Skip to main content

SADAUKARWAR SO

🔥 *SADAUKARWAR SO* 🔥

READ MORE BOOKS

 

 

*SADAUKARWAR SO..!!*
_(Labarin Yan"uwantaka,Soyayyah Tare da Sadaukarwa)_

*Wattpad:@Jamilaumar315*
*Mallakar:Jamilaumar(Janafty)*

*HAKKIN MALLAKAâš’ï¸�🚫Wannan Labarin Gabadayansa Mallakata ne juyasa ko Sarrafashi ta sigan maidashi Audio ko kuma Sakashi a Youtube Channels ko kuma Daukansa Zuwa wani kafar sada Zumunta batare da Izinina ko Sanina baâ�Å’Littafin Da Duka Labarin mallaki na ne...!🙅*


*Bismillahir Rahmanir Rahim in the name of Allah The most Beneficient the most Mercefull praise be to Allah load of The words*



*Page1�⃣*


*KANO STATE..*
_*Doguwa Local goverment.*_
_AREA:Ririwai_
*SHIMFIDA..*

"A karamar Hukumar Doguwa Dake Jahar Kanon Dabo a Wata anguwa mai Dauke da Gidaje masu karamin karfi na Hango Wani Karamin Gida na Ginin kasa da Misalin karfe 3:30pm na Talatainin Dare da Hasken Fitila Daga Tsakar Gidan da alamu wani Abu na Faruwa agidan Har takai masu Gidan basu saka Hakarkarinsu a kasa ba Domin kwanciya ba,kila saboda wani yanayi ko Rashin Sukunin Danayi Hashashen Mazauna Gidan mai Dauke da Shashe Guda Biyu Da ke matsaikacin Gidan.

Wani Matashi ne Domin akallah zai kai Kimamin Shekara Talatin da Biyar a Duniya ayanayinsa  Dogo ne Mai Cikar Ingarman Jiki Da kwanji Kallo Daya zakamai ka Fahimci ba Rago bane Domin akwai Tsantsan Jarumta irin ta Manoman kauye Tare Dashi Fari ne sai dai Wahala Irin ta Mazauna kauye yasa Kalarsa ta koma Duhuwa,wanda ya Sauya ya bada wani kala Dabam.

Safa da Marwa yake yi Kofar wani Daki Wanda yaji Filista da Shafan Farin Fenti Hannayensa Suna Goye a bayansa ne yadda yake Safa da marwan bakinsa na Motsi Alamun baya Cikin Natsuwa akwai Tashin Hankali Karara a Fuskarsa Da Hasken Jan Lantarkin Dake Bakin Kofar Dakin ya gama Gauraye Karamin Tsakar Gidan ya haskashi gabadaya.

Wata Yar Dattijuwa ce ta Yaye Labulen Dakin Ta Fito Lokaci Daya Tana gyara Haban Zaninta a kallah Ashekara bazata gaza 58 ba Sai dai kallo Daya zakayi mata kasan Tana da alaqan Jini mai karfin Tsakaninta da Matashin Dake Safa Da marwa abakin Kofar.

Yana ganin ta Fito Da Hanzari ya Isa Gareta yana Fadin"Innanmu..Innanmu..Ya ake Ciki..?

Ya Fada Cikin karaya da wani Fargaba wanda kallo Daya zakayi mai Kaga alamun Hakan ya Bayyana a saman Fuskarsa.

Inna Hasiya ta Sauke Numfashi Lokaci Daya Tana kallon Fuskar Dan"ta Habibu Daya Gauraye da Fargaba da Tsausayin Halin da mai Dakinsa Take Ciki Cikin son kwantar mai da Hankali Ta Rike Hannayensa Duka Biyu Tana Fadin"Har yanzu Bata Sauka ba Habibu..Ammh Tana kan gwiwa Insha Allahu yanzu Zata sauka Kadaina Damuwa Kaji ko..?

Cikin Karaya ya Girgiza kai yana Fadin"Innanmu Ko Zan Fita na samo Mota ne mu kaita nan General Hospital mugani..? Kai ta Girgizamai kafin ta samu Zarafin Mgana sukaji Numfashi mai karfi da Salati lokaci Daya Muryan Hajara ya Gauraye Gidan Inna Hasiya ta Saki Hannu  Habibu Ta Fada Dakin Shima kamar ya Bita Haka yaji ammh Ba Dama sai ya koma ya Jingina Jikin Ginin Dakin yana Maimaita kalmar.

"Hasbunallahi wani"imal Wakeel.."


Haka ya Dinga maimaitawa a sarari Saboda Fargabansa da Tashin Hankalin Dayake ciki ya Ragu Cikin Ikon Allah kuwa sai yaji ya Fara samun Natsuwa Ya Hada Hannnuwansa duka biyun Ya Daga sama Yana Fadin"Ya Allah..Kai ne Ubangijin Sammai da kassai..Kai ne Ubangiji Duka Hallitun Duniya baka Haifa ba kuma Ba"a Haifeka ba ya Allah kafi kowa sanin Halin da Duka Bayinka suke ciki Kashewa da Rayawa Duka suna Hannuwanka ne,yau in ka Dauke Hajara Zan yi Takwalli Zuwa Gareka na kuma yi Godiya mai yawa ammh In ka Sauketa Lafiya Ita da Abunda ke Cikinta Zan kasance Cikin Farinciki kuma Zan Cigaba da Godema Ni"imarka Har na koma ga Gareka ya Allah.."


Ya Karishe Fada wasu Zafafan Hawaye suna Zubo masa Daidai Lokacin da wani Farin Dattijo mai Farin gashi ya Bude Wata Kofa Daga Gabas din Dakunan Guda Biyu Dake Barayin ya Fito Yana gyara Carbin Hannunsa Lokaci Daya Da Kwanon sha Cike Da Ruwa a Hannunsa yana Fadin"Ya ka nam Habibu..Maza zo ka mikama Hasiya Ruwan addu"an ta bata tasha Insha Allahu yanzu Zata sauka..!

Tsohon ya Fada Lokaci Daya yana Kallon Habibu,Da Sauri Habibun ya taho zuwa gareshi yasa ka Hannu Biyu ya karbi Kwanon Shan Ganin yadda Hannuwansa ke Rawa yasa Baba Jibo ya kurama Habibin Ido Lokaci Daya yana Fadin"Anya Habibu..? Habibu na ne Jarumin maza kuwa..? Yayan Maryama kuma Uba Gareta..?yau kaine naga Rudewa da Damuwa akan Fuskarka mai Cike da Zati da Hakuri..?

Habibi Daya Karbi Ruwan addu"an Yana Fadin"Na kasa Zama Jarumi ne Baba..Bana son wani Abu ya samu Hajara ko Abunda ke Cikinta.."Yafada kamar Zai saki kuka Baba Jibo Ya Dafa kan Habibi Lokaci Daya Yana Fadin"Kada ka Damu...Insha Allahu Hajara Zata Haihu Lafiya da yardan Allah.."Da Sauri yace"Allah yasa Baba.."Yafada yana Juyawa Baba Jibo ya Bisa da kallon Tsausayi Lokaci Daya ya kada kai ya juya ya koma Ciki Lokaci Daya yana gyara Zaman Rawanin Dake kansa.

Da Hanzari Habibu ya isa Kofar Dakin yana Fadin"Innanmu ga Ruwan Addu"a Baba yace ki Bata Tasha.."Daga Cikin Dakin ta amsa mai Sai gata ta Leko Ta karba Kallonta yayi yadda Duk Ta Hada Zufa yana Fadin"Innanmu ko Zan Fita na Buga Gidan Mallam Haruna ko Zai Bamu Mairo Tazo ta kama Miki..?

Kai ta Girgizamai Tana Fadin"Bari dai mu gani Habibu..Muna Fatan Komai ya zama Daidai.."Cikin Son Aro Jarumta ya gyada kai yace"Allah yasa Innanmu.."Daga Haka ta koma Ciki Shi kuma sai ya koma Gefe ya Durkusa kawai yana karantar Duka Addu"a Da Tazo Bakinsa Ko Minti Sha Biyar ba"ayi ba yaji Kukan Jariri ya Karade Gidan Gabadaya Lokaci Daya da Gudan da Inna Hasiya ta Saki.

Cikin Farinciki Habibu ya Mike bakinsa kamar zai yage Saboda Murna Hannu ya Daga sama Lokaci Daya yana Fadin"Alhamdulillah bi Ni"imatis salihat.."Bai gama Rufe baki ba Baba Jibo Shima Dake Ciki yana ta Jan Carbi yaji kukan Jikansa akaron Farko a Duniya ya Fito Jikinsa na Rawa yana Fadin"Habibu Hajara ta Sauka ko..? Kai masha Allah.."

Habibu Da Murna ta Hanashi Mgana ya isa ga Baba Jibo ya Rumgumesa yana Fadin"Ta sauka Baba..Naji kukan Abunda aka Haifa naji gudan Innanmu Baba.."Baba Jibo ya Murmusa Lokaci Daya yana Dafa Bayan Habibu yana Fadin"Sai ka Godema Allah da Ni"imar da yayi maka Habibu.."Dagosa yayi Bakinsa Har kunni Basu samu Zarafin mgana ba Inna Hasiya ta Fito da Sauri Bakinta kamar Zai yage.

Kafin ma ta isa Garesu Habibu ya Fara karisowa Garesu Tana Fadin"Masha Allah..Hajara ta Sauka na samu Sabon Megida..Ya nan mai kama da Habibuna kamar yayi kaki.."Habibu sai kawai yaji ya Rumgume Inna Hasiya yana Fadin"Allah na gode maka.."Su kansu Farincikinsu suke bakinsu yaki Rufuwa nasan wasu zasu yi mamakin ina alkunyar nan..? Habibu Da iyayansa Tamkar Abokan juna ne Duk Duniya bayan su da kanwarsa Maryama yana jin bashi da kowa sai su sune Abokan Shawaransa da Sirrinsa Gabadaya.

Inna Hasiya ta kalli Habibu Tana Fadin"Bari na saka Ruwan wankan da zan gyara su..Na yanke Cibiya kuma an yi Sa"a Mabiya Ta Biyo baya itama.."Baba Jibo yace"Alhamdulillah..Allah kara Lafiya Allah ya Raya Abunda aka Samu.."Dukkansu suka amsa da Ameen da Sauri Habibu yace"A"a Innanmu Ki koma Ciki wajenta..Bari na Dora Ruwan  Zafin.."Inna Hasiya tace"Shikenan..Ka Dora Babbar Tukunyar nan ne.."Cikin Hanzari ya wuce karamin Madafin da aka ginashi da kasa yana Fadin"Toh Innanmu.."


Cikin Dakin ta koma Wajen Hajara Ta Cigaba da Goge Wajen daya Baci da Jini Mabiyan da Cibiyan Kuma ta Nannade su Cikin Wata bakar Leda,Yaron kuma Ta Namnadeshi Cikin wani Zani Ta Dorashi Gefen Hajara Dake kwance Tana Maida Numfashin Wahala.

Cikin kulawa Inna Hasiya ke Fadin"Sannu da Kokari Hajara..'Hajara ta Kauda kai ta kasa Hada ido da Inna Hasiyan Saboda kunya sanin Halinta yasa Innar Bata Damu ba ta Fice da Zanmuwan da suka Baci da Zani Tana Fadin"Kai sabon Megidana nawa Daga gani zai Taba Rigima.."

Tafada jin kukan Dayake yi Tayi Yana Inya..! Inya..Inya..! Koda ta Fita Har Habibu ya Hada Wuta da Itace ya Saka katuwar Gwarwa ya Cikata da Ruwa ya Dora,Daga ganin yadda yake aikin Zaka san ya Saba Da irin wadanan ayyukan Inna Hasiya na Fitowa da kayan Habibu yaki barinta Ta Wankesu Shi ya karba nan da nan Ya Dibi Ruwa Cikin Katon Bombin da shi ya Cikashi da yammah bayan ya Dawo Daga gona kamar yasa yau din Zata kasance Ranace ta Musamman awajensa.

Tsab ya wanke Zannuwan nan masu jini ya Shanya Lokacin Har Ruwan ya Tafasa Inna Hasiya Ta Diba tayi ma Yaron wanka ta Sanya mai kayam sanyi masu kyau wanda Maryama ta Siyo ta kawoma Hajara Cikin kayan Datake Tarawa ne na Haihuwanta Wanda har yau Allah bai Bata ba.

Shi kuma Baba Jibo Shi ya Karbi Cibiyar da Mabiyan Ya Haka Rami ya Binne su Duka acikin Gidan ta chan Baya ya maida kasa ya Dandade,Inna Hasiya na Gama gyara yaron ta Fito ma dasu Habibu Dashi wannan karon Sai Habibu yayi kara ya bar ma Baba Jibo ya Fara karban yaron Dake kama da Habibu sak Lokacin yana Jariri.

Inna Hasiya Daki ta koma Ta Kamo Hasiya zuwa Makewayin Dake Chan gefe Katange da Langa Langa Domin yimata wanka Habibu ya Bisu da kallo Kamar ya kamota ya Rumgumeta ya Jadaddamata Godiyarsa Baba Jibo Bakinsa yaki Rufuwa Fadi yake"Hajara Sannu Kinji ko..? Allah yayi Miki albarka.."

Bata samu Damar mgana ba,sai ma kanta Data Dinga Rufewa Domin Hajara mace ce mai kunya Da kawaici Sai da Suka Shige Makewayin kana Habibu ya Sauke Numfashi yana Leken yaron a Hannun Baba Jibo Shikuma Lura da hakan da yayi sai ya karisa addu"an Neman Tsarin Dayake ma yaron ya Mikama Habibu yana Fadin"Karbesa..Kayi masa addu"a ka kuma sakamai albarka Daga bakin ka mai albarka Habibu.."Hannunsa da Jikinsa na rawa ya karbeshi Lokaci Daya yana kuramai Ido Shima yaron kamar ya sani ya Bude Idanuwansa Tar yana kallon Habibu wanda Hawaye suka Cikama Kwarmin Ido.

Shekara Biyar sukayi da aure Shi da Hajara sai yau Allah ya basu Haihuwa sai dai ba wannan ne ya sakashi kuka ba yana Jin Raunin Dake Zuciyarsa Raunin Tunawa da Tilon kanwarsa ce Maryama Wacce ta Shafe Shekaru Goma da Aure Bata Taba ko Bari ba Kallesa yadda yake Farinciki Ya samu Karuwa yaya Zuciyar Maryama Take Ciki na Rashin Haihuwa..? rauninta me yawa ne ya sani Sai yaji Dama Dama Allah Ya bashi Zabi Tun Farko Da Zai ce ne Maryama Ta Haihu Taga kwanta aduniya ko da Shi Zai koma ga Allah bai Haihu ba Rauninsa bazai Bayyana ba Inhar Maryama Zatayi Farinciki kuma Zata Dauwama cikin Annurin Samun Haihuwa a Rayuwarta.

Cikin Siyasa ya Share Hawayensa Lokaci Daya ya Fara Tofamai addu"a Da Neman Tsari da albarka Duniya suna nan Tsaye Inna Hasiya ta Fito da Hajara Zuwa Daki Baba Jibo Ya Dauki Buta ya Shiga Makewayi zai kama Ruwa saboda an Fara Kiraye Kirayen Sallar Asuba a wasu massallatai,sai Habibu ya Bi bayansu Zuwa Dakin yana Shiga ya iske Har Inna Hasiya ta Turara Dakin da Turaran Kamshi Hajara na saka kaya Ganin ya Shigo sai ta Fita ta basu Waje Tace Zata je ta Dama ma Hajara kunu ta kuma Dumama mata Tuwo Taci.

Tana ganinsa ya Shigo Tayi Saurin Komawa Ta Zauna Daman kunzugu tayi ma kanta Saboda Tare Jinin Dake Zuba ajikinta,Kunya take ji sai Sunkuyar dakai take yi Bata son Hada ido Dashi Ganin haka yasa yayi Mirmishi ya isa gefenta ya Zauna Yana kallonta Cikin Taushin Murya yace"Hajara...!!

Cikin Sanyin Jiki Ta Dago kanta Tana kallonsa Mirmishi ya sakarmata yana Fadin"Sannu da kokari..Allah ya Biya Miki Bukatanki Nagode Yau sanadin ki zan amsa sunan Uba.."Kai ta kara Sunkuyarwa bata ce komai ba Sai ya kara Fadin"Ba ki ce Ameen ba Hajara..?

Kanta na kasa tana Tura kanta Cikin Lullubinta Tace"Na Fada acikin Raina.."Kai kawai ya Girgiza yana Tura Mata yaron Jikinta Lokaci Daya yana Fadin"Kinga Kyautar da Allah yayi mana ko...?

Kanta ta kara maidawa gefe Tana Fadin"Nagani.Allah ya rayamana shi.."Cikin Farincikin addu"an ta yace"Ameen Hajara..Ameen ya Allah."

Ta Fahimci acikin Jikinta kallonta yake yasa tace Cikin Sanyin murya"Ka Kira Adda Kuwa..?
Cikin Dafe kai yace"Kai..nayi Babban Mantuwa..Wlh ban Kira Maryama ba Bayan Kin Haihu..'

Inna Hasiya Dake Shigowa Dakin Tace"Hanzarta ka Kirata..Domin Nasan yanzu haka Tana chan hankalinta Tashe Tun bayan Kiran Dakayi mata ka Fadamata Hajara nakan Gwiwa.."

Cikin Sauri ya Mike yamikama Hajara yaron sai taki karba ta kauda kai Sai kawai ya Ijiyeshi Saman gado ya Fice Ya bar Inna Hasiya Tana Tsiyayama Hajara Kunun Kanwar Data Dama Mata acikin Katon Kofi Gefe Daya kuma ga Dumaman Tuwo Miyar kuka Tana Turiri.

Yana Fita ya Lalubo wayarsa Cikin Aljihun wandonsa wanda Tun Bayan da Ya kira Maryama da kansa ya Fadamata Abunda ke Faruwa bai kara bi Ta kan wayar ba Yana cirota ya Dannata sai ya iske Kiran Maryama har sau Uku Cikin Sauri yabi bayan Kiran Bugu Daya ana Biyu Ta Daga Tana Fadin"Yaya Habibu ina ta kiranka Baka Daga ba Hankalina ya Tashi Yaya Hajaran ta Sauka Lafiya kuwa..?

Cikin Mirmishi yace"Afuwan kanwata..Laifinane Wayar tana Aljihuna ban ji Kiranki ba..Hajara ta sauka an samu D"a Namiji Kanwata.."Yafada Cikin Farinciki Maryama Dake kan Darduma acikim kuryan Dakinta Bayan Ta idar da Raka"atulFajir,Domin Tun bayan Kiran da Habibu yayi mata Ya Fadamata Halin da Hajara take ciki bata koma Barci ba Alwala Tayi Ta zo ta Fara Salla Tana addu"an Allah ya Sauketa Lafiya Megidanta Sulaiman yana kwance yana ta Sharan Barcinsa Harda Minshari baisan Abunda yake Faruwa ba.

Cikin Farinciki Maryama Tace"Alhamdulillah..Yaya Barkanmu.Fatan Dukkansu suna Lafiya..? Yace"Lafiyansu kalau kanwata..Nasan baki koma barci ba Don Allah kada ki ce Zaki Taho Tun Safe Ki bari ki kwanta Ki Huta Kinji ko.?

Cikin Mirmishi Kaunar Dake Tsakaninta da Dan"uwanta Tace"Haba yaya Ace Yaya Hajara ta Sauka kuma sai Tun safe ban Taho ba..?kada damu kanka kayi mata barka kace ma Innanmu ta ijiyemin kunun kanwata Da Safe ina Tafe.."Bai da tace wa Sanin Ko yace kartayi Sammakon Zuwa sai Tazo Shiyasa yace mata"Shikenan kanwata sai kin zo..ki gaida Megidan naki.."

Daga haka suka yanke Kiran Maryama Ta Daga Hannu sama Tana kwaroroma Allah Godiya Cikin Zubar Hawaye,Sule mijinta Daya ji sheshhekan kukanta ya Farkar dashi ya Tashi ya Mitsike ido Cikim mamaki yake Fadin"Maryama Lafiya.?

Waiwayowa Tayi Tana Kallonsa kafin tace"Abun Farinciki ne..Yaya Hajara Matar Yaya Habibu ce ta Haihu an samu Da Namiji.."Tafada Cikin Farinciki Yana Daga kwance ya Tashi Zaune yana Fadin"ah ba Shakka..Kya yi Dariya..Allah ya Raya kema Allah ya baki naki Maryama.."Daya Fadi Haka sai kawai ta Murmusa kafin ta Mike Tana Fadin"Ka tashi an Fara Salla awasu masllatan fa.."

Daga Haka ta Tada Kabbaran Sallar,Da ido ya Bita dashi na Tsausayinta Allah ya sani yana son Maryama kuma Har yau har Gobe bai Taba Jin sonta ya Ragu Daga Zuciyarsa ba Rashin Haihuwanta Ba Daga ita bane Daga Allah ne,Ammh Goggo Tana Dora,komai kan Maryama Ganin ta matsamai ya kara Aure kuma Har sun Haihu da Zainabu Har ya"ya Biyu.

Yana Jin Muryan Goggon Tana Mgana da Zainabu Daga Tsakar Gidan Hakanan ya Mike Jikinsa a sanyaye ya saka Rigarsa ya Dauki Butan Da Maryama ta Cikamai Da Ruwa ya Fita Zuwa makewayi Goggo Bata Wajen Kila Ta idar da alwala ne ta Shigs Dakinta tayi sallah Zainabu kadai ya gani Tana alwala Gaisheshi Tayi ya amsa Sama sama ya Fada makewayi Tabisa da kallo Tana kunkuni Kasa kasa.

Shima Habibu suna gama Mgana da Maryama Ya Daura alwala suka Fita shi da Baba Jibo Zuwa massallaci Domin yin Sallar asuba koda suka je ba"a Tada Sallar ba sai suka koma Chan Baya suka Tada Raka"atulFajir Kafin Lokacin Sallah yayi suna Idarwa aka Tada Salla sai suka matsa Gaba suka Hada Sahu aka Tada Salla Dasu.

Kafin wayewar gari Haihuwan Hajara Matar Habibu ya gama Yada anguwa Har Gidan Iyayan Hajara Inno Domin Mahaifinta ya Rasu kuma Aminine ga Baba Jibo Baba Yahaya kenan ya Rasu Bayan Auran Hajara da Habibu Da Shekara Daya Abokiyar Zaman Inno Din Wacce suke Kira Ayyah ita tazo Da Safe ganin Sabon megida da kuma Taimaka ma Inna Hasiya da wasu ayyukan Kowa kagani Baki Har kunni Saboda Farinciki Makota sai Shigowa suke Barka Habibu kuma da Baba Jibo tun Safe suka Tafi Gona Dayake Tun kafin a Haifi Habibu Kowa yasan Sana"ar Baba Jibo Noma ce ammh Basu bar Gidan ba sai da Habibu ya Cika Duka ma zuban Ruwan gidan da Ruwa Saboda amfanin Masu Jego.

Wajen Karfe 9am na safe sai ga Maryama Ta iso Da kayan wanka Iri Iri Jakarta kuma Cike da kayan yara,Murna wajen Inna Hasiya ba mgana na ganin yarta Maryama Tare da Sule suka zo Shi ya kawota kan Mashin Karfe karfensa Dayake acikin Garin Maruka Take Aure Har Ciki ya shigo suka gaisa da su Inna Hasiya da Ayyah ya Shiga yayi ma Hajara Barka Ya Karbi Jaririn da Tunda Maryama Tazo Ta Daukesa Take kamkame dashi Yaji kamar yayi mata kwallah acikin Ranshi yana Rokon Allah ya Nuna ma Maryama Itama ta Haifi Danta Daga Cikinta.

Bai Dade ba ya barta nan ya tafi,Cikin kasuwar Doguwa Saboda anan yake da Shagon Sai da kayan Kwalliyan mata wato Costometic,Sai ya Tashi kasuwa da yammah Zai zo ya Dauketa su koma Gida.

Nan Maryama ta Wuni Har yammah Suna ta Hidima da Hajara da Jaririnta Sai Gabda mganriba kana suka Habibu Shigo Haduwar Yaya da kanwar wani Haduwane da kamar Zasu Hadiye Juna Daman hakan take kasancewa In dai suka Hadu kamar kada su Rabu Kuma ko yaushe ko Maryam Batazo nan Ririwai din ba Shi Habibun Koda yaushe yana Hanyan zuwa Maruka ganin Maryama din.

Sai da sukayi Sallar mangariba suka Dawo Inna Hasiya ta kaima Baba Jibo Abincinsa Dakinta Shi kuma Habibu Maryama Ta kawomai nan Dakin Hajara Ayya kuma ta Wuce Gida sai da Safe zata Dawo.

Umartanta Yayi data wanko Hannuwanta Tazosuci Tuwon Tare,Tashi Tayi taje ta wanke Hannuwanta Tazo Suna cin Tuwon suna Hira Sama sama,Hajara na gefe Tana kallonsu Abun nasu Sha"awa yake bata Tana ji Dama itama Tana da yaya mai kula da ita kamar yadda Habibu ke kula da Maryama..? Sai wata Zuciyar tace mata Ki Godema Allah Hajara Habibu ba iya Miji bane gareki Ya Shanye Miki Kuma ya kare Miki Duka Kishiruwan uba da yaya agareta yana Bata kulawa Daidai gwargwado.

Sai da suka gama Cin Tuwon Maryama ta kwashe komai takai Madafi kana ta Dawo Dakin Ta Dauko Jaririn Ta Mikamai Tana Fadin"Yaya kasan yaron nan Dakai yake kama..? Kayi ma yaya Hajara wayau..!


Yana Dariya ya karbesa yana Fadin"Kece kikayi mata wayau..Domin dake yake kama ke Hajara tayi ma Haihuwa kanwata.."Tana Zama agefensa Bakinta yaki Rufuwa tace"Da gaske Ni aka Haifama wannan yaron..? Cikin Tsausayinta yace"Tabbas..Shiyasa ma kece zaki Zabamai sunan da zamu sakamai kanwata..!

Hawaye suka kawo Idanuwanta Tayi Saurin Maida su Tana gyada kai kafin tace"A kullum Ina ganin nayi ma Sauran kanne Zarra wajen samun yaya kamar ka...Bantaba ganin mutum mai kyakyawan Zuciya ba irinka ba Yaya na Rasa da wani kalma zan Gode maka.."

Yaron ya Mika mata ta karba Yana Fadin"Karbi D'nki ki Zabi sunan da zamu Dinga Kiransa.."

Sai da Ta bata Lokaci Tana kallonsa kana Ta Dago Tana kallon Habibu da Hajara da suka Zuba mata ido Cikin Zubowar kwalla tace" MASTUR...! Mastur nake so a sakamai Yaya.."


Ko Gaddama bai yi mata ba ya gyada kai yana Fadin"Allah ya Raya Mastur Da"n Maryama Gobe da Safe Baba zai Mai Huduba da Mastur.."Farinciki ya kamata ta Hada da yaron da Ya Habibu taa Rumgume  Habibun Shi kuma yana Lallashinta Dagowa Tayi Tana kallon Hajara Tana Fadin"Yaya Hajara baki ce komai ba..?


Mirmishi tayi kafin tace"Me zan ce Adda..? Gaskiyasa ne Haihuwan taki ce..Allah ya Raya Mastur.."Atare suka amsa da Ameen suna Mirmishi Har Inna Hasiya ta Dawo nan Maryama Take gayamata itama tace Allah ya Raya Mastur suna nan zaune sai ga Sule yazo Daukanta ya shigo suka gaisa da Su Baba da Yaya Habibun,Nan Maryama sai da Tagayamai ita ta sakama Danta Suna,sai murna take Dukkansu sun ji Dadin ganinta Cikin Farimciki Dukkansu.

Dakyar Maryama Ta ijiye Mastur Tabi Sule Zuwa Gida Har Waje Habibu ya Rakata Yana Ta Faman Allah ya Kiyaye Hanya da Sakon in sun isa gida Lafiya ta Kirashi a waya ta gayamai ta Hau Mashin din Mijinta Tana Fadin.

"Toh Yaya in mun isa zan Kira ka Insha Allahu.."


_Hmm...Salon na Musammanne..Tafiyar akwai Nisan Zango Yanzu muke Cikin Shimfidan Labarin bamu ma Shiga Cikin Mafarin ba.._



_Albishirunku Masoyana wannan karan na bude muku wani Shashi na musamman Saboda ku..Ina masu Bukatan Atalla musu Hajarsu Ko wani iri ne Domin samun costumer ta ko"ina..? Ku garzayo kakarku ta kusa yanke saka Zan Tallata muku Hajarku a Duka Shafukana Domin inganta Sana"arku da kuma Samun Cinikaya mai Tsabta da kuma kara Hada hada wajen Masi siye da Siyarwa mai Bukatar A tallata mata Hajjarta Zata iya min mgana kai Tsaye ta wannan Lambar Tawa 09069067488 domin karin Bayani...Sai kunzo Kunsan dai mai kasuwa Shi ke da Riba.._


*Domin zama Daya Daga cikin wadanda zasu karanta Labarin SADAUKARWAR SO..! Zaku Biya kudin karatunku kamar haka Masu amfani da Banki Zasu Tura â‚?300 ta wannan asusun banki 0552179550 Jamila umar gtb,Masu Katin waya kuma zasu Turo â‚?400, ta wannan lambar wayar 09069067488 Adauki Hoton katin sai aturo kai Tsaye mutanenmu na Niger kuma zasu Tuntubi wannan lambar kamar haka +22794775574 domin karin bayani,Insha Allahu mutum zai tsinci kansa a paid group ina maraba da ku masoyana nagode*





*Janafty..*
*Intelligent writer"s asso*
*01/10/2021*
1/1/22, 18:50 - Maryam Badmsi: *SADAUKARWAR SO..!!*
_(Labarin Yan"uwantaka,Soyayyah Tare da Sadaukarwa)_

*Wattpad:@Jamilaumar315*
*Mallakar:Jamilaumar(Janafty)*



*Page2�⃣*



Kullum Maryama Tana Hanyar Zuwa Ririwai ganin Mastur wanda Tuni Baba Jibo yayi mai Huduba da sunan da Maryama ta Zabamai kowa ya sani Zabin Maryama Shine Zabin Habibu.

Har sai da akayi suna kana Ta Zauna agida anyi Shagali Daidai Gwargwado na masu karamin Karfi an yankama Mastur katon Ragon Sunansa wanda Maryama ita ta Kiyawata Ragon a Chan Maruka Daman Tun Samuwar Cikin Hajarah Din Tace Ragon da akuyarta ta Haifa na Sunan Abunda Hajara ta Haifa ne kaunar Dake Tsakanin Habibu da Maryama Wata kaunace da Allah ne kadai yasan Yawanta.

Inna Hasiya ce ta Cigaba da kulawa da Hajara da Mastur,Ayya ma Sai dai ta Leko su Inno kuma Bata zo ba Tana yi ma Inna Hasiya kara da kuma Ayyah Kuma Alhamdulillah Hajara Tana samun Dukkan kula Bata komai Inna Hasiya Ke Duka ayyukan Gidan Hajara ko Tace Zatayi sai Ta Hanata Gefe Daya Habibu na Tsaye da Duka Kafafunsa na ganin ya Yalwata Ahalinsa Gabadaya Duk da Baba Jibo Karfinsa ya Fara karewa ammh Karfin Noman na nan Tare Dashi,Baya barin Habibu Ya Tafi Gona Shi kadai Koda bazai yi wani aiki ba sukan Tafi Tare Domin ya Taimakamai suna Noma koda ba Damuna ba sukan Noma Irin su Tumatir da Sauransu kafin Damina Ta zo.

Koda Hajara Tayi arba"in da Haihuwa sai wanda ya ganta tayi Kiba ita da Mastur kamar ba su ba sun samu kulawa Sosai kuma suna cin abinci mai Gina Jiki Sai kuma akayi Sa"a Nonon Hajara mai kyau ne Tuni Mastur sai Kiba yake Maryama kuwa Duk sati sai Tazo Garin kawai Domin Taga Mastur wanda Soyayyar Datake yi mai Tun yana Ciki ne Har yazo Gidan Duniya.

Sai Hajara Da kanta takai ma Inno Mastur Ta gansa ta Daukesa Ta sakamai albarka Tare da Fatan Rayuwa mai albarka Chan ta wuni Tare Dasu Suna ta ina suka saka da ita ita da Mastur irin Soyayyar da Kowa ke Nuna mata ita da Abunda ta Haifa na sakata kuka Habibu Kullim ya Dawo Haka Zai Dauki Mastur ya Dinga mai wasa Tun yaron baya ganewa Har ya Fara gane mai kula Dashi Sosai Wani Lokacin Hajara ita yar kallo ce Domin Daga Inna Hasiya Har Baba Jibo Suna Rawan Jiki wajen Daukan Mastur yaron ya Shiga Ran kowa Saboda Nasabarsa da Kyansa Tun yana Jaririnsa.

*TUSHE..*

"JIBRIL Baba Jibo da Inna Hasiya sune Asalin iyayen Habibu da Maryama su din Dukkansu Haifffun Garin Doguwa Local Goverment Dake garin kanon Dabo awata anguwa mai Suna Ririwai.

Tsakanin Inna Hasiya da Baba Jibo auran Zumunci ne Tunda Abokan wasa suke da Juna iyayansu Tun suna da rai suka Hadasu Zama waje Daya saboda ganin Dacewarsu,Tun iyaye da kakanin Sana"ar iyayen Su Baba Jibo Noma ce da Kiwo kuma ita suka gada Dayake alokacin Ilimin Zamanin nan bai wani yawaita ba Sai karatun allo Daka Sauke Zaka Fara Noma Domin itace Sana"a Lokacin Da kowa yasan iyayenmu Musamman ma na kauye Dashi.

Tun bayan Auran Baba Jibo da Inna Hasiya Allah ya Dauki Ran Iyayan Baba Jibo Daman Inna Hasiya Iyayan Baba Jibon suka Riketa Ta rasa nata iyayan Tun Tana karama sai ya zamanto sun Rumgumi Maraicin su Dagasu sai Daidai kun yan"uwa da suka Rage wasu duk sun Tsallake Zuwa wasu garuruwan Domin neman nakai kuma Tunda suka Tafi basu Dawo ba.

Inna Hasiya itama ta Dade bata samu Haihuwa ba Domin sai da suka Fitar da Ransu kana Allah ya basu Habibu wanda Haihuwarsu yazo musu da wani Budi a Shekarar Amfanin Gona yayi kyau Baba Jibo Da abokinsa Mallam Yahaya sun samu Alheri sosai Shiyasa Tun Lokaci Baba Jibo Ke Kiran Habibi Jarumi kuma Gwarzo.
Tun Haihuwansa suke matukar sonsa Haka Habibu ya Taso Cikin Gatan Duka iyayansa Gefe Daya kuma ga Aminin Mahaifinsa Baba Yahaya da Inno da Ayya suma ba"a barsu abaya ba wajen kula Dashi Dayake Zumunta ne na Makota ka wanda alokacin Bayan Makocinka Shine Babban Amininka kuma Dan"uwanka Abokin Shawaranka.

Habibu ya taso Shi kadai ne agaban Inna Hasiya kuma Shi mutum ne mai kulafuncin Yan"uwa sai dai Allah bai bashi ba Tun yana ma Inna Hasiya kukan ta sama mai kanwa Har ya Gaji Lokacin da aka Haifi Maryama Habibu nada Shekara Tara a Duniya ne Lokacin yana Makarantar Allo ya Hada karatunsa na Izifi Talatin,Alokacin ko su inna Hasiya sun Cire ransu da samun wani karuwa sai gashi Allah ya basu Maryama Farincikin da Habibu yayi ko Inna Hasiya da Baba Jibo basu yi shi ba Haihuwan ta kasance shi akayi mawa.

Domin Tun da Maryama Tazo Duniya alhakin kula da ita ya koma Wuyan Habibu MKarantar allo Kadai yake iya Tafiya yabar Maryama Bayanan kuwa Yana Gida Tare da ita Tun Tana Wata Hudu a Duniya Da Rigima da komai Yake sakawa Inna Hasiya na goyamai Maryama Da karfi da yaji ya koya mata zama Komai ya samu Baya iya Cinsa shi kadai Sai ya Rage ma Maryama Tun kafin Maryama ta isa Fara cin Abinci Habibu ya Fara bama Maryama kayan kwalama Batare da Sanin su Inna ba sai Dai kawai suka ga Maryama Bakinta ya Bude da Cin Abu komai aka bata.

Maryama da Habibu ta Fara Bude Ido a Duniya,Tun Tana Shekara Daya a Duniya Ta Fara Tafiya Ko"ina kuma Habibu Zai saka Kafa Bata yarda sai ta Bishi In ko yamata wayau ya Tafi makarantar Allo bata da ita ba In ta Fara kuka sai ya Dawo Taji Muryansa Ya Dauketa ya Lallasheta ya bata Sweet din Daya Siyo mata take yin Shuru Ko Inna Hasiya ko Baba Jibo Bata yarda da kowa sai Habibu Mutane suna mamaki da Jinjina ma Wannan kaunar Dake Tsakanin Maryama da Habibu.

Tun awannan Shekarun nata Habibu ke Daukanta yana Zuwa Allo da ita Saboda In bai je da ita ba Ta Rika kuka kenan akwai Ranar ma Data Fakaici Ido Tabi Bayansa sai dai Tsinto ta akayi Tabi Hanya Tunda Ranar Bai kara yarda ya Tafi ya barta ba Duk inda Zashi da ita yake Tafiya Tun Alarammah na Fada har ya Daina Saboda Maryama Bata yarda da kowa sai Yayanta Habibu Kaunace Daga Allah data kuma Fara Tun Tasowarsu.

Haka Rayuwarsu Ta Cigaba da Gudana Cikin kaunar Juna Har Habibu ya Sauke alqurani aka yayeshi sai ya zamana Maryama kadai ke zuwa makaranta Shima ssi da aka sha Daga Domin Da Farko tace bazata kara zuwa makarantar ba sai da yayanta Habibu Shi kuma Lokacin ya Fara Bin Baba Jibo Gona sai yamma suke Dawowa Maryama wuni take kuka Kamar Wata wacce Za"a yanka In Ta Dawo Daga allo Bata ga Yayanta ba Inna Hasiya tagaji da Lallashi ta Fita Batunta Sai ya Dawo ya Lallasheta Take yin shiru Dole ta Hakura Tunda Inna Hasiya tacr Tana mace baza ta Rika Bin su Gona ba ta zauna agida.

Haka Rayuwarsu ta Cigaba da Tafiya Cikin Soyayya da kaunar Juna Daya baya son bacin Ran Daya musamman ma Habibu Da baya kaunar bacin ran maryama ko kukanta itama Haka Sai dai kuma Duk da wannan Kaunar Dake Tsakaninsu Bai Hana Maryama ta Girmama Habibu a mtsayinshi na yayanta Datake matukar Ji dashi.

Tana da Shekara 14 aduniya ta Sauke Qur"ani Akayi Walimar Saukarsu a makarantar allonsu Wanda Habibu yayi mata rawan Gani Sosai wajen Walimar Saukarta Wanda ya saka Maryama farinciki sosai Zuwa Lokacin kuma sai Manema Daga Ko"ina suka yi ma Maryama chaa Tunda alokacin Yara mata basa wuce Sa"anninta ake Aurar dasu Tunda ba karatun Boko suke yi ba.
Duk cikin manemanta Mutum Daya ta yarda Take kulawa Sule wanda yake Mutumin Maruka ne Shagon kayan Kwalliyan mata gareshi anan cikin kasuwar Ririwai,Maraya ne Mahaifinsa ya Rasu sai dai Yayyinsa Maza Suna Saune a Famiy House dinsu ne gidan Gado Shi da Mahaifiyarsu Da suke Kira Goggo Sule Shine karaminsu yana da Yayyi mata Da Maza Dukkansu su Biyar ne wajen Goggo Mata Biyu Maza uku.

Ganin Maryama Ta fi Son Sule yasa Baba Jibo da Mallam yahaya suka yi Bincike akansa kuma suka samesa da Nagarta Hallaye nan da nan suka bashi Izinin Turo mgabatansa Lokaci Habibu nada shekara 24 aduniya ya zama Matashin Saurayi,Cikin Lokaci Kadan Sule ya Turo mgabatansa aka Gudanar da Neman aure aka Saka Rana Har acikin Ran Habibu bai so Maryama Tayi Aure Nesa Dasu ba yaso Kusa da Gida Saboda ya Shaku da ita Zai ji ba Dadi in Tayi mai Nisa Sai Dai kuma bashi da tacewa ganin Maryama na kaunar Sulen kuma ya Tabbata in ya Furta Baya son ta aureshi Ko Maryama na Mutuwar son Sule ya Tabbata Saboda Farimcikinsa Zata Fasa Shi kuma Bazai so ya zama Sanadin Ruguza Farincikin Yar"uwansa ba kuma Tilon kanwarsa ba.

Haka akayi Auran Maryama aka kaita Maruka sun sha kukan Rabuwa ita da Habibu,Maryama Tayi kuka sosai Kuma Ta makale ma Habibun Sai da yaje dashi aka kaita Chan Maruka Gidan su Sule Inda zai zauna a Babban Gidansu Tun Wannan Zuwan Mahaifiyar Sule ta Fara yada mgana kan Wani Sabon Salo ne Za"a kawo amarya Harda Kato ana mata Bayani Yayanta ne, Bata ma Tsaya Saurara ba Domin Har acikinta Ranta Bataso Auran Sule da Maryama din ba an dai fi karfinta ne.

Tun da Maryama Ta auri Sule Take Cikin Mtsala Da goggonsa Mace ce mara Hakuri gata Fitinanniyar Bata kaunar Maryama Ko kadan kuma Sun Hada kai da matan ya"yanta yayyin Sule suna Muzguna mata Sai dai Tsiranta Daya Mijinta yana Matukar sonta Burinsa ya kyautata mata Saboda Habibu ya Jadaddamai ya Rike mai kanwarsa Amana Domin Duk Duniya ita kadai garesaa kuma baya son wani abu ya sameta bama Domin haka ba Yana Tsananin kaunar Maryama Tun baya Fahimtar Halin Dayake Ciki Har ya Fara Fahimta sai yaji ya kara Sonta Domin bata Taba gayamai Tana Fuskanta wata mtsala ba ballatana Kuma in taje ta gayamasu Inna Hasiya wani Abu Koda sun Tambayeta ya Zaman ta da Dangin Mijinta sai tace Komai Lafiya bata Taba Bude baki ta Fadi wata mgana Saboda bataso su Shiga Cikin Damuwa Saboda ita ba.

Habibu Shi ya Fara karantar Halin da Maryama ke Ciki..Domin Daman Duk Sati yana Hanyan zuwa Gidan Maryama Din Dauke da kayan kwalaman Dayake Siya mata na Tsaraba Duk Abunda yasan Tana so in ya samu kudi zai Adanasu baya Tsinana ma kansa komai sai Maryama,Tun yana zuwa yana Tambayanta me ke sakata Rama tana cewa bakomai Har dai Ranar yaje Gidan ya iske Goggo Ta tasata Tana Zaginta Maryama na Duke Tana kuka Ranar Duka Gidan sun ga Kalan Fushi da Bacin Ran Habibu Bai tsaya Jin ba"asi ba ganin Maryama na kuka yace ta Hado kayanta Su Tafi Gida Bata da yarda Zatayi Haka ta Hada Ta Bishi ita kanta Goggo sai Ta Raina kanta Daga baya.

Sai dai su Baba Jibo suka Gansu kwatsam,nan Habibu yake Maida musu abunda yafaru Inna Hasiya ta Fara Fada Tana Fadin bai kyauta ba Taya zai Dauko ta batare da Izinin mijinta ba Haka ta Dinga Fada Tana Nuna Bacin Ranta,Shi dai Habibu Bai ce komai ba Baba Jibo ma bai yi mgana ba Saboda Inna Hasiya ta Rigatayi mgana kuma Bayaso Habibun yayi wani Tunani Tunda Maryama kanwar sa ne ko suna da rai Shi mai Tsayawa kan mganar Maryama ne.

Adaran Sule ya zo Ririwai yana Rokon su Baba jibo suyi Hakuri su bashi Maryama su koma,Baba Jibo yace basu zai bama Hakuri ba Habibu zai bama Hakuri mgana na Hannunsa Dole ya Duka yana Rikon Habibu Shi kuma yace Zai Tafi da Maryama ammh Da Sharadin wlh ko kallon Banza aka kara mata ba Zagi ba sai ta bar Gidansa Ba Dole ba wai Basu sonta bane suka Aura mai ba kuma ba Jaka suka kai mai ya Dai ja mai kunni Daga karshe Sule yayi alkawarin Insha Haka bazata kara Faruwa ba,Cikin Girmamawa Sule ya Dauki Maryama suka koma Washegari kuma yayi Tsiya agidan ya kuma Tsoratar da Goggo Cewa in aka kara Takura ma Maryama Wlh zai Dauketa su bar garin Jin haka yasa ta koma Tayi Lambo Sanin Halinsa gashi kuma Auta ne tana Matukar Ji Dashi Bata son yayi mata Nisa.

Dalilin Faruwar haka yasa Maryama ta samu yanci Duk da Dai anayin ammh ba kamar baya ba Sai ta samu kwanciyar Hankali Ta maida Jikinta Har Aran Habibu yake jin Dadin ganin Maryama Cikin Farinciki Sai dai me Shekaran Maryama Biyu da Aure bata Taba ko batan wata ba Dalilin Daya saka Goggo Ta kara yunkurowa kenan Tana Fadin Maryama Juya ce bata Haihuwa,Tun abun baya Damun Maryama har ya Fara Damunta Itama Tana so ta Haihuwa ammh kana naka Allah na Nashi ne har ta kwarari Shekara Biyar Gidan Sule Bata Taba ko da Batan Wata ba zuwa Lokacin abubuwa sun Riga sun gama Rikicewa Goggo Ta Daka Tsalle tace sai Sule ya kara aure shi kuma yace bazai yi ba,Tun Maryam Din bata saka baki ba Har tazo ta Fara Rokon Sule Daya ji mganar Goggo ya kara Aure ko Zata samu Sassauci Daga Goronta mata da gorin Mutanen Gidan.

Daga bangaransu Baba Jibo basu da yarda zasu yi da Halin da Maryama ke ciki Sai dai suna Tayata addu"an Allah ya bata Haihuwa Tunda shi ne mai badawa Habibu kuwa Duka Salolinsa Maryama yake sakaawa Yana Rokon Allah ya bata Haihuwa sadaka kullum sai yayi Domin Farincikin Maryama Shine nashi Cikin wannan Halin Goggo ta matsa Sai da Sule ya kara aure da yar Aminyarta Zainabu kuma Ta tare nan kusa da Dakin Maryama din.

Auran Sule da Wata Biyar Habibu ya auri Hajara Diyar Mallam Yahaya wanda Hadin na Baba Jibo ne,Habibu yaro ne mai Biyayyah bai taba ma Iyayansa Gaddama ba Ballatana Hajara Data kasance yarinya mai kunya mai Hakuri alokacin Tana da Shekara 16 ne akayi musu auran Suka Tare nan Gidan Inda Baba Jibon da shi Habibun suka Gida Dakuna Biyu Dake Barayin Inda Habibun ke Zaune Ginin Jar kasa da mai yaben ganye aka Shafeshi da Farin Fentin Farar kasa na Mutanen kauye

Lokacin Maryama ta koma Maruka Bayan Tazo Bikin Yayanta Habibu ta iske Zainabu Nada Ciki Lokacin Gori da Habaice Habaice duk ya Tashi Sai Dai maryama ta koma Daki Tana kuka Domin Da Zarar ta Fito sunanta Juya Bata samun wani Jin Dadi sai Sule ya Dawo wanda Daman Goggo Tuntuni Take Fadin Ta asirceshi ne baya ji baya gani sai akanta.

Haka Zainabu ta Haifi yarta Mace Maryama na cikin Halin Tsagwama da Bakinciki Ko yar ma ba"a bataa ta Dauka ba,wai kada ta kasheta saboda bakincikinta Ranar tayi kuka kamar Ranta zai Fita sai dai Da Sule ya Dawo yaji Labari sai ya kara musu yace sunan yarsa Maryama aikuwa kan Haka sai da Goggo Ta mareshi Shi kuma yace bazai Sauya ba Maryaama Ta Riga ta sani Sule na Sonta kuma Har Abada bazai Taba Juya mata baya ba Shiyasa Koda Tana Cikin Damuwa da Zarar ya Dawo sai ta Kirkiro Fara"a da Annushuwa ta Dora saman Fuskarta aranta Bata Fatan Taga Damuwa akan Fuskar wadanda baza sukuni in suka ganta Cikin Damuwa Wato Yayanta Habibu da Megidanta Sule.

Daga Barayin Hajara ma Shuru ne ba wani Labari Su basu Damu ba Tunda sun yarda Allah ne bai bayarwa ammh Kuma Habibu Shima yana son Haihuwa Kodomin ya mallaka ma Maryama Abunda ya Haifa ta Daina kukan Rashin Haihuwa aduniya sai kuma Allah bai bashi Haihuwan da Wuri ba, ammh bai gaji ba yana gayama Allah akoda yaushe

Bayan Auransu Ba Dadewa Allah ya Dauki Ran Mallam Yahaya Hajarah Inno da Ayyah sai yayarta karime kadai suka Rage mata Sauran kaneenta yara ne itace Babbansu sai dai Bata da wani Damuwa Habibu dasu Baba Jibo sun kasance mata tamkar wasu garkuwa gareta Maryama kuma Ta kasance Kamar wata yayarta Shiyasa ma take kiranta Adda Maryama.

Kwantashi ba wuya awajen Allah har Zainabu ta kara Haihuwan Yarta Mace taci Sunan Goggo Mardiya,Maryama Shuru wanda ba Domin sule na kaunarta ba Tuni Goggo Da Zainabu sun yi Sanadiyar da Ta koma Gida Sai dai sun yi sun yi sun gaji Maryama ta Zame musu Ciwin ido basu yarda zasu yi da ita acikin wannan Halin ne Ciki ya Bulla Jikin Hajara Murna ba"a mgana Tun Daga Lokacin Maryama Take Shirin Tarban Abunda Hajara zata Haifa Cikin Kiwonta Ta Dauki Rago Daya ta wareshi na Sunan Abunda Hajara Zata Haifa Ko Habibu Baya Dawainiya da Hajara yadda Maryama take yi Ko bazata zo ba in Sule zai zo Zata aikosa da su Goriba aya da Sauransu aka wo ma Hajara Su Baba Jibo suna mamakin wannan kaunar Dake Tsakanin Maryama da Abunda ke Cikin Hajarah.

Haka Hajara Tayi ta Ronin Cikinta Da Taimakon Inna Asiya da Habibu Da Maryama Har Cikinta ya isa Haihuwa ta Haifi Mastur kamar yadda Maryama ta Zabamai suna da kanta Wanda Maryama bata iya Runtsswa ba Tun bayan da Habibu ya Kirata yace Hajara na kan gwiwa kuma Farinciki bai Saketa ba sanda ya kirata yace mata ta Sauka Ta gode ma Allah kuma Taji kaso mafi yawa Daga Damuwar Rashin Haihuwanta ya Ragu Tunda yau Taga Da"an Dan"uwanta Datake matukar so kuma Take ji Dashi.

Wannan kenan..!

*****

Haka Rayuwa ta Cigaba da Gungaruwa Cikin Koshin Lafiya da Tsarawan Ubangiji,Hajara na Cigaba da kulawa da Mastur haka ma su Inna Hasiya ba"a barsu abaya ba Balle sun samu Jika Lokacin da karfinsu ya Fara karewa
Bangaran Habibu ma ba"a barsa a baya ba ga Maryama wacce kusan kullum tana Hanyan zuwa ganin Mastur wanda yaron ya Shiga Ranta Kamar ta Daukesa Sai dai bata da yarda Zatayi Tunda bata da Nonon da Zata bashi,Abunda bata sani ba Habibu yayi ma kansa alkawarin Ko iya Mastur kadai zai Haifa zai mallakama Maryama Shi kuma ya Zauna Haka ya gwammace ya Cigaba da ganinta Cikin Farinciki Har Abada Daya ganta Cikin kunci Da Damuwa Shi kadai ya yanke ma kansa Hajara na yaye Mastur zai Damkama Maryama Shi Halas malak.




_Albishirunku Masoyana wannan karan na bude muku wani Shashi na musamman Saboda ku..Ina masu Bukatan Atalla musu Hajarsu Ko wani iri ne Domin samun costumer ta ko"ina..? Ku garzayo kakarku ta kusa yanke saka Zan Tallata muku Hajarku a Duka Shafukana Domin inganta Sana"arku da kuma Samun Cinikaya mai Tsabta da kuma kara Hada hada wajen Masi siye da Siyarwa mai Bukatar A tallata mata Hajjarta Zata iya min mgana kai Tsaye ta wannan Lambar Tawa 09069067488 domin karin Bayani...Sai kunzo Kunsan dai mai kasuwa Shi ke da Riba.._

*Domin zama Daya Daga cikin wadanda zasu karanta Labarin SADAUKARWAR SO..! Zaku Biya kudin karatunku kamar haka Masu amfani da Banki Zasu Tura â‚?300 ta wannan asusun banki 0552179550 Jamila umar gtb,Masu Katin waya kuma zasu Turo â‚?400, ta wannan lambar wayar 09069067488 Adauki Hoton katin sai aturo kai Tsaye mutanenmu na Niger kuma zasu Tuntubi wannan lambar kamar haka +22794775574 domin karin bayani,Insha Allahu mutum zai tsinci kansa a paid group ina maraba da ku masoyana Nagode*






*Janafty...*
1/1/22, 18:51 - Maryam Badmsi: *SADAUKARWAR SO..!!*
_(Labarin Yan"uwantaka,Soyayyah Tare da Sadaukarwa)_

*Wattpad:@Jamilaumar315*
*Mallakar:Jamilaumar(Janafty)*


*Page3�⃣*

Mastur nada wata goma sha takwas Hajara ta yayeshi a kuma lokacin ne Habibu ya bayyana ma Iyayansa da ita kanta Hajara Alkawarin Daya Dauka na Mallakama Maryama Mastur har Abada.

Dukkansu sun Nuna amincewarsu Hajara kuma Daman ita mai Biyayyah ce ga Lamarin Habibu sai dai Inna Hasiya Ta ce baza"a bama Maryama Mastur yanzu ba yayi kankanta abari yakai ko Shekara Biyar ne ammh ayanzu akwai Cutarwa Araba uwa da D'anta a irin wannan Lokacin Jin haka yasa Baba Jibo ya mara mata baya Dole Habibu ya yarda da Shawaransu sai sukayi Shuru da bakinsu basu Gayana maryama din ba.

Sai dai Tana jin an yaye Mastur Ta Shiryo tazo kan zata Tafi Dashi Chan Maruka ta yayeshi Habibu ko Hajara ba wanda yayi mata gaddama Suka Hada mata kayan Mastur suka Dankamata Daman ya saba da ita ganin itace yasa bai ma yi Rigima ba Duk da Tun yana jaririnsa bai da yawan Rigima da yawan kuka Maryama Taji Dadi Harda kuka Sulaiman yazo ya Dauketa suka koma Goggo Dataga Maryama Tazo da Mastur Sai da Tadinga mgangunu Tana Fadin Sai dai Taga ana Haihuwa ita kam Juya ce Harta Zainabu ta gama Raina Maryama sai dai Saboda Sule yasa bata tankasu Ta Cigaba da Sabgarta na kula da Mastur Datake Jinsa kamar Dan Da tahaifa acikin cikinta.

Mastur bai dawo gida ba sai da ya Shafe wajen wata Biyu a wajen Maryama kana ta Dawo Dashi Wanda kamar kada ta Dawo Dashi Saboda yadda suka saba Da juna Harta Sule sai da yaji kewa komai ita kemai Bata Gajiya Watarana Har Hawaye Sule yake mata a Boye yana Fatan Allah ya bama Maryama Haihuwa itama Taga kwanta Aduniya Lokacin Data Dawo da Mastur ba Domin mganarsu Inna Hasiya ba, da Tuni ya ce Maryama ta koma da Mastur Ya bata Shi ta Rikeshi sai bazai iya  ja da Abunda iyayansa suka ce ba, Shiyasa yayi Shuru da bakinsa ammh Tsausayin kanwarsa na nan Damkam aransa wanda Ko Barci baya Barinsa yanayi Cikakke.

Haka Rayuwa ta Cigaba da Tafiya da Dadi ba Dadi,Acikin Hakane Allah yayi ma Mahaifiyar Hajara Rasuwa Inno Sakamakon amai da gudawa Kafin Safe ta Cika Sosai Hajara da Habibu suka ji mutuwarta Inna Hasiya da ayya sunyi kuka sosai na Rashin Inno Baba Jibo Shi ya kasance kamar wani Shakiki Har akayi Sadakar bakwai aka waste Hajara ta koma Marainiya sai da Habibu bai barta ta kara kukan Maraici ba ya Tare mata Dukkan Gaban da Zataji yau Bata da iyaye.

Mastur Nada Shekara Hudu a Duniya Hajara ta kara Samun wani Cikin sai dai bai zauna ba Tayi Barinshi Haka Allah ya Tsara ammh Habibu yaji Ciwon Rasa Gudan Jininsa Sosai Fiye da Tunani Domin bai Dora ma kansa Kulafuncin Mastur ba Domin Maryama zai bama Shi Halak Malak.
Cikin Gudurin Allah Hajara ta kara samun wani Cikin Sai dai wannan karon Kusan Lokaci Daya Suka samu Ciki da Maryama Allahu akbar bawa Kada ya Cire rai da Rahamar Ubangiji..
Maryama Tayi kuka Kamar Zata Shide Saboda Murna Sule kam Kamar ya Zuba Ruwa akasa yasha Haka Habibu wanda ya bar Murnan Cikin Hajara ya koma Murnan Samuwar Gudan Jinin Maryamaa,Chan gidansu Sule kuwa Goggo da Zainabu kamar Bakinciki Zai kashesu Domin alokacin ma zainabu na Shayar da karamin Danta mai Suna Auwal Goggo Bata so Maryama ta Haihu ba Har Abada sai dai Kana naka ne Allah na nashi..Na Allah kuma Shine Daidai.

Sai kuma Tunda Maryama ta samu Cikin nan Lafiya yayi mata karanci Yau Lafiya Gobe Ciwo Cikin yana da Laulayi Sosai ta kwanta asibiti yafi Sau Uku Saboda Rashin karfin Jiki Bata samu Zaman lafiya ba sai da Cikinta yakai Wata 6 alokacin ne kuma Hajara Itama ta Sake Barin Cikinta wanda Tasha Wahala kamar bazatayi rai ba Saboda cikin ya zama Gudun Jini Dakyar ta Rayu Wanda Har su Habibu sun Fidda Rai da Hajara sai dai Rai mai alfarma sai gata tashi ammh fa an kashe kudi Tunda Har sai da aka Dangana da Asibitin General na Garin Doguwa,achan ne likitoci suke gaya musu Da wahala Hajara ta kara Haihuwa Saboda Mahaifiyarta Tana da Rauni ba Lalle bane in ta samu Ciki Ya zauna Har ta Haifeshi Saboda Raunin Mahaifan Dake Tare da ita wannan Labarin ya sanyayama su Inna Hasiya Jiki Suna ganin Tayaya Za"a Raba Hajara da Mastur alhalin kuma ba lalle bane ta kara Haihuwa sai dai jin Dadinsu Daya Cikin da Maryama ke Dauke Dashi Kila zai Tada wannan alkawarin da Habibu yayi Tsakaninsa da Ubangijinsa.

Lokacin da Hajara Taji Abunda Likitoci sukace bata Damu ba ta Fauwalama Allah Lamarinsa,Sai dai akasan Ranta Taji ba Dadi Ko bakomai Tana so Ta kara Haihuwa ko Saboda Habibu da Taga ya Damu Tun Lokacin Datayi barinta na Farko. ammh bata da yarda Zatayi Tunda Haka Allah ya Tasara mata Sai dai Tana yi ma Maryama Fatan Allah ya Sauketa Lafiya.

Tunda Maryama ta Shiga watan Haihuwanta sai Lafiya taki ta Kullum Cikin Ciwon kai da Jiri Ashe Tana da Hawan Jini iyayenta ko Habibu basu sani ba Daga ita sai Mijinta ganin Haka yasa Habibu yayi ma Sule mgana kan yana so Maryama ta Dawo gaban Inna Hasiya Saboda Ta samu mai kula da ita Tunda agidan sai dai Sule ya Taimaka mata ba dai Goggo Ko Zainabu Sule bai yi Gaddama ba ya Amince sai dai Goggo Taso Ta Hana Habibu bai tsayama Sauratanta ba Ya samu Tashar Mota sukaje har Gidan ya Dauko Maryama da Duka kayanta Dana Haihuwanta Data Tara Zuwa Gida sai dai su Inna Hasiya suka gansu kwatsam Hakika kuma Taji Dadi Domin Tana Tunanin yadda Maryama Zatayi Haihuwan Fari achan ba wani nata akusa Har Tana Tunani   Tayi ma Ayya mgana Taje Chan Maruka har Maryama din ta Haihu sai gashi ma Habibu ya gama mgana.

Nan Dakin Dake kusa da na su Habibu aka gyara ma Maryama Take Zaune Jiran Haihuwa kowa kula yake da ita ba Ba Baba jibo ba Inna Hasiya ba ba Ya Habibu ba ba Hajara ba Mastur kuwa murna ta kamashi Sai Tsalle yake Goggo Maryama ta Dawo Gidansu da Zama Tunda ta Dawo ya koma Dakinta da kwana ance yaro ma yasan mai Nuna masa kauna Shiyasa Tun yara yaronsa ya Shaida kaunar da Goggonsa kemasa.
Kullum Sule kafin ya Tafi Gida sai ya Biyo ya ga Maryama ya kawo mata tsire ko Nama bata ma wani ci Sai dai Mastur Da su Inna Hasiya Kwanan Maryama Goma agida Ranar Jumma"a da yammah ta Fara Naguda,Nagudan Data Dauketa Har Washegarin asabar bata Haihuwa ba,an kira anguwan zoman Gida sun kasa Kuma gashi ba wanda yasan Tana da Hawan Jini Habibu bai kwana agida ba agarin Doguwa ya kwana yaje siyar da Hatsi Daya Dawo ne yaga Halin Datake Ciki ya Fara Fada yana Ta ma Sule Fada tunda Tun da Maryama ta Fara Nagudan aka Kiraahi aka gayamai Inna Hasiya ne da Ayya keta Shiga da FitaHajara na waje Rumgume da Mastur Dake kuka ganin Halin da Maryama ke Ciki..

Habibu ko Hutawa bai yi ba ya je  ya samo Mota suje asibiti kafin ya Dawo Maryama ta Haifi Danta Namiji sai dai kuma me Tuni Jini ya yanke Mata Sai kuma ta Fara Jijjiga Tana Datse Bakinta da Harshenta Cikin Tashin Hamkali Ayyah ta Fito Tana kuka Da Neman Taimako Gabadayansu suka Shiga Dakin Har da Baba Jibo da Hajara da Mastur da Sule ganin Halin da Maryama ke Ciki yasa sule ya Duka da Jinin da komai ya Rumgumeta yana Kiran sunanta Inna Hasiya ita ta Dauki Jaririn Dake kuka ta yanke mai Cibi Ta nadeshi Cikin wani Zani Tana Tsaye Tana kallon Maryaman ta kakkafewa kawai sai ta Juya baya Tana Sharan kwallah Hajarama kuka Take Mastur kuwa Duk da yana karami ne ammh ya Fahimci wani abu mara kyau na Faruwa Baba Jibo ne ya karisa kusa da ita yana Tofa mata addu"a yana Kiran sunanta.

Habibu Dayaje ya samo Mota Da Gudu ya Shigo Gidan kamar zai Kifa sai dai yana Sawo kansa Dakin Mala"ikun Daukan rai suka Karisa Zare Ran Maryama Allahu akbar Kullu Nafsin Zaki"katul maut kowani Rai sai ya Dandani zafin mutuwa,Tun daga Bakin Kofar ya Tsaya Cak ganin Inna Hasiya na Hawaye Sule na kuka Baba Jibo na Sharan kwallah Hajara da Ayya na kuka Mastur ma haka sai yaji Kafafunsa sun Daina Daukansa Maryama ya kura ma Ido ganin ta Kwance Jikin Sule idanuwanta sun kafe sama bata Numfashi Tuni yaji wani Dum..! Dam..! Bai san ya akayi ba sai dai yaji Duhu ya mamayesa Lokacin Dayake neman karisawa ga gawar Maryama Yaji Salatin su Inna Hasiya Daganan bai kara sanin Inda kansa yake ba sai bayan Awa Daya da ya Farfado ya gansa kan Jikin Baba a tsakar Gida Ga Gida ya Cika da mata sai Koke koke akeyi sai komai ya Dawo mai Sabo Cikin Mutuwar Jiki da kunar Zuciya ya Mike Zaune yanabin Kowa da kallo kamar yadda suke masa kallon Tsausayi Idanuwansa ya Sauke kan Hajara Dake sanye da Hijabi Tayi kuka Har tabama uku Lada Mastur na Jikinta Shima Duk Hawaye sun Bushemai Gabansa ya kara wani Rugu Rugu bai Samu Zarafin mgana ba wani makocinsu ya shigo Dauke da Likafini da Turare da ganye magarya ya mikama Baba Jibo Batare da yayi mgana ba shi kuma ya Mike ya isa ga Kofar Dakin Maryama ya Kira Ayyah wacce ta Fito Tana goge kwallah ya Mikamata ya juyo Sai matan Dake waje suka Fara Fadin"Allah ya Jikan Maryama..! Allah yasa aljannah ce makota..Tayi Shahada ta Haihu Ko abunda ta Haifa bata gani ba Allah yayi mata Cikawa.."
.mganar haka ta Rika mai Amsa kuwa acikin kunnuwansa Yanzu Shikensn kanwarsa Maryama ta rasu..? Innalillahi wa'inna illaihirraju"un..Allah gareka muke kuma gareka zamu koma..Allah ya jikanki Maryama Allah ya sadaki da mala"ikun Rahma.
Yake yake ta Fada acikin ransa Mikewa yayi ya Fice matan suka Bisa da kallon Tsausayi.

Waje ya Fita yaga Mutane Dayawa a kofar gidan Duk sun yi Jigum Jigum Ga Sule agefe Shi da yayyinsa Yana ta Sharban kuka Suna bashi Hakura Habibu na Fitowa kowa ya Bisa da kallo ganin babu Hawaye ko Daya a idanuwansa Baba Jibo ya Nufa Dake Tsaye Cikin Sanyin Murya da wani Juriya yace"Baba ina gawan Maryama..?

Baba Jibo yace"Tana ciki iyayenka na shiryata.."Kai Habibu ya Kada kafin yace"Allah ya jikanta..Ina Abunda ta Haifa..? Baba jibo ya Dafa shi yana Fadin"Ameen Habibu kayi Hakuri kaji .? Abunda Ta Haifa Ayya tace Namiji ne ya na nan da Ransa.."Shi dai Habibu Gefe kawai ya koma ya Tsugunna yana Kiran sunan Allah acikin Ransa ya ma Nemi Hawaye ko Kuka ya rasa yana nan Tsugunne sai ga mata da yawa daga gidan su Sule Harda goggonsa da Matarsa Zainabu sukayi musu gaisuwa suka Shiga Gidan ba Dadewa Aka leko aka Kira Baba Jibo yana Shiga ba Dadewa yazo ya Kira Habibu da Sule yace suzo suyi ma gawa Sallama An gama gyarata.

Shidai Habibu Baba Jibo ke Jansa Har Zuwa gaban gawan maryama da aka Hadata Cikin Likkafani an sakata Cikin makara Shidai Habibu Durkusawa kawai yayi yana kallon Fuskar maryama da Sule ya saka Hannu ya yaye Zanin da"a Ka rufe ta da shi,Wani irin yake ji acikin Jikinsa kamar bashi da Lafiya yana jin kamar karya ne..? Maryama bata mutu ba Zata tashi Inna Hasiya Kasa Zama Tayi ta Fice Tana Sharan kwallah Sule ne ke ta ma Maryama addu"a yana Sharan kwallah Habibu kuma ko motsi ya kasa yi ganin Haka yasa Baba Jibo ya Dafa kafadarsa yana Fadin"Kayi Hakuri Habibu..Kayi mata addu"a Yanzu Maryama ba Shirunka Take Bukata Ba addu"an ka take Bukata.."Baba Jibo na mgana ya Runtse Cikin Kunar rai dana Zuciya ya Kura ma Fuskar Maryama Ido yana Fadin"Allah ya yi miki Rahma Maryama..Halinki na gari ya Biki..Allah ya karbi Shahadanki.."Daganan kawai ya Mike ya Fice Daga Dakin yana jin kamar Bashi ba kamar karyane Maryama nada Ranta Wata Duniya ce Ta Dabam yashigo Ko Daukan gawan ma Kasawa yayi Baba jibo da Sauran Mutane suka Shiga suka Fito da gawan yana jin kukan Mata Daga Cikin Gida Baba Jibo Shi ya ke rike da Hannunsa harzuwa cikin makabarta Daman Tuni an haka kabarin.

Habibu yana ganin Abun kamar a mafarki wai yau maryama ta bar gidan Duniya,Yana ji yana gani suka Sakata a kabarinta shi da Baba Jibo da Sule suka kuma maida kasa suka tula Tunda ya Durkusa gaban kabarin yana Mata addu"a yaji Hawaye sun Cikamai ido,ammh sun kasa Zubowa Saboda Juriya yana ta dai yi mata addu"a har Mutane suka watse bai sani ba Daga shi sai Baba Jibo Sule ma yan"uwansa sun jasa yana kuka.
Kafadansa Baba Jibo ya Tabo ya Mikamar Dashi yana Fadin"Tashi Muje Habibu...Maryama tatafi ta barmu..Sai dai muyi mata Fatan Allah ya karbi Bakuncinta.."Bai iya cema Baba Jibo komai ba ya wuce bayan ya kara waiwaya ya kalli Kabarin Wani Katako ya gani nan gefe kila na masu hakan kabari ne,ya Dauko Katakon Da Sauri ya Kafashi gaban Kabarin Maryama yana kara kallon Kabarin yana ji kamar Maryama bata mutu ba Tana Ciki Tana Kiran sunansa ganin haka yasa Baba Jibo ya Riko Hannunsa suka bar makabarta ya san yayi Rashin Ya ammh Habibu ne yayi Rashin Kanwarsa Masu Soyuwa garesa.

Har suka Dawo Gida nan waje suka yada Zango inda aka Shinfida Manyan Tabarmu ana karban gaisuwan Shidai Gashi nan ne yana zaune yayi Zuru Kamar wani gaula in ance ya Hakuri Habibu sai ya Daga kai yace Hakuri namu ne Duka.."Allah ya jikan Maryama Allah ya raya Abunda ta bari..Sai ya samu kansa da Saurin amsawa da Ameen yana jin wani Nauyi Daga saman Kirjinsa Baba Jibo na Lura Dashi bayason Rashin Fitar Hawayen nan Habibu yafi so yayi kuka ya Fitar da Abunda ke Ransa kada wata Cutar Zuciyar ta kamashi..

Acikin Gida kuwa Mata sai Koke koke suke Barin ma Hajara Tayi kuka Kamar Idanuwanta Zasu Daina gani Haka ma Mastur Duk da yana yaro ya Fahimci Tabbas Goggonsa Bata agidan nan yaga su Baba sun Fita da ita Inna Hasiya kuwa bata kuka sai dai Lokaci bayan Lokaci Tana Sharan kwallah Ayya ita ta wanke Jaririn nan tas aka Sakamai kaya kamar ya san maraicin Daya sameshi Tun Zuwansa Duniya bai yi kuka ba yana Hannun Hajara ta kamkameshi Tare da Maatur Tana kuka Dangin Sule suna Daga gefe Goggo Da Zainabu kamar ma Murna suke da Rasuwar Maryama da Bakincikin Abunda ta Haifa kafin Ta rasu suna dai Gefe suna kallon Kowa Daya bayan Daya bama wanda yabi takansu Zafin Mutuwar Maryama mai Radadi ce ga ahalinsu...

Haka akayi ta karban gaisuwan har Ranar uku..Ranar da Jaririn da Maryama ta bari ya kwana yana kuka Daman Daga Ruwa Sai Ruwa ake basa in ya fara kuka ganin haka yasa Habibu Daya zama wani Shuru Shuru ya Dauki Hajara da Jaririn Suka Tafi General Hospital na garin Doguwa aka Dubashi Bayan ya Shigar da bayanin Mahaifiyar shi Ta Rasu Lokscin Data Haifeshi likitan nata Fadan meyasa ba"a bashi madara akayi ta Bashi Ruwa yunwa ce ta kamashi kuma in son samu ne a samu wacce Zata Shayar Dashi Saboda ba lalle ne Madara ta Rikesa har ya Rayu ba Shi Nono Tamkar wani Sinadarin Jariri ne yana karaminsa da haka suka baro asibitin bayan Habibu ya kashe Sauran kudadensa Duka an Duba yaron Komai lafiya an Rubuta musu madaran da zasu Dinga bashi,Daganan gida ya maida su Hajara ya wuce kasuwa yaje ya siyo madaran ya kawo nan da nan Hajara ta Hada da Ruwan Zafi ta fara bashi sai gashi yasha da yawa Daganan sai barci Tsausayinsa da kaunarsa ya kamata Allah Sarki Yazo Duniya Lokacin da zai ji Dumin mahaifiyarsa mai Rabawa Tazo ta Rabasu.

Ranar da akayi bakwai da Rasuwar Maryama ranar Habibu yayi ma jariri Hakika kuma ya sanya mai Suna MANSUR.! Batare daya Jira Sule wanda sai dai yaji abun Daga sama Bai Damu ba Domin yasan Habibun Haushinsa Yake ji Tun bayan Daya gayamai Maryama nada Hawan Jini Tuni Ran Habibu ya baci yana ganin kamar Harda Sakacin Sulen ya Rasa Tilon kanwarsa Maryama.

Aranar kowa ya watse Gida ya Rage Daga Inna Hasiya sai Hajara da Baba Jibo da Habibu da Mastur sai Ayya Dake nan Tana Taimakama Hajara kula da Mansur Daman su goggo Tun Ranar uku suka koma Sule din ne ya zauna Har akayi bakwai Habibu bai samu Sararin kuka ba sai Ranar da aka watse chan kuryan Dakin Hajara ya shiga ya kwanta akan gado ya Fara kuka kuka mai Cike da Tsausayi da wani kewar na Rashin Maryama ba wanda ya Hanashi Domin kukan ne kadai zai saka ya samu Saukin Komai acikin Ransa.
Ya Dauki Mansur yana kallo ba inda ya Baro Maryama sai da ya kwaso Duhun Fuskar Babansa Tunda Maryama Fara ce kamar yadda Habibu yake Fari Tunda kakarsu wacce ta Haifi Inna Hasiya Mutuniyar Maiduguri ne irin Fararan Kanurin din nan ga kyau ga gashi Ita Inna Hasiya ta Dauko suma sai suka Dauko Farinta ta Duk da Shima Baba Jibon Yana Da Haskensa.

Habibu yaji Duk duniya Mansur ne kadai ya Rage mai wanda Zai kallah ya Tuna da Maryama Wacce Kullum yake kuka da Rashinta,Sai ya Dage Damtse Duk Gidan ba wanda yakai Shi kula da Mansur wanda ko Sule bai sami Damar mgana kan Mansur din ba ganin yadda Habibun ya Cika komai kuma Uwa Uba kwarjini garesa In ya Hade ran nan bamai iya ja Dashi.,Madaransa kuwa Duk Sati yake Hanyan Zuwa Siyowa Acikin Ransa kuma yana Wani Tunani Dole ya Nema ma Mansur wacce Zata Shayar Dashi ta zame mai Uwa.

Hatta Mastur Dake karami ji da Mansur yake haka zai zauna yayi ta kallonsa yana mai wasa Daukansa Kuwa in Hajara ta Hanashi kuka zai Tayi Dakyar yake yin Shuru Shi adole sai ya Daukesa kuma bazai iya ba Habibu ya yanke Shawaran Hajara Zata Shayar da Mansur kuma Daya Tuntube Hajara dasu Baba Jibo Tuni suka amince Domin Habibu yace bazai Taba Bama Sule Mansur ba ganin irin yadda Maryama ta Rayu agidansu baya Fata Mansur ma yayi irin wannan Rayuwar Dukkansu sun yi Na"am da wannan mganar ta Habibu.

Ranar da Maryama Tayi arba"in Ranar aka Raba komai Daga abunda Maryama ta bari na awakai ne na kiwonta Sai wasu yan kaya da aka Raba Sule ya samu nashi Sauran kuma na Mansur ne awajen ne Sule ya nuna yana son Karban Mansur wanda Goggo ce ta tada Bala"in sai ya karbosa Shi bashi da Ra"ayin Haka Tunda ya Rasa Maryama Yaji Duniyan Ta Juya mai Baya,nan take Habibu yace bazai Taba bashi Mansur ba Hajara Zata Shayar dashi Shi kuma zai zame mai Uba Har abada Mganar data kawo Hayaniya Yayyin Sule suka Shiga mganar kan sai sun karbi Mansur Shi kuma Habibu yace Wlh Ya Rantse bazai Taba basu Mansur ba Haka aka tashi Ranar Zuciyoyo ba Dadi Baba Jibo Shima wannan karon ya Goyi Bayan Habibu Domin bazai so ya Rasa Dan Maryama ba Akaro na Biyu ba kamar yadda ya Rasata ba Shi Sule yayi Shuru karfinsa akaci.

Wannan Dalilin yasa Goggo Mahaifiyarsa Sule tace suje su Rike Mansur ammh Gadon Mansur bazasu bada ba su Zasu Rike Habibu bai Damu ba Domin Basa gabansa Suka Tattara suka bar musu komai kayan Dakin Maryama ne kadai Ayya da Hajara suka je suka kwaso aka Saka Dakin Inna Hasiya Hajara kuma asibiti suka koma amtsayin wacce Zata Shayar da Mansur aka bata mgangunan da Zasu Kawo Ruwan Nono Tazo Gida Tana sha kuma Inna Hasiya na Hada mata da wasu gayyayyaki na gargajiya Cikin Sati Daya Nonuwa suka Shiga Taf Suka Fara Zuban Ruwa cikin Farimciki Hajara ta Fara Shayar da Mansur Wanda Daga ita Har Habibu Suke mai Son da basu son Meyasa ba ammh Suna Jinsa Aransu kamar Dansu Mastur Barin ma ita Dake Shayar Dashi..Wata kauna ce Daga Allah sai dai Mutuwar Maryama Har yau har Gobe ta saka barin Zukatansu barin ma Habibu Da koda yaushe sai yayi kukan Rashin Kanwarsa Dayafi so Fiye da kowa aduniya,Baya kwana Biyu bai Ziyarci kabarinta ba Har sai da Baba Jibo ya Dakatar dashi ganin Rashin Maryama din yana Neman Taba Habibun Sosai...!

Allah ya jikan Maryama da Rahma Allah yasa ta Huta..Allah ya karbi Shahadanta Ameen ya Allah..Tafiyar mai Nisan Zango ce yanzu muke kan Shimfida bamu isa Mafarin ba..


_Albishirunku Masoyana wannan karan na bude muku wani Shashi na musamman Saboda ku..Ina masu Bukatan Atalla musu Hajarsu Ko wani iri ne Domin samun costumer ta ko"ina..? Ku garzayo kakarku ta kusa yanke saka Zan Tallata muku Hajarku a Duka Shafukana Domin inganta Sana"arku da kuma Samun Cinikaya mai Tsabta da kuma kara Hada hada wajen Masi siye da Siyarwa mai Bukatar A tallata mata Hajjarta Zata iya min mgana kai Tsaye ta wannan Lambar Tawa 09069067488 domin karin Bayani...Sai kunzo Kunsan dai mai kasuwa Shi ke da Riba.._

*Domin zama Daya Daga cikin wadanda zasu karanta Labarin SADAUKARWAR SO..! Zaku Biya kudin karatunku kamar haka Masu amfani da Banki Zasu Tura â‚?300 ta wannan asusun banki 0552179550 Jamila umar gtb,Masu Katin waya kuma zasu Turo â‚?400, ta wannan lambar wayar 09069067488 Adauki Hoton katin sai aturo kai Tsaye mutanenmu na Niger kuma zasu Tuntubi wannan lambar kamar haka +22794775574 domin karin bayani,Insha Allahu mutum zai tsinci kansa a paid group ina maraba da ku masoyana Nagode*





*Shakira...*
1/1/22, 18:51 - Maryam Badmsi: *SADAUKARWAR SO..!!*
_(Labarin Yan"uwantaka,Soyayyah Tare da Sadaukarwa)_

*Wattpad:@Jamilaumar315*
*Mallakar:Jamilaumar(Janafty)*




*Page4�⃣*



*Bayan Shekaru Biyu..*

"Bayan Shekaru biyu da suka Gabata Da Rasuwar Maryama Da kuma Rikon Mansur Daya Dawo hannun Hajara.

Itace Madadin Uwa garesa Habibu kuma Uba ne garesa Mastur kuma ya kasance yaya garesa kuma Dan"uwansa Wanda yake Shekara ta bakwai Alokacin ya Fara girma an sakashi makarantan allo.

Girma da kuma Halin Rayuwa ya kara Kama Baba Jibo Ya Fadi a gona Sakamakon Jiri Daya kwasheshi  yasa yake gida bai da Lafiya ciwon baya sai dai yakan Fita zuwa masallaci dake kusa baya Doguwar Tafi sai al'amuran suka koma Hannun Habibu Bayan kula da gonakin Mahaifinsa sai ya Fara Kiwo anan Cikin Gidan kama Daga awakai da Shanaye kuma Allah ya saka ma Abun albarka Dayake Inna Hasiya Tana Tsaye da Kafafunta Tana kula da komai.

Mansur Tun yana da wata Goma sha Biyar aduniya ya fara Tafiyansa ba inda baya zuwa Tun yana karaminsa yake kama da Mahaifiyarsa Shiyasa Lokaci Bayan Lokaci In suka kalli Mansur suke Tunawa da Maryama Saboda ba inda ya barta Hajara da Habibu sun fi Nuna Kaunar Zahiri Ga Mansur Fiye da Mastur wanda bai Damu ba Dayake Tun yana yaronsa Miskili ne mara Hayaniya da son mgana Sai dai Yana Bala"in son D'an goggonsa wanda Hajara Ta Fadamai Tun Mansur na Jariri ta gayamai Yaron da Maryama ta Haifa kafin ta Rasu  Mansur kenan yaro, da rike abu ya rike komai acikinsa kansa Har yau har gobe bazai manta da Ranar da aka Fita da ita cikin wani Farin kyalle ba,Wanda Abun ya kasa bacemai acikin Kwakwalwarsa.

Tare suke Taruwa wajen kula da Mansur wanda Habibu kemai komai na Rayuwa Hajara kuma taci kashinsa Taci Fitsarinsa kuma Ta shayar dashi Shiyasa Take Jinsa ajikinta Kamar itace ta Haifesa,bangaran sule kuwa Koda yaushe yana Hanyan zuwa Ririwai ganin Mansur kuma ba laifi yana kawo Hidimansa a matsayinsa na uba da Farko har Habibu ya hana akarba sai Baba Jibo ya Dakatar Dashi yace Ya kyalesa ko bakomai Sule uba yake ga Mansur kuma Akwai Hakkinsa a Kansa Tunda yana Raye da wannan Dalilin Habibu yaja bakinsa ya Tsuke Ya zura ido Kawai Sai dai Bayan Sule Ba wanda ya kara Tako Kafarssa Daga Dangin Sule Harta kuwa da Goggo Mahaifiyarsa Suma basu wani Damu ba Shima kuma Sulen bai Taba Gigin cewa Zai Dauki Mansur ya Tafi Dashi Chan maruka ba Tunda yasan ba wani mai kaunar Abunda Maryama din ta bari,Duk da Mansur yaro ne ammh yawan zuwan Sule gidan yasa ya saba Dashi Sosai in ya gansa ya Fara Zillo kenan yana gaurancinsu na yara alamin yaga wanda ya sani ballatana Sulen baya zuwa Hannu Rabbana yan Minti da alawan yara yakan Riko musu shi da Mastur din wanda shi bai ma cika sha ba sai ya Tattara ma Mansur din shi da yake Sarkin Shan Zagi ne.

Haka Rayuwa ta Rika gangarawa Da Dadi ba Dadi Mansur nada Shekara Uku aduniya Wani Ifila"i da kaddaran Allah Daya baya wuce musulmi ya Fado musu Cikin Dare Gobara da ba"a san Daga Ina Take ba ko Daga ina ta Fara ba,Tatashi a Shashen su Inna Hasiya wanda Daga ita Har Baba Jibo sun kone aciki Koda aka Samu Nasaran Ceto su sun Riga sun Shaki Hayaki Sun Kone Daga wasu sassan na Jikinsu Allahu akbar Inna Hasiya da Baba Jibo sun amsa kiran Mahallacinsu alokaci Daya.

Wannan abunda ya Faru ya Girgiza Habibu Da Duka al"ummar Ririwai mutuwa Farar Daya kuma lokaci Daya,Hajara tayi kuka Mansur da Mastur su kansu sun san anyi Rashi Domin sun matukar sabawa da kakanin nasu barin ma Mastur Da ya fara Girma da wayau Habibu yasamu Jarabtan Mutuwan iyayansa alokaci Daya bai Nuna gazawa ba Yayi kukan Zucci ya Fauwala ma Allah komai ganin yana da Mata ga Ya"yansa Guda Biyu Daya kasance Shine garkuwansu Dole ya zama mai Juriya da kuma Jajircewa Domin inganta Rayuwar Mastur da Mansur.

Tun Rasuwar su Inna Hasiya garin Ririwai ya Fita kansa ya Fara Tunanin Sauya wata Rayuwar,Daman bayan Rasuwar su Inna Hasiya sai ya Dauko Ayya tana zama da Hajara Saboda ta Debe mata kewa Domin mutuwar ta Girgiza ta sosai Ta kasa Daina kukan Rashin su Inna gani take kamar kullum kwannan Duniya in ta Tashi Zata Iya Bude ido Ta gansu ta saka yardan ma kanta Cewa sun barsu acikin Duniyan su kuma sun Tafi Gidansu na gaskiya.

Batare da Habibu yayi Shawara da kowa ba ya Fara Shirinsa Gadonsa na Gonaki na wajen Baba Jibo da suka zama gadonsa Duk ya Hada ya Tattara ya Saida Tare da Duka Dabbobinsa Batare da yayi Shawara da kowa ba Shi kadai acikin Zuciyarsa ya yanke ma kansa Shawaran zai yi Nisa da garin kano Domin samun wani Waje da zai je ya gina wata Sabuwar Rayuwa Shi da Matarsa da ya"yansa Guda Biyu wadanda yake Fata da Muradin Da kuma Burin Inganta Rayuwarsu Ta zama wata aba mai ban Sha"awa anan gaba.

Su dai su Hajara sun ga dai an kwashe Dabobbi an Tafi Dasu kuma Habibu bai ce musu komai ba Ayya ce ma ta Tambaya Shine yace zai musu bayani Daga baya sai da yagama Hada Duka kudadensa Da Shawaran inda zasu koma kana ya samu Ayya da Hajara da mganar Sun yi kuka sosai na ganin Zasu bar Mahaifansu sai dai basu yi Gaddama da  Habibu ba Tabbas yaga Rashi da maraici yana Bukatar Nesa da garin Doguwa Gabadaya nan dai suka Bashi Goyon baya kuma nan take yace su Fara shiri suyi sallama da Makota Nan da Sati Daya zasu Koma ZARIA..!

Kuma ya sanar dasu bazai Saida wannan Gidan ba Ko Domin gaba Watarana zasu iya zuwa Ko bayan Ransa ko su Mansur bazasu Rasa wajen sauka ba Sai da zai saka wasu Amintattun da zasu kula da Gidan ba sai sun Biya ko asin su ba Ayyah Tayi Na"am sosai da wannan mganar Nan da kuma suka Fara shiri Bayan sun gayama Makota da yan"uwa da abokan Arziki cewa Zasu bar garin Doguwa Gabadaya dama Jahar kano Kowa yaji sai yaji bai ji Dadi ba sai dai Kowa yasan a irin wannan Rashin da Habibu ya Fuskata bazai Taba iya zaman garin ba Nisa da garin Kila zai sa ya Rumgumi Duka Kaddaransa.

