![]() |
🔥*NACINA YA JAWOMIN* 🔥 |
![]() |
READ MORE BOOKS |
[4/25, 1:38 PM] +234 814 129 2044:
WhatsApp Channel |
🔥 *NACINA YA JAWOMIN* 🔥 Narrnarhh Bukar✍️
🌹Perfect Essential Writer's
Association🌹
✨ P. E. W. A✨
Wattpad:@AISHAABUBAKAR812
Arewabook:Narrnarhh002
Bismillahir rahmanir rahim
Dukkan yabo da Godiya sun tabbata ga Allah mad'aukakin sarki, Wanda ya bani ikon fara rubuta farkon littafina mai suna NACINA YAJAWOMIN, Wanda kecike cike da abubuwa masu ilmantar, fad'akarwa, tausayi, yaudara, Dade sauransu.
Gargaɗi❌❌❌
Ban yarda a sauyamin littafi ta wani fanni ba tare da izinina ba ko kuma a copy wani ɓangare na littafina ba.
1----2
KADUNA
Zaune suke ɗaliban shiru a aji kasancewar malamin Maths ne kuma gashi mugu, hakan yasa ɗaliban maida hankulansu gaba ɗaya gun allon,calculations yake yana bayani amma babu mai ganewa, yana kai karshe yace "Do you all understand" ɗaliban sukace "yes" saboda tsoransa da sukeyi.
Uncle Musa yace"Good, now let me give class work ".
Nanfa ɗaliban suka ruɗe,Uncle Musa ya rubuta calculations guda biyu a board, sannan yace su fara.
Kwasam saiga wata yarinya wacca bata wuce shekara 15 a duniya tashigo da gudu tana haki, saboda gudun da tasha, kawai ɗaliban sukeyi Uncle Musa yace," Stop there!!!", cike da tsawa, haka yarinya ta tsaya jikinta na ɓari, kafafunta suna rawa.
Uncle Musa yace" why are you late in my class". Cikin rawar murya yarinyar tace"I'm sorry Sir". Kawai sai tafashe da kuka, suko ɗalibai daɗi suke taji, harda dariya ƙasa ƙasa kar malamin yaji su,Uncle Musa yace "kneel down and give me your hand, next time you won't there come late to my class".
Haka yarinyar ta miƙa hannunta tana kuka, yako zaneta babu sassauci, tashi tayi daga kneel down ɗin ta wuce seat ɗinta wanda yake gaba ta zauna, kuma yace saita yi class work ɗin.
Baiwar ALLAH haka ta ciro littafinta tafara rubutu,cikin wasu mintuna sai gata tagama class work ɗin taje yin submitting, cike da mamaki Uncle Musa ya bita da kallo, ɗaliban ma sai haushinta sukeyi saboda tafisu nacin karatu da hazaƙa, haka ɗaliban suka kasance har lokacin tashi break yayi suka fita.
Bayan sun fita suna wasa naji ance Sa'eeda, ashe yarinyar nan ce wacca Uncle Musa ya duka a aji ce, waiwayowa tayi tana kalonta tare da cewa "Maryam ya akayi ne" wacca aka Kira da Maryam ta ce "Sa'eeda meyasa kikayi latti, bayan kinsa yau Uncle Musa muke dashi" cike da damuwa Sa'eeda tace"Hmmmm Umma kande ce ta aikeni kuma wurin da nisa, shiyasa nayi latti" Maryam tana kallonta da mamaki ta ce"Amma tasan zaki makaranta ai, shi ne ta aikeki alhalin tanada mayyan Yara 'yan mata ", murmushi mai ciwo Sa'eeda tayi sannan tace" Bakomai ai lokacine, watarana sai labari ".
Haka suka cigaba da hiransu har aka koma aji, darussa aka cigaba dayi har 2:00pm tayi aka tashi gida.
@@@@@@@@@
Anatse suke tafiya ita da Maryam suna hiransu, har kowa yabi hanyar gidansu. Tana shanyo kwanar gidansu gabanta yafara dukan uku uku saboda tasan aikin gida na jiranta,hakan ta isa har zauran gidansu tana ɗauke da sallama, amma babu amsa duk da akwai mutane agidan, shiga tayi ɗakin mahaifiyarta tare da sallama, cike da so da ƙaunar ƴarta ta tilo ta amsa tana fara'a, gaisheta tayi sannan ta ajiye jakarta.
Zama tayi tana" Washhhhhh ALLAH na", Ummanta dake linke wankin kayan mutanen da tayi ta ce"ALLAH yasa dai ba'a miki dukan latti ba" marairaice fuska tayi kamar zatayi kuka sannan ta ce"ALLAH Umma saida Uncle Musa ya dukeni hada sani kneel down"cike da tausayin ƴarta ta ta ce"Karki damu ƴar albarkha watarana sai labari kinji, ki cigaba da haƙuri, in shaa ALLAH baza mu dawwama ahaka ba, Ubangiji zai taimake mu".
Sa'eeda tace "Umma bara nayi sallah sai inje inyi aikina" da kallo tabi ƴarta dashi tana tausayin halinda suke ciki.
Tuno kyara da tsangwamar da suke fuskanta ita da ƴarta wurin kishiyarta da mijinta yasa ta zubar da hawaye. Fitowar Sa'eeda daga ɗaki keda wuya taji Umma Kande na kwalla mata kira har da ɗura mata ashariya da ce wa "Ubanwa kika ajiye da zai miki aikin gidan! " a daburce Sa'eeda tace"Uhm... Uhmm sallah dama nakeso nayi sai nafito aikin ".
Tsaki mai karfi taja tana ce wa" Aikin banza, Ke ga ustaziya koh, maza kiyi sallar nabaki minti 10 kizo kiyi aikin ". A tsorace tace" To".
Haka taje tayi sallah Ummanta na kallonta cike da tausayi ko abinci bataci ba, taje ta gama aikin kafin ta dawo ɗakinsu tashi abinci.
@@@@@@@@@@
Wurin karfe 4:00pm na yamma tashirya zuwa islamiya wacca take bayan layinsu, tana tafiya tana karatunta cikin murya mai zaqi ga ƙira'ah mai daɗin gaske,har ta isa makarantar.
Faslul Imam Shafi'i naga ta shiga wato ajin ƴan sauka,zama tayi a bencin farko, duk da akwai ɗalibai amma basuda yawa, saboda yanxu ake shigowa, jakarta ta bude tafito da Hadisi tana dubawa,ahaka aka cika ajin har malaminsu yashigo tare da sallama, duka ɗaliban suka amsa , sannan ya zauna yana fuskantar ƴan aji.
Malam Yusuf yace "Alhamdulillah tunda kun sauke har sau biyar, kuma wasunku ma sun kammala haddar alqur'ani mai girma, toh don haka time table na jarabawan sauka zai fito gobe, kushirya sosai, sannan zamu fara Karatuttukan sauka cikin satin nan".
Farin ciki ne ya mamaye ƴan ajin banda Sa'eeda wacca tasan basuda halin biyan kuɗin saukar duk da tafi kowa hazaƙa a ajin gaba daya.
Malam Yusuf ya katse musu surutu da cewa"Sannan kufada wa iyayenka maganar kuɗin sauka akan anyanke naira dubu ashirin ga kowani ɗalibi (#25,000) ".
Haka ya bar ajin, su kuma sai murna sukeyi banda Sa'eeda wacca ko ƙawa bata da ita a ajin sede a boko, haka suka fara maraji'ah har lokacin tashi yayi aka tashe su, suna fitowa Sa'eeda tanufi office ɗin shugaban makarantarsu, don ita gaskiya ta fasa saukar don Ummanta batada halin biyan kudin saukar, gashi mahaifinta yana dashi babu laifi yana noma amma bazai biya mata ba, koda ma yayi niyyar biya, kishiyar Ummanta zata hana saboda taga yaranta basa karatu sai talla,da wannan zancen zucin tashiga office ɗin shugaban makarantar da sallama.
Malam Harun ya amsa cikeda fara'ah yace"Sa'eeda kace haka ". Tana murmushi ta ce" Eh malam, daman nazo ne wurinka".
Sai ya ce "To to inajinki Sa'eeda". Sai data lunfasa kafin ta ce "Malam dama game da maganar saukan mune, shi ne nazo incema ko za'a iya cireni daga cikin ƴan saukan saboda a gaskiya iyayena basu da halin biyamin kuɗin sauka, shi ne nace ko za'a cireni sai wani lokacin".
Shiru yayi yana kallonta tare da yin nazari, don gaskiya yasan basuda halin biya hasalima a scholarship Sa'eeda ta ke tun daga aji daya har zuwa aji shida saboda hazaƙar ta,haƙiƙa bai dace ya dakatar da Sa'eeda ba kodan ƙoƙarinta da natsuwarta.
Kawai ya ce "Sa'eeda ", cikin taushin murya ya ƙara da cewa" Naji bayananki, kuma na fahimta, in shaa ALLAH hukumar makaranta zata duba don baza muji daɗi ace mai hazaƙar aji batayi sauka ba saboda rashin kuɗin sauka ba, ki kwanatar da hankalinki in shaa ALLAH, ALLAH zai rufa asiri".
Haka sukayi sallama cike da farin ciki tawuce gida.
@@@@@@@@@
Isarta gida keda wuya aka fara Kiran sallah, jakarta ta ajiye taje alwala sannan tayi sallah, sai taci abincin dare kana ta dauko assignment ɗinta na makaranta tayi, sai tayi karatun littattafanta na boko da islamiya, sannan ta sanar ma Ummanta yanda sukayi batun sauka da shuganban makarantar su, cike da farin ciki ta ke jin ƴarta na mata bayanin yanda sukayi da shuganban makarantarsu.
Sa'eeda na kammala bayininta sai mahaifiyarta ta ce"ALLAH kaine abin Godiya, ka ƙara rufa mana asiri duniya da lahira". Ameen Sa'eeda ta bita dashi.
Washa gari ta tashi da wuri kasancewar tasan aiyukanta na gida, ta somayi don tsoron yin latti a zaneta, haka ta kammala tayi shirinta tsaf, sannan ta karya kumallo,ɗaukar jakarta tayi tafito tsakar gida tana shirin wucewa taji an ƙwalla mata kira, a tsorace ta waiwayo sannan ta amsa saboda jin wacca tai mata Kiran, "Ke dan uwarki zo nan".
Kanta aƙasa ta nufo inda take, kafin ta ƙaraso wurin taji an hankaɗeta, ji kayi timmmmm aƙasa gashi gidan nasu ko siminti babu, haka uniform ɗinta yayi buju buju da shi,a raunane ta ɗago idanunta cike da ƙwalla tana kallon budurwar wacce ta riƙe ƙugu tana girgiza kai alamun masifa.
Sa'eeda da ƙyar ta iya miƙewa tana dubanta ta ce "Haba Nusaiba, mai na miki kika tureni alhalin akwai filin da zaki iya wucewa ba tare da kin tabani ba" tana magana hawaye na zuba a idanunta, itako wacca aka kira da Nusaiba mai zatayi inba shekewa da wata bazawarar dariya ba tana tafiya left and righg tana girgiza jiki kamar wata karuwa.
Buɗan bakin Nusaiba ta ce "Hmmmm Sa'eeda kenan, to ke a tunaninki zan bi wata hanyar don ina jin tsoranki, to wallahi kinyi kaɗan, ke bama keba hatta wannan Uwartaki bata isa ba, eheh! Irin wai ita Allazi bokon nan, ana dai yawan tazubar ne kawai aka ɓige da boko!!!".
Duk wannan abinda yake faruwa a idanun ƴan gida banda mahaifiyar Sa'eeda da take ɗaki tana jinsu, saidai tayi murmushi da girgiza kai alamar ALLAH ya kyauta.
Sa'eeda ba mai hayaniya bace, haƙuri ta bata ta wuce wurin Umma kande,a ƙasƙance ta ke duban Sa'eeda, ta ce "Jeki wurin Maman Dije Kice nace tabani saƙon", da, "To" tabita dashi ta wuce don tasan idan tayi musumma ɓata lokacinta zatayi gashi gidan Maman Dije akwai ɗan nisa kaɗan.
Haka ta wuce tana sassarfa taje ta amso saƙon ta kawo mata ba tare da ta shiga ɗakinsu ba ta wuce school.
@@@@@@@@@@
A class kuwa, principal na gani ya shigo Jss3, ashe ajinsu Sa'eeda ne, a tare ƴan aji suka miƙe suna gaisheshi, ya amsa musu cike da kulawa kana ya ce cikin harshen turanci "Dan gane da Junior waec ɗinku, kowanne a cikinku zai biya #2500 sannan za'a zana exams ɗin 3rd na watan da zai shigo, don haka kowa ya maida hankalinsa sosai a karatu banda wasa". Principal ya ɗau tsawan lokaci yana jawabi kana ya fita daga ajin.
Ɗalibai sai murna sukeyi sun kusa zama seniors, haka darussa sukaita wakana har lokacin tashi yayi suka wuce gida .
BRIGHT STARS INTERNATIONAL SCHOOL shi ne sunan makarantar su Sa'eeda, makaranta ce mai kyau da tsari, ga koyarwa sosai,babbace sosai don tana da field ɗin football da handball duk aciki, tana ɗaya daga cikin makarantun da ake ji dasu a garin.
Kasancewa Sa'eeda ƴar talakawa ce kuma a cikin wannan makaranta yasamo asali ne a dalilin wani malamin primary dinsu wato Uncle Saleem wanda yake koyarwa a matsayin corper a government school ɗinsu, ganin Sa'eeda da ƙoƙari yayi cuku cuku har ALLAH ya ƙaddara tasamu scholarship a makarantar,wannan kenan.
@@@@@@@@@@@@
Bayan dawowarta makaranta ta sanar ma Ummanta batun Junior waec.
"lallai akwai karatu gabanki Sa'eeda, ga shima islamiya kun kusa fara exams" cewar Umma.
Murmushi Sa'eeda tayi tana fadin"Ai Umma yanxu zan fara karatu in shaa ALLAH ".
Umma ta murmusa da faɗin" ALLAH ya miki Albarkha, ya cigaba da tsare gabanki da bayani, yasa ku fara a sa'a ku gama a sa'a"
"Allah humma Aameen Ummina".
Haka dai Sa'eeda ta cigaba da zuwa islamiya da boko, ga kuma karatun da tasa gaba tanayi, ba kama hannun yaro, a wannan week ɗin time table ɗin exams ɗinsu na boko da islamiya ya fito, aka fara shirye shiryen exams.
Alhamdulillah sun gama exams ɗin islamiya sannan sukayi na boko wanda ya ɗaukesu har tsawan wata daya.
@@@@@@@@@@@@@@
KEBBI
"Mum, don ALLAH ki roƙamin Abba ya janye tafiyana UK karatu,duka abokaina Federal University, Birnin KEBBI sukayi applying , amma ace ni sai ƙasar waje"
A shagwabe yake magana kamar zaiyi kuka.
Mum tace " Haba Sadam, sai kace yaro, bayan kasan ƙa'idar gidannan, duka ƴan uwanka acan Oxford University sukayi, sai akanka kake so a canja tsari, haƙuri kawai zakayi katafi, kar Dad ɗinka ya ɓatama rai ba ruwana"
Kamar zaiyi kuka yace, "shikenan Mum", murmishi mum tayi sannan tace, "Yawwa Autana, kaga tafiyarka jibi ne sai ka fara shirye shirye ko", " Toh Allah ya kaimu" kawai Sadam ya iya cewa.................................
Comment and share🙏Fisabilillah
[4/25, 1:38 PM] +234 814 129 2044: https://whatsapp.com/channel/0029VaRTjCw8vd1HiLjaNK2y 🏵️ NACINA YAJAWOMIN🏵️
Narrnarhh Bukar✍️
🌹Perfect Essential Writer's
Association🌹
✨ P. E. W. A✨
Wattpad:@AISHAABUBAKAR812
Arewabook:Narrnarhh002
3----4
Tashi yayi ya wuce ɗakinsa, "Maa shaa ALLAH ", kawai na iya furtawa ganin haɗadɗan ɗaki, dan ko amarya sai haka, in fact ko amaryan ma sai wacca ta cika amarya,ɗaki ne mai kyau da tsari, gashi babu wani tarkace dayawa,paint ɗin ɗakin fari ne tas, bed ɗin ma fari ne haɗe da ratsin gold,acan ta gefe kuma akwai sofa da centre table mai kyau, gaskiya ɗakin ya kai ƙarshan haɗuwa.
Wanka yayi kana ya fito, a gurguje ya shirye saboda jin an kusa tada sallah, ash color jallabiya yasa mai taushi haɗe da sheƙi, sannan ya daddala kalolin turaruka masu ƙamshi da tsada sannan ya fito,wayarsa da take a aljihu ya ciro jin tana vibrating, ya kalla naɗan wasu seconds sannan yayi picking.
A can naji murya wani yana faɗin"Hello Sadam, yane kana gida ne", Sadam ɗan jimmm kaɗan yayi kafin ya ce"Eh, yanxu zan shiga masallaci",acan naji ance "OK, gani nan zuwa, in shaa ALLAH ", da OK da bishi dashi kana ya katse wayan.
@@@@@@@@@@@
Massallaci ya nufa don sallar Asr, bayan an kammala ya dawo cikin gida da yake a cikin gidan massallacin yake,kafin ya shiga ciki naga ya tsaya, ganin mai gadi ya buɗe tanƙameman gate, wata rantsatstsan motar ta danno cikin gidan, kana ta nufa inda ake parking tayi parking, wani guy ne nagani wanda bai wuce sa'ar Sadam ba ya fito d'an kimanin shekara 20 da haihuwa, Kamal kenan na hannun daman Sadam, abotarsu ba ta yanxu bane, sunyi makaranta tare tun daga primary har secondary saidai abinda kowa yakeson zama a rayuwarsa ya banbanta, Sadam nason ya gaji mahaifinsa kasancewar shi kadai ne ɗa namiji a gidansu wato cikakkyan ɗan kasu shiyasa yake son karantar Business Administration a Oxford University, UK.
Sa'annan Kamal nason zamowa ɗan Jarida, shiyasa yake da sha'awan karantar Mass communication.
@@@@@@@@@@@@@@
Rungume juna sukayi sannan suka nufa ciki a tare, hannunsu na sarƙafe dana juna, da sallama suka shiga, Mum dake a falon ta amsa musu tare da faɗin "Kamal kazo yin sallama da ɗan uwan naka ne? Kamal wanda yake a russune ya amsa mata da" Eh Mum ya faɗamin jibi ne tafiyar kuma jirgin safe zai bi ", Mum tashe" Toh maa shaa ALLAH ,Auta ya faɗamin kaima kasami admission", Kamal yace"Eh Mum"
"Toh ALLAH yasa Albarkha, yasa Kugama lafiya", da Ameen suka amsa sannan suka nufi sama ɗakin Sadam .
Nan suka fara hira kamar karsu rabu kasancewar Kamal akwai zuba kamar famfo, sai ƙarfe 8:00pm Kamal ya wuce gida.
Haka dai Sadam yayi shirye shiryen sa, sannan ya ziyarci sister ɗinsa ɗaya wacca ta ke aure a nan KEBBI, tana auran wani ƙusan gwamnati, ita ɗayar sister ɗinshi tana aure a Pakistan da ƴarta mace, sannan washa gari jirginsu ya cilla sararin samaniya sai UK.
@@@@@@@@@@@@@@
KADUNA
Wasa wasa lokacin sauka ya ƙarato, Alhamdulillah Umman Sa'eeda tayi bakin ƙoƙarinta wurin ganin tama Sa'eeda kayan sawa na fitan sauka dai dai gwargwado wanda da adashen kuɗin kayan wankin mutane da ta ke yi ne ALLAH yasa tasamu kwasan farko.
"Abban Sa'eeda don ALLAH ka taimaka koda na pure water ne mu samu tunda kaga ranar asabar ne saukan, gashi yau ne kasuwa ta ke ci",
Duk wannan zancan da Umman Sa'eeda ta ke yi yana jinta a kishingiɗe a ɗan gadonta yaƙi kulata, ta ƙara da faɗin" kayi shiru Abban Sa'eeda "
Buɗar bakinsa ya ce" Toh mekike so nace, nina sata makarantar dazan bada wata gudun mawa na ehhh! , tun farkon karatunta ai nace miki banda halin biyata mata kuɗin makaranta amma ke gaki ƴar iyayi ke don ace ɗiyar tana makaranta kikayi cuku cuku har tafara, kina wahalar da kanki da wankin dauɗar mutane!!!
saida ya lunfasa duk tana jinsa bata ce komai sannan ya ɗora da faɗin"Don haka karki sakemin maganar karatun Sa'eeda kuma wannan kashedi ne na miki, ban hanaki ba ko dako zakiyi don ƴar gold ɗinki tayi karatu bai shafeni ba, ki ƙarata can da gulmarki"
Zunbur ya miƙe ya kakkaɓa babbar rigarsa zai ƙara gaba, Umman Sa'eeda ta tashi da sauri tana dubansa sannan ta ce"Duk naji bayananka, kamar yanda kace karatun Sa'eeda bai shafeka ba,toh in shaa ALLAH daga yau bazaka sake jina na maka batun karatun Sa'eeda ba, wannan alƙawari ne, kuma sai Sa'eeda tazamo fila mai haske wannan gidan wanda yake cike da duhu, in shaa ALLAH "
Taɓe baki yayi kana yace" Wannan ke ta shafa, ni kinga tafiya ta"
da sauri ya ƙara gaba, Sa'eeda da ta ke bakin ƙofa tayi saurin matsawa, ALLAH yasa bai ganta ba,da tasha ranƙwashi, ita wallahi ta rasa mai tayiwa mahaifinta yake kyararta baya sonta, sai dai ƴan ɗakin Umma Kande wanda basuda aiki sai tsagwaran talla titi titi da garage garage din motoci, duk sun sha bleaching, har da sa'arta Iklima tafara bleaching da taɗi a zauransu.
Duk fa wannan zancan acikin zuci Sa'eeda ta ke yi,zumbur kamar wacca aka tsikara ta dawo hayyacinta ta shige d'akin.
@@@@@@@@@@@@@@
"Ummina mai ya sameki kike kuka, kinaso in fara kukane, Abbana ne koh, toh kiyi haƙuri wataran sai labari,banason zubar hawayanki Ummina"
tana maganar muryarta na rawa saboda zuciyarta na mata suya akan maganganun da mahaifinta ya faɗama Ummanta kamar bashi ya haife ta ba.
Hawaye suka fara sulalowa bisa kuncinta, ganin haka Ummanta tsagaita kukanta tana dubanta, don a rayuwarta ta tsana jin kukan ƴarta ta,haka ta tallafo kuncinta tana dubanta da murmushi ta ce " Haba sayyin idaniya na, bansanki da saurin karaya ba, da juriya da jarumta nasanki, don haka bar kukan nan, sha re tsadaddun hawayanki kinji, abar kaunata"
da wannan kalaman Sa'eeda ta tsagaita da kukanta ta ɗago sannan ta kalli Ummanta tace "Toh kema ki daina kukan kinji Ummina"
Cike da shagwaba ta ke maganar har taso ba Ummanta dariya, tace "Toh nabari tawan", a tare suka murmusa,sannan suka cigaba da sabgar su.
@@@@@@@@@@@@@@
Umma Kande ce da ƴaƴanta mata uku da namiji ɗaya wanda ya kasance babba a gidan ɗan kimanin shekara 25,suna zaune a ɗaki suna ƴar hirarsu cike da annashuwa har da shewa.
Nusaiba wacca ta ke bima Musa tace" Wai ni ya waccan Allazi bokon da mamanta suka ƙare da babane, ya basu gudun muwan ne, naji biki bamu chapter munsha ba"
Umma Kande ta sheƙe da wata bazawarar dariya har da buga cinya,"Yo kema kinsan maganar gizo bata wuce na koɗi,zan bari babanku ya bama wannan mai kama da mayun tallafi ne, haba ina bade ni jikan sarkin ruwa ba sai dai wata"
Sai suka ƙara sheƙewa da dariya sannan da ɗora ta faɗin"Ai kusha kurumunku, in har kunga kuɗi sun fita daga aljihun Babanku saidai ku za'a ma hidimar, don wlh ko zanyi yawo tsirara sai naga ƙarshen wa'incan mayun"
Alamar jinjina naga ƴaƴan suna mata tare da wasata kamar ƙaura. Haka suka cigaba da hirarsu har aka kira sallah amma babu wanda a cikinsu ya iya miƙewa don yin sallar(Wa iyazubillah🤔🤔🤔) .
@@@@@@@@@@@@@@
Yaune ranar sauka, fili ne nagani babba wanda yake cike da kanopils, ƙananun kujeru da na alfarma, filin ya cika maƙil da mutane har babu masaka tsinke, a bangare guda ƴan sauka nagani ajere suna shigowa filin don fara karatu, haka suka kammala karatun cikin tsari da burgewa.
Manyan baƙi tun daga kan wakilin sarki da na hakimi,ƴan siyasa da masu hannu da shuni duk sun hallarta . Alhamdulillah haka karatuttuka sukaita wakana da wa'azuzzuka da dai sauransu har aka fara shirin bada kyaututtuka ga wa'inda suka cancanta.
Mc mai magana ya fara da faɗin "Toh yanxu yanxu bada jimawa ba zamu fara bada kyaututtuka ga ɗaliban da suka cancanta sannan sukayi zarra"
Kowa a filin ya natsu don sauraron zakarun shekaran, Umman Sa'eeda na hango can a zaune tasa wata atampa roba taji jiki sosai, sai murmushi ta ke ganin yau ƴarta tilo ta kammala haddan Al Qur'ani mai girma cikin nasara da aminci duk da tasamu ƙalubale a baya sannan yanxu ma dai bata gama fuskan ƙalubalan ba hasalima wasan yanxu aka soma(wasa farin girki).
Mc ne ya fara da ce wa " Wacca tafi kowa hak'uri da natsuwa itace Sa'eeda Sulaiman", haka ta taso tana murmushi tazo filin inda za'a bata kyautar wanda wakilin mai girma sarki zai bada, haka akai ta bada kyatuttuka wanda kusan Sa'eeda tai ta tasamu.
Daga ƙarshe Mc ya fara wasa gwarzon/gwarzuwan shekaran, nan da nan fili da rincaɓe da hayaniya don jin zakara/zakariyan shekaran, Mc yace"Gwarzo ko gwarzuwan shekaran nan shi ne ko ita ce", sannan ya tsagaita, mutune sai tsuma suke da ƙosawa don jin overall best student, Mc ya ƙara da faɗin "ita ce Sa'eeda Sulaiman", filin ya ɗauka da kabbara"Allahu Akhbar!!!
haka taje ta amsa kyautarta had'e zunzurutun kuɗi har #100,000,wanda kyauta ne daga wakilin sarki abama wanda yayi Zarra.
@@@@@@@@@@@@@@@
Haka suka dawo gida ita da Sa'eeda da maƙotan da suke mutunci dasu, wa'inda kwata kwata ba sufi mata uku ba, don Umma kande woman leader ɗin unguwan ne . Daidai gwargwado Sa'eeda da gudanar da walimar saukanta wanda ƴan walimar basuda yawa daga Maryam aminiyarta ta boko sai wasu sa'oninta ƴan layi.
Bayan sallar Isha'i, Sa'eeda ta dubi Ummanta tace"Ummina ya za'ayi da wannan kuɗin da nasamu ", Umma Sa'eeda tace" Zan buɗe account asa kuɗin gobe in shaa ALLAH don tun yanzu zan fara tarin kuɗin karatunki na jami'ah, tunda nasan bazan samu daga Abbanki ba kuma Koda na fara sana'a ba karɓuwa zatayi ba, saboda Kande, ko ya kike gani ke"
Sa'eeda saida ta lunfasa sannan tace"Toh ummina duk yanda kika tsara banda jayayya, ALLAH yayi mana jagora ", da" Aameen ", umminta tabita dashi, sai sukeyi shirin bacci don garin ya soma yin shiru.
@@@@@@@@@@@@@@@
Haka dai rayuwa ta cigaba da tafiya yau da daɗi gobe babu daɗi, a bangaren Sa'eeda sai a hankali, hutun boko ya ƙare sun koma makaranta ka'in da na'in babu kama hannun yaro.
Ta shiga SS1 Art class saboda tun tana ƙarama ta ke da sha'awan kasuwanci kuma Ummanta tanason haka, shiyasa ta ke son karantar Business Administration,saboda fannin kasuwancine, haka ta fara SS1 cikin nasara da aminci.
Sa'eeda karatu ta ke ba dare ba rana tunda yanzu ba islamiya ta ke zuwa ba sai dai tilawan Al Qur'ani mai girma da litattafai,karatu yayi nisa sun fara shirin exams na kammala SS1 zuwa SS2.........................
Comments and share 🙏🙏🙏fisabilillah.
[4/25, 1:38 PM] +234 814 129 2044: 🏵️ NACINA YAJAWOMIN🏵️
Narrnarhh Bukar✍️
🌹Perfect Essential Writer's
Association🌹
✨ P. E. W. A✨
Wattpad:@AISHAABUBAKAR812
Arewabook:Narrnarhh002
5----6
Karatu yayi nisa sun fara shirin exams na kammala SS1 zuwa SS2. Sa'eeda ta shiryawa exams ɗin tsaf kuma takan koyawa Maryam inda bata fahimta ba kasancewar Maryam slow learner ce, duk da mahaifin Maryam ya kawo ma Maryam lesson teacher wanda zai dinga koyar da ita, hakan baisa ta cimma Sa'eeda Koda da taku ɗaya a karatu ba, a gaskiya hakan nama Maryam ciwo a zuci, gata ƴar masu kuɗi,ƴar gata gurin iyayenta amma ace ƴar talakawa tafita komai, ga kyau, ga ilimi, ga natsuwa, ga, ga, haba abin yayi yawa.
Duk wannan zancen a zuci ta ke yinsa,bayan Sa'eeda ta kammala koya mata wasu calculations a Economics kasancewar su ƴan Art students ne,itama tanada burin zamowa ƴar kasuwa daga jin Sa'eeda sanda suka kammala exams din ƙarshe tana faɗin ita Art class zata shiga saboda tanason harkar kasuwanci carab ta ce itama shi zata karanta saboda yanda taji Sa'eeda na kururuta course ɗin Business Administration, don haka tana zuwa gida ta sanar ma Mom ɗinta, da farko taso yin jayayya don ita tafi son ƴarta ta karanci bangaran likitanci(saikace tanada kwakwalwar ne😂😂😂),don ace ƴarta ta tanada ilimi amma jin ta ce ita Business Administration zata karanta kuma Dad ɗinta ya goya mata baya yasa ta haƙura.
Mafi ƙololuwan ɓacin ranta shi ne ashe saboda Sa'eeda zata karanci Business Administration yasa itama tace zatayi, amma babu yadda ta iya tunda mijinta ya bada go ahead. Cikin ikon Ubangiji su Sa'eeda sun kammala exams ɗinsu,makaranta ta basu hutun wata ɗaya da kwana huɗu saboda gab da azumi suka kammala exams kuma a ƙa'idan makarantar basa karatu cikin azumi shiyasa su ka yi hutu.
@@@@@@@@@@@@@
"Ummina anga wata, anga wata, yiriri!!! ", Sa'eeda da murnarta ta ke sanar ma Ummanta, dayake kusa dasu akwai masallaci wanda ladanin masallacin ne yayi shelar ganin watan, Umma dake zaune kusa da ƙofar ɗakinta tana shan iska tace " ALLAH ya sadar damu albarkarsa, ya kuma amsa mana addu'oin mun gaba daya," da "Ameen ", Sa'eeda ta faɗa wacca ke cike da zumuɗin ganin wata, don tun tana ƴar shekara 12 ta dena shan azumi, complete ta ke yi wanda har mamaki Ummanta ta ke yi ganin ko Nusaiba da ta ke budurwa da ƙyar ta ke yin azumi 15 Duk da tana shan na haila wanda wajibine ga duk wacca ta balaga saidai mai ciki, ko mai jinin biƙi, ko mara lafiya,wacca ta ke bi mata ma Zaliha itama duk kwanwar ja ce, balle Ilkima wacca ta ke sa'ar ƴarta sa'eeda.
"Yawwa Idi shigo da kayan ciki" Nusaiba ce ke bama wani almajiri wanda yake karatu a wata makarantar Allo dake kusa da gidansu, kwalin indomie ne da kret ɗin Kwai, carton ɗin madarar peak, Bournvita, da dai sauransu. Sai wani ɗadɗaga kai ta ke ita ga saurayi mai kud'i ya kawo mata Ramadan basket.
Umma Kande da futowarta kenan daga bayi ta cillara uban guda haɗe da faɗin"Arziki kashi, yau gashi ƴata ta tako mana ", harda wani rungume da murna.
Nusaiba dai sai murmushi ta ke kawai, don ita kadai tasan yadda ta samu ramadan basket ɗin, abinda Umma Kande bata sani ba shi ne, Nusaiba ta daɗe da zubar da mutincinta awaje, hasalima tun tana ƴar kimanin shekara 17 ta fara zubar da mutincinta,a lokacin Umma Kande na saida gyaɗa da aya soyayya, haka zata ɗora mata tallar tare da mata gargaɗin ta tabbatar ta saida sannan ta dawo gida, Umma Kande irin matan nan ne masu son abin duniya, da wannan gardaɗi da Umma Kande ta ke ma Nusaiba a kullum yasa ta fara bin maza, har daga ƙarshe ta zama gwana bata wannan hotel ɗin bata wancan, tanayi ne duk don faranta ran mahaifiyarta.
Yanxu ma wani sugar daddy ne ALLAH ya haɗata dashi, yana kashe mata kuɗi sosai kuma a lokaci guda yana amfanuwa da albarkatun jikinta.
**Ƴan Uwana iyaye mata, a rage son abin duniya da dogon buri, bakida gashin wance ba lallai sai kinyi kitson wanca ba, haƙiƙa iyaye mata wani lokacin mukan tafka kuskuran da a ƙarshe zamuyi dana sani mara amfani,ba dole saikin tsawatarwa ƴarki akan lallai saita saida ta kawo miki kuɗi ba, duk abinda ALLAH ya ƙaddara takawo miki sai ki godewa masa,ki roƙeshi yasa Albarkha,amma tirsasa yara musamman ƴaƴa mata akan sai an saida talla na ɗaya daga cikin abinda ke fara sasu bin maza wanda a ƙarshe siyo abin kunya,Allah ya tsare mana imani**
Sa'eeda dai da Ummanta kallon ikon ALLAH su ke yi kawai, don duk habaicin da Umma Kande takeyi da Umma Sa'eeda ne, amma ko ihhmmm batace mata ba hasalima da taga abun nasu ba gaɓa, ta ce ma Sa'eeda su wuce ɗaki, haka suka tattara tabarmarsu suka shige ciki abinsu.
Haka suka fara azumi abinsu, kuma ba laifi suna yinsa ciki kwanciyar hankali.
@@@@@@@@@@@@@
Azumi dai wasa wasa yasoma yin bankwana, don yanxu in sunkai sunkai na 25,har an soma shirye shiryen sallah, masu ƴaƴa tuni an siyawa yara kayan sallah, wasu ma har kala shida shida, kamar yanda hakan ta faru a gidansu Sa'eeda.
Abban Sa'eeda yama Nusaiba,Zaliha da Iklima ɗinkin sallah har kala biyu biyu,sannan kowacce da takalmi bancin wanda suka samu daga samarinsu , haka Umma Kande tafito da kaya niƙi niƙi waje daman saida ta fakaici Umman Sa'eeda na waje sannan tafito da kayan, da gayya take fito da kayan ɗaya bayan ɗaya tana faɗin "Kai! Kai!! kai!!!, daɗi kasheni, wannan gata haka, ƴaƴa masu ƙashin arziki bancin wanda babanku yayi kala biyu biyu har da wanda mazajenku sukayi(wai fa mazajenku😂😂😂su Umma Kande badai ilimi da sanin ya kamata ba).
Tana wannan surutan ne duk don ta ƙunsa ma Umman Sa'eeda baƙin ciki saboda tasan ba'ama Sa'eeda kayan sallah ba hasalima ita ta hanashi yayi mata, dan tsoranta yake sosai dalilin mugun asirin da take mishi akai akai tare da rufe bakin danginsa akan ƴar dukiyarsa wanda daga ita sai yaranta sukeci. Ko ƙala Umman Sa'eeda batace mata ba, saidai murmushi kawai tayi da girgiza kai,ita ba baƙuwar zafi bace hakan da Abbansu Sa'eeda yayi bai dameta don tasan watarana sai labari.Haka dai Umma Kande tagama iyayinta da kayan ta koma ɗaki.
@@@@@@@@@@@@@
KEBBI
"Oyoyo oyoyo mutan India, ashe dai da gaske kuke zakuzo sallah", Mum ce mai faɗin haka tana rungumar wata ƴar kyakkyawar yarinya mai kimanin shekara 3 a duniya da murmushi ita kuma yarinyar sai ciccijewa ta ke ita ala dole mai ƙyuya duk da sukanyi video call da ita hakan bai hanata nuna halin nata ba (ƙyuya) .
Wata kyakkyawar mata nagani ƴar wanka, fara tas kamar balarabiya ta ƙarasowa cikin falon tana samun guri kusa da Mum da faɗin "Washhhhh wallahi duk nagaji", cire veil ɗinta tayi wanda yayi daidai da kalan jallabiyarta marun,mai adon stones haɗe da veil ɗin, sannan ta russuna ta gaida Mum.
"Mum mun sameku lafiya? ", Mum da ta ke fama da Fanan ta amsa mata cike da kulawa tana faɗin "lafiya lau , ya mijin naki, ya aiki ", da "Duk lafiya lau" ta amsa mata
kai da Mum taga Fanan taƙi zama wurinta ta saketa da faɗin "Ja'irar yarinya zakizo hannu na ne" da gudu da haye saman cinyar mamata tana dariya sai duk suka fashe da dariya.
Mum tace " Sameera zoki ɗauki kayan Sadiya da tazo dasu kiwuce mata dashi ɗakinta", haka wata mai kimanin shekara 46 ta fito zuwa wurin Sadiya ta gaishe ta,Mum ce ta bada umarnin a dafa ma Fanan noodles taci.
@@@@@@@@@@@@@
Bayan sunyi wanka itada ƴarta a lokacin ankusa kiran sallar magrib dayake saukan yamma su ka yi, masallacin gidansu sukaji an kira sallah, sai suka fara haraman shan ruwa, sannan suka gabatar da sallah.
Bayan isha'i Sadiya ta wuce ɗakin Mum don yin hirar yaushe gamo,da sallama ta shiga, ganin Mum na lazimi yasata zaunawa a sofa tare da ɗaukar Fanan bisa cinya.
Sanda Mum ta kammala lazuminta har sarauniyar ƴan ƙyuya tayi bacci,Mum ce ta dawo itama kan sofar bayan ta cire mayafin sallarta,ƙara gaisawa sukayi sannan aka shiga hirar ƴa da uwa anan ne take sannar ma Sadiya dramar da tasha kafin Sadam ya yarda zuwa UK karatu.
Dariya Sadiya ta saki tana cewa "Mum ai duk ke kika sangartashi, in yana tare dake ji kike kamar ki komar dashi ciki, ba dole yaƙi yarda ba duk da most friends ɗinshi a nan KEBBI University suka samu admissions hakan bazai mai daɗi ba"
"Amma yasan qa'idar gidan ai, ke da Sakinah acan UK kukayi Karatunku", dariya Sadiya ta sukeyi tana fad'in "Auta ne fa", tsaki da ja Mum sannan tace " wallahi ranar Auta ya ɓatamin rai, da ƙyar na shawo kansa ya yarda da tafiyan" hamma Sadiya tayi tana faɗin "yanxu dai su Auta ana can ana boko, duk da nasan Auta da ƙoƙari Saidai sangarta in yana gabanki", Mum tace " Naji ina ruwanki imma yayi sangartar", wannan karon dariya Sadiya takeyi har da riƙe ciki "Ni!!! na'isa shiga tsakaninku", Mum tace "kyadai ji dashi", sallama sukayi don har 10:25pm yayi ta ɗauki Fanan suka nufi ɗakinta wanda tun tana budurwa ta ke ciki, ta shimfiɗar da Fanan sannan tabi lafiyar gado.
Washi gari kuwa har gidan ƴar uwarta Sakinah saida taje, nanma sukayi hira sannan ta dawo gida.
@@@@@@@@@@@@@
Yaudai ake sa ran ganin wata, Alhamdulillah da ƙarfe 11:45pm na dare Sarkin musulmi ya sanar da ganin wata,kowa sai murna yake, da addu'ar ALLAH ya karɓa ibadun da a kayi a watan.
Bayan an fito Idi Aunty Sakinarh da familinta suka iso gidan Mum, kasancewar mijinta tafiyar gaggawa ta samesa zuwa Germany. Maa shaa Allah🥰 Tabarakallah kawai na iya furtawa ganin wata hamshaƙiyar mata wacca baza tawuce shekara 28 a duniya ba, tasha peach colour lace da ratsin gold wanda ko makaho ya taba yasan lace ɗin na ɗaruruwan kuɗine, ga gwala gwalai ya cika mata wuya kasancewar ta ƴar duma duma, bayan awarwaraye da zobba a hannunta, ta yafa yalwataccan gyale mai adon stones da takalmi tu match, ga twins ɗinta Maa shaa Allah🥰 Tabarakallah, suma sun sha kyau.
Haka dai wannan family suka sha shagulgulan sallah, sai bayan sallah da sati ɗaya Sadiya ta koma India cike da kewar ƴar uwarta da mum ɗinta.
Bayan tafiyarta da kwana biyu Daddyn Sadam ya dawo Nigeria da yake yayi tafiya zuwa China akan wani harkar kasuwancinsa bayan ya gama ne ya wuce Saudia aikin Umra.
@@@@@@@@@@@@@
KADUNA
Bagaren su Sa'eeda sunyi shagalin sallah dai dai malisa, kaza ɗaya Umma Sa'eeda ta siyo musu suka yanka, suka soya suka ci, ita kuma Hajiya Umma Kande kaji ɗai ɗai har goma suka yanka haɗe da ginsamin naman shanu da Abbansu Sa'eeda yakawo taƙi rabawa taba Umman Sa'eeda, haka su Zaliha da iklima sukai ta suya tsabaragyan rashin mutinci a ƙofar ɗakin su Sa'eeda suka sa kaskon tuyar(Kai jama'a in kana duniyar nan kasha kallo😂😇), so suke Umman Sa'eeda ta tanka amma taƙi hasalima jawo ƙofarta tayi kasancewar akwai wutar nepa sai suka kunna fanka abinsu, duk wannan soye soyan da ake Nusaiba bata gida, tadai cema mamanta zataje tasha amsar saƙo wanda bata sanar da ita wani kala ne saƙon ba tun safe ta fita.
Ashe ashe Nusaiba tama sugar daddynta Alhaji Sagir alƙawarin goron sallah ne, yace su haɗu a hotel, saida tafito daga layinsu ta tari ɗan keke napep a lokacin tasa niƙaf da yake duk sanda zata hotel yin harka da niƙaf ta ke zuwa, tana isa hotel ɗin ta kira number sa, sai ya sanar da ita number ɗakin, sai da ta cire niƙaf ɗin sannan ta wuce direct ɗakin, isarta keda wuya ta ƙwanƙwasa, kamar jira Alhaji Sagir yake ya buɗe mata ta shige,ce mata yayi ta zauna yana son suyi wata muhimmiyar magana, ba musu ta zauna tana wani lanƙwasa da lashen lebe irin na tsoffin karuwan nan, (sai Kace mayya😀, Fans ai ita ta cancanta da zamowa mayyar ba Sa'eeda ba🙃).
@@@@@@@@@@@@@@
Alhaji Sagir zama yayi kusa da ita haɗe da rumgumota sannan ya ce"My sweet honey kinsan wani irin goron sallah nakeso kibani kuwa?
Nusaiba tace " Wanda nasaba baka mana ko akwai wani goron na daban ne?
Ɗan murmushi yayi sannan yace" Sosai ma kuwa my sweet honey"
cikin zaƙuwa Nusaiba tace "To sanar min naji sugar na"
Gyara kwanciyar Nusaiba yayi a ƙirjinsa sannan yace " Nusaiba inaso in ɗaga darajarki a duniya,zaki samu kuɗi kamar ba gobe,in har kika bani haɗin kai"
Ɗagon kanta Nusaiba tayi daga ji yace zai ɗaga darajarta a duniya sannan zatayi kuɗi, har ta fara harsaso yanda zata fantama da kuɗi ita da familinta wayyo daɗi
"Na yarda sugar na kuma zan baka haɗin kai"
murmushi yayi a zuci yake faɗin 'ai nasan zaki yarda mayyar kuɗi '
Ɗan lunfasawa yayi sannan ya cigaba da cewa "Inason in biya buƙatata dake ta baya ma'ana ba yanda na saba kasancewa dake ba kamar yanda kika sani, ta duburarki nakeson biyan buƙatana dake,sannan zan turamiki dubu ɗari biyar #500,000 in kin yarda kuma zan haɗaki da abokaina suma masu irin wannan harkar, wallahi Nusaiba kin gama kuɗancewa in kin yarda amma"
Shiru Nusaiba tayi tana tunani ta yarda ko ko A'a, can da ta tuna mamanta zataji daɗi kuma sun kuɗance, kawai saita amince(Ya Salam, Allah ka tsaremu daga faɗawa halaka da kuma zugar shayɗan).
Jin ta amince yasashi sakin wani munafikin murmushi, don haƙarshi ta cimma ruwa.
Haka suka fada halaka ita dashi duk da tasha baƙar wuya saboda farkon yinta kenan, bayan sun kammala masha'arsu sukayi wanka, ita Nusaiba har da gashi tayi don taji maza(kwaɗayi ma muɗin wahala🙃🙃🙃), sai huɗu na yamma ta iso gida duk da yanayin tafiyarta ya sauya amma Umma Kande bata gane wani abu game da Nusaiba ba, hasalima murna ta ke tayi saboda Nusaiba ta siyo kayan abinci haɗe da wasu kajin duk acikin kuɗin da Alhaji Sagir ya saka mata a account, murna iya murna Umma Kande tayi harda yima Umman Sa'eeda gori ƴarta batada mashinshini. (Umma Kande anyi bagidajiyar Uwa🤔).
@@@@@@@@@@@
Tunda daga wannan ranar Nusaiba ta zama ƴar hannu don Alhaji Sagir ya haɗata da abokanansa suna sharholiyarsu da ita.
Duk fantamawar da Nusaiba ta ke da kuɗi ko ajikin Umma Kande hasalima gadara ta ke ƴarta nada farin jinin samari, haka suma ƴan uwan nata duk da basa sharholiya irin nata amma suna ɗan matse matse da taɓe taɓe a zauran gidansu su da samarinsu.
Sa'eeda dai hutunsu ya ƙare sun koma makaranta,yanxu tashiga SS2, samari sun fara kai mata hari kasancewar ta kyakkyawa ga sexy eyes farare tas, gashi tanada ɗan girman jiki, don duk halittar ƴa mace ta gama bayyana a jikinta duk da ƙarancin shekarunta don yanxu take cikin shekara na 16,amma Maa shaa Allah.
Sa'eeda ta ɗaukar ma kanta alƙawarin sai ta kammala secondary kafin ta fara soyayya saboda soyyaya bata cikin tsarinta kwata kwata.
@@@@@@@@@@@@@
ABUJA
Ɗaki ne mai duhu sai ɗan wani haske kaɗan da nake ɗan iya hangowa wanda bai wadaci ɗakin ba, ga tururin hayaƙi daya turniƙe ɗakin, ni kaina da kyar na iya shiga ɗakin haɗe da addu'a dan ɗauko muku rahoto, wasu surutai kamar suddabaru naji muryar wata tana faɗi wanda nakasa gane mai ta ke cewa, kwatsam naga wani haske kamar walƙiyar ya ɓullo ta cikin bangon ɗakin ya haska ko'ina, wani halitta nagani kamar mutum amma wada, kansa a ƙasa yake, shi baiyi ƙasa ba kuma bayi sama ba, yana a tsakatsaki, tsawansa bai wuce tsawan hannu ba, sai rangwajejan kai kamar ƙwarya,yanada idanuwa kamar na mage, da sharɓa sharɓan kafakuwa kamar na babban mutum, kai in taƙaice muku, halittar nan batada kyawun gani hasalima mai ciki zaka iyayin ɓari ganin wannan muguwar hallitta.
Matar da naji na surutai sanda babu haske a ɗakin na sake kai dubana gareta tsohuwace amma ba can can ba, zata kai kimanin shekara 78 a duniya saidai a idanuwa kaɗaine zaka iya ganewa amma jikinta mai kyaune kamar ƴar shekara 40 a duniya. Sujjada naga tama wannan halittar, (wa'iyazubillah)..............................
Daga alk'alamin
🖍️📚Narnarhh Bukar📚🖍️
Comments and share 🙏🙏🙏Fisabilillah.
[4/25, 1:38 PM] +234 814 129 2044: 🏵️ NACINA YAJAWOMIN🏵️
Narrnarhh Bukar✍️
🌹Perfect Essential Writer's
Association🌹
✨ P. E. W. A✨
Wattpad:@AISHAABUBAKAR812
Arewabook:Narrnarhh002
7----8
Sujjada naga tayiwa wannan halittar tana cewa "yakai Sarkin Tsageru! yakai gagara badau!! , yakai buhun ƙara kafi ƙarfin danna!!!, ya kai Shugaban matsafan duniya!!!! , haƙiƙa ka cika alƙawarinka gareni akan bullowarka bayan shekara 43 da suka wuce, kuma ina nan ina bin dokokinka da ka sharɗantamin". (toh shikuma wannan nashi salon tsafin kenan sai bayan shekaru aru aru yake bayyana, babbar magana 🤔🤔🤔).
Wata dariya naji har ƙasa na girgiza ashe wannan halittar ne ke busar dariya, can ya tsagaita kamar ruwa ya ɗauke ya fara magana jikake kamar ƙasa zata tsage
"Haƙiƙa kinbi sharudɗanmu na ƙin sallatar Asr da Subh tare da ƙin azumin watan Ramadan haɗe da sadakar baƙaƙen karnuka 50 duk shekara, lallai ke tamu ce! Ke tamu ce!!!
Sai kuma ya fara kuka kamar ana ruwan sama can kuma ya tsaya,(fans nifa hallittar nan ta kusa sani fitsari tsabaragen tsoro, da ƙyar na iya tsayawa dan ɗauko muku rahoto 😖😖😭).
Sai can ya cigaba da cewa"Irinta basu gushe a doran ƙasa ba suna nan har yanzu, wasu na a cikin ƙasƙanci wasu na a cikin farin ciki ,tabbas sai sun dawo bada jimawa ba, wannan haka yake, he! he!! he!!!
A razane ta ɗago kanta zuciyarta na dukan tara tara cikin rawar murna da inda inda ta fara magana " Su..... Suss.... Sussa nan a ra.... raye da... daman basu mutu ba?
Daka mata tsawa yayi yana magana cike da amon muryar"Karya zamuyi miki,dole ne su dawo, munyi iyayinmu sun gagaremu, suna sallah biyar kullum arana, suna nafila, suna azkhar na safe da na rana, suna azumi, suna Tasbihi da Hailala"
Cak ya tsaya ya kuma sake fashewa da kuka wanda yafi na farko ko ita kanta ta razane matuƙa ainun, sai kuma ya dakata da kukan sai ya ɗora daga inda ya tsaya a magana " kullun sai sun karanta baqara mu kuma bamaso,ruhunsu baya zama wuri ɗaya,lokacin dawowarsu yayi dole su dawo!!!
Ita dai har fitsari ya soma zubo mata, can kuma ya ce"Mun muki alƙawarin halittar jikinki zata tsaya ahaka in har kika cigaba da bin sharudɗanmu, zan koma, zan koma sai bayan shekara 5!!!
Lokaci kuda hasken ya ɗauke kamar ɗaukewar ruwan sama, haka dai ta tashi jiki duk a sanyaye ta boye kayan tsubbunta a wani akwati mai shegen kyau sannan ta kuma sashi cikin wani akwati babba tasa a ƙarƙashin tamfatsetsan kadonta na alfarma wanda ko queen Elizabeth sai haka(🙃🙃🙃).
Duk wannan gyaran da ta ke yi bayan ta kunna bulb din ɗaki ne, dayake can cikin salisalin dare ne wanda alokacin bayin ALLAH suke ganawa da mahaliccinsu amma ita da shaydani ta ke ganawa dashi (ALLAH kasa mufi k'arfin zuciyoyinmu).
@@@@@@@@@@@@
Haka ta kwanta cike da tashin hankali duk da tawani bangare ya mata alƙawarin barin mata halittar jikinta batare da tsufaba, sai kuma kareta da familinta gaba daya, shi ne kadai yake sassuata mata zuciya.
Ta jima bacci ɓarawo bai saceta ba, sai gabanin sallar asuba bacci ya ɗauke ta.
Washe gari sai wurin ƙarfe 11:17am na safe ta tashi, ita daman ba sallar Subh ta ke yi ba. Ƙwankwasa kofar ɗakinta naji anayi, ko kala batace ba, sai kusan minti 8 kafin tace "A shigo" , wata mata ta shigo ƴar kimanin shekara 50,babu sallama saboda tasan halin Uwar ɗakinta, ta tsufa sosai hasalima tafi uwar ɗakinta tsufa, za kayi tunanin ko ita ƴar aikin ce yayar.
Shigowa tayi har wurin makeken gadon uwar ɗakinta kana durƙusa haɗe da gaisheta "Barkha da safiya Hajiya"
wacca aka kira da Hajiya dake kwance ta tashi zaune da faɗin "Barkha"
Mai aikin tace "An shirya abincin a dining room Hajiya ",
"To" kawai tace sannan ta wuce bayi don yin wanka.
Ita ko mai aikin karatun zuci ta fara'Toh wai lafiya naga yau batama son yin magana, meke faruwa ne', tunda babu mai bata ansa ta tashi ta fita daga ɗakin.
