ta fashe da kuka, domin ba ta son mahaifiyarta ta jiyo sautin kukanta, sai da ta yi mai isarta sannan ta shiga bandaki ta wanke fuskarta tana cike da fata da addu’ar kiran Mukhtar a kowane lokaci.
Ta dawo ta zauna tsakiyar gado ta zurawa wayarta ido jira take ta ji ya kirawo ta cike da murna da doki domin dai bai taBa haihuwa ba, tabba's dole zai yi murna .da wannan cikin, wata kila zata iya cin darajarsa ma ya yafe mata laifin da tayi, wanda ba ta sani ba. Sai dai ga dukkan alamu baShi da niyyar kiran nata.
Shi kam yana can ofis murna ta cika shi, da gaske Falmata tana da ciki? Tabbas da ya kasance mutum mai sa’a idan har ya samu da a wannan lokacin da ya fidda rai da shi. Ya janyo wayarsa da sauri da zummar kiranta, amma sai wani haushi da tsanarta ya cika masa ransa, ya rasa laifin da ta yi masa yake jin haushinta haka, tabbas yana neman taimakon Allah a kanta. Ya tashi ya kama sintiri a ofis din nasa gaba daya ya kasa yin komai, amma ransa ya cika da soyayyar abin dake cikin Falmata ko waye ma haka ya dinga zagaye dakin.
Daga karshe sai ya fara ambaton sunan Allah, domin Ya kawo masa dauki a bisa Wannan halin da ya shiga ciki.
************************
Malam da kansa ya kirawo Hajiya Mariya cike da tsananin kunya ta dauki wayar, kafin yace wani abu ta fashe masa da kuka cike da tashin hankali ya fara fadin.
“Subhanallahi, Mariya me ya faru haka?”
Cikin kuka ta ce, “Tabbas tsinanniyar matarsa ta‘yi mugun aiki a kansa, ta yi masa farrako, domin daya daga cikin masu aikinta ta tabbatar min da hakan. Ban san yaya zan yi da ita ba, kunya ta sanya na kasa kiranka kullum addu’a nake yi malam, amma abun Kara gaba yake yi”.
Malam yace“Ashsha, ki daina fadin haka, ina ce a baya ne ma kika ce ya yi auren ma yaKi yi, ai kuwa addu’a tayi aiki, ki daina fadin irin wannan maganr kada kiyi sabo. Yanzu ma bugowa nayi na gaya miki tasirin da addu’ar ta yi, domin babu wanda ya isa ya hana Allah ikonSa. Yanzu haka Falmata tana dauke da cikin Mukhtari, zuwan da ya yi kwanaki ya dauke ta suka fita, ashe har rabo ya shiga tsakanin...”
“Kana nufm ciki ne da Falmata? Kai masha Allahu, alhamdu lillahi, malam ku shirya kayanta jibi zamu zo mu tafi da ita, domin jiya na je gidan nasa na sanya a kammala duk abin da ya rage. Sam ban san ya dawo'ba ma tunda bai neme ni ba kwata-kwata, amma ina nan tafe jibi insha Allahu”.
Hankalin Malam din ya kwanta, yace “To Allah Ya kawo ku lafiya, amma ku bi komai a sannu, ni ma a nan zan yi wani dan kokarin insha Allahu”. Da haka suka yi sallama. .
Cikin kwanakin nan biyu aka gama shiri ganga-ganga domin tafiya babu fashi da ikon Allah' inji Hajiya Mariya, malam ya dukufa addu’a kamar yanda matansa su Hajja Basma suka dukufa bin bokayensu da malamansu, suna gani maganar tariyar ta tashi, amma Allah ya fito da ita. _
Tun da sassafe ‘yan daukar amarya suka iso, domin jirgi suka biyo, mutane shida ne nan da nan aka fara. shirye-shirycmen karrama su. Falmata kam labarin bai yi mata dadi ba, domin tasan ba da yawun Mukhtar aka zo daukar nata ba,
Hmmm su hajja basma sun takura fa shin zasuci nasara a wannan karon ko kuwa mu tara domin ci gaba da sauraron wannan qayataccen littafin.

MATACCIYAR RAYUWA

CHAPTER 14

amma ya ya ta iya da ranta? Ko domin ta ga ta haihu a dakin mijinta cikin rufIn Asiri ta yadda ta amince.
Washegari waJEN karfe biyar na yamma jirginsu ya daga, Falmata na ta zabga kuka a ranta tana jin kamar kurkuku za a kai ta, domin a yanzu ta gano Mukhtar bai sonta, ‘yan‘ . uwansa ne suka zo daukarta. Hajiya Mariya kam tana can tana shirin saukar surukarta. .
Jirginsu bai yi awa guda da tashi ba na Mukhtar ya sauka a garin, domin tunda garin Allah ya waye yau ya ji kamar an cire masa wani kulli daga zuciyarsa, Falmata kawai yake son gani, kai tsaye gidansu ya yi masauki.
Ya yi sa’a kuwa malam Abba-gana yana gida, don haka kai tsaye falonsa aka yi masa masauki, ya tadda shi a zaune akan kujera yana duba wani littafin addini, ya shiga da sallama kansa yana Kasa. Ya karasa kuSa da shi ya zauna akan kafet.
Fuskar Malam din ta fadada da fara’a, ya ajiye littafin yana fadin, “Lale marhabin da angon Falmata”.
Kunya ta kuma kama shi, ji yake kamar kaga ta tsage ya shige don kunya. A haka ya gaida malam din, ya amsa yana tsokanarshi .daga nan ya yi shiru yana raba ido ta ina ya . dace ya fara, yana son tambayar Falmata da abin dake cikinta, amma ta yaya? Kula da hakan da Malam din ya yi ya sanya yace. “Garin yaya ka bari jirgin nasu ya tashi baku tafi tare ba, ko makara ka yi ne?” Ya kalli malam din da rashin fahimta, da kyar yace, “Tafiya suka yi ke nan Malam?” Abinda malam yake son ji kenan don haka yace “Ai na yi zaton kasan da maganar tariyar Falmatan, da Hajiyarka ta turo aka d‘auke ta? Ai ina jin yanzu ma sun isa Kano ‘ ma . Ya Hayyu Ya Kayyum. ya ambata kafin
ya iy‘a cewa, “Hajiya ba ta sanar dani ba, daman ni ma zuwa na yi na tafi da su, hakan yayi kyau, sai dai ina kara neman‘ afuwark‘ malam. A yi hakuri don Allah akasi ne aka samu”.
Malam ya yi dariya yana fadin, “Kada ka damn Mukhtari, kai dai ka dinga yawaita yin
addu’a da neman tsari a duk wasu lamuranka na
rayuwa, amma mu ba ka yi mana wani laifi ba,
Allah Ya yi muku albarka, Ya ba ku zuri’a ta gari. Zaka koma yau din ne k0 sai gobe?
“Ai yau ya dace na koma, don kada a kaita ita daya, kuma komawar tawa ce zata zama ban hakuri ga Hajiyar tawa. Zan je na duba k0 zan sami jirgi idan bazan samu ba zan bi mota”. . '
Da haka suka yi sallama, malam Abba gana yana ta yi masa addu’a da nasiha. Shi kam wani irin dadi yake ji a ransa na son ganin Falmata da bebinsa a cikinta k0 yaya, ta koma yanzu? Yanayin yanda yake ta doki ya bai wa malam din mamaki, koda yake ba a ja da ikon Allah, kuma Shi ne Ya cc a rake Shi zai amsa, don'haka malam ya roke Shi da kyakkyawar niyya-, ga shi kuma Ya amsa masa, ya kawar da duk wani' surkulle’ da binne-binnen su Fatila da su Yakolo
Su Hajja Yakolo kam kamar za su mutu d‘omin abin biyu ya hade musu, ga karyewar aikin d‘a suka yi, sannan ga hana su ‘zuwa ganin kwaf da aka yi, domin malam din yace babu
inda za a je dasu. Wannan abu ya yi musu ciwo, sai kuma ga wani karin abin takaicin domin a daren Yakura ta dako yaji don ‘ya’yan gidan sun mata duka ga laulayi da take fama da~ shi, wannan shi ne takaici goma da ashirin.
FALMATA A KANO
Falmata ta dawo Kano karo na biyu da cikar burin auren masoyinta Mukhtar, sai dai ba ta sani ba k0 zata sami cikar burinta ko a’a. Wannan kam shi keba ta tsoro, sai dai ta tadda soyayya a gurin uwar mijinta da sauran ‘yan uwansa, wannan ya dan wanke mata zuciya, haka nan aka shiga ina aka saka da su. Hajiya Mariya bakinta kamar gonar auduga, sai da aka dinga tambayar Falmata abin da ta ke son,ta.ci ma, hakan ya dinga bata kunya, domin alama ce da sun sami labarin tana da juna biyu.
Washegari tunda safe ‘yan rakiyarta suka je suka gano gidan nata, daga nan aka yi musu jagora gun da ake sayar da kaya na garari, Chedi suka nufa suka dandatsawa Falmata kayan daki, tabbas an kawata gidan kamar diyar Wani Sarki.
Da sassafe Dr. Mukhtar ya iso gidan cikin hadaddiyar kuma dakakkiyar Ghalila sai wani kyalli yake yi.
' Hajiyarsa tana falo suna kallo da sauran ‘ya’yan gidan ya shiga da sallama, duk da ta ji dadin zuwan nasa sai ta basar ta kawar da kanta ' gefe da kyar ta iya amSa sallamar ma. Ya isa ya zauna kusa da ita yana gaisheta. Da jyar ta iya . amsawa tana wani share shi, hakan ya qara fadar masa da gaba da kyar ya daure ya fara magana. ' '
“Ki yi hakuri mun sami saBani ne, domin sanda na isa mu taho da Falmata na tadda sun taho... , “Kada ka raina min hankali, kana nufin karya Zaka yi min? To tsaya ka ji na gaya maka, ban dauko Falmata don ta tare a gidanka , ba nan zata yi'zamanta har sanda Allah zai sauke ta lafiya ka sauwake mata aurenka ta auri mai sonta, kuma a cikin gidan nan”.
‘ Hankalinsa ya tashi da sauri yace, “Subhanallahi, don Allah ki yi hakuri, wallahi ki tambayi malam Abba ki ji, a hanya na kwana ma, nasan nayi laifi amma don Allah a yi mini afuwa”.