Habibu Mijin Karimatu Yayar Hajara ya yi ma mganar su zo Gidan su sai su Zauna Tunda in da yake Zaune gidan gado ne awajen ba yalwa yana jin haka yafi Kowa Murna yadinga ma Habibu Godiya kamar zai kwantamai yace bakomai,Karima Tayi Bakinciki Rashin yar"uwata alokaci Daya da Ayyah sai dai in ma Tace Ayya ta zauna kada ta Bisu bata da karfin RiketaTana ji Tana gani Ranar wata Asabar Habibu ya samo Babbar Mota ya kwashe musu Dan Tarkacan kayan sawansu Basu Dauki Komai ba Bayan Haka Sule yana nan suka bar garin Doguwa Gabadaya Domin Habibun ya gayamai Zasu bar garin bashi da ta cewa Saboda yasan Ko Giyan wake yasha Habibu bazai bashi Rikon Mansur sai dai yaji Dadi dayayi mai alkawarin da Zarar sun isa suka samu Muhalli Zai Kirasa Da haka suka Rabu Suka kuma yi bankwana da garin Tare da Rakiyan yan"uwa da abokan Arzuka Mansur Nata Murna Sun Shiga Mota zasu yi Tafiya Mastur Dake da Wayau alokacin Sai Jikinsa yayi sanyi Jin Hajara ta gayamai Zasu bar garin Doguwa ne zuwa waje mai Nisa Shiyasa sai Jikinsa Duk yayi sanyi ya koma Gefe ya Rabe wani Lokaci yana Jin Sha"awar Mansur ganinsa yaro ne ba Ruwansa yayi ta Harkokinsa Sabanin Shi da sam Hayaniya ke Damunsa.

Habibu na gaban Motan da suke Ciki yana Sharan kwallah Na Kewa da kuma Alhiinin Yau zai bar Mahaifansa ba Inna Hasiya ba Baba Jibo ba Kuma maryama Allah Sarki Rayuwa kenan acikin Zuciyarsa yayi musu addu"an Allah yayi musu Rahma Gabadaya Daga Hajara Har Ayya sun yi shuru Jikinsu Duk yayi sanyi Mastur ma haka Mansur dai ke ta Burumtunsa Daga Jikin Hajara zuwa na Ayya ko na Mastur babu abunda yayi mai dadi..Yarinta mai Dadi.


*******

Sun sauka agarin Zaria Karamar Hukumar Dake kaduna garin gwammah ashe akwai wanda ke jiransu atasha da Waya da kwatance da Habibu ke yi suka yada Zango a kwangila Dake Zaria suka Hadu da wani Mutumin wani Fari gajere wanda bai wuce Sa"an Habibun ba suka gaisa dashi a Mutumce Kana ya Shiga Motar ya Dinga Nuna ma Direban Hanya sai gasu Cikin Hanwar Fulani Dake Wajen Kwangila anan Cikin garin Zaria.

Anguwa ce mai Cike da Gine Gine da zamani Daga Chan gefe kuma akwai Bukkan Fulani Yanzu ne da Gari ya Fara cika Gine gine ya fara yawaita Daga gani Sabuwar anguwa ce Domin wasu Gidajen yanzu ake ginasu ba"a gama ba Tuni Ayya da Hajara da Mastur suka Saki ido da baki suna bin Garin Zaria sa kallo suna mamakin Lalle kallo na Birni Sosai Sudai ana ta Tafiya suka ga an Tsaya kofar wani Dan Madaidaicin Gidan Bulo wanda yaji Shafen Filista da Fenti Mai Ruwan Kasa yayi kyau da Kofar gidan mai kyau nan suka tsaya Habibu yace su Fito kuma a sauke musu kayansu sudai sai bin Ko"ina da kallo suke gidan yana Tsakiyan Gine ginen manya manya ne na masu Kudi Hatta Jikin Gidan nasu wani katon Gida ne ake Ginawa ma"aikata sai kai da kawo suke.

Mutumin shi ya bama Habibu key din Gidan Daman gidan yana Bude ne, yace su Hajara su Shigo Yana Rike da Hannayensu Mansur Yara kuma Dake waje suka Taimaka musu da Shigowa da kayan suna Shiga suka ga Tsakar Gidan yasha Siminti Daga gani Sabon Gidane mai Dauke da Daakuna uku Reras abun mamaki Wata Mata ce ta Fito Tana Musu Maraba Ta karbi kayan Hannun yara Zuwa ciki Tana Faman yi musu sannu da Zuwa suka amsa suna kare ma Gidan kallo Harda Rijiya da makeyi nan Har Guda biyu Gidan dai yayi kyau sosai Ko"ina an Shafe shi da Fenti.

Har Dakin suka Bi matam katon Daki Ciki da Falo ne Dakin ba Komai sai katuwar Tabarman da aka Shimfida sai kololin abinci nan ta ce su Zauna suka zauna Tana ta yi musu Fara"a suna Binta da kallon Rashin Sani Ruwan Ta Fara basu wanda Ta mika musu mai Sanyi Cikin kwanon Sha,suka Sha sukayi Godiya Habibi suna waje sai da suka gama Zagaya Gidan kana suka Shigo Matar ta gaishe da Habibu Tana yi ma su Mastur wasa wanda Mansur ya tafi wajenta da Gudu Banda Mastur da bai sabo da Mutane.

Sai Lokacin Habibu yayi ma su Hajara Bayani sunan wannam Mutumin Usmanu Kuma wannan Da suka gani Matarsa ce Balaraba basu Taba Haihuwa ba suma baki ne Daga Rano Ta kano suka Dawo nan da zama saboda kasuwancin Sai da Hatsi da Usman din ya Fara sai ya Saida gidansa na chan yazo nan ya Siya gida ya Dawo Shi da Iyalansa Habibu yace yasan Usman a kasuwar Garin Doguwa ne in yaje saida Hatsi,Anan suka san juna suka kulla abota Duka Rashin da akayi Mishi ya zo mai gaisuwa Shi kadai ya gayama Burinsa na son barin Garin Doguwa Shi kuma ya bashi Shawaran ya saida Duka Gonakin sa ya kawo Kudi ya siya masa karamin Gida In suka Dawo Sauran kudin sai ya ja Jali ko irin Sana"arsa ya Fara Wanda yake Gudanar da ita akasuwar Zaria Dake Cikin Zaria City.

Ya gayamasu Shine bayan ya Saida Komai yazo suka Hadu ya bashi Kudaden shine ya Siyamai wannan gidan Sauran kudin kuma zai siya musu Kayan Zaman cikin Gida sauran kuma sai yaja Jali Daashi Mamaki ya kamasu jin wanman Gidan na Habibu ne Lalle Dayake Baba Jibo ya bar Manyan Gonaki Sosai shiyasa kudin sukayi auki Sosai nan Ayya Tayi ta ma Usman Godiya yace bakomai an zama Daya.

Nan suka Fita suka bar su da Balaraba Bayan ta saka musu Abincin Data yo Daga gida suka ci sukayi sallar suka zauna suna kara Hutawa Balaraba akwai baki sai Hira take musu Ayya ce mai Biye mata Hajara Shuru kawai tayi kewa na Damunta Tuni Mansur ya ware sai waasansa yake Mastur ne ke rakube ajikinta Shima ya kasa Sakin Jikinsa Balaraba Sai wajen yammah Tayi musu sallama ta koma Gida ta yi musu Tuwo ta kawo musu da Filo da Wata Tabarman sai Zanin gado suna ta yi mata Godiya su Dukkansu suka kwana anan Dakin Habibu kuma ya kwana Adayan Dakin bayan sun bashi Tarbama da Filo.

Washegari kuma Tun Safe Usman ya raka Habibu Kasuwa yayo musu Siyayyah,Ya siyo Kafita Babba Guda Daya sai Karama Guda Biyu Daya nasu Sauran kuma na Ayya da Su Mastur Tunda ya"ya Maza ne sai Ledan Daki da Tabarma da Filluka da Sauransu sai kayan girki da kayan abinci gabadaya abunda Zasu Bukata duk sai da ya Siyo musi Har sai da ma ya Shiga Cikin kudinsa Daya ijiye zai ja jari sai dai bai Damu ba Usman yace a Hankali sai ya Siya komai Ranar ma Balaraba ta basu abinci Domin sai yammah su Habibu suka Dawo da Kayayyaki Balaraba Ta taya su suka Jera komai Dayan Dakin aka sakama Ayya Katifarta da Katifarsu Mansur,da Ledan Daki Dayan Dakin kuma sai aka saka Kayan abinci da kayan Girki Tunda ba kowa Dakin Farko kuma nan ne Dakin Hajara nan aka saka babar Katifaan.

Sai Dare Usman da Balaraba suka Tafi Bayan tafiyarta Habibu ya Fita ya siyo musu Ruwan Zafi Da Buredi suka sha suka kwanta Da safe kuma suka Mike da aiki Hajara ta Fara Kokarin Sarrafa Girki Tun Safe Balaraba ta aiko mata Da icce da Murhu Tuni Ta Dora ta Dama musu Koko Tunda Har Kullin kamun sai da Balaraba ta aiko musu  Dashi Shiyasa Tsskaninsu sai dai Godiya Dayake basu da wani Nisa Sai dai Gidajensu ba"a jere suke ba Nasu na dagachan gefe ne ma"ana Suna kallon kallo.

Kafin a Rufe Sati Daya da Dawowarsu Zaria Tuni Usman ya Samar ma Habibu Gurbin Zama a kusa dashi a kasuwar Zaria inda yake saida Hatsi su Shinkafa,wake Masara, Dawa,da Sauransu kafin Habibun ya samu Shago,Sai ya Rabashi da Izinin Wakilan kasuwan Shima ya Saro Hatsin Ammh Shi Har dasu Barkonu da Su mangyada da Sauransu da yakinin Allah zai saka ma abun albarka Domin yana da Burin ya sakasu Mastur a makaranta Boko su samu ilimin Zamani,Saboda kudaden Hannunsa Duka sun kare Allah ne ma ya Rufamai asiri Komai ya Tafi kamar yadda yake Fata.

Allah yasa ma Fatan Habibu albarka bai Rufe shekara Daya da Fara sana"ar saida Hatsi ba komai ya Sauya Daga Rayuwarsu Allah yasa ma abun albarka komai na Bukatun Gida ya gama Siyan musu ya saka Mastur a makaranta Lokacin yana da Shekara 8 kenan aduniya firamari 1 aka sakashi ganin yayi girma wata makarantan Fimarin gwannati ce,Ya kuma Siya yar kekensa Dayake Zuwa kasuwa da ita akai yake Daukan Mastur yana Kaisa makaranta in zai wuce kasuwa,In kuma an tashi Mastur din ya Dawo da kansa Wanda sai da aka sha Daga da Mansur ya hakura da yace shima sai an sakashi Kuma Habibu yace sai ya cika Shekara Biyar zai sakasa Boko ammh Islamiyar da aka saka Mastur An saka Mansur din suna zuwa Tare,Zumunci Tsakaninsu da Balaraba da Usman Sai abunda yayi gaba sun Rike juna kamar yan"uwa.

Zuwa Lokacin Sule yasan Mazauninsu Domin yazo wajen sau Biyu ma,yana ganin Mansur Daya koma yana bama Goggo Labarin Cigaban da Habibu ya samu sai ta gwalesa Domin bata kaunar sake jin Sunan wani ahalin Maryama,jin haka yasa ya Yi shuru da bakinsa Ammah acikin Ransa yasan Son Dayake ma Mansur acikin ya"yansa Dabam ne.


****

*BAYAN SHEKARA BIYAR..*


"A zuwan wannan Lokaci Komai na Rayuwarsu ya gama Daidaita ba Dai  za'a kirasu masu kudi ba ammh Suna da Rufin asiri Tunda Yanzu haka Habibu ya mallaki Shagon kansa Na Hatsi a kasuwar Zaria Yafi ma Usmanu Habakan arziki da Costumer,daman haka Allah yake al"amarinsa.

Tuni an saka Mansur makaranta Inda yake da Shekara 9 a duniya Mastur kuma yana da Shekara 13 aduniya ne yaana aji Shida a primary ayayin da Mansur na primary 3 alokacin Suna zuwa Islamiya da yammah asabar da Lahadi kuma suna zuwa Hadda Na Safe Basu da kowa sai su Balaraba wacce suke kira da Inna Balaraba Hajara kuma Mansur ke kiranta da Hajja Tun yana yaro sai sunan ya Bita Harta da Mastur shima Hajja yake Kiranta Habibu kuma Daya Zama Magidanci yanzu Baba suke Kiransa Zuwa Lokacin Sule na yawan zuwa yana Duba Mansur ganin haka yasa Habibu ya gayamai Shine Mahaifinsa Saboda ya Girma Koda watarana Bashi da Rai yace bai san wannan ba Hatta da Suna a makaranta ma Mansur Sulaiman Doguwa yake amfani Dashi Sabanin Mastur Dayake amfani da Mastur Habib Doguwa Tun alokacin Akwai yarinta atare da Mansur so bai wani Damu ba ya Shiga Sabgarsa.

Tun alokacin Hallayarsu Ta Fara Bambamta Tun suna da kankanin Shekaru Mastur Miskilin Mutun ne wanda mgana bata Damunsa Shi dai barsa da karatu ina zaka Karatu ina ka Fito karatu bashi da yalwar Fara"a Ballatana Sakin Jiki da wanda bai sani ba yana da wuyar sabo da kuma Wuyar Mu"amala,Sabanin Mansur Dayake Tun yana karaminsa mai Fara"A mai Surutu mai yawan waasa da Sakin Jiki da Mutame Shiyasa Mastur yake mai Fada in kaga Mansur na Tura baki Mastur ne ya Tasa shi gaba sai yayi Karatu Shi yafi maida Hankalinsa  kan wasa Fiye da Karatu,Ko a makaranta Haka yake da wasa kamar me baya maida Hankali In Mastur yayi mgana Hajja tace yarinta ke Damun Mansur zai bari saboda bata son ana Takuramai Habibu kuwa kullum sai yayi ma Mansur Fadan ya Tsaya yayi karatu ya natsu Tamkar yayansa ammh Ina akace Hallita wani abu ne Wasa da Rashin maida hankali ga Abu ajinin Mansur yake sabanin Mastur da sai ya wuni bai yi mgana ba Shi dai karatu Domin yana da Burin Yayi ilimi mai Zurfi Domin Cika Burinsa na ganinsa Sanye da Kakin D'AN SANDA..!



*Wannan kenan..*



_Albishirunku Masoyana wannan karan na bude muku wani Shashi na musamman Saboda ku..Ina masu Bukatan Atalla musu Hajarsu Ko wani iri ne Domin samun costumer ta ko"ina..? Ku garzayo kakarku ta kusa yanke saka Zan Tallata muku Hajarku a Duka Shafukana Domin inganta Sana"arku da kuma Samun Cinikaya mai Tsabta da kuma kara Hada hada wajen Masi siye da Siyarwa mai Bukatar A tallata mata Hajjarta Zata iya min mgana kai Tsaye ta wannan Lambar Tawa 09069067488 domin karin Bayani...Sai kunzo Kunsan dai mai kasuwa Shi ke da Riba.._

*Domin zama Daya Daga cikin wadanda zasu karanta Labarin SADAUKARWAR SO..! Zaku Biya kudin karatunku kamar haka Masu amfani da Banki Zasu Tura â‚?300 ta wannan asusun banki 0552179550 Jamila umar gtb,Masu Katin waya kuma zasu Turo â‚?400, ta wannan lambar wayar 09069067488 Adauki Hoton katin sai aturo kai Tsaye mutanenmu na Niger kuma zasu Tuntubi wannan lambar kamar haka +22794775574 domin karin bayani,Insha Allahu mutum zai tsinci kansa a paid group ina maraba da ku masoyana Nagode*




*Janafty...
1/1/22, 18:51 - Maryam Badmsi: *SADAUKARWAR SO..!!*
_(Labarin Yan"uwantaka,Soyayyah Tare da Sadaukarwa)_

*Wattpad:@Jamilaumar315*
*Mallakar:Jamilaumar(Janafty)*


*Page5�⃣*


*MAFARI..*
*Kaduna State..Zaria*
_Area:Hanwanfulani_

"Dare ne Domin Duhu ya Shiga Misalin 8:30pm na Dare ne Tunda har anyi Sallar Isha"i kafa ya fara Daukewa Daga anguwa sai dai akwai Wutan lantarki Duhun bai yi yawa ba Tunda Haske kwaya kwayan Gidajen Jama"a ya Haske anguwan.

Suna Zaune a Tsakar gidan kan Katuwar Tabarman da Hajja take Shimfida musu bayan sun yi sallar Isha"i in sun gama cin Abinci sai Mastur ya Tasa Mansur gaba yana Karamai karatu inda bai gane ba Daga na Bokon har na Arabiyan.

Yau ma Hakan ce ta kasance Dukkansu suna kan Tabarman Bayan sun gama cin tuwo Miyar Kukan da Hajja tayi musu,Hajja ta kwashe kwanukan zuwa karamin Kitchen din da aka Gina mata a nan Tsakar gidan Tunda Dakin karshe Habibu ya gyarama su Mansur Na Tsakiyan kuma nan Ayya ke ciki   Dayake Duka Ciki Daya Daya ne Na Hajja ne kadai mai Dauke da Ciki Biyu.

Ayya da Hajja na gefe suna Hira Sama sama Mansur kuma na Zaune Daga gefe yana Dukufa yana Karatu Mastur na zaune gefensa yana kallonsa Shima Wani Littafin ne a Hannunsa na Koyin Turanci yana Dubawa ammh Rabin Hankalinsa na kan kanin nashi ganin Lokaci Bayan Lokaci yana Karatu ne yana wasa Saboda Akwai Hasken kwan Latarki a Tsakar Gida Shiyasa Mansur ya Shiga Taitayinsa Domin yasan In yayan nashi ya kamashi yana Wasa Ransa sai ya baci.

Tundaga waje sukaji Karar Mashin din Baban nasu Mansur Dake karatu ya Dago kansa da Sauri Lokaci Daya yana Mikewa Yana Fadin"Baba..Oyoyo Baba.."Mastur Dake Zaune ya Daga kai yana kallonsa kafin ma ya samu Zarafin mgana Mansur din yayi wuf ya Fita waje da Gudu Da kallo ya Bisa kafin ya Kada kai kawai ya maida Hankalinsa kan Littafin Dake Hannunsa na Teach ur Self.

Ayya ce ta Tabe baki Tana Fadin"Bansan yaushe yaron nan zai Daina wasa ba.."Hajja na kokarim Tashi Tsaye Tace"Ayya zai Daina yarinta ne.."Ayya tace"Ko yaushe haka kike Fadi Hajara ammh Mansur ai wasa yana cikin kansa ne..Shi ko Koyi baya yi da Dan"uwansa Megidana Mastur.."Hajja tana Dariya tace"Ai ba Hallitansu Daya ba Ayyah..Shi wannan Mijin naki ai Miskiline kafi mahaukaci ban Haushi.."

Ayya Tace"Yafi...Da wannan yaron naku mai son wasan Tsiya.."Hajja dai Dariya take yi Daidai Lokacin da Habibu Daya zama Mallam Habibu Uba ga Mansur da Mastur ya Shigo yana Gunguro mashin Dinsa karfe Karfe Mansur na Biye Dashi a baya Dauke da wata Bakar Leda Sai Washe baki yake kamar Gonar auduga Dayake Likafa Taci gaba Habibu ya bar ma Mastur kekensa yana Goya Mansur suna zuwa makaranta ya Siya Mashin.

Sallama yayi su Ayya suka amsa suna mai sannu da Zuwa ya amsa Cikin Fara"arsa Kusa da Madafin ya jingina Mashin Din Kafin ya Kariso kan Tabarma Lokaci Daya yana Cire Takalmin kafarsa Mansur na Biye Dashi kamar Jela ya zauna Bayan ya Kira Sunan Allah Ayya ya kara gaidawa yana mata sannu da gida Ita kuma tana Tambayansa ya kasuwa Hajja Data Fito Daga Daki da kwanukan abinci ta Ijiye gabansa Tana mai Sannu da Zuwa ya amsa yana Tambayanta ya Gidan sai Lokacin Mastur ya Dago kansa Daga Karatun Dayake ya kalli Baban nasu yana Fadin"Sannu da Zuwa Baba.."

Ya Kallesa yana Sakin Mirmishi kafin yace"Yauwa..Babban Mutum ana ta Karatu ne..? Kai kawai ya gyadamai Batare da yayi mgana ba Bai damu ba sanin Halinsa sai kawai yace"Masha Allah..Abada Himma Allah ya Taimaka ya baku Ilimi mai albarka.."Gabadayansu suka amsa da Ameen banda Mansur Dake ta kokarin Fito da Abunda ke Cikin Ledan da Baba ya shigo Dashi Mastur ne ya Lura Dashi Nan da nan ya Dakamai Tsawa Cikin Muryansa kamar ta Babba yace"Bana ce maka ka Daina Taba abunda ba"a baka ba Mansur..? Kai aka kawo mawa..? Bazaka ba Hajja ba Shine zaka zauna kana Budewa kabar Karatunka ka tafi kana wasan ka ko..?

Turo Baki Mansur yayi ya Ijiye Ledan yana Fadin"kayi hakuri ya Mastur bazan kara ba.."Jin yace haka yasa yace"Taso kazo nan..Ka cigaba da Karatun ka.."Ba Musu Mansur ya Mike ya koma gaban Mastur ya Dauki Littafinsa ammh fa Duk Fara"an Dake Fuskar Mansur ta Goshe Saboda ance yazo yayi Karatu Ayya ta kada kai tana Dariya tace"Dakyau..an Hada Mansur da makiyinsa Karatu Dole ya bata rai.."Waigowa yayi yana Bata rai yace"Hajja kinga Ayya ko..?

Hajja Tana Zubama Baba Ruwa yana wanke Hannu Take Fadin"Kyaleta Yi Karatunka Dan albarka na Insha Allahu sai ka Zama gwamna.."Ba Ayya ba Hatta Mastur sai da ya Murmusa bai ce komai ba Baba Daya Ke Dage Hannun Rigansa Zai Fara Cin Abinci yake Fadin"To Ameen Maman Mansur.."Yafada yana yar Dariya Ayya na Tayasa Mansur kuwa Sai Dariya Jin ance zai zama gwamna Mastur na kallonsa bai ce mai komai ba Sai Da ya Dago suka Hada ido kana Yayi Saurin Daukan Littafin Kada kai Mastur yayi yana Fadin"Ba"a zama gwamna ba Ilimi Mansur..Kayi karatu Sosai ka Daina wasa kanina Watarana sai Labari.."Yafada Cikin Sanyin Murya Mansur ya gyada kai yana Fadin"Zan yi Ya Mastur..Zanyi karatu na zama kamar kai Har na zama gwamna.."Ayya Dake jinsu Tace"Dakyau Kaga Daga ranar sai na koma ina Auran Dakai na Zama matar gwamna.."

Baki ya Tura yana Fadin"Lalle wazai aureki..? Sai dai kiyi ma gwamna aiki.."Zuwa yanzu Har Baba Dariya yake Mastur ne ya Murdemai kunni yana Fadin"Kada na kara Jin bakin ka anan wajen.."Da Sauri yace'Angama Yaya.."

Baba Dake cin Tuwonsa Farinciki Duk ya Cikasa yana kallon ya"yansa abun alfaharinsa Har ya gama cin Abincin ya Dauki Butan Dake gefensa ya wanke Hannu yana Fadin"Hajara Dauki Ledan nan Tsire ne aciki ki Raba muku.."Tunda ya ambaci Tsire Mansur ya washe baki Yana Ji kamar ya tashi ya gansa gaban ledan Ammh Sanin Halin Mastur yasa ya maida Zalamarsa Ammh dai Hankalinsa Rabi na kan karatun Rabi na kan Su Hajja Data Kwashe kwanukan zuwa Madafi kana ta Dawo ta Dauki Ledan ta Fito da Tsiren sai Taga Ledan Biskit guda Biyu Ta Dago Tana Fadim"Baban Mansur wannan Biskit din fa Dake Ciki..?

Yana Shan Ruwa ne Take mganar bai bata amsa ba sai da yagama kana yace mata"Daya na Mansur ne Daya na Babban Mutum Yaron Maryama."Daman hakan yake Kiran Mastur wani Lokacin ai Tunkafin Tayi mgana Mansur yace"Hajja bani nawa.."Dariya Tayi ta Mikamai Tana Fadin"Gashi Yaron Hajja..Mastur ga naka.."Kai ya Girgiza mata yana Fadin"ki ijiye ma Mansur Da safe in Zamu Tafi makaranta yaje Dashi.."Baki Mansur ya washe ya Mike yana Tsalle ya Rumgume Mastur yana Fadin"Nagode Yaya.."Ayya da Hajja sai Dariya suke mai Mirmishi kadai yayi mai ya Mike Dauke da littafinsa yana Fadin"Nasan ba karatun zaka karisa ba..Ka shigo ciki mu kwanta da Wuri saboda makaranta Gobe.."Mansur Dake Murnan Biskit dinsa kai kawai ya Dagamai Mastur bai bi ta kansa ba yayi ma su Baba Sai da Safe suka Rakashi da Allah ya Tashemu Lafiya ya Shiga ciki ya Cigaba da Karatunsa Domin Hayaniya ce Baya so Gashi Mansur kuma Hayaniya da Mgana Tamkar ajininsa suke shiyasa ya Gudo Ciki ,nan ma ba wai ya Daina Ji ba sai dai ba kamar yana Tsakar Gidan ba.

Bayan Shigarsa Mansur Cin Biskit Dinsa ya hau yi yana Wasansa da Tsirensa da Hajja ta Raba Ta bashi nashi Ta Diban ma Aiya nata Sai na Mastur Data ijiye mai Da safe,Baba Damsn bazai ci ba nasu ne ya siyo musu,Sai ita Hajja Data Diba nata Tana ci su kuma su Baba suna ta Hira da Ayyai itama Tana cin nata Tsiran suna Hiran yadda anguwan ta Cika Sosai ba kamar Dawowarsu ba,Baba yace"Ai anguwan ta cika Fiye da Zaton ki ayya..Kinga Duk Yawancin Gina ginan da muka samu anayi duk an tare..Bayan Chan gabanmu ma ana ta Saida Filaye ana gini.."Hajja tace"Sosai Nima na gani Dazu da muka je Barka Gidan Maman Anas nida Balaraba Naga ma wannan Katon Gidan Dake Jikin namu Ana ta kawo kaya acikin Kwalaye ma"aikata nata Shiga Dasu Ciki.."

Baba yace"Eh Nima yanzu da muka Fito Masallaci da Usmanu yake Fadamin Megidan zasu Tare Cikin Satinan Dayake anan Anguwan mukayi sallar Isha"i Bayan mun taso Daga kasuwa.."Ayya tace"Dankari wai ni wannan katon Gidan Benen nan na waye ne Habibu..?

Tafada Tana Daga kai tana kare ma Gidan kallo Domin yana kusa Dasu suna ganinsa Dayake Ginin Harda Bene Kerarran Gida ne kamar a kasar Turai san da suka Dawo garin ake Gina Gidan sai kwananan aka gamashi kai Dagaji kasan an kashe Dukiya.

Baba yace"Wlh Aiya ban sani ba Naji dai Usman na Fadin Gidan Mai Kamfanin Saida Motocin nan ne na Bakin Titi..TURETA AND SONS MOTORS LIMITED.."

Aiya ta Zaro ido Tana Fadin"Badai Dankakaren wajen Saida Motocin nan Dake Bakin Titi ba wanda ke Hajara kika Nuna min kwanaki da Zamu asibiti gaida Balaraba sanda tayi Barin din nan.."Hajja Tace"Ina ga nan ne Aiya.."Baba yace"Nan fa To shine megidan Ance Dan Sokoto ne a karamar Hukumar Tureta Dake Sokoto,Yana da kudi sosai yana Saida Motoci ne ance ya Fara zama asokoto ya Dawo kaduna Shi da Iyalansa toh bayan ya Gina wannan wajen saida Motocin ne yanzu yayi gina kusa da wajen yana so su Dawo nan gabadaya da Zama shi da Iyalansa..kuma abun Farincikin ma Masallacin nan Dake Jikin Gidansa da aka Ginashi muna cewa ko Gwannati ne an ce Duka nashi ne.."Aiya Ta gyada kai Tana Fadin"Allah sarki..Abun Duniya baya Boyuwa Duk a ina ka samu wannan Labarin Habibu.."Bashi kadai ba Hatta Hajja sai da tayi Dariya kai ya Girgiza sanin Halin Aiya da Tambayan Kaka uwarka ta kawo ka Duniya yace"Nima Dazu nake ji Da muka Fito masallacin Usman da Baban Anas makocinsa naji suna Hirar kinji inda naji Labarin.."

Aiya Tace"Au..Koda naji..Allah yasa to makotan arziki ne..Kuma Allah yasa kada bayan sun Tare acikin Gidanan Benen nan In yaji Mutane ya Fado mana acikin Agidan ba.."Baba na Dariya Hajja na Tayashi Kafin su Tsaigata Aiya Taji Haushi tace"Ai toh..Gani nayi abun asama haka.."Baba yace"Bazai Taba Fadowa ba Aiya ki kwantar da Hankalinki.."Mikewa Tayi Tana Fadin"Ai Shikenan..Kunga sai da Safenku..Ke Hajara ga Da'nki nan Shi bai yi Karatun ba ya gama cin Biskit yayi barci.."Daga haka ta Shiga Dakinta Baba ya Bita da addu"an Allah ya Tashe su lafiya.

Suma nan Hiran ya Tashi Hajja ta Dauki Mansur ta kai shi Dakinsu ta samu Har Mastur ya gama Karatunsa yayi Barci ta kwantar da Mansur nan gefensa ta Tofa musu addu"an barci kana ta gyara musu Labule bayan Ta kashe musu Hasken Dakin Ba Sauro Dayake tun Gabatowar mangariba ta saka Mastur ya yayyafa Fiya Fiya acikin Duka Dakunan.

Baba ya Shiga Daki Hajja ta Nannade Tabarman ta Shiga Dashi Dakin da Aiya ke kwanciya ta ijiye ta Sameta Tana Shirin kwamciya ta mata sai da Safe ta Fito Daman Kofar Gidan Tun Shigowarsa ya saka ma Gidan Sakata bata Shiga Ciki ba sai da ta gama Duka kaye kayenta a tsakar gida kana tayi alwala ta Shiga.

Baba har ya kwanta Saboda gajiya itama sai ta Shimfida sallaya ta tada salla Shafa"i da Wututri Tayi kana tazo Tayi Shirin kwanciya Sai alokacin Nepa suka Dauke Wuta sai ta kunna Fitila   kadan Saboda bata son Duhu sosai itama Tazo ta kwanta bayan tayi addu"an Barci Tana kallon Habibu Dake jan Minshari Mirmishi Tayi Domin tasan ya gaji Zaninta ta yafamai Daga kafa Zuwa Cikinsa kafin ta kwanta abayansa Tana Sauke Numfaahi Itama nan da nam Barci ya kwasheta.

Washegari kuma ta kama Talata ne Tun Safe tatashi Tayi abunda ya kamata na abunda karyawansu Mastur shi ke Sharan Tsakar gidansu ya kuma Cika mata Botikanta da Ruwa kana yaje yayi wanka yazo ya Tada Mansur yamai wanka Suyi Shirin makarata Tare suke karyawan kana Mastur ya Fito Da Kekensa ya Goya Mansur Zuwa makaranta Iyayansu na Binsu da Allah ya Kiyaye sai sun Fita kana Habibu keyin wanka Shima ya Fita Bakin Sana"Arsa abar Hajja da Aiya acikin Gida suna Debema Juna kewa Duk da Hajja bata barin Aiya Tayi aiki ammh ita bata san Zaman hakanan tana kama mata wasu ayyukan da bazu Gagareta ba.

Bayan Sati da yin wannan mganar Tsakanin Baba da Aiya Da yammah wasu manyan Motoci Tsala Tsala wajen Biyar ta Shiga Gidan Dake kusa dasu,Daga alamun dai masu gidanan ne suka Tare Tunda Sai shiga ake ana Fita,Baba ya Shigo da goro da Minti Bayan ya Dawo yace a Masallaci aka Raba Alhajin Da kansa yazo Salla masallacin ya kuma bada Kwalayen Sweet din aka Raba musu yana gayyatan Kowa da kowa zuwa wajen Walimar Tarewarsa da kuma Taya Yarsa Kwara Daya Da ta cika Shekara 5 aduniya uwa uba da kuma Addu"an Bude Sabon masallacin Daya Gina.

Baba na basu Hajja Labari yana Fadin"Aiya baki ga Alhajin ba wlh..Mai Mutumci da Fara"a sai gaisawa yake da Mutane har dani nan mun gaisa Dashi.."Aiya ta kada kai Tana Fadin"Masha Allah..Allah yasa Makota na gari ne.."Baba yace"Ameen..Ai Usman ke Fadamai Nine ke Zaune Kusa Da Gidansa yace Allah Sarki muka kara gaisawa yana Tambayana Iyalai.."

Hajja Tace"Ilkon Allah..Dama wasu masu kudin ance ba Ruwansu.."Baba ya kada kai yana Fadin"Ai Kowa da irin Tasa Zuciyar Hajara Kudi wawayen Abu ne suna Jefa Mutum ga Halaka.."Aiya tace"Allah ya karemu.."Daganan suka Cigaba Da Hiransu.

Washegari kamar yadda Aka Raba Sweet aka tashi Da Shagalin Walima Abinci kala da kala da ababen Sha Mutane Dadama yan anguwa sun Shiga Mata da Maza ammh Hajja bata Leka ba Ballatana Aiya Domin Har Baba ya Fita bai ce mata komai ba Shiyasa da Balaraba ta Biyo su Tafi tace taje kawai itace ma Tazo da abinci a Takeway da Lemuka Da Naman Kaza,Tana basu Labarin Irin Daular Dake Gidan Tana Fadin abinci gayinan Sai wanda ka Zaba Lemuka da Naman kaji kuwa kamar Banza ita bata ma gane Matar gidan ba Taga dai Manyan Mata da yawa sai dai Taga yarinyar da akayi ma Murna Cika Shekara Biyar Karamar yarinya ce Fara wacce Taci gayu da kayan Alfarma Balaraba na Labari Tana Jin Dadi Da Zata tafi tace Hajja ta Dibi Naman kaza Tace A"a sai tace ta Diban ma su Mansur jin haka yasa ta Diba ganin da yawa Cikin wata Roba mai Murfi Ta Diba Harda Aiya Saboda Tana ciki Tana Barci ne Su kuma su Mansur sun Tafi Islamiya.

Sai da Habibu ya Dawo Hajja ke Fadamai Balaraba ta Biyo mata Su Tafi Wajen Waliman Sai ya dafe kai yana Fadin ya manta bai ce ta Shiga ba ammh Ko Daga Baya su Shiga ita da Aiya su Musu Murna.

Wajen kwana Biyu kafin kafa ta Dauke Baki Duk suka koma Inda Suka Fito a kwana na uku ne da Tarewar ALHAJI SUNUSI TURETA..Ya nemi alfarman Limamin masallacin da su Baba ke salla ya sama mai Amintattun da Zasu kula da masallacin Daya Gina Wanda zai Zama an Fara salla da Ibadu aciki Alhaji Sunusin Tunda suka Dawo anguwan Sallah bata Wucesa in dai yana nan baya Fita bane,Nan da nan kuwa liman din yaji Dadi Karramawan Da Alhaji Sunusi yayi mai yace kada ya Damu Da kansa ya Nada Dalibansa masu Neman Ilimi Domin kula da masallacin Cikin kwana Daya aka Fara Gudanar da Salla Cikin kayattacen Masallacin Dake jikin Gidan Alhaji Sunusin.

Sai Wadanda ke kusa da Masallacin suka koma suna Sallan su anan ciki Harda Baba Habibu da Usman nan suka koma suna Sallah Tunda nan yafi kusa Dasu Shima Alhaji sai ya koma yana Salla masallacin Dake jikin Gidansa wanda ya kuma ya kasance mallakinsa ne.

Mutanen anguwan sun ji Dadin Masallacin ko bakomai ya"yansu ba zasu rika jin Nisan zuwa masallaci ba cikin masu Murnan Harda Baba Habibu ganin Mansur da Mastur suna Kokarin Zuwa masallaci Da sun ji Kiran Sallah Abun yana Burgeshi Dadin masallaci a kusa Dakai kenan Shi Da Rana baya Salla anan Tunda yana kasuwa ammh Isha"i da Asuba nan yake yinta,kowa na yabon Kirki da Dattako na Alhaji Sunusi Domin Bayan Sallar asuba Kafin a watse sai ya gaisa da Duka Mazan Dake masallacin Cikin Fara"a Son Mutane Cikin Lokaci kalilan Mutane suka saba Dashi suke kuma Yabon kyawawan Hallayansa.

Sati Biyu da Fara Amfani da masallacin Alhaji Sunusin ya Roki arziki Don Allah abude wani majalisun karatun Bayan Sallar asuba Asaka Littafi Domin atunartae da Juna Kowa yayi Na"am da wannan Shawaran ana Shawaran wazai Jagoranci majalisin Usman Mijin Balaraba ya Nuna Habibu yana Fadin Tabbas yana da Tarin Ilimin Addini Zai iya Jagorantan Majalisin Baba Habibu bai samu Bakin mgana ba Alhaji Sunusi ya Fara mai Godiya Tare da Rokonsa Don Allah kada yace A"a Bashi da yarda Zai yi ya amince bayan an yi Shawara an Tsaida Littafin da Za"a Fara mafi Rinjiye akace a Fara da Karatun Ahalari Yau in ayinshi Gobe sai atabo Tauhidi da Qur"ani Da wannan Shawaran aka Tsaya Baba ya koma Gida yana gaya ma su Aiya suka Bisa da Fatan Alheri.

Alhaji Sunusi bai Dauki Abunda da wasa ba,Yasa aka Kirgamai Mazan Dake zuwa masallacin ya bada kudi aka Siyo Duka Littafan Karatun aka Rabama kowa yara da manya Hatta da Mastur da Mansur sai da suka Samu Mastur dai yana ta Murna banda Mansur da baya son Karatu,Kwana Daya Tsakani aka Fara Karatun Bayan Sallar Asuba atashi karfe 6:40am na Safe Domin akwai masu Zuwa makaranta da masu Fita aiki Cikin Sati Daya Dattijan anguwan da yara da Mataasa suka Fara Jin Dadin karatun Baba Habibu Ko komai Shi ilimi Kogi ne ko ka sani in aka Tunatar Dakai Tamkar an Taimake kane,Abunda yabama Mutane Sha"awa Shine Karatun Baya wuce Alhaji Sunusi ba Ruwansa dashi mai kudi ne Haka zai Shiga Cikin su Baba ana Karatu Kwata kwata bai da Girman kai Ballatana Dagawa Mutun ne mai Son Takalawa da Datttako..!

_Albishirunku Masoyana wannan karan na bude muku wani Shashi na musamman Saboda ku..Ina masu Bukatan Atalla musu Hajarsu Ko wani iri ne Domin samun costumer ta ko"ina..? Ku garzayo kakarku ta kusa yanke saka Zan Tallata muku Hajarku a Duka Shafukana Domin inganta Sana"arku da kuma Samun Cinikaya mai Tsabta da kuma kara Hada hada wajen Masi siye da Siyarwa mai Bukatar A tallata mata Hajjarta Zata iya min mgana kai Tsaye ta wannan Lambar Tawa 09069067488 domin karin Bayani...Sai kunzo Kunsan dai mai kasuwa Shi ke da Riba.._

*Domin zama Daya Daga cikin wadanda zasu karanta Labarin SADAUKARWAR SO..! Zaku Biya kudin karatunku kamar haka Masu amfani da Banki Zasu Tura â‚?300 ta wannan asusun banki 0552179550 Jamila umar gtb,Masu Katin waya kuma zasu Turo â‚?400, ta wannan lambar wayar 09069067488 Adauki Hoton katin sai aturo kai Tsaye mutanenmu na Niger kuma zasu Tuntubi wannan lambar kamar haka +22794775574 domin karin bayani,Insha Allahu mutum zai tsinci kansa a paid group ina maraba da ku masoyana Nagode*



*Shakira..*
1/1/22, 18:52 - Maryam Badmsi: *SADAUKARWAR SO..!!*
_(Labarin Yan"uwantaka,Soyayyah Tare da Sadaukarwa)_

*Wattpad:@Jamilaumar315*
*Mallakar:Jamilaumar(Janafty)*

*Page6�⃣*


"Ba"a Rufe Wata Biyu ba Karatun da Mallam Habibu yake ya Daukaka sosai Saboda Karatun ma Mutane Dadama magidanta suna zuwa salla masallacin Saboda karatun da Akeyi ko bakomai zaka karu kuma Zaka Taimaki kanka ka Fita Daga Sahun Jahilai.

Bangaran Mastur kuwa yaron kowa Sha"awansa yake yi,Saboda Kaifin Hazakarsa da kuma Hankalinsa kamar wani Babba Duk sanda akayi karatu kafin abar masallacin ya Dauke sa akansa Duk da wasu ya sani wasu kuma bai sani ba kamar Bangaran Qur'ani yana cikin Izifi na Arba"in ne ya kusa Sauka su Ahalari Tauhidi da Hadisai kuwa yayi Nisa Saboda Mallam Habibu Baya musu waasa yana Kokarin koyar dasu iya abunda ya sani uwa uba Suna Islamiya da Hadda Domin Taimakon kansu.

Dattajai Dadama suna Sha"awan Kaifin Basiran Mastur Banda Mansur da banda wasa da barci Babu Abunda yake yin In kaganshi agaban Wajen karatu sai in Mastur ne ya Sakashi Zama Dole Shima kafin a tashi Zai nemesa ya Rasa sai chan zai gansa abaya yana Barci kana zai Tashe shi su Tafi Gida Mastur ke zai tamai Fada Mallam Habibu kuwa sai dai yayi Mirmishi Har acikin Ransa yana Jinjina ma Baiwar Mastur ya Tabbata Ko yau bashi da Rai Mastur zai iya Zama uba kuma mai Jajircewa kan Mansur.

Alhaji Sunusi Tureta ya Dade yana Sha"wan Mastur kullum yana ganinsa bai taba Tambayan yaron waye ba sa watarana Bayan sun gama Karatu Bayan Sun Firfito Daga masallacin ya kira Mastur din Bayan yazo ya Tambayeshi Sunansa sai ya gayamai sai yace Waye Babansa ga Mamakinsa sai ya Nuna Mallam Habibu Alhaji Sunusi ya Ji mamaki Cikin Girmamawa ya isa ga Mallam Habibu ya mikamai Hannu suka gaisa Daidai Lokacin da Mastur ya Riko Hannun Mansur suka kariso kusa Dashi Cikin mamaki yake kallonsu kafin ya kalli Malam Habibu yana Fadin"Ah..Mallam Habibu kada dai kace yaranan masu Kokarin karatu da zuwa Masallaci ya"yanka ne..?

Mallam Habibu ya yi Mirmishi kafin yace"Eh Ya"ya ne Alhaji Ashe baka sani ba..?Alhaji Sunusi yace"Wlh ban sani ba ina dai ganinsu Musamman ma Mastur gashinan ina yaba Kokarin yaron sosai sai yau na Kirashi   na Tambayeshi Sunansa ya gayamin kuma yace kai ne Mahaifinsa.."

Mallam Habibu yace"Allah Sarki.."Alhaji Sunusi ya Dafa kan Mansur Dake ta washe baki yana Fadin"Kai fa ya sunan ka yaro.? Da Sauri yace"Sunana Mansur Sulaiman Doguwa.."Gabadayansu suka Kalleshi Mansur akwai Surutu Alhaji Sunusi Cikin mamaki yana Fadin"Ah ba Da"n ka bane..? Naji yace Sulaiman kuma..?

Mallam Habibu yace"Eh bani na Haifeshi ba Yaron kanwatace Data Haifesa Ta rasu Mahaifiyar Mastur ta Shayar Dashi Tun yana Jaririnsa yake Hannunmu.."Alhaji Sunusi yace"Allah sarki..Masha Allah Allah ya mata Rahma..Sannun ku kunji..? Ayi takaratu Sosai Allah ya Taimaka.."Sai Lokacin Mastur yaBude baki yace Ameen Alhaji Sunusi ya bisa da kallo Lokacin Dayake Jan Hannun Mansur Daya makale ma Baba Habibu Suka kama Hanyar Gida Alhaji Sunusi ya Bisu da kallo Cikin Sha'awa kafin ya Juyo yana kallon Mallam Habibu yana Fadin"Babban bai da Sakin Jiki..Karamin kuma akwai Fara"a da mgana.."

Mallam Habibu yace"Mastur ai Miskili ne arana bazaka Taba Kirga maganarsa ba..Mansur kuma Yaro ne mai surutu da kuma Shiga Jama"a da waasa.."Alhaji Sunusi yace"Madallah Allah ya rayasu..Zan gayama Iyalina ta Shiga su gaisa da Iyalanka Sai DIZA ta samu abokan wasa barin ma Mansur tasu Zata zo Daya Domin itama akwai Son wasa Sosai.."Mallam Habibu yace"Naji kunya Alhaji..Wlh Nace Mamansu din ta Shigo bata samu Lokaci bane..Ammh Zata Shiga su gaisa Tunda Ita ya kamata ta Fara Shiga su gaisa.."Alhaji Sunusi yace"Bakomai kada kadamu..Mallam Habibu mungode kwarai muna karuwa da Karatu Allah ya bada lada.."Ya amsa da Ameen suka Rabu Cikin karammawa Mallam Habibu yajuya ya Nufi Gida Alhaji Sunusi kuma ya Shiga Cikin Gida.

Da Mallam Habibu ya koma Gida ya Iske Mastur nayi ma Mansur Fada kan Surutun da ba"a Tambayesa ba Aiya na Tayasa Dariya yayi yana kallon Mastur yace"Kaga Babban Mutum ka kyalesa..yarintan kenan Watarana sai Labari..""Da haka ya kashe mganar Ammh Aiya itama Dataji Surutun da Mansur din yayi sai da tayi ta Fada Hajja kuma Tana Shigar ma yaronta Shi kuwa sai Tura baki yake yi Halittansa ne baya iya Daina Surutu Haka sukayi Shirin makaranta Mansur na kunci ammh Kuma Mastur na Lallashinsa ya saki Ransa Shiyasa Sau Tauri bamai Shiga Tsakaninsu Domin wata kaunace Wanda Allah ne kadai yasan iyakarta a Tsakaninsu.

Kamar yadda Alhaji Sunusi yayi alkawarin Ranar da yammah Ta kama alhamis ne ba makarantan Islamiya Dukkansu Suna Tsakar Gida Hajja na Zaune kan kujera yar Tsuggo Tana wanke wanke Mansur na Gefenta yana mata Dauraya Aiya kuma Nadaga gefe Tana Tankadan garin Tuwo Mastur ke Zaune Kofar Dakinsu yana Dauke da Littafi yana karatu Domin suna gabda Zana Jarabawar Common ce Baya wasa da Karatu ammh Lokaci bayan Lokaci yakan Dakata da Karatun ya Shiga Madafi yana Iza ma Hajja Wutan Murhu Data kada Miya ta Dora Tuwo.

Hira suke yi Sama sama da Aiya da Hajja Mansur kuma yana ta Dauraya Rabi kuma yana   wasa da Ruwa Duk ya Jika Jikinsa Mastur na gefe Tunda ya zauna kala bai Bude baki yace ba sai dai Lokaci Bayan Lokaci yakan Dago ya kallesu basu wani Damu ba Sanin Halinsa Hajja Tuni ta sakamai Suna Miskili kafi Mahaukaci Ban Haushi.

Aiya ce Dake Tankaden Garin Masara Ta kalli Mansur Dake wasa da Ruwa tace"Mansur baka Jin mgana kalli yadda ka jika Jikinka da Ruwa.."Sai Lokacin Hajja ta lura da aikin Daya keyi Fuska ta bata Tana Fadin"Tashi kaje Nagode Dan barka..Kalli yadda kajika Jikinka daRuwa in sanyi ya kamaka ka Fara Mura ko Zazzabi fa..? Baka jin mgana ko Allah zan Fara Dukan ka fa Mansur.."Tafada Cikin Fada   Tashi yayi yana Fadin"Hajja kiyi Hakuri.."Mirmishi Ta saki kafin Tace"Nayi Dan albarka..Maza Ka shiga Daki ka cire kayan nan ka Sauya wasu..Sai ka Fito da wannan Ka shanya su sha iska kaji ko..?

Da Sauri ya Gyada mata kai Lokaci Daya ya kwashi Gudu Zuwa Dakin Aiya ta rakasa da Allah ya Shirya Hajja na Dariya Tana Fadin"Aiya na lura kina son Dan albarkana kina akai kasuwa.."Aiya ta tabe baki Tana Fadin"Bana son Raggon Miji bai iya komai ba sai Waasa..Gwara Mijina Mastur wanda ko komai akwai Jarumta ga Maida Hankali a Karatu.."Hajja na Dariya ta waiga Tana kallon Mastur Tana Fadin"Aifa..Ammh kina Hakuri da wannan Miskilin Megidan naki kalli fa Tunda ya Fito Bai Bude baki yayi mgana ba Wlh har ce ma Baban Mansur nake ko wani Cuta ke Damun Mastur ne bamu sani ba yace Ba ko Daya Tsabar Miskilancin sa ne na Hallitta.."

Aiya na Dariya tace"Shi wai ko Bakinsa baya wari ne..? Hajja ta Tsintsire da Dariya ita da Mansur Daya Fito Daga Daki ya Sauya kaya Jikakkun na Hannunsa Duk Dariyan da sukeyi yana Jinsu ammh bai Dago ba sai ya Nuna bai san ma me suke mgana ba Mansur ne ya Tabashi yana Fadin"Yaya Kaji Aiya na cema ka mai warin baki ko..?

Dago Idanuwansa yayi Cikin Sanyin Murya yana Fadin"Najita kyaleta..Ina Karatu ne kaima kaje ka Shanya kayanka kazo ka Dauko naka Littafin ka karanta.."Tuni Annurin Mansur ya Dauke ya Bata rai ganin haka yasa Mastur yace"Tafi kaje kayi wasanka..Kada kamin kuka.."Ai sai ya saka Dariya ya wuce da Sauri Kai kawai Mastur ya Girgiza kafin yayi Mirmishi ya Cigaba da Karatunsa,Hajja da Aiya na Ta Dariyan Murnan da Mansur yake yi Jin ance yaje ya Cigaba da wasansa.

Kamar Daga sama sukaji Sallama Daga saman kansu Kusan alokaci Daya Hajja da Aiya suka Juyo zuwa ga Kofar Shigowa gidan suna kallom mai Sallama Idanuwansu ya sauka kan Wata Mata kyakyawa Fara yar Duma Duma Da ita bata da Tsawo kuma ba Gajera ba mai Fadin Fuska Tana Sanye da wani Leshi Daga ganinsa kasan bana kananan kudi bane sai Babban Mayafin Data saba akanta Kafarta Fara cikin wani Takalmi baki mai Tudu Fuskarta Cike da Fara"a Hannunta kuma rike da wata karamar Farar yarinya ce Jajir kamar atabata Jini ya Fito mai kama da Matar sai dai ita yarinya Doguwar Fuska gareta kuma bata da kiba Lange lange Take kamar ta Balle Tana Sanye Cikin Bulawis din yara Doguwar Riga Ja Iyakarta Gwiwanta kafanta sanye da Sandal na yara mai kyau Harda Safa mai kyau sai kanta da akayi mata Kitso Chuku Wanda aka Tufke mata Daga Tsakiyar kan da wasu Ribhon masu kyau Hannunta kuma na Dauke da wata katuwar Teddy Mai kyau ta Yar Bby kamar Tayi mgana itama an Chaba mata ado Kamar yadda Yarinya taci ado kamar Zata Gasan kyawawan mata.

Fuskar Mata ta washe da Fara"a ganin su Hajja Aiya ce ta amsa Sallaman Tana mata maraba Hakoranta ta Bude Farare Har da Hakorin makkanta wanda ya karaa mata kyau da kwarjini,Hajja ta Tsame Hannunta Daga wanke wanken Datake yi Ta Mike Tana Mata Maraba Dukkansu suna mata kallon Rashin Sani Daki Hajja ta Shiga ta Dauko karamar Tabaarma ta Shinfida mata Lokaci Daya tana mata Maraba Takalminta ta Cire ta zauna Tana Zaunar da yarinyar agefenta wacce take ta kalle Kalle Lokaci Daya tana ta wasa da Teddy ta Mansur Dake Tsaye gabadaya Hankalinsa na kan yarinyar da yar gunkin Bby Dake Hannunta gabadaya Tatafi Dashi Sabanin Mastur da Tunda suka Shigo Sau Daya ya Dago kai ya kallesu ya maida kansa yana Cigaba da karatunsa bai kara Dago kansa ba.

Hajja ta zauna gefenta Tana Fadin"Sannu da zuwa.."Lokaci Daya tana ijiye mata ruwa awani kofin Silba Mai kyau Amsa mata tayi Cikin Fara"a Lokaci Daya tana gaisheta kana ta Juya suna gaisawa da Aiya Ganin kamar suna mata kallon Rashin Sani yasa tace"Sunana Hajiya Asiya..Wannan yata ce Khadija muna kiranta da Diza..Daga nan gidan makotan ku da muka Tare kwanaki.."

Daga Hajja Har Aiya sai suka washe Baki Aiya tace"Allah Sarki..Sannu da zuwa.."Hajiya Asiya ta amsa Tana kallon Mansur Daya tsaya yana kallonsu Hannu ta Mikamai Tana Fadin"Sannu Boy..Taho mai sunanka..? Da sauri Mansur ya isa gareta Lokaci Daya yana gayamata sunansa Mansur Sulaoman Doguwa Dariya Hajiya Asiya Tayi tana Fadin"Wow...primary nawa kake..? Kai ya daga yana kallon Mastur Dake Zabga masa Harara sai Hajiya Asiya ta Daga kanta suka Hada ido da Mastur da Sauri ya kauda kai Cikin Sanyin Muryansa yace"Ina wuni Hajiya..? Mirmishi ta saki kafin tace"Lafiya lau..Ammh ni ba Hajiya sunana ba Inda Zaka kirani da Mommy kamar da yadda Diza Take Kirana Danaji Dadi.."Mamakinta ya kama su Aiya basu samu Zarafin mgana Ba Mansur yace"Mommy Mommy.."Har sau Biyu kumatunsa Ta shafa Tana Fadin"Eh..Daz my Boy..Mansur.."Tafada Cikin Fara"a Diza ce ta Tureshi Tana Fadin"Ba Mommy ka bace..Is my Mom.."Hajiya Asiya na Dariya Tace"Ke Diza abokin ki ne..Na yi muku Abota ko baki son Abokin wasa..? Da sauri ta Daga kai Tana Washe baki Kallon Mansur Hajiya Asiya Tayi Tana Fadin"Yauwa toh kaima ga kawa nayi maka Daman Halin ku yazo Daya...Diza itama akwai mgana Sosai kamar aku.."Hajja tayi Dariya Tana Fadin"Kice Zamu ce ta Tatar da muje mu..Mansur Surutunsa Har ya baci da son wasa.."Hajiya Asiya tace"Itama Hakan take..Diza akwai som wasa Sosai barin ma in taga yara Dayake Sokoto da muka Fara zama muna zuwa Gidajen Yan"uwa tana samun abokan wasa Buh Tunda muka Dawo kaduna Sai ta zama sai ita kadai Daga Sch sai gida gata da son wasa fa Toh nan din ma Hakane naji Dadi Dana Shigo naga kuma da yara Diza Taji Dadi sosai.."

Daga Aiya har Hajja Mirmishi Sukayi Hajja Tace"Allah Sarki.."Shuru ya Biyo baya kafin Aiya tace"Hajiya baki sha Ruwan ba.."Hajiya Asiya tayi Dariya kafin tace"Wlh nasha Ruwa Daga gida..Ammh bari nasha ko Kadan ne.."Lokaci Daya Tana Daukan Ruwan ba kyama bakomai Tasha kadan ta Ijiye Daidai Lokacin da Mastur ya Mike Dauke da Littafinsa ya Shiga Ciki Ta bisa da kallo kafin ta Dawo da kallonta kan Hajja Tana Fadin"wacece Matar Mallam Habibun mai mana karatu..?Nima Daga cikin gida ina Karuwa sosai Alhaji ma nata Godiya yace akara muku Godiya Allah ya saka.."

Wannan karon Aiya ce tace"Gata nan Hajara sunanta Ya'yanta na kiranta Hajja..'Ta fada Tana nuna Hajja Lokaci Daya tacigaba da Fadin"Ni kakarsu ce Danake Zaune dasu Aiya suke Kirana Daga Doguwa ta kano muka Dawo nan da zama Shekaru Biyar da suka gabata.."Hajiya Asiya tace"Allah Sarki..Haka Alhaji yace ku Mutanen kano ne ni kuma haifaffiyar garin Sokoto ce Mijina ma Haka sai dai shi Dan Tureta ne Dake Sokoto.."

Aiya Tace"Masha Allah Tureta ai babban gari ne.."Hajiya Asiya tace"Sosai ma Aiya garin nata samun Cigaba.."Aiya ta karkace Zama tama bar Tankaden Datakeyi Tana Fadin"Wannan yarinyar ita kadai ce Diyarki kenan Hajiya..? Hajiya Asiya ta juya Tana kallon Diza da Mansur Dake wasa da Teddy kamar sun Shekara tare Ta Murmusa kafin tace"Ita kadai gareni Aiya..Shekararmu Goma sha Biyar da Aure sannan Allah ya bamu ita Nasha Wahala wajen Haihuwarta kamar ban yi Rai ba..Sai kuma Allah ya Takaita abun Mahaifta ta samu Mtsala Tun lokacin aka Ciremin ita Diza ita kadai ce yarmu kuma Sanyin Idaniyanmu.."Aiya da Hajja Fuskarsu ta Nuna Jimani suka Hada baki wajen Fadin"Allah sarki..Allah ya rayata.."Ta amsa da Ameem kafin Ta kalli Hajja tana Fadin"Wanchan Daya shiga Dakin chan shima Da'n ki ne..?

Da Sauri Aiya tace"Itama Shi kadai ne D'anta Data Haifa..Itama kamar kece Tana da mtsala a Mahaifinta Tun wani bari Datayi Likitoci achan Doguwa sukace da wuya ta kara Haihuwa.."Hajja ta Sunkuyar Dakai bata so So Aiya ta Fadi haka ba ganin ai yau suka Taba Haduwa da Hajiyar Cikin Wani Jimami Hajiya Asiya tace"Kai..Allah ka bamu Ikon cin wannan Jarabawan..Shi Mansur fa..?

Tafada Tana Nuna Mansur da suke ta waasa da Diza da Sauri Hajja Ta tare Aiya Tana Fadin"Shima kamar D"a yake garemu..Maryama kanwar Mallam ita ta Haifesa bata ga ma abunda ta Haifa ba ta bar Gidan Duniya Ni na Shayar dashi Nice kamar makwafin Mahaifiyarsa.."Hajiya Asiya tace"Wayyo..Allah ya Jikanta..Aikuwa uwa kike garesa Domin Nonon Uwa Tankar wani Sinadarin Soyayyane Tsakanin uwa da Abunda ta Haifa Allah ya Raya mana su..Ammh Shi wanchan din sam bai da mgana ne..?

Aiya tace"Mastur kenan..Baban Mutum..Baya mgana kuma bata Dameshi ba Kirarinsa kenan Miskili kafi mahaukaci ban Haushi..Wlh sai yaron chan ya wuni bai cema kowa Kanzil ba Shi dai barsa ina zashi karatu ina ya Fito karatu kamar wani Baturen Ingila.."Hajiya Asiya da Hajja sukayi Dariya kai ta kada kafin tace"Allah sarki..Daman haka Allah ke Hallitan wasu Mutanen sam zaki ga mgana bata Damunsu.."

Hajja Tace"Shi kam Mastur abun nashi kamar cuta..Ka wuni Shuru baka mgana.."Tafada Cikin bayanna Jimaminta Hajiya Asiya tace"Ba fa Cuta bane..Haka suke irinsu Nature su ne haka.."Daganan sai Hira ta tsinke a tsakaninsu har Hajja tatashi tayi Talge,ta Dawo suka Cigaba da Hiransu sai ana gabd da kiran mangariba Tayi Shirin Tafiya Diza kuma tace bazata Bita ba Taga abokin waasa ganin haka yasa Hajiya Asiya ta kalli Hajja Tana Fadin"Hajja bari na barta Wajen Mansur..anjuma zan aiko Fadime mai aikina Tatafi da ita.."

Hajja Tace"Bakomai Hajiya.."Ta saka Takalminta Lokaci Daya Tana gyara zaman mayafinta Tana Fadin"Sai anjuman ku..Ammh fa Aiya zaku sha Fama da ita Bata jin mgana Ku kwabata kada tayi muku Barna.."Aiya tace"Ai muna da irinta Shima wannan da kike ganin ba jin mgana yake yi ba.."Dariya sukayi gabadayansu Har Kofar gida Hajja ta Rakata Tana Gayamata sai sun shigo Kafin ta Dawo Ta samu Aiya na kallon su Mansur Dake ta waasa Diza akwai baki sai Bashi Labarin Kaduna take da makarantansu da Daddyta dinta yayi mata kaza yayi mata kaza Hajja ta Dauki Sauran garin Tuwonta Tana Fadin"Gaskiya Daga Megidan har Matan gidan suna da Kirki..Jifa bamu shiga ba ita ta Shigo mana.."

Aiya Tace"Nima Zencen da nake yi kenan araina..Matar ta Burgeni ba Ruwanta Kalli yarinyar mana ki gani Daga gani bata da bakunta ballatana kyama ace wacce ke Rayuwa awannan gidan   ne zaune anan Gidan Tana wasa cikin kasa.."Hajja Tace'"Irin Mansur ne ba Ruwansu..Ba irin megidan ki ba mai Tsoron mutane ba Yana jin anyi baki zai Shige Ciki yaki Fitowa kamar za"a yanka sa..Ka Fito Bakuwar Tatafi.."Ta Karishe Fada Tana Daga Murya Aiya na gefe Tana Dariya.

Yana Daga Cikin Dakin yana Jinta bai Fito ba sai da ya Kimta Littafan karatunsa waje Daya kana ya Fito Aiya ta Kallesa Tana Fadin"Har an fito Megidana..? Kai ya gyada mata bai yi mgana ba Mansur yake kallo da Diza Dake wasa kafin ya Isa bakin Rijiya ya isa ya saka Guga ya jawo Ruwa ya Ciccika Butoci Da Ruwa ya Dauki Daya ya kai ma Aiya Har gabanta ta karba tana sakamai albarka kallon Hajja yayi yana Fadin"Hajja ga ruwa nan in zaki yi alwala.."Zata Shiga Madafa da Garin Masara a Faranti tace"Tom Babban Mutum.."

Mirmishi yayi kafin ya Dauki Butan Dake da Ruwa ya Fada Makewayi Bai Dade ba ya Fito yana Tsugunnawa Lokaci Daya yana kallon Mansur yace Cikin Kakkuran murya kamar wani Babba"Mansur kabar wasan nan Baka ji an kira sallah bane..?

Dagowa yayi yana kallonsa bai basa Daman mgana ba ganin Diza Itama ta waigo Tana kallonsa Kansa ya Kada kawai yace"Kai da ita Duk ku zo ku Dauki Buta kuyi alwala.."Ayadda yake mgana kamar wani Babba Hatta Aiya Dake gefe sai da ta kara Jinjina ma Jarumtan Mastur Hajja na Madafi kuwa Sai da taMurmusa Miskilin Dan nata Jajirtattace ne Sosai kamar Ubansa.

Ganin yayi mganan ba wasa yasa Mansur din ya Mike yana kallon Diza yace"kawo Yar bebin nakai Dakin Hajja..In mun Yi sallah sai mu Cigaba da wasan.."Make abunta Tayi taki basa ganin haka yasa yace Mata"kina son ya Mastur ya Dake ki..? Sai ta girgiza kai Kamar Zatayi kuka Da Sauri yace"Toh kaima Aiya ta ijiye Miki Kizo muyi alwala."Ba musu Tatafi ta kaima Aiya Datagama Alwala Zata Shiga Ta karba Tana Fadin"Maza kiyo alwala Kizo muyi sallah kawata.."Baki ta washe mata ta amsa da Toh Tatafi ta koma Wajen Mansur Lokacin Har Mastur ya idar da alwalansa Sai Mansur ya mika mata wata karamar Buta Shima ya Dauki Nashi Suka Fara alwala In Tayi Kuskure sai ya gyara Mata Har suka Idar Mastur na Gefe yana Kallonsu suna Idarwa Hajja na Fitowa Daga Madafa Mastur yace"Hajja ki kaita Tayi sallah zamu tafi masallaci. ".
Daga Haka yaja Hannun Mansur suka Fice wanda ke tta waiwayanta Har yana mata Bye Bye.

Hajja Ta kaita Dakin Aiya ta Bata wani karamin Gyale ta yafa mata Sukayi sallah Tare da Aiya suna idarwa Ta zauna tana Motsi da baki ganin Aiya na Addu"a itama Sai ta Fara Motsi da baki Aiya na kallonta yarinya sai ta Burgenta Sunanan Su Mansur suka Dawo Daga masallacin saboda Sauri Baya yabar Mastur ya Rugo Zuwa Gida ya Fada Dakin Aiya yana Kiran Diza Tana ganinsa ta Mike Tana Murna Aiya ta Dauko Musu Bebin suka Cigaba da wasansu,Mastur kuwa yana Dawowa ya koma Daki ya Cigabq da Karatunsa.

Har Hajja ta tuka Tuwo taje Tayi Salla ta Dawo ta kwashe ta saka Ruwan Zafi na wanka Tazo ta Zubama Aiya nata ta sakama Diza nata Duk da bata da Tabbacin Zataci,Sai Mansur yace ta Hada musu sai ta sakama Mastur nashi Dabam Kamar yadda suka saba Ta Shinfida katuwar Tabarma suka Zauna Abunda ya bama Aiya da Hajja mamaki yadda Diza taci Tuwo Harda kari ita da Mansur Suna gama cin Tuwon kenan aka Kira salla wannan karon ma Mastur ya tasa Mansur suka Tafi masallaci itama Dizan sukayi sallah Tare da Aiya Sun idar kenan sun Fito su Mansur suka Dawo suka kara Murna Diza da Mansur Har Hajja da Aiya na mamaki koda yake wasa ne ya Hadu da wasa ne.

Mallam Habibu ya Dawo ya iske Diza yarinyan Sam bata da Bakunta ta saki Jikinta Ya siyi ma Mansur Sweet sai aka Raba Musu Aiya ce ke koramai Bayanin Shigowar Hajiya Asiya da Abunda ya wakana Cikin Fara"a yace"Allah sarki..Mutanen Kirki ne Allah ya bar Zumunci.."Yana cikin Cin Tuwo Sai ga Wata yar Matashiyar yarinya Wacce bata Wuce Shekaru 30 ba ta Shigo da sallama bayan sun gaisa dasu Hajja tace sunanta Fadime yar aikin Gidan Hajiya Asiya an ce Tazo Tatafi da Diza Dizan na ganinta ma ta Fara Kiran sunata alamun sani Data Fahimci Tafiya da ita za"ayi sai ta Fara kuka Dakyar da Lallashi Ta yarda tabi Fadime Mansur din kansa Kamar zai yi kuka Ranar da Wuri yayi barci haka itama Dizan Daga bangaranta..

Washegari Karfe 9am Sai ga Fadime ta kawo Diza sai dai Su Mansur suna makaranta Fadime take Fadin tun Safe Take kukan sai an kawota Wajen Mansur Hajja ta karbeta tace sun Tafi makaranta ammh sun kusa Dawowa zata zauna..? Diza tace eh sai Fadime tatabi ta barta Wajem Hajja Aiya ta Fito Tajata Daki Suna ta Hira kamar Wata babba Duk da yarinya ce ta Fahimci yar gatace Diza ta gaba da baya.



_Albishirunku Masoyana wannan karan na bude muku wani Shashi na musamman Saboda ku..Ina masu Bukatan Atalla musu Hajarsu Ko wani iri ne Domin samun costumer ta ko"ina..? Ku garzayo kakarku ta kusa yanke saka Zan Tallata muku Hajarku a Duka Shafukana Domin inganta Sana"arku da kuma Samun Cinikaya mai Tsabta da kuma kara Hada hada wajen Masi siye da Siyarwa mai Bukatar A tallata mata Hajjarta Zata iya min mgana kai Tsaye ta wannan Lambar Tawa 09069067488 domin karin Bayani...Sai kunzo Kunsan dai mai kasuwa Shi ke da Riba.._

*Domin zama Daya Daga cikin wadanda zasu karanta Labarin SADAUKARWAR SO..! Zaku Biya kudin karatunku kamar haka Masu amfani da Banki Zasu Tura â‚?300 ta wannan asusun banki 0552179550 Jamila umar gtb,Masu Katin waya kuma zasu Turo â‚?400, ta wannan lambar wayar 09069067488 Adauki Hoton katin sai aturo kai Tsaye mutanenmu na Niger kuma zasu Tuntubi wannan lambar kamar haka +22794775574 domin karin bayani,Insha Allahu mutum zai tsinci kansa a paid group ina maraba da ku masoyana Nagode*





*Shakira...*
1/1/22, 18:52 - Maryam Badmsi: *SADAUKARWAR SO..!!*
_(Labarin Yan"uwantaka,Soyayyah Tare da Sadaukarwa)_

*Wattpad:@Jamilaumar315*
*Mallakar:Jamilaumar(Janafty)*

*Page7�⃣*



"Wannan Dalilin shine zan iya cewa Mafarin Zumunci mai karfi da ya koma Tamkar yan"uwantaka ko Jini Daya Tsakanin Iyalan Alhaji Sunusi Tureta da kuma iyalan Mallam Habibu.

Domin Wata Shakuwa ce mai Girma ta Shiga Tsakanin Mansur da Diza kamar wasu yan"uwana na Jini kullum Kwanan Duniya Tana Gidansu nan take wuni suna wasa Tun ana Maidata Gida Tana kuka Har Alhaji Sunusi yace a kyaleta ta Rika kwana abun kamar wasa sai karamar mgana ta zama Baba Ya zamana Ko Dizan bata zo ba Da sun dawo makaranta Mansur ko abinci baya Tsayawa yaci zai shiga Gidansu Diza megadi baya Hanashi Saboda ya Riga ya sansa Kuma Alhaji ya bada Umarnin kada ataba Hana Iyalan Gidan Mallan Habibu Shiga Gidansa Duk sanda suke so.

Tun iyayansu na mamakin irin Shakuwar Da ke tsakaninsu Har suka Dawo suka Daina ganin Haduwar jini ce da Allah ya Hada sannan uwa uba Halayyansu yazo Daya son Surutu da kuma son wasa,Mastur ya kasance babu Ruwansa baya shiga harkansu sai dai yakan tsawatar musu suyi karatu ko sallah da Sauransu ya zamana kamar wani Babban yaya garesu Diza Tana Jin Tsoron Mastur ko mgana Yayi yanzu Zata Shiga Taitayinta ganin baya mgana kuma Baya Dariya,Bata san Haka Hallitansa take ba Balle ma Da Mansur ke Tsorata da Fadin In bata jin mgana Mastur din yana Duka ita kuma bata son Duka Shiyasa da taji mganarsa Take shiga Taitayinta sai dai baya musu da wasa Duk Jin Dadin wasan da suke da an kira sallah zasu Tashi Mastur ya Dake ma wannan Tarbiyan nasu wanda Hatta da Hajiya Asiya ta Shaida haka Domin Ko Sallah aka Kira bata Tashi ba Tana Zaune in Diza na wajen yanzu Zata kama Hannunta Tana Janta Lokaci Daya tana Fadin Tatashi Tayi sallah Kada Ya Mastur ya mata Bulala wannan abun Farinciki ne Sosai Diza bata wasa da sallah balle karatu wanda da karfi da yaji Ta shiga islamiyansu Mansur Domin in zasu Tafi sai ta Fasa kuka Tun suna barinta agida Har watarana Mastur yace Ta saka Hijabi su Tafi Tare,Jin haka yasa sai dai Suka ji an saka Diza a makarantan Islamiya Mallam Habibu ya sakata kuma Mastur yace Baba ya Dinka mata Hijabai Ta Daina yawo ba Hijabi ko Hula Diza kuma ta Rike wannan Ko Barci bata yarda Tayi saida Hula akanta ko Zamewa yayi sai tace Mommy Ya Mastur yace in ina Barin kaina abude Shedan zai Min Fitsari akaina Hajiya Asiya ssi dai Tayi Dariyan Domin ko itace Diza Ta ganta ba Dankwali Haka take ce mata Har gida Taje tayi ma su Hajja Godiya da Mastur wanda Haka kurum Natsuwarsa Take Burgeta ko Baya son mgana Haka Zatayi ta Jansa Da Hira sai dai ya kalleta ya gyada mata kai ko ya Girgiza mata kai bata Damuwa da Hakan ita dai Haka kurum Mastur din ya Shiga Ranta.

Kusan kullum Hajiya Asiya na Shigowa Gidan Su Hajja kuwa sai Jefi Jefi sun kanshiga su gaisa Mansur kuma ai ya zama Dan Gida Mastur ne ya Taba Shiga Sau Daya shima Lokacin islamiya ne yayi kuma Diza taja Mansur zuwa Gidanasu sai ya Shiga ya Kirasu wannan ne Shigansa na Farko Daga Ranar kuma bai kara Shiga ba Saboda Shi mutum ne mara son Hayaniya da kuma Yawan mgana Tun Farko.

Makaranta kuwa Diza kuka ta saka ma Alhaji Sunusi kan sai an sakata makarantan da Mansur yake zuwa Tunda lokacin Mastur sun zana Jarabawan Fita Daga primary suna Jiran sakamako,Sai Mansur ne kadai ke zuwa Daman achan kaduna an sakata makaranta Tana Nursing2 Dawowarsu nan ne karatun ya Tsaya wannan Dalilin yasa Hajiya Asiyata bada Shawaran ya Sauya ma Mansur din makaranta sai ya sakasu tare da Diza haka kuwa akayi Saidai Hajiya Asiya tazo Tatafi Dashi Batare da tayi wata mgana ba taDai ce Zasu anguwa Mastur kuma baya Zaman gidan Mallam Habibu yake bi kasuwa kafin sakamakon Jarabawan nasu ya fito.

Zaria Acadamy aka kaisu akayi musu yan Tambayoyi,Tare da Sauran abubuwa Cikin Lokaci Daya akayi komai aka gama Tunda akwai kudi Diza Primary 1 aka sakata Shi kuma Mansur Primary 4 uniform da komai Da Littafai Duka makarantan ta basu Ranar chan ma suka barsu sai da suka Dawo ne Hajiya Asiya ke Fada musu Mansur suna makaranta Hajja da Aiya suka rasa bakin mgana Sai Godiya sai 4pm na yammah Ranar suka dawo Kuma Audu Sabon Direban da Alhaji Sunusi ya Dauka yaje ya Daukosu Bakin Mansur da Diza kamar Zai Tsage saboda Farinciki Mallam Habibu sai dai ya Dawo yaji Labari mai Dadi Har gida yaje ya Kara ma Alhaji Sunusi Godiya yace kada ya Damu ai sun Saba Daya yanzu.

*******

Alhaji Sunusi Tureta Mutumin Jahar Sokoto ne A wata Karamar hukuma mai suna Tureta Bashi da iyaye tun yana Gabar samartaka Allah ya yi musu Rasuwa Alhaji Sunusi yayi gwagwarmaya sosai Kafin yayi Karatu sai da ya Saida Duka Gonakin da iyayensa suka Rasu suka barmai ya samu Gurbin Shiga jami"ar Usmanu Dan Fodiyo inda yayi Digree dinsu kan kasuwanci anan ne ya Hadu da Amininsa wanda ya Zama kamar Dan"uwan garesa Alhaji Muhammed Wamako Wanda Shima Dan Wamako ne Shima Karatu ya kawosa suka Hadu nan kuma sai ya zamana abu Daya suke Karanta,Tare suka yi Digree dinsu suka kuma yi Mastes dinsu Lokacin nr suka Fara Tunanin Gudanar da waata Sana"ar Alhaji Muhammed wamako shi ya Fara kawo Shawaran su Fara Sana"ar Shigo da Motoci ba Laifi Suna yan kudade a Hannunsu Tunda bayan gama Digree dinsu sun Fara aiki a wani karamin kamfani suna samun albashinsu suna Tarawa Domin Tsayawa a kan kafafunsu.

Cikin Ikon Allah wani bawan Allah yayi musu Hanya suka Fara Sana"ar Motocin Daga kwatano,Kafin su Rufe Shekara Daya sun samu karuwa Sosai Lokacin Dukkan sun kamallah Karatasu,Alhaji Muhammed ya Riga Alhaji Sunusi Aure in da akayi mai Auran Zumunci da yar"uwarsa Farida,Anan Sokoto ya siya Gida suka zauna sai bayan Auransu da Shekara Uku kana Alhaji Sunusi yayi Aure da Asiya ita yar asalin Garin Sokoto ne kuma Tayi Karatunta anan Usman Dan Fodiyo University.

Bayan sun yi aure suka Hada kan Matansu Waje Daya suna Zaune Lafiya gefe Daya kuma Suna Cigaba da Kasuwancinsu Duk da Shuru basu samu Haihuwa ba Ammh basu Damu ba Suna Cigaba da addu"ansu Cikin Lokaci kadan Allah ya sama Abun albarka shekara Goma da suka shude har kowa ya mallaki katon Gida da Motar hawa sunje sun sauke Farali su da matansu kuma Har sun kai wasu Daga Cikin Danginsu,kana sun Bude wani karamin ma"aikata Da suka saka ma suna WAMAKO AND SONS  MOTORS LIMITED..!,Cikin Lokaci Daya sukayi suna suka kuma Shahara Ajahar Sokoto har zuwa Lokacin kuma Allah bai basu Haihuwa ba.


Farida ita ta fara Haihuwar yarta mace wacce taci sunan Mahaifiyar Alhaji Muhammed Wato RUMANA,sai bayan Haihuwan Rumana da Shekaru Uku kana Hajiya Asiya ta Haifi Diza wacce kamar bazatayi rai ba wajen Haihuwarta ba dakyar aka samu kanta,Tun kuma Daga ita bata kara Haihuwa ba haka itama Farida sai ya kasance sun Rumgumi Abunda Allah ya basu Sun gode ma Allah.

Komawar Alhaji Sunusi kaduna kasuwancinsu ne ya Bunkasa Har Kaduna da Sauran Jahohi sun Hada Hannun Jari da wani Kamfani Dake Shigo da Motoci Daga kasashen Waje Dalilin Dayasa ya Dawo Kaduna da zama kenan Hajiya Asiya taji kewa Sosai Domin Sun Saba da Hajiya Farida Tamkar wasu yan"uwa ga Diza da ta saba da Rumana ammh basu da yarda Zasuyi yanayin kasuwancin ne Shekararsu Duka Duka Biyu ne a Kaduna suka Dawo Zaria da Zama Saboda Bude wannan Rishen da sukayi anan,sun Riga sun Raba abun Kamfaninsu na chan Sokoto Takardun da sunan ciki na Alhaji Muhammad Wamako ne na nan Zaria kuma sai ya zama na Alhaji Sunusi Tureta ne sun Raba abun saboda Halin Rayuwa sai dai,Sauran Hannayen Jarinsu Dake wasu kamfanonin Dake makwafta dasu.

 

Dawowarsu nan Zaria yan"uwan Hajiya Asiya suna zuwa Sosai Lokaci bayan Lokaci hakama Hajiya Farida Tazo ssu Biyu Ita da Alhaji Muhammed Domin Lokacin da suka Tare basu samu zuwa ba Rumana na makaranta ammh bayan sun samu Hutu sun zo sun kwana Biyu yaje yaga wajen sosai yaji Dadin ganin yadda abubuwa suka Tafi Daidai kamar yadda suka Tsara.

*****

Mansur da Diza suna Cigaba da Zuwa Zaria Acadmy,Ayayinda Mastur ke zaman Jiran samakonsa kwatsam Sai gashi ta Fito kuma Daman ya Cike makarantar kwana ne Harda Hassan Gwarzo,kuma Alhamdulillah yasamu da Farko Hajja taso taki yarda yaje makarantar kwana ammh sai Mastur din ya nuna yana so kuma yana Bukata Sai Mallam Habibu ya maramai baya Hajiya Asiya ne Data Shigo Taji Aiya na Fada Taje ta gayama Alhaji Sunusi Shi kuma ya samu Mallam Habibi yace ya kawomai Takardun Makaran nashi,haka kuwa akayi ya Dauko ya bashi ba"a Rufe wata Daya ba Komai ya kamallah Mastur ya samu Gurbin karatu a makaranta Hassan gwarzo Duka abubuwan da suka Biyo baya Alhaji Sunusi yayi komai Harda Provison dinsa da komai da komai yace baya Bukatar Mallam Habibu yace komai Mastur kamar D'a yake garesa bashi da bakin Godiya sai dai yacigaba da mai addu'an Allah yasa ya gama Lafiya.

Ranar da Mastur zai tafi makaranta Mansur haka yake kuka kamar ransa zai Fita haka Diza ma ganin Mansur na kuka sai itama ta kama Ranar itace Rana ta Farko Daya Taba Rike Hannuwan Diza yana bata Hakuri ya Hadasu ita da Mansur din yayi musu Fadan su maida Hankali a karatu Don Allah banda wasa sukayi mai alkawarin Insha Allahu Zasu yi karatu kamar yadda yake so,Hajja ita kanta sai da Tayi Hawaye Hakama Aiya Ga Tsufa Sai kuka Tana Fadin ina zai Tafi ya barta Shi kansa Domin yana Namijin Duniya ne bai yi kuka Haka suka Shiga Mota dashi da Alhaji Sunusi da Mallam Habibu Audu Direba zai kaisu su Hajja na waje suna Daga musu Hannu.
Tabbas Sabo wani abu ne..Ranar Mansur da Diza wuni sukayi wasu sukusuku dasu Kamar basu da lakka Barin na Mansur Dayafi Kowa Shakuwa Dashi Haka Aiya da Hajja su kansu Sunji Dabam yau koda Mastur baya Yawan mgana Ai Sabo wani abu sai dai sun Ji Dadi da su Mallam Habibu suka Dawo suna sanar dasu makaranta ce mai kyau inda Mastur din ya zaba kuma Insha Allahu zai samu karatun Dayake Fata kuma in anyi Hutu zai Dinga Zuwa ganin gida da Haka suka samu suka Saki Ransu Kowa yacigaba da Harkokinsa...

Tafiyar Mastur Kano Shi ya kara Saka Karatun Diza da Mansur kara Lalacewa makarantan Kadai suke zuwa da sun Dawo ba mganar su dauko Littafansu su Duba sai wasa,islamiya kuwa sai sun ga dama suke zuwa Daman Mastur ke matsa musu ko mallam Habibu shi kuma yana kasuwa Mastur kuma baya nan Hajja Ko tayi musu mgana Sau Daya bata karawa Ballatana Aiya,Hajiya Asiya kuwa Tana da i don"t Care kuma bata som mtsama yara In tayi musu mgana Sau Daya suka Nuna basason zuwa kyalesu Take yi Alhaji Sunusi kuma Baya zama yana Kamfani inda yake da Office dinsa sai Dare yake Dawowa ba wanda ya Fahimci karatunsu ya Fara Rauni Ballatana ya kwaba musu.

Dawowar Hutun Mastur na Farko ya Fahimci Sai a Hankali Karatun Bokon suna Zuwa Dole na addinin kuwa Duk sun watsar wanda suka sani a baya sun manta Dashi yayi Musu Fada Sosai suka nuna sun ji Zasu gyara a hutun da yayi sun Dage saboda yana mtsa musu ammh Da Zarar ya koma Shikenan sai ungulu ta koma Gidanta na Tsamiya kuma Laifin Duk na Mansur ne Shine Babba Im ya ce Diza tayi abu bata Tsallake mganarsa toh shima ba son karatun yake ba sai Su wuni agidan su Diza suna kallo ko suna Buga Game Hajiya Asiya bata da wata Damuwa balle Har ta kwaba musu.
Zuwa Lokacin Zumunci mai karfi ne ya Shiga Tsakanin Gidajen Biyu,Alhaji Sunusi ya Dauki Mallam Habibu kamar Dan"uwasa kaninsa baya Zartar da komai sai da Shawaransa wani Zakka ne im zai Fitar shi zai samu kan mganar Alhaji Sunusi Duk wata kamar yadda zai Siya kayan abinci agidansa haka zai aika Dashi Gidan Mallam Habibu komai na Rayuwar nan babu abunda suka Nema suka rasa Tun Mallan Habibu na Jin Nauyin Alhaji Sunusi har ya Daina Dalilin Haka yasa Shima in ya samu alherin yake ma Mutane irin su Usman Tunda ko bakomai bazai manta da karamincin Usman garesa ba.

Doguwa kuwa sau Daya suka Taba zuwa sanda karime ta Haihu Yayar Hajja sun je Dukkansu sun kwana Biyu sun Dawo Lokacin Mastur na makaranta da Mansur suka Tafi Da Diza wacce tace sai taje suka Tafi da Ita a zuwan da sukayi ne Sule mahaifin Mansur yazo ya Roki Mallam Habibu kan zai Tafi da Mansur chan maruka yan"uwan su gansa Shima ya gansa Mallam Habibu bai yi Gaddama ba ya amince sai dai Diza tace itama da ita za"a je sai yace ya Tafi dasu Dukkansu Lokacin da Goggo da Zainabu suka ga Mansur sunyi mamakin ganin girmansa da yanayinsa Lalle ya samu Chanjin Rayuwa Ballatana Sauran yan"uwan nashi Duk ya Fita Dabam Dasu Goggo Kasa Boye Bakincikinta Tayi balle da suka ga Diza Sulen yace musu da ita suka zo Daga Zaria yar makotansu ne sun ganta yar gayu Kuma Daga ganinta Sun ga Jinin Kudi da Jin Dadi,Da sule yaso su kwana ne ammh Diza ta saka,kuka Dole acikin Daran ya Dawo Dasu Doguwa Gari na waye suka koma  Saboda makaranta kuma Daman Audu Direba ne ya Taho Dasu kuma yazo ya koma Dasu.

Jin Dadin Rayuwa Sai dai su mallam Habibu su bama wasu labari,Suna Cikin Rufin asirin Allah,Mansur kuma ya zama Dan gata Domin komai Tare da Diza ake musu Mastur kuma Duk wata Alhaji Sunusi na Turamai Kudi ta Hannun Wani malami amakaranta lokacin da suka kaisa ya karbi Lambarsa Shi yake Turama kudin yayi mai Siyayyah Shima baya Cikin Wata Wahalan Rayuwa in sukayi Hutu ya Dawo yayi kiba ya kara Haske sai da Ramar Makaranta da kuma Chanjin Rayuwa Hajiya Asiya da Hajja sun zama kamar kawaye ko nace yan"uwa basa iya Boye ma Juna Komai Hajiya Farida Tasha Zuwa sukan Shigo Tare da hajiya Asiya su gaisa da Hajja Har ma suyi ta Hira Sau Daya dai suka Taba zuwa da Rumana itama kamar mastur Take bata da Hayaniya Ballatana yawan mgana sai dai ta zauna Tayi Shuru Tana kallon Diza da Mansur suna abunsu.
Tun Mastur na Dawowa Hutu yana Matsama Su Mansur da Karatu har yagaji ya saka musu Ido ganin sun yi Nisa basa Jin Kiran sai kawai ya Fita batunsu ammh bai Fasa yi musu Fada ba sai su nuna kamar sun ji da sun Fara kwana Biyu sai su Bari,Bawai basa Karatun bane suna yi ammh basa maida Hankali Har gwara ma na Bokon Dole sukeyi ammh na Addini kuwa Har suna manta na Baya Diza kuwa Daman Karatu ba Damunta yayi ba Tafi son waasa Data Fara wayau kuwa Game da kuma Kallo Sai Shima Mansur yake Biye mata ba wanda zai iya ma wani Fada acikinsu.


******

Tafe Tafe Rayuwa haka tacigaba da Gangaragarawa Cikin Kudiran Ubangiji Gashi Har Mastur ya zana Jarabawar Fita aji 6 ya dawo gida yana Jiran Sakamako Lokacin yana da Shekara 19 aduniya ne,ayayin da Mansur ke da Shekara 15 aduniya yana SS1 ita kuma Diza Tana da Shekara 11 aduniya Tana kuma JSS1 ne,Dukkansu sun Girma sun Fara mallakan Hankalin kansu.

Mastur da zuwa Lokacin ya riga zama Babba sai abubuwansa su ka Karu manyace Rashin mgana da Rashin son Hayaniya sai da ma ya Girma kana Miskilancinsa ya kara Bayyana,,Mansur kuma Rashin ji sai abunda yayi gaba Sarutu kuwa kamar yamai yawa,Diza ma Haka sai dai ita bata kai Mansur Surutu ba sai dai tafi kalkali da Mgana,Mastur yana Shan Takaichi in yaga Sakamakon su na Jarabawa Basa wani karatu sai wasa yagaji da mgana ya kyalesu sai kallo sai game Dayake ma Nan din ma Alhaji Sunusi ya saka musu kayan kallo,wuni suke abu Daya basa ko Gajiya In suna Buga game kuwa Su cika gidan da Hayaniya kuma in ya Fito yayi musu mgana sai suyi kamar sun Daina yana komawa Daki zasu Lallaba su Fice su koma Gidan su Diza su Dasa Daga Inda suka Tsaya Tun yana mamakinsu har ya Daina Shi dai karatu yana da Dadi Kuma Amfanin wanda ya Tsaya yayi ne,shi har yau har gobe bai Daina Karatu ba a makaranta kuwa ya karishe sauke alqur"ani Ya Fara sauran Littafai yanzu ko daya Dawo Gida da mallam Habibu Suke karatu bayan Sallar Isha"i Mansur kuwa yana Daki yana kallo ko kuma yana Gidansu Diza ya Saka musu ido ne,ya bari Har watarana su gane Illar Abunda suka zaba ma kansau.

