Skip to main content

Rashin Sani - Hausa Novels


 

Chapter 1

 

Hayaniya ce ke tashi sosai daga cikin department din ISC biology, group group ne na daliban a ciki, kowa na harkar gaban sa, babu wanda ya damu da wani, kamar dai yanda kuka san yanda rayuwar jami'a take

Can gefe na hango wani matashi zaune shi kadai da siririn farin glass a idon sa, wanda yafi kama da na likitoci, sanye yake da bakin wandon jins da T-shirt milk color sai takalmin sa combos wanda ya dace da yanayin kalar kayan sa.

Yanayin sa kana kallo zaka san matashi ne ma'abocin gayu, amma ba irin fitinannun matasan zamani ba, kana ganin shi kasan ya fito daga gidan tarbiyya, amma yanayin shigar sa, kadai zai tabbatar maka da bai fito daga gidan masu da shi ba, ma'ana masu hannu da shuni.

Zubin sa yayi yanayi da fulani, dan fari ne ba irin can din nan ba, sannan yana da matsakaicin tsaho, bashi da alamar kiba, amma bazaka kira shi da ramamme ba, masha Allah a takaice dai irin samarin nan ne, masu tafiya da imanin yam mata a lokaci daya.

Umar faruq ke nan, wanda mafi akasarin mutane suke kiran sa da Faruq, takarda ce a gaban sa, yake nazarin ta, tunda ya duka bai dago ba, gaba daya hankalin sa naga wannan takarda.

Wani daga cikin samarin dake cikin wajen suna ta hira, naga ya taso, yayo wajen da Faruq ke zaune, leka takardar dake gaban sa yayi, yayi murmushi, sannan ya buga desk din da takardar take kai, har sai da iska tayi gefe da takardar, yayi sauri ya riko abar sa, haba Salim wai kai dan Allah yaushe zakai hankali.

Dariya Salim yayi, yace dan Allah dube shi, kamar wani yana sama dani, wai yaushe zanyi hankali, sai sanda kayi, sannan zanyi, yanzu dan Allah Faruq har kai zaka cewa wani bashi da hankali, bayan kai irin rashin hankalin da kake nema kayiwa kan ka, ka samu damar da kowa a cikin department din nan yake nema, sai kokarin yin watsi kake da ita.

Kaga dan Allah idan dai wannan maganar ce ta kawo ka, tashi ka tafi, ina da abin yi, waige waige ya fara, ina abinyin yake, sai kuma ya kamo takardar hannun sa, ya kalla, au wannan ko, ture shi Faruq yayi, kaga dan Allah Malam tashi ka bani waje, nayi abinda zai amfane ni, yanzu har akwai abinyin da zai amfane ka, sama da abinda nake ta kokarin nuna maka.

Yanzu kai Faruq, har kana tunanin abinda zaka samu a waka, yafi wanda zaka samu idan har ka amincewa wannan yarinyar, amma wllh Salim ban taba sanin baka da hankali ba sai yau, dama kai yanzu kana nufin nine zanyi auren jari, wllh Allah ya kiyaye.

Haba aboki na, taya ma zakai wannan tunanin, ko daya ba haka nake nufi ba, abinda nake so ka gane, sanin kan ka ne yanda aiki yake matukar wahala a kasar nan, kuma dai kasan kasuwanci idan dai ba iyayen ka yan kasuwa bane, sama ta ka ba'a fada masa, kuma ma idan kace zaka shigan dame zaka shiga.

Idan kuma kace wakar da kake ce kake so ta kai maka, kasan dai sai mai matukar sa'a ne, zai iya kaiwa wani abu a cikin wannan harkar, ba tare da ya samu wanda zaiyi sponsoring dinsa ba, kaga Malam dan Allah kaje inda kake son zuwa, ina da abinyi, dariya Salim yayi, yace ai ina kai ka, abinda nake so ka fahimta, idan har ka amincewa yarinyar nan, kaga na farko dai, babu yanda za'ai ka taba samun matsala a makarantar nan har ka kammala.

Na biyu kana gamawa, baka da matsalar aiki, kamar ma zaka gama ne da aikin ka a hannun ka, kuma aiki mai kyau, wanda zaka tallafi rayuwar ka da kuma yar Kakar mu, ko ba haka ba, ehe ina jin ka, sannan hakan zai baka damar daukan nauyin kan ka, ta bangaren muradin ka wato zama mawaki, ba tare da ka tsaya neman wani sponsor ba, kaine da kan ka zaka zama sponsor din kan ka.


Chapter 2


Yanzu Faruq wannan ba abinda duk wani mai kaunar ka zai hango maka bane, ka gama, ya tambaye shi, eh na gama, idan kuma abinda na fada bai maka ba, kayi hakuri, amma insha Allah bazan kuma hango maka abinda zai maka kyau, na sanar da kai ba, tunda kana min kallon kamar wani mai son zuciya, dan kawai ina son ci gaban ka.

Jikin sane yayi sanyi, akan irin abinda yake yiwa Salim din, wanda kuma ya tabbatar da duk abinda Salim din ya fada shine a ransa, ya sani a duniya bazai taba samun aboki kamar Salim din ba, wanda yake kaunar sa tsakanin sa da Allah, Salim yama fi karfin aboki a wajen sa, sai dai dan uwa.

Tare suka taso, sunyi primary tare da secondary, sannan suka nemi admission tare, kuma Allah yasa duka suka samu, kuma course din da suka nema shi aka basu, hakan yasa suka cigaba da kasancewa tare.

Kayi hakuri Salim, kaima kasan bazan taba kin daukar shawarar ka haka kawai ba, sai dai idan ina da kwakwkwaran dalili, menene dalilin naka Faruq, bana tunanin kana da wani dalili, sai dai kawai irin halin ka na kunbiya kunbiya, kamar wanda yake tsoron mata, wanda yake sakawa wasu da yawa suna maka kallon mai girman kai, sabida kaga Allah ya maka baiwar kyau, da kuma farin jini.

Dariya maganar Salim din ta karshe ta bashi, yace Allah ya raba ni da girman kai, kaima kasan ba hali na bane, to amma ai kai kake tilastawa mutane yarda da cewa hakan kake, to ai sai suyi ta fada, tunda Allah yasan ko kadan ba hakan bane a rai na ba, kuma amini na ma yasan ba haka nake ba, kaga duk masu fadan sai suje suyi tayi, sunga zasu iya ne.

To naji, yanzu ai sai ka fada min dalilin naka naji indai kana dashi, ba fada kawai kayi ba, niko nake da dalili, tashi muje waje sai na fada maka, wajen nan yayi hayaniya da yawa, wai har yaushe ma aka cika wajen nan haka, naga dai sanda muka zo ba haka wajen yake ba.

Ina zaka sani tunda hankalin ka baya jikin ka, kana can kana shirya labarin karya, yama fa kamata ka fara tsara mana wakar da zaka mana idan mun tashi graduation, lallai ma amma Salim baka da hankali, duka duka ma yaushe muka fara makarantar da har zaka fara zancen gamawa.

Au kai kake ganin haka, ai wuyar aiki ba'a fara ba, amma mu tunda mun riga mun fara kamar yaune zaka ga mun gama, to Allah ya nuna mana, ka sani ma ko kafin mu gama din na zama babban mawaki, da zan shirya mana wakar da sai ta zaga gaba daya kasar nan, Allah yasa aboki na, muna fatan haka, da wannan rahar suka fita kofar department din, yana cewa muje muyi sallah tukunna sai muyi magana, naji an fara kira.

Suna tafe suna hira, yaji yana taba shi kuma yana dariya, meye ne ya juyo yana tambayar shi, kaga mutuniyar ka nan tafe, wa ke nan, bai bashi amsa ba, shima ya hango ta, tana tafe cikin kawayen ta, ana ta hira, yana ganin ta ya dauke kai, dan baya son taga damar sa.