‘ Ya marairaice murya yana ta bata hakuri, .abin da yake kwararta kenan, dashi da zarar yaga ta yi fushi zai kwantar da kai ya yi ta bada hakuri kamar zai mata sujjada. Da kyar ta ce, “Komai ya wuce”.
Ya yi zaune burinsa tace ya shiga ya ga
Falmatan, amma kememe ta qiya, domin tasan abin da yake so kenan. Ya dinga satar kallon kofar dakin baccinta k0 zai yi katari ta leko amma shiru, har Hajiya Mariya ta gaji da zaman nasa ta ce. “Kazo ka wani sanya ni a gaba,. ka tashi ka bani guri, domin yanzu bakina zasu dawo. daga kasuwa, kuma bana son binbini idan lokacin da ya dace na neme ka ya yi zankira wayarka".
Kamar ya fasa ihu jin abin da tace tabbas an yi niyyar gasa shi kenan, ga shi daga jiya zuwa yau wata irin kaunar Falmata ke yawo a ransa kamar zai fasa zuciyarrsa ta
Sullo. Ya miqe salo-salo ya nufi kofa gwiwarsa duk tayi sanyi ‘ yaji mahaifiyar tashi ba fadin
“Saura kuma ka je ka gayawa ‘yar mulkin naka an kawo Falmata, ka bari sai ta tare tukunna”.
Da sauri ya juyo yace “Insha Allahu ba zan sanar da ita ba Hajiya”.
Ya fice jiki sanyi kalau, yana waige.
' Falmata kenabn duk abin da ya faru akan . idonta,akai domin tunda ta jiyo sallamarsa ta gane muryarsa ta taso da sauri ta laBe jikin labule.. Tabbas ta so ace Hajiyar ta Kyale shi k0 'gaisaWa ne su yi, haka nan ta koma cikin dakin sumi-sumi ta zauna, maganar Hajiyar na mata . yawo a kunne, wai dole anan zata zauna, idan ta . haihu a raba auren a aura mata wani. Shin sun , san' irin n son da take yiwa Mukhtar kuwa? Ita kam ta amince a kyale ta da mijinta ko yaya ne tunda yana sonta, zata yi ta masa addu’a Allah ,Yajuyo mata da hankalinsa kanta. Washegari tunda safe 'suka yi haramar ' komawa, sun so tun a daren su kai Falmata dakinta, sai dai Hajiya tace su kyale ta akwai , wani gyara da zata yi mata, inyaso daga baya ' ‘yan uwa na nan sa kai ta.
Sanda suke shirinsu gaba daya hankalin Falmata ya tashi, gani' ta ke kamar idan suka tafi ba zata kara ganinsu ba. Rarrashin da Hajiya Mariya ke mata ne ya sanya ta yi kokarin Boye damuwarta, amma zuciyarta cike ta ke da tashin hankali matuka, tana ji tana gani suka tafi, sai a sannan kuka yazo mata.
** ** **
Kwanakinta uku a gidan nan duk wani jin dadi da kulawa tana samunsa daga gurin . Hajiya, kullum sai an tsare ta an bata ruwan rubutu ta sha da wasu turaruka da aka yi mata addu’o’i na karya sammu. Ita da kanta tana jin dadin jikinta matuka, don ma dai sunkayi ya sanyata a gaba kullum sai an yi mata wani abu na kwadai. Hajiyar takan tsare‘ta da tambayar abin da ta keso a dafa mata, kunya 'ba ta barinta ta iya fada.
Shi kam Dr. Mukhtar ya gamu da sintiri, kafin ya wuce ofls sai ya biyo, bayan ya dawo ma sai ya biyo. Mahaiflyarshi kam ranta yana yin sanyi da hakan, domin dai rabon da ta more ganin danta irin wannan akai-akai tun kafin ya
auri Fatila, amma taKi nuna masa yanda ta keji din. Sai dai ma ta dinga share shi tana dauke kai, ga shi taKi yadda ya ga Falmata, shi rashin ganin nata ne yafi daga masa hankali, ga. shi kullum sonta karuwa yake yi a cikin ransa, domin kullum ana kuma karya wasu sammukan ne na jikinsa. Idan yazi sai ya shantake ya yi ta hira yana kame-kame, duk wanda ke gidan kam abin ya zame masa bako.
Sai dai a Bangaren Fatila duk hankalinta ya tashi ganin mijin nata yana yin dare a waje, tun tana binshi da kissa har abin ya kai ta bango, domin yau dai ya kai kusan goma da rabi‘ na dare sannan ya shi’go gidan. Ta yi kwalliya har ta gaji ta tuge domin sai tsaki ta ke ja, tana jiyo horn dinshi ta Kara hade rai kamar ta ji sakon mutuwa. Ya shigo‘ da sallama maimakon ta amsa sai wata uwar harara data wurga masa kamar idonta zai fadi. Sarai ya kula da abin da ta yi din amma sai ya share ta ya wuce yana fadin.
“Madam har yanzu ba ki yi bacci ba kenan?”
Bai jira ta ba shi amsa ba ya wuce sashinsa. Ta mike da sauri' ta bi bayansa ta tadda shi yana Balle botiran hannun riga. Ta tsaya a kansa kerere kamar zata rufe shi da duka tace
“Wai Mukhtar me kake nufi ne dani, iye?”
Ya daga kai ya kalleta sarai yasan abin da take nufi, amma sai ya basar yace, “Yanzu na dawo babu wani sannu da zuwa balle ki dan kawo min ruwa na sha, kin tsare ni da masifa kamar wani danki. Shin haka ya dace ki tarbe ni?”
Ta kuma hasala cike da mamakin maganarsa tace Ka ga bana son rainin wayo, wai daga ina kake ne ma a wannan daren?”
Ya kalle ta kamar ba zai yi magana ba, sai kuma ya dake ya ce, “Kin damu kanki bayan na gaya miki aiki ke tsare ni a OfiS, idan na tashi kuma nake wucewa can babban gida, shin kina tunanin zan iya zuwa wani guri na jima haka ne Fatila?” '
Maimakon ta sauko sai ta kuma hawa. domin idan akwai abin da ta tsana bai wuce yace ya je gidansu ba, don yawan kulafucin gidan nashi shike karya mata duk wani shirinta, domin mahaiflyarsa ta dinga ba shi ruwan "addu’o’i na karya sammu kenan har ta lalata mata aikinta. ,
. A hasale tace, “Wannan bai dace ba, ta yaya zaka ajiye ni a gida ka dinga wani tafiya -' gidanku, idan haka ne ni ma ai muna da gidan ko? Gaskiya ba zan dinga yadda da wannan , rashin adalcin ba, ace ka fita tun safe sai dare zaka shigo mini, wannan cuta ce karara”.
_ Mitar tata ta ishe shi, domin babu abin da ' yake‘so illa ya watsa ruwa ya kwanta ya yi ' tunanin Falmata da bebinsa don haka cikin tsawa yace mata.~ _ .
"‘Don Allah ki kyale ni na huta Fatila, -idan ba haka ba wallahi zan fice na bar miki gidan‘ na tafi can gidanmu na kwana. Haba mace sai shegiyar mita kamar. makauniya?”
Jin' haka ya sanya ta yin shiry, domin tasan -zai iya tafiya din, don idan ya birkice mata irin haka tabbas aikinta ya fara girgidi kenan, don haka dole taja bakinta ta yi shiru, amma zuciyana tana tukuki, tsoronta d‘aya ma
kada yarinyar nan da suka aura masa ta dwo ransa tunda har yau bai sanar da ita ya saketa ba, ita kuma ba ta son ta yi masa maganarta, don kada ta tsokanowa kanta abin 'dazai hanata bacci, haka nan ta hakura ta Kyale shi da zummar gobe ta nemi Diyana su san yaya zasu Bullowa abin.
Kwanaki bakwai cur ya gama iyakacin kaguwa, son Falmata ya cika ransa ya tunbatsa rashin ganinta ya zame masa wani miki da ke cin ransa ga rigima kullum shi da Fatila, har C.I.D ta sanya a gano mata inda yake yin dare aka tabbatar mata da gidansu yake tafiya, ga shi kullum aikin ake yi 'mata amma a banza kamar an shuka dusa abin duk ya cakare mata.
Yau kam hakurinshi ya kai karshe, matarshi yake bukatar gani, ya kuma tabbatar dole yau ya roqi a bashi ikon koda ganinta ne, daga ofls sai da ya koma gida ya yi wanka sanda zai fita rikici suk yi sosai da Fatila tana tabbatar masa da yana fita zata fita ita ma don ta gaji. _ Ya watsa mata wata harara yace, “Ida‘n kin fita ba da izinina ba ai kin san mala’iku tsine miki zasu yi k0? Ki yi duk abin da kike so, amma hakan ba zai hanani zuwa gurin mahaiflyata ba”.
Ta kulu matuqa, sai dai kafln ta kai ga cewa wani abu ya wuce da sauri ya barta a nan. Ta yi shiru cike da takaici kamar ta bishi sai ta fasa, ba wai don tsoron tsinuwar Mala’iku ba, a’a sai don tana son jin abin da Diyana zata ba ta shawara akai. Ta janyo wayarta ta fara neman layin Diyana din.
Ta daga tana dariya tana fadin"‘Mukhtar din ne k0? Kai Fatila kina tare da wahala, namiji daya tal yayi ta kodaki haka ba ki yin sati cikin kwanciyar hankali fa, to wai ki yada kwallon mangwaro mana k0 Kudaje sa daina binki.
