![]() |
🔥 *RANAR MUTUWA* 🔥 |
Chapter 1
Wata jibgegiyar mota ce kirar Benz tsaye a kofar wani makeken gida, driver ya danna horn' take mai gadin yazo da gudun sa ya wangale tafkeken get din gidan ya tura hancin motar cikin gidan" masha Allah na furta sabida tsayawa fadin girman gidan da tsaruwar sa ma bata lokaci ne take ma'aikatan gidan maza suka tattaso duk suka yo wajen motar suna wa mai gidan nasu barka da zuwa glass din motar ya zuge cikin sakin fuska yake amsa gaisuwar ko wannen su" kana driver yaja motar zuwa rumfar da aka tanada domin ajiye motocin, bayan yayi parking ya fito da sauri ya zo ya bude murfin motar' ya zuro kafar sa ya fito daga cikin motar magidanci ne wanda ba zai haura shekaru hamsin da biyar ba zuwa sittin dogo ne baki amma ba can ba dan zaka iya kiran sa da wankan tarwada ya ajiye gemu da kasumba amma ba canba wanda yake karawa fuskar sa kamala da cikar dattako, Alhaji Mudassir kwangila kenan gawurtaccen dan kwangila kenan a duk fadin Nigeria wanda ludayin sa yake kan dawo ake damawa dashi a kasa.
Da gudunta ta karaso inda yake bai ankara ba sai ji yayi ta dane jikin sa ta cukwuikuye farar malum malum din dake jikin sa, oyoyo Abba na ta furta cikin farin ciki sai kuma ta tabe fuska alamar shagwaba we missed you Abba murmushi ya saki ya kamo hannun ta sannan yace I missed you too my baby, sanna ya juya inda sauran suke Siyama ce ta juya ta hade rai kamar zata saki kuka ta furta ni wllh nayi fushi Abba tunda Yasmin kadai kayi missing ni banda ni, matsowa yayi yana murmushi itama ya kama hannun ta ni na isa nace banyi kewar yaya taba' ya kike Siyama ta murmushi tayi ina lafiya Abba na to masha Allah, ya waiga ya kalli Khairat da take tsaye tana murmushi cikin yanayin miskilancin ta' na same ku lafiya mama na' lafiya lau Abba ya hanya lafiya lau uwa ta, sannan ya juya ga uwar gidan tasa hajiya Maryam wacce take tsaye tun dazu tana kallon diramar tashi da yaran wanda ya zamar masu jiki a duk lokacin da ya dawo daga tafiya, uwar gida sarautar mata na same ku lfy' lfy Alhmdllh ay naga hankalin ka yana kan yan rigimar naka muje ciki ka samu ka huta ta juya tayi gaba duk suka rufa mata baya ban da Khairat da ta tsaya ta karbi jakar Abban nasu a hannun driver sannan ta juya ta rufa musu baya.
Suna shiga sama ya haura dashi da hajiyan ta hada masa ruwan wanka ya shiga ita kuma ta fito masa da kayan da zai sa sannan ta sakko ta shiga shirya abinci da ita da yaran wanda suka girka da kansu domin tarar mahifin nasu, domin hajiya Maryam wacce yaran suke kiran ta da Mamy tsayayyar mace ce wacce bata da wasa wajen kula da tarbiyar yaran ta da koyar da su abinda ya shafi aikin gida musamman ta bangaren girki domin tana cewa yaya mata ne babu gatan da zatai musu da ya wuce wannan shiyasa duk irin yawan ma'aikatan gidan bata sakar musu girki ba musamman dan mai gidan.
Suna cikin shirya dining din suka ji sakkowarsa yana kiran su da sigar tsokana mutum ne mai matukar barkwanci musamman idan yana tare da iyalin sa' gamu nan Abba cewar Yasmin ta taso tana yowa inda yake hannun ta ya kama suka karasa dining din suka zazzauna Khairat ce tayi serving kowa da abinda yake so sannan ta zuba wa kanta ta koma ta zauna kowa ya fara ci suna ta hira kadan kadan wanda duka akan tafiyar Abban ce yake basu labari akai suma suna bashi labarin abinda ya faru a sanda baya nan.
Ranar Mutuwa Part (2)
Aisha Muhammad
Bayan sun gama suka dawo falo suka dasa sabuwar hira wacce yawanci duk akan karatun su ne yana wa kowa tambaya dangane da karatun nasa, basu tashi ba har sai da aka kira sallar magariba sannan kowa ya tashi Abban yayi hanyar waje domin zuwa masallaci yayin da su kuma kowa yayi dakinsa, domin yin sallah, bayan an idar bai fito daga masallacin ba har sai da akai sallar isha'i sannan ya fito kuma bayan fitowar tasa ya tsaya sun gaggaisa da mutannen unguwa da masu naiman taimako' dakyar dai ya samu kan sa ya shige gida, lokacin da ya shiga ya tarar da Khairat tare da Aliyu daga can kofar wani corridor da zai mai da kai garden din gidan zaune kan wasu kujeru na concrete suna fuskantar juna, hira suke cike da nishadi, basu lura da shigowar Abban ba har saida ya kusa karasawa kofar falo, da sauri Aliyun ya mike ya nufe shi' tsayawa Abban yayi har Aliyun ya karaso inda yake ya durkusa da zummar gaida shi da sauri Abban ya kamo hannu sa ya tada shi tsaye ya ruke hannu sa suka gaisa ya tambaye shi mutanan gida ya amsa sannan ya shige ciki bayan ya bashi sallahun ya gaida mahaifin sa, bayan shigewar Abban ya dawo inda take ya kalle ta kamar yanda itama take kallon shi, yace Alkhairi na kamar yanda yake kiran ta a yawancin lokuta, ni zan tafi dare yayi kema ki shiga ki kwanta da wuri kince gobe kina lecture 8, mikewa tayi eh wllh amma fa ba don na gaji da ganin ka ba, murmushi yayi ay nima ba gajiya nayi da kallon ki ba kawai dai kinga dare ya fara har Abba ya shiga ciki kinga kar Abba yaga rashin hankali na ko ba haka ba ya fada da sigar wasa dariya tayi itama bata ce komai ba shine ya sake magana yace ki gaida su Mamy da yasmin rigima murmushi tayi kawai tace zasuji insha Allah sai da safe ka gaida Ummi zataji, ya tsaya yana kallon ta tasan mai yake nufi dan haka ta juya ta nufi kofar falon sai da taje kofar ta juyo ya daga masa hannu shima ya daga mata alamar bye ta shige sannan shima ya juya ya shiga motar sa ya bar gidan.
Sanda ya shigo cikin falon ba kowa sai tibi da take ta ayki ya karasa ya kashe sannan ya haye sama, dakin yasmin ya fara lekawa tayi bacci ya kashe mata wutar dakin yaja mata kofa ya leka dakin Siyama ya ganta a zaune tana homework, Abba ka shigo" na shigo yaya ta homework ake ne" eh wllh Abba na manta dashi gaba daya harna kwanta na tuna gashi malamin bashi da mutunci, murmushi yayi eyya yaya ta ay so yake ku koya ne shiyasa kinji ko, Allah ya taimaka ayi karatu sosai, insha Allah Abba, ya juya tai masa sai da safe ya fita yaja mata kofa, dakin Mamy ya leka bata ciki ya juya ya koma dakin sa a nan ya same ta tana kara gyara masa gadon sa, da sallama ya shiga ta dago ta kalle shi, sannu Alhaji na ka kwaso gajiya amma daga fita masallaci naji ka shiru, wllh Maman yara a hakan ma da kika ganni da kyar na wafto, Allah ya kyauta tace kawai tace, ta juya ta fita a dakin bayan tace masa tana zuwa, kitchen taje ta dauko flask din tea ta dawo,sanda ta dawo ta tarar dashi ya canja kayan jikin sa zuwa na bacci yana zaune akan doguwar kujerar da take can gefe a cikin bedroom din yana waya, dan karamin table ta dauko ta ajiye a gaban sa dai dai lokacin yana sallama da wanda suke wayar, sannu Hajiya tayi murmushi tayi ay kaine da sannu Alhaji, zama tayi a gefen sa tana tsiyaya masa black tea din a cup tasa masa siga cube biyu kasan cewar baya da son siga sosai, mika masa tayi yasa hannu ya karba tare da fadin tnx.
Ranar Mutuwa Part (3)
Aisha Muhammad
Shiru ne ya ratsa dakin sai bayan ya gama shan tea din yayi hamdala sannan ya juya ya maida kallon sa gare ta, yayi gyaran murya, yanda taga ya maida hankalin sa gare ta sosai tasan tabbas akwai magana mai muhimmanci da yake son gaya mata dan haka itama ta maida hankalin ta kacokan kan sa, wato kina jina ko Maryama jinjina masa kai tayi alamun tana sauraran sa" akwai abinda na dade ina son fada miki to amma tsoron yanda zaki dauki abin ya sanya ni kawo wa har wannan lokacin ba tare da na fada din ba, ita dai tayi shiru NATA sauraren sa amma fa zuciyar ta ba karamin bugu take ba domin duk wanda aka fadawa haka yasan to tabbas duk maganar da za'a fada din mai daga hankali ce, cigaba yayi ganin tana sauraren sa to amma a yanzu ta kai lokacin da ya zama dole ne a gare ni fada mikin, wato abinda nake son fada miki zan iya kiran sa da wasiyya koma kai tsaye nace miki wasiyya nake son bar mini duk da babu wanda yasan ranar mutuwar sa, ban fahimce ka ba Alhaji" wace irin wasiyya wahayi aka maka da cewa zaka mutu yau ko gobe, murmushi yayi wanda yafi kama da yake ko daya kawai dai ina so kiyi abinda zan fada miki a yanzu ki dauke shi a matsayin umarni na dake na karshe, mikewa tayi da sauri hankalin ta a tashe haba Alhaji wai wace irin magana kake ne haka gaskiya idan ma wasa kake ka daina don kwakwalwa ta ba zata iya dauka ba, mikewa yayi shima cikin rashin kuzari ya kama kafadun ta a hankali ya zaunar da it a sanna cikin dabara ya dinga kwantar mata da hankali da nuna mata babu fa wanda yasan ranar mutuwar sa dan haka gara mu dinga zama cikin shiri wannan shine cikar imani, har ya samu ta sauko wa ka sani ma ko ni zan riga ka mutuwar ma murmushi yayi haka ne sai Allah kadai ya sani, amma ni dai ga tawa wasiyyar idan har ni na riga ki, to mece ce wasiyyar taka, shiru yayi yana nazari can kuma ya nisa" ina son duk randa na mutu ki tabbatar ba'ayi min zaman makoki ba sannan kuma kada ku yarda ku kai ranar bakwai a cikin gidan nan, ina da gidaje da yawa a cikin garinnan da ma kasar baki daya zaku iya zabar daya daga ciki ku koma, idan kuma kun fi son nan din zaku iya dawo wa amma ku bari ko arba'in ayi tukunna, shiru tayi kawai tana nazarin maganar tasa, hannun ta ya kama ki min alkawari zaki cika min wannan wish nawa, insha Allah tace jikin ta a sanyaye daga haka ta mike ka tashi ka kwanta dare ya fara ga gajiya, bari na leka yaran nan nima naje na kwanta, Allah ya tashe mu lfy kawai yace da ita ta juya ta fita taja masa kofar.