Amma ina hakar sa bata cimma ruwa ba, dan suna zuwa gab dasu ta ganshi, ai kuwa tana ganin shi, taja ta tsaya, tacewa sauran kawayen nata, suje zata same su, haka suka wuce suna tsokanar ta, Salim ta yiwa magana, ai kuwa kamar yana jira, yaja ya tsaya, kuma ya kama hannun Faruq ma, ya hana shi yin gaba.

Haka yana ji yana gani dole ya tsaya, sannun ku tace, Salim kadai ya amsa, ai kawai, sai ta fara kukan karya, Salim kaga abokin ka ko, wai me na masa ne haka da zafi, wanda gaba daya baya kaunar gani na, duk yanda yake cikin walwala, matsawar nazo waje to shifa tashin hankalin sa yazo.

Laifi ne dan naji ina son sa, dan Allah Salim ka bashi hakuri idan ma wani abun na masa, wllh ina son sa, kuma koda zai cigaba da wulakanta ni har zuwa mu bar makarantar nan, wllh bazan iya daina son sa ba, dan haka dan Allah ka rokar min shi, yayi hakuri ya soni, wllh idan akwai abinda nakeyi baya so ya fada min, nayi alkawarin zan bari, amma wllh bazan iya rayuwa da ko wane namiji ba idan ba shi ba.

Tana gama fadar haka ta juya da sauri tayi gaba, sosai Salim yake tausayin ta, yake kuma jin jina yarinta, da kuma rashin kunya irin ta yayan masu kudi, yanzu dan Allah ace yarinya kamar wannan zata iya tsayawa a gaban saurayi tana rokon sa akan ya so ta, ko da yake idan akai duba da inda ta taso hakan ba abin mamaki bane.

Dan ance a London aka haife ta, kuma a can ta girma dan tama kusa gama secondary acan sannan suka dawo, nan Nigeria, dan haka gaba daya dabi'un ta ba irin namu bane, dan ma mahaifiyar ta tana kokari sosai wajen ganin ta cire mata irin wannan dabi'ar ta banza, wanda idan ta mahaifin ta za'abi, yana ganin hakan ba komai bane, wayewa ce.

Bai ankara ba yaji Faruq yaja hannun sa, dalla Malam kazo mu tafi, na mamajo kawai, kai ko wace mace a cikin makarantar nan kulawa kake, amma wllh ka min sharri, kaga ni bama wannan ba, yanzu dan Allah Faruq yarinyar nan bata baka tausayi ba.


Chapter 3


Tausayi akan me zata bani tausayi, yarinyar da sanin kan ka ne gaba dayan mu tafi mu gata, to meye abin tausayi a tare da ita, kaima kasan me nake nufi, wllh kai dai Faruq mugun banza ne, alkhairi na bin ka kana sa kafa kana fatali dashi.

Wllh dani na samu wannan damar da yanzu ba wannan zancen ake ba, dan kuwa da tuni nayi amfani da dama, an dama dani, Allah ko, to ai yanzu ma baka makara ba, zaka iya kai tallan kan ka, kamar yanda itama takeyi, kaga hakan bazai zama bakon abu a wajen ta ba.

Allah ya kiyaye nayi takara da amini na, kuma ma da kake wannan maganar, wannan abin mafa da kaga yarinyar nan tanayi, kar ka dauke shi a wai rashin tarbiyya ne ko kuma rashin kamun kai, wllh ko daya, kawai yana da nasaba ne da irin rayuwar da ake a wajen da ta taso, kaga kuma wllh yanda yarinyar nan  take mutuwar son ka, duk abinda kace baka so, ta barshi ke nan, ai kama ji da kunne ka abinda tace.

Tsaki yayi baice komai ba, yayi gaba abinsa, Salim ma bayan sa yabi yana mitar irin halin abokin nasa, bayan sunyi sallah sun fito, daga can gefen masallacin suka samu kasan wata bishiya suka zauna.

Nan yace Salim idan dai kaga naki abu, to fa tabbas idan ka duba sosai zaka san ina da kwakwkwaran dalili, musamman akan maganar yarinyar nan, Salim sanin kan kane, a yanda wannan yarinyar tafi karfin tace tana son wani namiji ya bijirewa bukatar ta, koda kuwa yana daga cikin jinsin larabawa, dan duk inda ake neman mace yarinyar nan ta kai.

Dariya Salim yayi shegen kaya, to kai da duk kasan da haka, to meye dalilin ka na kin amince mata, hmmm kaima nayi mamakin yanda ka kasa fahimtar dalilin tun da wuri, ai yanzu sai ka sanar dani, tunda ni dai ban hango ba.

Salim zan iya cewa idan aka dauke kaka ta a duk duniyar nan kafi kowa sani na, babu abinda naki jini irin a wulakanta ni, shiyasa tunda na taso bana kai kaina inda Allah bai kaini ba, kuma na sabawa kaina da neman na kaina, musamman idan nayi duba da irin rayuwar dana taso a ciki, rayuwar kunci da talauci, da rashin matallafi.

Kana sane da cewa, ban taso naga mahaifi na ba, hasali ma ko hoton sa ban sani ba, mahaifiya ta ma bani da wayo ta tafi Saudiya neman kudi ta bar ni a wajen Kaka, tunda na taso nasan Kaka ta da sana'ar sai da kuli kuli, wanda ba wani abun kirki take samu a ciki ba, shike nan fa abinda muke dashi, sai dan abinda Mahaifiya ta ta turo mana, lokaci zuwa lokaci, kuma shima ba wani mai yawa ba.

Hakan yasa ina fara girma na fara zuwa koyar aikin Kafinta wanda yake rufa mana asiri sosai, wanda badan wannan aikin ba, da watakila ko secondary bazan gama ba, sabida biyan kudin WAEC, kai fa duk ka riga da ka san wannan dama sauran mafi yawancin abinda yake tafiya a cikin rayuwa ta.

Dan haka baka ma bukatar sai na bata lokaci na wajen maka bayanin komai, yanzu da wannan matsayin nawa kake so na jefa kaina a inda karshe zan kare a wahala da ganin wulakanci, Salim ina mai tabbatar maka da, ko ita yarinyar nan ba so na take ba, kawai yarinta ke dawainiya da ita.

Amma ina mai tabbatar maka da nan da mu kammala karatun mu, zuwa lokacin ta kara hankali, sannan ta hadu da samari iri iri wadan da suke dai dai da ita, musamman tana da kyau dan haka babu irin samarin da bazatayi ba, wllh Salim idan na maka rantsuwa bana tunanin zanyi kaffara, sai yarinyar nan ta guje ni, ta watsa min kasa a ido.

Bayan lokacin ta gama koya min son ta, ta lasa min zuma a baka, sai daga karshe ta barni da ciwon da warkewar shi, abu ne mai wahala, kuma ka ma ture ta ita yarinyar ace ma duk bazata aikata wannan ba, yanzu kana tunanin mahaifin ta zai amince yar sa ta auri talaka kama ta, kwarai ma kuwa idan dai mai mutunci ne, idan kuma bashi da mutuncin fa, kai haba Faruq mai yasa ne baka taba hasashen alkhairi ne, ka fa dinga yiwa mutane kyakykyawan zato, gaskiya nake fada kai kuma baka son ta.



Chapter 4


Babu wani batun gaskiya, ni dai rokon da zan maka na karshe akan yarinyar nan, shine ka taimaka ka bata dama guda daya tal, idan har akwai wata matsala a tarayyar ku, nasan zaka iya fahimta tun da wuri, kaga sai kayi dabara ka janye mata, kuma itama tasan ka mata adalci, sannan maganar iyayen ta, tun a farkon kayi dabara ka bugi cikin ta akan su, sannan kuma kasan duk yanda zakai ka samu ma kaje gidan nasu, sai kaga karbar da zasu maka.

Wannan shine mafita, amma ba ka zauna wahalar da yar mutane ba, wllh hakkin yarinyar ma sai ya kama ka, tunda duk hujjojin nan naka daka kawo min, kana hasashen faruwar su ne, ba wai sun farun bane, kaga kamata yayi ka gwada ka gani, idan sun farun, kaga tun wuri sai ka dauki duk matakin da kaga yafi dacewa da kai.