Kamar ta kurmawa Diyana ashar, amma
ta dake dai a fusace tace “Ai kin fi kowa sanin yanda nake son Mukhtar k0? Kuma kin san shi din ya bambanta da sauran maza, ko ke kanki kina yaba shi da komai nasa, shin kina tunanin zan iya rabuwa da shi na zauna lafiya ne? Son Mukhtar ya zame min bala’i da shi na rayu a zuciyata shi ne ma ya sanya ni kasa kallon koWane‘ namiji da gashin arziki, don haka neman mafita kawai zaki taya ni, tunda wancan Bataccen bokan ya debar mini wasu kwanaki da nake ganin kamar numfashina ba . zai iya riskarsu ba saboda nisa”. ' ’°' Diyana 'ta fashe da dariya, tana fadin, "‘Sheg‘en kishinki ne ya yi Yawa Fatila, amma ai kin san dai duk sintirin da Mukhtar yake yi . ' gidansu bai isa ya auri uwar tasa ba ko kuma ita ' duk wani asiri da aka ce tana yi nata janye hankalinsa kanki ba ta isa su kwanta gado guda ba k0? Ki kwantar da hankalinki kiga iyakacin ‘ gudun ruwansa mana, 'tunda dai boka ya tabbatar miki da har abada bai isa ya kalli wata mace da sunan so ba balle har ta kai su ga aure ' ko ya kwanta da ita ba. Ya sha gaya miki 'mijinki yana da wahalar sha,’ani yana yawaita karya aikin da aka yi masa ba irin mazajenmu ba ne ba wadanda ibadar ma bata wadace su ba,balle har su yi wata addu’ar kirki da zata lalata mana aiki ba”. Ta kwantar da kai ta feso huci mai ciwo tana fadin, “To wai me kike nufi nayi kenan yanzu? Shin Zuba masa ido zan yi, wata katuwa da ta gama cin moriyar mijinta ta raba ni da nawa mijin ke nan?”
“Ina baki kina Kin amsa, duk jidalin Hajiya Mariya 'iyakacinta hirar baki da Mukhtari, idan kika kwantar da hankalinki kika ja shi a jiki sai kin ji duk‘wani abu da ta ke kullawa, kinga lalata shirin nata zaizo da sauKi k0?” '
Ta girgiza kai, “Haka, ne, sai dai lna ganin kafin sanda buqatar zata biya zuciyata ba zata buga ba, kin san fa yanda nakeson Mukhtar k0?”
“To ai saiki yi, ana kai ki kina dawowa, duk wani abu da zaki yi na asiri kinyi a banza ba kuma sai ki gwada baiwar kissa da kisisina ba, kishi ai kowa ma yana da shi, idan baki yi da gaskcme ba zaki rasa mijinki a wannan karon".
Jikin Fatila ya yi sanyi, ita kam ba ta san ta inda zata fara ba, yaushe zata yadda mijinta ace wata tsohuwa ke juya mata shi, amma yaya
ta iya, dole ta bi shawarar Diyana din.
*************************
Ya yi sa’a sanda ya isa gidansu sai ‘yan samarin gidan kawai ya gani a falo suna kallo, suka gaishe shi ya amsa, sannan ya tambaye su Hajiya. Nan suka sanar da shi ta tafl gidan Inna Zulaihatun da ‘yan uwa (yayanta)
Wani irin farin ciki ya kama shi, kamar ya tashi ya taka rawa~ amma ganin kannen nasa a gurin ya sanya ya dan dake ya shige da saurinsa, kannen nasa suka bishi da kallo. Sanda ya shiga suka fashe da dariya.
Rabi’u me yace, “Ka ga man din nan kamar Fatila ba ta duniyar har yana rawar kafar son wata”.
Hamisu ya ce, “A toh, ai daman nasan komai dadewa sai Allah Ya tona mata asiri, ka manta sharrin da ta taBa kulla min kawai daga naje irin gidan yayana' tace wai ina shigar mata har dakin bacci yazi nan ya dinga min bala’i ban da Hajiya na gurin ma ina jin dukana zai yi, shi bai san ba ta son kowa yaje gidansa. babe, amma yanzu tunda an auri yar uwarmu ai ka ga babu shegen da ya isa ya yi mana iyaka da gidan dan uwanmu”.
.
MATACCIYAR RAYUWA
CHAPTER 15
Shi kam kai tsaye dakin da aka yiwa Falmata masauki ya nufa. Tana kwance akan gado rigingine kunnenta sanye da headphone ta . lumshe ido tana sauraron, karatun Sheik Sudeis cikin suratul Rahman karatun ke ratsata, tai tsam kamar tana bacci sai dai rabin hankalinta yana ga tunanin mijinta ne.
Ya dade a tsaye yana kallonta gaba daya ta sauya masa, kirjinta ya kara cika, fuskarta ta yi haske, Rugunta ya Kara fadi, sai yake ganin kamar ba Falmatansa ba, komai nata ya sauya
zuwa na cikakkiyar mace. ' Ya isa da sassarfa ya sarkafo ta, abin da ya sanya ta bud‘e ido a razané zata kurma ihu, kenan sai dai tuni ya toshe mata baki. Ta waro ido waje cike da tsoro sanda ta ga shi ne, ya kura mata ido wani abu yana sauka a ransa mai sanyi.
Ta runtse idonta cike da kunya mai tsanani, amma gabanta faduwa yake yi kada wani ya shigo ya tadda su a haka. Sun d‘auki tsawon lokaci a haka kowa ya kasa ccwa komai, da kyar ta daurc ta ce.
. “Kasan kowa yana iya shigowa dakin nan fa”.
“Sai me idan an shigo, ko kwartanci na shigooyi? Ashe haka kike Falmata ba ki da kirki?” Yana kokarin janye ta daga jikinsa suka tashi zaune.
Da sauri ta ce, “Lah! Me na yi maka? Ka yi hakuri don Allah”.
Ya yi dariya, “Ai kin san laifinki, kullum sai na shigo gidan nan sau uku k0 hudu amma anKi barni na ganki, ke kuma kika Ki satar jiki ki fito mu hadu, ga wayarki kin kashe, haba Falmata kin kyauta mini kuwa? Ina‘ son na ji , numfashin diyana amma kema kin biyewa Hajiya k0 kuma fushin kike yi dani?”
Ta sunkuyar da kanta wani abu mai sanyi yana ratsa jikinta, irin kalaman da ta ke bukata daga mijinta ke nan, ashe har. yanzu yana sonta? Farin ciki ya sanya idonta ya fara zubda hawayen dadi Sai dai ta runtse ido kam, ta kasa bud‘ewa, ya dinga bin hawayen nata yana lashewa a hankali. Gaba daya ya kashe mata jiki ya dinga yi mata wasu abubuwa dake Kara narkar mata da zuciya ta ma manta a inda suke
sam, ta shiga duniyar bege da soyayyar mijinta, ganin abin nashi na neman wuce gona da iri, ya sanya ta farkowa daga duniyar da suka shiga, don zata ji kunya wani ya taddasu a wannan halin.
Ta yi kokarin kwace kanta amma ya rike ta gam, ta kama kici-kicin kwacewa da ‘wata . raunanniyar murya da ta shagala yace “Ki barni don Allah na shaqi numfashin diyoyina, ba ki tausayina Falmata? Haba Falmata kina son sanya ni a wani hali ne ko’?”
Yanda yake maganar ke kara kashe mata jiki, da kyar ta iya ta maze ta ce, “Kasan fa . muna gidan Hajiya, don~Allahka kyale ni kada ta ji ka shigo dakina ta yi mini fada”.
Sai kawai ta fashe masa da kuka.
Ya kasa janye jikinshi daga gare ta, kamar yanda ya kasa lallashinta. Shi dai duk sanda ya hadu da yarinyar sai ya ji komai yana sanya shi farin ciki, tabbas wata baiwa ce ita a gare shi, ganin kukan yaqi karewa ya sanya ya janye ya koma gefe ya zauna ya zuba mata ido, ya yi tagumi da hannuwa biyu, duk kunya ta cikata kamar ta nutse a gurin. Yanayin
yanda yake kallonta ke kuma tsoratata, ya kwantar da kai yace, “Sai me? Ai na cika ki Ta kasa cewa .komai cikin kwantar da murya, yace “Fatima kina jin Hajiya tana son rabamu bayan muna son juna., don Allah ki daure ki ‘cire kunyarki kice mata kina son mijinki yanzu a cikin gidan nan akwai wanda za ki so sama dani ne? Ni fa ta sanya duk haushin mazan gidan nake ji ma”.
" ‘Dariya taso Kwace mata, lallai wannan mutumin idan yana wani abu sai ta ga kamar ba malam mai darasun Ba gaba daya ya sauya mata, ta dai kasa cewa komai.
Ya daga ido yana kallon agogo sha daya da kwata, ya dafe kai cike da fargaba, domin dai yasan duk inda Hajiyar take ta dawo gida kenan yanzu. ‘
Da tsoro yace “Fatima kika ki gaya min dare ya yi na gudu tun Hajiya ba ta rutsani ba, ‘ yanzu dai gaya mini zaki sanar da ita kina 'sona?”
Ta dan saci kallonsa tana cike da mamakinsa, cike da takaici, yace“Wai ke
kurma cc ne? To idan ba zaki ce kina sona ba ma ki ce akai ki gidan mijinki ta haka zata fuskanci kina sona”.
. Dariya ta so kamata yaushe zata iya irin wannan rashin kunyar? Ya matsa kusa da ita cikin kinnenta yace, “Shi ke nan zan yi ta zuba rashin kunya, idan suka ga ciki guda biyu ai sa kai mini matata, bari na gudu kada Hajiya ta kai karshe, sai da safe, ki yi mafarkina fa Fatima na .
Ya fice da sauri yana waigenta, ta bishi da kallo tana girgiza kai cike da murmushi, 'wani irin dadi yana bin gabobin jikinta, ashe dai mijinta yana sonta, sai ga ta tana daga hannu sama tana godiya ga Allah, sai ta ji kamar ta kirawo Yagana a waya ta sanar da ita abin da ya faru, domin ta -barota cike da damuwa ita ma, amma dai bari gari ya waye.
Gogan kam ya fita sadaf-sadaf da sandaaa. cike da farga‘ba yana ta addu’a Allah Ya sanya Hajiya ba tasan ya shigo ba, tana daki. Sai dai me? Kicibus ya yi da ita a falo tana kallo, ya tsaya turus cike da fargaba kamar ba zai ci gaba da tafiyarba, can ya dake ya ci gaba da tafiya
yana shafa gemunsa. Tabbas da akwai wata kofar da ta can zai wuce.
Sanda ya iso inda take ya daure yace, “Barka da hutawa Hajiya”.