Ko bayan taje ta kwanta kasa bacci tayi tana ta faman sake sake har sai wajen asuba sannan bacci barawo ya sace ta, kasancewar bata samu bacci da wuri ba yasa ta makara bata tashi ba har sai da haske ya hasko cikin dakin nata, firgigit ta farka tana ambaton sunan Allah, a hankali ta sakko da kafafun ta kasa, tana jin kanta na sara mata sakamakon rashin samun ishashshen bacci sannan gaban ta sai faduwa yake, haka dai ta sakko a hankali ta nufi kofar toilet ta tura ta shige tayo alwala ta fito tana hanzarin shimfida sallaya ta saka hijab ta tada sallah, tana idarwa addu'a ta shafa tana mikewa a hanzarce tayi hanyar kofa, domin dubo Alhaji ko ya tashi don tayi mamaki da bai tashe taba" kasancewar ya saba duk asuba shi yake tashin su koda kuwa ka tashi dai zai leko ya tabbatar kafin ya wuce masallaci.
Ranar Mutuwa Part (4)
Aisha Muhammad
Ta tura kofar dakin nashi da sallama tana saka kai zuwa ciki tana shiga gaban ta ya sake faduwa sosai har saida tasa hannu tana dafe kirjin ta, hango shi tayi kwance a kan gadon nashi yana kallon sama a hankali ta karasa gaban gadon tana kiran sunan sa, abinda taci karo dashi yasa ta kwalla karar da taja hankalin yaran dake dakunan su, suka fara rige rigen fitowa duk suka yo dakin Abban inda suke kyautata zaton daga nan suka jiyo ihun Mamyn, suna shiga suma abinda suka gani din yasa jikin su fara rawa Khairat ce tayi karfin halin rike Mamyn gani tana neman faduwa innalillahi kawai suke ambato Yasmin ce ta kalli Mamy tana kuka Mamay meya samu Abba babu wanda ya iya bata amsa illa Khairat da ta juya da sauri dattijon mai gadin su taje ta kira, da saurin sa ya biyo bayan ta gani yanayin ta suna shiga ya tarar da Alhaji a kwance baya numfashi ga jini ta idon sa da hanci da kunnen sa ya zubo sosai har ya bata zanin gadon da yake kai, a firgice yaja da baya, Hajiya garinya ya mai ya faru ya fada cikin kidimewa wllh baba sa'idu muma haka muka zo muka same shi, to yanzu abinda za'ayi dole a fara kiran yan sanda sannan kuma a kira yan uwan sa, kai kawai ta jinjina masa, ya juya ya fita, wani makwabcin su ya fara kira wanda dama duk sunfi kusa tsakanin sa da Alhajin a unguwar, bayan ya shigo tare da matar sa, yasa su Hajiyan dawo wa falo suka zauna tare da matar sa sai faman kuka suke tana ta aykin basu hakuri, bayan fitar sa police ya fara kira sannan ya kira yan uwan Alhajin ya sanar dasu bayan ya karbi number din su a hannun Hajiya.
Kan kace kwabo gidan ya cika da yan uwa da abokan arziki sai koke koke matan keyi yayin da mazan suna waje tare da police bayan sun shiga sun gama daukar dukkan wasu bayanai, sallama suka musu tare da ta'aziyya suka wuce bayan sun karbi number din daya daga cikin yan uwan Alhajin akan duk abinda ake ciki za'a neme su, sannan zuwa nan da ayi uku zasu dawo domin daukar baya nan Hajiya da na yaran domin yanzu suna cikin tashin hankalin da baza su iya bada wani bayani ba, godiya suka Yi musu sannan suka koma ciki domin shirya Alhajin zuwa gidan sa na gaskiya, dukkan wani mai rai sai ya dan dani zafin Mutuwa Allah kasa mu cika da imani Ameen.
Bayan an kai shi an dawo, Wasiyyar Alhaji ce ta jiya ta fadowa Hajiya hawaye ya zubo mata ta saka gefen hijabin ta ta share a hankali ta tashi kamar zata fadi ta nufi dakin da Hajiya yaya take ciki wacce ta kasance babbar yayar su Alhajin ce koma a kira ta da uwa domin kuwa ita ta rike su tun basu mallaki hankalin kansu ba shiyasa suma suka dauke ta tamfar uwa da wasu daga cikin yan uwa, ta tarar da Hajiya yayan sai sambatu take da gunjin kuka kasan cewar mutuwar ba karamin dukan ta tayi ba sannan kuma dama ga rikicin tsufa, karasawa tayi inda take ta zauna daga dan gefen ta ai kuwa kamar an kara tura ta kara kaimin kukan tayi Allah sarki baiwar Allah yarinyar kirki kunyi maraici ta kamo hannun mamyn tana ta sambatu wai rarrashin ta take, dakyar ta samu tayi shiru sannan ta kara matsawa kusa da ita tace Hajiya dama akwai wasiyyar da Alhaji ya bani a jiya da daddare shiyasa nace bari nazo na same ki a kira su Kawu da su yaya a sanar dasu, to Maryama bari na saka a kira su, juyawa tayi ta kalli Mama Saude itama kanwa ce a wajen Alhajin tace Saude tashi kije ki kira su Kawu da Saminu kice su same mu a falon bayan, to tace tana mikewa tayi waje suma tashi sukayi suka wuce zuwa falon,
Ranar Mutuwa Part (5)
Aisha Muhammad
bayan duk sun hallara take shaida musu wasiyyar dan uwan nasu, ay take Hajiya yaya tayi tsalle ta dire tace ba'a isa ba, ba wanda ya isa ya hana ay wa dan kanin nata zaman makoki kuma a cikin gidan sa za'ayi, ita bata son kiturun munafirci dan cewa tayi ma Hajiya Maryam din ce ta tsara saboda wata manufa tata, babu yanda ba'ayi da ita ba amma fur taki amincewa karshe ma tashi tayi tabar musu falon ta koma inda ta baro tana ta faman mita, Hakuri suka bawa Hajiya Maryam din da take ta shafar hawaye, tare da cewa tayi hakuri har a share makoki inyaso daga baya bayan Hajiya yayan ta tafi sai su tashi su koma wani wajen kamar yanda Alhajin ya bukata, Allah ya gani tayi kokari wajen cika masa alkawari tunda ta isar da wasiyyar tashi, dan haka duk mazan suka tashi suka koma waje aka cigaba da karban gaisuwa.
Kwanci tashi ba wuya A wurin Allah yau akai sadakar ukun Alhaji zuwa yamma wasu duk suka tattafi gidajen su da zummar sai kuma ranar bakwai gidan ya rage yawan jama'a sai yan uwa na jiki sosai sai kuma masu shigowa gaisuwa su tafi, hakan ya kara sawa mutuwar dawo wa iyalin nashi sabuwa sun zauna su kadai sai kuka haka yan uwa keta kokari wajen kwantar musu da hankali da nuna musu mahimmancin tawakkali ga wanda Allah ya jarabbata a haka dai har akai bakwai a ranar ne kuma kowa ya watse ya zama daga su sai Hajiya yaya da tace baza ta tafi ba har sai taga sun kwantar da hankalin su tukunna, a ranar da daddare suna zaune a falo su biyi daga Hajiya yayan sai Mamy Yasmin da Siyama sun tafi sun kwanta sai Khairat kuma tana waje Aliyu yazo ya kara mata gaisuwa suma duk jira suke da shigo suje su kwanta, wani razanannan ihu sukaji daga sama mai matukar kara wanda ya sanya su mikewa a tare suka nufi saman daga dakin Alhaji suke jin ihun da sauri suka tura kofar dakin suka shiga amma suna shiga sai suka daina jin ihun, sai kuma suka hango wani flower vase akan dan table din gaban gado a hankali suka karasa wajen jini ne a jikin abun faca faca da sauri suka rike juna duk jikin su na rawa kamar mazari, wanda yayi dai dai da turo kofar dakin hakan ya kara razana su Hajiya yaya har tana sakin fitsari daga tsaye, Khairat ce tare da Aliyu wanda suma ihun ne ya gigita su ya saka su sauri shigowa cikin gidan, karasowa ciki sukai suna tambayar su Hajiyan abinda ya faru, da hannu suka shiga nuna musu table din abinda suka gani suma ya girgiza su Khairat ce tace mamy menene wannan haka muka gani muma Khairat bamu sani ba, to Mamy ina su Yasmin sai a sannan duk suka tuna da sauri suka nufi dakin Yasmin da suka bar Aliyu yana nazari akan lamarin, dakin Yasmin suka fara shiga wanda ya kasance na farko bacci suka tarar tana yi shiga Mamy tayi ta dauko ta ta fito da ita tana shafa kanta ta sukai dakin Siyama a kwance suka ganta tana kallon sama yanayin kwanciyar ta kawai ya sanyaya musu jiki kasancewar a haka suka tarar da Alhaji a ranar daya rasu a hankali suka karasa gaban gadon da sauri Mamy taja baya tana rike bakin ta tana sakin kuka Hajiya yaya ce tayi saurin riko ta ganin tana neman faduwa, Khairat ma kukan take tana kallon yar uwar ta ta jini ne ta idon ta hanci da kuma kunnen ta the same irin na Abban nasu, kururuwar kukan Hajiya yaya ne yaja hankalin Aliyu da yeke can yayi nisa cikin tunani da gudun sa yayo dakin da yake jin kukan na tashi, abinda ya tarar shima ya daga masa hankali ba kadan ba waya ya dauka ya kira police din da suke bincike akan mutuwar Alhaji duk da har yanzu sun kasa gano komai, sannan ya karbi wayar
Ranar Mutuwa Part (6)
Aisha Muhammad
Khairat ya fita yana neman number kanin Alhaji Kawu Saminu.