Hakane Salim, amma wllh zanyi wannan abun ne kawai sabida kai, amma wllh in dan ta ni, bani da niyyar saka kaina a wannan rigimar, to nagode kuma insha Allah sai kayi alfahari da shawara ta, Allah yasa daga nan suka tashi suka wuce lecture.

To fa tun daga sannan ya dan fara kula ta, Salim na kara encouraging din sa, har suka zo suka kulle, soyayya mai tsanani ta shiga tsakanin su, har suka fara zama abin kwatance a cikin department din su, soyayya suke gudanarwa mai tsafta, dan Faruq mutum ne mai matukar kula da hakkin addinin sa akan dukkan abinda zai aiwatar.

Hakan nema yasa suke yawan samun matsala, sabida yanda yake yawan yi mata karan tsaye ya hana ta aiwatar da wasu dabi'un nata wadan da ita a wajen ta ba komai bane, amma ko kadan bai dace da tsarin addinin mu da al'adar mu ba.

Amma ko kadan halayyar ta bata dame shiba, dan sosai yake samun nasarar raba ta, da dayawa daga cikin dabi'un ta marasa kyau, albarkacin irin son da take masa, shiyasa bata iya masa musu akan komai, ta bangaren iyayen ta kuwa yasha bugar cikin ta, amma kullum tana nuna masa, Daddyn ta bashi da matsala, duk abinda take so, shima shi yake so, dan haka babu yanda za'ai ya hana ta auren wanda take so.

A irin maganganun tama sai ya fuskanci, mahaifiyar ta ce, kullum suke cikin samun ban bancin ra'ayi, amma daga ranar daya ziyarci gidan su, sai gaba daya hankalin sa, ya gama kwanciya da ita, yana ganin ya gama samun matar aure, dan gaba daya babu ta inda ya hango matsalar da zata iya raba shi da ita, sabida irin karbar daya samu daga mahaifiyar ta, sai yaga kamar babu wanda ya kaishi dacen sirikai, duk da bai ta ba haduwa da mahaifin ta ba, amma baya tunanin shima za'a samu wata matsala daga gare shi.

 

Chapter 5



A gajiye ya shiga gida, dan yau tun karfe bakwai ya bar gida, yana da lecture karfe takwas, kuma bayan ya gama lecture ya wuce wajen aiki, akwai aikin wasu kaya da suke kokarin hadawa, yau za'a dauka, na wasu amare ne su biyu, yayan mutum daya, basu suka kammala kayan ba, sai ana kiran sallar magariba.

Bayan yayi sallar magariba ya shigo gida, da sallama dauke a bakin sa, amma muryar shi can kasa, sabida gajiya, ga kuma yunwa, dan yau da naira dari biyar kadai ya tashi, kuma da ita yake son yayi kudin mota zuwa makaranta, a hakan ma sai yayi trecking kafin ya hau mota, sabida ya samu kudin ya dawo dashi.

Shiyasa ma ya fita da wuri dan gudun makara, gashi tun safe koko ne kadai a cikin sa, wanda Kaka ta dama musu da yar guntuwar ragowar gasarar da ta rage musu suka sha, kuma haka ya fita bai bar mata komai ba, dan sosai a kwana kin nan suke fama da rashin kudi, wanda dama kamar hakan ya zame musu jiki.

Amma na kwanan nan din ya hadu ne da, wata daya kusa karewa, komai ya kare gashi ba'a biya su, dan abinda ake biyan su a wajen aikin su, ga kuma kwana biyu Kaka bata da wadatacciyar lafiya, bata samun yin dan kuli kulin da takeyi, ana shigowa ana siya, shima dashi suna samu suna dan ragewa.

Shiru yaji gidan, baiji muryar Kaka tana amsa masa ba, kamar yanda ta saba, dakin ta ya leka, wanda yaga babu alamar haske, haske ya hango a dan daki, hakan ya tabbatar masa tana ciki, fitilar wayar sa ya kunna, ya shiga cikin dakin nata, gaba daya jikin sa babu kuzari, sabida yunwa, da kuma damuwar yanda yau ya bar Kakar tasa bai bar mata komai ba, sannan kuma yanzun ma dai haka ya dawo ko kudin da zai yi kudin mashin zuwa makaranta babu.

Waje ya samu ya zauna daga gefen yar katifar Kaka, idon sa ya sauka akan wasu jerin hadaddun flask kala kala daga gefe a ajiye, mamaki ne ya kama shi, na inda Kaka ta samu wadan nan kwanuka.

Yana nan zaune yaji shigowar Kaka tana fadin, sannu Umaruru, sai yanzu, wllh sai yanzu Kaka aiki ne yayi mana yawa yau, to Allah ya dafa, lafiya kuwa kake, tana zama a kusa dashi, lafiya me kika gani, naga duk kayi wani laushi, wllh kawai gajiya ce Kaka, to sannu, ai kana yin sallar isha'i sai ka kwanta.

Amma dai gobe ba da wannan sassafen zaka fita ba ko, aa Kaka ai ina ganin ma goben nan bazan shiga makaranta ba, meyasa ta tambaye shi, wllh Kaka garin ne sai a hankali, wllh yanda na fita haka na dawo, ko kudin mashin bani dashi, ni abinda ma ya dame ni, yanda na fita na bar ki a gidan nan babu komai.

Aa kwantar da hankalin ka, kalli can, ta fada tana masa nuni da wadan nan kwanu kan, wannan kuma daga ina Kaka, ya tambaye ta, wllh wannan yarinyar yar albarka wacce ban iya fadan sunan ta ba, wai ka fada mata bani da lafiya, shine fa tazo duba ni, tayo min tuwo ta kawo min, harda su kayan marmari, kala kala, ni wasu ma ban san sunan suba.

Kuma wllh dan nan, wai ashe yarinyar na da zata tafi harda kudi ta ajiye min, sai bayan ta tafi na gani, dariya yayi ke dai Kaka ki fadi gaskiya, kodai kin gani kika dauke ido a zuwan baki gani ba, rantse rantse ta fara masa, sai da ta fahimci abin nasa shakiyanci ne, ta masa banza.

Da yaga ta daina kula shi, sai cewa yayi Kaka meye ma sunan nata, ban sani ba dan kaniyar ka, wai Umaru ina wasa da kai ne, aa ni na isa, wai dama so nake naji idan baki iya ba, na koya miki, kada ki fada a wani wajen a miki dariya, an dade ba'ayi ba, dan kaniyar ka yaushe ma aka haife ka, Sahaman ne ban iya ba, me Faruq zaiyi idan ba dariya ba, dariya ya dingayi har da hawaye, sai da yaga ran Kaka ya baci sannan ya bari, ya shiga lallashin ta.

 

Chapter 6


Suhaima fa ake cewa Kaka, ai wllh idan bani din ba ma babu mai gane inda kika dosa, eh naji din ta fada a harzuke, aa yi hakuri ba abin fada bane, da kyar ya samu ya shawo kan ta, har ta saki ranta.

Kwanukan ta janyo, bari kaima na zuba maka abincin kaci, dan nasan wannan sanyin da jikin ka yayi ba iya gajiya bace harda yunwa, aa Kaka kawai ke kici ni a koshe nake, kaniyar ka, ni zaka yiwa fulako, to wllh idan baka ci ba zaka yi nadama, dan wllh wannan tuwo badai dadi ba, wllh ko ni da nake tsohon hannu ba zanyi irin saba.

Dariya ta bashi sosai, dama idan banda abin Kaka ina za'a hada girkin masu kudi dana talaka, suda suke girkin komai yaji, sabanin talaka da kayan miya ma wani lokacin ba isa suke ba, balle kuma azo maganar kifi ko nama, su kuwa sai su hada kifin ma da nama duka a girki.

Tana niyyar zuba masa ya dakatar da ita, kinga Kaka bari tukunna nayi sallah, kinji an fara kira, ya fada yana mikewa, tace to bari nima na tashi nayi, yasa kai ya fita, itama Kaka ta dauki sallaya, ta tada sallah.