Ta daga kai ta galla masa harara cike da takaicin yanda ya hurewa Falmata kunne, domin k0 minti goma bai yi da shiga ba ta dawo, samarin gidan ke gaya mata zuwansa, tayi zaune tana jiran ta ga fitowarsa, ko kuma ta ‘ ga Falmata ta fito a zuciye, sai dai shiru hakan ya nuna mata ya riga ya gama' kama wuyanta, abu mawuyaci ne ta bata hadin kai su ci gaba da wajiga shi.
’ Ya yi kasa da kansa ganin irin hararar da take wurga masa, ta ce, “Mutumin kawai, dube ka da gemu kamar mutumin kwarai, amma idan aka tona cikinka Kuda ba zai ci ba. Yanzu to me kake nufi? Ina ce cewa ka yi ba ka son yarinyar nan na je na daukota da zummar ta haihu shi ne ka.fara shiga kana hure mata kunne k0?” _
Ya yi kasa da kai cike da ladabi yace “Tuba nake Hajiya, wallahi ban taBa jin kin Fatima a zuciyata ba, k0 dana second guda ne,
sai dai nasan na tsinci kaina cikin wani kunci da takura a kwanakin da suka gabata, don Allah ki yi haquri ki ci gaba da mini addu’a kamar yanda kika saba, akwai shaidan cikin ‘lamarina da ita, amma tabbas ina sonta, ki yi haquxi”.
Tausayinsa ya so kamata, amma ta dake don batason badakai dawuri,tace,“Kaga shige ka bani waje,‘ ni ba Falmata bace da zaka yaudare ni‘da zakin bakinka. Ai daman Hamisu ya ce duk mai son a binne shi da ransa k0 a sanya zuciyarshi karaya ya saurari lafazinka, nasan da hakan ma ka yaudari diyar mutane, wuce ni ka bani guri ka ji k0".
Sumi-sumi ya fice cike da fargaba don ~ yasan halin Hajiyar tasu akwai ta da jajircewa akan abu, yana fita ta mike ta nufi dakin Falmata waccc ke kwance cike da nishadi da farin ciki, bude kofar ya sanya ta waigawa da sauri, suka yi ido biyu da Hajiya, duk sai kunya ta cikata, kamar kasa ta tsage ta shige da kyar ta iya daurewa tace
“Ashe kin dawo? Sannu da zuwa...“
“Yaushe za ki san daman na dawo? Ana
nemar miki martaba gurin mijinki kina yadda
da yaudararsa, kece kika ce yazo bana nan k0? tana sane ta yi mata haka
Da rawar murya Na rawa tace “Wallahi ba ni bace ba, kawai gani na yi ya shigo... ina ta cewa “ya fita ya kiya, don Allah kiyi hakuri”.
Dariya ta kamata, mace da mijinta amma take wannan rawar jikin, amma ta dake ta cc, “A’a ke ya dace na bai wa hakuri. Ai ban san kina son mijin kiba, ki shirya gobe za a kai ki gidan mijinki kowa ma ya huta”. Tana kaiwa nan ta fice
Hankalin Falmata ya tashi gaba daya, ta dafe kai tana fadin, “Na shiga uku, malam ya ja mini jidali yanda Hajiya ke kokari a kaina ya ja ta ga gazawata, har tana tunanin ni na kirawo shi a waya, da sam tama manta da ta yiwa kanta‘ alkawarin daina kiran wayarsa ta kirawo shi.
Ya shiga harabar gidansa ya ji kiranta, Allah Ya sanya bai dade da cireta daga diverd ba, da sauri ya faka motar ya dauki wayar har da kwantar da kujerar yana kashe murya, ya ce, “Hello amaryata yaya aka yi?”
.Sai ya ji ta fashe da kuka, tana fadin, “Ka cuce ni malam, ka sanya Hajiya tana ta yi mini fada, yanzu ma tace gobe dole za a kai ni gidanka, wai ta yi fushi da ni mai tsanani”.
Wani irin dadi ya kama shi kamar ya taka rawa ya ce, “Au to, me ye abin kuka? Ai ni gaba ta kai ni, da na san hakan zata ce ma ai da tuni na yi inrin haka din, kwantar da hankalinki, yarinya gidan masoyinki .za a kaiki na yi ta baki nama da juice a baki, k0 ‘yar amaryata?”
Wani malolon takaici ya tokare wuy’anta,‘ sai kawai ta kashe wayar da sauri tana ci gaba da kuka, ya biyota tana ta ringing amma ta Ki d‘agawa; daga karshe ma sai ta kashe wayar gaba daya ta yi wurgi da ita. Ta fada gado tana kuka, da wanne ido zata kalli ‘yan gidan da safe idan suka ji abin data aikata? Mutanen dake karramata da muumtata,.ita kam ta ga ta kanta, dole ta kirawo Yagana da sassafe ta gaya mata abin da kc faruwa. ',
***********************
Washegari tun da safe Hajiya ta fara yiwa ‘yan uwa waya‘tana sanar da‘su. Ita kam
Falmata ta kule a daki abin duniya duk ya isheta, ‘yar hirar da take fitowa suyi da Hajiyar ma yau dai ta kasa saboda kunya,_ ita kam Hajiya dariya kawai ta keyi a ranta,. da kuma kara jin soyayyar Falmata a ranta, tana ganin wannan ita ce mace ta gari da take yiwa danta fatan samu.
Shi ma Malam mai darasu yana ofis yana tsaka da aiki ya fara jiyo kiran Hajiyarsa, da sauri ya dauka cikin ladabi ya fara gaisheta, ya so ya shiga da safe ya gaishe su amma yana tsoron kyaran da zata yi masa, don haka dole ya samawa kansa lafiya ya wuce ofis din kawai.
“Ka je ka gyara gidan yau da daddare za a kawo maka matarka sai na huta da rashin kunya”.' ,
Tana fadin haka ta kashe wayar da sauri, malam mai darasu ya rasa wanneya dace ya yi murna k0 takaici domin dai a yanda Hajiyar ta yi masa magana ya kula kamar a kule ta ke yi, amma dai yasan ta bata da wuyar saukowa, don haka dai farin ciki ya dace ya yi. Ji ya yi kamar ya doka tsalle amma da yake manya ne sai ya daga hannu yana yiwa Allah godiya.
Sai ga malam ya fara tattara takardunsa zai bar ofis din, sai da ya fara biyawa OflS din abokinsa Dr. Shamsuddin yana dariya yace Kai malam zan wuce'gida, domin yau ina da sabuwar amarya a sabon gida”.
Dr. Shamsuddin ya fashe da dariya yana fadin, “Mai darasu a ji tsoron Allah, amaryar nan fa abar tausayi ce, ya dace ka sallami diyar mutane tun Fatila ba ta nakasata ba”.
Ya yi dariya yana fadin, “Kai dai ka sani, zan gayawa Fatila kana cikin ‘yan adawarta, don tunda na auri Falmata kake mimi”. “Ka yi. ta fada din, an gaya maka ina tsoronta ne, gidanta ma ba zuwa nake ba balle kace, ihe!” Da daga murya yake fada don ganin Malam mai darasu ya wuce da sauri, shi kam dariya ya kama yi yayi gaba.
Cikin wunin nan ya dinga zirga-zirga da gyare-gyaren gidan, gab da sallar magriba ya nufi gidan nasu domin doki ya hanashi sakat. Ya dinga leke-leke ko zai hango Falmata amma ko keyarta bai hango ba, sai abokan wasansa ne. ke tsokanarsa. Hajiya kam cewa ta yi, “Yauwa daman ina son magana da kai, zo nan".
Da saurinsa ya bita, a zatonsa fada zata yi masa, amma k0 fadan ne ya sanyawa ransa ba zai -ji haushi ba, domin yau ranar farin ciki ce a gare shi, sai ya ji maganar ta sha banban. Cikin kwantar da murya take magana.
“Ga Falmata nan amana ce na baka, ka dubi yanda mahaifinta ya girmama mu ya yi mana halacci ya ba mu ita, don Allah ka riketa da amana da daraja, kada ka ga auren hadi ne ka. wulakantata, sannan bana son ka sanar da matarka batun tarewar a yanzu saboda akwai wani shiri da nake yi, ka sanar da ita tafiya zaka yi har kayi sati dayan, duk sanda zaka je gidan Falmata ko sanar da ita tafuya zaka yi, kada ka sake ta sani har sai zuwa lokacin da ya dace ta sani din”.
Mamaki ya cika shi, don wannan doka ta Hajiyarsa ya rasa abin da suka dauki Fatila, shi dai yasan tana kishi mai tsanani wanda kuma yasan tsabar sonsa ne ya sanya ta ke kishinsa, amma yasan Su daukarta suke yi a mai asiri, shi kuwa ya san ba ta yi sam.
Haka ya fice daga gidan cike da zanccn zuci, sai ya ji duk ya kagu yaga Falmatan,
amma ganin babu fuska kuma dai yau za a kai masa ita ya sanya ya hakura ya fice kai tsaye gidansa ya nufa.
'.Su Fatila anci kwalliya an shirya'girki mai dadi na tarbar miji, daya daga abin dake kara sanya ta shiga ransa, akwaita da gyara da kula da duk wani abu da yake so abinci kam ta iya girkawa kala-kala, koda yake ai ‘yar gado ce. . '
Tana wata kwarkwasa ta tare shi, har ranshi yaji dadi, don haka ya bata kyakkyawar 'sumba. Sun jima a haka sannan suka wuce dakinsa. Yana cire kaya ya d’an saci kallonta, yace, “ansan abin dana samu? Wai visiting lacture a jami,ar Abuja, sai dai na gaya musu ba lallai ne su dinga samun yanda suke so ba, yanzu haka wani aiki aka tura ni a makaranta wai har Dubai sai yau ake sanar dani, ga shi karfe tara jirgin zai tashi ma".
Babu damuwa a ranta domin tasan duk ci gaban mijinta ne, sai ma ta tashi tana taya shi cire kayanshi har gindin motarshi ta raka shi. har ya fice daga gidan tana d’aga masa hannu, tafiyar tafi komai farin ciki a gare ta,
domin duk wani abu da zai hada shi da ‘yan uwansa ba ta kaunarsa k0 miskala zarratin.