Sakamakon Jarabawan Mastur ta Fito kuma komai yayi Kyau Alhaji Sunusi ya Tambayeshi Wata makaranta yake so yace Jami"ar Dan Fodiyo kuma Shi Dan Sanda yake so ya zama Alhaji Sunusi yaji Dadin Hakan Sosai nan da man ya Fara Nema mai Jami"ar ta Hannun Alhaji Muhammed wamako Cikin Nasara kuma Mastur ya samu Gurbin Karatu a jami"ar zai karanta chemical engerneering Domin yaso ya sama mai makarantan Horarwa ta yan sanda ne sai Alhaji Muhammed wamako ya bada Shawaran Ya farayin Digree Tukunnah in yagama saiya Tafi police Staff Collage yayi Short Service da wannan Shawaran yayi amfani har komai ya kamallah kuma Alhaji Muhammed yace Mastur yazo Gidansa ya zauna Har ya kamallah karatunsa.

Haka kuwa akayi Mastur bai kara wani Zama ba ya Tattara ya Tafi Sokoto ya samu Tarba Sosai Wajen Hajiya Farida wacce Rumana ke kira da Umma,Rumana ta girma Domin Shekaranta 14 kenan aduniya Tana Jss3 zata Ss1 yarinya ce mai kwazo da son karatu ga Kokari da kuma Natsuwa bata da Hayaniya,Shuru Shuru da ita ga Naci kan karatu Gabadaya Daga Boko har islamiya na Daya take zuwa Mastur Farkon zuwansa Gidan yarinyar tayi ta Burgesa yayi ta cewa aransa Dama Diza ce Dama Mansur ne Domin yana son yaga yaro mai kokari da mai da kai a Karatu ammh Sam su ba wannan ne agabansu ba sai Shirmen banza.

Farkon zamansa agidan bata sake Dashi ba sai daga baya Ganin ko abu ne ya Shige mata Duhu Data Nuna ma Alhaji Muhammeda Datake kira Abba sai yace takai ma Yayanta Mastur Tun Tana Nokewa Har Ta fara sakin Jiki ganin Komai ta kaimai zai koyamata Dallah Dallah Yadda zata Fahimci Komai sai gashi Cikin Lokaci Rumana ta kara zama mai Kokari Sosai Fiye da Baya saboda Mastur na Taimakonta Abba da Umma suna Jin Dadi saosai Har sai da sukayi waya da Alhaji Sunusi yana gayamai irin Kokarin Mastur shi dai ba mai Hayaniya bane ammh kuma Yana da Hankali Da Natsuwa.

Nan gidan yake Zaune sai dai in suna da Karatu ya shiga Cikin makaranta ko kuma in zai yi Karatu baya waasa da abunda ya kaisa In ya Dawo yana Daki yana Karatu,in ba Karatu ba yana Barci Saboda ya samu Hutu Rumana ma bata wuni agida sai 4 take Dawowa makaranta da Tadawo sai Islamiya sai Dare take zama agida kuma bata Wani kallo ko Game da zai Dauke mata Hankali da anyi sallar Isha"i taci abinci Zata kawo ma Mastur ya koyama Math Sosai take son Taga ta zama Wata kwaruwa akan Math Shiyasa ta Dake mai in ya koya mata Daganan Zataje tayi Homework dimta Data gama sai Shirin kwanciya Saboda makaranta da Safe
Mastur har acikin Ransa yake Sha"awar Rayuwar Rumana kuma yake jinta Tamkar wata kanwarsa ta Jini Haka itama ya Fara Burgeta da Dabi"unsa da Hallayansa ya zama na kowani Lokaci Tun Tana kankanuwarta Tayi Ta Tunaninsa Shikuma Mastur ba wacce yake Fama da Tunaninta irin Diza yana so tayi Karatu ta Daina wasa yana so Ta Mori iliminta watarana yanaji aransa Dama Rumana Diza ce Dayafi KowaFarinciki Saboda Takaichin su ita da Mansur ko Hutu suka samu zamansa yake asokoto yaci Hutunsa,ko waya ya kira Mansur din ya Karba yana mai Magiyan yazo sai yace wani abu yaTsayayi,Dayake Alhaji Sunusi ya Siyama Mastur wayan Hannu Saboda Karatu da kuma Kiran Gida a koda yaushe sukayi mgana Dasu awaya sai yayi musu Fadan su Daina Biye ma Kalle kallen Banza su maida Hankali Da Karatu Zasu ce mai Toh ammh Abun ya zama Jinin Jikinsu akwai wani Hutu Daya koma lokacin Mansur na Shirin zama Jarabawar su ta Fita,Diza kuma Zata Shiga SS1,yana musu Fadan Maida kai a karatu Bude bakin Mansur sai yace mai shi Siyasa fa zai yi yana so ya zama gwamna,Diza na gefenta ta kada kai tace"Wlh daka Biyani..Domin inason na Auri Dan Siyasa Haka kurum suke Burgeni.."

Mastur ya Dade yana kallonta wani abu na Shiga Ransa Mansur kuwa Tunda yaji Diza ta Fadi Haka yaji Ra"ayin Abun ya Shiga Ransa sosai abaya Kawai Shirmensa yake yi na zai yi Siyasa ammh yau da Diza ta Furta Haka yaji Duk Duniya Bai da Buru Face Cikama Diza Burinta,Shi kuwa Mastur Jikinsa ne yayi sanyi Domin Diza ta nuna Daga Secondary Bazata Cigaba ba bata da Burin yin Karatu mai Zurfi Dukkansu bai matsama kowannen acikin su ba,yadai yi musu Fatan alheri ya sallamesu ya Dade yana Tunanin Abunda Diza ta Fada yaji acikin Ransa Kamar shima yaShiga Siyasa saboda ita Saboda a yan kwanakin nan yana Jinta Sosai acikin Ransa Wanda yake jin zai iya komai sabida ganin Cikar Burinta sai dai me Yana da Burin zama D'an Sanda Ko Domin Taimakama kasarsa Bazai kara mtsama musu ba,Abunda suka zama Rayuwarsu shine daidai zai musu addu"an Allah ya cika ma kowanensu Burinshi.






_Albishirunku Masoyana wannan karan na bude muku wani Shashi na musamman Saboda ku..Ina masu Bukatan Atalla musu Hajarsu Ko wani iri ne Domin samun costumer ta ko"ina..? Ku garzayo kakarku ta kusa yanke saka Zan Tallata muku Hajarku a Duka Shafukana Domin inganta Sana"arku da kuma Samun Cinikaya mai Tsabta da kuma kara Hada hada wajen Masi siye da Siyarwa mai Bukatar A tallata mata Hajjarta Zata iya min mgana kai Tsaye ta wannan Lambar Tawa 09069067488 domin karin Bayani...Sai kunzo Kunsan dai mai kasuwa Shi ke da Riba.._

*Domin zama Daya Daga cikin wadanda zasu karanta Labarin SADAUKARWAR SO..! Zaku Biya kudin karatunku kamar haka Masu amfani da Banki Zasu Tura â‚?300 ta wannan asusun banki 0552179550 Jamila umar gtb,Masu Katin waya kuma zasu Turo â‚?400, ta wannan lambar wayar 09069067488 Adauki Hoton katin sai aturo kai Tsaye mutanenmu na Niger kuma zasu Tuntubi wannan lambar kamar haka +22794775574 domin karin bayani,Insha Allahu mutum zai tsinci kansa a paid group ina maraba da ku masoyana Nagode*




*Janafty..*
1/1/22, 18:52 - Maryam Badmsi: *SADAUKARWAR SO..!!*
_(Labarin Yan"uwantaka,Soyayyah Tare da Sadaukarwa)_

*Wattpad:@Jamilaumar315*
*Mallakar:Jamilaumar(Janafty)*

*Page8�⃣*



*Bayan wasu shekaru..*
*The Nagerian Divisional Headquater*
_Porthercourt_

"Wani babban Headquater ne na Gamayar yan sanda Dake Jahar Parthercourt,Babban waje ne,Da akan bama yan Sanda Horo sosai Kuma Babban Headquater ne mai Dauke da Yan Sanda Shashe Shashe Bayan Haka kuma akwai Gidaje Quaters na mallakan manyan ma"ikatan wajen da ma wasu Daga Cikin kananun.

Daga yammah ne ginin Police Station din yake,Wanda yaji ginin Zanani mai farin Dutse Daga gaban wajen Motocin yan sanda ne da mashina gasunan Fake a parking Space sai kuma Kaida kawon wasu Daga cikin Mutane da kuma Sargents din Dake wajen.

Da Misalin karfe 8:30am na Safe ne Ana Zirga zirga awajen Cikin hakane wata Bakar Mota Prado,Mai kyau da Daukan ido,ta Shigo wajen cikin Slow Driving,cikin Hankali ma mallakin Motar ya karisa Faka Motar kuma ya zauna aciki yaki Fitowa kamar kiftawa kuma sai ga wani Sargent ya Fito sanye da kayan yan sandansa Bakake ya Tsaya Wajen Kofar Motar sai da ya Sara kana ya saka Hannu ya Bude Murfin Motan Lokaci Daya kuma ya koma ya kame Yana Raba Idanuwa kamar wanda yayi karya.

Sai da aka bata wajen Mintina uku kafin ma mallakin Motan ya Zuro kafarsa Guda Daya waje wanda Take cikin wani Bakin Takalmi Sawu Ciki mai Tsada na Fatar Damisa,ayayinda Kafarsa Take Fara mai Cike da gargarsa,an Dauki Lokaci kafin ya zuro Da dayan kafan sai dai wannan karon Cikin Zafin nama ya bayyana Gabadaya awaje.

Wani Muradden Matashin Namiji ne Dogo mai ingarman Jiki da mazantaka mai kwarjini mai Haiba da Dattako,yana da Haske ammh Ba Fari ba sosai Sai dai Fatarsa yafi kama da Kalan yan Moroco,Yana da Fadin Kirji mai nuna Zallar Jarumta da Sadaukantaka atsaye yake Daga ganinsa kaga Cikakken Namiji Sosai Damtsen Hannayensa Muscle dinsa Duka Sun Bayyana Tsabar karfi da kuma Nuna Jarumta,Doguwar Fuskarsa Tana Dauke da Dogon Hancinsa da bakinsa Dan Daidai sai Sajensa Daya Zagaye Bakinsa Dake karamai kyau da kwarjini yana da Idanuwansa Daidai Misali masu Dauke da wani Sirri,Gashin kansa a Nannade yake kamar na Fulani Sai Gashin Idanuwansa da suke wani Zara zara Dasu Idanuwansa ya Toshe su da wani Bakin glass,Jikinsa Sanye da Kayan yan Sanda Bakin wando da Riga mai Ruwan Blue ya saka Belt ya matse kugunsa Dashi,Daga yammah Da Kafadarsa Anininsa na igiyan matsayinsa,sai Daga Dama wajen aljihu wani Dan gold ne makale awajen an Rubuta *DCP M.B DOGUWA..* Daga saman kansa kuma Hularsu ne na yan Sanda kafe akansa wacce ta karamai wani Sirrin kyau kamar don shi akayi Hulan da Uniform din gabadaya.

Sargent din Dake Tsaye ya Kara saramai yana Fadin"Gud Mrning Sir.."yana Tsaye yana kallonsa Lokaci Daya yana saka Hannu acikin Aljihun wandonsa bai mai mgana ba kai kawai ya gyada mai kafin naga ya Dagamai Hannu Cikin Sassarafa da Takun Jarumta yayi gaba Lokaci Daya yana Duba agogon Dake hannunsa na kamfanin Rado.

Shi kuwa Sargent din jiki na rawa ya Sunkuya cikin Motan ya kwaso System sai wasu Tarkardu da wayoyinsa Guda Biyu,Sauri Sauri ya Rufe Motar Lokaci Daya ya saka Key din Motar ya kulleta yabi bayansa Da Gudu Gudu Sauri.

Yana Shiga wajen aka Fara kamewa ana mai sannu da Zuwa Ko Daga kai baiyi ba Sai dai yana Kallonsu Daya bayan Daya ta Cikin Bakin glasa dinsa Sanin Daman ba mgana zai yi ba basu Damuba   kamar zai Tsaya  sai kuma ya Cigaba da Tafiya Har zai Shige Koridon da Zai sadashi da Office dinsa Sai kuma ya Juyo Cikin Dakakkiyar Muryansa yace"Where is Sargent Alotuwa..? Gabadayansu suka kame atsaye kafin wani in yamurin Dan sanda yace"He is not well Sir.."Shuru yayi kafin ya kada kai bai ce komai ba ya Juya ya Fara Tafiya Cikin kasaita wannan Sargent din na Bin bayansa da kayansa Daya kwaso mai amota sai da suka ga Basa ganinsa kana kowa ya Sauke Hannuwansa suna Sakin Numfashi Sargent Bala Dayake Bayarbene yace"Kai Sir fa akwai Kwarjini..In ya kalleni Har Hanjina nake jin suna Kadawa.."

Dayan Sargent din mai Suna Sargent Gashuwa,Ba Musulmi bane ya karbe da Fadin"Shiyasa yake saka Glass yasan Idanuwansa na Tsorata Mutane..He is Hausa man Buh I recpect Him sosai He Know his work sosai sosai fa."Gabadayansu kai suka gyada Domin Shekara Biyu da Fara Aikin sa anan wajen Wlh suna Jin Dadin sa sai dai Wanda baya son gaskiya ne bazai yabe sa ba ammh Mutum ne nagari mai gaskiya da Amana sai dai Illarsa Daya Miskilin Dan Sanda ne Baya son Hayaniya Ballatana Doguwar magana ko su Da Suke karkashinsa bazasu Taba Kirga mganarsa Dasu ba mganarsa ko Ta bangaran aiki ne baya wuce Daya Biyu Zuwa uku..Ko kuma wani Lokacin ya gwammace ya Rubuta a takarda ya bama wani Sargent ya Karanta musu Saboda baya son Doguwar mgana Hakan kamar Takurace Garesa Da Farko suna mai wani kallon mai girman kai da Wulakanci sai da Tafiya Tayi Tafiya suka Fahimci Haka Halinsa yake Yawan mgana Ko Hayaniya Tamkar sune abokan gabansa.

Kafin ka isa ga Office din nashi Sai ga wuce wasu kananan ofishoshi Kamar guda Uku haka kafin ka Hango wani Dan Korido wanda kana Binsa zai kai bakin wannan Babban Ofishin,Wanda Daga bakin Kofar an saka wani Dan Anini da aka Rubuta *DCP MASTUR HABIB DOGUWA..*

Kafin ya saka Hannu ya Bude Office din Sargent Inuwa Dake bayansa yayi saurin Taran gabansa ya saka Hannu Daya ya Bude mai Kofar Office din Daya Sha gyara wanda Daga gani Duk Safiya ana Tsabtacesa Domin ga kamshin nan na Tashi na Turaran wuta Domin kowa yasan DCP Mastur Habib Doguwa akwai Tsabta kuma baya Shiri da kazamai Shiyaaa in masu Shara suka zo kafin su Fara Tsabtace ko"ina Office dinsa ne na Farko wajen gyrawa da Tsabacesa Baya African Time 8:30pm Daidai yake Shigowa Cikin police Station din.

Cikin Takunsa na Jarumta mai Cike da Sanyinsa ya Saka kansa Office din bayan Daga Labbansa yayi Sallama,Sargent Inuwa na Binsa abaya kamar Jela,Kan Kujeransa ta Zama ya zauna Lokaci Daya yana Kiran Sunan Allah sargent Inuwa kuwa sai da ya kame kana ya Sauke kayan Dake Hannunaa Saman Babban Teburin Dake gaban Yallabai Cikin kwarewa ya sake Saramai ya kame Lokaci Daya bai Dago kansa ba yace cikin Wata Murya mai cike da Umarni"Ka kawomin Fayel din nan na Case din old man din nan da yaransa.."Yafada Cikin Harshen Turanci Lokaci Daya yana Jawo System din gabansa ya kunna Ta Dagani Gani aiki mai Muhimmanci zai gudanar Cikin Saramai yace"Ok sir.."Daga haka ya Juya ya Fita bayan ya Rufomai Kofar Office din.

Abunda zai baka mamaki Shine ganin irin Tsaruwan Ofishin Domin Daga ciki akwai wasu Kujeru Guda Hudu na zamani da sukayi ma Office din kwanya Harda Karamin Center Table Atsakiya, sai Daga Chan Kuma Babban Tuburu ne mai Dauke da Manyan Takardu da kuma System Sai Kujeran mai zama Daga Mai kallonsa kuma Kujeru Biyu ne na maraba da baki,Akwai Hotunan Shugabanin Nageria da wasu manya Da ke jagoranta Bataliyan yan sandan Gabadaya,Daga Gefe kuma karamin Daki ne shima na Hutawa Domin Har da karamin gado akwai aciki sai karamin Bandaki Domin Kama ruwa ko wani Lalura in ta kama Mutum
Daga Gefensa Zamansa kuma karamin Fridge na Bukatar ma mallakin wajen In hakan tataso.

Sargent Inuwa bai Dade da Fita ba sai gashi ya Dawo bayan yayi Knooking Daga ciki yayi gyaran Murya kana ya Shiga ya Ijiye Fayel din Saman Tuberin ya Juya ya Fita Ko Kansa bai Dago ba yana ta aiki kan System din gabansa Ammh Idanuwansa sun nan Danne Cikin Bakin Glass dinsa wanda ke karamai kyau da kwarjini Bantaba ganin wanda kayan sanda yayi ma kyau da saka Tsabar Haiba ba irin Mastur Domin Daya kara Girma sai ya zama kamar Mallam Habibu yayi kaki ne Harta Da yanayin Mirmishin su Iri Dayane Tamkar Yana Matashinsa Lokacin Suna Doguwa sai dai wannan Mai kama da Habibun Na yanzu Ilimi da waye da kuma Rayuwa sun Dabaibaye Rayuwarsa Sosai wanda suka kawo Babban Chanji mai yawa da kana gani Zaka Fahimci Hakan.

Ya Zurfi Cikin aikinsa Karar wayarsa ta dawo Dashi Daga Duniyar Daya tafi wanda in ya Shigo Office dinsa ya fara aiki baya kaunar wani abu ya tsaidashi,Karamin Tsaki yaja ya na Zare Glass din Dake Fuskarsa A kasalance ya Jawo Wayoyinsa Duka Biyu A inda Sargent Inuwa ya Ijiye mai Duka Wayoyin Manya ne Kirar Kamfanin Samsung.

Idanuwansa ya lumshe Lokaci Daya yana kara Bude su ganin Sunan mai Kira *SIS RUMANA* lokaci Daya kuma da Faskeken Hotonta Daya bayyana a kan Scrren din wayar nashi Wata kyakyawan Farar Matashiyar yarinya,wacce a Shakaru bazata wuce Shekaru 25 aduniya ba Sai dai yanayin Jikinta ya Boye Hakan Tana da Tsawo ammah ba Sosai ba Daga samanta Har kasa Tana Cike ne,Fuskarta yar Doguwa ce mai Dauke da Dogon Hancinta sai Dan bakinta mai Fadi haka da Kumatunta Turbarkallah masha Ba laifi Tana da Kiban Murjewa da Jin Dadi Tana da Manyan idanuwan da Matsaikatan Gashin Ido Dana Gira, a kallon Farko in kayi mata sai kaji kana so ka kara Domin duk inda ake neman mace mai kyau da aji Da Ilimi Rumana ta wuce nan Daga ganinta Ilimi Ya gama Ratsata Ajikin Hoton ma kamar acikin makaranta aka Dauketa Tana tsaye bakin wani Aji,Tana Sanye da Doguwar Rigarta Baka sai tayi Rolling da Jan Vail Hakama Jakarta Ja ce da Takalmin kafarta Hill wanda ke kara mata Tsawo,Tarin Littafan karatu ne taRumgume a Hannunta Sai Idanuwanta Dake Cikin wani Farin Siririn Gilashi mai kyau Daga ganinsa na kara karfib gani ne na masu karatu Gabadaya Hakoranta suna waje ne har Wushiryanta mai kara mata kyau da kwarjini suka Bayyana cikin Jerun Fararan Hakoranta masu Haske da Daukan Ido Daga gani Duk wata takan Ziyarci Dental Domin Tsabtan Hakorin nata.

Kura mata Hotonta ido yayi yana kallo Har Kiran ya Katse bai Daga ba kansa ya Dafe Lokaci Daya yana wani yamutsa Fuska kamar irin ya gaji Sosai Bayansa ya koma ya Jingina da Kujeran kafin ya Fara Lalubanta Cikin Sanyi Tabbas yasan bai kyauta ba Domin shi yayi mata alkawarin zai kirata din yau da Safe ammh kuma sam ayyuka sun sha mai kai ya manta Yanaji Wayar ta Fara Ringing sai kawai ya Sakata a Speaker ya ijiyeta nan saman Tuburin ya koma ya Jingina da kujeran yana Kara Lumshe Idanuwansa masu Kama da na Mage.

Cikin Sirriyar Muryanta da kuma Natsuwarta Daya santa Dashi Yaji ta Daga wayar tana Fadin"Nayi Fushi Yaya Mastur.."Tafada Cikin yanayin yar Shagwaba Bai Bude Idanuwansa ba ya muskuta yana Fadin"Afuwan kanwata..Ina kwana.."Jin ya gaisheta sai taji kunya Tafara DariyaTana gaishesa ya amsa mata Cikin Muryansa a Dake Tambayan aikinsa Tayi yace Mata Alhamdulillah Sanin Halinsa na Rashin Hayaniya yasa Daga nan Tayi Shuru bata kara mgana ba Sai shine Dakyar ya samu Damar ce mata"Ya karatu..?

Tayi Mirmishi kafin tace"Lafiya kalau..Mungode ma Allah.."Ya Dade bai yi mgana sai chan Taji yace"Allah ya taimaka..Ki maida Hankali Kinji ko..?

Har acikin Ranta Taji Dadi Cikin Karya Murya tacce"Insha Allahu..Ka kularmin da kanka kaji..? Bai bata amsa ba Illah Taji Sautin Motsinsa sai kuma Taji Sanda ya yanke wayar Kurama wayar ido Tayi Tana kallon kyakyawan Hotonsa da kayam yan sanda Wanda aka Daukesa sanda IG na kasa ke basa mikamin Dcp,Tana son Hoton Saboda Kaunar Hoton Datake yi ne yasa ta Sakashi a Wallpaper dinta na Wayarta Saboda Ta Rika ganinsa Duk Lokaci Data Dauki Wayarta.

Haka Allah ya So da bayinsa kuma haka Allah yake Tsara Lamarinsa Ita kanta bata san yaushe bane ko wani Lokaci ne ta wayi Gari taji Zuciyarta na Cike da Kaunar Mastur,Ammh Ta Lakanta Hakan da Wannan Soyayyar ta Faro asali ne tun Zamansa Da yayi agidansu da Koyamata Karatu Dayake yasa ta Shaku Dashi Taji yana Burgeta bata sani ba Har ya Rikide ya koma Soyayyah Wanda Tana Kokarin Boye Abunda acikin Ranta ammh Da Zarar Taji Muryansa Sai Taji ta Rasa Duk Natsuwarta.

Kiran Sunanta da akayi Shiya Dawo Da ita Daga Hayyacinta Tayi Saurin Mikewa Tana gyara zaman Lapcoart Din Dake Jikinta,Suna Tsaka da aiki na taTsaigata ta Kirashi Domin indai Abunda ya Shafi Mastur din bata Hadashi da kowa Wayarta ta saka Cikin Jaka Ta Fice Daga karamin office din lokaci Daya Tana kara gyara zaman Rolling din Vail din Dake Jikinta.

Shi kuwa Mastur bayan ya kashe Wayar sai kuma Jikinsa ya Mutu ya kasa Cigaba da ayyukan Dake gabansa Sai kawai ya Kara gyara zama yana kara Maida Idanuwansa ya Lumshesu kamar mai Barci Lokaci Daya yana Tirayo Wasu abubuwan da suka Gabata da ira iran kulawan Rumana akansa Gabansa ne ya Fadi baya so Ace yau Rumana ta kamu Da Sonsa Domin bai Taba Sonta ba Kallon Kanwarsa yake mata Shi Tuni Zuciyarsa da Duka mafarkinsa suna ga Mace Daya kwara daya Tak Daya bama Dukkan Zuciyarsa da Gangan jikinsa Shi kansa bazai fadi yaushe ne..?ko kuma Wata Rana ne ya kamu da Sonta ba sai Dai kawai ya wayi Gari ne Cikin Soyayyarta mai karfi Wacce Ta Dade acikin Zuciyarsa Tana Yabanya da Rassa.

Ashekarun da suka Gabata abubuwa na Cigaba Dadama sun Faru Dashi da iyalansa Ya Faro Rayuwarsa tun Saurayin Jami"a Dayake ta Fafutukar Neman ilimi wanda ya Zauna agidansu Rumana Har ya kamallah Digree dinsa,sai Yaje Service dinsa ya Dawo Daddy Alhaji Sunusi Tureta da suke Kira Daddy ya shiga ya Fita har ya samu Gurbi a police staff Colloge Acadamy Dake Jos chan yaje yayi Short Service dinsa Ya Fito a matsayin ASP,yayi aiki A bambamtan wurare kamar Kaduna,Zamfara,Kano Lokaci Bayan Lokaci kuma kwazonsa na sawa yana samun karin Girma Shekaru Biyu da suka Gabata ne ya samu Mikamin DCP lokaci Daya kuma ayi Posting Dinsa zuwa wannan Babban Headquater din na Parthercourt,Lokaci Daya suka Bashi Quaters Din ma"aikata inda anan yake Zaune ya mallaki Motan Hawa da kudade da baisa iyakarsu ba da Kudin albashinsa Duk da yayi ma iyayansa Hidima kuma yana kan yi musu Har yau har Gobe bai Gaza ba.


Rumana yarinyar da Har yau har gobe Yake Girmama Muradinta da Burinta na Son karatu da Zama Wata Mace abun Alfaharin Iyayanta Wata Rana ayanzu Haka Rumana Tana University of Lagos Tana Shekarta ta Karshe ne A medicine Alokacin Data Fadamai Ambition dinta bai kalleta a mtsayin wacce Zatayi ba sai gashi ta bashi mamaki yau tana ma Shekararta Ta Karshe ne,Jaruma ce kuma Jajirtattace kan Abunda ta sakama Gaba Mayyar karatu ce ko shi Wani Lokacin yana Sara mata Sai dai Duk yadda yaso Diza ta kasance irin Rumana Burinsa bai Cika ba Tunda ba Ra"ayinta bane,Diza tundaga Secondary Bata Cigaba da makaranta ba Duk kuwa da Kudin Mahaifinta bai zai cega wani Abu na Cigaba da Diza ta samu Bayan Shudewar wannan Shekarun ba abu Daya zai yi Tunawa Shine Bata zauna Haka ba Tashiga makaranta Koyon Sanks Na Shekara Daya Tayi Training har ta kware Sai kuma ta shiga Makarantan Koyar daMakeup Har ta kware ta zama makeupartics,Yanzu haka Ta Bude Classes din a Online na Kiyar da Snaks,Tana Odar ko'ina kake so a Fadin Nageria Ashekaran Daya gabata Daddy ya Gina mata katon Waje Inda akayi Lonching din Bude wajen mai Suna *DIZA SNAKS AND MAKEUP CENTER..* anan Zaria dogara Dake cikin zaria,anyi Lonching din ammh bai Hallarta ba Sai dai Daga Dizan Har Uban Gayyar Mansur sun Turomai Hotonan su Aranar da akayi Murnan Bude wajen.

Banda wannan Abubuwan Guda Biyu bai hango ma Diza wani Cigaba data samu ba,Ammh a wajenta Tana ganin Hakan ma babban Cigabane gareta Domin Ta samu Abunda Take Nema kuma Burinta ya Cika Daga Daddy Har Mommy ba wanda ya Takura mata kan sai Tayi karatu Domin suna Bin Ra"ayinta ne kan Abunda take so ne,Bangaran Uban gayyar Kuwa Zai iya cewa Duka Burinkansa Allah ya Cikamai a yanzu Haka Mansur Ya shiga Siyasa Tsudum Tun Kuruciyarsa yana Da Shekara 25 aduniya ya Nemi Kujeran Kansilan Yankinsu na Zaria Daddy ya goyamai baya kuma ya samu Nasara ayanzu Haka Mansur yafishi kudi da samun Abun Duniya ya mallaki Gidaje Da Motocin Hawa,yakai Hajja da Baba makka da Aiya Sun Hada Hannu Shi da Mastur sun Buge Gidansu sun Sauyamai Fasali ZUWA na zamanii kuma sun Fadadama Ma Babansu kasuwancinsa Yanzu Baba Habibu sai yaga Dama zai je Kasuwa Shagunansa na Hatsi ba su adadi Duka ya saka yara Har yazo ma yau Usmanu awajensa yake cin arziki Tunda shi Jalin nashi yana Tarawa ne suna karewa.
Son Siyasar Mansur ajininsa Take Da kuma Biye ma Muradin Diza Tun bayan kamallah Secondary ya samu nasarar Fadawa Jami"ar ABU dake Zaria inda ya karanci Political Sceince,Kuma Shigarsa makarantan Yazo mai da Nasarori masu yawa Domin Tun yana aji Daya ya Fara Siyasan makaranta,Har takai Suna aji 3, ya rike Mukamin President na Daliban ABU Gabadaya,Bayan Kamallawansa kuma Daddy ya Takamai Baya ya Fada Siyasa,ka"in da Na"in Alokacin Baba Habibu yaso ya nuna Rashin Amincewarsa Mastur ya yi mgana Dashi kan ya barsa yayi Ra"ayinsa Toh in kace abu nan ne Zakaci abinci Cikin Lokaci Kadan Sunan Mansur Sulaiman Doguwa ya Zagaye Zaria da kaduna Gabadaya alokacin Zaben kasililon ya samu Barazana ganinsa yaro kuma bashi da mata ammh kuma Daddy ya Shige mai gaba komai har ya samu kujeran Kansilan Shiyar Zaria,Bayan sun Gama Shekara Biyunsu sun sauka Yanzu Haka Neman Kujeran Chairman yake yi Domin yace sai ya Cikama Diza da Hajja Burinsa sai ya zama gwamna Watarana,Ayanzu Haka Mansur Dake da Kimamin Shekara 29 aduniya ammh kudi da Nasaran Rayuwa sun Lullubesa ya sauya kamar bashi ba kuma Har yau gobe Duk inda ya saka Kafa nan Diza take sakawa sai dai bata zuwa Taronsu na Siyasa ammh Ta karan Rakashi Taronsu na Partynsu Duk wanda yasan Honourable Mansur Doguwa yasan Lady Diza Sunusi Tureta mai mallakin Wajen yin Snaks da kuma Kwalliya mai kayatarwa Ayanzu da Girma ya kamasu akwai Cigaban Rayuwa sosai atare dasu.

Ajiyar rai kawai ya Sauke lokaci Daya ya Bude Dara Daran Idanuwansa kafin ya Dago da kansa yana Mikewa alamun gajiya agogon Hannunsa ya Duba 12:40pm na Rana kansa ya Dafe Lokaci Daya yana Mikewa ganin yadda ya bata Lokaci yana wasu Tunane tunane ko Daya bai yi aikin gabansa ba,Karamin Tsaki yaja kafin ya Ture kujeran Dayake kai ya Mike bai Dauki Komai ba Daga wayoyinsa Har System din nan ya barsu ya Shige karamin Dakin Lokaci Daya yana Balle Botirin Hannun Rigansa bai Dauki Lokaci ba sai gashi ya Fito Fuskarsa da Ruwa alamun alwala yayi Hulan kansa ya ijiye kan Tebur din kafin Ya Tura Kofar Office din ya Fice Domin Zuwa Dan karamin masallacin Dake Cikin Headquater Domin Gudanar da Salla,Dayake Gari ne Daya Hada Mutane Dabam Dabam akwai ma"aikatan da ba Musulmai ba Ko acikin Yan Sanda basu da yawa Shiyasa Inda suke Gudanar da Ibadansu wani Kebenttacen Wajene da suka samar dashi da kansu.



*Yanzu ne muka Shiga Mafarin Gudarin Labarin....Ku cigaba da Bibiyata na Tabbata bazaku yi Nadama ba..*

_Albishirunku Masoyana wannan karan na bude muku wani Shashi na musamman Saboda ku..Ina masu Bukatan Atalla musu Hajarsu Ko wani iri ne Domin samun costumer ta ko"ina..? Ku garzayo kakarku ta kusa yanke saka Zan Tallata muku Hajarku a Duka Shafukana Domin inganta Sana"arku da kuma Samun Cinikaya mai Tsabta da kuma kara Hada hada wajen Masi siye da Siyarwa mai Bukatar A tallata mata Hajjarta Zata iya min mgana kai Tsaye ta wannan Lambar Tawa 09069067488 domin karin Bayani...Sai kunzo Kunsan dai mai kasuwa Shi ke da Riba.._

*Domin zama Daya Daga cikin wadanda zasu karanta Labarin SADAUKARWAR SO..! Zaku Biya kudin karatunku kamar haka Masu amfani da Banki Zasu Tura â‚?300 ta wannan asusun banki 0552179550 Jamila umar gtb,Masu Katin waya kuma zasu Turo â‚?400, ta wannan lambar wayar 09069067488 Adauki Hoton katin sai aturo kai Tsaye mutanenmu na Niger kuma zasu Tuntubi wannan lambar kamar haka +22794775574 domin karin bayani,Insha Allahu mutum zai tsinci kansa a paid group ina maraba da ku masoyana Nagode*






*Janafty...*
1/1/22, 18:53 - Maryam Badmsi: *SADAUKARWAR SO..!!*
_(Labarin Yan"uwantaka,Soyayyah Tare da Sadaukarwa)_

*Wattpad:@Jamilaumar315*
*Mallakar:Jamilaumar(Janafty)*

*Page9�⃣*




*Zaria..*
_Hanwanfulani_

Kofar Dakinta Ta Turo ta Fito Zuwa Falon kasa Lokaci Daya Tana Mika da Mitsike ido Domin Barcin bai isheta ba,Hamma ta saki bayan ta saka Bayan Hannunta Ta Rufe bakin,kan Daya Daga Cikin manyan Royal Chairs Din da sukayi ma Falon kwanya Ta zauna Tana Dora kafarta Kan kujeran dayan kuma Tana kara Mutsiketa kan Tattausan Cafet din Dake malale a tsakar Katon Falon Dayaji kayan More Rayuwa.

Doguwar macece Fara mai Dauke da Doguwar Fuska Da karan Hanci Dogo,Bata da kiba Lange Lange Take har yanzu bata Sauya ba sai dai ta Kara Murjewan Girma da kuma Hutu da wayewa,Farar Fuskarta kamar na Mahaifiyarta Hajiya Asiya Take sai dai Tswon kafan na Alhaji Sunusi ta Debo da karan Hancinsa,Rayuwa da kuma Girma sun Sauyata ammh Barkwancinta da Surutunta suna nan Kama Daga yadda take wani Motsi da bakinta Kamar Tana so Tayi mgana kuma ba Mganar take yi ba Hankalinta dai kacokan ta maida kan wayarta Daga gani Abu take yi mai muhimmaci kuma ya Dauke mata Hankali
Khadija Sunusi Tureta kenan Wacce akafi Sani Diza.

Wayarta Kirar iphone12 ce a hannunta Tana Sanye da kayan Barci Riga da wando Farare masu Taushi kanta da irin Hulanan mai Taushi na Barci mai Boye Duka kan Mutum aciki ,Gabadaya Hankalinta ya tafi kan Mutanen Dake son Oder Cake da Donut Duk ayau Diza Tayi suna ta Shahara Tana Harka da masu kudi da masu Mulki da masu garin Dayake tasan kan aikinta kuma ta kware akai Shiyasa Duk wanda Tayi ma aiki Sai ya kara Nemanta Tana Harka da Social Media Sosai Saboda Tanan take Dora Duka Harkokinta kuma Tana samun kasuwa Ba Laifi Duk da achan Catering din nata Tana da ma"ikata mata masu kular mata da wajen da masu aikin Bata Cika Zuwa ta Tube Tayi aiki ba sai ya zama Dole,ammh Takan je Lokaci bayan Lokaci Duba mike Faruwa, duk suna mgana Dasu ta waya, Musamman Bangaran Makeup dinta Wanda Daga ita Hauwa ce wata Ma"ikaciyarta masu kula da Wajen so in ayi Buking Makeup ma Tafi yawan zuwa Bangaran Domin yima wadanda sukayi Buking Din Makeup din bata Zuwa Gida In kuma Bukatar Hakan Tataso sai dai Hauwa Taje.

Diza Ta tara kudi da bata san iyakarasu ba Bayan Kudin Aikinta Daddy Duk wata yana Tura mata Kudi acikin Bankinta,Tmai mgana ya bari yace Hakkinsa ne,Diza bata sin Takura Ballatana wani abunda zai zama Takura gareta Shiyasa Taki Karatu Tafi son social Life Dinta kuma Iyayanta sun mara Mata Baya,Arayuwarta Babu Abunda Ta Nema ta rasa komai Tana samunsa Daidai Gwargwado.

Abu Dayane Bata samu ba Har yau Abunda Take kwana Dashi Aranta Tana Tashi..Shima Din ta Dangantanshi da Lokaci ne bai yi ba ammh Tabbss In Lokaci yayi Zata mallaki Abunda Take so,Duk yadda suka Shaku Da Mansur Bata Taba gayamai wannan Sirrin Zuciyar nata ba Bata san Dalili ba Gashi Dai baimai yawan Fara"a bane gareta bamai yawan Dariya bane gareta ba,bamai yawan Mata Wasa bane Bata ganin Sakin fuskarsa bane Ballatana Sakin Jiki Da Mutane Haka Allah yayi sa Kuma ahakan Take jin sonsa Aranta Kamar tama fi sonsa akan karan kanta Wanda Gashi dai ba wata Shakuwa sai Tsakanin Girmamawa Ta yaya da kanwa Ammh kuma Batasan ya akayi ba Itadai ta wayi Gari da Soyayarsa wacce kullum Take Huda Duka Gabobinta Tana kara Ninkaya acikin Zuciyarta.

Sai da Ta gama Duba Duka Sakon nin Dake Cikin wayarta,Hauwa ta Kira sukayi mgana kan Wadanda sukayi Buking din kwalliya sun Rabu kan Zata Shigo Zuwa anjuma Merry ta kira sukayi mgana kan Gidan Sarki suna Bukatar oder Cake,Wajen Spicess 3000,Daman ta Sanar dasu Ta kara kira ne Taji komai na Tafiya Daidai Merry Ta Tabbatar mata da nan da Zuwa 1pm komai zai kamallah Sai da suka gama wayar ne ta kalli agogon wayarta pass 10,Cikinta ta Shafa Domin Tana jin Yunwa Tashi Tayi Tana wani naka naka da Fuska Tana kallon Upstairs Baki Ta Tura gaba Ta Nufi Hanyar Kitchen bayan ta Cillar da wayarta kan kujera kamar ta Wurgan da wani abun banza.

Da Sallama ta Shiga Kitchen din Ganin Fadime Datake kira Mama wacce ta Manyanta yanzu Kimamin Shekaru 54 aduniiya Fadime Ta Dago Tana Washe baki tace"A"a Uwar Dakina Har kin tashi..?

Diza Ta Daka Tsalle ta Dane kan Kitchen Cabinet Tana Fadin"Na tashi Mama..Na Fito Ma ko"ina is To Booring Daddy da Mommy basu Sauko ba.."Ta Fada Tana Tura Baki irin na Shagwabbun yaranan da suka samu gata.
Fadime na Soya kwai Daya Cika Kamshin Kitchen din Tace"Zasu Sauko yanzu ai Uwar Dakina.."

Diza TaRausayar dakai Tana Fadin"Ina kwana Mama Fadime.. ? Tana Saka kwan Cikin wani Filet take Fadin"Lafiya lau UwarDakina ya gajiya..? Saukowa Tayi Daga kan Cabinet din Tana Fadin"Ba wata gajiya fa Mama..Ni yau bana jin cin irin wannan Breakafsat din naku Mama bari na Leka wajen Hajja Allah sa Kunu da Kosai Tayi Mana.."

Mama Fadime na Dariya Tace"Hanzarta Domin Kisan Bata Kiyuwan yin kosai Hajja.."Diza ta Fice tana Dariya Fita Tayi Ta koma katayyacen Dakinta kamar Dakin Wata Matar Aure Saboda yadda yaji kayan alatun Rayuwa Babban Wardrope dinta ta Bude ta Dauki Wata Abayarta ta Zura bayan ta Cire kayan Barcin Jikinta Sai ta Dauki Bakin gyalen Abayan ta Yane kanta Dashi,Ta Fito Falo Bayan ta Sauya takalmin kafarta Direct Fita Tayi zuwa Falo ta Dauki Wayarta kana ta fita zuwa Haraban Gidan inda Tsala Tsalan Motoci guda uku suke Fake a Wajen Daya nata ne Daya kuma na Hajiya Asiya ne Dayan ce Ta Alhaji Sunusi.

Gaisawa Sukayi da Baba megadi kana ya bude mata karamar kofa ta Fice Tana Fita Taga matasa Da yawa akofar gidansu Hajja Mirmishin Saman Lebe Tayi Domin tasan mai girma Honourable suke jira Dama Jiya ya gayama ta yau zasu yi Taro da Shugaban Jamiya anan Zaria Bata kula kowa ba duk da wasu sun santa aido Suna ta mata barka da Fitowa Bata tankasu ba Ta Tura Get din Gidan Baba Habibu daya Dawo na Zamani mai Dauke da Sashe Biyu.

Shashen Farkon na Su Hajja ne Shashen Ciki kuma na Mansur da Mastur wanda ke Dauke da Babban Falo sai Kitchen sai Bedroom guda Biyu Daya na Mansur Daya na Mastur ne Gabadaya Gidan kamar bashi ba Bambamacinsa Dana su Diza kawai Bene,Ammh Shima gidan sun kashemai kudi wajen Tsarashi Filin Dake kusa dasu suka Siye sukaHadeshi da Gidansu Shiyasa Filin ya wadata Har aka samu ma"adanar Motoci da Dan Haraban Gidan da suka Fitar ma Get.

Tana Shigowa Haraban gidan da bai Cika Girma ba sosai Taga Mashin din Baba Habiba Domin Yaki yarda Mastur ya siya masa Mota yace su dai su hau shi Mashin dinsa itace Daidai Dashi,Dole suka kyalesa ammh Sun Sauyamai da Roba Roba mai kyau ta Zamani,Sai Motar Mansur kirar Matric Baka,Tana gani ta gane dukkansu basu Fita ba kenan kai Tsaye kofar da sadata da Babban Falon Gidan ta Nufa ta Tura da Sallama Cikin Siririyar Muryanta ta Shiga.

Aiya ce ke Zaune kan Daya Daga Cikin kujerun katon Falon Tana kallo Duk da Tsufa ya kara kamata ammh Jin dadi sun sauka Har yanzu da karfinta sai dai Ciwociwo na Tsoffafi wadanda ba"a rabasu Dashi Tana jin muryan Diza Ta Dago Cikin Fara"a Tana Fadin"Muryan wa nake kamar ta Hadizatu..?

Tafada Cikin muryan Tsufa Wanda Daman kanta Duk ya Cika da Furfura,Diza data kariso ta zauna agefenta Tace cikin Tura baki   "Ni fa Aiya ba sunana Hadizatu ba suna Khadija ko kice min Diza.."Tabe baki Aiya Tayi Tana Fadin"Kwaji Dashi dai..Ku yaran zamanin nan akwai Sanabe..Sunanki suna ne mai Daraja sunan matar ma"aki Sallallahu alaihi wasallam Kuma itace mace ta Farko Data Fara Karban kalmar Shahada a mata kuma ta bada Rabin Dukiyanta wajen yima addinin Allah Hidima ammh Shine kike wasa da sunanki kina maidashi wani wai Dizza.."Ta fada Cikin bayanna Takaichinta Dariya ta kama Diza ta Fara kyakyatawa Sai ga Hajja ta Fito Daga Cikin kitchen din Dake Falon Ta kara zama Babban Mace,Ta kara kyau Domin yazu Rayuwa tayi musu Daidai Tana Fadin"Aiya ke da wa kuma..?

Sai kuma Taga Diza Baki ta Washe Tana Fadin"Diza ashe kece..?ni danaji mgar Aiya ma na Zata Dan albarkan nanne yazo yana Tsokarnata Mansur.."Diza ta Sauko Daga kan kujera ta Duka tana gaida Hajja ta amsa Cikin Fara"a Tana Tambayanta iyayaanta tace suna Lafiya,Kafin tatashi ta koma ta zauna Tana Fadin"Hajja ina Baba..?baifito bane..?

Hajja Tace"Yanzu zai Fito..Na barsa yana wanka ne Dazu.."Diza tace"Ok..Allah sa Koko da kosai kikayi mana Hajja Shi nazo sha nagaji da cin Kwai da Tea wlh.."Hajja na Dariya tace"Kamar kin sani..Yau Daga Baban Mansur Har Mansur din Shi sukace suna son su karya Dashi..Sha kurumakin yanzu zan karisa Toyan kosan.."Tsalle Diza taBuga Tana Fadin"Yauwa..Hajjanmu Har naji Dadi wlh..Muje na Tayaki Soyan Kosan.."

Hajja Tayi Saurin Fadin"a"a barshi..Kwaskon Karshe ya Ragemin Zan karisa aikina Kinji Diza.."Diza ta bata rai Zatayi mgana Hajja tace"kar ki damu Maza Tashi ki leka Abokin naki Yanzu ya bar nan Naji yana Fadin suna da Taro kilama yana chan yana yana Shiriritarsa na Fama.."Mirmishi Diza Tayi ta Mike Tana Fadin"Shikeman Hajja Tunda kin Hanani Tayaki aikin..Bari na lekasa na Dawo.."

Hajja Tace"Yauwa kafin ku Dawo na Gama komai Diyata.."Dariya Diza Tayi Aiya Dake Zaune Tatabe baki Tana Fadin"Katon Saurayi ammh Har yau bai bar Shiririta ba ni bansa ma ya akayi aka Zabe wannan Talasurin ba wlh..Allah sarki Megidana Mastur Namijin Duniya Dan Sanda mai ma kasar sa Hidima.."Daga Hajja Har Diza Dariya suka saka Diza na Ficewa Take Fadin"Zaki maimaita agabansa.."Tana Fada ta Fice ta Fita Zuwa Shashen su Mansur din.

Knooking Ta Farayi Daga Kofar Falon Mansur Daya Ke cikin Dakinsa yana Kokarin Saka Links dinsa na rigar Blue din Shaddan Dake Jikinsa yayi Tsai da Rai sai kuma ya kara,jin Knooking din Cikin Tunanin ko waye ya Fito Daga Bedroom dinsa yana Kokarin saka Links Din Kofar Falon ya isa ya Zare Key din Jiki Bayan ya Bude sai ga Diza ta Bayyana Tana Tsaye Tana kallonsa Shima Idon ya kafeta Dashi kamar zai Cinyeta.
Aduniya in akwai Hallitan Da Baya gajiya da kallo Diza ce..Ita ce wacce ke jan Ragamar Rayuwarsa Gabadaya,Ko Bata gabansa ya Riga ya gama Zana Duka Hotonta acikin Zuciyarsa ko Bata Tare Dashi Da Zarar ya kadaice ita yake gani kuma yaji Har ya samu Sukuni Duk Duniya Bayan Iyayansa da Yayansa Mastur bai Taba son Abu kamar Ransa Kamar yadda yake son Diza ba zai iya Mutuwa Duk Ranar Daya Rasata,
Wani kallon kauna da Muradi mai Girma yake Jifanta Dashi   cikin Matsakaitan Idanuwansa Mansur ya Sauya ya Kara Girma Da Cikar mazantaka,Kallo Daya zakamai kaga kamar Hoton Maryama ce saboda Tsabar yadda kamminsu ya Bayyana Mansur Dogo ne,Sai dai ba Sosai ba Bai kama Kafar Tsawon Mastur ba A kafadan Mastur yake in suka Jera da juna,Mansur yana da Haske sosai Har yafi ma Mastur sai dai Shi Fuskarsa Mai Yalwar Fara"a ce da Barkwanci mai wasa da Dariya da Dadin Zama,Mansur ya zama Cikakken Mutum da Cikar Zati da kamala a Shekarunsa Daya Taka Matakin Rayuwa mai Cike da Nasara da Sa"a Mutane Dadama suna mamakin ganinsa yaro Matashi Ya samu Sa"ar Rayuwa har yake amsa sunan Honourable Mansur Sulaiman Doguwa.

Diza ce Taga ya Shagala da kallonta sai ta Saka Gefen Mayafinta Ta Daki Fuskarsa Tana Fadin"Wannan kallon fa  My Honourable,ko baka Taba ganina bane..? Daman haka take Kiransa Shi kuma sai yace mata My Firstlady

Sai Lokacin Mansur ya Dawo Daga Cikin Hayyacinsa Ya saki ajiyar rai bai ce mata komai ba ya Bata Hanya yana Fadin"Bismillah My First lady.."Tayi Dariya kawai Ta Shige Shikuma yamaida kofar ya Rufe yaBiyo bayanta yana Fadin"Kamar kin sani yanzu nake Shirin Kiranki..'"

Tana Zama kan Daya Daga Cikin kujerun Falon Take Fadin"Gani nazo..Ai kasan ko baka nemeni ba Duk inda aka ga gwamna sai anga Firstlady dinsa.."Ta karishe Tana Dagamai Gira Dariya yayi yana Karisa Saka Links Dinsa yace"Nagode My Firstlady.."

Tana Mirmishi ta Kalleshi Sama da kasa Tana Dariya Shima sai yabi kansa da kallo yana Fadin"Ya akayi ne..? Ko Kayan basu yi bane na Sauya su..?

Kai ta Girgiza Tana Fadin"A"a..Kayi kyau My Honourable na..kayan sun maka kyau sosai..Ammh pass 8 fa kada ka makara wajen Taron.."Tafada Tana kallonsa agogon Azurfan Dake Hannunsa ya kai Duba kafin ya dan Yamutsa Fuska yana Fadin"Sai10am za"a Fara Taron..Bari na je na Dauko Hulata da wayata da key din Motata muje Shashen Hajja mu karya kafin na wuce ko..? Zaki fita yau ne ko zakimin Rakiya ne..?

Diza Tace"Eh zan je Office Anjuma akwai wadanda sukayi Bukking din kwalliya..kuma Hauwa Zataje House Service ni kadai ce.."

Kai ya gyadaa mata yana Fadin"Ok..Bari na shiga na Fito.."Yafada yana wucewa Ciki ita kuma sai ta sauke idonta kan Karamin Frime din Dake kan Tv Stand din dake Falon Hoton Mastur ne da Mansur Mastur da Uniforms dinsa ajikinsa Ranar da aka bashi Rank din Zama Dcp ne,Abuja Mansur din yaje mai shine Sukayi Hoton Sun yi Bala'in kyau Mastur yana Rike da Kafadan Mansur Dukkansu Suna Dariya,Fararan Hakoransu a waje in ga gansu Zaka Fahimci Tsantsan kaunar juna atsakaninsu.

Hoton ta kurama Ido ko Kiftawa batayi Gabadaya Hankalinta ya tafi kan Mastur shi take kallo Lokaci Daya Tana Sakin Mirmishi Wani Shauki da muradi mai girma yana kara Shiga Zuciyarta Bata ma san Mansur ya Fito ba sai da Taji mganarsa sama sama yana cewa Tatashi su tafi Kasalance ta Mike tana gyara Mayafin kanta Kallonta yayi kafin ya Dan Dakata yana Fadin"Kash..Nayi mantuwa.."

Kallonsa Tayi Tana Fadin"Ai daman baka Rabo da mantuwa..me kuma ka manta..? Wayarsa yake Dannawa Loksci Daya yana Fadin"Ban kira Ya Mastur ba Diza..Kuma Duk Safiya Bayan su Baba dashi nake Fara mgana kafin na Fita.."Komawa Tayi ta zauna Ranta na mata Fari yau zataji muryansa Data kwana Tana Marari ba wata Shakuwa Tsakaninsu Shiyasa Take jin kunyar kiransa ammh Lokaci Bayan Lokaci suna Waya Dashi ta wayar Mansur,Abunda ke bata mamaki Kusan kullum sai ya Kira Daddy ko Mommy ta Ammh Ita bai Taba kiranta ba Ko Da sau Daya itama Bata Kiransa ba Saboda Bata san Tana ina Zata Fara ba.

Mansur ta kura ma Ido ganin ya kara bata rai Ido ta waro mai Tana Fadin"Ya ya dai..? Yana zama gefenta yace"Bai Daga kiran ba.."Ta rausayar dakai Tana Fadin"Kila yana Aiki ne..Kasan fa baya Hada aikinsa da komai Gwamna na ."

Bai samu Zarafin mgana ba Dayar wayarsa Kiran Samsung wacce Mastur ya siya musu iri Daya, ta fara Tsuwwa Ya Daga yana mgana Yan Siyasansu ne ya Dade yana mgama kafin ya katse Kiran Daidai Lokacin da Dayan wayar tasa Ta Dauki Neman agaji Tare da Shi Da Diza suka kai kallonsu kan Wayar sunan wanda suka gani ne ya saka kowannensu Sauke Boyayyiyar ajiyar Zuciya
Ya Mastur ne Baro baro yake Kiran Wayar Mansur da Sauri ya Dauki wayan ya Daga Cikin Shagwaba kamar karamin yaro yace"Nayi fushi ya Mastur..Ban kiraka ba kuma baka kirani ba Tun Safe..Na kuma kiraka baka Dauki kirana ba Mansur ne fa Mansur dinka Wanda baka da kamarsa.."

Yafada yana Tura baki,Diza kallonsa kawai take Tana yar Dariya sanin Halin Mansur Shi Haka yake Rayuwarsa mai Sauki ce,Hulan kansa Zanna Bukar ya Tura gefe Lokaci Daya ya saka wayar Speaker Daidai Lokacin da Mastur yayi Mirmishi Cikin Kayattaciyar Muryansa yace"Honourable Mansur Sulaiman Doguwa..Am Sorry Sir.."

Yanayin yadda yayi mganar sai da ta saka Diza Taji bugun Zuciya Mansur kuwa Baki ya washe yana Fadin"Kai ne Sir ai Yaya..Ya aikin..? Ka tashi lafiya..?kaci abinci..?kana wajen aiki ne..? Mirmishi kawai yayi Lokaci Daya yana Sagala wayar a kunnuwansa da Hannu Daya Dayan Hannun kuma yana Danna System dinsa Sargent Inuwa na Tsaye agefensa yana Jiran Umarni.
Cikin Sanyin sa yace"Oh..Wata Tambaya zan Fara amsaka Daga Ciki. ?

Mansur yace"Duka yaya Nidai.."Yafada yana Dariya yana kallon Diza Datayi Kasake Tana Sauraran Muryan da Bata gajiya da Sauraranta ko Jinta Mastur kuma Dagachan Bangaran Bai yi Dariya ba sai dai ya saki Fuskansa Cikin Dakiya yace"Komai Lafiya..Mansur Fatan kaima haka..? Yafada Kamar an sashi Dole Sargent Inuwa na Gefe aransa yana ayyana Duk Duniya banda wannan Dan"uwan yallabai bai mai sakashi mgana takai Goma Arana Ko da su bai taba gani ba ammh yasha jin wayarsu Yanajin yadda Mansur din ke yawan saka Ogan nasu mgana ko bai so ba

Mansur kuwa Daga Chan Bangaran ya tsike da Zuba yana gayamai Taron da zasu yi da Irin kayan da ya saka ya Karishe da Fadin"Yaya Mastur Shaddan fa Dana Tura maka Hotonta nasakafa..Diza tace nayi kyau Sosaifa ko nayi maka Hoto ne kagani..? Zamu yi Vidoe callne..?

Kansa ya Dafe kawai yana Dan Jizan Lebensa jingina yayi da Jikin Kujeran Dayake kai bayan ya Ture Computer din gabansa Da Hannu ya Nuna ma Sargent Inuwa Fayel din gabansa Har ya gane me yake Nufi da Sauri ya kame mai Lokaci Daya ya Dauki Fayel din ya Fice sai Lokacin Mastur yayi mgana yana Jan Numfashi saboda kiran Sunan Diza da Mansur yayi sai da Zuciyarsa ta amsa.

Cikin Sanyin Murya yace"A"a ina aiki ne Mansur..ammh nasan kanina mai kyau ne..Kowani kaya ya saka suna mai kyau.."Yafada yana Dan Mirmishi Mansur yace"Daz my Yaya ni kadai..Yaya when zaka zo ne..? Wlh muna kewarka Hajja Baba Aiya Mommy,Daddy Har da Diza Gata agefena.."

Mastur yaji gabansa ya Fadi Cikin Taushin Murya yace"Ok..Tare zaku Tafi Taron kenan..? Mansur ka Daina Zuwa da yarinyar nan cikin Taron maza fa Ita macece ka kiyaye Abunda nake gayamaka.."Ya karishe Kamar Kamar Zuciyarsa Zata Fito Saboda Takaichi da Kishi Sanin Halin Mansur din Da Diza yawo kamar sun ci kafar kare Last Month yaje Zaria bai kwana ba ko da yaje basa nan wai Suna Catering din Dizan Tun Safe Dagachan Mansur din zai je Taron su na Siyasa Zata Rakashi Saboda Takaichi ko Jiransu bai yi ba shi da Tawagarsa suka Dauki Hanyar Porthercourt Daman Abuja suka zo Sunyi Meeting da IGP na kasa.

Mansur ya kalli Diza itama Ta kallesa Tana Tura baki Abunda na Cimata Tuwo a kwarya Intaga yadda Mastur bai Damu da ita ba Ballatana Lamarinta Sai dai bai Chanza ba yana nan da Fadansa da Tsare Gidansa Data Sanshi Dashi Tuntuni.

Mansur yace"Ni ba Tare zamu ba..Catering dinta zata tafi Tana da aiki...Gata ma ku gaisa.."Yafada yana Tura mata Wayar gabanta Mastur yayi Saurin Bude idanuaansa jin Sallamar Diza Cikin Siririyar Muryanta Bai amsa mata Sai da ya Fara Kokuwa da Numfashinsa kafin yace"Kina lafiya..?

Daman ai gaisuwansa bata wuce haka tace"Lafiyata kalau ya aiki..? Kamar baya som mganar yace"Alhamdulillah.'Daga nan bai kara mgana ba sai Kokuwa yake da Numfashinsa itama sai ta kasa mgana Karban Wayar Mansur yayi yana Fadin"Wai Yaya Mastur Ita har yau Diza Bata Saki Jiki Dakai ba..Tsoronka Take ji Tun Lokacin ina ce mata kana Duka.."Yafada yana Dariya Mastur bai biye masa ba yace"Ka tashi ka tafi kada ka makara..Ka tuna ka girma yanzu kai ba yaro bane..Mansur din Baya Bashi bane na yanzu Honourable ne wanda Hakkin Jama"a Dadama ke kansa.."

Cikim kwamciyar Hankali yake mganar wanda duk wanda yaji Sai Muryan ta sakamai Natsuwa Mansur yace'Insha Allahu Yayana.."Mastur yace"Ina aiki ne..U took Later..Kada ka manta ka Kira Baba Sule ka gaishesa bana son in kara maka mgana Mansur ok..?
Da sauri yace"Allah zankirasa yaya.."Gud..yace Lokaci Daya yana katse Kiran.

Diza Datayi wani Sanyi da ita ya kallah yana Fadin"Bari na Kira Baba Sule kamar yadda yaya yace..kije ganin nan zuwa.."Bata yi musu ba ta mike Dauke da wayarta Sanin Da Tayi bazaiTaba waya da Mahaifinsa agabanta ba Bata san meyasa Mansur ba wata Jituwa ko Shakuwa Tsakaninsa da Yan"uwansa ta Bangaran Uba ba Duk ko da yadda Baba Sule ke yawan zuwa abaya ganin mansur din Yanzu ne ma ya Rage zuwa Saboda Shekarin sun ja,iyalai sun kara yawa da wasu matsalolin Rayuwa Har Mastur da Ba D'ansa ba yana Kiransa aka kai suna gaisawa,Shi haka yake kowa sai dai kaji yana yabonsa Haka Abba da Umma na Sokoto Suna ji da Mastur kamar Dan su na Cikinsu Kullun sai ya Kirasu sungaisa Yana da Kyawawan Hallayan Ga ita ne kadai bashi da kyawawan mu"amala.

Tana Fita ya Kira Baba Sulen suka gaisa Bashi da lafiya ne Typiod bai ma sani ba Mastur din ya Kirashi ya gayamai Baba Sule yace ma Mansur yaushe zaizo yace sai ya samu Lokaci nan yake gayamai Bikin kanwarsa Sakina ya taso..Kuma Auran Yayarsa Maryama ya kare Tana Gida Mansur yace sai ya samu Lokaci zai zo Insha Allahu Daganan suka Rabu ba wata Shakuwa Ballatana Fahimtar juna Baba sule Koda yaushe in ya Tuna sai yayi Hawaye Ba kowa bane Silan komai sai goggo Da yau Mansur a wajensa ya tashi Daya Tabbata Ya Fahimci acikin ya"yansa shi na Dabam ne.

Chan Shashen Su Hajja ya iske Diza Baba Habibu ya Fito,Daman sungaisa Tun Safe Zaman karyawa sukayi Dukkansu Aiya sai Tsokanarsa Take yana Ramawa ko Hajja Ta Tare mai Baba Dai na jinsu yana Dariya Yana gama karyawa yayi musu Sallama ya Fice Zuwa kasuwa Mansur ma bai jima ba ya Fita Domin Samarin anguwan da matasa sun Cika kofar Gidan Suna Jiransa Dakyar ya samu ya Fitar da Motarsa Saida ya sallamesu kana suka Raka Motarsa da sai kayi Gwamna Honourable Mansur Har Bakin Titi.

Diza kuwa Nan ta kai Har 12 suna Hira dasu Hajja kana ta baro Gidan Zuwa gidansu ta iske Daddy ya Fita sai Mommy Da Tayi bakuwa kawarta Hajiya Baraka wacce suke Business Tare,suna Zaune ne afalon Mommy na sama chan ta shiga suka gaisa kana taSauko ta Fada Dakinta wanka Tayi ta Shirya Cikin Doguwar Jallabiya ta yane kanta da Vail din Rigar Daman ita Duk kayanta Jallabiya ne Saboda Tana sonsu sosai,Takalminta ta saka ta Dauko karamar Jakarta ta Fito Ta Shiga Kitchen ta samu Mama Fadime na Girki tayi mata sallama Tace Zata wajen aiki,Daganan ta Haura sama Tayi ma Mommy Sallama ta kuma Karbi key din Motarta tace yau da ita Zata Fita.

Daga Gidan Direct Dogarawa ta wuce Tanayi Tana Duba agogon Fatan Dake Hannunta Bata so Tayi african Time koda ta ta samu Mutum Biyu na Jiranta,Rigar aikinta kawai ta Dora a saman Kayanta ta Fara aiki Daman sunyi mgana da Hauwa Ta wuce,So take tagama Ta Leka Cikin Catering Taga Abubuwan Dake wakana anan wajen.



_Albishirunku Masoyana wannan karan na bude muku wani Shashi na musamman Saboda ku..Ina masu Bukatan Atalla musu Hajarsu Ko wani iri ne Domin samun costumer ta ko"ina..? Ku garzayo kakarku ta kusa yanke saka Zan Tallata muku Hajarku a Duka Shafukana Domin inganta Sana"arku da kuma Samun Cinikaya mai Tsabta da kuma kara Hada hada wajen Masi siye da Siyarwa mai Bukatar A tallata mata Hajjarta Zata iya min mgana kai Tsaye ta wannan Lambar Tawa 09069067488 domin karin Bayani...Sai kunzo Kunsan dai mai kasuwa Shi ke da Riba.._

*Domin zama Daya Daga cikin wadanda zasu karanta Labarin SADAUKARWAR SO..! Zaku Biya kudin karatunku kamar haka Masu amfani da Banki Zasu Tura â‚?300 ta wannan asusun banki 0552179550 Jamila umar gtb,Masu Katin waya kuma zasu Turo â‚?400, ta wannan lambar wayar 09069067488 Adauki Hoton katin sai aturo kai Tsaye mutanenmu na Niger kuma zasu Tuntubi wannan lambar kamar haka +22794775574 domin karin bayani,Insha Allahu mutum zai tsinci kansa a paid group ina maraba da ku masoyana Nagode*



*Janafty...*
1/1/22, 18:53 - Maryam Badmsi: *SADAUKARWAR SO..!!*
_(Labarin Yan"uwantaka,Soyayyah Tare da Sadaukarwa)_

*Wattpad:@Jamilaumar315*
*Mallakar:Jamilaumar(Janafty)*



_*Assalamu Alaikum Fanmily ya Jimarin zaman jirana..? Daman na sanar daku zaku jini Shuru Saboda auran kanwata da akayi Satin Daya wuce Masha Allah Alhamdulillah anyi Taro Lafiya an Tashi Lafiya ankai Amarya dakinta lafiya Fati na�😘 da Angonta Muhammad Tukur Allah ya basu zaman lafiya da Hakuri da Juna,da Wannan zanyi amfani na mika sakon Godiya da Bangajiya ga Bakin mu da sukazo Daga nesa Dana kusa da wadanda basu samu zuwa ba ammah sun bimu da Fatan alheri ,sai kuma Masoyana da yan"uwana marubuta da sukayi ta kwararama Fati na addu"an zaman lafiya Dukkan ku mun gode Allah ya saka da alheri Allahu ya bar zumunci Tanque all.._*



*Page1�⃣1�⃣*


"Sakon daya Turomata Shi ya Wanke mata zuciya har taji Kwarin gwiwan Cigaba da karatunta ta dauki lokaci mai Tsawo kafin Tattara komai gefe Daya ta kwanta Bayan ta Saka Hoton Mastur Gaba tana Kallo Tana auna Yadda take kaunar wannan Bawan Allah wanda Rabonta Dashi Tafi Shekara Hudu Tun Tana aji Biyu a makaranta lokacin tazo Hutu gida Shi kuma yazo gaida su Abba.

Haduwarsu Kamar almara ce Domin bazata iya Dora komai a game da Haduwar tasu ba bayan gaisuwa da Tambayan karatu Wata mgana bata Shiga Tsakaninsu ba bai wani Jima ba ya Tafi Lokacin yana Kano ne yana aiki,kafin kuma ya samu karin Girma Rumana Bazata iya Fadan Lokacin Dataji ta kamu da matsananciyar Soyayyar Mastur ba sai dai Hakan ya samo asali ne Daga Burgenta Da yake yi da kwazonsa da kuma kyawawan Dabi"unsa da kowa yake Mgana akansa.

Ya bar Gidansu Tun Bayan Daya gama Digree dinsa Azaria yaje yayi Service dinsa Har ya tafi Staff Collage Basu kara Haduwa ba,har ya Dawo Lokacin ita kuma ta Fara karatu anan Uduth kafin ta samu Course din Data ke Nema tatafi University of Lagos ta Fara karantar Medicine Kuma Mastur ya Taimaka Wajen zamowarta mai kwazo kuma ya bata kwarin gwiwa kan Abunda tasakama Gaba Saboda Farincikinsa yasa Ta Zage Damtse ganin Ta Zama Likita Ta lura Dashi akwai son Mace mai son Karatu da kwazo Shiyasa ta Dage.

Mastur baya Cika Hawa Sociol Media Kullim aiki kamar agogo Waya ma ba koda yaushe kake Samunsa ba ita da kanta ta Dauki Lambarsa a wayar Umma take Kiransa,kullun in ta Kirashi sai ya Tambayi mai mgana Wannan Dalilin yasa Bayan sun Hadu agidansu Lokacin Dayazo gaida su Umma ta karbi Wayarsa Tayi Saving din Sunanta.

Tana ji aranta Burinta zai Cika Da Zarar ta kamallah Karatu bata Damu da yanayinsa ba Tana Lakanta da Abun da Haka Nature Rayuwarsa Take abun Har mamaki yake bata bashi da Amini ko Aboki Sai Dan"uwansa Shi kadai ne Kaninsa kuma Amininsa wanda bai da Kamarsa sai Abokinsa guda Daya wato abokin aikinsa Acp Saleem kabir kumo tare suka samu Horo a Jos, Bazata iya Dora wani abu kan Mansur ba ko Diza Rabonsu da juna Tun Suna yara Sau Daya Umma taje da ita Zaria Lokacin Tana karama Daga wannan Zuwan bata Tunanin ta kara Zuwa ko Wamako Sun Dauki Shekaru basu gantaba Sun gaji dayi ma Abba mganarta sun Hakura sai dai yace Tana karatu,Diza zata Dora wani abu kan kamminta Saboda suna gaisawa ta Social media kuma Tana ganin Hotunanta ammh Ido da ido kam Bazata Dora komai a kanta ba,bata damu ba itama Haka take ayanzu Haka bata da wata Cikakkiyar kawa Tafi jin Dadin Rayuwarta Ita kadai Shiyasa Bata da wani Sakin Jiki Ballatana Saurin Sabo.

Kamar yadda yayi alkawari Da Safe karfe 7am sai ga Kiransa Shi ya tasheta Daga barci Bayan gaisuwa da Tambayan karatu Basu Tsawaita mgana ba yadai Bata Shawaran ta yi karatu Sosai kada tayi wasa Daga karshe yayi mata Fatan alheri da Fatan Samun Nasara Tayi Godiya suka Rabu,Farinciki ya Cika Zuciyar Rumana da wannan Farincikin ta Wuni Har Umma sai da Tayi mgana bata ce mata komai ba Tadai yi Mirmishi kawai Ta kauda kanta ita kuma Umma Sai ta barsa a Kila Farincikin Dawowarta Gida ne yasa ta Fara"a haka.

Da Daddare da Abba ya Dawo yace mata Sabuwar Motar Da yayi mata Oder ta Iso Gobe Za"a kawota Gida Tana Company Rumana Tayi Murna Sosai ta Rumgume Abba Tana Godiya yace Gift ne in Tagama karatu Zata Fara Intenship Tayi amfani da ita Daman Rumana bata da Mota Saboda bata zama agida Tana Makaranta Shiyasa wannab karon ne in Tagama Zata Dawo Gida Tayi ta Murna Ranar da wannan Farincikin ta kwana Tare da Kaunar iyayan nata Har cikin Ranta.

*****

*Zaria..*

Zaune take acikin Karamin Office dinta Dake Shashen Makeup dinta Tagaji Sosai yau Tayi ma Mutane Dadama Kwalliya Sosai wuyanta ke Ciwo Tashi Tayi ta Shiga Tiolet din Dake office din ta wanko Hannunta Lokaci Daya ta Dauro Alwala Tazo ta Shimfida Sallaya Ta Tada Sallar azahar Bayan ta Idar ta Jawo Wayarta Tana Latsawa kafin ta Mike bata Cire Hijabin Jikin nata ba ta Zura Flat din Takalminta ta Fito Ta iske Hauwa na mooping din Wajen kallonta Tayi Tana Fadim"Hauwa Dubamin Littafin Nan gobe mutane nawa ne sukayi Buking din makeup..?

Da Sauri Hauwa Ta ijiye Sandan Mopping dim Ta Nufi Wani Durowa ta Jawo Cikin Zafin Nama ta Dauko wani katon Littafi ta Bude Tana Dubawa Kafin Ta Dago Tana Fadin"Madam Mutum 8..2 Daga Ciki House Service ne.."Kai ta gyada kafin tace"Hauwa na Fara gajiya da wannan aiki..Ki Sanar muma neman Mutum Daya mace Tazo ta Rika Taimaka Miki Am Tired.."

Hauwa Tace"Tom Madam..kuma naji ba kina Fadin zamu bude Wajen Saloon ba.."Diza Tana Kokarin Fita Daga wajen tace"Shima sai na samu mai kula da Wajen...Bafa zan iya wannan aikin ba Hauwa ni ba irinki bame Girman kauye kiyi ta aiki bakya jin kin gaji.."Tafada Lokaci Daya Tana Ficewa Daga wajen Hauwa Tayi Dariya kawai Domin kullum Haka Madam din Take Fada wai ita bata gajiya Ta Saba Aiki Ita Renin kauye ne Gaskiya ne ita yar kafachan ne Dake kaduna Anan Zaria Tana Hannun kanwar Babarta ne ita Ta Sakata Makaranta Koyin kwalliya Har ta kware Diza Ta Dauketa aiki Tana Biyanta albashi mai Tsoka Ammh Tabbas Bata Tashi Cikin Jin Dadi ba Ta Horu da aiki Sosai.

Diza Tana Fita Shashen Catering Dinta Dake Jikin Bulding din Wajen makeup dinta ta Nufa Tana Shiga ma"aikatan suka Fara Wlcming dinta suna Kiran ta da Madam Tana amsawa Marry ce Shugabar ma"aikatan ta na wajen ta Biyo Ta da Gudu Tana Mata Wasu Bayanai Bata Tsaya ba Tace"Merry muje Kitchen din..Hajiya Batula Ta GRA tamin Complain Cake na Rugujewa Ya akayi haka Merry..?

Merry Tace"Mah ba laifin mu bane.."Diza bata kara mgana ba Har suka Dangana da Katon Kitchen din Dayaji kayan Eletronic na wuta,gasu nan kala kala,Saboda ayyikansu ga Ma"aikata ne sai aiki suke Layi Layi Tabi Tana Dubawa Tana kallon Merry tace"Merry ki Rika Dubawa Fa..Bana son mtsala..Bana son Complain in bazaki iya wannan aikin ba Juz Tell me.."

Da Sauri Merry Tace"Sorry Mah.."Diza tayi karamin Tsaki Tana Fadin"Ma"aikatan da kika Dauka basu kware bane Merry..?Kinsan bana son aikin son rai ko..? Kizo kina Korarmin Costumer saboda Shirmenki Bazan Dauka ba.."Ita dai Merry Hakuri kawai take bata suma Ma"aikatan Catering Din Bangaran Kitchen din sai Hakuri suke bata akwai Musulmai Sosai Yaran Ciki kadan ne Gyara Tsayuwa Tayi Tana Fadin"Wacece Tayi Cake din Jiya..?

Merry Ta Nuna Wata Farar Budurwa Tace"Gata nan Fatima ce..Kin santa ai Mah..Tana da kwarewa She know her work Sosai.."A Karkace Diza ta kalli yarinyar kafin Tace"Fati..ya akayi haka kuma..?

Bayani ta Fara mata inda ta Samu mtsalan Karamin Tsaki Taja Ta Cire Hijabin Jikinta da wayarta ta mikama Merry ta Rawan Jiki ta Karba Cikin Takunta na isa ta isa gaban Fatima Tana Fadin"Yau ni zan gasa cake dina Da kaina..Ku koma gefe ku bani Waje.."Tafada Muryanta na Bayyana Bacin Ranta da Gudu Merry ta Dauko Wata FararRiga kamar ta ma"aikatan Kitchen din ta Dorama Diza Duk suka koma Gefe suna kallonta nan da nan ta Fara aiki Lokaci Bayan Lokaci in Tana Bukatar wani abu Zata ce su miko mata.

Agabasu Tayi komai ta gama aikin Diza na Musamman ne Bayan Ta gama gasa Cake din tace kowa yayi Testing haka suka Dauka suna ci suna Mirmishi suna yaba mata,Mirmishi Tayi ta isa gaban Merry Ta Cire mata Rigar Jikinta ta isa ga fomfon dake kitchen din ta wanke Hannunta,Tazo ta karbi Hijabinta da wayarta Ta Juya Tana Fadin"Bana so in sake jin wata Mtsala ok..?

Dukkansu suka amsa da Yes Mah.."Merry Tabi bayanta da Gudu Tana Bude wani Littafi Tana mata mgana Har Haraban Catering din,Kanta ta Dafe Tana Fadin"Merry kiyi yadda kika saba..Everthiny yana Hannunki..Ki turomin komai ta Wayar kamar yadda kika Saba zan Duba in na isa gida yanzu am Tired bana gane komai.."

Merry Ta Rufe Littafin Tana Fadin"Ok mah.."Diza bata kara mgama ba ta wuce Bangaran makeup dinta ta samu Hauwa Tagama gyara Wajen Ciki taa Shiga Ta Cire Hijabin Jikimta ta Ninkesa gefe,ta Dauki Vail dinta Ta saka asaman kanta,ta Dauki karamar Jakarta da key din Motarta Ta Fito Tana kallon Hauwa Tace"Ki kulle ko"ina go Home and Rest.."

Hauwa Ta Bude baki Zatayi mgama Diza ta Fice Tana Fadin"Ke ki tafi Gida nace ko..? Duk wanda yazo ba ma nan Saboda Buking din mu na yau is Over.."Daga haka ta karisa Ficewa Daga kofar glass  din,Haraban Adana Motocin na Haraban Wajen ta Nufa Ta Shiga Motarta Ta Bata Wuta Megadin Dake Tsaron Kofar Wajen ya Bude mata get ta Fice Daga wajen da Gudu ta Dauki Hanyar gida Ta gaji so take tayi wanka Taci abinci ta kwanta ta Huta Mansur Baya nan Tun Jiya yana kaduna Taron su na Siyasa kuma sun yi waya Dazu yace Ba lalle ya Dawo yau ba sai gobe Duk kewa ya Isheta Gidan ma ba Dadi Shiyasa tazo Office nan ma aiki Duk ya gajiyar da ita.

Koda ta isa Gida Mommy nada Bakuwa direct Dakinta ta Shige Tayi wanka kafin ta Fito Mama Fadime ta kawo mata abinci Ta Zauna taci ta koshi Tasha Ruwa Ta Ture komai gefe tabi Lafiyan gado sai barci bata Farka ba sai da Taji kiran Sallah Daga masallacin gida kana ta mike ta Fada Tiolet ta Dauro alwala Tazo Tayi Sallah kana ta gyara Fuska ta Fito Zuwa Falo Har Lokaci   Bakuwar Mommy bata Tafi ba Abokiyar kasuwancinta ne Samata Haura Suka gaisa Tace mata ta Dawo Tun Dazu yanzu Zata leka gidan su Hajja suyi Hira da Aiya tace mata adwwo Lafiya..

Gidan su Mansur ta Shiga Suka Hadu da Aiya sukayi ta Shan Hira Sai Da ta Tsaya taci Tuwo Miyar Dan kubewan da Hajja Tayi ta koshi kana lokacin Har Baba Habibu ya Dawo Tare da Usaman suka Fita itama Tazo Gidan duk irinsu Aiya nw masu Barkwanci Gida ta Koma Lokacin Daddy ya Dawo Ta Haura Dakinsa suka Sha Hiransu Har Mommy Tazo ta Samesu Lokacin Tuni Bakuwar ta Tatafi Abinci Daddy yaci ta zo suci tace ta Koshi Taci Tuwon Hajja,Nan Mommy ta Daga waya ta Kira Hajja tace itama Zataci Tuwon ga Fadime nan Zata zo ta karban mata Jin Haka yasa Shima Daddy yace Tuwon ZAICI Diza nata Dariya Mommy ta Sauka kasa Tayi ma Fadime mgana ita taje ta karbo musu sukaci Har da Saura na Dumamen gobe Mommy na Fadin Kwalelen Diza ita kuma Tace Ai Tana da Hajja Bata da wata Damuwa,sun Dade suna Hira sai Wajen goma ta Baro saman Zuwa Dakinta Daman Tayi Duka Sallolinta agidan Su Mansur Tana komawa Tayi wanka Ta Saka kayan Barci,sai ga kiran Mansur nan suka Sha Hira yana Ta bata Labarin abubuwan da suka Faru a wajen Taronsu na partysu har sai da ta Fara Jin Barci kana ya kyaleta suka Rabu kan sai gobe Zai Dawo Daganan barci ya kwasheta mai Cike da mafarkin Abun Sonta.


*****

Zaune yake acikin Office dinsa yayi Nisa cikin aikinsa yaji wayarsa Dake gefensa ta Dau kukan neman agaji Lokacin Daya ga sunan mai Kiran Wato BABA SULE sai da Ransa ya kara Baci da al"amarin Mansur a karo na ba adadi.

Bai Dauki kiran ba saboda yana Tsakar aiki ne sai da lokacin Sallar azahar yayi ya fita yabi Jam"i sukayi sallar Sai bayan sun Idar ya koma gefe ya Kira Baba Sule din Sun Dade suna mgana Ran Mastur in yayi Dubu ya baci da al"amarin Mansur Hakuri ya bama Baba Sulen Tare da mai alkawarin wannan Weekend din Insha Allahu Zai je Zaria kuma Zasu zo Har Maruka din da Mansur din Tunda ya Rainasa Bayajin mganarsa Da haka suka Rabu da Baba Sulen Cikin Bacin rai ya Kira Mansur din ammh bai Daga kiransa ba Ransa ya kara baci Shiyasa Sam bai so Mansur ya shiga Siyasa ba Sanin Halinsa na Shiririta da Shirme,Da Rashin maida Hankali kan abu mai Muhimmanci ammh anfi karfinsa bashi da yarda Zai yi ne.

Akalan kiran ya maida kan Baba Habibu Shi kan sun Dade Suna mgana Baba Habibu ya gayamai Mansur baya gida yana Kaduna Shima ba mganar da bai mai ba ammh bai Sauraresa ba Sai yace zai je bai samu Lokaci bane,Mastur Yayi shuru kawai bai ce komai ba baisan meke Damun kanin nashi ba ammh Wannan karon zai ji Dalili sun Rabu da Baba Habibu kan zai zo wannan Weekend din Sai ya saba ma Mansur Ransa sai ya baci da wannan Shirmen nashi ace kai baka san Mahaifinka da yan"uwanka ba..? Kamar wani Sakarai ya zama Dole ya Fuskanci bacin Ran abunda ya aikata.

Aranar da Daddare Mansur ya Dawo,sai daya Dawo ne ya samu Lokacin Kiran Mastur yana ganin Kiran yaki Dagawa Saboda Ransa ya baci Har Washegari ma yayi ta Kiransa yayi masa Banza Sai Mansur din ya Tashi Hankalinsa yasan Tabbas akwai wani abu,Har Baba Habibu da Hajja ya sama cikin Damuwa yana Magiyan su Kira Ya Mastur sun Tambayesa yayi mai wani Laifi ne..? Hajja ce ta Biye mai ta Kira Mastur din Bai Daga ba sai Daga baya ya Kirata Yana jin Korafin yace bakomai ya kashe wayarsa Duk sai Mansur ya Tsargu Baba Habibu kuwa daya san Komai sai bai Tanka ba baice komai ba,Ya bari ne Shi Mastur din su gamu da Mansur din Tunda bayajin mgana.

Mansur ya Damu matuka Dalilim haka yasa ya kira Diza Tace mai Tana Office Tana da aiki bai jira cewarta ba ya Datse kiran Mota ya Dauka sai Ma"aikatanta,Kuma fa jiransa ake yi a Karamar hukumar Sabongari suna da Taron Matasan yan Siyasa ammh suna ta Kiransa yaki Dagawa Dubasu Diza na Tsaka da yi ma wata Budurwa Makeup Mansur ya Shigo Wajen Hankali tashe bai ma Jira mganarta ba ya Finciki Hannunta ya Turata Cikin Karamin Office dinta itama Hankalinta atashe take kallonsa kafin tace"Mansur Lafiya..?

Tafada Cikin yanayin Damuwa da kuma Halin Data gansa Neme neme ya Fara Kafin yace"Ina wayarki..?
Mamaki ya kara kamata tace"Menene wai..? Wayata Tana Falon chan.."Bai ma Tsaya Sauraranta ba ya Fice Hauwa Data Karbi aikin Diza Tana karisawa ya tambaya ina Wayar Diza ta nuna mai Inda take ijiye nan Saman Madubi,Dauka yayi a gauggauce ya koma Ciki Diza Da Tayi Tsaye Tana kallonsa Hannayenta Saman kirjinta Bata Tankamai ba Har ya Lalubo Lambar Mastur Datayi ma Saving da Ya Mastur ya kira ammh Wajen kira uku bai Daga ba kawai sai ya Dafe kansa yarasa Abunda kemai Dadi.

Diza tazo kusa Dasshi Ta warce Wayarta Tana Duba wanda ya Kira Da Sauri Ta Dago kanta Cikin Dimuwa kada ace wani abu ne ya samu Ya Mastur din Tace"Me ya Faru..? Wani abun ne ya Faru da Ya Mastur din..?

Mansur bai sami Zarafin mgana ba sai da ya samu Waje ya zauna yana Sauke Numfashi yace"Dani dai ya sama My Firstlady,..Tun jiya nake kiran Ya Mastur yaki Daga Kirana bansan Laifin me nayi mai ba..kuma fa yana Amsa Kiran Kowa Sai nawa ne inata kira bai amsani ba.."Diza Datake kallonsa ta Sauke Numfashi acikin Ranta kuma Hamdala Take yi,da ba wani abu bane mara kyau ya samu ya Mastur din ba.

Mirmishi Tayi Tana Fadin"Laifi kayi mai.Yanzu haka wani abu yace kayi kaki yi Saboda Halinka na Shiririta.."Hararanta yayi yana Fadin"Ni ke Shiririnta ko... ? Lalle ma kin ga gadon Barcina.."Dariya Diza Tayi Tana Zama kujeran Dayake kai Tace"Eh mana ai ba karya nayi ba..Kai da kayi Tunani kila ka gane Laifinka..Nima Laifinka ya Shafeni yaki Daga Kirana..saboda yasan Dole muna Tare.."Mansur yayi Shuru yana wani Tunani Shi dai bai gano Laifinsa ba ga wayarsa sai Kira akeyi a kira wanchan akira Wannan yaki Dagawa Diza ta Mike Tana Fadin"Wai baka ji ana Kiranka bane..?

Karamin Tsaki yaja yana Fadin"Kan Taron Matasanan ne Dana gayamiki Zamuyi a karamar Hukumar Sabongari.."Tabe baki Tayi kafin Tace"Ka Tashi to ka tafi mana..Bafa Dadi haka kada ka manta Kujeran Charman kake nema kuma Matasa suke da Zabe in kayi haka kuma Yaushe Zamu Samu nasara..?

Tafada Tana Tsareshi da ido Kai ya gyada yana kallonta kafin ya Sauke ajiyar rai yana Fadin"Kuma fa hakane..Shiyasa nake Sonki Firstlady na akwai Hangen nesa.."Yafada yana Dariya itama Dariyan tayi Domin inda Sabo tasha Jin wannan kalmar Daga bakinsa Bata Taba Dsukanta awata kalma mai Muhimmanci ba ganin Shakuwar Dake Tsskaninsu da Mansur din Itama Takance mai Haka Tunda ai kaunace da Shakuwa mai karfi a Tsskaninsu.

Kai ta kada mai Tana Fadin"Toh ka tashi kaje gida ka Shirya ka Tafi..Mganar Ya Mastur kuma Laifi fa kayi mai kasan Irin Hukuncinsa ai bana mgana bane..Kaje ka Dawo Zamu Tattaina mu gano Laifinmu.."Tafada Tana yar Dariya Mikewa yayi yana Fadin"Shikeman bari..Naje kinsan Dole na Damu  Kinfi kowa Sanin Halin Yaya Mastur Bana son na Bata mai rai..Balle har yayi Fushi Dani yayi min Fada.."Diza tace"Kaje zamu yi mgana in ka Dawo Nima ba Dadewa zanyi yanzu zamu yi Cloosing duka Buking din mu na yau ya kare..Hauwa kuma House Service Zata tafi yanzu.."Bai yi mgana ba ya Fice kawai ta Tako mai baya Har Kofar Wajen ta Rakashi Tana kara Bashi baki ganin ya Damu Har ya saki ransa suka Rabu kan sai sun Hadu agida ahaka ya Fito ya Shiga Motarsa ya Fice Dagawajen Gida ya koma yayi Wanka yan Party dinsa da magoya Bayansa na waje suna Jiransa suka Rankaya suka Tafi ammh Zuciyaraa sam ba Dadi kuma yakasa gano Laifinsa.

Shi kuwa Mastur yaga Kiran Diza yana gani yasan Mansur ne,Domin Diza Bata kiransa yana mamakin Girman kanta Bazai iya Tuna Ranar Data Kirasa ba Shiyasa yaki Daga Kiran kuma bai bi Baya ba ya Sharesu kawai so yake Yaje gida su kebe adaki Shi da mansur yaci Mutumcinsa Sosai yadda Zai Shiga Tataitayinsa.