Hajiya ta fito daga wanka ta shirya cikin haɗadɗan boyel lace milk color wanda ya ɗinku wurin masana ɗinki kuma ya zauna mata a Jiki ɗas,takalmi ta saka wanda ya dace da kayan, sannan ta sauko zuwa ƙasa don yau batajin hawa lifter kasancewar akwai lifter a gidan.
Saukowa tayi zuwa dining room don karin safe, baya ta kammala ne ta fito falo, kallon falon nayi wanda ya tsaru iya tsaruwa, saikace falon shugaban ƙasa saboda yanda naga annarka dukiya a ɗakin kai in taƙaice muku gidan ma gaba daya ya haɗu don idan kashigo gidan zakayi tunanin a Dubai kake, zama tayi sannan ta kanna TV.
@@@@@@@@@@@@@
Ƙararrawar ƙofar aka danna, alamun ana son shigowa, bata tashi ba sai dai naji tana kiran"Saude zo ki buɗe"
Mai aikinta naga tafito daga kitchen da sauri ta nufa ƙofar, budewa tayi sannan da ɗan ja baya, wata budurwa nagani mai kimanin shekara 17 tashigo da gudu da faɗa jikin Hajiya tare da fad'in"Granny I really miss you alot, da ƙyar dad ya barni nazo Nigeria saboda rashin tsaro"
Magana ta ke ma Hajiya amma cike da shagwaba, murmushi Hajiya tayi don yau bata cikin good mood ɗin magana, shafa bayanta tayi tana faɗin"yanxu ai gaki a Nigeria koh"
murmushi budurwar tayi sannan tace "Granny bara naje nayi wanka I'm very tired" da "ok" Hajiya ta bita dashi.
Gaskiya a rayuwarta tana tsanani son ahalinta don zata iya komai don farin cikinsu, yaranta uku ne duk mata, biyu suna aure a cikin garin Abuja ita kuma ɗayar wacca ta ke ƙaramarsu tana aure a UK da yarinyarta ɗaya Fadila wacca tazo Nigeria hutun 1 week.
Amina itace babbar 6arta wacca ta ke da yara biyu duk mata amma sunyi aure da kuma yaransu,sai Jamila mai yaro daya shima yayi aure da yaro ɗaya.
Duk babbar sallah duka familin suke haɗuwa don yin shagulgulan sallah.Fadila bayan tafito ta wuce taci abinci sannan ta dawo wurin grannyn ta don yin hira, a nan ne ta ke sanar ma Hajiya zuwa next year zata shiga Oxford University don karantar bagaren jarida.
Haka suka cigaba da hirarsu sannan kowa ya nufi ɗakinsa ita Fadila taje sallah duk da ba iya sallar tayi ba ita kuma Hajiya ta wuce ɗakinta don yin bacci,Wannan kenan.
@@@@@@@@@@@@@@@
KADUNA
Zaliha ce tafito da kayan wanki tanayi, sai taji an kwaɗa sallama, ɗagowan da zatayi tayi arba da Maman jummalo da ita Jummalon, haba sai ta saki wankin ta ruga da gudu ta rungume Jummalo, itama Jummalo rungume tayi tana murna, ƴar uwar sharholiya ta dawo, ji kawai sukeji ance "Ai saiki saketa ta huta mana, kin wani rirriƙeta sai kace za'a ƙwace maki ita"
Umma Kande ce tafito daga ɗaki jin Zaliha na ihu, Maman Jummalo ce ta nufi ɗakinta wanda yake kusa da na Umman Sa'eeda,ta buɗe ta shiga,Jummalo ma shiga tayi sai Zaliha tabisu da kayan da suka zo dashi tana murna.
Maman Jummalo ƙawar Umma Kande ce kuma ta hannun damarta, duk wani makirci tare suke ƙullashi,mijin Maman Jummalo ya rasu kuma abokin Abbansu Sa'eeda ne, shiyasa bayan mutuwarsa yaga ya dace ta zauna gidansa tunda daman a gidan haya suke kuma ƴan uwansu suna ƙauye da zama, wannan shi ne dalilin fara zaman Maman Jummalo a gidan.
Sai kuma akayi rashin sa'a halinsu yazo ɗaya da Umma Kande nan da nan suka ɗinke suna gallazama ma Umman Sa'eeda, batajin daɗinsu kwata kwata, sun haɗe mata kai. Tafiyar Maman Jummalo da Jummalo ƙauyen su ne Umman Sa'eeda ta ɗanji sassauci kaɗan.
@@@@@@@@@@@@@@
Kasancewar Umman Sa'eeda bata gida taje barka a maƙotansu wa'inda suke ɗan abun arziƙi yasa bata san da dawowarsu ba, itama Sa'eeda taje makaranta.
Umma Kande ce ta shigo da kula mai kyau da abinci sai kuma jug ɗin ruwa mai sanyi tana ƙara musu sannu da zuwa, Maman Jummalo ta amsa da fara'arta tana faɗin "Har da ɗawainya ƙawas"
Umma Kande tayi murmushi ta ce "Haba ƙawas ai babu komai, bari kedai gama cin abinci mufara chapter"
dariya Maman Jummalo ta kwashe dashi tana cewa " Haba dai ƙawas bara naci sai mufara sana'ar".
Haka dai Maman Jummalo da Jummalo suka kammala cin abinci, ita Jummalo ta wuce ɗakin Umma Kande don yin hira da ƴan uwanta Zaliha da Iklima Kasancewar manyan mata Nusaiba bata nan ta tafi nata harkokin(Ni kuma nace ta tafi tata sana'ar karuwanci ba koya kukaci my esteem fans🙃😂).
Maman Jummalo ce ta fara magana "ƙawas naga sauyi sosai a gidan nan, ko Babansu Nusaiba ne ALLAH ya buɗa masa ko ko Musa ne halan "
murmushi Umma Kande tayi sannan tace"Ai ƙawas duk basu bane hasalima Musa na Calabar kasuwanci ,Nusaiba ce ALLAH ya haɗata da wani attajirin mai kuɗi Alhaji Sagir, yana matuƙar sonta,kuma yana sakar mata kuɗi sosai, to shi ne ya gyara mana wannan gidan ai"
Ɗan jimmm Maman Jummalo tayi a zuciyarta tana faɗin 'zama bai ganni ba, dole Jummalo tasamo saurayi mai kuɗi wanda muma zamu fancama'
Umma Kande ce ta katse mata tunani da faɗin"Ni na kawo wata shawara yanzu, mai zai hana mu komawa wurin boka Sankeru ya samoma Jummalo, Zaliha da iklima samari masu kuɗi kamar yanda Nusaiba tasamu mai kuɗi kinga shikenan munyi sallama da talauci ko ya kikace ƙawas"
Shiru Maman Jummalo tayi tana nazari acikin ranta tana faɗin 'Kamar kin shiga raina aminiyar ƙwarai, nima nayi wannan tunanin saboda gaskiya bazan koma ƙauye ba'
Can ta fara magana "Gaskiya yau nasan kin cika aminiyar arziƙi mara baƙin ciki don da wata ce shikenan ta daina abota dani"
Murmushi mai sauti Umma Kande tayi tare da cewa "Ai a duniya banga abinda zaiza nabar abota dake ba, kin manta, kefa ce kika fara haskamin hanya har nazo wannan gaɓar kuma sai nabarki, a'a ba haka nake ba"
Ɗan dariya Maman jummalo tayi da cewa " Shiyasa nake yinki Over kawas".
Tare suka saki dariya haɗe da shewa harda tafawa, can Maman Jummalo tace" Wai ina waccan mayyar da ɗiyarta su ke ne, naga banji motsinsu ba"
dariya tasaki da faɗin"Ohon musu naga ɗazu ta fita ita kuma ɗiyarta ta tafi gantali wai acewarta makaranta, ni kinga yanxu wallahi basu a gaba na, don na gaba yayi gaba"
Dariya Maman Jummalo tayi sannan tace"Da kyau ƙawas kina wuta Ina binki ta petrol " tare suka sake kwashewa da dariya.
Umma Kande ce tace" Ranar lahadi saiki shirya muje wurin boko Sankeru ɗin", Maman Jummalo tace "To ALLAH ya kaimu".
@@@@@@@@@@@@
Haka suka cigaba da hirarsu, a nan ne sukaji sallamar Umman Sa'eeda amma babu wanda ya amsa, ita dama ta saba ko akwai mutane a tsakar gida babu mai amsa mata sallama ita da ƴarta ( Hmmmm wannan rayuwa🤔).
Ɗakinta ta wuce babu jimawa sai ga Sa'eeda ta shigo itama da sallamarta haka akai banza da ita, ta shiga ɗaki da sallama sai ta gaida Ummanta tare a rataya jakarta, ta ɗauki buta sannan ta nufi bayi da sauri saboda fitsari ya matseta tun a hanya.
Bayan ta fito daga bayi tayi kiciɓis da Maman Jummalo ta fito daga ɗakinta, sanin Maman Jummalo ta tsanesu yasata razana tare da ɗan russunawa da gaisheta.
Wani mugun kallo Maman Jummalo ta ke ma Sa'eeda a zuciyarta tana faɗin 'Haka wannan yarinyar ta dawo, ga kyau kamar mayya, ga diri saikace wata babbar mace,ko ƴan matan gidan duk tafisu kyau, gata da gashi kamar mamanta, ai dole na tsaneki tunda kinfi ƴan matan gidan nan kyau,gashi kyaunta yanxu yake ƙara bayyana'
Duk wannan zancan a zuci Maman Jummalo takeyinsa, ko amsata batayi ba ta wuce abinta, daman Sa'eeda tasan hakan zata kasance,tafiyarta tayi abinta tayo alwala ta wuce ciki.
A ɗaki kuwa Sa'eeda ke hira da Ummanta, tana cewa "Ummina mun kusa hutun babban sallar, mai zai hana muje ƙauyen Damari sallah, don mun rabu da zuwa tunfa banida wayo"
Shiru Umman Sa'eeda tayi tana sauraranta, can tace " Hakane kuwa, sai muje tunda kinason zuwa,babbar sallarma ai saura kwanaki yanzu"
Duk da Umman Sa'eeda ba son zuwa ta ke ba, saboda ba daɗin garin ta ke ji ba, haka suka cigaba da hirarsu.
@@@@@@@@@@@@@
Yau ta ke lahadi, su Umma Kande tun daren jiya suka kintsa tsaf saboda inda boko Sankeru yake akwai nisa don a machine ake zuwa wurin dajin sai a ƙarasa da ƙafa still shima ɗin akwai tafiya sosai, haka su ka ƙula sammako sai tasha,sai suka hau motar ƙauyen da dajin inda boko Sankeru yake,bayan sun sauka sai suka hau machine guda saboda k'arancin ƴan machine a ƙauyen , haka sukai ta tafiya har aka sauke su a wani gefen daji,Umma Kande ta biya mai machine sannan suka dosa dajin da tafiya a ƙafa.
Sunsha lafiya sosai kana suna isa wurin wata ƴan bukka wacca ta ke zagaye da manya manyan bishiyoyin kuka sunkai bakwai kana suka tsaya, dukkansu cire takalma sukayi sai suka fara tafiya da baya da baya har suka shiga bukkar(Fans kunsanni da ganin ƙwaƙwaf haka nabisu ciki don ɗauko muku rahoto🙃😇😇). Shigarsu keda wuya naga sun zube ƙasa suna mai kirayi kamar haka "Sankeru namu Sankeru na duk mai son ya dace,Shugaban matsubban duniya, Ka cire tuta,Kowa na bayanka, gamu yau munzo da ƙoƙon bararmu agareka mai share kukanmu", (Wa'iyazubillah, ALLAH kasa mufi ƙarfin zuciyoyinmu, wannan kafirci haka duk don son abin duniya🤔).
Bukkar naga tafara girgiza kamar samanta zai buɗe, ga bishiyoyin kukan nan sai jijjiga suke,ga wani irin wari mai saka mutum kamar yayi amai ya fara tasowa (my esteem fans dole na saka nose mask ɗina saboda warin da yake tasowa don idan bansaba sumewa zanyi shikenan ba ɗauko muku rahoto 😷😷😷), wani jibgegyan mutum ya bullo cikin bukkar kamar walƙiya, mummuna dashi, ga ƙaton timbi kamar randa, gashi a tsirara ya bayyana garesu, Umma Kande da Maman Jummalo sai duƙar da kai suke, duk da ba zuwansu na farko bane.
Bayyanarshi keda wuya ya fara tintsirar dariya, timbinsa na wata girgiza kamar ana bubbugata ƙwarya ,can bayan yaɗau wasu ƴan mintuna yana sheƙa dariyarsa can kuma ya tsaya a sannan ne ya fara magana cikin sautin da yake sa bukkar girgiza haɗe da bishiyoyin yana faɗin"Basai kun ɓata makunanku wurin sanarmin ba nasan meke tafe daku, kuma wannan kamar yankar wuƙa ne, amma kunason ƴaƴan naku susamu kowani irin masu kuɗine"
Cikin ladabi suka amsa da"Eh mai sha re kukanmu"(Ni kuma nace zai saku ku cikin wahala da bala'i ba😂😂😂).
Dariya ya kuma sakeyi wannan karon harda miƙewa yana taka rawa da juyi duk ilahirin jikinsa yana raws saikace wani alade in yana gudu,su Umma Kande kansu dai har yanxu a duƙe yake, can kuma ya dakata da rawar, sannan ya nufa wata ƴar ƙwarya ya ɗauko kullin magani ya cilla musu da cewa "Ku basu acikin abinci suci dukkansu alokaci guda"
Godiya sukai ta faman yimishi tare da kirari, daga baya Umma Kande taciro kuɗi zata miƙa mishi sai ya dakatar da ita da cewa"Yau jikinku shi ne fansarku don haka kowacce saina kwanta da ita"
Basu kaɗai ba har ni mai ɗaukar rahoto saida na zaro ido, sake cewa yayi " In kuma kukayi jayayya to tun anan zaku fusanci hukunci don dole sai kun haukace"
Da sauri suka amsa da"Mun aminci "
Dariya ya kece dashi ya faɗin" Shegu mayun kuɗi", can ya sake miƙewa yana taka rawa kamar alade(Fans anya wannan bokan bai fara hauka ba, wannan irin rawa haka😂😂😂).
@@@@@@@@@@@@@@
Da Maman Jummalo aka fara masha'ar, saida ya shafe tsawan awa 2 cur kana tafito dayake Umma Kande tafito waje saboda umarnin boka Sankeru, sai Umma Kande ta shiga yayi bidirinsa da ita har tsawan awa biyu da rabi sannan itama ta fito.
zai goge zufa sukeyi, haka suka lallaba har zuwa bakin dajin duk jikinsu sai wari yake kamar mushe, can Umma Kande tace"Wai ba naga kamar kin ɗauko turare ba sanda zamuzo har kika sake fesawa a mota"
Maman Jummalo tashe"Wannan haka yake bara na ɗauko mufesa don kar a ƙi ɗaukar mu''
Da ƙyar suka samu mai machine suka hau su biyu, basu suka dawo gida ba sai wurin yamma lilis.
A daren kamar yanda boka Sankeru ya Umurcesu, suka sa musu maganin cikin abinci suci a tare, kamar yanda yace.
***Gareku ƴan uwana mata, haƙiƙa wani lokacin idonmu yakan rufe saboda abun duniya kamar yanda su Umma Kande da Maman Jummalo nasu ya rufe ruf, saboda son abin duniya mai ƙarewa suka lalata rayuwarsu da na ƴaƴansu baki ɗaya, haƙiƙa sun tafka babban kuskure domin ko sallarsu bazata amsu ba har na tsawan kwana arba'in kuma sun kafirta kamar yanda yazo acikin hadisin manzon ALLAH (S. A. W) yana cewa "Duk wanda yaje wurin boka ko mai duba haƙiƙa ya kafirta kuma sallarsa baza ta amsu ba har na tsawan kwana arba'in",.ALLAH kasa mufi ƙarfin zuciyoyinmu gaba ɗaya.***
@@@@@@@@@@@@@
Tun daga ranar su Umma Kande sukaga sauyi wurin ƴaƴansu don yanzu kowacce cikinsu nada saurayi mai kuɗin gaske gashi suna sakar musu da kuɗi sosai. Tabbas kamar yanda Umma Kande tace sunyi hannun riga da talauci lallai kuwa sunyi don suna fantamawa da kuɗi sosai.
Bangaren su Sa'eeda sun fara shirin 1st term exams na SS2 har time table ya fito, ita da uwarta basa shiga sabgar ƴan gidan haka Abban Sa'eeda yanxu ko ɗakin Umman Sa'eeda ya daina shiga kwata kwata. Sa'eeda karatu ta ke baji babu gani, yanda ta ke karatu zakayi tunanin a University ta ke, haka sukayi exams ɗinsu cikin hukuncin Ubangiji.
A lokacin saura kwana biyu sallah, haka suka fara shirye shiryen tafiya ƙauyen Damari, ana gobe sallah kuwa suka kama hanya.
@@@@@@@@@@@@@
ƘAUYEN DAMARI
Dayake da safe sukayi tafiyar, sai wurin 11:00am na safe suka iso tashar garin, haka suka ɗau mai machine da ƴan kayansu kala bibbiyyu saboda ba daɗewa zasuyi ba. Wani gida mai ginin ƙasa naga mai machine ɗin ya faka, suka sauka Umma Sa'eeda ta biya mai machine ɗin kana suka shiga cikin gidan da sallamarsu.
Wata tsohuwa nagani mai kumanin shekara 69 zana zaune kan tabarma tare da ita kuma ɗan ƙaramin radio ne tanajin labarai, ganinsu yasa wannan tsohuwa miƙewa zunbur kamar an tsikareka tana faɗin "Miya kawoki gidan nan, ba nace miki karki kuskura na sake ganin baƙar ƙafarki agidan nan ba"
Russunawa Umman Sa'eeda tayi cike da girmamawa ba tare tabi takan zantuttukan tsohuwar ba ta gaishe ta, ƙin amsawa tayi tare da cewa"Riƙe gaisuwarki, in kinje birni tamiki amfani marar asali kawai"
Hawaye suka fara kwaranya a idanun Umman Sa'eeda, a zuciyarta tana faɗin 'ALLAH ka kawomin mafita nida ƴata, kabamu ikon cin wannan jabawar'.
Jin sallamar wani dattijo mai kimanin shekara 76 amma inka ganshi zakace baikai haka saboda jikin mutan da dana yanzu ba ɗaya bane,shigowarsa ya katse mata tunani da faɗin"Lale marhabin da mutan birni, Hussaina ce nake gani ba'a mafarki ba"
Umman Sa'eeda ne juyo tare da russunawa wurin gaisheshi da cewa"Baba mun sameku lafiya"
Cike da murna Baba ya amsa da "lafiya lau Hussaina, ya kuke, ya bayan rabuwa"
Umman Sa'eeda tace"Alhamdulillah Baba duk sunce a gaisheku"
suna cikin gaisawa wannan tsohuwar da katse musu hirar da faɗin "Tsintacciyar mage bata taɓa zamowa mage"
Daka mata tsawa tsohon nan yayi tare da cewa "Ladi ya isheka haka, wannan gidana ne, kuma ni nakeda iko akansa bake ba, kar na sakejin maganarki anan, ko kuma ranki in yayi dubu wallahi sai ya ɓaci", (Fans dama tsoho kamarsa yana fad'a haka, tabbb, ni nayi nan karya had'a dani wallahi🙃🙃🙃).
Shiru kuwa wacca aka kira da Ladi tayi , can kuma ta wuce ɗaki, juyowa yayi gun Umman Sa'eeda tare da cewa"Kiyi haƙuri nasanki da haƙuri kamar mahaifiyarki, ga ɗaki can kukai kayanku ciki,zansa Mairi da girko muku abinci yanxu"
da "Toh" Umman Sa'eeda ta bishi dashi, Sa'eeda mutuwar tsaye tayi tunda suka shigo gidan da farajin masifar Ladi ta tafi nisan zango a ranta tana cewa'Wai yaushe zamuyi masoya a duniya, kowa bai son mu,toh meyasa ta ce Ummina batada asali, daman ba ita bace kakata toh wacece kakata................
Daga alk'alamin
🖍️📚Narnarhh Bukar 📚🖍️
Comments and share 🙏🙏🙏Fisabilillah.
🏵️ NACINA YAJAWOMIN🏵️
Narrnarhh Bukar✍️
🌹Perfect Essential Writer's
Association🌹
✨ P. E. W. A✨
Wattpad:@AISHAABUBAKAR812
Arewabook:Narrnarhh002
9----10
Sa'eeda mutuwar tsaye tayi tun daga shigowa gidan da kuma farajin masifar Gwaggo Ladi ta tafi nisan zango a ranta tana cewa 'Wai yaushe zamuyi masoya a duniya, kowa bai son mu,Toh meyasa ta ce Ummina batada asali, daman ba ita bace kakata, toh wacece kakata, kenan Gwaggo Ladi ba ita bace ta haifi Ummina ba'.
Haka taita karatun zuci daga ƙarshe ta dauki kayansu zuwa inda Baba ya umurcesu, ɗaki ne ɗan ƙarami da ƴar katifa itama ƙarama wacca batafi ta kwanciyar mutane biyu ba, sai labulen ƙofa da na window, ɗakin ba laifi a gyare yake kamar ansan da zuwansu.
Ciki ta iske Ummanta a zaune akan katifar tayi tagumi, da sauri Sa'eeda ta ajiye kayan hannunta ta nufi gun Ummanta don arayuwarta bata ƙaunar ganin damuwa a fuskar Umman nata, haka da sassarfa ta isa gunta tare da cewa " Ummina don ALLAH kidena tagumi, Banaso please kidaina "
Sai kuma ta fashe da kuka,har da shashsheka, don ita ta rasa wannan baƙin jinin da suke dashi, kowa baya sonsu, ko a makaranta haka ta ke fuskantar tsana da tsangwama daga ƴan ajinsu, wurin Maryam kaɗai ne ta ke samun sassauci.
Ummanta ne riƙo haɓarta tare da girgiza maka kai alamun tayi shiru duk da itama kanta hawayan ne suke kwaranya a bisa kuncinta tare da cewa " Duk wani ƙunci da tsanani maganinsa yana ga UBANGIJI ne, haƙuri da juriya suna kai mutum mataki babba arayuwa, kasancewarmu a wannan yanayi baya nuni akan dawwamarmu cikinsa, don haka mu cigaba da haƙuri tare da juriya wataran sai labarin kinji sanyin idanuwa na"
Sa'eeda da tunda Ummanta ta fara magana ta ke shashshekar kuka ɗan ɗaga mata kai tayi tare da tambayarta alokaci guda " Ummina meyasa Gwaggo Ladi ta kiraki da mara asali?
Tirƙashi lokaci guda yanayin Umman Sa'eeda ya sauya ita a tunaninta Sa'eeda bataji surutan Gwaggo Ladi ba, saida ta ɗan sauke nauyayyan ajiyar zuciya kafin ta fara magana "Banso kika ji zantuttukan Gwaggo Ladi ba, hasalima shiyasa tun kina ƙarama rabona da zuwa garin nan saboda banason hankalinki ya tashi,nabar hakan ya zamo sirri agareni ba tare dana sanar miki ba, amma tunda allura ta tono garma, kibari anjuma da daddare bayan munyi sallar Isha'i sai na baki tarihina kamar yanda nima mamata ta sanar min, kinji"
Sa'eeda da ke kallon Ummanta ta amsa da "Toh, ashe nima inada kaka"
Murmushi Umman Sa'eeda tayi ganin wauta da shirme irin na Sa'eeda tare da cewa "Daman ance miki babu wanda baida kakane, kema taki ALLAH Yayi mata rasuwa ne"
Ɗan lunshe sexy eyes ɗinta Sa'eeda tayi sannan ta ce " Allah ya kai haske a ƙabarinki kakata da na al'ummar musulmai baki ɗaya"
da "Ameeeeeen", Umman Sa'eeda ta bita dashi, kana suka cigaba har hirarsu.
@@@@@@@@@@@@@@
Kamar yanda Baba ya faɗa za'a girko musu abinci hakan ta kasance, don ɗan saƙon da aka aika gidan Mairi yana sanar ma ta fara murna saboda duk acikin ƴaƴan Gwaggo Ladi tafi kowa sonta tare da mahaifiyarta kafin ta rasu.
Habawa ai da ɗan aiken ya sanar mata, daman tana kiyon zabbi , kaji da awakai, sai tasa a yanka mata zabbi guda biyu, bayan an yanka mata su, tayi zaman gyaransu ita da ƴarta mai kimanin shekara 14 dayake bata haihu da wuri ba,sannan ta ɗora sanwan girki, tayi musu tuwon dawa da miyar kuka wacca tasha manshanu haɗe da naman zabbi duk da ba duka tayi miyar dasu ba, ta soya sauran tasa alanga haɗe da na tuwon da miyar, nan fa ta aiki ƴarta ta dashi a babban kwando.
@@@@@@@@@@@@@
Da sallama ɗiyar Mairi ta shiga gidan, sai tayi sa'a Gwaggo Ladi na ɗaki kasancewar lokacin azahar ne, sai ta wuce ɗakin baƙi dayake mamanta ta faɗa mata inda baƙin suke.
Sallama tayi a lokacin Sa'eeda na sallah ita kuma Umman Sa'eeda ta kammala sallah tana zaune,jin anyi sallama yasata amsawa tare da cewa"A shigo"
yarinyar ce ta shigo tare da russunawa ta gaisheta, Umman Sa'eeda cike da fara'a ta ke amsa mata ganin kamannin ƴar uwarta ta kuma masoyiyarta wacca bata da kamarta, cike da ladabi yarinyar ta ce"Mamata ta ce gashi in kawo muku kuma tana muku sannu da zuwa, gobe bayan sallar Idi tana nan zuwa "
faɗaɗa murmushinta tayi da faɗin" ALLAH ya kaimu, kice mata ina godiya sosai, sannan tsarabarta na nan saita zo"
yarinyar tace "Toh", har lokacin Sa'eeda na sallah bata idar ba.
Yarinyar na tafiya Sa'eeda ta kammala sallah,ta cire hijab ɗinta suka fara cin abinci, duk da yau ake hawan Arfa, Sa'eeda na period ita kuma Umman Sa'eeda na fama da chronic ulcer kuma yanxu an ɗorata akan magani shi ya hanata ɗaukar azumin Arfa. Haka suka kammala cin abincinsu tare da hamdala sannan kowa ya sami wuri don warware gajiyar tafiya.
@@@@@@@@@@@@@@@
Baba dai har lokacin bai dawo ba, dayake Umman Sa'eeda tasan ɗabi'arsa na sai bayan Isha yake dawowa, yau ma sa'a tayi ganinsa a gidan.
Bayan sallar Isha ya dawo gida, ita dai Gwaggo Ladi alwala ce ta ke fito da ita sai kuma girkin abin shan ruwa da tayi su kaɗai ne yasaka ta fitowa don ita ta tsani Umman Sa'eeda matuƙa ainun gashi tana aure a birni ita kuma yaranta a ƙauye dukkaninsu suke aure, a duk sanda ta tuna sai ranta ya baci(Fans da alama dai batasan baƙar wahalar da Umman Sa'eeda da ƴarta suke sha a gun Umma kande da Maman Jummalo ba shiyasa ta ke wannan bacin ran🤔).
Gwaggo Ladi ce ta fito da tabarma don shimfiɗama Baba kasancewar yafi son cin abinci a waje, bayan ta shimfiɗa tabarmar sai ta kawo mai abinci sannan ta wuce ɗaki don batason haduwa da Umman Sa'eeda kuma tasan yana gama cin abinci sai kirata(Gwaggo Ladi duniya🙃, wannan tsana sai kace kishiyarta ai ko kishiyarta sai haka😂😂😂).
Kamar ta sani bayan ya kammala cin abin yako kira Umman Sa'eeda, tako fito ta samu wuri gefan tabarmar ta zauna.
Ƙara gaisawa sukayi sannan suka fara hirar yaushe gamo, tun tana ƙarama ta saba da Baba,saboda yana jawota a jiki sosai kamar ƴaƴansa,sun shaƙu da juna sosai. Sun daɗe sun hira abinsu har kusan awa sannan sukayi saida safe, shi ya wuce ɗakin Gwaggo Ladi ita kuma ta wuce masaukinsu.
@@@@@@@@@@@@
Shigarsa ɗaki ya samu wuri kusa da Gwaggo Ladi ya zauna don yanada buƙatar magana da ita saboda ya gaji da wannan ƙiyayyar da ta ke nunawa marainiyar ALLAH, ya isheshi haka, tun tana yarinya ta ke fuskantar ƙalubale har auranta.
Gwaggo Ladi da tun shigowarshi ɗakin tana kwance tana jinsa amma tayi burus sai tayi kamar tayi bacci, don yau ya bata haushi sosai akan marar asali yake daka mata tsawa wanda rabon da suyi hayaniya ko fada ta manta ranar.
Zama yayi tare da cewa " Ladi ina son magana dake yanxu"
tana jinsa amma taƙi amsawa, saida ya sake magana kana ta tashi daga kwancen ta zauna.
Shiru ɗakin yayi , sai can Baba ya katse shurun da faɗin"Yanxu Ladi abinda kikayi ya dace kenan, yarinya tazo ko zama bata yi ba, kike mata masifa tare da faɗa mata marar asali, wai shin kinada hankali kuwa,kina da tabbacin marar asalin ce da kike kiranta dashi tun kan tasan hankalinta har girmanta, wata hujja kike da ita Ladi "
Gwaggo Ladi dai ko Uhmmm bata ce ba, tana nan zaune, saida ya ɗan lunfasa sannan ya ɗora da cewa" Don ALLAH ki canja halinki, tsufa kike ƙarayi amma kullum kina abu kamar wata yarinya haba, a kullum inaji a jikina Husaina na da asali saidai ƙaddarar da ta afka ma mamanta na ciwo "
Yanxu ne Ladi ta buɗe baki tace" Ni tunda ka kawo su gidan nan na tsane su,bara kaji har na koma ma mahaliccina da tsanarsu zan koma musamman Husaina, don haka ba ruwana da har karta, tunda gidan kane, ta shekara a ciki wannan kai ta shafa bani ba,sannan idan wa'azin kake sonyi ka tafi masallaci kayi, baza kazo kana min wata nasiha ba, ehehhh!
haka Baba ya kyaleta ya kwanta tare da roƙon mata shiriya don da alama tayi nisa. (Ni kuma nace hassada ne da baƙin ciki ya mata katutu a zuciya 😂🙃😇).
@@@@@@@@@@@@@
A bangaren su Umman Sa'eeda kuwa, bayan ta shiga ɗaki ita duk a tunaninta Sa'eeda tayi bacci, ashe tana nan tana karatu,(Jikar Mongo Park ba ko kuma Al huda huda🙃🙃🙃) .
shiga ɗakin tayi tare da cewa"Ashe bakiyi bacci ba, duk azatona zanzo na nasamu kinyi bacci"
murmushi Sa'eeda tayi sannan tace "Ummina Ina zanyi bacci banji tarihin kakata ba, ai bacci bai ganni ba"
dariya Umman Sa'eeda tayi sannan tace " Toh karkaɗa kunnuwanki yanxu zakiji tarihin kakarki"
Gyara zama Sa'eeda tayi tana fuskantar Ummanta, sannan Ummanta tafara bata tarihin kakarta.
Labari
***Na taso a gidan nan tare da mahaifiyata cikin ƙasƙanci, a lokacin mamata tana da tsohon ciki ni kuma ban wuce skekara 6 ba,Baba na kula ta mamata tare da ni sosai kasancewar cikinta na a watan haihuwa,a lokacin mahaifiyar baba na araye,duk sanda Gwaggo Ladi kema mamata masifa mahaifiyar Baba wacca muke kira da Tasalla ta ke shigar mamata faɗan tayiwa Gwaggo Ladi tatas, don Tasalla na son mu kamar yanda Baba ke son mu.
Sanda mamata zata haihu alokacin babu asibiti, Tasalla ta amsa haihuwar, mamata ta haifo ƴan biyu duk maza kyawawa amma ɗaya yazo babu rai sai kuma ɗan uwansa yabi bayansa, bayan haihuwa da kwana huɗu, tun sanda mamata ta haihu ta kamu da ciwo kuma ankasa gane kan ciwon, wanda ko fita da ƙyar ta ke yi.
Kuma duk sanda aka tambayeta ina ne ahalinta suke to ranar babu wanda zai rintsa, ta dinga firgita haɗe da iface iface a gidan, dalilin haka yasa tunda su Baba suka tambayeta sau biyu hakan ta faru basu ƙara tuntuɓarta da batun inane ahalinta suke ba.
A duk sanda Gwaggo Ladi tai min gori ko ta kirani da marar asali sai mamata tace min "Husaina ke ƴar gata ce, kuma kinada asali, kin fito daga tsatso mai kyau, kuma ƴar dangi ce, bancin ƙaddar da ta afka mana tare da ɓatan ɗan uwanki Hassan wanda kullum zuciyata dashi ta ke kwana kuma dashi ta ke tashi, inaji a jikina yana araye bai mutu ba,nasan ko ba daɗe ko bajima zaki sadu da ahalinki, inaso kikasance mai haƙuri da juriya a duk inda kika tsinci kanki,ki kasance mai ibada a koda yaushe, don inajin lokacina ya kusa Husaina "
Haka mamata ta ke faɗamin a duk sanda Gwaggo Ladi ko ƴaƴanta suka kirani da marar asali,na ɗau nasihar mamata na adanata acikin ƙwaƙwalwata, duk da a lokacin banfi shekara 12 a duniya ba, mahaifiyar Baba ta rasu, Ina gab da shiga shekara da 13 mamata tabar duniya, nayi kuka iya kuka wanda babu mai lallashina daga Baba sai Mairi wacca ɗiyarta ta kawo mana abinci ɗazu, duk da sa'a ta ce amma tanada hankali, ita kadai da Baba nake samun natsuwa wurinku.
Bayan rasuwar mamata rayuwa ta ƙara min zafi don lokacin na fara fuskantar asalin gallazawa wurin Gwaggo Ladi, ga aikin gida duk da ƙarancin shekaruna haka nake komai agidan sai afakai ce Mairi ta ke tayani aiki, kasancewar Baba ba zama yake a gida ba shiyasa baisan meke faruwa dani ba,sai dare yake dawowa, a daran ne nake samu naci abinci sosai.
Haka rayuwa da cigaba da tafiya ina a wannan yanayin har na zama budurwa, kyakkyawa dani, don samarin garin nan sunyi harsashe babu wacca ta kaini kyau, hakan ba ƙaramin batama Gwaggo Ladi rai yake ba saboda lokacin itama ƴan matanta sun girma, don akwai mata biyu wa'inda suka girmeni sannan Mairi wacca muke sa'a da juna, haka samari sukaita zuwa wurin Baba neman aurena alokacin inada shekara 16,gasu masu kuɗi harda yaron mai gari,saboda wannan farin jini da ALLAH ya bani na ƙara samun ƙuntata gun Gwaggo Ladi.
Alokaci guda aka saka mana rana da sauran ƴan matan Gwaggo Ladi har da Mairi,duk samarinsu a ƙauye suke har da na Mairi, Ni kuma mahaifinki a lokacin ba laifi yanada kuɗi kuma a birni yake da gida, haka aka daura mana aure wanda ko tsinke ban samu daga Gwaggo Ladi ba saidai Baba,shi yayi ruwa yayi tsaki, bayan ɗaurin aure aka wuce dani birni gidan mahaifinki duk da bamu samu tarbar arziƙi wurin Umma kande ba, haka suka tafi suka barni, inata kukan rabuwa dasu, a da maihaifinki na matuƙar sona wanda baya iya ɓoyewa a gun kowa, sai daga baya lokacin na haifeki kinyi yawo, na fara ganin sauyi wurinsa har yakai ya fara nuna min kyara da tsangwa, wanda ni kuma na rasa abinda nayi masa, a haka dai har aka kawo yanxu, wanda a kullum nake Addu'ar ALLAH ya karkato da hankalinsa guna dake.
Toh kinji tarihin kakarki mai suna Maimuna, kuma har yanxu ban cira rai da saduwa da ahalina ba kamar yanda mamata ta ke faɗamin duk sanda aka min gorin marar asali***
@@@@@@@@@@@@@@@
Cikin labari
Sa'eeda dai tun sanda Ummanta ta fara bata labari da natsu har zuwa ƙarshe sannan ta saki nauyayyan ajiyar zuciya har seda Ummanta taji kana ta fara magana " Ummina yanzu baki san asalinki ba koda gari ne"
Umman Sa'eeda murmushi tayi sannan tace " Tabbas bansan asalina ba, kuma mamana bata taɓa sanar min daga wani gari muke ba, saidai a kullum tana maimaita inada asali, ni ƴar gatace kuma ƴar dangi ce haka ta ke fadamin, kuma inaji a jikina zan sadu da asalina"
Sa'eeda ce tace " Ummina shi Uncle Hassan har yanxu bakisan inda yake ba",(Uhmmm su Sa'eeda masu Uncle tun Kan aganshi har an bashi wannan respect d'in😂😂😂).
Dariya Umman Sa'eeda tayi kana tace " Niko ina zan sanshi tunda tun muna Yara ya ɓata, kinga bazan sanshi ba, saidai mamata na yawan cemin muna kama dashi sosai sede nafishi hasken fata"
Shiru ɗakin yayi kuwa na nashi tunanin,Umman Sa'eeda ce ta katse shirun da cewa" Dare yayi zoki kwanta, yanzu dai sai a sakarmin mara na huta tunda kinji tarihin kakarki ko"
Dariya Sa'eeda tayi tare da cewa " Eh Ummina yanxu na gamsu sosai da bayananki, kuma zan cigaba da yi mana addu'ar ALLAH ya sadamu da ahalinmu"
murmushi Umman Sa'eeda tayi sannan tace"yawwa sayyin idaniya na, ALLAH ya amsa mana"
da "Allahumma Ameen" Sa'eeda ta bita dashi kana kowa ya kwanta.
@@@@@@@@@@@@@@
Yau ta ke babbar sallah,da sassafe su Sa'eeda suka tashi tare da gyaran gida sukayi wanka sannan suka shirya zuwa masallaci kasancewar Umman Sa'eeda tasan masallacin.
Bayan sallah suka dawo gida wanda a lokacin ne aka yankawa Baba ƙaton ragonsa, a nan Umman Sa'eeda da Sa'eeda sukayi ma Baba Barkha da sallah, sannan suke nufi cikin gidan, direct Umman Sa'eeda ta musu jagora zuwa ɗakin Gwaggo Ladi, a nan ta tarar da ƴaƴanta tare da jikokinta suna hira haɗe da raha abinsu, suna ganinta suka tamke fuska banda Mairi wacca tun shigowarta gidan ta ke alla alla su dawo taga ƴar uwata ta.
Russunawa sukayi ita da Sa'eeda suka mata Barkha da sallah, a daƙile da amsa sannan suka gaida ƴan ɗakin, suma dai a daƙilan suka amsa musu sannan suka wuce ma saukinsu.
Mairi ce ta bisu da fara'arta ko takan ƴan ɗakin bata bi ba ta wuce wurinsu. Koda zuwansu ɗaki sukaga an ajiye musu abinci wanda babu shakka Mairi ce ta kawo musu, zamansu keda wuya sukaji sallamar Mairi, da fara'a Umman Sa'eeda ta amsa mata sannan suke rungume juna haɗe da murnar ganin juna bayan rabuwa.
Haka dai sukayi hirarsu cike da annashuwa, sallah kadai ta ke tayar dasu kasancewar agidan Mairi zata kwana haka al'adar garin take.
Haka dai su Sa'eeda sukayi shagulgulan sallah sannan suka dawo gida tare da ɗumbin alkhairai daga wurin Baba da Mairi.
Bayan dawowarsu da wasu kwanaki su Sa'eeda suka koma makaranta. Wannan kenan
@@@@@@@@@@@@@@
ABUJA
Kasancewar duk babban sallah wannan family suke taruwa wurin shagalin bikin sallah yasa wannan Karon ma haka ta kasance.
Maa shaa Allah kawai zan iya furtawa ganin wannan family duk sunzo tun daga wa'inda suke Nigeria har ƴan UK ba sunzo banda Fadila saboda ƙaranci hutu da suka samu yasa Dad ɗinta yace baza tazo ba tunda ai tazo tayi 1 week a Nigeria, haka tayi ta kumbure kumbure daga ƙarshe haka ta haƙura da zuwan saboda school.
Garden ne nagani an ƙawatashi da wasu balloons kala kala anyi decorating garden yayi kyau sosai gashi an shimfiɗa wata babbar tabarma ammafa mai shegen taushi kamar carpet ƴan aikin sunata kai kawo wurin ganin an cika wurin da abubuwan ci da na sha tun daga soyayyun kaji, abinci kala kala tun daga na Nigeria har na ƙasar larabawa haka aka jerasu ga gasashshan naman rago an banƙareshi a tsakiya, haɗe da wuk'an yanka mai kyau.
Gaskiya wurin nan ya ƙayatu matuƙa ainun, bayan gama gyaran wurin da ma'aikata sukayi sannan wannan familin suka zagaye wurin suna murna da ganin juna, haka suka ci suka sha suna dariya da shewa.
A nan ne na hango Hajiya zaune a tsakiyar jikokinta tayi shiru, yaran suna mata wasa amman sama sama ta ke amsa musu,babbar ɗiyarta ne ta kula da yanayin mahaifiyartasu kasancewar tana kusa da ita.
@@@@@@@@@@@@
Bayan an kammala ci da sha suka koma cikin gida,direct Hajiya ta nufi ɗakinta don batason hayaniya yau hasalima tun sanda shaiɗanin bokan nan ya mata maganar basu mutu ba hankalinta ya gaza kwanciya, bacci ma saidai ya saceta saboda tunani da zullumin daya addabi ruhunta, haka akayi sallama a ƙofar ɗakinta bata amsa ba saidai ta bada umarnin a shigo.
Babbar ɗiyarta ce Amina tashigo ta zauna kusa da ita tare da cewa "Hajiyata meya sameki ne ko bakida lafiya ne"
murmushi tayi a ranta tana cewa 'dama rashin lafiya ne ai mai sauƙine akan tashin hankalin da nake ciki'
sai kuma afili tace " kwana biyu nan ina fama da ɗan zazzaɓi da kuma rashin bacci"
habawa ai tuni Amina ta rikice da sauri ta ɗauki wayarta jikinta na rawa ta ke danna ma number family doctor sun don arayuwarta batason damuwa ko kuma rashin lafiya atattare da Hajiyarta, kiransa tayi tare da cewa yazo yanzu yanzun nan banda ɓata lokaci.
Abinka da Naira duk da lokacin sallah ne amma haka Doctor ya taho gidan saboda yana girmama ƴan gidan sosai. (Ni kuma nace yana girmama Hajiya Naira ba😂🙃😇).
@@@@@@@@@@@@@@
Haka Doctor yazo ya dubata amma ya ce shi gaskiya baiga abinda yake damunta ba, hasalima tana cikin ƙoshin lafiya,duka familin suna ɗakin don Amina ta sanar da rashin lafiyar Hajiya ga kowa, suma da tashin hankali suka isa ɗakin nata.
Bayan Doctor ya gama bayaninsa ya tafi,ɗakin ya koma shiru can Amina ya katse shirun da cewa " Kodai ashirya miki Visa ne yau, gobe mu wuce India a dubaki acan"
Hajiya ce tayi murmushi tare da cewa "karku damu zan samu sauki don hakan na faruwa dani tun kuna yara, karkusa damuwa aranku"
Haka dai sukayi jimaminsu sannan kowa yayi shirin komawa inda ya fito. A haka aka bar Hajiya cikin tunanin da yanxu ya zamo mata jiki.
@@@@@@@@@@@@@@
KEBBI
Familin Alhaji Kabir Dikko family babbane kuma sanan ne acikin birnin Kebbi, wanda ko mai machine ka sanar ma gidan Alhaji Kabir Dikko zai Kaika, yasan gidan kasancewar babban gidane wanda ya shafe layi guda cur da zuri'ar Alhaji Kabir Dikko da na ƴan uwansa, gidan yakama tun daga ƴaƴan Alhaji Kabir Dikko da ƙannansa, wanda duk sun rasu saura ƴaƴa da jikoki suka rage kuma har yanxu suna zumuncinsu ba tare da nuna banbanci ba.
Cikakkun ƴan boko ne kuma ƴan kasuwa sanannu a harkar kasuwancin cikin Nigeria da wajanta.Mom da kuka sani Maman Sadam(Auta) ta kasance jika ga Mariya ita ce babbar ƴa ga Alhaji Kabir Dikko.
Duk babban sallah suke haɗuwa a family house ɗinsu ayi shagalin sallah tare da family meeting wanda ya ƙunshi magance matsaloli da kuma tallafama juna wurin ganin family ya samu daidaituwa.
Alhaji Abubakar ɗa ne na biyu ga Alhaji Kabir Dikko kuma wanda ya rage a duk gidan tun daga kan ƙannan Alhaji Kabari Dikko har sauran ƴan uwansa wanda keda kimanin shekara 80 a duniya yanada yara hud'u a duniya. Kowa a familin yana matuƙar girmama Baba Garba wanda haka suke kiransa dashi tun daga kan yara har jikoki da ƴaƴan jikoki haka suke kiransa dashi.
Wannan Karon ma haka suka gudanar da shagulgulan sallah tare da family meeting ɗin da suka saba na kowani babban sallah, daga haka taro ya watse kowa ya nufi idan ya fito.
@@@@@@@@@@@@@@
UK
Bangaren Sadam autan Mum karatu ya soma zafi gashi Dad ɗinsa ya hanashi zuwa Nigeria sai ya kammala degree ɗinsa complete sannan ya dawo bautar ƙasa na shekara ɗaya, kana ya ƙara tafiya China don yin Masters ɗinsa don ƙara sanin harkar.....................
Daga Alk'alamin
🖍️📚Narnarhh Bukar 📚🖍️
Comments and share 🙏🙏🙏Fisabilillah.
[4/25, 1:38 PM] +234 814 129 2044:
🏵️ NACINA YAJAWOMIN🏵️
Narrnarhh Bukar✍️
🌹Perfect Essential Writer's
Association🌹
✨ P. E. W. A✨
Wattpad:@AISHAABUBAKAR812
Arewabook:@Narrnarhh002
11----12
UK
Ɓangaren Sadam autan Mom karatu ya soma zafi gashi Dad ya hanashi zuwa Nigeria sai ya kammala degree ɗinsa complete sannan ya dawo bautar ƙasa na shekara ɗaya.
Kana ya ƙara tafiya China don yin Masters ɗinsa don ƙara sanin harkar kasuwanci,sosai hakan bai masa daɗi ba,yaso tafiya hutunsa na farko wurin sister ɗinsa Aunty Sadiya wacca a da take Pakistan kafin yanzu su dawo India da zama saboda yanayin aikin mijinta,haka dai ya haƙura da zuwa ko'ina ya ƙara maida hankalinsa kacokan a karatunsa.
Sadam miskili ne na ajin ƙarshe don yanzo miskilancin nasama ƙaruwa yayi saboda ganinsa a wata ƙasar,ƴan mata tun daga kan turawa da na baƙaƙen fata suna son ya kulasu saboda classy guy ne haɗadɗe ga girman jiki wanda idan ka gansa zakayi tunanin ɗan shekara 30 saboda ya aje ƙasumba sosai.
Yanada aboki guda ɗaya ɗan Nigeria amma shi ɗan kaduna ne mai suna Sadiq,kusan halinsu ɗaya shiyasa abotar tasu tazo ɗaya,duk da course ɗinsu ba ɗaya bane,shi Sadiq yana karantar ɓangaren Computer Engineering ne,hakan baisa abotar tasu ta lalace ba, kowan nansu yana ziyartar ɗan uwansa duk da faculty nasu ba ɗaya bane amma haka suke abotar tasu,har takai yanzu iyanyansu sun san da abotar tasu.
Haka Sadam ya cigaba da karatunsa a UK don cika burin mahaifinsa akansa kasancewarsa ɗa ɗaya wurin mahaifinsa ,gashi mahaifinsa ya soma tsufa duk yayyinsa mata ne saboda haka dole ya jajirce sosai akan karatunsa dan nan gaba harkar kasuwancin mahaifinsu da kamfanoninsa duk zasu dawo hannunsa ,shiyasa yake jajircewa sosai.Wannan kenan
@@@@@@@@@@@@@
KADUNA
Bayan sallah hutun su Sa'eeda ya ƙare,sai suka koma makaranta don cigaba da karatu.Sosai Sa'eeda take mai da hankalinta akan karatunta a bangare ɗaya kuma tana koyawa Maryam inda bata gane ba kasancewarta very slow learner ce duk da tana da lesson teacher a gida amma haƙarta bata cimma ruwa ba,gashi koda yaushe Mum ɗinta cikin zigata take akan Sa'eeda hakan yasa take ƙara shige ma Sa'eedan jiki sosai,ita ko Sa'eeda da zuciya ɗaya take tare da Maryam.
Haka suka kammala SS2 cikin nasara da aminci wanda a lokacin Sa'eeda ta samu matsala da ƴan ajinsu saboda shugabancin ɗalibai da aka bata wato Head girl,haƙiƙa ta fuskanci tsana da barazana akan sai ta sauka daga Head girl ɗin don a ganin ƴan aji ƴar talaka bata cancanta da wannan muƙami ba sai dai ƴaƴan masu kuɗi irinsu,da ƙyar abubuwa suka lafa daga baya ƴan aji suka yarda duk da wasu basa sonta da Head girl ɗin.
@@@@@@@@@@@@@
Sun shiga SS3 wanda kowanni ɗalibi na shirya shiryen zana jabawan waec,neco da jamb ,hakan ta faru ga Sa'eeda don Ummanta ta shiga adashe har kala biyu duk don karatun ɗiyarta bancin savings ɗin kuɗi da take yi a account tun daga #100,000 wanda Sa'eeda ta samu lokacin saukarta har da adashen da take kwasa tana saving ɗinsu duk don karatun ƴarta ta,koda yaushe tana samun wankin kayan mutane duk da ma Sa'eeda na tayata sosai da yake Sa'eeda ba raguwa bace akwai son aiki,wani lokacin ma cema maman take ta bari ita zatayi duk don su rufama kansu asiri tunda Abbanta an mallakeshi,sai yadda akayi dashi a gidan.
Wasa wasa su Sa'eeda sun fara shirin zana exams ɗinsu na ƙarshe,sun fara rubuta Jamb wanda within 1week sakamakon su ya fito.
Alhamdulillah yawancin ɗaliban makarantar sun samu nasarar wuce cut of mark na jamb har da su Maryam don ta dage akan sai ta wuce Sa'eeda a score. (Haba Hajiya Maryam na gaba yayi gaba,sai dai a nema wani sarkin dan ko Sa'eeda tayi zarrah😂😂😂).
Sa'eeda tafi kowa marking a school ɗin har ma tawuce 270 a Jamb ɗinta, da wannan score ɗin ba ƙaramin ƙarama kanta baƙin painti yayi ba a idon ƴan ajinsu,hakan bai dameta ba don basa gabanta.
Bayan sun kammala jamb sai suka zana waec da neco sai bayan wasu watanni waec da neco ɗinsu suka fito shima sakamakonsu yayi kyau sosai ,haka Sa'eeda da Maryam sukayi applying post utme a Kasu kasancewar shi suka sa a Jamb ɗinsu sai lokacin screening yayi suka tafi wanda cikin hukuncin Ubangiji duk suka tsallake har aka basu admission a Business Administration 100L.wannan kenan
@@@@@@@@@@@@@@@
Bangaren su Umma Kande liyafa ta cigaba don yanzu haka an canja tsarin gidan nasu,anyi painting gidan baki ɗaya sannan aka siminta gidan ya fito kamar sabo,duk wannan aikin ba na kowa bane sai na Nusaiba wacca yanzu ta zama karuwar kanta ,bata cika zama a garin ba yanzu,bata waccan state ɗin bata waccan.
Duk wannan abun da take yi bai damu Umma Kande ba,duk da ansha kawo mata gulmar layi akan maza take bi kuma tana luwaɗi amma sai ta ce ana ma ƴarta sharri da baƙin ciki don anga tanada farin jinin samari.Ƴan layi sunyi gulmar har sun saka ido don har mazan layi sukan tun kari Abbansu Sa'eeda da magana akan abinda yaransa sukeyi amma sai yace baisan yanda zaiyi da uwarsu ba koya mata magana ba amsa shi zatayi ba,gashi baida ikon yima yaran faɗa zata hayayyaƙo mai da masifa akan ya tsana yaranta,ko kuma tace yana bin zugar mazan layi,babu yanda ya iya sai dai ya zuba ido.
@@@@@@@@@@@@@
Umma Kande ce da Maman Jummalo zaune a ɗakin Umma Kande sun baje pepper soup din kaza suna ci haɗe da gwangwanin maltinarsu mai sanyi suna ci suna ƴar hirarsu cike da annashuwa.
Maman Jummalo ce ta sauya hirar tasu zuwa magana mai muhimmanci game da yaransu don ita gaskiya tafi son suyi aure akan wannan tara samarin da sukeyi gashi idan suka fita waje aita zunɗansu akan sun bar yaransu babu aure sai tara samari a layi.
Gyara zama tayi sannan tace "Ni kuwa ƙawas nazo da wata shawara akan yaran nan "
Umma Kande dake gwaguyar ƙashin cinyar kaza ta ajiye sannan ta baida hankalinta sosai ga Maman Jummalo sai ta ce "Ina jikin ƙawas hala wani alkwairi ne ya ƙara samuwa"
Maman Jummalo tace "Kinga yaran nan duk Allah ya basu samari masu kuɗi sosai gashi shekarunsu ƙara yawa yake ba raguwa ba,shi ne wani tunani ya zomin akan mai zai hana muce musu su fidda samarin da suke so ayi musu aure don gaskiya hankanlin mu zaifi kwanciya kuma zamu hutu da gulmar ƴan layi,ko ya kikace ƙawas?