Bayan ya fito daga masallaci, bai karaso gidan ba, sai da ya kira Suhaima, bayan sun gaisa, yake mata godiyar zuwa duba Kaka da tayi, yace kuma harda dawainiya, anfa gode, haba dan Allah ni wllh har ka bani kunya, ko kuma nace ka bata min rai, kana nufin ke nan ni ba Kaka ta bace ko.

Aa ni na isa nace haka, Allah ya baki hakuri, kawai dai gani nayi kamar dawainiyar da kike yiwa Kaka tayi yawa, to ina ruwan ka, ai nima jikar tace, dan haka babu ruwan ka, ka daina shiga tsakani na da Kaka ta, to ai shike nan, Allah ya bar ku tare, tace amin.

Yanzu yaya jikin nata, da sauki, tunda har taci tuwo tana ta santi, harda cewa wai ko ita da take tsohon hannu, kin fita iya girki, sosai maganar ta bawa Suhaima dariya, tace kai Kaka akwai abin dariya, hmm ai haka take, akwai kuma abin haushi ba, aa wllh ai ni zan so ace a gidan mu take, da wllh bani da wajen hira sai wajen ta.

Hmm baki san ta bane, da zaku zauna tare na kwana daya sai kince ta ishe ki, kaine dai watakila mai damun, kake dorawa baiwar Allah, kuma sai na fada mata, rufa min asiri, kisa ta kulle min gida na kwana a waje kenan, ai da ya fi, au haka kika ce ma, to sai anjima, aa yi hakuri, wasa nake, ni ina zanso ka kwana a waje, wasa nake maka.

To ai shike nan, yanzu dai kinga sai anjima, zanje naci abinci ban dade da dawowa ba, yanzu ma daga sallah nake, to sai anjima, kayi sauri ka shiga gida, kasan bana son kana barin cikin ka da yunwa, to bye bye, kada kiyi bacci zan kira ki, to bye.

Bayan ya koma yaci abinci, Kaka ta kawo kudin da Suhaima ta bata, ta bashi, karba yayi ya duba yaga dubu biyar, dubu daya kawai ya dauka, ya mikawa Kaka sauran, to gashi nagode, aa ka rike mana, ai naki ne Kaka, wannan ma na dauka ne, dan nasan bani da ko kudin fita makaranta gobe, amma da bazan dauka ba.

Jayyayya suka fara, sai daga baya dabara ta fado masa, yace kinga Kaka ki ajiye mana kudin nan a wajen ki, idan zan fita bani da kudi zan tambaye ki sai ki bani, kema kuma randa muka tashi babu komai, kinga sai kiyi amfani dashi, ki ci wani abun, kafin a biya mu.

To shike nan, Allah dai ya sakawa da wannan yarinya da alkhairi, yace amin, daga haka ya mata sallama, ya shiga dakin sa, dan a gajiye yake sosai, yana kwanciya kuwa yayi bacci, ya manta da kiran Suhaima, da yayi alkawari, bai ma tashi tunawa ba, sai da gari ya waye, ya dauko wayar sa, ya tarar da tarin missed call din ta, yasan yau zai sha mita.

 

Chapter 7



Bayan shekara uku, abubuwa da yawa sun faru, ciki kuwa harda yanda baiwar da Allah yayiwa Faruq ta fara bayyana, bayan haduwar sa da wani mawaki a social media, har ya zame masa uban gida, yana dan yi masa hanya, ya rubuta Waka, ko kuma wani dan speech, ana biyan sa, yana kara samun dan abinda zasu rufawa kansu asiri, kuma ma ko baya samun komai, at least yana ganin ya dauko hanyar cikar burin sa, dan wata rana zai rubuta kuma ya rera kamar yanda a kullum yake fata.

Tafe suke Suhaima, dukan su daka kalle su kasan ba karamar gajiya suka kwaso ba, musamman ita Suhaima da ba wai ta saba da wahala bane, shi kuwa a bangaren Faruq, jigatar da yayi ta hadu ne da azumi da yake na litinin da alhamis, wanda ya zame masa jiki, ko rashin lafiya yake indai ba ta kwantar dashi ba, baya fasa yi, kamar dai yau daya kama Monday, ya tashi da azumin sa, duk da yanda abubuwa suka musu yawa a makarantar, kasancewar sun taho gamawa, yanzu haka suna gab da fara jarabawa.

Suhaima ce ta kalle shi, Habibi wai ina kake Shirin kaini ne, siyar dake zanyi, ya fada da sigar wasa, itama dariya tayi, tace koda ka siyar dani, da kan ka zaka koma ka fanso ni, sabida me, sabida idan aka cire Daddy na to fa zan iya cewa kafi kowa so na, idan kuwa a bangaren kulawa da nine da bani farinciki, to zan iya cewa hatta da Daddyn ma ka fishi.

Kallon ta yayi, harda Mommy ma, kwarai ma kuwa har ita, to kai idan banda abinka, baka ji da nace idan aka dauke Daddy kaine mutum na biyu a cikin wadan da suka fi kowa so na ba, ita fa Mommy bana tunanin ko a cikin ta uku zata iya zuwa, gaskiya sai dai ta hudu, dan wllh ko Kawata Mufidah, zan iya rantse maka tafi Mommy so na.

Baki kawai ya saki yana kallon sakarci irin na Suhaima, yanzu ace harda su kaza a cin danko, idan ma ana maganar iyaye ai ko shi bai kamata ya shigo ciki ba, balle kuma wata kawa, idan banda abin Suhaima da dai ita kullum bata girma balle tayi hankali, kullum idan tana acting kamar yar shekara goma, idan ba haka ba, ai ko uba baza'a hada soyayyar sa data mahaifiya ba.

Kai kawai ya girgiza, dan baya da bukatar ya tambaye ta dalilin, dan ba tun yau ba, take fadin ire iren wadan nan kalaman, wai dan kawai Mommy tana yawan mata fada akan wasu halayen da take yi, ita kuma take ganin basu dace ba, shiyasa take ganin kamar Mommyn bata son ta, bata san wannan shine son ba, ko kadan irin gatan da Daddyn nata yake nuna mata ba so bane, illa ne kawai, yana lalata rayuwar diyar tasa ne, tunda ko babu komai mace ce ita, wata rana karkashin wani zata koma.

Bai ankara ba yana tunani sai gani yayi taja ta tsaya tana diddira kafafu, wai ita wllh ta gaji, idan bazai fada mata inda zasuje ba, to ya barta ta tafi gida, tsayawa kawai yayi yana kallon ta, ba yau ya fara ganin irin wannan shagwabar tata ba, sai dai a duk lokacin da tayi irin wadan nan abubuwan sai mamaki ya kusa kashe shi, yana alawadai da tarbiyya irin wannan da mahaifin ta ya bata.

Gaba daya ya gama sangarta ta, a kullum ganin kanta take a yarinya wacce zata iya yin ko wace irin tabara, kuma har gobe idan tayi irin wannan a gaban mahaifin nata, gani yake kuruciya ce, shi ko kadan baiga illa a hakan ba, shiyasa suke yawan samun sabani da Mommy akan ta, kuma idon ta na gani, shiyasa take ganin ita Mommy ba kaunar ta take ba.

 

Chapter 8

 

Da yaga abin na neman yayi yawa ne, ya daka mata tsawa, wacce tasa a take ta shiga taitayin ta, tana kallon sa kamar idon ta zai zazzage, sabida tsabar yanda tayi narai narai dasu, kiris take jira ta saki kuku.

Ganin yanda tayin sai kuma yaji baiji dadin tsawar da yayi mata ba, ya shiga bata hakuri, ai kamar yace ta saki kukan, ta fara rera shi, kamar karamar yarinya, ikon Allah yace, yana kallon ta, ita kuwa kara kaimin kukan ta take.

Da dai yaga abin bana kare bane, sai ya shiga lallashin ta, ya samu yaja ta, gefe suka zauna kan wasu kujeru, ya dinga aikin lallashin ta, har ya samu ta daina kukan, sai faman ajiyar zuciya take saukewa, sai kuma tace to ka fada min inda zaka kaini.