Bayan ya kira shi zama yayi kawai a falon yana kara fadada tunanin sa a kan lamarin amma dai har yanzu babu abinda kwakwalwar sa ta hasa so masa cikin mintina da basu wuce sha biyar ba Alhaji Saminu ya karaso direct falon ya nufa a nan ya tadda Aliyun yayi shiru yana nazari, shigowar sa ce ta sanya Aliyun saurin mikewa yana isa kusa da shi suka gaisa sannan yace masa meya sami Siyaman ne Aliyu, hanyar stairs din kawai ya nufa yana cewa Kawun muje Kawu, da sauri Kawun ya bishi har yana wuce shi ya haura saman, dakin Siyaman ya nufa kai tsaye yana zuwa abinda ya gani shima ya sanya shi cikin dimuwa sosai haka ya samu waje ya zauna dafe da kan sa ya kasa furta komai a haka har police suka iso suka gama binciken su da yan tambayoyi sannan suka fito suka zazzaga gidan, duk Aliyu na biye dasu suna kara tattaunawa akan lamarin, bayan sun gama binciken duk abin da ya dace su bincika suka musu sallama da ta'aziyya suka fito Aliyu ne ya biyo su suna kara tattaunawa da inspector din kasan cewar dama yasan shi tare sukai karatu sanda suna secondary school sallama sukai tare da exchanging phone number akan duk abinda ake ciki zasu dinga comnicatin.
Haka alummar gidan sukai kwanan tashin hankali bayan anyi wa mamaciyar sutura zuwa washegari a mika ta gidan ta na gaskiya, washe gari bayan an kaita an dawo ana zazzaune a falon Khairat na kwance akan cinyar Mummy matar Kawu Saminu bayan tasha magani kasancewar ta kwana da zazzabi mai zafi ba yanda ba'ayi da ita taje asibiti ba amma fur taki, Hafsat ce yar gidan Kawu Saminu ta shigo tare da yan department dinsu kawayen su Khairat din kasancewar department dinsu daya da Khairat din sunzo musu gaisuwa, bayan sun gaggaisa da mutanen falon sunyiwa Mamy gaisuwa, Mamy tace Hafsa kaisu garden akwai carpet da aka shinfida dakin Khairat din ma akwai mutane, amsawa tayi tana tashi suka bi bayan ta, Mamyn ta juya inda Khairat take tace Khairat ki daure ki tashi kije ku gaisa kinga dan ke suka zo, Mummy ma tace eh zama ki fi warwarewa da to ta amsa sannan ta mike a hankali ta fice daga dakin duk suka bita da kallon tausayi, bayan fitar ta ne Yasmin dake manne da jikin Mamy tun jiya tace Mamy nidai bazan kuma barin kusa dake ba kar wani abu ya same ni, tausayi ta bawa mutane Mamy ta shafa kan ta babu abinda zai same ki da yardar Allah, to tace kawai cike da kuruciya.
A hankali take tafiya cike da yanayin sanyin ta wanda ya kara haduwa da ciwo da kuwa matsanan ciyar damuwa da take tare da ita, Aliyu ne ya hangota yana daga can bakin gate din gidan tare da police din da aka bari su dinga kula da masu shige da fice a cikin gidan, da sauri yayo inda take bata kula dashi ba dan haka ta tsorata da ganin sa kawai a gaban ta, Alkhairi na ya jikin naki da sauki ta amsa masa a takaice to ina zaki kuma bayan jikin ki ba kwari, yan school dinmu ne suka zo gaisuwa suna garden, ok to sai kin dawo, cigaba tayi da tafiya ya tsaya kawai yana kallon ta son ta da tausayin ta na kara shigar sa har saida ta bacewa ganin sa sannan ya nisa insha Allah sai Allah ya toni asirin duk wanda keda hannu akan lamarin nan ko wanene shi,
Ranar Mutuwa Part (7)
Aisha Muhammad
Bayan Isar ta garden suka kara gaggaisawa tare da kara yi mata gaisuwa sannan sukai dan shiru, shiru zuwa can kuma suka fara tattaunawa akan exam da zasu fara karshen wata, ita dai tana zaune tana jin su can aka kira hafsa a waya ta mike tayi can baya suna tsokanar ta da ba'a so suji hirar masoya, ita dai banza ta musu ta cigaba da wayar ta saurayin tane wanda zata aura Jabir hira suke sosai cike da shauki ji tayi ta fara gajiya da tsaiwa sai ta fara takawa a hankali can daga dan nesa da ita ta hango wasu kujeru, nufar gurin tayi tana tafe tana wayar ta bata ankara ba ashe tayi tafiya mai nisa kafin ta iso wajen kujerun tana zuwa taga sunyi masifar datti ba zai yiwu a zauna ba tare da an wanke ba, sai kawai taga wani dutse daga gefe ta karasa ta zauna ta cigaba da wayar ta sunyi wajen minti talatin suna wayar sannan suka yi sallama, sannan ta tashi da niyyar komawa, sai taji kamar kuka daga bayan ta, ta dan juya da sauri tana duba bayan ta amma bataga kowa ba ta kara juyawa sai ta hango wata kofa daga can cikin wasu ganyayyaki kusa da bishiyar da ta jingina tana waya, kusan rassan bishiyar sun kusa rufe kofar a hankali ta karasa wajen kofar tana kara jin kukan yana kara kusanto ta hannun ta tasa ta dan taba kofar, sai taji gaba daya tsigar jikin ta tana tashi hannun ta kamar ta taba shocking da sauri ta janye hannun ta kuma ta fara jin tsoro na shigar ta da sauri ta juya tabar wajen tana sauri kamar zata tashi sama, har saida ta kusa karasawa inda ta baro kawayen su sannan ta tsaya ta dan daidaita nutsuwar ta sannan ta karasa, tsokanar ta suka shigayi ita dai tayi shiru jikin ta duk a sanyayaye, daga nan suka mike ma suna musu sallama za su tafi domin daman daga makaranta suka yo nan din, tashi sukayi suka Dan taka musu sannan suka musu sallama tare da karin addu'a ga mamatan, su kuma suka musu godiya, suka fice daga gidan su kuma suka juya domin komawa.
A hanyar su ta komawar ne Hafsat ta kasa hakuri har sun kusa shiga falo tayi saurin kamo hannun Khairat, Khairat dama akwai wani bangare a gidan nan wanda ba'a amfani dashi? Kamar yaya ban gane ba, eh ta can bayan garden, Aa ke a ina kika gani, wllh na gani dazu da na zaga nayi waya sai na hango wasu kujeru daga can wajen bishiyoyin nan dai bayan na karasa sai naga duk sunyi datti sai naga wani dutse daga jikin wannan babbar bishiyar, na karasa na zauna har na gama wayar na tashi zan tafi sai nake jin kamar kuka na jujjuya amma banga kowa ba kawai ina juyawa jikin bishiyar dana tashi sai naga kamar kofa duk rassan bishiyar duk sun rurrufe kofar sai kadan ake hango ta, har na karasa wajen sai kuma naji tsoro na bari na taho, kallon ta kawai Khairat tayi kedai wllh kin cika tsoro waye ma yake zuwa wajen bare har yayi wani kuka nifa kinga wani kwatancen ki da kike min ma ba ganewa nake ba don Abba bai taba bari wani yaje wajen ba, dai dai da masu aikin gidan nan maza ya hana su zuwa wajen sabida yace wajen ya dade a haka ba za'a rasa wani abu mai cutarwa a wajen, dan haka babu wanda ya taba zuwa wajen a gidan nan, amma wllh nidai naji wani yana kuka a wajen, tsaki ta yi ke dai wllh tsoron ki yayi yawa dan Allah ki bar wannan maganar mu shiga ciki na kwanta kinga ba dadi nake jiba.
A haka har akai sadakar uku kowa ya watse amma Hafsat tace bazata tafi ba har jikin Khairat ya sake warwarewa, amma a zuciyar ta so take ta samu damar da zata koma wajen nan.
Ranar Mutuwa Part (8)
Aisha Muhammad
domin ta tabbatar da abinda ta gani, mahaifiyar ta bata so ba domin yanzu ita gidan tsoro yake bata, amma ganin kowa yayi na'am da maganar tana yin wata magana Hajiya Yaya zata hauta da bala'i yasa ta amince.
Kashe gari da safe bayan sun tashi sunyi sallah kowa ya koma bacci Hafsat ta tashi ta fito ta sauka a hankali dan kar wani ya tashi ya tambaye ta inda zata, bayan ta sauko ta tarar da yan aiki kowa yana nashi aikin suka gaggaishe ta kasancewar Hafsat din dama yar gida ce duk sun saba da yan aikin kuma dama gwanar faran faran da jama'a, haka suka gaisa tare da dan barkwanci, tasa kai ta fice cikin hanzari kada wani ya tashi a cikin mutan gidan, da sauri ta zaga tayi hanyar garden mai bawa fulawa ruwa yana aikin sa yaga wucewar ta ya bita da kallon mamaki kan abinda zai kaita garden da wannan farar safiyar, ya juya ya cigaba da aikin sa, bayan ta karasa bakin kofar wannan kukan da taji a wancan lokacin yanzu ma shi take ji kamar ma yafi na jiya, kuma sai tsoro ya fara kamata tayi karfin hali tasa hannu ta tura kofar ga mamakin ta sai taga ta bude kanta ta fara zurawa ta leka kawai sai kafar ta ta zame ta sulala cukin dakin na jiyo sanda tayi kara daga nan kuma sai naji shiru har wannan kukan ma babu.