Ɗan shiru Umma Kande tayi tana nazari don maganar ƙawarta na kan hanya gwara suyi aure suma su hutu da zunɗen ƴan layi da ba dama su fita sai an nunasu da yaransu,ɗan lunfasawa tayi sannan tace " Maganarki dutse ƙawas, to yanzu ya kike ganin zamu ce da su,don kinga na farin jinin samari masu kuɗi kawai muka amso musu banda na aure,kinga koda mun musu maganar aure samarin ba fitowa za suyi ba"
"Hakane ƙawas, to yanzu menene mafita" cewa Maman Jummalo
"Mafitar ɗaya ce,sai dai mu sake komawa gun boka Sankeru akan maganar auran nasu,ko ya kikace"
"Tafiyarmu wurin boka Sankeru wajibi ne gaskiya,gwara suyi auran mu huta"
Umma Kande dake matsar da tiran pepper soup ɗin ta ɗora da cewa "Yaushe kike ganin zamu je wurin boka Sankeru ɗin"
"Mu shirya ranar alhamis tunda baya son ana zuwa ranar jumma'a da litinin sai dai lahadi da alhamis" cewar Maman Jummalo
"Na tuna kuwa,Allah ya kaimu"
Da "Ameen " Maman Jummalo ta bita dashi.
Can kuma suna zaune sai Umma Kande tace"Ƙawas ba kiga waccan mayyar yarinyar mai kama da aljanu sai ƙara kyau take yi ba,kamar basa cikin wahala"
"Abinda ke raina kenan kika rigani fada wallahi,nima hakan na damuna,tsorona kar tazo tafi yaranmu samari masu kuɗi tunda kinga duk tafisu kyau sai kace ƴar india,ke nifa tunani nake anya ƴan ƙasar nan ne kuwa" cewa Maman Jummalo
Umma Kande ta ɗan sauke gauran ajiyar zuciya tace "Bari ke dai,ina ganin tafiyar mu wurin boka Sankeru zai zama biyu har da maganar Sa'eeda don gaskiya baza mu bari tafi ƴaƴanmu ba wallah"
"Sosai ma kuwa dole musan abunyi tun kafin wankin hula ya kaimu dare,don naga alama tanada farin jinin samari sai dai kamar bata kulasu" cewa Maman Jummalo
"Wannan haka yake kar kuma ta samo wanda yafi na yaranmu kinga gwara muyiwa tufkar hanci "
"Haka ne kuwa,Allah dai ya kaimu alhamis musan abunyi kuwa" cewar Maman Jummalo
Hamma Umma Kande tayi tare da cewa "Ameem dai ƙawas,kinga mun jefi tsuntu biyu da dutse ɗaya"
"Hakane kam".
@@@@@@@@@@@@@
Kamar yanda suka shirya ,yau take alhamis tun daran alhamis suka kammala shiri tsaf don da sassafe zasu tafi.Da sassafe suka nufi tasha acan suka hau motar da zata kaisu ƙauyen,bayan sun sauka ne suka hau machine ɗaya kasancewar ƙauyen ba'a cika samun abin hawa ba,kamar yanda suka je waccan zuwan a gefan dajin mai machine ya sauke su suka ƙarasa da tafiya har zuwa bukkar boka Sankeru.
Bayan sunzo kusa da bukkar sai suka cire takalmansu kamar wancan zuwan,sai suka juya suna tafiya ba baya da baya har cikin bukkar. (Ni kuma na saka nose mask ɗina saboda tsaro,kar a samu matsala wurin ɗaukar rahoto😷😷😷).
Isarsu cikin bukkar keda wuya suka zube a ƙasa tare da yima boka Sankeru kiraki duk da ba kowa a cikin bukkar suna cewa"Sakeru namu Sankeru na duk mai son ya dace,Shugaban matsubban duniya, Ka cire tuta,Kowa na bayanka, gamu yau munzo da ƙoƙon bararmu gareka mai sha re kukanmu"
Tunda suka fara kirari bishiyoyin nan dake zakaye da bukkar suka fara jijjiga ga warin nan ya soma tashi ,kamar walkiya sai ga boka Sankeru a gabansu zindir haihuwar uwarsa,yana bayyana agabansu sai ya bushe da dariya timbinsa na jijjiga kamar wani alade,sai da yayi mai isarsa kana ya tsagaita.
Dubansu yayi da kyau sannan ya fara maganar cike da amon murya "Nasan zaku dawo,dole sai kun dawo don kammaluwan aikinku hehehe! " kamar an tsikareshi zumbur ya miƙe ya soma tiƙar rawa kamar wani alade.
Su dai su Umma Kande kansu a ƙasa,sai da yayi mai isarsa sannan ya ɗora da cewa"Zancen ku na biyu gane da yarinyar kishiyarki" yana nuna Umma Kande yace"Hmmmmmmmmm bayanku akwai wasu da suke da halin irin naku akan yarinyar da mamanta"
Da sauri Umma Kande ta ɗago idanunta.....................
Tofa ƙaƙa ƙara ƙaƙa,kenan su Sa'eeda da Ummanta sunada wasu maƙiyan a ɓoye bayansu Umma Kande 🤔🤔🤔 ko suwaye......???
Muje dai zuwa✍️✍️✍️
Daga alk'alamin
🖍️📚Narnarhh Bukar 📚🖍️
Comments and share 🙏🙏🙏Fisabilillah.
🏵️ NACINA YAJAWOMIN🏵️
Narrnarhh Bukar✍️
🌹Perfect Essential Writer's
Association🌹
✨ P. E. W. A✨
Wattpad:@AISHAABUBAKAR812
Arewabook:@Narrnarhh002
13----14
Da sauri Umma Kande ta ɗago da idanunta mamaki duk ya cika ta a zuciyarta tana cewa 'wato bancin ni akwai wasu ma kenan,babbar magana'
Katse mata tunani yayi da cewa"Su nasu ba irin naki bane hasalima tun daga tsatso ne ake bibiyarsu,sannan ita yarinyar nan da kuke gani hmmmmmmmmm"
Shiru yayi na ɗan wasu mintuna sannan ya cigaba da cewa"Akwai ƙalubale a rayuwarta ita da mamanta,sannan maganar samari wannan kusha kurumunku indai wannan ne kuke tunani akai bazata taɓa samun samari kamar na yaranku ba"
Can kuma ya miƙe tsaye tare da jijjaga yana wani sumbatu ,sai kuma ya ɗaga ƙafarsa ɗaya sama tare da sakin wata tusa mai ɗoyin gaske,tuni su Umma Kande suka toshe hancinsu.(Ni kuma da sauri da ƙara ɗora nose mask har uku akan nawa😷😷😷🙃)
Dariya ya sheƙe dashi tare da cewa "Akwai ƙamshi ko? "
da "Eh'' suka amsa masa, sai kuma ya juya musu baya tare da sakin wasu zafafan tusa ajere ,ji kake"ɓur ɓuɓurr ɓuɓuɓuurrr ɓuɓuɓuɓurrrrrrr"
Haba saiga Maman Jummalo da amai daman ita akwai ta da saurin gurɓacewan ciki,ita kuma Umma Kande ƙara toshe hancinta tayi sosai.(Ni kuma ba arziƙi na fita da gudu ina haki don kar na sume ku gaza samun rahoto sai can kuma na dawo cikin bukkar😷😷😷)
Juyowa yayi tare da tintsirewa da dariya sai wani tattakawa yakeyi tare da juyi,sai kuma ya tsagaita tare da cewa"kuna son yaranku su auri mazaje ko wanni iri kuma masu kuɗi"
Atare suka ce"Eh boka Sankeru mai sha re kukanmu"
Zama yayi ya ɗaga hannunshi na hagu sama sannan yayi wasu surkullensa sai ga wata ƙwarya ƙarama baƙa ta bayyana a saman hannunsa,sai ya ajiyeta gabansa sannan ya saka hannunsa ciki tare da ciro wani ƙullin magani ya jefa musu haɗe da cewa"Ku nemi kare baƙi da fari ku yanka su sannan ku tara kofin da wannan garin maganin yake a ciki ,jinin karnukan ya zuba ciki sannan ku samu ruwa tafashashshe ku zuba maganin wanda ke haɗe da jinin ku ƙara tafasasu sannan ku bar ruwan yayi ɗumi sai kusa yaran su wanke fuskarsu sau uku uku,na tabbata auransu yazo,yazo yaaaazooooo ho ho ho!!!
Godiya suka shiga yi masa,Umma Kande ce ta ciro kuɗi a tunaninta yau babu abinda zai shiga tsakaninsu dashi amma daka mata tsawa yayi tare da cewa" Jikinku muke so don haka dole ku bamu,wannan dole ne,he he he!!!
Ai ba shiri suka zare idanu don sunsan babu daɗi haɗuwarsu dashi amma ya zasuyi tunda son abin duniya da dogon buri ya rufe musu ido.
Kamar wancan lokacin haka wannan karon ma ya kasance dasu kuma ya ɗau tsawan lokaci da ko waccansu yana masha'arsa da ita kana suka taho wanda lokacin kusan yamma ne,a haka suka biyo cikin dajin sai wari da hamami jikinsu ke tayi,sun iso bakin dajin da kyar sannan Maman Jummalo da fito da turare suka fesa sai suka tari mai machine wanda a nan ma sai da suka daɗe sannan suka samu mai machine ya ɗaukesu zuwa cikin ƙauyen daga nan suka nufo tasha sai gida wanda basu suka iso gida ba sai wurin 5:00pm na yamma,a gaggauce sukayi wanka sannan suka baje don huta gajiya.
***Tunatarwa***
****Shin bakwa tunani akwai mata masu irin wannan ɗabi'ar irin nasu Umma Kande da Maman Jummalo na son abin duniya da dogon buri a duniyar nan ???
Tabbas!!! Har yanzu akwai mata masu wannan ɗabi'ar zuwa wurin boka da neman biyan buƙata wanda a ƙarshe halaka suke faɗawa sannan imaninsu ya ragu!!!
Yake ƴar uwata mai daraja kisani zuwa wurin boka ko malamin duba ba mafita bace agareki hasalima ƙara nisanta kanki kike daga rahmar Ubangiji,amfaninsa na ɗan wani lokaci ne zai miki wanda a ƙarshe illarsa tafi dutsen Uhudu a girma.
Shin mai zai hana cikin salisalin dare a lokacin da wasu suke bacci ke kuma ki tashi ki ɗauro alwala kiyi sallar nafila koda raka'a 12 ne sannan kiyi wutri ki sallame,kina mai kirari ga Ubangijin Talikai akan ya biya miki buƙatunki na fili da na ɓoye kina mai ƙan-ƙan da kanki a garesa.Tabbas zakiga canji a rayuwarki imma kishiya ce ta tasoki a gaba kina sallar dare tare da azkar ɗin safe da na yamma wallahi kinfi ƙarfinta da tsafinta da ikon mai sama.amma karki ɓata lokacin a banza tare da aljihunki wurin zuwa gun boka,wai shin ba kuga Umma Kande da Maman Jummalo yadda suke wahala bane gun boka sannan koda ya biya musu buƙata a ƙarshe wahala ce zata koma.
Misalin nemama yaransu mazaje da sukayi wurin boka Sankeru bayan yace musu suna son kowani irin mazaje ga yaransu masu kuɗi suka aminta sun manta da kalmar kowani iri yana nuni da koda mara kyau ne ko kuma masu cutarwa amma suka yarda,zakuga yadda zasu ƙare a ƙarshe.Allah yasa mufi ƙarfin zuciyoyinmu ya kuma tsafe mana imaninmu.******
@@@@@@@@@@@@@
Cikin Labari
Maman Jummalo ce bayan sun ɗan huta sunci abinci ta ce ma Umma Kande wacca tayi ɗaiɗai da ƙafafunta a tabarma "ƙawas ina kike ganin zamu samu jinin karnuka har kala biyu ,sannan muyi yanda boka Sankeru yace damu?
"A tunani na mai zai hana mu samu gwarawa tunda kinsan suna cin karnuka da aladu"
" Haba! "
"Allah kuwa,ke bara ma kiji har tsire da balangun karnuka sukeyi"
"To ke ina kika san suna tsire da balangun karnuka" cewar Maman Jummalo tana riƙe baki tsabar mamaki
"Nima Musa ne wani zuwa da yayi yake bani labari,inyamurai da gwarawa suna cin karnuka sosai,ya ƙara da cewa acan Calabar suna da kwa'ta nasu na kunsu,inda ake siye da siyarwan naman aladu da na karnuka,shiyasa ma bayacin namansu don baisan ko naman alade ko na kare ne suka sa a abincin ba"
"Allah ɗaya gari bambam,to shikenan faɗuwa tazo dai dai da zama,kinga sai mu nema inda gwarawa suke a nan ko"
"Hakane kuwa,Allah ya kaimu gobe sai mu nema kwa'tan nasu,shikenan ma cika aikin boka Sankeru da wuri"
"Sosai ma kuwa,wallahi na ƙagara yaran nan suyi aure mu huta"
"Nima kuwa ƙawas"
Da wannan hirar su Umma Kande sukaci lokaci suna yi sannan Umma Kande ta nufo ɗakinta dan kwanciya kasancewar a ɗakin Maman Jummalo suke hirar.Ƴan matan nasu suna waje suna hira da samari sannan daga baya kowacce ta shigo gida wanda lokacin kusan ƙarfe 10:00pm da wasu ƴan mintuna,amma ko ajikin iyayen nasu.
@@@@@@@@@@@@@
Kamar yanda suka shawarta akan neman inda kwatan gwarawa yake aiko sunyi sa'a don sun samu kwa'tan gwarawa a cikin Farin gida wanda yake hanyar Mando.Sun samu ana gab da fara yankan karnuka da aladu dayake da sassafe suka fita,nan suka fara ai watar da aikin boka Sankeru sannan suka nufo gida dan kammala aikin.
Haka suka yi exactly yanda boka Sankeru ya ce dasu don kar asamu kuskure.Yaransu suka taru wuri ɗaya kamar yanda boka Sankeru ya ce dasu.
Da Iklima aka fara,matsowa kusa da bottle ɗin ruwan tayi sannan sai Umma Kande tace ta wanke fuskarta sau uku,haka tayi yanda tace ba tare da musu ba,sai Jummalo itama tayi yanda Iklima tayi, sannan Zaliha.
Duk wannan abun da suke Nusaiba na gefe ta chatting abinta.Maman Jummalo tace da Nusaiba tazo itama tayi,dan taga alama batada niyyar yi kamar yanda ƴan uwanta sukayi.
Buɗar bakin Nusaiba tace"Nifa gaskiya bazanyi wannan abun ba,kawai kuyi haƙuri dan komai zakumin bazanyi ba"
"Laaaaa!ehhh lallai Nusaiba wuyanki ya isa yanka" cewar Umma Kande
Kowa a ɗakin duban Nusaiba yake da mamaki itako ko ajikinta don ta rantse bazata wanke fuskarta ba kamar yanda taji jiya Mamanta suna hira da Maman Jummalo.
Waiwaye
Alokacin da su Umma Kande suke tsaka da hirar yanda zasu samo jinin karkuna susa a maganin da boka Sankeru ya basu,ita kuma Nusaiba ta dawo kenan zata shigo ɗakin Maman Jummalo dan nuna mata wani sabon film a waryata dayake Maman Jummalo akwai son kallon fina finai.
Isarta ƙofar ɗakin keda wuya ta jiyo hirarsu akan aurar dasu zasuyi aikuwa tsayawa tayi wurin ƙofar ɗakin taji komai sannan ta wuce ɗakinsu a zuciyarta tana faɗin 'Wallahi ba auran da zanyi,kurum ina cikin cin duniya ta da tsinke zaku wani tado da batun aure to wallahi bazata saɓu ba wai bindiga a ruwa,bazan taɓa yin yadda kuka ce ba,bayan auran babu komai cikinsa sai wahala da bauta,gashi sugar ɗina Alhaji Sagir yamin alƙawarin dani zaije Dubai muyi sati ɗaya kuma nasan zan ƙara wayewa ,da sake wallahi inaaaa tabb!!
Ɗaukar buta tayi ta nufa bayi dan karma mamanta tasan da dawowarta gidan.
Cikin Labari
Maman Jummalo ce ta katse shirun da mamakin da ya cika ƴan ɗakin dashi "Haba Nusaiba gata fa muke muku,kowace mace ba tada buri inta girma tayi aure ta hayayyafa,kinga ba daɗinmu bane ace muganku haka ga samari Allah ya baku amma ba kuyi aure ba,kuma ku kanku kunsan da zunɗen ƴan layi da muke sha mu da ku"
"Nasan da wannan Maman Jummalo amma gaskiya kumin uzuri bazan wanke fuskana ba da wannan ruwan, shi aure ai nufi na Allah ne ,kuma yanada lokaci,idan lokacin aure na Allah ya nufa nayi ai zanyi basai kun ɓata kuɗinku".(Hakane kam Malama Nusaiba ikon Allah😂😂🙃).
"Yanzu Nusaiba watsa mana ƙatsa a ido zakiyi kenan ,kinsan wahalar da mukasha duk don faranta muku rai amma da abinda zaki saka mana dashi kenan" cewa Umma Kande
"Nifa sai dai ayi haƙuri amma bazan wanke fuskana ba wallahi" cewar Nusaiba tare da mikewa ta fita daga ɗakin,kowa ya bita da kallo haɗe da mamaki musamman su Umma Kande da Maman Jummalo don su kaɗai suka san wahalar da suka sha kafin samin wannan maganin.
Babu yanda suka iya tunda tace bataso ,ai ba tilas farin cikinsu ma shi ne su sauran yaran sunyi musu biyayya kuma suna sa ran haƙarsu zata cimma ruwa koda Nusaiba kaɗai ce batayi aure ba sun rage jin surutun mutane akan yaransu.
@@@@@@@@@@@@@@
Bangarensu Sa'eeda ita da Ummanta sunata shirye shiryan fara karatun Sa'eeda a KASU.Babu laifi Sa'eeda ta ɗinka ƴan kalolin kayanta kala shida da hijabai uku da veils guda uku, sai takalma uku da jakar makaranta ƴar madaidaiciya sai kuma side bag ɗaya baƙa.Umman Sa'eeda ta siyoma Sa'eeda waya Vivo ƴar ƙarama second hand wacca batasha jiki ba saboda tasan zata buƙaci babbar waya tunda yanzu tana a university ne.
Haƙiƙa Sa'eeda tayi farin ciki sosai da wannan wayar duk da ƙarama ce amma ji take kamar iphone 14 pro max aka bata,tana tama Ummanta godiya yafi cikin kwando.
Kasancewar yau asabar,Umman Sa'eeda da ita suna ɗaki suna hira akan batun shirin fara karatun Sa'eeda ranar Monday
Umman Sa'eeda tace "Sa'eeda Monday zaku fara karatu,ina mai miki nasiha da kiji tsoran Allah a duk inda kike,ki guji ƙawayan banza wa'inda suke kai mutum ga halaka,ki maida hankalinki sosai akan karatunki,banda samarin banza duk da inada yaƙini akan tarbiyar da na ɗoraki akai,amma kiji tsoran Allah ba mutum ba,ki kasance mai haƙuri da juriya tare da yafiya wa wa'inda suka zalinceki,amma karki yarda a wulaƙantaki ko kuma a takaki ,ki kasance jaruma mai fuskantar duk wani ƙalubalan da zaizo miki a rayuwa hakan zaisa ki cimma babban rabo a rayuwarki,banda kwaɗayi da hangen nesa,kinga dai yanda Allah ya yayi damu don Allah ki gode masa banda kallon na sama dake a kullum ina baki shawaran ki dinga duban na ƙasa dake hakan zaisa miki natsuwa da kuma godewa Allah akan ni'imar da yayi miki bisa wasu"
Ta ɗau lokaci tana ma ƴarta nasiha game da rayuwa tare da hankaltar da ita abubuwa da yawa dangane da rayuwa,kasancewa University zata fara zuwa,akwai kala kalan mutane a can,wanda kamar bariki ne kazo nazo kowa yana yin yanda yaso ne babu takura ba kamar secondary ba shiyasa tayi mata nasiha duk da ta yarda ɗari bisa ɗari akan tarbiyar ƴarta.
Sa'eeda dai shiru tayi tanajin nasihar Ummanta wanda ke ratsa ƙashinta ya shiga cikin jijiyoyinta har ya kewaye ko'ina na jikinta,haƙiƙa jikinta yayi sanyi sosai kuma tasa aranta duk wuya duk rintsi bazata wofantar da nasihar Ummanta ba,kamar painti ne a dutse wanda baya taɓa goguwa ,haka kamar kwaɗone wanda aka kulleshi ta key sannan aka jefa key ɗin a tsakiyar taiku wanda babu ranar ɗaukowa to haka ta ɗau nasihar Ummanta.
Bayan ta kammala mata nasihar ne ta ƙara da cewa"Niko Sa'eeda na manta ban faɗa miki ba na samu aikin gwamnati za'a dinga biyana dubu #20,000 duk wata,kinga zan dinga saving ɗin #5000 a banki saboda registration ɗin karatunki na duk shekara,sai kuma #15,000 na dinga baki kuɗin mota sannan kuma sauran muci abinci dasu"
Murna Sa'eeda ta somayi don jin wannan abin alkhairi daya samesu,haƙiƙa Allah abin godiya ne,cikin murnar Sa'eeda tace "Ummina wani kalan aikin gwamnati kika samu kuma waya miki hanyar aikin?..................
**Maa shaa Allah Fans wani kalar aiki kuke tunanin Umman Sa'eeda tasamu???
**Shin kuna ganin Sa'eeda zata ɗauki nasihar mahaifiyarta idan ta fara karatu a University???
**Da gaske kamar yadda boka Sankeru yace auran yaransu Umma Kande da Maman Jummalo yazo shin yazo ɗin ko akwai matsala???
Duk ku tattaro ku hanzarto ku biyoni muje zuwa amsoshinku suna nan tafe✍️✍️✍️
Ina matuƙar alfahari daku my Esteem Fans🏵️🌹🌼,I love y'll💖💓💝💗
Daga alk'alamin
🖍️📚Narnarhh Bukar 📚🖍️
Comments and share 🙏🙏🙏Fisabilillah.
[4/25, 1:38 PM] +234 814 129 2044:
[4/25, 1:38 PM] +234 814 129 2044:
🏵️ NACINA YAJAWOMIN🏵️
Narrnarhh Bukar✍️
🌹Perfect Essential Writer's
Association🌹
✨ P. E. W. A✨
Wattpad:@AISHAABUBAKAR812
Arewabook:@Narrnarhh002
15—-16
Murna Sa'eeda ta somayi jin wannan abin alkhairi daya samesu,haƙiƙa Allah shi ne godiya ,cikin murnar Sa'eeda ta ce "Ummina wani kalan aikin gwamnati kika samu kuma waya miki hanyar aikin?"
"Aikin sharan titi ne gwaggo Lantana maƙociyarmu tamin hanya shima da ƙyar na samu kasancewar banyi makaranta ba,dayake ina da rabo ɗanta yayi min cuku cukun primary certificate sannan suka ɗaukeni,wani watan mai zuwa zan fara aiki in shaa Allah"
Shiru Sa'eeda tayi tana duban Ummanta 'Ya Salam yanzu Ummanta ce da sharan titi duk don ta rufama mana asiri kar mu tagayyara,Allah ka kawo mana agaji a lamuranmu baki ɗaya '
Duk wannan zancen a zuci takeyinsa , shiru tayi tana duban Ummanta sannan ta sauke sassanyar ajiyar zuciya sai kuma ta ce"Ummina yanzu sharan titi zaki fara yi kenan"
Tayi magana cikin sanyin muryar mai nuni da tsintsar damuwa.
Murmusawa Umman Sa'eeda tayi don tasan za'a rina shiyasa ma tun farko bata nemi shawararta ba don tasan hanata zatayi,amma wannan ce damarsu wacca zasu rufama kansu asiri tunda wankin da takeyi ba iya ɗaukar nauyin karatun ɗiyarta zaiyi ba hasalima iya abinci kawai yake isarsu shima ɗin ba mai daɗi ba.
"Nasan zaki ce haka,amma Sa'eeda bamu da wata hanyar bayan wannan kuma da kike cewa sharan titi ,ai zan dinga saka niƙaf saboda maganar mutane,kinga yanzu ba komai zan samu daga Abbanki ba,hasalima hankalinsa ba akan mu yake ba,to idan banyi wannan aikin ba ina zan samu kuɗin motan da zan dinga baki kullum sannan ina zan dinga zamun kuɗin biya miki registration duk shekara,ko da kuɗin wanki ne zai biya mana dukkanin buƙatun mu? "
"Hakane Ummina,Allah ya cigaba dayi mana jagora tare da rufa mana asiri duniya da lahira"
Da"Allahumma Aameen"Umman Sa'eeda ta bita dashi.
@@@@@@@@@@@@@@@
Yau take Monday,Sa'eeda tayi shirinta tsaf,tafito ɗas abinta,doguwar riga six pieces na roba tasa ajikinta,tare da ƴar jakar makarantar ta wanda ƴan wasu litattafai ne sai biro guda biyu a ciki.
Zama tayi bayan tasaka rigar, ta shafa ɗan viseline ɗinta sai ta yamutsa powder kaɗan ba mai yawa ba a fuskarta sai ɗan kwalli a idanunta sai lipglow da tasha fa ɗan ƙaramin bakinta.Maa shaa Allah kawai zan iya furtawa,this is what we call natural beauty a turance,gaskiya Sa'eeda nada kyau sosai duk da ba wata kwalliya tayi ba amma tafi wacca tayi make up kyau da haɗuwa.
Abinci taci sannan tayi nafila raka'a biyu saboda neman sa'a tare da neman tsari daga shirrin abubuwan da suke a cikin makarantar.
Daukan veil ɗinta tayi kalar kayan sai ta yafa sannan ta goyo jakarta a baya,sai ta dubi Ummanta tace"Toh Ummina zan tafi school"
"Ina nema miki tsari na daga abin cutarwa,tare da fatan Allah yasa ki fara a sa'a ki kuma kammala a sa'a tare da samun nasarori masu yawa,Allah ya albarkaci karatunki, ya kuma albarkaci rayuwarki baki ɗaya" haɗe da shafa kanta tana murmushi
"Aameen ya Hayyu ya Gayyum" haka Sa'eeda ta furta tare da ƙara jin so da ƙaunar Ummanta, haƙiƙa tayi dacen samun uwa ta gari mai tsoran Allah haɗe da haƙuri.
Kuɗin mota ta miƙa ma Sa'eeda sannan sukayi sallama,Sa'eeda ta fito daga ɗaki.
A tsakar gida kuwa Maman Jummalo ce tafito yin alwala kasancewar bata tashi sallar asuba ba,hasalima gwara ita akan sauran ƴan gidan don Umma Kande sai wurin 9:00am take sallah su kuma sauran yaran sai sanda suka tashi daga bacci,kai kai kai abun dai babu tsari.
Da wani mayan kallo Maman Jummalo take bin Sa'eeda dashi tana ayyanawa a zuciyarta 'Gaskiya kyawun yarinyar nan ƙara fitowa yake kullum kamar ba cikin ƙangin rayuwa suke ba'
Katse mata tunani Sa'eeda tayi da gaisuwa "Ina kwana Maman Jummalo"
"Lafiya lau,sai ina haka" tayi maganar ne dan ta bigi cikinta
"Makaranta zani" kasancewar Sa'eeda tasan kanta yasa taƙi sanar mata University zata tafi,hasalima ba susan yanayin karatunta ba.
Taɓe baki tayi irin ko ajikinta ɗin nan,saboda yaransu sun wuce da ajinta. (Ni kuma nace sun wuce ajinta a jahilci ba😂😂😂).
Ko irin a dawo lafiya Maman Jummalo bata iya ce mata ba haka tana kallonts wuce zuwa makaranta,dayake tsakanin gidansu da Kasu tafiyar mintuna arba'in ne shiyasa dole ta dinga hawan keke napep zuwa school.
Bayan ta fito gida ta tari mai keke napep a layin nasu kasancewar keke napep suna yawan wucewa saboda hanyar mai kyau ne babu tudu da kwararo sosai.
@@@@@@@@@@@@@@@
Lokacin da mai keke napep ya sauke Sa'eeda,ɗalibai maza da mata suna shiga cikin makaranta, mutane ne ba bambamta addini,al'adu da yaruka,itama sawunsu tabi zuwa cikin makarantar, dayake sanda suka zo screening har department ɗinsu sunje ita da Maryam yasa bata wani ɓata lokacin neman faculty ɗinsu ba,direct ta wuce department ɗinsu,sannan ta nemi ajin ƴan 100L ta shiga.
Tana shiga ta samu front sit ta zauna kasancewar ita ma'abociyar zaman gaba ne tun tana primary,bata daɗe da zuwa ba sai ga Maryam ta shigo,tasha tsadaddun kaya kamar zata biki ga make up da tasha,ta ɗauro jakar ƴan gayu ,ga takalmi high heel da tasaka,tana wani cat walking ita ala dole ƴar jami'a.
Nufo inda Sa'eeda take da zama tayi tana murmushi suka gaisa sannan tace ita bazata iya zaman gaba ba daman itama tun primary a middle seat take zama,ai kuwa taci sa'a mace ɗaya ce a seat ɗin,tako je ta zauna.
A haka ɗalibai sukaita shigowa har Head of Department ɗinsu ya shigo yayi welcoming ɗinsu tare da yi musu nasiha da jan hankali akan karatunsu,sannan daga baya lecturers suka fara shigowa haɗe da introducing kansu ga ɗaliban da course ɗin da zasu dinga offering ɗinsu dashi.
@@@@@@@@@@@@@
A nan ne kowa ya bada number wayarshi saboda za'a buɗe class group,haka kowa ya bada number shi,kasancewar Sa'eeda sabon layi ne akan wayarta bata haddace ba ya sakata ciro wayarta dan ta duba number nata,ji tayi a bayanta ance
"Ikon Allah ashe daman har yanxu akwai vivo,ai duk na zaci ƴan primary suke amfani da vivo dan yin games ba ƴan University ba" cewar wata matashiyar budurwa
Ta kusa da itace ta amsa da cewa"Wallahi kuwa kamar ma second hand ne a hannunta"
"Second hand ne kuwa,tabb wallah ko ƙanina wanda yake secondary infinix daddy ya siya mai"
Suko ƴan aji kowa kallonta yakeyi ,wasu na zunɗenta,wasu kuma na gulmarta,duk tana jinsu amma babu wanda ta kula,hasalima haddace numbanta tayi sannan ta maida wayarta jaka ta bada number ko a jikinta.
Kasancewar yau ne aka fara karatu,ajin nasu bai ciki ba kuma ma lecturers ba kowa ya shigo ba sai next week karatu zai fara zafi,shiyasa suka tafi gida da wuri.
Bayan tun fito ne Maryam ta dubi Sa'eeda ta ce"Yanxu ki rasa wayan da zaki siya sai vivo kuma ma vivo ƙarama,haba wannan ba class ɗinki bane wallahi,duk da bani aka yarfa a ji ba amma duk naji kunya"
Dariya Sa'eeda tayi sannan ta ce"Akwai wanda a cikinsu ya bani kuɗin shiga wannan makarantar ne,ina ruwansu da wayana,inason wayana kuma ina jinta kamar iphone ,don ko a jikina don sun yarfani,hakan bai dameni ba,karatu ya kawoni ba nuna waya ba"
Taɓe baki Maryam tayi sannan ta ce" Mu kuwa duka ya kawo mu"
"Toh Allah ya bada sa'ar haka"
Dayake hanyarsu ɗaya ne haka suka nemi mai keke napep suka nufo gida wurin ƙarfe biyu.
Haka Sa'eeda ta cigaba da zuwa school har satin ya ƙare,a sannan ne class time table ɗinsu ya fito,zama tayi tama kanta special time table na gida don tanaso tafito da flying colours kuma hakan bazai samu ba sai ta maida hankalinta ɗari bisa ɗari a karatunta sosai. Wannan kenan
@@@@@@@@@@@@@@@
Bangaren su Umma Kande kuwa sai dai sambarka,kamar yanda boka Sankeru ya musu alƙawarin yaransu za suyi aure to hakan ta kasance.
Kwana ɗaya da wanke fuskokinsu samari musu kuɗi suka musu ca wurin neman auran yaransu.A satin ne kowaccansu ta fidda miji wanda iyaye suka shigo ciki,haka Maman Jummalo ta tafi ƙauyansu dan sanar da auran Jummalo, itama Jummalo da saurayinta suka je ƙauyansu gaishe da dangin mahaifinta , saurayin ya gabatar da kansa kuma yace nan bada jimawa ba zai turo da iyayensa ayi maganar aure.
Bangaren Abban Sa'eeda hakan ta kasance saida yaje garinsu duk da ya jima rabonsa da garin nasu dayake iyayensa duk sun rasu saidai yayyi da ƙanne,duk da Umma Kande taso ta hanashi zuwa amma Maman Jummalo ta hane ta saboda gulmarta za'ayi a ce babu dangin mahaifin yara sai dai na uwa kuma hakan ba daidai bane ,da wannan yasa Umma Kande haƙura don batason danginsa su raɓeshi gashi ba sonta suke ba sunfi son Umman Sa'eeda.
Duk wannan zancen auran da akeyi banda Nusaiba, hakan baima Umma Kande daɗi ba amma babu yadda ta iya,ƙarya Nusaiba ta shiryawa Mamanta wai ƙawarta zatayi aure a sokoto kuma sun shaƙu da juna sosai tanason taje bikin,babu musu Umma Kande ta amince da tafiyar.(Anyi daƙiƙiyar Uwa a nan,gaskiya su Nusaiba basuyi dacen Uwa tagari ba🤔🤔🤔)
Haka ko Nusaiba ta shirya ƴan kayanta a ƙaramin akwati a cewarta ta tafi sokoto biki,ashe Dubai zasu ita da Alhaji Sagir,fitarta gida ta kirashi yazo ya dauketa daman ya daɗe da mata visa nafita ƙasar waje,a ranar suka cillar sararin samaniya zuwa Dubai.(Nusaiba ikon Allah,ba sabamba an hau jirgi,banda ƙauyanci dai acan😂😂😂)
Bayan dawowan Abban Sa'eeda ya sanar da Umma Kande akan amincewar danginsa,sai kuma ya ƙara da cewa"Lokaci kaɗan za'a sa ranar bikin nasy,ayi a huta gaba ɗaya"
Hakan yama Umma Kande daɗi sosai,kamar yanda yace lokaci kaɗan za'a saka bikin,haka kuwa akayi dan wata ɗaya aka saka bikin nasu su ukun,haka su Umma Kande suka fara shirye shiryan biki.
@@@@@@@@@@@@@@
Bangaren su Sa'eeda kuwa lectures ya soma zafi,gashi kullum sai sunje school harda ranar asabar wani lokacin.
Duk karatun da aka musu a aji idan ta dawo gida sai ta tabbatar da ta iya sosai kuma ya zauna a brain ɗinta sannan hakalinta yake kwanciya,ta lura ƴan ajin basa sonta saboda yanda idan akayi tambaya a aji take bada amsa har wani lokacin lecturers na mata kyautan marks hakan baya musu daɗi sai suyita hararta wasu har tsokanarta suke da hajiyar Vivo,tana jinsu amma bata tanka musu hasalima ita ta saba da irin wannan halin na ƴan aji tun tana secondary ake mata hassada kuma hakan ba damunta yake ba karatu tasa agabanta,duk da ba cika son bada amsa take ba sai idan malamin zai zagi ƴan aji shi ne take tashi ta bada amsa.
Bangaren Umman Sa'eeda kuwa ta fara zuwa aikinta na sharan titi ta wurin makarantar su Sa'eeda kasancewar nan ne portion ɗin da aka ɗibar mata, kullum a tare suke fita gidan ita da Sa'eeda,dayake da wuri Umman Sa'eeda take kammala sharanta ta dawo gida sannan kuma da ɗora da wankin mutane.(Allah sarki Umman Sa'eeda wataran sai labari😞😞😞)
Umman Sa'eeda tasan da maganar auransu Zulaiha amma tunda ba'a sata ciki ba,nata kallo ne,don wani lokacin habaici da gori suke mata wai ƴarta batada farin jinin samari,idan taji suna wannan zancen sai tayi dariya tace kwata kwata nawa Sa'eedar take da za'a ace batada farin jinin samari.
@@@@@@@@@@@@@@@
Wasa wasa lokacin biki ya ƙarato,baifi saura kwana biyar ba.A wannan lokacin ne akaita kawo lefan ƴan matan guda uku,babu laifi Naira tayi kuka,saboda dukkaninsu akwati 12 aka kawo musu kamar haɗin baki(Ni kuma nace maganar asiri ce fa ske malam,ai har fin haka ma zasuyi,saidai su jira sakamako 😀🤔), ga kayan ciki nagani na faɗa ne bancin gwala gwalen da aka narka aciki.
Maƙota da ƴan layi kowa zuwa ganin kwakwaf yake don aji daɗin gulmar dakyau,su Umma Kande da Maman Jummalo sai ɗaga kai suke suna yada magana tare da habaici akan gorin da ake ma yaransu akan sun ƙi aure sai tara samari yau gashi Allah yayi ƴan baƙin ciki saidai su mutu.
Ƴan uwa na nesa da na kusa sun fara zuwa tun daga dangin Umma Kande na Maiduguri,da na dangin Abbansu Sa'eeda tare da dagin Maman Jummalo duk sun fara zuwa,kasancewar gidan an sake gyarashi haɗe da ƙarin ɗakuna dayake gidan akwai fili sosai.haka baƙin suka samu wurin kwana.
A wannan satin ne Musa ya iso garin bayan tsawan lokaci rabonshi da gida,yana sallama cikin gida kowa ya bishi da kallon kurilla kowa bakinsa a sake don mamaki da al'ajab da ya cikasu........................
****Tofa ya akayi daga sallamar Musa Kowa ya bishi da kallo har da sakin baki,mai hakan yake nufi🤔🤔🤔
***ya kuke tunanin rayuwar Sa'eeda a jami'a,shin halayanta masu kyau zasu ɗaure ko ko zata sauya hali.....???
***My Esteem fans ga dai su Umma Kande da Maman Jummalo ana shirin aurar da yara,shin kuna tunanin sunyi dacen mazaje ko ko akasin haka kamar yadda Boka Sankeru yace zasu samu kowani irin mazaje.........???
Duk ku biyoni zuwa next page don jin amsoshinku✍️✍️✍️
Ina Matuƙar alfahari daku my Esteem Fans💖💖💖
Daga alƙalamin
🖍️📚Narrnarhh Bukar 📚🖍️
Comments and share 🙏🙏🙏Fisabilillah.
[4/25, 1:38 PM] +234 814 129 2044:
🏵️ NACINA YAJAWOMIN🏵️
Narrnarhh Bukar✍️
🌹Perfect Essential Writer's
Association🌹
✨ P. E. W. A✨
Wattpad:@AISHAABUBAKAR812
Arewabook:@Narrnarhh002
17---18
A wannan satin ne Musa ya iso garin bayan tsawan lokaci rabonshi da gida,yana sallama cikin gida kowa ya bishi da kallon kurilla kowa bakinsa a sake don mamaki da al'ajab da ya cikasu.
"Mai zan gani ni Hafsy,Musa haka ka koma !!!" cewar Maman Jummalo wacca fitowarta kenan daga ɗaki.
Wa'inda ma basu san da dawowarsa ba kowa ya bisa da kallon ƙurilla,gaskiya dole Maman Jummalo ta ce mai zata gani ita Hafsy,haƙiƙa duk wanda yasan Musa dole yayi mamakin ganinsa haka.
Mutumin da a da baƙi ne sosai yanzu ya koma fari sai kace bature,bancin haka ga wani askin ƴan iska da yayi,an saisaye ƙeyar kan ambar tsakiyar kai da mirɗe-mirɗen gashi sai kace kan zakara,ga kayan da ya saka wanda zakayi tunanin cikakken inyamuri ne ba Bahaushe ba kuma ɗan musulmi,wannan duk bashi ne matsalar ba kuma bashi ne abin mamakin ba yanayin maganarsa duk ta canja takoma kamar na ɗan daudu.
Cike da barikanci Musa ya fara magana kamar mace"Hi Maman Jummalo ƴar uwa, ya jin nice,kwana da yawa,ashe zamu aurar da yara"
Sai wani lanƙwasa da karairaya yake kamar wata mace,macan ma karuwa.Haba gida ba sai ya kaure da salati da sallalami ba,ma gulman layi an samu sabon rahoto.Matan gida na cikin wannan yanayi sai ga Umma Kande ta shigo gidan,dama bata nan ya dawo ba,taje siyayyar wasu kayan biki a kasuwa,saukanta kenan daga keke napep aka ce mata Musa ya zama ɗan daudu sai zance yakeyi a gidan da matan aure,bata ɓata lokaci ba ta shiga gidan cike da tashin hankali.
"Musa!,Musa!!,Musa!!!,kai ne haka!!!"
Waro idanu tayi waje tare da dafa ƙirjinta hannu bibbiyu sai kuma ta fashe da kuka har da shassheƙa don tayi mamakin a ce wai yau ɗan da ta haifa da cikinta ya zama ɗan daudu,to ya hakan ta faru ne,mai ya maida shi haka,tana kukan ne ya zo kusa da ita tare da cewa
" Oh My God,haba mommy na,why cry naaaa,keda zaki ji daɗin ganin ƴan matanki amma sai kuka,no no no,stop mommy na"
"Ƴan matana fa kace Musa,da hankalinka kuwa,kai macace da kake kiran kanka da ƴan mata,mai ya shiga ƙwaƙwalwarka Musa,wayyo ni Saratu jikar sarkin ruwa,naga ta kaina!!! "
"To miye a ciki don na zama mace,ai normal ne wallahi chass Mommy na,kinga nazo miki da tsaraba harda kayan mata ma wallahi sai kiba su Zaliha su gyara jikinsu kinsa ina harka da kayan mata kuma ina saidasu,naga ƙannena zasuyi aure shiyasa nace bara na kawo musu suma"
Ai ba shiri da tsagaita kukanta,jin ɗanta na wa'inan kalamai,yau mai ke faruwa da ita ne.
"Musa anya ƙwaƙwalwarka a daidai take aiki kuwa,kodai maƙiyana suka ma asiri ne,na shiga uku ni Saratu,wayyo ni wayyo ni shikenan sun mai damin ɗa ɗan daudu!!!
Kowa a gidan na mujiya ya zuba musu,jin wannan sabon salo sharri wai asiri a aka ma Musa,habawa tuni Umma Kande ta katse ma kowa tunani da kururuwanta wanda ya karaɗe gidan gaba ɗaya,har wasu ƴan waje sun fara shigowa cikin gidan don kashe kwarkwan idanunsu saboda har an fara kai rahoton Musa ya zama ɗan daudu.
" Wallahi bazata saɓuba,wannan aikin asiri ne! Wallahi bazan yarda ba,asiri akama yarona don anga arziƙi ya fara samun mu,to wallahi ƴan baƙin ciki sai dai su mutu,wallahi bazan yarda ba,sai na ɗau mataki wallahi kawai a maida min ɗa mace, wayyo ni Saratu,wayyo ni sarere jikan sarkin ruwa,yau naga ta kaina,yiiiiiiiiii,yiiiiii,wayyo niiiiiiii!!!"
Da sauri Maman Jummalo tayi cikin ɗaki da ita saboda ta fara sakin layi,kar ƴan layi suji sirrinsu,da ƙyar ta shigar da ita ɗaki,ta ce kowa ya wuce gidansa.
Ƴan uwan Umma Kande ne da dangin Maman Jummalo d'a ɗakinta tare da ita kanta Maman Jummalo suna bama Umma Kande baki akan tayi haƙuri,ta kwantar da hankalinta bayan biki sai a bi lamarin na Musa a hankali.
Haka dai suka lallaɓata har da rage kukan sai dai shassheƙa wanda lokaci bayan lokaci take ajiyar zuciya.
Shiko Musa ko a jikinsa hasalima fita daga gidan yayi,daman baida niyyar kwana gidan,hotel na garin yaje ya kama na kwana huɗu har a gama biki ya koma Calabar abinsa.
Ƙarin Haske
*****Abinda bata sani ba game da Musa shi ne,tun farkon tafiyarsa Calabar halayansa suka fara canjawa,duk da lokacin akai-akai suna waya da Umma Kande, zuwanshi gida wanda daga shi bai ƙara zuwa ba sai wannan zuwa duk halayansa sun canja,kasancewarsa mai sanyin murya,gashi ba mai hayaniya ba yasa a lokacin da yaje Calabar abubuwa suka mishi wuya,tunda baida zafin nama da karsashi a komai nasa kamar wata mace haka yake ji da kansa.Farko ya fara dako sai daga baya yaga babu ci ya daina,sai wani abokinsa da suke kwana a ɗaki ɗaya yaji tausayinsa yayi mishi hanyar aiki gidan abinci wanda yawancin ƴan aikin hausawa ne amma fa cikakkun ƴan bariki mai gidan abincin ma bahaushiya ce,haka ya fara aiki gidan abinci wanda daga ƙarshe ƴan daudun gidan abinci suka fara bashi sha'awa ganin suna samun kuɗi sosai,manya-manyan matan garin suna zuwa ɗaukarsu fita cikin manyan motoci,shima kawai ya tsunɗuma cikin wannan harkar,abinda yafi ƙarfafa mishi son shiga harkar shi ne Mamansa Umma Kande,a duk sanda sukayi waya da ita sai ta mishi ƙorafin rashin turo kuɗi akai-akai da ba yayi,wai ya cika son jiki kamar mace,shi yasa bai samun komai a acan, ga abokanansa wasu har da gidaje da mata amma shi ko sisi bai turowa balle tunanin yin aure,shi kuma a gaskiya maganganunta suna ƙona mai rai sosai,shi yasa ya bama kanshi shawaran zai naima kuɗi kota y'halin ƙaƙa ne in har Mamansa zata daina ce mishi rago ne.Wannan ne asalin dalilin da yasa Musa shiga cikin harkar ƴan daudu a Calabar har shi ma yanzu yayi suna a can ana kiransa da Pretty Mussy,don ba laifi tana kai mai yanda ya kamata.Daman wannan zuwan da yayi bayan biki yake son ya siya gida sannan ya siya shagugguna a kasuwa wanda kuɗi zai dinga shigo masa akai-akai har Mamansa tayi alfahari da shi kamar yadda take alfahari da Nusaiba wai tafishi samun kuɗi kuma tana tallafa musu a gidan****.
@@@@@@@@@@@@@@
Bangarensu Sa'eeda ita da Ummanta Allah yasa basama gidan a lokacin da Musa ya dawo,balle suga abin mamaki da al'ajab,kuma koda suka dawo ɗaki suka shige abinsu,daman ba shiga harkar bikin suke ba tunda ba'a sakasu ciki ba,Sa'eeda da take budurwa ma babu wacca a cikin ƴan uwan nata ya gayyace ta balle taje ƴan matanci a bikin.
Dangin Abbansu Sa'eeda tun fil-azal ba son Umma Kande suke ba shi yasa koda wannan lamari ya afku suna ɗaki basu fito ba sai dai Allah ya kyauta suka iya cewa, dayake mata uku ne sai namiji ɗaya sukazo bikin.Ƙannan Abbansu Sa'eeda mata da yayarsa ɗaya sai kuma ƙaninsa namiji sukazo bikin.
Dayake suna shiri sosai da Umman Sa'eeda haka sukai ta janta da Sa'eeda a jiki.Hakan yama Sa'eeda daɗi a rai,ganin yanda suke janta a jikinsu da hira har da Ummanta.
Daman auran Umman Sa'eeda su ne suka ƙarfafa gwiwar sai ya ƙara aure saboda halin Umma Kande,bata girmama iyayansu tun suna raye,gashi da tsani wani daga daginsu ya raɓa Abbansu Sa'eeda saidai ita da yaranta kaɗai,wannan dalilin ne yasa aka aura masa Umman Sa'eeda saboda tanada hankali da girmama na gaba da ita ba kamar Umma Kande ba.
@@@@@@@@@@@@
Umma Kande dai ta dangana,tayi haƙuri sai bayan biki kamar yanda Maman Jummalo ta ce da ita saboda bikin,ta haƙura ta cigaba da shirya shiryan biki sosai,tun ana saura kwana uku amare suka fara shagalin biki har yau da ya kasance gobe ɗaurin aure suna shagali kala-kala.
Day 1 sunyi ƙauye day, sai day 2 sunyi fulani day sai yau kuma ana kamun amare,anyi kashe kashen kuɗi,ba laifi angwaye sunyi ɓarnar kuda don Naira tayi kuka😁.Nusaiba tayi ɓarin Naira sosai dan yanxu ta zama wata himmm da ita sai kace wata babbar mace ,tayi ƙiba sosai ga bleaching ɗin da take yanxu na allura ne, tayi haske sosai sosai.
Duk wannan bidirin da ake yi a gidan bai hana Sa'eeda zuwa makaranta ba,sannan Ummanta ma haka kullun sai ta fita shara abinta,a tare suke fita da safe abinsu.
@ @@@@@@@@@@@@
Ranar ɗaurin aure
Yau take asabar kuma ranar ɗaurin auran yara uku a gidan Malam Sulaiman Sani,a Masallaci aka ɗaura auran na ƴaƴan uku akan sadaki Naira dubu #100,000 lakadan ba ajalan ba ga kowaccansu,sannan aka shafa fatiha aure ya ɗauru(Su Umma Kande sai a zuba ruwa a ƙasa a sha😁😁😁😁).
Angwaye babu wanda yazo gaisuwan iyayen amare kamar yanda ake a al'adan ce,nan ma akaita surutai musamman ƴan layi( Ƴan layi akwai gulma,kunsama su Umma kande da Maman Jummalo ido,kun hanasu rawar gaban hantsi haba😁😁😁🙃🤔) ,wurin ƙarfe 8:00pm aka zo ɗaukan Jummalo, sai kuma Zaliha,ita kuma Iklima sai 11:00pm aka ɗauke ta,wannan abu ya janyo surutun mutane da dama, su Umma Kande hakan bai dame su ba tunda an ɗaura mai ya rage can tamatse musu da gulmar,duk lokacin da suka zo ɗaukar amare suna mara ba dasu tunda dai an ɗaura auran ƙarshen tika-tiki-tik.
Haka aka kai kowacce ɗakinta,babu laifi angwaye sunyi bajinta sosai,sai dai bamusan ya yanayin zaman auran nasu zai kasance ba.
@ @@@@@@@@@@@
Bayan kwana biyu da biki,dangi na kusa da na nesa kowa ya koma gidansa da abin arziƙi daga wurin su Umma Kande da Maman Jummalo banda dangin Abbansu Sa'eeda taƙi basu abin biki wai tunda dama ba sonta suke ba kuma wannan zuwa biki wurin su Umman Sa'eeda suka tare to wallahi babu abin biki da zata basu,har Abbansu Sa'eeda saida ya roƙa amma taƙi,haka suka wuce garinsu daman su can basu sa rai a abin bikin ba balle hakan ya damesu.
A ranar bayan tafiyar ƴan uwan Abbansu Sa'eeda daman su kaɗai suka rage, Musa ya shigo gidan,tun sanda yazo gidan ta fara kuka bai sake zuwa ba kuma koda yaje ɗaurin auran bai zo nan gida ba.
Lokacin ƙarfe 12:00pm na rana,shiga ɗakin Umma Kande ya yi da sallama kamar mutumin arziƙi amma muryar nan a lanƙwashe take kamar mace,ya samu wuri akan kujera ya zauna.
Maman Jummalo ce ta amsa masa sallamar amma Umma Kande ko kallan inda yake batayi ba.
Ɗakin shiru ya ɗauka na ɗan wani lokaci kowa na zancen zuci kafin Musa ya ƙatse shirun da gaishe dasu.
"Mommy na barka da rana,na same ku lafiya,ya gajiyan biki"
Yana maganar yana yanga sai kace mace,su Umma Kande dai ido suka zuba mai babu ɗaya a cikin wanda ya iya amsa mai,tsabaragyen mamaki da ya cika su musamman Umma Kande wanda har yanzu ta kasa yarda ɗanta ne Musa,shi Musa ɗanta ya zama ɗan daudu.
"Yanxu Musa wannan wani irin ɗabi'a ne ka ɗauko,kaga kuwa yanda ka koma yanzu sai kace mace wallahi abinda kakeyi ko wata macan baza tayi ba,haba Musa ya kamata ka dawo cikin hayyacinka don Allah" cewar Maman Jummalo
"Nahiiiiii Maman Jummalo inji ƴan india kinsa nayi yaransu , wannan ra'ayina ne,babu ruwanki koma mai zanyi,haka nake da ra'ayin zama,kuma ina alfahari da zama na haka,chass wallahi"
Miƙewa yayi duk suna binsa da kallo yayi wani juyi a ɗakin tare da girgiza ɗan ƙaramin kafaɗunsa sannan ya ce
"Yanzu ki kallo dubeni kyakkyawa dani san kowa ƙin wanda ya rasa,ke a Calabar ma har bukin ɗina akai manya manya Mata suna ji dani,zaki wani ce in dawo hayyacina,to da ba a hayyacina nake ba"
"Shikenan ni Saratu, ta faru ta ƙare Musa,yanzu a gabana ni mahaifiyarka kake girgiza kafaɗunsa haɗe da rangwaɗa,wayyo ni Sarere jikar sarkin ruwa!!!,na shiga uku!!! "
Kuka take yi mararan,da sauri Musa yazo wurinta haɗe da dafa kafaɗunta tare da cewa" Sorry mommy mi,kibar kukan nan don Allah babyn ki da kika sani a da bana yanzu bane,don nayi kuɗi sosai sosai "
Tsagaita kukan Umma Kande tayi tana dubansa tare da cewa"Da gaske kake Musa na ɗan albarka"
Ɗaga mata kai ya yi alamun eh,haba sai Umma Kande ta haɗe ido da Maman Jummalo nan suka kwace da dariya.