Shiryen Shiryen Tafiya Weekend ya Fara Yaso ya Tafi a Jirgi sai kuma yasa yace bari yayi Tafiyar Mota yaso yatafi da Sargent Inuwa Daman shine Sargent dinsa sai kuma ya Sauya Shawara gwara yayi Driving da kansa wannan karon yaje Gida Duk da akwai Nisa bai Damu ba ya saba Tafiye Tafiye masu Nisa Duk da wani Lokacin ajirgi yake yinsu....!





_Albishirunku Masoyana wannan karan na bude muku wani Shashi na musamman Saboda ku..Ina masu Bukatan Atalla musu Hajarsu Ko wani iri ne Domin samun costumer ta ko"ina..? Ku garzayo kakarku ta kusa yanke saka Zan Tallata muku Hajarku a Duka Shafukana Domin inganta Sana"arku da kuma Samun Cinikaya mai Tsabta da kuma kara Hada hada wajen Masi siye da Siyarwa mai Bukatar A tallata mata Hajjarta Zata iya min mgana kai Tsaye ta wannan Lambar Tawa 09069067488 domin karin Bayani...Sai kunzo Kunsan dai mai kasuwa Shi ke da Riba.._

*Domin zama Daya Daga cikin wadanda zasu karanta Labarin SADAUKARWAR SO..! Zaku Biya kudin karatunku kamar haka Masu amfani da Banki Zasu Tura â‚?300 ta wannan asusun banki 0552179550 Jamila umar gtb,Masu Katin waya kuma zasu Turo â‚?400, ta wannan lambar wayar 09069067488 Adauki Hoton katin sai aturo kai Tsaye mutanenmu na Niger kuma zasu Tuntubi wannan lambar kamar haka +22794775574 domin karin bayani,Insha Allahu mutum zai tsinci kansa a paid group ina maraba da ku masoyana Nagode*







*Shakira...*
1/1/22, 18:53 - Maryam Badmsi: *SADAUKARWAR SO..!!*
_(Labarin Yan"uwantaka,Soyayyah Tare da Sadaukarwa)_

*Wattpad:@Jamilaumar315*
*Mallakar:Jamilaumar(Janafty)*



*Page1�⃣0�⃣*


*SOKOTO*
_Area:Sama Road_


"Misalin karfe 7:50am na Safiyar Ranar Asabar ce Garin yayi sanyi Dayake an kwana ana Ruwa jiya Da Daddre Dayake Lokacine na Damuna sai aka wayi Gari cikin Sanyi Sanyi da Ni"ima mai Dadi.

Mai adaidata ne ya sauketa Adaidai Kofar wani katon Gida mai Bakin get,Tana Daga Cikin adaidatan ta Sauko Waje Tana Laluban karamar Jakarta Dake Rataye a Kafadanta ta Ciro Kudi Dubu Daya ta bama mai adaidaitan yana Shirin bata Chanji Tace ya barsa nan da nan ya Fara mata Godiya,Fitowa yayi ya taimaka mata Ya Fito mata da Manyan akwatunta guda Biyu Har Zuwa Gaban get din Gidansu Godiya tamai yace bakomai Kafin ya koma yaja adaidaitansa ya kara Gaba.

Tsaye Take bakin get din bayan ta saka Hannunta ta Buga Lokaci Daya tana gyara zaman karamin Hijabin Jikinta Ta gaji matuka sai wani lumshe ido Take Gasu sun Dan kumbura Saboda Rashin Barci Pakiatan ne Riga da wando ajikinta Sai ta Saka Karamin Hijabi a saman kanta Saboda Zafi Tun karfe Shida na yammah Jiya ta Hawo Motar Express din masu Zuwa arewa Daga Lagos Kawai Tana so Tayi Tafiyar Mota,Hakan na Burgeta,Sun samu Break ne na Sati Biyu Kafin su Fara Final Exam dinsu taso ta zauna Cikin makaranta Tayi karatu sai kuma Kewar Gida ya kamata Shiyasa ta yanke Shawaran Tahowa ko Sati Daya Tayi ta koma Bata Kira Kowa ba Daga Abba Har Umma basusan da zuwanta ba sai dai su ganta kwatsam Tana son ta basu Big Suprise ne.


Lokacin da Megadi ya Bude karamar Kofar yaga Rumana Shima kansa yayi mamaki sai ya Shanye ya Fara mata Sannu da Zuwa,ta amsa Cikin Fara"arta Tana gaishesa Shi ya Daukan mata Akwatunan nata Zuwa Cikin Gidan bayan ya Bude karamar Kofar.

Tunda Taga Babu Motar Abba Tasan ya Fita ammh Duk da haka sai ta kalli megadin Tana Fadin"Abba na ya fita ne..? Cikin Girmamawa yace"Eh bai Dade da Fita ba karamar Hajiya.."Dama haka yake Kiranta kai ta gyada Cikin mamakin Fitan Abba yau da wuri haka sai tayi Tunanin kila wani Uzuri ne ya taso mai da Gaggawa Haka Suna Tafe har suka Shiga Babban Falon Gidan Megadin ne agaba Tana Binsa da Abaya.

Ba kowa afalon sai karan  Talabijin din Dayake ta Faman Ruru ita kadai,Bude Murya Rumana Tayi ta kwada Sallama Tana Fadin"Umma..Gani na Dawo..Goggo Jummai kina ina..?

Take Fada Tana Bin Hanyar Kitchen din Megadi kuma nan Tsakiyar Falon ya ijiye mata akwatunan ya Fice,Wata Yar Dattijuwa ce ta Fito Daga Cikin Bakinta Kamar zai yage Saboda Farinciki cikin Murna Take Fadin"Muryan wa nake ji kamar ta Diyata Rumana..?

Bata idasa Rufe baki ba Rumana ta Fada Jikinta Tana Murnan ganinta Itama Goggon Jumman Rumgumeta Tayi Tana Fadin"A"a Bakin Ikko..Da Safe haka..?barka da zuwa.."Dagowa Rumana Tayi Tana Fadin"Daman Surprise nake son baku..Ina Umma Megadi yace min Abbana ya Fita..?..

Goggo Jummai tace"Umman ki Tana sama Abban eh ya Fita Tun Safe ko karyawa ma bai Tsaya yayi ba..Rumana Kin Rame ko Duk karatun Bokon nan da kuka sama Ranku ne..? Rumana na Dariya Fararan Hakoranta suka Bayyana Ta Lumshe ido Tana Fadin"Bakomai Goggo Jummai watarana sai Labari. baki son Kiji ana Kirana Dr.Rumana ne..?

Goggo Jummai ta Shafa kanta Tana Fadin"Sosai ma..Ina son Diyata ta zama Likita Watarana Ko Bana Raye Ta zama abun alharin kasarta.."Rumana Tace"Kina ma Raye Goggo Jummai kinsam bana son irin wannan mganar ko..? Kina so mu Fara Fada Daga Dawowata ko.?

Kafin Tayimgana wata Matashiyar bakar yarinya Ta Fito Daga Cikin Kitchen Din Tana Fadin"Sannu da Dawowa karamar Hajiya.."Tafada Harda Rankwafawa Amsawa Tayi Tana kallonta Kafin Tace"Juma Daman kina Nan..? Kai ta gyada Tana Fadin"Eh ina Ciki ne ina aiki.."Goggo Jummai tace"Kina dai Shiriritarki ta Fama Juma..Maza kwashi kayan Ruma ki kaimata Cikin Dakinta Kamar Umma ta san kina Tafe Shekarajiya tace ma Juma ta Shiga Dakin ki ta gyara Miki yayi kura.."

Rumana Tayi Mirmishi Tana Fadin"Shiyasa nake son Ummata.."Tafada Tana Shafa Jikinta,Lokaci Daya tana wani Yamutsa Fuska Tana Fadin"Goggo Jummai yunwa nake ji Wlh..Rabona da abinci Tun Jiya.."Ta Fada Daidai Lokacin da Juma ta kwashi Akwatunan Rumana Ta Haura Dashi Upstair inda Dakin Ruman yake Dagachan gefe yammah Daga Inda na Iyayanta yake.

Goggo Jummai Ta Juya tana Fadin"Jeki wanka ki Sauya kaya Kafin Lokaci na Hauro Miki Da kayan karyawan naki Sama.."Kai ta Girgiza Tana Fadin"A"a Bazan saka Kakata aiki ba..Keda baki da lafiyan kafa Sai ki Hau Bene da Kaya ahannunki.? Salon ki kara Turdemin yar kafan taki a rika Kirana kakar Rumana mai Karyayyiyar kafa..? Ta karishe Fada Tana Dariya Goggo Jummai tace"Ai Diyata Likita ce bani da Damuwa.."Juyawa Rumana Tayi Tana Fadin"Nidai kada ki Hauro Dashi..Zan sauki na karya Tare daku Goggo..Umma kuma Ko Ta Fito kada kice mata na Dawo so nake ta ganni kamar Daga sama.."

Cikin Kaunar Rumana Har Cikin Ranta Tace"Shikenan Diyata Afito Lafiya.."Daga haka ta juya Tana Tafiya sannu Sannu ta Shiga Kitchen ita kuma Rumana ta Fara Haura step Zuwa saman Bene Tana Shiga Dakinta Taga Juma gaban Madubi Tana ta kallon kanta Rumana ta Dade Tana kallonta Tana Dariya kasa kasa Halin Juma sai ita.

Gyaran Murya Tayi Tana Fadin"Juma Sarkin kallon madubi An fara kenan ko .? Jin muryan Ruma yasa ta waigo da Sauri Tana Sosa keya Tace"Ayi Hakuri karamar Hajiya.."Bata ce mata komai Har ta Fice Tana wani Sunne kai Binta Tayi da kallo kafin tace"Juma Bansan yaushe Zata Gane ta zama yanmata ba..

Tafada Lokaci Daya Tana Ijiye Jakarta Saman gado,Kafin ta Fada kan gadon Lokaci Daya Tana Fadin"I miss My Bed.."Take Fada Tana Dariya Ta Dade kafin Ta Mike Karamin Hijabinta ta Cire Ta Tura Kofar Tiolet din ,Ta Shiga Bata wuce Minti Talatin ba sai gata Ta Fito Dauke da Rigan wanka ajikinta kanta Ta nannadeshi da karamin Towel.

Kan Madubi Ta Nufa Ta ja karamar Kujeran Dake wajen ta Zauna Ta Fara Shafa Lotion dinta na Man Olive,Har ta gama batayi wani kwalliya ba ko Hoda bata Shafa ba,Ta Mike ta isa Gaban makeken wardrope dinta Ta Bude ta Dauko Wata Doguwar Rigar Atamfa,Ta Saka Bayan ta Zare Rigar Wankan Dake Jikinta da Towel din,Dankwalin Atamfan ta Daura a saman kanta Ta Dauki Rigan wanka Ta maida Tiolet bayan ta Shanyasu Cikin wata karamar Igiya Ta Fito kenan Taji karae Bude Kofa Tana Dagowa suka Hada Ido Hudu da Umma Waro Ido Tayi Tana Fadin"Ummata.."

Tafada Cikin Murna Da Farinciki Lokaci Daya ta isa Gareta Ta fada Jikinta suka Rungume juna Hajiya Farida na Dariyan Farincikin ganin Yarta kwara Daya aduniya ta kara Riketa Tana Fadin"Ai ni Fushi nake dake Ruma..ace ki Dawo gidanan bansani ba.."Dagowa Rumana Tayi Ta Shagwabe Tana Fadin"Waya gaya Miki..? Nafa cema Goggo Jummai is a Suprise"

Umma na Dariya tace"Juma ta Gayamin..Ai kinsan Goggonki bazata Fadamin ba Tunda bakin ku Daya.."Rumana ta Tura Baki Tana Fadin"Kai Bakin Juma kamar Sikat ba"a Sirri da ita.."Umma na Dariya ta Shafa kumatunta Tana Fadin"Ruma ta ta Rame sosai.."Tafada Tana Taba Wuyanta Cikin Shagwaba Rumana ta kara Rungumeta Tama Fadin"Umma na Karatu ne..Dole na Rame bama ssamun Hutu sosai..kuma ba Jirgi na Biyo ba Jiya na Taso kwana mukai Tafiya Doguwar Motar nan ta Express na Shigo ."

Umma Ta Zaro Ido Tana Dagota Daga Jikinta Tana Fadin"Mota..? Baki da Hankali ne Ruma..?yadda Kasar nan ta lalace ba Tsoro da wani abu ya Faru Dake fa..? Ta Fada Cikin Bacin Rai ganin yasa ta Kama kunnuwanta Duka Biyu Tana Fadin"Ba gashi na iso Lafiya ba Umma..? Kiyi hakuri bazan Kara ba.."Bata iya Fushi da yar nata Sai Ta Cire mata Hannunta a kunnuwan Tana Fadin"Shikenan ya wuce..Muje kasa ki karya Na kira Abban ki na gayamai kin Dawo yana ta Murna wai kun samu Hutu ne..?

Rumana Ta juya Tana Fadin"Umma bari na Dauko Wayata..Eh..Mun samu Breaks ne na  Sati Biyu Zamu Fara Final Exam dinmu Shine nace Bari nazo nayi ko Sati Daya ne Sai na koma kewarku keda Abba Duk ta Isheni bata barina ma Cin Abinci.."Tafada Bayan ta Dauko Wayar nata Daga Cikin Jakar Data Dawo da ita Ta zo Gaban Umman,Wacce ta Rike Hannunta suka Fice Daga Dakin Tana Fadin"Muma muna kewarki..Bamu da yarda Zamu yi ai Karatun yazo karshe..Sai Service ko..?

Tafada Tana kallinta suna Saukowa Daga Upstair kamar wasu yaya da kanwa Ruma Tace"No Umma sai munyi Intenship na Shekara Daya kana zamu Tafi Service.."Kai ta gyada Tana Fadin"Kuma..? Allah ya Taimaka achan zaki Intenship din...?


Tafada suna Zama kan Daya Daga Cikin kujerun Falon,kai Rumana ta Girgiza mata Tana Fadin"A"a Umma..Arewata zan Dawo..Nan Uduth zan yi in na samu Insha Allahu..'"Umma tace"Allah ya Tabbatar mana da alheri.."Daga haka suka Cigaba da Hiransu Sama sama Rumana da latsa wayarta Lambarsa ta Kira ammh kuma bai Daga ba Sunfi Sati basu mgana Dashi ba Karatu ya sha mata kai Shi kuma bai Kirata ba sako Ta turamai Ta gayamai sun samu Hutu Tazo Gida da kuma Rokon Addun"a Zasu Fara Final Exams dinsu.

Juma ce ta Gabatar musu da Breakafast Saboda Ruma yasa Umma tasaka ta Shimfida Babbar Darduma Saboda in Tana Gida Bata son cin Abinci Saman Dining tafi son Ci kam Darduma a kasa,Nan aka Baje musu komai Rumana ta matsa Tace Tare da Juma da Goggo Jummai Zasu karya Umma bata Damu ba sanin Halin Rumanan Goggon jummai ce ke Baya Baya Juma dai ba Ruwanta Shirishirintanma ya Isheta Yan Garinsu Abbanta ne Daga Wamako Abba ya Dauko Goggo Jummai Domin ta Taimakama Umma Tun Tana da Karfinta Tazo Gidan Tun Ruma na karama akwai Shakuwa Sosai Tsskaninsu Kuma Ruman tana Daukanta kamar kakarta Ita ta sakaa mata ma sunan Goggo Jummai,Lokacin da karfinta ya kare ciwon kafa da Ciwon Baya sai Umma Dataji Dadin Zama da ita tace ta Dauko mata Daya Daga Cikin Jikokinta sai su Zauna Tare ita ta rika yin aiki,goggo Jummai Taji Dadin karamincin Su Umma Juma Jikarta ce Diyarta ta Fari ta Haifeta ta Rasu,ita Dauki yar Shekara 15 aduniya suna Zaune Tare Duk da Ciwon kafan Datake Fama Dashi Bata zama Haka batayi aiki ba komai na Bukatar Rayuwa Umma da Abba suna yi musu a yan"uwansu suka Daukesu ba masu aiki ba.

Tare Dukkansu suka karya Suna Hira suna Raha bayan sun gama Juma ta kwashe komai Zuwa Kitchen Goggo Jummai Tatafi Dakinta ta Dan kwanta ta huta suka bar Ruma da Umma anan Falon suna Hira Har wajen Azahar sai da aka Kira Sallar azahar kana kowacce Tayi Dakinta Ta gabatar da Salla,Rumana Barci ne a Idonta Sai kawai Tabi Lafiyan gado Ta kwanta Domin jiya Batayi barci ba kasawa tayi,Tana kwanciya Barci ya kwasheta Cike da Tunanin Mastur acikinsa.


Sai Bayan La"asar TaTashi Shima Sai da Umma ta Shigo ta Tasheta Tayi sallah Kana tatashi Tayi wanka ta Sauya kaya Zuwa Riga da wando na pakistan Daman yawancin kayanta kenan Bayan ta idar da Salla ne ta Bude akwatunanta Dama Daya na kayan sawanta ne Daya kuma na Littafan karatunta sai System dinta,System din ta Dauka Littafan kuma ta Xube su Kan gadonta Domin karatu Zatayi kamar Hauka irin karatun da masu wasa bane,Earphone dinta Ta Dauko ta Saka a wayarta Bayan ta saka Karatun alqur"ani ta Toshe kunnuwanta Ta Bude System dinta ta Fara Karatu bayan ta saka Sirrin Gilshinta mai kara Mata karfin gani Umma ta Lekota ganin tana Karatu yasa ta Kyaketa Ta yi Karatunta Rumana Bata Tashi Daga Karatunta ba sai da aka Kira Mangariba kana Tatashi ta Fada Tiolet ta Dauro alwala Tazo Tayi Sallah Ta Zauna Tana azkar Umma ta leko Tana gayamata Dawowar Abbanta Ko Hijabin Jikinta Bata Cire ba tabi Bayanta Tana Murna.

Afalon Sama ta gansa Rumgumeshi Tayi Tana Murnan ganinsa Shima Riketa yayi Cikin Farinciki,Yana Shafa kanta Gefensa ya Zaunar da ita yana Fadin"Rumana ya karatu..?

Shagwabe Fuska Tayi Tana Fadin"Ba Dadi Abba..Wlh Kamar zamu Haukace fa..Yanzu fa Bayan mun bar asibitin Cikin makaranta ne aka bamu Sati Biyu muyi Karatu kafin mu Fara Jarabawar Karshe.."Yana Shafa kanta yace"Masha Allah..I know my Dota..Zata iya da yardam Allah..Allah ya bada Sa"a Dr Rumana Muhammed wamako.."kanta yayi Girma da Kirarin Abban nata ta Washe Baki Tana Fadin"Nagode Abbana..Ina alfahari Dakai sosai kaida Umma.."Shima Mirmishin yayi mata yana Dafa kanta yace"Muma muna alfahari Dake Rumana.."Umma ce Dake jeramai abinci nan gabansa Take Mirmishi Nam Abba ya Sauko Da Rumana da Umma suka Hadu sukayi Dinner a sama Bayan sun gama Ruma ta kwashe komai Zuwa Falon kasa Juma ta karba Zuwa Kitchen Dakin Goggo Jummai ta Leka ta gaisheta,Ta isleta Tana kan Sallaya Tana Lazimi Bata wani Jima ba ta Koma Dakin Umman nata ta Zauna Gefensa suna Hiran su Sama sama Tana sska musu baki Cikin Farinciki yau gata ga iyayanta Masu Soyuwa Gareta.

Suna Cikin Hiran ne Wayar Abba ta Dauki kara Ya Dauko Ta Daga Cikin aljihunsa yana Ganin mai Kiran ya saki Mirmishi yana Fadin"D'anki Farida Mastur.."Umma ta Washe Baki Tana Fadin"AllH Sarki DCP zakace min Nima da Safe ya kirani ya gaisheni Yaron nan Wlh bantaba ganin mai Datttako irinsa ba Kamar wani Babba.."

Abba yace"Bari..Bari Farida..Yafada Lokaci Daya yana Daga Wayar Cikin Sallama Rumana Dake gefe Tayi Lambo ajikin Abba kamar bata jinsu nan kuwa Gabanta ne ke Fadi Kiran sunan Mastur kadai da Abba yayi yasa Jikinta ya saki Ta Tuna Ta Turamai sako ammh Bai Kirata ba Daman baya Kiranta sai in ita ta Kirashi baya Daga Kiranta zai bari ta yanke ya Biyo baya Tana ji suna mgana da Abba yana gayamai ta Dawo Gida Daganan aka Bama Umma suka gaisa sai kuma Sukayi sallama.

Umma ta kada kai Tana Fadin"Iyayensa sun yi Dacen D"a..Wlh Ina Sha"awarsa..Babu Ruwansa akwai Hankali da Tarbiyan gashi dai bashi da yawan mgana Ga shi ba wani Babba ba sai Halin Girma.."Abba ya Jinjina kai yana Fadin"Ai Alhaji Sunusi yace Sak Hallsyansa Ubansa ne..Haka Mahaifinsa yake Baba Habibu.."Umma tace"Ai har Mahaifiyar tasa..Hajja ai akwai kawaici da Halin Girma.."duka Hiran nasu na Yabon Mastur ne Tana Jinsu Batace komai ba Sai da Abban ya kalleta yana Fadin"Rumana kinyi Shiru baki ce komai ba..? Kina kiran yayan naki kuna gaisuwa kuwa..?

Kai ta gyada Tana Fadin"Eh Abba.."Mirmishi yayi yana Fadin"Allah yayi miki albarka..Babanki na Zaria nata Cigiyanki yaushe zaki mai Hutu ki kwana Biyu.."Rumana Ta muskuta Tana Fadin"Abba sai na Gama Exams na Dawo Gida kafin na Fara Intenship.'Umma tace"Yadai kamata kam Ruma..Hajiya Asiya ma Tagaji Da min Magiyan yaushe Ruman Zataje Suna Daga Kafa ne saboda Karatunta.."

Abba yace"Zataje Tayi Musu Hutu Insha Allahu  Koma kije Chan Asibitin ABU Kiyi Intenship Dinki ko Service dinki.."Rumana ta Dago kanta Tana Fadin"Abba sai inda na Samu fa..Sai anyi Exam duka zan je nayi in na samu Shikenan.."Umma tace"Zama ki Samu..ko nan Sokoto ko Chan Zaria Duk inda kika samu duk Gidane..'Rumana bata kara mgana ba Abba ne yace"Kuna waya ko da yar"uwanki Diza..? Kinsan Ta Bude Wajen Makeup da Snaks,..?

Rumana Tace"Eh Abba...muna Taba Chart da ita sama sama..Ina kuma Following dinta Duka Social medianta Ina ganin posting din abubuwanta na Tayata Murna Abba sai dai Why Taki Karatu..?

Umma tace"Bata Ra"ayi ne Rumana..Ba gashi kuma Allah yasa ma Abun albarka Hajiya Asiya na gayamin irin Ficen da Dizan Tayi a Chan Zaria da kaduna.."Abba yace"Sosai ma..Kowa fa da hanyar Cin Abinsa baka ga Mansur ba Dan Wajen Shi Habibun Daya ke Riko .Kamar waasa Siyasa Ta zama Hanyar Cin Abincinsa.."Umma tayi Dariya Tana Fadin"Honourable kenam..Shi kuma ai dan Barkwanci ne ko Wasa da Dariyansa yaci a Zabesa...Abokin Diza kenan Tun na yarinta.."

Rumana Duk Tana jinsu Bata ce komai ba Ganin Ta gundura da yin Hiran yasa ta Tashi Tana Fadin"Umma Da Abba..Sai da Safe Zanje nayi karatu na kwanta.."Sukayi mata sai da Safe Kana ta Fice Zuwa Dakinta suka Bita da kallon Sha"awa.

Wanka ta sakeyi tayi Sallar Isha"i kana ta saka Kayan Barci Tazo ta Hau gado Duk yadda Taso Tayi Karatin ta kasa Saboda Tunaninsa,Shiyasa wani Lokacin bata so Tunaninsa yazo mata Sai ya Hanata Sukuni wani Lokaci sai ta maida kanta Kullum Cikin karatu Saboda kaucema Tunaninsa Sai dai yau yaci karfinta Kowa yabonsa yake..Kowa Sonsa yake saboda kyawawan Hallayansa Ture Littafan gabanta Tayi ta Jawo Wayarta Ta Lalubo Lambarsa Data sakama Emoji na Zuciya da makulli ta Dokamai kira.


******

Fitowarsa Daga wanka kenan Daure da Towel a kugunnsa Jikinsa Duk yana Digan Ruwa Daga kan gadon da wayoyinsa ke Zube yaga Babbar Tana Haske a Silent ya sakata kafin ya Shiga wanka.

Karisawa yayi kusa da wayar ganin Sunan Rumana yasa ya Dafe kansa bai Daga Kiran ba Sai da ta katse kana ya Dauko Wayar ya Shiga wajen Sako ya Fara Mata Rubutu.

*Me kike yi baki kwanta ba Har yanzu Rumana..? Akwai Exams agabanki..ya kamata by Now kin kwanta saboda kwalkwawarki ta zama Fressh Abunda kika Karanta ya zauna Miki..Kada ki Damu ki kwanta u Took in d Mrning Gud Night..*

Daga Haka ya Tura mata Lokaci Daya ya Maida wayar saman gado ya isa gaban Madubin Dake Dakin ya Fara shafa  Lotion,sai da ya gama kana ya isa gaban wardrope din Dake Dakin Cikin Hanger ya Dauki Jallabiya ya saka yunwa yake ji Silafas dinsa ya Zura ya Fita Zuwa Kitchen ya manta bai yo Takeway ba kafin ya Shigo Gida kuma ya Kira Wani Sargent din Kamar Shiga Hakki ne.


Kitchen din Dake Cikin Apartmemt din da gwannati ta bashi yake zaune ya Shiga gas ya kunna ya Dora karamar Tunkunya ya saka Ruwan Zafi Yana Zafi ya kashe Gas dim ya Fito Falon Dayake Babba yaji kujerun alfarma wajen Dinning ya Nufa inda kayan Tea suke ya Hada nan ya Zauna yasha kadan bada yawa ba ya Ture kofin ya Mike Zuwa Falom kan Daya Daga Cikin Kujerin Falon ya Zauna ya Dauki Remot  yana Sarrafa Tibin Dake kunne Tun Fitowarsa..

Tashar NTA Ya kamo yana kallon Labarai Cikin Harshem Turanci kansa ya maida Saman kujeran ya Jingina Lokaci Daya yana Dora kafa Daya kan Center Table din Dake Tsakiyar Falon ya Rage ma Idanuwansa Karfi Kamar mai jin Barci nan kuwa Duka Hankalinsa na kan Abunda yake kallo ne.


*Kuyu hakuri da jina Shuru da kuke yi..Wlh na Shiga wata Sabgace Biki gareni Dis week Shiyasa Posting din zai zama sai Lokaci bayan Lokaci ammh da Zarar an gama Biki Lafiya da yardan Allah zamu dawo mu Dora Insha Allahu,Sannan Zaku cigaba da Payment din kudin Karatun Sadaukarwar so Ina maraba daku Masoyana sai kunzo..Nagode..*




_Albishirunku Masoyana wannan karan na bude muku wani Shashi na musamman Saboda ku..Ina masu Bukatan Atalla musu Hajarsu Ko wani iri ne Domin samun costumer ta ko"ina..? Ku garzayo kakarku ta kusa yanke saka Zan Tallata muku Hajarku a Duka Shafukana Domin inganta Sana"arku da kuma Samun Cinikaya mai Tsabta da kuma kara Hada hada wajen Masi siye da Siyarwa mai Bukatar A tallata mata Hajjarta Zata iya min mgana kai Tsaye ta wannan Lambar Tawa 09069067488 domin karin Bayani...Sai kunzo Kunsan dai mai kasuwa Shi ke da Riba.._

*Domin zama Daya Daga cikin wadanda zasu karanta Labarin SADAUKARWAR SO..! Zaku Biya kudin karatunku kamar haka Masu amfani da Banki Zasu Tura â‚?300 ta wannan asusun banki 0552179550 Jamila umar gtb,Masu Katin waya kuma zasu Turo â‚?400, ta wannan lambar wayar 09069067488 Adauki Hoton katin sai aturo kai Tsaye mutanenmu na Niger kuma zasu Tuntubi wannan lambar kamar haka +22794775574 domin karin bayani,Insha Allahu mutum zai tsinci kansa a paid group ina maraba da ku masoyana Nagode*



*Janafty...*
1/1/22, 18:53 - Maryam Badmsi: *SADAUKARWAR SO..!!*
_(Labarin Yan"uwantaka,Soyayyah Tare da Sadaukarwa)_

*Wattpad:@Jamilaumar315*
*Mallakar:Jamilaumar(Janafty)*



*Page1�⃣2�⃣*



""Kwata kwata yaki Daukan Wayan Mansur Ballatana ya Sauraresa Duk kuwa da nacin Kiran da yake mai da Turamai Sakonnin ban Hakuri yayi mai Biris Abunda ke bashi Mamaki da kanin nashi Har zuwa yanzu bai iya zama ya natsu ba Ballatana ya gano Laifinsa Sai Shirmensa kawai yake in ya Tuna Haka sai yaji Dacin wani abu Ba haka yaso kanin nashi ya zama ba ammh bashi da yarda Zai yi Kullum Mansur ya Girma ne baisan ya Girma ba in yayi wani abun kamar wani yaro karami.


Ya gama gayamawa Kowa yayan nashi na Fushi Dashi..Harda Daddy Da Mommy Sai da suka Kirashi Suna Tambayan Dalili yace musu bakomai Zai kira Mansur aiki ne yamai yawa kowa ya yarda da kalaman Mastur sanin Halinsa kaifi Dayane sai ake Tausan Mansur din yayi ma yayan nashi Uzuri yanayin aikinsu ne Nan kuwa Mansur yasan waye Mastur Irin Horansa kenan kuma yana da Tabbacin Koma wani Laifi ya aikata mai Girma ya bata ran Yayan nashi da bai da kamarsa Duk Duniya Yayan Da baya son ganinsa Cikin Damuwa yayan Dayake Samin abu ya Hanawa kansa Saboda shi..Ya Tabbata Koma Miye ya Faru ya batama Mastur rai matuka Dalilin Dake Hanashi Kwanciyar Hankali kenan Ko Itama Diza tun bata Damuwa Har tazo ta Fara Damuwa ganin yadda Mansur din ya Hana kanshi Sukuni.

Daran Jumma"a ya baro Parthercourt da yammah ya iso Zaria da Safe Misalin Karfe 10:30am nasafe,Ba wanda yasan da zuwansa ko Habibu Bai gayama  Ga Ranar da zai Taho ba,Kuma Shi kadai yazo Dan Rakiya Ko Daya bai Taho Dashi ba,Sai dai su Hajja suka gansa kwatsam Lokacin Tuni Baba Habibu ya Tsufa akasuwa Gogan kuwa Yana Ciki yana Barci bai ma Tashi ba Diza ma Tana Gida Bata da masaniya Ita Fita Zatayi Domin Tana da aiki Sosai Yanzu Suna samun yawan Costumer sosai arana gashi Daga ita sai Hauwa,an kawo mata Wasu mata wadanda suka samu kwarewa akan Makeup din ammh Duk basu yi mata ba Bata Daukesu ba Tana dai Cigaba da Dubawa Tun Safe tayi wanka Tashirya Bayan Tayi Taking Breakfast Daddy ya Fita kamfani sunyi baki Abokan Cinikanyasu ne,Mommy kuma Tana Sama bata Sauko Falo ba Ta Fito ta zauna Tana latsan waya Tana Jiran 11am ta cika sai ta Fita.

Shi da kansa ya Bude ma kansa get Daman basu da megadi Bayan nan kuma ya Shigo da Motarsa Cikin Haraban Gidan,Motar Mansur Daya gani yasa yaji Dadi Allah ya Taimakeshi yau ba"a Fita Gantalin Siyansa ba Sai da ya kashe Motar yaDauko Duka Wayoyinsa bai zo da kaya ba Saboda aiki zasu zame mai yana da kaya anan gidan System dinsa kawai yazo Dashi Saboda aiki ita ya Dauko Ya Taka zuwa kofar da Zata sadashi da Falon Hajja Yana Sanye da Riga da wando na Kamfanin Dkny,Black and White sai P.Cap din Dake kansa da Takalmi Booth Daya Rufe kafarsa Dashi.

Sallama yayi da Muryansa mai Cike da Zati Aiya dake zaune ta Fara Jinsa Domin Aiya Gashi dai ta Tsufa ammh akwai son kallo Haka zata gwafe a falo Tana Dale ido,Hajja ma kallon bai Dameta ba,Bata cika Zama ba ko Tana Daki ko Tana Kitchen,Kamar a mafarki Taji Muryansa Cikin Sauri Aiya Ta Dago kai Tana Fadin"ah..ah..Muryan wa nakeji Kamar ta megidana..Lah..Wlh Shine Hajara ke fito ga yaronki Da Safe haka Maraba Maraba da Zuwa..!

Take Fada Cikin Fara"a Kamar bakinta Zai yage Saboda Murna Mirmishi ya saki Har Hakoransa Farare suka Bayyana Dukawa Yayi ya cire Takalmin Kafarsa kana ya kariso Cikin Falon kasa ya Zauna Daidai kafafun Aiya ya ijiye abunda ke Hannunsa yace"Aiya na same ku lafiya..?

Ya Fada yana kallonta Kansa ta Shafa tana Fadin"Lafiya Megidana Dan albarka..Zuwa Haka ba Sanarwa.."Kansa na kasa yace"Saboda yanayin aiki ne Aiya..Kada nace gani zuwa kuma ban samu zuwa ba..! Ina Hajja da Baba..?

Yafada Yana Kara gyara Zama Cikim Fara"a Tace"Eh hakane kam..Hajja tana ciki Habibu kuma ya fita kasuwa Ke Hajara..Ki Fito ga Mastur ya Dawo.."Tafada da dan karfi Hajja Dake Cikin Dakimta Tana Gyaran kayanta Taji kamar Muryan Aiya Dayake ta Kunna Radio ga kuma karan Tibi baisa Taji ba Fitowa Tayi Tana Fadin"Aiya naji..."Mganarta Ta makale ne ganin Mastur zaune yana kallonta Baki ta Washe Tana Fadin"A"a Babban Mutum ne..? saukar yaushe..?

Tafada Cikin Farinciki Tana karisawa Kusa Dashi kansa Ya maida kasa ya Danrankwafa yana Fadin"Ina kwana Hajja..? Yanzu na iso.."Cikin Fara"a ganin Dan nata take amsa mai Lokaci Daya Tana Tambayansa Wajen aikinsa yace Alhamdulillah Mikewa Tayi bayan Aiya tace"Ke Hajara Kawo mai abun kari mana..Kin barsa Zaune kuma kinsan Tafiyar Safe yayi.."Shi dai kawai Mirmishi yayi bai yi mgana ba Hajja Ta Shiga Kitchen Ta Zubomai Soyayyan Dankalin Da Suka karya Dashi Dama na Mansur ne ta Diban mai da kwai sai Fulas din Ruwan Zafi da kayan Tea ta Fito Dauke da Faranti Da Sauri ya Mike ya karba yana Fadin"Sannu Hajja..Da baki Dauki ba da kin Kirani na Dauka Dakaina.."

Yafada yana Ijiyewa nan Saman Cafet Din Daya Malale a tsakar Falon,Hajja Tayi Mirmishi Tana kallon yaron nata Daya kara Sauyawa Tace"ai ka girma da wannan aikin Babban Mutum.."Yana Zama gaban kayan Karyawan yace"A"a Hajja Kin Taba gani ko Jin inda D'a ya girma da yima iyayansa aiki..?

Dariya Tayi Tana kara Godema Allah Daya bata D'a kamar Mastur in yayi mgana ko Baba Habibu albarka,Tea ya fara Hadawa ya Fara kurba Aiya na Gefe Tace"Hala Habibu bai son da Zuwanka bane..? Hajara ko Zaki Kirashi ne ki gayamai..?

Da Sauri ya Girgiza kai yana Fadin"A"a Aiya a kyaleshi ai ina nan ba yau zan koma ba sai Gobe in Allah ya kaimu.."Hajja Tace"Gobe goben nan Babban Mutum..? Kallonta yayi yana Fadin"Eh Hajja..Monday akwai aiki fa..Zuwan Daman Domin na ganku ne..Na kuma Bata ma Mansur rai."Aiya tace"Aifa Koda naji yana ta Sambatun nan nasan wani abu yayi.? mansur sai Shirin Allah ni Habibu ma yayi mai aure ko Zai yi Hankali.."

Hajja na Dariya Tace"Ai ya isa Auran Aiya.."Aiya ta Tabe baki Tace"Ahakan..? Ammh Irinsa Mashiririciya irin yarinyar nan Hadiza ko..? Daman sun Dace da juna a aura musu juna suje Chan su karata bamai ma wani Fada.."Yana kurban Tea ne Aiya ta Fadi haka Sai da yaji Ruwan Zafi ya kasa Shiga Cikinsa ya Tsaya Cak Makogwaronsa Sai kuma Numfashinsa ya Fara sama Sama nan da nan ya Kware ya Fara Tari Hajja da Aiya suka Rude suna mai Sannu nan da nan sai ga Tea din na Biyo Hancinsa Ruwa Hajja ta Ruga Kitchen ta Debomai na sama wanda Take Tarawa a kofi Ta Bashi ya karba ya kafa kai yasha Sosai kana ya Dire Kofin ya Koma yana Jingina da kujera yana Maida Numfashi Su kuma suna aukin Jeramai Sannu.

Ya Dade yana kai da kawo Tsakaninsa da Zuciyarsa da kalaman Aiya kafin ya Iya Daidatuwa Dakyar ya iya Bude Idanuwansa da sukayi Jajir Dasu Kamar Garwashi,ya Muskuta yana Kallon Hajja da Aiya da suka Kwabe Fuska kamar Suyi kuka Mirmishi ya saki kafin yace"Kada ku damu..Bakomai Hajja.."Yafada Lokaci Daya yana Mikewa Domin Gabadaya Cikinsa ya Cushe ne Duk da rabonsa da wani abu Tun Daya Bar Porthercourt ya taho yana mararin abincin Hajja ammh Kalaman Aiya sun saka komai ya Fita kansa.

Ganin ya Mike yasa Aiya Tace"Ah ya haka..?baka karisa karyawan ba Ka tashi..?
P.cap dinsa yadan Ja baya ya Shafa Goshinsa yana Fadin"Sai anjuma Aiya.."Yana Fadin haka ya Duka ya Kwashi Wayoyinsa da System dinsa ya dago yana Kallon Hajja Datayi wani iri kafin yayi mgana Ta Rigasa da Cewa"Kana dai Lafiya ko..,?

Mirmishi yayi mata kafin ya gyada kai yana Fadin"Eh..Hajja bari naje nayi wanka.."Da Sauri tace"Dan"uwanka na nan bai Tashi ba.."jinjina kai yayi bai yi mgana ba ya Fara Takawa zai Fita Tace"Me zan Dafa maka da Rana..?

Yana jin Haka ya waiwayo yana kallonta kafin yayi Mirmishi yace"Nayi kewar Tuwonnki Hajjanmu.."Farinciki ya kamata da Sauri tace"Angama Babban Mutum..Yau zakaci Tuwon Hajja Har ka Koshi.."Kai ya gyada kafin ya Duka ya Zura Takalminsa Ya Dago Hajja Ta Juya Zata Shiga Kitchen da Tiren kayan karyawan Data kawomai yace"Hajja Inna Karime ta Kirani...!

Waigowa Tayi Tace"Yaya karime.? Lafiya..? Cikin Sigan Tambaya Juyawa yayi yana Fadin"Sai na Fito Zamu Tattauna.."Ajiyar rai ta Sauke Tadanyi Mirmishi kafin Tace"Afito Lafiya..'Ranta ba Dadi Domin tasan mganar kenan Yaya karime bata bar mganar Hada Auran Babban Mutum da Yar wajenta Bushira ba,ta Ina Rayuwar Bushara da mastur ta Dace in da ace Zai yi Na"am Datafi kowa Murnan ammh kuma hakan akwai karuwa ga wanda yayi Karatun Boko mai Zurfi ya Rayu a Wayewan waje a Hadashi da wacce ko Hanyar makaranta Bata sani ba Ta Tabbata Mansur bazai karbi Bushara ba Ballatana Babban Mutum.

Bayan Fitansa ne Zata Shige Kitchen Din Dake Falon Taji mganar Aiya Tana Fadin"Uhm..aini Laifin Habibu nagani da bai Takama Karime Burgi ba..Ina Bushara Ina Megidana..! Ai ko Mansur dai Da ba wani Hankali ya Cika ba bana so ya aureta ba Tsakani ga Allah da akwai Cutuwa.."Mirmishi kawai Hajja TayiSanin Halin Aiya Tunda karimen Ta Tako da kanta Tazo Da mganar Aiya ta Kushe Tace bazata Sabu ba Baba Habibu kuma Daman bamai mgana bane yace mgana tana Hannun Mastur Inya amince Shi bai da Ta cewa Mansur kuwa ba wanda ya gayamai mganar ansan Bakinsa Kamar Sikat kada ya gayama Mastur sai gashi Ta Kirashi Da kanta kuma Tunda yace Ta Kirashi Aranta Tasan mganar ne.


Cikin Sanyi  jiki da wani Raunin Zuciya ya Cigaba da Takawa Zuwa Shashen nasu,Gabadaya Zuciyarsa ta Shiga wani Sake sake na Daban kodai kodai Soyayyah suke yi ne..? Tunanin haka sai da Yaji Gabansa ya yanke ya Fadi Da Sauri ya karyata mganar bayan ya Girgiza kansa Acikin Zuciyarsa yana Fadin Da ace suna Soyayyah Tabbas da Mansur ya Fadamai baya Taba Boye masa komai,Tabbas da akwai Wani abu a Tsakaninsu Dashi ne zai Fara jin Labari Yin wannan Tunanin yasa yaji Hankalinsa ya kwanta har ma ya Karisa Shiga Shashen nasu Dayake Shuru Kamar ba Kowa.

Kamar zai wuce Bedroom Dinsa sai kuma ya Fasa ya Karkata Zuwa Dakin Mansur din ya Tura sai yaji a bude sai ya Tura ya Shiga gogan na kwance Baje Baje akan gado yana Barci Dagashi Sai Gajeren wando Dakin kaca kacs Daga gani ya Dade bai ga gyara ba Chan kaya Chan waya chan System Chan Takardu Takarce dai Gasunan.

Kai ya Dafe Cikin mamakin yaushe Kanin nashi Zai Sauya ne..?wata zuciyar tace mai kila sai Ranar da yayi aure ya zama magidanci.."Tuna Haka da yayi yasa ya Murmusa kamar zai Juya ya Fita sai kuma ya Fasa ya Fara Taku Zuwa Gaban makeken Gadon da Mansur Yake kai yana Sharar Barcinsa,Ya Dade Tsaye yana kallonsa kafin ya Duka yayi amfani da Hannunsa Guda Daya ya Murdemai kunninsa da karfi wanda yana Cikin Barci yaji kamar an Rike masa Kunnuwa sai yayi Tunanin mafarki ne,Sai ya kara Juyawa zai kara Bajewa Mastur ya kara Damke Kunnuwansa da karfi Wanda ba Shiri yasa Mansur ya Bude Idanuwansa da suka kankance Saboda Barci ganin wanda ke gabansa yasa ya Zabura ya Mike Zaune yana Mitsike ido Cikin Muryan Barci yace"Yaya Mastur na u..?

Bai ce mai komai ba Illah gyara Tsayuwa kawai da yayi yana dan Hararansa ganin haka yasa ya Sauko da Sauri Daga kan gadon ya Daka Tsalle ya Rumgume Yayan nashi yana ihun Murna da Faman Tambayansa yaushe ya Dawo bai sani ba Yana jinsa yayi masa Shuru bai tankamai ba bai Damu ba ya Dago yana Fadin"Yaya me nayi kake Fushi Dani..?
Yafada a Shagwabe kamar zai yi kuka Sai Lokacin Mastur ya kallesa yace"AU baka ma sani ba ko..?

Shuru Mansur yayi kafin yace"Allah Yaya duk iya Tunanina na kasa Tunawa..'Kunnensa Daya ya Murde yana Fadin"Ka manta da wayar da mukayi Dakai ta karshe..? Me nace maka..?ka Rainani ko Mansur yanzu ka Daina Jin mganata baka saka Komai agaba ba sai wannan Shanshancin Siyasan ko Daya maida kai wani kazami ko kanka Baka iya gyarawa,ji kanka Ka Tara suma ba aski ba gyara Kalli Dakinka kamar na Mahaukata bazaka iya gyarawa ba..? Whta Wrong With u ka Fara Hauka ne..?

Yafada Cikin Husky Vioce dinsa ammh Cikin Fada Saboda Bacin Ran abunda Mansur din ya aikata Mansur Zafi ya Isheshi Domin da Zafi ya Rikemai kunnin kuma yaki Saki,kara ya Saki yayi kasa da kansa yana Fadin"Wayyo yaya..Wlh kunnina Zafi ka Sakeni Plz...'Kara Matse kunnin yayi Da Karfi Har sai Da Mansur yaji kamar yayi kwallah Mastur yace"Yanzu ka Tuna Laifinka ko baka Tuna ba..?

Da Sauri yace"Na Tuna..Na Tuna..Wlh na Tuna yi hakuri Yaya bazan kara ba.."Sai Lokacin ya Sakeshi Lokaci Daya ya juya yana Barin Dakin yace"Ok..Kafin mu Fara Ainihin Fadan namu kafim ka Fito u Bettrr Clean dis Room ka gyara komai In bahaka ba Ranka sai yafi haka baci.."Da Sauri Mansur yace"Yes Sir...!Fita yayi yana Kyafci bai yi mgana ba yana Fita Mansur ya koma yana Rike kunnunsa Lokaci Daya yana Fadin"Wlh Ya Mastur yasan Lagon mugunta..Allah ma ya Taimakeni ya Daina kolo akai..Ai da naci Ubana yau.."Yafada yana yar Dariya Lokaci Daya Yana Tuna mganarsu ta karshen kan Gidansu ne Da auran kanwarsa Sakina Dayace yaje Chan Maruka ya gaida Baba Sule ya kuma Yi musu abunda ya kamata ammh Sam ya Manta Kansa ya Dafe kawai bai da ta Cewa Karamin Tsaki yaja jin ana ta Kiran Wayoyinsa Kamar Zai yi kuka ya Mike ya Fara Tattara Kayan daya watsar a kasa ko Ta kan wayoyin Dake Zube kan gado suna neman agaji bai bi ya Fara gyaran Dakin Sanin Da yayi in yayi wasaa Mastur ya Dawo bai gyara Dakin ba Yasan Sauran..


Diza kuwa Batasan Mastur ya Dawo ba 11am nayi ta HauraSama Tayi ma Mommy Sallama ta Hau Motarta ta Fice taso ta Shiga su gaisa da Hajja da Aiya Mansur kuma tasan bai Tashi ba yana Barcin gajiya Sai kawai ta wuce Tunda ana Jiranta Hauwa sai waya take mata tace in ta Dawo sai ta Shiga Ta isa wajen keman ba Dadewa ta Fara aikinta Sagir Abokin Mansur ya Kirata Tare sukayi Makaranta anan ABU,Shi bai samu aiki bane har yanzu sai Yake bin Mansur din yana Taimakamai Kamar dai P.A dinsa Shine ya Kirata yana Fadin yayi ta Kiran Wayar Mansur bai Daga ba Tace bata Gida Ammh bari ta Kirashi Taji itama Dai Kamar Sagir din ne Domin bai Daga kiranta ba sai ta Kira Sagir din Tace Kada ya Damu kila bai Tashi bane ya Bari zuwa anjuma ya Sameshi agida yace mata Shikenan ya gode da Haka suka yanke kiran..

Mastur kuwa yana Shiga Bedroom Dinsa yagansa Tsaf Dashi,Duk da ba haka ya barsa ba Daga gani an kara gyarashi kuma ba kowa bane ya gyara sai Hajja Mirmishi kawai ya Saki yana Jin Kaunar Mahaifiyar Tashi acikin Ransa Kayan Hannunsa ya Zube kan Katuwar Katifar Dake Shimfide adakin Wacce Taji Shinfidun alfarman Mastur Bai Cika son Gado ba Shiysa sai makeken Wardropr dinsa Dake Shake da kayansa Bai Tsaya wani Bata Lokaci ba yaTura Kofar Tiolet Din Dake Dakin ya Shiga wanka Yayi ya Fito Daure da Babban Towel Gaban Madubin Dake Dakin ya isa yaShafa mai kansa SayeSaye da gashi kadan Kadan Domin Mastur ya Tsani Tara Gashi Duk Sati yake Zuwa aski,In yaga Mansur ya Tara Gashi Ya Dinga mai Fada kenan Tun ba yau ba ammh bayajin mgana sam Har yau ya girma ammh bai San ya Girma ya Daina aikin Yarinta ba Shi yana mamakin yadds Har ya Fito Siyasa Partyn Dayake Ciki Ta karbeshi Sai dai kuma Bai da ja Mansur Mutun ne mai Dadin Zama Barkwanci da Son Mutane ya Tabbata Duk inda ya zauna Ko na awa Biyu ne sai sun ji suna kaunarasa Sau Tari In gayansa ya Shige Cikin su Hajja yana ta Hira sai ya Rika Bashi Sha"awa Domin shi bazai iya ba Mgana da Hayaniya kamar Lalura suka zamemai.

Jallibiya ya Zura Kawai ya Samu waje ya kwanta Domin ya gaji Tafiye ce fa ba Kadan ba Daga Porthercourt Zuwa Zaria Bai saba ba Domin Sau Daya suka Taba Tafiyan Mota kuma alokacin bashi ya Tuko Motar ba Sargent Inuwa ne,Ko takan Wayoyinsa bai bi ba daman suna Kashe ne ya Kwanta Yana Lumshe ido Saboda gajiya bai Dade ba barci ya kwashe Sai dai Mansur ya Shigo ya gansa yana Barci sai ya Fita ya Rufomai Kofa Ya Fice Daga Shashen Bayan yayi wanka ya Saka kananun kaya Na kamfanin Armani Shashen iyayen nasu ya Shiga suka gaisa da Hajja da Aiya suka Fara Diraman nasu ta Fama Hajja Tace Ina Mastur yace mata yana Ciki yana Barci ya Dade anan Shashen su Hajja kafin ya koma Barayinsu ya Dauko Wayoyinsa Kira ya Samu ba adadi Kiran Diza Shi yafi Muhimmanci ita ya Kira Take gayamai Kiranta da Sagir yayi.

Karamin Tsaki yaja yana Fadin"Kyalesa..Nifa yau ba Inda Zani..ina Fita Zan kara Laifi Wajen Ya Mastur..!Da Sauri Diza tace"Bangane ba..? Kunyi waya ne..? Da sauri yace"Ai Diran makiya yayimin Firstlday ta...Tun Safe ya Shigo..Kinga yadda ina barci ya Murdemin kunni Kamar zanyi kuka..Yana Dakinsa yana Barci yanzu Kafin  ya Tashi Barci na karbi Hukuncina.."Farinciki Daya Cika Zuciyar Diza Yaushe Rabon Da Taga Abun Sonta Wannan Labarin yayi mata Dadi.

Cikin Farinciki tace"Ka gano Laifinka kenan My Honourable..?yana shafa kansa yace"Eh..Kanmganar zuwa Maruka ne.."Kai ta gyada Tana Fadin"Uhm..Ai na sani.Mansur Allah ya Shiryeka.."Yana Dariya ya amsa mata sun dan Taba Hira Yacr yaushe Zata Dawo Tace Sai ta gama Sallaman Mutane Zuwa La"asar Zata Dawo kana suka Katse Kiran Diza Taji kamar an sakata a ajannah Tana aiki Tana Mirmishi ita kadai Har Hauwa sai Da ta kalleta Tana fadin"Madam kamar an biya miki Kujeran makka..?
Diza tayi dariya Tana Fadin"Kai hauwa saka ido ko..? Ai wannan Farincikin nawa yafi Biyamin Kujeran maakka."Tana Dariya Tace"Allah Madam..?

Bata kara mgana ba ganin basu kadai bane Ashagon akwai masu Jiran kwalliya da wadanda akeyimawa ammh Ranar Duk wanda yaga Diza Sai ya Fahimci Fara"anta ya Karu Sauri Sauri Take tana son Ta gama Komai Ta koma Gida Ta Sakashi acikin Idanuwanta.

Mastur bai Tashi ba sai Bayan Azahar Ya tashi da bacin ran Barci yasa bai samu sallah ba agurguje ya Fada Tiolet yayi alwala ya Fito ya Shimfida Darduma yayi sallah yana Zaune yana Addu"a Mansur ya Shigo Dakin sai ya gansa ya Tashi Cikin Fara"ansa ya isa Kusa Dashi ya zauna yana Fadin"Ashe ka tashi..?daman yanzu nake Shirin Zuwa na Tasheka Har munyi sallah
Baice komai ba sai da yagama addu"an kana ya waigo yana kallinsa Fuska ya Hade yana Fadin"Kasan Girman Matsayin Mahaifi Kuwa Mansur..?
Ganin irin kallon Dayake mai Da kuma yanayim Muryansa yasa ya gane ba wasa kai ya Dukar yana Fadin"Nasani yaya..Kayi Hakuri abubuwa ne..!

"Har akwai wani abin da zai hanaka zuwa ganin mahaifinka bai da lafiya..? Mansur ka bani kunya Bantaba Zaton Haka ka koma Da bana nan ba..Ka baci Sam yanzu baka da Tsausayi.."Mansur kamar zai yi kuka yana son mgana ya Hanashi Mikewa Mastur yayi yana Nimke Darduman Dake Hannunsa yace",Ko ka Dawo Cikin Hayyacika ko kuma na Dakatar da wannan Takaran naka na Dauke ka na maidaka makaranta ka Cigaba da Masters Dinka..Tunda naga Siyarsace ke Sakaka kana Raina mganata Data Baba kuma kana Banzatar da Mahaifinka da yan"uwanka.."

Yafada Lokaci Daya yana wucewa ya barsa a wajen Wajen Wayoyinsa ya isa ya Dauka Yana kunnawa Bayan ya Zauna da Rarrafe Mansur ya Kariso gabansa Hannunayensa Saman kunnnuwansa yana Fadin"Afuwan Yaya..Bazan karaba Insha Allahu.."Kamar bazai kallesa ba ganin ya Isheshi Da magiya ne yasa ya Sauke mai Hannuwan yana Fadin"Is ok..Ya wuce..Ammh ka Shiga Hankalinka.?
Da sauri Mansur yace"Nama shiga..Na Dade da Shiga Yaya Mastur.."Mganar sai tabama Mastur Dariya Sai da ya Murmusa yana Saka Hannu ya Dago Mansur din suka Mike Tsaye ya Rumgumesa Mansur Shima yaRumgumesa yana Murna Cikin Bubbuga Bayansa Mastur yace"Ba ina maka Fada bane..Ko ina so in ta kuraamaka ba..No..Nafi kowa Son kanina da kuma somganin Rayuwarsa ta Inganta.."

Hawaye suka Cika Idon Mansur ya Dago yana Kallon Yayanshi yace"Na yarda da Yayana..Yau ko Bayan Raina na Tabbata bazan yi kuka Rashin mai Zama Bangon na ba data ahalinmu ba."Hararansa yayi yana Fadin"Ka Shirya gobe ma muje marukan tare..Sai na Koma Jibi."Tsalle ya saka yana Fadin''Yauwa.."Mirmishi kawai yayi mai ya Dauko wayoyinsa yana Fadin "Muje Shashen su Hajja..Nasan yanzu Tagama min Tuwona.."

Mansur yace"Au daman wai kai take ma Girki.? Lalle Hajja son kai.."Mastur bai kulasa ba ya Fice yana Fadin"Ai daman kai kanka ka sani.Kullum haka kake Fadi.Alhalin kai kana Gida Ni kuma sai Lokaci Bayan Lokaci nake Zuwa.."
Mansur nabin Bayansa yace"Uhm..Ba wani nan Yaya Allah Hajja yanzu tafi sonka.."Yafada yana wani Tura baki Tsayawa Mastur yayi har yazo Suka Jera Suna Dafe da kafadun Juna kamar wasu yara In kagansu alokacin sai ka kara kallonsu Domin zasu Burgeka da ganin Irin Shakuwar Dake Tsskaninsu.



_Albishirunku Masoyana wannan karan na bude muku wani Shashi na musamman Saboda ku..Ina masu Bukatan Atalla musu Hajarsu Ko wani iri ne Domin samun costumer ta ko"ina..? Ku garzayo kakarku ta kusa yanke saka Zan Tallata muku Hajarku a Duka Shafukana Domin inganta Sana"arku da kuma Samun Cinikaya mai Tsabta da kuma kara Hada hada wajen Masi siye da Siyarwa mai Bukatar A tallata mata Hajjarta Zata iya min mgana kai Tsaye ta wannan Lambar Tawa 09069067488 domin karin Bayani...Sai kunzo Kunsan dai mai kasuwa Shi ke da Riba.._

*Domin zama Daya Daga cikin wadanda zasu karanta Labarin SADAUKARWAR SO..! Zaku Biya kudin karatunku kamar haka Masu amfani da Banki Zasu Tura â‚?300 ta wannan asusun banki 0552179550 Jamila umar gtb,Masu Katin waya kuma zasu Turo â‚?400, ta wannan lambar wayar 09069067488 Adauki Hoton katin sai aturo kai Tsaye mutanenmu na Niger kuma zasu Tuntubi wannan lambar kamar haka +22794775574 domin karin bayani,Insha Allahu mutum zai tsinci kansa a paid group ina maraba da ku masoyana Nagode*






"Janafty...*
1/1/22, 18:53 - Maryam Badmsi: *SADAUKARWAR SO..!!*
_(Labarin Yan"uwantaka,Soyayyah Tare da Sadaukarwa)_

*Wattpad:@Jamilaumar315*
*Mallakar:Jamilaumar(Janafty)*




*Page1�⃣3�⃣*


Shashen Hajja suka koma,Lokacin Hajja ta gama Tukama Mastur Tuwon Dayace yana so Tuwon Farar masara Tayi mai na gargajiya ba na Garin Semovita ba Da Miyar Bushashiyar Kubewa Dataji Bushashan Kifi wanda Shi Mastur din ne yazo musu da Kifin wanchan Dawowar da yayi.

Mastur yaci Tuwon nan Sosai Wanda Rabonsu Dayacii Abinci mai yawansa Har ya manta Yana Bala"in son Abincin Gargajiya Musamman kuma wanda Hannun Hajja ya Dafa Tun Lokacin Daya Tafi Hassan Gwarzo karatu Dandanon Abincin Hajja ya Wahalar Dashi kafin ya saba Hakama Dayaje Sokoto,A porthercourt kuwa Kowa ya sani ko Takeway zai bada ayimai ko Tuwon Masara ko Tuwon Shinkafa Miyar Alaiyahu,in dai aka ga yaci Shinkafa toh Babu Wadanan ne kuma yana jin yunwa bai da mafita.

Tare da Mansur sukaci Abinci kamar yadda suka Saba achan Baya ko ayanzu ma in ya Dawo Tare suke Cin Abincin Bayan sun Gama suka kara Zaman Hira Duk da Rabin Hiran Tsakanin Aiya da Mansur Sai Hajja Dake Saka musu Baki Jefi Jefi Mastur kuwa Duk da Hayaniya Lalurace garesa yau din ya Danne bai Tashi ba yana Zaune gefe Daya yana Bin Kowa da ido Baya Umh ballatana Uhm Ko Aiya ko Mansur in wani ya Sakosa Cikin Zencen baya mgana Sai dai yayi yake kawai Ya Lumshe ido basu Damu ba Sanin Hallinsa Haka kurum yake ji aransa Dama Shine Mansur fa Yana son ya zauna ya Dinga Hira da Mutane yana Sakin Jiki Dasu ammh Kwata kwata Baya iyawa ko yana so ya Daure ya Rika Shiga Cikin Mutane sai ya kasa Daya Shiga sai yajisa wani iri da an Fara Hayaniya da Surutu zai ji ya Tsani Zaman wajen Yau din ma Saboda Cikin Ahalinsa ne kuma ya Dade baya Gida Shiyasa ya Daure kawai ya Zauna yana Jinsu kuma yana Kallonsu Daya Gaji ne ya Tashi ya Shige Dakin Hajja ya kwanta,da kallon suka Bisa Sun Tabbata yayi kawaicin ne ya gaji ya Tashi ya Gujema wannan Hiran ta Mansur da Aiya wacce Duk Rabinta Gaddamane da Labaran da bai ma Shafesu ba,yana Shiga ba Dadewa Shiima Mansur ya Fita Sagir ne yazo bayan ya Fita sunyi mgana ya Dawo yace su Hajja zasu Fita da Sagir in Yaya Mastur ya Tashi Ta gayamai ba Dadewa Zai yi ba tace toh.

Mastur barci yayi akan gadon Hajja bai tashi ba sai da aka Kira Sallar La"asar kana ya Tashi ya koma Shashensu ya Dauro alwala ya Tafi masallaci Bayan ya Dawo ne ya Koma Dakinsa ya kunna System dinsa ya Fara Duba Sakonnin Muhimman Bayanan da aka Turomai ta Email Dinsa,Jefi Jefi kuma yana amsa waya Hajja ta gayamai Fitan Mansur ammh yana ta Tsumayin Dawowarsa Shuru.

Diza kuma Bayan La"asar ta baro Wajen aikinta Zuwa Gida Tana Dawowa Zumudin ganin Mastur yaki barinta Ko Abinci Bata iya ci ba tayi wanka tayi Sallah Tayi Shigan Wata Ubansu Jallabiya Red Colour mai kyau da ita ta yane kanta da Mayafin Jallabiyan ta Saka Wani Takalminta mai Tudu Ja Mai kyau Dashi Wayarta ta Dauka acikin Jakanta ta Haura Sama Dakin Mommy Ta isketa Tana Lissafi kusa da ita ta Zauna Tana Fadin"Mommy barka da yammah.."

Mommy Ta Dago Tana kallon yar nata Tana Fadin"Yauwa..Diza yaushe kika Dawo..?Diza tace"Ban dade da Shigowa ba..Wanka kawai nayi sai nayi sallah.."Kai ta kada Tana Fadin"Oya tashi kije Fadime ta baki abinci kici ki Huta nasan Kin gaji.."Mirmishi Tayi Tace"Mommy bana Jin yunwa Fita ma zan sake yi.."

Sai Lokacin Mommy Ta Lura da Kayan Dake Jikinta Cikin mamaki Tace"Ina kuma Zaki Daga Dawowarki ko Hutawa bakiyi ba .?ko Fita zaku yi da Mansur ne Nasanku Sarakan yawo kamar kafarku taci kafar kare.."Dariya ta saka ta Mike Tana Fadin"Kai Mommy kema Idon kika Sama na kamar yadda Aiya ta Riga ta sakamana.."

Mommy tace"ai gaskiyanta ne..Bakwa Zama waje Daya..Kune Chan kune chan Kamar wasu Sabbin Aure.."Diza ta Murmusa Tana Fadin"To ba inda Zamu Tunda an sakamana Ido..Gidan Hajja zan Leka in yi ma Yaya Mastur barka da Zuwa.."Mommy tace"Mastur.! ? Yaushe ya Dawo   ? Tafada Cikin Farinciki Diza Tace"Yau da Safe Dazu mukayi waya da Mansur yake gayamin bai Shigo bane..?

Mommy Tace"A"a kila sai anjuma In Daddynki ya Dawo..In kinje kice ina mai Sannu da Zuwa Ina nan ina Jiransa Ban yi Fushi ba..Ki gaida Hajjan da Aiya.."Diza Ta Juya Tana Fadin"To Mommy Zan Fadamusu.."Daga haka ta Fice ta Sauko kasa kenan suka Hade da Mama Fadime tagaisheta ta amsa Tana Tambayanta ya aiki tace ba Dadi Tayin Abinci Tayi mata Tace Sai anjuma bari ta Shiga Gidan Hajja Mama Fadime ta Bita da adawo Lafiya.

Lokacin Data Shiga Gidan Aiya Tagaji Da Hiran Ta Shigo Ciki Tunda Ta Shiga yin Sallah Hajja ne aharaban Gidan Tana kwashe Shanyan kayan Aiya Data Wanke mata da Safe,Diza ta Duka ta gaisheta ta amsa Cikin Fara"a Tana Tambayan ta Mommy Tace Tana gaishesu ita da Aiya Mikewa Diza Tayi ta Karbi kayan Hannun Hajja Tana Fadin"Hajja Ina Aiya ne Banji Motsinta ba.."Tafada Lokaci Daya Tana kallon Motar Mastur Dake Haraban Gidan Daman tasan yana Gida in yazo garin Baya Zuwa Ko"ina Daga Gida sai kuwa in ya Shiga gaida su Mommy ko ya Leka Gidan Balaraba Gaishe da Kawu Usman.

Hajja Ta bata amsa da Fadin"Aiya Tana Ciki..Suna nan Zaune Tun Wajen azahar ita da Mansur da Babban Mutum..Babban Mutum ya Gaji da Hayaniyarsu kinsan Halinsa ya Tashi ya Shiga Ciki ya barta Ita da Mansur Shima dai ba"a Daden ba Abokinsa Sagir din yazo Suka Fita yacr bazai Dade ba Shuru dai Har yanzu..Shine Ana kiran La"asar ta Shiga Daki Tayi Sallah bata Fito ba Kila Ta Dan Kishingida ne.."

Diza na Bin Bayan Hajja Zuwa Falon tace"Ayyah..Yaya Mastur din Fa Hajja..? Hajja tace"Yana Shashensu Bayan ya Dawo Sallar La"asar yace min zai Shiga yayi wani aiki ne.."Diza Ta Zauna kan Daya Daga Cikin kujerun Falon Tana Taya Hajja Ninke kayan Take Fadin"Bari na Shiga mu gaisa..Mommy ma tace nace Tana nan Tana Jiransa Batayi Fushi ba.."

Hajja na Dariya Tace"To Daman Ta ina uwa ke fushi da Danta..Zai shiga inajin Sai Zuwa Dare Lokacin Baban nashi ya Shigo da Alhaji.."Diza tace"Hakane.."Hajja Tace"Kinga Hadiza Ijiye Kayanan ki Tashi kije ku gaisa..Bana komai Zan karisa Dakaina kin Dawo Daga wajen aikin ki kin gaji bazan kara Sakaki wani aikin ba..'Diza Tace"Kai Hajja Don Allah ki barni na kusa karisawa.."Dole Hajja ta kyaleta suka Karisa Ninke kayan ita ta karbi kayan Tayi sallama Dakin Aiya Ta ganta Akan Abun Sallah Tana ta Barci Azaune Dariya ya kamata aranta Tace Dole kiyi Barci Aiya..Ko Gajiya da Surutu Bakyayi.Kan karamin gadonta ta Ijiyemata Kayan ta Fito Tace ma Hajja Bari ta Shiga ta Fito Daganan ta Fice Zuwa Shashensu Mansur din Lokaci Daya Taji gabanta na Faduwa Wanda Inda ZataTunkari inda Mastur yake Haka Zata Rika Fama da wannan Faduwar gaban,wanda in Zata Shiga Wajen Mansur bata jin irin Haka kanta Tsayr ma take Shiga Sanin Mastur din Baya nan sai Mansur din shi Kadai.!

Cikin Sanyin Jiki ta Fara Knooking a kofar Falon nasu ammh kuma Shuru Har tsawon wasu Mintina Sai kawai ta yanke Shawaran Tura kofar sai gashi ta Bude,Sai ta sawo kanta Falon da Karamar sallama abakinta Sanyin Ac Dake Falon ya Daketa Ta Lumshe kafin ta Fara Taku zuwa Cikin Falon Dakin Mastur Take kallo Data gani adan Bude Sabanin Dakin Mansur Dake Rufewa Tana Takawa Zuwa Dakin Gabanta na Faduwa kamar Ta jiya Haka takeji ammh ta kasa.

Sai da ta Tsaya akofar Dakin Tayi Sallama Cikin Siririyar Muryanta Lokaci Daya Taji Kafafunta na Rawa Lokacin Dataji Muryansa yana Fadin Ashigo Cikin Karfin Hali da Jarumta Ta saka Hannu Ta Tura Kofar ta Shiga Cikin Dakin tana karayin Wata Sallaman.

Kansa na Kasa yana ta aiki Bisa System dinsa atsakiyar gadonsa Tun Datayi sallaman Farko Yaji Muryantq ya Shaidata Ko Mutuwa yayi ya Dawo zai iya Shaida Muryan Dizan Daya gama Tantaceta Tun Shekarun Baya,lokacon Data Shigo Cikin Dakin Bai yi Saurin Dagoewa ba Duk da Yadda Zuciyarsa Tayi Tsalle Waje Daya Saboda Murna ganinta sai ya basar ya Dago kansa a Hankali yayi mata kallo Daya ya kauda kai Bayan ya amsa Sallamanta.

Lokacin Daya kalleta kamar TaKafafunta Zasu kadata Saboda wani irin yam Dataji ya Tsirgamata Tundaga Kafarta Har saman kanta Dakyar ta iya Zare Takalmin Kafarta Ta Fara Taku Har Cikin Dakin Gefen Gadon Ta samu matsunguuni Ta Dofana Duwawunta Tana Gaisheshi ya amsa batare daya Dago ba,Sai da Tagama gaishesa ya Dago yana kallonta Kasa kasa ganin Ta wani Zauna kamar Ana Koranta kuma ta wani Sunkuyar Dakai yana mamakin Yadda yarinyar take mai Girman kai ko don Yana mata Fada ne in tayi ba Dadai ba Ko kuma Saboda Baya musu wasa Tun Baya Daga ita Har Mansur din.

Cikin Dakakkiyar Muryansa yace"Ki zauna Dakyau mana.."Jin Abunda yace ne yasa ta Dan gyara Zamanta Taa Dan Muskuta Tana Fadin"Mommy Tace tana gaisheka..Kuma wai Tana nan Tana Jiranka batayi Fushi ba.."Kamar bazai Tankata ba Sai da ta Saci kallonsa Taga yana Dan Mirmishin nan nashi mai Tsada Chan Taji muryansa Cikin Kasaita yace"Zan shiga anjuma in Daddy ya Dawo.."Daga haka bai kara mgana ba itama Sai ta Dauke kanta Kamar bata kallonsa Tana ta wasa da wayarta Dake Hannunta.

Shuru na wani Lokaci ita Tana Zaune kanta a kasa Bata kara mgana ba ammh Zamansu a waje Daya yana kara Sakata Cikin Natsuwa bataki su Dauwama ahaka ba Har Abada ba,Shi kuma yana auna Yadda Dizan ta koma ne yanzu yana mamakin Inya gansu Tare da Mansur Wani bayama wani Fada ammh In suka Hadu kamar Salaha take komamai Sai yake Danganta Haka da Girman kai takemai ko kuma wani Shariyace bai sani ba..
Wayarta ake ta Kira Tana kin Dagawa yana jinta karan Wayarce ta Dameshi Da wani Zafin Zuciya yana Tunanin kada ace wani Namiji ke kiranta Cikin Muryansa Ta Dakiya yace"Ki Daga wannan wayar taki..Kararta na Damuna..".
Da sauri tace"Hauwa ce ke kirana..Wacce ke taimakamin Bangaran Office dina na Makeup.."Bai kara mgana ba ya Dai kalleta ta gefen ido Ganin Ta Daga Kiran Tana Fadin"Ya akayi ne Hauwa..?
Baisan me ake ce mata ba Daga Karshe dai tace"Hauwa kiyi ma wadanda sukayi Bukking na Gobe..Kuma ina Gayamiki bana sin zari..Kada ki Cikamana Mutane Mutane Goma sun isa in kuma kika Cika Wlh ke zan bari da aiki Am Telling u.."Dagachan Bangaran Hauwa na Dariya tace"Bakomai Madam.."Daga haka ta yanke Kiran Duk yana Jinta ita kuma Sai Ta gama wayar ta gano Laifinta da Sauri Tace"Kayi Hakuri..Zan yi waya ban Fita ba Allah sa Hayaniyata bai Dameka ba..'

Bai tankata ba Har ta Cire rai Sai Taji yace"Kin fi jin Dadin wannan Sana"ar taki da Cigaban Karatunki Khadija..?
Yafada yana Kafeta da Idanuwansa masu Firgitata da Sauri ta Sadda kai ta kasa Mgana Ba Tun yau ba yasha mata mganar Cigaban Karatunta Dama Dama ace Zata iya Karatun Datayi Saboda Cikama Mastur Burinsa Sai Dai kuma Bazata iya Juran Wahalhaun Karatun ba kuma Ba Ra"ayinta bane yin Karatu bai Zurfi Hakan tafi jin Dadin Rayuwarta So Simple.

Ganin ta kasa Mgana yasa ya kada kai yana Fadin"Is ok..Tashi kije..Tunda haka kika zaban ma kanki..Ammh ki Sani akwai Watarana da Zatazo kina son Kiyi Karatun..Ammh kuma Lokaci ya Riga ya Kure Miki.."Yafada yana Jin wani Takaichi acikin Ransa Kamar akan kaya take ta Mike da Sauri Ta Juya ta Fara taku Zata Fita yayi Galala yana Binta da kallon Soyayyah Muradi Sha"awa da Kauna Ta Har abada Sai gaahi ta waigo Sun Hada ido Irin kallon Dataga yana mata yasa ta Saka takalminta da Sauri ta Fice Ta Rufomai Kofan tana Sauke Numfashi Dakyar ta iya Jan Kafa ta Fice Daga Shashen Saboda Halin Datake Ciki Ko Shashen su Hajja bata koma ba ta Fice Daga Gidan Zuwa Gida Gabadaya Soyayyar Mastur Data Binneta acikin Ranta Taji Tana ta Fitowa Daya Bayan Daya,Har ta Shiga Cikin gida Jikinta bai bar Rawa ba Dakinta Ta Fada ta Rufo Kofa Ta Dire kan gado Tana Haki kafim Lokaci Daya kuma wasu Hawaye suka Fara Zubomata kanta Ta Dafe Tana Fadin"Ya zan yi ya gane ina Matukar Sonsa..?me zan yi Nima ya Soni Kamar yadda Nake sonsa..?
Haka take ta Fada kafin ta Sulale kan gadon ta Fashe da wani marayan kuka wanda yake Fitowa Daga Karkashin Zuciyarta.

Shikuwa abagaran Mastur yayi kokarin Zama Namijin Duniya Bayan Fitan Diza bakinsa ya Cija yana Kada kai Har sai yaushe ne zai iya gayamata Yana Sonta..? Watarana ne zai gayamata Ya Fara sonta ne Tun bata mallaki Hankalin kanta ba..? WaniDare zai Tabbata Dare mai Albarka da Tarihi a garesu..?shima bai sani ba ammh Tabbas in ya Cigaba da Zama ahaka yarinyar Zata kasheshi Lokacinsa bai yi ba.
Sai dakyar ya iya yakice Tunaninta ya Cigaba da aikinsa Har Mansur ya Dawo Dole ya Ijiye aikin ya Cigaba da yima Mansur din Fada da lallashi yana kara Nunamai Muhimmancin Iyaye da kuma yan'uwa Har Mansur din ya gamsu yace mai insha Allahu Hakan bazata kara Faruwa ba,Da haka suka Cigaba da Hiransu Rabin Hiran Duk Mansur ne yana Bashi Labarin Siyarsu da Halin da ake Ciki Sjidai yana jinsu wani wajen yayi Mirmishi wani wajen kuma Dayaga yana da ta cewa sai ya Tofa albaarkacin Bakinsa Har aka Kira Sallar mangariba suka Fita Zuwa masallaci Mastur bai bari sun Dawo ba sai da suka Tsaya akayi Sallar Isha"i wanda Tare da Daddy da Baba Habibu akayi ta Sai Bayan an Idar da Sallan ne suka ga Mastur wanda ya Duka yana Gaishesu Daddy ya amsa Cikin Farinciki ya Dagosa yana Shafa kansa Basu Tsaya wata mgana ba Su Mansur da Baba Habibu suka Nufi Gida Bayan Mastur din yace Zai Shigo kafin ya kwanta.

Suna komawa suka Hadu anan Falon Hajja,Baba Habibu nata Tambayan Mastur wajen aikinsa yana amasa mai,shi kuma Mansur yana Kitchen Wajen Hajja sai gasu sun kawo Abinci Shinkafa da Miya da Salat,Sai Tuwon da Mastur yace a Dumamai Shi zai ce,Baba Habibu na gani yacr Hajja Tayi Sonkai Shima Tuwon yake so Mastur yace Bari ya wanko Hannu sai suji Tare Mansur na jin Haka yace Shima Dashi Za"aci,Haka kuwa akayi su uku suka Taru suna ci Tuwon Cikin Farinciki Bayan sun gama ne Mansur da Baba Habibu suka Kara da Shinkafa Shi kuma Mastur yana gefe yace ya Koshi Yaje Kitchen ya wanko Hannu yazo ya zauna yana Kallon Baba Habibu ganin haka yasa ya gyara Zama yana Fadin"Babban Mutum ya akayi ne..?

Mastur yace"Baba kan mganar Zuwa Maruka Duba Baba Sule..Gobe zamu Tafi da Mansur in Zaka samu zuwa sai mu Tafi Tare ."Baba Habibu yace"Ba Mtsala Allah ya kaimu..Kayi Tunani kwarai kuma ina Fatan kayi mai Fadan Sakacin da yake yi da Iyayansa da yan"uwansa."Mastur ya gyada kai yana Fadin"Namai Fada Baba.."Mansur ya Tura Baki yana Fadin"Ni wai Baba sai kayi ta cewa amin Fada.."Aiya Dake gefe tace"Kana jin mgana ne..? Tun kana yaronka kake Laifi.."Hararanta Yayi yana Fadin"Kefa Daman yar saka Ido ne Aiyan nan.."Yafada yana wani Mele mata baki Ta Jefeshi da Murfin kula Tana Fadin"Kada kamin Rashin kunya..Ga megidana akusa in saka ya sakayamin kai.."Dariya ta kama su Baba Habibu Mastur ma sai da ya Murmusa.

Hajja ce ta kalli Baba Habibu Tana Fadin"Kaji ashe ya karime ta Kira Babban Mutum..? Baba Habibu Dake sakacen Hakori ya Kalleta yana Fadin"Topha..Me tace mai..?kardai kan mganar Busharan ne..?
Hajja na kallon Mastur tace"Bansani bai gayamin komai ba ammh ina Zaton akanta ne.."Baba Habibu zai yi mgana Mansur yace"Wata Busharan kuma Hajja..?Kafin suyi mgana Aiya tayi karaf Tace"Busharan Karime mana..Wai Saboda Shirmenta Taga Megidana ya zama Ubansu Take so ta Hadashi da Bushara yarta.."Mansur ya waro ido Yana Fadin"Wai ya tafi da ita Porthercourt tayi mai aiki..?

Dariya Ta kama Mastur Sai da ya Murmusa Allah ya Shiryi Mansur Baba Habibu ne yamai Dakuwa yana Fadin"Kaga naka nan Mansur..Ko Zai dauki yar aiki mai Zai Hadasa da Daukan mace Kuma ma yar"uwansa.."Mansur yace"Ah Baba in ba yar aiki ba Bushara fa..!wlh a yar aikin ma xai Taimaka mata ne.."Aiya Tace"Kai Sakarai waye yace maka yar aiki ce..? Wai fa ya Aureta..?

Mansur ya Zaro Ido Kamar yaji Mugun Abu yace"Au...? Na shiga Uku ni Mansur Sulaiman Doguwa..Ammh Inna karime Ta Gama da Ya Mastur wannan Bakauyan yarinya Kazama da wani katon Bakinta kamar Dankalin Kasa ne Zata Auri Yayana Son kowa kin Yarinyar Data Rasa..? chab wlh da Sake wannan ma Allah Yaya in ya kalleta ayyada yake zai iya yin amai.."Hajja ce Dake kusa Dashi Ta Sakarmai Dundu Tana Fadin"Zan ci Mutumcinka fa Mansur.."Yana Dariya ya Tashi Da Gudu Zuwa Bayan Mastur yana Fadin"Wlh Yaya kada ka yarda..Uhm.Wlh ka yarda ka Aurta achan Wajen aiki Sai an Daina ganin Girmanka.."Hajja ta Sake Dakamai Tsawa Aiya tace"Ke Hajara ki kyaleshi mana..Karya ya Fada..? Kamar yadda Karime take yaya gareki Ni Uwa nake gareta ammh fa Bana Goyon bayan Karya da Cuta Kin gani nan."
Mansur ya Daga mata Hannu yana Fadin"Yauwa Aiya..Ko kefa..Zan yi meneji Dake in na zama gwamna ko Shugaban Tsoffin mata na baki.."Baki ta Washe Tana Fadin"Haba Honorobul ko dai Mukamin Fisladi din.."Gabadaya Su Baba Habibu suka saka Dariya Mansur Har yana Tuntsirawa Ya Dago yana Fadin"Aiya bafa Honorobul ba Honourble akace..Ba kuma Fisladi ba Firstlady akace mtsalan ba Turanci.."Mastur ne ya Murdemai kunni yana Fadin"Baakajin mgana ko..? Ihu ya Fara yana Fadin"Na bari Yaya kunnina..Srry.."sakinsa yayi yana Mirmishi Aiya kuma Rai Ta Bata Tana Fadin"Koma miye..dai nadai Fada Daidai ehe..Dakace cewa ba Turanci kafi ni iya Fada ne..?

Mastur ne yace"Bai fi ki ba Aiyata..'Baki ta Washe Tana Fadin"Yauwa Megidana na kaina.."Baba Habibu ne yayi gyaran Murya yana Fadin"Babban Mutum me kace game da mganar Kariman..? Abunda ka yanke Shine Daidai Tunda Kaine keda Wuka Da Nama..?

Shuru yayi bai yi mgana ba Mansur yayi karaf yace"Baba Allah baya sonta baz.."kallon da Mastur ya bishi Dashi ne yasa yayi Shuru yana Sosa keya Kai Mastur yadan gyada kafin yace"Baba nifa ba yanzu zanyi Aure ba..Ta aurar da ita in ta samu Miji nayi mata alkawarin Bata Dukkan wani Taimako in Hskan Tataso.."Aiya tace"Shikenan Fakat.kagama mgana.."Baba Habibu yace"Hakane kayi mgana..Ammh mganar ba yanzu Zakayi aure ba ai Shirme ne Babban Mutum kafa Girma ga Mansur Dukkanku kun Isa Aura Shi yama sani Lokacin Daya samu Kujeran kansila ya samu Tawaye kan Rashin Auransa ba Domin Alhaji ya Shiga ya Fita da bai Samu Ba..Yau da yake neman kujeran Chairman Bamai Zaban sa bai da mata Shima ya sani Ballatana kai da Kake gaba Dashi.."Hajja da Aiya suka Hada Baki wajen Fadin"Gaskiya ne.."Shuru Daga Mastur Har Mansur sukayi Mansur yana so yayi mgana ammh kuma yana Tsoro ganin Mastur bai ce komai ba.
Mikewa Baba Habibu yayi yana Fadin"Ku tashi kuje ku gaida Babanku..Shima nasan mganar zai yi muku Domin Ya Dade Daman yana tuntubata kan mganar.."Batare da Mastur yace komai ba ya Mike yana Fadin"Sai da safen ku.."Mansur ma ya Mike Hajja da Aiya sukayi   ma sai da Safe sukuma suka Bisu da Allah ya tashemu Lafiya Domin Daga Gidan Daddy Shashensu zasu wuce.

Har suka shiga Gidan Daddy Ba wanda yayi mgana Mansur yana so yayi mgana kuma ganin Mastur ya Hade rai yasa ya kama Bakinsa Afalon kasa suka Zauna Mama Fadime ta Haura Sama Ta gayama Mommy,Diza na Cikin Dakinta Tun Bayan kukan Datasha bata Fito ba Wanka ta Sakeyi ta Saka Kayan Barci Riga da wando masu Taushi,Ta Fita Kitchen ta Hado Tea ta koma Daki Tana Sha Tana Duba Sakonnin Da aka Turomata Duk Ranta ba Dadi Mommy Data lekota sai tace Batajin Dadi.
Kamar wasa taji muryan Daddy da Mommy a Falon kasa alhalin Tasan basu cika zama ba sai Falon Sama batare da Tayi Tunanin Yafa komai ba ta Fito Ko Dankwali Bata Dashi Kitson Kalaban da Hauwa Tayi mata sun Bazu a Kafadanta Dayake Tana da gashi Wadanda ta gani Zaune saman Cafet gaban Daddy da Mommy ne suka Sakata Ta kasa Karisowa Jikinta sai ya kama Rawa Mastur Da yayi mata kallo Daya ya kauda kai Yana Jin Bugun Zuciya da wani Sanyi Sanyi na Shigarsa Mansur kuwa Kura mata ido Yayi Cikin Soyayyah da Muradi..
Mommy ce ta Ganta Sai ta kalli Daddy Tana Fadin"Ga wata ma Gandamemiyar Budurwan ka manta da ita Alhaji..Itama Diza ya kamata in sun Fito da matan Aure itama kce ta Fitar da Miji mu Aurar da ita mu Huta Tunda ba Karatu take ba.."Ta Fada Tana Nunata
Jin Abunda Mommy tace ne yasa Diza ta Zaro Ido Lokaci Daya ta juya ta koma Cikin Dakinta Gabanta na Faduwa Ta Fito da Mijin Aure..? Suma su Ya Mastur mganar Matan Auran Daddy ke musu..? Wani Mirmishi Ta saki kafin tace"Inaga Lokaci ne yazo..!

Achan Falo kuwa Diza na Shigewa Mansur ya Juyi yana kallon Daddy Cikin Sosa kai yace"Ai ni Daddy ta kwana Gidan Sauki..Daman Lokaci nake jira da kuma Yaya Mastur kada ace nayi gaggawa.."Daddy da Mommy Harda Mastur suka Kafeshi da ido Daddy yace"Gaggwan me Honourble..?
Mansur na sosa kai Duk kunya ta kamashi yace"INA DA WACCE NAKE SO TUN TUNI..!

Gaban Mastur ya Fadi Ras..Ya kara Ware ido yana kallon Mansur Daddy da Mommy suka Washe baki suna Fadin"Masha Allah Abu yayi kyau.."Mommy tace"Yar ina ce Surukar tawa..?

Kan Mansur na kasa yace"Mommy Yaya Mastur zai gaya  muku zan Fadamai Daga baya.."Daddy na Dariya yace"Ba Damuwa muna Jira..Kai kuma Babban yaya kaima ka Kokarta a Duba dai zaman haka Bai Dace ba Shekaru nata Tafiya.."Mastur Dayaji Jikinsa yayi sanyi Cikin Ladabi yace"Insha Allahu.."Daganan sukacigaba da Hira Rabin Hiran Ta Bangaran aikin Mastur Ne shiyasa Saboda Daddy nema yake Bude baki yana Bashi amsa,anan ne ma yake Fadamai Tafiyansu Maruka Gobe Daddy yace Shima zai Bisu Goben Daman bazai Fita Kamfani ba,Basu bar Gidan ba sai 11saura na Dare kana suka yi musu Sallama suka Tafi Diza kuwa Farinciki yasa tuni tayi Barci da Wuri batasan Tafiyarsu ba...
Suna Shiga suka Kulle get din suka Nufi Shashensu Ranar Mansur Dakin Mastur ya Tattaro ya kwana ganin Dare yayi ga Gajiyasa yasa bai mai mganar Diza ba ya bari sai Gobe to Gari na Wayewa Karyawa kadai sukayi suka Dauki Hanyan maruka su Hudu Daddy,Baba Habibu ,Mansur da Mastur a Motar Mansur sukayi Tafiyan Kuma Mansur ke jan Motan.



_Albishirunku Masoyana wannan karan na bude muku wani Shashi na musamman Saboda ku..Ina masu Bukatan Atalla musu Hajarsu Ko wani iri ne Domin samun costumer ta ko"ina..? Ku garzayo kakarku ta kusa yanke saka Zan Tallata muku Hajarku a Duka Shafukana Domin inganta Sana"arku da kuma Samun Cinikaya mai Tsabta da kuma kara Hada hada wajen Masi siye da Siyarwa mai Bukatar A tallata mata Hajjarta Zata iya min mgana kai Tsaye ta wannan Lambar Tawa 09069067488 domin karin Bayani...Sai kunzo Kunsan dai mai kasuwa Shi ke da Riba.._

*Domin zama Daya Daga cikin wadanda zasu karanta Labarin SADAUKARWAR SO..! Zaku Biya kudin karatunku kamar haka Masu amfani da Banki Zasu Tura â‚?300 ta wannan asusun banki 0552179550 Jamila umar gtb,Masu Katin waya kuma zasu Turo â‚?400, ta wannan lambar wayar 09069067488 Adauki Hoton katin sai aturo kai Tsaye mutanenmu na Niger kuma zasu Tuntubi wannan lambar kamar haka +22794775574 domin karin bayani,Insha Allahu mutum zai tsinci kansa a paid group ina maraba da ku masoyana Nagode*










*Janafty..*
1/1/22, 18:53 - Maryam Badmsi: *SADAUKARWAR SO..!!*
_(Labarin Yan"uwantaka,Soyayyah Tare da Sadaukarwa)_

*Wattpad:@Jamilaumar315*
*Mallakar:Jamilaumar(Janafty)*



*Page1�⃣4�⃣*


"Sun isa Doguwa Local goverment da wuri cikin maruka Sun iske Jikin Baba suLe da sauki har ya fara Fita Kofar gida haka yana ganin gari ammh baya Doguwar Tafiya.