Shi dariya ma yanda tayi maganar ya ba shi, amma ya danne kada ya kuma janyowa kansa wani darun, yace bafa wani wajen zan kai ki ba, abinci zan kai ki kici a cafeteria, naga duk kinyi laushi, kuma dama kince baki yi breakfast ba yau kika fito, shine zaki fara min darun naki, kamar wacce zan sace da gaske, kina neman ki tara min jama'a.

Fuskar ta ta rufe da tafin hannun ta, to kayi hakuri, ai ban sani bane, kuma kaga na gaji ne, kuma ina so na koma gida da wuri, kaga yau kana azumi, zanje na maka abin buda baki, kallon cikin idanun ta yayi, yace kallan ni nan, dara daran fararen idanun ta, ta dago ta zuba masa, a cikin nashi, wanda yasa shi saurin janye nashi.

Allah ya yiwa Suhaima baiwar kyau gata da wasu irin idanu manya, masu yalwar gashi, ga cikin idon nata da wani irin haske, suna wani maiko maiko, kamar wanda hawaye ya taru a ciki, shiyasa duk wanda ta zubawa su, sai ya ji su har kwakwalwar sa, shiyasa, ba kasafai ake iya yin ido cikin ido da ita ba.

Kamar yanda ta faru da Faruq, sai da yaji kallon da ta masa har cikin kwanyar shi, sai da ya janye idanun sa, sannan yace, Habibty dan Allah yau ki hutar da kan ki wannan aikin, wllh na yafe miki wannan wahalar, Kaka zata min girki, yau daya ki huta.

Bata rai tayi, au kula da kai din shine wahala, to wllh bana fatan ranar da zan kasa yi maka hidima a matsayin wani nauyi a gare ni, dan haka daga yau ma kar ka kara Kiran wannan abun da nake da wahala.

Sai kuma ta saki ranta, tace koya fa nake dan kada sai anyi auren na gagara kula da kai kace zaka min kishiya, kuma fa har Mommy ma akan wannan abun da nake ba kaga yanda take goyon baya na ba, dariya yayi, au ashe dai ana kishi na, har wani tsoron kishiya kike, tun ma kafin ayi auren, baki ta turo gaba, yasa hannu ya dalle mata bakin, ta saka yar kara, yace gobe ma ki kuma, kinsan ai na hana ki turo min baki.

To na daina, ka tashi mu tafi gida, ta fada dan ita kam ta gaji bata son wani kara jan magana, mikewa yayi Shima suka jera suna tafe suna hira gwanin sha'awa, har suka isa bakin motar ta, ta bude ta shiga shima ya shiga tayiwa motar key suka bar cikin makarantar, suna tafe suna hirar Salim wanda yau bai samu shigowa makarantar ba, sabida tafiya garin Kaduna da yayi, an musu rasuwa sunje gaisuwa tare da yan gidan su.

A dai dai wajen aikin su ta ajiye shi, bayan sunyi sallama akan sai tazo gida anjima, yace to Allah yasa ta same shi, tace amin taja motar tayi gida, yana shiga wajen, sauran abokan aikin sa, suka shiga tsokanar sa, wai Romeo da Juliet, shi dai ya musu banza, ya kama aikin wani tv stand da ya fara jiya bai kammala ba.

 

Chapter 9



A bangaren Suhaima kuwa tana zuwa gida ta watsa ruwa taci abinci ta shiga kitchen, ba ita ta fito ba sai bayan biyar ta wuce, tana fitowa, ta wuce dakin ta ta shirya, ta dauki basket din da masu aikin suka hada mata, ta leka tayiwa Mommy sallama ta fita.

Mommy ta bita da kallo, tana addu'ar Allah ya nuna mata randa diyar tata zata sauya wadan nan halayen nata, ba laifi bane idan ta yiwa Faruq din girki, amma kai masan ne har gida ko kadan baiyi ba, a matsayin ki na mace ace kullum kina yawo zuwa gidan saurayi, wanna ai sam bai dace da al'adar Malam bahaushe ba, amma ya ta iya, tana yin magana zatace ta fiya takura mata, bata kaunar farin cikin ta.

Haka ta bita da addu'ar Allah ya dawo da ita lafiya, ko babu komai soyayyar su da Faruq ba karamin sauya ta yayi ba, dan a yanzu babu rabi daga cikin halayyar ta, gaba daya ta zubar, kuma tasan aikin Faruq din ne, dan wani lokacin ma tana fada, idan zatai wani abun, sai kuma tace au Habibi ya hana ni.

Mommy ta kanyi dariya tace lallai wannan Habibi Allah ya saka masa daya iya canza min wannan mai taurin kan, kuma ko a bangaren girki da takeyi, tun kafin ta kai haka, babu yanda Mommy batayi da ita ba, akan idan ana girki ta dan dinga shiga tana koya ba wai dole sai tayi ba, aa kawai dai ta dan dinga saka ido, tunda dole dai wata rana aure zata yi.

Amma fur taki, tace Allah ya kiyaye tayi girki, ai wllh ko auren tayi, idan shi mijin bazai dauko mata mai girki ba, tasan Daddyn ta zai dauko mata, karshe da maganar taje wajen Daddyn cewa yayi kwarai tayi gaskiya, idan mijin bazai dauko mata ba, shi zai dauko, da dai Mommy taga bazasu taba ganewa ba sai ta rabu dasu.

Amma yanzu gashi rana tsaka Faruq ya canza ta, tun wata rana da ta kai masa abinci, yace yayi dadi, tace masa ai ba ita fa take yi ba, shine yace mata to daga yau indai ba ita ta girka abu ba, kada ta kara kawo masa bazai ci ba, shine fa, ta dage koyar girki, gashi zuwa yanzu abinda bata iya ba kalilan ne.

Sanda ta isa gidan ana gab da kidar sallah, da sallama ta shiga, Kaka dake zaune akan kijera yar tsugunno tana daura alwala ta amsa mata sallamar, tana fadin wa nake ji, kamar yar albarka, dariya tayi, tace nice Kaka, lale maraba, Bismillah.

Karasa shigowa tayi, ta nemi gefen tabarmar data gani a shimfide, da alama anan Kaka ta tashi, dan ga redion ta nan a wajen, da carbi, da sallaya, da alama ta dauko ne domin tayi salla a wajen.

Kayan dake hannun ta ta ajiye, itama tazo ta dauki buta tayi alwalar, tazo ta tada sallah, a lokacin ita Kaka ta riga ta tayar, itama ta shimfida mata sallaya a gefen ta, tazo ta tada sallar, bayan sun idar, ta gaida Kaka, ta amsa tana tambayar ta wajen Maman ta, tace tana nan kalau tana gaishe ta, ina amsawa.

Basket din ta janyo tana bubbude warmer's din dake ciki, kai wannan yarinya Allah dai ya miki albarka, dan ko an so a hana ki ba hanuwa zakiyi ba, sai dai kawai muce Allah ya miki albarka, Ameen Kaka, ni bari nazo na koma, dare nayi, to mun gode, ki gaida iyayen naki, zasuji Kaka, ta fita tana jiyo Kaka nata saka mata albarka.

A kofar gida sukayi kicibus da Faruq yana niyyar shiga gidan, sun kusa yin gware ma, yayi saurin yin baya, ita kuma ta dafe kirji, tace wayyo Allah, wllh ka bani tsoro, matsoraciya kawai, to Allah ya baki hakuri, gyara tsayuwar sa yayi, ta kalle shi, tace ya dai, murmushi yayi, yace hira zamuyi mana.



Chapter 10



Aa na yafe, kaje kayi buda baki, ai ni indai baza kazo gidan mu hira ba, to sai dai kada muyi hirar, dan a makaranta ma na kusa daina kula ka, sai kazo gidan mu, ni kuwa dan Allah Habibi mai yasa baka son zuwa gidan mu, wai ciki na wllh yunwa nake ji, kije gida kawai dare nayi nima zan shiga naci abinci.