************************
Hajiya kam ta shirya Falmata yanda ya dace da kayan tsari 'da komai, domin kuwa tasan k0 wace ce abokiyar zamanta, ita kam tunda aka fara shirin kaita ta ke kuka, domin tana ganin kamar ba ta kyauta ba abin da ta yi, sai da Hajiya ta lallashe ta tana sanar da ita, ta kwantar da hankalinta, tsokanarta ta keyi, fatan dai bai wuce ta zauna da mijinta lafiya ba, sannan taci gaba da yin addu’o’i na tsari da ma’,aiki ya bada, ta kauracewa jin kide-kide marasa kan-gado, wannan ne ya dan sanyaya ranta ta rage kukan, har aka fice da ita daga gidan.
Suna fita Hajiya ta daura alwala ta fara sallah tana sanar da Allah halin da take ciki na bakin cikin auren danta da Fatila tsawon shekaru goma sha hudu.
Shin
WACE CE FATILA NE?
Mu tara gobe donjin ko wacece ita

MATACCIYAR RAYUWA
CHAPTER 16
Asalin Hajiya Kumatu mutumiyar Katsina ce, sai dai aure ya tsallako dasu Kano, ita da maigidanta Alhaji Sada mai kwai, sana’arshi ke nan sayar da Kwai tun yana garin Katsina, ‘yan uwanshi basajin dadin aurensa da Hajiya Kumatu domin ba mutumiyar .arziqi bace ba, sai dai yanda ta mallake shi ya sanya kowa ya kyale shi, tunda iyayensa sun jima da rasuwa sai yayye domin shi ne karami.
A unguwar Tarauni suke zaune Allah Ya sanya masa wasila a harkar tasadon haka ya gina katon gida yana“ wadaqa da iyalansa. Hajiya Kumatu tana. mulkinta yanda ta so a gidan, cikin wannan halin Allah Ya doro masa karayar arziki ya zamana yau da kwai gobe babu, da yake Hajiya Kumatu ta karanci fannin girki har tayi diploma .ya sanya ta fara sana‘ar kek da yambal da meat pie da sauran dangin wadannan, kayan, wannan ya-sanya suka dan sami rufin asiri tunda ta fara a sa’a, shi kuma yaci gaba da fita yana zagawa kasuwa yana dan samo abin da ba za a rasa ba,
‘Ya’yansu uku ne‘ Fatila ce babba sai kannenta Hassan da Usaini sai Lariya wacce
Hajiya ke riko ‘yar Kanwarta, amma dai ba ‘yan biyu bane ba, duk wanda ya kwana ya hantse a unguwar yasan yanda Hajiya Kumatu ke mulki a gidan, sai abin da tace za a yi a gidan, gidan kuma sai ya kasance wata matattara ta samarin da basu da mafadi saboda su Hassan kam babu dama ne, ita kanta Fatila halinta kamar Hajiya kumatu ta yi kaki ta tofar ne, har ma kamanninta. Sun taso a shagwaBe, domin babu kwaBa balle hantara, tsakaninsu da gidan su Mukhtar gidaje hudu ne, sam babu wata mu’_amala a tsakaninsu, kasancewar su gidansu na malamai ne, don haka ake zaman doya da manja. Kusan duk unguwar ma haka suke zaune da gidan ‘Hajiyar Fatila.
Ita kam Fatila ta taso irin ‘yammatan nanne masu shegen girman kan tsiya da yanga, ga shi koda yaushe shigarta irin ta ‘ya’yan Turawa ce, hakan ya sanya koda yaushe zaka ga nigogin samari suna sintiri a kanta zuwa Unguwa a motar samari ba wani abu bane a. gurinta, sukan zugata da suna Fatila Senior hakan kuwa yana fasa mata kai
Sai dai ita tunda ta tashi Allah Ya jarrabe ta da Kaunar Mukhtar, wanda ko kallo ba ta ishe shi ba, ya taso nutsattse mai cike da tarbiyya, a nan B.U.K yake karatunsa na Islamic Studies dai-dai lokacin da Fatila ke karatunta a F.C.E, duk yanda ta so yiwa Mukhtar shisshigi ya kulata a banza hakan yana na kona mata rai a wannan hali ya kammala karatunsa na digiri na farko ya sami gurbin karatu na biyu a Jami’atul Madina, ya wuce abinsa ya bar Fatila da ciwon zuciya.
Wani hutu ya dawowanda ya yi dai-dai da shekararsa guda a Madina fatarshi ta murje ya yi kyau ya ajiye dan karamin gemu da saje wanda ya kara haskaka fuskarsa, har lokacin yana nan a dan gayensa, zaka yi zaton yana karantar medicine be ba Islamic ba saboda gayu. ‘ Wata rana ya fita daga gidansu da wani yammaci yana sanye da blue din wando jeans da farar T. Shir wacce aka rubuta da koren launi a gaban rigar, ‘I’am pround to be a muslim’, kansa ya sha taza da sajensa. Yana sanye da farin tabarau sai Kamshin turare ke tashi daga jikinsa. Gidan abokinsa Sani zai je dake makota da gidan su Fatila, suka ci karo ta fito ta dauki wankan yamma da wani dogon siket da ya kamata daga kugunta da' kasa,~ kuma ya bude sai wata ‘yar mitsitsiyar body hug da ta kamata, fara kal mai kwalliyar zaiba a jiki ta yafa siririn gyale da ya tsaya a kafadarta ta hau bisa dogon takalmi mai tsini ana tafe ana yada hannu.
Ta tsaya turus tana kallonsa, gabanta yana harbawa da sauri da sauri, shi kam kallo daya yayi mata ya dauke kansa, ita kuwa cikin rawar jiki tace.
“Yaya Mukhta: ina wuni?”
Ya juyo ya kalle ta da mamaki akan fuskarsa sosai, domin yasan ba abokiyar maganarsa bace ba, amma sai ya dake ya yace Lafiya lau”. Kawai ya wuce da sauri.
Ta bishi da kallo kirjinta na ci gaba da bugu kamar ta ruga da gudu ta kamo shi ta rungume, wani irin azababben so take yiwa Mukhtar wanda ya kulla shekaru k0 kusa ba ta gabansa, sai ta ji ba zata iya zuwa inda ta yi niyyar zuwa ba ma, don haka ta koma gida da sany’in jiki.
Hajiya Kumatu ta dame ta da tambayar abinda ya dawo da ita, sai ta ce kawai kanta ke mata ciwo, ta fada dakinta ta cusa kai cikin filo, dama zata iya yin kuka da ya fiye mata sauqi.
Kusan kwanaki uku kullum sai ta labe ta ganshi, wasa-wasa ciwon soyayya ya kwantar da ita, hankalin mahaifiyarta ya tashi matuka domin ‘yar lelenta ce.
Da wani yammaci ma suma ta kama yi, aka kwasheta sai asibiti, anyi mata duk gwajegwajen da ya dace, likita ya tabbatar jininta ne ya hau, idan kuwa aka yi sake zuciyarta na gab da kamuwa da ciwo, wannan labari ya dagula wa Hajiya Kumatu hankali ta tsare diyar tata har da kuka tana rokon ta sanar da ita abin ke sanyata wannan tunanin.
Fatila ta fashe da kuka tace, “Hajiya son Mukhtar ne ya haifar mini da wannan ciwon, na kula shi kuma ina cikin mutanen da yafi tsana da alama ko kallona baiyi ma”.
Hankalin Hajiya Kumatu ya kuma tashi, tace “Waye wannan Mukhtar din da har yake yawo da hankalinki, dan gidan uban waye da ba ki sanar dani an nemo miki sonshi k0 ta gurin boka bane?”
Cikin kuka tacc, “Momy babu abin da boka zai iya yi masa, domin dan gidan malam mai darasu ne, kin san gidansa gidan malamai ne...” Sai ta kuma fashewa da kuka.
Hankalin Hajiya Kumatu ya kara tashi, lallai sun dauko ruwan dafuwar kansu, amma dai ai sai an gWada akan san na kwarai. Ta taBa jin an ce wasu irin malaman nan anfi jin dadin yi musu asirin ma, domin sunfi maida‘ hankalinsu ga taimakon mutane ba kansu ba, balle shi Mukhtar da yake kamar dan boko, kuma wanda ake tsoron mahaifin nasa ya kwanta dama, don haka bai dace lokaci guda su sare ba. Ta dinga lallashin diyarta tana nuna mata babu abin da zaifi karfin .boka, zata je ta Sanardashi halin da ake ciki.
Sunyi kokarin buga.duk wani tsafinsu, amma a banza bai yi k0 kyas a zuciyar Mukhtar mai darasu ba, haka ya koma hutunsa ya bar Fatila da ciwon zuciya kamar zata haukace bai san tana yi ba.
Shckara daya ce da watanni zai kammala karatun nasa, don haka a cikin wannan shekarar kam Fatila bata sami kwanciyar hankali ba, don ta sha carry over ma a makaranta, hankalin Hajiya Kumatu ya tashi matuka, duk wata
hanya da zata kulla zumunci da gidan marigayi malam mai darasu ta bi, amma a banza, domin sai hali yazo daya ake abota.
Da wani' yammaci Hajiya Mariya tayi sallama cikin gidan su Hajiya Kumatu, Hajiyar taji abin a bazata ta mike har da rawarjiki tana fadin, “A ’a Hajiya a gidan namu? Sannu da
zuwa”. '
Hajiya Mariya ta sami guri ta zauna suka gaisa a mutumce, ta dora da cewar, “Daman Baba ne zai dawo jibi daga tafiyar da yayi karatu, shine nace bari na shigo idan badamuwa da saina baki kwangilar yi masa spring rolls da 'cak ranar, juma,a zai dawo”.
Wani irin dadu ya kama Hajiya Kumatu domin wannan wata dama ce a gare ta. Da sauri tace mezai hana haba Hajiya, ai Mukhtar d’ana ne, k0 ranar kika sanar ma ai sai a yi masa, kamar na tiya nawa ne zai ishe shi?”
Hajiya Mariya ta rike baki “Kai har tiya? A’a rabin tiya ma ai ya ishe shi, haka ma kek din, na gode, a nawa kike yi ne?”
Hajiya Kumatu ta Kara gyara zama, lokacin fara cusa kai yazo, ta karkata kai ta ce.
“Haba dai ba zan amshi kudinki ba, zan yi masa da kaina, zan shigo da safiyar ranar ma na kawo masa, ki bar kudinki kawai”.