Wajen karfe goma Khairat tayi mika tare da salati sannan ta mike tayi toilet ta dade bata samu bacci irin na yau ba tunda wannan iftila'in ya fado musu cikin gidan, toilet ta nufa tana mamakin sanda har Hafsat din ta tashi amma ko motsin ta bataji ba, brush tayi sannan ta watsa ruwa a gurguje sabida yunwar da ta tashi da ita kasancewar rabon da ta sakawa cikin ta wani abincin kirki tanaga tun randa Abban su ya dawo daga tafiya, bayan ta fito ta shirya cikin wata doguwar riga ta wani material mara nauyi ta dauki dan kwalin kayan ta daura shi akan ta sannan ta dauko wayar ta tana kunnanwa tana fita a dakin, dakin Mamy ta fara lekawa bata nan hakan ya tabbabtar mata tana kasa, itama saukar tayi, alamar motsin su taji a dining ta nufi wajen ta tarar dasu suna karyawa duk da ba wani cin abincin suke ba suna dai tsakura ne, karasowa tayi ta nemi waje ta zauna sannan ta gaida su suka amsa suna mata ya jiki da sauki ta amsa sannan taja flask ta hada tea ta dauki flate ta dan zuba chips ta fara ci tana kurbar tea din, ta kalli Mamy, Mamy ina Hafsat tayi ko ta leka school ne, aa Hafsat kuma ai ke zamu tambaya na dauka bata tashi bane aa ni tunda na tashi bata dakin na dauka ta sauko ne, aa bari na duba ta tashi tayi ta lelleka dakunan gidan amma bata ganta ba ta dawo ke nifa ban ganta ba kira ta a waya ko ta fita ne muna bacci, wayar ta ta dauka ta kira Hafsat din amma bata daga ba saida tai mata kira uku, sannan tace Mamy bata daga ba bari na tambayi su ladi mai aikin su ko sunga fitar ta da to Mamyn ta amsa tana komawa ta zauna akan daya daga cikin kujerun falon, bayan ta tambaye su suka ce tabbas sunga fitar ta amma bada shirin fita ba kayan bacci ne ma a jikin ta sai dai a tambayi sauran ma'aikatan gidan maza dake waje domin sunga wajen ta fita, fita tayi taje ta tambayi baba mai gadi, sanda taje ta tambaye shi yace shidai gaskiya baiga fitar ta ba mai bawa fulawa ruwa ne daya karaso wajen bayan ya gaishe ta yake cewa wai wa ake nema ne, baba mai gadin ne yake ce masa yarinyar nan Hafsa yar kanin Alhaji, aiko na ganta sanda nake yanke fulawoyin can tayi hanyar garden, gaban Khairat ne ya fadi kawai tunawa tai da maganar da sukai jiya ta juya da sauri taje ta gayowa Mamy sai sukai kicibus ta biyo bayan ta jin
Ranar Mutuwa Part (9)
Aisha Muhammad
taji ta shiru, ya akai ne Khairat wai ance an ganta tayi hanyar garden to muje, hanyar garden din sukai can gaba dayan su suka samu kansu da faduwar gaba haka kawai, sun duba duk cikin garden din amma basu ganta ba, dawowa sukayi suka kara tambayar sa tabbas ya ganta sanda tayi wajen, ya tabbatar musu da tabbas ya ganta kamar ma tana sauri sannan kuma yana bangaren wajen har sai yanzu ya baro wajen kuma baiga fitowar ta ba, baba mai gadi ne tare da mai musu wanki sukaje muje a kara dubawa hajiya, dai dai lokacin da Hajiya Yaya itama ta karaso wajen tana jin abinda ake fada tace hakane muje a kara dubawa, amma fa a lokacin hankalin kowa ya fara tashi sakamakon irin abubuwan da suka faru a gidan.
Ko bayan sun dudduba suma basu ganta ba Hajiya Yaya tace to muyi ta can wajajen mana, mai kula da fulawa ne yace hajiya Alhaji ya hana zuwa wajen koda wasa, kaniyar ka ta watsa mai dakuwa to ni uwar Alhajin nace aje ko baza kuje ba aa kiyi hakuri Hajiya wane mu, suka saka kai suka nufi wajen tun kafin su karasa suke hango wani abu kamar mutum a kwance, da sauri suka karasa suna zuwa ko wannen su sai da yaja da baya matan suka hade kansu waje daya suna fashewa da kuka su kansu mazan abun ya basu tsoro, baba mai gadi ne yayi karfin halin basu hakuri, mai wanki yace yanzu mene abinyi, eh to kaga dai bama taba ta cewar baba mai gadi, yanzu abinda za'ayi kai lawan jeka gidan Alhaji Muktar Allah yasa bai fita ba ka kira shi, inyaso sai ya kira yan sanda da mahaifin ta, haka ne kam bari naje.
Tare suka dawo da Alhaji Muktar hankalin sa a tashe, bayan yazo police ya fara kira sannan ya kira Alhaji Saminu yace maza suzo gidan babu lfy, sannan ya samu ya lallaba matan suka shiga ciki, bayan shigar su da yan mintina Alhaji Saminu ya iso tare da matar sa, Alhaji Muktar ne ya fito suka shiga tare, ita Mommy direct cikin falon tayi wajen su Hajiya yayin da shi kuma Kawu Alhaji Muktar yaja shi zuwa bayan gidan sai faman tambayar sa yake abinda ya faru amma yayi masa shiru ya bari idon sa ya gane masa, aikuwa yayi mummunan gani domin har saida Alhaji Muktar ya rike shi domin har yana neman faduwa ban fa gane ba Alhaji nifa ina zargin wani abu, anya kuwa, kayi shiru kawai Alhaji zamu tattauna amma yanzu dai ka bari tukun na kaga ma kamar yan sanda nake ji sun iso .
A can cikin gida kuwa Mommy na shiga ta fara jera musu tambayar abin da ya faru suka ji irin wannan kira sannan gashi tazo ta same su a cikin wani hali, amma an rasa mai amsa mata tambayar ta, ana haka police suka iso, jiniyar yan sanda da taji ya kara gaya mata tabbas ba lfy ba wai Hajiya me yake faruwa ne kun barni a cikin duhu, naji harda yan sanda, wai ina Hafsat ne ma, nan ma shirun suka mata, tana ganin haka jikin ta ya bata akwai wani abu, da sauri ta juya tayi waje, sanda ta fita yayi dai dai da shigowar police din tare da Alhaji Muktar suka yi hanyar garden, da sauri tabi bayan su, abinda taci karo dashi yasa numfashin ta daukewa na wucin gadi, take ta yanke jiki ta fadi da sauri aka yo kanta da sauri, tuni ta suma nanda nan Alhaji Saminu ya dauke ta yayi cikin gidan da ita, su Hajiya Yaya suna ganin shi da ita hankalin su ya kara tashi dama sun san za'ai haka yanda suke masifar son Hafsat din kasan cewar ita daya suka haifa bayan dogon lokaci da suka dauka kafin ma su sametan, sama aka wuce da ita,
Ranar Mutuwa Part (10)
Aisha Muhammad
dakin Mamy aka kai ta aka kwantar a gado sannan tuni Mamyn tayiwa family doctor din su waya yace gashi nan zuwa, haka suka zauna jigum jigum a dakin suna jiran karasowar doctor yayi da shi kuma Alhaji Saminu ya dauka ya koma wajen police din.
Sosai police din sukai iya kokarin su wajen yin dukkan nin abinda ya kamata domin suna matukar tausayawa iyalin gidan, dan haka suna yin duk mai yiwuwa wajen ganin sun gano gaskiyar al'amarin amma abin yaci tura, bayan sun gama abinda ya dace suka musu sallama tare da ta'aziyya sannan suka wuce da alkawarin duk abinda ake ciki zasuji sannan suma idan sun dan sami wata shaida ko kuma wani da suke zargi suyi gaggawar tuntubar su, musabaha suka kara yi da Alhaji Muktar sanna suka juya suka fita domin shi Alhaji kawai yana zaune ya dafe kan sa cikin rashin sanin makama da tsantsar tashin hankali, bayan Alhaji Muktar ya dan taka musu ya dawo yazo ya data kafar sa sai hakuri Alhaji, yanzu ba lokacin tuna ni bane kamata yayi ka tashi mu samu aje ayiwa yarinyar nan sutura akai ta makwancin ta Allah gafar ta mata, da amin ya amsa masa sannan ya mike ya dauki wayar sa ya shiga kiran wadan da ya kamata su sani.
A can wajen Mommy kuwa bayan likita yazo yayi duk gwaje gwajen daya dace ya shaida musu ba wata matsala kawai dai ta firgita ne wanda hakan ya sanya jinin ta hawa sosai dan haka sai an kula da ita sosai, sannan ya mata allur bacci sabida ta samu hutu sosai, godiya sukai masa ya musu sallama ya tafi, bayan nan Alhaji Saminu ya shigo ya duba jikin ta sannan yake tambayar Hajiya Yaya akan inda za'ai jana'izar Hafsat din, tace kawai ayi anan tunda dama ana kan wani zaman makokin ne, ya amsa da hakan ma yayi tunda ai duk gida ne, sannan ya tashi ya fita yana neman layin yan uwan Mommy domin ya sanar musu.
Bayan an kai ta an dawo, bayan gidan Kawu Saminu yaja Alhaji Muktar can bayan gidan, wllh Alhaji bazan yarda ba akan me za'amin haka menene kuma ya sako yata a cikin wannan.
A can kuma Mommy ta farka sai faman kuka take ana bata baki amma taki sauraron kowa, hakan yasa Hajiya Yaya ta fita da niyyar kiran kawu Saminu taji ya kuwa kira yan uwan Mummyn, bayan fitar ta kuma sai ga yayyen ta da kannen ta sun iso, haka suka zauna suma suka dora bata bakin amma taki shiru har sai da babbar yayar su ranta ya bacci ta hau ta da fada, haba Saratu kamar ba musulma ba, ke kadai aka tabawa mutuwa, kowa ba tawakkali yake ba, yanzu ke baki ga misali akan Hajiya Maryam ba, naga a cikin abinda baifi sati daya ba akai mata mutuwa har biyu gata miji ga ta ya kuma naga ay Hafsat din ma yarta ce dan kowa zai shaida yanda ta dauke ta amma ba tayi tawakkali ba, yanzu gashi har da ita ake baki baki, to ni bana son sakarci, kija bakin ki kiyi shiru kiyiwa yarinyar nan addu'a muma duk ita muke mata, da kika gan mu haka bawai ba muji mutuwar bane ai Hafsat yarinya ce mai shiga rai ba wanda za'a ce yasan ta kuma ace baiji mutuwar ta ba, kawai muna daurewa ne sabida mu musulmaine ne shi kuma musulunci ya koyar da mu tawakkali akan kowacce irin jarabawa, mutanan dakin suka amsa da hakane, a hankali ta tashi ta shiga toilet ta wanke fuskar ta sannan tayo alwala tazo ta gabatar da sallar azahar wanda ake ta kira, bayan ta idar ta daga hannu ta dinga kwararowa tilon diyar tata addu'ar samun rahamar ubangiji tana hawaye, sannan tana rokon Allah ya bata dangana da hakuri
Ranar Mutuwa Part (11)
Aisha Muhammad
bayan ta shafa ta mike ta koma kan gadon tana jan carbi, yayar tasu da suke kira da Aunty, tace yauwa ko kefa saratu kinga abinda ya kamata kiyi kenan tun farko domin shi mamaci babu abinda yake bukata illa addu'a, Allah ya gafarta Allah yasa ta huta, gaba daya aka amsa da ameen, sannan duk suka mimmike domin dauro alwala, wasu sauka sukayi kasa wasu suka nufi dakin Hajiya da na yaran.