Hmmm zaka ce haka mana tunda na maka maganar da baka so, amma na maka uzuri, tunda azumi kayi, kaje kaci abinci, sai da safe, to na gode sai munyi waya, muje na raka ki bakin mota, aa na yafe kaje kawai, yasan ranta ne ya baci, shiyasa ya mata banza, har saida ya raka ta bakin motar, ya bude mata ta shiga, yaga taja ta tafi, sannan ya juya ya shiga gida.

Bayan kwana uku ana sauran sati daya su fara jarabawar su ta karshe, ranar lecture karfe takwas ce dasu, a makare Suhaima tazo, har an fara lecture, Allah yasa Malamin ba mai hana shiga bane idan ya shiga, a hanzarce ta shigo cikin hall din, akan idon Faruq ta shigo, dan dama tunda yazo yaga bata zo ba, idon sa yake kan kofa, yana dakon zuwan ta.

Fuskar ta a sake ta shigo, da fara'a, duk da dama kusan kullum haka take, amma nayau din yafi na kullum, hakan yasa ya kagu a gama lecture su fita, yaji abinda yasa masoyiyar tasa farin ciki haka, dan yasan ba sai ya tambaye ta ba, shine mutum na farko da take fara sanarwa da farinciki ta ko kuma damuwar ta.

Ilai kuwa yana fita, ya hange ta tsaye a jikin wata bishiya dake kallo hall din, yasan shi take jira, dan haka kai tsaye ya nufi wajen ta, a bataji zuwan shi ba, sai kawai ji tayi an hure mata ido, wanda take kallon wani waje, da alama tunani ta tafi.

Figigit ta juyo ta kalle shi, idanun su ya sarke da juna, kowannen su ya kasa cire nashi har na wani tsahon lokaci, sannan Faruq yayi karfin halin janye nashi idon, itama cikin jin kunya ta dauke kanta daga kallon sa, dariya ta bashi, da data tsare shi da ido bata ji kunyar ba sai yanzu.

Cikin son kawar da yanayin yace, wai yau menene sirrin abinda yasa ki farin ciki ne, da irin wannan annashuwar, ai kuwa da sauri, ta juyo fuskar ta ta kuma cika da fara'a tace, yau Daddy na zai dawo daga China, kasan ya shafe sama da wata daya da tafiya, kaga kuwa dole ka ganni cikin farin ciki.

Gaskiya kam haka ne, kuma kasan ma wani abu, kai ya girgiza mata alamar aa, tace Daddy yace akwai wani surprise da yake son sanar dani, nayi nayi ya fada min amma yaki, yace sai ya dawo, to idan banda abinki, ai tunda yace surprise taya kuma zai fada miki, hakane fa, amma kasan me nake tunani, aa sai kin fada, ina tunanin sabuwar mota ya siyo min.

Murmushi yayi, meye na duk wannan zumudin, ke dai ki bari ya dawo mana, koma menene ai zaki gani, ba dai yau zai dawo ba, eh amma sai yamma, karfe biyar jirgin su zai sauka, Allah ya dawo dashi lafiya, Ameen.

Basu ankara ba sukaji muryar mutum a kusa dasu, tsuntsayen soyayya, da sauri duka suka juya suka kalle shi, Salim ne, Faruq yaja tsaki, yace banza baka iya sallama bane, zaka durowa mutane haka kawai, kaji ka, yanzu a wannan duniyar da kuka lula ko duk sallamar da mutum zai yi, zakuji shi ne.

Eh dai ko baza muji ba ai ya kamata dai mutum yayi, ko babu komai ya fita hakki, to naji Malam Liman, assalamualaikum, wslm, Suhaima tayi saurin amsawa, kaga rabu dashi, abokin mu, rigima kawai yake ji, yaya hanya, ashe ka dawo.


Chapter 11


Eh wllh tun a jiyan ai muka dawo ba kwana mukai ba, to sannun ku, shi kuma wanda ya mutu Allah ya jikan sa, duka amsa da amin, daga nan suka dunguma sukayi cafeteria, dan duk a cikin su babu wanda ya karya.

Daga cafeteria dukan su gida suka wuce, dan basu da wata lecture a ranar, da yake exam ta kusa, duk wasu Malaman ma sunyi covering, dan haka ita Suhaimah tace gara ta wuce gida, ta fara shirin tarar Daddyn ta, su kuma su Furuq, wajen aikin su suka wuce.

Ranar Suhaima wuni tayi tana shirye shiryen tarbar mahaifin nata, bama ita kadai ba, har kowa da yake cikin gidan kokari yake yaga yayi wani abu da zai burge mai gidan, har ya yaba, Mummy kuwa har lalle taje tayi, da su kitso, dukan su dai suna cikin farincikin dawowar tashi.

Tana yin sallar la'asar ta shirya ta dauki mota ta fita dauko dauko Daddyn a airport, dan tafi son jirgin nasu ya sauka a kan idon ta, bata son ko kadan ya jira ta, bayan taje, sai da tayi zaman a kalla mintina talatin, sannan aka fara sanarwar saukar jirgin, mikewa tsaye tayi, tana ta hange, gaba daya ta gagara zama.

A kan idon ta jirgin ya sauka, bayan ya dauki wasu yan lokuta, kofa ta bude alamun fasinjojin zasu fara fita, da sauri ta karasa kusa kusa da inda zata hangi fitowar Daddyn nata, tana tsaye tana ta kallon fasinja nata fita, a haka har ta hango  mahaifin nata abin kaunar ta, yana sakkowa daga stairs din jirgin.

Take fuskar ta ta cika da fara'a mara misaltuwa, sai faman bude hakora take, yana gama sakkowa ta isa da gudu, bai ankara ba sai ji yayi an rungume shi tana dariya sai kuma ta fashe da kuka, dariya yayi, ya shiga shafa kanta.

Yasan dalilin kukan nata, mafi yawancin lokuta idan yayi tafiya irin wannan ya dawo tana ganin sa kuka ne abinda take fara masa sallama da shi, wai acewar ta tayi missing din sa ne, kanta ya shiga shafawa alamar lallashi, haba gimbiya ta, meye kuma na kuka, bayan gani na dawo.

Cikin sheshsheka tace ba kai bane Daddy kaje kayi zaman ka a can kamar bazaka dawo ba, kumatun ta ya dan kama yaja, yace to yanzu ba gani dai na dawo ba, nima fa ba dadin zaman can din nake ji ba, nafi son ina tare daku, amma na miki alkawarin daga wannan dawowar da nayi, bazan kara wata tafiya ba, sai na tabbatar da na barki a hannun da bazaki taba shiga kadaici ba.

Murmushi tayi tace Allah daddy, kwarai kuwa, ke dai muje gida, Kinga a gajiye nake, to Daddy tace tana kama akwatin hannun sa, ta fara ja, shi kuma ya rike mata hannu suka jera har bakin mota, a baya ta saka akwatin sannan ta zagayo ta shiga mazaunin driver, dama tuni shi Daddy ya shiga, taja motar suka nufi gida.

Motar su na shiga harabar gidan Mommy na fitowa kamar dama a bakin kofa take jira, bayan sunyi parking, ita ta budewa Daddy mota ya fito, tana masa sannu da zuwa, ya amsa fuskar sa cike da annuri, nan da nan ma'aikatan gidan maza suka karaso bakin motar suna masa barka da zuwa, da sakin fuska yake amsawa kowa, dan shi mutum ne mai daraja wadan suke karkashin shi.

Suhaima na fitowa ta bude baya ta dauko masa akwatin sa, da gudu mai bawa flower ruwa yazo ya karba a hannun ta, yayi cikin falo dashi, ita kuma ta karbi briefcase din sa dake hannun Mommy, suka karasa cikin falon.

Suna shiga kai tsaye bangaren shi suka wuce, Suhaima bayan ta ajiye masa jakar sa, ta juya ta fita, dan ta bashi damar ya shirya ya fito kuma yaci abinci, kasa ta sauka da kanta ta shiga kokarin shirya masa tarin abinciccikan da aka tanada domin shi, tare da yan aiki suna taya ta.
Bayan ya shirya ya sakko, a dining suka same ta tana jiran sakkowar su, sannu da sakkowa ta musu, suka amsa, Mommy taja masa kujera ya zauna sannan tayi sarving dinsa tuwon shinkafa miyar zogale.