"Haba sai yanzu naji sanyi a raina,mai yasa tunda kazo baka faɗamin ba,kabarni ina kuka akan yanayin da ka koma,ai babu laifi tunda akwai samu"
"Wallahi mommy naso faɗa miki amma sai naga duk kin rikice kawai sai na bar gidan na tafi hotel abuna,daman na bari sai bayan biki nazo muyi maganar dake"
"Toh yanzu dai fadamin maganar ina jinka kace kayi kuɗi,ni kuma banga komai ba"
Dariya Musa yayi yana wani lanƙwasa ƙafa ɗaya kan ɗaya sannan ya ce"Suna account Mommy,daman nazo ne da niyyar siyan gida,tare da shaguna koda biyar ne a kasuwa,sai nasa haya,kinga zaki dinga samun kuɗi akai-akai ko Mommy na? "
"Da kyau ɗan albarka,naji daɗin wannan batu wallahi, Allah yama albarka,amma gaskiya idan zakazo garin nan,inaso ka koma yanda kake a da,bayan ka tafi sai ka juya saboda ƴan gulmar layi kaji ɗana"
"Bakida case Mommy mi, yanzu sai ku fara cigitamin gidan haɗe da shagunan ko"
Da "Eh" dukkaninsu suka ce suna murmushi ,sai ya ciro bandri ɗin dubu kuda uku ya miƙa ma Umma Kande da Maman Jummalo, haba wannan karon harda kuɗa tare da rungumeshi su duka(Allah ya kabamu wadatar zuci da ƙarin imani).Wannan kenan.
@@@@@@@@@@@@@
A bangaren karatun Sa'eeda sai dai muce maa shaa Allah,tana maida hankali sosai da sosai dan yanzu har sun kammala first semester suna a second semester a lokacin first semester result ɗinsu har ya fito.Sa'eeda ce ta samu highest score a class ɗin nasu wanda baima da yawa daga cikin ƴan ajin daɗi ba.
Yanzu ma haka su Sa'eeda sun tashi a school kasancewar yau Friday da wuri suke tashi.Bayan sun fito daga department ɗinsu ita da Maryam zasu nufo wajen gate ɗin makarantarsu don su samu mai keke napep ya kaisu gida,sukaji horn ɗin mota a bayansu,dukkansu babu wacca ta zuyo suka cigaba da taifiyarsu,mai mota da yaga alamun ba tsayawa zasuyi ba,yayi saurin parking a gefen titi sannan ya fito daga motar.............
****waye wannan mai yima su Sa'eeda horn kuma mai yazo dashi wurinsu?.......
****Gashi dai burinsu Umma kande ya cika an aurar da ƴaƴa,koya zaman nasu zai kasance da mazajensu?.........
🌹🌹🌹Shin ya kuke ganin mugun son kuɗin Umma Kande wanda ko kallon yanda ɗanta ya koma batayi ba,mai zakuce akai........
Sai mun haɗu da pages na gaba in
shaa Allah🙃🙃🙃
Ina matuƙar alfahari daku My Esteem Fans💝💝💝🌹🌹🌹🌹
I love y'll lodi lodi domin da bazarku nake taka rawata💝💝💝💝🙃🙃🙃🙃🤗🤗🤗🤗
Daga alƙalamin
🖍️📚Narrnarhh Bukar 📚🖍️
Comments and share 🙏🙏🙏Fisabilillah.
[4/25, 1:38 PM] +234 814 129 2044: 🏵️ NACINA YAJAWOMIN🏵️
Narrnarhh Bukar✍️
🌹Perfect Essential Writer's
Association🌹
✨ P. E. W. A✨
Wattpad:@AISHAABUBAKAR812
Arewabook:@Narrnarhh002
My Esteem Fans ina matuƙar alfahari daku, i love y'll all Lodi Lodi🤗🤗🤗🏵️🏵️🏵️🌼🌼🌼🌹🌹🌹🙃
19---20
Yanzu ma haka su Sa'eeda sun tashi daga school kasancewar yau Friday da wuri suke tashi.Bayan sun fito daga department ɗinsu ita da Maryam zasu nufo gida,sukaji horn ɗin mota a bayansu,dukkansu babu wacca ta juyo suka cigaba da taifiyansu,mai mota da yaga alamun ba tsayawa zasuyi ba, sai yayi saurin parking a gefen titi kana ya fito daga motar.
Wani handsome and classy guy ne ya fito daga motar,yana sanye da shadda mai kalar sararin samaniya,sanye yake da hula mai ƙube wacca ta saje da kalar kayan.Yana da tsayi sosai,baƙi ne amma ba cancan ba,sannan fuskarsa zagaye take da gemu wanda kana gani kasan yana shan gyara,his face look very innocent,babu laifi guy ɗin ya haɗu sosai,da murmushi a fuskarsa ya nufo wurinsu da ɗan sauri kasancewar tafiya suke.
"Assalamu Alaikum Malamai"
Maryam ce ta amsa mishi da fa'arta,ita ko Sa'eeda ko kallansa batayi ba,idonsa na kan Sa'eeda yana murmushi,don mace mai aji tana burgeshi sosai.
"Naga akwai rana sosai yau,gashi kuna tafiya babu mai keke napep suka balle ku hau,mai zai hana na rage muku hanya koda ban kaiku gida ba,kar kusha wahala"
A lokacin ne Sa'eeda ta bashi amsa da cewa"Kaga munyi ma kana da musu son a rage musu hanya ne,to karka damu,mun gode da kulawarka amma......."
Bata ƙarasa zancen da tayi niyya ba Maryam tayi saurin cewa"Babu komai muje Sa'eeda, kinsan uzirin da ya bari ya ce zai rage mana hanya ne? "
Sunan ya sake maimaitawa a zuciyarsa ' Sa'eeda suna mai daɗi'
Babu yadda Sa'eeda ta iya tunda abokiyar tafiyarta tana son a rage musu hanya amma a ranta baso take ba tuno da nasihar Ummanta akan kula samari,haka dai ta shiga motar.
Maryam ce ta zauna a front seat,ita kuma Sa'eeda ta shiga baya,tada motar yayi suka fara tafiya.
Motar shiru babu mai magana sai can ya katse shirun da cewa"Wani department kuke? "
"Department of Business Administration muke,100level" cewar Maryam
" Woow,ashe fresh students ne ku"
"Eh wallahi amma yanzu muna a second semester ne"
"Allah ya taimaka,ya bada sa'a"
"Ameen ya Rabbi" cewar Maryam
"Wai ƙawarki kurma ce,bata magana ne? "
Dariya Maryam tayi sannan ta ce"Magana kuwa sosai,saidai da alama ƴan surutun basa nan yau"
"Oh really ai naga alama kuwa"
Maryam ce take nuna mishi hanya,har ya kai daidai inda take so a sauke su wato hanyar da zata sadasu da layinsu,sannan yayi parking gefen titi,ya juyo yana duban Maryam yace.
"Sunana Sauban Muhammad ƙaraye,ina aiki a wani kamfinin sarafa shinkafa a matsayin Manager nice meeting you friend"
"Nice meeting you too"cewar Maryam
Dukkansu fitowa sukayi,a tare har shima don yana son magana da Sa'eeda amma ta mishi kwarjini a fuska.Har zasu wuce yayi saurin cewa
"Friend ko zaki aramun wannan ƙawarta taki mara son magana,zsmuyi magana ne just for 2 minutes"
Yana maganar da zolaya duk don Sa'eeda da tanka amma shiru,hasalima ƙara murtuke fuska tayi.
Ɗan jimmm Maryam tayi sannan ta ce "Haba bara na matsa,sai ku tattauna da ita"
Matsawa tayi ɗan gaba dasu,shi kuma ya matso kusa da Sa'eeda da murmushi a fuskarsa,sai da yayi gyaran murya sannan ya fara magana da cewa.
"Nasan ba a jinki bane magana a hanya amma taimako nake nema wurinki,don Allah ba dan ni ba ki taimaka min da number wayanki,Don girman Allah"
Hannu biyu ya haɗa alamar roƙo,fuskar nan ta shi tayi kalar tausayi,Sa'eeda a da bata da niyyar ba shi numbarta amma haɗata da Allah da yayi yasata aminta saboda ta tuno nasihar Ummanta da ta ce ' Sa'eeda duk wanda ya nemi abu wurinki kuma ya roƙeki da Allah koda cutarki zaiyi ki basa,sannan ki barshi da Allah' tuno da wannan nasihar yasata amsar wayarsa tasa numbarta sannan ta miƙa mai wayar tare da wuce wurin Maryam suka nufo gida.
@ @@@@@@@@@@
Ƙarfe 11:53am ta iso gida,lokacin Ummanta ta dawo daga aikin sharanta tana ɗaki.
Da sallama ta shiga gidan kasancewar yanxu babu ƴan mata a gidan daga ita sai Nusaiba,ita kuma Nusaiba ba zaman gidan take ba, yanxu ma kamar kodayaushe shiru gidan saika ce babu mutane ko a da can da akwai mutane a gidan ba amsa sallamarta da Ummanta suke ba.
Direct ta wuce ɗakinsu,haɗe da sake Sallama, Umman Sa'eeda dake a tabarmarta ta amsa mata tare da cewa.
"Da wuri haka"
"Eh Ummina,kinsa ranar jumma'a bamu cika lectures da yawa ba,yau kuma lecturer ɗaya ne ya cigo ajin namu"
"Ai gwara,zaku ɗan dinga hutawa,ba ace kullun sai wurin biyar zaku dinga ta shi ba,wahalar yawa zata muku"
"Nima Ummina nafi son duk ranar Friday mu dinga tashi kamar haka wallahi"
Buta Sa'eeda ta ɗauka ta zagaya bayan gida,bayan ta dawo ne taji wayarta na ringing,sai ta nufa jakarta ta ɗauko wayar.Sabuwar numbar ta gani,ɗan jimmmm kaɗan tayi har saida Ummanta ta ce
"Kina ji ana kiranki amma kin wani tsaya kamar hoto kina kallon wayar"
Picking call ɗin tayi haɗe da karawa a kunnanta sai tayi shiru,acan bangaren aka fara magana.
"Tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gareki Sa'eeda"
"Wa'alaikumussalam"
A gajar ce ta amsa haɗe da tsuke fuska kamar mai shirin kuka Ummanta dai na binta kawai da kallon mamaki ganin yadda take amsa wayar,a can a ka cigaba da Magana.
"Nasan kin gane mai maganar don koda jin kamar kina ɗaure fuska nasan yes kinsan mai maganar"
A zuciyarta ta ce 'Sai ka ce maye,to taya yasan na tsuke fuska na,ohon masa' katsa mata tunani yayi da cewa
"Sa'eeda ganinki na farko da nayi a ɗazo,lokaci guda kika shiga raina,kuma a gaskiya bazan ɓoye miki ba ina sonki da aure ne ba da yaudara ba,zuciya ta gama yarda da ke ce wacca take adduarka samu a kullum haɗe da burin kasancewa tare da ita a matsayin miji da mata,please Sa'eeda ba nazo dan na yaudareki bane ko ko wata manufa tawa don in cimma,a'a ko kaɗan nazo ne a gareki saboda ƙaunarki da nake yi wanda lokaci kuda ya shigeni,don Allah ki aminta dani please,in ma kina tunanin karatunki ne ni a shirye nake tare da goyon bayan karatunki ɗari bida ɗari,inaso kiyi tunani akai don girman Allah Sa'eeda bada wasa nazo gareki ba"
Duk wannan surutan da yake wayar na a kunnanta kuma tana ji amma ta kasayi mishi magana,hasalima shiga kogin tunani tayi 'Wai yana sonta da aure huhh',ita da a tsarin rayuwarta bata kawo aure nan kusa ba,amma shi yanzu yana mata maganar aure.
"Hello,baki jina ne Sa'eeda"
Firgigit ta dawo hayyacinta tare da fara magana cikin murya mai sanyi da dadi ta fara magans"Ina jinka,but can you please give me some days to think about it?
"Quite sure dear"
"Alright Nagode da kulawa"
Bata jira mai zai ce ba ta katse kiran,sai da dubi Ummanta da tun ɗazu da zuba mata na mujiya.
"Naga sai wani taɓe baki kike haɗe da ya mutsa fuska tunda kika ɗau wayan lafiya? ”
" Wallahi Ummina wani ne mai suna Sauban ɗazu ya takuramin haɗe da haɗa ni da Allah in taimaka mishi da number na,lokacin mun taso daga school ni da Maryam kuma yanzu da ya kirani sai sai..."
"Uhmmm ina jikin sai kuma me"
Kwashe duk abinda ya ce mata tayi ta sanar da Ummanta har aikin da ya ce yakeyi duk ta sanar mata, shiru Ummanta tayi tana kallonta sannan ta ce
"To ke kuma me kika ce masa"
"Nace ne ya bani lokaci zanyi tunani a kai"
"To ai shikenan,amma dai ki kula da kanki Sa'eeda,don mazan yanzu wasunsu ba abin yarda bane,sun iya kalamai masu daɗi ga ƴan mata duk don suja hankulansu,ina ƙara fadamiki ki kula da kanki sosai,ban hanaki kula samari ba amma ki duba wanda yasan ya kamata sannan kuma mai addini da halaye masu kyau a cikinsu sai ki kulashi,amma ba kowani kala ba,ko kuma kita tara samari,kin jini ko"
"Toh Ummina,zan kula sosai in shaa Allah"
"Allah yasa"
"Aameen"
Sai kuma suka cigaba da wata hirar .
@@@@@@@@@@@@@
Bayan ƴan wasu kwanaki
Sa'eeda dai ta aminta da soyayyar Sauban,dan yanzu yakan zo har ƙofar gidansu,duk da a wata baifi sau ɗaya yake zuwa ba kasancewar Sa'eeda bata cika son hira ba hasalima shi yake matsa mata akan yanason yazo koda sau ɗaya ne a wata.
Sunyi exams ɗin second semester wanda azumi baifi saura kwana shida a ɗauka ba suka gama,duk wannan lokacin suna tare da Sauban wanda yanzu soyayyarsa ta riga da ta gama mamaye ilahirin jikinta da gaɓoɓinta gaba ɗaya.
Sauban ya iya kashe mace da salon soyayyarsa,don zance professor ne a ta wannan fannin,ya kama zuciyar mace taji duk duniya babu wanda take so sai shi,haƙika ya rikita Sa'eeda da kalaman soyayya masu saka mutum shauƙi,sannan yana kula da lamarinta sosai duk da idan ya bata kuɗi bata amsa sai in ya mata jan ido kana take amsa haɗe da yi masa godiya.
Haka sanda aka fara azumi ya kawo mata ramadan basket da ƙyar ta amsa saboda Ummanta ta hanata yawan amsar kaya wurin samari,haka zalika lokacin sallah kaya kala biyar ya mata haɗe da jaka da takalmi masu tsada,shima da ƙyar ta amsa sannan ta masa godiya sosai.
Duk wannan abubuwan da Sauban yake ma Sa'eeda sai ta faɗama Maryam tun daga kalaman soyayya da yake mata,kyaututtuka da dai sauransu,duk da wani lokacin ba Sa'eeda take fara bata labari ba,ita Maryam da kanta take tambayar ta ya friend ɗinta,to a nan ne sai ita kuma Sa'eeda tai ta zubo mata zancansa.
Haƙiƙa wannan sallar su Sa'eeda sunyi shi cikin farin ciki da annashuwa ba kamar saura shekarun da suka gabata ba kasancewar yanzu babu laifi Umman Sa'eeda na ƙoƙarin ganin sunyi cima mai kyau.
Bayan sallah da sati ɗaya suka koma 200 level,soyayyar Sauban bai hana Sa'eeda karatu ba hasalima yanzu karatun nata ya ƙara bada wuta saboda tana so taga a kowanni result ta fito da flat A,shi yasa kullun zaka ganta da littafi a hannu tana karatu.
Akwai specific time da taba ma Sauban zai dinga kiranta ba koda yaushe ba,kuma hakan ta faru sai lokacin yake kiranta don baya son matsa mata da yawa.
@ @@@@@@@@
Waje guda kuma,rayuwarsu Umma Kande da Maman Jummalo ta cigaba da tafiya cikin daɗin rai da annashuwa duk da ba kamar sanda yaran nasu suke gida ba,don yanzu basa samun ko sisi a hannun yaran nasu wa'inda suka aurar hasalima tunda a kayi auran nasu babu wacca ta leƙo gidan da sunnan gaishesu,kuma idan suka tuntuɓi mai yasa sai dai suce mazajensu sun hanasu zuwa,abu fa kamar haɗin baki.
Kamar kullum Sa'eeda da Ummanta sun fito daga ɗaki zasu wuce sai ga Abbansu Sa'eeda ya shigo gidan da sallama, amsawa su ka yi,sai ya dubi Sa'eeda fuskarsa ɗauke da murmushi ya ce
"Sai ina Kuma Sa'eeda "
Banbaraƙwai Sa'eeda taji maganar tazo mata sai ta ce
"Abba makaranta zani"
"To ina unifoam ɗinki,a haka zaki makarantar ne,ko kinaso a miki duka ne"
"A'a Abba,yanxu ba nasa unifoam ai"
"Bangane ba,makarantar kuma yanzu bakya mata unifoam idan zaki,kodai unifoam ɗinki ya lalace ne,sai ki siya wani? "
" A'a Abba,ai yanzu ba'a secondary school nake ba"
"To kina ina ne yanzu"
"Abba ai na shiga university ina karantar Business Administration a Kasu"
"Au haba!,yaushe kika fara zuwa makarantar,ai bansani ba"
"200 level nake ma yanzu ai saura shekara biyu na gama"
"To to,maa shaa Allah,ki maida hankali sosai a karatunki kinji Sa'eeda"
"To Abba in shaa Allah"
"Yawwa ƴar albarka"
Hannu yakai aljihunsa ya ciro kuɗi ƴan dubu dubu da yawa wanda ni kaina mai ɗaukar rahoton bansan nawa bane ya miƙa mata sannan ya ce
"Ki ƙara kuɗin mota,tunda makarantar da nisa"
Har ƙasa ta ɗurƙusa hannu bibbiyu ta amsa kuɗi haɗe da yi masa godiya da adduar buɗi agaresa,Sosai ya amsa mata cike da kulawa.
Haka suka fito ita da Ummanta cike da ɗunbin mamakin sauyawansa lokaci guda.
Tun daga fara maganar Abbansu Sa'eeda da Sa'eeda Umma Kande dake da niyyar fitowa don tayi alwalar sallar subh duk taji kuma a gaban idonta Abbansu Sa'eeda ya fito da maƙudan kuɗi ya miƙa ma Sa'eeda.
Tashin hankali wanda ba'a sa mai rana ai a rikice ta shiga ɗakin Maman Jummalo ko sallama babu ta banko ƙofar ɗakin ta shiga,Maman Jummalo dake bacci cikin kwanciyar hankali tayi saurin buɗe ido jin an banko mata ɗaki babu sallama balle izinin shiga.
"Lafiya Ƙawas? "
"Ina fa lafiya Maman Jummalo, shi ke nan,tawa ta ƙare! "
"Bangane ba ƙawas,fahimtar dani,kin barni a duhu"
"Aikin gama ya gama ƙawas,yau da idona naga Babansu Nusaiba na miƙa ma Sa'eeda kuɗi masu uban yawa harda sa mata albarka wai ta maida hankalinta akan karatunta"
"Kuɗi!!! Kuɗi!!! Kuɗi fa kika ce,anya kin gani da kyau kuwa? "
" Wallahi tallahi,billahillazi Kinga har da salati nayi ko, to nagansu da idona Maman Jummalo! Nace miki nagansu! Ke kwarankwatsa tannatsa! Na gansu da idona kuma ni ganau ce ba jiyau ba,har da tambayarta makarantarta haɗe da samata albarka,yihuhuuuuu ni Serere jikar sarkin ruwa na mutu! Na mutu ho ho hooooo! "
"Kwantar da hankalinki duk wannan kururuwan da kike bashi bane bafita Ƙawas"
"To ne kike so inyi bayan hankalin Babandu Nusaiba ys fara karka garesu,ai wallahi kashina ya bushe"
"Haba don Allah nace ki kwantar da hankalinki,zamu samu mafita akan wannan lamarin,ke bari kiji akwai mafita amma mafita ɗaya ce garemu yanzu "
"Akwai mafita kika ce MamanMaryam
lo,to mecece mafitar? "
"Ba wata mafita bace illa...................
Sai mun haɗu a pages na gaba in shaa Allah🙃🙃🙃
****ya kuke ganin soyayyar Sauban da Sa'eeda, shin zai kaisu har aure ko ko wata ƙaddara zata gitta???
****Shin wace mafita ce Maman Jummalo ta ce akwai??
***Mai yasa ƴaransu Umma Kande da Maman Jummalo kamar haɗin baki babu wacca tazo ganin gida???,Mai hakan yake nufe??? Mai yasa mazajansu suka hanasu zuwa ganin gida?? sannan yaya zamansu da mazajansu yake???
Duk ku biyoni zuwa next pages domin samun amsoshinku✍️✍️✍️🙃🙃🙃🙃🙃🙃💝💝💝💝💝🌹🌹🌹🌹
Ku cigaba da zubo ruwan coments da reactions My Esteem Fans ni kuma zan cigaba da suburbuɗo muku updates wanda zaku nishaɗantu tare da ilmantuwa🌹🌹🌹💝💝💝🏵️🏵️🏵️🏵️😁😁😁🙃🙃🙃
Ina matuƙar alfahari daku my Esteem Fans🤗🤗🤗🏵️🏵️🏵️🏵️🙃🙃🙃
Daga alƙalamin
🖍️📚Narrnarhh Bukar 📚🖍️
Comments and share 🙏🙏🙏Fisabilillah.
[4/25, 1:38 PM] +234 814 129 2044:
🏵️ NACINA YAJAWOMIN🏵️
Narrnarhh Bukar✍️
🌹Perfect Essential Writer's
Association🌹
✨ P. E. W. A✨
Masu telegram zaku iya following ɗina acan🤗🌹👇👇👇
https://t.me/+439Pdx2UbLZlOTNk
Wattpad:@AISHAABUBAKAR812
Arewabook:@Narrnarhh002
🌹🌹🌹I'm not born to be a writer but born to be a great professional writer✍️✍️✍️🙃🙃🙃🌹🌹🌹
🤗🤗🤗Special greetings to y'll my Esteem fans,i love y'll💝💝💝💝🤗🤗🤗
21---22
"Kwantar da hankalinki duk wannan kururuwan da kike bashi bane bafita Ƙawas"
"To mai kike so inyi bayan hankalin Babansu Nusaiba ya fara karka garesu, wallahi nasan kashina ya bushe idan na bari hankalinsa ya koma kansu"
"Haba don Allah nace ki kwantar da hankalinki ko,zamu samu mafita akan wannan lamarin,ke bari ma kiji akwai mafita amma mafitar ɗaya ce garemu yanzu "
"Akwai mafita kika ce Maman Jummalo,to mecece mafitar? "
"Ba wata mafita bace illa mu shiya ranar lahadi muje wurin boka Sankeru,ita kadai ce mafitar tamu kinga sai ya duba yaga ko asirin ne ya warware"
"Haka ne kuma,kin kawo shawara mai kyau amma anya zan iya bari har lahadi Ƙawas,lahadi tayimin nisa ji nake kamar yanzu na ganni gaban boka Sankeru,ko hankalina zai kwanta"
"Haba Saratu,kin cika gaggawa a al'amuranki wallahi ina nan ina ranar lahadi,kin manta yau alhamis baifi saura kwana biyu ba amma duk kin bi kin tada hankalinki a banza,haba don Allah"
"Allah ya kaimu ɗin"
A haka Maman Jummalo ta cigaba da kwantar ma Umma Kande hankali har ta natsu,sai daga baya ta wuce ɗakinta ,sallar subh ma da ta ce zatayi tafasa sai bayan ta dawo daga wurin boka Sankeru zata cigaba da sallah.(Ohhhh niii!!! Duniya ina zaki damu🤔🤔🤔,wannan wani irin jahilci ne haka,kai! Kai!! Kai!!!,to Allah ya kyauta🤔🤔🤔).
Haka duk wunin ranar jikinta a sanyaye yake,abinci ma sai da Maman Jummalo ta lallabata sannan ta samu taci shima kaɗan,duk tayi sukuku da ita kamar mai ciwo ko kuma ance wani shaƙiƙinta ya rasu haka take ji a jikinta.
@@@@@@
Bayan su Sa'eeda sun fito waje sai ta dubi Ummanta tace
"Ummina kinga ikon Allah ko"
"Haka ne sanyin idaniyata,tabbas wannan ikon Allah ne ba na mutum ba,amma a gaskiya nayi mamakin sauyawan Abbanki lokaci guda haka"
"Nima haka Ummina,Allah shi ne abin godiya"
"Haka ne kuwa Allah shi ne abin godiya, don ba yin mu bane,nufin Allah ne"
"Hakane Ummina,kinga kuɗin nan da ya bani saina ƙara kuɗin mota sannan zanyi sadakar naira dubu ɗaya wa almajirai ko ya kika ce Ummina"
"Wannan haka yake,Allah dai ya cigaba da maido da hankalinsa gare mu"
"Aameen Aameen Ummina"
Haka suka cigaba da hira har kowa ya nufi hanyarsa.
@@@@@@@@
Cigarta aji keda wuya saiga Maryam itama ta shigo,murmushi Sa'eeda ta sakarma Maryam sai itama ta maido mata da ɗan murmushi wanda bai kai zuciya ba, babu yabo babu fallasa a fuskar Maryam ta gaida Sa'eeda don yanzu Maryam ta fara jan baya baya da Sa'eeda dalilin samun ƙawaye ƴan gayu masu ji da kuɗi tare da class da tayi.
Yanzu ko karatun da Sa'eeda ta ke koyama Maryam ta daina saboda yanxu Maryam bata ce mata ta koya mata karatu,kusan yanzu Maryam hankalinta yafi karkata ga ƙawaye da gayu,sun haɗe kai su biyar wanda har suka sama group ɗinsu suna da (high classic babes squad).Duk yaran masu kuɗi ne sosai,asha wanka iya wanka sannan a ratayo fashion bags ana yanga amma brain ɗin empty😁😁😁.
Akwai lokacin da Sa'eeda ta taɓa samun Maryam da magana akan ko ta mata laifi ne yanzu take jan baya baya da ita,sannan yanzu kuma bata son suna tafiya gida tare,babu komai Maryam ta iya ce ma Sa'eeda kawai yanzu bata da ra'ayin tafiya gida tare da ita ne,shi kenan Sa'eeda ta ce da Maryam ta wuce abinta,tun daga ranar bata sake yiwa Maryam magana ko kuma ta ce su tafi gida tare ba, saidai idan ta ganta tayi mata murmushi sai ita ma Maryam ɗin ta maida mata.
Karatunsu ya fara zafi yanzu kuma suna gab da fara first semester exams ɗin na 200L,gashi Vice Chancellor ya ce continous semeter zasuyi babu hutu,shi yasa lecturers suke zafafa musu da karatu babu ji babu gani saboda lecterers ɗin suna so su kammala lectures ɗinsu complete kafin a fara exams.Wannan kenan.
A haka a haka har lokacin exams ɗinsu yayi suka rubuta exams dinsu cikin nasara da aminci musamman Sa'eeda da take karatu babu kama hannu yaro.
Suna kammala exams ranar Friday suka fara karatun second semester 200 level ranar Monday duk da ba duka ɗaliban suka zo ba kasancewar basu daɗe da kammala exams ba amma lecterers suka ɗaura sabon babi a karatun nasu.
@@@@@@@@@@@@
Ɓangaren Sa'eeda da Sauban baza muce komai ba don suna soyayya sosai,Sa'eeda har ji take anya zata iya auran wani inba Sauban ba,zata iya zama ta rayu da wani wanda ba Sauban, a kullun wutar soyayyar Sauban a cikin zuciyar Sa'eeda ƙare ruruwa take.Sauban yana nuna mata tafi kowacce mace daraja a idonsa kuma ita kaɗai ce a cikin zuciyarsa.
Sauban yanzu ya gama gane Sa'eeda ta mutu a so da ƙaunarsa sosai,don wani lokaci idan bai kirata a waya ba ita take kiransa taji lafiya kuwa,hakan na mugun yima Sauban daɗi a rai don yanzu haƙarshi ta cimma ruwa.
Wanene Sauban?
****Sauban Muhammad Ja'afar Ƙaraye shi ne asalin cikakkyan sunansa,wanda shi ne ɗa na uku a familinsu,su biyar ne mahaifiyarsu ta haiha,yana da ƙanne biyu mata tare da yayyi biyu duk maza,mahaifinsu asalin ɗan ƙauyen ƙaraye ne a jihar Kano,ita kuma mahaifiyarsu ƴar Zaria ce a jihar Kaduna.
Muhammad Ja'afar Ƙaraye cikakkyan ɗan kasuwa ne amma baiyi karatun boko ba kasancewar a ƙauye ya taso,a lokacin da yake ɗan 20 ya fara zuwa ci rani a kaduna,yana saro kaya a Kano ya kawosu Kaduna ya saida har Allah ya mai jagora a kasuwancin nasa ya zamo mai kuɗi sosai,a Kaduna ne yaga mahaifiyarsu Sauban lokacin tazo ita da yayarta mace kasuwar bacci siyayya wanda a lokacin sunzo biki tufun wada ne, a nan ya ganta har Allah ya ƙaddara ya aureta.
Allah ya azurtasu da ƴaƴa har biyar,da yake mahaifinsu Sauban yanada sha'awar karatun boko kasancewar shi baiyi karatun boko ba sai dai karatun Allo yasa ya bada himma da ƙwazon ganin yaransa sun tashi cikin karatun boko da na islamiya.
Babu laifa daga mazan har matan sun samu karatu daidai gwargwado duk da matan su biyu da yayyinsa maza ma duk sunyi aure shi kaɗai ne ya rage baiyi ba.Mahaifiyar Sauban ita kaɗai ce a wurin mahaifinsu Sauban.Allah yama mahaifinsu Sauban rasuwa a shekarar da ta gabata wato shekara ɗaya ke nan.Wannan shi ne taƙaitaccan tarihin Sauban Muhammad Ja'afar Ƙaraye.****
@ @@@@@@
Ɓangarensu Umma Kande kamar yadda Maman Jummalo ta bada shawarar suje ranar lahadi haka ko akayi,da sassafe suka buga sammako zuwa wurin boka Sankeru.
Isarsu keda wuya suka ga mata dayawa na layi a wurin bukkar boka Sankeru,mamaki da al'ajab ya cikasu har da riƙe baki,lallai boka Sankeru ya fara shahar sduba da yadda suka bugo sammako har sun tarar da layi ba kamar da ba da zaku shige direct.
Haka suka jira har layi yazo kansu,Umma Kande ce ta shiga kasancewar ita Mamam Jummalo rakiya tayo,tana shiga kamar yadda suka saba ta mishi kirayi tare da ƙasƙantar da kanta garesa(Wa'iyazubillah,Allah kasa mufi ƙarfin zukatanmu baki ɗaya😞😞😞).
Bayyanarsa keda wuya ya tintsire da wata mahaukaciyar dariya yana bubbuga ƙafa tare da nunata da yatsa yana ƙara tintsirar dariyarsa.Ita dai Umma Kande kanta a ƙasa.(ummm su Umma Kande masu ladabin ɗan tsako😂😂😂🙃).
Saida yayi mai isarsa kana ya tsagaita yana dubanta tare da cewa
"Yanzu tafi ƙarfinki Umma Kande!!! Tafi ƙarfinki!!! Saidai kiyi haƙuri"
A razane Umma Kande ta ɗago kanta tare datakai dubanta ga boka Sankeru sai kuma ta fashewa da kuka tana roƙo da magiya akan ya taimaketa kar asirinta ya tonu saboda tasan mijinta yafi son Umman Sa'eeda akanta bayan haka danginsa da batason su raɓesa yanzu zasu dinga zuminci sosai daga ƙarshe zasu maidata saniyar ware ita da ƴaƴanta,haka taita roƙonsa tana kuka sao kace wata yarinya.
"Naji! Naji!! Najiiiii !!! "
Sai kuma yayi shiru na tsawan wasu mintuna,Umma Kande har ta zaci bazai sake magana ba,sai kuma taji ya fara magana cikin amon muryar nan nasa mai sauti tare da firgitarwa.
"Akwai sharaɗi mai girma Umma Kande!!! Sharaɗi babba Umma Kande!!! Sharaɗin shi ne,zamu baki kwalba wanda ruhinsa ke aciki,sannan karki sake!!! Karki kibari!!! Karki yarda !!! A hir ɗinki !!! Kibari kwalbar nan ta fashe!!! Idan kuma ba haka ba....................
Pages ɗin yau babu yawa kasancewar banda caji a wayana,in shaa Allah pages na gaba zai kasance🔥🔥🔥
Ku cigaba da kasance da alkalamin Narrnarhh Bukar✍️✍️✍️ zaku nishaɗantu tare da ilmantuwa harda ma wa'azantuwa In shaa Allah🤗🤗🤗🙃🙃🙃💝💝💝💝
***Anya babu wani dalilin da yasa Maryam ta sauya Sa'eeda kuwa bancin ƙawaye???
****Shin bakwa tunanin soyayyar da Sa'eeda takewa Sauban baiyi yawa ba,karfa a samu matsala fa???
****Mai kuke tunani akan kwalbar da boka Sankeru yake da niyyar bawa Umma Kande??? Sannan mai yasa yace karta bari kwalbar ta fashe??? Shin wai idan ta fashe mai kuke tunani????
Ku cigaba da kasance dani taku har kullum Narrnarhh Bukar🤗🙃🌹💝 domin tafiyar tamu ta dabance🙃🙃🙃 na tabbata zaku ilmantu sosai tare da nishaɗantuwa in shaa Allah🤗🤗🤗 kudai ku cigaba da zubomin ruwan comments🤗🤗🙃🙃🙃 ni kuma bazan gaji da suburbuɗo muku da sababbin updates a kullum ba wanda zaku wa'azantu sosai da sosai🤗🤗🤗🤗💝💝💝💝💝💖💖💖💖🏵️🏵️🏵️🏵️🏵️🌹🌹🌹🌹🌹
Ina Kaunarku da yawa da yawa my Esteem Fans Allah ya barmu tare har a jannatul firdausi💖💖💖💖🏵️🏵️🏵️🏵️🌹🌹🌹🤗🤗🤗🤗🙃🙃🙃
Ina yinku over my Esteem Fans🤗🤗🤗🤗🌹🌹🌹🌹🏵️🏵️🏵️🏵️💗💗💗🌼🌼🌼
Daga alƙalamin
🖍️📚Narrnarhh Bukar 📚🖍️
Comments and share 🙏🙏🙏Fisabilillah.
[4/25, 1:38 PM] +234 814 129 2044: 🏵️ NACINA YAJAWOMIN🏵️
Narrnarhh Bukar✍️
🌹Perfect Essential Writer's
Association🌹
✨ P. E. W. A✨
Wattpad:@AISHAABUBAKAR812
Arewabook:@Narrnarhh002
Masu telegram zaku iya following ɗina ta wannan link ɗin🤗,🙃🏵️👇👇👇
https://t.me/+439Pdx2UbLZlOTNk
🌹Special greetings to y'll my Esteem Fans, ina kaunarku over,ina alfahari daku domin da bazarku nake taka rawata🙃🙃🙃💖💖💖💖💝
23----24
Sai kuma yayi shiru na tsawan wasu mintuna,Umma Kande har ta zaci bazai sake magana ba,sai kuma taji ya fara magana cikin amon murya mai sauti tare da firgitarwa.
"Akwai sharaɗi mai girma Umma Kande!!! Sharaɗi babba Umma Kande!!! Sharaɗin shi ne,zamu baki kwalba wanda ruhinsa ke aciki,sannan karki sake!!! Karki kibari!!! Karki yarda !!! A hir ɗinki !!! Kibari kwalbar nan ta fashe!!! Idan kuma ba haka ba asirin zai karye kuma zaki kuka da kanki Umma Kande!!! Tabbas zaki kuka da kanki!!! Sannan muma zai shafe mu, don haka dole ki kula !!! Dole ne ki kula !!! Ki kula da kwalbar kamar ruhinki Umma Kande!!! Idan ba haka ba komai naki zai rushe!!! Komai zai taɓarɓare miki Umma Kande!!! "
Bayan ya gama faɗin sharaɗinsa sai kuma ya ɗaga hannunsa na hagu sama yana a tsayan tare da yin wasu surkulle,yana cikin yin surkullen ne sai wata guguwa mai ƙarfin gaske da taso,duka bishiyoyin nan da suke zagaye da bukkar sai karkaɗawa suke,gayyayakin suna kakkaɓa,kamar za'ayi ruwan sama,tabbas wannan asirin mai girma ne ba irin kowani asiri da boka Sankeru yake basu bane,Maman Jummalo da take a zaune a wajen wata bishiya saida da tsorata matuƙa ainun,ganin yadda lokaci guda guguwa ta taso gashi yanzu ba lokacin damuna bane balle ace ruwan sama ne zai sauka,haƙiƙa da tsorata harda ma sauran matan da suke kan layi saida suka tsorata wasunsu ma harda ƙankame juna saboda firgici da ya shigesu lokaci guda.
A cikin bukkar kuma bayan ya gama surkullensa sai kuma guguwar ta tsaya cak kamar daukewar ruwan sama,bishiyun suma suka daina rangaji,haba kamar walƙiya sai ga wata kwalba matsakaiciya ta bayyana a hannunsa sannan ya miƙa ma Umma Kande tare da cilla mata hararar gargaɗi,a natse kamar ƙwai ya fashe ma Umma Kande ta miƙa hannayanta bibbiyu tare da russunawa cike da girmamawa ta amsa kwalbar jin gargaɗi haɗe da kashe din da aka mata akan kwalbar,a zuciyarta take ayyana dole ta kiyaye wannan kwalbar kamar ranta.
Bayan ta amsa kwalbar sai ta cire ɗankwalinta tare da nannaɗe kwalbar sosai kasancewar ɗankwalin nata mai girma ne sosai sannan ta lallaɓa a hankalin kamar ƙwai tasa kwalbar a cikin jakarta cike da kulawa kana ta kulle jakarta ta.
Boka Sankeru ne ya ƙara da cewa bayan ta saka kwalbar a jakarta.
"Wannan sihirin na daban ne Umma Kande!!! Ba kowa muke bamawa ba sai wanda yayi tsawan lokaci yana mana biyayya tare da bin dokokin mu haɗe da sharudɗanmu,haƙiƙa kinyi tsawan lokaci kina bin dokokinmu tare da sharudɗan mu,shiyasa muka baki,don haka ki kula!!! Ki kula Umma Kande!!! Sihirin nan ba irin wanda kika saba sani bane,dole ki kula kar asamu matsala!!! Don muma zai shafemu idan aka samu matsala Umma Kande!!! "
Cikin rawar murya Umma Kande ta fara magana saboda tsoro da firgicin da ya shigeta tun lokacin da guguwan nan ta taso har zuwa yanzu da ta ƙara jin kashedi tare da gargaɗi akan kwalbar.
"Zzzan kula shugabanmu,mai sha re kukanmu,ba.. ba.. bbaza a masu matsala da yardarka "(wa'iyazubillah,shirka!!! Shirka,ke duniya ina zaki damu🤔🤔🤔,Allah shi kyauta)
"Da yafi miki!!! Ko kuma kiyi da nasani mara adadi Umma Kande!!! "
Kamar yanda boka Sankeru ya saba kasancewa da Umma Kande yau ma hakan ta kasance,sai daga baya Umma Kande ta fito waje tana tafiya a hankali kamar ƙwai ya fashe mata a ciki sannan ta nufa inda Maman Jummalo take.Zaune ta sameta wurin wata bishiya tana shan iska,miƙewa tayi da sauri tare da tambayarta ya ta ƙare da boka Sankeru sannan mai ya haddasa guguwa.
Shiru tayi tana dubanta idanunta duk sun shige ciki kamar wata mars lafiya, har wata ƴar rama tayi,cikin murya mai sanyi ta fara magana.
"Dole na kula ƙawas,dole na kula da kwalbar nan ko kuma in shiga uku"
"Wace kwalba kuma"
"Kwalba boka Sankeru ya bani tare da min gargaɗi mai tsauri akan karna kuskura na bari kwalbar ta fashe saboda ruhin baban Nusaiba na a cikin wannan kwalbar,idan kuma nabari ta fashe shikenan komai nawa zai taɓarɓare"
Tare da nuna mata jakar a hankali sannan ta cigaba da cewa
"Yanzu ƙawas wani irin mugun ɓoyo kike tunanin zanyi ma kwalbar nan don wallahi na shiga ruɗu haɗe da tsoro Maman jummalo? "
Maman Jummalo shiru tayi tana nazari tare da tunanin yanda za'a ɓoye kwalbar ta yadda babu abinda zai sameta,bayan ta gama tunani sannan ta ce
" Mai zai hana tunda yanzu baki da yara duk sunyi aure,ki ɗau kwalbar kisata cikin akwati ƙarami saiki saka a ƙarƙashin gadonki,koya kike ce ƙawas? "
"Haka za'ayi kuwa ƙawas,yanzu dai mu wuce gida ma kammala zancen a can kar a samu matsala don ni tsoro nakeji "
"Haba ƙawas kin cika tsoro wallahi,kidai kula da kwalbar sosai"
Haka suka doshi hanyar garinsu wanda basu suka iso gida sai wajan magrib kasancewar layin da suka bi wurin ganin boka Sankeru wanda a da babu layi saidai kawai ka shiga yanzu saida tabi layin kafin ta samu shiga ciki.
Kamar yadda Maman Jummalo ta bawa Umma Kande shawara akan tasa kwalbar a cikin ƙaramin akwati sannan tasa a ƙasan gadonta haka tayi.Kuma tun daga wannan lokacin kuma a ranar Abban Sa'eeda ya ƙara rikicewa tare da juyawa su Umman Sa'eeda baya haɗi da musguna musu sosai.
Tun a ranar da Umma Kande tazo da kwalbar gidan,abubuwa suka ƙara rincaɓewa,don saida ya kusa dukan Sa'eeda ba tare da tamishi laifi ba,kuma abinda ma baita taba yi ba a baya,yana faɗa tare da zage-zagen da babu dalili haka nan daga shigowarsa gidan kaar yaji a duniya ya tsani ya buɗe ido yaga su Umman Sa'eeda tare da ita Sa'eeda,ji yake kamar ya koresu daga gidan ko zuciyarsa zatayi sanyi.
Ranar Umman Sa'eeda da Sa'eeda sunyi kuka iya kuka a ɗaki babu mai basu haƙuri ko tausaya musu,abinda bai taɓa musu ba a baya duk da a lokacin hankalinsa ba a kansu yake amma bai taɓa musu irin cin mutunci da wulaƙanci kamar na wannan ranar ba.
Umma Kande da Maman Jummalo daɗi kamar ya kashesu saboda abin baita taɓa yima su Umman Sa'eeda ba yau yayi musu wato wulaƙantasu,ita Umma Kande wallahi taso a ce ya kore su Umman Sa'eeda daga gidan,shikenan sun yada ƙwallan mangoro su huta da ƙuda.(Kai kai kai wannan baƙin kishi haka,Allah karka bamu irin wannan zuciyar mai baƙin kishi da hassada🤔🤔🤔)
@@@@@@@@@@
Wai ina amare?
Bangaren Jummalo tun sanda aka kaita gidan mijinta ta soma cin karo da ƙunci haɗe da baƙin ciki tun a daran farkonta.Kamar yadda a al'adar malam bahaushe take,a duk sanda aka kai budurwa ko bazawara ɗakin mijinta,Ango yana zuwa da kaza tare da drinks don raya daren cikin farin ciki da annashuwa tare da amaryarsa.
Amma Jummalo bata samu wannan farin ciki ba saidai ma Angon ya shigo mata ɗaki a bige,ya sha giya yayi tatil sai sumbatu yake tare da jayo duk abinda ya gani ya bugashi a ƙasa yana surutai marasa ma'ana,ita kuma lokacin tana kan gado an lullubeta da mayafi babba,jin surutai da jefe jefen kaya ya sata tayi saurin fitowa daga bedroom ɗin a firgice haɗi da tsoro,fitowarta falo taga abinda ya kusa zautar mata da ƙwaƙwalwa tare da birkita mata lissafi,wai yau da zai kasance ranar farin cikinta,ranar da take so da ganin Allah ya kaita lokacin amma sai yaza mata a matsayin ranar baƙin ciki mara misaltuwa,ace angonta yazo mata ɗaki a bige,wannan wani irin ƙaddara ne,wani irin tashin hankali ne haka.Jin motsi Ibrahim angon nata yayi saurin duban wajan,haba kamar an tsikareshi ya nufota gadan-gadan yana huci kamar wani kurcin maciji tare da ɗaukar abu a hannunsa saikace yaga abokin hamayyarsa.
"Bbbanna kiraki tun ɗazo ba,amma sai yanzu kkkika ga ddammann zuwa ehe!!! Sssaboda ni ni ɗanki ne ko!!! Kkkaruwa,shegiya mayyar mmmaza kawai"
Jummalo da take tsakanin falo da bedroom tayi saurin juyawa tare da rugawa toilet a guje haɗe da saka key,ganin akwai abu a hannunsa kuma kanta yawo tare da surutai wanda bama fahimtar me yake cewa take ba.Kamar kuwa ta sani kanta yayo,tsayawa wurin ƙofar toilet ɗin yayi tare da bubbugawa haɗi da faɗin
"Ki buɗe na ce!!!,madara da kaza zan baki,ki buɗe! Ki buɗe mmana Jummalota,tawan taaawan...."
Bai ƙarasa da zancan ba ya fara kwararo amai babu ƙakƙautawa,mai uban wari da ɗoyi sai kace mushe.Jummalo dake a toilet ta fashe da matsanancin kuka a ranta tana faɗin 'Yanzu a daren farkona a ɗakin mijina nake fuskantar wannan baƙin cikin,meyasa na biyewa mamata ne da Umma Kande akan saina aure mai kuɗi kaicona ni Jummalo,gashi tun kan aje ko'ina,a daren farkona na fara fuskantar bacin rai da damuwa,kaicona da biyewa mamana akan dole saina aura mai kuɗi,gashi yanxu na aura mai kuɗin amma babu kwanciyar hankali tana zancen zuci a lokaci guda tana kuka.(Hausawa suka ce kwaɗayi mabuɗin wahala😁😁😁,gashi tun a daren farkonki kin fara fuskantar baƙin ciki,Allah ka tsare mana imaninmu 🤔🤔🤔)
Shiru taji ɗakin yayi,a tunaninta ko yafita ne,a hankali da buɗe toilet ɗin,ta fito da sanɗa,taka ƙafar da zatayi a ƙasa sai taji ƙafarta ta tako wani abu mai yauƙi yauƙi,da sauri ta ɗaga ƙafarta haɗi da duba wajen,ai ba arziƙi ta toshe hancinta da mayafinta jin wani wari ya taso kamar mushe tare da duban mijin nata a gefe yana ta sharɓar baccinsa hankalinsa kwance,ko'ina na wurin ƙofar toilet ɗin duk ya ɓaci da amai,da sauri da yaye mayafin nata tare da cillashi kan gado sannan ta koma toilet ɗin,ruwa ta zubo a bucket saita saka dettol haɗe da omo sannan ta ɗauko mopper ta fito.
Tana kuka tana mopping ɗin aman,saida ta goge wurin tsaf sannan ta saka air freshner a ɗakin lungu da sako sannan ta cire kayanta ta saka na bacci tayi kwanciyarta haɗe ta tunani iri iri wanda ya sata kasa bacci da wuri,sai wajan 2:12am bacci ɓarawo yayi awan gaba da ita.
Da safe kuma ita ta rigashi farkawa,still yana nan a wurin yana bacci abinsa,ɗauro alwala tayi don yin sallar Subhi duk da gari yayi haske tar haka tayi sallarta kasancewar ko a gida sai wurin 9:00am suke yin sallar subhi wani lokacin ma bayi suke ba harda iyayen nasu.
Sai wurin 10:39am ya farka haɗe da miƙa babu salati babu adduar tashi daga bacci ya wuce toilet direct, wanka yayi sannan ya fito yasa kaya,a lokacin da yake saka kaya ne Jummalo ta shigo cikin bedroom ɗin tare da sallama,amsawa yayi babu yabo babu fallasa.Wuri ta samu a gefan gado ta zauna,saida ya kammala shirinsa tsaf sannan ta dubeshi hade da yi mishi maganar abinda ya faru jiya da daddare,har complain din rashin kawo mata kazar amarci da yayi duk saida ta fadama masa.
Tunda ta fara magana yake kallonta sheƙeƙe,a ransa yana faɗin 'Wai mai wannan yarinyar take dashi a jiki ne da ya sakani nace dole saina aureta,ko fasali bata dashi,mtwsss' saida ta kammala ƙofarinta sannan ya fara magana cike da izgilanci.
"Ke! Ni sa'arki ne da zaki dinga min magana irin haka,to indai shan giya ne kike ma wannan ƙorafin to yanzu na fara ke banda ma shan giya har ƴan mata inna gadama zan kawosu gidan nan muyi yadda mukeso babu abinda zaki iya saboda gidana ne inada iko dashi,don haka karki sake min magana akan shan giya na,is my choice so you can't change me,ok"
Shiru tayi a zuciya tana faɗin 'Ni Jummalo na ɗebo ruwan dafa kaina da kaina.
Haka dai rayuwar Jummalo ta cigaba da tafiya a gidan mijinta duk da bata taɓa faɗawa mamanta ba don kar hankalinta ya tashi,gashi ko nan da can ya hanata fita,kullum cikin ɗibo ƴan matansa yake kala kala,kuma buba abinda ta isa tayi.Duk da bai hana ci da sha amma fa wani lokacin har duka yake mata idan ƴan iskan nasa suka motsa.Wanan kenan.
@@@@@@@@@@@@
Ɓangaren Zaliha kuwa sai dai in ce gwara Jummalo so dubu akan nata zaman auran.A sanda aka kaita gidan mijinta bayan kowa ya wuce,angon ya shigo ɗakin nata babu sallama lokacin ita ma kamar Jummalo an lulluɓeta da mayafi,zama yayi kusa da ita baice mata komai ba,can sai taji abu na mata waiwayi a jiki,da sauri ta yaye mayafin nata takai duba gun inda abun yake.
Wani irin ihu ta saki tare da ƙanƙame mijin nata tana tura fuskarta cikin ƙirjinsa duk ilahirin jiki yana rawa,shi kuma mijin nata kunnanta ya lalubo ya fara magana.
"Ɗayan mijin naki kike gudu ummmm Zaliha,shima yazo angonci ne haɗe da kazarsa"
A razane ta ɗago kanta tare da fashewa da matsanancin kuka, tana kukan ta fara magana
"Na shiga uku ni Zaliha!!! Wayyo ni!!! Wayyo ni!!! Don Allah ka fitarmin dashi,wallahi ina matuƙar tsoransa,na roƙeka da Allah"
"Mijin naki kike tsoro kuma"
"Don Allah ka cireminshi daga kan gadon nan"
Ƙara ƙanƙameshi take tare da runtse idanunta da ƙarfi
"Wallahi babu inda zaije Zaliha,kamar yanda kowani ango yake angoncewa a daren farkonsa tare da amaryarsa to haka shima zai angon ce dake"
"Niii!!! Kana nufin da...................
Mu haɗu a pages na gaba My Esteem Fans,domin tafiyar ta fara ɗaukar🔥🔥🔥🤗🤗🤗🙃🙃🙃🏵️🏵️🏵️🌹🌹🌹💝💝💝💖💖💖
****Hmmmmm🤔🤔🤔,ita kuwa Zaliha da wani abu ne zata angon ce haka gashi tana tsoransa??? Dama maza biyu ne ta aure ba ɗaya ba??? kai kai kai gaskiya da alama ita ma ta ɗebo ruwan dafa kanta da kanta😁😁🙃🙃🏵️.
***Shin a tunaninku Umma Kande tayi kyakkyawan ajiya ga kwalbar da boka Sankeru yabata kuwa???
Ku biyoni don jin amsoshinku a pages masu zuwa🔥🔥🔥
Ina matuƙar alfahari daku My Esteem Fans,taku har kullum Narrnarhh Bukar✍️✍️✍️ 🤗🤗🤗
Ku cigaba da zubo ruwan comments🤗🤗🤗🤗🤗🌹🌹🌹🌹🏵️🏵️ni kuma bazan gaji ba wurin sambaɗo muku new updates wanda zai nishaɗantar daku tare da fadakar daku haɗi da wa'azantar daku🤗🤗🤗🤗🙃🙃🙃🏵️🏵️🏵️🌹🌹🌹🔥🔥🔥
I love y'll My Esteem special fans,ina alfarahi daku sosai,Allah yabar ƙauna 🤗🤗🙃🙃🙃🏵️🏵️🌹🌹🌹
Daga alƙalamin
🖍️📚Narrnarhh Bukar 📚🖍️
Comments and share 🙏🙏🙏Fisabilillah.
[4/25, 1:38 PM] +234 814 129 2044: 🏵️ NACINA YAJAWOMIN🏵️
Narrnarhh Bukar✍️
🌹Perfect Essential Writer's
Association🌹
✨ P. E. W. A✨
Wattpad:@AISHAABUBAKAR812
Arewabook:@Narrnarhh002
Masu telegram zaku iya following ɗina ta wannan link ɗin🤗,🙃🏵️👇👇👇
https://t.me/+439Pdx2UbLZlOTNk
25----26
"Wallahi babu inda zaije,kamar yanda kowani ango yake angoncewa a daren farkonsa to haka shima zaiyi dake"
"Kana nufin da wannan ƙasurgumin macijin zan angon ce dashi yau ba dakai ba? "
"Sosai ma kuwa,ai daman shi naje nema ma auran bani ba,ko kin zaci ni ne angon?"