Yaji Dadin ganinsu Baba Habibu karin Farinciki ma Har da Daddy,Haka aka Dinga ina aka Saka dasu yan"uwan Mansur kuwa haka suka Zagayesa,Mariya Dake gidan Auranta ana gayamata sai gata Maryama Daman Tana Gida Tunda auranta ya mutu,Sakina kuma ana Shirya Shiryan Auranta ne sai karamar su mardiya,da sauran yaran,Fadan da Mastur yamai yasa yaja su acikin Jikinshi Zainabu kuma tayi sanyi yanzu Tunda Goggo Ta rasu bamai goyamata baya Kuma Taga Mansur din ya Girma Allah ya Daukakashi Shike Taimakonsu Shi da Zuru"an Maryama din.
Sun Dade anan Marukan Da Zasu Tafi Dubu 100k Daddy yabama Baba sule na Hidinar Bikin Sakina Mastur kuma ya bashi 50k yace yaje asibiti a Dubashi Suka Fita waje suka Barsa Tare da Mansur su gana amtsayin D"a da Mahaifi ga Yayyin Babansa Baffanshi suna Waje suma suna Jiransa...

Mansur Shima Dubu 100k ya bama Baba Sule yace na Hidimar Gida,Mgnar kayan Dakin Sakina da komai da komai kuma ya Daukeshi yana Hannunsa,wannan kudin Daya bashi yaje asibiti sauran kuma ayi Hidiman Gida Dashi Baba Sule yana ta Godiya kamar ya kwantamai ya Shiga Dakin Zainabu yayi mata sallama ya bata Dubu 10k ya kuma ce Maryama ta Shiga makaranta Ko ta addini ne Tunda auranta ya Mutu zaman haka ba amfani Tunda sunyi sskaci basu yi karatun Boko ba,mardiya kuma in ya dawo zai tafi da ita wajen Hajja tayi karatu Zainabu ta karba Tana ta Godiya Harda kwallah Tana Tuna irin Zaman daya Gudana Tsakaninta da Maryama sai gashi yau Abunda ta Haifa ne Bangonsu.

Daya Fita suma Baffanin nashi Duk sai da ya Sallamesu 10k kana suka Rabu kan sai Bikin Sakina wanda Zatayi aure Acikin Garin Doguwa,daganan Ririwai suka yada Zango Gidan Karime Wacce kamar ta Fadi Saboda murna bakinta Kamar zai Cire Saboda Fara"a Ita a tunaninta mganar Bushara da Mastur ne ya kawosu nan da nan ta aika akira mata Bushara Daga Bakin Kasuwa inda take Saida Masara Dafaffiya,Bayan tazo Tayi mata Rada a kunni sai gashi tazo gaishe dasu Baba Tana ta wani Sunne kai wai kunyar Surukai Sai Lokacin Baba Habibu ya gayama Daddy mganar da Karime tazo Dashi Kan Bushara din Shima sai da yayi Dariya Shi ko Mansur Vidoe ya Dinga Daukanta Lokacin Datake gaishe da Ya Mastur kanta a kasa Kamar Zata mai Sujada Sai wani Sunne Kanta Take cikin Hijabi Mastur ko bi ta kanta bai yi ba ma Balle ya Fahimci wani Hali take ciki ba Ruwa Kadai suka sha agidanta Saboda sun sha Fura agidan Baba Sule Lokacin da Inna karime Taji bayanin Baba Habibu kan Ra"ayin Mastur kan Bushara sai da taji kamar Tayi kuka Har suka Tafi Bata kara Dariya ba Bayan sun ijiye mata kudi Daga Mansur har Mastur din sai bayan sun Fita ne Bushara ke Tsallen Murna Inna karimen ta Zabgamata Harara Tana gayamata yadda suka kare Dasu sai ga Bushara Har da kuka Tana Tunanin ta Samu Zankadeden Saurayi kuma sai taga samu Taga Rashi..Inna karime najinta Tana kuka Tayi mata Banza Babanta ma Dayazo Yaji Sai da yayi Dariya Daman karime bata jin mgana Sai da ya gayamata Ina Bushara Data Tashi a Kauye ina Mastur wanda Yayi gwagwamaryan ilimi ai Hadin ba Daya bane sai tace ai shima Mastur din A kauyen aka Haifeshi Duka Daya suke Dole yayi mata Shuru,Ammh Yanzu Dataji mganar Daga bakin masu yi ai sai ta bar mganar Dolenta.

Aranar da suka koma kano Mansur yaso yayi ma Mastur mganar Diza sai dai kuma bai Samu Dama ba sun Dawo a agajiye kuma Shima adaran Shugaban Partysu ya Kirashi Dole ya tafi bai dawo da wuri ba Koda ya Dawo Mastur ya gaji Har ya kwanta Gari na waye kuma Karfe 8:30am na Safe Mastur yayi sallama dasu Hajja Da Baba Sule ya shiga Har wajen Daddy da Mommy yayi musu Sallama Har ya Tafi Diza bata sani ba Tana chan Tana Barci mai Cike da Tunanin Burinta ya kusa cika Lokaci yayi da Zata Bayyana ma Mastur Mtsayinsa aranta Saboda tafi Kowa sanin Halinsa in ta Zauna Tana Jiran sai ya gayamata Yana Sonta Haka Zasu yi ta zama Sai dai Tafi Kowa sanin mgana Yana masa matukar Wahala.

Shima abangaran Mastur Yaso matuka yaji wata yarinya ce Mansur din yake so bai taba gayamai ba duk yadda suka kasance abokan Sirrikan juna Wata Zuciyar tana ta wani sake sake Kada abunda take Hasasomai ya zama gaskiya in ya Lura da Statement din Mansur din sai dai baya bama Zuciyarsa Daman yadda da hakan Bai samu Lokacin da zasu zauna suyi mgana bane kuma Daya koma Porthercourt Hankalinsa ya koma kam aikinsa ko sunyi mgana da Mastur Sai dai kawai su gaisa basu samu Lokacin da zasu Tattauna ba Duk da Mansur din yana Su Tattauna mganar Domin yana so kafin Lokacin Zabensu Ayi bikinsu da Diza din Shi kuma Mastur din yace ya bari in ya samu Lokaci zai Kirasa su Tatttauna.

Diza kuwa har Titsiyeshi Tayi Tana Tambayansa wayake so..? Daman yana da wata wacce yake so ne ko Labarinta bai taba Bata ba,Kin gayamata yayi yana ganin kamar ta sani kawai jan ajin nan ne na mata ammh Shi anashi Tunanin yana Tunanin Da Zaton kamar yadda yake sonta Ba tun yau ba ita ma hakan take Sai dai ya saba Lamba Bai san Diza bashi take so ba Dan"uwansa yaya mafi Soyuwa garesa take son ya Zama Bangonta Har Abada,Kuma ma yaso ya Fahinci wani abu Lokacin Daya bata Labarin Busharan Inna karime Har da Nuna mata Vidoe Yaga Tsantsan Tashin Hankali da Damuwa Da Kishi acikin Idanuwan Diza yaso ya Fahinci wani abu ammh kuma sai bai Taba Saka Tunanin haka aransa ba sai yayi Tunanin kila Saboda Taji mganar Busharan Daga sama ne Sai da taji yace ya gayamata yadda suka kare da Inna karimen da Abunda Mastur yace ne yasa yaga Ta Sauke Numfashi Fuskarta ta Saki Daga Lokacin kuma Tatashi ta koma Gida Wuni Tayi Cikin Damuwa aranar ma Ta gwada kiran ya Mastur yafi sau goma Tana Fasawa Tana ji kamar ta Kira Mastur ta gayamai Sirrin Zuciyarta kafin wata ta Rigata Samun Zuciyar abun sonta sai dai kuma ta kaasa Tana Jin Nauyi Kuma uwa uba ba wani Sakewa ko Sabawa a tsakaninsu Tayi Tunanin ko Mansur Zata gayamawa ya gayamai Sai kuma ta Fasa Tana sakawa tana Warwarewa ammh Tabbas mganar Bushara ta girgizata Duk da Taji ance yar kauye ne ammh Kishinta ya Turniketa Diza Tana san Tana da Kishi ammh Kishinta kan Mastur Dabam ne bata kaunar ma wata taRabeshe abaya ma Datake Zaune bata Damu ba Sanin Datayi Shi Mastur Daman yake Aboki ma bashi Dashi ballatana Wata Budurwa kuma ta Tabbata inda akwai wata Tabbas Mansur zai Sanar da ita,ammh yanzu kam Lokaci yayi da Sirrin Boye zai Fito Fili itama Tana Bukatar kasancewa dashi a matsayin Matarsa.

*******

*Bayan Wata Daya..*

University of Lagos Da Misalin karfe 12:30pm na ranar Jumma"a
Alhamdullillah su Rumana sun kamallah Jarabawansu ta Karshe Aranar Sun Firfito Kowanne kagani Fuskarsa Cikin Fara"a da Farinciki mazan su da matansu suma sanye da Farar Lapcoat ne,Suna ta Daukan Hotuna Cikin Murna mara Misaltuwa Ruma gefe ta koma Ta Dauki wayarta ta kunnata Wanda Tunda suka Fara Jarabawan ta kasheta Karatu kadai ta saka agaba,ba kama Hannun yaro bata kira ba"a kiranta  Umma ta kira Tana Dagawa Cikin Farinciki tace"Umma Mun fito Last paper dinmu yanzu.."

Umma Dagachan Bangaran Tace"Masha..Allahu Ruma..Allah yasa abunda kika karanta albarka Allah yasa kiga sakamako mai kyau.."Cikin Farinciki Rumana ke amsawa Da"Ameen Umma..Nayi kewarku keda Abba..Ina Goggo Jummai da juma..? Umma tace"Kowa lafiya..Abbanki ya Fita yana kamfani Goggo Jummai na Daki ta kwanta Kafarta na matsa mata Juma kuma tana Kitchen..Muna kewarki Rumata yaushe Zaki Dawo..?

Ruma tace"Allah sarki..Ki gaishemin da goggo ta Umma..Zan Dawo sai Next week.Zan tsaya in yi Clearence,sai kuma akwai Dinner da muka Haada In kuma gama Sai na Dawo gida,in sakamako ya Fito da kuma in sunkiramu Indection..'Umma tace"Shikenan Allah yayi Jagora Ruma..Ki kira Abbanki Ya Damu kullum sai yayi Zencenki.."

Rumana Tace"Zankira shi yanzu Umma.."Da haka suka yanke kiran Abba ta Kira Cikin Farinciki ya Daga wayar,yayi murna da Farinciki Da Rumana tace sun gama jarabawa yayi mata addu"a sosai ya Tambayeta yaushe zata dawo tamai Bayanin da tayi ma Umma ya Fahimta suka Rabu bayan ya Tambayeta ko tana Bukatar Wani abu tace A"a bata Bukatar komai da haka sukayi sallama ko Cikin makaranta Bata bari ba zuwa Hostel Taga Sakon 100k Daga Abba ya Turo mata Murna da Farimciki ya Cikata Har Abada tasan ita yar Gatace.

Abba kuwa Farimcikinsa Daya Rumana ta gama karatu zata Dawo gabansa,Yana son Ruma Tayi aure yaga Jikokinsa Ita kadai ya Haifa aduniyar nan yana Bukatar ganin Tsatsaon Ruma kafin ya bar Gidan Duniya Ko da Farko bai so ta Fara Karatu bai aurar da ita ba Sunsha mgana da Alhaji Sunusi kan hakan Shiya ya Dinga Bashi Shawaran ya barta ta Cika Burinta,Nayi karatu Allah barshi In Allah ya kawo mata Mijin ko Tana cikin yin ne sai aurar da ita sai ta Cigaba da karatunta adakinta da wannan Shawaran ya Tsaya mata Har ta Cimma Burinta Sai dai abu Daya na Damunsa na ganin Rumana bai Taba gani ko Jin Labari wani Saurayinta ba Har Umma ya Tambaya tace Batajin Rumana Nada wani Saurayi ammh dai bata sani ba,Hakan yasa Hankalinsa ya tashi yana so Rumana Tayi aure yana son yaga ya'yanta.

Alhaji Sunusi ya kira yagamai Abun Farinciki Shima ya Tayashi Murna sosai ya kuma ce in Lokscin Indaction dinsu ya Tashi ya sanar dashi Shida Mommy Har da Diza zasu je mata Har Lagos Abba yaji Dadi Sosai yace insha Allahu,Daganan suka gangaro kamar mganar kasuwancinsu Da haka suka Rabu,Daddy yana Dawowa yake gayamawa Mommy Lokacin suna Falon Sama Har da Diza Mommy ta kalli Diza Tana Fadin"Diza Zaki ma yar"uwarki Lagos ko..?ki tayata Murna ta Zama likita.."

Diza na Faman latsa wayarta Tace"In bani da wani aiki Mommy..zani insha Allahu.."Daddy yace"In bata da Lokaci ki kyaleta Asiya..Ni Dake sai muje.."Mommy tace"A"a da ita zamu je..Haka zasu ta zama basu san juna ba..? Tun suna Yara ba Rabonsu da juna.."Daddy yace"Zasu san juna mana..Ai Rumanan ta Dawo Gida ko Daga baya Sai taje Tayi musu ko Kwana Biyu ne suga juna.."Mommy tace"ai shikenan.."Diza na jinsu bata tankasu ba,Bata jin ma Zata samu Zuwa bata kaunar Tafiya mai Nisa kuma in Tatafi wazata bar ma aikinta,Sai dai in kafin Lokacin ta samu wacce Zata rika Taimakonta Tana nan dai tana Dubawa bata son ta Dauki Shirmanmu ne,So take ta samu Kamar Hauwa wacce Take da kokari kan aikinta.

******

Ranar lahadi ta kama Weekend ne Tun Safe Mastur na Apartment dinsa bai Fita ya gaji Shiyasa yasha Barcinsa Sallar Azahar ma acikin Gida yayita sai da ya idar ya Daga waya ya Kira Sargent Inuwa yace yazo Gida yana Nemansa ba Dadewa sai gashi yazo kudi ya bashi yace yace yayimai Takeway din Tuwon Shinkafa miyar agushi da Nama ba Dadewa ya Dawo ya kawomai,ya Sallameshi cikin Gidan ya Dawo yaje kitchen ya Dauko Filet ya Juye ya Zauna yaci ya koshi ya Dora da Ruwa Dayake shan Lemukan Turawa basu Dameahi ba Nan Falon ya Zauna kan Daya Daga Cikin kujerun Falon yana Hutawa,Sai Tunanin Mansur ya Fadomai kan mganar Dayace zasu yi Tashi yayi ya koma Cikin Bedroom dinsa ya Dauko Wayarsa Wacce Sai personal mutane yake kira dashi kamar su Hajja Daddy da Sauransu Yana Dawowa yaje ya Dauko Karamin Kofi na Tangaran ya Zubo Coffea Daya Dafa da Safe yazo ya zauna yana kurba yana Laluban Wayar mansur din sai yaji wayar tana Ringing bai Daga ba sai ya Juya akalan kiran ga  Baba Habibu suka gaisa yana kasuwa sai ya Kashe ya Kira Hajja suka Dade suna mgana Har ta bama Aiya sukayi mgana Daganan ya Kira Umma da Abba dake Sokoto suka gaisa nan ne ma Abba ke gayamai Gama Karatun Rumana Gobe ma Zata Hau jirgi ta Dawo Gida ya Tayata Murna kwarai yace zai Kirata Daganan sai ya Kira Wayar Daddy bayan sun gaisa Daddy ya karamai mganar da sukayi Dayazo Kan mganar Aure ya kuma ce yakamata Tunda Mansur yace Yana da wacce yake so shima yasan Abunda yake Ciki Dahaka suka Rabu da Daddy Duk sai Mastur yaji ya Damu ba wai bai Tashi Aure bane baisan Ta Ina zai Fara ba yaso sai sun samu Daidata da Fahimtar juna Tsskaninsa da Diza kafin komai ya Biyo baya,Shi bai san ta ina zai Fara ba kwata kwata bai da wani sani kan Harkan Soyayyah ba Shiyasa ya kasa yin wani yinkuri,Abunda ke Damunsa ma Rashin Sakewar da bashi Dashi Tsskaninsa da ita.

Yana cikin wannan Tunanin Wayar Mansur ta Shigomai bayan ya Dauka sun gaisa Mastur yace ina ya shiga ya Kira bai Daga ba Mansur yace"Ina Daki Ya Mastur..Na kwanta ne nagaji banga kiranka ba.."Mastur yace"Ina Fatan kayi sallah ko..?

Mansur yace"Yanzu na tashi..Nayi yaya ya aikin..?Mastur yace'Aiki Lafiya lau..Ya Siyasar taku..? Mansur na Dariya yace"Siyarku dai Ya Mastur..Kai ma ai yayan Dan Siyasan ne.."Mastur Mirmishi kadai yayi bai yi mgana ba Mansur yace"Yaya Mastur kun kara mgana Da Daddy kan Mganar nan ne..?

Mastur ya lumshe idi yana kara kwantar da kansa Saman kujera yace"Eh yanzu ma da mukayi waya sai da yamin mganar.."Mansur ya mike Zaune yana Fadin"To yaya kai kana da wacce kake so ne..? Ni dai nasan baka Dashi..Baka iyama Hira da Namiji Dan"uwanka ballatana Mace..? Ya fada yana yar Dariya Mastur yayi Shuru kafin yace"Kai ma ka sani ashe..? Ni na rasa ta ina Zan Fara ne Ammh Tunda ka iya Zan zo ka Koyamin Honourable.."Dariya ta kama Mansur yace"Nima ban Fara Gwajin bafa Yaya Mastur.."Mastur ya gyada kai yana Fadin"Meyasa..?bakace aleady kana da wacce kake so ba.."?

Mansur ya mike Tsaye yana Shafa kansa yace"Ai ban taba gayamata Sirrin Zuciyata ba ya Mastur..Ina sonta Tun ban san kaina ba na Fara sonta Tun Ranar Farko Dana Fara ganinta a Lokacin kuruciyarta..Ban Fahimci hakam ba sai da na Fara mallakan Hankalin kaina na Fahimci itace komai nawa ya Mastur.."Mastur Dayaji kalaman Mansur kamar dashi yake yasa yaji Jikinsa yayi sanyi Zuciyarsa ta Fara Tsalle waje Daya kada yazo Suna Tarayyah Shi da Dan"uwansa wajen son Abu Daya Bai ma samu Zarafin mgana ba yaji Mansur na fadin"Duka Tsarin Rayuwata Burinta ne ya Mastur...Duk da ban gayamata ba na tabbata itama Tana Sona kamar yadda nake sonta.."Mastur Dayaji Kamar Wutar Lantarki yajashi ya Mike tsaye rike da Kofin Coffea din Dake hannunsa Cikin Bushewar baki yace"Waccece..ita Mansur.."?

Mansur yayi Mirmishi yace'"Nasan zakayi mamaki ya Mastur..Yar gida ce...DIZA ce...!! Dam! Dam! Dam! Mastur yaji gabansa ya Fadi kansa yayi wami Mugun Saramai,Hannunsa da Jikinsa na rawa Lokaci Daya Kofin Hannunsa ya Sulale ya Fadi ji kake Tus ya Fashe Tsakar Dakin Saman Cafet din Dake Falon,Wayar ma Dake Hannunsa sai ta Sabule ta Fadi Saman Cafet din Jikinsa Jallabiya ce ammh Haka yake gumi da Zufa Har yana Tsiyaya Har kuwa da A.C dake Falon da Fanka wacce ke Gudu Tana bada iska.

Dagachan Bangaran Mansur yaji karan Faduwan abu Tus..Rike wayar yayi yana Fadin"Hello Ya Mastur..Kana jina..? Hello..? Yaji Shuru Domi  Mastur yana jin Hello din Mansur ammh Jikinsa ya Daskare waje Daya ba zai iya Daga Hannunsa ba Ballatana har ya Duka ya Dauki Wayar kansa yana wani Saramai Lokaci Daya yana jin Amsa kuwan Mansur na Fadin Diza ce Zabinsa itace wacce yake so Tun tana Lokacin kuruciyarta Kenan Sun Fara son Diza Shi da Mansur alokaci Daya kenan..? Hasbunallahi wani"mal wakeel.."Yafada Lokaci Daya yana Dafe kansa Dayaji kamar zai Cire lokaci Daya yaji yayi yaraf ya Fadi na saman Cafet din Har hannunsa yana Dafa Glass din Daya fashe na Kofin,jini ya fara zuba ammh bai takai ba Halin da Zuciyarsa take ciki yafi Jinin Dayake Zuba Mansur kuwa gajiya yayi ya yanke wayar yana Tunanin Network ne sai dai kuma ya kara Kiran Wayar Mastur naji ammh ya kasa ma kallon Wayar Balle ya Dagata Har ta karaci Ringing dinta bai iya wani Motsin Kirki ba.

Kansa ya Dafe da Hannun Bibbiyu Jinin Daya bata Hannunsa Dashi yasa ya Dafe kansa Dashi Bai damu ba Cikin Wani irin Fuzgar Numfashi yake yi Domin Yanajin kamar Numfashinsa zai bar gangar Jikinsa Numfashi ya Fara saki Daya Bayan Daya Lokaci Daya yana Jawo Numfashin nashi kafin yaji ya dawo Daidai,Maida kansa ya jingina jikin kujera yana Jin kamar ya Rusa ihu,Ajiyar Numfashi kadai yake Saukewa yana jin Wayarsa nata Neman agaji yama kasa Tashi ganin kamar zai iya Shiga wani Hali yasa ya fara Kiran Sunan Allah,Cikin ikon Allah sai yaji shi ya Fara dawowa Cikin Hayyacinsa har ya iya Rarrafawa ya Mike Tsaye kan kafafunsa,Allah ya Taimakeshi bai Taka kwalban ba ya Tsallake komai Harda Wayarsa ya Fada Bedroom dinsa yana Rangaji kamar zai Fadi ya Fada kan Katifarsa Kamar wani matacce Yana so ne yaji ya yi kuka ko Radadin Dake zuciyarsa Zata Ragu gabadaya Jijiyoyin kansa sun mike Radau kamar mai wani Cuta Haka yake jin gabansa na wani Rugurugu kamar ajalinsa yazo Innalillahi wani'inna Illaihirraju"un wannan wani irin al'amarin ne Taya sukayi Tarayyah wajen son Abu Daya da Dan"uwansa..?meyasa ma bai Taba Tunanin Soyayyah Tsakanin Mansur din Diza ba..? Yake kallon haka kamar Shakuwa ce..?kuma itama Tana sonsa..Bazai Taba zama Sanadin Shiga Tsakanin Abunda Dan"uwansa yafi so  akan kowa ba ko da Soyayyar Diza zai Kasheshi ya Zama Dole ya Binne wannan Soyayyar har Abada ya Cireta aransa Ta zama wani mafarki na Dabam Ya zama Dole yayi SADAUKARWAR SO ga Dan"uwansa Mansur Dagashi sai Allah suka san yana kaunar DizaDaga Rana mai kama ta yau bazai Taba bari wani ko wata yasan wannan mganar ba Ballatana Mansur ko Dizan susan da wannan labarin ba,kansa yaTura cikin Filo yana so yayi kuka ko zai ji sanyi ammh kuma abun akasan Ransa yake sukansa abu kamar waasa sai ga ciwom kai da Zazzabi mai Zafi har ya RufeShi Har yamma yana cikin wannan HALIN Har akayi Sallar La"asar bai iya Tashi ba yanaji Zuciyarsa ta Saukar ma da Jikinsa wani Nauyi,har aka Kira Mangariba ya kasa Tashi Sargent Inuwa ne yaga anyi Sallar La"asar ba Yallabai anyi mangariba ma Shuru yadda kowa yayi Shedansa baya wasa da Sallah akwai mtsala Shi yazo Gidan Ya Duba Tundaga Falo ya Tsorata ganin Fashashen glass ga Jini Sai daiHalin Daya samu Mastur aciki yafi Firgitashi Cikin Firgici yaje ya Kira Sauran Sargent din suka Tarairayesa zuwa mota Sai wani private Hospital,suna kaisa Sanin matsayinsa yasa nan da nan aka karbesa aka fara bashi Taimakon gaggawa,basu samu sukuni ba sai da suka Tabbatar da an kaisa Daki na musamman Bayan an sakamai Drip an mai alluran barci.


Mastur Farkawa kawai yayi Washegari ya gansa a asibiti sai alokacin abunda ya Faru ya Dawomai wannan Nauyin kan nashi yana nan har yanzu,Ba zai iya Tuna Rabonsa da Ciwo mai Zafi irin haka ba tun wani Ciwon Typiod Daya Taba yi yana Hassan Gwarzo har sai aka Dawo Dashi gida a Tearm din bayan Lokaci bazai iya Tuna wani DogonCiwo Dayayi ba ma sai dai irin Ciwon kai haka da Ciwon Gabobi na gajiya,ya takura azaman asibiti sannan kuma shi ba Ragon Namiji bane Jarumi ne Tsayayye bazai Taba zama saboda mace ya zama haka ba Dole ya gagice yana cema Likita ya bashi Sallama ya samu Lafiya sai dai bai Saurareshi ba Domin ya gayamai Jininsa ne ya Hau Lokaci Daya bai yi mamaki ba Domin yanayin Daya shi ga Ya zata ma Mutuwa zai yi.

Ransa bai kara baci ba sai da Sargent inuwa yazo ya kawo mai wayarsa da Jallabiyansa da Boxers Dayaje gida ya Daukomai Shine yake gayamai yaga wayar nan yashe afalo Shine ya Dauko mai yana Hanya Mansur ya kira ya Daga yagamai Yana asibiti bashi da Lafiya Ran Mastur ya baci kamar ya kwada ma Sargent Inuwa Mari,Haka ya karbi Wayar bai iya amsa Wayoyinsu Baba da Daddy da suke ta Kiransa ba Yariga ya sani Mansur ya gaya musu Bashi da lafiya,kuma shi yanzu bai san me zai ce musu ba shiyasa ma ko Taba wayar bai yi ba Duk da yaga Tarin Kiransa da akayi tayi kuma baya Raba Daya Biyun Kiran Duk na Mansur ne.

Sai da ya kwana Biyu Likita ya sallameshi da mganguna da kuma Gargadi mai girma kan kada ya saka ma kansa Tunanin Daya fi karfinsa Saboda Kada ya Kamu da Hawan jini Shi kuwa aransa yacr na nawa kuma ai yama kamani Tunda na Rasa Diza da toh kawai ya amsa bayan ya karbi Duka mgangunan Sargant Inuwa ya Tukasa Zuwa gida a Daya Daga Cikin Motocin Heaquater nasu Kudin asibitin ma da komai su suka Dauki Nauyin komai.

Koda ya koma gida ya iske har an Tsabtace Falon kuma yasan ba kowa bane sai Sargent inuwa bai ce komai ba ya Shiga Ciki ya Bisa da kayansa da magungunansa kafim ya saramai ya Fice Bai iya wani Tunani ba Domin Tun Daga Lokacin da Mansur ya gayamai Diza yake so ya rasa Duka wani Tunaninsa wanka yayi Ya zo ya saka Saukakkun kaya Saboda Jikinsa ba karfi,Lokacin an kira Sallar azahar Sai kawai yayi Sallarsa sai ya Dauko Wayarsa yaga Tarin Misseds na su Baba,Hajja,Mansur Daddy,Mommy Harda Diza abun mamaki Da kamar zai kyalesu sai yayi wani Tunanin kada suji Shuru su Zata ba Lafiya su Dauko Hanya Mansur ya Taba zuwa Har Cikin Apartment dinsa kuma ya Tabbatar da zai iya cewa Su Taho wannan Tunanin Da yayi yasa ya Lalubi Lambar Baba Habibu ya Kirashi wanda ya Daga da Gaggawa yana Tambayansa Lafiyansa..!

Cikin Dauriya Mastur yace"na samu sauki Baba har na Dawo Gida..likita ne ya Hanani Daga waya Shiyasa kukajini shuru.."Baba Habibu Dake kasuwa yayi ajiyar Zuciya yana Fadin"Alhamdulillah..Ai mu hankulanmu ya tashi..tunda Mansur yazo yagayamana Sargent dinka ya gayamai baka da Lafiya kana asibiti Muke ta kiran wayarka Shuru baka Daga ba Hankulanmu sun Tashi har ma Zuwa gobe Babanka da Mansur din sukace zasu bi jirgi Suzo nan Porthercourt din su Dubaka Ko lafiya..!?

Mastur yace"Basai sun zo ba..Suyi Zamansu Baba na samu Lafiya.."Baba Habibu yace"Shikenan Allah kara Lafiya."Mastur yace"Ameen..Ka gayamusu Baba basai sun zo ba..Zan kwanta ne nasha mgani zuwa anjuma zan kirasu.."Baba Habibu yace"Shikenan..Allah kara lafiya.."Daga haka suka katse kiran Mansur Baba Habibu ya kira ya gayamai sunyi waya da Mastur ga Abunda yace sai Lokacin Hankalinsa ya kwanta ya gayama su Hajja kowa yaji Natsuwa jin yana Lafiya,Daddy kuma Mastur din ya Kirashi da kansa ya gayamai sun Dade suna mgana yana mai Fadan ya Rika kula da kansa.

******

Bayan kwana Biyu Mastur ya gyagije ya Fara Fita Office ba wai Domin Zuciyarsa ta warke ba ya mike ne Tsaye ga Kakafunsa Saboda kada Gyambon da Raunin Dake Cikin Zuciyarsa ya shafi gangan Jikinsa alhalin ya Riga yayi ma kansa alkawarin Sadaukar da Soyayyar  Diza zuwa ga Dan"uwansa Mansur.

Kowa ya kirashi a waya yamai ya jiki,Hatta da Abba da Umma Dake sokoto sun ji Labari kuma sun Kirashi Daddy ya gayamasu Rumana ma ta Kirashi Har sau Biyu Tayi mai Sannu da Jiki kuma Text dinta yana Shigowa Wayarsa Lokaci bayan Lokaci na kulawa Gareshi bai taba bi takai ba,Diza ma ta kirashi ammh bai Daga ba,Domin bashi da wannan kwarin gwiwan kwana yake baya Barci Sallah kawai yake yana Rokon Allah ya bashi Juriya ya kuma yaye mishi Soyayyar Diza acikin Ransa ya bashi Ikon kauda kai da Sadaukarwa Gashi nan ne dai kamar yana Tsaye ammh Cikin Lokaci kadan Ramarsa Ta Bayyana wanda yake Daga Cikin Zuciyarsa ne Lalle Soyayyar Bala"i ce Tana Azabatar da masu yinta bai Taba Zaton Soyayyar Diza Zata iya maidashi haka ba sai gashi Cikin kwanaki Kadan Rayuwarsa ta Fara Sauya kwana yake da Mugun Ciwon kai,kuma yana shan mgangunan da likita ya Bashi Sai dai baya kiyayewa da yawan Tunani Mansur bai kara Tadamai mganar ba ganin Halin Dayake Ciki Shima bai yarda sun kara Tattauna mganar ba kada wannan karon Mansur ya Fahinci wani abu Wanda baya Fatan Hakan Ta Faru..!



_Albishirunku Masoyana wannan karan na bude muku wani Shashi na musamman Saboda ku..Ina masu Bukatan Atalla musu Hajarsu Ko wani iri ne Domin samun costumer ta ko"ina..? Ku garzayo kakarku ta kusa yanke saka Zan Tallata muku Hajarku a Duka Shafukana Domin inganta Sana"arku da kuma Samun Cinikaya mai Tsabta da kuma kara Hada hada wajen Masi siye da Siyarwa mai Bukatar A tallata mata Hajjarta Zata iya min mgana kai Tsaye ta wannan Lambar Tawa 09069067488 domin karin Bayani...Sai kunzo Kunsan dai mai kasuwa Shi ke da Riba.._

*Domin zama Daya Daga cikin wadanda zasu karanta Labarin SADAUKARWAR SO..! Zaku Biya kudin karatunku kamar haka Masu amfani da Banki Zasu Tura â‚?300 ta wannan asusun banki 0552179550 Jamila umar gtb,Masu Katin waya kuma zasu Turo â‚?400, ta wannan lambar wayar 09069067488 Adauki Hoton katin sai aturo kai Tsaye mutanenmu na Niger kuma zasu Tuntubi wannan lambar kamar haka +22794775574 domin karin bayani,Insha Allahu mutum zai tsinci kansa a paid group ina maraba da ku masoyana Nagode*





*Shakira...*
1/1/22, 18:53 - Maryam Badmsi: *SADAUKARWAR SO..!!*
_(Labarin Yan"uwantaka,Soyayyah Tare da Sadaukarwa)_

*Wattpad:@Jamilaumar315*
*Mallakar:Jamilaumar(Janafty)*


*Page1�⃣5�⃣*

"Rumana taje tayi Jarabawan gwaji a asibitin Uduth na Intenship dinta kuma Alhamdulillah ta samu nasara,zasu fara dis coming Monday Taje Lagos ta karbo Result dinta daya riga yayi Ready Lokaci daya kuma nan da   sati uku Makarantar zatayi Bikin Yayesu wato Indection dinsu suna ta Shirye Shiryensu.

Cikin Nasara Rumana ta Fara Intenship dinta asibitin Uduth,ba kwana take yi ba Ranar Datake da aiki Tana zuwa ta Dawo ne Tunda an kawo Motarta Kirar 4matic,Bata da mtsalan komai Gefe Daya kuma ita da iyayanta suna ta Shirya Shiryan Indaction dinsu Umma ta saka an yimata Littafi da jaka mai Dauke da Hotonta na Rabo Sai Kofuna kanana na Shan Shayi Na Tangaran da Farantin Voul na Cin nama ko Saka Miya,Daddy kuma yayi mata Key holder mai Dauke da Hotonta,sannan kuma Umma ta Kira Mommy ta mata mganar su Cake da Donout da Sauran kayan Fulawan da za"a raba achan in sun isa Mommy tace ai Ta kwana Gidan Sauki Ta Dauki Nauyin komai Diza bangaranta kenan Komai zai Tafi Daidai da wannan mganar Mommy Tayi ma Diza mgana kan Tana son Tayi mata Kowannen Spicess 300 each,Tana son Spring rol sai Samosa Duka ayisa ana Gobe Tafiyarsu Saboda sai sun je Chan Sokoto Zasu Tafi Tare da Su Umma Diza Batayi kasa agwiwa ba Ta Kira Merry ta gayamata kuma ta bata a Rubuce Kuma taje da Kanta Taga yadda aikin ke tafiya,Dayake bangaran makeup dinta ta samu wata ma"ikaciya mai kwazo mai suna Madina itama Qualified ce kan Harkan kwalliyan da gyaran Jiki yanzu Har gyaran Kafa Diza sunayi a wajen sai aikin yazo mata Cikin Sauki Saboda Abun na Mommy ne da kanta Take Zagewa anayin Komai da kanta Saboda Tana so komai ya tafi daidai.

Mansur yasan da Labarin Zuwa Lagos yasan Rumana sai dai ba wani kyakyawan sani bane,Mastur kuma Abba da kanshi ya kirashi ya gayamai Kuma zai ji Dadi in zai samu zuwa Sai dai Mastur din bai da Ra"ayin zuwa ahalin Dayake ciki na Bama kansa kwarin Gwiwa kuma sunyi mgana da Daddy yace Dukkamsu Zasu Tafi Harda Diza Mommy kuma Tace Zata Roki Baba Habibu Ya bar Hajja da Aiya su Tafi Tare dasu,Jin haka yasa bai saka ma ransa ma zai je ba bayaso yaje Kowa ya Fahimci Halin Dayake Ciki..Domin ya Rame sosai sai Dan Wuya Duk yayi Zuru Zuru ga Rashin Barci ga Ciwon kai Bayason ya koma asibiti ace za"a kara kwantar Dashi yana so ya zama Very Strong ne baya son Saboda Mace ya kwanta Warwars Har wata Cuta ta kamashi kuma baya son koda wasa a Fahimci ya Taba son Diza acikin Ransa Shiyasa ya bama Abba Excuse da cewa aiki ya Rike shi bazai samu zuwa ba.
Abba ya Fahimceshi yace bakomai jin haka yasa Mastur ya kira Baba Habibu sukayi mgana kan ya bar Hajja da Aiya su Tafi Tare Baba Habibu yace ayi haka..? Shikenan Daman Mansur Shima yace Diza tace in bai je ba ita bazata jeba Zai Shirya su Tafi Tare Sai su Tafi Gabadaya shi dai bazai samu zuwa ba Saboda kasuwa Duk da akwai yara ammh ya kamata dai ya Tsaya Mastur na jin haka sai da Zuciyarsa ta Buga ya Riga ya Tabbatar ma kansa Shine yayi kutse Cikin Rayuwar masoyan Biyu suna Kaunar juna ya Zama Dole ya Binne abunda ke Ransa kada ya Fito Filo hakan ya Haifar da wata Mtsala wacce bayan Fatan Hakan.

Rumana da kanta ta Turamai gayyatan,yana ganin Kima da girman yarinyar yasa ya kirata ya bata Hakuri yace Hajja da Mansur Zasu Wakilceshi kamar yana wajen kana yana Tayata Murna Allah yasa taci Moriyan Abu Taji Dadi Sosai suka Rabu Cikin Girmama da juna da jin Nauyin juna,Bangaran Rumana kuwa ba Haka taso ba taso ne Lokacin da zata karbi Rantsuwarta Mastur din na wajen Domin da Taimakonsa da Jajircewansa Yasa ta kawo yanzu a matsayin likita Ta kuma Kalli idanuwansa ta gani Shin yana mata kallon Datake mai..? Yana tsananin Begenta kamar yadda take Begensa..? Ammh ba komai duk da haka batayi La"asar ba ba kuma ta Hakura ba Zata Cigaba da Bayyana alamu Har ya Fahimci inda ta Dosa..
Umma da Abba sun ji Dadin karan da Baba Habibu yayi musu sun Tsara Tafiyan Ranar asabar ne Taron Daga Zaria suka Tafi Sokoto Ranar jumma"a Baba Habibu kadai suka Bari agida gidansu Diza kuma megadi da Mama Fadime Wannan karon ma Diza na Motar Mansur  ita da Aiya Dayake Shatar Motocin Haya sukayi guda Biyu Dayan Motar kuma Daddy kuma Hajja da Mommy ne sai Direba Dake jansu Da suka isa sun samu Tarba Sosai da karramawa,Umma da Abba suka Rasa ina zasu saka Bakinsu Goggo jummai da juma Suna ta kai da kawo Daga Kitchen zuwa Falo Suma Hardasu Za"a je Lagos Rumana tace don Allah azomata dasu Dayake ita Tun Jiya ta wuce Saboda Shirye Shirye.

Hajja da Aiya basu yi wani bakunta ba,Domin Daga Umma har Abba ba bakonsu aciki,Hajja ma sun Taba zuwa da Mommy Lokacin da Umma Tayi Rashin Lafiya sukazo suka kwana Daya suka gaisheta,suka koma Dayake sun je har gidan iyayan Mommy din Tafiyar ma Harda kannenta Guda Biyu maza da kanwarta Mace za"ayi ta Domin suma zasu yi ma Abba da Umma kara Hakan matukar yayi musu Dadi Mansur Da Diza kuma suna Gefe suna yan Hiransu Ba wanda ya damu dasu,Sanin Halinsu in Daya na Wajen Daman yana Tare da Daya Tun kafin ma Mansur din ya Furta Akwai wacce ya Dade yana so Kowayana kallon Soyayya ce mai karfi Tsskanin Diza da Mansur din Tun suna yara Shiyasa ba wanda ya Damu dasu Jiran Lokaci kawai akeyi ayi komai agama.

Mansur da Daddy Daki Daya aka Saukesu,Mommy da Hajja Kuma Dakin Umma Aiya kuma Dakin Goggo Jummai Diza kuma Dakin Rumana aka Sauketa Tasha mamakin ganin Tarin Littafan karatu Dakin Rumana Tajinjina mata gaskiya ita bazata iya wannan Wahalar ba Sam,Tun adaran Juma ta gama Hada Duka abubuwan da zasu Tafi Dashi Jirgin karfe 7am na Safe Zasu bi zuwa Lagos Domin Taron karfe 9am za"a Farashi Rumana sai kira Take Tana magiyan su Taho da Wuri Mastur kuwa Mansur ya Kirashi ya gayamai gasu a Sokkoto Gobe Zasu wuce Lagos yayi musu Fatan Isa Lafiya da Dawowa Lafiya basu Tsawaita Hiran ba Domin Tun bayan Bayyanar al"amarin Mastur ya Daina yadda yana wata Doguwar Hira Da Mansur din bayason ya Tado mai da Mikin Dake Zuciyarsa alhalin yana son ya zama Very Srong akan lamarin

Washegari Tun kafin 7 suka isa Filin Jirgi Tare zasu yi Tafiyan Har da yan gidan su Mommy,Lokaci na cika bayan an Tantacesu suka Lula sai Lagos wajen 10 suka isa Wani Abokin Kasuwancinsu Abba Alhaji yusuf Dake nan lagos din ya zo da Dan"sa Mas"ud da Matarsa da suka zo da Motoci suka Daukesu Dirrct sai Cikin makaranta Sun iske ma an Fara Taron Hall din ya Cika makil ba Tsaka Tsinke Dakyar suka samu Wajen shiga Daliban suna Chan gaban Wajen Prof  dinsu Dukkansu Sanye da Gown din makarantan na gamawa Dama Tun Dazu Rumana ke waige waigen Neman Danginta sai ga Kiran Abba yace ta Juyo gasu nan abaya Lokacin ta Data mike Ta Dago musu Hannu Umma ta mike ta Daga mata sai da taji Tahowar kwallah Tayi matukar murna da ganinsu Duka Don ita suka zo Daman tasan da zuwan su Diza Uncles dinta ne bata san da Zuwansu ba sai da ta gansu kawai Diza kuwa Daga nesa ne Shiyasa basu yi wata mgana ba.

Bayan Bayanai Daga malamai,Masu Ruwa da Tsaki magabata da Masu Makarantar sai aka Fara kiran Daliban Daya Bayan Daya Rukuni Rukuni Domin karban licence da Rantsuwa Wanda prof da kanshi Zai basu,Rumana Tana Daga Farko Farko Lokacin da aka Damkamata Licence dinta Sai ga Hawayen Farinciki Haka ta Dagashi Sama su Umma suna gani Diza da Mansur kuma sai Video suke,Umma Hawayen Farinciki take suka Rumgume da Mommy Suna Murna,bayan angama basu Rantsuwa sai aka koma Kiran Dalibai da suka Fita da Firstcallas,sai ga sunan Rumana Muhammad Wamako a mtsayin wacce ta Fita da Firstcallupper,Murna Farinciki kamar ta suma Bata Taba Zata ba ammh Sauran abikom karatunta sun san ta Chanchanta Domin akwai ta Da kokari Hazaka guruwa ce ta karshe Rumana Har kan Step ta Taka aka karramata kuma aka Bata Waje Tayi jawabin Godiya ga Iyayanta kana aka Gayyaci Alhaji Muhammed Mahaifin Rumana shima ya isa kan step dim yayi jawabin Godiya Cikin Alhafari.

Farinciki ya cika Zuciyar Umma da Abba yau din Rana ta Musamman ce Rumana Tana kuka Tana Rike da kambon karramarta da licent dinta,Murnan Burinta na Farko ya Cika Saura na Biyu cikin Shaukin Farinciki ta Fito da Wayarta Ta Tura ma Mastur Text.

_Salam Alhaamdulillah..Yau na Cika Burina na Farko..Na zama Likita..Saura Dayan Burin nawa Wanda ba wanda ya sanshi Sai Allah..I LOVE U Ya Mastur..And i Mean it.._Daga haka ta Turamai Tana jinkamar ta sauke wani Nauyi Daya Dade acikin Zuciyarta.

Shikuwa Mastur yana Cikin Office dinsa yana aiki yaji Shigowar Sakon Rumana Zuciyarsa sai da ta Buga Daya ga Sakobta Daman yasan Za"a Rina Ya dade yana Tunanin hakan sai dai bai taba Zaton shi nan kusa ba,kansa ya Dafe kawai yana jin wani irin Faduwar gaba,Tun bayan Daya Fahimci Mansur na Son Diza ya gama Tsara Rayuwarsa na cewa bashi ba wani jin Dadi ballatana wani abu na Farinciki ba aikinsa kadai zai sakama gaba bai kawo ma zai iya auran wata mace ba Domin zai Cutar da ita ne ya zauna da ita baya sonta Hakan kamar karuwa ce Zai zauna haka koda bazai Dorar da wani Farinciki ko Jin Dadi game da Rayuwarsa ba Ammh Zai ji sukuni da jin Dadi in har Mansur ya auri Diza ya kasance Cikin Farinciki.

Yana ganin Sakon yayi sauri ya goge bai maida mata da amsa ba Sai ma Tsausayi da ta bashi ta Fada son wanda bai Dace da ita ba Bai taba mata kallon so ba Kallon kanwa yake mata Tunda yake mace Daya ya mallakama Zuciyarsa kuma Ita Din ya Riga yayi alkawarin Sadaukar da ita ga kaninsa Bashi da wani Gurbi da zai iya sakata,Shiyasa ya nuna kamar bai ga Sakonta ba ya koma ya Jingina da kujera yana Fama da Sukan Zuciya ayadda yake kwana baya Barci ga Nauyin kai da Saranwan kai ya Tabbata da yana zuwa asibiti aka auna sa Za"a ga Ya kamu da Hawan Jini Gashi mgungunansa sun kare kuma bai koma baya son yaje a Bayyanamai Wata gazawar Tashi ne Shiyasa kokarinsa Da sai ya Nuna bakomai bai sani ba Hatta Ma"aikatan Dake karkashinsa Sun Fahimci Yallabai baya Cikin kwanciyar Hankali Jarumin Namiji mai cikar Zati da Haiba Duk ya Susuce ya koma wani iri Dashi Rashin son Hayaniya da rashin son mganarsa sai ya karu Yawan kadaicin Dayake samar ma kansa yana kara Hadasamai Abubuwa Dadama bai sani ba.

Achan Lagos kuwa Taro ya Tashi Lafiya su Rumana bayan sun gama Hotuna da Mate dinsu da malamansu ta Nufo inda iyayanta suke ita da Wata kawarta yar Kaduna Basma Lawal ita iyayanta na London Mamarta ta raka Babanta adubashi yana Fama da Mtsalan koda Sai yayanta ne da kanwar Mamanta suka zo mata ita kadai ce kawarta Basma Duk Fadin Jami"an saboda bata da Sakin Jiki da mutane.

Ta gabatar da Basma gasu Umma Suka gaisa cikin Fara"a suna Tayasu Murna nan ta kira yayan nata da Anty ta suka gaisa da su Umma Duk da Abaki suka san Labarin Rumanan sai yau suka ganta,Rumana bakinta Har kunni suka Sarke Hannu da Diza Suna gaisawa yau da sun Hadu bayan sun kwashe Shekaru Rabonsu da ganin juna Sai dai ta Waya ganin Hotunan juna,Diza ta sakar mata kayattacen Mirmishi Tana Fadin"Congratulation Sister..Allah yasa albarka.."

Rumana Cikin Muryanta mai Cike da Natsuwa Ta amsa mata Tana Fadin"Ameen ya Allah..Nagode.."Diza ta kada kai Tana Fadin"Sunana Khadija Sunusi Tureta(Diza).."Rumana tayi Karamar Dariya Tana Fadin"Haba Diza ke din ce bangane ba..?umma kinji Diza Tana Zaton ban ganeta ba..?Umma tace"Ai ku kuka sani. in baku gane juna ba..Kunyi Sakaci da Zumunci Alhalin kuna yara Baku da aiki sai akaini Wajen Diza akaini Wajen Ruma.."Gabadaya aka saka Dariya koda ganin yadda Umma Tayi mganar Rumana Har kasa ta Duka ta gaida Daddy da Alhaji Yusuf suna ta saka mata albarka cikin Sha"awa Daddy yana ji aransa yau Dama Diza Tayi karatu ita da ta sakashi alfahari,Haka ta duka ta gaida Mommy da Hajja da Aiya Sai Matar Alhaji Yusuf Hajiya Laure,Suka Rumgume da Goggo Jummai Juma kuma an samu nayi sai Faman saki baki akeyi ana kallo,Suma Uncles dinta haka ta bisu Daya bayan Daya ta gaishesu suka amsa cikin Alfahari da ita Umma ita ta kalli Rumana Tana nuna Hajja Tace"Kin ko gane Hajja Mahaifiyar Mastur.?

Rumana ta Sunne kai Tana Fadin"Umma naga kamar su ai.."Mommy Tayi Dariya Tace"Kai Dota har kin ga kamarsu..Ai Mastur ma yafi kama Sosai da Baba Habibu.."Rumana tace"Shi nasanshi ai suna Zuwa Da Daddy.."Umma tarike Baki Tace"Kaji ja"ira sau daya ne fa..Lokacin da sukazo Daurin Auran kanina Salisu Asiya Lokacin ita kuma Ta Dawo Hutu.."Mommy tace"Anyi haka Tare kuwa suka zo..Yar nawa akwai kwalkwalwa gashi mun ga Ranarsa yau..'Hajja dai na Gefe Batace komai ba sai Mirmishi Take Aiya ce ta gyara Tsayuwa Tana Fadin"Wai ni baza"a nemi wajen Zama bane..Mufa ba iyalan Megidana bane Yan Sanda da suke kwana atsaye basu gaji ba..Wlh nagaji.."Tafada Tana yamutsa Fuska Umma Tayi Dariya Tana Fadin"Yi hakuri Aiya..Mu karisa Wajem Inuwar Chan a Shinfida Manyan Darduma sai mu Zauna mu Huta muci abinci..Ruma Taho muje kayan ki na Mota.."Rumana tace Toh Har zata Bisu sai ta waiga Tana kallon Diza wacce ke jan gefe Tare da Mansur da Mas"ud suna Hira Basma kuma Daman Tatafi ita da Anty da yayanta inda sukayi parking dim Motarsu itama Jama"a sai Binta suke Juniors dinsu Domin ita ta Kirasu Zata basu kayan Rabon duk su Raba kamar zata Bi bayan su Umma sai ta Fasa Domin ta gane Fuskar Mansur Ta Taba ganinsa yazo Gidansu Wajen Mastur Lokacin Ta Fara Uduth kafin ta samu Addmission ta koma Lagos da karatunta.

Sallama Tayi musu Lokaci Daya Tana gyara Zaman gown din Rigarta Gabadayansu suka waigo Suna kallonta Diza ce tace"Yauwa Taho muyi Hoto.."Jin haka yasa ta karisa kusa da ita Diza ta kalli Mansur Tana Fadin"Dauke mu da wayarka.."Tun kafin ma ta gama mgana ya Fara Daukansu Mas"ud na Gefe Shima yana ta Daukansu Rumana kawai yake kallo yana mata Mirmishi Domin kallon Farko Da yayi mata ta Shiga Ransa a kasar Waje yayi karatunsa yanzu Haka Shine Manaja a kamfanin Sarrafa Biscuit Warrper,Yana ganin Rumana kawai yaji ya samu Matar Aure ta gama Tafiya da Duka Tsarinshi na Macen Dayake son Aura.

Sai da suka gama Hotunan kana Diza Ta kalli Mansur Tana Fadin"My Honourable ga Fa Rumana..My Childhood Friend kuma Diyar abokin Daddy Abba da Umma.."Mansur ya saki Mirmishi yana Fadin"Naganta Jinta yafi ganin Hotonta Firstladyta..Ina kallon yanayinta ta Sauyamin kenan ta zama wata so Classic koda yake Likita ce fa da kanta sai mun zo allura Allah ya Sa albarka.."

Yafada Cikin barkwanci Mirmishi kadai Tayi kafin tace"Ameen Nagode.."Kai ya kada yana Fadin"Sunana Mansur Sulaiman Doguwa...Shakikin kani ga Dcp Mastur Habib Doguwa nasan kin Ganeshi shi.."Wani kayattacen Mirmishi ta saki kafin tace"Haba dai kaima ai na ganeka Ko ba kai bane Honourable..?Baki ya Rike yana Dariya yana kallon Diza ita kuma sai ta Dauke kai tana Dariya Mus"ab ya kallah Shi kuma ya Daga hannu yana Fadin"A"a bani na gayamata ba..Ni yau ma nasan da Honourable nake Son abota.."Sai Dariya ta kamasu Dukkansu banda Rumana Data Murmusa Mansur ya kalli Diza yana Fadin"Kalli Rumana..Don Mirmishinta da yanayinta bai miki da Kama dana Yaya Mastur ba..? har ajinsu iri Dayane Basa son mgana da yawan Dariya sai basarwa.."Rumana ta kafeshi da ido Lokaci Daya kamar yadda Diza ta kafeshi da Ido nan da nan Annurin Fuskarta ya Dauke Shi kuwa ko ajikinsa Ya juya yana Gayama Mas"ud yana bashi Labarin yanayin yayan Nashi Rumana kuwa Juyawa kawai tayi tace suzo su Tafi chan wajen iyayan nasu Diza kuma wani Wutan kishi ne ke cin Ranta Don me Mansur zai Hada Abun kaunarta da wata Duk Sai taji Dan Sakin Jiki Datake da Rumana ma ya Dauke,ahaka dai suka karisa wajen su Umma inda suka Saka manyam Dardumai suna Zaune zaune Rumana kuma su Mansur suka Firtotomata da Manyan Ledojin da Kayan Rabonta ke Ciki ta Dauka ta bama wasu Mata Sauran kuma ta tafi Wajen Basma suna Rabaawa itama Yayanta sun zo mata da nata.

Sai La"asar suka bar Cikin makarantan zuwa Gidan Alhaji Yusuf Domin suyi Salloli suci abinci su Huta acikin makaranta sukabar Rumana Zata Tsaya tayi Parking din Duka kayanta Sai gobe Zata Taho da ita zasu Wuce,Haka kuwa akayi Washegari da Safe Tayi bankwana da Jami"ar lagos Basma ma da Safen suka Tafi Mus"ab Abba ya wakilta yaje ya Taho da ita Shi da Mansur Duk da Mus"ab din sai saka baki yake bata bashi wani Fuska ba suna Mota sanda suka Daukota Tafi maida Hankali Wajen Hiran Mansur wanda Haka kurum yake sakata Nishadi ko Domin yana Dan'uwan abun kaunarta ne Bata sani ba Diza kuwa da Mansur yace Tazo suje tace Tana wani abu Alhalin kuwa Tun mganar jiya ce Take jin Haushin kowa Mussmman ma Rumana bata kaunar ganinta.

Jirgin karfe 4pm suka Shiga Zuwa Sokoto suka yada Zango a Gidan Abba Dake Sokoto,Sun so su wuce aranar Abba ya Hana sai da suka kara kwana Anan Sokoton,mommy dai Gidansu Taje ta kwana Diza kuma ta bita Hajja da Aiya ne da Mansur da Daddy suka kwana anan Gidansu Rumana,Washegari kuma Sai da suka Fara Biyawa ta Gidansu Mommy aka gaiggaisa kana Suka wuce Filin Jirgi Daganan suka Shiga Jirgin Kaduna,Rumana Da ita akaje Rakiya sai dai ta Fahimci Diza ta Dauke mata ba kamar Haduwarsu a Lagos ba sai bata kawo komai ba ta Danganta Hakan da kila gajiyace,Sun Rabu Cikin aminci Umma da Abba nata Godiya Mansur ya karbi Lambar Rumana yace Dayaji Ciwin kai zai kirata ya Dauketa Personal Doc dinsa sai Dariya ake a kaduna suka sauka Motor Haya kamar yadda sukayi a zuwansu suka Hau Zuwa Zaria Wajen mangariba suna Gida Hankalin Abba da Umma ya kwanta da suka yi waya sukace sun sauka Lafiya kowa Gidansa ya Nufa Domin sauke gajiya sai dai Baba Habibu ya Dawo ya iske sun Dawo Daman bai da Mtsalan komai Megadi gidan Daddy Mama Fadime ke bama abun karinsa na safe da Abinci Dare in ya Dawo Daman Mommy Ta bar mata Sallahu
Sai da Safe Baba Habibu ya Shiga yayi ma su Daddy barka da Dawowa Daman Ya kira Abba awaya ya Tayashi Murna Tun Ranar.

Kafin Barowar Daddy Sokoto sunyi mgana Sosai da Abba kan Rumana ya gayamai yana son Tayi aure,Damuwarsa Daya bata da wani Tsayayye,Daddy ya nusar dashi da kuma Shawaran kada ya matsa mata sai Ta Fito da Miji ya Cigaba mata da addu"'a Allah zai Fito mata da miji nagari kada ya Damu anan ne yake Tambanyanshi Diza fa Daddy yake gayamai ita ai suna Hashashen sun Daidaita da Mansur nan ya gayamai duk yadda ake ciki Abba yace Tabbas ko bai Furta ba akwai Soyayyar a Tsakaninsu,Daddy yace Dukkanmu Haka muke Tunanin Iyayansu Mata ma sun Dade suna Zargin haka sai dai kasan yaran Zamani gwara abari su Furta sai ayi komai Cikin Farinciki,Sun Rabu kan cewa Duk yadda ake ciki zai Kirashi ya gayamai Domin shima ya gayamai Baya son Diza ta Fita wannan Shekaran bai aurar da ita ba.

Sati daya da Dawowarsu Daga Lagos Bikin kanwar Mansur yazo Tafiya ta kama Dole Mommy Bata je ba ammh Da Diza aka Tafi da Hajja da   Balaraba da Aiya wacce Tace sai taje Ranar Daurin Aure kuma Mansur da Daddy da Baba Habibu da Kawu Usman suka taho aka Daura aure Dasu Aranar suka Juyo Daman Mansur yana da Taro Washegari bai kwana ba Dayake ya zo garin kafin Bikin har ya bada Duka Kudin Kayan Dakin Sakinan A Maruka suka kwana Daya Suka koma Ririwai suka kwana Daya,Duk da Diza tasha zuwa Saboda Tana Rako Mansur in zai Taho Diza Taga Busharan da aka so a likama Abun sonta Duk da Taga yanayinta Sai da taji Kishinta itafa bata kaunar Wata Mace ta Rabi abunda take kauna Sam,Sai washegari Daddy ya Turo da Direba ya Taho ya Daukesu suka koma Zaria Mastur kuwa Daman yace  bazai samu ba,bai gaya musu bane bashi Da Lafiya Ciwon ya kara kwantar Dashi wannan karon dai bata kaishi asibiti ba sai agida Likita yazo ya Dubashi gwajin Farko ya Tabbatar mai ya kamu da Haawanjini shi bai ma yi mamaki ba Domin yasan ko Ciwon Zuciya akace yana Dashi bazai musa ba akwanakin yana ji kamar bazai iya Wannan Sadaukarwan ba yana ji kamar zai gaza sai dai kuma karfin Halinsa da Juriyansa sun gaza Ya nuna Rauninsa.

Dalilin haka yasa ya Fara Rubuta Labarinsa da Soyayyarsa da Diza Tun Ranar Daya Fara sonta acikin wani karamin Diary dinsa Dayake Rubuta Muhimman abubuwansa,In yana Rubutawa yana jin Sauki acikin Ransa,Shiyasa yake Rubutawa ammh yana mai Boye mai kyau Domin baya Fatan wannan mganar ta Fito har wani Daga Cikin Ahali yasan da ita.





_Albishirunku Masoyana wannan karan na bude muku wani Shashi na musamman Saboda ku..Ina masu Bukatan Atalla musu Hajarsu Ko wani iri ne Domin samun costumer ta ko"ina..? Ku garzayo kakarku ta kusa yanke saka Zan Tallata muku Hajarku a Duka Shafukana Domin inganta Sana"arku da kuma Samun Cinikaya mai Tsabta da kuma kara Hada hada wajen Masi siye da Siyarwa mai Bukatar A tallata mata Hajjarta Zata iya min mgana kai Tsaye ta wannan Lambar Tawa 09069067488 domin karin Bayani...Sai kunzo Kunsan dai mai kasuwa Shi ke da Riba.._

*Domin zama Daya Daga cikin wadanda zasu karanta Labarin SADAUKARWAR SO..! Zaku Biya kudin karatunku kamar haka Masu amfani da Banki Zasu Tura â‚?300 ta wannan asusun banki 0552179550 Jamila umar gtb,Masu Katin waya kuma zasu Turo â‚?400, ta wannan lambar wayar 09069067488 Adauki Hoton katin sai aturo kai Tsaye mutanenmu na Niger kuma zasu Tuntubi wannan lambar kamar haka +22794775574 domin karin bayani,Insha Allahu mutum zai tsinci kansa a paid group ina maraba da ku masoyana Nagode*




*Janafty....*
1/1/22, 18:53 - Maryam Badmsi: *SADAUKARWAR SO..!!*
_(Labarin Yan"uwantaka,Soyayyah Tare da Sadaukarwa)_

*Wattpad:@Jamilaumar315*
*Mallakar:Jamilaumar(Janafty)*

*Page1�⃣6�⃣*

"Shuru Daddy yana ta jiran kiran Mastur kan mganar da sukayi zuwan da yayi   mganar auransu Shi da Mansur ammh shiru bai jisa ba yayi mai uzuri saboda baida Lafiya kwanakin baya ammh ai yanzu ya samu sauki.

Mommy ne ta Shigo Falon Tana Dauke da kofin Coffea har ta isa gabansa bai sani ba,Sai da taja Center Table din gabansa ta Dora Kofin Tangaran din Tana Fadin"Alhaji lafiya kuwa..?
Ajiyar rai ya saki yana Fadin"Bani Coffea din.."Daukowa Tayi ta mikamai ya karba ya fara sha Gefensa ta Zauna Tana kallonsa Dago kansa yayi yana Fadin"Ina khadija..?

Mommy tace"Tana Dakinta.."Kai ya gyada yana Fadin"Mastur Shuru bai nemeni ba..Kuma bai zo ba.."Mommy tace"Topha..wani abu ne ya Faru..? Daddy ya ijiye kofin Gabansa saman Center Table din yana Fadin"Kan mganar auransu ne Asiya..Tun Zuwan da yayi mukayi mgana Dashi kan su Fito da Matan Aure Duk da Mansur yace akwai wacce yake so Tuntuni shifa..? Munyi mgana da Mallam Habibu shi kanshi ya kosa yaga kowannensu ya mallaki iyalinsa na kansa"Mommy tace"Hakane kam..Ai iyali Shine mutum..Toh Shi Mansur waya ce yana so..?

Daddy ya Dauke kai yana Fadin"Bai Fada ba..bansani ba..Yadai ce zai Fadama yayansa.."Mommy Na yar Dariya tace"Ai ni nagaya Tuntuni...Mansur Har gida Za"ayi da Diza.."Daddy ya Kada kai yana Fadin"Tunanin ku kenan..! In kuma ba ita ya Zaba bafa.."Mommy tace"Ai itama zai Zaba..In sun Boye Kaunar Dake Tsakaninsu mu ai basu isa su Boye mana ba.."

Daddy bai kara mgana ba illah Wayarsa Dake gefensa Daya Dauko yana Laluban Layin Mastur Sai da tagama Ringing bai Daga ba sai bai kara kira ba ya ijiye wayar ya Cigaba da Shan Coffea dinsa yana Sauraran Hiran da Mommy kemai kan Hujjansu na Soyayyace mai Tsanani Tsskanin Diza da Mansur bai ce mata komai ba Shima anashi Tunanin Hashashensa kenan Har Baba Habibu sai da ya Fadi haka Allah yasa dai Tunaninsu ya zama Daidai da Tunanin Mansur.

Kamar Minti Goma Tsskani da Kiran Mastur sai gashi ya Biyo Bayan kiran Daddy ya ijiye abunda ke Hannunsa ya Daga Kiran da Sallama Daga chan bangaran Mastur Daya Fito Daga Wanka Ruwa na Diga ajikinsa bai Tsane ba ya Zura Jallabiya mai Ruwan Toka,Sallar Isha"i yake son yayi Data kubcemai sai Shafa'i da wuturi yake da Niyyar yi sai yaga kamar wayarsa na Haske Dayake ya sakata a Silent ne,yana Dubawa sai gaya kiran Daddy,bai Daga ba sai ya Tada Sallar sai da yayi sallar Isha"i yana Zaune kan Darduma yabi bayan Kiran Daddy gabansa na Faduwa.

Bayan sun gaisa da Tambayan Mutanen gida,Daddy ya Tambayeshi jikinsa da kuma aiki yace komai lafiya Daddy ya gyara Zama yana Fadin"Mastur ya najika Shuru ne..? Mastur yaji Faduwar gaba Cikin Sanyin Rai yace"Shurun mene Daddy..? Daddy yace"Kan mganar da mukayi kwanaki mana mganar Auran ku kaida Mansur..Kun kai mun zali kuma zaman hakan bai dace ba.."

Mastur yaji wani irin yam acikin jikinsa cikin wani irin Yanayi da kuma Dauriya Da Sadaukarwa   yace"Daddy ai Mansur ya gayamin Diza yake so.."Daddy ya kalli Mommy yana Mirmishi yace"Alhamdulillah..Dama Hashashenmu kenan Allah yasa albarka..Kai kuma fa..? Kana da wacce kake so ne..?

Mastur Dayaji wani irin Shock acikin Jikinsa kenan kowa yasan suna son juna Shine bai sani ba..! Allah ya gode maka da Yasani Tun kafin ya Furta yana sonta Da bai iya yafe ma kansa ba in har ya Fara Takara da Abunda kaninsa ke so,Cikin Karfin Hali ya Bude baki yace"Babu Daddy..Ni bansaka aure nan kusa ba..Amin hakuri zuwa gaba.."ya karishe Fada yana Jingina kansa da Bango Jinsa kamar zai Fadi yana Daga Zaune,zuciyarsa Tana wani Zafi kamar Zata kama da wuta.

Daddy yace"ba mganar ayi maka hakuri Mastur..Mansur fa kaninkane..Kai ya kamata ka farayi kafin shi..Tunda abun ya zama haka ya zama Dole kaima ka Fito da matar aure a Hadaku Dukkanku mu aurar daku Rana Daya.."Mastur yama kasa mgana sai maida Numfashi kawai yake Har sai da Daddy yace"Mastur Lafiyanka kuwa..?

Cikin Dafe kansa yace"Bakomai..Daddy adai kara min Hakuri ban da Wacce nake so..Ban kuma san a ina zan samu ba.."Daddy yayi Dariya yana Fadin"Baka dai Nema ba...In da ka nema zaka samu mana..Yanzu dai ka Kokarta ka Shigo wannan Satin sai muyi mgana Gabadaya.."Mastur Daman yana Cikin wani Hali Da Sauri yace"A"a Daddy basai nazo ba.."Daddy ya katseshi da Fadin"Sai fa kazo...mganar kuma wacce kake so kafin kazo ka Duba ina son inji Labari mai Dadi in kuma babu Ni ina da wacce Zan Baka ka aura wacce nan gaba Zaka Dawo ka Godemin.."

Mastur yaji kamar ya kurma Ihu saboda mganar Daddy ammh kuma bazai iya mai gaddama ba,Kansa kawai ya Sunkuyar kamar yana gabansa yana jin yadda yake saramai Shi dai Toh kawai yace bai ma san Sadda Daddy ya Datse kiran ba Kamar ya kwanta anan kasa yayi ta kuka da Birgima haka yake ji Saboda ya samu Saukin Nauyin Dake Cikin Zuciyarsa ammh kuma yakasa kukan Zucci da Yawan Tunanin Dayake yi suna karamai Rashin Lafiya da Rashin Natsuwar Zuciya wanda baya Fatan haka ya Shafi Lafiyansa da karfin Gwiwansa.

Daddy na gama Waya da Mastur ya kalli Mommy yana Fadin"Hashashemu ya zama gaskiya..Mansur dai yar gida Za"ayi da yarki Khadija.."Da sauri Mommy ta Washe baki Tana Sakin guda Daddy yana Dariya yace"Shi Mastur yace bai da wacce yake so kuma baisan ina zai samu ba.."Mommy tace"Kaji wani Zence..? Kamar sa ne zai ce ina zai samu mai Sonsa..!?

Daddy ya mike yana Fadin"Ki barni dashi..In yazo ban ji wata mgana ni Zan Samo mai wacce ta Dace dashi.."Mommy Ta Bisa da kallo Tana Fadin"Wacece ta Dace dashi Alhaji..? Yana Shiga Cikin Bedroom dinsa yace"Nima bansani ba Tukunnah.."Daga haka ya Shige ya barta Tana Tunanin wacece bata bama mganar Muhimmanci ba Ta koma Murnan Abunda Daddy ya gayamata Bata Bakinciki Domin Mansur ya auri yarta Daman Ta Dade Tana Hangen Dacewarsu da juna ba Tun yau ba,Kamar tatashi taje Ta gayama Diza sai kuma ta kwabu kanta tace yaran Zamani yanzu haka kar suke kallonmu Farinciki yaki barin Ranta Taso ta Kira Hajiya Farida Ta gayamata abub Arziki sai kuma Taga Dare yayi ta bari sai gobe Tashi Tayi ta Tattara kololin abincin da Daddy ya gama ci ta Kai Kitchen dim kasa da Mama Fadime suka Hado suka ma Juna Sai da Safe Dakin Diza ta Leka Ta iske tayi barci Wayarta Ta Fadi gefe Dariya Tayi ta Shiga Dakin ta gyara mata kwanciya ta Dauke mata waya ta Dora saman Side Drower din gadon ta KasheMata Wutan Dakin ta Fito Bayan taja mata Kofa Sama ta Haura zuwa Falonta sai da ta Rage Hasken Falon kana ta Tura Kofar Bedroom ta Shiga ta maida kofa ta Rufo.

****

Bangaran Rumana kuwa Ta shiga Tashin hankali na Damuwa na Rashin ganin Amsan Sakon Mastur Zuwa gareta,bayan ta Riga ta gayamai Sirrin Zuciyarta Wanda kuma Batayi nadama ba,abun yaki barin Ranta Ta shiga Damuwa Rashin Sanin makomar Soyayyarta.

Gashi Bayan Dawowarsu Daga Lagos Mas"ud nata kiranta Bata san ina ya samu Lambarta ba,ya riga ya gayamata Sirrin Zuciyarta kuma Ya gayamata He is Ready,aure yake so in har ta bashi Dama zai gayama Mahaifunsa Ita ta Dakatar Dashi Ta gayamai akwai wanda Take so ammh bai Hakura ba kiran Safe Dabam na Dare dabam yana Beging dinta Ta soshi Text kuwa baya gajiya na kalaman kauna Gareta,Ammh bata Taba maida kai ba Bashi bane agabanta Wanda Take son wannan Kulan Daga gareshi bata son makomarta ba,abun ya Dameta yau haka Tatashi Sukusuku aikin Dare tayi Wato Call,Sai wajen 7am na Safe ta baro Cikin asibitin a Motar ta Zuwa Gida Ta gaji Ga barci acikin Idanuwanta ga Damuwa sai taji kamar ta Kirashi sai kuma ta kasa batasan me Zata ce mai ba ko Sirrin Zuciyarta Dakyar ta iya Fadamai shima Sakon Text masages.

Haka ta shiga gida Tana layi saboda gajiya da Barci,Da juma ta Fara cin karo Ta gaisheta da kwana bata iya amsa mata ba ta mika mata Karamar jakar hannunta da Lapcaot dinta Ta Haura Sama Juma ta Biyo bayanta Zuwa Dakinta Tana Shiga gado kawai ta Fada tana jin kamar kanta na Sara mata nan Saman gadon juma ta ijiye mata kayan ta Fita zuwa Kasa Kitchen ta shiga Domin Hadama karamar Hajiya Abun karyawa.

Rumana ta Dade kwance kafin Tatashi Tana Rangaji ta Fada Tiolet Tayi wanka Tazo ta Shafa Lotion dinta ta Sauya kaya zuwa Saukakkiyar Doguwar riga,Koda taFito Har Juma ta Hayo mata da Breakafst dinta Tea kadai tasha Ta Fito Daga Dakin Zuwa Falon Ummanta ta same su ita da Abba suna karyawa nan ta zauna kusa da Abbanta Tana gaishesu da kwana suka amsa mata Cikin Fara"a da soyayyah.

Umma ce ta kalleta Tana Fadin"Lafiyanki kuwa Ruma..? Naganki kamar baki da lafiya..? Rumana ta Sauke Idanuwanta Cikin gajiya Tace"Bakomai Umma..Gajiya ce Kawai sai Dan Ciwon kai dana Dawo Dashi.."Da Sauri Abba ya Dafa Kanta yana Fadin"Ayyah Sannu..Tashi kije Ummanki Ta baki Mgani kisha zuwa anjuma in bai sauka ba kije kiga Likita.."Umma ta mike Tana Fadin"Bari na Dauko mata panadol,tasha..Gajiyan Aiki ne Da Zirga Zirga.."Tafada Tana Shiga Cikin Bedroom dinta Sai gata Ta fito bata Dade ba,Ta mika ma Rumana panadol din Ta karba Lokaci Daya Umma ke Fadin"Kin karya..? Rumana ta gyada kai Tana mikewa Tace"Bakomai fa Umma..Call din ne ke Wahalardani baka samun yi   barcin kirki.."Abba yace"Watarana sai Labari Rumana..Allah ya bada Lada.."Umma na Zama Lokaci Daya Tana Dariya Tace"Ameen dai..Ammh fa Gwannati na Biyansu Alhaji.."Shima Dariyan yayi yana Fadin"Duk da haka Aikin su na Taimakon al"umma ne.."Rumana na jinsu bata ce komai ba ta Fice suka Rakata da Ido Cike da Tsausayinta da Kaunar Diyar nasu Tilo Dasu ka Mallaka.
Rumana na zuwa Daki Ta Sha panadol ta kwanta Sai barci Bata Tashi ba sai wajen 10am na Safe wanka ta sake yi Taji tana jin yunwa ta fita zuwa Kitchen Ta Hada Complex ta Dawo Daki Bataji Motsin Goggo Jummai baTafi Tunanin Tana Dakinta ta kwanta Sama ta Haura Tana Tunanin sai Zuwa anjuma Zata Shiga ta Dubata.

Kan gadonta Ta Haye da Mug din Da Cokali Tana shan Complex din a Hankali,Lokaci Daya ta Jawo wayarta Tana Latsawa Kiran Basma Tagani Lokacin kila Tana barci ne,Kiranta Tayi suka gaisa Ita Basma a Zaria Abu Take Intenship dinta Labari sukayi kadan kafin suyi sallama Kurama wayar ido Tayi Tana wani Tunani bata son ta Kirashi Bata da abun Fada sai kawai ta yanke Shawaran Turamai Sako da Sauri Ta ijiye mug din hannunta saman Side Drower din Gadonta ta Fara Rubutamai Sako.

_Salam ya Mastur How are u Doing..? Kaga sako na baka ce komai ba..? Ko baka sona ne..? Kuma ban yi maka a mtsayin irin Macen Dakake Muradin ta Zama Abokiyar Sirrinka ba nan gaba..Plz ka Fadamin mtsayina awajenka..Nidai kaji Sirrin Zuciya Am in love wit U..Bazan iya Rayuwa mai cike da Sukuni Da Jin Dadi ba in baka..Plz Help ur Sister Rumana Muhammad Wamako.._.

Tana gama Rubutamai ta Turamai Cikin karfin gwiwa ta koma ta Kwanta kawai jin komai ya Daina mata Dadi wayar na Hannunta Tana Bukatar amsar ko Cewarsa So take ta Dakatar da Mus'ab kafin ya Sanar da Mahaifinshi mgana ta Dawo kunnin Abbanta Tana da Tabbanci bazai mata auran Dole ba ammh kuma bazata iya mai gaddama akan komai ya Umarceta ba.."

Suna Tsaka da Meeting yaji Shigowar Sakon Rumana bai Duba sai da suka Tashi Daga Taron ya kuma Office dinsa ya Zauna kana ya Duba Sakon nata kalamanta sun kara kashemai Jiki kamar wani mara Lafiya,Gabadaya yau yazo dai Office ne ammh bayajin zai iya yin wani aiki kasala Duk ya Rufeshi da Nauyin Zuciya Shi yama manta da Sakon ta Domin Halin Dayake Ciki yafi Tunanin Rumana sai da yaga Sakonta ya Tuna da ita da Abunda ke Tafe da ita.

Kansa ya Dafe yana Tunanin Rumana Zata Kara Sakashi Cikin Wani Halin Daya ke Fatan fitansa nan kusa sai dai kalamanta sun kashemai jiki Sosai Yasan Zafin so da Dafinsa Tunda yana cikinsa Har yanzu bai kai ga Fita ba in yace Yana Sonta Domin ya Farantamata ya Cutarda ita..Zuciyarsa bata da wani Wajen da Zata sakata Har Abada Bazai ce Rumana ba ta Cika macen da kowani Namiji zai iya mallakanta ba No Rumana mace ce Kin kowa kim wanda ya Rasata sai dai ba ita Zuciyarsa taso ba Bai taba kallonta da wani Siga ta Soyayyah ba Kada ya barta Jira   ya kasa maida mata da amsa sai da yaga wunin Ranar Kiranshi ta Dingayi Sai da ya koma Gida Bayan yayi wanka yayi sallah kana ya Dauko Wayarsa ya Rubuta mata sako.

*Wslm..Rumana ya aiki..?Ko Daya Taya zan ce bana sonki.? Alhalin kin mallakin Duk Abunda wani Lafiyayyan Namiji yake nema wajen mace..! Kawai dai bana so ki shiga Damuwa ne Saboda ni ko ki zauna kina Bata Lokacin ki akaina..Ni ba yanzu Zanyi aure ba Rumana..Kiyi Facing din Reality dinki Ina Miki Fatan alheri Arayuwarki..Mastur Habib Doguwa..*

Yana gama Tura mata ya Kashe wayarsa ya koma ya kwanta yana Jin kamar bai kyauta mata ammh kuma Hakan shine Daidai.Inhar ya amsa mata yayi mata karya kuma yaci Amanarta yagayamata yana sonta ahalin bai taba sonta ba auranta ayanzu Tamkar wani Nauyi ne Za"a Doramai akansa Wanda kuma Faruwar hakan kamar wani babban al'amari ne na ganin irin Halin Dayake Ciki na Kokarin Binne Diza Daga Cikin Ransa.

Rumana kuwa Lokacin Data ga Sakon Mastur Kamar ta Suma Saboda bakinciki Ta Takaichi Tayi kuka awannan Daram har ta bama uku Lada Kenan ya Mastur baya sonta..? duk irin Tarin kaunar Da take mai..? Sai wata Zuciyar tace mata a"a ba haka yace ba yace ne kada ya barki kina Jira Ba yanzu zai yi aure ba Tuna haka yasa taji Sanyi aranta Tayi alkawarin Zata iya Jiransa ko nan da Shekara Goma ne in dai zai aureta Bazata Damu ba Koda gari ya waye Ta Shiga Dakin Umma gaishe su ita Abba sai da sukayi mganar Kumburin idonta sai tayi karyan Da Safan ne Wani abu ya Fada mata Abba yace in ta isa Wajen aiki ta bada a Dubata Inda wata matsalan tace to,allah ya taimaketa aikin Safe gareta 2pm zata Dawo Gida sai abun yazo mata da sauki ammh ko achan asibitin Sai da abokan aikin nata suka Fahimci ba Lafiya ba saninta mai kazar kazar da Zafin nama ammh yau ta zama wata so Silent da ita.

******

Duk yadda Mastur yaso Zillema Zuwa Zaria hakan bai samu ba Domin Bayan Kiran Daddy Baba Habibu ma ya kirashi yakaramai mgana bashi da Wata Mafita na Shiryawa ya Tafi Zaria Ranar Friday yabi Jirgi Zuwa kaduna Daga chan ya Kira wani Sargent Dake aiki nan Headquater yan sanda ta Jahar kaduna ya Daukeshi amotar Aikinsu Zuwa Zaria,wajen 9pm na Dare ya iso bai gayama kowa ba sai da suka gansa kwatsam Adaran Sargent din ya koma Kaduna.
Mansur da Hajja Haka suka Tasa Mastur gaba suna Tambayansa Wani irin Ciwo yayi ya Rame haka..? Yayu baki kamae wanda yaShekara yana wata Cuta Aiya ma ta kasa mgana Baba Habibu ma bai ce komai ba ammh Shi kanshi yasan Dan nashi ya Rame duk ya Lalace sai kashin Wuya da kwarmin Idanuwa ammh Dai bai yi mgama ba Mastur kuma Sai yace yanayin aiki ne ammh Lafiyarsa kalau ko da Gigi bai Fada musu ya kamu da Hawan Jini Saboda baya son a Mtsamai sai an ji Dalilin kamuwarsa da Ciwon yana Matashinsa mai kananan Shekaru.

Sai da asuba suka Hadu da Daddy a masallaci Shi kansa sai da yayi mganar Ramar Mastur yace Gaskiya zai bincika in za"a iya mai Trasfer ya bar kudu ya Dawo arewa ammh Mastur yace A"a domin abaya ne yake son Zama kusa da gida banda yanzu da komai ya Riga ya Lalace Daddy yayi mgana da Baba Habibu kan zuwa anjuma zasu Hadu dukkansu nan Falon gidansa su Tattaauna da Haka suka Rabu Shi kanshi Mansur bai ji Dadin Ganin yayan nashi haka ba Duk da ya san sa Miskili ne ammh wannan karon Miskilancin nashi ya karu Sosai Sai ya Shige Daki baya Fitowa Ko Falon Hajja Daya kan Zauna wannan karon ko Sau Daya bai Zauna ba suna gaisawa yake Mikewa ya koma Shashensu Mansur kuma Baya samun Zama Saboda Zabe ya kusa suna ta Shirye Shirye in ya Dawo kuma da Daddare Domin su zanta Daya Fara mgana sai Mastur din ya Fara Hamman karya kamar yana jin barcin in yaga haka sai ya kyaleshi yana mai Uzuri saninsa agogo ne Sarkin aiki Shi kuwa Mastur gujema mganar Diza yake bayason Ya bar wata alama da Za"a Fahimci wani abu.

Aranar Diza bata nan Tana kaduna sun je wani Training ne na Koyon Wasu Snack din kayan Fulawa Wajen Kwana uku anayi kullum sai taje kaduna ta Dawo Ranar ne na Karshe sai Gabda mangariba ta iso Gida ita bata ma san Mastur yazo ba Mansur ne ke gayamata kuma suna Dan Jumawa basu Hadu ba Zabe ya kusa kansa yayi Zafi baya zama agida,Watarana ma Baya kwana agida yakan kwana agidansa Dake GRA wanda ya mallakeshi Lokacin Daya Zama kansila Sai da sukayi mgana ta waya sama sama Shima din Ba Lokaci basu yi mgana ba kwana Biyunan sai Bayan tayi wanka Tayi Sallar mangariba ta Fito Falo ta Haura Saman Wajen Mommy Tayi mata Sannu da gida anan ne Mommy ke Fadamata akwai Zama Yau da Daddare inji Daddynta.."

Diza ta kada kai Cikin mamaki Tana Fadin"Mommy wani irin Zama kuma..?kuma dawa dawa..? Mommy tace"Kanmganar ku ne keda Mansur..Sai Mastur..Zama Kuma da Duka Iyayanki mana.."Diza Taji mamakin abunda Mommy Tace Cikin Dubanta Saka saka tace"Mganata ni da Mansur kuma Mommy..? Wata mgana..?
Mommy Data ga Kamar Diza na Raina mata wayau ta Harareta Lokaci Daya ta Mike Tana Fadin"Bansani ba..Kinga In kin Sauka kasa ki Fada Fadime ta Shirya komai da wuri Alhaji ya kusa Karisowa.."Tafada Lokaci Daya tana Shiga Cikin Bedroom Dinta.

Galala Diza ta Bita da kallon Bata gane inda ta Dosa ganin ba wanda zai gayamata yasa ta Zakuda Kafada ta Fice Zuwa Falon kasa,Tana Latsa wayarta,Kitchen ta Shiga suka Gaisa da Mama Fadime ta gayamata sakon Mommy kana ta Fice Zuwa Dakinta Duk yadda Taso ta manta da mganar ta kasa Lokaci Bayam Lokaci abun na Fado mata sai da Merry ta Kiratanr suka Fara lissafinsu Kana Ta saki mganar suna gama wayar kuma ana Kiran Sallar Sai ta tashi Daman Tana da alwalanta ta tada Sallar Tana Idarwa Ta zauna nan kan Darduma Tana Addu"a Lokaci Daya kuma Tana Tunanin wani irin Zamane Mommy Take nufin Za"ayi a kansu..?Rashin samun amsa yasa ta Jawo wayarta Ta Kira Mansur ammh bai Daga ba sai ta kyaleshi gefen gadon ta Zauna ta Rafka Tagumi haka kurum Take ji Jikinta Duk ba Dadi da Faduwar gaba.

Tana nan Zaune Tayi Nisa a Tunaninta Taji mganar Daddynta ya Dawo chan kuma Taji Muryan Hajja suna gaisawa da Mommy Taji kuma mganar Aiya Data Mansur bata dai Taji ta Mastur din ba Bata Dauka ma ya Dawo ba,Zuruf ta Mike Jikinta na Rawa Daidai Lokacin da Wayarta Ta shiga kara Tana Dubawa Taga Mansur ne Gabanta sai ya Fadi ta kasa Daga Kiran Har ta katse Haka kurum Tunda Taji mganar Mommy Gabanta ke Fadi Ta na nan Tsaye Taji Shigowar Mommy Dakin Tana Fadin"Diza ki Fito Falo..Ana mgana.."

Zuru Diza Tayi mata da idi Ita kuma Mommy bata gane ba ta Dauka irin kunyar nan ne na Mata Mirmishi kawai Tayi Ta Fice Tana Fadin"Ja"irai Daga ke Har Mansur din.."Diza bata jita ba ita daj jikinta ne yayi sanyi Da Hijabin Sallar Dake Jikinta TaTaka ahankali ta Fita Zuwa Falon Tana jan kafa sai dai Tasha mamakin ganin Mastur Zaune Gefen Mansur,Sai Baba Habibu kan kujera kusa da Daddy sai Mommy agefe Chan Nesa Ita da Hajja Wacce ta saka Hijabi Sabanin Mommy Data saka Mayafi Aiya kuwa na Kujeran mai kallon su Daddy.
Kafafunta Taji sun fara rawa Tunda ta Fito Falon Mansur ya kafeta da ido yana Mirmishi Mastur kuwa da gabansa ke Faduwa bai iya Dago kansa ba Hailala kawai acikin Ransa Allah ya Rufamai asiri kada yayi acting din da za"a gane He is Love with Diza Shiyasa bai ji ma Sha"awar kallomta.

Aiya ce ta kirata tace tazo ta Zauna kusa da ita shi ya bata kwarin gwiwan karisawa ta Zauna Wajen kafafunta Lokaci Daya Tana gaida Baba Habibu da Hajja Mansur Dake kallonta ta Kallah sai taga yau yana mata wani irin kallo Mastur kuma bazata ce komai akansa Ba Domin kansa yana kasa ne ko Motsi ya kasa.

Daddy ne ya Bude Taron da addu"a kafin ya Kora da Jawabin Abunda ya Tarasu ya Karishe da Fadin"Kai Mastur kai ne Babba Ta kan ka Zan Fara Yaya muke ciki..? Ka samo Yarinyar da zaka aura..?
Dam gabansa ya Fadi Lokaci Daya Dana Diza Data Dago Tana kallonsa Lokaci Daya Tana Zare ido,Mastur kuwa kansa na kasa yakasa Dagowa Dakyar ya iya Muskutawa ganin Kowa Shi yake jira yace"A"a Daddy..Ban samu ba.."Daddy yace"Kaji Aikin ko Habibu..? Baba Habibu yace"Mastur ai Halinsa kenan komai Sai yace bai Duba ba..Bansan yaushe zai saki Jiki da Mutane haka ba.."

Yafada yana kallonsa Mastur kuwa kai ya kara Saddawa gabansa na Faduwa,Kai Daddy ya Jinjina yana Fadin"Bakomai Tunda kai baka Duba ba..Ni zana Duba maka na samo maka wacce ta Dace Dakai.."Mastur dai bai ce komai ba Aiya ce Tace"Da hakan ma akayi..Domin Dagani ai megidana baya kula kowa.."Diza kuwa ji Tayi kamar Ta Suma Saboda Zafin kishi Dana Zuciya Mastur din nata ne ake mganar an zabamai mata bata Dawo Cikin Hayyacinta ba Taji Daddy na cewa"Duk da Mansur ya Turo Yayansa Mastur ya gayamin Zabinsa.Ban yi Musu ba sai dai gashi gamu ya Sake maimaita abunda yace ma Dan"uwan nashi.."Sai kallo ya koma kan Mansur ita Diza ma Lokacin Ta Daina Fahimtar komai So take ta Mike tayi mgana ammuh kuma Jijiyon jikinta sun saki.
Mansur ya Zunguri Mastur Dake zaune kamar mutum Mutum Tunda ya sadda kai Kala bai ce ba Kansa na kasa yana Fama da Zuciyarsa wajen Raunin Datake so ta bayyana.