Bayan ya gama cin abincin, masallaci ya nufa dan ana gab da fara Kiran sallar magriba, Suma dakunan su suka nufa domin gabatar da sallar, Suhaima dai Allah Allah take Daddy ya sanar da ita bazatan da yace zai mata, bayan ta idar da sallah.


Chapter 12

 
Suna shiga kai tsaye bangaren shi suka wuce, Suhaima bayan ta ajiye masa jakar sa, ta juya ta fita, dan ta bashi damar ya shirya ya fito kuma yaci abinci, kasa ta sauka da kanta ta shiga kokarin shirya masa tarin abinciccikan da aka tanada domin shi, tare da yan aiki suna taya ta.

Bayan ya shirya ya sakko, a dining suka same ta tana jiran sakkowar su, sannu da sakkowa ta musu, suka amsa, Mommy taja masa kujera ya zauna sannan tayi sarving dinsa tuwon shinkafa miyar zogale.

Bayan ya gama cin abincin, masallaci ya nufa dan ana gab da fara Kiran sallar magriba, Suma dakunan su suka nufa domin gabatar da sallar, Suhaima dai Allah Allah take Daddy ya sanar da ita bazatan da yace zai mata.

Bayan ta idar da sallah, ta dauki waya ta kira Faruq, dai dai yana fitowa daga masallaci, tanaji ya daga tace hello, Habibi nayi fushi, ko ka kira ni kace ya Daddy, bai bi ta kan maganar ta ba, ya mayar mata da assalamualaikum, bakin ta ta kama, a ranta tace na shige su.
Shaf ta manta irin yanda ya tsani ka daga waya da hello, tana wannan tunanin taji ya kara maimaita mata sallamar, bata amsa ba ta fara dan Allah Habibi kayi hakuri wllh mantawa nayi ne, to yanzu dai bazaki amsa sallamar ba ko.

Aa kayi hakuri wa'alaikumussalam, dan Allah kayi hakuri subul da baka ne, ba hakuri zaki bani ba Suhaima, kawai so nake ki daina, insha Allah daga yau bazan kuma ba, Allah yasa, yaya Daddy ya sauka lafiya.

Ai bazan amsa ba, tunda kai baka kira ka tambaye ni ba, sai da na kira ka sannan zaka tambaya, aa haba gimbiya kada kice haka mana, bafa haka bane, to yaya ne, dama wai bana so na dame ki ne, nasan yau kina busyn kula da Daddy.
Dariya tayi kamar kuwa ka sani, sai dai amma ai kasan kai ko a wane irin yanayi nake dole ne ka samu lokaci na, haka ne to amin afuwa, tunda dai yanzu kinji dalili na, na kin kiran ki da nayi, babu komai ya wuce, ai kasan kai baka laifi.
Yasu Kaka, suna nan qalau, tamace ayiwa Daddy sannu da zuwa, zaiji insha Allah, to nima bari na tambaya, yaya Daddy da fatan yana nan lafiya, lafiya Alhmdllh, nima har yanzu ban wani samu zama dashi ba, yanzu dai ya tafi sallah, amma wllh yau bazan iya bacci ba, sai naji bazatan da Daddy zai min, dan wllh na kagu, naga ma kai ko ka tambaye ni, koya fada min.

Dariya yayi, Suhaima kenan, ai nasan daya fada miki nine mutum na farko da zaki fara fadawa, shiyasa ban tambaye ki ba, amma tunda hakan laifi ne a gafarce ni, zan dinga tambaya har sai munji bazatar tamu, to shike nan bari na barka, naje na duba ko ya dawo.
To shike nan ki mika min gaisuwa ta kafin nazo da kaina, insha Allah zan fada masa, ka gaida min da Kaka, sai anjima, aa yau dai na yafe, kiyi hira da Daddy, ni idan Allah ya kaimu gobe, sai muyi waya kinji ko, au yanzu ma dai ka kuma yin wani laifin.

Baki ya rike, to kuma dai, to na nemi gafara tun kafin naji laifin nawa, an yafe maka tun ma kafin ka roka, dan kafi karfin hakan, to meye laifin nawa, har yanzu kana nuna baka damu kaji bazatar tamu ba ko, bayan kasan duk abinda ya shafe ni, tare ya shafe mu ko, to Allah ya huci zuciyar ki, nayi alkawarin da kaina ma zan kira ki anjima naji koma menene, yauwa ko kaifa, Bye bye.


Chapter 13

 
Tana gama wayar ta mike ta fita, kai tsaye bangaren Daddy ta nufa dan tasan ma suna can, ilai kuwa a zaune ta same su da Mommy suna hira, sallama ta musu sannan taje ta zauna a kan carpet kusa da kafafun Daddy.

Kallon ta yayi da mamaki, sannan ya juya ga Mommy, Hajiya Badi'a da alama fa yarinyar taki ta girma, me ka gani ta tambaye shi, kinga fa yanda take abu kamar tana jin kunya tane, yaushe kuma Suhaima har ta san kunya.

Lallai kinyi aiki sosai, gashi kuma dai hakar ki ta cimma ruwa, dariya Mommy tayi, aa wannan dai ba aiki na bane, kar kayi saurin yabo na, da mamaki ya kalle ta, to idan ba aikin ki bane aikin waye, aa ni babu ruwa na, ga ta nan ka tambaye ta.

Juyawa yayi ga Suhaima, yace Mama na kinji abinda Mommyn ki take cewa, meyake faruwa fada min naji, dariya tayi ta sunkuyar da kanta, aa Daddy, nifa gaba daya tun jiya ka hana min kwanciyar hankali, gara kawai ka fara bani bazata ta tukunna kafin ayi ko wace hira.

Wace bazata zan baki kuma Mama na, tura baki tayi gaba, ta fara kokarin bubbuga kafa, dariya yayi, aa ashe dai abin yana nan ba tafiya yayi ba, kinga yi hakuri ki fada min, wllh na manta, amma shine ni ka fada min duk kasa na damu, amma kai kace ma ka manta.

Kunnen sa ya kama, yace to na tuba, ban kyauta ba, ayi hakuri a yafewa Daddy, kinsan aiki yayiwa Daddyn naki yawa ne, shiyasa nake saurin manta abu, yi hakuri ki tuna min.

Sai da ta kara tura baki gaba, Mommy dai na zaune tana kallon wannan tabara, sannan tace, ba kaine kace min na shirya zaka zo min da wata bazata mai girma ba, baki ya rike yana dariya, au Mama na ai  indai wannan ne ba mantawa nayi ba, ina sane, na bari ne sai na nutsu, ina zan manta da wannan magana mai muhimmanci.

Au Daddy magana ce ma, eh mana, ke da me kike tsammani, ni na dauka ma sabuwar mota ka siya min, dariya yayi, kai Mama na bakya rabo da shirme yanzu motar ce har sai nace miki wani bazata, yanzu motar kike so a canza miki.

Eh Daddy ina son motar ma, to shike nan gobe ki shirya, kije Sulaiman Motors ki zabi duk kalar motar da kike so, zan kira shi, zamuyi magana, idan kinje kawai kice masa ni na turo ki, to Daddy na gode sosai, Allah ya kara budi, amma dan Allah Daddy ni hankali na ya kasa kwanciya, kawai ka fada min abinda kace zaka fada min.

Murmushi yayi, yace kai Mama na irin wannan doki haka, badan ban fadawa kowa ba, da sai nace ko dai an riga ni sanar miki, to wai Alhaji wannan wace magana ce, nima ai har ka sa na fara kwadayin jin ko menene, cewar Mommy da tun dazu take sauraron su amma bata saka musu baki ba sai yanzu.

Murmushi Daddy ya kara yi, sannan yace, to ai shike nan tunda naga nema kuke ku min taron dangi, dama fa yaron nan ne, Mahmud dan wajen amini na, Alhaji Sambo, ya yiwa mahaifin sa magana, wai yana son Mama na.