"Innalillahi Wa'inna ilaihi Raji'un,na shiga uku na lalace ni Zaliha,Don Allah kace wasa kakeyi ba da gaske ba,kace mafarki nake ba'a zahiri ba,na roƙeka da Allah Ubangijin halittu kace wasa kakeyi,Shikenan ni Zaliha na kawo kaina ga halaka,wayyo Allah ni Zaliha!!! Wayyo Allah na!!! Na shiga uku na lalace!!! "
Kuka takeyi harda majina,ji take kamar a mafarki hakan take faruwa da ita,ina zata kai wannan ƙasurgumin macijin mai girman gaske,ita fa tunda take bata taɓa ganin maciji kamarsa ba.
"Wasa! Wasa!! Wasa!!! hhhhhhh!!!! Lallai ma yarinya,kinga na miki kama da mai tatsuniya ne,ko ko mai wasan kwaikwayo ne ehhh!!! "
"Na shiga uku ni Zaliha na lalace,wayyo mamana Don Allah ka rufamin asiri kace wasa ne"
"Ke!!! Baki shiga uku ba yanzu zaki shiga uku yarinya kuma dole sai ya lashi gabanki kullum,sannan kisani babu ke babu fita a gidan nan,kin riga da kin shigo,don irin ku nake nema ruwa ijallo,sai gashi na haɗu dake,sannan an tabbatarmin kece sauran cikon ɗaukaka tare da arziƙin da ya rage nayi,na aure mata ɗaiɗai har 29,saura ɗaya su cika 30 kamar yadda dodona ya bayyanamin saura ɗaya,shiyasa farkon ganinki da nayi dodona ya tabbatarmin da kece cikon na 30 ɗin,sannan kisa a ranki mutuwarki tazo kuma a ƙasƙan ce domin bazaki taɓa kuɓuta daga hannuna ba,son kuɗi da dogon burinki zai zamo ajalinki Zaliha!!! Hhhhhhhhhhhhhhhhh!!!"
Kamar a marfarki Zaliha take jin wannan zancen,maganar zuci ta fara 'yau ita ce da wannan ƙaddarar aurar ɗan mafiya kai bama ɗan mafiya ba mai aiki da dodo ,mamana da maman Jummalo sun ja min wahala,kaicona ni Zaliha,kaicona da biyewa ruɗin duniya mai ƙarewa,garin kwaɗayina da son abin duniya na jefa kaina ga halaka,na rasu ni Zaliha,na mutu na lalace,daman ance kwaɗayi mabuɗin wahala yau gashi ya tabbata a kaina,wayyo wayoo' tana cikin wannan zancen zucin ya katseta da cewa
"Kashe dinki Zaliha! Idan naji daidai da rana ɗaya kin sanar ma wani ko iyayanki ne akan wannan mijin naki to ki tabbata a ranar mutuwa ki tazo kenan,kuma dole ya lashi gabanki ko kinƙi ko kinso,tunda auran kuɗi kikayi,kuma gashi kin masu kuɗin ,iyayenki ma sun samu musamman mamarki mai kama da dumɓaru,shegiya mayyar kuɗi,kunci kuɗina kuma dole in samu abinda nakeso wurinki Zaliha! Hhhhhhhh!!!"
"Na haƙura da auran,ka sakeni don Allah,wallahi na haƙura da auran kuma zamu maido maka da kuɗinka Allah,ka yarda dani zamu maido maka komai kuma koda tsinke ne wallahi"
Hannu bibbiyu take haɗawa tana roƙonsa haɗe da magiyar ya saketa ta haƙura da auran,ga hawaye sun kasa tsayawa a idonta,idanunta har sun fara kumbura kasancewar tanada manyan idanu,gashi fuskarta tayi ja sosai saboda kukan da tayi,bleaching ne iya bleaching dole fuska tayi kamar jan ƙosai.(Da sauranki Zaliha badai kuɗi kikeso ba ai gashi nan ki ɗiba iya ɗibarki amma zakici ubanki lakada awaje wallahi😂😂😂).
Dariya ya tintsire dashi harda bubbuga ƙafa,shi kuma kumurcin macijin ya nannaɗe kamar kwando sai kuma ya miƙar da kansa yana fitar da harshensa waje tare da huci,baƙi ne macijin sosai gashi yana da tsawo da kauri kai in taƙaice muku zan iya cewa Anaconda ne saboda girmansa da tsayinsa,kansa babba ne sosai.Sai da yayi dariya mai isarsa kana ya tsagaita tare da dubanta,ita ko jikinta sai rawa yake ga gumi sai ƙara tsuttsubo mata yake a duk ilahirin jikinta.
"Kin makaro yarinya wallahi,kefa da kanki kikace zaki aure ni,kina sona har na biya kuɗin sadakinki dubu ɗari lakadan ba ajalan ba,nayi lefe,sannan a daran farkonki dan na kawo miki angonki tare da kazar amarcinki gasassa sai kice kin fasa auran ai wannan zancen ƙanzon kurege ne ƴan mata,kidai sake tunani Zaliha"
Macijin ya wani fasa kai tare da kai fuskarsa wurin fuskar Zaliha yana kallonta ita kuwa mai zatayi inba sumews ba,a haka mijin nata ya tuɓe ta sannan wannan macijin yayi yanda ya keso da ita.
*TUNATARWA*
****Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un,yake ƴar uwata mai dajara tare da ƙima shin bakya tunani akwai mata dayawa masu shiga irin wannan bala'i kamar yanda Zaliha ta shiga duk saboda son abin duniya,idan a inda kike babu amma kisani a wasu wuraran akwai su da dama.Akwai maza masu kuɗi wanda ba na halal bane,sun sameshi ne ta hanyar haram,kodai ta hanyar sata,ko kidnapping,ko safaran miyagun ƙwayoyi,ko ta hanyar tsafi da shan jini da dai sauransu,sannan irin wa'innan mazajen suna sakarwa mata kuɗi sosai ta yadda zasu ja hankalinsu dana iyayensu wadda a ƙarshe wahala ce zasu shiga.
Kaicon wasu mata masu kwaɗayi da son abin duniya,wallahi musulinci yayi a rayuwa, ki duba ƴar uwata mai dajara hadisin manzon Allah (S.A.W) daya ce''Ana auran mace don abubuwa guda hudu ne,don addininta,arziƙinta,nasabarta,kyawunta amma duk a cikin abubuwan babu abinda ya bada shawara abi illa addini,ya cigaba da cewa "ina baku shawara da ku aure mace mai addini''. Kisani ƴar uwata mai daraja hadisin nan ba ga mata kawai ya tsaya ba a'a harda maza suma hadisin ya shafesu,don auran namiji mai addini amma mara dukiya yafi kwanciyar hankali akan auran namiji mai dukiya amma babu kwanciyar hankali.Allah ya tsare mana imaninmu,ya bamu wadatar zuci ya kuma bamu ikon yin daidai a rayuwarmu****
Cikin Labari
Zaliha ba ita ta farka ba sai wurin 10:02am,a hankali ta buɗe kumburarrun idanunta,da ƙyar ta tashi ta zauna sai ta duba jikinta taga babu kaya,tuno da abinda ya faru jiya da daddare yasa ta fara russan kuka babu ji babu gani,tana da nasanin auran kuɗi,gashi ya mata kashe din karta kuskura da faɗawa wani koda iyayenta ne, tayi da nasanin biyewa mamanta da maman Jummalo akan auran mai kuɗi gashi yanzu tana cikin masifa tare da tashin hankali wanda tasan yanzu zamanta a gidan ya fara.
A sanyaye ta tashi duk jikinta na mata ciwo musamman gabanta,ji take kamar tayi tsarki da barkono saboda zafin da yake mata.Wanka ta shiga tare da gasa jikinka,tana yi tana kuka wannan wace irin musiba ce ta sameta, wace irin ƙaddara ce haka,Allah sarki Sa'eeda haƙiƙa tayi dacen uwa ta gari ba mai son abin duniya irin na mamanta ,gashi yanzu ta biyewa mamata ta aura ɗan mafiya mai aiki da dodo,haka dai tana wanka tana tunanin zuci har ta kammala wankan ta fito,tana cikin shiri ne sai ga mijinta ya shigo babu sallama,sai ya samu wuri ya zauna tare da cewa.
"Amarya bakya laifi ko kin kace ɗan masu gida,to ya baƙunta ya kuma daran farkon naki ya kasance da jarumin angonki duk da ma sume masa kikayi,hhhhhhhhh!!! "
Bata ce dashi ko kanzil ba ta cigaba da abinda takeyi a zuciyarta tana tsine masa tare da adduar Allah ya fitar fa ita daga gidan ko ta naimi yafiyar Ummansu Sa'eeda tare da Sa'eeda domin tasan hakƙinsu ne ya fara bibiyarsu,surutansa ya gama ba tare da tace dashi komai ba ya fita abinsa.
Haka dai rayuwar Zaliha da cigaba da gudana a gidan mazajan nata guda biyu,wanda kullum sai wannan kumurcin macijin ya lashi gabanta tun tana sumewa har ta daina wanda yanzu idonta biyu yake lasar gaban nata babu yadda ta iya sai kuka,gashi yanzu gaban nata wani irin ruwa yake fitarwa mai ɗoyin gaske duk da gashin gabanta da take tare da fesa turare amma haka ruwan yake fita daga gabanta.
A duk sanda su ka yi waya da mamanta,idan ta ce mata akwai matsala saita ce da ita a'a,tuno da kashe din da ya mata akan karta kuskura ta sanarwa mutane,haka dai Zaliha ta cigaba da rayuwa a wannan gida cikin ƙunci da baƙin ciki duk da akwai kayan mo re rayuwa a gidan amma na banza a wurinta,ji take gwara ta aura talakan talaka wanda baida ko sisi akan wannan ƙaddararran auran da takeyi(Allah sarkin daɗi inji ɓarawon takanɗa,haba Zaliha yanzu kuma talakan kikeso,tab ai kin makaro😂😂😂😂😉🙃).
Gashi a gidan babu halin guduwa saboda matakan tsaron da suke a gidan masu tsauri ne,akwai sanda ta taɓa yunƙurin guduwa amma haƙarta ta kasa cimma ruwa saboda mai gadin gidan uban gidan nashi ya mishi kashe din kar ya bari ko nan da can ta fito,kuma haka a kayi,tun daga ranar bata sake yunƙurin guduwa ba saita haƙura tare da jiran ranar mutuwarta,Wannan kenan .
@@@@@@@@@@@@@@
Ɓangaren Iklima ita ma dai gidan auran nata sai a hankali,duk da mijinta ba mai shan giya bane, kuma sannan ba ɗan mafiya bane mai aiki da dodo amma fa mijin nata duk kanwar ja ce da na sauran ƴan uwan nata,saboda mijin nata cikakkyan ɗan luwaɗi ne wanda har ƙungiya suke dashi kuma yana ɗaya daga cikin ƴan ƙungiyar wa'inda suke faɗa aji.
Itama dai Iklima daren farkonta baizo mata da sauƙi ba,kasancewar angon nata ba ta hanyar daya dace ya nemi biyan buƙatarsa da ita ba,wanda hakan ya kawo musu saɓani sosai,kasancewar iklima akwai tsiwa yasata turo baki da cewa
"Mai kake nufi,a ta bayana zaka biya buƙatarka,babu kyau biyan buƙata a ta baya fa "
"To ni ina ruwana da rashin kyayunsa,kinga malama in kin gama wa'azin naki kizo don ni a matse nake"
" Tab,wallahi haramun ne,bazanyi ba"
"Haramun ɗin ubanki! Nace haramun ɗin uwarki! Shegiya mai suffar masu ciwon ƙanjamau,ke kike ganinsa haramun amma a wurina halas ne,don haka karki ɓatamin rai idan kuma ba haka ba kici na jaki don naga alama bakida kunya,to ni sanda ake rabon kunyar bana kusa,shegen kaina ne wallahi,kina ɓatamin lokaci" ranshi a ɓace yake maganar haɗe da zaƙuwa kasancewar yasha maganin ƙarin ƙarfi sosai.
"Yanzu mai iyayena suka maka da zaka sasu ciki ehh..."
Bata ƙarasa da maganar ba ta fara kuka har da shassheƙa,duk da iyayenta su suka ja mata wannan fitinar da bala'i,amma a ce saboda kafirci haɗe da yahudanci ya rasa inda zai nemeta sai a ta duburarta kuma a daren farkonta wannan wani irin musiba ne haka,bata ƙarasa zancen zucin da take yi ba taji an fijgota da ƙarfi.
"Wayyo Allah na,yau na mutu shikenan mamana zai kashe miki ni!!!"
"Duk wannan kururuwan da iface ifacen da kikeyi na banza ne domin babu mai cetonki a gidan nan,dama kin natsu na biki a hankali da yafi miki,amma tunda irin wannan salon kika zaɓa muje zuwa ɗan halak ka fasa "
Dambe suka fara yi,tana fizge fizge haɗe da tsugunli da cizonsa amma ƙyam kamar ba da mutum take ba,tayi iya ƙoƙarinta don ta ƙwaci kanta amma jikin mace da na namiji ba ɗaya bane haka yaci galaba akanta,kuma ya biya buƙatarsa da ita a ta duburarta,wanda tana kuka tana magiyar yayi haƙuri ya ƙyaleta babu kyau Allah ya haramta amma ina gogan naku yayi nisan kiwo.(Subhanallah,Allah ka tsare mana imaninmu baki ɗaya🤔🤔🤔)
Biji-biji yayima Iklima wanda ko motsin kirki ya gagareta saidai hawaye,shi kuma tunda ya biya buƙatarsa ya tashi daga kanta ya ma fita daga ɗakin ko kallon inda take baiyi balle tunanin taimaka mata, ya ƙara gaba abinsa.
Wuya tayi wuya,kuka kam Iklima tashashi kamar ba gobe, ( Fans karku manta fa Iklima auta ce ga Umma Kande kunga ko dole tayi taɓara,gashi anji maza😂😂😂).
Iklima da taga kuka ba shi ne mafita a gareta ba yanzu,miƙewa tayi da ƙyar tana dafe da bango har ta isa toilet ɗin sai ta haɗa ruwan zafi don gasa jikinta,a toilet ɗin ma kuka ta dinga yi tana masa Allah ya isa bazata yafewa ba har kabarinsa naci da wuta(Wayyo Allah na😂😂😂,gaskiya an taɓo autoci,wannan sangarta haka,kai kai kai😂😂😂🙃🙃🙃).
Kuka ta cigaba dayi har ta kammala gasa jikin nata sannan ta ƙara dafe bango ta fito zuwa stool ɗin da yake a gaban mirror,haka ta shirya cikin kaya marasa nauyi kasancewar kamar zata faɗi haka take ji,tayi wani fayau da ita.Saida akayi kwana uku batasa mijinta a ido ba,Allah yasa ma akwai kayan abinci a store ɗin shi ne sauƙin ta.
A washa garin ranar sai gashi ya shigo gidan har ɗakinta kamar abun arziƙi ya kirata tazo ga abokansa sunzo su gaisa har da sakar mata murmushi wanda baikai zuci ba,ita a tunaninta ƙila bazai ƙara yi mata abinda ya mata a kwanaki hudun da suka wuce ba.Hijab ta ɗauko zatasa yayi saurin riƙewa tare da cewa.
"Don Allah wani irin ƙauyanci ne haka zaki fita da ƙaton hijab sai ka ce matar liman"
Galala Iklima ta tsaya tana kallonshi,ko ya manta ne abokansa fa zataje gaisarwa kuma sai tafita daga ita sai ƴar yaloluwan riga wacca batakai gwiwaba,maido da ita yayi cikin hankalinta da cewa
"Look banason wannan halin naki,duk sanda abokaina zasu to banaso ki dinga saka hijab,kawai kizo a wadda kike,ok"
"To"
Shi ne amsar da ta iya bashi ta ta mike zata fita kitchen ɗauko musu ruwa shima wannan karon da sauri ya hanata abinda tayi niyyar ɗaukowa ya ce su tafi suna jiransu,haka suka isa falon a tare.
"Assalamu Alaikum"
Cikin murya mai sanyi tayi maganar tare da russunawa saidai kafin ta ƙarasa da maganarta taji wani yace
"Wow,gaskiya babe ɗinka ta haɗu wallahi"
Cikin abokansa wani ya faɗa,kuma babu wanda ya amsa mata sallama a cikinsu,idanunsu kyar akanta har ta soma jin wani iri da kallon da suke mata,data gaji da tsayuwa kuma babu mai magana a cikinsu saidai kallonta da sukeyi kamar sun samu television yasata shirin komawa bedroom sai kuma taji mijinta ya ce.
"Ina zaki kuma"
"Bedroom mana"
"Aka ce miki angama dake ne"
"Naga mun gaisa to me yayi saura "
"Wurinki suka zo ai"
Kallonshi tayi da mamaki,wai wurinta suka zo kuma shi ne suke mata irin wannan kallo haka kamar mayu,can kuma ta ce.
"To ai mun gaisa ko,shikenan ai,ko kuma in musu girki ne yanzu ba yanzu zasu tafi ba? "
"No karki takura kanki akan wani girki can,abinda ke a gareki ma ya wadatar dasu ". Shafa gemunsa yayi yana kallonta haɗe da yin wani munafikin murmushi, suma abokan nasu murmushi suke tayi suna kallonta.
Waro idanu tayi waje jin abinda ya furta wai abinda ke agareta ya wadatar dasu,me ke nan kuma,ƙara tambayarsa tayi
" Ni kuwa wani abu nake dashi da zai iya wadatar dasu banda abinci? "
"Sosai ma kuwa babe"
Wani daga cikin abokansa ne yayi maganar yana shafo sumar kansa haɗe da kashe mata ido ɗaya,ita fa a gaskiya bata gane wannan abun da yake agareta wanda zai wadatar dasu ba sannan kuma kallon da suke mata shima bata gane masa ba,ƙara tambayarsa tayi wanda amsar da ya bata yasata saurin dafe ƙirji haɗe da waro ido waje tana dubansa
"Ka ce me? "
"Na ce abinda yake a wurinki wanda zai wadatar dasu ba komai bane illa....................
Mu haɗu a pages na gaba my Esteem fans✍️✍️✍️
*** Tofa ƙaƙa ƙara ƙaƙa,wannan wani abu ne haka wurin Iklima da zai wadatar da abokan mijinta???🤔🤔🤔
****hmmm da alama dai su Umma kande da Maman Jummalo garin nemo ma yaransu mazaje masu kuɗi sun ɗeboma ƴaƴansu bala'i haɗe da wahala wanda ƙilama har ta shafesu baki ɗaya,kaiconsu da bin ruɗin duniya,Allah ka kare mu daga faɗawa halaka.
Ina sonku,ina ƙaunarku,ina ji daku my Esteem Fans,Allah yabar ƙauna🙃🙃🙃🤗🤗🤗🤗💖💖💖💖💝💝💝🌹🌹🌹🏵️🏵️🏵️
Ina jin daɗin sharhin da kukeyi akan littafina Allah yabar ƙauna yasa mu amfana da abinda ya ƙunsa a ciki🙃🙃🙃💝💝💝💖💖💖🏵️🏵️🏵️🌹🌹
Ku cigaba da zubo ruwan comments🌹🌹🌹🤗🤗🤗🙃🙃🙃 ni kuma bazan gaji ba wurin sambaɗo muku new updates wanda zaku nishaɗantu tare da ilmantuwa gami da wa'azantuwa🌹🌹🌹🤗🤗🤗🙃🙃🙃
Daga alƙalamin
🖍️📚Narrnarhh Bukar 📚🖍️
Comments and share 🙏🙏🙏Fisabilillah.[5/23, 8:09 AM] Narnarhh Bukar: 🏵️ NACINA YAJAWOMIN🏵️
Narrnarhh Bukar✍️
🌹Perfect Essential Writer's
Association🌹
✨ P. E. W. A✨
Wattpad:@AISHAABUBAKAR812
Arewabook:@Narrnarhh002
Masu telegram zaku iya following ɗina ta wannan link ɗin🤗,🙃🏵️👇👇👇
https://t.me/+439Pdx2UbLZlOTNk
🌹🌹🌹Da rarrafe yaro kan tashi,wata rana jiriri ango ne🌹🌹🌹
🌼🌼🏵️🏵️🌹🌹🙃🙃🤗🤗Special greetings to y'll my Esteem Fans,Allah yabar ƙauna,I love y'll Lodi Lodi🤗🤗🙃🙃🌹🌹🏵️🏵️🌼🌼
27----28
"Ka ce me? "
"Na ce abinda yake a wurinki wanda zai wadatar dasu ba komai bane illa duburarki"
" Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un,mene! Kasan me kake cewa kuwa,da alama baka cikin hayyacinka"
"Da hankalina kuma ina cikin hayyacina,and so what idan kin basu duburarki ai abokaina ne ba wasu can ba sannan da izinina ai"
Wannan karon maganar tasa a zafafe yayi ta tare da cilla mata wata uwar harara.
"Wannan wani irin jahilci ne,a ce ina matarka ta sunnah kake faɗamin irin wannan maganar tare da umurta ta,lallai duniya tazo ƙarshe kuwa,idan ma mafarki kake to ka farka don wallahi bazan biye maka ba na saɓawa Ubangijina yasa sakani wuta"
"Daman ba biyemin nakeso kiyi ba ,hasalima idan kina ihun yafi kawo light"
Iklima da taga ba jinta zaiyi ba sannan ga abokansa har su uku yake mata zancen yahudancinsa tare da jahilci,ai wannan yahudanci ne mararan wallahi,bin shawarar zuciyarta tayi akan ta gudu toilet tasaka key kota tsira,hakan kuwa tayi amma ta makaro dan batafi taku biyar ba mijinta da abokansa suka bita tare da riƙota ta ihu tana cewa
"Ku sakeni la'anannuuuu!!! Jahilai marasa imani da tsoran Allahhhh!! Wa'inda bazasu gama da duniya lafiya baaaaa!!! Allah sai ya sakamin,ku sakeni wayyo Allah naaaaa!!"
Babu wanda a cikinsu ya kula mai take cewa hasalima mijinta cushion ya samu tare da zama ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya haɗi da ɗauko wayarsa don yin videon abinda sukeyi (Wa'iyazybillah,Ya Rahman kasa mufi ƙarfin zuciyoyimu😞😞😞).
Haka tana kuka tana magiyar suyi haƙuri babu kyau haramun ne,amma ina babu wanda ya kulata balle ya tausaya mata,haƙiƙa tasha wuya matuƙa ainun a hannun abonkansa kusan sumanta huɗu,datà sume wahala zata sake farfaɗo da ita,shi kuma mijin nata mara imani yayita videon abinda sukeyi hasalima shi nishaɗi abinda sukeyi yake sakashi sosai.(Subhanallah,kaico da irin rayuwar yahudawa🤔🤔🤔)
Saida kowan ne a cikin yayi yadda yakeso da ita sannan suka ƙyaleta,tana nan a yashe a ƙasa babu kaya jikinta,don rashin imani a haka suka bar gidan batare da waiwanta ba.
Iklima ba ita ta dawo daga suma ba sai cikin tsakiyar dare,kasa tafiya tayi saidai rarrafe,a haka ta rarrafa zuwa toilet,da ƙyar ta iya zama a cikin ruwa zafin saboda both her front and back duk zugi suke mata kasancewar abokan nasa wuri biyu sukayi amfani da ita,tana kuka ta gasa jikinta tare da da nasanin biyewa mamanta akan sai ta auri mai kuɗi gashi yanzu ta saka kanta cikin wahala da damuwa,a haka ta kammala gasa jikinta wanda haƙiƙanin gaskiya tamayi namijin ƙoƙari duba da yadda shi mijin nata ya afkar mata wanda bata daɗe ta warkewa ba hasalima wurin bai dena mata ciwo ba gashi yau har mutane uku sun afka mata.
Da ƙyar ta iya rarrafowa zuwa bed ɗinta ba tare da tasaka kaya ba taja bargo ta lulluɓa kasancewar zazzaɓin ya rufeta jikinta sai kakkarwa yake saboda mugun zazzaɓin daya shigeta lokaci guda,haka ta kwanta sai daga baya bacci ya sureta haɗe da mugayanmafarkai bila adadin mafi yaws duk akan mijinta ne da abokansa.
Haka Iklima ta cigaba da rayuwa a gidan mijinta cikin wahala da tashin hankali gashi kusan every week shi da abokansu sai sun biya buƙatarsu da ita wani lokacin da taji isowarsu zata ruga toilet ta saka key ta kuma ƙi cire key ɗin haka zasu wuce wani lokacin kuma su yagalgalata son ransu,babu halin ta faɗama mamanta saboda kashe din da ya mata haɗe da nuna mata videos ɗin da yayi mata a lokacin da suke biyan buƙata da ita tare da cewa tana faɗama wata ko iyayenta sai ya ɗaura a social media kowa ya gani,da wannan ya toshe bakin Iklima,koda sunyi waya da Umma Kande bata faɗa mata komai hasalima lafiya take cewa idan Umma Kande ta tambayeta suna lafiya babu wata matsala. Wannen kenan
TUNATARWA
*****Ƴan uwana mata mubi duniya a sannu,muyi taka tsantsan da duniya domin idan ba muyi taka tsatsan ba zamu kai kanmu ga halaka,baki da gashin wance ba lalle sai kinyi kitson wance ba,izina ga mata masu zuwa wurin boka ko malamin tsubbu don biyan wata buƙata tasu,kisani yake ƴar uwata mai daraja da a ce cikin salisalin dare kika tashi tare da ɗauro alwala sannan kikayi sallah koda raka'ah biyar ne haɗi dakai kuka gurin Ubangiji maji kukan bawansa to wallahi da kinga canji a rayuwanki basai kin bata aljihunki ba tare da imaninki ba.
Milasi ne mai ƙarfi a nan domin kasancewar Umma Kande da Maman Jummalo sun aurar da ƴaƴansu wahala da damuwa bata ƙare musu ba hasalima yanxu zasu fara girbar abinda suka shuka domin kuwa ba turbar Allah da manzansa suka bi ba wurin aurar da ƴaƴansu hasalima taimako suka nema wurin ɗan Adam kamarsu ba wurin Allah ba wanda su a nan imaninsu ya soma rauni sannan kuma zasu girba abinda suka shuka da hannunsu tare da ƴaƴansu da basu samu tarbiyya mai kyau ba.
Allah kasa mufi ƙarfin zuciyoyinmu,ka ƙarama mana imani tare da tsarkake zukatanmu,ka bamu ikon bin dokokinka,ka kuma hanamu kallon haram koda da ƙwayar zarra ne.********
@@@@@@@@@@@
"Assalamu Alaiki"
Wata ƴar matashiyar budurwa ce tama Sa'eeda sallama haɗe da zama a seat ɗinta tana ɗan murmushi har dimples ɗinta na lotsawa.
"Wa Alaikissalam"
Sa'eeda ita ma ta mayar mata da martanin murmushin data mata.
"Sunana Halima Ɗalhat amma anfi kirani da Iman"
"Ni kuma sunana Sa'eeda Sulaiman"
"Maa shaa Allah, duk da nasan ba wani sanina kikayi a class ɗin nan ba hasalima a 200 level na shigo saboda direct entry nayi"
"Allah sarki,ina ganinki a class ɗin nan amma bamu taɓa magana ba,kinsan wallahi nayi mamakin ganinki a cikin class tare damu alhalin bamu fara karatu dake ba"
"Eh wallahi, nayi ND na a Nuhu Bamalli polytechnic Zaria a business administration sai nayi applying DE (Direct Entry) saboda banason HND,shi ne suka bani admission a 200 level"
"No wonder!!! I'm so surprise seeing you in our class"
Dariya sukayi lokaci guda,zakayi tunanin ƙawaye ne tun tali-tali ba yanzu suka fara magana da juna ba,Iman ce ta katse dariyar tasu da cewa
"Please Sa'eeda will you be my friend? Ba zan ɓoye miki ba,tun da na fara karatu a class ɗin nan ban ga mai natsuwa,hankali tare da ɗumbi karatu kamarki ba,bana yin ƙawaye amma kece ta farkon da naji zan iya ƙawance da ita ba tare da nayi tantama ba ko shakku akai,Sa'eeda ni ba irin ƙawayen banza bane,a lokacin da na fara karatu daku na lura ƴan class ɗin nan basa son tarayya dake,bayan haka suna gulmarki a ɓoye wai ke ƴar talakawa ce kaza da kaza"
Katse mata magana tayi Sa'eeda da cewa
"Koda za'ayi gulmana banda Maryam a ciki saboda aminiyata ce tun muna secondary school,so i know she will never be among them"
Galala Iman tayi da baki tana kallonta,kardai tana nufin Maryam Tukur,sai kuma ta ce
"Kina nufin Maryam Tukur"
"Sosai ma kuwa"
Iman mamaki ya cikata sosai jin Maryam wacca tafi kowa gulmarta tare da fallasa sirrinta ga friends ɗinta yanzu take cewa she trust her and she will never be among those that will hurt her,how is that possible,tab akwai lauje cikin naɗi kenan.Sai kuma can ta ce
"Amma duk da haka be very careful,karki yarda da mutum ɗari bisa ɗari dan wani lokacin mutum kan canja daga yadda kika sansa"
"Hakane Iman amma zuciyata tana faɗamin a kullum Maryam will never betray me"
"Naji hakan kuma ina fatan she will never betray you,amma dai kibi a hankali "
"In shaa Allah dear,nagode da shawararki sosai,sannan maganar friendship dani you are always welcome,Allah yasa ƙawancanmu ta kaimu har zuwa Jannatul Firdausi"
"Ameen ya rabb,nagode sosai da yarda da kikayi akan na kasance ɗaya daga cikin friends ɗinki"
"Babu damuwa Iman nike da godiya"
Rungume juna sukayi suna jin ƙaunar junansu na ratsasu.
Tun daga wannan lokaci Iman ta kasance ta hannun damar Sa'eeda sannan idan ƴan aji suna gulmar Sa'eeda da sunga Iman zasu kama bakinsu saboda sunsan halinta,bata musu da wasa har Maryam ma shakkar Iman take saboda akwai ranar da Iman tazo wucewa ta gefansu taji Maryam na gulmar Sa'eeda tare da fallasa sirrin Sa'eeda ga ƴan group ɗinsu,su kuma sai dariya suke suna tafawa,taso ta wuce ba tare da ta kulasu ba amma jin Maryam tayi wani lafazi akan Sa'eeda yasata tsayawa cak tare da juyowa ta duba Maryam sannan ta ce
"Me kika ce? "
Maryam ta zaci Iman itama ta tsani Sa'eeda ne yasata ƙara maimaitawa tana dariya
"Kina nufin Sa'eeda bata da asali? "
"Sosai ma kuwa Iman"
"To ke waya faɗa miki bata da asali? "
"Da kanta ta fadamin ai"
Iman girgiza kai tayi tuno da yabon da Sa'eeda take yi game da Maryam akan ta yarda da ita,lallai ɗan Adam ba abun yarda bane a wannan rayuwa,can kuma ta ce
"Yanzu ke Maryam da ta faɗamiki sai ta ce kizo cikin friends ɗinki ki fada musu,kina faɗa musu kuna dariya lokaci kuda ko,shin bakisan yarda da amintuwa da tayi dake ne yasa har ta iya faɗa miki wannan sirrin nata wanda ba kowa zata iya fadama mawa ba,amma sai gashi kinci amanar yarda da amintuwar da tayi dake kinzo cikin ƙawayenki kina fallasa sirrinta garesu"
Taɓe baki Maryam tayi sannan ta ce
"To ni ina ruwana,ni na ce ta faɗamin "
"Tabbas bake kika ce ta faɗamiki ba amma she trust you that's why she is revealing her precious secret to you but you betray her,shame on you Maryam,kin ban kunya,na zaci idan kika ji wani yana fallasa sirrinta sai idan ƙarfinki ya ƙare amma sai gashi ke da kanta,wannan kuskure ne Maryam sannan idan baki tuba ba kin daina fallasa sirrin mutane sai Allah ya kamaki"
"To miye a ciki don na fallasa sirrinta,sannan ni ai bance ta faɗamin ba,hasalima in zaune na har seat ɗina tazo ta sanar min,sai kuma inƙi faɗa don ina jin tsoranta Allah ya bani baki,a'a wallahi ke idan ta ƙara fadamin wani sirrin nata bazan fasa zuwa fallasashi ba,ke yanzu ma na fara wallahi"
"Eh lallai Maryam kin cika munafuka amma baki da hankali,ke a tunaninki don kin fallasa sirrinta shi zai hana Allah ya ɗaukakata,wallahi kinyi kuskure,kuskure ma babba,wanda zakiyi nadamar da bata da amfani a ƙarshe,sannan kiji tsoran Allah kisan cewa Allah baya barci yana kallon kowa,yasan abinda ke a cikin zuciyar kowa,ita da kuke ganin she is nothing wata rana sai kuga she becomes something,sai Allah ya ɗaukakata sama daku,sannan rashin asalin da kike cewa bata dashi wataran sai kiga Allah ya haɗata da asalinta,who knows she comes from a rich family ƙaddara ce yasata zamowa haka,ki kula Maryam, ki kula,daga yau idan ina wuri karki sake aibanta Sa'eeda inba haka ba,ubanki zanci lakada a waje wallahi,ni ba kamar Sa'eeda bace shiru-shiru ayita cutarta tana haƙuri,bana ɗaukar iskanci ko raini,idan baki kiyaye ba to wallahi zansa a koreki daga makarantar nan sai inga uban da zai tsaya miki munafuka,da alama baki san koni wacece ba ,ina ƙara faɗa miki ki kula,idan na sake ji kin aibanta Sa'eeda,hmmmm Wa Rabbul Ka'abah you will regret staying in this school"
Nuna Maryam Iman tayi da yatsa ɗaya tare da cilla mara harara har saida Maryam ta tsorata kasancewar Iman akwai manyan idanu sannan ta wuce abinta ba tare da tabi ta kansu ba.Kowa a wurin shuru yayi har da Maryam saboda sun san mahaifin Iman ƙani ne ga VC wato Vice Chancellor ɗin makarantar ,sannan Uncle ɗinta HOD ne a department of computer science banci yayyinta da suke lecturing a makarantar don haka babu yadda zasuyi da ita dole su shiga taitayinsu.Haka kuwa akayi tun daga ranar idan suna gulmar Sa'eeda da zarar sunga Iman tazo wucewa zasu kamar bakinsu.
Ƙawancan Sa'eeda da Iman ƙara ƙarfi yake,babu laifi Iman akwai ƙoƙari da maida hankali a karatu shiyasa Sa'eeda take ƙaunarta sosai,wanda a yanzu komai tare sukeyi,ko masallaci tare suke zuwa.
Ƴan aji sun rage yima Sa'eeda wulaƙanci haɗi da gulmarta saboda Iman, koda ma zasu mata shegan taka sai in sunga Iman bata nan sannan suke mata iya shege. Wannan kenan
@@@@@@@@@@@@
A ɓangaren soyayyar Sauban da Sa'eeda yanzu dai sai a hankali saboda Sauban ya fara canjawa Sa'eeda daga yadda ta sansa a da zuwa wani Sauban na daban,ba kodayaushe yake kiranta ba sannan koda ya kirata basa tsayawa hira sosai kamar da,bayan haka ya daɗe da dena zuwa gidansu hira,koda Sa'eeda ta mishi magana akan rashin zuwansa sai ya ce abubuwa sun mishi yawa sosai.Kalaman soyayyar da yake mata a da yanzu ya rage in fact ya daina .Haƙiƙa Sa'eeda kwanakin nan bata cikin hankalinta saboda sauyawar da Sauban ya mata kuma idan ta tambayeshi ko ta mishi laifi ne sai ya ce a'a kawai dai yanzu aiki yana riƙesa sosai.
Haka dai rayuwa ta cigaba da tafiya da daɗi da babu daɗi,ta fannin Sa'eeda kuwa kwata-kwata hankalinta baya jikinta kullum cikin tunanin Sauban take gashi exams ɗinsu na second semester ya kusa,karatun ma da ƙyar take yinsa ba kamar da ba.Ummanta ne ta kula kwana biyu Sa'eeda da sauya kullum shiru sannan karatun da take yawanyi ta rage .
Wata rana a ɗaki suna zaune kasancewar asabar ne dukkansu suna gida,Sa'eeda na zaune akan tabarma ga littafi a gabanta tayi shiru kamar wata mara lafiya da ita.Umman Sa'eeda ta dubeta da kyau sannan ta ce
"Sa'eeda, wai meke damunki ne kwana biyu duk kin susu ce kamar wata mara lafiya,saidai ki zauna kina tunani,gashi kin daina karatu kamar da kuma kinsan exams ɗinku ya kusa,karki ɓoyemin komai,meke damunki Sa'eeda? "
Shiru Sa'eeda tayi tana tunanin kota faɗama Ummanta ne sauyawan Sauban gareta ko kuwa,wata zuciyar ta ce mata kawai ta faɗa mata tunda bata ɓoye mata komai da ya shafi rayuwarta,katse mata tunani Umman Sa'eeda tayi da cewa
"Dake fa nake Sa'eeda"
"Ummm,umm Ummina daman Sauban ne"
"Sauban kuma! Yayi me? "
"Sauban ne.......................
Mu haɗu a pages na gaba my Esyeem Fans,ina yinku over🤗🤗🤗🙃🙃🙃🌹🌹🌹🏵️🏵️🏵️🌼🌼🌼
****Hausawa suka ce idan wani ya ƙika wani a lokacin zai soka,Sa'eeda dai ta samu aminiya mai sha re kukanta🙃🙃🙃
****Shin me Sauban yake nufi da Sa'eeda ne??? Mai yake ƙullawa a ransa game da Sa'eeda??? Miye dalilin sauyawarsa a gareta???
Ku cigaba da zubo ruwan comments 🤗🤗🙃🙃🌹🌹🏵️🏵️🌼🌼 Ni kuma aradun Allah bazan gaji ba wurin suburbuɗo muku new updates wanda zasu ilmantar,nishaɗantar tare da faɗakar daku In shaa Allah🤗🤗🙃🙃🌹🌹🏵️🏵️🌼🌼💗💗
Daga alƙalamin
🖍️📚Narrnarhh Bukar 📚🖍️
Comments and share 🙏🙏🙏Fisabilillah.
[5/23, 8:09 AM] Narnarhh Bukar: 🏵️ NACINA YAJAWOMIN🏵️
Narrnarhh Bukar✍️
🌹Perfect Essential Writer's
Association🌹
✨ P. E. W. A✨
Wattpad:@AISHAABUBAKAR812
Arewabook:@Narrnarhh002
Masu telegram zaku iya following ɗina ta wannan link ɗin🤗,🙃🏵️👇👇👇
https://t.me/+439Pdx2UbLZlOTNk
Wannan pages ɗin sadaukarwa ne gareku my Esteem Fans,ina sonku,ina ƙaunarku,ina jin daɗin comments ɗinku Allah yabar ƙauna🤗🤗🙃🙃🌹🌹🏵️🏵️🌼🌼
29----30
Shiru Sa'eeda tayi tana tunanin kota faɗama Ummanta ne sauyawan da Sauban yayi gareta ko kuwa,wata zuciyar ta ce ta faɗa mata tunda bata ɓoye mata komai da ya shafi rayuwarta,katse mata tunani Umman Sa'eeda tayi da cewa
"Dake fa nake Sa'eeda"
"Ummm umm Ummina daman Sauban ne"
"Sauban kuma! Yayi me? "
"Sauban yanzu baya sona Ummina,bansan me nayi masa ba,yanzu ko kirana ya dena yi "
Fuskarta da matsanancin damuwa take sanarwa Ummanta rashin kulawar Sauban a gareta kwana biyun nan ba kamar da ba,Ummanta dake saurararta ta ce
"Yanzu akan Sauban ne duk hankalinki ya tashi kika kasa karatu Sa'eeda, saboda kwana biyu ya sauya miki shi kenan kuma saiki canja daga yadda nasanki Sa'eeda, akan soyayya kike tada hankalinki"
Shiru Sa'eeda tayi tana sauraran Ummanta, jin faɗan da take mata,baza ta gane soyayya ba,batasan yadda take mutuwar so da ƙaunar Sauban bane wanda take ji bazata iya rayuwa babu shi ba,kaunarshi ta riga da gama zama jinin jikinta,zata iya komai saboda ƙaunar da take mishi.
Sa'eeda tasha faɗa sosai wurin Ummanta wanda daga ƙarshe sai ta bita da nasiha ta cewa
"Sa'eeda idan zaki so mutum,ki soshi ba dayawa ba sannan idan zaki ƙi mutum ki ƙishi ba dayawa ba saboda yanayin rayuwa,mutum yakan canja a kowani lokaci,na daɗe da sanin kina ma Sauban so wanda ya zarce ƙa'ida Sa'eeda shi yasa daga sauyawarsa gareki har hankalinki ya tashi,ki dawo cikin hayyacinki Sa'eeda,ina alƙawarin da kikamin akan maida hankalinki kacokar a karatunki Sa'eeda, ina yake ko soyayya ta rufe miki idanu yanzu ko "
Tabbas ko ba'a faɗa ba nasihar Umman Sa'eeda ta ratsa Sa'eeda sosai ganin yadda jikinta yayi sanyi.
"In shaa Allah zan cika miki alƙawarin da na ɗauka akan maida hankalina akan karatuna sosai sannan kuma zan rage tunanin Sauban a zuciyata duk da bani na ɗaurawa kaina ba"
"Hakan yanada kyau,Allah ya miki albarka ya kuma shige miki gaba a al'amuranki gaba ɗaya"
"Ameen Ameen Ummina"
Haka suka cigaba da hirarsu,Umman Sa'eeda na ƙara nusar da Sa'eeda akan abubuwa da dama.
Sa'eeda ta rage tunanin Sauban sannan ta maida hankalinta a karatunta sosai kasancewar exams ɗinsa na second semester 200 level baifi 1week ba,haka tayita karatu babu ji babu gani har sukayi exams ɗinsu cikin nasara da aminci sannan aka sabu hutu.
Duk da alƙawarin da Sa'eeda tama Ummanta akan rage tunanin Sauban amma ina zuciya bata da ƙashi,haka zaka ganta a class tayi shiru a lokacin kafin suyi exams,wani lokacin ma koda akwai littafi a gabanta haka take kasancewa,ƙawarta Iman tasha tambayarta meke damunta kwana biyu kodai bata da lafiya ne amma amsar ita ce a'a,daga ƙarshe Iman ta fara fushi da ita wai tana aminiyarta amma ta kasa sanar mata da damuwarta alhalin fuskarta ta nuna ƙarara damuwa fal a cikinta,ganin ran Iman ya ɓaci ne yasa Sa'eeda sanar ma Iman a kan halin da take ciki game da Sauban don yanzu kota kirashi baya picking wani lokacin ma number busy yake danna mata.(Maza maza hmmm abarsu kawai da halinsu🤔🤔🤔).
A gaskiya ran Iman ya ɓaci sosai jin wannan wulaƙancin da Sauban yake ma Sa'eedarta duk da bata taɓa ganinsa ba amma lokaci guda tsanarsa ta shiga ranta.Haƙiƙa Iman aminiyar kirki ce mai hankali da hangen nesa,sosai tayi ta ba Sa'eeda haƙuri tare da shawara akan kawai da rabu dashi don yaga tana mutuwar so da ƙaunarsa ne yasa yake mata wulaƙanci amma idan zata iya kawai ta fita daga harkarshi ko don karatunta kar ya samu matsala,haka Iman tayi ta ba Sa'eeda haƙuri tare da nusar da ita abubuwa da yawa a rayuwa kasancewar Iman tasan kan rayuwa sosai.Wannan kenan
@@@@@@@@@@@@@
BACK TO SCHOOL
Maa shaa Allah yanzu su Sa'eeda suna a shekarar ta kusa da ƙarshe wato 300 Level,farin ciki fal a ran ƴan aji saboda sun kusa zama graduate nan da shekara ɗaya,kamar yadda aka saba,satin farko ba'a wani lectures sosai sai sati na biyu,a sannan ne lectures ya fara zafi sosai kasancewar suna a advance class ne sannan level ɗin da yafi kowani level wahala musamman a University.
Sa'eeda ta rage son Sauban a ranta tare da fawwala ma Ubangijin talikai lammuranta sannan ta maida hankali sosai a karatunta kasancewar yanzu lectures ya ɗau zafi sosai,tare da Iman suke karatu abinsu.
A haka result ɗinsu na second semester na 200 level ya fito,Alhamdulillah Sa'eeda kamar yadda ta saba ita ce overall ɗinsu duk da current Gp ɗinta ya sauka saboda tunani da tasa a ranta amma duk da haka ta kasance jagaba a ajin nasu,Itama Iman result ɗinta yayi kyau sosai,amma squad ɗinsu Maryam sai a hankali wasunsu ma harda carryovers,Maryam dai Allah ya tsallakar da ita bata da carryover.
Haka suka cigaba da karatu a first semester na 300 level wanda yanzu suna gab da fara exams kuma daga shi zasu tafi IT na tsawan wata shida sai kuma sannan su shiga final year wato 400 level.Wannan kenan
@@@@@@@@@@@@
Bayan sati ɗaya da fitowar results
Sa'eeda ce ke zaune a seat ɗinta ita kaɗai kasancewar yau Iman batazo school ba suna da biki a faliminsu,hakan yasata duba wasu handout ɗinta kafin lecturer ya shigo aji,tana a zaunan kawai taga an ɗaura mata wani envelope me ɗauke da flowers akan handout ɗin da take karatu a saman desk,ɗago kanta tayi tana duban wacca ta ɗaura mata envelope ɗin ba tare da yi mata magana ba.
"Lafiya babu magana sai ajiye envelope ba tare da magana ba"
Ƙawar Maryam ce da suke zama tare tunda daga 100 level har zuwa yanzu da suke a 300 level suna zama tare,aminiyarta ce yanzu ta ƙut da ƙut.
"Lafiya lau Sa'eeda kasancewar bakisan da auran Maryam bane yasa mukaga ya dace kema ayi inviting ɗinki don bikin baifi saura sati biyu ba,kinga kenan kafin muyi exams ne,shi yasa na baki katin gayyata "
Shiru Sa'eeda tayi tana mamakin Maryam a ce suna ƙawaye amma ta kasa sanar mata da bikinta sai a wajen wasu wa'inda a nan ta haɗu dasu,sune zasu gayya ce ta ,haba hakan ba daidai bane hasalima ita ya dace a ce take rabawa ƴan aji invitation card ba wasu ba, Rahma ce ta katse mata tunani da cewa
"Baki duba card ɗin ba"
"No karki damu zan duba ai"
Maryam ce ta shigo class ɗin tana wani taku da takalminta mai tsini,ji kake ɗas! ɗas! ɗas! kowa na ajin ya juyo kasancewar Maryam latti tayo lecturer sun san yana hanya.
"Amaryar 2 weeks"
cewar wata daga cikin ƴan ajin,Maryam ko sai murmushi take zubawa tana wani ɗadɗaga kai.
"Mrs Sauban in 2 weeks coming "
Cewar Rahma da a lokacin take wurin seat ɗin Sa'eeda. kamar mashi Sa'eeda taji an caka mata a ƙahon zuciyarta zaro ido tayi tana cewa
"Mai naji kinje Rahma,Mrs Sauban? Wani Sauban kenan"
"Keda ga invitation card a gabanki ai ba sai kinya tambaya ba,sai ki duba ki gani wani Sauban ne malama Sa'eeda"
Maryam da tazo wucewa ta side ɗinsu ta tsaya jin abinda Sa'eeda take cewa,a zuciyarta ta ce 'Yau akwai ƙaramin hauka a ajin nan kuwa'. Sai kuma ta fasa zuwa wurin seat ɗinsu taja gefe da tsaya tana kallon yadda Sa'eeda ta wani daburce tana kici-kicin buɗe invitation card.Miƙewa Sa'eeda tayi da sauri tana zaro ido tare da cewa
"What! Me zan gani yau anya ba mafarki nake ba ni Sa'eeda"
Duk ta ru ɗe,jikinta sai rawa yake kana ganinta kasan a rikice take,ƴan aji kowa yakai dubansa gun Sa'eeda.
"Ba mafarki kike ba Sa'eeda tabbas abinda kika gani haka yake"
Cewar Rahma da take kusa da ita tana cilla mata harara,ita daman tun a 100 level ta tsani Sa'eeda kasancewar duk tafi ƴan ajinsu kyau da ilimi ga uwa uba natsuwa,shi yasa tayi duk yadda tayi ta raba Sa'eeda da Maryam hasalima ita ce ta cigaba da bawa Maryam shawarar ta auri Sauban tunda tana sonshi sosai duk dan ta ƙuntata ma Sa'eeda saboda ta gano tana mutuwar sonsa ganin yadda Maryam take yawan basu labari idan Sa'eeda ta bata labarin Sauban,duk da itama Maryam akwai shirin da suke akan Sauban ɗin ita da Mom ɗinta, bayan haka Rahma ce tabawa Maryam shawarar ta dena tafiya gida tare da Sa'eeda kar ta shafa mata baƙin jini gun samari aƙi sonta tunda ita kadai samari suke ma magana banda Maryam,haka kuwa akayi don ta aminta da Rahma sosai kuma tana jinta a ranta.
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un!!!,Allahumma La Sahla Illama Ja'altahu Sahla Wa'anta zaja'alul Hujni iza shi'ita Sahla!!!"
Abinda Sa'eeda take ta furtawa hawaye na gangarowa bisa kuncinta ba tare da gogesu ba,zuciyarta wani zafi yake mata wanda tunda uwarta ta haifeta bata taɓa jin irinsa ba,ga gumi na tsuttsubo mata a koshinta sai kace mai zazzabi.Duban Maryam tayi idonta cike da hawaye ta fara magana cikin murya mai rauni
"Maryam yanzu abinda zakimin kenan,cin amanata zakiyi ki auri saurayi na bayan kinsan ina sonsa,sannan kinfi kowa sanin alaƙata dashi mai ƙarfi ce kuma akwai maganar aure a tsakanin mu,mai nayi miki Maryam dana cancanci irin wannan muguwar sakayya,mai nayi miki Maryam, Why Maryam! why!! why!!!..."
Haba sai ta fashe da matsanancin kuka mai tsuma rai ba tare da ta gama maganar.Maryam da Rahma kallon junansu sukayi tare da taɓe baki irin ko a jikinsu kukan da take yi.ƴan aji kowa ya bar abinda yakeyi sun natsu tare da sauraron abinda ke faruwa,wasu ma har da miƙewa duk don suji gulmar dakyau.(ƴan aji akwai gulma😂😂😂)
"Maryam mai yasa kika yaudare ni keda Sauban, me yasa kinsan kina sonsa tun farko baki sanar min ba,ni mai iya bar miki shi ne,amma sai yanzu da na shaƙu dashi,ina sonsa shi ne kuka munafurceni Maryam"
Kukan nata sai ƙara ƙarfi yake saboda tanada raunin zuciya abu kaɗan ke sakata kuka,tana kukan sai kuma ta cigaba ta maganarta duk da ba sosai ake gane maganar ba saboda kukan da takeyi.
"Maryam mai nayi miki haka,mai na shige miki a rayuwa, babu abinda nake ɓoye miki na game da rayuwata duk saboda yarda da amintar da nayi dake ashe aaaashe........"
Nan ma kukan ta sake fashewa dashi tuno sirrika da dama da ta sanarwa Maryam wanda ya shafi rayuwarta ita da Ummanta ,haƙiƙa tayi kuskure babba a rayuwarta kuma yanzu ta tuno da maganar Iman da ta ce ' Ba'a yarda da mutum ɗari bisa ɗari,saboda yakan iya canjawa a kowani lokaci'.
Sai a yanzu Maryam ta samu damar yin magana cike da izza da taƙama take maganar.
"Naji duk abinda kika ce Sa'eeda, amma na taɓa cewa ki faɗamin sirrinki ne ko ko na taɓa tambayarki akan dole sai kin faɗamin sirrinki,ni ba yaudararki nayi ba saboda shi ya ce yana sona bani nakai kaina ba da zakizo kina min wani gani-gani ba ehehh! "
Tana maganar tana wani juye idanunta haɗe da murguɗa baki.
Waiwaye
Abinda Sa'eeda bata sani ba shi ne,tun ranar da suka haɗu da Sauban, Maryam ta mutu akansa hasalima ita a tunaninta da farko ita yakeso sai kuma daga baya taga Sa'eeda ce yakeso,wannan abu ya ɓatama Maryam rai matuƙa ainun.tunda taji ya ce yanason ta bashi aron Sa'eeda ta tsinke da lamarinsa kenan duk surutun da take mishi yana kulata duk ba ita yake so ba?.
Bayan Sauban ya wuce ita da Sa'eeda kowa yabi hanyar gidansu,da kuka ta shiga parlonsu inda ta samu mom ɗinta da wata yayar mom ɗinta suna hirarsu kice da annanshuwa,kawai sukaji an banko ƙofar ɗaki babu sallama, Maryam suka gani fuskarta jiƙe da hawaye alamun kuka tayi,duk a tare suka ce
"Lafiya Maryam! "
Bata basu amsa ba ta faɗa jikin Mom ɗinta haɗe da sake fashewa a wani matsanancin kuka,duk ta ruɗasu ,yayar Mom ta matso kusa dasu tana tambayar Maryam lafiya mai ya sameta ,shiru babu amsa sai kuka,saida ta gaji don kanta ta fara basu labari cikin shasshekar kuka da jan majina
"Mom inason sonsa,shi kuma Sa'eeda yake so Mom,ya zanyi da rayuwata wallahi ina sonsa,zan iya mutuwa idan ban auresa ba Mom help me plsss...."
Bata ƙarasa maganar ba ta ƙara fashewa da kuka,kallon junansu sukayi ita da yayarta cike da mamaki.