Cikin Rada Mansur ya Sunkuyo yana Fadin"Ya Mastur ka Fada musu.."Mastur ya kalleshi da Lumsassun Idanuwansa masu cike da Damuwa yace"Ka gaya musu da kanka..!.
Daddy ne yayi gyaran murya yana Fadin"Mansur kayi mgana mana..?duk da Sunsan mganar suna Bukatar kara jinta Daga bakinsa.
Kansa ya maida kasa Bayyan ya kalli Diza ita kuwa So take taji wayake so Wacce bata Taba saninta ba Alhalin basa Boye ma juna komai kamar a mafarki taji yace"Baba Daddy..Ni ba wacce na Dade ina son acikin Raina sai DIZA ita nake son Aura ta zama Matata.!
.
Diza Dataji mganar kamar saukan aradu akanta Ta Zabura Ta mike Dafe da kirji bayan Tayi Cilli da wayarta Mommy kuwa da Hajja da Su Daddy Sai Washe baki suke Mastur dake duke bai Dago ba yana kokarin Sarrafa kansa yaji muryan Diza da karfi Tana Fadin.

"A"a..Kada muyi haka Dakai Mansur..Wata Dizan ni..? A"a ni ba Soyayyah muke ba..A Dan"uwa Amini na Daukeka Mansur kar ka Hanani mallakan mafarkina..Tun Bayan Dana Mallaki Hankalin kaina Na Fahimci ba wanda nake so Sai YAYA MASTUR...!


_Topha yaya wannan Badakalan zata kare..? Ga dai Diza ta Fassala Sirrin zuciyarta Bayan kuma Mansur shima ya Fallasa nashi..? Shin kuna ganin Mastur zai yi amfani da wannan Damar ya Saba alkawarin Da yayi ma kansa na Binne soyayyar Diza a ransa ki zai bayyana..? Wace ce wacce Daddy yake so ya zaba ma Mastur..? Waye zai yi Sadaukarwar so kuma waye zai ci Riban Hakan..? duk wannan Tarin Tambayoyin suna Cigaban wannan Labarin Kamar yadda na Fada muku Daga wannan Shafin ne karshen Free page mai Bukatar jin ya zata kaya Zai iya Bin wannan Tsarin Domin mallakan nashi.._

_Albishirunku Masoyana wannan karan na bude muku wani Shashi na musamman Saboda ku..Ina masu Bukatan Atalla musu Hajarsu Ko wani iri ne Domin samun costumer ta ko"ina..? Ku garzayo kakarku ta kusa yanke saka Zan Tallata muku Hajarku a Duka Shafukana Domin inganta Sana"arku da kuma Samun Cinikaya mai Tsabta da kuma kara Hada hada wajen Masi siye da Siyarwa mai Bukatar A tallata mata Hajjarta Zata iya min mgana kai Tsaye ta wannan Lambar Tawa 09069067488 domin karin Bayani...Sai kunzo Kunsan dai mai kasuwa Shi ke da Riba.._

*Domin zama Daya Daga cikin wadanda zasu karanta Labarin SADAUKARWAR SO..! Zaku Biya kudin karatunku kamar haka Masu amfani da Banki Zasu Tura â‚?300 ta wannan asusun banki 0552179550 Jamila umar gtb,Masu Katin waya kuma zasu Turo â‚?400, ta wannan lambar wayar 09069067488 Adauki Hoton katin sai aturo kai Tsaye mutanenmu na Niger kuma zasu Tuntubi wannan lambar kamar haka +22794775574 domin karin bayani,Insha Allahu mutum zai tsinci kansa a paid group ina maraba da ku masoyana Nagode*


*Janafty...*
1/1/22, 18:54 - Maryam Badmsi: *SS....0017*




"Gabadaya sai kallo ya koma kan Diza Hatta da Mastur da kansa ke Duke Kalaman Diza na karshe yasa yayi saurin Dagowa Cikin wani mamaki da Razana Lokaci Daya da Faduwar gaba mai Tsanani.

Haka bangaran Mansur ya mike Tsaye da karfi kamar Wuta yajashi yana kallon Diza kowani Daki Daya na kalamanta na mai amsa kuwwa acikin kunnuwanasa,Diza kuwa Kuka take wurjajan Lokaci Daya Tana Girgiza kai Tana Fadin"Kada muyi haka Dakai Mansur..Ba Soyayyah muke ba..Ban taba sonka ba kada kayi amfani da Shakuwar Dake tsakaninmu ka Shiga Tsakanina da abunda nake so ...Ni Ya Mastur nake so Shi ne Burin Zuciyata Tun bansan kaina ba.."
Ta karishe Fada Tana Zube Duka gwiwoyinta akasa Cikin Wani irin gunjin kuka na Fitan Hayyaci

Kowa Sakin baki yayi yana kallon Diza Mommy da Hajja suka Kalli Juna cikin Wani mamaki,Daddy ma sai jikinsa yayi Sanyi Baba Habibu kuwa yama kasa wani motsi,Aiya Ba bakin mgana sai kallon Diza kawai take Mastur kuwa Nauyi yaji Duka gabobinsa sun saki,kamar an mai Dukan Tsiya Bakinsa gabadaya ya Bushe Lokacin da kunnuwansa ke karban bakon al"amarin da bai Zata ba Daga Bakin Diza ba.

Mansur kuwa Yana so yayi mgana ammh kuma kalaman bakinsa sunki Fitowa Wani jiri jiri yake gani Dakyar ya iya Takawa Zuwa gaban Diza Cikin Tashin Hankali Shima ya Duka mata Cikin Rawan Murya ya Fara Fadin"A"ah..Diza.Don Allah kada kimin haka kina sona mana..Nima ina sonki..Kin manta Soyayyarmu Tunmuna yara..Wlh Da Soyayyarki na Tashi Rasaki Cikin Rayuwata Tamkar Rasa Rayuwta ne kada kimim haka Don Allah Diza.."Yafada Lokaci Daya wasu Zafafan Hawye suna kwarayomai Daman Mansur akwai Rauni da Saurin kuka.

Diza Datake Cikin Hijabinta ta Dago kanta Tana kallon Mansur Tace"Ni ba soyayya ce Tsakanina Dakai ba..Shakuwa ce irinta yan"uwanta Tsskanina Dakai Mansur..Bakai nake so ba Ya Mastur nake so .Don Allah kada ka Shiga Tsakanina da Farincikina.."Ta karishe Fada Tana Hada Hannayenta alamun Roko Garesa Ji yayi kamar zai Suma cikin Rawan Hannu ya kama Hannuwanta ya Dunkule yana Fadin"Ni ina sonki..Kece Rayuwata..Kalli fa Shi ya Mastur ba sonki fa yake yi ba..? Ya Mastur Don Allah ka gayamata baka sonta Nine nake sonta kamar Rayuwata.."
Yafada bayan ya Juya yana kallon Mastur yana kuka Zuwa Lokacin Jikin kowa ya gama yin Sanyi Aiya ce ta Sauke Numfashi Tana Fadin"Innalillahi..ya ana Zaton Wuta amakera sai gata mun gata a wani wajen Dabam..Kowa ya zata Soyayyace Tsakanin Mansur da Hadiza Yanzu kuma tana mganar Megidana wannan wani irin Lamari ne..?

Ta karishe Fada Cikin Sanyi Jiki,Daddy kam ya kasa mgana Baba Habibu ne yayi gyaran Murya yana kallon Mansur yace"Kai Mansur Saketa..Ka koma ka zauna muyi mgana.."Yafada yana kallonsa Diza na jin haka Ta Fizge hannunta ta matsa Baya Tana kuka Dole Mansur ya Rarrafowa Zuwa Wajen Mastur ya Zauna yana Dora kansa saman kafadansa sai kuka Gabadaya Jikin Mastur rawa yake Zuciyarsa na wani Tsalle ga Koshi ga kwanan yunwa Duk da Diza ta Furta shi take so Har Abada bazai Taba Karya nashi alkawarin ba Bazai juri ganin Kaninsa na kuka Saboda Mace ba Macen ma Duka aduniya Zasu barta,Hannunsa ya Daga ya Dora saman kan Mansur yana Shafawa alaman Lallashi ammh ya gaza Furta ko kalma Daya.

Baba Habibu ya kalli Diza yana Fadin"Khadija..Dukkanmu nan mun Dauka kun gama Daidaita kan ku keda Mansur Sai kuma mukaji wata mgana wacce ba Haka ba.."? Diza da kanta ke kasa Tana kuka Ta Dago Tana Fadin"Wlh Baba Ba soyayya Tsakanina da Mansur..Bai taba cewa yana sona ba..Ban san wannan mganar ba sai yau Baba.."

Baba Habibu Zai yi mgana Daddy ya Tareshi Yana kallon Diza yace"Da Mansur bai ce yana Sonki ba..Da kike Fadin Mastur kike so Shi din ya Taba cewa yana sonki ne..? Diza sai ta kasa mgana Kallo ya koma kanta Dakyar ta Dago kanta Tana kallon Mastur Shi kuma sai ya kauda kai ba ita yake kallo ba Cikin Daka mata Tsawa Daddy yace"Dake nake mgana.."
Da Sauri Diza Tace"A"a Daddy.Ammh.."Hannu ya Dagamata ya Dakatar da ita kafin ya Juya kan Mastur yana Fadin"Mastur ka gayamin Tsakaninka ga Allah..Kana son Diza ko baka sonta..?
Mastur Dayaji Tambayar Daddy Daga sama Mansur sai da yaji Gudun Numfashinsa da Bugawar Zuciyarsa,Daburcewa yayi Ya kasa mgana Domin Idanuwansa na Cikin na mansur yana kallon Raununsa Har Abada bai Taba bari wani yasan Sirrin Zuciyarsa ba kansa na kasa yace"A"a Daddy.Daga ita Har Mansur Daya na Daukesu.."Yana Fadar haka Aransa yace Astagafirullah Da karyan da yayi Domin yasan Duk Duniya Diza ce Sanyin Idanuwansa.
Daddy na jin haka ya kalli Baba Habibu yana Fadin"Mganar bata da Rudani Habibu..Tana son Mastur shi kuma baya Sonta..Saboda Haka Mansur na Sonta Mganarsa Tafi Tata Muhimmanci."
Bai bama Baba Habibu Damar mgana ba ya kalli Diza yana Fadin"Ki cire mganar Mastur Domin ni da kaina Zan zabamai Matar Data Dace Dashi..Ko kina son Mansur ko baki sonshi..Ki koyama Zuciyarki Sonshi Khadija. ...Domin babu fashi Shi Auranki Dashi.."

Yafada Cikin kakkausan Murya da Sauri Mommy Ta kalleshi kamar Zatayi mgana sai ta Fasa Diza kuwa Kuka ta saka kamar Ranta Zai Fita Aiya Dake kusa da ita Tana Lallashinta Mansur na jin haka ya saki Mirmishin Jin Dadi Baba Habibu yace"Haba Alhaji Taya zaka Tursasata..?
Mikewa Daddy yayi yana Fadin"Ba Tursasata nayi ba..Dolen ne nayi mata..Kai kuma Mansur bansan kana kuka gaban mace..Kamar ba Namiji ba..Daga yau ka Fara Shirinka..Kai ma Mastur Kafara naka Domin Duka Rana Daya Sha"anin zai kama..Allah ya bamu ikon Sauke Nauyin Dake kanmu.."Kowa ya amsa da Ameen Cikin Sanyin Jiki Hannu ya bama Baba Habibu sukayi Musabaha,kafin ya Haura sama Cikin Sassarfa Diza kuwa Tashi Tayi da Gudu Tana kuka ta Fada DakintaTa Bango Kofa Mommy Ta Bita da kallon Tsausayi Hajja ce ta Fara Mikewa Tana Fadin"Hajiya ki lallashi Alhaji..Dom Allah kada yayi ma Hadiza Dole.."Gyada mata kai kawai Mommy Tayi ta Mike Tana yi musu sai da Safe Dukkansu jiki a sanyaye suka Mike Mansur dai kaso na Damuwansa ta Ragu Mastur kuwa gashi nan ne dai Bai san Wani Hali yake ciki da wannan Sabon Lamarin ba.

Mommy na haurawa Sama ta Iske Daddy na Zaune yana Duba wayarsa Gefensa ta zauna Tana Fadin"Ammh Alhaji sai naga kamar wannan Hukuncin naka yayi Tsauri..Taya zamu yima yarmu kwara Tal Auran Dole..?
Kallon Da yayi mata ne yasa tayi Shuru Cikin Girgiza kai yace"Ku mata kuna da karamin Tunani Asiya..Ba auran Dole zan mata Na nema mata nayi Inda Rayuwarta Zata Ingata ne ta kuma cigaba Asiya.."Ya karishe Fada Cikin kwantar da Murya.
Mommy ta kallesa Cikin mamaki Tana Fadin"Kamar ya bangane ba..?
Daddy ya gyara Zama yana Fadin"Mansur yace yana Sonta..Ita kuma bashi take so ba wanda bai Sonta take so..Da na Tilastama Mastur ya aureta alhalin Baya sonta da kuma Tursasa mata Auran Mansur Dake sonta Rayuwarsu ta Dace da juna wanne kike ganin Zaifi mata damu gabadaya Asiya..? Ya karishe Fada yana kura mata Ido Shuru Tayi tana Wani Tunani Tabbas Mganar Gaskiya Daddy yayi Tunani Bazata so Diza Taje inda va"a sonta ba kuma ayanayin Tsarin Rayuwa da Hallayar Diza Tafi Dacewa da Mansur Mastur Muraddan Mutum ne mara Sakewa bazata Taba Jin Dadin Zama Dashi ba Matukar baya sonta ba.
Ganin Tayi Shuru yasa batayi mgana ba ya Girgiza Hannunta yana Fadin"Baki ce komai ba Asiya..?
Mommy ta Sauke Numfashi Tace"Sai da kamin bayani na Fahimce ka Alhaji. ...Agaskiya a tsarin Rayuwar Diza Mansur ne Daidai da ita kuma karya Take tace Bata sonshi Duk Duniya banga wanda Diza Tafi Shakuwa Dashi bayan mu irin Mansur ba Sun Dace da juna..Mastur kuma Haka Tsarin Rayuwarsa take mara Sakewa..in ta aureshi bazata Taba jin Dadinsa ba.."Daddy ya Daga mata Hannu alamin Jinjina yana Fadin"Dakyau..Bravo..Alaiki ya Asiya Shiyasa nake kara Sonki akwai Hikima ga Hangen nesa.."Dariyan jin Dadi ta saki Da Yabonsa tace"Ko Alhajina..!?Nagode yanzu shi Mastur din wa Zaka Hadashi da ita..! Kasan yaran Zamanin nan Kada fa baya sonta Daga baya azo ana kuka Dakai Duk da Dai nasan Halin Mastur Dabam yake.."Daddy yace"Bangama Tsara komai ba Tukunnah..Mganar Kuma Kada daga baya azo ana kuka bata Taso ba..Na yarda Mastur Duk abunda na Zabamai zai karba da Hannu Bibbiyu,Munyi mgana da Mallam Habibu Tuni ya bani Damar haka.."Kada kai Mommy Tayi kafin Tace"ai shikenan..Allah ya zaba abunda yafi Zama alheri.."Daddy yace"Ameem..Yanzu ki tashi kije ki Lallasheta ki bata baki..Kada kukanta ya Haifar mata da wani Cutan kuma.."Da Sauri Mommy ta Mike Tana Fadin"Yanzu kuwa..Daman Tana raina Allah Sarki Dizata.."Tafada Tana Dariya Ta kama Hanyar Ficewa ya Rakata da Mirmishi Har ta Fice sai da yaga Fitan ta kana ya Koma yana Wani Tunanin abunda yake kokarin yankewa yana Fatan Abunda ke cikin Zuciyarsa ya Hadun ammh kafin nan zai Tuntubi Mallam Habibu in sun gama mgana sai ya Kira Alhaji muhammad din su Tattauna.

Mommy kuwa Ta iske Diza Sai kuka Take Kamar ranta zai Fita Hawa gadon tayi ta Tarairayota Zuwa Jikinta Ta Fara Lallashinta da ban baki da kuma Nasihu ammh Diza Taki jin ko Daya kawai Fadi take ita bata son Mansur bazata aureshi ba Mommy dai ganin taki Daina kukan sai ta Lallabata da an bar mganar Bazata auri Mansur din ba Shikenan da wannan mganar ta samu ta Daina Kuka ta Rakata Tiolet Tace Tayi wanka Kana ta fita ta barta nan Dakin ta Jirata har sai ta Fito ta Lallabata ta saka kayan Barci ta kwamta Tana Shasshekan kuka Ta ja mata Blanker tana kara bata baki sai da Taga Tayi Shuru kana ta Fice ta barta Tana Fita Diza ta kara saka kuka Tana Hararan Wayanta Domin Tun Dazu mansur ke kiranta Taki Dagawa yau rana ta Farko Dataji Tana jin Haushin Mansur Tunda yana neman Shiga Tsakaninta da wanda take so.

Agidan su Mastur kuwa Haka suka koma Jiki duk yayi sanyi Mansur da Mastur Barayinsu suka wuce Domin Dukkansu Suna Bukatar kadaici Baba Habibu da Aiya da Hajja suka wuce Barayinsu suka yada Zango a Falo Cikin Jimami Hajja ce ta Kalli Baba Habibu Tana Fadin"ni kam mallam Don Allah kayi ma Alhaji mgana kada atursasama Hadiza auran Mansur Tunda bata so sai ta Auri Babban Mutum Tunda Shi Take so bana so ayi abunda Xumunci zai Lalace fa.."

Aiya Dake gefe Tace"Kinji ke kuma Hajara da wata mgana..Yo shi megidan nawa yace baya sonta a kanwarsa ya Dauketa Shi ma sai ayi mai Dole..ni banga Laifi Alhaji ba Abunda yayi Daidai ne Mansur din Shi ya Dace da Hadizan kuma karya Take suna son Juna Akwai Wadanda suka Shaku da juna irinsu ne.."Hajja Tace"Aiya bazaki gane ba Shakuwa Dabam so fa Dabam.."Aiya ta karkace kai Tana Fadin"Duka dai Dayane Hajara..Gwara ayi abunda Za"aji Dadi da ayi abunda rai zai baci Daga baya..

Hajja tayi shuru bata kara mgana ba Zuciyarta Zafi take ganin Halin da Mansur yake ciki tana kaunar Mansur Bata kaunar Duk abunda zai batamai rai sam Baba Habibu kuwa na Zaune kala bai ce ba Sai da Aiya ta kalleshi Tana Fadin"Baka ce komai ba Habibu..?
Baba Habibu ya muskuta yana Fadin'Me zan ce Aiya..? In nayi mgana sai Alhaji yaga kamar na Raina mganarsa ne yana iya bakin kokarinsa akanmu da yaran nan asali ma Shine Silan Zamowarsu wasu yau..Yana da Cikakken Iko akansu..abunda nake so Daku kuma kuyi Shuru da bakin ku abu Daya kawai zamu yi tayi Shine addu"an Allah yasa Alheri acikin Lamarin in babu alheri Allah ya Warware komai Cikin Sauki.."Aiya Tayi karaf Tace"Shikenan kuwa mgana ta kare.."Hajja tayi Shuru sai Chan Tace"Mansur fa Mallam..?
Baba Habibu ya mike yana Fadin"Kada ki Damu Dashi..Yana Tare da Dan"uwansa.."yafada Lokaci Daya yana Shiga Cikin Bedroom din Aiya ma bata kara mgana ba Tatashi Ta Shige suka bar Hajja nan Ta Zabga Tagumi kamar tatashi Taje Shashensu Taga Lafiya sai kuma ta Fasa Tuna yana Tare da Babban Mutum Ta Tabbata Zai kula dashi Jiki a Sanyaye ta mike ta Shige ciki Zuciyarta Duk ba Dadi.

Bangaran su Mansur kuwa Suna Shiga Shashensu Mansur ya Rumgume Mastur Ya fashe da kuka Mastur yaji wani Dum a tsakar kansa Dafa Kansa yayi yana Fadin"Kai miye haka..? Kan Mace Honourable da kansa yana kuka Saboda mace..?
Yafada Cikin karfin Hali Dago kansa Mansur yayi Idanuwansa sun kala sun yi jajie Hannun Mastur Guda Daya ya Damka ya Dora Saitin Zuciyarsa ya lumshe ido yana Fadin"Ya Mastur kaji yadda Zuciyata take Bugawa ko..? To duk Saboda Diza ce..Wlh itace Rayuwata in ta ce bata sona Zaku Rasani.."Yafada Lokaci Daya Hawaye na Gangaromai Mastur Daya zama out of Control yabi sa da kallon mamaki da Rudani Da Sauri ya Dauke Hannunsa ya Share ma Mansur Hawaye yake Fadin"Bata isa tace bata sonka ba. duk Duniya ba macen da Zata saka kanina kuka.."Mansur na jin haka kawai ya duka gaban Mastur yana Fadin"Yauwa na sani kana Sona..Duk Duniya kafi kowa son ganin Farimcikina..Don Allah ka Roki Diza Ta soni Kada ta juyamin baya.."Mastur Dayake jin kamar Shima ya Fashe da kuka ya Saka Hannu ya Dafa kafadun Mansur ya Dagoshi yana Fadin"Kasa aranka ka gama Zama Mijin Diza Insha Allahu.'
Waro idanuwa Mansur yayi yana Fadin"Really..! ? Mastur ya Daki kafasansa yana Jinjina masa kai,Mansur ya saki Mirmishin Farinciki yana Fadin"Promise.."Mastur yayi shuru yana kallonsaa kafin ya gyada mai kai yana Fadin"I promise u.."Rumgumesa kawai Mansur yayi yana Fadin"Tanque..Tanque Very much Yaya..Allah ya barmin kai.."
Mastur ya yi Yake kawai kafin su saki juna Mastur ya kalli Mansur yana Fadin"Ka shiga Dakinka kayi wanka..Ka kwanta ka Huta Banda Damuwa kaji ko..? Kamewa yayi ya saramai yana Fadin"Yes Sir.."Cikin nuna Farimcikin Dayake Ciki,Shima Mastur din Murmusawa kawai yayi ya juya ya taka zuwa Dakinsa Mansur ma ya wuce Cikin Dakinsa Cikin Farinciki ya Fada kan gado yana Fadin"Yes...Yes..!!
Mastur kuwa yana Shiga Dakinsa ya maida Kofa ya Rufe ya Sulale nan kasa yana Dafe da kansa Haka kurun yake so yayi kuka ko zai samu Saukin Wani lamarin ammh kukan yaki zuwa..Wannan Sadaukarwan da zai yi mai girma ne kuma mai Nauyi ne yanajin kamar yayi arauni kuma ya gaza Ballatana Dayaji Diza ma ashe shi Take so   Sai kuma bashi da yarda Zai yi Mansur na sonta yana Fadin zai iya Mutuwa Saboda ita kuma yayi mai alkawarin auranta Ya zama Dole ya samu Diza suyi mgana ya Roketa ta auri Mansur Don Allah kada ayi biyu babu Shi kwance mansur kwance gwara shi ya kasance Cikin Halin Ciwon soyayyah Mansur kuma ya kasance Cikin Farimciki.

Dakyar ya iya mikewa ya Rarrafa ya Shiga Tiolet ya yi wanka ya Dauro alwala yazo ya Shimdifa Darduma ya tada Salla Shafa"i da wuturi yayi kafin ya Sallame ya Dade yana addu"an juriya,kafin ya koma ya Jingina da Katifarsa jakar kayansa ya Jawo ya Bude ya Dauko Karamin Diary dinsa da Biro ya Bude ya Fara Rubutu kamar ko yaushe yakai wani Lokaci kafin ya kamallah ya Tattara,komai ya maida Cikin Jakarsa ya Tashi ya Hau kan gado,sai lokscin ya Tuna da mgangunansa sai dai kuma ya Riga ya kwanta bazai iya Tashi ba Kwanciya Sama yayi yana kallon Rufun Dakin ba Domin barci zai iya kwaasansa ba.

******
Washegari Haka Mansur,Diza da Mastur suka Tashi Zukata babu Dadi Dukkansu barci barawo ne ya iya satansu,Da Safe Da Diza Taje gaida Daddy sai ta kara sakamai kuka Tana kara Rokonsa Kada ya aura mata Mansur Shi kuma sai ya Dinga Lallashinta yana Nuna mata Illar Auran wanda baya sonka..Ko bata Hakura ba ammh Tabbas mganar Daddy ta Shigeta,Dakinta ta koma kawai Tayi Shuru sai Hawaye Tana Tunanin irin Tata kaddaran kenan Son wanda baya sonta Tana ganin kiran Hauwa bata iya Dagawa ba batajin Zata iya Fita yau Daga gida Cikin wannan Halin Datake ciki.

Mastur kuwa da kwarin gwiwa ya Tashi..Mansur ma cikin Farinciki ya Tashi Saboda alkawarin da Mastur yayi mai ya kuma san Tabbas He make it,Dukkansu a Shashen Hajja sukayi Breskafast Kuma ba wanda ya kara Tada mganar Har Baba Habibu ya Fita Zuwa kasuwa Sai bayan Fitan sa ne Hajja Tayi mganar Bata son Zuminci ya Lalace,Mansur yace"Kada ta damu..Yayansa yamai alkawarin Diza matarsa ce.."
Mastur dai bai yi mgana ba Ballatana aji bakinsa yana ta Hada Tunanin wani kalma Zai yi amfani Dashi Wajen Lallashin Diza ta Fahimceshi Kuma bazata gane Menene acikin Zuciyarsa ba.
Suna gama karyawa Ya Mike ya kalli Mansur yana Fadin"Bari naje na sameta..Ka jirani yanzu zan Dawo.."Mansur ya kallesa yace"Wajen Diza zaka ka..? Kai Tanque Yaya..Sai ka Dawo Don Allah ka Lallasheta nasan Tana chan Tana kuka Tun Jiya nake kiranta akashe..Tel Her am giong to be a good Husband To her.."Mastur ya Rausayar dakai bai ce komai ba ya Fice Hajja Da Mansur suka Rakashi da ido Ba wanda ya sake mgana Shi Mansur Murna ta kamashi Shi ita kuma Hajja Tunaninta ya Rabu Biyu ganin Mastur yadda Duk ya koma Kamar bashi ba Duk da bai da Hayaniya wannan Karon abun ya wuce Tunaninta.
Yana isa Falon kasa ya iske Daddy ya Riga ya Fita Bayan sun gaisa da Mama Fadime yace ta Haura sama Tayi ma Mommy mgana kan Daya Daga cikin kujerun Falon ya Zauna yana Faman lumshe ido yana Sanye da Wata Bakar Jallabiya da Hulansa Tabani kaji Hadisi.
Mommy Da mamakin jin Mastur ne yazo ta Sauko Kasa ya Sauka suka gaisa kansa na kasa ya kasa mgana Tace"Mastur Lafiya..? Ko da wata mgana ne..?

Kai ya girgiza yana Fadin"A"a mommy..Nazo nayi mgana da Diza ne.."Mirmishi Mommy Tayi kafin Tace"Kuma Shine ka kasa mgana..Allah mai mutane..Bari na Shiga na sanar mata.."Ta Fada Tana Kama Hanyar Dakin Diza Ta Tura Kofa ta Shiga Ta Iske Diza na kwance ta Kurama Waje Daya ido,Sai tazo gabanta ma ta Lura da Mommy gyara kwanciya Tayi kafin Tayi mgana Mommy ta Rigata da Fadin"Ga Mastur yazo wai yana son mgana Dake.."
Zuruf Diza ta Mike Zaune Tana Fadin"Ni wai Mommy..?hararanta Mommy Tayi Tana Fadin"Ya shigo nan ne..!? Kai kawai Diza ta gyada ma Mommy Tana jin Wani Dadi Daga kasan Ranta na Tunanin kila yazo ya gayamata Shima yana sonta ne,har mommy ta Fice Bata sani ba Sai da Taji Budewar kofa ta Siriiriyar Sallamarsa Cikin Muryansa mai Cike da Zati kana Diza ta Zabura Ta Mike Tana Raruman karamin Vail Dinta ta yafa Duk ta Daburce.
Shi ko kallo Daya yayi mata ya kauda kai Daga bakin Kofan ya Tsaya Goye da Hannanunsa abayansa yana Bin Dakinta da kallo Wanda Shine karonsa na Farko kenan da Shigowa.
Bakinta Diza na rawa Tace"Ina kwana.."bai yadda ya kalleta ba Kada ta sakashi Rauni yace"Baki Daina kukan ba kenan Saboda Daddy yace Zaki Auri Mansur..!?ya fada Cikin Dakiya
Da mamaki ta Dago Jajayen Idanuwanta da suka Kumbura Tana kallonsa Shi kuma sai yayi Saurin kauda kansa yana Fadin"Nayu mamakin abunda kikayi Khadija..Bantaba Zaton Zaki yi ma Mansur haka ba..ayaddan nassan Tsskaninku Dashi..Ban zata Zaki ki shi Lokaci Daya ba.."yafada yana Cije bakinsa
Diza ta Durkusa kan kafafunta ta Fashe da kuka kafin ta samu Zarafin mgana mastur yace Cikin kakkausan murya.
"Kin ce ni kike so Ko..?toh indai Gaske ne kina sona..Ina so Ki Tattarashi Duka ki maidashi kan Dan"uwana Mansur Domin Dani Dashi Duk Daya ne Khadija..In kika kishi Tamkar ni kika Watsama kasa acikin Idona.."

Ya karishe Fada yana Sauke Numfaahi Lokaci Daya yayi Saurin Juya baya ganin irin kukan da Diza ke yi wanda ya Fara sakamai Rauni yana neman Fallasa abunda ya Binne acikin Ransa.


*Ki biya ki karanta cikin Salama Mace mai aji bata jiran abun Sata takan mallaki nata na kanta ne saboda ta isa..Domin neman karin bayanin 09069067488*




*Shakira...*
1/1/22, 18:54 - Maryam Badmsi: *SS....18*

"Diza ta Durkusa Cikin Rawan jiki Idanuwanta masu kyau da kyalli suna Zubar da Hawaye Tafara mgana cikin Raunin Murya

"Ya Mastur kamin rai..Ka juyo ka kalleni kada ka juyama Soyayyata baya wlh bantaba Son Mansur ba Banta jinsa araina amtsayin Wanda zan Karishe Rayuwata Dashi ba kai kadai nake so Tun ban mallaki hankalin kaina ba kai nake mafarkin ka zama Uban ya"yana kai nake Hange ka Zama Bangona da garkuwata In kace baka sona bazaka Aureni ba Tabbas Rayuwata ta kusa Zuwa karshe...!!!""

Ta karishe Fada Cikin wani gunjan kuka yana Tsaye kikam Allah yasa ya Juya mata baya data Fahimci Rauninsa a wannan gaban,Jijiyoyin kansa sun Tashi Radau Idanuwansa sun Sauya Launi Kirjinsa na wani Suya Gangar Jikinsa na bari kansa na wani rin Saramai Dama Dama ace Zai iya Juyowa ya Dago Diza ya Rumgumeta Cikin Jikinsa yagayamata Cewa Duk Duniya ba Macen Dayake Fatan mallakan Bayan ita..Sai dai Ina bazai Taba bari wani yasan da wannan Sirrin ba..ya Riga yayi Wannan SADAUKARWAR ga Kaninsa kuma Dan Goggonsa Mansur bazai Taba bari wani yasan Yana son Diza ba Bazai Taba yarda aga wata alama ba Ya riga ya binne abun acikin Ransa Bazai Taba bari ya Fito Fili ba koda Soyayyarta Zata iya Zama ajalinsa.

Cikin Dakiya da Jarumta ya Juyo ya Fuskanceta yana Fadin"Diza ki daina wannan mganar..Ban taba Sonki ba..Ban taba miki kallon macen da Zan iya Auranta ba..Ina miki kallon kanwata ce wacce muka Fito Uwa Daya uba Daya..Ki Taimakeni ki Tallafeni indai kina min Soyayyarki ta gaskiya ki Sadaukar da Soyayyar da kikemin Zuwa ga Dan"uwana Mansur kimin alkawaarin Zaki aureshi ki kula Dashi...Na Tsawon Rayuwarku Har Abada..zaki min wannan Alfarman da alkawarin khadijaaaa..?

Yafada Cikin Wata irin murya mai Cike da Rauni da wani irin Tafarfasa Dake Fitowa Daga kasan Zuciyarsa

Diza Dake kuka ta Dago Idanuwanta Taf da Hawaye tana kallonsa Shi kuma sai  ya kauda Idanuwansa yana ganin kamar Zata Fahimci Halin Dayake Ciki Cikin kuka Tace"Wannan ne kadai alfarman Dakake so ya Mastur..?Tafada Bayan ta Mike Tsaye Kai ya gyada mata baya son mgana Cikin kwarin Gwiwa Tace"Nayi maka..Kuma nayi alkawarin Sadaukar da Soyayyata Zuwa ga Mansur. zan kula Dashi Zan Zauna Dashi Muddin Rai indai Hakan zai saka ka Farinciki.."Ta karishe Fada Hawaye suna kwaranyomata Lokaci Daya Tana saka Hannu Tana Sharewa Domin Ta nuna Yadda Dakiya ta kamata Saurin Bude baki yayi yace mata"Tanque so Much khadija..Har Abada Mastur bazai manta da Alfarman ki ba .Allah ya Tabbatar da alhrinsa acikin Rayuwarku Don Allah ki Cireni aranki Kada Hakan ya Cutar da kanina.."ya fada kamar Zai mata kuka gyada mai kai Tayi Tana Fadin"Insha Allahu..Bazai Taba kuka da Hakam ba.."Kai kawai ya gyada mata yana jin kafarsa na Rawa sai kawai ya juya ya Fita kafin ya Zube mata anan Wajen yana Fita ta Fada kan Gado ,tana Toshe bakinta kada kukanta ya Fito Zuciyarta Tana wani kuna kamar Zata mutu haka take ji..

Koda ya fito bai ga kowa afalon ba sai kawai ya fice yana Rangaji maimakon ya Nufi gida kawai sai ya samu kansa da Mikewa kawai yana Tafiya batare Daysan inda yake jefa kafarsa ba, Bayaso ya koma gida Mansur ya gansa cikin wannan Halin zai iya Fahimtar wani abu,Yayi Tafiya mai nisa bai sani ba Sai Daga baya ya Dawo Cikin Hayyacinsa kana ya Juyo Zuwa Gida Duk ya Sharba Zufa Fuskarsa Tayi wani iri Idanuwansa sun kala jijiyoyin kansa duka sun mike Kansa na wani Saramai kamar zai Rabe gida Biyu baya so ya Nuna Rauninsa yaRiga yayi ma kansa alkawarin Sadaukarwan Soyayyarsa Har Abada.

Koda ya koma Gida Direct Shashensu ya Shiga ya iske Mansur na Zaman Jiransa yayi ta kiran Wayarsa ma bai Daga ba ashe adaki ya Barta Cikin karfin Gwiwa ya Tabbatar ma da Mansur komai ya Zama Daidai Haka Mansur ya Rumgumeshi yana Murnan Farinciki Hakan kadai ya isa ya saka Mastur Samun Natsuwa Daman So yake ya Fita kan dai harkan Siyasansu ne Zabe yakusa Dalilin wannan mganar ya kasa Fita nan yamai Sallama ya Fice ya shiga wajen su Hajja yana Murna yana gaya musu Komai ya Zama Daidai Diza ta amince Zata aureshi Farinciki ya Cika Zuciyar Hajja da Aiya Domin Daga Jiya Zuwa yau Basu ga Fara"ar Mansur ba duk da kuwa Yana da Yalwar Fara"a komai sai da Farinciki yake gudana.

Abangaran Diza kuwa Kuka taci kamar Zata Shide bata Taba Sanin Tana son Mastur ba sai da wannan abun ya Faru ji Take yi gabadaya Duniyan Tayi mata kunci Gashi Alkawarin Data Daukan mai na Sadaukar da Duka Soyayyarsa ga Dan"uwansa Mansur bazata iya cemai A"a Domin yaci Darajan Darajan Soyayyae Datakemai Zata auri Mastur ammh Ba Lalle ya samu Zuciyarta ba zai auri gangar Jikinta ne Ammh Tabbas Ruhinta da komai nata yana Wajen Mastur ne acikin wannan Halin Mommy Tazo ta Sameta ganin kukan Datake yi ne ya Bata Tsoro Cikin Razana Take Fadin"Subhanallah Diza..?me kuma ya Faru..?ko Mastur din yace miki wani abu ne..?
Diza Ta Dago Idanuwanta na Zubar da Hawaye tace"Mommy ki gayama Daddy na amince da Auran mansur..Na Shirya kowani Lokaci kuka yanke am Ready.."Ta karishe Fada Cikin Zubar kwallah Soyayyah da Sadaukarwa.

Mommy ta Tsaya Tana kallonta Cikin wani yanayi kafin Tace"Da gaske kike..? Toh inhakane meyasa kike kuka..? Da sauri ta Fara goge Hawayenta Tana Fadin"Da gaske nake Mommy na amince.."Mommy Dataji Dadi ta Rumgume Diza Tana Fadin"Masha Allah..Ko kefa.Allah ya Tabbatar mana da alherinsa Khadijata.."Tana Jikin Mommy Tana jin wani Hawayen na Tahowa ammh ta Danne Mikewa Tayi Tana Fadin"Mommy Cikina ya juya bari na Shiga Tiolet.."Mommy tace"Me kika ci ne haka.?
Diza Na Tafiya Tana Fadin"Bansani ba Mommy.."Tafada Tana Boye kukanta da Sauri ta Shige Tare da Rufo kofa Daidai lokacin da Mommy Ta Mike Tana Fadin"In bai tsaya ki gayamin."Daga haka Ta Fice Daga Dakin Cikin Farimciki Diza na jin Karam Kofa taSulale nan Kofar Tiolet din ta Saki kukanta da Dukkan karfinta Tana jin Zuciyarta na wani irin Zafi Kamar mai Ciwon Zuciya Tayi kuka Kamar me Sai da Taji Mommy ta Dawo Dakin Tana Kiran sunanta kana Tayi Saurin Tubewa ta Fara wanka da Mommy ta kara kiranta sai ta amsa mata Cikin Dashewar Murya Cewa Tana wanka ne ajiyar zuciya Mommy ta sauke kafin ta Fice bayan ta ijiye mata Mganin Tsaida Bayan gida.

Haka Diza ta Fito Tana ganin Jiri Da Dafa Bango Tazo ta Fada kan gado Tana Cigaba da kukanta Wata Zuciyar Tana bata Hakuri kan Diza kiyi hakuri Taki kaddaran kenan Auran wanda baki so ammh kuma Wanda kike son ya Furta miki baya Sonki bai Taba sonki ba gwara ki Rumguni mansur koda baki Sonshi Zai Zauna Dake haka yayi ta Hakuri wannan kukan bazai Fisheki ba gwara ki mike Kiyi Takwalli ga Allah ki kuma karbi Duka Kaddaranki da wannan Tunanin Ta Mike da Sauri Cikin Karfin Gwiwa Ta Fara Shirya kanta ko Minti goma Batayi ba ta Shirya Cikin Doguwar rigar atamfa Ta saka mayafi ta Dauko karamar JakaryTa ta jefa wayarta Ciki ta Sako wani Falt Shoe ta Fito Sama ta Haura Falon Mommy Tayimata sallama Mommy Taji Dadin ganinta Zata wajen aikinta Tayi ta mata Nasiha Duk da Taga idanuwanta sun kumbura Batayi mgana ba ta Dai Tambayeta Ciwon cikin ya Daina kuma tasha mganin Data kai mata tace eh Cikin jin Dadi Tayi mata adwwo Lafiya Key din Motar Mommy ta karba Tace bata ga nata ba ta Sauko kasa Duk da yanayin Data ke Ciki Bata Sare ba Ta koma Dakinta ta Dauko Bakin glass dinta ta saka Saboda Kada Ma"aikatanta su Fahimci Something is wrong.

Bangaran Mastur ma sai nace Abun yafi Zafi sosai Tunda ya koma Daki ya kwanta Ciwon kai mai Zafi ya Danneshi aammh bai Nuna ba Ko Sallar Azahar bai samu zuwa ba Cikin Daki yayi shi Mansur bai Dawo ba Su kuma su Hajja sun zata shima ya Fita ne Duk sun san ba kasafai yake fita ba in ya Dawo bai iya Tashi yayi wanka ya Sauya kaya ba sai bayan La"asar ya saka kananun kaya ya Fita Zuwa Shashen Hajja ya Zauna kawai Shuru baya mgana Lokaci bayan Lokaci kuma yana Dafe kansa Hajja Dake da kai da kawo Tsakanin Kitchen da Falo Ta Shiga Damuwa ganin yanayinsa yasa kawai Tazo ta Zauna agefensa Tana kallonsa Cikin kauna irin ta Uwa da Danta Ta Saka Hannu Ta Ciremai Tagumin Tana Fadin"Babban Mutum wai meke Damunka ne..!? Ina lura dakai tunda kayi wannan Dawowar baka cikin natsuwarka duk ka Rame ka Lalace kamar akwai abunda ke Damunka..?

Da sauri ya kwakwalo Mirmishin Kafin Hali yana Riko Hannayen Hajja yake Fadin"Bakomai Hajja Gajiyan aiki ne Hajja bamu samun Cikakken Hutu sosai.."Yafada yana Fatan ta yarda Dashi ita kuwa ido ta kara sakamai Tana Tamtaman amganarsa ganin yadda Tayi yasa ya saki Jikinsa yana Kara Fadin"Ki yarda Dani Hajja bakomai..In ma da wani abu ai da na gayamiki.."Ajiyar Zuciya ta Sauke Tana Fadin"Tun kana karaminka akwai Shanye Damuwa..Ko mallam baka bari ya Fahinci wani abu na Damunka ba bana son kana Haka Watarana sai abun ya Dameka ka kasa Fadama kowa Har Hawan Jini yazo ya kamaka.."Aransa yace"Na nawa kuma Hajja..Sai dai kuma Allah ya Sauwake kawai.."Ammh a Fili Sai yace"Bakomai Hajja..Ki daina Damuwa..Kuma wannan Ramar da kika ga nayi Ciwon da nayi kwanaki ne Hajja ba wani abu ba..Sai rashin Abincin Hajja mai Dadi Duk shi ya sakani Rama.."Yafada yana Mirmishi Kansa ta Shafa Lokaci Daya ta Mike Tana Fadin"Allah yasa Hakane..Allah ya yi muku albarka Kai da Dan"uwanka."Mastur ya amsa da Ameen Ameen Saboda ma ta kara yarda Dashi Binta yayi Kitchen wai Zai  Tayata aiki Tana Hanashi ammh yaki Hanuwa Dole Ta kyaleshi Sanin Tun abaya Mastur ai ba Malalaci bane Ayya Tana Daki Batasan Wainar Da ake Toyawa ba,Suna aiki suna Hira na Tsakanin uwa da Danta sai gashi Mastur ya saki Jikinsa Taresuka gama komai Daman Tuwon Shinkafa ne Miyar Zogale Hajja Tayi suna gamawa ana kiran Sallar mangariba Sai Lokacin ya Fita Zuwa masallaci Yayi sallah ya Dawo,ya koma Shashensu ya Dauko Wayarsa yaga Tarin Kira ya zauna ya Fara Bin Baya Lokacin Ayya ta Fito Ta Zauna tana mai Hira yana amsata da Mirmishi ko Eh ko A"a.

Sai gabda Isha"i Mansur da Baba Habibu suka Shigo Gidan kusan Lokaci Daya suna Shigowa alwala sukayi Dukkansu suka wuce masallaci Sukayi salla Bayan sun Fito sun Dade suna Gaisawa da Daddy Mansur da Mastur ma gida suka Dawo suka bar Daddy da Baba Habibu suna kara Tattaunawa ananne ma Daddy ke Fadamai Bayan ya Dawo Mommy ta gayamai Diza tace agayamai ta amince da Auran Mansur Baba Habibu ya nuna jin Dadinsu sun Rabu kan Baba Habibun zai Kira Baba Sule su Tattauna yadda Sukayi Shikenan sai azo ayi mganar Bikin Lokacib ya gama Tunanin Wacce Mastur din Zai nema da Haka sukayi Sallama Kowa ya Shiga Gidansa.
Koda Baba Habibu ya Dawo bai gayama su Mansur abunda suka Tattauna ba Sun zauna dai sunci abinci Tare Cikin Farimciki Mastur yana ta Kokarin ya zama Normal Shi kanshi Baba Habibun yaji Dadin ganinsa ahaka sabanin Dawowar da yayi Shekaran jiya.
Sun gama cin Tuwon kenan Hajja da Mansur suna Hira Sama Sama Diza ta Kiraahi awaya ya Dauka Cikin Rawan Jiki Sai tace yazo gida ya Sameta Mansur kamar zai suma Saboda Dadi yana gayama Mastur Dayayi Galala kawai yana kallonsa yana Tunanin Shi da Mansur wayafi son Diza ne,Fitan Mansur ne yasa Baba Habibu ya gaya musu mganar da suka Tattauna da Daddy Ayya tace hakan ya kamata Domin Mahaifinsa ne yana da Hakki akansa,Mastur dai na Jinsu kala bai ce ba sai ma wayar karyan Daya Fara yaTashi ya Fice Shashensu Dakinsa ya Shiga ya maida Kofa ya Dauko Diary dinsa ya Fara Rubuta abunda ya Faru yau Filla Filla Kamar yadda ya Saba.

Mansur kuwa yana Gidan su Diza afalon kasa suna Shan Hira da Diza Bayan ta Bashi Hakurin Abunda ya Faru Duk da Ta Rage Sakin Jiki Dashi bai Damu ba Shi kadai yake Surutunsa tana Binsa da kallo kawai Lokaci Bayan Lokaci Takan saka baki ko ta Bisa da Mirmishi Duk kokarinta Ta sZama Normal kuma ta Rumgumi kaddaranta kuma ta Cikama Mastur alkawarin Datayi ma Mommy Da Daddy sun ci Dadi Sosai hakan kuma ya Tabbatar musu da komai yayi Daidai Sai wajen 10pm kana ta Rakosa ya Tafi Gida Mansur yaji kamar yana yawo a Sama Saboda Farinciki Daya koma yaso ya Fara bama Mastur Labarin Tsskaninsa da Diza ammh kuma sai yaji Kofarsa Tana Rufe sai yayi Tunanin kila ya kwantane bai san Mastur din yana Jinsa kawai Baya so yana yaki da Zuciyarsa kuma Mansur nakokarin maidashi Baya ba.
Da garin Allah ya waye Mastur da Shirin Tafiyarsa ya Fito yace zai Hau Motar Haya zuwa kaduna Dagachan zai Hau Jirgi Zuwa Parthercourt Jin haka yasa Mansur yace bazai barsa ya Hau Motan Haya ba shi Zai kaisa Duk da yaso ya kauce ma Hakan ammh ba Hali Anan suka karya Falon Hajja kafin yayi ma iyayansa Sallama Bayan ya Cika su da kudi suka Rabu suna Faman sakamai albarka Kafin ya wuce sai da suka Shiga wajen Daddy yamai Sallama Suka Rabu kan Sai ya Kirashi kan mganar Mastur din yace yana Jira bakomai Diza Bata nan ta Fita Mommy ke Fada musu akwai wani Order da akaayi a wajenta ne na Cake da Samosa yau Za"a karba Shine Tatafi da kanta kada ayi Shirme da Haka sukayi musu Sallama Mansur ya Fito da motarsa Mastur ya Shiga suka Mika Hanyar kaduna suna Tafiya Mansur namai Hiran Diza da Abunda ya Faru jiya Mastur na Jinsayana Rakasa da Mirmiahi Har acikin Ransa yaji Dadin ganin Mansur Cikin Farinciki.
Da wuri suka isa kaduna Zaman Kamallah Tiket din Tafiyar Mastur bata wuce awa Daya ba Komai ya kamallah Sai da Mansur yaga Tashinsu kana ya Kamo Hanyar Dawowa Zaria Cikin Farinciki.

******

*Bayan kwana Biyu..*

Diza tayi kokarin nuna ma Mansur komai ba komai bane,Dalilin haka ya saka kowa Cikin Farinciki,Barin ma uban Gayyar Mansur Tuni ya Fara yada ma Mutanensa Diza da zai aura kowa yaji sai yace ai Daman Tuni kowa yasan Soyayyace Tsskaninsu.

Baba Habibu ya kira Baba Sule sun Tattauna ya nuna matukar Jin Dadinsa kuma yace wuka da Nama na Hanun Baba Habibu su nasu kawai yan zuwa Biki ne wannan karon Tayi ma Habibu Dadi Sosai koda yake gaya ma su Hajja suma sun ji Dadi Da Daddy yaji yace ba wani abu Tunda abun Duka na Gida ba sai an Bata Lokaci ba Shi yayi alkawarin koba Diza Mansur Zai aura ba Shi Zai Biya musu Sadaki Shi da Mastur Hade da Muhalli Kuma Daman yayi mgana da Danginsa nachan Tureta yayi musu bayani sukace bakomai basai sunzo ba Shima ya isa yayi Komai Tunda duk abun Gida ne alokacin ne yake gayama Baba Habibu ya zaunayayi Tunanin ba wacce Zata Dace da Mastur sai Rumana Diyar Alhaji Muhammed Duk da Baba Habibu bazai Shaida yarinyar ba ammh Alhaji muhammed Dattijon kwarai ne kamar Alhaji Sunusi Karan Dayake musu a Rayuwa da Dawainiya Baba Habibu ya kasa mgana Saboda ko Yayi Godiya sai Daddy ya nuna bai ji Dadi ba da wannan Daddan Labari Ya isa gida ya Shaida musu Hajja Ayya Tayi ta saka albarka Hajja kuwa bakinta yaki Rufuwa Fadi kawai Tace"Wadanan Mutanen Allah ya saka musu da aljannah."
Baba Habibu yace"Ameen..Kina ji fa Yace shi Zai Biya musu Sadaki Harda muhallin Zama..Aduniyan ko akwai Mutane irin Alhaji Kuwa..? Ya bama Mansur yarsa..Yanzu kuma Zai bama Mastur Diyar abokinsa Alhaji muhammad.."Hajja Tace"Babu kam..Dukkansu mutanen Kirki ne..Hajiya Farida ai Mutum ce in Har tazo da abun arzikinta nida Ayya haka Zata kawo mana Ita kanta yarinyar sosai Tske da Hankali kuma sun Dace da Babban Mutum bata da Hayaniya.."Baba Habibu ya Rausayar dakai yana Fadin"Allah yasa Tayi mai Ara"ayinsa.."Hajja Tace"Ai shi bai da mtsala koda yaushe mai Biyayya ne.."Suna cikin mganar sai ga Mansur nan Hajja ke Fadamai Farinciki ya Cikashi ya kalli Hajja yana Fadin"Hajja yan Ameen sun amsa mganata..Kinsan da muka je mata Indection din ina ganinta da yanayinta nace Da Ya Mastur ta Dace..Allah Sarki gaskiya Yaya yayi sa"a gata Educated Baba Likita ce fa.."Baba Habibu yace"Haka Alhaji yace..Masha Allah..Allah yasa albarka.."Shidai Mansur bakinsa yaki Rufuwa Shashensu ya koma ya kira Mastur bai Daga ba sai ya kira Diza ya Fesa mata,komai yace yana nan Shigowa zai yima Daddy Godiya basu gama wayar ba Diza Ta katse Saboda kukan Daya Taso mata Daman Ashe Rumana ce Zata auri Mastur Shiyasa Daman Tun tuni Take jin Kishinta Jin wannan Labarin yasa Taji ta Tsani Rumana da ganinta gabadaya Koda Mansur yazo yima Daddy Godiya a madadin Shida Mastur Diza kin Fitowa Tayi sai tayi barcin karya Dole ya kyaleta Da Safe ma Hajja da Ayya sun Shigo Godiya Daddy yace bakomai Mommy ma bakinta yaki Rufuwa yau da sukayi waya da kawarta Hajiya Farida Tace itama Jiya Da Daddare Baban Rumana ke Fadamata Tayi kwanan Sallar da Farinciki Zasu aurar da ya"yansu Rana Daya,kuma Wajen Mazaje na gari musssman Mastur Da Daman ya Shiga Ran Alhaji Muhammed Da Hajiya Farida suna jinsa Kamar su suka Haifesa.

Daman yadda abun ya Faru..Tun da suka je Lagos Daddy yaga Rumana ba wanda yayi ma Sha"awarta sai Mastur,Ya bar dai abun aransa Toh jin Mastur din yace ba wanda yake so sai abun yamai Dadi,ya kira Alhaji Muhammed sun Tattauna sosai Abba yaji Dadi kamar yayi kwallah Allah ya Cikamai Burinsa zai ga auran Rumana,sun Rabu kan cewa Zai gayama yan"uwansa Dake wamako da ita kanta Rumanan Abunda ake ciki zai gayamai,Nan yake gayama Umma Itama sai da tayi Sujjadan Farinciki acikin Ran Abba kuma Godiya yake ma Allah Daman Ba tun yau ba Koda yaushe yaga Mastur sai yayi ma Rumana Sha"awanta sai Sanin yaran Zamani ka Haifi Mutum ma ya watsa maka kasa a ido balle baka Haifeshi ba Shiyasa bai Furta ma kowa ba

Rumana kuwa Ta kusa Suman Dadi Lokacin da Abba ya Kirata yana gayamata bata iya Boye Farincikinta ba Tatashi ta Rumgume Umma Tana Hawayen Murna Abba na Dariya yace"Ja"ira ashe daman kina sonsa.."Kunya Taji ta saki Umma ta Fita Daga Dakin da Gudu suka Bita da kallon Farinciki Sai da ta Fita Umma Tace"Kaji ka da wani mgana..Abban Ruma..Wazai ki Namiji kamar Mastur..Ai irinsu basu da yawa.."Abba yace"Sosai ma Fatana Allah yasa alheri Zamu kullah.."Umma ta amsa da Ameen nan suka cigaba da Tattaunawa kan Bikin Rumanan da Mastur Farinciki ya Cika Ransu.
Rumana na komawa Daki ta Saiti gabas Tayi Sujjuda Tana mikama Allah Godiyarta Daya Cikamata Burinta Lokacin da batayi Tsamnani ba Farinciki kamar ya kasheta ta rasa wa zata kira kawai sai ta Kira Basma Tana gayamata Tana kuka Rumana bata Taba gayama Basma Tana son Mastur ba ammh ita ta Fahimta Domin gabadaya Wayarta Hotonsa ne,kuma Ita dai bata Taba ganinsa Ido da ido ba ammh Tana da Duka Labarin abakin Rumana Tatayata Murna Sosai Tana ta Zolayanta ta samu Abunda take so Rumana nata mamakon ashe ana iya Fahimtar kana son abu..? Gashi Basma ta Fahimceta Ranar Rumana kwana Tayi batayi barci ba Saboda Murna Tayi Sallar Tayi Godiya ga Allah ji Take kamar mafarki take yi ba gaskiya bane.

Shi kuwa Mastur kafin ma Daddy ya Kirashi ya gayamai Mansur ya Kirashi ya gayamai
Jikin Mastur yayi sanyi kenan Kowani bawa Datashi kaddaran Ita Rumana Allah ya bata abunda Take so Cikin Ruwan Sanyi sai dai bai ji mata Dadi ba Zata auri wanda Zuciyarsa ta Riga Ta Mutu gabadaya ba Shauki ba Wani Kulawa acikinta Sai Duhu Itama Zatayi Sadaukawar kan wanda take so ba Domin yana sonta ba, bazai iya Watsama Daddy kasa a Ido ba Dimbin alherinsu ya wuce Misali Koda Daddy ya Kirashi yagamai yayi Fatan alheri ya kuma amince Tare Dayi ma Daddy Godiya,Abun da ya kara Saka ma Daddy Farinciki kenan Kafin su yanke kiran sai da ya Jaddamai daya Fara Shirin Bikin bazai Dauki Lokaci ba yace Insha Allahu.


*Mace mai Daraja bata jiran Abun Sata..Mallakan nata take yi ki biya kiranta Cikin Salama Hajiyata 09069067488*



*Janafty....*
1/1/22, 18:54 - Maryam Badmsi: *SS...19*

"Ko Sati ba"a Rufe ba Alhaji Muhammad ya kira Daddy suka Tattauna kan yadda abubuwan Zasu Tafi Daidai ya riga yayi mgana da Yan"uwansa Dake wamako,Saboda kara yasa yace su zasu Tattaro su zo nan Zaria sai ayi mganar komai gabadaya Daddy yaji Dadi Sosai nan suka Tsaida Lokaci Ranar Lahadi mai Zuwa Alhaji muhammad din zai zo shida kaninsa domin ayi komai agamashi.

Daddy na jin haka ya samu Baba Habibu suka Tattauna Baba Habibu ya kasa bakin Godiya bayan an basu Rumana kuma ma ace bazasu je ba su Dagachan zasu zo Lalle kara da karamcin Mutanen nan ya wuce Duka Yadda Suke kwatance haka ya shiga Gida yana gayama su Hajja Ranar Duka Hiran kan Kirki da Dattakon Daddy da Abba Dukkansu suna Halin kwarai suka wuni yi.

Diza Da taji labari abakin Mansur Ranar kwana Tayi kuka Gani taki kamar zata Raunana Bazata iya cika wannan alkawarin ba gefe daya kuma Tsanar Rumana ya samu wajen Zama acikin Ranta,Gefe Daya kuma Ta Fara Jin Haushin Mansur Duk wani rawan kafa Dayake mata kallonsa kawai take yi ta Daina Sakar mai Fuska Haka kurum Take kallonsa amtsayin Wanda yayi mata katanga da abum sonta ammh Shi baya Damuwa bai ma Wani Fahimci Wani Hali Take Ciki ba yana nane da ita indai yana Gida bai je wani waje ba yanzu Har wajen aikinta yake Binta Tayi ta Shan kamshi yana Biye mata Saboda Tsananin Son Daya ke mata.
Bangaran Rumana kuwa bazata Dora komai ba Domin Ko Sau Daya Mastur bai kirata ba itama Bata kirashi ba ta Dai Turamai Sakon Murna da Godiya Daya karbeta amtsayin mata Domin Daddy bai nuna Hadin Nashi bane ya Nuna Mastur din yana Ra"ayin Rumana sai Tayi Tunanin Tabbas Tunaninta ya Zama Gaskiya kan Mastur yana Sonta auran ne bai so yinsa yanzu ba sai kuma Allah ya kawo Lokaci Bata Damu Da Rashin Kulawarsa ba ita dai abu Daya ta sani She Love him So bata Bukatar komai Daga gareshi ya gama mata komai Tunda Zai aureta.

Shi kuwa Mastur Tsausayama kansa yake yana Tsausayama Rumana Zata Shiga Sahun masu   Sadaukarwan so Domin zata auri Zuciyar da batada Gurbin Wata Soyayyah sai Gurbin Kunci Damuwa da Fidda Rai Yaga Sakonta bai da tace mata kawai yasa ya kyaleta Zuwa Lokacin Dayaji Zencen zuwan su Abba sai yagama Sarewa gabadaya kan al"amarin ya Zauna yana ma kansa Fada da Cewa Rumana itace Gaskiyansa ayanzu..Diza kuma karyace Tayi mai Nisa Har Abada Tunda Zata Zama mallakin Mansur,ya Zama Dole ya Cireta aransa ya yakiceta Har Abada sai dai bashi ya Dora ma kansa ba kwana yake kuka yana Sallah yana addu"an Allah ya Ciremai Soyayyar Diza acikin Ransa ammh kuma abun kamar kara gaba yake ba wani Sauki yana neman yafi karfinsa Duk da Haka yana Faman yaki da Zuciyarsa,bayan ya Dawo sai da ya koma asibiti aka kara gwadashi aka Tabbatar da jininsa ya kara sama Likita sai Fada yake mai kan ya Rage yawan Damuwa Da Tunani Toh shi kam baisan Ta Ina Zai Raba kansa Da Tunani da Damuwa ba abunda suka Daura aure Dashi ai kuma sai abunda Allah yayi.

*****

Kamar yadda Abba ya Fada Ranar Lahadi Jirgin Safe suka Biyo Zuwa Kaduna Daddy yaje ya Taho Dasu Shida Mansur nan Falon kasa agidan Daddy aka Sauke su,Mommy ita ta Taimaka ma Mama Fadime akayi Abincin Tarban baki Diza Bata gida Tana wajen aiki Hajja ma tayi Tuwon Shimkafa Miyar agushi ta aiko Dashi RANAR Baba Habibu bai Fita aiki ba Sai yayi ma Kawu Usman kara ya Kirashi Domin ayi komai agabansa.

Alhaji Muhammad Shi da kaninsa Alhaji Hamza suka zo..Sai Baba Habibu sai kawu Usman,sai da suka ci suka sha kana suka Fara Tattauna abunda ya Tarasu Abba Dayaji Daddy yace shizai Biya Sadaki da kuma Muhallin da zasu zauna Shima sai ya Hade rai yace Duk Daddy ya kame komai saboda haka yaji shi ya Dauki Nauyin Kayan Daki Both da Diza da na Rumana,sai kuma Motocin Hawa Sabbin Yayi Guda Biyu Kowane nashi Dana Matarsa ai sai Baba Habibu ya kasa Mgana Kawu Usman ne keta Godiya Cikin Mutumci Daddy shi ya bada Sadaki Kowanne 200k mutum Daya sai kuma Baba Habibu ya Fito da da Goro da Dabino sai kwalayen Minti da Cimgam sai Katan katan din Lemuka na saka Rana sun Tsaida Ranar nan da Wata uku masu zuwa sai Daddy yayi mgana kan Aikin Rumana Abba yace bakomai zai san yadda Zai yi ta Dawo nan Cikin asibitin ABU ta karisa,sai ta Dora da Bautar kasarta Kafin atashi Taron sai da Baba Habibu ya Roka kan Kada su kara Daukan Nauyin wata Dawaniya Su bar Mansur da Mastur su hada kayan Lefe da kansu kada Dawainiyar Tayi yawa Suga kamar an basu matan akyauta ne Domin yaji Abba na Zencen kayan Lefe,Basu ja da alfarman Baba Habibu ba suka Karbeta Hannun Bibbiyu su Abba basu Juya ba sai bayan Sallar Azahar kana Mansur ya Tafi kaisu kaduna Ina Zasu Hau Jirgi su koma Sokoto.
Duka kayan Uku aka Raba Abba ya Juya da Daya Daddy suka Dauki Daya Baba Habibu Daya achan gidan ne Hajja ta Raba uku suka Dauki Kashi Daya Kawu Usman Daya,Daya kuma na Mutanan maruka ne Dangin Mansur Sadaki kuma Daddy ya Rike na Diza Shi kuma Abba Ya Bama Alhaji Hamza ya Rike a Hannunsa Lokacin da Baba Habibu ke maimaita musu Shima abun Alheri Abba sai da Hajja Ta Saki Guda da Mansur ya Dawo yaji Bakinsa yaki Rufuwa Diza na wajen aiki ya Bita Chan yana gyamata an saka musu Ranar aure nan da 3 month..Ta kasa Boye Halin Datake Ciki agabansa kawai sai ta sakamai kuka sai kuma ajikinsa yayi sanyi ya kalleta yana Fadin"Har yanzu baki sona ko..?
Yadda yayi mganarsa Taji Jikinta yayi sanyi,Da Sauri ta Girgizamai kai Mirmishi kawai yayi yana Fadin"Ko baki Fada ba nasan baki sona..Kina pretending ne saboda iyayenmu da kuma Darajan ya Mastur..Koma yaya ne Diza ki samamin Waje kadan acikin Zuciyarki Domin Ina Sonki..Son da bazan iya Rayuwa baki ba..!
Yana gama Fada mata haka ya Fita Daga office din ya barta Daman aciki ya ssmeta su Hauwa suna Daga Falon suna aiki Yana Fita ta kifa kanta Tsakanin Kafafunta Tana Rafzan kuka haka kurun Take jin wani Rauni Daga kasan Ranta kamar Bazata iya Daukan abubuwan kamar yadda Wasu ke son su Faru ba Ranar dai bata iya Tsayawa Ta kai Tsawon Lokaci ba ta jawo motar ta Zuwa Gida Mommy da ta Fahimci bata cikn Mood mai Dadi bata Bi ta kanta ba Tana Cikin Farinciki ko Su Kayan saka Ranar ta Diban ma Danginta na Sokoto akwai kaninta da zai zo zai Tafi ma iyayanta Dashi suma su Shaida duk ta Fada musu ta waya.

Ta bangaran Umma ma haka yake bakinta yaki Rufuwa da Abba suka Dawo da kayan saka Rana da Sadaki Da Rnar aure nan da wata uku sai saka albarka take da addu"an Zaman Lafiya Rumana kuwa Tamkar Mafarki Haka take ganin abun takasa gasgasta nan da wata uku Zata Zama matar Mastur abun kamar almaara Alhaji Hamza sai Washegari ya wuce Wamako Shida Abba suka Tafi ya Tafin musu da kayan Saka Ranar Duk da sun sani ammh hakan ya zama Shaida garesu.

Mastur Baba Habibu ya kirashi ya gayamai Abun alherin da Abba yayi musu Shida Mansur sai kawai ya saki komai Domin bai da ta cewa Dagashi Har Mansur auran gata Su Daddy zasu yi musu,Wannan Dalilin yasa ya kauda kunya ya Kira Abba yamai Godiya Abba yaji Dadi sai saka albarka yake suka Dade suna mgana kan Aikinsa kafin suyi Sallama Mastur na son Abba da Darajashi,Mutum ne mai ilimi da Saukin kai Ba Ruwansa Tun Lokacin yana Jami"a in Abba ya Dawo Gida da Daddare haka zai kirsa Falo suyi ta Hira Duk da Rashin son Saki Jiki na Mastur sai da ya saki Jiki da Abba Domin mutun ne da ba Ruwansa ya iya mu"amala da mutane ba a iya D"a ya Daukesa ba yana Daukansa kamar wani kaninsa ko Abokinsa,bayan sun gama waya da Abba ya Kira Umma suka gaisa sai mai Tsiya take yana Mirmishi Ba isa yace zai ki Rumana ba Domin gaba Da baya ta Fito Daga Tsatson Tarbiya Umma da Abba Har Abada bazai manta karamcinsu ba Har ya gama Degree dinsa a Sokoto bai Taba Neman wani abu ya rasa ba Umma ta Daukeshi kamar kaninta ta kula DashiTamkar yana gaban Hajja Shiyasa yake jin wani Tsausayi Daga kasan Ransu Watarana ya Zasu ji bayan Auran in yarsu ta Gayamusu baya sonta..! ? Ya Tabbata Hakan bazaimusu Dadi ba ammh kuma Bashi da Mafita Bashi ya Sa Zuciyarsa ta zama ba Tashi ba wannan kuma kudirin Allah ne.

Mansur da kansu yaje Maruka yakai ma su Baba sule kayan saka Ranar chan ya kwana ma sai Washegari ya Dawo Kannensa suna ta Murna,Sakina Tana Gidan mijinta Maryama ma ta koma makaranta  Sauran kannensa ma Yasaka su a makaranta harda mardiya Rayuwar Gidansu ta Inganta Ya Taimaka ma Mahaifinsu ya Taimaka Yan"uwansa bashi kadai ba Hatta Mastur wani abun Alherin sai yazo Baba Sule zai ce mai Mastur ya Turo musu kaza ya Turo musu kaza,Shuru kawai yake sanin Halin Dan"uwan nashi Domin da Taimakonsa ya gyara Mu"amalansa da Yan"uwansa da Mahaifinsa shi ya Biya Ririwai yakai ma Inna karime Bushara Dataji An sakama Mastur Ranar aure Harda kuka nan Inna Karimen ke Fadamai wai ita nan Jiran Mastur din Take Mansur Dariya ta kamashi Yana Hanyan Dawowa yana Dariya Bisa Hanya Tun ahanyan ya Kira Mastur ya Labartamai Shina Abun sai da ya sakashi Nishadi Diza kuma Tun Ranar basu kara mgana ba ta Dai Turomin Sakon SORRY sai kawai yayi Mirmishi ya kyaleta yasaka aransa ko Diza bata sonshi Haka zai yi Hakuri da ita ya Aureta Domin shidai yana Sonta In bata Cikin Rayuwarsa bazai iya Rayuwa ba.
Yana komawa gida ya Labartama su Hajja Ayya nata Dariya Hajja dai bata ce komai ba Baba Habibu kuwa kai kawai ya Jinjina aransa yana Fadin kuruciya ce kawai
Diza Dataga mansur ya Dauke mata Kafa da kanta Tayi Bikonsa Domin Mastur ya Kirata yayi mata Godiya Bisa Cika alkawari da kuma alfarman Da tayi mai na auran Dan"uwansa Mansur ya Gode Har Abada bazai manta da karamincinta Da wannan Dalilin ta Fahimci Har Abada abunda take so yayi mata Nisa Gwara ta Rumgumi Mansur Shine Kadddaranta.

Rumana ta Fara Damuwa ganin Tunda aka saka Ranar auransu Mastur bai taba kiranta ba ko Sau Daya ba sai dai taji Umma ko Abba suna Fadin sun yi mgana Tun Tana Danne Abun har ya Fara Damunta ta rasa wa zata Fadamawa Taji Dadi,ammh Sai take mai Uzuri Saboda yanayin aikinsa Tayi kokarin Ta Kirashi sai kawai ta kyaleshi Tana so Ta Fahinci ya Damu da ita ko a"a abunda bata sani ba Mastur ba ta ita yake yi ba yanzu aikinsa kadai ya saka ma Gaba ba Dare ba Rana sai yakai 10pm a office kuma 7am yake Fitowa Barci Ragagge yake yi ya Lura maida kai ga aikinsa shi zai Ragemai Tunani ya Tashi Daga Miskili ya koma Uban Miskili Domin yanzu mgana ma Tafi mai Wahala Fiye da Baya Sai ya kwana Biyu bai Tuna da ita ba balle Zencen auransa Diza ce kadai bata Taba Gushewa aransa ko na Sakwan Daya ba Mastur yasha Rayawa a aransa ya siya Giya ya Farasha Indai Zata Dauke mai Tunanin Diza sai kuma ya kasa Tuna Irin Tarbiyan Baba Habibu da Hajja Garesa sai yake ta addu"a kawai ya maida ma Allah Lamarinsa.

Mus"ab kuwa yasha Takaichi da Mansur ke Fadamai Zencen Auransa da Diza da mganar Runana da Mastur domin Alhajinsu ma bai gayamai ba yaji Takaichin biye ma Rumana Da yayi bai gayama mahaifinsa ba Daga baya sai ya barma Allah komai Yayi Tunanin Dama ba Matarsa bace Suka cigaba da Shirye Shirye da Mansur Domin sun Zama Abokan juna Tun Haduwarsu a Lagos.

Mansur Zumudi har ya Fara mganar kayan Lefe Hajja yayi ma mganar sai tace basai sun Wahala ba Mommy nan Harkantan ce yar kasuwa ce su Bata kudi zata Hada musu kaya na gani na Fada Baba Habibu ma Dayaji yayi Na"am da mganar jin haka yasa Mansur ya Kira Mastur ya Tuntubeshi shi kuma yace ma Mtsala in sunyi mgana da Mommy ko nawa tace yamai mgana sai ya Turo mata Mansur kafin yayi mgana da Mommy sai da yayi mgana da Diza kan kayan Lefen Tace Tabbas Mommy tasan kan kaya Sosai,ba musu yaje da kansa yayi mata mgana Tana Murna Wai Zata Hadama ya"yanta kayan aure Tace Kowannsu ya bada miliyan Daya da Rabi ita Zata ji da Sauran itama amtsayinta na uwa Zata bada nata Gudummuwar,Mansur ya kira Mastur ya gayamai Daya Tashi Turowa sai ya Turo 4million nashi Dana Mansur,Mansur kamar ya suma saboda murna yaje Falon Hajja yana ta rawa yana kwaso Shoki wai ya zama Dan gata auransa Diza komai yimai akayi Kowa sai da yaji Labari yana ta saka ma Mastur albarka ashe bayan nan ya Kira Mommy ya Tura mata 100k yace ta Siya ma Ayya kaya da Hajja da Inna karime sai Shaddodi na Abba Dana Baba Habibu sai Daddy sai Ita da Umma yace in ya samu albashi Watansa zai ciko mata kudin Ta barshi kawai kowa yaji wannan abun Alkairin sai saka albarka yake,Shi kuma Mansur Dayaji haka sai ya bada wasu kudi a Siyoma kannensa, kaya da Mahaifinsa sai Inna Zainaba,Sai kawu Usman da Balaraba Saboda yi ma Baba Habibu kara.

Mommy ta san Size din komai na Diza na Rumana ne bata sani ba sai ta kira Umma sukayi mgana Umma tace ai yarta ce ta Kirata suyi mgana Mommy ta kira Rumana tace ta Turomata Size din Dogayen Rigunanta da bra da pant da Takalma Rumana Taji abun kamar Daga sama Tana ta mamaki bata dai yi mgana ba sai ta Tura sai Daga baya Umma ke Fadamata Lefensu ne su Mastur suka bama Umma kudi Zata Hada musu Rumana Tayi ta mamakin Mastur an kai ga Hada lefe ammh ango bai taba Kiranta ba Ranar ta Kauda kunya ta Kirashi Har sau Biyu bai Daga ba Sai Waahegari Tana Wajen aiki ya Kirata kamar bazata Dauka ba sai ta Daga bayan sun gaisa da Tambayan aiki da Mutanen gida,kamar yasan Tunaninta sai ya bata Hakuri kan yanayin aikinsa na karancin Lokaci Tana Sonsa sai ta karbi Uzurinsa kafin ya yanke kiran take Tambayansa yaushe zai zo..?
Abun sai ya bashi Dariya ma kawai Ita yanzu in akace mata zai zo sai ta yarda..? Cikin Dakiya yace"Kina so nazo ne..?
Kamar yana kallonta ta gyada kai Tana Fadin"Eh mana..Ina son na ganka..Na Dade bamu Hadu ba.."
Mastur yace"Uhmm Zaki ganni Soon..Mu da zamu zama Miji da mata..Ba zan yi miki alkawari ba nazo nayi Failing dinki ba..Kinsan Allah ba Lalle bane naje Zaria kafin Bikin ne sai Lokacin Komai dai ake ciki u can Tok on phone.."Rumana bata da tacewa sai Fatan Alheri kawai Daganan suka yanke kiran Ta Dade ta auna wasu abubuwa ganin bamai Tallafamata ta Fahinci wani abun Dole ta watsar da komai ta Cigaba da aikin gabanta.

*********

*Bayan Wata Biyu..*

Lokaci yana ta Tafiya Cikin Nasara da Tsarawan Allah Biki kuma yana ta gabatowa Kuma Shiryen Shiryrn nata Tafiya yadda ya kamata kamar Barayin Mansur shi dai yana ta Shirinsa Mastur kuma sai abunda Mansur ya kirashi ya gayamai Sukan yi waya da Rumana itama sai in ta Kiraahi Tagaji da Korafi Ta Hakura Domin Ta Fahinci Haka Halinsa yake...
Bangaram kayan lefe Mommy Ta gama Hada komai akwatuna Kowanne 7,Both Diza da Rumana Cike da kayan alfarma masu Tsada kayan kuma da Mastur yace a siya an siya komai har an bama kowa nashi yana ta saka albarka Mansur ma ya aika ma su Baba sule nasu suna ta saka albarka nasu Hajja kuma Diza yasa takai Musu Dinki inda suke kai nasu Mommy Duk iri Daya ta Dauko musu Atamfar Domin suyi anko Hakama Daddy da Abba da Baba Habibu Shaddodin iri Daya ne suma Domin suyi anko Ranar Daurin auran.

Mansur kuma bai jira Mastur ba yaSiya Shadda kala uku Da Yadi kala Daya ya Bada Dinki nashi Dana Mastur Tunda Shi ko Zuwa ma bai yi ba kullun Excuse kan aikinsa,Bangaram kaya kuwa Mommy na gama Hadawa ta kawo nan Wajen Hajja ta Zube su Baba Habibu kuma yace iyayan Mansur Zasu zo su gani kafin ashirya kai na Rumana Chan Sokoto in an Dawo sai akai na Diza Tunda ita Gida ne haka kuwa akayi Inna Zainaba da Matan yayyin Baba Sule sun zo sun kwama sunga kaya suna ta saka albarka da Zasu koma Baba Habibu yayi musu na Komawa sukace sai Lokacin Sha"anin zasu Dawo Kai kayan Rumana kuwa Inna karime sai Balaraba sai Mommy Sai Mansur Dake Namiji aka Tsara Tafiyan Ajirgi Zasu Tafi Mastur yana Daga Chan shi dai i an Kirashi mganarsa Eh kawai bayacewa komai kan Al"amarin.
Ana Bikin Saura Sati uku suka Tafi Sokoto suka Hadu da Dangin Abba dana Umma yan Wamako sun zo Taransu Dayake abun Duk Gida ne sun ga karba da karramawa nan suka kwana sai Washegari suka Daawo Zaria Ranar da suka Dawo Da Daddare su Ayya da Inna Balaraban da karime suka kwashi na Diza suka maida su Wajen Mommy Tunda Daman su suka Hada Daman Chan Sokoti sun je da 50k kudin Dinki Diza kuma Daman sun gama mgana da Mansur Washegari Tun Safe suka kwaahi kayan suka Tafi kai Dinki Shi ya Biya komai da komai .

Sai Shirya Shirya kawai ke gudana A tsaida za"a Dauran Dukkansu agarin Iyayansu ne Za"a fara Daura auran Mastur da Rumana a Wamako sai a Wuce Tureta a Daura na Diza da Mansur Daganan sai a Dauki Amarya Rumana su yada Zango Zaria gidan da Daddy ya basu a Hanwa Loswost ne Tuni Ya gama Biyan kamfanin Marhaba sun zo sun Tsarama kowacce Flat dinsu,Su mommy da Umma kawai bangaran labulai da Zannuwan gado sai kayan kitchen zasu ji dasu,Flat ne manya Guda Biyu Suna kallon Juna masu Dauke da manya Falo Guda Biyu sai 3 bedroom each yana Dauke da Tiolet,sai Kitchen,Haraban gidan kuma Kato ne wanda Zai Dauki akallah Motoci Fin Goma zasu Faka wasu basu matsu Juna ba Mommy da Hajja da Ayya da Baralaba sunje sunga Gidan suka Dawo suna saka albarka Diza ma Mansur ya kaita Ta gani Tafi Tsayawa kyan Tana ganin Shashen Mastur da Runana Tana auna Taya Zata iya wannan Sadaukarwan Zasu Zauna Gida  Daya da Mastur da Rumana Kamar Rauninta zai iya Bayyana.

Mganar katin Aure kuwa da abokan Mansur yan Siyasa sukayi mai na waya dana Kati Shida Mastur Daman komai Zai yi Biyu yake yinshi,Bangaram Daddy ma ya Buga nashi ya Bama Baba Habibu Shima yayi taRabo a kasuwa Wajen abokan Kasuwancinsa Su Hajja ma suna ta aikawa makota chan Sokoto kuwa Mansur ya aika ma da Rumana nata Mastur bai ma Sani ba Sai da Rumanan Take gayamai Chan ma Abba yayi nashi katin gayyatan suna ta Rabawa yan"uwa da abokan arziki Rumana bata da wasu kawaye yan asibitinsu kadai ta Rabawa sai Basma Data aikama ta Waya Tace Zata Shigo Satin Bikin in Allah ya yarda Mganar Intenship dinta kuma Abba ya Shiga ya fita An yi mata Transfer zuwa ABU zaria,Takarda Kadai zata karba wanda Zata je chan ta Nuna mganar abubuwan Datake abukata kuma Ita tayi ma Mastur mgana Domin ta Lura in Tayi Shuru Lokacin Bikin zai ZO batayi komai yace ta Lissafa abunda take abukata tamai Text zai Turo mata Kudin Bta ma kai ga Fadamai ba ya Turomata 200k yace in bai isa ba tamai mgana tace sun isa dasu ta Fara Shirinta Daman Tuni kanwar Ummanta Saratu Daga Wamako Tazo Tana mata gyaran Amarci Diza ma achan Zaria itama kanwar Mommy Hadiza sunansu Daya tazo Taje chan da kayanyyaki Tana gyarata,Ita gayyatan ta Duk ta waya tayi sai Lokacin ma"aikatanta suka san Zatayi aure kowa yaji mansur Zata aura sai yace Daman Za"a Rina mganar su Snak da Za"ayi amfani Dasu duk Nan Mommy tace ta saka ayi komai game da kayan abinci kuma Baba Habibu ya Jigke komai na gidansa Dana Gidan Daddy babu abunda Zasu nema su Rasa Bangaran kayan Sha na Ruwa yan Siyasa abokan Mansur suka kawo su Mota Mota aka Sauke nan Gidan da Daddy da gidan Baba Habibu mganar auransu Tana Sauran Sati Daya Tagama yada Zaria da kaduna ta kewayanta Balle mansur Dan Siyasa kowani Gidan Radion sai kaji Sanawarwan Auran Honourable Mansur Sulaiman Doguwa da Amaryansa Khadijat Sunusi Tureta(Diza) sai Dcp Mastur Habib Doguwa da Amaryansa Dr.Rumana Muhammad wamako Kowa yaji wannan Sanarwan yasan abun na manya ne kuma Daurin aura a ajirgi Wasu zasu Tafi Wasu kuma Tafiyan Mota ne Ba Laifi abokkan Mansur sun mai kara Soasai Ga Sagir agefensa ga Mus"ab da zai Diro shima ayi komai Dashi Diza Dai basa Haduwa sai dai mgana ta Waya Walima kadai Zasu yi Sai Kayattacen Dinner da Yan partyn din su Mansur suka Shirya musu Shi da Dan"wansa asabar da Daddare Dayake Daurin Auran Ranar Jumma" ne Mastur kuwa Daga barayinshi bai Shirya komai ba gwara ma Rumana ta Shirya Walima da Sister Evening,Duka Tsarin na Mansur ne dasu Daddy Daga chan ma shi ba wani gayyay yayi ba Daga wadanda ke kasansa sai wadanda ke samansa ya gayyata Da sukayi Mganar Bikin da zasu Shiryamai nasu na yan Sanda sai yace matar ba da ita zai zo ba Chan Zaria ne ganin baya Ra"ayi Dole suka kyaleshi.
Gidaje Tun ana Saura kwana Hudu Biyar suka Fara cika yan Maruka duk sunxo Kannen Mansur su Sakina da Maryama da mardiya da mariya da Inna zainaba Inna karime da Bushara suka Dawo,makotansu da suka zauna aririwai ma duk sunzo Umma kuwa Danginta yan Sokoto Cike da gida da Dangin Daddy yan Tureta Chan Sokoto ma Hakan take yan wamako sun cika Gidan sai Harkan arziki akeyi Rana Daya Diza da Rumana sukayi walimarsu Ranar Laraba bayan kowacce tasha Lallinta da Gyaran kai da Jiki Diza ba wata kawa agefenta sai Diyar Anty Hadiza Meena Tasha makeup masu abu da abunsu Wajen kuwa Diza Catering ne suka zo suka Raba Snaka abun Yayi Taaari sosai,Rumana kuwa Basma na gefenta itace babar kawarta Mansur kuma Ga Sagir ga Mus"ab sune sa"aninsa Aranar Mus"ab ya Shigo suna Shashensu Tunda shashensu Hajja dai ya Cika da mata Washegari Alhamis Diza Tayi Bridal Shower anan Haraban Gidansu Sai Kuma Rumana sukayi Sister Evening Akuma Ranar ne Mastur ya iso da Daddare ya Jigata Domin Tafiyan Mota yayi bai Shiga Jirgi ba Wajen bayan Sallar Isha"i ya iso.


*Ki biya ki karanta cikin Salama Domin mace mai aji bata jiran Abun Sata sai dai ta mallaki nata 09069067488*




*Janafty...*
1/1/22, 18:54 - Maryam Badmsi: *SS...20*

*Bazan ce Allah ya isa Ko ban yafe ba,ga duk wanda ya karantamin Labari bai biya ba..Sai dai ya sani Akwai Nauyi da Hakkin Daya Dibar ma kansa nawa dana Mutanen da suka saka Kudinsu suka siya kuma Allah (Swa)Baya yafe Laifin wani da wani..Ki Biya ki karanta Cikin Salama Mace mai aji mallakan komai nata take yi batajiran Abun Sata 09069067488*


"Allah yasa ma tare da Sargent Inuwa yazo shi ya tukoshi Shiyasa bai galabaita sosai ba ammh duk wanda ya san Mastur ya gansa yanzu sai ya Janjanta Ramarsa Duk ya Lalace yayi baki kamar bashi ba ya kara Zama wani mara karkashi da kuzari kamar ba Namijin Duniya Mastur Habib Doguwa ba.

Sai da yayi wanka a Shashensu aka samar ma Sargent Inuwa Wajen kwana kana ya shiga Shashensu su Hajja ya gaisa da baki Suna ta Zolayansa da ango Hajja Kallo Daya tayi mai ta Fahimci ya kara ramewa Fiye da Zuwansa na baya,Ammh Saboda Mutane bata samu Damar mai mgana ba,Mansur ma sai da yayi mai mgana yana Taba wuyansa yana Fadin Yaya ka Rame Mansur din ne bai bama mganar Muhimmanci ba Yana ganin Mansur da abokansa Mus"ab da Sagir ammh Shi aboki ko daya bai dashi Daman amininsa Daya ne Kaninsa kuma Dan"uwansa Mansur bai yarda ya saki Jiki da kowa ba sai shi,ayanzu hakama Aboki Daya gareshi Shima Dan Sanda ne kamarsa Wato Acp Saleem kabir kumo Mijin Malika maleek Tare sukayi StaffCollage jos duk alokaci Daya aka Rarraba su wajen ayukkansu suna waya sosai Duk da Ba domin Salem din ba da Zumuncinsu bai kai haka ba Yanzu haka Zashi Daurin auran ammh Zasu hadu ne a sokoto.

Adaran suka samu Labarin an Maida Daurin auran Ranar asabar Saboda ba Lokaci ga Nisa kuma an fasa Tafiyar Jirgi sai Mota sai aka Dagashi Zuwa ranar asabar saboda a samu Ishashen Lokaci,Mastur bai da wani Shiri sai Shirin Mansur Shiyasa yana jinsa ne kawai yana Koramai jawabi ba Domin yayi mai Dinkunan Fitan angonci ba Da haka zai ci Bikin Domin bai Taba kawo Tunanin Dinka wani Sabon kaya saboda Bikin ba Tunda Baya gabansa Gabadaya ma Zullumi Tunani yake Taya zai Fara Rayuwa da Rumana wacce bai Taba Tsara Rayuwa da ita ba,Taya zai zauna Gida Daya da Mansur da Diza Wacce yake so aduk Duniya anya Zai iya..? Wannan Sadaukarwan bazata Raunana ba..? Tunani da Damuwa sun gama Shiga Jikinsa ya rasa Sukuni Haka ya Taho ba Domin ya samu Cikakken Natsuwa ba ko Madafa ba.

Washegari Jumma"a tun safe masu Tafiya Daurin Aure suka Shirya,Daddy da Baba Habibu sai Kawu Usman da wasu Makota,Sai Mansur da Sagir da Mus"ab sai Mastur da Sargent Inuwa wanda ke Tuka Motar Mastur din da Daddy ke Ciki da Baba Habibu da kawu Usman,Motar mansur kuma shi da Tawagarsa Sauran abokan nashi Duk achan Sokoto zasu Hadu dasu Harda Mutanen Maruka Su Baba Sule suma Duka achan Zasu Hadu.
Sai da sukayi sallar Jumma"a suka Dauki Hanya wajen 6pm suna garin Sokoto ko kafin suje Abba Duk ya kama musu Dakuna a Hotel,kusan Tare suka iso da su Baba sule da yayyinsa Sai Mijin Kanwar Mansur Sakina,Duka Hotel Daya Abba ya kama musu Suka zauna Saboda Chan Gidan ya Cika da Baki mata ana ta Hidima.
Saboda gajiyan da suka kwaso basu samu Fita ko"ina ba ko Mastur da Rumana ta Dameshi da kiran yazo bai Samu Fita ba agajiya yake ga Ciwon kai ga Damuwa wai yazo ya gaisa da kawayenta jinta kawai yake Wani Lokacin kuma Tsausayi tske bashi Domin Zata auri Zuciyar Data Riga ta yanke kauna Zuciyar Data Riga Ta gama Sadaukar da komai bata da komai atare da ita.