Damm Damm Suhaima taji a zuciyar ta, kamar an caka mata wani mashi, duk da tana da yakinin Daddy bazai taba mata auren dole ba, amma dole ne abin ya girgiza ta, dan a wajen ta fitar irin wannan kalmar daga bakin wani da namiji ba Faruq ba, kamar sabo ne, dan ita tuni ta haramtawa kanta kula wani namiji a duniya, koda ma wani yayi kokarin tarar ta da maganar soyayya, takan yi saurin dakatar dashi, da cewa tana da aure.

Wllh kinji fa Hajiya abinda yake tafiya, shine naso sai na huta na nutsu tukunna sai na muku bayani, ai wllh wannan abu ba karamin dadi ya min ba, dan zai kara mana dankon zumunci sosai, har ya kai aya baiji Mommy ta tanka masa ba, sai a sannan ya lura da yanayin fuskokin su, wanda yai matukar daure masa kai.


Chapter 14

 

Damm Damm Suhaima taji a zuciyar ta, kamar an caka mata wani mashi, duk da tana da yakinin Daddy bazai taba mata auren dole ba, amma dole ne abin ya girgiza ta, dan a wajen ta fitar irin wannan kalmar daga bakin wani da namiji ba Faruq ba, kamar sabo ne, dan ita tuni ta haramtawa kanta kula wani namiji a duniya, koda ma wani yayi kokarin tarar ta da maganar soyayya, takan yi saurin dakatar dashi, da cewa tana da aure.  Wllh kinji fa Hajiya abinda yake tafiya, shine naso sai na huta na nutsu tukunna sai na muku bayani, ai wllh wannan abu ba karamin dadi ya min ba, dan zai kara mana dankon zumunci sosai, har ya kai aya baiji Mommy ta tanka masa ba, sai a sannan ya lura da yanayin fuskokin su, wanda yai matukar daure masa kai. Ya juya ga Suhaima, wacce tuni ta shiga cikin wani hali, kiris hawaye yake jira ya wanke mata fuska, yace Mama na meya faru akwai wata matsala ne, ai yana fadin haka kamar yace ta fara kuka, ta fashe da wani matsanancin kuka, ta mike da gudu tayi hanyar dakin ta.  Duk da tana cikin tashin hankali, amma  ko kadan ba tashin hankalin da take ciki ne ya sata kuka ba, tayi hakan ne dan tasan yanda Daddy ya tsani zubar hawayen ta, shiyasa tayi masa hakan, dan ma kar ya fara kokarin lallashin ta akan ta amince da auren Mahmud din, wanda take da yakinin ko me za'ayi, bazata taba auren sa.  Amma sanin yanda Daddy suke da Alhaji Sambo, yasa ta dole ta dauki mataki mai matukar tsauri, idan ba haka ba, zata iya fadawa matsalar da tafi karfin tunanin ta, dan bazata so a kai matakin da Daddy zai roki alfarma a wajen ta ba, dan ta san Daddyn ta yafi karfin ko wace irin alfarma indai tana da halin ta, to amma fa, shima rabuwa da Faruq ba abu bane da zai iya yuwa a wajen ta ba, sai dai idan daya daga cikin su ne ya daina numfashi, wanda bata yi musu wannan fatan.  Da kallon mamaki Daddy ya bita har ta bacewa ganin sa, sannan jiki a sanyaye ya juya ga Mommy, Hajiya Badi'a lafiya kuwa, akwai wani abinda ban sani ba ne, numfasawa Mommy tayi, sannan tace kwarai kuwa Alhaji akwai, dan a gaskiya bazan boye maka ba an samu matsala.   Matsala kuma ya maimata kalmar, tame ke nan, a gaskiya Suhaima dai akwai yaron da take so dan makarantar su, kuma sun dauki tsahon lokaci suna tare, dan har gidan nan ya zazzo, kai ne dai Allah bai taba hada ku dashi ba.  Kuma gaskiya yaron bana tunanin yana da wata matsala, dan Alhmdllh babu laifi yana da tarbiyya dai dai gwargwado, dan wannan sauyawar ma ta Suhaima da ka gani, to yana da nasaba da wannan yaron, dan ba karamin so Suhaima take masa ba, hakan yasa bata iya masa musu, shi kuma yayi amfani da wannan damar yake ta dorata akan hanyar da ta dace. Hannu Daddy ya daga mata, dakata Badi'a bana son maganar banza, da kike ta jero min irin wadan nan maganganun, meye ne hadin ki da yaron nan, har nawa ya biya ki da kike ta masa irin wannan kamfen haka.


Chapter 15

 

Haba Alhaji ka fara halin naka, yanzu akan Suhaima har sai an biya ni kudi sannan zan iya fadar gaskiya, eh hakane mana, idan ba haka ba, shi Mahmud din meye aibun sa, ko kin taba samun labarin yana da wani hali mara kyau ne, balle kice bakya son yar ki ta aure shi.  Ni a yaushe nace bana son Suhaima ta auri Mahmud, naga ma kai ka fara tambaya ta akan abinda yake faruwa, sai kuma bazan fadi gaskiya ba, eh ai ke haka kike duk abinda zan kawo a gidan nan sai kinyi adawa dashi, to wllh akan wannan baki isa ba, wllh in dai ina raye sai Suhaima ta auri Mahmud.  Ai sai aje ayi, dama ni ai bance zan hana ba, daga haka ta mike ta bar mishi falon, shima tana fita ya mike ya nufi dakin Suhaima.  A kwance ya same ta akan gado tayi ruf da ciki, tana jin bude kofar sa ta fara sheshshekar kuka, da sauri ya karasa shigowa cikin dakin, yana fadin haba my daughter mai yasa zaki dinga batawa kan ki rai, ki tsaya muyi magana mana ai sai mu fahimci juna ko.  Kin tashi tayi, har sai da ya zauna a bakin gadon ya kamo hannun ya mikar da ita zaune, tashi my daughter tashi kinji, zama tayi tana ta faman murtsukar ido, ya kama hannun ta ya cire a idon yace dai na kinji kar ya miki ciwo.  Sai da yaga ta dan nutsu sannan yace yauwa yanzu fada min, meya bata miki rai, Daddy ba kai bane kace wai zaka aura min Mahmud, aa ni bance haka ba, nace dai Mahmud yace yana son ki, to Daddy meye banbancin, akwai banbancin mai yawa ma kuwa, amma yanzu dai tsaya, fada min  Mahmud din ne bakya so, da har naga hankalin ki ya tashi haka, ko kuwa akwai wani abu daya taba miki, haba mai babban suna, keda dan uwan ki.  Ni babu abinda ya min kuma bashi da wani aibu, to meyasa bakya son shi, nifa Daddy bance bana son shi ba, kawai dai ni ina da wanda nake so ne, shiru yayi na wani dan lokaci, a ransa yace lallai da gaske fa yarinyar nan zata bani matsala sosai, gaskiyar mahaifiyar ta fa da kullum take fada min na bari a koyawa yarinyar nan yi mana biyayya, amma naki yanzu ga lokacin amfanin hakan yazo.  Can yace, iyye ashe Maman tawa ta girma, har yaushe kika fara sosayya, hannu tasa ta rufe fuskar ta, a ranta tace Allah na gode maka, dama nasan Daddy na bazai bani matsala a soyayya ta ba, yaya sunan sirikin nawa.  Ta kara wani kunshe fuska, sai da yace au naga alama bakya son hira dani yau ko, to bari na tashi nayi tafiya ta, tunda naga alama baki missing dina ba, ya fada yana mikewa, kai Daddy sosai ma nayi missing dinka, to amma bakya son ki bani labari, to ka zauna zan fada maka, komawa yayi ya zauna, sannan yace ina sauraron ki.  Sunan sa Umar Faruq, amma anfi kiran sa da Faruq kawai, aa babban suna, wane ne baban sa kuma, Daddy baban sa ba kowa bane, yama rasu daga shi sai Kakar sa suke yanzu dan yace min Maman sa tana saudiyya, wllh Daddy idan kaji labarin sa sai ya baka tausayi, basu da karfi, amma yana da kokarin neman na kansa.