Ita Hajiya Maryam bayan ta shiga daki sai da ta fara watsa ruwa sannan ta dauro alwala ta fito ta shirya sannan ta tada sallah, hakan yasa duk suka riga ta idarwa, tun tana sallah take jin hayaniya sosai da ta wuce ace ana yinta a gidan mutuwa hakan ya bata mamaki tana alla alla ta idar taji ba'asi domin hayaniyar ma kara yawa take, tana yin sallama ta juya ta kalli kanwar wacce ta kasance autar su Safiyya wacce ke kwance akan makeken gadon dakin tana waya don ita tun tuni ta idar da sallar ta, safiyya wai bakya jin hayaniyar da ake agidan ne amma kina kwance, sallama tayi da wanda suke wayar, wllh Aunty ina taji amma na dauka wasu bakin ne, tsaki ta ja, haba Safiyya yanzu ace kalau a gidan mutuwa mutuwar ma irin wannan ace ana wannan hayaniya haka kinji fa kamar harda kuka ma, kai Aunty to dama wai ana raba gidan mutuwa da kuka, uhmm kinga fita ta naga alama baki da hankali zaman hijabin dake jikin ta ta gyara tana yin waje, itama Safiyyan saukowa tayi tabi bayan ta, a falo suka tarar duk anyi cirko cirko masu kuka nayi wasu kuma kawai sun rafka tagumi, harda Hajiya saratu ( Mommy) ta juya ta kalli Mama saude kanwar su Alhaji tana ta rabzar kuka, hankalin tane ya kara tashi wai me yake faruwa ne ku sanar da ni mana, kowa ya kasa magana, inda Khairat take tsaye itama matsar kwalla take tace ke Khairat wai me yake faruwa ne, cikin muryar kuka ta fara magana Mamy Hajiya Yaya sai kuma kuka yaci karfin ta, ke bana son shashanci meya sami Hajiyan, ana haka sukaji shigowar police, nan kowa ya maida hankalin sa gare su, nan suke sanar da suna bukatar a tattaro musu dukkannin wadan da ke cikin gidan a hadu a harabar gidan, kuma a tabbatar da koda yaron goye ne indai yana a cikin gidan an fito dashi, nan fa Hajiya Maryam ta kara shiga rudu tambayar ma ta gagara cigaba da yinta taja bakin tai shiru nan fa kowa ya dunguma zuwa waje, Yasmin ce tai saurin zuwa jikin Mamy ta rirrike ta sosai kamar za'a kwace mata ita, Mamy wai da gaske Hajiya Yaya ta mutu, kenan muma duk mutuwa zamuyi tayi tambayar cike da yarinta, jikin Mamyn ma rawa yake amma ta gayyato jarumta ta sakawa kanta, cikin karfin hali tace babu abinda zai same mu da izinin Allah kinji ko, naji Mamy amma ni dai tsoro nake ji, kada kiji tsoro kinji baby na Allah yana tare damu kiyi addu'a, haka dai suka je kowa ya nemi waje ya zauna wasu kuma suna tsaye, police din suka shiga cikin gidan suka gama duk binciken da zasuyi suka fito, sannan suka ce kowa zai iya tafiya amma kafin nan zasu dauki bayanan kowa da yake cikin gidan domin idan bukar sa ta taso za'a neme ka, domin kowa abin zargi ne akan mutuwar Hajiya Yayan domin ita mutuwar ta ta ban banta da ta su Alhaji, ita alamu ya nuna kamar an buga mata wani abu ne akanta wanda yayi sanadiyyar mutuwar ta, Alhaji Muktar ne tsaye akan komai domin shi Alhaji Saminu daya kamata ace shike tsaye akan abun bazai iya tabuka komai ba yana can zaune daga gefe yana ta sharar hawaye kamar mace, dan dole yai kuka dan Hajiya Yaya uwa ce a gare su kuma tsayayyar mace ce data tsaya musu
Ranar Mutuwa Part (12)
Aisha Muhammad
akan duk wata dawainiyar rayuwa har suka zama mutane dan baza suce sun san dadin iyayen suba itace tazamar musu uwa kuma uba dole yai kuka, bayan Alhaji Muktar ya raka police din sun tafi shi ya dawo yasa matan suka koma ciki sannan ya samu yasa Alhaji Saminu kiran su Kawu da sauran yan uwa ana sanar dasu rasuwar Hajiya Yayan.
Bayan an shigo da gawar domin yi mata sutura nan fa gida ya kuma kacamewa da koke koke haka dai aka manta wanka aka shirya ta domin kaita gidan ta na gaskiya, Hajiya Maryam dai zaune take kawai amma abubuwa sai yawo suke mata a kwakwalwa tunani kala kala take a ranta har saida taji kanta ya fara sara mata sannan ta saurara, amma har lokacin tunani take akan lamarin, har a lokacin babu digon hawaye idon ta dan zuwa sannan zuciyar ta ta kekashe, tashi tayi ta haura sama domin gabatar da sallar asar, bayan ta idar ma zama tayi a wajen tana lazimi da addu'ar Allah ya kawo musu karshen musiba, ba ita ta sakko ba har saida tayi sallar magriba duk abinda ake bukata sai dai aje a tambaye ta, tana fitowa suka hadu da Khairat wacce itama take niyyar sauka, sannu Mamy, yauwa Khairat kema sannu ta tsaya tana kallon yanda duk ta rame ta fita hayyacin ta, tausayin kansu ne ya kamata yanda gaba daya rayuwa ta sauya musu a lokaci daya, Mamy ta kira sunan ta ganin ta tafi duniyar tunani, firgigit ta amsa tana kokarin dai daita yanayin ta, uhmm kema sauka zaki eh wllh Aliyu ne yazo ya mana gaisuwa ya sami labari dama yanzu nake niyyar na leka na miki magana zai shigo falo ya muku gaisuwa, OK ba damuwa muje.
Bayan ya musu gaisuwa ya fita Khairat din ta tashi ta shiga kitchen ta dauko masa robar ruwa da cup tabi bayan sa, a zaune ta same shi a inda suka saba zama, sallama ta masa ya amsa, sannan ta karasa ta ajiye masa ruwan daga dan gefen sa kadan sannan ta sami waje ta zauna tana gaida shi ya amsa mata sannan cikin son kawar mata da damuwar daya hanga sosai akan fuskar ta, yace to ai baki karasa aikin naki ba wife, hararar wasa ta masa dama yayi ne da gayya ya san bata so yana kiran ta haka tace tukunna dai ai bata zama ba da saura mai yawa, hannun sa ya daga alamar ban hakuri, afuwa Alkhairin Allah murmushi tayi sannan ta mike ta zuba masa ruwan a cup ta dauka ta mika masa, ya karba sannan ta koma mazaunin ta ta zauna tana wasa da gefen hijabin ta, shi kuma yana sha a hankali yana satar kallon ta, sai da ya shanye tas sanna ya ajiye kofin yayi hamdala, na gode amarya ta insha Allah ai dai yanzu banyi laifi ba, kallon sa tayi kawai dan ta fuskanci yana sone yasa ta dan saki jikin ta dan ya fahimci damuwar ta hakan yasa tayi kokarin ganin ta dan ware suka kara gaisawa tana tambayar sa yan gidan su sunje gida lafiya dan jiya suka zo musu gaisuwar Siyama amma bata sami yi musu ban gajiya ba, amsa mata yayi da lfy, sannan yake yi mata gaisuwar su Hafsat din da kuma Hajiya Yaya, ta amsa masa da godiya, wllh banji bane da wuri ai da dani za'ai jana'iza, sai dazu dazu na kira inspector Kabir kan wancan case din shine kuma yake sanar dani abin da yake faruwa, kai kawai ta iya jinjina masa, Allah ya jikan su Ku kuma ya baku hakuri da dangana, ameen ta amsa dashi, sai kuma yace amma naji ita Hajiya Yaya ba kamar su sauran ba ita ance kamar an buga mata abu ne akai, eh wllh haka akace, dan ni banma je wajen ba saida aka mata sutura aka ce muje muyi mata addu'a sannan na ganta dan haka ban ban gani ba.
Ranar Mutuwa Part (13)
Aisha Muhammad
amma Khairat idan baza ki damu ba ina so na miki wata tambaya, ina jinka, kai ya jinjina sannan yace kin san dama ina dan nawa binciken akan wannan case din ko, eh na sani, to bayan munyi waya da Kabir ya sanar dani abinda yake faruwa, nace masa ya bari yanzu zan zo to bayan naje yamin bayani akan komai naji ina so na miki wasu yan tambayoyi, OK ba damuwa Allah yasa na sani, Ameen, meya kawo Hafsat gidan ku da sassafe har hakan ta faru da ita tunda akai rasuwar nan dai dai kun ranaku ne bana zuwa amma ban taba ganin ta ba har na taba tambayar ki kika shaida min bata kwana tafiya gida take sai da safe idan su Kawu zasu taho suke zuwa tare koba haka bane, eh haka ne amma a ranar da akai uku ne da zasu tafi ta dage ita ba zata bisu ba sai ta kwana biyu dan ba yanda Mommyn ta bata yi ba akan tayi hakuri ta tafi idan yaso gobe ta dawo amma taki har saida Hajiya Yaya ta saka baki suka tafi suka barta, to daga nan kuma sai mai ya faru, ba komai shikenan muka gama abinda zamuyi mukaje muka kwanta, to ba tare kuka kwana ba, tare muka kwana dan ni har na so na makara ita ta tashe ni muka yi sallah sannan muka koma muka kwanta, bayan nan fa, bayan nan nayi bacci sosai bayan na tashi nayi wanka na sakko don yin breakfast har na fara shan tea nake tambayar su Mamy ina Hafsat ne dan ni a tunani na ta rigani tashi ne ta sauko amma ga mamaki na sai naji suna cewa wai su basuga ma saukowarta ba haka dai duk ta bashi labarin abinda ya faru, shiru yayi yana nazari tare da auna maganganun ta, can ya nisa sannan ya dago ya kalle ta to amma me ya kaita garden a wannan lokacin ance ma ko kayan bacci bata cire ba, eh wllh ban sani ba nima nayi mamaki amma sanin halin Hafsat na shegen bin kwakwkwafi yasa ma na daina mamaki, ana haka wayar ta ta dauki kara Mamy ce hakan yasa ta saurin duba agogo har 9 saura suna ta magana basuji ma lokacin da aka kira isha ba, hello Mamy gani nan, to kiyi maza dare yayi kuma kin san akwai gajiya a jikin mutane za'a so kwanciya da wuri, to Mamy ta fada tana yanke kiran, cab gaskiya lokaci na gudu tashi ki shiga gida kiyi sallah ki kwanta nima bari na wuce to ka gaida gida sai da safe, Allah ya kaimu, ya juya yayi wajen motar sa yayin da ita kuma tayi cikin gida.