"Daman saboda namiji ne kike wannan kukan kamar wani babban abu ya sameki duk kin tada mana da hankali eh Maryam"
Cewar yayar Mom ɗinta,ita dai Mom kallon ɗiyarta take da mamaki ta kasa magana,yayarta ta ce ta ƙara da cewa
"Wanene shi? "
"Sauban Muhammad Ja'afar Ƙaraye,ya ce shi manager ne a wani kamfanin sarrafa shinkafa"
"Sauban Muhammad ƙaraye,ƙaraye dai da na sani"
Kallonta dukkansu sukayi alamun ƙarin bayani,murmushi tayi tare da cewa
"Indai Sauban ne to sha kuruminki kamar anyi angama kin zama matarsa"
Maryam ce ta kalleta tare da zaro ido alamu mamaki sannan ta ce
"Da gaske Aunty? "
"Sosai ma kuwa,ai mahaifiyar Sauban aminyita ce sosai muna zumunci da ita sosai,kuma tanada kirki,shi Sauban shi ne ɗa na Uku a yaranta"
"Maa shaa Allah,faɗuwa tazo daidai da zama"
Cewar Mom wanda sai yanzu ta fara magana,sai murna Maryam take can kuma ta ce
"Aunty shifa baya sona Sa'eeda yake so,to ya kike ganin zai aureni bayan yasan ni ƙawar Sa'eeda ce"
Tana magana cike da damuwa,ɗan murmusawa Auntyn ta tayi tare da cewa
"Wannan ai mai sauƙi ne Maryam,kissa da makirci zamu haɗa tare da aibanta yarinyar kun Mahaifiyarsa,kinga ai dole tasa ya haƙura da ita,sai kuma na bijiro dake a matsayin ko zai aureki tare da yabonki da kururuta kyaunki"
"Nice Aunty,wannan shawara ce mai kyau,dan tabbas Sa'eeda nada abun ai bantawa saboda a lokacin da muna secondary ta taɓa sanarmin Mamanta batasan danginta ba hasalima a wani ƙauye ne aka tsinci kakarta da mamanta suna garari a tiri wani ya taimaka ya daukosu zuwa gidansa "
"Kenan basuda asali"
"Eh Aunty"
"Kinga kuwa wannan ma hujja ce babba wanda zamu riƙe,shima kansa nasan bazaiso auran mara asali ba balle mamansa da take son surukai masu nasaba,kinga kuwa auransu bazaiyu ba kenan"
"Wannan haka yake,don wallahi na tsani yarinyar nan,gata ƴar talakawa sai shegen kyau da ilimi" ,Cewar Mom.
A ranar suka ƙulla komai akan yadda zasu rushe auran Sa'eeda da Sauban don ya dawo kan Maryam.
Haka kuwa akayi don a lokacin da Auntyn Maryam ta sanarwa maifiysr Sauban rashin asalin Sa'eeda ta ce dole Sauban sai ya fasa auran Sa'eeda, da ya tambayi dalili sai ta sanar masa,haka shima ya ce ya fasa,nan kuma maganar Maryam mahaifiyarsa ta bijiro masa akan ya aureta tafi Sa'eeda komai,a da yaso jajjaya ganin ƙawar Sa'eeda ce amma da mahaiyarsa da dage sai kawai ya amince,nan kuwa soyayya tsakanin Maryam da Sauban ta ƙullu,sai kuma Sauban ta fara canjawa Sa'eeda, ya daina zuwa gidansu,kira ma ya daina,idan ta kirashi wani lokacin ya ɗauka wani lokacin yaƙi dauka.
Haka dai suka cigaba da tafiya har yanzu da ake maganar auran Maryam da Sauban saura 2 weeks.
Cikin Labari
Maryam ce ta ƙara da cewa
"Sannan ba dagani bane,rashin asalinki ya sashi fasa auranki"
Ajin ne ya kaure da surutu jin abinda Maryam take faɗa,kowa sai kallon Sa'eeda yake a ƙasƙan ce jin ashe marar asali ce.Sa'eeda ce taji maganar kamar a mafarki Maryam na fallasa sirrinta a gaban ƴan aji,bayan ta sanar mata amana ne karta sanarwa kowa kuma tayi alƙawari bazata sanarwa kowa ba amma shi ne yanzu take sanarwa ƴan aji duk dan ta wulaƙanta ta a gabansu,cikin kuka Sa'eeda ta ce
"Maryam yanzu sirrina da kika ɗau alƙawarin ɓoyewa kike sanar wa ƴan aji,ban cancanci haka daga gareki ba Maryam,ko a mafarki wani ya ce min zaki fallasa sirrina bazan taɓa yarda balle a zahiri,Why Maryam! Why! Why! "
Taɓe baki Maryam tayi,sai kuma wata a aji ta fara ai banta Sa'eeda, can wasu a ajin suka fara aibanta ta daman haushinta sukeji akan tafisu ilimi.
Ana cikin haka saiga lecturer ya shigo ajin kasancewar yau bada wuri ya shigo ba sai wurin 9:26am ya shigo,kowa ya nufi gun zamansa,ita kuma Sa'eeda jakarta ta ɗauka ta fita daga ajin tana sharar ƙwalla,ko takan malamin batabi ba ta wuce.
Kuka take har ta fito daga gate ɗin school ɗin ta tari mai keke napep ta hau duk a lokacin tana kuka,bayanin inda zai kaita tayi yaja keke napep ɗinsa suka tafi.
Isarsu ƙofar gida,ta ciro #500 ta bashi ba tare da ta amsa canji ba ta shiga gidan ko sallama babu,sa'arta ɗaya Ummanta bata daɗe da dawowa ba daga aikinta na shara ba,banko ƙofar ɗakin tayi babu sallama tare da cewa
"Ummina,Ummina na shiga Uku,sun yaudare ne Ummina"
Kawai ta ƙara ƙarfin kukan nata,Umman Sa'eeda dake zaune akan ƴan tabarmarta tana hutuwa ta miƙe a rikice tare da duban ƴarta ta da kuma maganar da take cewa,cikin ruɗewa Ummanta ta ce
"Suwa suka yaudarki Sa'eeda ?"
"Ummina Sauban da Maryam aure zasuyi saura sati biyu Ummina,na shiga Uku!!!"
"Baki shiga uku ba Sa'eeda kwantar da hankalinki"
Jiri ne ya fara ɗiban Sa'eeda ji take duniyar na juya mata,haba kan kace me Sa'eeda tayi ƙasa tana dafe da kai da sauri Ummanta ta riƙota a rikice tare da cewa
"Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un!!!Sa'eeda!!! Sa'eeda!!!...............
Mu haɗu a pages na gaba don cigaba da jin wannan chakwakiyar duk daga alƙalamin Narrnarhh Bukar✍️✍️✍️
****Wata Sabuwa inji ƴan caca,tofa,me yasamu Sa'eeda ne haka da Ummanta ta rikice tare da kiran sunanta da ƙarfi???
***Daman Sauban ba son Sa'eeda yake tsakani da Allah ko ko yaya???
***kuna ganin auran Sauban da Maryam bazai shafi karatun Sa'eeda ba ganin sun kusa fara Exams????
Ku cigaba da zubo ruwan comments🤗🤗🤗🙃🙃🙃💝💝💝,Ni kuma bazan gaji ba wurin suburbuɗo muku da zafafan updates wa'inda zasu nishaɗantar,ilmantar tare da faɗakar daku🤗🤗🙃🙃💝💝🌹🌹🌼🌼🏵️🏵️
Ina matuƙar alfahari daku my Esteem fans,Allah yabar ƙaunar🤗🤗🙃🙃💝💝🌹🌹🌼🌼🏵️🏵️💖💖💗💗💓💓
Daga alƙalamin
🖍️📚Narrnarhh Bukar 📚🖍️
Comments and share 🙏🙏🙏Fisabilillah.
[5/23, 8:09 AM] Narnarhh Bukar: 🏵️ NACINA YA JAWO MIN🏵️
Narrnarhh Bukar✍️
🌹Perfect Essential Writer's
Association🌹
✨ P. E. W. A✨
Wattpad:@AISHAABUBAKAR812
Arewabook:@Narrnarhh002
Masu telegram zaku iya following ɗina ta wannan link ɗin🤗,🙃🏵️👇👇👇
https://t.me/+439Pdx2UbLZlOTNk
31-----32
Isarta ƙofar gida,ta ciro #500 ta bama mai keke napep ba tare da ta amshi canji ba ta shiga gidan ko sallama babu,sa'arta ɗaya Ummanta bata daɗe da dawowa ba daga aikinta na shara,banko ƙofar ɗakin tayi babu sallama tare da cewa
"Ummina,Ummina na shiga Uku,sun yaudare ne Ummina"
Kawai ta ƙara ƙarfin kukan nata,Umman Sa'eeda dake zaune akan ƴan tabarmarta tana hutuwa ta miƙe a rikice tare da duban ƴarta ta da kuma maganar da take cewa,cikin ruɗewa Ummanta ta ce
"Suwa suka yaudarki Sa'eeda ?"
"Ummina Sauban da Maryam aure zasuyi saura sati biyu bikinsu Ummina,na shiga Uku!!!"
"Baki shiga uku ba Sa'eeda kwantar da hankalinki"
Jiri ne ya fara ɗiban Sa'eeda ji take duniyar na juya mata,haba kan kace me Sa'eeda tayi ƙasa tana dafe da kai da sauri Ummanta ta riƙota a rikice tare da cewa
"Innalillahi Wa'inna I'aihi Raji'un!!!Sa'eeda!!! Sa'eeda!!! "
Jijjigata takeyi amma ko motsi,da sauri ta ɗebo ruwa a babba roba jikinta na rawa ta watsa mata a jiki,haba nan da nan Sa'eeda ta sauke nauyayyen a ajiyar zuciya lokaci guda kuma tana dafe da ƙirjinta wurin saitin zuciyarta,cikin sanyin murya mai rauni ta fara magana
"Ummina zuciyata zata fashe,ƙirjina zai tsage Ummina,wayyo Allah Ummina zuciyata zuciyata Ummina zan mutu zan mutu!"
Haka Sa'eeda tayita nanatawa hannunta na a saman ƙirjinta daidai zuciyarta,ƙara ruɗewa Umman Sa'eeda tayi,da sauri da ɗauko hijab ɗinta tare da jakarta sai ta riƙota suka fito waje,zaunar da ita tayi sannan ta kulle ɗakinsu, taimaka mata tayi ta miƙe daƙyar sukayi hanyar fita waje,suna gab da fita saiga su Umma Kande da Maman jummulo sun shigo gidan,tsaya sukayi ganin Umman Sa'eeda ta riƙo Sa'eeda suna tafiya a hankali zasu fita,da sauri Maman Jummalo tace
"Babu lafiya ne Sa'eeda"
Fuskar Umman Sa'eeda a ɗaure ta amsa mata da bata da lafiya ne,don tasan halinsu da shegantaka,tayi tambayar ne don su samu abun aibantasu,Umma Kande ce ta taɓe baki tare da huro guntayen hancinta da cewa
"Sai wani ƙunbuya-ƙunbuya kuke,an faɗa muku bamu san mai kuke ciki bane,dan nasan kullum fitar da take da sunan makaranta sai anjawo abin kunya,ai gashi nan za'aje a zubar da cikin shege"
Ba Umman Sa'eeda ba hatta ita kanta Sa'eedar saida ta waiwaya jin wannan sabon sharri kawai daga mutum baida lafiya shikenan sai sharri,Umman Sa'eeda ta mayar mata da martani cike da ɓacin rai
"In shaa Allahu bakinki saidai ya sari ɗanyen kashi,sannan sharri da kike nufin mu dashi Allah bazai barki ba,Allah yana tare da masu gaskiya a kowani yanayi,abinda kikewa Sa'eeda fata saidai ki ganshi a ɗakinki bi'izinillahi"
Rai a ɓace take maganar dan yau Umma Kande takaita bagon,haƙurinta ya fara ƙarewa,ita kuwa Umma Kande ƙara taɓe baki tayi irin ko a jikintan nan,ƙara jefo mata wata mummunar maganar tayi da cewa
"A hayye chassssssss!!! Umman Sa'eeda kenan ai na gaba yayi gaba na baya kuma hhhhhhhh!!! Sai tsintar hula,nida na aurar ina zanga abin kunya ai seke mai karuwa a ɗaki wacca kullum saita fita da sunan karatu,zamu gani dai koya kikace ƙawas"
"Kkkkwaraiiiiii da gaske aminiyar arziƙi,wannan haka yake,zamu gani,ayi mugani in tusa zata hura wuta"
Bata ƙara bi takan zantuttukansu ba ta wuce waje da Sa'eeda, sauƙinsu ma ana samun keke napep sosai a unguwar kasancewar akwai titi yasa basu wani ɓata lokaci ba suka samu keke napep ya kaisu asibiti.
Isarsu asibitin keda wuta jikin Sa'eeda ya rikice da sauri nurses suka amsheta direct suka nufi emergency room da ita don taimakon gaggawa,Alhamdulillah likitoci da nurses ɗin sunyi nasarar maido da ita hayyacinta tare da mata allurar bacci don ta huta,sai aka basu gado wata nurse tasa mata drip don tasamu ƙarfin jiki sosai.
Kwananta biyu a asibiti, a rana ta uku saiga Iman tazo kasancewar tazo school bata ga Sa'eeda kuma tasan bata fashin makaranta saida dalili,kiran wayanta tayi sai Umman Sa'eeda ta ɗauka kasancewar ita Sa'eedar bacci take a lokacin,sanar mata tayi Sa'eeda bata da lafiya yau kwanansu uku kenan a asibiti amma Alhamdulillah ta samu sauƙi.A ruɗe Iman ta tambayi asibitin da aka kwanantar dasu da kuma numban ɗaki,sanar mata tayi da sunan asibitin da numban ɗakin da suke,babu ɓata lokaci Iman ta hau sabumar motarta da Daddyn ta ya siya mata kwanan nan ta nufi asibitin a ruɗe.
Shigarta asibitin keda wuya tayi saurin parking motarta sannan ta nufi females ward direct zuwa numban ɗakin da Umman Sa'eeda ta sanar mata,tana shiga ɗakin ta tsaya cak ganin yadda ƙawarta ta koma lokaci guda,ga hancinta ya ƙara fitowa saboda ramar da tayi,idanunta kuma sun shige ciki sosai,tabbas duk wanda yasan Sa'eeda dole ya zubar mata da ƙwalla idan ya ganta a yanzu,a hankali ta nufi gadon da Sa'eedar take a kai tare da riƙo hannunta wanda ba'a saka canula ba,hawaye ne suka fara ganganrowa bisa kuncinta wanda batasan da zubowansu ba,cikin sanyin murya mai cike da rauni Iman ta fara magana
"Allah ya baki lafiya Sa'eeda, yasa kaffara ne a gareki,in shaa Allah bazasu gama da duniya lafiya ba sai Ubangiji yabi miki hakƙinki,Allah ya baki lafiya Sa'eeda, Allah ya tashi kafaɗunki Sa'eeda,sai Allah ya saaakkata mik.........."
Bata ƙarasa maganar ba ta fashe da matsanancin kuka mai ratsa zuciyar duk wani mai sauraronta,kuka take sosai tare da tausayawa aminiyarta ganin irin halin da take ciki duk saboda yaudara tabbas Ubangiji baya yafe hakƙin wani akan wani,sai Allah yabi mata hakƙinta.Tana cikin wannan kukan ne sai Umman Sa'eeda ta dafata tare da girgiza mata kai alamu tayi haƙuri tabar kukan amma ina kamar ƙara ƙarfin kukan nata akeyi tuno da labarin da wata ƴar ajinsu Emmanuella ta bata akan abinda ya faru ranar Friday.
Waiwaye
*******Kasancewar ranar Friday Iman batazo school ba saboda suna da gagarumin biki a familinsu sai Monday ta shigo,Iman ta shigo class amma babu Sa'eeda har wurin ƙarfe 9:12am na safe kuma tasan bata latti balle fashin makaranta,gajiya tayi Iman da zama sai ta tambayi wata course mate ɗinsu Emmanuella da suke mutunci da ita akan akwai wani abu ne daya faru ranar Friday,Emmanuella ta cire mata biri har wutsiyar abinda ya faru harda shiƙiyancin da ƴan aji sukaita ma Sa'eeda akan rashin asalinta sannan kuma tace mata saurayin Sa'eeda ne Maryam zata aura in 2 weeks coming kafin exams.tashin hankali wanda ba'a saka mai rana,dole Sa'eeda taƙi zuwa makaranta, lallai ma Maryam wato kashedi haɗe da gargaɗin da ta mata bai shiga ƙwaƙwalwarta kenan.Ita tama rasa da wanne zata fara,shin kiran Sa'eeda zatayi taji halin da take ciki ko ta fara cin Uban ƴan aji lakada a waje,wata zuciyarta ne ta bata kyakkyawar shawara akan ta fara saita Maryam da muƙarrabanta sai daga baya ta kira Sa'eeda, hakan kuwa a kayi godiya tama Emmanuella sannan ta tashi daga seat ɗinta ta nufi seat ɗinsu Maryam wanda a lokacin suna hira abinsu cikin annashuwa,babu wanda yasan da zuwanta saidai sukaji saukan mara Tasss!!!! Tassss!!!! Babu wanda a cikin bai riƙe kuncinsa ba a tunanin kowa koshi aka mara amma jin babu abinda ya samu kumatunsu sukayi saurin kallon Maryam wacca a lokacin tayi sumar wucin gadi tsabar shigar marin,Rahma ta ɗan taɓa ta kamar an tsikareta ta dawo hayyacinta hade da sakin wata razananniyar ƙara wanda ya karaɗe ilahirin ajin ,babu shiri ƴan aji suka waiwayo jin wannan ƙara kamar drum,sai a sannan ne ta fashe da matsanancin kuka saboda ba ƙarya marukan sun shige ta matuƙar ainun.
Ita kuma Iman tana tsaye ƙyam a wurin sai wani jijjiga take riƙe da ƙugu,ga manya-manyan idanun nan nata sun kaɗa sunyi jajur kamar garwashi,duk wanda ya ganta a lokacin dole ya firgita ga wani huci da takeyi kamar wani kumurcin maciji mai jiran casss! yakai sará,cikin muryar da babu wanda santa dashi ba ta fara magana
"Wato kashedin da naki akan Sa'eeda bai shiga cikin ƙwaƙwalwarta ba ko ehhhhh!!!!! Ba nace ki fita a harkarta ba ko bance miki ba ehh!!! Ba dake nake ba kosai na ƙara saukar miki da wasu lafiyayyun marukan da sukafi na dazun zaki bani amsa !!! "
Diffff kamar an ɗauke ruwan sama haka Maryam ta tsagaita kukanta jin za'a ƙara mata wasu sabbin marukan da sukafi na ɗazun,cikin rawar murya haɗi da inda-inda ta fara magana
"Ehhh ddddda ddammman kin min kkashedi wallahi tallahi bani na fara mata magana ba ki yarda da........."
Kafin ta ƙarasa maganar taji Iman ta ƙara jefa mata wata tambayar
"Uban waye ya fara mata maganar a cikinku!!! "
Da sauri kowa ya nuna Rahma wacca tayi tsuru-tsuru da idanu kamar na mujiya,kafin ta lalubo amsar da zata ba Iman taji saukan maruka hagu da dama wanda lokaci guda duniyar ta fara mata juyi,wasu taurari tagani suna zagaye mata kai,haba itama razananniyar ƙara ta taki tare da fashewa da kuka tana taɓa kumatunta don ta tabbata suna nan ko ko sun cire.Haƙuri sukaita bata tare da cewa bazasu ƙara shiga sabgar Sa'eeda musamman ma Maryam tafi kowa a cikinsu bada haƙuri,buga desk ɗinsu Iman tayi da ƙarfi wanda saida suka ƙanƙame juna saboda ƙarar daya bada sannan ta ce
"Wallahi tallahi duk randa na sake ji daidai da rana ɗaya wata a cikin ko kuma ƴan aji tama Sa'eeda kallon hadarin kaji saina ci Ubansa lakada a waje sai kuma naga uban da zai tsaya mata,ƴan iska,musamman ma ke Maryam"
Nunata tayi yatsa sannan ta cigaba da cewa
"Ke gaki butulu mayaudariya,shegiya,munafuka,ke a tunanin Allah zai barki ne,kije ga auran kiyi wallahi ko ba daɗe ko bajima sai Allah ya sakama Sa'eeda tata-izan da gaggawa,sai Allah ya ɗaukakata sama daku,sannan kuma rashin asalin da kike cewa bata dashi in shaa Allah sai Allah ya sadata da asalinta,kuma inaji a jikina Sa'eeda ƴar babban gida ce, kaddara ce ta samesu ita da Ummanta,badai saboda ɗa namiji bane kika yiwa Sa'eeda muguwar sakayya to ki jira ƙarshanki keda munafin saurayin nata, wallahi da ƙafafunku zakuzo kuna roƙonta akan ta yafe muku la'anannu kawai,aje asha biki but put that at the back of your mind ƙarshanku yana nan zuwa bi'izinillahi!! "
Tabbas bama su Maryam da muƙarrabanta ba kowa a ajin saida jikinsa yayi sanyi don sun tsorata sosai da Iman,haka ta koma seat ɗinta ta zauna saboda natsuwarta ta dawo mata,sai can daga baya ta kira Sa'eeda wanda a lokacin bacci take sai Ummanta ne ta ɗauka,a nan ne ta sanar mata da Sa'eeda bata da lafiya an kwantar dasu a asibiti amma Alhamdulillah ta samu sauƙi, cikin ruɗewa Iman ta tambayi asibitin da aka kwantar dasu,babu ɓata lokaci Umman Sa'eeda ta sanar mata da sunan asibitin da numban ɗakin da aka kwantar dasu.*******
Cikin Labari
A hankali Sa'eeda ta farka daga bacci tare da motsa hannunta wanda babu canula jin kamar an riƙe mata hannun,da sauri Iman ta ɗago kanta jin Sa'eeda ta farka daga bacci,kallon junansu sukayi sai Sa'eeda ta sakarma Iman murmushi,ita ma mayar mata tayi da martanin murmushin sai ta ce
"Sa'eeda ya jikin naki,wallahi bansan baki da lafiya sai yau, dazu da naje school aka sanar min abinda Maryam ta miki sai na kira wayarki Umma ta ɗauka sai a lokacin ta sanar min da baki da lafiya kuma an kwantar daku a asibiti"
Cikin muryar marasa lafiya Sa'eeda ta fara magana
"Eh wallahi amma Alhamdulillah naji sauƙi sosai yanzu"
"Maa shaa Allah, Allah yasa kaffarane agareki "
"Ameen ya Rabbi"
Likita ne ya shigo tare da wata nurse tana biye dashi,dubata yayi tare da mata wasu tambayoyi,ita kuma amsa mata cikin sanyin murya, sai ya dubi Umman Sa'eeda ya ce
"Alhamdulillah jikinta ya samu sauƙi sosai don haka yau za'a sallame ku in shaa Allah tare da baku magungunan da zata dinga sha, ki kula da ita sosai sannan a daina barinta ita kaɗai tana tunani,saboda shiyake haifar da damuwa wanda a ƙarshe mutum yakan samu matsala ko ciwon hawan jini ya sameshi ko kuma ciwon zuciya,dan Allah a kula sosai"
"In shaa Allah likita zamu kula sosai"
Fita yayi shida nurse ɗin,sai Iman ta bisu waje don tanason ta biya kuɗin sallama da na magani,nurse ɗin ce tayi directing ɗinta kun chasheir don ta biya kuɗin.Bayan ta biya ne sai ta komai ɗakin wanda a lokacin Umman Sa'eeda na haɗa kayansu sai a sannan ne ta faɗa ma Umman Sa'eeda akan ta biya kuɗin sallama dana magani su wuce kawai gidan yanzu.kasa magana Umman Sa'eeda tayi don batasan wani irin godiya zatama Iman ba saboda ta taimake su sosai da badan zuwanta ba da shikenan kuɗin da take saving na registration ɗin Sa'eeda zata cire ta biya.Iman tasha godiya sosai wurin Umman Sa'eeda harda ita kanta Sa'eedar,haka suka ɗunguma suka nufo gida a motar Iman.
Bayan sun sauka ne sai Umman Sa'eeda da Sa'eeda suka nufo cikin gidan ita kuma Iman ta tsaya kashe motarta,a lokacin su Umma Kande da Maman Jummalo kowa da ɗaurin ƙirji sun baje kan tabarma suna hira abinsu,da sallama suka shigo gidan amma babu wanda a cikin ya amsa masu saima Umma Kande da ta miƙe kamar an tsikareta tare da cewa
"Yiririiiii! Wata sabon gani,ƴan zubar da cikin ne sai yau Allah yayi dawowarku gida,ai bamu san asibitin ba da kun ganmu"
Iman ce da shigowarta gidan kenan taji kamalan Umma Kande,kasa daurewa tayi saida ta mayarwa Umma Kande da martani
"To tsohuwar kilaki,mai kama da gwaggwan biriya,mai baki saikace na jaɓa,yaranki ne zasu zubar da ciki ba Sa'eeda,shaiɗaniyar tsohuwa kawai"
"Aww iyyeeee,ke kuma waya sako bakinki a ciki maganar gida ehhh"
Kafin Iman ta mayar mata da martani Umman Sa'eeda taja hannunta suka shiga ciki,saboda batason tashin hankali,haka ta zaunar da ita tare dace mata karta biyema haukansu don ita mahaukata ta ɗaukesu.
Haka Iman ta wuni a gidan sai da yamma ta wuce gida tare da tabbatar ma Sa'eeda zatazo gobe dubata in shaa Allah.
Kusan sati biyu Sa'eeda tayi tana shan magungunanta,Alhamdulillah babu laifi sauƙi yazo domin yanzu har ƴar ramar da tayi ta ciko ga haske da fresh da jikinta ya ƙara kasancewar bata zuwa makaranta taimakonta ɗaya sun gama lectures ɗinsu gaba ɗaya,revision kawai da tutorial sukeyi a aji.
Kasancewar yau asabar Umman Sa'eeda bata fita shara ba,suna zaune dukkansu a ɗaki suna ƴar hirarsu ta uwa da ɗiya,sai a sannan Sa'eeda tayi tunanin ta sanar ma Ummanta shawarar da ta yanke game da karatunta,ƙara gyara zama tayi sannan ta fara magana da cewa
"Ammm Ummina daman inaso da sanar miki da cewa kawai zan ajiye karatuna saboda ƴan ajin mu basa sona ga iya shegen Maryam takemin ita da ƙawayanta"
Shiru Umman Sa'eeda tayi tana kallon ƴarta ta cike da dunbin mamaki,a ce duk wahala da suka sha a baya sai yanzu da baifi saura shekara ɗaya ba amma ta ce ta fasa,haƙiƙa ran Umman Sa'eeda yayi ƙololuwan ɓaci jin kalaman ɗiyarta ta,cikin takaici da baƙin ciki Umman Sa'eeda ta fara magana
"Lallai Sa'eeda ashe ina miki kallon mai hankali da tunina ashe ba haka kika ba,yanzu saboda ƴan ajinku da Maryam zaisa ki fasa karatunki Sa'eeda, mai ya shiga ƙwaƙwalwarki ne Sa'eeda, ina jarumtar da nasanki da ita,ina NACIN da nasanki dashi akan karatu,ina kika kai so da ƙaunar da kike ma karatunki,ina yake Sa'eeda,yanzu duk wahala da nasha babu ko sisin mahaifinki akan karatunki zai tashi a banza kenan Sa'eeda,sakayyar da zakimin kenan a matsayina na mahaifiyarki wacca bata da wani buri illa ganin rayuwarki ta ginu,ban damu da ci ko sutura mai kyau ba duk ganin rayuwarki ta ginu amma aaaam.........."
Fashewa tayi da matsanancin kuka harda shessheƙa,da sauri Sa'eeda da dawo hayyacinta daga tunanin da da nasanin faɗawa mahaifiyar wannan magana,cikin rawar murya Sa'eeda ta fara magana cike da dana sani
"Ummina kiyi haƙuri don Allah ki daina kuka,wallahi na haƙura zan cigaba da karatuna Ummina, ki yarda dani Ummina"
Girgiza mana kai Umman Sa'eeda tayi tare da cewa
"A'a Sa'eeda shikenan ai sai ki haƙura da karatun naki,saboda wasu wa'inda basu suke baki ci da sha ba kikeso ki rushe tsarin ginin rayuwarki Sa'eeda, saboda wani can banza wanda baisan kina sonsa ba kikeso ki lalata rayuwarki Sa'eeda, ina juriya da jarumtar dana sanki da ita,ina kika kaisu Sa'eeda!!! "
Tabbas maganganun Umman Sa'eeda ya ratsa ƙashi har zuwa ɓargon Sa'eeda sannan ya shiga kusufa-kusufa na jini dana jijiyar Sa'eeda tabbas yanzu zata dawo da NACINTA a karatu,sannan tana saka ran NACINTA ZAI JAWO MATA NASARA,dole ne ta farka daga nauyayyen bacci da take,dole ne ta iya fuskantar kowani irin ƙalubale a rayuwarta,cikin dakiya tare da tabbatarwa Sa'eeda ta fara magana
"Na ɗau miki alƙawari Ummina, zan dawo da juriya da jarumtar da kika sanni da ita,zan kasance jaruma mai fuskantar kowani irin ƙalubale da zaizo min a rayuwa,zan dawo da NACINA domin zai JAWO MIN NASARA babba a rayuwata,ki yarda dani Ummina,daga ranar irin ta yau na cire so da ƙaunar da nikewa Sauban a zuciyata,bazaki sake jina da maganar Sauban ba koda shi ne autan maza,in shaa Allah zan cigaba da addu'ar Allah ya zaɓamin wanda ya fisa zama alkhairi a rayuwata"
Jinjina kai Umman Sa'eeda tayi saboda ganin gaskiya tare da tabbatuwa a cikin zantuttunkan ƴarta,murmushi ta saki sannan ta ce
"Dakyau sanyin idaniyata,haƙiƙa naji daɗin cire Sauban da kikayi a zuciyata sannan da maida hankalinki da zakiyi a karatunki,Allah ya miki zanbin miji na gari mai sonki da ƙaunar,ya baki nasara a karatunki,ya tsare gabanki da bayanki,ya miki katangar ƙarfe tsakaninki da maƙiyanki,ya albarkaci rayuwarki baki ɗaya"
"Allahu Aaaamen Ummina, in shaa Allah daga yau kin daina kukan baƙin ciki a kaina saidai na farin ciki"
"Allah ya yarda sanyin idaniyata"
Haka suka cigaba da hirarsu cike da annashuwa kamar ba wani ɓacin rai mai samesu ba,tun daga ranar Sa'eeda tayi deleting contact ɗin Sauban,messages ɗinsa,hotunansa,da komai nasa a wayarta sannan ta ƙara bada himma a kan karatunta saboda exams ɗinsu baifi saura kwana biyar ba.Wannan kenan.
TUNATARWA
******Ƙalubali ga mata masu makauniyar soyayya,kusani wasu mazan suna amfani da wannan damar ne don su cimma wata manufa tasu a gareku saboda suna ganin baza ku iya rayuwa babu su ba,tabbas wannan hanya ce dayawa daga cikin maza suke amfani dashi wurin lalata rayuwar mata wanda daga ƙarshe zusa wulaƙantasu,su ɓata tarbiyyar ta iyayensu suka daɗe suna ginawa,mu kula ƴan uwana mata,Allah ka tsaremu da samari shaho,ka haɗamu da masoyanmu na gaskiya.
Ƙalubale ga mata masu bayyana sirrikansu da ƙawayen,kamar caka ma kanka wuƙa kake ba tare da kasani ba domin wasu ƙawayen ba tsakani da Allah suke tare da suke,bayan haka ma ɗan Adam yakan canja daga yadda kasansa,mu kula ƴan uwana mata,Allah mana tsari da ƙawayen banza masu nuna suna son a bayyane amma a ɓoye suna sukarmu******
@@ @@@@@@@
Ɓangaren Sauban sai shirya-shiryan bikinsa yake yama manta da wata Sa'eeda a rayuwarsa hasalima komai nata ya gogeshi a wayarsa,hankalinsa kacokar ya koma kan Maryam saboda a ganinsa tafi Sa'eeda wayewa gashi bata da asili.
Kasancewar yau asabar saura ƴan kwanaki bikinsa,yana zaune shida da amininsa Captain Fu'ad suna tattaunawa game da bikin wanda Captain Fu'ad ya gaza haƙuri saida ya yayi masa magana saboda abin na ci masa tuwo a ƙwarya
"A gaskiya Sauban bazan ɓoye maka ba,kaci amanar Sa'eeda wallahi,mai tayi maka da zaka mata irin wannan muguwar sakkaya,in fact bama kai kaɗai harda wacca zaka aura,guna ganin kun mata adalici ne musamman ma kai"
Taɓe baki yayi irin ko a jikinsa ɗin nan, a da baiso tanka masa ba sai kuma yace
"Naci amanarta huhhhh!!!,mai zanyi da marar asali wacca bata waye ba,kai ko ɗan taɓa hannun Sa'eeda ban taɓa yi ba,common outing Sa'eeda bataso wai sai munyi aure,haba i'm tired of her stupidity "
Girgiza kai Captain Fu'ad yayi tare da cewa
"Marar asali kuma,bata da mahaifi ne?"
"No tanada mahaifi saidai mamanta da kakarta tsintarsu akayi a titi suna gararamba"
"Innalillahi Wa'inna Ilahi Raji'un yanzu saboda wannan ne yasa ka fasa auranta Sauban,ina hankalinka da tunaninka ya shiga ne,who knows asiri akama kakarta ko kuma ƴan gudun hijira ne,haba Sauban wallahi kaban mamaki,tukunna ma waya faɗa maka bata da asali"
"Ƙawar Mum ce sannan kuma Aunty Maryam ta sanar mata hakan kuma kasan ba ƙarya zata faɗa ba"
"Mata! mata! Akwai makirci wallahi, yanzu in mum ta kasa gane makirci ne suka ƙulla don ka auri Maryam kai bazaka iya hankalta ba Sauban"
"Mtssss! Don Allah mubar zancen nan mukoma yadda zamu tsara bikin kaina ma harya fara ciwo"
"Dawa Allah ya sawwaƙe ni Fu'ad na zauna don aci amanar wata,Allah ya kiyaye,ai tunda nasan dalilin rabuwarka da Sa'eeda wallahi kaji na rantse bazaka ga ƙeyata a bikinka ba domin ni ba mayaudari bane"
Sauban kallon Captain Fu'ad yake da mamaki sai kuma yace
"Mai zai hana ka aureta mana sai ka tusa mana baƙin ciki"
Dariya Captain Fu'ad yayi sai ya ce
"Wallahi da badan ansa ranar aure na ba da kuwa babu abinda zai hana na aureta saboda she is complete"
"Can ta matse maka"
"Kasani Allah baya barin hakƙin wani akan wani,kaji tsoran Allah Sauban, kasan yanzu wani hali take ciki dul saboda kai,in shaa Allah sai Allah yabata wanda ya fita komai wallahi kuma muna nan dakai"
Fuuuuuuu ya ɗau makullin motarsa ya ƙara gaba ba tare da yama Sauban Sallama.wannan kenan
@@@@@@@@
Ɓangaren Umma Kande ita da Maman Jummalo komai na tafiya musu normal,kamar kullum yau ma suna zaune a kan tabarma suna hirarsu cike da annashuwa kawai sukaga mutum ya faɗo cikin gidan babu sallama, haba da sauri suka miƙe dukansu,cikin tashin hankali Maman Jummalo tace
"Ni Hasfy wazan gani haka babu ɗan kwali balle hijabi,meya sameki....................
Mu haɗu a pages na gaba domin cigaba da suburbuɗo muku wannan cakwakiyar labari🙃🙃🙃💘💘💘💖💖💖✍️✍️
*****tofa,wacece a cikin yaranya su Umma Kande ta shigo babu ɗan kwali balle hijabi
Ku cigaba da zubo ruwan comments🤗🤗🤗🙃🙃🙃💝💝💝,Ni kuma bazan gaji ba wurin suburbuɗo muku da zafafan updates wa'inda zasu nishaɗantar,ilmantar tare da faɗakar daku🤗🤗🙃🙃💝💝🌹🌹🌼🌼🏵️🏵️
Ina matuƙar alfahari daku my Esteem fans,Allah yabar ƙaunar🤗🤗🙃🙃💝💝🌹🌹🌼🌼🏵️🏵️💖💖💗💗💓💓
Daga alƙalamin
🖍️📚Narrnarhh Bukar 📚🖍️
Comments and share 🙏🙏🙏Fisabilillah.
[5/23, 8:09 AM] Narnarhh Bukar: 🏵️ NACINA YA JAWO MIN🏵️
Narrnarhh Bukar✍️
🌹Perfect Essential Writer's
Association🌹
✨ P. E. W. A✨
Wattpad:@AISHAABUBAKAR812
Arewabook:@Narrnarhh002
Masu telegram zaku iya following ɗina ta wannan link ɗin🤗,🙃🏵️👇👇👇
https://t.me/+439Pdx2UbLZlOTNk
🌹🌹🌹I'm not born to be a writer but born to be a great professional writer✍️✍️✍️🙃🙃🙃🌹🌹🌹
🌼🌼🌼Special greetings to y'll my Esteem Fans🙃🙃🙃💖💖💖🌼🌼🌼
33----34
Ɓangaren Umma Kande ita da Maman Jummalo komai na tafiya musu normal,kamar kullum yau ma suna zaune a kan tabarma suna hirarsu cike da annashuwa kawai sukaga mutum ya faɗo cikin gidan babu sallama, haba da sauri suka miƙe dukansu,cikin tashin hankali Maman Jummalo tace
"Ni Hasfy wazan gani haka babu ɗan kwali balle hijabi,meya sameki Jummalo? "
Wuri-wuri takeyi da idanunta kamar wata motsattsa,gata tayi baƙi sosai kasancewar bleaching take,yanzu babu kwanciyar hankali balle a shafa cream😀.Maman jummalo ce ta riƙo hannun Jummalo da sauri Jummalo ta fizge hannunta tana ja da baya tare da girgiza kai hawaye na zuba a bisa kuncinta ta ce
"A'a! A'a! Karki taɓani mama,wallahi nayi da nasanin zamowarki uwa a gareni,baki bani tarbiyya mai kyau ba,kin ɗorani akan turbar son abin duniya da dogon buri,gashi tun a daren farkona naaa........."
Bata ƙarasa abinda tayi niyyar faɗa ba Umma Kande tayi saurin rufe mata baki,ita kuma Maman Jummalo ta jata ɗaki har uwar ɗaka tare da rufo ƙofar har da jan labulan windo don kar ajisu,suna shiga ɗakin Jummalo ta ƙara fizge hannunta daga hannun Maman Jummalo don yanzu ta ɗau ma kanta alƙawarin baza da sake biye musu sukaita ga halaka,zama Jummalo tayi akan gado su kuma suka zauna kusa da ita duk hankalinsu a tashe.Lokaci guda ta fashe da matsanancin kuka harda shassheƙa,bata jira mai zasu ce ba tara magana cikin shassheƙan kuka mai ratsa zuciya
"Nayi nadama tafi dubu,nayi da nasani tafi cikin kwando,kaicona da biyewa ruɗin duniya,Mama kin cuce rayuwata,kin cuceni Mama,baki bani tarbiyya mai kyau ba,Allah sarki babaaaa naaaaa!!!........."
Ƙara sakin wani sabon kukan tayi mai ƙarfin gaske,Umma Kande ce tace ta rage sautin muryarta kar ajisu,galla mata harar tayi sannan ta cigaba da maganarta,ita dai Maman Jummalo kallon ƴarta take babu ko ƙiftawa saboda muguwar ramar da tayi,ga wani mugun baƙi da tayi kamar baƙin tukunya.
"Tun ranar da aka kaini gidan aurena,a ranar na fara fuskantar baƙin ciki da tsangwama,ga duka,zagi,tozarci,aikin wahala duk babu wanda bangani ba a zaman aurena,kullum cikin baƙin ciki da da nasani nake akan biye muku,Allah ne yanzu ya kuɓutar dani,kuma daga yau bazan sake biye muku ba sannan su Zaliha da Iklima ku gaggauta zuwa ɗaukosu saboda nasan suna cikin halin dana tsinci kaina a ciki,kuma ku jini dakyau wallahi na daina biye muku ,sannan Islamiya zan koma in shaa Allah"
Miƙewa tayi ba tare da ta kallesu ba ta fito falon ta ɗau buta don zagayawa,su kuma su Umma Kande binta sukayi da kallo,sai can Umma Kande ta fara magana cike da damuwa
"Mun shiga uku ƙawas,anya ba zuwa zamuyi muga halin da su Zaliha suke ciki ba"
"Hmmmmm ni nama kasa magana wallahi don bansan me zance ba Ƙawas,kinsan me kawai gobe da sassafe mu shirya muje gidan nasu,inta kama ɗaukosu zamuyi kawai mu ɗaukosu,ji yadda Jummalo ta kuma don Allah"
"Allah ya kaimu,a gaskiya hankalina yayi ƙololuwan tashi ganin Jummalo a irin wannan hali,amma a gaskiya boka Sankeru bai mana adalci ba,ai ba haka mukayi dashi ba,daga munce munason yaranmu su samu mazaje masu kuɗi kawai zai haɗasu da bala'i,kai kai kai ni Saratu jikar sarkin ruwa munga takanmu"
Haka sukaita jimamin abinda ya samu yaransu,Jummalo kuwa zama tayi ta basu labarin tun daga daren auranta har zuwa yau da wuya tasata barin gidan afujajan babu ɗan kwali balle hijab.Umma Kande ta shiga tashin hankali tare da zullumin su Zaliha da Iklima ko a wani hali su kuma suke ciki da mazajen nasu,idan ita Jummalo mai shan giya ne mijinta su kuma fa gashi daman suna son saka ranar zuwa gidan kowaccansu saboda basu taba zuwa ba,sai gashi kan susa ranar zuwa Jummalo tazo musu da labarin da ya kirkita musu ƙwaƙwalwa tare da lissafi.
@ @@@@ @@@@ @@@@
Ƙarfe 9:45am na safe su Umma Kande da Maman Jummalo suka shirya tsaf don zuwa gidajen su Zaliha, Umma Kande ce ta bada shawarar su fara zuwa gidan autarta Iklima sai daga baya su zarce gidan Zaliha, haka kuwa akayi direct suka ɗau drop ɗin keke napep har gate ɗin gidan Iklima,basu sha wahala ba kasancewar layinsu Iklimar sananne ne.Bayan sun sauka daga keke napep ɗin, sai Maman Jummalo ta biya mai keke napep kuɗinsa sannan suka nufa gate ɗin gidan,babu laifi gidan hadɗaɗe ne ya tsaru iya tsaruwa,ga wasu flowers masu ban sha'awa an shukasu a gefe-gefan gidan masu launin orange colour da milk,kowannansu bakin buɗe yana kallon kyau da tsarin gidan wanda ya tafi da imaninsu,Maman Jummalo ce ta ce
"Kai gidan nan ya tsaru saikace a ƙasar waje?"
"Ke dai bari Ƙawas ni namá kasa cewa komai,don gidan nan ya tafi da sauran imanina"(Tofa Umma Kande ɗan sauran imanin naki gida ya tafi dashi tun kan ki shiga ciki,jahilci baiyi wallahi😂😂😂)
Ƙarasawa sukayi bakin gate ɗin gidan tare da ƙwanƙwasawa,shiru babu amsa,ƙara ƙwanƙwasawa sukayi,sai a sannan mai gadin gidan ya buɗe ƙofar,kallonsu yayi ƙasa da sama kafin ya ce
" lafiya,wa kuke nema"
Gyara tsayuwa Umma Kande tayi irin gamai ɗiya tana auran mai kuɗi ta ce
"Munzo ganin ƴar muce Iklima fatan dai tana nan"
Shiru yayi mai gadin yana kallansu sai can kuma ya ce
"Ina zuwa"
Bai jira mai zasu ce ba,ya juya tare da kulle ƙofar ya nufa ɗankinsa ya ɗauko waya haɗi da kiran mai gidansa,kira yakai sau uku yayi masa,sai ana huɗun ya ɗauka,cikin girmamawa ya fara gaida mai gidan nasa sannan ya ce
"Yallaɓai iyayen madam ne sukazo amma nace su jira sai na kirata"
A can mai gidan nasa ya bashi amsa da cewa
"Good,ka barsu su shigo,amma idan sun shigo tsakiyar gidan bayan ka kulle ƙofar sai ka sakar musu Pistol da Ninja su tayasu exercise"
"An gama yallabai"
Katse wayar yayi tare da sakin wani munafikin murmushi,har ya fara harsashen yadda zasu kaya da Pistol da Ninja.
Kamar yadda mai gidansa ya umurcesa haka yayi,bayan su Umma Kande sunkai tsakiyar gidan,sai ya kulle ƙofar gidan tare da nufar cages ɗin Pistol da Ninja,ya buɗe kowannan su,fitowa sukayi tare da girgiza jikinsu,manyan karnuka ne na turawa baƙaƙe,kumatunsu duk sun zazzago ga miyau da dalala,fuskar nan tasu a kwaɓe take,haba kamar jira suke,tunda sukayi tozali dasu Umma Kande suka nufo inda suke da gudu tare da haushi ganin baƙi a gidan.
Umma Kande da Maman Jummalo da basusan meke faruwa ba,suka ji haushin karnuka a bayansu,juyawar da zasuyi sukayi aran gama da jibga-jibgan kurnaka wanda tunda suke basu taɓa ganin irinsu ba,ganin kansu karnukan sukayo,habawa ƙafa mai naci ban baki ba,kowa sakin jakarsa yayi ya fara gudu,karnukan biyosu sukayi,gudu suke suna ihun a kawo musu ɗauki amma ina gidan shiru alamun babu kowa,Umma kande ce tana gudu tana da cewa
"Mun mutu mun lalace! Mun kawo kanmu ga halaka! Jama'a! Jama'a! A kawo mana ɗauki zasu cinyemu ɗanye! Wayyo ni Sarere jikar sarkin ruwa! Iklima dan Ubanki ki buɗe ƙofar! Iklima! Iklima! Auta! Auta buɗe mana ƙofar! Karnuka zasu cinyemu! Iklima!!! "
Haka tayita nanatawa tana gudu,zaninta ma da yaji wahala saida ya kwance,saukinta ma akwai skirt da abin ya munana kasancewar tana da manyan ɗuwawuka,sai saɓaɓar saɓaɓar suke tana gudun.Ita ko Maman Jummalo babu bakin surutu sai ihu,mai gadi dai na zaune akan benchinsa sai video yake musu yana dariya,saboda yadda suke ihun da gudun dole idan ka gani ya baka dariya,karnuka bisun suke babu ƙakƙautawa,idan sukeyi hagu suma suyi hagu haka idan sukayi dama suma suyi dama,abin gwanin ban dariya.
Iklima dake baccin wahala kamar a mafarki taji muryar mamanta tana kiranta ta kawo mata ɗauki,buɗe idanu tayi tare da sake jin tabbas muryar mamanta ne da Maman Jummalo suna ihu,da sauri ta sauko daga kan gaɗon ta nufo falo tana tafiya a gwale kamar wacca aka mata kaciya haka nufi wurin windonta tare da jaye labulan,zaro idanu tayi waje tana ganin yadda Maman Jummalo da mamanta babu zani a jiki suke shan gudu babu ƙakƙautawa ga karnuka na biye dasu a duk inda suka nufa suna haushi,da sauri ta buɗe ƙofar tare da kiransu Maman Jummalo da mamanta, ai a sittin sukayo ɗakin suma karnuka basu fasa binsu ba,saura ƙiris karnukan su shigo ɗakin,Allah ya taimake su Iklima tayi saurin rufe ƙofar ɗakin.
Su Umma Kande na shiga falon kowaccansu ta baje a ƙasa tana haki,ga uban zufar da take tsuttsugo musu a duk ilahirin jikinsu sai kace sunyi gudun kilometer 3 haka suke ji.
Iklima ce take bin kowaccansu da kallo,kallon ma irin na takaici sai kuma can ta ce
"Yanzu saboda ɗan wannan gudun da kuka sha kuke haki haka,Allah ya bani haƙuri nida kusan kullum sai maza sama da biyu sun afkamin ta gaba da ta baya"
Zaro jajayen idanunsu sukayi suna kallonta cike da mamakin furucinta,Maman Jummalo ta ƙara tambayarta don ta gasgata zancen nata
"Maza sama da biyu suke afka miki Iklima,to shi ina mijin naki? "
Taɓe baki tayi irin na autoci sannan ta ce
"Harda dashi ai,a daren farkona ma a ta duburana ya biya buƙatarsa,sannan bayan kwana hudu yazo da abokansa kusan su uku sukayi lalata dani,ta baya da ta gaba,kuma tun daga wannan ranar kusan duk sati sai sunzo sunyi lalata dani gashi harda videon abinda suke aikatamin yake,yanzu tafiyata ma ta canja,a gwale nake tafiya saboda muƙurƙusar da nake sha gunsu"
Kowacce a cikin zaro idanunta tayi waje tare da dafa ƙirji kamar haɗin baki,Umma Kande ta fara magana da cewa
"Innalillahi Wa'inna Wa'innar Raji'ana,Iklima shi ne tunda muke waya dake baki taɓa sanarmin ga halin da kike ci ba,na shiga uku ni Saratu,mun kawo yaranmu cikin bala'i,innalillahi Wa'inna Wa'innar Raji'ana,Sambuhanillahana!!! " (My Esteem Fans ku koyi Innalillahi wurin Umma Kande tare da Sumbuhani.....kai! kai! kai! bazan iya ƙarasawa ba😂😂😂😷😷😷)
"Yamin kashedi akan kar na sanar ma kowa idan ba haka ba,zai ɗora videos ɗin da yimin a sanda suke lalata dani a social media kowa ya gani"
Maman Jummalo ce ta cire tagumin da tayi sannan ta ce
"Hmmmm ni nama sara mai zance yanzu,kalmomi duk sun ɓacemin,ƙwaƙwalwata ta rikice ta daina bani haɗin kai,ke yanzu Iklima ko guduwa kin kasa yi,ace kina cikin irin wannan mawuyacin hali kin zauna kina kwasar baƙin ciki Iklima ummm"
Zama Iklima ta gyara a hankali kamar wacca akama kaciya sannan ta ce
"Nayi yunƙurin guduwa amma ban samu dama ba,ni tsorana ma yanzu kar yazo shida la'anannun abokannan nasa su afka muku"
Ai da sauri suka kai dubansu ga Iklima jin abinda take faɗa,nan da nan suka rikice suna dube-dube kamar sunyi ajiya duk tsabar ruɗewa ne da sukayi,Umma Kande jikinta na ɓari ta fara magana
"Mun shiga Uku mun lalace,su afka mana kikace Auta,yanzu ya zamu gudu daga gidan nan harda ke"
Maman Jummalo ce ta cafke maganar da cewa
"Iklima musan abunyi kar mutanan suzo gidan nan mu shiga Uku"
Dogon tunani Iklima ta lula,tare da tunanin yadda zasu kuɓuta daga hannu mijin nata da abokansa,dubara ce tazo mata sai ta dubi su Umma Kande tare da cewa
"Mafita ɗaya ce yanzu,akwai ƙofar sirri wacca idan misali gidan yayi gobara mutane suke fita don su samu su tsira da rayukansu,amma yanzu matsalar saina nemi key ɗin ƙofar wacca zata sadamu har wajen gidan ba tare da mai gadi yasan da fitarmu ba,bara in tashi yanzu nan kar suzo don nasan suna hanya wallahi"
Ƙara rikice su Umma Kande sukayi jin ƙilama suna hanya,a gwale Ikilima take tafiya tana botsaro ɗuwawunka waje ta nufi gun drawers ɗin bedroom tana dubawa,suma tayata dubawa sukayi,daƙyar Iklima ta gano key ɗin,ai da sauri tabama su Umma Kande manyan hijabai kasancewar sun zubar da gyaluluwansu a sanda karnuka suka biyosu,harda zani Iklima taba Umma Kande, komai nata ta ɗauko har kuɗi masu yawa da mijin nata yasa a jaka ta ɗauko suka nufo ƙofar,cikin sa'a ta buɗe suka fito ta wani layin daban,samun mai keke napep sukayi babu ciniki suka shiga,sai a sannan ne Umma Kande ta sauke nauyayyen ajiyar zuwa tana da cewa
"Kaiiiii! Wannan bala'i haka,hmmmm"
Maman Jummalo itama ta sauke nata ajiyar zuciyar sannan ta ce
"Yanzu gidan Zaliha zamu nufa ko sai gobe"
"Sai gobe mana,yanzu direct zamu fara zuwa asibita a duba Auta,don gaskiya a yadda take tafiya ya nuna akwai matsala"
"Hakane "
Haka suka nufi asibitin da Iklima don a dubata,bayan likita ta dubata sai ta fito tare da cema su Umma Kande su biyota office rai a bace.Isarsu office keda wuya ko zama basuyi ba likita ta rufesu da faɗa akan ya zasu bar ƴar yarinya wacca bata girma cikin irin wannan halin,sannan suwa suka mata wannan muguwar aika-aikar.Tsuru-tsuru sukayi da idanu babu amsa,to wai me zasu ce bayansu suka siya wahalar da kuɗinsu,haka likita tayi masifarta ta gama ko ummm babu wacca tace a cikinsu.Likitar ce ta ce za'a ba Iklima gado saboda an illata ta sosai Allah ma ya rufe asiri bai kai stage ɗin da kashi zai dinga fito mata ba bisa ƙa'ida ba saboda afka matan da akai ta dubura.
Kasancewar akwai kuɗi a hannun Iklima wanda ta ɗauko na mijinta ,dashi suka biya kuɗin asibitin sannan aka bata gado,Maman Jummalo ce ta zauna da Iklima sai Umma Kande taje gida kiran Jummalo dan ta zauna da ita saboda gobe suke so suje gidan Zaliha suga ita wani kalan bala'i take a ciki.
Haka kuwa akayi,Jummalo ce ta zauna da Iklima,sai suka bata kuɗaɗan da zasuyi amfani dashi,sai suka tafi gida.