Mamaki ya kama Hajiya Mariya, a ranta take ayyana a darin gamme kuma, amma a fili sai tayi dariya ta ce, “A’a ai ba za a yi haka ba, kema ai ba kyauta ake ba ki kayan ba, ga wannan”. Ta ajiye ‘yan dubu-dubu guda goma don tasan kudin dai ba zai wuce haka ba.
Hajiya Kumatu ta mike dai-dai lokacin da Hajiya Mariya ta mike tana fadin, “Haba Hajiya nifa nace ki barsu, don Allah...”
Hajiya Mariya ta katse ta, “Kada muyi jayayya dake don Allah, sai anjima”. Ta nuflli kofa da sauri.
Hajiya Kumatu ta koma ta zauna tana Kirga kudin, duk abin da zata yi koda na
siyarwa ne ai ba zai wuce dubu hudu zuwa biyar ba, amma ga shi an ajiye mata dubu goma, lallai dole tasan yanda zata tura diyarta ' wannan gidan da suka gaji arziki da ilimi‘. Sanda Fatila ta shigo gidan ta ji abin da ya faru, sai da ta. doka tsallen murba ta rungume mahaiflyar tata tana fadin, “Kai Momy amma na ji dadi don Allah yanzu ki dage‘ ki nemo min soyayyar Mukhtar don Allah, don tabbas idan ban aure shi ba mutuwa kawai zan yi”. Hajiya Kumatu ta fashe da dariya, tana fadin, “Kwantar da hankalinki kamar kin zama matarsa kin gama, yanzu ma don yamma ta yi ne, amma a gobe zan tafi gun'boka na sanar da shi duk yanda muka yi. Da kanshi zai zo yace yana kaunarki, dole ne ma ya gaya miki. Dadi ya cika Fatila, daren ranar kam kasa bacci ta yi, burinta bai wuce ta dora idonta akan Mukhtar a gobe ba, duk lokacin sai ya yi mata tsawo. ’ Ranar da zai dawo kam tun asuba suka kama Kiri-kirin aikin shiryawa Mukhtar cak da spring rolls wanda aka barbade shi da magungunan gurin boka, kafin Rarfe goma na
safe sun kammala, aka shirya cikin wasu kwanuka masu hakorin Hajiya irin na da can, Hajiya Kumatu ta dauko da kanta ta nufi gidan da kudirinta a zuciyarta.
Hajiya Mariya kam da murnarta ta tari Hajiya Kumatu, sanda ta buda ta ga yanda aka tsara kayan kuwa kasa godiya ta yi don murna, kusan duk sanda zasu yi sabga a gidan Hajiya Kumatu suke kai wa kwangilar kayan snacks amma ba ta taba tsara shi irin wannan ba, nan fa ta dinga godiya da sanya albarka. '
Dadi ya cika Hajiya Kumatu sai ta share gindi aka kama hira tana ba ta labarin ai ita daman girki ta karanta, tun lokacin ba a bai wa karatun mata muhimmanci ba. Hira dai ta miKa sosai har take tambayar Hajiya Mariya k0 ya kusa aure ne Mukhtar din.
Hajiya Mariya ta taBe baki tana fadin, “Wannan dan tsurfar duk matar da ya gani sai yace batayi masaba aikinsan shikam ya fita daban a gidan nan, ga shi da karatun addini a kansa kamar me, amma akidunsa irin na Turawa ne, mutum da k0 kaya bai sanyawa balle rubutu, zanzaro mafa har yau sau' nayi da
gaske yake dainawa, Allah Ya taimake ni tunda farko malam akan karatun addini ya dora shi, da karatun boko ne kam irinsu ne masu cewa tirinrin girki ke 'dunkulewa ya zama hadari. a sauko da ruwa, ga shi duk gidan nan babu wanda yafu shi haddar karatun tunda da ka zai karanta miki duka qur’ani da tafsirai kowa yana ganin shi ne ya gado karatun malam, amma ban da dabi’ ar malam sam” .
Wani irin dadi ya kama Hajiya Kumatu ta gyara zama ta karkatar da kai, tace,“Lallai kam kice irin halinsu daya da Fatila, ita ma yanda kika san diyar mangora akan boko, haka ta ke...”
Ta Kara rage murya, “To me zai hana muyi tuwona maina Hajiya‘?”
Hajiya Mariya ta gumtse fuska da sauri tana kallon Hajiya Kumatu da mamaki akan fuskarta tace “Ban gane abin da kike nufi ba Kumatu
Jikinta ya danyi sanyi ganin yanayin da Hajiyar ta nuna, amma sai ta dan dake tana karanta lamarin da boka ya bata, tace Da...
dama ina nufin wai mu hada Mukhtari da Fatila aure...”
“Aure kuma? Ai kin san Fatila ba dai-dai auren Mukhtar bace ba' Kumatu”.
Ran Hajiya Kumatu ya dan fara Baci, tace “Ban gane abin da kike nufiba, shin muni gare ta k0 baqin tabo ne da ita, k0 kuma shi dan naki dan gwal ne da za,a ce yafi karfin diyata iye?” Ta karasa maganar a hasale.
Hajiya Mariya ta ce, “K0 daya amma dai ai kin san Manzon Allah 'yace, ka nemarwa’ ‘ya’yanka uwa ta gari, yanda Fatila takw kuwa ai sai irin ta niga, 'sannan ina ganin yanda mahaifinta ya zama hotiho ai ba zan so nima,, dana ya zama haka ba, kiyi hakuri amma”.ba
Hajiya Kumatu ta hasala matuka, ta miqe jikinta yana rawa ta ce, “Ai dama duk gulmarta da ake yi a layin nan yana dawo‘wa kunnena‘, kuma aure tsakanin Mukhtar da Fatila babu ‘ fashi muddin ina raye wallahi, sai dai duk abin da Zakiyi ki yi ehe”.
Mamaki ya cika Hajiya Mariya kamar
da wata a Kasa, amma da yake ita mai ilimi Ce sai ta ce, “Allah ke kaddarawa idan Fatila
matar Mukhtar ce babu wanda ya isa ya hana, amma zan nemar masa tsari da wannan muguwar kaddarar insha Allahu mace ta gari wacce ta fito daga gidan daraja zai aura insha Allah”.
“Mu zuba ni dake dan halak ka fasa”.
Ta fice cike da Bacin rai tana huci, Hajiya Mariya ta rike haBa cike da mamaki, sai ga Hajiya Babba ta shigo dakin (uwargidanta).
Ta kalle ta tace,“Lafiya Mariya yanzu naga Kumatu ta fita rau a Bace tana masifa ko amsa gaisuwata ma ba ta yi ba?”
Hajiya Mariya ta yi ajiyar zuciya, tace, “Bari ke dai Yaya, tsautsayi zan ce ya kai ni nan ta kwashe duk yanda aka yi ta sanar da ita. Hajiya Babba tace“Cabdijan, lallai na yarda da ake cewa Kumatu tana da taBin hankali, banda haka ina gamin Muhammadu da wannan fitsararriyar diyar tata? To gaskiya ki tashi tsaye kin san yaran yanzu da sakaci da addu’a, ga shi dai sun sani din amma aiwatarwa sai ya zama aiki, Allah Ya raba mu da sharrin Kumatu tunda dai ba tsoron Allah take ba
Hajiya Mariya tace “Ke ni kek din nan
da spring rolls din nan ma ban yarda da shi ba,
bari na bada a kaiwa almajirai, domin naga
ab‘i’n daman kamar ta shirya masa, Allah kadai Yasan irin kulle-kullen da ta keyi”.
“Gaskiya kam, ki amso masa take away gidan abinci kawai”.
Da wannan maganar suka share zancen aka baiwa almajirai, ta bada aka yo masa take away "aka ci gaba da shirin tarbarshi. '
Karfe hudu yayansa Malam Hamza ya isa airpozt don hudu da kwata jirginsu zai sauka, sai dai har karfe biyar yana airport din amma bai ganshi ba, ga shi ya kira lambarsa ta can Madina an tabbatar masa da lallai tana rufe alamar ya daina amfani da ita, haka ya hakura ya nufi gida ya sanar da su halin da ake ciki.
Hankalin Hajiya Mariya ya tashi, domin ya tabbatar musu da lallai yau zai iso, amma dai ta‘dake tana ta addu’a tunda ba shi ne zuwansa. na farko ba balle ace bata ya yi. Malam Hamza ne ya kwantar musu da hankali yace, yana tunanin makara yayi jirgin ya taso, amma zai
bincika idan zuwa washegari bai iso ba, da wannan hankalinsu ya dan kwanta, Hajiya Mariya ta zubawa kayan da ta shiryamasa ido cike da takaici.
Shi kam Mukhtar karfe hudu ya iso Nigeria daidai, a airpor tayi yaci karo da Hassan wanda ke bin Fatila suka gaisa a mutumce. Hassan ya ce.
“Daman kai muka zo dauka ga mota can”. Ya nuna motar wani abokinsa, babu musu Mukhtar ya nufi motar yana godiya. A motar ya dinga' jan Hassan din da hira yaron kam abin har lokacin mamaki yake ba shi, domin tunda Hajiyarsa tace yazi airport ya dauko Mukhtar a motar abokinsa ya cika da mamaki ya ce, _“Momy meye kuma hadinmu da shi da zaki ce muje mu dauko shi, su da suke da motoci kala-kala a gidansu?”
Cikin fada tace, “Ni dai abin da nace maka ke nan, kai ba ka san shi zai auri yayarku ba, tun daga can ya yi waya don ya ce ita yake bukatar ya fara gani kafin ya ga kowa”.
Da farko ya dage yana musu sai da ta matsa sannan ya yarda ya tafi cike da mamakin
sanda aka kulla soyayya tsakanin Mukhtar da yayarsa, sai kuma ga shi Mukhtar din da ko magana ba sa yi sosai bayan gaisuwa yake janshi da hira.
Shi kam Mukhtar yana sauka a Nigeria yaji gaba daya kansa ya juye babu abin da yake buKata illa ya ga Fatila, da kanshi ya dinga mamakin kansa, meye hadinsa da yarinyar? Sai ga shi yaci karo da Hassan kuma, yaji idan bai bi shi ya ga Fatila ba zuciyarsa zata iya tsagewa aikin boka yayi kenan).