Bayan anyi sadakar uku Kawu Saminu da Kawu bala kanin mahaifin su Alhaji da sauran shakikan yan uwa harda yan uwan Hajiya Maryam duk suka taru a falon Alhaji, aka kira Hajiya da yaran, bayan an bude taron da addu'a sannan anyiwa mamatan addu'a, suke sanar dasu shawarar da suka yanke akan Hajiya Maryam da yaran zasu koma gidan Kawu Saminu da zama har zuwa yanda hali yayi tunda dama tuntuni shi Alhajin kafin rasuwar sa yaso da iyalin sa su bar gidan zuwa wani lokaci, amma idan taga ita bata ra'ayin hakan zata iya zabar daya daga cikin gidajen Alhajin su koma, ko kuma idan gidan su take son komawa sai ta fadi ra'ayin ta, shiru tayi ta sunkuyar da kanta tana sharar hawaye, wani yayan ta ne yayi magana, a haba ai baza ai haka ba taya suna cikin wannan halin zasu kuma komawa gida su kadai, kuma ai da gidan shi Alhaji Saminu da gidan nasu ai duk daya ina da yakinin babu abinda zasu nema su rasa, sannan kuma sa dinga debewa juna kewa da ita Hajiyan(Mommyn Hafsat), Allah dai ya bar zumunci duk suka amsa da Ameen, Kawu Saminun shima yace to gaskiya na gode Allah ya bani ikon rike amana, suka ce Ameen, daganan akai addu'a aka tashi ita dai Mamy tana zaune tana ta sharar hawaye
Ranar Mutuwa Part (14)
Aisha Muhammad
tanajin babu dadi da alhinin rabuwa da gidan da take zaune tun auren ta bata taba barin gidan ba sai dai idan taje wani waje da ziyara, nan mutuwar ta sake dawo mata sabuwa, taso ace an barta ta koma gidan su duk tsiya akwai wasu yan uwan ta a gidan zatafi sakewa, to amma bazata watsawa Kawu Saminu kasa a ido ba domin tun Alhaji na da rai a tsaye yake akan abinda ya shafi gidan, dan haka kanwar ta da take bi tazo ta kama ta suka wuce domin shiryawa, dan ance baza su kara kwana a gidan ba.
Haka suka fito aka kukkulle ko ina na gidan, masu aiki da masu gadi duk aka sallame su tare da musu alkawarin idan komai ya dai daita za'a neme su Kawu Saminu shi ya cire kudi duk ya sallame su sallama mai kyau, dukkan nin su hawaye suke dan suna jin dadin aiki a gidan babu takurawa ba tsangwama ga alheri mutanan gidan mutane ne masu karamci da sanin darajar dan Adam.
Bayan sun isa dama tun safe an saka masu aiki sun gyara musu wani bangare dake can gefe daura da part din Kawun, dan Haka suna isa direct can aka raka su Kawu da kansa ya shiga ya nunnuna musu komai dan ita Mommy bata da ishashshiyar lafiya tunda akai rasuwar dan haka suna shiga tai musu sai da safe ta shige part dinta, bayan nuna musu shima yayi musu sallama sannan ya fita yana cewa za'a kawo musu abinci su daure su ci, bayan fitar sa suna zaune a falon sunyi shiru akai nocking suka bada izinin shigowa wata dattijuwa ce tayi sallama ta shigo duk suka amsa mata, ta karaso cikin falon dauke da katon tire ta karasa ta ajiye akan dining, sannan ta dawo ta rissina ta gaida Mamy ta amsa mata da dan sakewa yaran ma suka gaida ta, ta amsa tana mai jin dadin yanda suka girmama ta, Hajiya ga abinci akwai kuma abinda kuke bukata, aa babu mun gode nice da godiya Hajiya saida safe ta juya ta fice a falon, bayan fitar ta Mamy ta janyo wayar ta ta duba lokaci goma saura, ta juya ta kalli Khairat dake zaune suna chat da Aliyu tana sanar dashi dawowar su gidan Kawun, ki ajiye wayar nan ki tashi kije ki zuba muku abinci kuci muje mu kwanta dare yayi, to Mamy amma kefa, aa na koshi kawai muje kuci, haba Mamy muma fa muna ci ne badan yunwa ba sai dan kiyaye lafiyar mu amma Mamy kalli yanda kika rame bakya son cin abinci ga damuwa so kike kema wani ciwon ya kama ki ki tafi ki barmu, ina zamu saka kanmu, kiyi hakuri Khairat damuwa ta zama dole kalli fa irin halin da muka tsinci kan mu cikin kankanin lokaci, Alhaji ya tafi ya barmu ga Siyama, Hajiya Yaya, ga Hafsat, dama saida Alhaji ya fada, sai kuma ta fashe da kuka, tunda akai mutuwar bata samu tayi kuka sosai ba sai yau tana ta daure karta sare idan ta kasa jurewa to ina ga yaran fa, sai a yau da share makoki taga da gaske ne fa gashi har ta bar gidan da suke gidan tarin memory, ayau abin yafi karfin ta idan bata fitar da abinda ke ranta ba itama za'a iya wayar gari babu ita yaran ta kuma suyi yaya, Yasmin dake kwance a cinyar ta tuni ta mike ta rungume Mamyn Khairat ma tasowa tayi tazo ta rungumeta, itama kukan take sonyi amma idan tayi wane mai lallashin su, hakan yasa ta tattaro jarumta ta azawa kanta a hankali cikin hikimar da Allah yayi mata ta fara lallashin Mamyn kiyi hakuri Mamy Allah daya karbe su ya fimu son su, sannan su da suka tafi basuyi gaggawa ba muma ita muke jira, kiyi hakuri Mamy mu barwa Allah komai ya fimu sanin dalilin faruwar hakan, muyi musu addu'a Allah yasa mutuwa ta zama hutu a gare su.
Ranar Mutuwa Part (15)
Aisha Muhammad
sannan in tamu tazo Allah yasa mu cika da imani Ameen, da kyar ta samu suka fara lafawa da kukan tana ta musu nasiha haka dai har ta samu sukai shiru, sannan ta tashi taje dining din ta zubo musu abincin a plate daya ta hado musu ta sako cokula uku ta doro akan tray tare da ruwa da cups ta kawo dakyar ta samu suka sauko suka ci abincin a tare tana ta dan musu nasiha da jan hankali har ta samu suka dan ci da yawa, bayan sun gama ta kwashe kayan ta mayar sannan ta dawo suka zo suka wuce daki ranar Yasmin taki yarda su raba daki da Mamy haka Mamy tace Khairat bar ta kije ki kwanta, to Mamy saida safe amma dan Allah Mamy karki zauna tunani ki kwanta kiyi barci, insha Allah Khairat ai nima bacci nake ji kinsan an dauki bashin sa, hakane to sai da safe, ta juya ta fita ta wuce dakin ta.
Da Asuba Khairat na tashi sai da taje ta duba Mamy ta same ta tana zaune akan sallaya tana lazimi, jin bude kofar yasa ta dago ta kalli mai shigowar murmushi tayiwa Khairat din tana mata alama da hannu akwai wani abu ne aa ta fada tana girgiza kan ta ta juya ta fice, bayan ta koma dakin ta alwala tayi tazo tayi shafa'i da wutiri sannan ta dora da raka'atil fajr, tana idarwa taji za'a shiga masallaci itama ta mike ta tada salla, bayan ta idar da azkar din ta fita tayi taje kitchen ta duba abinda zasuyi breakfast amma sai bata ga kayan grain ba, hakan yasa ta fita ta wuce dakin Mamy, ta tarar itama ta gama azkar tana nade sallaya, ta shiga da sallama, ta amsa mata da sakewa, a hankali ta karaso kusa da Mamyn da ta zauna a gefen gado, zama tayi a gefen ta daga kasa, ina kwana Mamy, lafiya lau Khairat ya kike lafiya Mamy da fatan dai kin samu bacci, eh nayi bacci wllh Alhmdllh, masha Allah, wannan bata tashi ba ta fada tana kallon Yasmin, na tashe ta tayi sallah tana idarwa ta koma kin santa, murmushi tayi kawai, Mamy naje kitchen ban sami abinda zan dafa ba, ba komai kije ki kwanta nasan za'a kawo anjima kawai dai idan Kawun naku ya shigo koshi ko Hajiya saratu zance kawai a kawo mana grain din zamu dinga dafawa tunda dama can ku kuke girki, kada ku sangarce, to Mamy sai anjima kema ki kwanta ki huta, ta juya ta fice.
Bayan ta koma daki ta dauki wayar ta ta kunna, tana kunnawa sako na shigowa, budewa tayi Aliyu ne, dama tasan shi dinne domin dama al'adar sa ce tura mata sakon barka da safiya ko wacce safiyar duniya, hakan yana kara mata kaunar sa dan kuwa yana matukar nuna mata kulawa, tunda akai rasuwar nan yake tsaye wajen ganin bai barta ta shiga mummunar damuwa ba, murmushi tayi ta mayar masa da amsa, aiko kamar yana jira ya tura mata ta hau WhatsApp, data ta kunna suka shiga chat, anan yake fada mata zai zo anjima babu matsala, babu wata matsala ai da nan da gidan mu duk daya ne, to shike nan saina zo ki kwanta kiyi bacci ni zan fara shirin office, da wuri haka, eh wllh akwai wani case ne da muke kai, dan inaga zuwan nawa ma sai zuwa yamma koma dare, amma dai zami waya, okay Allah ya bada sa'a Ameen Ameen Ngd, da haka sukai sallama kowa ya kashe wayar sa, daga haka taja bargo ta lula duniyar barci.
Ba ita ta tashi ba sai around 10, shima juyi tayi taga rana ta hasko ta window, taja wayar ta ta duba time shine taga har 10, mika tayi tare da salati ta janye bargon jikin ta ta mike ta nufi toilet brush tayi sannan tayi wanka ta fito ta shirya tsaf cikin bakar Arabian gown tayi rolling da
Ranar Mutuwa Part (16)
Aisha Muhammad
mayafin kayan masha Allah gaskiya tayi kyau kasancewar ta fara tas a cikin bakin kaya sai ta fito kamar balarabiya simple makeup tayi dan powder kawai ta shafa sai kwalli da lipstick, takalmi ta dauka da jaka wanda zasu dace da shigar ta, domin yau tana da niyyar lekawa school ta samu ta danyi covering abinda aka wuce ta kafin lokacin exam da zasu fara karshen wata.