@@ @@@ @@@@ @@@@
Washe Gari
Kamar jiya har yau da safe suka nufi gidan Zaliha, amma a wannan karan basuyi kalle-kallan gida ba saboda wuyar da sukasha jiyan,bayan mai keke napep ya saukesu,sai suka sallameshi,gabansu na dukan uku-uku suka ƙwanƙwasa gate ɗin gidan,wani basamuden ƙato ne ya buɗe ƙofar gidan,ja baya su Umma Kande sukayi ganin wani gabjejan ƙato ga kwalli ya rambaɗa a idanunsa sai mazurai yake,cikin deep voice irin na manya-manyan gardawa ya ce dasu
"Wa kuke nema!"
Inda-inda suka fara yi,kowacce ta kasa magana,sai can Maman Jummalo tayi kasadar fara magana,wacca a rikice takeyin maganar haɗi da inda-inda
"Ammm amm amm dddamman wwwurinnn Zzzalihaaaa mukazo neeee yeeee"
"Ina zuwa"
Haka kawai yace musu ya kulle ƙofar,sauke ajiyar zuciya su Umma Kande sukayi a tare sai Maman Jummalo ta ce
"Oonii Hasfy!! Yara duk babu sa'a,Allah yasa gidan babu karnuka irin gidan Iklima"
"Ameen dai Maman Jummalo dako mun shiga uku"
Bayan mai gadin ya kulle ƙofar sai ya kira Ogansa akan iyayen Zaliha sunzo wurinta,dariya Ogan nasa ya tintsire dashi tare da cewa
"Aikin gama ya gama ai,barsu su shiga su ɗau sauranta"
"To Oga"
Katse wayar yayi sannan ya buɗe musu ƙofar suka shiga.Cikin sanɗa su Umma Kande da Maman Jummalo suka fara tafiya saboda tsoran kar suma sunada karnuka irin gidan Iklima. A haka har suka isa ƙofar ɗakin tare da ƙwanƙwasawa.
Zaliha dake a zaune a falon ta ce a shigo kasancewar ƙofar kodayaushe a ɓude take ba'a sa mata key,saida ta maimaita a shigo har sau uku sannan su Umma Kande suka shigo kasancewar Zaliha bada ƙarfi take magana ba,shigarsu ɗakin suka fara salati haɗi da sallalami,Umma Kande ce ta fara magana cike da ruɗewa
"Me zan gani ni Saratu! Zaliha haka kika koma,maiya sameki! "
Ɗan murmushin wahala Zaliha tayi sannan ta ce
"Kunzo ɗaukar gawata ne mama,Allah ya amsa addu'ana akan ƴan uwana suzo ɗaukar gawana saboda mutuwata tazo banaso in mutu a acikin ahalina ba,mama kin cuci rayuwata, kaicona da samun uwa irinki mai son abin duniya,gashi ta hanyar son abin duniyar zan rasa raina,don Allah mama ki roƙamin yafiya gunsu Umman Sa'eeda da ita kanta Sa'eeda akan su yafemin duk laifukan dana musu,son abin duniya ya kaini da halaka gashi mutuwata tazo"
Babu wacca a cikinsu bata zubda ƙwalla ba ganin yadda Zaliha jikinta ya koma kore shar ga idanunta sunyi yellow kamar wata aljana ba mutum ba,babban tashin hankali ma shi ne wani fari-farin ruwa yake fita a ta gabanta sai uban wari,cikin rawar murya Umma Kande ta ce
"A'a! A'a! Zaliha bazaki mutu ba,bazaki mutu ba Zaliha, muje asibiti Zaliha! Na shiga uku yau ni Saratu"
Girgiza kai Zaliha tayi tare da cewa
"Karku ɓata kuɗinku a kaina saboda ni tawa ta ƙare yannnnnzzzz......."
Tari ya saƙeta babu ƙakƙautawa a lokaci guda jini na fito mata ta baki ta hanci,da sauri su Umma Kande sukayo kanta tare da tallafota sukayo waje, sunci sa'a gidan a buɗe yake,direct sukayi hanyar waje,Maman Jummalo ce ta tarin musu keke napep suka shiga,cikin tashin hankali Maman Jummalo ta ce su tafi asibiti,a hanyarsu ta zuwa asibiti ne tari yasha ƙarfin Zaliha wanda a ƙarshe ta ce ga garinku nan.
Cak abubuwa suka tsayawa Umma Kande a ƙwaƙwalwarta,ji take kamar duniya ta juye babu sauran kows,lissafi ya ɓace mata kwata-kwata,wani ƙaramin hauka Umma Kande tayi a cikin keke napep ɗin tare da girgiza Zaliha wai ta tashi,amma ina rai yayi halinsa.
Haka akayi zaman makokin Zaliha wanda sai a lokacin Nusaiba ta dawo gida shima don kiranta akayi akan Zaliha ta rasu,da labarin abinda ke faruwa da ƴan uwan nata,tayi kuka tayi baƙin ciki sosai tare da godewa Allah da bata wanke fuskarta da wannan ruwan da boka Sankeru ya bada ba,da yanzu itama tana cikin tashin hankali.
Ko dayake hanyar da itama ta ɗauko ba mai ɗore mata bane,domin yanzu Nusaiba ta zama INTERNATIONAL HOMOSEXUALITY GANG STAR,tauraronta ne ke haskewa yanzu,bata waccar ƙasar bata waccan,har competition ɗin cin duri suke wanda yawanci ita ke ci,shiyasa bata cika zama gida ba saidai ta turo da kuɗi masu yawa,kuma Umma Kande da Maman Jummalo duk sun san mai take aikatawa amma ko ajikinsu tunda kuɗi na shigo musu babu ƙakƙautawa.
A haka a haka har akayi bakwan Zaliha sai a sannan ne Jummalo da Iklima suka dawo gida an sallamesu daga asibiti kasancewar yanzu Alhamdulillah sauƙi yazo ma Iklima,dan yanzu ta rage gwala ƙafa idan tana tafiya,kwana goma da rasuwar Zaliha Nusaiba ta koma ƙasar da tafito wato Germany,shi kuma Musa bai samu zuwa ba saida ya kira waya yayi ta'aziyya.Wannan kenan
@@@ @@@@@ @@@
A ɓangarensu Sa'eeda rayuwarsu na tafiya normal babu wata matsala,koda ma akayi rasuwar,tare dasu akayi zaman makokin,kasancewar Abban Sa'eeda ba'a hayyacinsa yake ba duk surutan da mazan layi suke masa akan yadda yaransa suka koma ko ajikinsa,hasalima idan ya tafi kasuwa bashi ke dawowa gida sai 8:00pm kuma yana dawowa yake wucewa turakarsa yayi kwanciyarsa,dayake yanzu lokacin rani ne baya zuwa gona,shidai rayuwa yakeyi gashinan gashinan dai.
Wasa-wasa lokacin exams ɗinsu Sa'eeda yazo kamar yadda tama Ummanta alƙawarin maida hankalinta kacokan a karatunta haka tayi,kwata-kwata ta daina tunanin Sauban aranta,gobe ne zasu fara exams duk shirin daya dace tayi duk tayi,a ranta take cewa
'I'm ready to face every single challenge in my life! I'm ready to face the battle with great speed! I want to become my own hero! Ready for whosoever come my way! I have change to a new version !!! '
Da wuri Sa'eeda taje hall ɗin exams ɗinsu,Iman ma acan ta sameta,shigorwa Maryam hall ɗin sai ƴan ajin suka kaure da ihun Amarya! Amarya!Amarya!
Sa'eeda taɓe baki tayi ko a jikinta,in fact ko kallon inda ake cewa ga Maryam ɗin batayi ba,focusing tayi ga summary dake a hannunta tana jiran su fara exams,haka suka fara exams,hall ɗin yayi tsit! Invigillators sai zagaye hall ɗin suka don tabbatar da tsakani da Allah ɗaliban suke rubuta jarabawan babu satar answer.
Bayan sun gama exams ne suka fito ita da Iman zasu nufo gida,Iman ce tama Sa'eeda raɗa a kunne tare da nuna mata wani abu da yatsa,Sauban ne yazo ɗaukar Maryam,kuma shiɗin Iman tama Sa'eeda raɗa a kunne ta kallesu.
Direct Sa'eeda fuska a ɗaure ta nufi inda su Maryam suke,Iman na kiranta amma inaaa,bata saurareta ba,saidai Iman ita ma ta biyota kar a samu matsala.Sa'eeda bata tsaya ko'ina ba sai a wurin inda Sauban yake,tsayawa tayi tare da kallonsa ido cikin ido ta fara magana cike da Izza wanda ba'a santa dashi ba
"To munafiki,mayaudari,annamimi,kai a tunanin zan mutu ne saboda soyayyar da nake maka ko! Never!!! Wallahi kayi kaɗan ɗan akuya,wato ka nunamin halinku na maza tare da waccan munafukar"
Nuna Maryam tayi wacca tayi mutuwar tsaye don jin irin lafuzzan dake fitowa daga bakin Sa'eeda wacca tasan bata magana,in fact ko yatsa kasa a bakin Sa'eeda bazata ciza ba amma yau gata tana magana cike da izza ta ƙasaita,katse mata tunani Sa'eeda tayi da cewa
"Ni Sa'eeda Sulaiman bana manta alkhairi haka zalika bana manta sharri, I hate deceivers in my life,ku jira ƙarshen ku ku ɗinnan"
Nunasu tayi sannan ta cigaba da cewa
"In shaa Allahu sai Allah ya sakamin tata-izan da gaggawa,wallahi wallahi wallahi idan inada da hakƙi daidai da ƙwayar zarra akanku sai Allah ya bimin hakƙina,sannan rashin asalina da kuke ta ja-inja a kai kusani,haka Allah yaso ya ganni kuma ina ji a jikina na kusa haɗuwa da ahalina,daga ƙarshe ina tabbatar muku da sai kunzo da ƙafafunku wurina kuna roƙon inyafe muku,trust me Sauban that time will surely come in shaa Allah"
Raf!Raf!Raf! Iman tayi da hannunta tare da jinjina ma Sa'eeda tabbas Sa'eedarta ta canja,Sa'eeda batabi takan mai zasu ce ba taja hannun Iman sukayi gaba.
Mutuwar tsaye Sauban yayi,saida ƙwaƙwalwarshi ta tafi wucin gadi na wasu seconds kana hankalinsa ya dawo jikinsa,Sa'eeda ce da wannan kalaman,yarinyar da batada magana,to yaushe ta fara zubo zance.(ba Sa'eedar da kasani a da bace ehe😏,ta yanzu bata ɗaukar raini🙃🙃🙃😂😂😂).
Juyowa yayi kan Maryam tare da hararta haɗi da cewa
"Uban me kike jira da baki shiga motar ba ehhhh!"
Da sauri Maryam ta shiga motar don yanzu tsoran Sauban take sosai,tunda ya mata dukan tsiya akan zagin Mom ɗinsa da tayi take shakkarsa,gashi ya hana a ɗauko mata ƴan aiki,ita take aikin gidan,har part ɗin Mom ɗinsa kasancewar a gidan suke da zama,babbar matsalar ma rashin iya girkinta,kasancewar ko a gida ƴan aiki suke musu girki shi kuma Sauban yace girkinta yakeso,kwaɓa takeyi wanda a ƙarshe saidai da zubar da abinci shi kuma waje resturant ya musu takeaway,sannan ya ce da ita zuwa resturant bazai fisshesu ba gwara ta koya girki ko kuma ya ƙaro wata(Tofa tun a first week of marriage an fara maganar kishiya,babbar magana su Maryam sai a gyara🤔🤔🤔).
Abu dayawa ga tsangwamawan da Mom ɗin Sauban take mata tun ran da ta zageta taji Maryam ɗin ta fitar mata a rai,sati guda da auransu amma tafara fuskantar challenges daban-daban.
Bayan Exams su Sa'eeda suka tafi IT a wajaje ma banbanta,sai bayan wata shida zasu dawo school kuma ajin ƙarshe wato 400 level.wannan kenan.
@@@@ @@@@@@@
ABUJA
Ƙarfe 2:30am na dare
Ɗaki ne mai duhu sai ɗan wani haske kaɗan da nake ɗan iya hangowa wanda bai wadaci ɗakin ba, ga tururin hayaƙi daya turniƙe ɗakin, ni kaina da kyar na iya shiga ɗakin haɗe da addu'a dan ɗauko muku rahoto, wasu surutai kamar suddabaru naji muryar wannan matar ta shekarun baya tana faɗi wanda nakasa gane mai ta ke cewa, kwatsam kamar wancan karon naga wani haske kamar walƙiyar ya ɓullo ta cikin bangon ɗakin ya haska ko'ina, wannan halittar nagani kamar mutum amma wada, kansa a ƙasa yake, shi baiyi ƙasa ba kuma bayi sama ba, yana a tsakatsaki, tsawansa bai wuce tsawan hannu ba, sai rangwajejan kai kamar ƙwarya,yanada idanuwa kamar na mage, da sharɓa sharɓan kafakuwa kamar na babban mutum, kai in taƙaice muku, halittar nan batada kyawun gani hasalima mai ciki zaka iyayin ɓari ganin wannan muguwar hallitta,sujjada tama wannan hallitar tare da cewa
"Yakai Sarkin Tsageru! yakai gagara badau!! , yakai buhun ƙara kafi ƙarfin danna!!!, ya kai Shugaban matsafan duniya!!! Haƙiƙa ka cika alƙawarin da ka ɗauka akan bayyanar bayan shekara biyar!!! "
Wata dariya naji har ƙasa na girgiza ashe wannan halittar ne ke busar dariyar, can ya tsagaita kamar ruwa ya ɗauke ya fara magana jikake kamar ƙasa zata tsage
"Karki yarda ayi auran!!! Karki bari ayi auran!!! Idan kuma ba haka ƙarshenki yazo Zulfa'u,yaaazoooo ƙarshenki Zulfa'u!!! "
Da saura ta ɗago kanta tana kallonsa don a gaskiya ita batasan da wani aure ba,to wani aure yake magana akai,kasa haƙuri tayi ta tambayesa cikin girmamawa tare da ƙan-ƙan dakai
"Ya kai Sarkin matsafan duniya, yakai Boka Burumbuɗu wani aure ne zan hana afkuwarsa"(daman sunan wannan halittar Boka Burumbuɗu,tabbb yaci sunnansa kuwa🤔🤔🤔😂😂😂😂)
Dariya ya tsintsire dashi har ƙasa na girgiza,sai kuma ya fara kuka ko'ina na ɗakin rawa yake can ya tsagaita tare da cewa
" Karki bari!!! Karki yarda!!! A hir ɗinki ki bari ayi auran..........
Mu haɗu a pages na gaba hmmmmm wuta kan wuta🔥🔥🔥🔥
****Auransu waye ne Boka Burumbuɗu yace kar Zulfa'u ta bari ayi????.......
****Shin su Umma Kande da Maman Jummalo sun tuba ko kohar yanzu basu saduda ba???........
****Yaya zamantakewar Maryam zata cika ba a gidan Sauban ganin tun a satin farko Maryam ta fara fuskantar ƙalubalai iri-iri???.........
Ku cigaba da zubo ruwan comments🤗🤗🤗🙃🙃🙃💝💝💝,Ni kuma bazan gaji ba wurin suburbuɗo muku da zafafan updates wa'inda zasu nishaɗantar,ilmantar tare da faɗakar daku🤗🤗🙃🙃💝💝🌹🌹🌼🌼🏵️🏵️
Ina matuƙar alfahari daku my Esteem fans,Allah yabar ƙaunar🤗🤗🙃🙃💝💝🌹🌹🌼🌼🏵️🏵️💖💖💗💗💓💓
Daga alƙalamin
🖍️📚Narrnarhh Bukar 📚🖍️
Comments and share 🙏🙏🙏Fisabilillah.
[5/23, 8:09 AM] Narnarhh Bukar: 🏵️ NACINA YA JAWO MIN🏵️
Narrnarhh Bukar✍️
🌹Perfect Essential Writer's
Association🌹
✨ P. E. W. A✨
Wattpad:@AISHAABUBAKAR812
Arewabook:@Narrnarhh002
Masu telegram zaku iya following ɗina ta wannan link ɗin🤗,🙃🏵️👇👇👇
https://t.me/+439Pdx2UbLZlOTNk
🌹🌹🌹I'm not born to be a writer but born to be a great professional writer✍️✍️✍️🙃🙃🙃🌹🌹🌹
🌼🌼🌼Special greetings to y'll my Esteem Fans,Ina ƙaunarku,ina alfahari daku domin da bazarku nake taka rawata🙃🙃🙃💖💖💖🌼🌼🌼
35----36
Wata dariya naji har ƙasa na girgiza ashe wannan halittar ne ke busar dariyar, can ya tsagaita kamar ruwa ya ɗauke ya fara magana ji kake kamar ƙasa zata tsage
"Karki yarda ayi auran!!! Karki bari ayi auran!!! Idan kuma ba haka ƙarshenki yazo Zulfa'u,yaaazoooo ƙarshenki Zulfa'u!!! "
Da saura ta ɗago kanta tana kallonsa don a gaskiya ita batasan da wani aure ba,to wani aure yake magana akai,kasa haƙuri tayi ta tambayesa cikin girmamawa tare da ƙan-ƙan dakai
"Ya kai Sarkin matsafan duniya, yakai Boka Burumbuɗu wani aure ne zan hana afkuwarsa"(daman sunan wannan halittar Boka Burumbuɗu,tabbb yaci sunnansa kuwa🤔🤔🤔😂😂😂😂)
Dariya ya tsintsire dashi har ƙasa na girgiza,sai kuma ya fara kuka ko'ina na ɗakin rawa yake can ya tsagaita tare da cewa
" Karki bari!!! Karki yarda!!! A hir ɗinki ki bari ayi auran jikarki da ɗa daga tsatson maƙiyiyarki,domin idan kika bari auran ya tabbatu,hooo hoo hoooo,asirinki na gab da tonuwa!!!
Tsuru-tsuru Haj. Zulfa'u tayi da idanu tana sauraransa,a zuciyarta tana cewa. 'Na shiga uku ni Zulfa'u daga wancan sai wancan,da wanne zanji,da farko ance karna bari muhadu da tsatsonta,yanzu auran da ma bansan da wanzuwansa ba ake cemin karna sake ayi auran,yau naga ta kaina'. Kamar Boka Burumbuɗu yasan mai take ayyanawa aranta ya ce
"Zulfa'u duk abinda muka sanar miki tabbatacce ne in har baki bi umarninmu ba! Kisani munyi iya yinmu domin mu halaka sauran ahalinta ammaa.....!!!
Wani irin gigitaccan kuka ya fashe dashi wanda duk ilahirin ɗakin na girgiza gashi shi kanshi ƙarar kukan babu daɗin ji,kai in taƙaice muku kamar saukan ruwan sama mai ƙarfin gaske haka kukan nasa yake.Yakai tsawan mintuna 10 yana wannan kukan,ita kuma Haj. Zulfa'u abin duniya ya mata katutu a yuwa,kanta a duƙe tana sauraran kukan nasa,sai kuma can ya tsagaita tare da cewa cikin amon muryarsa mai firgitarwa
" Basa wasa da sallolinsu biyar a duk rana,suna azkar ɗin safe da na yamma,suna nafilfilun dare,sun tsare yaransu da addu'o'i masu ƙarfi,mun kasa Zulfa'u!!! Mun kasa!!! "
Jinjina kai Haj.Zulfa'u tayi saboda abinda Boka Burumbuɗu zaice ya kasa to ba ƙaramin abu bane,tabbas ya zaman mata dole tayi taka tsantsan kar asirinta na shekaru aru aru su bayyana dako kashinta ya bushe,dole ta hana faruwan wannan auran duk da batama san dashi,wannan dole ne ta hana,haka tayi ta ayyana abubuwa a ranta kafin daga bisani Boka Burumbuɗu ya ƙara da cewa
"Zamu barki yanzu! Sai bayan shekara biyu wanda a lokacin zamu linka miki kariyar da muke baki sosai,domin lokacin abubawa zasu fara rincaɓewa,dole mu kareki Zulfa'u! Dole mu kareki domin kina mana biyayya tare da bin umarninmu haɗi da sharudɗanmu! Zamu tafi! Zamu tafi Zulfa'u! Sai bayan shekara biyu! Muna ƙara jajjada miki ki kula! Ki kula Zulfa'u kar iya auran jikarki da ɗa daga tsatson maƙiyiyarki Zulfa'u! Karki bariii!!! Karki bariii!!! Mun tafiii!!! Sai watarannn!!! "
Ɗif kamar walƙiya ya ɓace a lokaci guda hasken ya ɓace sai duhu ya mamaye ɗakin bayi ɗaga,a cikin duhun ne Haj. Zulfa'u ta lallaɓa ta kunna bulb ɗin ɗakin sannan ta harharɗa kayan tsafinta ta sakasu a cikin ƙayataccan akwati ƙarami mai kyawun gaske saita saka akwatin a wani akwati babba shima mai kyau saita maida a ƙarƙashin gadonta.Sannan ta hau tanƙameman gadonta na alfarma ta kwanta,ta kai tsawan awa ɗaya amma ɓarawo bacci yaƙi ziyartatta sai kusan sallar subhi bacci ya ɗauke ta,ba ita ta farka ba sai wuraran 11:23am na safe kasancewar babu sallah a tsarin rayuwarta hasalima tun tana da shekara 35 a duniya tayi sallama da bautar Allah hatta zuwa Hajji tun a wannan lokacin ta daina saidai bautawa aljan tare da zubar da jinin baƙaƙyan karnuka 50 a duk shekara.
Bayan ta farka daga baccin ta nufa hadɗan toilet ɗinta mai shegen kyau tayi wanka haɗi da brush sannan ta fito ta shirya cikin lafiyayyan atamfanta super holland wanda tasha duwatsu a duk ilahirin dokuwar rigan,ga gwalagwalen da ta saka a wuyanta da kunnenta harda awarwarayansu guda shida,flat shoe ne ta saka sannan ta fito daga ɗakinta,kai kai kai ta haɗu iya haɗuwa wallahi idan ka ganta zakayi tunani ƴar shekara 50 ba 78 a duniya ba,domin jikinta kwata-kwata bai nuna alamun tsufa ba ko kuma furfara a gashinta wanda zai nuna tsohuwa ce,tafiya take mai cike da taƙama da izza,zakayi tunanin ƴar sarki ce har ta isa dining room wanda tasan already mai aikinta ta gama shirya mata kayan kalaci a food warmers,zama tayi a ƙayattaciyan kujerarta wanda babu irinta a wurin,serving kanta tayi duk da kaɗan ta saka abincin kasancewar yau tana cikin damuwa sosai saboda ganawar da tayi da Boka Burumbuɗu, shiyasa yau ta tashi da kalasa a cikinta.Haka taci abincin kaɗan sannan ta koma falo ta zauna haɗi da kunna television, kallon tv kawai take amma babu abinda take fahimta na daga abinda suke cewa,lulawa tayi cikin tunaninta tare da nema ma kanta mafitar yadda auran jikarta da ɗa daga tsatson maƙiyiyarki bazai faru ba.Haka tayita zama a falon ita kaɗai kasancewar daga ita sai mai aikinta ne a gidan sai kuma in yaranta da jikokinta sunzo mata ziyara.
Wurin ƙarfe 3:09pm na rana Haj. Zulfa'u na zaune a falon taji alarm ɗin ƙofa na ƙara alamun ana son shigowa,mai aikinta ne da sauri da fito daga ɗakinta zuwa ƙofar tare da buɗewa,baki ta sake tana kallon baƙin sai kuma ta ce
"Laaa!!! Ƴan ƙasar waje a gidan,oyoyo sannunku da zuwa"
Tayi maganar tare da basu wuri suka shigo ɗakin,Fadila ce da Amminta suka musu zuwan bazata,da gudu Fadila ta shiga falon tare da daka tsalle ta rungume kakarta don tsabar farin ciki.Haj Zulfa'u dake zaune ta lula wani sabon tunanin jin ƴar aikinta ta ce ga baƙin ƙasar waje,wato autarta Hannatu da Fadila kenan, 'wayyo na shiga uku ni Zulfa'u, ya tabbata Boka Burumbuɗu, kenan maganar auran ya kawosu,dole na hana auran nan,dole ne'. Tana cikin zancen zuciya taji an wani rungumeta,tasan wannan aikin bana kowa bane illa na Fadila,ilai kuwa ita ce.Fadila ce ta ce cikin murna
"Oyoyo Granny wallahi nayi missing ɗinki sosai,ke kuma naga alama bakiyi missing ɗina ba"
Tana maganar cike da shagwaɓa irin na ajebos rainon ƙasar waje,murmushi Haj.Zulfa'u tayi duk da ba a cikin yanayi mai kyau take ba amma dole ta kula da jikarta wacca tafi soyuwa a gareta a duk jikokinta,cewa tayi
"Ni awa naƙi missing ɗin jikata wacca tafi soyuwa a gareni,ai kullum da kewarki nake kwana kuma da ita nake tashi Fadilatuwa tahh! "
Suna cikin hirar ne saiga Ammin Fadila ta iso gunsu da fara'arta,samun kujera one seater tayi ta zauna tana ganin dramar Mamanta da ƴarta,hakan na sata nishaɗi sosai,katse musu hirar tayi ta cewa
"Hajiyarmu mun sameku lafiya? "
"Lafiya lau auta,ya kuke da mijin naki"
" Duk muna lafiya ya ce ma a gaidaku,shima yana nan kan hanya idan ya gama abinda yake, zaizo har nan ku gaisa in shaa Allah "
"Maa shaa Allah, toh Allah ya kawoshi lafiya"
"Ameen ya Allah"
Kallon Fadila Haj. Zulfa'u tayi tana murmushi sannan ta ce
"Kwana biyu da banganki ba sai naga kin ƙaramin girma da kyau"
Murmushi Fadila tayi don Fadila na mugun son a yabi kyaunta,sai ta ce
"Awwwn Granny,shiyasa nake ƙara sonki Muah! Muah! Muah! "
Hannunta ta sumbata har sau uku alamun kiss tare da hura ma Grannyn nata,haba mai Hannatu da Haj.Zulfa'u zasuyi inba dariya ba,don idan da Fadila a wuri ka dinga shan dariya saboda shirmanta yayi yawa.Haj .Zulfa'u ce tace
"Ku tashi ku watsa ruwa nasan kafin kugama angama abinci sai kuci ku huta,da daddare mayi hirar da hujja,babu musu suka tashi don watsa ruwa suji daɗin jikinsu,bayan sun fito sukaci abinci kana kowa ya baje don huta gajiyar jirgi da suka sha.
Da daddare su Fadila da Amminta sukaje ɗakin Haj. Zulfa'u don yin hirar yaushe gamo,sun sameta tana zaune akan sofa a tare da ita kuma coffee ne tana kurɓa,zama suma sukayi a sofar dake kusa da ita,a lokaci guda suna gaisheta amsawa tayi cike da kulawa tare da cigaba da kurɓar coffee ɗinta,a sannan ne Hannatu ta gyara zama don su tattauna akan maƙasudin zuwansu Nigeria.
" Hajiyarmu kin kusa aurar da jikarki fa"
Murmushi a fuskar Hannatu take sannarwa Hajiyarta,ita kuma a lokacin da kurɓi coffee ɗinta kenan taji ance ta kusa aurar da jikarta wato Fadila dai ta bokanta yamata kashedin karta bari ayi auran,habawa da sauri da zubar da coffee dake a bakinta, ƙirjinta na dukan uku-uku tare da cewa
"Da gaske!!!"
A tunanin Hannatu duk murna ce ta sakata zubar da coffee na bakinta,sai ta ƙara da cewa
"Da gaske Hajiyarmu,a can ƙasar yaron yake karatu,babu laifi yanada tarbiyya don Daddyn Fadila har Nigeria ya aiko aka tambayi halayyarsa tare da asalinsa,ɗan Kebbi ne yaron,gasu da dukiya gida da waje"
Da sauri Haj. Zulfa'u ta dakatar da Hannatu da cewa
"Yaron waye a Kebbin? "
Caraf Fadila ta cafke wacca tunda aka fara maganar bata tsoma bakinta ba sai yanzu ta ce
"Granny Mum ɗinsa jikar Alhaji Kabir Dikko ne sannan Daddynsa sunansa Alhaji Dauda Gali mai Nass.........."
"Dakata Fadila!!! "
Jikin Haj. Zulfa'u na rawa jin tabbass yaron daga ahalin maƙiyiyarta ce batasan sanda ta daka ma Fadila tsawa ba,hankalinta a tashe ta fara magana
"Inaa!!! Inaa!!! Bazaiyu ba auran nan,kunsan halinsu kuwa Auta da zaku kai Fadila gidan,duk da binciken da kukayi ba komai kuka sani akan wannan mugayan ahalin ba sai ni Haj.Zulfa'u"
Tare da nuna kanta,ƙarya ce ta sumbuɗo musu akan ahalin basu da kirki bayan ita ce ma ta rushe musu farin cikinsu,yanzu kuma tana niyyar goga musu baƙin fenti duk don a fasa auran,domin tama kanta alƙawarin bazata taɓa bari ayi auran ba inhar tana araye.Dole ta ɗau mataki don auran ya rushe ko ta halin ƙaƙa.Fadila da tunda Haj Zulfa'u ta daka mata tsare tayi gummm da bakinta bata sake magana ba sai yanzu da taji kakarta na niyyar tasa a fasa auranta da masoyinta,wani malolan baƙin ciki ne ya tsaya ma Fadila a wuya batasan sanda ta fashe da wani matsanancin kuka ba tana cewa
"Wallahi yana da kirki ga addini,ina sonsa,karku rabani a masoyina"
A hasale Haj .Zulfa'u ta ce
"Masoyin Ubanki! Nace masoyin Ubanki! Wawuya don ana taimakon rayuwarki karta faɗa ga halaka amma ke baki gani,kaunar da nake miki ne yasa nake faɗa miki illar auran wannan ahalin amma ke gamai masoyi kin fara kuka,waya sani ma ke kika fara cewa kina sonsa"
Kuka Fadila take sosai domin a gaskiya tana ƙaunar Sadam sosai,gashi yanzu taga Amminta ta yarda da maganar kakarta har tana cewa gobe zata kira Daddynta ta sanar masa kawai ya fasa zuwa Nigerian daman saboda maganar auran Fadila ne yasa yakeso yazo wurin danginsa su tattauna amma yanzu kawai ya fasa zuwan Allah ya kawo mata miji na gari.
Haka akaita drama a wannan family a kan batun auran Fadila da Sadam wanda Haj. Zulfa'u ta nace akan Fadila bazata auri Sadam ba saboda ahalinsa ba mutanan arziƙi bane,kowa a family ya yarda da zancen Haj. Zulfa'u har Daddyn Fadila domin shi dama yanada wanda yakeso Fadila ta aura amma taƙi ita sai Sadam, ita ko Fadila yanzu ne wutar so da ƙaunar Sadam ke ƙara ruruwa a cikin zuciyarta.Anyita bata haƙuri akan ta haƙura da Sadam amma ina.wannan kenan
Bari mu leƙa Birnin Kebbi🙃🙃🙃
@@@ @@@@@@@
KEBBI
Motoci ne har biyu na alfarma sukaje Airport ɗin AHMADU BELLO INTERNATIONAL AIRPORT wanda yake a Sokoto state domin ɗaukar Sadam Dauda Gali Mai Nasara,sun isa a international Airport ɗin a daidai lokacin jirginsu Sadam ya sauka,saida akayi tsawan mintuna 30 kafin mutanan cikin jirgin suka fara sauka,VIP section na jirgin ne suka fara sauka,wanda Sadam yake a ciki,mutum daya-biyu- uku na hudun ne wani ƙyakkyawan gaye ya fito daga jirgin yana taku cike da izza da jarumta irin na masata masu jini a jika,taku yake har ya sauko daga jirgin yana riƙe da briefcase baƙa a hannunsa,shi kuma ya saka black suit mai shegen tsada,ga gemunsa da gashin kansa duk sunsha gyara,daga gani kasan ana kashe musu maƙudan kuɗi,duk inda ya gilma sai an kallesa saboda kyau da kwarjini da Allah ya masa,a can naji wasu yara ƴan biyu lokaci guda suka ce
"Uncle! Uncle! Uncle! "
Inda yaji ana cewa Uncle ya waiwaya habawa kafin ya gama tantan ce yaran tuni sunyo kansa da gudu suna masa oyoyo oyoyo Uncle,rungumesa sukayi tsabar murna saboda a lokacin da yake gida yana ɗaukar yaron yawan shaƙatawa,shiyasa suke sonsa kuma koda ya tafi karatu,kusan kullun sai sun dami Mom ɗinsu akan yaushe Uncle ɗinsu zaizo ya kaisu shopping.Shima rungumesu yayi sosai tare da shafa kansu,a sannan ne Aunty Sakina da Kamal abokinsa suka zo inda suke da murmushi a fuskarsu sannan kuma a bayansu akwai body gaurd kasancewar yanzu Daddyn Sadam ya ƙara shahara sosai,fuk inda zaije saida bodygaurd masu kare lafiyar,shiyasa a sanda zasuzo daukar Sadam aka tafi da mota biyu haɗe da body gaurds.
"Ai sai kubari mu ƙarasa gida kuyi mishi oyoyon dakyau "cewar Aunty Sakina tana murmushi
Ɗago kansa yayi yana kallonta tare da mayar mata da martanin murmushi yana cewa
" The great Aunty! Wallahi nayi missing ɗinku sosai,kai duk wanda yabar gida, wallahi gida yabarshi"
Dariya Kamal yayi yana cewa
"Kaga Malam yunwa nakeji tun ɗazu muke jiranku,don haka bar zancen in munje gida kwarasa,don ni ƴar Gusau nakaji wallah"
Daƙuwa Sadam yama Kamal yana murmushi tare da cewa
"To Sarki ƴan yunwa sai mu tafi kafin ka cinyemu ɗayye,nida nasha tafiya banyi ƙorafi ba sai kai"
Dariya dukkaninsu sukayi sai Sadam ya riƙo hannuwan twins bayan yaba Kamal briefcase ɗinsa,haka suka isa Birnin Kebbi kasancewar jirginsu a Sokoto ya sauka,buɗe musu katafaran gate akayi domin da jiniya suka iso gidan,bayan sun sauka ne sai suka ɗunguma zuwa cikin gidan.
Mom ce da Daddyn Sadam suna zaune suna jiran isowarsu gidan saboda sunyi waya da Sakina ta ce musu suna hanya,bayan sun shiga falon da sallama a bakunansu Mom ta miƙe da sauri haɗi da rungume autanta tana farin ciki,shima ƙara rungumeta yayi yana farin ciki,suna cikin hakane sai Daddyn Sadam ya ce
"Wato kaga Mom ɗinka ka manta dani ko"
Dariya Sadam yayi tare da nufa inda Daddyn sa yake haɗi da rungumesa yana cewa
"I really miss you Dad,nayi kewarku sosai Dad"
Mom ce da murmushi fuskarta tace
"Kaje ka watsa ruwa muna jiranka a dining room"
"Ok Mom"
Tafiya yayi ya watsa ruwa ya sako sassauyar jallabiya fara tas ya fito,haka wannan familyn suke jeru suna cin abinci cikin farin ciki da annashuwa wanda ko ba'a faɗa ba saboda dawowan Sadam ne daga UK,bayan cin abinci sai suka ɗunguma zuwa falo,anan suka fasa hirar yaushe gamo,sai wurin Asr kowa ya miƙe don yin sallah,wanda Sakina ta tafi gida da yaranta,shi kuma Kamal sai dare ya wuce gida saboda bayan da sukayi sallar Asr ɗakin Sadam suka wuce,sun ɓata lokaci suna hira wanda sai dare Kamal ya tafi.
Bayan kwana biyu lokacin Sadam ya huta sosai Daddynsa ya kirasa part ɗinsa,a lokacin daya shigo falon ya tarar da Mom ɗinsa tana zaune itama,samun wuri yayi a ƙasa ya zauna tare da musu barkha da dare,cike da kulawa suka amsa masa,Daddyn Sadam ne yayi gyaran murya sannan ya fara magana
"Alhamdulillah ala kulli halin,yau gashi Allah ya nuna mana kammaluwan karatunka Sadam cikin nasara da aminci,muna ƙara gode masa da wannan ni'imar da yayi mana,sannan yau zan danƙa maka companies,plazas haɗi da gidajan mai wa'inda mallakinka ne tun a ranar da aka haifeka,akwai companies guda uku,ɗaya a kaduna wanda ake sarrafa shinkafa,biyu kuma a kano,sannan akwai gidajen Mai guda huɗu,biyu a hanyar Zaria,ɗaya a cikin garin nan sai ɗayan a Zamfara,wanda dukkaninsu suna aiki tare da manya-manyan motocin mai guda shida,sai kuma Plazas guda Uku dukkaninsu suna kaduna,don haka ka jajirce ka maida hankalinka akansu,a da nasu sai kayi Masters kafin zan danƙa maka su amma sai wani tunani yazomin akan gwara ka fara gudanar da kasuwancinsu kafin daga bisani ka koma ƙaro karatun"
Kasa magana Sadam yayi saboda wannan kyautar bazata da ya samu daga Mahaifinsa,tabbas dole ya maida hankalinsa kacokar a kasuwancinsa domin Daddynsa yayi alfahari dashi,cikin murna Sadam ya fara magana
"Dad bansan wasu kalmomi zan saka wurin gode maka da wannan kyauttukan bazatan da kamin ba,ina godiya sosai, Allah yasaka da alkhairi,ya ƙara buɗi da nisan kwana,tare da lafiya mai amfani,ina godiya sosai da sosai Dad,kuma in shaa Allah zan maida hankalina sosai a kasunwancina,in shaa Allah zakuyi alfahari dani sosai,Mom ki tayani godiya ga Dad"
"Karka damu Auta,ai tuntuni na miƙa godiyarka ga Dad ɗinka"
Kallon mijin nata tayie haɗi ta sakar masa murmushi mai ƙayatarws'a, shima murmusawa yayi sannan ya ce
"Bayan haka,magana ta gaba ita ce maganar auranka,shin akwai wacca kama alƙawari ?"
Duƙar da kansa yayi irin yaji kunyar nan,ya ce
"Eh Dad akwai wata wacca muka haɗu da ita a can UK amma ita a can take da iyayenta,sunanta Fadila Marwan Ɗan galadima,sannan suna da kaka a Abuja,wacca take zuwa hutu wurinta,nasan ƙila Mom kinsanta,sunanta Hajiya Zulfa'u Sani Mai Gad........."
" What!! Hankalinka Sadam!! Jikar matsafa zaka kawo mana!!! "
Mom ce da wannan maganar jin an kira sunan wacca tayi silar rugujewar farin cikin ahalinsu,wacca tabar musu tabo a zukatansu,wacca har su mutu maza su manta da illar da ta musu ba,inaa Inaa.ƙarawa tayi da cewa
"Ban yarda ka auro jikar matsafa ba gidan nan,tun daga kan Hausawa, fulani,shuwa arab,ethopia,india,saudia da dai sauran ƙasashe kaje ka auro amma ban yarda da auro jikar matsafa ba "
Sadam da tun sanda ta daka mai tsawa,yayi shiru yana sauraron faɗan da take masa,wanda ya daɗe rabon Mom ɗinsa ta sama irin wannan faɗan,in fact idan zai iya recalling to tun yana ƙarami rabonsa da tayi masa faɗa.Buɗe baki Sadam yayi zaiyi magana Dad ɗinsa ya dakatar dashi da hannu tare da cewa
"Have patient Sadam! yi haƙuri da wannan yarinyar domin ni kaina ban yarda ka aureta ba,sannan kayiwa Mom ɗinka biyyaya ka naimi wata,Allah ya zaɓarma wacca tafita zama alkhairi a gareka"
"Na haƙura da ita Mom,Allah ya bani wacca ta fita"
"Ameen"
Daddynsa ya amsa,ita kuwa Mom duk da taji daɗin biyayyar da yayi mata,amma tuno a abubuwa da dama da suka faru shekaru aru aru,yasata zubda ƙwalla,murmushi tayi masa haɗi da cewa
"Allah ya maka albarkha Auta,ya haskaka gobanka,ya kareka daga sharrin masu sharri,naji daɗin yi mana biyyaya da kayi,in shaa Allah sai Allah ya baka wacca tafiya komai"
"Allah ya yarda Mom"
Daddy ne ya kallesa sannan ya ce
"Gobe sai kazo muje court domin kayi signing ƙaddarorinka in shaa Allah,sannan idan naga ka bada himma da ƙwazo sauran ƙaddarorin zan danƙa mata don cigaba da kula dasu tunda yanzu tsufa ya fara tasomin"
"In shaa Allah Dad,ina godiya sosai Allah ya ƙara nisan kwana da lafiya mai amfani"
Da Ameen suka amsa masa kana yayi musu sallama ya wuce part ɗinsa wanda yake sama,duk da Fadila ce ta fara cewa tana sonsa amma yanzu kuma sonta ya fara shigarsa kaɗan-kaɗan
Waiwaye
*****A lokacin da Sadam yake a shekararsa ta uku a UK ya haɗu da Fadila,ita kuma tana a shekarar ta biyu,a wurin taron musulman Nigeria suka haɗu,kasancewar shi ne AMEER ɗin ɗalibai a makarantar,abinda yaja hankalin Fadila shi ne kyaunsa,ƙwaƙwalwarsa da miskilancinsa shi yake burgeta,gashi yanada saje a fuskarsa mai ƙara masa annuri haɗi da kwarjini.
Bata ɓoye ba ta cuci kanta ta samesa,shi kuma a lokacin yana tare da abokinsa Sadiq suna zaune,tayi musu sallama haɗe da gaishar dasu,Sadiq ne ya amsata amma Sadam ko kallon inda take baiyi ba,ya cigaba da sabgarsa,a nan ne ta bayyana soyayyar da take masa,wanda a ƙarshe daƙyar Sadiq ya shawo kansa akan babu kyau wulaƙanta mutum,sai a sannan ne ys aminta suka fara soyyaya,har iyayen Fadila suka san da Sadam,Daddyn Fadila har Nigeria yasa akayi bincike akan Sadam,sannan ya aminta da auran nasu,wanda a yanzu komai ya taɓarɓare a duka ɓangarorin guda biyu*****
Cikin labari
Bayan ya zauna a saman sofarsa ya kira Fadila don sanar mata suyi haƙuri da junansu tunda iyayensu basa so,daman duk rikita-rikitar da take faruwa a gidansu Kakarta Fadila duk ta sanar masa.
Haka dai suka haƙura da juna duk da a ɓangaren Fadila ba haƙura tayi ba saida babu yadda ta iya tunda Sadam ya fita daga sabgarta,yayi deleting komai nata a wayarsa.
Sadam yanzu ya maida hankalinsa complete a harkar kasuwancinsa wanda maa shaa Allah komai yana tafiya yadda ya kamata.wannan kenan
@@@ @@@@@@
KADUNA
A ɓangaren LOVE BIRDS🕊️ wato Sauban da Maryam abubuwa ƙara zafafa suke.Kasancewar yanzu su Maryam suna IT kuma da wuri take dawowa gida,halayanta munana sai ƙara bayyana suke,gashi yanzu kwata-kwata basa shiri da surukarta kuma duk saboda halayanta ne.
Yau Saturday Sauban na gida suna hutawa a falo,ya dubi Maryam ya ce
"Dear ki shirya abinci ajima abokaina zasuzo,don Allah Maryam karki bani kunya gun friends ɗina musammam Captain Fu'ad wanda tun asali ba son auranmu yake ba,please Maryam kiyi girki mai daɗi wanda zasu yaba ba irin wanda kullun kikeyi muna asarar kayan abinci ba,na roƙeki "
Hannu bibbiyu yake roƙan Maryam don yasan idan aka samu matsala,shikenan Captain Fu'ad ya samu abin tsokanarsa.
Haka Maryam ta saka apron irin ƙwararrun kuku ɗin nan ta shiga kitchen,tayi alƙawarin yau zata birge mijinta.(Har ni mai ɗaukan rahoto zanci hadɗan girkin Maryam kuku🙃🙃🙃)
Tayi tsawan awa huɗu a kitchen tana kwaɓe-kwaɓe wanda ni kaina bansan mai take kwaɓawa ba,duba da yadda take sharɓan uban gumi,ta ɓata tukane da robobi sun kai biyar ƙananu da manya,ga wani juice data haɗa wanda bansan wani iri bane,ƙila sabon fitowa ne ohon mata🤔.Haka da sakasu a food warmers sannan ta jerasu a dining table,ta wuce ɗaki tayo wanka ta shirya tsaf don tarbar baƙin mijinta.
Da sallama suka shigo falon su uku,wato Sauban,Captain Fu'ad da kuma ɗaya abokinsu wanda yake aiki a Abuja sukazo.A falo suka babbaje suna hutawa sai Sauban ya miƙe don kiran amaryar tasa, gaban da dukan uku-uku akan Allah yasa tayi girkin hankali kar yaji kunya,samunta yayi tana chatting a wayarta tasha kwalliya abinta,kiranta yayi akan tazo su gaisa da abokansa,babu musu ta tashi zata fita,Sauban yayi Saurin ce mata
"Da alama baki da hankali,da wannan shigar zaki je gun abokaina,wai yaushe zakiyi hankali ne Maryam,nidai na shiga uku an kawomin rainon yarinya,ke kullum sai ance miki kiyi kaza,kibar kaza haba mtsw!!! "
Fita yayi ita kuma ta saka hijab ta fito suka gaisa da abokan nasa,cewa yayi suje dining suci abinci,babu musu suka miƙe musamman Captain Fu'ad wanda ya ɗebo yunwarsa,yazo yaja girkin amarya.(hmmm Captain Fu'ad a shirya cin girkin Maryam kuku😂😂😂🙃)
Zama sukayi a dining room ɗin sai Sauban yayi serving ɗinsu,kasancewar ya umurci Maryam ta wuce ɗaki,serving ɗinsu yake amma zuciyarsa na dukan tara-tara bama uku-uku ba,ganin yadda colour ɗin abinci yayi so scary babu kyan gani,gashi baya fidda wani aroma mai daɗi sai uban ƙauri,haka dai ya gama serving ɗinsu shima yayi serving kansa sannan ya samu guri ya zauna.
Captain Fu'ad ne farkon fara kai spoon ɗin abinci a bakinsa wanda a lokaci guda amai ya tasa sama jin wani uban ƙarni,ga yajin data zambaɗa a ciki,kai kai kai,amai Captain Fu'ad yake kwarawa babu ƙakƙautawa lokaci guda ya ɗau gorar ruwa ya kwankwaɗe,baiji yajin ya daina masa zafi a baki ba,ya ƙara ɗaukar wata sabuwar goran ruwan ya shanye,su kuma Sauban ganin yadda Captain Fu'ad ya rikice lokaci guda suka kasa cin abinci tare da miƙewa suka nufo inda yake suna masa sannu.Bai amsa musu ba ya miƙe ya dauki key ɗin motarsa ya fita,har waje Sauban ya bisa yana basa haƙuri haka ya ƙyalesu suka tafi,a fusace ya shigo falon har bedroom,lokacin Maryam na kwance abinta,batayi aune ba taji saukan zafafan maruka har guda huɗu lokaci guda,habawa a haukace a miƙe tare da sakin wani razanannan ihu,bai ƙyaleta ba saida ya mata dukan tsiya tare da ce mata ta tafi gidansu gobe,sannan ta tabbata ta goyi girki tare da gyaro munana halayanta kafin ta dawo gidan.Fita yayi baibi takan kukan da take ba ya wuce wani ɗakin ya kulle tare da kwanciyarsa.
Washe gari Maryam ta tattara kayanta ta nufi gidansu,wanda Sauban yasha tsinuwa a hannun iyayenta kasancewar ƙarya da gaskiya ta faɗa musu,su kuma babu bincika ba sukaita zaginsa.Wannan kenan
@ @@@@@@@@@
Ɓangarensu Umma Kande da Maman Jummalo da alama basuyi nadamar abubuwan da suka faru da yaransu ba,domin har yanzu ƙiyayyar Umman Sa'eeda da ita Sa'eedar na nan daram! A zukatansu.
Suna zaune su duka da yaransu wato Iklima da Jummalo,sai Umma Kande ta ce
"Kodai mu ƙara komawa gun Boka Sankeru ne muji a ina aka samu matsalar"
"Tabb wallahi ko kusa Mama karku fara,yanzu duk abinda ya samemu bai zamo muku isharaba,harda rasa ɗiya kikayi amma bakiyi ladama ba Mama"
Cewar Iklima wacca ta harzuƙar sosai saboda halin uwarta ta domin haushinta take ji sosai,Maman Jummalo ce ta ce
"Haba Iklima daɗi da hutu muke nema muku ai,wannan ma matsala aka sam....."
"Matsala! Matsala! Kika ce fa Mama, wallahi bazamu sake biye muku ku kaimu ga wahala ba,da alama kema kamar yadda Iklima ce bakiyi nadama ba,to bara kuji tun a asibiti ni da Iklima muka shirya komawa Islamiya,don ƙara sanin Allah da addinin mu,wanda kuka kasa bamu"
"Tabbas kuwa Jummalo zan tambayi Sa'eeda yadda karatun islamiyarsu take"
Umma kande ce ta hayayyaƙo Iklima da masifa tana cewa
"Ɗiyar maƙiyiyata zaki nema shawara wurinta Iklima"
"Maƙiyiyarki ko ko ce maƙiyiyarta,wani irin asiri ne baku musu ba,amma gashi sai cigaba suke, ku kuma kuna nan jiya iyau"cewa Iklima
"Rufemin baki dan Ubanki,da hassadar Umman Sa'eeda aka haifeni sannan yanzu ma na fara nuna mata ƙiyayya wallahi, koya kika ce ƙawas"
"Ƙkkkwaraiii da gaske yanzu muka fara nuna mata ƙiyayya"
Suna cin hakane akan kira numban Umma Kande wanda tsabar masifa bata duba mai kiranta ba ta amsa kiran
"Hello"
A can ne ake mata magana,wanda lokaci guda ta rikice tana cewa
"Mai wayar!!! "
A can aka ƙara tabbatar mata,habawa sakin wayar tayi a ƙasa haɗi da zaman ƴan bori,tana ihu da kururuwan ta bani ta lalace shikenan ta mutu.Kanta su Maman Jummalo sukayi suna tambayar lafiya mai ya rafu,cikin kuka haɗi da majina take cewa
"Na shiga Uku ni Sarere jikar Sarkin ruwa!!!na mutu na lalace wayyo ni Saratu!!!! Yanzu..................
Mu haɗu a pages na gaba My Esteem Fans🙃🙃🙃🌹🌹🌹
****Wata sabuwa inji ƴan caca,wani bala'in ya kuma saukar ma Umma Kande ne???.....
****Anya Zaman Sauban da Maryam zai cigaba da wanzuwa ganin yadda tun kan aje ko'ina an fara kai duka tare da tafiya gida???.....
****Shin Fadila zata haƙura da Sadam kamar yadda ya haƙura da ita koko yaya???......
*****Shin wasu abubuwa ne suka faru shekaru aru aru a baya wanda Momin Sadam da ahalinta suka kasa mancewa???........
Ku cigaba da zubo ruwan comments🤗🤗🤗🙃🙃🙃💝💝💝,Ni kuma bazan gaji ba wurin suburbuɗo muku da zafafan updates wa'inda zasu nishaɗantar,ilmantar tare da faɗakar daku🤗🤗🙃🙃💝💝🌹🌹🌼🌼🏵️🏵️
Ina matuƙar alfahari daku my Esteem fans,Allah yabar ƙaunar🤗🤗🙃🙃💝💝🌹🌹🌼🌼🏵️🏵️💖💖💗💗💓💓
Daga alƙalamin
🖍️📚Narrnarhh Bukar 📚🖍️
Comments and share 🙏🙏🙏Fisabilillah.
[5/23, 8:09 AM] Narnarhh Bukar: 🏵️ NACINA YA JAWO MIN🏵️
Narrnarhh Bukar✍️
🌹Perfect Essential Writer's
Association🌹
✨ P. E. W. A✨
Wattpad:@AISHAABUBAKAR812
Arewabook:@Narrnarhh002
Masu telegram zaku iya following ɗina ta wannan link ɗin🤗,🙃🏵️👇👇👇
https://t.me/+439Pdx2UbLZlOTNk
🌹🌹🌹I'm not born to be a writer but born to be a great professional writer✍️✍️✍️🙃🙃🙃🌹🌹🌹
🌼🌼🌼Special greetings to y'll my Esteem Fans,Ina ƙaunarku Lodi Lodi🙃🙃🙃💖💖💖🌼🌼🌼
37----38
Suna cin hakane aka kira wayar Umma Kande wacca tsabar masifa bata duba mai kiranta ba ta amsa kiran
"Hello"
A can ne ake mata magana,wanda lokaci guda ta rikice tana cewa
"Mai wayar!!! "
A can aka ƙara tabbatar mata,habawa sakin wayar tayi a ƙasa haɗi da zaman ƴan bori,tana ihu da kururuwan ta bani ta lalace shikenan ta mutu.Kanta su Maman Jummalo sukayi suna tambayar lafiya mai ya rafu,cikin kuka haɗi da majina take cewa
"Na shiga Uku ni Sarere jikar Sarkin ruwa!!! Na mutu na lalace wayyo ni Saratu!!!! Yanzu mai yayi saura gareni,yiiiiii!!! Yiiiiii!!! "
"Ƙawas wai meya faru ne,kinsamu a duhu,ga kuma kuka kina yi"
"Maman Jummalo gobara ta tashi da Musa!!! Shikenan ɗana a duniyi,yanzu ya tafi ya barni,ina ganin bala'i da masifa ni Saratu!!! Wayyo Musana!!! Shikenan ko gawan ɗana bazan gani baaaaa!!!! Yiiiiiii!!! Yiiiiiii!!!