Daman an kammala shirya masa girki, abinci wajen kala hudu Hajiya Kumatu ce da kanta ta tare shi cike-da farin ciki tana fadin
“Marhabin malam Mukhtar sannu da zuwa”. . Wani irin farin ciki da kaunar matar ya dinga shigarsa, cike da ladabi ya gaisheta ya sami guri' ya zauna, tabbas banda aikin asiri babu abin da zai kai Mukhtar wannan gidan domin tunda yake baifu sau uku ya shiga gidan ba shi ma tun yana yaro lokacin mahaifinsa Yana:yana aikensu rarraba zakka ga makota, ne amma yau sai ga shi a gidan.
Hajiyeir ce da kanta ta dinga kawo masa
kayan abinci, sai dai ya kasa Ci, domin har lokacin zuCiyarsa tana cike da mamakin abin da 'ke faruwa, amma ya kasa tunanin dai-dai, sai da tace “Haba Mukhtar ka ci mana, ai da nan da gidanku duk daya ne, k0 ba ka son wannan a ‘sake girka maka'wani ne?” . Da sauri ya ce,"‘A’a”. Ya kama Ci, sai "dai 'zuciyarsa sai azalzalarsa take yi akan Fatila, babu abin da yake so illa ya ganta, suna sane suka Boyeta saboda cika umarnin bokansu
la’,ananne. . Ya kasa daurewa yace“W’ai ina Fatila
ne Hajiya'? . ‘ Wani irin dadi ya kamata domin ta tabbatar aiki ya yi kyau, ta kyalkyale da dari'ya
sannan tace . ’ ' “Tana ciki, bari na kirawo maka ita ku
'gaisa”. , ' ' Ta mike jikinta yana rawa ta nufi dakin .Fatila cike da zumudi '
Fatila tana can a daki tana jin duk abin da suke fad'a, tana jin shigowar Hajiyar tata ta doka tsalle ta rungumeta tana fadin.
“Kai Momy na gode, dame zan saka miki wannan abu da kika yi min? Wai yau Mukhtar ne a gidan nan har yake tambayata, tabbas wannan hatsabibin boka ne”.
Hajiya Kumatu tace, “Kinga ki yi sauri ki je, domin na ga ya matsu ya ganki, ina fatan kin sanya kwallin nan da turaren da boka ya ba ki?” _ . _ . .
, “Duk na sanya momy, bari na je naga yanda 'zamu kare”.
Ta nufi tsohon falon nasu da sauri, wanda a can baya cike yake da kayan alatu a yanzu kuwa sai tsofaffin kujerun da suka ci duniya da tsohon kafet da ya kukkurje ya koke don wahala.
Tunda ta nufo kamshin turaren da ta sanya ya fisgi zuciyarsa matuka ya kurawa kofar da zata ,fito ido, ta fito tana kwarkwasa. amma cikin shigar mutumci, domin boka ya kafa musu sharadin dole ta guji duk wani abu da
Kut wannan hajiya kumatun fa
.
MATACCIYAR RAYUWA
CHAPTER 17
da ba ya so, domin idab har tana yawaita bata masa ransa asirin ba zai yi tasiri ba. ‘
Bakinsa yaqi rufuwa sai kallonta yake yana murmushi, a ransa wani irin sonta ke. masa yawo, tunda yake bai taBa jin son wata mace kamar haka ba, da yake shi ba ma’abocin .kallekallen mata bane ba, ta karasa ta zauna tana wani yauki.
Har lokacin. bakinsa ya gaza rufuwa saida ta ce masa, “Ina wuni”. Sannan ya dan dawo hayyacinsa ya dan dake yana fadin. ' '
“Fatila manyan gari, lafiyalau, yaya jin dadi?
Tana dariya ta ce, “Yana gurinku, ashe kana magana haka?” ..
“Au kin yi zaton ni kurma ne ke nan?
Ta yi wata shagalalliyar dariya, “Ni kam bance ba, amma ai ko kallona baka yi ballé har
Kayimin ya gyara zama yana fadin magana “Wannan ai maganar baya kika yi, amma a yanzu ai kece
Abokiyar maganata domin kece uwar yayana
Wani irin farin ciki ya shige ta ta dube shi a lalace, “Da sauri haka malam?”
“To me zan jira na kammala karatuna, kuma tun kafin na iso garin na sami aiki, daman kuma Hajiyata ta dage na yi aure tun tuni, to kinga me zan jira Fatila idan dai kina sona ai magana ta kare kawai”.
Haka nan suka dinga hira kamar wadanda suka shekara suna soyayya, Hajiya Kumatu dake labe har rawa ta taka don dadi, lallai dole gobe ta je ta sanarwa da boka yanda aka yi aiki kam ya yi kyau.
'Bai yi shirin barin gidan ba sai da aka .fara kiraye-kirayen sallar magriba ya yi musu sallama akan sai an jima zai kuma shigowa.
Kai tsaye masallacin dake Kofar gidansu wanda mahaifinsu ya gina, wanda kusan duk jama’ar da ke unguwar a nan suke sallah ya nufa, ya shiga bandakin masallacin ya dauro alwala ya shiga da sauri aka tada sallaha da shi.
Bayan an yi sallama kannensa suka ganshi suka yi gida da gudu kai labari kai tsaye gidansu ya shiga bayan ya gama addu’a, gida ya rude da ihu da murnar dawowamhi, ya shiga
ya gaida Hajiya Babba, sannan ya wuce gurin mahaifiyarsa bakinta har kunne ta ce.
“Baba ashe dai zaka iso garin yau, yayanka ya je airpor tun hudu saura ya karaci yawonsa bai ganka ba”.
Ya yi dariya yana zaune a kujera ya ce, “Lallai sabani muka yi, ni kuma da na yi ta dubansa ban ganshi ba na biyo motar wani yaro dan nan unguwar. Mun same ku lafiya dai k0?”
“Lafiya lau, ya ya hanya? Da fatan dai an samu duk abin da ake so dai?”
Ya ce, “Masha Allah tafiya kam ta yi kyau, Yaya Hamza bai sanar dake har ya samar min aiki a makarantar gaba da sakandire ta Legal da na aiko da takarduna tuntuni ba?”
“Yaushe? Bai gaya min ba, kai amma na ji dadi, Allah Yabar zumunci ya saka da alheri, ya kuma jikan mahaifinku da ya d‘ora ku akan wannan nagartaccen zumunci. Bari na kawo maka abinci, ai da har mun fidda rai da zuwanka”. Tana kokarin mikewa take maganar.
Da saurinsa yace, “Na koshi wallahi Hajiya, sai dai ko zuwa anjima k0 gobe naCi”.
tajuyo da mamaki tana kallonsa, domin tasan duk sanda ya iso garin ya dinga d'okin a‘ kawo masa abincin gida ya ci, domin ya ce sam ba ya jin dadin abincin cin can kamar na nan, amma yau kuma ya cc ya Roshi, ta daure dai ta _ ce.
“Kai sarkin dokin cin abincin gida kace ka koshi, kamar kaci a wani gurin, ko kuma dai ba ka jin dadi ne don daman na ganka
kamar a firgice kake”. ' Ya sosa keya yana fadin, “Lafiya ta kalau wallahi, na dai biya gidan Hajiya Kumatu na ci ne....”
A rude ta ce, “Hajiya Kumatu kuma‘.’ Wacecc me wannan sunan ma?” Duk ta rude don ba ta son zarginta ya tabbata.
Cikin sanyin jiki ya ce, “Aida yaron gidan muka hadu a airpor ta suka rage min hanya, sai na ga ya dacc na shiga na gaida mahaifiyarsu nayi godiya, sai ta yi min tayin abinci, to babu dadi naqi ci don ba zata ji dadi ba shine na
“La’ilaha illallahu na shiga uku, yanzu ka
ci abincin gidan kenan Baba?” A rude ta ke maganar. , Mamaki ya cika shi ganin yanda duk ta, rude, yace “Lafiya dai hajiya? K0 suna da kazantane? Ganin abincin na yi fes-fes ga kamshi yana tashi, nasan kuma kuna aikawa da kwangilar girki gidan idan kina sabga shi ya sanya naci don....”
“Ka ga tashi kaje ka bani guri don Allah”. Ta fada a zuciye.
Ya mike jikinsa sanyi Ralau domin idan akwai abin da ya tsana a duniya bai wuce Bacin ran mahaifiyarsa ba, ya nufi Kofa har ya kai
kofa ta ce. . . _. “Ka tabbatar yau ka yi tsayuwar dare ka
kuma nemi tsari da dukkan sharrin mutum da aljan kaji k0?” Yace “Insha Allahu Hajiya, ki yi hakuri ban san cin abincin nawa zai bata miki rai ba”. “Shi kenan jeka Allah Ya yi maka albarka, Ya shige mana gaba”. . Yana fita dakin Hajiya Babba ta shigo a rude, ta fashe da kuka, hankalin Hajiya Babba ya tashi matuka, domin suna yin zama na amana tun maigidansu yana raye har zuwa yanzu da kasa ta rufe masa ido, don haka zaka ga gidan sam babu wani ‘yan ubanci.
Cikin kuka ta sanar da ita duk abin da ya faru, hankalinta ita ma ya tashi amma dai ta dake ta dinga lallashinta, da nuna mata muhimmancin yin addu’a domin ita ce maganin komai Tun daga wannan lokaci soyayya mai zafi ta kullu tsakanin Fatila da Mukhtar duk wata muguwar shiga da kule-kulen samari ta daina sai shi kadai, ga shi Allah Ya doro mata kissa da iya zama da mutum, don haka ta shiga .zuciyarsa matuka ya zamana yana mata so na gaskiya ma don haka yawaita add’a da ba shi ruwan tofi da mahaifiyarsa ke yi ya sanya duk asirin da suka yi masa ya karye ya zama sai son Fatila na gaskiya wanda su suke ganin kawai aikin boka ne, shi kuma halinta da yanda take masa biyayya ya sanya ta shiga ransa matuka, domin a can baya yana mata kallon fitsararriya ne
Sannu a hankali maganar soyayyar Fatila da Mukhtar ta watsu a unguwa har ta kai kunnen ‘yan uwansa samari, su kuwa ba su yi kasa a gwiwa ba suka sanar da iyayensu da abin ya dagulawa Hajiya Mariya rai domin da farko ta yi zaton duk aikin da Hajiya Kumatu ta yi akan Mukhtar ya lalace, sai ga wannan muhimmiyar maganar ta flto, ta dinga zuci-zucin ya iso gidan ta ji tabbas. .