Sanda ta fito ta sami Mamy da Yasmin a falo sun gama karyawa suna zaune suna hira jefi jefi, da sallama ta shiga falon suka amsa mata ta karaso inda suke kujera ta samu ta zauna tana kara gaida Mamy, amsa tana fadin kinsha bacci, wllh kuwa Mamy har naso na makara ma, Yasmin ce tace yaya Khairat ina kwana, lafiya lau auta ya kike, ina lafiya, to masha Allah, kinga jeki ki hado min tea ki kawo min nan, to tace tana tashi tayi hanyar dining, Mamy ta kalle ta ina zaki ne naga kamar fita zaki, eh wllh Mamy ina so na leka school ne kinga karshen watan nan zamu fara exam gashi anyi abubuwa da yawa bana nan, gaskiya kam ya kamata Allah ya bada sa'a, ta amsa da Ameen dai dai lokacin Yasmin ta kawo mata tea din ta hado mata harda chips da kwai, karba tai tana tsokanar ta aa kaga auta an girma an san abinda ya dace to nagode, dariya duk sukayi, Mamy tace to ke da so kike tayi ta zama jiya i yau, aa maida wukar Mamy wasa nake ta fada tana dan murmushi kowa yana kokarin boye damuwar sa ga dan uwan sa, Mamy itama Yasmin ai ya kamata zuwa Monday ta koma makaranta ko, eh wllh nima haka nake tunani insha Allah zanyiwa Kawun ku magana sai a sama mata mai kaita tunda kinga yanzu wurin ya mata nisa, hakane Allah ya kaimu, bari na wuce ta fada tana daukar kayan data gama karyawa da nufin kaisu kitchen, Yasmin tayi saurin karba, kawo na kai, bata tayi tana fadin ngd, ta tsugunna ta dauki jakar ta da mukullin motar ta Mamy ni na wuce sai na dawo Allah ya tsare, amma ki fara shiga ki gaida Mommyn ku kafin ki wuce, to Mamy, ta juya tana fita Yasmin ta leko daga kitchen sai kin dawo, to Yasmin.
Da sallama ta shiga falon Mommy babu kowa a falon sai karar tivi da take ta aikin ta, daga kitchen taji motsi ta karasa kofar kitchen din ta leka tani ce mai girkin gidan a ciki tana ta aiki, jin motsi yasa ta dagowa, sannu da zuwa Hajiya, yauwa Tani Mommy bata tashi bane, aa ta tashi tana bangaren Alhaji, ok to idan ta shigo kice mata na zo na gaida ta na wuce school, to Hajiya Allah ya tsare, Ameen tace tana barin wajen.
Tana zuwa ta shiga mota tayi addu'a sannan tayiwa motar key mai gadi ya bude mata get taja ta bar gidan, bayan ta isa department dinsu ta nufa, tana zuwa tayi parking ta fito, ta tarar ana lecture dan haka itama tayi join din su, bayan an fito duk aka zagaye ta ana kara mata gaisuwa, ta amsawa kowa tare da musu godiya, daga haka ta nemi class captain dinsu ta samu handout da kuma wasu jotting na abinda aka wuce ta, daga nan ta wuce cafeteria domin yin photocopy, dan dama ita bata da wata shakikiyar kawa idan ba Hafsat ba duk sauran yan ajin kawai ana gaisawa ne amma bata da wata kawar yawo idan ba Hafsat ba shiyasa yau din take ta jin ta wani iri kewar Hafsat din na damun ta fiye da ko yaushe, dan haka bayan ta bada photocopy din ta wuce inda suke cin abinci ta samu waje kawai ta zauna tana tunani, can masu kawo abincin suka zo suka tambaye ta abinda za'a kawo mata, lemo kawai tayi order.
#hausa #arewa #drama #Labari
Ranar Mutuwa Part (17)
Aisha Muhammad
Aka kawo mata tana sha tana dan danna wayar ta kira ya shigo a wayar tata tayi saurin dagawa ta kara a kunnen ta, hello Mamy ya gida lfy Alhmdllh dama kira nayi nace ya karatun, Alhmdllh Mamy da nayi salllah ma zan taho lecture daya gare mu kuma har mun fito yanzu ma naje photocopy ne daga nan sai nayi sallah na taho, to shike nan sai kinzo Allah ya tsare, Ameen daga haka ta mike jin an fara kiran sallah, tayi wajen masu photocopy din ta fara gani ta tarar kuwa har sun gama ta karba sannan ta wuce masallaci tayi sallah daga nan kuma tayi gida.
Tana hanya Aliyu ya kira ta bata daga ba kasancewar bata fiya son amsa waya ba idan tana tuki, sai da ta isa gidan tukunna, bayan tayi parking kafin ta fito ta kira shi aiko tana shiga yana dagawa, dariya tayi kamar kana jira, eh jira nake mana tunda na kira baki daga ba nasan yan jan ajinne suka motsa ba dole ne nayi hakuri na jira ba ya fada yana dan lankwasa murya kalar abin tausayi, to kai daga dagawa ka hau korafi bazaka tsaya kaji ma abinda ya hana ni dagawar ba amma har ka yanke hukunci, eh mana ai an saba min hakan ne, dan haka ni gaskiya na gaji yau dinnan idan nazo zan sami Kawu nace ai mun gama dai daitawa kince ma nazo na same shi ayi ta ta kare nan da karshen watan nan, baki ta rike kamar yana ganin ta, na shiga uku yaushe mukai hakan harda kuma sharri ka koyo, to nidai babu ruwa na, da ruwan ki mana tunda ke kika ja, kaga ni dai sai anjima tunda kaki ka tsaya ka saurare ni kaji ma mai ya hana ni daga wayar, sorry na tsaya ina saurara, ina fa driving ne, ayya to sorry, ina kikaje, na shiga school ne kasan mun kusa fara exam, kuma anyi abubuwa da yawa bana nan, hakane kam kuma har kin dawo, eh wllh ko ciki ma ban shiga ba, ayya na tsaida ke da surutu, sai anjima ki shiga ki samu kici abinci ki huta, dan nima yanzu zan bar office, ana yin la'asar zan zo insha Allah, to Allah ya kawo ka, Ameen ya fada yana yanke wayar, daga haka itama ta jefa tata wayar a jaka tana fitowa ta kulle motar ta nufi part dinsu.
Da sallama ta shiga madaidaicin falon nasu, Mamy ta tarar tare da Mommyn Hafsat suna gaisawa da alama yanzu ta shigo, suka hada baki wajen amsa mata sallamar, da murmushi ta karaso cikin falon, kusa da Mommyn ta karasa ta zauna sannan ta dan rissina tana gaida su ina wunin ku Mommy ya gida, duka suka amsa, Mommy na tambayar ta makaranta ta amsa mata da lafiya, sai kiji babu dadi yanzu ke kadai, ta fada muryar ta na dan rawa, itama Khairat din haka ta amsa da alhini wllh kuwa Mommy, Mamy ta amsa da Allah ya musu rahama duk suka amsa da Ameen, daga haka falon ya dauki shiru, can Khairat ta kauda shirun da furta dazu na shiga ai ban same ki ba Tani take cemin wai ko kina part din Kawu, eh wllh ta fada min, nace idan na gama abinda nake zan shigo, kuma kinga ma sai yanzu na samu na shigo, eh wllh ai dama ba wani abu bane kawai na shiga ne na gaida ke, ai kuwa na gode Allah yayi albarka, ta amsa da Ameen tana mikewa bari na shiga na watsa ruwa, to sai kin fito, har ta juya ta fara tafiya sai kuma ta tsaya ta juyo Mamy ina Yasmin ne, tana dakin ta tunda dai ta shiga sallah bata fito ba, idan kin shiga kice mata ma tazo ta gaida Mommyn ku dama itama bata shiga ba LA ba komai da kin barta aa wllh a taso ta, ta amsa da to tayi ciki.
Ranar Mutuwa Part (18)
Aisha Muhammad
Bayan ta leka ta yiwa Yasmin din magana ta wuce dakin ta, toilet ta shiga ta watsa ruwa ta fito tazo ta sami wata gown mara nauyi ta saka sannan ta haye gado ta samu ta dan rintsa kafin a kira la'asar, a razane ta farka sakamakon mafarkin da tayi wanda ya zame mata jiki tun bayan rasuwar Hafsat indai zata kwanta bacci sai tayi mafarki da Hafsat din tana kuka tana kiran ta, kuma wajen da take ganin nata kamar ta san wajen a gaske, abun yana damun ta amma ta rasa dawa zata tauna, yanzu bata son duk wani abu da zai tadawa da Mamy hankali shiyasa ma batai tunanin tunkarar ta da maganar ba, amma ayau tana ganin tabbas ya kamata ta sanarwa wani domin a yau ta gane inda take ganin Hafsat din kamar a cikin garden din gidan su, to amma wa zata tun kara da maganar, zuciyar ta tace kawai kije ki sami Mamy wata zuciyar tace kai aa bazan tayarwa da mahaifiya ta hankali ba na barta da halin da take ciki ma to kodai Kawu zan fadawa ko wani Malamin ya samu ya dinga min rubutu kai ta girgiza kai aa ai shima sai na daga masa hankali yace kamar ko yarsa tana cikin wani mawuyacin hali, tana cikin wannan tuna nin wayar ta ta fara ringing tana dubawa Aliyu ke kira a zuciyar ta tace Aliyu shine kadai wanda ya rage da ya kamata na fadawa koda ace wani taimako za'a karbo min nasan zai karbo min, ana haka har wayar ta tsinke wani kiran ya kara shigowa, da sauri ta daga ta kara a kunnen ta tare da sallam, amsawa yayi yana tambayar ta ya yaji muryar ta wani iri, wllh bacci nake ban sani ba ashe har anyi sallah, ayya sai ki tashi kije kiyi ina waje ina jiran ki, har ka karaso, tun dazu ma na kira ki ai da bata shiga ba, ayya network ne bari nai sallah, daga haka ta mike ta shige toilet.