Washegari asabar Tun safe kowa ya gama Shiryawa Mansur da Mastur Shigansu iri Daya ne Shadda Fara Riga da wando da Babban Riga wacce akayi ma bakin aiki sai sukayi anfani da bakin agogo da Takalmi Sawu ciki baki da Hula baka Duka kuma Mansur ne ya Tanadar musu sai gashi sun Fito kamar basu ba Daman Tun Jiya a Zaria Mansur ya matsa sai da Mastur din ya Bisa sukaje sukayi gyaran kai aka Rage musu gashi aka gyara musu Sajensu,Mansur bakinsa yaki Rufuwa Sabanin Mastur da kadahan kadahan bamai gane Wani yanayi yake ciki Ba wanda ya Damu sanin Daman Shi din mai karancin Fara"a ne

Kafin su wuce Wamako sai da suka jira Tawagan Abokan Siyasan Mansur Mota wajen Goma Harda Motar parytn su Cike da matasa Shima Mastur akwai abokan aikinsa da suka zo..Acp Saleem kabir kumo ya cika alkawari yazo Shima yasha Farar Shadda kamar shine angon, Hakama Abokan kasuwancin su Abba da Daddy Dake nan Sokoto Baba Habibu kuma Tuni yabama abokan sa na Zaria Hakuri musamman yan kasuwansu Saboda Dawainiya ga Nisa Tare suka Rankaya duka gwanon Motocin suka Tafi Daurin Auran Wamako suka Fara Zuwa karfe 11am na safe aka Daura auran Mastur Habib Doguwa da Amaryarsa Rumana Mahammad Wamako kan Sadaki mai Daraja akofar agidan kakaninta wato Family House din gidansu Abba kenan Alhaji Hamza ya bada Auran Rumana Daddy ya karban masa,Daganan bayan gaisuwa da addu"an Zaman Lafiya basu wani bata Lokaci ba suka Dauki Hanyar Tureta Kowa kagani Cikin Farimciki ammh banda Mastur wanda Tunda aka Tabbatar dashi a matsayin Mijin Rumana yaji komai ya tsayamai bai kara wani motsin Kirki ba,Duk da kowa ya Lura da hakan ammh ba wanda ya Damu Sanin Halin Mastur din Mansur kuma basa ma Mota Daya yana chan Tare dasu Mus"ab bazai iya sanin wani Hali yake Ciki ba Suna Motar Saleem Kabir kumo ne shi kuma yasan yanayin Abokin nashi bai Matsamai da Mgana ba Duk da bai Taba Mganar auransa Dashi ba ammh ya Fahinci Wani abu Shiyasa ya Dafa Kafadarsa yana Fadin"Easy DCP..koma miye ka Daukeshi da Sauki..Watarana Zaakaji Dadim haka har ka kara Godema Allah..!

Yafada yana kafe Mastur da ido Wanda ya saki ajiyar rai kafin yace"Meyasa kace haka..!? Saleem yace"Saboda ya Faru akaina..Lokacin dana auri Matata Malika Daukan Fansa ne Burina Daga karshe meya Faru..? Komai ya kwabe Dani Malika ta zama apple of my eyes..Uwar ya"yana Sanyin Idanuwan Dangina dani kaina Gabadaya.."Mastur ya jinjina kai yana Fadin"Hakane..Allah yasa mu dace.."Saleem yace"Ameen Ameen..!.
Daganan Shuru ya Biyo baya ba wanda ya kara mgana Shi Mastur aransa Fadi yake Gwara kai Saleem Zuciyarka bata Mutu ba Ni kuwa fa..? Tamkar wani matattace ne mara wani amfani Sai Godiyar Allah da haka suka isa Tureta shima ba wani bata Lokaci 1pm na rana aka Daura auran Honourale Mansur Sulaiman Doguwa Da Matarsa Khadija Sunusi Tureta kan Sadaki Mafi Daraja itama nan Kofar Gidan iyayan Daddy aka Daura auran Duk basu agidan Duniya Babban Gida ne akwai Sauran yan"uwa da aboksn arziki aciki Daddy yayi ma Baba Habibu kara kamar yadda yayi mai Shi ya bada Auran Diza Shi kuma Abba ya karban ma Mansur,wanda Tabbatuwar Daurin Auran ya Saka mansur kamar ya sha Ruwa akasa Saboda Farinciki Sabanin Mastur Dayaji Tamkar al"amara ko mafarki Yana jin kamar Sanyi na Shiga Jikinsa kamar bazai iya Tsayuwa da Kafafunsa ba Shikenan ta Faru ta kare Diza Tayi mai Nisa nisa kuwa na Har Abadan Abadina da zai iya kuka da yayi Ammh kuma Zuciyarsa ta Bushe haka Mansur yazo ya Rumgumesa yana Murna Shima ya Rikeshi  yayi yana Yake sunyi Hotuna sosai kuma anan sukayi Reception Daddy ya saka anyi Tsire da Gashasshen Nama sai Lemukan da suka zo Dashi Tun Daga Sokoto,basu baro garin ba sai da   3Pm na rana Daman Tun suna chan Abba ya kira Umma yace a Shirya Rumana suna zuwa Zasu wuce da ita saboda Dare da Farko ma har Abba yace abari Zuwa Gobe Ta biyo Jirgi ita da yan Rakiyanta ammh Mansur yace A"a saboda Dinner da aka Hada musu in bata abun zai Rage amarshi.

Duk Saurinsu da Hanzarinsu sai da suka kai la"asar Domin Shiryawa da yan Nasihu da suka Biyo baya Rumana tasha kuka Rabuwa da iyayanta da gida gabadaya haka ta Rumgume Umma Tana Sharban kuka Hakama Abba,Sun mata Nasihu Sossi tun kafin Ranar Mutanen da suka Tafi Daga Rumana sai kawarta Basma sai Anty Saratu sai Wata Hajiya Baraka Kanwar Alhaji muhammad ne Daga wamako,sai Wata yayarsu Umma Mama Adama su kadai suka Tafi kai  Rumana Amotar Mastur aka Daukesu yayin da Sargent Inuwa ya Tukasu,Rumana bata saka Mastur i donta ba sai lokacin da aka Fito Da ita Tana cikin Mayafi ne ta hange sa Lokacin Daya shigo Cikin Gidan su gaisawa da Baki tana Sama afalon Umma koda aka Fito Da ita sun Fita Haraban gidan.
Duka Tare suka Dumguma suka bi Hanya bayan sunyi Sallama Dasu Abba Tawaga guda Haka suka kara Daukan Hanyan Komawa Zaria a manyan Motoci Gudu suke sosai Saboda karfe 8pm na Dare za'a Fara Dinner din kuma gashi Sokoto ba kusa ba,Mastur yana Motar Acp Saleem ne ya maida kansa ya jingina jikin kujeran Mota ya lumshe ido Motarsu na Sawun baya ne nasu Mansur Tuni sun yi gaba,Baba Habibu ne ya kira Wayar Mastur yace ya kira su Mansur don Allah yace su Rage Gudu Shi mastur din baya Fahintar komai Motar Amarya Tana gabansu ne Abba sai da ya Rokesu banda gudu Bisa Titi Shiyasa Sargent inuwa yake bi a Hankali Saboda kada yayi wani Ganganci Yallabai ya batamai rai,Mastur ya kira Mansur yace su Rage gudu ya fara mai complain din cewa zasu yi Dare a Hanya ga Dinner Kada suyi african Time,Sai waya ma ake mai Ana Tambayansa ko suna ina Domin komai ya kamallah su kadai ake jira,Mastur bai Damu kansa ba yana Fama da kansa sai kawai ya kashe wayarsa.

Achan Zaria kuwa Diza Da Farko Ta saki Jikinta Tasha gayunta Taci makeup kamar Zata gasan Tauraruwar kyawawar Duniya gabadaya,Sai dai Ta Lalata komai ne Lokacin Da Daddy ya kira Mommy yace an Daura auranta da Mansur,Ta Fara kuka duk ta bata kwalliyanta kowa ya Dauka kukan Rabuwa da gida ne Dangin mamanta sai Bata baki suke suna Fadin Ta daina kuka ai Batayi nisa ba,in tana son ganin iyayenta Zata gansu nan kuwa basu san kukan Rauni ne da Rasa Abunda kake so ne,Tana jin wani nauyi a kasan Ranta na Wannan Sadaukarwan Ta auri Mansur Ba domin tana sonsa ba sai Domin Daddy da Mastur Ta kara jin kunar Zuciya Dataji sai da aka Fara Daura auran Mastur da Rumana Haka tayi ta kuka gwanin ban Tsausayi Meena ce ke kusa da ita Tana bata baki sai chan da yammah ta Daina kuka,Aka sake mata Kwalliya ta Sauya kaya sai dai idanuwanta duk sun Kumbura saboda kuka.

Achan Gidan Hajja kuwa sai Shiryan Shiryan Taran Amarya akeyi Rumana,Daman wasu Daga Sokoton sun Taho Tun Safe matan kannen Umma ne suka zo da Sauran kaya,suna chan Gidan suna kara gyare gyare Bangaran Diza daman Tun Jiya su Anty Hadiza suka gama komai,Diza Hankalinta ya tashi ganin Har pass 8 basu iso ba ita Har an yi mata makeup dinta Ta saka Kayan da Mansur ya Tanadar mata saboda Dinner din Wani Ubansu less ne Fari mai Ratsin golding,sai Head dinta goldem sai Takalminta Halfcover mai Tsini Shima Golden sai Karamar Pos dinta itama Golden yana ta kyalli,Dinki Riga da Zani ne Ciki da alaku kayan ya amshi Jikin Diza ga Hauwa ta Tsara mata kwalliya kamar Wata Sarauniya suma Sauran kawayenta duk sun Shirya da nasu less din Golden Colour,Ssi kiran Wayar Mansur take taki Shiga ta kira na Daddy ma bata Zuwa Sai Tayi Tunanin ta Kira na Mastur Shi kuma ta kira ta Shiga ammh bai Daga ba,Sai Hankalinta ya Tashi Ta Fito Daga Bedroom din mommy Hankalinta tashe Domin anan Ta zauna akayi mata kwalliya Tana neman Momny sai a falon kasa Ta ganta Cikin Tashin Hankali take gayamata Mommy ta Lallasheta tace sunyi mgana Da Daddy yace suna Hanya Insha Allahu nan da 9 zasu iso sai Lokacin Hankalinta ya kwanta,kowani Bugawar Minti da Fargaba aranta Ikon Allah kuwa 9pm nayi Daidai Motocin su na parking a Kofar gida Tuni Labari yakai kunnin Gidajen Duka Biyu,Mommy da kanta ta Fito Tarban Rumana ita da Inna karime da Inna Balaraba sai Maryama da Sakina da mariya kannen Mansur,Rumana Na rike da Hannun Anty Saratu gam aka Fito da ita Daga Mota,Daganan sai Gidan su Mastur a Falon Hajja akayi musu masauki Mastur kuwa da Tawagansu Mansur Shashen su suka wuce Ba Zencen Hutu sai kawai Zencen Shiryawa Zuwa Wajen Dinner Baba Habibu dasu Baba Sule Gidan Daddy suka yi musu masauki a Shashen BQ,Mansur ya Kira Sakina kanwarsa ya bata kayan da Rumana zata saka yace zai kira Diza yanzu Zai kirata za"a zo ayi ma Rumana kwalliya suyi Sauri ba Lokaci,lokacin da Mansur ya kira Diza yana gayamata sai tace sai dai Rumanan tazo nan Gidan ta Shirya saboda kaucema Jama"a Dole ya kira Sakina ya gayamasu ita da Mommy suka tafi da Rumana da Basma Zuwa Gidan su Diza suka bar su Anty Saratu nan Gidan su Hajja Har Falon Sama na Mommy aka kaita sai Lokacin suka Hadu da Diza Sama sama suka gaisa Rumana ta Mata Fara"a Duk da itama Idanuwanta sun kole saboda kuka ammh ta sakarma Dizan Sabanin ita da ta amsa mata sama sama Umarni kawai ta bama Hauwa Tayi mata makeup din da Sauri ita Basma Lokaci na Tafiya Daganan ta koma Bedroom din Mommy Cikin Lokaci kankami sai ga Rumana ta Fito Tas da ita Ciki Ta shiga taSauya kaya ta saka komai iri Daya Dana Diza wacce ganin haka abun ya bakanta mata rai Taso ta kira Mansur ta sauke Haushin akansa sai ta kirashi bai Daga ba.
Bada wasu jama"a Zasu Tafi ba Daga Rumana sai kawarta Basma Sai Diza da kawarta Meena sai wasu kawayenta su Biyu Rumana Duka kawayenta Suna chan Sokoto Taron Biki Kadai suka Zo mata Basma ce kadai Kawarta sosai Shiyasa ta biyota Har Zaria.

Bangaran Mansur kuwa Tuni ya gama Shiryawa Cikin Dakakkiyar Shadda gezner mai Ruwan Brown,Aikin jikinsta Golden hakama Takalminsa da Hulansa da agogon Hannunsa komai Brown ne,Mansur ma irin Shigarsa kenan Dakyar ma aka samu ya Shirya Cikin Irin Shigar Mansur sai dai kayan ya gama Daukansa sosai Ramarsa da Duhun da yayi,Acp Saleem ne kan gaba yana Tursasa yin wasu abubuwa gajiya ce ajikinsa,yaso ya kwanta kansa na matukar saramai ammh Mansur   da Saleem sunki barinsa,duk saurinsu da Kada ayi Dare sai da suka kai goma kana aka kawo Motoci Domin Daukan Amare da kawayensu da angwaye,Amare dai a Mota Daya zasu shiga da angwayensu Motar Mastur Sargent Inuwa ya Tukasu Rumana Da mastur da Diza da Mansur sai gashi ana kallon kallon Diza Tana kallon Mastur wani kolilin abu na Taso mata Tana kokarin Dannewa yayinda Mansur ke kallonta Kamar ya lasheta Mastur kuwa kallo Daya yayi ma Daga Dizan Har Rumanan bai kara ba yayi Saurin kauda kansa yana Kokarin Rinjayan zuciyarsa Daga Bekem Matar kaninsa ita kuwa Rumana kallon Manstur kawai take Tana Godema Allah da tafi kowacce mace sa"a.

A Dove event Center,Dake kwangila aka Shirya Dinner din Tuni Motarsu Tayi gaba Sauran Motoacin suka Biyo baya wasu abokan su Mansur din duk suna Chan su Mus"ab ne suka Taho Dasu Basma da Sauran Mutane Saboda Dare yayi suna zuwa ba bata Lokaci suka Shiga Mansur ya Rike Hannun Diza da zasu shiga ammh Mastur ki yayi da Suka matsamai yace zai koma mota Dole suka barsa suka jera batare da sun rike Hannuwan juna ba Wajen ya Hadu soai Wajen Zamansu Daya ne Kowa da kujeran sa saboda ba Lokaci gabatarwa kawai Mc yayi aka Fara Gabatar da Tarihin Mastur wanda Saleem kumo ya bada,Sai Rumana wacce Basma ta bada Mansur kuma Sagir ya bada nashi Diza kuna Meena Daganan aka ci abinci sai aka Saka Kida akace Amare da angwayen su Fito Diza dai da Mansur suka Fito ammh Mastur yace baya Rawa ganin suna Lallabasa Dole suka kyaleshi Anyi Ruwan kudi da Diki Sosai yan Siyasa da yan jam"iyar su Mansur sun yi Halin Girma bayan nan Sun yanka Cake Mansur dai shi yake Tafiyar da komai Diza kuma Bata da yadda Zatayi Rumana kuwa Tun awajen Dinner ta Fara Sarewa na ganin nata angon kwatakwata baya mata Rawan Jiki Cake ma bai yanka ba yace bashi da Lafiya kuma gasiiya kansa kamar Zai Tsage 11:30pm Daddy ya kira yace su Dawo gida Za"a mika Amare Dakunansu Daman Mastur ya gaji da Zama su suka Fara yin gaba Shi da Saleem Sai dai aka Nemeshi aka rasa Rumana ma Mansur da Diza suka Dawo da ita Dole dai kanwar Naki Dare yayi akace abari sai Gobe akai Amaran Gidajensu.
Dukka Amaran A Dakin Mommy na sama suka kwana ammh Daki Dabam Dabam,Rumana ita da Basma suka kwana Anty Saratu suna Gidan Hajja chan suka kwana Rumana ta kwana Tunanin me ya Samu Mastur ne Taga kamar baya Farinciki kamar yadda Mansur yake ba Bata da mai bata amsa ba Dole Tayi Shuru.
Tun safe akaFara Shirin mika Amaran Dakunansu Daman Rumana Daga chan Sokoto matan kannen Umma sun zo da kayan gara Damota guda Snkas kuma Mommy Tayi musu ita da Diza wanda a Diza Catering dinta akayi komai,Biyu suka Raba kayan suka bama su Hajja Hakama na Bangaran Diza Baba Habibu nata Fada abu kamar Ba Gida Daya ba,Dukkansu Shigar Lifaya sukayi Da za"a kaisu Gidansu Daddy ya saka musu albarka Baba Habibu ma haka Baba Sule ma ya saka musu albarka Hajja da Ayya ma sun saka albarka Ayya dai tace kafarta kafar Amare sai ta Rakasu,Daman tuni su Wasu Mutanen suna cham Gidan karfe 10am na safe Aka tafi kai Amare Dakunansu Amotar Daddy aka Kaisu Inda Mus"ab ya Tukasu Mansur da Mastur suna Gida Mansur dai yana wajen Motocin Rakiyan Amaran suka Tashi,Ammh Mastur yana Ciki yana Warware gajiya ga Ciwon kai Duk bayajin Dadin Jikinsa.

Motoci Har cikin Haraban katom Gidan suka Shiga Diza itace karama sai da ta Fara Raka Rumana Shashenta wanda yaji Kayan alfarma kallon Sashenta Purple and White ne,Duka Daga Falo Har Bedroom Har sai da suka Danganta da kan gadonta na alfarma Kama suka Hadu suka Mika Diza Ita kuma nata Shashen blue and Ash ne Lokacin Da Diza Tajita Zaune kan gadon Auranta sai ta saka kuka Yi takeyi ba Saurarawa kowa ya Zata kukan Rabuwa da gida ne nan kuwa ba wanda ya sani Tana kukan Rasa Muradin Ranta ne na Har Abada.

Ranar anan akayi idasa Bikin Abinci ma da komai Duka Daga Gida Mommy ta aiko da komai,Sai Bayan La"asar akayi Walima a Haraban Gidan inda aka Gayyato Malama Safiya Muhammad Ba"are tayi Wa"azi ga amare wadanda sukayi Shigar Bakaken Jallabiya anyi Rabon abuwawan ci sosai Dama na Sha sai wajen 6pm aka tashi aka Fara Shirin barin Amare bayan Kowacce an gyara mata Shashenta yana Tashin kamshi Rumana tana Tare da Basma suna Sallama wacce Zata koma kaduna Gobe ammh Rumana tace kafin Tatsfi ta Biyo,Su Sagir ne suka zo da Motoci kwasan Mutane su maidasu Gida Bayan Dukkansu sunsha Nasihan Zaman lafiya da kuma Hakuri da juna duk da ba Mazajensu Daya ba ammh kuma Zasu zauna Waje Daya ba Abokin Mastur ko Daya Saleem ne kuma ya Wuce katsina Dazu Sargent Inuwa ne kadai ke kaida da kawo da Motan Yallaban.

Koda akayi mangariba Gidan ya Koma Tsit kowacce abarta ita kadai ashashen ta tana kuka Rumana Haka ta rike Anty Saratu Tana kuka Dakyar ta kwaci kanta Sai da Hajiya Adama ta tsawatar haka itama Diza Tayi ammh ita kukanta Harda Rashin Masoyinta.
Har yanzu gidajen Biyu acike suke Saboda Baki sai gobe kowa zai koma Gidansa Basma Tana Tare da Meena yar"uwa Diza nan Gidan Su Diza zasu kwana.

Bangaran angwaye kuwa Mansur Sai Zumudi yake yau zai Shiga Dakin Amarya yayin da Bangaran Mastur ji yake kamar Rayuwarsa ta Shiga Halin kila wa kala na har Abada kuma kenan.






*Shakira...*
1/1/22, 18:54 - Maryam Badmsi: *SS...21*


"Inda Mastur yasan Hanyar da zai Zillema auran da Haduwa da Rumana Amaryasa Da Tuni yayi sai dai ba mafita kuma ba Hanya,Dole yanaji yana gani ya Shirya cikin Sabuwar Shadda mai Ruwan Kasa,duk cikin wadanda Mansur din ya Dinkamai sai dai yau kowa kalan nashi ya saka Mansur Mai Ruwan Bula ya saka abunsa kowa ya gansa yasan yana Farinciki Sabanin Mastur kamar wani mara Lafiya mara kuzari mara karkashi mara Fara"a kamar wanda yake cikin wani Halin ni yasu kowa ya gansa sai yace baya fara"a kamar ango Duk da kowa yasan yanayinsa na lokacin ya bambamta da yadda Kowa ya saba ganinsa.

Mansur shi ya bama Sagir kudi yaje ya siyo kaji gasassu leda Biyu,Kowanne da Kilishi da Madaran Holladian mai Sanyi,sai Lokacin ya Sallami Sagir Mus"ab dai yana nan sai da Safe zai Hau jirgi ya koma,Da ace mastur yana da mafita kwanciyarsa zai yi a Dakinsa bayan ya kulle kansa ammh Ina bayaso yayi wani abun da za"a Tambayeshi meyasa yayi haka..?bai Shirya amsa wadanan Tambayoyin ba.

Kafin su wuce sai da suka Shiga Wajen Hajja da Ayya suka saka musu albarka Kana suka je wajen Baba Habibu da Mallan Sule Da Daddy da suke Tare a BQ,sukayi musu Nasiha suka sa Musu albarka,Daganan kowa ya Shiga Motarsa da Ledan kazansa Har zasu Tafi ma Mansur yaga Mastur zai Shiga Mota bai Dauki Jakar kayansa ba yasa ya Tunamai sai Lokacin ya Tuna ya koma Daki ya Dauko Jakarsa Gabadaya Mansur Mus"ab zai Rakasa Shi kuma Mastur shi kadai ya Shiga Motarsa Motar mansur ne ke gaba nashi na Binsu abaya Har Zuwa Hanwa Lowcost,sukayi Hon megadi yazo ya wangale musu get suka Sulala da Motocinsu ciki megadi na ganinsu ya Gane Zaratan Samarin Gidan ne Wanda Daddy ya Riga yayi mai Bayani.
Shi ya ruga yaje ya Bude ma Mastur Mota Mansur kuma da kansa ya Bude Daman ya kosa a kage yake ya kosa yagansa Dagashi Sai Diza hakan ne Kadai Burinsa da Farincikinsa.
Bayan sun Firfito Suka gaisa da Megadin,ba wani babba bane iyakarsa sa"ar Mastur da Mansur Gabadaya Mastur bai san ma ina ne Barayinsa ba Sai da Mansur ya nuna mai kansa kawai ya Dafe Ya Taka zai wuce Mansur ya Bisa da kallo yana Fadin"Yaya ina zaka kuma..?
Baka Dauki Ledan Kazan Anty tawa ba..Kuma baka Dauki Jakar kayanka ba..?
Sai Lokacin Mastur ya Tuna Da Sauri ya Dawo ya Bude Mota ya Dauki Jakar da ledan Mus"ab da mansur suka kalli juna Cikin mamaki Mastur kansa ya Dafe kafin yace"Na manta sam.."

Mansur ya kariso kusa dashi Yana Fadin"Ko mu Rakaka ne Yaya..? Da sauri yace"A"a ku barshi kawai kaima Amaryanka nachan na jiranka kada ka Damu.."Mansur ya kallesa sosai kafin yace"Meke damunka yaya..? Tunda aka Fara Sha'anin nan naganka ba yadda na sanka ba..?
Mastur ya Dago Idanuwansa yana kallon Mansur kafin yace"Wlh gajiya ce..Akwai gajiya Sosai ajikina.."Mansur ya Rausayar dakai yana Fadin"Ashiga a huta ya Mastur..Ina Tsausayama Anty Rumana yau duk zaka sauke gajiyanka akanta kenan.."Da Sauri Mastur ya waro ido yana kallonsa Dariya Mansur ya saka Sai da Mastur ya Daki Kafadansa yana Fadin"Kai yaron nan fa naga alaman ka Fara Lalacewa Tunda ka Shiga Siyasa.."yafada yana Turesa baya Mansur kuma na Dariya juyawa yayi kawai yana Fadin"Sai da safe.."Mus"ab ne dake gefe ya Daga murya yana Fadin"Allah Tashe mu Lafiya Ranka ya Dade.."Mastur yana jinsa sai ya waigo kawai ya Daga mai Hannu Suna kallo ya Kwankwansa Kofar Falon kadan kafin kuma ya Tura ya Shiga Ya maida kofar ya Rufe Sai da suka ga Shigarsa Kana Mansur ya wuce gaba Mus"ab yabi bayansa suka Nufi kofar da Sada Sadasu da bangaran Diza Amarya wacce ke chan Tana Rafzan kuka.

Suna Shiga Falon Mus"ab ya zauna kan Daya Daga Cikin kujerun Falon Shi kuma Mansur ya Taka ya Shiga Bedroom din Daya Hangi Haske domin akwai Wutan lantarki Haske ya gama gauraye ko"ina,yana Tura Kofar yaga ta Bude ya Tura kai ya Shiga Da Sallama asaman Bakinsa.
Cak ya Tsaya ganin Diza zaune kan gado ta hada kai da gwiwa Tana ta Rafzan kuka kamar wacce akace uwarta ta Mutu Da Sauri ya Karisa kan gadon yana Fadin"Subhanallah...My Firstlady ya da kuka haka..? Yafada Lokaci daya yana Cire Takalmin kafarsa ya Haye kan gadon lokaci Daya ya Tarairayota Zuwa jikinsa cikin Tashin Hankali,Dago kanta yayi da Fuskarta ta gama Damewa da majina da Hawaye Cikin Matsancin Tashin hankali ya Tallabo Habanta yana Fadin"Meya Faru ne..? Meyasa kike kuka..? Baga ni ba..? Kin manta i promise u indai ina Raye sai kin fi matar gwanna jin Dadi da Rayuwa mai yanci.."Yake Fada yana Share mata Hawaye da Hannuwansa Diza sai taji jikinta yayi sanyi Meza tace..? Tunda aka Fara mganar auran nan Mansur bai taba Bata ransa ba..Koda tace bata sonsa yayansa take so ba ta ga ya Sauya mata ba Kullim Sai dai ya Farantamata Koda bazata Godemai ba Tun suna yara Mansur mai Hidima gareta ne Balle yanzu da ta kasance matarsa Tana Matukar Tsausayamai Rayuwarsa Cikin Sauki da salama ko abokin Fada bai dashi bata Taba ganin Fushin Mansur ba Mutum ne nagari mai Hakuri da kawaici Wanda take kuka Domin sa bai san Tanayi ba da bakinsa yace baya sonta Yana chan da matarsa,Meyasa Zata zo Tana kuka Domin ta bata ma wanda ke matukar sonta rai..? Da wannan Tunanin Tayi Saurin Saka Hannu ta riko Hannuwansa Tana Fadin"Ina kukan Rabuwa da Mommy ne da Daddy..'Mirmishi yayi yana kallonta Cikin Begen so da kauna yace"in wannan ne baki da Damuwa..in kullum kike son Zuwa Kiga Mommy da Daddy nayi miki alkawarin bazan gajiya ba.."yafada Lokaci Daya ya Sakarmata Idanuwansa Cikin kallon Sha"awa da muradi mai girma Diza da taji kamar ta Suma Saboda kukan Dake cin Ranta kawai ta Fada jikinsa ta kamkameshi ta Fashe da kukan Takaichin Zuciyarta da bata son wannan bawan nata sai Damuwa da wanda bai Damu da ita ba.

Yana jinta Tana kuka ya kara Rumgumeta yana lallashimta Cikin Dadaddan kalamansa Har ya samu Tayi Shuru Tana ajiyar Zuciya,Dagota daga jikinsa yayi ta kara makalewa Dariya yayi yana Jin karan wayarsa Dake Cikin aljihunsa yace"Mus"ab na Falo yana jirana fa My Firstlady..."Dago Jajayen idanuwanta tayi Tana Fadin'Tare kuka zo..? Yana shafa Bayanta yace"Eh Da Yaya Mastur kinsan ba abokai ne dashi ba..Ya wuce Shashensa ni kuma Mus'ab ya Rakoni Sagir ma yayi gida.."Tunda ya ambaci Mastur Tayu Dif da ita sai taja jikinta ta koma Gefe Ta kwanta Tana Sauke Numfashi mikewa yayi yana Gyara Rigarsa data Fara Yamutse yace"Zaki samu Fita ku gaisa ko sai gobe..?
Kai kawai ta gyada mai kafon tace"Nagaji..Banma son Tashi."Tafada Cikin Sanyin murya bai Damu ba ya juya yana Fadin"Bari naje na sallameshi.."Daga haka ya Fice ta Rakashi da ido Cikin Taruwan Hawaye.
Mansur na Fita Mus"ab ya balbeleshi da masifa wai ya Shanyashi Shi dai Hakuri kawai yake bashi yana Dariya Sallama sukayi bayan ya gayamai Dizan bazata samu Damar Fitowa ba Karamin Tsaki Mus"ab yaja kawai ya wuce Mansur ya bashi key din Motarsa ya koma da ita Saboda Dare har Haraban Gidan ya Rakasa saida yaga Ficewarsa Daga gidan kana ya koma Ciki.

Shi kanshi a gajiye yake barci yske son yayi ya Huta Domin yafi Sati baya samun wani Ishashen Barci,Dakyar ya Lallashi Diza ta shiga Tayi wanka yaje Kitchen ya Dauko Filet da kofuna sai fork,Yazo ya Saka Kazan a Filet ya bita dashi Har kan gado yana bata tana amsa Dakyar,Ya matsa mata taci ne saboda yasan tana jin yunwa Kadan taci ya bata madaran Tasha ta koma ta kwanta,Shi ya karishe sauran kazan ya Danna da madara Sauran kuma ya kai kitchen ya saka Cikin Fridge ya Dawo Falo ya Dauki Jakar kayansa ya Shiga Ciki ya Samu Diza kwance acikin Bargo Idanuwanta a lumshe bai mata mgana ba ya Fada Tiolet yayi wanka Koda ya Fito Barcin gajiya ya kwashe Diza Bata sani ba,Mirmishi kawai yayi ya Bude Jakarsa ya Dauki kayan barcinsa Riga da wando ya saka ya Fesa Turare ya Shinfida Darduma yayi Shafa"i dawuturi Dakyar kamar ya Kifa Falo ya Fita ya RarrageHasken wajen kana ya Dawo Ciki ya Rage Hasken Bedroom din ya kunna Dumlight,Kan gadon ya Hau Lokaci Daya yana Jawo Diza jikinsa wacce ke sanye da Daguwar Rigar barci mai Taushi,Daman barcin ya kwasheta da Fargaba ne,Tana jinta ajikinsa Tayi Saurin Zabura Riketa yayi yana fadin"Relex..Babu abundaa Zan yi miki kwanta kiyi barcinki..Nima gajiya bazata barni na iya Moranki Dakyau ba.."Yafada yana Raban Wuyanta wani yamm taji acikin Jikinta ammh Ta kasa Motsi Tama jinsa ya kara Rumgumeta Bisa Kirjinsa yaja Bargo ya Rufesu yana Sauke Numfashi Lamo Diza Tayi Tana Shakam Kamshin Turaransa Tunani na neman Shigo mata Yasa Tayi Saurin Kiran sunan Allah Saboda yadda suke agajiye yasa basu wani jima ba Barci ya kwashe su Dukkansu.

Bangaran Mastur Rumana dai ba haka Tagani Domin Har Mastur ya Shigo Gidan nan bata sani ba,ba Dakinta ya Fara Shiga ba Dakin kusa da nata ya Bude ya Shiga shima agyare yake Tsab nan ya Sauke kayansa Domin bai yi Tunanin Fara Rayuwa da wata a Daki Daya ba Sai da ya Shiga yayi wanka ya Saka Wata Jallabiya mai Ruwan Madara Shafa"i da Wuturi yayi Ya Dade Zaune yana Tufka yana Warwara kafin ya Mike Cikin Sanyin Jiki ya Fita Zuwa Falon Lokaci Daya yana karema Falon kallon aransa yake fadin Nice Ledan kazan Daya ijiyeta nan Saman Dinning ya Dauka ya Nufi Dakin Rumana yana Addu"a da Fatan Allah yasa Tayi barci sai addu"ansa bata ci ba yana Taba Kofar ta Bude Daman an Dan Sakayata ne sai ga Rumana Zaune kan Tsakiyar gadonta Taci kuka ta Koshi Har ta Dago Fuskarta Tana kallon Kofa Sai gashi sun Hada Ido Hudu da Mastur Dake Tsaye da Leda ahannunsa,Mamaki ya kamata Bayan ta Sauke Numfashi Ita nata angon da Shigar Jallabiya zai Shigo mata..! Da alama ma ba yanzu ya Shigo Gidan ba.

Shi kuwa Mastur saurin Karisowa Cikin Tsakiyar Dakin yayi yana kaucema Idanuwan Rumana Gefen gadon ya Zauna kamar wani mara gaskiya ya Dora mata ledan kazan kan gadon agabanta Cikin mamaki Tabi ledan da kallo kafin ta Sadda kanta kasa Tana kara jan mayafinta Shuru shuru yana Zaune bai ce mata komai ba Ganin haka yaasa ta Muskuta Tana Fadin"Ina wuni..!"
Dakyar ya iya Bude baki ya amsa mata Cikin wani irin kasala,Dif kuma yayi ya kasa mgana Domin bai sam ta ina Zai Fara ba itama sai tayi Shuru gabanta na Faduwa Wajen kimamin minti goma Sha Biyar ya mike tsaye yana Fadin"Kici kafin ki kwanta..Sai da Safe."Daga haka bai jira cewarta ba ya juya yana Tafiya kamar zaiFadi Rumana ta bishi da kallo,baki Bude har ya Fice Saboda mamaki,Daidai Karar Rufo Kofar da yayi daidai Zubar kwallarta Sai yanzu ta kara yarda Mastur baya sonta..Domin Angon adaran Farko Doki da Zumudin Amaryansa yake ammh ita ba wani kulawa ba Tattali ba mgana mai Dadi,yadda take karantawa a Littafan Hausa da Turanci Daran Farko Kazan amarcin ma Ango ke lallashin Amaryansa Tana ci kauda kai Tana bata rai yana bata abaki ammh ita anata barayin ba Haka yake ba Dakyar ma angon nata ya Shigo wajenta ya Tura mata Ledan kaza yace taci Kafin ta kwanta Daganan ya Fice abunsa ya barta Bayan yayi mata Sallama kemsn Ita kadai Zata kwana Adaran Farkonta Angonta ya Raba makwanci da ita wannan wani irin Rana ce Gareta,Sai kuka Haka Rumana ke kuka Kamar ranta zai Fita Tagaji ne ta Mike ta Rarrafa Ta Shiga Tiolet tayi alwala ko wanka Bata iya yiba ta zo Tayi Sallar Isha"i da batayi ba Tana jin yunwa kwarai Domin Rabonta da wani abincin Kirki Tun Breakfast din da sukayi agidan Daddy ammh bazata iya cin komai ba Saboda bakinciki Ture ledan kazan Tayi kasa ta Kudundune akan gadoTana Cigaba da kukanta ko kayan Jikinta bata cire ba,Ta kwanta Bata san iya adadin Lokacin Data Shafe Tana Kuka ba da Tsausayama Rayuwarta Bata san Lokacin da barci ya kwasheta ba.

******

Washegari Bangaran Diza da Mansur sun tashi Cikin Farimciki Domin Diza Tana ganin Soyayyah da Tattali wajen Mansur wanda yayi Sanadiyar goge Duka kukanta,Sai dai kawai ta Rika Binsa da ido Tana addu"an Allah ya Dora mata kaunarsa ya Cire mata son wanda baya sonta.

Daga gidan Daddy aka aiko musu da Breakfast,Kwando Biyu Mansur Daya Mastur Daya,Dukkansu mazajen su suka Fita suka amsa Bayan Mommy ta kirasu ta sanar dasu ga abun karyawa nan zata aiko Dashi,Mansur shi yayi komai ya Lallaba Diza yayi mata wanka ya Sauya mata kaya shima yayi wanka ya sauya kaya,suka Fito Falo ya Zuba musu abun karyawn Tana kan Cinyarsa yana bata abaki Tana kauda kai yana Lallashinta Har taci ta koshi kana shima ya samu yaci ya koshi Daganan ya Dauketa suka Koma Cikin Bedroom suka kara Nannadeawa suka koma Barcin gajiya.

Bangaran Rumana kuwa bata da wannan gatan Domin a falo Mastur ya iijiye mata kwandon Abinci Ruwan Lipton kadai wanda yaji Na"ana"a   ya Diba yssha kadan Saboda Cikin sa ya warware,ya Dade Rabonsa da abinci Tun Jiya Daya bar Dakin Rumana bai kara Lekata yaga wani Hali Take ciki ba Daganan Dakimsa ya koma ya Rufo kofar ya kwanta kan gado,Har idanuwansa suna Rufewa saboda gajiya da Barci yayi mamakin yadda ya samu Barci Jiya da Daddare har ya makara Sallar asuba Kiran Mommy ne ya Tadashi bayan sun gama mgana ya Fada Tiolet yayi wanka ya Dauri alwala yazo Yayi sallah bayan yasauya kaya Cikin Riga da wando Lokacin yaji Direban gidan Daddy nayi Knooking ya Fita suka gaisa ya karbi katon kwandon Abincin ya Shigo Dasu.
Rumana kuwa Tana ciki Tana jin Motsinsa bata Fito bane Domin tun asuba Data Tashi bata koma ba Tayi wanka Ta Sauya kaya tayisallar ta koma Tana azkar dinta,yunwa Tana galabaita ta sosai Domin bata ko kara kallon Ledan kazan jiya ba Tana jin sanda ya Fito Daga Dakinsa bayan taji knooking,Tana ji ya karbo koma miye ya Dawo taji Motsinsa afalon chan kuma Taji shuru jiri Jiri Tske gani bayan ta mike Tana Dafa bango kan gadon ta koma Ta Zauma tana kokarin rike kanta sai dai ko Minti Goms batayi bata gaza Domin bata gani Sosai Saboda yunwa Bata san Sadda ta Sauko kasa ba ta Jawo Ledan kazan nan ido Rufe Ta Fara ci kamar wata Mara Natsuwa Duka ta Cinye kazannan Kilishim ne kadai Bata ci Ba madaran Holladian din kuwa Tana Budeta ta Dagata ta kwankwade Sai da tafi Rabi kana ta Direta tana maida Numfashi Lokaci Daya tana Jingina da gado,Tana sauke Numfashi.
Lokaci Daya da wasu Zubowar Tawagen Hawaye Acikin Zuciyarta take fadin Dama Baya sona ya aure ni..?sai dai kuma ita Abba ya gayamata Mastur din da kansa yace Daddy ya nema masa auranta,Sai dai kuma Zatayi la"akari da yanayin Rayuwarsa Tun yana Gidansu da abubuwan da suka Biyo baya,ammh ko yaya ne ka nuna kulawa ga wacce ka aura ammh kalli yadda ta kare kamar Wata amarya Mara galihu Tana Tunani Tana Sharan kwallah jinta ta Dawo Daidai ne yasa ta Tattara Sauran ta maida Cikin leda Ta koma gado ta kwanta Tana Sauke Numfashi Daganan bata san yaushe barci ya kwasheta ba Sama Sama Taji Muryan kamar ta mansur acikin Falon Kafin kuma Taji Taku Da mgana kamar ta mastur kafin ta gama mamaki Ya Bude kofa ya sawo kansa Cikin Dakin da Sauri ta Mike zaune Tana Laluban Dankwalin leshin Dake jikinta,Ta Daura Tana Saukowa Da kafarta Daga kan gado Daga bakin kofan bai kariso ba kamar bako ta kasan ido ta kalleshi yana Sanye da Shadda Fara Riga da wando da Hula kafarsa Sanye Cikin Sawun cikin Takalma Hannunsa Daya na Cikin Aljihun wandonsa Dayan hannun kuma Wayoyinsa ne da key din Motarsa Fuskarsa baFara"a ko kadan Sai dai Kana   kallonsa Zaka Fahimci Duk ya Zabge ya Rame ita kanta yayi mata Rama a ido Sosai.
Saukowa Tayi Daga kan gadoj Ta rankwafa Tana Fadin"ina kwana..!
Bude bakinsa yayi Dakyar ya amsa da Fadin"Lafiya lau...Ni zan Fita Ga breakfast nan afalo Mommy ta aiko mana Dashi.."
Kanta na kasa Tace"Adawo lafiya.."Ta Wutsiyar ido ya kalleta Daga sama Har kasa kafin ya Basar kawai ya juya acikin Ransa yana Fadin"Itama ta Rame kamar ba Rumana ba.."har ya Bude kofar sai ya juyo Karaf suka Hada ido Da Sauri Ta Sadda Kanta Cikin Dakakkiyar murya yace mata"Mansur yana Falo ko Zaki Fito ku gaisa..?
Tana jin haka Tayi Zaraf ta Mike Tana Fadin"To.."Daga haka bai Tsaya Sauraranta ba ya fice ya Rufo mata Kofa Yana Fita ta Sauke Numfashi Wardrope dimta ta Bude ta Dauko Mayafinta ta Saka Sai da ta kalli madubi Taga Fuskarta Normal kana Ta Fito Falo Ta iskesu Tsaye kamar ita suke jira Tana Fitowa Mansur ya Duka yana gaisheta Cikin Shakiyancinsa Mirmishi Ta saki Tana Fadin"Ina Yar"uwata.? Fatan Tatashi lafiya..?Mansur yace'Lafiyanta kalau..Tana chan na barta Tana Rigiman sai ta Bini Hanwa wajen su Mommy.."Wani Iri Rumana taji acikin Ranta kamar yadda Mastur yaji Ta wutsiyar ido ta kalleshi Taga ya Dauke kai ma yana Duba wayarsa sai tayi yake Tana Fadin"Ai sai ka lallasheta.."Tafada Batare ma Da ta Tauna mganar ba Mikewa Mansur yayi yana Fadin"Dole na..Lallashin Firatlady ai zama Dole..Sai dana Lallasheta Tayi barci na samu Fita muje muyi Sallama da Sauran baki da Zasu Tafi yau..Kuma ai nasan kafin su Tafi Duk zasu Biyo kuyi Sallama.."
Rumana Tace"Allah sarki.."Daganan sai ta kauda kanta shi kuwa Mastur Hanyar barin Falon ya nufa batare da yayi mgana ba ganin haka yasa Mansur yace"Anty na Mun tafi..Ga Mijinki chan Sarkin Sauri Zai tafi ya barni.."jikinta a sanyaye Tace"adawo lafiya.."Ya amsa mata yana Bin Bayan Mastur Daya Riga ya Fice Da kallo tabisu wani abu na sukan Ranta.
Batajin Yunwa Shiyasa kawai taDauki Kwandon Abinci ta kai kitchen Sai Lokacin ta samu leka Shashen nata Tana Kara Jinjina na Abba Har Dakin da Mastur ya kwana sai da taso Shiga ammh Abun mamaki ya Rufe Dakin baki ta Rike mamaki ya cika ta dawota Zauna kenan Saman Daya Daga Cikin Kujerun Falon ba Dadewa Taji karan Hon da Bude get,sai Hayaniya kafin ta yunkura tamike sai ga Basma ta Shigo Bayanta Anty Saratu ne da Anty Baraka da gudu Tatashi ta Rumgumesu Tana murna suna suna murnan ganinta kan kujerun suka zauna suna gaisawa suna Tambayanta ya bakunta Tana jin kunya nan sukace sun zo yi mata sallama ne yanzu Zasu Wuce ne,sai idonta yayi kwalkwal,Dakinta suka Shiga ita da Basma sukayi Sallama Bayan Tace su Anty Saratu su Dibann ma Basma kayan Snkas wanda Mommy tayi musu Ita kuma da Basma suna Ciki Basma na mata Shakiyanci Dataga Ragowan kazan jiya ita dai Rumana bata ce komai bata da abun cewa Domin bazata iya Dora,komai kan Daranta na Farko ba,nan basma ta karishen Ragowan kiloshin Tana ci Tana yi ma Rumana Tsiya ita dai sai Mirmishi bata mgana.
Da zasu Tafi Rumana da Basma suka Rumgume juna Kafin su saki juna Basma ta kalleta Tana Fadin"yauahe zaki koma Asibiti..? Rumana tace"Sai Monday..Dis coming..zan je na kai musi Takardan da Uduth suka bani.."Basma tace"Allah ya kaimu..Anzo miki da duka Takardunki da kayanki kuwa..? Anty Saratu Dakewajen tace"Eh.
duka Ummanta ta bani akwatin na Cikin Wardrope dinta."
Rumana tace"Eh nagani..Zan Duba zuwa gobe in na samu natsuwa.."Nan suka mimmike Rumana ta Fara kuka Anty Baraka Tace"Sawo mayafinki muje Shashen yar"uwanki Daina kuka.."Da Sauri Rumana ta koma Ciki ta Saki mayafi da Takailmi suka Nufi Shashen Diza itama su Anty Hadiza duk suna ciki da su Meena da yan"uwan Mommy na Sokoto wadanda Tare ma zasu Tafi da su Basma.
Nan suka Hada Rumana da Diza sukayi musu Fada da Nasihan su yan"uwan juna ne ko ba aure Balle ma Zaman aure ya Hadasu a gida Daya kuma sunaAuran yan'uwana juna sai su Rumgumi Junansu su zama abokan Shawaran juna Rumana dai Ta Dauka Domin Tun agida Umma Tayi mata sosai Ammh banda Diza Datake ganin kamar Rumama wata makiyiyarta ce ko Fara"a batayi ba Fuskar nan A Hade Rumanan sai mata Dariya Take Diza kam sai yake basu wani jima ba nan suka Firfitowa Har Aharaban Gidan Diza da Rumana suka Rakosu Kowacce TanaRumguman yan"uwanta Tana kuka Daman Daganan wucewa zasuyi Domin sunyi Sallama Dachan gidan Shatar Mota aka sama musu Sharon Suka Shiga Har suka Fice Daga gidan Suna Daga musu Hannu Rumana taso komawa Shashen Diza Domin su Debema juna kewa sai dai Kafin ta isa gareta Diza ta Juya ta koma Cikin Shashenta ta Turo Kofa Mamaki ya kama Rumana Kafin ta kada kai ta koma Shashenta Lokaci Daya Tana auna Wasu Sauye Sauye Data gani game da Diza.

****
Banganransu Angwaye kuwa suna gidansu basu samu Sukuni ba sai da baki Dadama suka Dauki Hanyar komawa Gida Ciki Harda Baba Sule da iyalansa Inna karime ce kadai ta Rage Daga Gidan Hajja sai Gobe Zata koma Gidan Mommy kuwa Duk an Watse itama Daga yan Tureta Wadanda suma agoben Zasu Tafi sai kanwata Anty Saratu Datace Ta bari sai Sati na Sama Tatafi,gidajen duka sunyi Tsit kamar ba wani Sha"ani mutane Rahma ne,Hankalinsu bai kwanta sai da yan Sokoto suka kira sukace sun isa da Yan maruka Umma ta Kira Mommy Tana ta Godiya da kuma kara Dankamata Amanar Rumana tacr bakomai Rumana yarta ce.

Mansur ya samu Fita da yammah Domin ya Kai Mus"ab kaduna ya Shiga Jirgi Daganan ya Shiga garin kaduna sunyi wani Taro wanda Na partyn su ya zama Dole ya Hallatar sai Dare ya Dawo Mastur kuwa yana Shashensu acikin Dakinsu yana ta Barcin gajiya Har su Hajja Tunda suka Shigo da Safan suka gaisa basu kara ganinshi ba zatonsu baya gidan Har Mansur ya Dawo bai Zauna ba yayi musu sallama ya wuce tunda Hajja tace Tana Tunanin Mastur din ya Tafi Shiyasa bai kira wayarsa ba sai da yazo gidan yaga ba motarsa kuma ya Tambayi megadi Sai yace bai kariso ba,Sai Lokacin ya kirashi a waya kuma wannan kiran Wayar ya Farkar dashi Daga Nauyayyan Barcin Daya kwasheshi ba La"asar ba mangariba ba Isha"i Cikin Kasala ya mike bayan ya gayama Mansur yana gida Barci yakwashe ammh yana Rama Salollinsa Zai Taho Tiolet ya Fada yayi wanka yazo ya Sauya kaya Daman Kayansa kala Biyu yaje dasu Chan gida,kana ya Fara rama Salololinsa Yayi mamakin barcinsa Tunda ya Sallami Sargent Inuwa Kafin La"asar ya koma porthercourt shi an kakabamai Hutun 1 week sai Sunday zai koma ya shigo kwanta bai kara sanin komai ba kuma Motarsa Tana Gidan Daddy chan ya kaita Dazu Daya ga Mutane na kai da kawo a Haraban Gidan nasu.
Sai da ya shiga Wajensu Hajja ne suka san yana Gida Sallama yayi musu agurgiuje ya Wuce Gidan Daddy bai Shiga ba iyakarsa Haraban Gidan ya Shiga ya dau Motarsa megadi ya Bude mishi get ya Fice.

9pm Daidai ya Shiga Gidan wani barcin kuma aidonsa kamar yasha kayan maye Wayoyinsa ya Dauka da System dinsa Dake Cikin Motan ya nufi Barayinsu Yana Shiga Falon yaga wani kwadon Abinci wanda baya Raba Daya Biyu Mommy ce ta kara aikowa Dashi Dakin Rumana ya kallah yaga da Haske kuma bata Tura kofan Duka ba bai yi Tunanin Shiga ba ya Saka makulli ya Bude Dakinsa ya Shiga ya maida Kofa ya Rufe.
Rumana Dake Cikin Dakinta ta Saki Numfashi Bayan taga Shigowarsa Hankalinta ya tashi Tana cikin Zullumin ganin Tun Dazu Taji Shigowar mansur ammh Shuru bata gansa ba Tayi Tunanin kiransa sau ba adadi Sai ta kasa kiran Wayar Umma ya Dauke mata Hankali basu Dade da gama waya ba ya Shigo.
Wayar ta ijiye saman gadon ta Bude kofar tiolet ta Shiga wanka take so Tayi ta kwanta yau bata Cuci kanta ba Mommy na kara aiko musu da abinci Taci ta koshi na Safe kuma ta bama Dirban ya maida shi Domin ta Lura Daga ita Har shi basu Taba komai Daga cikin abincin ba Har gwarama Dazu Basma Taci Soyayyan Dankalin Dazu kafin su Tafi.



*Ki biya ki karanta cikin Salama Mace mai aji mallakan komai nata take yi bata jiran Abun Sata 09069067488*






*Janafty...*
1/1/22, 18:54 - Maryam Badmsi: *SS...22*

"Har ta gama abubuwan da Zatayi ta kwanta bata kara jin Motsin mastur ba sai da Safe Wajen misalin 10am lokacin Taji Knooking din kofa Tayi Zaton Baya gidan ne ta Fito da Niyar taje ta Bude domin tasan Sakon Mommy ne na Breakfast dinsu sai kuma sukayi karo ya Fito Daga Dakinsa Saurin ja da Baya tayi tana gaisheshi ya amsa kamar mai ciwon baki Kitchen ta Shiga ta Dauko mai Kwandon Jiya Domin ta bama Direban ya maida ma Mommy sai ta iske har Mastur ya ijiye kwandon nan Falo ya Shige Ciki Har Haraban Gidan ta leke Daidai Lokacin da Motar Direban ke Fita Daga Haraban Gidan Baki ta Ciza kafin ta Dawo Falon,Kitchen ta maida Duka Kwamdunan Abincin Ta samu Filet ta Dibi Soyayyan Dankali da kwai sai ta Samu wani Mug ta Diba Ruwan Lipton Ta Fito Falo Saman Dining ta Zauna inda taga an jera kayan Tea ta hada komai ta fara sha Zuciyarta na wani Tunani Kofar Dakin nashi ta Kura ma ido kamar Tana ganinshi Lokaci Daya Tana auna wasu Tunane acikin Ranta Kenan haka zasu Gudanar da nasu Zaman auran..? Abunda ke bata mamaki baya taba komai na abincin da Mommy ke aikowa Dashi sai dai ita taci kadan kuma ta Tabbata Mommy Tana Fahimtar basa cin abincinta Tunda in aka kawo wani Tana maida wanda aka kawo kada Ta barsa ya Lalace tunda ita ba ci Zatayi ba kuma Uban gayyar Shi bata son ina ya saka gaba ba Tana Tsoron kada Mommy ta kula da hakan har takai ga Tayi mgana.

Haka ta gama karyawanta Tana ta Tunanenta,nan ta bar komai Saman Dinning din ta Kariso cikin Falon ta Zauna kan Daya Daga Cikin kujerun Falon Tana Sauke gajiyan cin Abinci,Zaman Shuru Duk ya isheta yasa ta mike Tana kokarin Hada Kayan kallon Dake falon,ammh ta kasa sai kawai ta barshi bata kara zama afalon ba ta koma Cikin Dakinta Bata son ta zauna haka Tunani zai mata yawa sai ta Dauki Wayarta ta kira Abba bai Daga ba sai da ta katse kana ya Kirata suka gaisa,Yana Tambayanta Mastur tace yana Lafiya Basu Dade suna waya ba sukayi sallama bayan ya kara mata Nasihan Zaman hakuri da Zama lafiya ya ba Umma sun gaisa Sama sama Daganan sukayi Sallama.

Wardrope dinta ta Bude ta Dauko Trolley dinta Wanda aka Sako mata Takardunta da Sauran muhimman kayanta Daga gida Kan tsakiyar gadon ta Zazzage komai Tana gani Tarkadunta na makaranta ta Hadasu waje Daya Taji Dadi Dataga Har da System dinta zai Debe mata kewa sai Sauran abubuwanta masu muhimmanci Duk ta Dauka Tana adanasu Inda suka Dace Musamman Takardan da suka bata a Uduth wanda Zata je dashi ABU chika ta nuna Ranar Monday,Aikin shi ya Dauke mata Hankali Bayan ta gama ta Koma Kan gado ta Zauna Ta tankwashe kafa,Bayan ta saka Gilashinta Ta Bude Syatem din Ta kunna,Daman Rumana akwai son karatu bata Bata Lokaci ba ta Fara Karatun Abunda ya Shafi Abunda ta karanta Domin Tana da Burin Bayan ta gama Service dinta Zata Dora Karatunta Wato Resendency,Tana so ta samu kwarewa kan Abunda ya shafi yara Hakan yasa Hankalimta ya Dauke Daga Tunani ko Motsin Mastur Daya shige Daki kamar baya gidan.

Har ya Fito Falon yaje Kitchen ya Dauko Mug ya Dibi Ruwan Zafi yahada Tea din yasha Bata sani ba Tadai ji Rufowar kofar Dakinsa Sai Lokacin ta Fahimci Ya Fito kenan,Ranar haka suka wuni acikin Gidan Tana da Tabbacin bai fita ba ko kofar Gida Direban gidan su Mommy sai Dare ya kawo musu kwandon Abinci Lokacin Tana Falo ita ta Fita ta karba bayan sun gaisa tace mai ya tsaya ta koma Kitchen ta Dauko mai kwanduna Biyun na jiya dana yau da Safe ta bashi ya Juya ya tafi Bata wani jin yunwa Domin Ta kara cin Ferfesun Kayan cikin sosai kuma ya cika mata Ciki.
Wannan karon Tuwon Shinkafa ne Miyar Agon,Da yaji Nama da Kifi,Rumana nasan Tuwon Bata tsaya wasa ba takai komai Kitchen tasamu Filet ta Dibi Tuwon Leda Daya taci Ta Hada da Ruwa,Abunda yake kara bata mamaki da Mastur kamar ya manta da akwai Mutum acikin Gidan ko Motsin shi bataji kuma ta Tattabata yana Cikin Gidan kuma bata ga Fitarsa ba,Bata ji wani Dadi ba anan Falon ba ana kiran Sallar Isha"i ta Shige Ciki abunta yau ko Motsin Mansur da Diza bata ji ba Tana Tunanin Kila suma Daga Barayinsu yau basu Fita ba.

Haka suka kwana Washegari ma Haka suka sake kwana bata Sauya zani ba Hana Rantsuwa Da Rana tana Falo ya Fito Daga Cikin Dakin yana Sanye Da Jallabiya Ruwa ya fito Dauka Kishi ya Fito Dashi,Sai alokacin Suka gaisa bayan sun kwana sun Wuni basu ga juna ba,Gaishe tayi ya amsa Batare Daya kalleshi ta ba,Ya shiga Kitchen bai Dade ba ya Dawo daGoran Ruwa mai Sanyi ya Shige Ciki ta bisa da kallon mamaki Domin ita dai bata ga yana cin Abinci ba sai dai Ruwa ko Lemo ko kuma da Safe yasha Tea da Daddare kuma yasha Ruwan lipton kuma bata ga wani alaman yunwa ko Damuwa a tare dashi ba Tagumi Tayi aranta Tana Janjanta ma kanta irin Mijinta Data aura kenam...?gashi Tun ranar Litini Da Safe da yan Sokoto suka zo musu sallama ba wanda ya kara Lekosu daga su sai Halinsu Diza ma da Mansur bata kara,jin Duriyarsu ba sai Ranar alhamis da Sassafe Lokacin Tana ma kam Darduma bayan ta idar da Sallar Tana azkar Taji karan Bude kofar dakin Mastur Dayake Dakin na kusa da nata In dai zai Fito ya Taba Kofar Dakin Tanaji Ita dai tana Zaune Bata motsa ba Tunaninta ko Kitchen zai shiga neman wani abu Tunda ko Masallaci basa zuwa acikin Gida suke yi Dayake ba wani masallaci kusa dasu da Nisa gaskiya ita kamta Lokaci takan Duba awayarta Take gane Lokutan sallah.

Ta na nan Zaune batasan me ya Faru ba sai taji Muryan Mansur acikin Falon suna mgana da Mastur,Da sauri tatashi Tana Tunanin Lafiya Kamar ta Fita sai kuma ta fasa ta koma ta Zauna Mastur Dake chan Falo Shi da Mansur Cikin Yamutsan Fuska ya kalli Mansur da Duk ya Firgice yana Fadin"Lafiya na ganka haka..?

Yafada yana kara kallonsa ganinsa kamar baya cikin Natsuwansa,Mansur na Shafa kai yace"Yaya Mastur aron Anty Rumana nazo ka bani..Diza ce ba Lafiya don Allah muje ta Dan Taimaka mata."Ya karishe Fada yana Sosa kai Daga yanayin mganarsa Mastur ya Fahimci Abunda ya Faru wani irin Dam yaji akan Kirjinsa,Da sauri ya Juya yana Fuzgar Numfashinsa bai ce ma Mansur din komai ba ya isa ga Kofar dakin Rumana ya kwankwasa mata Daman Tana Zaune ne kunnenta na Falon da Hanzari ta Mike Tana gyara Zaman Hijabin jikinta ta isa ga Kofar ta Bude,Taci karo da Mastur tsaye akofar Dakin Da Sauri ta rankwafa Tana gaisheshi kallo Daya yayi mata ya amsa da "Lafiya lau..Kije Mansur na neman ki..!

Daga haka ya juya Hannuwansa na Cikin alijuhun bakin Wando   Dake Jikinsa kawai ya Tura kofar Dakinsa ya Shige ya Rufo kofa ya barsu nan suna Binsa da kallo Mansur bai Damu ba yafi kowa sanin Halin Mastur hankalinsa Baya jikinta Ya bar Diza Tana ta kuka Ya riga yayi aika aika Dole ta kwana tana kuka kuma yaji mata Rauni Domin jiya ya amshi Budurci Diza

Rumana bata samu komawa Ciki ba Tunda tana da Hijabinta Ta Fito Tana Fadin"Mansur Ina kwananmu..?Mansur na sosa kai yace"Lafiya lau Anty Rumana..Taimakom ki nake nema Muje ki Dubamin Diza Don Allah.."Rumana tace"Subhanallah..Me ya sameta..? Mansur duk Surutunsa bai iya cewa komai ba kai kawai ya sosa kai yana yar Dariya Sama da kasa Rumana ta kalleshi sai ta Fara Daukan Saunan abunda ya Faru ganinsa da Jallabiya ajuye Daga gani dai baya Cikin Natsuwarsa batayi gaddama ba ta Bisa Tana Fadin"Muje nagani.."
Daga haka suka Rankaya zuwa Shashen na mansur Mastur Dake Ciki Duk yanaji suka Fice Hannu ya sska ya Dafe kansa yana maimaita"Innalillahi wa'inna Illaihirraju"un.."Kawai yake Maimaitawa Acikiin ransa afili kuma ya Furta"Me kenan yake Faruwa dani..? Matar Dan"uwa ne fa..? Yanzu ta fi karfina Tamin Nisa ya kamata na Cireta araina na Daina Tunaninta..Ammh ya zan yi..?na kasa Cireta araina Ballatana na kallo Matar da take Halaliyata,Zufa kawai yake ketomai Lokaci Daya yana jin kansa na saramai bai tsaya ba ya Tura kofar toilet ya shiga Batare Daya cire kayansa ba ya Tsaya kikam ya saki Shower ruwa yana Dukansa Lokaci Daya Tare da Bugun Zuciyarsa.
Sai da ya samu Saukin Jiki Dana Zuciya kana ya Tube kayansa ya Wurga cikin kwandon kayan wankin Daya ke Tara kayansa na Datti in ya Cire yayi wanka kana ya Dauro Towel ya Fito hankalinsa Duk ya tashi bayan ya Sauya Kaya har dakin Rumana ya Leka bata nan hakan ya Tabbatarmai bata dawo ba kenan sai ya fara Tunanin ko Mtsalan ta wuce yadda yake Tunani ne Kamar ya Daga waya ya Kira Mansur haka yake ji ammh yana Kokarin Danne abun acikin Ransa.

Bangaran Rumana kuwa Kafa kafa ta Dinga Bin Mansur Har cikin Bedroom dinsu inda suka iske Diza dungunkune kan gado da blanket Tana kuka Rumana Daga Gefe ta Tsaya Bata karisa ba Mansur ne ya karisa har kan gado ya Dago da Diza yana Fadin"Kinga am sorry tashi..Ga Anty Rumana tazo Dubaki."
Diza Dake kukan abu Biyu na Farko kukan azaban Datasha Hannun Mansur na Biyu kukan Yau wani wanda bata taba Mafarkin zai karbi Budurcinta ba,ya karba Yanzu Shikenan ita da Mastur sai kallo Kallon kenan Kila kuma yazun sun riga sun zama Daya da Rumana itace ke Haukan banzanta in ta Tuna haka sai ta karajin wani Kishi ya Turketa ta Kara jin kuka na Taso mata ammh jin Abunda Mansur yace ne yasa ta Dago Fuskarta Datayi Jage Jage da majina da kuka Tace"Wata Anty Ruman..."Mganarta ne ta makale ne Lokacin Da suka Hada ido da Rumana Dake tsaye Tana kallonsu wani kololon abu Diza Taji Ya Tokare mata Kirji Lalle ba karamin Tozarta Ta mansur yayi ba,ya rasa wacce zai kira mata sai Wacce ta Tsana irin Rumana wacce ta aure mata abun sonta wacce take jin Kishinta Sosai Fiye da kima itace Zai tona mata asiri a wajenta ita da nata ya Faru wa ta kira .? Ko wata gayamawa shine shi zai zo yayi mata Terere haka kurum.

Kada kai kawai Diza Tayi tana wani Cin mgani Saboda karin Haushi sai ga hawaye na Zubo mata Shi kuma Mansur sai ya Rude ya Tarairayota yana Bata baki Rumana na gefe Tana kallon Ikon Allah ita waya bata wannan Damar Mastur ko kyakyawan kallo bai Taba mata ba ballatana Tayi Fatan zai iya karban wani abu Daga wajenta ba.
Ganin Tabaran nasu yayi yawa ne yasa Ta kalli Mansur Tana Fadin"Mansur ko na Jira ku a falo ne..! mansur Dake Lallashin Diza Kamar yayi kuka yace"A"a Anty Rumana taimaka ki Dubamin ita don Allah.."Mirmishi ta saki kafin Tace"Shikenan zan Dubata..Ammh sai ka dan bamu Waje.."Wata uwar Harara Diza ta banka mata ta gefen ido Shi kuwa Mansur da Sauri ya Kwantar da Diza saman Filo ya Sauko Daga kan gadon yana Fadin"Shikenan in kina Bukatar wani abu ina Falo.."Daga haka ya fice bayan ya kalli Diza yana Fadin"Plz My Firstlady ki bari ta Dubamin ke..Tunda aikinta ne.."ko kallonsa Diza Batayi aranta kawai Allah ya isa take yi na Cutar ta da yayi yagama Tona mata asirinta wajen Rumana.

Bayan Fitan mansur Rumana ta Dade Tsaye ta rasa ta ina Zata Fara ganin Dizan ta nuna kamar bata ganeta ba,Ganin Tsayuwa ba nata bane yasa ta karisa gareta Tana Fadin"Sannu Diza..Zaki iya tashi..? Diza da kanta ke gefe Ta muskuta bata ce komai ba Sai Rumana taji ta Raina kanta ammh Bata Dandara ba ta kara Cemata"Sannu..Ki Daure ki Tashi..Muje Tiolet na Hada,miki Ruwa mai Zafi ki Shiga ki gasa Jikin ki.."Sai Lokacin Diza ta waigo da Fuskarta ba Annuri tace cikin Masifa.."Me kike son gani ne.? Tsiraicina ko.? To bani da kaya ajikina Taya zan mike agabanki kina kallona ina Kallon ki.."
Ta karishe Fada ta wani Tsume Fuska Rumana Taja da baya Tana Fadin"Kiyi hakuri ban sani bane.."Daga haka ta isa ga wardrope dinta ta Bude tana Neman mata Zani bata samu ba sai wata Doguwar Riga bata da Nauyi sosai ita ta Dauko mata ta Ijiye mata nan gefen gado Tana Fadin"Gashi ki tashi ki saka..Bari naje na Hada Miki Ruwan Zafin.."Daga haka ta Tura Kofar Tiolet din ta Shiga Diza ta rakata da Harara Lokaci Daya da jan wani Dogon Tsaki Duk Rumana na jinta bata Juyo ba Mirmishi Takaichi kawai tayi ta karisa Cikin Katon Toilet ta Fara Tara ma Diza Ruwan Zafi a babban Jacuzzin dake Bayin Sai da ta Daidaita Ruwan Zafi yadda zai gasa ma Diza jiki kana Ta Fito Tana Gyara Hannun Hijabinta ta iskeDiza Ta Rarrafa ta Mike ta Saka wannan Rigar tana Dafe da Bango Rumana na Fitowa Ta Ganta sai ta bata Hanya Tana Fadin"Kada ki Surka ruwan..Ki gasa Jikin ki ahaka..In son samu ne ki yi Ruwa uku kana kiyi wanka Daga baya.."Tak Diza Bata Ce mata ba ta Wuce ta Shiga Cikin Tiolet Tana jij kamar Bakinciki zai kasheta Lokaci Daya ta Rufo kofar Tiolet din a Fusace Rumana ta Rakata da ido Domin ta Daina mamakin Sauyawar Dizan gareta sai dai Abu Daya yake bata mamaki Kuma takeson Taji Menene yasa Dizan ta Chanza mata..? Shine Abun Tambayan.

Ganin Duk Zanin gadon ya baci Da Jini yasa ta Tattarashi Ta Cireshi Gefe ta Bude Wardrope din Diza ta Dauko wani Sabon Zanin gado Ta Shimfida Mata ta gyara mata gadon Tsaf wanda ya baci kuma ta ijiyeshi nan gefr in Diza ta Fito zata Shiga Tiolet din ta Wanke inda ya baci Duk da bazata iya wankewa Duka ba Fita Falo Tayi ta samu Mansur Zaune ya Zabga Tagumi,Yana ganinta ya mike yana Tambayanta lafiya,Nan Rumana tace yaje ya Siyo ma Diza mganin pain killer ita kuma Zata shiga Kitchen ta sama mata Ruwan Zafi tasha Tea Hanjinta ya warware,Mansur bai Tsaya Gaddama ba ya Zura aguje ya Fita Rumana na mai Dariya sai gashi ya Dawo bai Dauki key din Mota ba da kudi sai da ya koma Cikin Bedroom din ya Dauka Har Lokacin Diza bata Fito ba,Da gudu Sauri Sauri ya Shiga Motarsa ya bata Wuta yayi Hon megadi ya Budemai Kofa ya Fice Mastur na ganin Fitarsa Domin yana Jikin Window yana kallon Shashen nasu Mansur hankalinsa ya kasa kwanciya da Mansur ya Fito da Sauri ya Koma sai da yaji kamar Zuciyarsa Zata Buga sai gashi kuma ya kara Fitowa ya Shiga Mota ya Fita Tuni Mastur yaji kamar kasa bazata iya Daukansa ba komawa yayi ya zauma yana Dafe da kansa.

Ita kuwa Rumana Kitchen ta Shiga ta Dora Ruwan Zafi a gas bayan yayi Zafi ta kashe ta samu wani mug ta Hadama Diza Shayi ta Dauka ta Shigar mata Dashi Ciki ta iske ta Fito Har taSaka wata Doguwar Rigar atamfa Tana Zaune Da ta bata Tea din Bata ki Karba ba Domin Tana Jin yunwa ta karba Rumanan ta Bita da sannu kana ta kwashi Zanin gadon Daya baci ta shiga Dashi Tiolet yayi girma da yawa bazata iya wankewa ba sai kawai ta Dan Taran wajen da Jini ya bata ta wankeshi kana ta Jefashi Cikin Kwandon kayan wanki Tana Cikin Tiolet din taji shigowar Mansur yana Tambayanta Diza na Zaune na shan Tea kala bata ce mai ba sai ga Rumana ta Fito ya Mika mata mganin ta Karba ta gani kafin ta maidamai Tana Fadin"Ka balla Biyu ka bata tasha..Kuma ya kamata Taci wani abinci mai Ruwa Ruwa haka.."Mansur ya karba yana Fadin"Ok..To yanzu ya zamu yi..?kafim ma Rumana Tayi mgana Diza tace"Bana jin cin komai..Anjuma Mommy Zata aiko da Breakafaat zan kirata na gayamata abunda nake so Zata Dafo ta aiko Min dashi..Nagode.."Daga haka ta Mikama Mansur hannu ya Bata mganin Tasha ta kora da Tea Kafin ta mikamai Mug din ta koma ta kwanta Tana Kauda kanta Rumana bata Damu ba Tace"Shikenan..Allah kara sauki.."Mansur yace"Mungode Anty Rumana..Muje na rakaki Gida kada ya Mastur yaga kin Dade.."
Rumana ta wuce Tana Fadin"Ahaba ba komai.."Da Wani Hararan Tara saura kwata Diza ta rakasu Dukkansu suna Fita ta Saki Tsaki Afili Ta Furta"Rubbish..."

Suna zuwa Kofar Apartment dinsu Rumana ta waigo Tana Fadin"Ka koma Mansur..Kaje ka kula da Diza.."Kai ya gyada mata yana Fadin"Ok..anjuma zan Shigo..Mungode.."Bata ce komai ba illah Mirmishi ta Tura Kofa ta Shiga shi kuma ya Juya Abun mamaki Mastur na Zaune afalon yana ganin Shigowarta ya Dago da Idanuwansa da suka Sauya Launi ya kalleta sau Daya ya kauda ita kuma Sai Ta Saci kallonsa kafin ta Dauke Kanta itama Tataka zuwa Dakinta Kamar bazai yi mgana ba sai kuma ya kasa abun nacin Ransa Dakyar taji sanda yace"Ya take..?

Da mamaki ta waigo Tana Fadin"Ita wa..?bai kalleta ba illah Mikewa da yayi yana Fadin"Wa kika je Dubawa..?yafada yana Takawa Zuwa Gabanta sai da ta tsorata Tunaninta ko wani abu zai mata sai kawai Taga yayi kwana zuwa Dakinsa Miyau ta Hadiye Tana Fadin"Taji Sauki..."Bata san ko yaji ko bai bai ji ba Yadai Shige ya barta nan tsaye Jikinta ba kwari ta Shige Bedroom dinta Wanka ta Fada Tana Jin Jikinta Duk ta gaji Ta Dade batayi wani Dogon aiki ba sai yau,Bayan ta fito wanka ta Shirya Cikin Leshinta mai kyau Riga da Zani ta kashe Dauri Taji Knooking din Kofa Tasan Direban Gidan Mommy ne da Sauri Ta fito Falo ta karisa bakin Kofa ta Budesuka gaisa Kana ta amshi kwandon abincin ta koma Ta Dauko mai Na jiya Da Daddare ta bashi ta maida kofarta ta Rufe Kichen Ta Nufa Dashi ta Duba Taga Harda Ferfesun kayan Ciki,Aranta kawai Taji Wanda Diza tace ayo mata ne Duk da Ranar da suka Fara kwana agidan Taga cikin kayan karyawa Harda Ferfesun kayan Ciki Daga Ranar dai bata kara gani ba sai yau,Cikin Zumudi ta Zuba Filet sai Tea Data Hada ta Dawo Falo Tana ci tana Hadawa da Ruwan Tea din Hankalinta kwance.

Bangaran Diza ma Mansur ne ke ta Fama da ita kan taci Tunda ita ta Kira Mommy tace tayo mata Ferfesun kayan Cikin Tunda Mommy taji Diza na Fadan haka Cikin Shagwaba tasan Yarta ta shiga kwaryan manya da kanta Tatashi Tayi Ferfesun Shine ta Diban ma Diza Sauran ta saka ma su Rumana Mommy kam sai Godiya Hakkin abincin Sati Dayanan yana Wuyan su Hajja ne ammh ita ta Dauke hakan gabadaya Saboda an Riga an Zama Daya bangaran abinci su Rumana da Da ake dawowa dashi Ba"a wani ci da yawa ba Bata yi wani mamaki Sanin Mastur bamai cin abinci bane,Rumana kuma sai ta Dauka Mtsayin Amare Kila kayan kwalama suke Fita suci Gwara nasu Dizqa sukan ci suma bada wani yawa ba Hakan bai Dameta ba Sha"anin yara ne bai kamata kana Babba ka Dinga katsaladan va

Diza Ta sha shagwaba da Tabara Mansur na Biye mata sai da taci Ferfesun sosai ta Hada da Lemo kana Ta kwanta barci ya kwasheta sai Lokacin yayi wanka ya sauya kaya yaci Abinci ya samu yar Natsuwa Falo ya Fita ya Fara Bin bayan Kirayen Kirayen Daya rasa a wayarsa kan dai Siyasa ce Domin Saura Wata Biyu Zabe abubuwa sun karato yau ma suna da wani Taro Saboda Rashin Lafiyan Diza ne yasa bai Fita ba sai Zuwa gobe.
Rumana kuwa chan da Rana Bayan Sallar Azahar Ta shiga Shashen su Diza ta iske Mansur afalo ya leka mata ita yace Tana Barci sai ta koma Tace Zata Dawo anjuma Tana Komawa Ta ci karo Mastur ya Fito da key din Mota yau din yasha Tea kuma Taga yaci Ferfesun aranta Tace Daka rika zama da yunwa Da aadawo Lafiya ta rakashi bata sani ba ko yaji ko bai bai ji ba ya Dai Fice Tana jinsa ya Dade a Haraban gidan kafin Taji knooking din Kofa Tana Zuwa Taga Mansur ne nan yake Fadamata Zasu je gida shi da Ya Mastur ta shiga ta Zauna da Diza tace bakomai bari ta Sanyo Mayafi Ciki ta koma ta Dauko mayafi da wayarta ta Fito Bayan ta Rufo kofar Shashen nata ita dai Ta Shige Barayin Diza bata san Yaushe suka bar gidan ba.

Ta leka Diza Taga Tana Barci sai ta Dawo Falo ta zauna tana Latsa wayarta Umma ta kira ta mata mganar Motarta nan take Fadamata Dama sun yi mgana da Abba yace Direba zai kawo mata,Tunda Sabbin Motocinsu nasu basu Riga sun zo ba ita kuma ga Dawaniyar zuwa Wajen aiki,Sun Dade suna mgana da Umma kafin suyi Sallama Daganan kan kujeran ta mike sai barci bata tashi ba sai 4pm Ta Farka Tana mika agogon wayarta ta Duba Taga Lokaci yaja Dole ta Mike takara Leka Diza Taga bata akan gadon Sai Tayi Tunanin Tana Tiolet ne itama sai kawai ta kwashi Wayarta da mayafinta ta koma Barayinta Tayi sallah ta koma Bangaran Diza kenan sai ga Abincin an kawo musu Duka ta karba nata dana Diza nan take cema Direban yace ma Mommy ta bari sai gobe wannan Duk ya Ishesu ya amsa da Toh Na Diza nan Falo ta ijiye musu ita kuma nata takai Shashenta cikin Kitchen bata wani jin yunwa sai an juma Tana komawa Shashen Diza Ta ganta ta Fito Falo Tana ta waya sai ta Zauna tana Jiranta Daga yanayin wayar Tagane daga Catering dinta ne sai Fada take Ta Dade kafin ta Gama wayar ta Juyo Tana kallon Rumana Dakyar tace mata Sannu Domin Dazu Datashi ta Leko Falon ta ganta Tana Barci tasan aikin Mansur ne kuma ya barmata Note zasu je Gida Inna karime Zata tafi bata samu Tafiya baWashagarin Datace ba, ga Rumana nan Zata Taya ta Zama.
Nan Rumanata gaisheta da Jiki ta amsa kamar bata so Itama kujera ta samu ta zauma Tana wani Bata rai kamar bata san Rumana ba,Rumana Har tayin Abincinta tayi mata tace ko ta Zubo mata,tace ta koshi bata bukata Haka suka Zauna Dugum Dugum kamar Basu Taba Hada wani Danganta ba,Diza dai sai amsa waya take yi Rumana kuma tana ta karatu a wayarta Tunda Taga yanayin Dizan sai taja Girmanta bata son Tatafi Mansur yaji ba Dadi Bata koma Shashenta ba sai Da aka kira sallar mangariba kana tayi mata sallamanta Tatafi kuma Bayan takoma tayi wanka Ta yi sallar sai ta Dawo ta Tambayeta Tana jin wani abu..? Ta na Yamutsa Fuska Diza tace ta Gode Ita babu abunda ke Damunta Jim haka yasa Rumana Tayi mata sallama ta koma Barayinta Tana Tunanin Wani irin Laifi Tayi ma Diza da Zafi haka Data tsaneta..? Abinci ta Diba taji Fride rice wanda yaji Hanta ta Hada da Lemo ta Shige Cikin Dakinta Bayan tayi sallar Isha"i ta saka kayan Barci ta Sanya Glass dinta ta Jawo Syatem dinta bata Dade Tana aiki ba Taji barcita Tattara komai ta Ijiye ta kwanta Sai barci ,bata san Lokacin da suka Dawo ba sai da Safe Bayan ta gama Abubuwan da Zatayi ta karya Ta Shiga Barayin Diza Ta gaisheta ta isketa taji Sauki suna Zaune kan Dining ita da Mansur suna karyawa Mansur nata mata Godiya yace jiya sun Dawo ya Shigo Ya Mastur ya leka ta Tana Barci Mirmishi Tayi tace Barci ne ya kwasheta da wuri,Bata wani jima ba Tayi musu Sallama ta koma Barayinta Bata dai ji Motsin Mastur ba Bata wani bi ta kansa ba ta koma Dakinta.






*Ki biya ki karanta Cikin Salama Mace mai aji bata jiran Abun Sata..Mallakan komai nata take yi 09069067488*



*Janafty...*
1/1/22, 18:54 - Maryam Badmsi: *SS...23*


"Tana Cikin aiki Bisa System dinta kiran Umma ya Shigo wayarta Bayan ta Dauka sun gaisa take Tambayanta Tana Bukatar wani abu ne ga Direban Abbanta zai Kawo mata Motar ta yau Cikin Farinciki tace bata Bukatar komai sai Kayan Girki na Kamshi Wanda Daman Sunyi mgana da Umman Tace ai tabama Bashi nan Rumana tace ma Umma ta Duba Dakinta Cikin karamar Dirowarta akwai Novels Dinta Datake karantawa na Turancin Don Allah ta bada akawo mata Umma tace Shikenan Zata Bashi Suka Rabu bayan Umma ta Shaida mata ta Gidan Daddy zai Sauka Kana Za"a kawosa Gidansu nan zai kwana sai gobe zai Shiga Motar Haya ya koma Chan Sokoto.

Tunda Rumana sukayi waya da Umma tasamu kanta Cikin Tsananin Farimciki ko bakomai Zata koma aikinta Ranar Monday Ga kuma Novels Dinta da Za"a kawomata Zata Rage zaman kadaicin Datake Fama Dashi Sannan Tana so ta Fara Girki Da kanta ko bakomai Girki wajen Macen Tamkar wani abu ne Dake Rage mata kewa da Zaman Banza.
Tattara System din Tayi ta ijiye ta Fito Falo Ba kowa Mastur yana Ciki bataji Motsinsa ba,Kitchen ta Shiga Ta Fara Duba Store Shake da Kayan Abinci Nau"i Nau'i SaiDai Fridge din Kichen din Babu Kayan Cefene,Kai kawai ta Girgiza Tana Tunanin ta wata Hanya Zata Shaidama Mastur Tana Bukatar kayan Cefane Zata Fara Girki.? Bata so yaga Kamar Zata Zage da yawa ne ga Mommy tana aiko musu Dashi gani Tayi Gwara Ta Fara Ko Mommy ta Huta da Ita da Direban Dake Faman Zarya Tsakanin Hanwa da Loscost.
Gyara Kitchen din Tayi Duk da bai yi komai ba ta goge Shi Tas yana kyalli sai kuma ta Wanke Filet da Kofin Datayi amfani Dashi Daman aikinta kenan In Taci Abinci Zata wanke Saboda bata kaunar kazanta in kuma Shi Mastur din ne yaci wani abu ko kuma yasha Tea Yana barin Falon Zata Fita Zuwa Kitchen ta wanke komai ta maidashi ma"adansa..
Sai da tagama komai ta koma Daki ta kwanta Batare Data san me Zatayi ba Bata san Zaman Falo ne,saboda bata kaunar Haduwa Da Mastur yana sa Taji Duk ta Muzanta Tariga ta gama Sadaukarwa nata irin Salon Auran kenan wanda Har yau bazata Dora komai akai ba.

Barcin Daya kwasheta Sai wajen Azahar ta Farka ta Fada Tiolet Tayi alwala Tazo Tayi sallah Ta gama kenan Taji Knooking din Kofar Bedroom dinta da Hijabin Sallah ta isa ga Kofar ta Bude Suka ci karo da juna ita da Mastur Tunda yayi mata kallo Daya bai kara ba Yana Sanye Cikin Wani Farin yadi Riga da wando Hannayensa Duka Biyu acikin Aljihun Wandonsa Tana mamakinsa ko Gajiya bayayi Kawai juyawa yayi Yana Fadin"Kina da Bako..!
Daga haka ya koma Saman Daya Daga Cikin kujerun Falon ya Zauna yana maida Hankalinsa ga Talabijin din Cikin Tashar Sunna Tv,Mamaki ya kamata Domin bata san yaushe ya hada kayan kallon ba Tana Kokarin Tambayansa Taga kawai ya juya ya barta Tsaye Komawa Ciki Tayi Tana Tunanin Bako..? Daga ina Domin Sam ta manta da mganar su da Umma Tana Kokarin Sauya mayafi ne taji wayarta na kara Tana Dubawa Taga Umma ne Bayan ta Dauka sun gaisa nan Umma ke Tambayanta Auwalu Ya iso kuwa..? Sai Lokacin ta Tuna tace eh Tana ga ya iso Domin ance mata Tana da bako Umma tace Shikenan in ya iso Cikin Sakon nan akwai Dambun Nama da pepe chicken sai Yaji Dakakke Roba Biyu Dambun Nama Babba da karami ne a botiki ta Dauki Babban Ta bama Diza karamin haka ma Yajin da Pepe din din Rumana tace Insha Allahu suka Rabu bayan Tayi mata Godiya Acikin Ranta tana mai Farinciki Domin Dambun Naman da pepe din Duka Fovrite dinta ne.

Sai da Saka wani Babban Mayafi ta Rufe Jikinta kana ta Fito Falon,Mastur na nan Zaune inda ta barsa sai dai wannan karon waya yakeyi Wucesa Tayi Batare Data kallesa ba ta Fita zuwa Haraban Gidan taci karo da Motarta Auwalu Direba na Jikin ne jikinta Shi da Direban Daddy yana ganin ta Fito ya washe baki ya Duka Har Kasa yana gaisheta ta amsa Tana Fadin"Sannu Auwalu ya Hanya..? Ya mike yana Fadin"Alhamdulillah Karamar Hajiya..Juma da Goggo Jummai Suna gaisheki.."
Rumana Tayi Mirmishi Tana Fadin"Allah Sarki Juma ina amsawa. zan kira Umma ta bama Goggo Jummai mugaisa Ya kafarta Taji Sauki ko..? Auwalu Direba yace"Taji Dama Sosai Karamar Hajiya.."Rumana ta gyada kai Tana Fadin"Allah kara lafiya.."Suka amsa da Ameen key dim Motar ya mika mata ta karba Lokaci Daya yana Fadin"Akwai kuma Sako da Hajiya Tabada akawo Miki "Cikin Sakin Fuska Tace"Ok..Ka Shigo Min Dashi Auwalu..Da Sauri yace Tom Karamar Hajiya nan ta Tsaya suka gaisa da Direban Daddy kafin ta Koma Ciki Daman Tuni Auwalu ya Fito da kayan Daga Cikin Motar suka Dauka suka bi bayanta.
Da Sallama ta Shiga Falon,suna bin Bayanta Auwalu Dauke da wata katuwar leda sai Direban Daddy Dake dauke da karamar Ledan suka Shiga suma da Sallama Daidai Lokacin da Mastur ya gama wayar Rumana bata tsaya ba Kitchen ta Shiga ta Dauko Ruwa da Kofuna ta Fito ta iskesu Tsaye Bayan sun ijiye Kayan Hannuwansa Center Table din Dake Tsakiyar Falon taja ta Dora Musu Ruwan da Kofunan Tana Fadin"Ya kuka Tsaya..! Don Allah ku Zauna ku sha Ruwa..!
Tafada Lokaci Daya Tana kallon Mastur Da Hankalinsa ke kan wayarsa akasa suka Zauna Ta Mika musu Ruwan suka karba suna Godiya Ganin Mastur din yaki mgana yasa ta Sanyaya Murya Tana fadin"Auwalu ne Direban Abba Daga Sokoto yake Sako ya kawo min.."
Harta Fidda rai da zai ce wani abu Sai taji yace"Nasani.."Daga haka kawai ya Mike Lokaci Daya yana kallon Auwalu Direba daya gama Shan Ruwa yace"Ammh sai gobe Zaka koma ko Auwalu..? Auwalu yace"Eh sai gobe Zan koma Yallabai.."Yafada Cikin Ladabi Bai kara mgana ba ya Tattara Wayoyinsa ya Nufi Dakin Daya zaba yazama mallakinsa sai Lokacin ta Tuna ai Mastur yasan Auwalu Direba Tunda yazauna agidansu Sai daya Shige kana ta Sauke ajiyan Zuciya Ledojin taKwasa Zuwa Ciki Tana Fitowa sukace Zasu Tafi Nan sukayi Sallama Ta bashi 5k cikin kudinta Data tazo dashi,Cikin kudin Sadakinta ne wanda ita Abba ya Damkamawa da Hannunta.
Bayan sun Tafi ne ta Bude Sakon Kamar dai yadda Umma ta Tsara ne Sai Novels dinta data kwashe taZube Cikin Side Drower din gadon Sakon kuma ta Dauki nata Kayan kamshin Girki kuma Spicess,Itama Harda Diza ta Dauki Nata takai Kichen na Diza kumaTace sai Tayi La"asar ZataShiga ta kara Dubata sai takai mata,Ferfesun kayan Cikin nan ta kara ci tasha Ruwa ta Dauki Daya Daga Cikin Novels dinta ta Fara karantawa Sallar La"asae ya tada ita Ta tashi Tayi wanka ta Sauya kaya tayi sallah Kana ta Sanya Mayafinta ta Dauki Sakon Diza Lokacin Data Fito Falo suka kusa yin karo da Juna ita da Mastur ya Fito Daga Kichen Dauke daMug Baya Taja Tana Kara Rike ledan Hannunta Sama da kasa ya kalleta batare Da yayi mgana ba ya Rabata ya wuce Zuwa Saman kujera Jikinta sai yayi sanyi Dakyar ta Taka Zuwa Tsakiyar Falon Tana Tunanin me Zata ce...Shi kuma Sai yayi kamar bai ganta ba yana Kurban Coffea din Dake hannunsa Dayan Hannun kuma yana Sarrafa Remot Dashi..