Jin abinda Umma Kande ta ce gidan ya kaure da kuka haɗi da iface-iface musamman Iklima wacca suka fi shiri da Musa,tayi kuka haɗi da birgima a ƙasa kamar sabuwar kamu.Maman Jummalo itama tayi kuka sosai tare da ba Umma Kande haƙuri,amma ina Umma Kande kamar wata zautatta haka tayi,gashi tayi zaman ƴan bori haɗi da cire ɗan kwalin kanta tana ihu da kururuwa
" Musa! Musa! Musa! Ka dawo karka tafi ka karbi,kaine rayuwata,ka dawo,ka dawo Musana na roƙekaaaaaa!!! "
Waiwaye
******Abinda su Umma Kande basu sani ba game da rasuwar Musa shi ne,kasancewar Musa ɗan daudu ne kuma mai harka da manya-manyan mata a Calabar,manyan matan suna zuwa ɗaukarshi har gidajensu domin suyi sharholiyarsu sannan su biyashi maƙudan kuɗi saboda yasan sirrin mata sosai.
Hausawa suka ce tsautsayi baya wuce ranarsa,ranar data kasance ranar da Allah ya ɗauki ran Musa shi ne,wata customersa ce tazo har gidan karuwai ta ɗaukeshi suka tafi gidanta,zama yayi a falonta sai tace bara ta girka musu abinci sai suji daɗin harkar dakyau,bayan matar da ɗaura girki a gas cooker mai mazaunai hudu sai ta fito falon,tana zuwa sai Musa yayita janta da kissarsa ta riƙakƙun ƴan daudu,habawa tuni mata ta manta da abinda ta ɗaura kan gas cooker suka fara masha'arsu,wanda har girkin ya ƙone,tukunyar tayi baƙi amma hankalinsu baya a jikinsu balle suji ƙauri,nan da nan wuta ta tashi a kitchen kan kace me ta gauraye ko'ina,su Musa kafin suyi wani aune,wuta ta shigo falon,haka su biyu suka ƙone ƙurmus sai ƙashi,wannan ne asalin sanadin mutuwar Musa******
*Cikin Labari*
Suna a wannan yanayin ne saiga Baban Nusaiba ya shigo gidan kamar an jefosa,tun daga zaure yake jin ihu da kururuwansu Umma Kande wanda hakan ne ya sashi saurin shiga gidan,samun Umma Kande yayi a zaune a ƙasa,ta wage ƙafafunta haɗi da saka hannuwa a kai tana ihu.cikin sanyin murya ya tambayi lafiya,Iklima ta sanar mishi Musa ne ya rasu,bai sake ce da ita komai ba ya fita daga gidan,fuskarsa babu yabo babu fallasa,shidai gashi nan,mutuwar ma ba damuwa yayi da ita ba,to baya cikin hankalinsa.
Tun safe Sa'eeda da Ummanta basa nan,ita Sa'eeda taje IT, ita kuma Ummanta daga shara ta wuce aikin biki a bayan layinsu,basu san da abinda ke faruwa ba.
Da sallama Sa'eeda ta shigo gidan,cak ta tsaya ganin ikon Allah,yau su Umma Kande ne ke kuka haka duk da lokacin rasuwar Zaliha tayi kuka amma wannan karon kamar hauka take,wai meke faruwa ne? Mai ya samesu haka?,tambayar kanta tayi,wanda babu amsa,taso ta buɗe ɗakinsu ta shiga ba tare da ta tambayi mai ya samesu ba,amma ina bazata iya ba,ita mai raunin zuciya ce ga mutane,haka tayi kasadar tambayar Iklima mai ya faru.Cikin kuka Iklima ta sanar ma Sa'eeda Musa ne ya rasu yanzu.
"Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un,Allahumma gafir lahu,warhamhu,wa'afi anhu,Allah ya gafara masa,yasa ya huta,yasa kuma aljanna ce makoma a garesa,Allah ya baku haƙuri tare da juriyar rashinsa"
Iklima da Jummalo ne suka iya bata amsa,amma Maman Jummalo tare da mai gayya mai aiki wato Umma Kande basu san mai take cewa ba tsabar tashin hankali da ruɗun daya samesu.Ɗaki Sa'eeda ta wuce wanda bata jima ba saiga Ummanta ta dawo,itama tambayarsu tayi mai ya faru,Iklima ce ta bata amsa,salati tayi tare da yi mishi addu'ar Allah ya gafarta masa ta wuce ɗaki.
Haka su Umma Kande suka ci-gaba da zaman makokin Musa wanda har ƴan uwanta da Maiduguri saida sukazo ta'aziyya,yanzu kullum da hijabi zakaga Umma Kande haɗe da carbi saikace tasan me ake cewa😂😂😂,bayan anyi arba'in ɗin Musa wanda ba'a kawo gawarsa ba kasancewar ƙurmus ya ƙone,Umma Kande ta yaki ce saka hijabi haɗi da riƙe carbi,wannan karon Nusaiba batazo ba saidai kira a waya tai musu ta'aziyya saboda yanzu bata samun lokaci sosai,tauraronta ƙara haskawa yake a harkar luwaɗi da kuma lesbianism,wanda bata wannan ƙasa bata waccan.
Bayan rasuwar Musa da wata biyu su Iklima da Jummalo suka shiga islamiyar da Sa'eeda tayi sauka,ajin matan aure suka shiga saboda babu wani abun kirki da suka sani dangane da addinsu su.Wannan kenan
@@@ @@@@@@@@
*Bayan Wata Shida da Sati Biyu*
A ɓangaren karatun Sa'eeda kuwa,sun kammala IT yanzu kuma sun shiga shekarar ƙarshe a karatunsu wato 400 level,yawanci lecturers ɗin da suke ɗaukarsu sababbi ne,masu zafi babu wasa a tattare dasu.Farkon shigarsu ajin wata sabuwa lecterer ƴar gayu ta fara ɗaukarsu wani course,shigowanta ajin tayi tozali da Sa'eeda, cak ta tsaya tana kallonta babu ko ƙyafta ido,kowa a ajin kallansu suka komayi ganin wannan ikon Allah, mata daga zuwa aji ta kafe Sa'eeda da kallo babu ko ƙyartawa,kusan seconds 20 sai kuma lecterer ta ƙarasa cikin ajin still idanunta akan Sa'eeda, kasa haƙuri matar tayi ta tambayeta da harshen turanci
"Young Lady what's your name please? "
Sa'eeda da tunda ta haɗa ido da wannan sabuwar lecterer ƙirjinta ya fara duka,gashi taga matar sai kallonta take babu ko ƙiftawa,miƙewa tayi cikin ladabi ta amsa mata cikin hatshen turanci
"My name is Sa'eeda Sulaiman"
"From which State"
"From Kaduna"
"Alrght seat down"
Ba haka ran matar yaso ba domin akwai abinda takeso ta tabbatar akan garinsu,saboda wani abu take ji a zuciyarta game da wannan yarinya,amma ya zata tabbatar tunda ta ce ita ƴar Kaduna ce,sha re zancen tayi,tazo gaban Allon haɗi da gabatar da kanta cikin harshen turanci wanda take magana cike da ƙwarewa
"Good morning class,My name is Dr.Nabila Abubakar Kabir Dikko,nice to meet you all"
Duka ajin suka amsa mata cike da murna saboda matar ta gama tafiya da imaninsu,ga turancin da takeyi daga ji kasan ba'a Nigeria tayi karatu ba,saboda yadda take amfani da phonex wurin lanƙwasa harshenta.Cike da ƙwarewa Dr. Nabila take musu karatu,gashi ta iya bayani mai gamsarwa,lokaci-lokaci idanun Dr.Nabila na kanta Sa'eeda wanda har yanzu ta kasa gasgata abinda zuciyarta take ayyanawa game da yarinyar,haka ta kammala musu lecterers ta fita,kamar jira ƴan aji suke tana fita kowa ya fara yaba Dr. Nabila saboda ƙwarewa da gayunta.
Haka suka ci-gaba da karatunsu a 400 level first semester cikin nasara,a semester ɗin ne aka rarraba ɗalibai ga project supervisors nasu,luckily Sa'eeda aka bama Dr.Nabila, haƙiƙa Dr Nabila taji daɗin bata Sa'eeda da akayi a matsayin project student ɗinta,koba komai zata samu damar tambayanta abubuwa da dama wanda suke cikin ranta tun a ranar da tayi tozali da ita.
Sa'eeda ma haka abin yake a wurinta domin har labarin Dr Nabila take ba ma Ummanta,saboda tanada kirki sosai gashi tunda Dr.Nabila ta zama supervisor ɗinta take taimakonta da kuɗi ko wasu abubuwa,duk da Sa'eedar bata son amsa amma babu yadda ta iya saboda jan idon da Dr. Nabila take ma Sa'eeda idan taƙi amsa,ƴan aji sunyi gulmar har sun gaji musammam squad ɗinsu Maryam wai Sa'eeda na shisshigema Dr.Nabila saboda taga tanada kuɗi sosai,ga sabuwar Land Cruiser baƙa wanda take hawa,haka dai suka gaji da gulmar suka sa musu ido.
A ɓangaren ƙawancen Sa'eeda da Iman baza muce komai ba saidai muce maa shaa Allah,domin ƙawancen da sukeyi na tsakani da Allah ne babu hassada balle ƙyashi,ba ƙaramin daɗi Iman taji ba ganin yadda Dr.Nabila take son Sa'eeda, hakan na mata daɗi a rai koba komai ganin ƙawarta cikin farin ciki na daɗaɗa ranta.Wannan Kenan
@@@@@@@@ @@@@
A ɓangaren LOVE BIRD🕊️🕊️🕊️ wato Sauban da Maryam,tunda ya ce ma Maryam taje gidansu gyaro hali tare da koyan girki har yanzu bata dawo ba kusan wata biyar kenan,gashi har sun koma makaranta amma taƙi dawowa hasalima acan take tafiyarta makaranta abunta,tunda iyayenta sun ɗaure mata gindi akan sai Sauban yazo da kansa ya bada haƙuri kafin ta koma gidansa,shi kuma ya rantse koza ta shekara a gidansu ba zaije bikonta ba,domin laifinta ne ba nasa ba.Maryam nasan komawa gidan mijinta amma bata samu fuska gun iyayenta ba saboda sun kafe akan lalle-lalle-ilalla sai yazo ya bada haƙuri da kansa.
Shi kuma Sauban yanzu ya fita a harkarta musamman shawarar da Mom ɗinsa tazo mishi dashi wanda ya aminta sosai akan shawarar da ta yanke.
Yau ne ya shirya zuwa gidansu Captain Fu'ad domin yanason ya bashi shawara tare da ƙara bashi haƙurin abinda ya faru a gidansa kasancewar Captain Fu'ad auransa ya matso saura sati ɗaya,kuma ya samu hutu a wurin aikinsa Port harcourt.Bayan mai gadi ya buɗe ma Sauban gate ya shigo da motarsa yayi parking tare da nufar part ɗin Captain Fu'ad, da sallama ya shiga falon kasancewar ƙofar a buɗe take, amsa masa Captain Fu'ad yayi tare da miƙewa yana sakin wani shegen murmushi babu gaira babu dalili,tunda Sauban yaga yana mishi wannan munafikin murmushin yasan mugunta ya gani,cikin ɗaure fuska Sauban ya ce
"Malam ya da shigowa na ka mike tare da sakin murmushi"
Dariya Captain Fu'ad yayi tare da cewa
"Haba Angon Mairo kuku,kyau naga ka ƙara shiyasa ni sakin murmushi ganin aminina kuma ɗan uwana na samun kwanciyar hankali"
Eh tabbas! Yau naga ta kaina da Fu'ad, nasan kashina ya bushe,badai yazo gidana yaga yadda muke rayuwa ba shikenan ai na kaɗe ni Sauban, katse mishi tunani yayi da cewa
"Ka zauna mana Angon Mairo kuku,kana hutawa fa"
"Oooo God!!! Haba Fu'ad wani irin iya shege ne haka,ko ruwa baka bani nasha ba amma ka wani cikani a surutu marasa ma'ana"
Dariya Captain Fu'ad ya tintsire dashi harda riƙe ciki yana nuna Sauban yana sake tintsire dariya,ɓacin rai iya ɓacin rai Sauban yake ƙololuwa.Cike fusata yace da Captain Fu'ad
"Wallahi zanbar maka ɗaki naje na gaida Mom tunda naga alama ƙwaƙwalwarka ta taɓu"
"Sorry friend wallahi yadda ka koma ne yasani dariya"
"Ok nagane wato ga mahaukaci yazo ko? "
"A'a fa Sauban,why are misunderstanding my words,ummmm wallahi ba haka bane"
"No hakane mana,ga angon Mairo kuku ba wacca kaja girkinta harda amai da shan gorukan ruwa har biyu,ai dole kamin dariya Fu'ad"
Dariya Captain Fu'ad yayi tare da yima Sauban waƙa harda rawa yana cewa
"Da so samu ehh!!! Ace ta iya girki,ƴar fara first lady mai kyau sannan ace tanada kirki ehh,inba kasamu ehh! Inba kasamu ehh!! Inba kasamu ehh ehh ehh habawaaa!!! "
Dafe kansa Sauban yayi yana cewa
"Kai kai kai yau naga ta kaina,shikenan ai tunda kasan sirrin gidana na kaɗe,don Allah mubar wannan shirma,muyi abinda ya dace Fu'ad"
"Tohhh Angon Mairo kuku,ina sauraranka"
Baza yayi da abinda ya ce don idan ya biye halin Captain Fu'ad sai su shekara a haka,cikin muryar damuwa Sauban ya fara magana
"Fu'ad wallahi ina cikin matsala babba"
With serious voice Captain Fu'ad ya ce
"Subhanallah,meke faruwa Sauban"
" Ai komai ma ya faru Captain, Mom ce tazo min ta wata shawara a lokacin Maryam nace taje gidansu gyaran hali akan na ƙara aure,duk da nima inada wannan burin amma ba'a nan kusa ba,kwata-kwata yaushe akayi bikinmu ace har na ƙara aure, gashi Maryam duk yadda naso ta natsu tasan hakƙin mijinta amma ya gagara,idan na lanƙwasota ta nan saita ɓalle ta can,tana da matsaloli masu yawa wallahi,rashin iya girki,baƙar magana,rashin girmama na gaba da ita,ga uban ƙazanta,gayu kawai ta iya amma duk abinda matar aure ya dace ta sani babu abinda Maryam ta sani,could you imagine pads ɗin da tayi amfani dashi after her mensturation a toilet ta barshi saidai ni dana shigo toilet ɗin na ɗauke tare da jefarwa,how did you think i can tolerate her stupid atitude Fu'ad, common gyaran ɗaki Maryam bata iya ba,balle akai kan uwa uba girki,inaa inaa dole na samo ma kaina mafita wallahi,don bazan iya jurar halayanta ba,gashi tunda nace taje gidansu gyaran hali har yau taƙi dawowa,kuma na rantse babu inda zani bikonta"
Shiru Captain Fu'ad yayi yana kallon aminin nasa cike da tausayi duk da shi yajama kanta tun farko,sauke ajirar zuciya Captain Fu'ad yayi kafin ya ce
"Kaga illar dana hango maka tun a baya kaƙi ganewa,irin wannan matsalar na hango maka Sauban amma ina sai kayi burus da shawarata,ka irinta nan Sauban kwata-kwata yaushe kayi auran amma har ka fara fuskantar matsalolin da ko wa'inda suka shekara goma basu fuskanta ba,i told you from initial not just by mere looking zaka san wacca ta dace ka aura ba,shi aure da kake ganinsa akwai features da mutum yake bi kafin yasan wacca tafi cancanta ya aure,amma kai ina kyau da gayu haɗi da social life ya ruɗeka,kai kafi son mace very social,beautifuland classy bayan the most impotant features ɗin aure ka barsu,like addinin mace,kamewarta,natsuwarta,tsaftarta,ɗabi'unta da dai sauransu,duk da wannan baka duba ba sai kyau da wayewarta kawai,taya zakuji daɗin auran bayan turbar da kuka ɗauka kaida ita ba mai ɓulle muku bane,alhakin Sa'eeda ne tun kan aje ko'ina Allah ya fara saka mata,mace mai hankali, natsuwa,ilimi,ga uwa uba tarbiyya duk Sa'eeda ta tattarasu amma saboda wani dalili wanda baikai ya kawo ba,ka wofantar da damarka Sauban"
Shiru Sauban yayi yana sauraron abokinsa,wanda sai yanzu yake gane kuskuransa,tabbas yayi wasa da damarsa,sauke ajiyar zuciya yayi kafin ya ce
"Duk abinda ka faɗa Fu'ad gaskiya ne,na riga na ɓata rawata da tsalle,sai yanzu na gane illar da kake nunin abaya amma nayi burus da shawararka,yanzu dai nothing we can do tunda is already a past"
"Hakane,yanzu wacece Mom ta baka shawarar da aura "
"Cousin sister ɗina ce wacca take a Malaysia tana karatu,yanzu haka baifi watanni huɗu ya rage ta dawo ba"
*Waiwaye*
****Wata ɗaya da tafiyar Maryam,Mom ɗin Sauban ta kirasa har bedroom ɗinta,bayan ya shiga da sallama ya samu wuri ya zauna,cikin girmamawa ya gaisheta,ita kuma ta amsa masa cike da kulawa tana murmushi,shiru ɗakin yayi na tsawan wasu seconds duk a lokacin idanun Momin Sauban yana kan Sauban ganin ya rame sosai,gashi ba annuri a tattare dashi,gyaran murya tayi sannan ta kira sunansa cikin sassayyan murya
"Sauban"
Gaban shi ne ya faɗi jin irin wannan kiran sunan da ta masa,domin idan Mominsa tanason ta faɗa mishi wata muhimmiyar magana,sunansa take fara kira cikin sanyin murya.Dagowa yayi yana kallonta tare da cewa
"Na'am Mom"
Cikin muryar damuwa ta fara magana
"Yanzu haka Sauban ka koma? Duk ka rame kayi baƙi,ko baka da lafiya ne?"
Girgiza mata kai yayi alamun a'a sannan ta cigaba da cewa
"Sauban wata shawara na kawo maka kuma na tabbata mai ɓullewa ce da yardar Allah"
"To Mom ina sauraranki"
Ci-gaba da maganarta tayi tana cewa
"Aure nake so ka ƙara Sauban,tunda ita waccan batasan mai yake me yake mata ciwo ba"
Daramm! Gabansa ya faɗi jin wani sabon tashin hankali,ba wai bayason ƙara aure bane,a'a da wuri haka ko shekara ɗaya ba suyi ba,cikin girmamawa ya ce
"Momina da wuri haka,nifa ko budurwa banda ita yanzu"
"Da wuri kuwa Sauban tunda ba samun kulawa kake wurin Maryam ba,hasalima ban ga amfanin auran ba tunda ana yinsa ne don samun natsuwa,amma kai sai akasin haka,yanzu dai akwai Khairat ƴar wajan Auntynku Habiba wacca take karatu a malaysia,tana da hankali da natsuwa ga ilimin addini dana boko,ita naso ka aura tun farko amma ka nuna kai Sa'eeda kakeso wanda ni sai yanzu nagane ashe makirci Haj.Labara ta ƙulla don ka auri ƴar ƙwantarta,gashi dai yanzu aure baiyi riba ba hasalima faɗuwa aka samu,zan baka numbanta ku daidaita kafin ta dawo tunda ta kusa kammala karatun nata"
"To Mom ba damuwa,Allah yasa hakan shi ne mafi alkhairi"
Daɗi ya kama Momin Sauban jin ɗanta ya karɓi shawarata,murmusawa tayi sannan tace
"Allah ya maka albarkha,yasa ƴaƴanka sumaka biyayya irin yadda kamin kuma kake faranta mun rai,Allah yasa ta zamo sanyin idaniyarka tare da farin cikinka"
"Aaaameen ya Hayyu ya Qayyum"
Tashi yayi haɗi da mata sallama ,yasan khairat farin sani,tabbas ba ƙarya tanada tarbiyya sosai da natsuwa, haba sai yanzu yaji hankalinsa ya fara dawowa jikinsa.
Tunda ya amshi numban khairat soyayya ta ƙullu a tsakaninsu,babu laifi akwai natsuwa a tattare da ita.*****
*Cikin labari*
Bayan Sauban ya gama faɗawa Captain Fu'ad yadda sukayi da Mominsa harda soyayyarsa yanzu ta ƙullu a tsakaninshi da Khairat, ya wuce gida.
Kwana uku da zuwansa gidan Captain Fu'ad sai ga Maryam ta shigo gidan kamar an jefota,a lokacin yana falo ya baje abincin da yayo takeaway ɗinsa yana ci.Sallama tayi ta shigo tare da akwatinta,babu yabo babu fallasa ya amsa sallamarta ya cigaba da cin abincinsa hankalinsa kwance.Kasa haƙuri Maryam tayi ganin yadda bai nuna yayi maraba da zuwanta ba ta ce
"Haba Sauban ko sannu da zuwa babu"
"Oooh sorry,sannu da zuwa"
Ƙara maida hankalinsa yayi ga abincinsa,sai can ya ce
"Hope kin gyara halin naki da nace ki gyara"
Kallonsa tayi da mamaki wai halinta,to ita wani hali take dashi da zata gyara mtsw! Sai kuma can ta ce
"Na gyara shikenan"
"Better"
"Wai Sauban wani irin wulaƙanci ne haka,jiba yadda kake amsamin magana babu kulawa haba"
Cak ya tsaya daga cin abinsa,sai ya ɗago yana kallonta ƙasa da sama a zuciyarshi yana cewa 'Wai me wannan take dashi da na dage sai na aureta,gashi babu abinda na mora sai wahala,damn it! ' katse mishi tunani tayi da cewa
"Ko zuwa gidanmu bikona bakayi ba,gashi ba kira a waya balle nasan ka damu dani,yanzu kuma na dawo ko maraba ba kayi da zuwana ba,wai miye haka,nima fa shegiyar kaina ce wallahi,bar ganin kana duka na ina ƙyaleka,kaci darajar son da nake maka ne wallahi"
Wannan karon miƙewa yayi yana mata wani shegen kallo irin na in kin isa,sai kuma ya saki ƙyayataccan murmushi yana kallonta kamar bazaiyi magana ba sai kuma ya ce
"Darajar so huhhh!!! Kina sona ne kike zagin Mom ɗina? Kina sosa ne kike ƙin abinda nake so? Kina sona ne kike faɗamin baƙar magana,haka ake so a garinku? To bari kice gwara na sanar miki tun yanzu karki ce na munafin ce ki AURE ZAN ƘARA"
Darammm!!! Dammm!!! Darammmm!!! Tashin hankali wanda ba'asa mai rana,zuciyar Maryam ce ta tsinke lokaci guda,ƙwaƙwalwarta ta tafi hutun wucin gadi na wasu sakanni,kirjinta dukan tara-tara ya fara bama uku-uku ba,dafe ƙirjinta tayi da hannu bibbiyu tare da waro idanunta waje tana cewa
"Kishiya Sauban zakamin!!! "
"Ƙwarai kuwa Maryam"
Ai wani irin daka tsalle Maryam tayi,haɗe da cira gyalanta da ɗan kwalinta lokaci guda tana cewa cikin masifa da bala'i har idanunta sunyi ja
"Kan bura Uban can!!! Wallahi tallahi baka isa ba!!! Yau akwai bala'i a gidan nan!!! Yau akwai yaƙin duniya na uku a gidan nan!!!...............
Mu haɗu a pages na gaba don jin wannan Chakwakiyar chakwalkwalin da yake faruwa a gidan LOVE BIRDS wato🕊️🕊️🕊️ Sauban da Maryam😂😂😂😂✍️✍️✍️
*****shin su Umma Kande da Maman Jummalo sunyi nadama ko ko har yanzu akwai sauran rina a kaba???......
*****Shin mai yasa Dr Nabila take kyautatawa Sa'eeda sannan wasu abubuwa takeso ta tabbatar game da Sa'eeda???......
****shin Maryam zata yarda Sauban ya ƙara aure kuwa,ganin yadda ta haukace lokaci guda???......
Kai! Kai! Kai! Abubuwa da yawa🙃🙃🙃,amsoshinku na nan tafe a pages masu zuwa,kudai ku cigaba da zubo ruwa comments da reactions🌹🌹💖💖🌼🌼💘💘,ni kuma bazan gaji ba wurin suburbuɗo muku new updates zafafa🌹🌹🙃🙃💖💖🌼🌼💘💘😂🔥🔥🔥🔥🔥
Ina ƙaunarku My Esteem Fans Lodi Lodi🌼🌼💖💖🌹🌹🙃🙃💘💘
Daga alƙalamin
🖍️📚Narrnarhh Bukar 📚🖍️
Comments and share 🙏🙏🙏Fisabilillah.
[5/23, 8:09 AM] Narnarhh Bukar: 🏵️ NACINA YA JAWO MIN🏵️
Narrnarhh Bukar✍️
🌹*PERFECT ESSENTIAL WRITER'S ASSOCIATION*🌹
✨ *P. E. W. A*✨
Wattpad:@AISHAABUBAKAR812
Arewabook:@Narrnarhh002
Masu telegram zaku iya following ɗina ta wannan link ɗin🤗,🙃🏵️👇👇👇
https://t.me/+439Pdx2UbLZlOTNk
39----40
Darammm!!! Dammm!!! Darammmm!!! Tashin hankali wanda ba'asa mai rana,zuciyar Maryam ce ta tsinke lokaci guda,ƙwaƙwalwarta ta tafi hutun wucin gadi na wasu sakanni,kirjinta dukan tara-tara ya fara bama uku-uku ba,dafe ƙirjinta tayi da hannu bibbiyu tare da waro idanunta waje tana cewa
"Kishiya Sauban zakamin!!! "
"Ƙwarai kuwa Maryam"
Ai wani irin daka tsalle Maryam tayi,haɗe da cira gyalanta da ɗan kwalinta lokaci guda tana cewa cikin masifa da bala'i har idanunta sunyi ja
"Kan bura Uban can!!! Wallahi tallahi baka isa ba!!! Yau akwai bala'i a gidan nan!!! Yau akwai yaƙin duniya na uku a gidan nan!!! Yau akwai tashin bama-bamai a gidan nan!!! Ni Sauban zaka ci amana tare da yimin kishiya,mene ne bana maka a gidan nan,aikin da ko a gidanmu banayi amma a gidan shi nakeyi,nace ka kawo ƴar aiki kace a'a,still na haƙura duk don saboda soyayyar da nake maka Sauban,amma da kishiya Sauban zaka sakamin,da kishiya, kishiya fa Sauban, inaaaa wallahi bazata saɓu ba bindiga a ruwa,banzan yarda ba wallahi,ban taso gidanmu naga Mom ɗina da kishiya ba,haka duka familinmu baki ɗaya babu mai kishiya saini wacca ko shekara ɗaya banyi ba,Wallahi baka isa ba Sauba......."
"Dallah malama kin cikani da hayagagarki wacca babu abinda zatasa balle ta hana,ke kin isa ki hanani aure ne,yooo ke awa awani dalili,you are just nothing for nothing in the absence of nothing in terms of nothing stupid human being,Mahaukaciya kawai"
A hargitse shima ya taso mata don yaga alama hauka take shirin yi masa,hala kuws domin idanunta duk sun kaɗa sunyi ja,ga kannan nata duk ya yamutse saboda matsifar da take cinta,dole ya taka mata birki,shi yama rasa waca ƙaddara ce ta sakashi auran wannna jalilar da batasan komai a zaman aure ba.
Rashin nasani hausawa suka ce yafi dare duhu domin da Sauban yasan abinda zai ɓallowa kansa da baima ko fara fada zai mata kishiya ba saboda hauka tuburan Maryam ta fara,tare da kururuwa tana cewa
"Yi huhu!!! Wallahi baka isa ba Sauban!!! Yau zan nuna maka ni cikakkyiyar mahaukaciya ce wacca take da cerficate a psychiartry mai tambarin shugabar mahauka mata a Nigeria yeeeeee!!! Tabbas ni mahaukaciya ce a sonka da ƙaunarka kuma ban yarda wata ta raɓeka da sunan soyayya ko kuma na illata rayuwarta gaba ɗaya!!! Yi huhu ni Maryam mahaukaciya!!! Mallahi saina nuna maka cikakkyar mahaukaciya ce mai certificate yanzu nan!!!
Ai bata jira mai zaice ma ta fara watsi da abubuwan da yake a falon kama daga flower vest,show glasses,television,centre table da dai sauransu,tabbas Maryam ta kwance kamar yadda ta faɗa,domin mai hankali da tunani bazai fara kwatanta irin wannan haukan ba da sunan kishi.Sauban mutuwar tsaye yayi ganin irin aika-aikar da Maryam take yi,tabbas ta hauka ce saboda yadda take watsi da kayan falon zai tabbatar maka ba'a hayyacinta take ba,anya bata da aljanu kuwa,idan fa ta taka wani uban tsalle kamar wata buriya zata sauka akan abinda tayi niyyar tarwatsawa,sai dai kaji Tatsatsa!!! Tas!!! Ɓas!!! Kas!!! Ya tabbata yaƙin duniya na uku ake a gidan Sauban,ko'ina na ɗakin ya birkice hatta curtains ɗin ɗakin basu tsira a hannun Maryam.
Sauban da yaga alamun tabbas noties ɗin kan Maryam sun kwance yayi saurin cafkota habawa wani gagarumin dambe suka kacame dashi,yana riƙita tana dukansa haɗe ta yaƙushinsa tana cewa
"Kasakeni in cigaba da aikina Sauban!!! Kasakeni!!! Sauban!!! Yau ake yaƙin duniya na uku a gidan nan!!! Saina tarwatsa gidan nan!!! Saina ƙona gidan nan!!! Sauban!!!"
Kamar mai almatsutsai haka Maryam ta koma,da bala'i yayi bala'i zuciyar Sauban takai maƙura haba tuni ya fara jibgarta kamar Allah ne ya aikosa,tun Maryam na iya ramawa har takai ko matsin kirki ta kasa,a fusa ce ya bar gidan baki ɗaya,Allah yasa ma Mom ɗinsa bata nan tayi tafiya lamarin ya afku da ko da ita za'ayi dramar saboda dole idan taji hayaniya ta fito ɓangarensu taji mai ke faruwa.
Sai dare Sauban ya dawo gidan,ko daya shigo falon samunta yayi a idan yabarta a kwance kamar bata motsi,da sauri ya isa inda take,tattaɓata yayi amma ina shiru da sauri jikinsa na rawa ya ɗauketa cak direct sai cikin mota,da sauri ya fizgi motar da gudu wanda har mai gadin saida ya tsorata dashi,gudu yake bisa titi kamar ya samu titin ubansa har ya isa hospital ɗin dake kusa dasu,direct nurses suka ɗauketa zuwa emergency room domin bata taimakon gaggawa.
Safa da Marwa Sauban yake domin ya kasa zama,ga uban gumi dake tsuttsugo masa a duk ilahirin jikinsa,tunani ne ya addabi ransa kala-kala,yama rasa wanne zai ɗauka ya fara,shin da tashin hankalin Maryam zai fara ko kuwa da aikinsa na office wanda tun sanda asalin mai company wato CEO ɗinsu yazo da wasu tsararraki masu tsauri ya daƙile handama da babakeran da Sauban da sauran ma'aikatan sukeyi,kasancewar CEO ɗin companyn nasu wayayye ne,ɗan boko kuma gogagge a harkar kasuwanci,wuta iya wuta,ga kuma auran khairat da immediately tana dawowa daga ƙasar Malaysia Mominsa tace za'a saka ranar auransu,tabbas ko ba'a faɗa ba kan Sauban ya ɗau caji sosai,shi saima yanzu yake ƙara da nasanin mai yasa ya auri Maryam bayan ga Sa'eeda mai hankali ga alkunya,wacca tasan girman naga ba da ita,kacona ni Sauban, nayi wasa da damana.Tunaninsa ne ya ɓace ganin likita ya fito daga emergency room ɗin,da sauri ya isa inda yake,likitan ne ya ce ya sameshi a office,babu musu ya bisa.
Bayan likitan ya zauna sai Sauban shima ya zauna zuciyarsa na dukan uku-uku,yana addu'ar Allah yasa babu wata matsala.Likitan ne ya dubesa tare da cewa
"Kwantar da hankalinka,ba wata matsala sosai,matarka was shock on something sannan kuma jikinta ya nuna alamun an duketa,su ne suka haifar mata da suman har na tsawan lokaci,amma Alhamdulillah she is under treatment zuwa nan da kwana biyu ko uku zamu sallameta saboda sai mun bata gado gaskiya"
"Ok Doctor,ina godiya sosai"
"Karka damu aikinmu ne,yanzu zan rubuta mata wasu allurorai tare da magungunan da zaka siya a pharmacy"
"Ok toh"
Rubuta masa abubuwan da zai siya yayi a paper sannan ya miƙa masa,fita yayi zuwa pharmacy ya siyo maganin tare da allurorin sannan ya tambayi wata nurse da a lokacin daya kawo Maryam tana daga cikin nurses ɗin da suka kai Maryam emergency room,ya tambayi ina ne room ɗin da aka kwantar da ita,direct ta kaishi har ɗakin sannan tayo gaba abinta.Shiga yayi ɗakin da sallama sannan ya duba ta ,sai kuma ya fito saboda yanaso yaje gida ya ɗauko musu kayan da suke buƙata a asibitin.Wannan kenan
@@@ @@@@@@
*ABUJA*
A ɓangaren Haj. Zulfa'u kuwa,hankalinta yanzu ya kwanta sosai saboda tama tifkar hanci sannan ta dage Daddyn Fadila ya bana ɗan aminsa da yake sonta aure saboda ayi-ayi auran kowa ya huta,babu musu yabi shawararta saboda shima kansa yafi amincewa Fadila ta auri yaron abokinsa Ambassador.Ranar biki aka saka wanda ba a ɗau lokaci mai tsayo ba just in 5 month coming,hakan yama Haj. Zulfa'u daɗi a rai domin koba komai asirin da ta daɗe tana ɓoyewa bazai tonu ba saboda idan Fadila tayi aure shikenan wani ɓangare na matsalarta ta kau,saura kuma ɗayan wanda kullum dashi take kwana kuma dashi take tashi wato arangama da tsatson maƙiyiyarta,wannan abu naci mata tuwo a ƙwarya idan ta tuna,gashi batasan wace hanya zatabi wurin ganin hana faruwan wannan matsalar ba irin na Fadila, kullum cikin taraddudi ta tsoro take,ta hana kanta saƙat,fita ma ta daina yinta yanzu duk saboda tsoran kar watara ta fita su haɗu wani bala'in ya hau kanta.
Bikin Fadila baifi saura wata Uku ba yanzu,shirye-shirye ne har an fara yinsa musamman Haj. Zulfa'u saboda ta ƙosa ayi-ayi auran hankalinta ya kwanta,an shirya bikin na gani na faɗa wanda yawanci abubuwan auran ba'a a Nigeria aka siyesu ba,gidan ma complete aka sake gyarashi.Haka sukayi ta shirye-shiryansu.
@@@ @@@@@@@@
*KEBBi*
Ilimi shi ne tubalin komai a rayuwa,sannan idan rayuwa ta kasance bisa tsari haɗi da ilimi to tabbas tasha bambam da wanda baya da ilimi tare da tsari a rayuwarsa.Sadam Dauda Gali Mai Nasara yazama tauraro a cikin matasan Kebbi state masu ji da kuɗi da ilimi, domin cikin ƙanƙanin lokaci tauraronsa ya haska saboda a komai nasa zaka samesa yana aiki da lokaci,baya wasa da lokaci,komai nasa a rubuce yake kama daga cin abincinsa,fitarsa kasuwancinsa da komai nasa a tsari yake shiyasa a lokacin da Daddyn ya ɗanƙa mishi ƙaddarorinsa ya ƙara maida hankalinsa kacokan a harkar kasuwancinsa,wanda yanzu ƙaddarorinsa sun ƙara yawaita kama daga companies,plazas,petroluem companies harda gidajen gona wanda bai daɗe da siyansu har uku manyan-manya ana noma kayan lambu,kiwon kifi,kaji,talo-talo,geese,da dai sauransu ana fitar dasu zuwa ƙasashen waje, duk fa a tsakankanin watanin da Daddynsa ya bashi ƙaddarorinsa ne.
Bangaren soyayya tuni Sadam ya ajiyets,bama ya kallon ƴan mata balle wata ta birgeshi ya ce zai aura,lokacinsa kawai na kasuwancinsa ne,don har P.A garesa da bodygaurds masu kare da lafiyarsa,kuma duk inda yaje suna nan tare dashi.Mominsa tasha mishi magana akan yaushe zaiyi aure,amma amsarsa a kullum ita ce shi baiga yarinyar da ra'ayinsu yazo ɗaya ba,ko a lokacin da yake tare da Fadila saboda darajar Sadiq abokinsa ne yasa ya aminta ya soyayyarta ba dan yana son ba,babu yadda Mom ta iya,haka ya ƙyalesa.
Kamar yadda kuka sani duk babbar Sallah familin Alhaji Kabir Dikko suna family meeting don magance matsalolinsu,wannan karon da Sadam akayi family meeting ɗin,harda ƴan Kaduna wato Dr. Nabila da mijinta wanda auran dangi ne aka musu.A nan ne Dr .Nabila take ma Sadam tsiya akan baya da mutunci a ce yana zuwa Kaduna amma ko sau ɗaya bai taɓa cewa zaizo gidanta ba koda da wasa ne,hakuri yayi ta bata akan in shaa Allah idan ya shigo Kaduna zaizo gidan yamayi kwana biyu,duka familyn sai dariya suke musu ganin yadda suke drama kamar ba ɗa da uwa bane.Haka taro ya tashi bayan anci ansha an gwangwaje.Wannan kenan.
@@ @@@@@@@@@@
*KADUNA*
A ɓangaren su Umma Kande da Maman jummalo sun ƙara komawa gidan jiya,domin haka kurin bazasu bari gulmar layi ta kashesu da ransu ba,dole su samo mafita kuma mafitar ɗaya ce wato ƙara komawa gun boka Sankeru don tuntuɓar ko basuyi yadda ya umurcesu bane,sannan da ƙara nemama yaran nasu wasu mazajen daban.(Oooo! Su Umma Kande da alama wahala bata ƙare musu ba kenan😂😂😂🙃🙃🙃).
Kasancewar jiya asabar sukayi shawarar,yau suka buga uban sammaka direct sai tasha,bayan sun sauka a mota sai suka hau machine su biyu,haka a ɗaukesu har gefan dajin inda zai sadasu da wurin boka Sankeru.Bayan ya saukesu suka nufa dajin a ƙafa har bukkar boka Sankeru,Allah yasa yau babu layi sosai mata uku ne a gaban su.lokacin da layi yazo kansu suka shiga ciki a tare .Kamar yadda suka saba mai kirari haka sukayi.
Kamar walƙiya haka ya ɓullo cikin bukkar daman daya gama aiki yake ɓacewa sai kuma idan wasu sunzo sai ya sake bayyana.
Bayyanarsa keda wuya ya tsintsire da wata mahaukaciyar dariya,tumbinsa sai jijjiga yake,su Umma Kande da Maman Jummalo kansu a ƙasa har ya gama dariyarsa sannan ya dubesu dakyau musamman Maman Jummalo na tsawan lokaci sannan ya fara magana cikin amon muryarsa mai firgitarwa
"Nasan Zaku dawo la'anannu!!! Nasan Zaku dawo dangin shayɗanu !!! Kun yarda da shaydanu irinmu hhhhhhhh!!! Ba kuyi kuskure a aikin da nasaku ba saidai ku kuka zaɓama yaranku mazaje !!! Kun nasar damu kuna son yaranku su auri mazaje kowani iri shiyasa muka basu mazaje kowani iriiiiii!!!! "
Har yanzu su Umma Kande babu wacca a cikinsu ta ɗago kanta balle tayi magana,cigaba da maganarsa yayi
"Karku damu tunda kun yarda damu!!! Zamu baku kwalli su shafa gobe da safe idan zasu fita!!! Na tabbata komai yazo ƙarshe!!! Zasuyi aure ba irin wancan ba !!! Zasuyi aure tabbas! Tabbas! "
Yana gama magana yayi wata jijjiga kamar wani alade tare da sakin wata uba-uban tusa mai ɗoyin gaske,tuni suka toshe hancinsu saboda warin kamar mushe ya mutu.(Da sauri na ɗauko nose mask ɗina na saka saboda kar a samu erro mai Esteem fans😷😷😷)
Zuwa wurin wata ƴan ƙwarya dake rataye a ɓukkar ya ɗauko kwallin tare da cilla musu, sannan kamar yadda ya saba kasancewa dasu a duk sanda sukazo hakan ta faru,amma fa yafi daɗewa da Maman Jummalo wanda har Umma Kande taji tsoro saboda da ita ya fara,kusan awa biyu yayi da Maman Jummalo kana tafito tana gumi tare da ɗingisa ƙafa kamar mai ciwo.Haka suka taho gida wanda basu suka iso gida ba sai wurin Isha'i saboda daɗewan da boka Sankeru yayi da Maman Jummalo.
Bayan sunyi wanka sun huta,sannan Umma Kande ta dubi Maman Jummalo tare da cewa
"Ƙawas yanzu ya zamu shawo kan yaran nan su saka wannan kwallin ba tare da sun bamu matsala ba"
"Wata sabuwa inji ƴan caca,tab akwai drama kuwa,kinsan yanzu sun fara biyewa Sa'eeda har da ce mata tayi musu ƙari a karatunsu,kinga da wuya su yadda su saka wannan kwallin kuwa"
Shiru ɗakin yayi kowa na neman mafita,sai can Umma Kande cikin murna ta ce
"Yawwa!!! Na samo mafita ƙawas!!! Wallahi nasamo mafita!!! Kinsan me Ƙawas"
Girgiza kai Maman Jummalo tayi,sannan Umma Kande ta cigaba da cewa
"Mu musanya musu kwallinsu da wannan ta hanyar cire bayan kwallin nasu saimu saka musu wannan kinga ai bazasu gane ba,muyi shiru abunmu,koya kika ce"
"A yyiriri nanaye!!! A Gaskiya ƙawas kin iya bada shawara,haka kuwa za'ayi wallahi, yooo ina dalili ai gwara su sake wani auran mu huta"
"Wallahi kuwa"
Haka suka cigaba da hirarsu cike da annashuwa,abinda su Umma Kande basu sani ba shi ne,Iklima tazo shiga ɗakinsu taji Mamanta da Maman Jummalo suna shawarar yadda zasu sake aurar dasu harda kwallin da zasu musanya musu duk don su shafa a rashin sani,ai tuni ta wuce ɗakinsu Maman Jummalo kasancewar a ɗakin Umma Kande suke hirar,babu ɓata lokaci Iklima ta sanar ma Jummalo abin iyayensu su shirrin aikatawa akansu,haka suka yanke shawarar kar kowaccansu tasa kwallin,tunda ita Jummalo tanada wani sabon kwallin wanda mamanta batasan dashi ba kawai saisu shafashi amma tare da taku kar susan basu shafa ba.
Da wannan shawarar Iklima da Jummalo suka kwana,haka suma su Umma Kande da shawararsu sukaje suka kwanta,da safe kamar yadda su Iklima suka tsara haka sukayi ba tare da iyayensu sun gane ba kwallin da suka sauya musu bane suka shafa ba.
Bayan wasu satittaka saiga Maman Jummalo da sassafe da fito ɗakinta da gudu tazo wurin inda ake wanke-wanke haɗi da kwara amai babu ƙakƙautawa,da sauri Umma Kande ta ƙasaro inda take domin a lokacin da Maman Jummalo ta fito da gudu,Umma Kande fitowarta kenan zata zagaya bayi.
"Ƙawas lafiya kuwa,meya sameki haka"
Cikin galabaita Maman Jummalo ta fara magana
"Nima na rasa meke damuna ƴan kwanakin nan wallahi, sai inji zuciyata na tashi kamar zanyi amai,ga yawan bacci da kasala,anya ba shawara bane kuwa? "
"Da alama tunda kina yawan bacci,shirya kawai anjima muje asibiti"
"To"
Taimaka mata Umma Kande tayi ta wanke bakinta sannan tayi brush,sai ta ƙara taimaka mata ta shiga ɗaki.Da ƙarfe 10:21am na safe su Umma Kande da Maman Jummalo suka shirya zuwa asibiti,a gwajin farko likita ta tabbatar musu da Maman Jummalo na ɗauke juna biyu na sati uku da kwana ɗaya,ai kan likita ta kammala bayaninta Maman Jummalo ta miƙe tsaye,jiki na rawa ta fashe da kuka tana cewa
"Na shiga Uku na lalace ni Hafsy,wace baƙar rana ce yau a gareni ni Hasfy"
Umma Kande tayi saurin rufe mata baki kar tayi ɓaran-ɓarama a gaban likiti,jawota tayi suka fita zuwa gida,ko a cikin keke napep ɗin kuka take sosai,bayan sun isa gida Maman Jummalo ta nufa ɗakin ita ma Umma Kande ta biyota bayan ta sallami mai keke napep ɗin.Allah yasa ma gidan babu kowa kasancewar Iklima da Jummalo suna Islamiya,ita kuma Umman Sa'eeda da Sa'eedar duka basanan.
Tana shiga ɗakin ta yakice gyalenta tare da ɗan kwalinta tana kuka tana cewa
"Na shiga Uku ni Hafsy !!! Yau na ɗau ciki boka,shikenan zan haifi ɗan boka,wayyo Allah ni Hafsy,shikenan tawa ta ƙare!!! Yiiiiiii yiiiiiiiii yiiiiiii !!!! "
Haƙuri Umma Kande tayita bama Maman Jummalo akan tayi hakuri sai a zubar da ciki kawai kar mutane su sani,tun bata da aure,da maganar zubar da ciki Maman Jummalo hankalinta ya ɗan kwanta.
A ranar sukaje inda ake zubar da ciki na sirri,maƙudan kuɗi suka bada sai aka bata magunguna tasha tunda cikin nata ƙarami ne baikai a saka engine a makare tayin ba(Wa'iyazubillah🤔🤔🤔)
Haka suka dawo gida tayi tashan magani babu ƙakƙauwata,amma ikon Allah sai cikin yaƙi fita,har ya fara ɓullowa ana gani, haka suka zuwa a cire cikin amma likitan ya ce idan aka cire cikin Maman Jummalo zata iya rasa rayuwarta saboda yanayin mahaifarta mai rauni ce.Haka suka ƙi haƙura da yawan inda za'a zubda cikin,amma kamar haɗin baki duk inda sukaje magana ɗaya ce,Maman Jummalo zata iya rasa ranta.Wannan Kenan.
@ @@@@@@@@@@
A ɓangarensu Sa'eeda kuwa,babu abinda ke damunsu,ga karatun Sa'eeda nata tafiya abun sai sam barkha,shaƙuwarsu da Dr.Nabila kullum ƙara yawa take,ga Iman ma suna ƙawancensu mai tsafta babu munafinci a ciki.
Tun Sanda Sauban ya yaudari Sa'eeda taji ta tsani maza a rayuwarta,tunani take duk halinsu ɗaya ne babu bambamci.Kasancewar Exams ɗinsu na first semester 400 level ya kusa,kowani lecturer yana alla-alla ya gama lecturer ɗinsa ga ɗalibai ya huta,hakan ta faru ga Dr. Nabila.
Kasancewar yau Thursday kuma yau Dr. Nabila take shirin yima su Sa'eeda test,gudu take a titi babu ƙakƙautawa saboda tayi latti,wayar ce a gefanta take kukan agaji,tana tuƙin ta dau kiran
"Hello Abban Twins baidai har kun isa airport ɗin ba"
Mijin nata ne a can ya amsa da cewa
"Eh wallahi muna jira a kiramu ne,kinsan sai 11:00am jirgin namu zai tashi"
"Maa shaa Allah ya kaiku lafiyyyyyyyy"
Ƙkkkkkkkkkkkkiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiii!!!! Motar Dr .Nabila tayi da ƙara kamin ta kusa bige wata mata da niƙaf a fuskarta tana sharan titi,taso kaucewa matar amma ina saida motar ta kwance a hannun Dr .Nabila haba tayi sama da matar nan,Allah yasa Dr. Nabila tayi saurin gyara kan motar da motar ta ƙarabi ta kan matar nan.
Da sauri tayi parking a gefen titin haɗi ta fitowa da sauri jiki na rawa ta nufa inda mutane suka taru a inda matar take,da sauri ta ce a dauki matar a saka a motarta su tafi asibiti, da sauri aka saka matar a motar Dr. Nabila suka nufi asibiti wanda daƙyar aka anshesu wai sai sun kawo police,direct emergency room aka nufi da matar wanda a lokacin niƙaf ɗin na a fuskar matar hankalin kowa baikai wurin a cire mata ba,wani wanda sukazo da Dr.Nabila a asibiti ya ɗau wayar matar don kiran makusantanta,ganin an rubuta *SANYIN IDANIYATA* da manyan haruffa yasaka shi kiran numban bugu ɗaya ana na biyu ta ɗauka tare da sallama
A ɓangaren Sa'eeda tun safe ƙirjinta ke bugu ta rasa dalili,har ta kasa haƙuri ta sanar ma Iman,sai Iman ta ce tayi ta addu'a in shaa Allah alkhairi ne,sai kuma yanzu ga kiran Umanta wacca tasan bata kiranta a wannan lokacin,cikin sanyi murna tare da tsoro ta amsa kiran
"Assalamu Alaikum"
A can mutumin bai amsa mata basaima ya sanar da ita mai wayar mota ta kaɗe ta yanzu tana asibiti
"Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un,Allahuma ajurni fi musibati wa'aklifni khairan minsa"
Cikin kuka ta tambayi wani asibiti ne,sanar mata yayi tare ta katse wayar,fadama Iman tayi Ummanta yanzu mota ta bigeta ashe shiyasa ƙirjinta yake bugu ɗazu,babu ɓata lokaci Sa'eeda da Iman suka nufi asibitin da aka sanar musu Umman Sa'eeda na can.
A ɓangaren Dr.Nabila kuwa,sai a lokacin ta tuna wayar na mota,da sauri ta ɗauka wanda taga missed calls ɗin mijinta yafi goma,kiransa tayi tare da sanar dashi abinda ya faru sannan yace suma baifi mintuna ashirin su tashi ba,sallama sukayi sai a lokacin aka fito da Umman Sa'eeda a gadon marasa lafiya,idanunta a rufe suke har ɗakin da aka kwantar da ita,Dr. Nabila ce ta kefe Umman Sa'eeda da ido babu ƙyaftawa,haka tabisu har ɗakin da aka kwantar da Umman Sa'eeda still idanunta na akan Umman Sa'eeda ƙirjinta da fat! fat,tana a wannan yanayin ne saiga su Sa'eeda sun bako ɗakin babu sallama turus sukayi ganin Dr. Nabila a ɗakin,itama da mamaki take kallonsu,cikin murya mai sanyi Dr. Nabila ta ce
"Umman kice wannan Sa'eeda"
"Eh malama"
Waro idanu tayi waje,idan ta kalli Umman Sa'eeda sai ta kalli Sa'eeda don tabbatar da abinda zuciyarta take rayawa game dasu,ai tuni Dr Nabila jikinta ya fara rawa tana kallon kowannansu lokaci guda ta ɗauko wayar,dailing numban mijinta tayi,shi kuma a lokacin yana gab da shiga jirgi,da mamaki ya kalli wayar,lafiya kuwa take kiransa yanzu duka-duka yaushe suka gama wayan,amsawa yayi da
"Hello darling hope lafiya"
Dr.Nabila da duk ta ruɗe ta ce mishi
"Abban Twins kazo asibitin nan yanzu don Allah"
Cikin mamaki yace
"Ban gane nazo asibiti yanzu bayan kinsan tafiya zanyi kuma mai muhimmanci..."
Katseshi tayi da cewa
"Ba tada muhimmanci yanzu Abban twins,na roƙeta kazo kaga abinda nagani da idona,wallahi ƙwalƙwalwata ta rikice,don Allah ka fasa tafiyan sai gobe ka tafi ................"
Mu haɗu a *BOOK 2* in shaa Allah don cigaba da jin wannan rikita-rikitar wanda zaizo muku bada daɗewa ba🙃🙃🙃🙃📚📚📚✍️✍️✍️
*Waye mijin Dr. Nabila da take cewa dole yazo yaga abinda ta gani??? Wai idan yazo mai kuke tunanin zai faru??? Mai yasa Dr. Nabila take kallon Umman Sa'eeda da Sa'eeda lokaci guda???*........
*Tofa🤔🤔🤔yanzu dai a Maman Jummalo da cikin boka Sankeru,koya zata kaya????*.....
*a tunaninku kwalbar nan bazata fashe ba har abada ko kuwa akwai wa'adinta indan Allaj yayi????*.....
****Ya zata kasance Shugabar ƴar lawuɗi Nusaiba????......
*Anya Maryam zata yarda da auran da Sauban zai ƙara kuwa???....kuma wani mataki kuke tunanin iyayenta zasu ɗauka idan sukaji za'ama ƴarsu kishiya ko kuwa???*......
*Wace ce Haj Zulfa'u sannan wani sirri ne tale ɓoyewa wanda bataso asani????*........
*Shin kuna ganin Sa'eeda zata samu wanda yafi Sauban ko kuwa????*
*Wasu abubuwa ne suka faru shekaru aru-aru da suka gabata???*........
*Alhamdulillah ala kulli Halin,anan na kawo ƙarshen littafina na ɗaya wanda na biyun yana nan tafe,in shaa Allah, in fatan kun ilmantu,kun nishaɗantu tare da wa'azantuwa a littafina na ɗaya,na biyun ma yana nan tafe wanda yake ɗauke da amsoshinku wa'inda na 'issafa da wa'inda ma ban lissafa ba in shaa Allah, ina godiya sosai da goyon bayan da kuke bani ta hanyar like,comments da luma sharing,ina matuƙar alfahari daku my Esteem fans,Allah yabar ƙauna,sai mun haɗu a BOOK 2 in shaa Allah*💖💖💖💘💘💘🌼🌼🌼🌹🌹🌹🌹🙃🙃🙃🙃✍️✍️✍️
Daga alƙalamin
🖍️📚Narrnarhh Bukar 📚🖍️
Comments and share 🙏🙏🙏Fisabilillah.