Bayan ta idar powder kawai ta dan gogawa fuskar ta sannan ta gyara hijabin jikin ta ta fito a falo ta tadda Mamy da Yasmin suna gyara carbin Mamyn da ya tsinke, sannu da hutawa Mamy, yauwa Khairat kin fito, eh Mamy Aliyu ne yazo yana waje, to sai kin dawo, tasa kai ta fita, bata ga motar sa ba kuma shima bata ganshi ba, tasa waya ta kira shi kana ina ne na fito ban ganka ba, ina waje, waje ina, bakin get mana, kai haba meye hakan kuma, aa kinsan masu gadin basu sanni ba ni kuma kin san bana son yawan tambayoyi, to ai shike nan ta fada tana yowa bakin get din, magana tayiwa mai gadin ya bude masa get din sannan ya shigo da motar sa, waje ya samu yayi parking, sannan ya bude ya fito, gaba tayi ya bita a baya har zuwa wata yar rumfa ta kaba wacce ke dauke da kujeru a ciki da zagayayyen katon table a tsakiya, kujera ta samu ta zauna shima tace masa bisimillah tana nuna masa waje, kujerar dake fuskantar ta ya zauna yana kare mata kallo, naga damuwa sosai a fuskar ki akwai abinda ya sake faruwa kuma, kai ta girgiza masa babu komai tana kokarin kawar da damuwar dake fuskar ta, sannu da zuwa ya gida yasu Ummi, Ummi tana lafiya tana gaida ke ma, ina amsawa ya aiki, Aiki Alhamdulillah, ke kuma ya makaranta lfy Alhmdllh, bari na kawo maka ruwa na manta, barshi kawai bana jin kishi zuwa nayi mu karasa maganar mu ta rannan, wacce ke nan, kina bani labarin abinda ya faru tsakanin ki da Hafsat har naji kamar kince wai ta fiya kwakwa, ohh na tina, eh a ranar bayan mun raka kawayen mu sun tafi muna dawo wa sai take cemin wai akwai wata kofa a cikin garden kamar ma gidan kasa, an kira ta ta zaga wajen tana amsa wayar sai take ta jin kuka, bayan ta gama wayar ta duba amma bata ga kowa ba a haka tana dubawa taga kofar, ta karasa wajen kofar taji kukan kamar daga cikin kofar ne, taso ta bude sai kuma taji tsoro ta fasa, shine take fada min.
Ranar Mutuwa Part (19)
Aisha Muhammad
Yayi shiru kawai yana kallon ta har ta gama sannan ya nisa amma ke kina nufin baki san da kofar ba, eh ban sani ba dan Abban mu yayiwa kowa na gidan gargadi akan kusantar wajen har masu mana aiki shiyasa gaskiya ni ban san da wata kofa ba, kuma fa ni nafi tuna nin tsoro ne irin na Hafsat sabida tun rasuwar su Abba take cewa tana tsoron gidan, shiyasa nayi mamaki sanda tace a barta ta kwana.
Kuma ance a garden din aka sami gawar ta, eh hakane, sanda take fada miki ke me kika ce mata, nace mata kawai gizo ne amma ta dage, da naga zata dame ni nace dan Allah ta barni bana jin dadi, kenan idan na fahimce ki tayi shiru amma ba wai ta yarda da ke bane, ta bari ne amma dai tana kan bakan ta, eh tabbas, to tabbas Hafsat ta ce a barta ta kwana ne dan ta sami damar komawa wajen domin ta tabbatar da abinda kunnen ta ya jiye mata kuma ta gani, tunda an tabbatar da anga shigar ta garden din, hakane, nima dama akwai abinda nake son fada maka, ina sauraron ki, tayi shiru tana tuna nin ta fada masa ne ko kuwa, katse mata tunanin yayi ta hanyar tafa hannun sa a saitin fuskar ta, dagowa tayi ta kalle shi, gira ya daga mata ina sauraron ki, dama wani mafarki nake tun bayan rasuwar Hafsat indai zan kwanta bacci ko da rana ne sai nayi, kwana nake ina mafarki, Hafsat nake gani tana kuka tana kiran suna na, kuma ada da nake mafarkin bana gane wajen da take, sai yau na gane a cikin garden din gidan mu ne kuma wajajen inda aka tsinci gawar ta, hakan nema ya bani tsoro na yanke gara na fada maka.
Shiru yayi na dan wani lokaci yana nazari, zuwa can ya dago ya kalle ta tace akwai kofa a wajen, eh haka dai tace, to a gaskiya akwai bukatar a sake bincika wajen domin ni ina tunanin akwai kanshin gaskiya a maganar ta, na gode da sanar da ni wadan nan abubuwa da kikayi domin zasuyi matukar taimakawa a binciken da muke kan yi, babu komai mune da godiya, yanzu inaga abinda za'ayi zan sami Kawu da maganar, kinga sai a samu muje tare da police a bincika ko za'a sami wata madafa, hakane Allah ya taimaka, Ameen, daga nan ya fara janta da hira ko ya samu ta ware, kika ce karshen wata zaku fara exam,eh insha Allah, Allah ya nuna mana, daga nan kuma sai me, babu komai, hararar ta yayi ban gane ba komai ba, ta fahimci inda ya dosa hakan yasa ta galla masa harara ban sani ba, dariya yayi ko kinki ko kinso sai kuma azo a saka mana rana tunda dai an gama karatun shine dai burin Abba, kuma Allah bazan taba yarda a saka min biki da nisa ba, kallon sa kawai take, to sannu da yake kai kake da ikon saka bikin ba iyaye ba, bani ke da iko ba amma ina da bakin fadar gaskiya, haba ai nayi hakuri shekara nawa kina karatun nan, dan haka gaskiya ni tun wuri zan fadawa Ummi kada a saka bikin nan sama da wata biyu, kai sai ka iya fadawa Ummin haka, to me zai hana sosai ma, to amma Allah ya kyauta maka, Ameen duk abinda zaki fada kiyi ta fada, daga haka suka cigaba da hirar su, ana haka har Kawu ya dawo, duk suka tashi suka karasa wajen motar sa, Aliyu ne ya bude masa ya fito, Khairat ta sa hannu ta karbi jakar hannun sa ta masa sannu da zuwa sannan ta wuce zuwa part din Mommy da jakar, shi kuma Kawun tsayawa yayi suna gaisawa da Aliyun yana tambayar sa wajen manyan, a nan ne ma Aliyun yake sanar da shi yana son ganin sa, sai ya saka masa lokaci yazo ya same shi, babu damuwa Ali inaga idan babu damuwa kuma maganar ba mai tsawo bace, idan mukai sallar magariba ai sai na ganka kawai, to godiya nake Kawu a fito lafiya, babu damuwa ya fada yana wucewa zuwa falon Mommyn.
Ranar Mutuwa Part (20)
Aisha Muhammad
Bayan shigar ta ta tarar da Mommyn tana shiryawa Kawu abinci a dining da alama taji shigowar sa kasancewar yawanci duk wani Abu nashi a bangaren Mommyn yake yin shi indai ba tana da wasu baki ba kwana ne kawai yake kaishi nashi part din, tana shiga ta ajiye masa jakar ta karasa tana taya Mommyn shirya abincin, bayan sun kammala suka nufo falon sannan ne Kawun yayi sallama tare da shigowa falon, suka amsa masa Khairat ta sake masa sannu da zuwa ya amsa yana zama a daya daga cikin kujerun falon, Mommy ma sannun take masa yayin da Khairat ta nufi hanyar fita tana yiwa Mommy saida safe.
Bayan fitar ta ta tarar da Aliyu yana tsaye daga gefe da alama fitowar ta yake jira, inda yake ta karasa sannu da tsayuwa, meyasa bazaka je ka zauna ba, kinga ai an kusa kiran sallah kawai ki shiga gida nima zan shiga masallaci nayi sallah, Kawu yace na jira shi, na masa wannan maganar ne, OK ba damuwa Allah ya taimaka, Ameen ki shiga kawai sai munyi waya daga nan zan wuce, idan kin shiga kice ina gaida Mamy, Ummi ma tace a gaishe ta tana ta kiran ta bata samu, ayya zan fada mata ka gaishe su, zasuji, daga haka ta juya ta nufi bangaren su shima wajen masu gadi ya nufa domin daura alwala.
Bayan an idar da sallah ya riga Kawu shigowa kasancewar ya tsaya yana gaisawa da mutane, bayan ya shigo a zaune ya sami Aliyun a wajen masu gadi, aa Ali kamar wani bako, shigo daga ciki mana, ya fada yana yin gaba Aliyun yabi bayan sa har zuwa kofar falon sa ciki ya shiga yanawa Aliyun iso, shiga yayi ya nemi waje daga kasa kan carpet ya zauna, tashi ka zauna a sama mana, aa Kawu nan ma yayi ya fada yana sunkuyar da kansa kasa, murmushi Kawun yayi, to ai shike nan ina sauraron ka me ke tafe da kai, kara gyara zaman sa yayi wato dama Kawu akan maganar bincike da ake ne akan case din rasuwar su shi Abban su Khairat da kuma yan uwan ta, musamman ma abin dai yafi shafar ita Hafsat, to mun sami wani dan bayani da ya shafi case din muke son a bamu dama tare da police din da suke binciken case din, muna so a bamu mukullin gidan akwai wani bincike da muke so zamu kara gudanarwa a gidan, shiru yaji Kawun yayi har ya dago ya dan dube shi yayi zurfi cikin tunani, can ya nisa, wato Aliyu ba na katse maka hanzari bane amma ni a nawa ganin kawai a bar wannan magana, wadan da suka mutu dai ba zasu dawo ba dan haka kawai muce Allah ya jikan su binciken da akai ma ya isa haka, da mamaki ya dago ya kalli Kawun, Kawu a barshi fa kace, duka ma yaushe aka fara binciken bare har a bari, kuma ma insha Allah zamu gano gaskiyar wannan al'amari, dan insha Allah mun fara gano bakin zaren, da sauri ya dube shi akwai wani wanda kuke zargi ne, kallon sa Aliyun yayi sannan yace ko daya meya kawo wannan maganar kuma, kawai dai muna iya bakin kokarin mu, to Allah ya taimaka, nima bawai cigaba da binciken ne bana so ba, ko daya kawai dai abubuwan da suka faru ne yasa ni bana ma son zancen gidan gaba daya, sannan ko su kansu iyalan sa cigaba da tada maganar kamar cigaba da yi musu fami ne na abinda ya faru, amma dai ka bari zanyi shawara, haka dai yayi ta kawo masa zantuttuka marasa tushe, da yaga dai Kawun bazai taba fahimtar sa ba sai ya barshi a haka ya masa sallama ya fito, ya dade.