Nan fa ta nuna sam ba ta yarda ba duk matan da suke garin masu tarbiyya da mutumci ya rasa waccc zai ce yana so sai Fatila, me tafi sauran? Nan ya marairaice ya fara ba ta hakuri, amma ko a jikinta abu kamar zai yi sauki doniin ganin yanda hankalin mahaifiyarsa ya tashi ya ga gwara ya hakura da Fatila tunda ba zai iya kin bin umamin mahaifiyarsa ba, sanda Hajiya Mariya ta ji hukuncin da ya yanke ta ji dadi ta dinga sanya masa albarka tana godiya ga Allah da Ya sanya danta mai biyayya ne a gare ta.
Sai dai me? Sanda ‘ya tadda Fatila da bayanin shawarar da ya yanke sai ta kama yi masa kuka, hankalinta ya yi matukar tashi ta fashe masa da kuka sosai, ya dinga lallashinta haka ya rabu da ita tausayinta ya cika masa zuciya wanda hakan ya kuma sanyawa yaji sonta ya shige shi, sai dai sanda labarin ya isa kunnen Hajiya Kumatu ta ji shigar abin da zafu k0 da yake yanda ta ga hankalin diyar tata ya tashi har dasu jinya don haka babu shiri ta nufi gurin boka a rude tana kuka domin a wannan karon tana ganin kamar zata iya rasa diyar tata ne.
Boka kam ya ba ta abubuwan da za a haukata tunanin Mukhtar, ita kuma ta zube kudi don duk wata kadararsu sai da suka saidata a wannan lokacin, aiki kam ya yi kyau domin lokaci daya malam Mukhtar ya gigice ya hauka ce bai san sanda ya koma gurin Fatila ba, suka ci gaba da soyayyarsu a wannan karon ma labari ya koma kunnen Hajiya Mariya, ta kirawo danta da haushi da fad'a, sai ya fashe mata da kuka abin da ya tsoratata, amma ta 'tabbatar masa ko kukan jini zai yi Karya yake ya auri Fatila tunda tasan ba auren Allah bane.
Da rikici ya kacame tsakanin dan da mahaifiyar abin da ke kara ba ta tsoro bai wuce
ganin yanda danta dake matukar yi mata biyayya yau da shi ta ke sa’insa ba, wato tun bai auri Fatilar ba ma kenan, to idan ya aureta ya ya za a yi kenan?
Shi kam Mukhtar ya shiga tsaka mai wuya, ga shi ya Ki yarda da wai asiri Fatila ke 'yi masa ya sota balle har ya nemi tsari da shan'insu kamar yanda mahaifiyarsa ke so. Sai ya ce, wai shi yasan soyayya ce daga Allah, duk wani dadin baki ya yi a banza har rantsuwa ta yi' muddin nononta ya sha ba zai auri Fatila ba, su kuma can basu daina aikinsu ba, daga karshe dai ya yanke shawarar taflya gurin Abbagana ,tunda yasan ‘iya’yen nasa da yayyensa suna jin maganarsa kamar ta mahaifinsu domin ya bada goyon b‘aya ta kowane Bangare, sanda Abba ya iso ya dinga yi masa nasiha da nuna masa duk abin da Allah ya Kaddara babu makawa sai ya faru.
Ya nuna Hajiya, “Idan Allah Ya kaddara da'rabon aure k0 haihuwa a tsakaninsu sai ya kasheta,' da' wannan ya sanya suka amince amma ransu basa kauna, bai bar garin‘ba sai da aka kai dukiyar aure.
Su Hajiya Kumatu kam murna suka ..' Dingayi, domin sun tabbatar fatsarsu ta kama qaton kifi, da fara shirye-shiryen bikin Karya.
Tunda aka yi auren Fatila ba ta mu’amala. da kowa da ya shafi Mukhtar din a cewarta basa kaunarta ba ta ga amfanin hulda da su ba, duk yanda yake son ya kulla alaka tsakaninsu da mahaiflyarsa abin ya ci tura, domin ita kanta Hajiyar ba ta kaunar ganin Fatilar, dole haka ya hakura k0 sabga ake yi a danginsa sai ta ga
dama ta ke zuwa. Burinta ya ta’allaka akan ta haihu, domin
tasan tana haihuwa ta gama da shi, sai dai Allah ya Ki amincewar zata iya zame musu gibin da komai zai iya faruwa, hakan kuwa aka yi mahaifiyarsa ta fara fadan ya kara aure tunda an kwashi shekaru hudu matarsa k0 batan wata bata yi ba, saboda son da yake yine ya dawo da alakarsa kamar da mahaifiyarsa ya sanya ya amince ya fara neman auren wata yarinya Binta, wacce shi kam yake ganin zai aureta ne kawai don babu yanda zai yi, an sanya rana an gama komai kwatsam! Labari 'yaje kunnen Fatila Allah Ya yi ta mace mai kishi wanda ya wuce irin na ka’idar addinin musulunci, don haka a rude suka yi gurin boka akan duk yanda za a yi a fasa wannan aure.
Sai aka turawa Binta aljanu yarinyar ta dinga fama da wahala ta fara kamar haukahauka hankalin iyayenta kam ya tashi suka dinga nemar mata magani, daga karshe suka ji matar Mukhtar ce ta yi mata shunen aljanu, don haka suka ce sun fasa ba shi, tun ba a yi auren ba ma ana turowa diyarsu iskokai balle an yi auren? Wannan ce ta watsa maganar auren, Mukhtar kam bai wani damu ba yace ya bar musu duk abin da ya kai.
Hajiya Mariya kam kamar zata hadiyi zuciya ta mutu don bakin ciki, amma da ta yi masa magana sai yace ai ba laifinsa bane daga nan ta ce ya Kara neman wata.
An dan jima kafib su hadu da Shamsiyya, ita kam tana cikin' dalibansa a nan Legal, kamun kan yarinyar ya sanya ya fara sonta, sanda ya tadda mahaifiyarsa da maganarsa taji dadi aka fara neman auren a Boye har kayan lefe aka kai. Ya rage saura kwana goma aure labarin ya isa kunnen Fatila ta sanar da mahaiflyarta, ba su yi kasa a gwiwa gurin tafiya gurin bokansu ba. Ita kam Shamsiyya jini aka sakar mata, abu kamar da wasa sai ta yi ta sako pad sai ga abu ya haikake ko taflya take jini zai ta zubowa kawai, an kaita asibiti an tabbatar ba daga mahaifarta yake zubowa ba, dole suka koma na Hausa.
Shamsiyya duk ta rame ta kare saboda bakin ciki, domin bata iya flta k0 kofar gida kullum tana daki, wuni ake wanke zannuwanta da jini ya Bata. Hankalin Mukhtar kam ya tashi tunda yana son Shamsiyya ya dinga taimaka mata da addu’o’i idan abin ya yi sauqi sai ya dawo, su ma daga karshe aka sanar da su wadanda suka aikata abin dole hankalin iyayenta ya tashi matuka, tunda shekara guda ana ta abu daya duk diyarsu ta kare ta rame
' kamar mai fama da ciwon kanjamau, su da
kansu suka fara tattara kayan Mukhtar da kudinsa suka kai gidansu suna ba su hakurin cewa sun fasa.
Hankalin Hajiya Mariya ya tashi ta fara yi musu nasiha, amma sun tsorata suka ce sam ba su yarda ba., dole haka ta hakura shi kansa
da ya ji an dawo masa da kayansa, saida hankalinsa ya yi mugun tashi, da ya je gidan su Shamsiya ba su barshi ya ganta ba, suka kama ba shi hakuri, haka dole ya haKura ya tafi
Amma shi ya Ki yarda wai Fatila ce ke hana shi aure kamar yanda iyayensa da ‘yan uwansa ke fada, domin duk sanda ta ji labarin auren ba ta nuna damuwarta har kaya take siya ta bada gudunmawa, yasan tana‘da matukar kishi, don k0 kallon mace ta ga ya yi ranar sai ' sun KWana tashin hankali, amma idan taji labarin auran da kanta ta ke sanar da shi ta ji, har ta yi ta masa tsiya tana cewa, “Ai ni ban isa na hanaka aure ba, ni wannan soyayyar ce bana so ta titi”.
Da haka dai aka rufe babin Shamsiyya, bai kuma yunkurin kara neman aure ba.
Sai da aka yi shekara daya sannan mahaifiyarsa ta tura shi ya ga diyar kawarta, bai musa ba yaje ya ganta babu laifi shi dai bai ji wani sonta ba, amma kuma bai nuna ba ya sonta ba, ita kam sati guda kacal aka sanya auren don kada taji daren da za, a daura auren ya shigo da kayan da zai sanya na daurin aure nan fa hankalinta ya tashi da ya sanar da ita auransa za a daura gobe da safe.
Nan fa ta tuBure ta kama kuka tana nuna mai yasa yaqi sanar da ita tun da farko? A daren ta sanarwa da Hajiyarta ta a waya, ai kuwa a wannan daren Hajiya Kumaru ta nufi gurin boka a rude, ko tsoron duhuwar dajin ba ta ji ba.
Tsakar dare ana tsaka da bacci aka jiyo ihun Samira tana buge-buge tana surutai, da gudu iyayenta suka nufi dakin nata aka dinga'yi mata tofi da kyar ta kwanta, sai dai k0 minti daya ba a yi ba ta kuma farkawa a gigice, haka suka kwana a gigice domin idan dai zata runtsa to kuwa lallai zata ga bakin aljanin da ake . turowa ya ba ta tsoro, gari yana wayewa ana shirye-shiryen daurin aure amarya ta kama aman jini, aka kwasheta aka yi asibiti a gigice likitoci suka taru a kanta.
Daurin aure dai bai yiwu ba domin sai da aka sanya mata jini laida biyu, aka daga bikin sai wani satin. Kwananta uku a asibiti ta warke, sai dai ana dawowa gida ta kuma ci gaba da aman sai da aka yi haka kusan sau hudu, idan
Hmmm lallai kumatu da fatila anyi shaidanu