Gyaran Murya Tayi sai ya Dago Yana kallonta Fuskarsa ba Fara"a Cikin Dakiya tace"Zan leka Diza..Na Kara dubata kana na Kai mata sakon da Umma ta aiko mana Dashi.."Sai Da Tayi Tunanin Ta Muzanta kana Taji yace"Adawo lafiya.."Kasa kasa Kamar baya son mgana Ita dai bata kara wani Tsayuwa ba tawuce da Sauri yaBita da kallo Yana wani Tunani Saurin kauda kansa yayi kamar yaga wani abu kamar Rumann ba Matarsa bace.
Rumana kuwa ashashen Diza Ta Dade Tanasallama afalo suna Ciki basu Jita basai chan Mansur ya Fito ganin itace yasa yawashe baki sukagaisa Tace tazo ta kara Duba Diza ne sai kuma Sako da Ummata aiko Dashi Mansur yace Diza tana Sallar bari ta Fito nan ya Zauna sunata Hira da Rumana nan yake cemata ai ya Fito Dazu yaga Mota sai Mastur yakecemai Motarta ce Rumana Tayi mamaki Ashe yasan Za"a kawomata Mota Abunda batasani ba Abba ya Kira Shi ya gayamai Auwlu Direba na Tafe acikin Hiranne takegayamai Monday Zata koma Bakin aikinta Shiyasa Mansur yace Ai Shima Mastur Monday din Zai koma Porthercourt,Suna Cikin mganar Sai Diza taFito Tana Wani Yauki Tana Sanye da wata Riga Mai Shara Shara Tana Fitowa Mansur ya Taso ya Tarota ita kuma tana Narkemai Rumana Kauda Kanta Tayi kawai Domin ta lura wasu abubuwan kamar dagayya Diza ke mata su.
Bayan ta zauna sungaisa ta Tambayeta Jikinta Tace da Sauki Sai ta Turaa mata Ledan tace inji Umma Diza Bata Dauki Ledan ba Tace Angode kawai ba Rumana ba Hatta Mansur yaji wani iri Ganin haka yaja ledan yana Budewa Cikin Murna ganin su Dambun Nama da Pepe da Akayi Rapping dinsa ya Rika Nuna ma Diza yana Fadin"Kalli ki gani..Eh kefa yar gatan Mommy ce da Umma.."Yafada yana Lakutan Kumatunta Ko Dariya batayi ba Sai ma yamutsa Fuska Datayi ta Mike Tana Fadin"Wai ni ina ka sakamin Rigar nan ne..? Ciki   mamaki yace"Wata Riga..!?
Hanyar Bedroom dinsu ta kama Tana Fadin"Nidai kazo ka Dubamim.."tafada Cikkin Shagwaba Rumana sai taji ta Raina kanta da Sauri ta Mike Tana Fadin"Bari naje..Sai da Safe.."Mansur ya Mike yana fadin"Tun yanzu Anty mu..? Toh Allah taahe mu Lafiya sai gobe ki gaidamin da Yallabai ya Mastur.."Dakyar ta iya mai Mirmishin yake har Bakin Haraban Shashensu ya Rakota kana ya Koma ita kumata karisa Shashensu Inda ta Bar Mastur nan tagansa Ayanzu dinma Waya yake yi Bata Bukatar Wani abu kuma Da Sauri ta wucesa Zuwa Dakimta Tana Kokuwa da Bacin Ranta Tana Shiga Daki ta Danna ma Kofa Key sai da Mastur Dake waya ya waigo Yana Bin kofar da kallon Mamaki ganin Bai Dameshiba yasa ya Zakuda kafada ya Cigaba da Wayarsa.

Ita kuwa Rumana Tana Shiga Dakin Ta Fada Kan gado Tana Jin kamar ta Fashe da kuka na Cin Zarafin da Diza Take mata Me tayimata..?ita dai aSaninta Mgana ma Mai tsawo bata taba Shiga Tsakaninsu ba..? To wannan karan Tsanan Daga ita..?ta kasa gano bakin Zaran ta kuma kasa gano Dalilin wannan kiyayyar da Dizata Dora mata ga Gaira ba Dalili,Ta rasa gane Daga ina Abun yafara ballatana ta kamo Bakin Zaran ammh Tabbas Lamarin ya Dameta matuka Da irin wannan Wulakancin da Jizganta da Diza take ta girmeta ammh Haka ta Sauke kanta Tana Binta Tana mata yadda taga Dama.
Ta Dade Tana saka tana warwara,ammh bata samu Mafita ba Sai dai tayi ma kanta alkawarin Tabbas Zataja Baya da Diza Kodomin Tsira da Martabarta.
Sai Dare Mommy tasake aiko Musu da abinci,Tuwon Semo Miyar Kubewa Danya ita bata wani ci ba Mastur dai Dayake Mutuminsa ne Tuwo yaci Sosai ita Tun Da ta shiga Dakinta bata kara Fitowa ba sai Washegari Shima ta Fito ne Tana son Tayi mgana da Mastur ta Nuna mai kayan da Umma ta aiko Musu Dashi da kuma mganar Cefene.

Kallo Ta kunna ta Saka Tashar Zeeword Tana kallo Tana Tsumayin Fitowarsa Gefe Daya,kuma Tana latsa Wayarta Gajiya Tayi Tatashi ta Koma Daki Ta Dauko Dambun Naman nan da Pepe chicken takai Kichen ta Dauki Filet ta Dibi Dambun Naman da Pepe din Breakafast din yau tun Safe Mommy ta aiko Musu Dashi Tea kadai Tasha ta Fito Falon kenan Sai ga Mastur ya Fito cikin Jallabiyansa mai Ruwan kasa Ramkwafawa Tayi Tana gaisheshi ya amsa Yana Wuceta Yayi Zuwa Kitchen Ruwa mai Sanyi ya Dauko Yazo zai Koma Daki Rumana Dake Zaune Tace"Armm..!

Tayi gyaran Murya Bai waigo ba Illah ya Tsaya Cak alamun yana Sauraranta Mikewa Tayi Tana Fadin"Dama Dambun Nama ne Da Pepe Chicken Ummata aiko Mana dashi.."Yana Tsayen Taji yace"I know.."Kallonsa kawai Take Tana mamakinsa komai sai yace yasani..? Kokarin Shigewa Dakinsa yake Tayi Saurin Cewa"Don Allah ina son Kayan Cefene Ina so na Fara Girki da kaina..Saboda Dawainiyar da Mommy take Damu yayi yawa.."

Sai da Tagama mganarta Kana ya kada kai ya Shige Dakin ya maida Kofa Batare da yayi mata Wata mgana ba Komawa tayi ta Zauna Aranta Tana ayyyana Haka Matan Miskilai suke Fama Bata sani ba Allah ya gani itama Miskila ce Mara son Hayaniya ammh Mastur ya Damata ya Shanyeta.
Ita dai bata kara jin Motsinsa ba Har tagaji da kallon Bayan ta Cinye Abunda ta zubo ta,koma Daki ta Dauki Novel dinta tacigaba da karantawa wayar Umma ce ma ta Katseta inda take gayamata Auwalu har ya kamo Hanya nan ma take gayamata Mommy ta Kirata Tana ta yi mata Godiya ita da Hajja ashe Hardasu ta aiko ma Sakon Bata sani ba Umma Har kara Tambayanta Tayi ta Aiko ma da Diza nata Sakon Tace eh Ammh Bata yarda Ta gayamata Yadda Diza Ta karbi Sakon ba Har sukayi Sallama.
Batayi Gigin komawa Shashen Diza ba ta riga ta Daukan ma kanta alkawarin kama Girmanta Insha Allahu ai tana gaba da ita ba ita ya kamata ta Dinga Binta ba Ita ya kamata ta Bita ammh Ko Kofar Shashenta ai Bata taba Takowa ba sai ita Datake ijiye Girmanta Tana Binta Tanamata Wulakanci Bazata Dauka ba ta Riga Tagama Daukan iya Abunda Zata iya Dauka.

Tana Dakinta Taji Fitar Mastur Bai Dawo ba sai Da Daddare Shi da Mansur suka Shigo Mansur yaShigo Da kayan Cefane Leda Leda yakai Kitchen Lokacin Tana Dakinta Ta Idar da Sallar Isha"i Tana Ji Mansur na Tambayanta Taki Fitowa Domin Batasan mgana ba Sai da tajiShuru alaman ya Fita kana ta Fito Kitchen din Ta Shiga Taga Ledoji Ta Duba Taga su Kwai ne da Dankalin Turawa sai kayan Miya sai Su Cabej green beans,Carrot da Sauran Kayan Girki nan da nan ta Cicciresu a ledata Sakasu Cikin Babban Fridge din Dake Kitchen din Taga ma Harda Nama daKifi ya Siyo Karamin Fridge din kuma kayan Sanyi ne aciki Bayan Tagama ta gyara Kichen din Ta kai Dattin Dusbin din Dake Wajen kana ta Fito Falo nan Taga Mastur Zaune wannan karon yana aiki Bisa System Dinsa ne Gaisheshi Tayi ya amsa da Lafiya lau Daganan ya Cigaba da aikinsa Dakinta takoma Tayi Shirin Barci Domin Tagaji yau ko Barcin Rana bata samu Damar yiba Tana kwanciya kuma sai Barci.

Washegari ta kama Lahadi Rumana Tatashi da Shiryan Shiryan ZUwa wajen aiki Gobe Shiyasa Take Cikin Farinciki Ta gama Shirya kayanta Duka acikin Wardropr Tun Safe Bayan Ta gama Hada Breakfast Ruwan Tea ta Dafa sai Buredi da kwai sai Plantai Kan Dinnig ta Jera komai Bayan Tagama cin nata ita dai ta Fita Hakkinsa koda bazai ci ba Mommy kuma Ita da kanta ta Kirata awaya bayan sun gaisa tace mata Ta bar kawo musu Abinci Hakanan Zata dinga girkawa da kanta Mommy tace Har Zata Fara Girki Da Sauri haka..!? Rumana tace bakomai Tana so Ta Dinga yi Da kanta Mommy Taji Dadin Tunanin Rumanan tace Shikenan Hakan Nada kyau Daganan sukayi Sallama Mommy Tana Sha"awar Rumana yarinya ce mai kwazo Ta kowani Fanni Diza sunyi mgana Tace Mansur yayo Cefane Itama Tana so taFara Girki Hamdala Tayi ma Sarki Allah Tare da Fatan Zaman Lafiya aTsakanin Ma"auratan Har Gaban Abada.

Bata san yaushe ya Fito Har ya Sha Tea din ba,Sai Plantain din Taga yaci kadan Mamaki ya kamata Bata Taba Zaton Zai Taba wanu abu ba Kwashe komai Tayi ta maida Kitchen tayi wanke wanke wani Karsashi take Ci Gre ing din Kayan Miya Tayi Ta Dora Girki Farar Shinkafa Miyar Kifa Tayi Cikin kayan da Ummata Aiko mata akwai Kayan Hadim Lemuka sai ta Hada Lemon kankana Ta saka a Fridge,Sai ta gyara Kitchen din kana taje Tayi wanka Tayi sallah Tazo Taci Abincin Tagama kenan sai ga Mastur ya Fito Cikin Shirin Fita Sanye Cikin Riga da wando Black and White Na kamfanin Armani Sai key din Motarsa Dake Hannunsa Rankwafawa Tayi ta Gaisheshi ya amsa yana kallonta Tashi Tayi Daga Saman kujeran Dinning din Tana Tattara Filet din Dataci Abinci dashi Kai Tsaye Taji yace"Anjuma ki Shirya zamu je Ki gaida su Hajja.."

Daga Haka kawai ya kada kai ya Fice Da kallo ta Bisa kafin ta gyada kai kawai ta wuce Kitchen Yanzu kam ta Daina Damuwa da Sha"anin Mastur,Ta Fahimci ya Wuce yadda Take Tunani
Abunda   ke bata mamaki Bashi yaje ya Nemi Auranta da kansa ba..? Ko kuwa Domin ta Fara Bayyanamai Sirrin Zuciyarta ne ta Chanchanci haka ita dai ta kasa Gane masa,Bayan Fitarsa Sai Tayi Tunanin Ta Diban mai Dambun Naman nan yaTafi Dashi pepe din kuma tasaka Cikin Fridge kada ya Lalace Wata Karamar Roba Ta samu ta Diban mai Tayi Rapping dinsi sai kuma taFara Tunanin bazata je Gaidasu Hajja Hakanan ba Ta samu Leda TaDiban musu Cincin da Cake da Donut mai yawan gaskiya,Pepe  chicken din ma Ta Diban musu Fin Rabi Saboda kada ta barshi ya Lalace Tun kafin Mangariba tayiwanka Ta Shirya Tana Jiran Mastur ammh bai Dawo ba Mansur Baya nan Saboda Tun Safe Taji Tashin Mota Kodata Leka sai Taga Shine Ammh Taji Hayaniya Daga Shashen Diza Kila Tayi Baki ne,Zaune take afalo Tana kallo Har aka Kira Sallar Mangariba ta Shiga Ciki Ta idar da Sallah kenan Taji Shigowar Mota Ammh Bata ji Bude Kofar Shashenta ba Mastur yana da key Da yazo Zai Bude sai Zuwa Chan Taji Bude Kofarsa da Shigowarsa ya Shiga Dakinsa Daganan bata kara Jin Motsinsa ba Bayan kamar Minti Talatin Taji karan Wayarta Dake kan gado Mikewa Tayi ta Dauketa sai Taga Mastur ne Tana Dagawa Taji yace"Ki Fito mu Tafi.."
Daga Haka ya yanke Kiran Ajiyar rau ta Sauke kafin Ta ijiye wayar Hijabin Datayi Salla Dashi taCire ta Dauki Mayafin Leshin Dake Jikinta Kalan Golden ta Saka ta Dauki Karamar Jakarta ta Tusa wayarta Sai Flat Shoe din Data Saka ta Fito Batayi kwalliya ba Hoda kadai ta saka sai Lipstick Tana Fitowa ta Iskeshi Tsye yaJuya Baya yana Waya yana Sanye da Wata Shadda Sky Blue Dinkin Riga da wando na Zamani da Hula Kafarsa Sanye Cikin Wani Bakin Budadden Takalmi mai kyau da Tsari Ta manta da Sakonta Ta zo Gabansa Ta Tsaya Har ya gama wayar bai mata mgana ba kuma bai kalleta ba ya Wuceta Harta Fara Taku Zata Bishi ta Tuna da Abunda Zata kaima Hajja da Mommy sai ta Juya Waigowa yayi kawai yaga Bata Bayansa Cikin mamakin Ina Taje yake karema Falon kallo Sai Gata Ta Fito Daga Kichen din da leda Dakinta ta kara Shiga ta Dauko Atamfofi Guda2 din Data saka aciki Sai Kayan Kwalliya irin su Tiraran Wuta Dana Daki Wanda Zata kaima Mommy Atamfofin kuma na Hajja ne da Ayya Umma tace duk SandaZataje kada taje Hannu Rabbana ita kuma sai ta Hada musu da Zannuwa Mommy kuma tasan ko ta bata ba karba Zatayi ba Shiyasa Zata bata Turaran.
Mamaki ya kamashi Daya ganta da Leda kamar zai mata mgana sai kuma ya Fasa Shi ya Fara fitasai ita Suna Fitowa ya saka key ya Kulle Kofar Apartment din nasu Har ta Tatafi Wajen Motarsa Wacce Tata ke kusa Da nashi Taga Shi bai Taho ba Tana waigowa Taga yana Waya ne Sai Taji yana Fadin"Muna Haraba Mansur.."Sai abunda ya bata mamaki kenan Tafiyar basu kadai bane Tabbas Mansur ne ma ya Tsara ya kamata su kai su Gida su gaidasu Hajja dasu Mommy Tunda Gobe Shi Mastur Zai Koma Porthercourt Mansur Gobe Jirgi Zai Bi Zuwa Abuja Suna da wani Taro Dalilin Daya sa Mastur yace ma Rumana ta Shirya kenan.

Bata gama mamaki ba Sai ga Mansur ya Fito Shima Cikin Shigan Shadda mai Ruwan kasa Harda Hula Hannayensu Rike da Juna Shida Diza Taji Ubansu Gayu kamar Zata gasan kyau Wata Atamfa ta Saka Doguwar Riga mai kyau da yarari da gyalejta da Jakarta da Takalminta mai Tudu,Mansur ya Kulle Suma Kofar Shashensu kafin su kariso Mansur na Fadin"Yaya ayi Hakuri..Mun barku kuna Jira.."

Mastur dai bai ce komai ba kansa ya Kauda Domin baya son ganin Diza ita kuwa Shi take kallo Kafin ta isa Gabansa Rumana ce Takegaisawa da Mansur Diza kuma Sai da tazo Gaban Mastur kana Tace"Ina yini ya Mastur..! Cikin sanyin Murya Duk yadda yakai ga Dauriyansa sai da yaji Wannan muryan Har tsakar kansa Batare Daya kara mata wani kyakyawan kallo ba Yace"Lafiya.."Daga haka ya Wuceta Zuwa Motar Mansur wanda Har ya Shiga Mazaunin Direba,Shima Gaban ya Bude ya Shiga yana Kokuwa da Numfaahinsa Mansur ne ya Leko Yana Fadin"Bismillanku ku shigo mu Tafi.."Rumana Ce tayi Kokarin Tasowa Itama Diza ta kawo Sai suka Hade kallon kallon Sukayi ma Juna kafin Rumana ta Murmusa Tana Fadin"Diza ya Jikin naki..? Wlh Diza sai ta kauda kanta kawai ta Bude Murfin Mota ta Shiga Rumana bata Damu ba ta Zagaya itama ta Bude taShiga da Sallama Mansur kadai ya amsa Banda Diza da Mastur wanda ko sun amsa itadai bataji ba Ribas Mansur yayi Lokaci Daya da Hon Megadi ya wangale get din suka Fice Daga Gidan Yana Binsu da Fatan Dawowa Lafiya.


*ki biya ki karanta cikin Salama 09069067488*



*Janafty...*
1/1/22, 18:54 - Maryam Badmsi: *SS.. 24*


*Ki biya ki karanta cikin Aminci da Salama 09069067488 mace mai aji mallakan komai nata takeyi bata jiran abun sata*



"Tunda suka Dauki Hanya ba wanda yayi Mgana Tsakanin Mastur ko Diza Mansur ne  ma Ke ta Surutunsa Da Mastur wanda yayi kamar bai Jisa ba,Yana Ta fama da Zuciyarsa Domin ganin Diza kamar Fami ne ga Tabon Daya Riga ya Binne acikin ransa haka Itama Diza sai taji Gabadaya Jikinta ya Mutu Ta Madubin da Mansur yasaita ya Dinga kallonta take kallon Fuskar Mastur Daya Hade rai kamar bai Taba Dariya ba,Kallonsa Take Cikin So da kauna da wani Muradi mai Girma ayayinda Gefe Daya kuma Mansur ke aika mata da kallon kauna Tuni Wata Zuciyar ta kwabeta Data Kallo Gefen Rumana Taga Hankalinta ma yana Kan Hanya ne Tana Bin Ko"ina da kallo Saurin Ta"awizi Tayi acikin Ranta Tana Neman Gafaran Allah Hakika Bata son Mansur ammh akwai Shakuwa da Fahimtar Juna atsakaninsu Sosai In Har tace Ta taba ganin Fushin Mansur tayimai karya Mutum ne mai Dadin Mu"amala da Dadin Zama bataji mamaki ba In Taga Dimbin Magoya Bayansa a Bangaran Siyasan sa Haka Jininsa yake shi na Kowa ne karya ne kayi Mu"amala Dashi na Wuni Daya bai Shiga Ranka ba yana da Sadaukarwa kan Abunda yake so ko akanta ma Mansur yakai makura Shiyasa Bata ji Tana Nadamar Auransa ba Ko Bakomai ta auri Mai Sonta Wanda Zai Ta Hidimta  mata Har Karshen Rayuwarsa Mastur ya Riga yayi mata Nisa Nisa kuwa na Har Abada.
Ajiyar Zuciya ta Sauke Daidai Lokacin da Mansur Dake Tuki ya kusa kwashe wani mai Mashin Gabadayansu suka Furta Subhanallah.

Mastur ne ya kalli Mansur da Sauri yana Fadin"Kagani ko..? Kana chan wajen Surutunka na Fama zaka Jama kanka Damu Gabadaya.."Mansur na Dariya yace"Haba ai Normal ne..Shi ya Shigomin fa Yaya.."Mastur ya kada kai yana Fadin"Bana son jin Wata mgana Keep Quit and Drive Well.."Yafada Cikin Bada Umarni da Sauri Mansur ya Saki Sitiyari da Hannu Daya yana Fadin"Yes Sir...yallabai DCP.." ya fada yana yar Dariya Keyarsa Mastur yaDaka yana Fadin"Am i ur Mate..? Ka rainani ko..? Saboda munyi aure Rana Daya ko..? Zan kama ka ne..!
Yafada yana Rausayar Dakai Juyowa Mansur yayi yana kallon su Rumana Dake baya Cikin Muryan sangarta yace"Antynmu kina gani Mijinki ya Dakeni ko..? Kema Diza kin yi shuru yana Dukan miki Miji ko..?
Rumana Dai Mirmishi kadai tayi yayinda Diza ta dago ta sakarmai Harara Dariya yayi Domin Sanin Halinta Sosai Shi bai Dauka wani abu ba Ita kuwa Haushi ne da Takaichi ya isheta wai Antynmu to Shi da wa..? Badai da ita ba Allah ya kyauta Rumana ta zama Antynta.

Gidan su suka Fara yada Zango sun shigo Falon,Mansur ne kan gaba sai Mastur Dake Binsa a baya Sai Rumana sai Diza Dake Baya Tana Tafiya kamar ba zata tayi ba.

Dukkansu suna zaune afalon na Hajja,Baba Habibu na Zaune akan Cafet din Kuloli ne agabansa yana Cin Tuwon Semo Miyar Dan kubewa sai Hajja Dake zaune gefensa Ayya kuma Tana gefe Itama zaune a kasa Ta Mike kafarta Tana Shafa man Zafi Cikin Farinciki Suke Hiransu Sama sama Sukaji Sallaman su Mansur din.

Hajja ta Mike tana ta yi musu maraba Daman Mansur ya gayamata zasu zo ammh Tunda Taga Dare yayi sai ta Cire ran zuwansu ta Dauka sun Fasa ne

Mansur da Mastur Bayan kowannensu ya Cire Takalman kafarsa suka Nufi Baba Habibu Cikin Fara"a da Farinciki kamar yadda ya Dakata da Cin Abincin nashi ya Dago yana kallonsu Falon akwai Haske Tunda akwai Wutan lantarki.

Gefe da gefensa suka zauna suka sanyasa a Tsakiya kenan Mastur ne ya Fara gaisheshi kafin Mansur dukkansu ya amsa musu Cikin Sakin Fuska,Rumana kuwa Kasa Ta Zauna kanta a kasa Tana gaida Baba Habibu ya amsa mata Cikin Fara"a da Sakin Fuska Ayayinda Diza Dake gefenta itama ta gaishesa ya amsa Cikin Fara"a Kafin Su juya suna gaida Hajja Ayya ce Ke ta Musu Maraba Lale Rumana ta gaishe da Ayya Cikin Kunya da kawaici ta amss Tana yaba Tarbiyan Rumanan..!

Mastur ne ya Leka kulan gaban Baba Habibu Tunda yaga Tuwo sai yaji Ransa ya Biya Cikin Sanyinsa yace"Baba zan ci Tuwo.."Baba Habibu yace"wanko Hannunka kazo muci Babban Mutum.."Da jin Haka Shima Mansur ya Shagwabe Fuska yana Fadin"Nima fa Zan ci Baba.."Baba Habibu Na Dariya yace"Dukkanku ku wanko Hannayen ku kuzo muci..."

Ayya Dake gefe Tayi karaf tace"Dole kace zaka ci..Tunda Kishiyanka yace zai ci..'Tafada Tana Hararansa Mansur ya kalleta ya balla mata Harara yana Fadin"Eh din ina Ruwan ki.."Rumana sai Mirmishi take,Yayin da Hankalin Diza na kan waya Hajja kuma ta Fita Zuwa Kitchen Tsam Mastur ya Tashi ya Bita Chan Kitchen din ya isketa Tana Kokarin Kunna gas Cikin mamaki yace"Hajja me zaki yi..? Tace"Girki zan Dora ma Matan ku..Nasan kila basa cin Tuwo Gwara ma Diza Takan ci bansan Rumana ba..'Mastur yayi Mirmishi yana Fadin"Hajja kenan..Kada ki Damu.."Yafada yana Diban Ruwa a karamin Kofi Cikin wani Roba yawanke Hannunsa Hajja ta kallesa Tana Fadin"Haka Nan zasu zauna Babban Mutum..? Yana Shirun Ficewa ya Dawo kawai batare Da yayi mgana ba ya ja Hannunta suka Fito Falon duk sai su Mansur suka Bisu da kallon Sha"awa yadda ya Fito yana Rike da Hannayenta bai Direta ko"ina ba sai kan kujera yana Fadin"Ki zauna ki Huta Hajja..!
Ayya na gefe tace"Ai bata son ta Huta Megidana wani Lokacin in tayi ma Hajara Fada Halan me tace zatayi..?
Mastur na kokarin zama Gefen Baba Habibu yace"Wani girkin zata Sake yi.."Mansur yace"Girki kuma..? Bayan wannan Hajja..?

Hajja Da bataji Dadi ba Ta Raunana Murya Tana Fadin"Matan nan naku naje sama ma wani abu..Sun kawo mana Ziyara a barsu bako Ruwa.."Ayya Tace"Eh kema kin ce wani abu Hajara Akawo musu koda Ruwa ne in Hadiza yar gida ce ai Rumana kan bakuwa ce.!
Rumana Dake gefe Tayi Saurin girgiza kai Tana Fadin"A"a Ayya ni ba bakuwa bace..Nima yar gidace kamar Diza..Alhamdulillah wlh a koshe nake ban san ko Diza ba.."Diza Dake Latsan wayarta Daman Duk Haushin iyayin Rumana ya gama Isarta ko Dagowa Batayi ba Tace"Nima Am Ok.."Ayya Ta tabe baki Tana Fadin"Koma Amkake ne Ina ruwan wani da Turancinki.."Gabadaya Falon suka saka Dariya Banda Mastur Daya Natsu kawai yana cin Tuwonsa Hankalinsa kwance Hira ce ta Tsinke tsakanin Ayya da Diza Sama sama Rumana kuma na gefe sai dai ta Murmusa,Har su ka gama cin Tuwon Suka wanke Hannuwansu a wata Roba Mansur ya kwashe komai ya maida Kitchen kana ya Dawo nan Baba Habibu ya Tarasu yayi musu Nasihan Zaman Lafiya da yadda Zasu gyara zamantakewarsu Ayya ma Tayi nata Hajja dai Kunya addu"a kawai tayi musu Jikin Rumana yayi Sanyi Ballatana da Ayya tayi ta jan Hankalinsu su zauna Lafiya da juna ita da Diza alokacin ta kuduri Niyar Insha Allahu Zata samu Diza ta Tambayeta kotayi mata wani abu ne..? Domin su sami Fahimtar juna..!

Mikewa Mastur ya Farayi ganin pass 10 ya kalli Mansur bayan ya Duba agogon Fatan Dake daure a Tsitsiyan Hannunsa Ya kalli Mansur yana Fadin"Muje ko..? dare nayi..! Mansur ya mike yana Mika Lokaci Daya yana Fadin"Baba gobe fa Abuja zani Taron mu na partyn mu kila sai nayi kwana Biyu zan Dawo.."Nan Baba Habibu da Hajja Harda Ayya sukayi mai Fatan alheri Ammh Mastur na gefr bai ce komai ba Baba Habibu ne ya kalleshi yana Fadin"Babban Mutum kai yaushe ne zaka koma..?Mastur na Tsaye ya karkace kai yana Fadin"Munyi mgana jiya Baba..Gobe zan koma Insha Allahu..!

Baba Habibu yace"Anyi haka na Shafa"a ne..Allah ya kiyaye Hanya.."Dukkansu suka amsa da Ameen Ayya ce tace"Toh ita Rumanan fa..? Yashe zata koma wajen aikinta Tunda naji Alhaji na Fadin zata dawo nan da aiki.."

Mastur ya dago suka Hada ido da Rumana sai kawai ya Dauke kai ya kama Hanyar barin Falon Lokaci Daya yana Fito da wayarsa Daga aljihun gaban Rigansa ganin haka yasa Rumana ta sadda kai Tana Fadin"Gobe nima zan koma Ayya In Allah ya kaimu.."Baba Habibu yace"Allah ya kaimu Allah ya bada Sa"a..'Dukkansu suka amsa da Ameen Ameen Baba Habibu ne ya kalli Diza yana Fadin"Hadiza ke yaushe zaki koma naki aikin..?kafin tayi mgana Fit Mansur yace"Zata koma Baba..Sai na Dawo Insha Allahu..."Baba Habibu ya amsa da Cewa"Allah ya kaimu Allah ya Bada Sa"a..!
Suka amsa da Ameen Ameen Mansur ya kalli Diza yana Fadin"ku tashi muje ko..? Yafada yana gyara zaman Hulan kansa Hajja tace"Zaku shiga wajen su Hajiya kenan..? Mansur yace"Eh Hajja.."Ayya Dake gefe tace"Ku hanzarta Dare nayi..Gashi ance Gidan naku Chan Daji Yake.."Hajja na Dariya tace"Ai chan zamu kai musu ke Hutu Ayyah.."Ayya ta tabe baki Tana Fadin"Sai dai mutuwa Zata Rabamu da Zama daku Hajara.."Fadin Hakan datayi sai Jikin kowa yayi sanyi Baba Habibu ne ya katse Shurun da Fadin"Da yardan Allah Ayya..Allah yasa mu cika da kyau da Imani.."Dukkansu suka amsa da Ameen Daidai Lokacin da Mastur ya leko Cikin Falon Cikin Dakiyar Muryansa yana Fadin"Wai me kuke jira ne..? Dare nayi kuma kusan akwai Tafiya agaban mu gobe kunje kun Zauna.."Ya karishe Fada yana Hararan Mansur Shi kuma sai ya Fara Dariya yana Fadin"Naga kana kallona Ranka ya Dade ba ruwana..Gasu nan Tun da zu nake ta Fama Dasu sun ki su tashi Kamar masu Tsohon Ciki ko Hajja..? Baba ma Shaida ne..? Ya karishe Fada yana wani Daga Hannu Dariya ta Kama su Hajja Shi kanshi Mastur din sai da ya Murmusa Jin Haka yasa Rumana ta yunkura ta Mike Babbar Ledan Dake Gabanta ta Dauka ta karisa gaban Ayya ta Ijiye Batare da tayi mgana ba Ayya ta Kalli Ledan Tana kallon Rumana Tana Fadin"Yar'nan wannan Ledan fa..?Rumana kanta na kasa Tace"Naku ne keda Hajja Ayya..!Ayya ta washe baki Tana Jawo Ledan Lokaci Daya Tana Fadin"Masha Allah..Kai Hajara Kinga Surukarki Harda Wata Dawainiya..La Harda Turaman Zannuwa Habibu kalli Abun arziki Megidana Na yarda Zan yi zaman kishi da Rumana Daga gani zata ji Dani.."Ta karishe Fada tana yar Dariya bayan Tagama Fidda abubuwan Dake Cikin Ledan Duka.
Ba Mastur kadai ba Hatta Mansur yaji Rumana ta Burgesu Ba wanda Cikinsu yayi Tunanin zuwa da wani abu ammh Gashi ita tayi wannan Tunanin Diza kuwa Bakinciki da Kishin Rumana ya kusa kasheta ganin yadda Ayya ke kwararo mata addu"a da saka albarka Hajja kuwa Fadi take"Rumana Harda Wata Dawaniya..? Ummanki Fa ta aiko mana da Zannuwa da kayan Fulawanan da yawa Harda Dambun Naman Nan fa.."Rumana kanta na Duke Take Fadin"Wanchan Daga Umma ne Hajja..Wannan kuma naku ne Daga yarku Rumana.."Baba Habibu Dayaji Yarinyar ta Burgeshi Saboda Ladabinta da Hankalinta ya kada kai yana Fadin"Shikenan kuwa..Allah yayi Miki albarka Dukkanku Allah yayi muku albarka.."Suka amsa da Ameen kafin ta Mike Dauke da Karamar Ledan Zata kaima Mommy Itama Dizan mikewa tayi Hajja na Tsaye Tana ta Godiya Mansur dai yabi bayan Mastur sun fita Diza saboda Haushi ta Fara Ficewa kana Rumana tabi Bayanta a waje suka ga su Mastur kana suka Rankaya zuwa Gidansu Diza.

Mama Fadime suka gani a Falon kasa Tana ganinsu ta washe baki Tana Musu Maraba,Daya Daga Cikin kujerun Falon suka yada Zango Mansur da Mastur,Ita kuwa Diza Mgana tayi ma Mama Fadime ta Hado Ruwa da Lemo ta kawo ma su Mansur Kana ta Kalli Mansur Fuskarta ba Fara"a Tana Fadin"Bari na Haura sama..Na gayama Mommy da Daddy Zuwan mu.."
Mansur yace"Ok..Ku tafi Tare da Anty Rumana mana.."Diza ta kallesa kamar tace wani abu sai kuma ta Fasa kawai taja Jikinta ta wuce Rumana Dake tsaye taja ta Tsaya Mastur Dake Zaune hankalinsa nakan wayarsa ya Dago suka Hada ido da Rumana wani kallo yayi mata wanda yasa Itama Jam jiki tabi bayan Diza zuwa Sama.

Diza na tura kofar Falon Mommy da Sallama Ta iske Daddy zaune yana Shan iske yana Sanye da Jallabiya Mommy na gefensa Suna Shan Fruit suna Hira Sama sama Lokaci Daya suna Kallon Babban Telebijin din Dake Falon sukaji Sallaman Diza Mommy ta Mike bakinta kamar Ya yage Tana Fadin"Wa nake gani kamar Diza..? Diza da Farimcikin ganin iyayanta ya kamata ta Cire Takalminta ta Nufi Mommy da Sauri suka Rumgume juna Daddy na gefe yana Dariyan Farimciki yana Fadin"Khadija..Wato Uwarki kadai kika gani ko..? Jin haka yasa ta saki Mommy ta karisa Garesa ta zauna gefensa ta Yada kanta saman kafadansa Tana Fadin"Nayi kewarka Daddy..Mommy nidai Ki Dawo Wajena mu zauna..'Ta fada Cikin Shagwaba Mommy da Daddy suka Hada ido suka Saki Dariya Sai Diza ta Fara kukan Shagwaba Daddy ya Fara Lallashinta yana Shafa kanta dukkansu Farinciki ya Cikasu sun ma manta da Tambayarta Ita da wa suka zo..? Rumana Dake Tsaye bakin Kofar Falon Tana kallon abunda ke wakana Bata karisa ciki ba saboda kada ta Shiga Lokacin su.
Mommy ce ta Dago kanta sai kawai Taga Rumana da Sauri ta Mike Tana Rike baki Lokaci Daya Tana Fadin"Kai innalillahi..Diza ashe tare kuke da Ruma kuma baki mgana ba Tun Shigowarki..? Sai lokacin Diza da Daddy suka kai Dubansu wajen Rumana Daddy ne ya washe baki yana Fadin"A"a Diyata..Rumana Maraba kariso mana Daga Ciki..!
Jin haka yasa Rumana ta Tako Zuwa Cikin Falon tana Mirmishi Tana Cire Takalminta Mommy ta kariso ta tarota Tana mata maraba Har sai da ta Danganta da Gefen Daddy ta zaunar da ita da Sauri Rumana ta zamo tasauko kasa Tana gaida Daddy Cikin Ladabi ya amsa yana Dafa kanta Lokaci Daya yana saka Mata albaerka.
Diza Dake gefe Sai wani Cika Take Tana batsewa kamar wacce taga wani abun kinta Eh mana ai Rumana Abun kinta ne.

Mommy ce ke fadin"Sannun ku da zuwa..Yanzu kuke tafe da Daran nan..? Ina Mazajen naku..? Rumana ta Dago suka Hada ido da Diza sai kawai Taga ta balla mata Harara ta kauda kai sai kawai itama ta kauda kanta Tana Fadin"Tare dasu muke Mommy suna Falon kasa..Tun dazu muka zo mun FaraShiga wajen su Hajja ne.."Mommy ta Rike baki Tana Fadin"Ikon Allah Gaskiya Diza baki kyauta Shine tun Shigowarki baki yi mgana ba..? Diza ta Tura baki Tana Fadin"To ba yanzu na Shigo ba.."Tafada tana Hararan Rumana ta kasan Ido Mikewa Daddy yayi yana Fadin"Nidai bari na sauka wajen Ya"yana..Asiya sai kun Fito ."Yafada yana Ficewa Daga Falon.
Yana Fita Mommy tace"Bari naje na sako mayafina Mu sauka kasa ko Zakuyi zaman ku anan ne Rumana..? Kafim ma Rumana tace wani abu Diza ta Mike Ta wuce Bedroom din Mommy Suka Bita da kallo Mommy sai abun yayi mata wani iri ammh bata Nuna ba ta kalli Rumana Tana Fadin"Bari na Dauko mayafina Rumana.."Ruma ta gyada kai Lokaci Daya tana Mikama Mommy ledan Hannunta Tana Fadin"Gashi Mommy.."Mommy ta karba da mamakin Tana Fadin"Rumana Miye wannan din..? Tafada Tana Bude ledan ganin Abunda ke Ciki yasa Ta saki Mirmishi Tana Fadin"Duk wannan nawa Ruma..? Allah yayi Miki albarka Nagode kwarai.."Tafada Cikin Farinciki Rumana kanta na kasa Tace"Ameen Mommy.."Mommy Tana Murna ta Shige Ciki Tana Nuna ma Diza Datagani kwance Kan gadomta Tana latsa wayarta ko Dagowa batayi ba tace"Kin gode.."Daga haka ta Cigaba da Latsa wayarta Mommy sai taji Ranta ya baci ta kalli Diza Tana Fadin"Khadija miye haka..!?ya kin zo Tare da yar"uwanki kuma kin Shigo kin barta kin kwanta..?
Diza ta Gyara kwanciya Tana Fadin"Kai Mommy nida Dakin Mamata.."Mommy ta ijiye ledan Hannunta Saman Madubi Tana Fadin"Bana son Shashanci tashi kije wajenta..."Tafada Tana Kari sowa Gaban wardrope dinta ta Bude ta Dauko katon mayafinta ta Saka Tana kara kallon Diza tace"Oya tashi muje gabadaya.."Diza tasan Halin Mommy da Kafiya tunda tace sai ta Fito sai ta Fiton hakanan Tana Tura baki ta Sauko Daga kan gadon Tana Fadin"Shikenan Ni da Dakin uwata baza'a barni na Shakata ba.." Tafada Lolaci Daya tana Wucewa ta Fita Fuu..Mommy ta Bita da kallo Kafin ta Girgiza kai tabi Bayanta koda Mommy ta Fito Diza takai Kofa ta Fice,Mommy taji wani irin Haushin Dizan sai dai bata Nuna ba Ta kalli Rumana Tana Fadin"Mu sauka kasa Ruma.."Rumana ta mike tabi Bayan Mommy zuwa Falon kasa sun iske Mansur da Mastur da Daddy suna ta Hira ga Kayan Sha da Kwalama nan agabansu Diza bata wajen Dakinta na Baya ta Shige abunta.

Mommy ta karisa ta Zauna Dukkansu suka Ramkwafa suna gaisheta ta amsa Cikim kulawa Daddy ya kalleta yana Fadin"Mastur zai koma bakin aiki gobe..Shima Mansur goben Abuja zai tafi Taron su na Siyasa.."
Mommy ta washe baki Tana Fadin"Masha Allahu..Allah ya kiyaye Hanya kace duka zaku bar ya"yan nawa da kewa kenan..? Tafada Tana yar Dariya Daddy yace"A"a ai itama Rumana gobe Zata je Chan asibitin Chika din ko..? Yafada yana kallon Rumana Dake Zaume kasa gefen kafafun Mommy Kai ta gyada Tana Fadin"Eh Daddy..."Daddy ya kada kai yana Fadin"Ai munyi mgana da Abban naki dazu yace ya baki Lambar Dr Hambali da zaki nema in kinje Chan asibitin ko..? Rumana tace"Eh ya Turomin Daddy..Zan nemeshi da Zaran na Shiga asibitin Insha Allahu.."Daddy ya jinjina kai yana Fadin"Shikenan Allah bada sa"a..Ki kirani indai gobem kikaje kika ga akwai wani mtssla kin ji ko..? Rumana tace"Insha Allahu Daddy.."Mommy tace"Allah ya Taimaka Ruma..Ita Diza ai inaga sai ta kara Hutawa Saboda Tana da Ma"aikata sosai a wajen.."Daddy yace"Ai nata aikin ba wani mtsala bane ba kamar na Rumana ba ita Data karancin Harkan Lafiya.."Diza Ta Fito keman Taji Daddy na Fadin sai taji kamar ta koma ammh ba Hali wato ita Bata da wani Feature mai kyau tunda batayi karatu ba sai Rumana ya zama Dole itama Gobe ta koma Catering dinta ba wanda zata ma gadin gida.
Ita bazata zauna akasa ba Gefen Mommy ta zauna tana wani Yamusta Fuska nan Daddy Shima da Mommy suka kara Musu Nasiha kafin su tashi suyi Shirin Tafiya,ba wanda ya Taba wani abu sai Mansur Daya sha Ruwa Har Haraban Gidan Mommy da Daddysuka Rakosu suna musu Fatan alheri Dayake Motar a wajen suka barta Kofar gidan su Hajja Mommy nayi ta yi ma Rumana Godiya Bayan ta gayama Daddy gabansu Mansur Shima sai saka mata albarka yake Dalilin Da Yasa Diza taji ta kara Tsanar wannan Fitan da sukayi yau tare da Rumana.

Gidan su Hajja suka koma sukayi musu sallama Bayan Mastur ya Shiga Shashensu Dake kulle yanszu ya Dauki wasu Takardu suka wuce sun bar anguwan Misalin 10:30pm na Dare wannan karon ba wanda ke mgana Harta Mamsur din yayi gum ganin Diza ma ta Hade rai duk sai ya Shiga Damuwa Suna komawa Gidan Bayan Mansur yayi parking a parking Space Suka Firfito Mastur wucewa yayi Dauke da Takardun Hannunsa Rumana ne ta Tsaya tana cema Mansur sai da Safe da Sauri yace mata"Ai shiga zamu yi Shashen ku tare da Diza..Bamu taba Shigowa tare ba.."Rumana kamar ta sani ta kalli Diza sai ta kamata Tana Hararan Mansur kamar idonta zai Fado kasa,baki kawai ta Tabe ta wuce Tana Fadin"Maraban ku.."Mansur yabi Bayanta Yana Rike da Hannun Diza Dake bankamai Harara yayi kamar bai ganta ba..
Mastur ya riga ya Bude kofar Shashen shiga kawai sukayi Wlh Diza Kin zama Tayi mansur ya zauna yana ce mata ta Zauna Daga Tsaye ta Coge tana karw ma Falon kallo Take fadin"Bafa zama zamu yi ba..Ni kam barci nake ji.."Rumana Dake tsaye da kamar Zataje ta kawo musu Ruwa sai ta Fasa Kawai jin Abunda Diza tace Mastur Daman koda suka Shigo ya Shige Ciki ko yana Jinsu ma bai leko ba.
Mansur da kunyan Abunda Diza Tayi ya Ishesa sai ya Mike yana kallon Rumana yace"Anty Rumana bari muje sai da safe..Tunda tana jin barci in na Dawo Duk Ranar dana Dwo nan zamu yi Dinner ranar."Rumana ta saki Mirmishi Tana Fadin'"Is ok..Allah ya kaimu Allah ya kiyaye hanya."Ya amsa da Ameen Yana Fadin"Yaya Mastur ya Shiga Ciki ko..? Rumana ta gyada kai kawai Mansur sai ya kama Hannun Diza yana Fadin"Shikenam zamu hadu gobem kafin ya tafi..Sai da Safe.."Rumana tabi bayansu Har suka Fice ta maida Kofa ta Rufe aranta tana ayyana Diza Da ta Koyo wasu mugayen Hallayar me ta mata ta Tsaneta ta rasa Dalilin haka itama ta Gaji Hasken Falom kadai ta Rage ta Shige Bedroom dinta gyalen da Jakar kan gado ta watsar ta Fada tiolet ta Rage mara Tayo wanka tazo ta saka Kayan Barci tabi Lafiyan gado Tana ganin Missedcall din Basma Ta kirata Lokacin suna gidan Su Diza sai bata Daga ba sai taace bari zuwa Safe sai ta Kirata.







*Shakira...*
1/1/22, 18:54 - Maryam Badmsi: *SS....25*

*Ki biya ki karanta cikin salama 09069067488 Mace mai aji mallakan komai nata take yi bata jiran abun sata*

"Rumana ta kwanta da Sanin cewa gobe zata Fara zuwa Aikinta Shiyasa barcin nata ya zama Ragagge ne Karfe 5:30pm tatashi Daga Barci ta Fara Shiryan Shiryanta ta Fito da Kayan da zata saka tare da Karamar jakarta Hadi da Takalmin Jakar ta saka Takardan da suka bata a Uduth Saboda kada ta manta,Bata manta da cewa yau Mastur zai koma Wajen aikinsa ba ko bakomai Miji yake gareta kuma akwai hakkinsa akanta Shiyasa ta Fita Zuwa Kitchen ta Dibo masa Cake da Cincin da Donut,Ta samu wani Roba Duka ta Cika mai kananan Wasu Robobi ne masu kyau Duka ukun Ta saka su ta Mai rapping dinsu,Sai tayi Tunanin tayi mai Miya wanda in yaje zai Dinga Dafa wani abu yana ci Tunda chan bai da kowa kuma Girki kamar zai mai Wahala.

Tunanin haka yasa nan take ta Bude Fridge ta Dibi kayan Miya ta Dauko Blander ta Markada bayan ta gyara tafara Soya Nama Kafin ta Tafasa kayan Miya,sai da Tagama kana ta Hada mai Miyar Ta barta Tana Soyuwa Jin ana Kiran Sallar Asuba yasa ta baro Kitchen din bayan ta Rage gas Din Tana Fitowa Falo Mastur na Fitowa Daga Dakinsa yana Sauri Zashi Masallaci Yayi mamakin ganinta kwarai Har sai da ya Nuna Domin ya kalleta Sau Biyu kafin ya Dauke kansa Sabanin abaya sau Daya yakan kalleta ya basar Da sauri tace mai Ina kwana ya amsa mata Da Lafiya yana Wucewa Itama bata kara bi ta Kansa ba ta Shige Dakinta Wanka Tayi Lokaci Daya ta Dauro alwala Tazo Tayi Sallah Tana Idarwa Ta koma Kitchen ta Duba Miyar taga tayi sai ta Sauketa Ta Dora Ruwan Zafi Bayan ta saka ganyen Tea da Na"a Na"a,Ta koma Daki ta Cigaba da azkar dinta sai Lokacin Taji Dawowar Mastur ya Shiga Dakinsa.
Misalin 6:00am ta koma Kitchen din Ta Juye Ruwan tea din a Wani Fulas ta Fere Dankali Ta Soya ta Fasa kwai ta Soyashi Kana ta Soya Buredi mai kwai,agurguje tayi komai Ta jera Saman Dining Miyar kuma ta samu Wata Lafiyayyar Kularta mai kyau ta Juye mai aciki ta Rufe Duka Naman Datayi Miyar Dashi ta kawo Falo Saman Dining,Daki ta koma ta Fara Shiryawa Domin 8am take so Tayi mata a Abu Chika Cikin Lokaci Ta Shirya Cikin Riga da Sikat na Wani Leshi mai kyau da yarari Mai kalan Ja ta yafa Gylenta ja da Jakarta da Takalminta,Wayarta ce tayi kara Tana Dubawa Taga Abbanta ne ta Dauka suka gaisa nan yake tambayanta ta isa Asibitin..? Tace mai A"a yanzu take Shirin Tafiya ya kara mata Bayanin in taje Ta Tambayi Dr Hambali ya riga ya gayamai komai Data isa Ta tambayeshi ana  Nuna mata Shi Ta bashi Takardan Hannunta ta amsa mai da toh Basu sallama basai da Yabama Umma sukayi mgana Dukkansu sukayi mata Fatan alheri kana suka yanke Kiran Tana Kokarin Fitowa Taji Knooking din Kofarta Sai ta Rarumo Jakarta da Key din Motarta ta Fito Bayan ta saka Takalminta mai Dan Tudu kadan Tana Bude kofar Taci karo da Mastur Tsaye Cikin Shigar Riga da wamdo Duka Bakake na Kamfanin Armani Rigar mai Dogon Hannu ce,kafarsa sanye da Takalmi Sawu Ciki Bayansa Goye da wata Jaka baka,Hannunsa Daya na Aljihunsa Dayan kuma Wayoyinsa da key din Motarsa Tana Bude Kofar bai Tsaya ba ya Juya yana Fadin"Ki fito zan tafi.."haka Kawai ya fada Ya juya Zuwa Cikin Falon Da Sauri Rumana tabi Bayansa Zuwa Falon bai Zauna ba ya na Daga Tsayen ya Juyo yana Mikamata Atm din Daya Fito Dashi Daga aljihunsa Ta saka Hannu ta karba Tana kallonsa na neman karin Bayani Cikin Dakewarsa yace"Daya Daga Cikin katinan Bankina ne...akwai kudi aciki Ki rika amfani Dashi in wata Bukata tataso ko kuma dai In kima Neman wani abu.."Yafada yana kara gyara zaman jakar Dake Bayansa,Rumana ta Sadda kanta kasa Tace"basai ka bani ba..Ina da kudi a Hannuna Na Sadakina kuma akwai kudi acikin Bankina wanda Chan asibitin Uduth ke Biyana na Intenship dina sun Isheni Komai ."
Ko kallonta bai yi ba ya Fara Taku yana Fadin"Ai nasan kina da kudi kuma na bar Miki..So ni zan wuce ba lalle na Zo da wuri ba..Ki kula da kanki.."Daga Haka taga yana Shirin Barin Falon da Sauri ta Bude baki tace"Plz ka Tsaya kayi Breakfast gashi Chan na Hada.."Cak ya tsaya Yana Jinta Yaki Juyowa ba alaman zai Dawo ya Daga kafa ya Cigaba da Tafiya tace"Don Allah ka Tsaya kaci wani abu ya Mastur..Bai kamata ka Dauki Hanya baka ci komai ba.."Ta karishe Fada Cikin Sanyin murya da Shagwaba muryan Datayi amfani Dashi yasa ya kasa Tafiya kawai taga ya Juyo kan Kujera ya ijiye Jakarsa da Wayoyinsa Ya wuce saman Dining Din Rumana Cikin Farinciki itama ta Sabule Jakarta nan Saman Daya Daga Cikin kujerun Falon tabi Bayansa.
Dasauri ta isa Wajen Taja mai Kujeran Dinning ya zauna akai Tafara Kokarin Daukan Filet zata Zubamai Dankalin da Sauri yace"No..Ki Hadamin Tea.."Daga haka ya Dauke kai da Sauri ta Dauki Mug ta Zubamai Ruwan Tea din Ta Tura gabansa Tare da kayan Tea kamar baya so haka yaja ya Hada Tea din Madara kawai ya saka ya fara sha sai ta Turamai Buredin Data Soya Daya kawai ya Dauka yaci Itama dai Sama Sama tasha Tea din Taci Dankalin,Tana Cikin hakane Taga ya ijiye Mug din Hannunsa ya Mike Lokaci Daya yana Ture kujeran Daya tashi ta Dago Tana kallonsa Lokaci Daya tana Fadin"Tafiyar kenan..?
Kamar bai jita ba kuma ya Jita Tissue yaja ya goge Bakinsa ya Wuce zuwa Falo ya Dauki Jakarsa,Ganin haka yasa Tatashi da Sauri Tana Fadin"Bari nazo.."Da gudu ta Rumtuma Zuwa Kitchen Har sai da ya Juyo yana Binta da kallom Mamaki Abun sai ya Bashi mamaki yayi Tsaye yana Jiranta Chan sai gata ta Fito Dauke da Wata Farar leda Mai Dauke da kananun Robobin Guda uku sai kulan Miyan Tana Zuwa Gabansa Tace"Gashi..Kayi amfani Dashi in kaje Chan.."kamar zai Tambayeta Menene sai kuma ya fasa ya Juya kawai Ita kuma Tabi bayansa Bayan ta yafa Mayafinta Har Haraban Gidan suna Fitowa Mansur da Diza ma suna Fitowa tayi mai Rakiya Dauke da Jakarsa Shima Sai wani Shagwaba take mai Rumana na gefe Tana kallon Ikon Allah Dayake Daga bakin Shashenta ta Tsaya Mastur ya Juya yakarbi kayan Hannun Rumana yana Fadin"Ki kula..Ki Rika Tuki a hankali nan ba Sokoto bace..Zaria ce.."Daga haka ya wuce ya Bude bayan Mota ya saka Kayan Hade da Jakarsa kana ya Rufe Mansur ya kariso sukayi mgana Kafin kowanne ya Juya ya Shiga Motarsa Rumana dai Hannu kawai Ta daga ma Mansur Shima ya Daga mata Diza Dai Har bakin Mota ta isa bayan ta Bude Gaba mazaunin mai Zaman banza Ta Saka mai Jakarsa sun Dade suna mgana Domin har sai da Mastur yayi Ribas yayi Hon Megadi ya Budemai get ya Fice Rumana na Dagamai Hannu Mansur na ganin haka Shima ya Tada Motar kafin a Rufr get din yabi bayansa Dukkansu Daga nan sai da sukaje gida Baba Habibu Da Hajja sukayi musu Fatan Alheri kana kowannensu ya Dauki Hanya Mansur dai sai ya Jira Tawagarsa kana suka Dauki Hanya Mastur kuma Dayasan Tafiyace agabansa Tuni ya Daura Set Belt yana Ta kwarara Gudu Bisa Tituna.

Bangaran Rumana kuwa Tayi kokarin sakarma Diza Mirmishi Duk da suna Nesa ne ammh sai Diza Tayi kamar Bata ganta ba ta Taka ta Bude Kofar Shashenta ta Shige,Tabar Rumana na Binta da kallon Mamaki Kai kawai ta Girgiza ta Koma Shashenta Bata Tsaya Bata Lokaci ba ta Dauki Jakarta da Wayarta Ta Rage duka Fitulan Dakunan kana ta FitoKofar Shashen nata ta Kulle Daman key din Biyu ne Daya na Hannun Mastur,kamar ta Shiga Tayi ma Diza Sallama sai kuma ta Fasa Ta Bude Motarta ta Shiga da Bismillah Ta saka Set Belt Bayan ta ijiye Jakarta agefenta ta kunna Motar Daman Anyi mata Full Tank ammh Duk da Haka zata Tsaya saman Hanya ta kara sakamai ko bayan ta Dawo ne,Hon tayi ma Megadi ya Bude mata get ta Fice yana mata Allah ya Kiyaye Diza na kallonta ta Window Falon Takaichi ya Isheta waya ta Daga ta Kira Mommy tace Direban Daddy ya kawo mata Motar ta 10am take so Ta Fita Zuwa Catering dinta Mommy tace Shikenan Daganan ta yanke kiranta Tana wani Bata rai Daman sun gama Sham Fama da Mansur kan bazata koma ba sai ta kara Jin Sauki ita kuma tace ai taji Sauki sai taje Dayake bayason Bacin ranta bai Ja ba yace Ta koma,Ita Bata yi Niyar komawa ba sai ta kara Hutawa ammg ganin Rumana zata koma yasa Taji itama Zata koma Saboda Kada ta Dauka itace kadai mai Zuwa aiki agidan Kada ta Rainata.
Ba jimawa kuwa sai ga Direban Daddy da Motar Diza Kudin Mota ta bashi ya koma Gida ita kuma Tayi wanka Ta Shirya Cikin Shigar Abaya Daman da Safe Tea sukasha da kwai batajin yunwa Kwan ma Mansur ya Soya tanakwance 10am din Datace ta Fito Itama ta Hau Motarta ta Fice Daga Gidan suka bar Megadi da Gadin gida Diza na zuwa Catering Dinta Ma"aikatanta nata mamaki sun Dauka sai wani Sati Bangaran Catering din ta Fara Shiga Ta Duba Komai Merry tasha Masifa Ita da sauran Ma"ikatan Data Fito sai Shashen Makeup dinta Ta iske Hauwa da Meena suna aiki mai kyau Taji Dadi Sosai Hauwa sai Murnan ganinta Take Tana Hajiya Amarya Diza na Mirmishi Officr dinta ta Shiga ta zauna ta Dauko Wayarta Ta Kira Mansur Tun Tana Cikin Catering yake ta Kiranta Bata Daga ba Basu Jima suma mgana ba yadai ce mata sun isa Abuja 12pm za"a Fara Taron nan itama tace Tana wajen aikinta Daganan sukayi sallama.

Rumana kuwa Tana Isa Cikin Asibitin Chika ta Kira Lambar Dr Hambali da Abba ya Turo mata Bayan ya Dauka sun gaisa tace sunanta Rumana Muhammad wamako Kafin tayi wani Bayani yace yaganeta,cewa Yayi ta Nemi waje ta Tsaya Shi baya Cikin Asibitin kuma bada Wuri zai zo ba Ammh yanzu zai kira wani Likita zai Bashi lambarta zai Nemeta Nan da nan kuwa sai ga wani ya kirata yace Tana ina ta kwatatanta mai ba Dadewa sai gashi yazo Matashin Saurayi Fari Dogo Yana zuwa suka gaisa ya gayamata Sunansa Dr.yahaya Shima Likita ne anan asibitin a Shashen yara,Rumana Tayi Mirmishi tace ita Sunanta Rumana Wamako Daga asibitin Uduth Dake Sokoto ita Intenship take yace ai Dr.Hambali yamai Bayani Suna tafe suna Hira kamar sun saba Balle ma Da Dr Yahaya ya kasance Likitan yara Fannin da Rumana keson ta kware sosai.
Dr Yahaya ya taimaketa Kamar Shi Dr.Hambali ya wakilta Cikin Lokaci kadan hukumar Asibitin Chika ta Karbeta Da Cuku Cuku da Hanya ammh Sai da sukayi mata Jarabawa ta baki kuma ta amsa Tambayoyi kuma Ta amsa Alhamdulillah Zatayi aiki a kowanne Shashe take so Sai ta Zabi Shashen Mata da kananun yara,Zata Rika aiki Sati Na Safe Wani Satin kuma Col ma"ana na Dare Duk bataji Dadi ba ammh Tasan za"ayi haka Da sukayi waya da Abba ta gayamai yace kada ta Damu ta Fara Zuwa Gaba Zata koma na Safe Gabadaya Saboda Ita Matar aure ce,Daga haka Zuciyarta Tayi sanyi Sun Rabu Da Dr.Yahaya Bayan sun karbi Lambar Juna Female ward Ta isa Tun Ranar ta Fara aikinta Ta Hadu da Nurses Sanininta da kuma Likitoci da kuma Mata da Maza irinta masu Intenship Sai dai Dayake bata da Sakewa da Mutane Sama sama ne.


Karfe 5:00pm Tatashi Daga asibitin,Bata koma Gida ba sai da ta Biya Gidan mai ta Zuba mai a Motarta Ta koma Gida ta Iske Diza ta Dawo Domin taga Bakuwar Mota hakam kuma ya Tabbatar mata da Motar Diza ce agajiye ta Dawo,Daman tayi sallarta acikin asibiti,Bata Jin yunwa Ta Siya Lemo Tasha Da Cake,Kwanciya kawai Tayi bayan ta Kira Mastur bai Daga ba sai ta Turamai Sako,Bata tashi ba sai gabd Mganariba Tayi sallah bayan tayi wanka Ta Fito Falo Ta kunna Kallo Tea ta Hada tasha Ta Hada Soyayyan Dankalin Data Soya da Safe Tana zaumen Tana kallon Sai ga Kiran Basma ta Daga sukayi mgana duk akan aikinsu ne Bayan sunyi Sallama Ta Kira Umma sukayi mgana Har aka bama Goggo Jummai da Juma sukaayi mgana hakan ya sakata Farinciki kiran Sallar Isha"i ya katse Hiran ta koma Daki Tayi Salla ta Saka kayan Barci ta Dauko Laptop dinta da glass dinta Ta Je Kichen ta Debo Dambun namanta Tazo Ta zauna Tana ci Tana kallo kuma tana Karatu Cikin System dimta Ko Ta kan Diza bata Bi ba kamar yadda Itama bata Nemeta ba sai 9pm ta tattara komai ta koma Daki Bayan ta kashe Kayan Wuta Har Tayi Shirin kwamciya Taji Karar wayarta Sako ya Shigo Tana Dubawa Taga Mastur ne.

*Kin kirani ina Kan Hanya..Buh na Sauka Lafiya..GN*

Shikenan iyakar sakon kenan batayi wani mamaki ba Domin Tun Tana Gida Sakon sa Baya wuce Layi Daya zuwa Uku Bata yi kokarin Kiransa ba ta kashe wayarta Ta kwanta Harga Allah ta Daina Damuwa da Sha"anin Mastur Tun zaman Satin Dayan da sukayi Tare agida Daya ta kara Fahintar Sanin Datayi mai abaya ya kara Ninka Hallayarsa ne Kwanciyarta kawai Tayi bayan Tayi addu"an Barci Duk Da Tana dan Jin Tsoro ita kadai a Shashen ammh Ta Dake,ko bakomai Tana jin Sanyi ba ita kadai bace agidan Akwai Ran Diza koda basa kusa Numfashin Raina ma wani abu ne.

Rumana bata Kira Mastur ba sai da Safe Bayan ta Shirya Zata tafi asibiti kana ta kirashi Taci Sa"a ya Daga Sama sama suka gaisa Tamai ya Hanya Sukayi sallama Shima yace mata yana Shiri ne zashi wajen aiki Daganan sukayi sallama.

Rumana kafin Tatafi Sai tayi Breakfast dinta Ta kuma Soya kwai ko Dankali ko Buredi sai ta Zuba Cake Tatafi dashi da Lemo Wamda in taji yunwa Zata sha Daga gani kuma Tana Jin Dadin aikinta Sosai Ita da Diza basa Haduwa ssi dai kowa yaji Hon din kowa in ya Dawo Rumana tana Riga Diza Fita Ita kuma Diza Tana Riga Rumana Dawowa,Rumana taso Ta rika Shiga Tanayi ma Diza Sallama ammh Rashin Samun Fuska yasa ta kama kanta.

Kwana uku da Fara Zuwa aikin Rumana Ranar Data Dawo sai bata wuce Gida ba Ta fara Biyawa ta Gidansu Hajja Chan ta wuni sai Dare Data tashi Sai taShiga wajen su Mommy suka gaisa Lokacin Daddy bai Dawo ba tace a gaisheshi in ya Dawo ba Mommy kadai ba Hatta su Hajja suna yaba Tarbiyan Rumana da Natsuwarta ganin bayan Tatashi aiki Zaman gidan ita kadai ne sai Take Biyawo Gidan su Hajja Sai yamma take komawa Gida Bata Zama Zagewa take Tana Taya Hajja aiki Duk Tana Fadin Rumana ta bari ammh Bata iya bari,Ta Fada musu yanayin aikinta Harda na kwana Baba Habibu yace ba Damuwa Ceton Al"umma ne Allah ya Taimaka Shi kanshi Mastur bai san Rumana na Biyowa Gida ba sai dasukayi mgana da Hajja Take Fadamai Lokaci Daya Tana yabon kyakyawan Hallyarta Shi kansa Ai bazai ce Rumana bata da Tarbiya ba Shine Babban Shaida akanta Tun Bayan Tafiyarsa sau Biyu Sukayi mgana awayaShi bai kirata ba Itama aikinta ta saka ma gaba Bata kara Nemansa ba ganin Shi Daya kamata ya Nemeta ya manta da ita.

Mansur sai Ranar jumma"a ya Dawo da Safe,Bata ma san ya Dawo ba Domin Ranar bata je aiki ba Bata da Duty sai Monday Zata Fara Call Chan da yammah ne Taji Hayaniya a Haraban Gidan Shine ta Leko ta Window ta Gansa Shi da Tawagarsa yan Siyasa Domin Zabe ya kusa sai Lokacin Tasan ya Dawo bai Shigo ba Sai Washegari ya Shigo suka gaisa ya kawo mata Tsaraban Chaculate da Bicuit sun Dan Taba Hira Kadan kafin ya tafi ya gayamata Baya samun Zama Saboda Zaben su Daya gabato Sai a Hankali Tayi mai Fatan alheri.

Washegari kuma Lahadi ashe Tun Safe Dataji Fitarsu Shi da Diza ne Tana Falo Lokacin Tana Gyarawa Ganin Karshen mako ne gobe kuma Bazata samu Zama ba Batasan Halin da ake Ciki ba sai da sukayi mgana da Umma take Tambayanta Me yasa bata Bi su Mansur Sunje Doguwa ba Jikin Mahaifin Mansur ya Tashi Baba Sule Rumana Tasha mamaki Domin ba wanda ya Gayamata Mansur dai bai Shigo ba Diza kuma Daman bata Cikin Lissafinta Mastur kuma Shi da Babu Duk Daya Su Hajja kuma Bata Je aiki ba Bata Biya Gidan ba Duk da Tana da Lambar Hajja da Mommy tana Kiransu su gaisa Yau din dai basu yi mgana ba Sai Tayi ma Umma karya Tace Batajin Dadi ne Shiyasa bata so ta Fahimci wani abu ba.

Bayan Gama Wayarsu da Umma ne Ta Kira Mansur bai Daga ba Sai ta kauda Komai ta Kira Diza Har wajen Kira Uku itama BataDaga ba sai ta Kyaleta Chan Bayan Sallar mangariba Mansur ya Kirata Bayan ta Dauka sun gaisa Tamai yamai Jiki yace da Sauki yanzu hakama Bayan sun Isa Garin Yaga yanayin Jikinsa ya Dauko sa sun kawo sa asibitin Garin Doguwa,har An sakamai Drip an mai allura ya samu Barci Jikin da Sauki Shi yake Fadamata ma Shi da Baba Habibu da Diza suka Taho Dare yayi sai Gobe zasu Dawo akwai Taron dayake Dashi yau din bai Sami Hallarta ba Rumana Tayimai Fatan Samuwar Lafiya ga Baba Sule kafin Suyi Sallama Mastur Kuwa Daman yaRiga kowa Samun Labari Domin Shi ya kira Wayar Baba Sulen da Safe Maryama ta Dauka Tagayamai Bashi da Lafiya yana kwance Jin Haka yasa ya Kira Mansur yace ya Ijiye Komai da komai Dayake gabansa yaje ya Duba Mahaifinsa ya kuma Kaishi asibiti Shime fa Ya Shirya zai Tafi Diza tace Zataje Baba Habibu kuma Mastur ya Kirashi Jin haka sai ya Kira Mansur yace yazo ya Dauke sa su Tafi Tare.

Basu dawo ba Sai Washegari Da yammah Lokacin Har Rumana Tatafi asibiti Tagaji da Jiran Dawowarsu nan Gida wajen Hajja Tun 2pm take Gidan Har Ta Taya Hajja sukayi Dambun Shinkafa Miyar Zogale Sai 4pm ta Wuce asibitin Tana Tafiya ba Dadewa suka Dawo Da Labari mai Dadi,Baba Sule ya Samu Sauki Sosai Daman Hawan Jini ne da Ulcer sai maleria Data Kamashi Sosai da kuma Rashin Wataddacen Abinci,sun bari Zuwa Gobe za"a Sallameshi Bayan Mansur ya gama Biyan Komai agida kuma ya bada kudi Za"ayi Feshin mgani Kuma ya Siya Kayan Abinci masu yawa kuma ya bar ma Inna  Zainab kudi a Hannunta yace sai Zuwa Sati mai Zuwa zai Dawo yaron Yayan Baba Sule Gaddafi suka baro awajensa yana kula Dashi Mansur dai a asibitin ya kwana Baba Habibu kuma Ririwai yaje ya kwana Gidan Inna Karime Diza kuma Dakin Mama zainaba Ta kwana ita da Maryama da mardiya suna ita ina zasu saka da ita.
Mastur Da Mansur ya Kirashi yana gayamai Halin da da ake Ciki,ya dinga mai Fadan meyasa Bai Dauko Baba Sule Zuwa Wani asibitin Kudi Dake nan Zaria ba Har ya samu Lafiya ba sai ya barshi a nan da Mansur ya kawo mganar Uzurin Siyarsa Da Zaben Dake Matsowa Mastur ya Fara mai Fada Yana Fadin Siyasar Tafi Mahaifinsa ne Shidai Mansur sai Hakuri kawai yake bashi Sai da Baba Habibu ya karbi wayar ya Tabbatarmai da komai Lafiya kana ya yarda.

Rumana bata Dawo ba Sai Washegari da Safe Tana Shigowa Gidan Bayan ta Fito Daga Motarta Dauke da Jakarta da Wayarta Sai key din Motarta Dayan Hannun nata kuma Lapcoat dinta ne ta Nufi Shashen Diza Tafi Minti Goma Tana mata Knooking kafin tazo ta Bude mata Shekeke taTsaya Tana kallonta Tana Sanye da Rigar Barci Doguwa mai Taushi ta kuma Saka Hannuwanta ta kare Kofar alamun bata Bukatar Rumana ta Shigar mata Gida.

Mirmishi Rumana ta sakar mata Tana Fadin"Ina kwana Diza.."Tabe Baki Diza Tayi kafin ta amsa da "Lafiya.."Tafada Tana wani Mele baki Rumana bata Damu ba ta gyara Zama Tana Fadin"Kun Dawo Lafiya..? Ya kuma Baba da Jiki..? Jiya nayi ta Jiran Dawowarku agidan Hajja baku Dawo ba Har na Tafi asibiti Chan na kwama Dayake Call nayi...Shine nace bari na Shigo nayi muku ya mai Jiki.."
Har tagama Mganarta Diza na Binta da wani kallon Tara Saura kwata Tana gama mganarta Ta Wani Yarfa hannu Tana Fadin"Ayya mai Jiki da Sauki..Angode..!
Daga haka ta juya tana Shirin Rufe Kofa Rumana tace"Mansur din yana Ciki..!? Diza tace"Baya nan.."Da karfi Tana wani Zare Ido Da Sauri Rumana taja Baya Tana Binta da kallon Mamaki kafin tace"Ikon Allah..Ni kuwa Diza kowani Laifi nayi Miki..?
Diza Ta Sakarmata Idanuwanta Tana Fadin"Bangane ba..? Rumana tace"Tun bayan auran mu naga kin Sauyamin Diza Duk Da Daman Chan bamu da Alaqa mai karfi ammh Yanzu da muke Zaune Gida Daya bana gane kanki.Sai naga Kamar ko Nidin ce nayi Miki wani abu wanda bai Miki Dadi ba ko kuma Nake yi wanda bai miki Dadi ba.."
Tafada Tana kallon Dizan wacce Daga alamu ta Gaji da tsayuwar da Mganganun Rumanan Duka.

Mirmishin Rainin wayau ta Saki Kafin tace"Ke kike ganin haka..Ammh nikam Babu abunda kikamin..Ni kuwa Diza me zakimin Dr Rumana..? Ta karishe Fada Cikin Salom Rainin Wayau Rumana sai kawai ta kada kai Tana Fadin"Shikenan..Daman Bana son muna zaune waje Daya muna Shiga Hakkin juna ne.."Diza Tace"Kada ki Damu.."Daga haka kawai ta maida Kofarta ta Rufe Ta bar Rumana Tsaye Tana Bin Kofar da Kallon Ciki wani Takaichi da Bakinciki Lokaci Daya da Mamakin Diza..








*Janafty..*
1/1/22, 18:54 - Maryam Badmsi: *SS...26*

*Kibiya ki karanta cikin Aminci da salama 0969067488 Mace mai aji mallakan komai nata take yi bata jiran abun sata*

"Har Rumana takai Shashenta Mamaki da Takaichin Diza mai Barta ba bata ma samu Shiga Ciki ba kan Daya Daga Cikin kujerun Falon ta yada Zango Cikin Juyayin Takaichin Diza da kuma karin mamakinta.

Ta Dade zaune Tana Tufka Tana warwara Daga karshe ta yanke Shawaran Fita Daga Dukkan Abunda ya Danganci Diza Domin Tsira da Mutumcinta ko bakomai Ai tana gaba da ita Ita ce karama Da ita kamata yayi ita ta Dinga Binta ba ita Zata Dinga Binta Tana mata wulakanci ba Hakan yasa ta watsar da komai ta Shiga Ciki Bedroom dinta tayi wanka kana ta Shiga Kitchen ta Dafa Ruwan Tea ta Soya kwai taci ta koma Daki ta kwanta Duk da Tana Kokarin Boye Abunda ke aranta ammh Tabbas Sha"anin Diza da Hallayarta ya fara Fita kan Rumana gabadaya.

Ranar Acikin Shashenta ta Wuni Bata Fita ba sai Washegari da yammah Ta tafi asibiti,chan ta kwana sai da Safe ta Dawo Taso ta Hadu da Mansur tamai yamai Jiki ammh Hakan bai samu ba Shima baya Zama Tunda ya Dawo,In Dare yayi Rumana Har dakon Dawowarsa take yi ammh Har Lokacin Barcinta yayi baya Dawowa Diza kuwa Wajen Catering Dinta take zuwa Wani Lokacin Tana Jin Dawowarta Da yammah Tunda yanzu Call take da Safe take dawowa Gida.
Ganin bata samu ganin Mansur ba yasa ta kara Kiransa a waya tamai yamai Jiki yace Jiki yayi Sauki Yayi ta bata Hakurin Insha Allahu zai zo yaci Girkinta Baya Samun Zamana ne tace bakomai da Haka suka yanke kiran.

Wannan Satin Gabadayansa Call Rumana Tayi,Ranar Jumma"a Ta gama Call dinta Da Safe Data Fito Daga asibitin Wata Aisha Bala Bayarbiyace mazauniyar Sabongari Sun kan gaisa Sama Sama da Rumana Har in Ranar Aikin yazo Rana Daya in sun Tashi Takan Rage mata Hanya,ita taji Tana son zuwa kasuwa sai Itama Rumana ta bita suka Tafi Tare Daman kayan Cefenanta Duk sun kare ta Cire kudi Cikin Kudinta Dake banki Tayo Cefananta Hardasu Nama da Kifi Domin duka sun kare Kwai ma ya kusa karewa da Dankalinta sai kayan Miya Tumatur kuma sai ta Siya na gwangwani ta Siya kayan su Magi sai kayan Hadin Zobo da Aya na kunun aya Tadai yi siyayyah Sosai wanda zai kwan nan mata Biyu kafin ya kare,Bata Taba amfani da Katin Bankin da Mastur ya bar mata ba, da Kudinta Take amfani balle ma Tana da kudi Sosai aciki Tun abaya Abba yakan saka mata 50k duk Wata ne kuma ko yanzu bai fasa ba Domin Shekaran jiya ma ya Turo mata Kudi 50k yace ya bata ne kyauta ta Kirashi Tamai Godiya.

Ranar Bayan ta Dawo Zagewa Tayi ta gyara Shashen nata Tayi Mopping Dinsa kal kal Ta saka Turaran Wuta Dana Tsinke,Dakin Mastur ne kadai bata Gyara ba Toh Ta ina ma zata gyara ya Kulle Dakin ya Tafi da makulli Kichen ma ta gyaraahi ta gogeshi yana kyalli Ta Jera kayan Cefanan Datayo kowanne da Muhallinsa Kana ta Tattara kwanukan Data Bata Jiya Tayi wanke wanke Gobe Take ayyanawa aranta Zata je gida Wajen su Hajja ta Gaisheshi Kuma zatayi abinci Tatafi dashi Kula Biyu Daya su Hajja Daya kuma Mommy Tunda dai Gobe Tana Gida sai Ranar Talata Zataje aikin kuma na Safe ne.
Bayan Tagama ta Shiga Tiolet dinta ta wanke kananun kayanta da Sukayi Datti Ta Shanya anan Cikin Tiolet din Sauran kayan kuma Bazata iya wankewa ba Ko agida ba ita ke wanki ba Suna da mai wanki da guga Sai ta bari in Taje Gidan Hajja Gobe Ta Tambayeta in da Zata kai a wanke mata Harda guga.
Sai da tagama Komai kana Tayi wanka ta saka Wata Doguwar Riga wacce bata kai mata kasa ba mai Hannun Shimi fenten wake Tayi mai Allayahu taci da Daddare Tayi kallonta Kana tayi Shirin kwanciya.

Gari na waye da Wuri tatashi Ta Fara aikinta Fride rice Tayi Shirin yi musu,Sai Zobo da kunun Aya,Ta Kichen Tana Girki wayarta kuma Tana Falo Batasan ana ta Kira ba Sai da ta Gama Fride rice din Gabadaya wacce Taji Hanta ta juye a Kololi guda 2 duka Girmansu Daya Sauran kuma ta Zuba awata karamar kula Zobon ma Ta gama Hadashi Yana Cikin Fridge saboda yayi Sanyin Kunun ayan ne Zata Hada Daga Baya.
Tana Zuwa Falon Zata Shiga Bedroom taji karar wayarta Dake kan Center Table Tana zuwa Ta Dauko Abunda ya bata mamaki Sunan Mastur Dataga yana yawo kan Sreen din wayarta Sai mamaki yasa ta kasa Daga Kiran ma Saboda Rabonta Dashi yau kwana Biyar bai kirata ba itama Bata Kirashi ba Tana Tsaye Har wayar ta katse Bata Daga ba Sai kawai ta Maida wayar ta ijiye Tana jin wani Daci acikin Ranta Daman Daurewa kawai take Saboda kada ta Nuna gazawarta Ammh Tabbas Lamarinta da Mastur Yana Cimata Tuwo akwarya Bata son Daura ma kanta Damuwa ne Shiyasa take Kauda komai ta Nuna komai ba komai ba..

Bedroom dinta ta koma ta Dauko Abunda Zata Dauko ta koma Kitchen ta Fara Hada kunun Ayanta Daman ta nikan Ayan a Blander Duk sai kuma Kuzarinta ya Ragu har ta gama Komai ta saka Madaran Ruwa Ta Saka Cikin Fridge ta gyara Inda ya Baci ta goge komai Kana ta Fito Bedroom ta koma ta Shiga wanka ganin 12pm tawuce Tana Fitowa ta Shirya Cikin Shadda Mai Ruwan Hoda Doguwar Riga wacce Taji Stone work mai Ratsin Blue sai ta Dauko Blue din Takalmi da Jakarta ta ijiye agefe,Kitchen ta koma ta Samu Manyan Gororin Data Siyo akasuwa Jiya Guda Hudu Biyu Ta Zuba Zobe Biyu kunin Aya Ta Shiga Store ta Dauko Manyan kanduna guda 2 Ta Jera kowacce kula da Goran Zobo da Kunun Aya Guda Daya Daya,Ta bar shi nan acikim Kitchen din Ta koma Daki ta Tada Salla Saboda Taji an Fara Kiran Sallar a wasu masallatai,Bayan ta idar ta fito Taje ta Dibo Abincin afilet ta Fito Falo Dauke da Filet din Abincin da Mug Data Zuba Kunun Aya nan Kan Daya Daga Cikin kujerun Falon taci ta Koshi ta Kora da Ruwa kana ta Tattara komai Zuwa Kirchen ta koma Daki Ta Shiga Tiolet Ta wanke Baki Tazo ta gyara Daurinta Daman ba wani Makeup take yi ba Hoda kadai ta saka sai man Baki ta Dauki Jakarta Da key din Motarta ta Fito Sai da ta Shiga Kitchen ta Dauki Kandunan ta Fita Zuwa Wajen Motarta ta Bude baya ta saka Hade da Jakarta kana ta koma Ta Dauko Wayarta Ta Rufo Kofar Shashen nata batayi mamaki Rashin ganin Motar Diza ba Domin Daman Da Safe Taji Fitanta Mansur kuma Daman Baya zama yanzu Hon Tayi megadi ya Bude mata ta Fice Daga Gidan ya Bita da Allah ya Tsare.

Gidan Daddy ta Fara Yada Zango Har Cikin Haraban Gidan ta Shiga da Motarta Megadi na Mata maraba ta Fito Tana kara gyara Zaman gyalenta asaman kai Bayan Motan ta Bude ta Dauko Kwandun abinci guda Daya Ta Nufi Cikin Gida Tana Shiga Taci karo da Mommy a Falon kasa Tayi bakuwa Tana ganinta Tatashi Tana Mata Maraba Kasa Rumana ta Duke Tana gaida Mommy da Bakuwarta Bayan ta ijiye Abunda ke Hannunta agefenta Mommy ta Shiga kwalama Mama Fadime Kira sai gashi ta Fito da Gudu Tana Zuwa Mommy tace"Maza ki kawo ma Rumana Ruwa da Lemo.."tafada Tana komawa Ta zauna Da Sauri Rumana Tace"A"a Mommy a koshe nake..Ai Daga Gida ne ma.."Mommy tace"Allah Sarki..Nazata Daga asibitin kike Domin Yanzu nan Diza tatashi Daganan ta Shiga wajen su Hajja ne Zata je ta Duba Usmanun Balaraba ba Lafiya nake Tambayanta kina ina tace kila kina asibiti.."Rumana Ta Murmusa Tana Fadin"Yau ban je ba Mommy sai Ranar Talata.."Mommy tace"Ayya..Kice Mastur ya gayamiki kenan Zaku je gaida Usmanun Balaraban kenan..? Sai yanzu Rumana Ta Fahimci Dalilin kiran Da Sauri Tace"Eh Mommy.."Mommy tace"To Tashi maza ki Hanzarta Ku tafi Tare da Diza Ta Shiga wajen su Hajja.."Rumana Batayi gaddama ba ta yunkura ta Mike Tana Fadin"Mommy ga abinci.."Tafada Tana Turamata gabanta sai Mommy ta saki Baki ta Juya tana kallon kawarta Hajiya Barira Tace"Hajiya kinga Abunda nake gaya Miki ko..? Rumana Diyar albarka Harda Abinci kuma..? Rumana  tana Mirmishi tace"Eh Mommy..Na kawo muku ne keda Daddy.."Mommy tace"Mungode Allah yayi Miki albarka Rumana.."Mommy ta Fada Cikin Bayyana Farincikinta Rumana Batace komai ba sai Mirmishi take Tace"Mommy bari naje..Zan Dawo kafin mu tafi gida.."
Mommy tace"Ok.Sai kun Dawo ki samu Diza gidansu Hajja.."Rumana ta amsa da toh ta Fice Daga Falon Mommy ta Bita da kallon Sha"awa Kafin ta maida kallonta kan Hajiya Barira Tana Fadin"Kinga abunda nake Fada Miki yanzu ko..? Rumana tafi Diyarki wayau da Hankali Wlh yarinyar nan bata Zuwa min Hannu Rabbana Koda ace muna Dashi ammh ai Wayau ne kasan zaka zo waje ka Riko wani abu..'Hajiya Barira tace"Hakane..Kinsan kuma da yanayin gogewar ilimi da ita Rumanan Tafi Dizan Hajiya Asiya.."Mommy ta Jinjina kai Tana Fadin"Da wannan kuma don wannan..'Tafada Lokaci Daya tana Jawo kwamdon Ta Bude ta Ciro kulan ta Bude Kamshi ya Dakesu,Mommy Ta shaki Numfashi Hajiya barira ta Leka Kulan Tana Fadin"Kai wannam Delecious din fa..Zuba min Zan ci Hajiya.."Ta karishe Fada Tana yar Dariya itama Mommy Dariyan taketa Dago Zobon Tana Fadin"Harda Abunda nafi so Zobo.."
Mama Fadime ta kwalama Kira tace tazo da Filet da Cokula.


Rumana na Fita Bata Tsaya Daukan Motan taba ta Dauki Kwandon Abinci da Jakarta ta Fita Zuwa Gida wajen su Hajja Tana Sallama kuwa taci karo daDiza Zaune afalon Kan Kujera Ayya na gefenta suna Hira Batayi msmaki ba Domin taga Motarta a Kofar Gidan Wanda Dazu Bata lura da ita ba Ayya na ganinta ta Fara mata Maraba sai ga Hajja ta Fito Daga Daki Da Hijabinta wanda ta idar daSalla Kasa Rumana taZauna tana gaishesu da Tambayan yamai Jiki suka amsa mata Cikin kulawa Hajja ta kalli Rumana tana Fadin"Yanzu nake Zuci Zucin na idar da Sallah nace Diza ta kiraki taji ko kin Taho..Tunda munyi mgana da Babban Mutum yace zai kiraki ya gayamiki Kizo ku leka Gidan Balaraba ku gaida kawunku bashi da Lafiya.."Rumana ta Sadda kai Cikin Ladabi Tana Fadin"Eh Hajja..ban dade da zuwa ba Dayake na Shiga Wajen Mommy mun gaisa.."Hajja tace"Allah sarki..Tana Lafiya..? Rumana tace"Lafiyanta kalau..Daga haka ta Mike da kwandon Abincin zuwa gaban Ayya ta Ijiye Tana Fadin"Ayya ga Girkin nayo Miki.."Ayya ta Washe baki Tana kallon kwandon lokaci Daya Tana Fadin"Ah..Kaga Uwargida mai kaunar Amaryata..Lalle na yarda kina Maraba Dani Diyar nan Hajara kalli wani abun Arzikin..! Tafada Tana Nuna ma Hajja wacce take gyada kai tana kara Girmama Rumama acikin Ranta Cikin Farinciki Ta kalli Rumana Tana Fadin"Rumana Bakya gajiya Da Hidima..? Kan Rumana na kasa Tace"Bakomai Hajja.."Hajja ta gyada kai Tana Fadin"Allah yayi albarka Rumana."Ayya ta amsa da Ameen Diza na gefe Tana Latsa wayarta Daman tun Shigowar Rumana ta Dauke kanta Kmar bata ganta ba yanzu ma Kara Hade Ranta Tayi Kamar bata Taba Dariya ba Rumana ganin Idanuwan su Hajja yasa ta Daga kai Tana kallon Diza Tace"Diza ashe kin Taho kina ta Jirana..? Kuyi hakuri abincin ne ban Karisa da wuri ba..!
Diza ko kallonta Batayi ba Ta Tabe baki Lokaci daya Ta Mike Tana Fadin"Uhmm muje ko..? Tafada Tana Yarfa ma Rumana wani kallo Mikewa Tayi Tana Kallon Hajja tace"Hajja bari muje mu dawo.."Hajja tace"Ku gaisheshi..Sai an juma zamu leka Nida Hajiya.."Ayya ma tace su gaishesa suka Fice Daga Falon Ayya da Hajja suka koma Yabom kyawawan Hallayar Rumana.

Diza kuwa suna Fita Bata ma Tsaya Jiran Rumana ba Tayi gaba tana wani Takun yanga Da Takalminta mai Tsini ita dai Rumana tana Binta abaya Sanin bata san Gidan ba Bawani Nisa sai gaahi sun iso Diza ce kan gaba suka Rafka sallama suka Shiga Gidan ba kowa a tsakar gidan Balaraban ne ta Leko Daga Dakin Kawu Usman din Tana musu Maraba ta ganesu Gaisheta sukayi kafin ta musu Jagora zuwa Cikin Dakin yana kishingide kan Katifa yana Jin radio suka Shigo,Kan Tabarman Dake Dakin suka Zauna Diza ta Fara gaisheshi ya amsa sai Rumana sukamai ya Jiki yace da Sauki ganin yana musu kallon Rashin Sani ne yasa Inna Balaraban ta kallesa Tana Fadin"Baka gane su ba ko..? Surukanka ne Matar Mastur ne Rumana da Matar Mansur hadiza fa.."Baki ya Rike yana Fadin"Ba Shakka..kuyi hakuri Tsufan yazo..Sannunku Allah yayi muku albarka Allah ya baku Zaman lafiya.."Balaraba ce ke amsawa da Ameen Ita dai Rumana kanta na kasa Kawu Usman ya kalli Rumana yana Fadin"Megidan naki yana chan wajen akin nashi ko..? Ai dazu ma munyi mgana Dashi Allah dai yayi ma Mastur Albarka Kullim sai ya Kirani yaji Jikina..Shima Mansur din kullum sai yazo ya Dubani Duk da Siyarsa tasu ta karato Allah ya Biyasu Duka Hidimata su sukayi su da Iyayansu Habibu da Alhaji Sunusi Babu Abunda Zance iya ce musu sai Allah ya Biyasu da aljannah.."Suka amsa Dukkansu da Ameen kafin ya Dora Da Fadin"Ya wajen Jikin Baban Mijin ki Khadija..? Diza ta Rausayar dakai Tana Fadin"Da Sauki kawu..Gobe ma zamu koma mu Dubasa Har dasu Ayya.."Ya gyada kai yana Fadin"Masha Allah..Ba Domin ina kwance da Balaraba ta Biku taje ta gaisheshi.."
Diza tace"Bakomai kawu ai ma ya samu Sauki Har an sallamosa Daga asibiti.."Yace"Toh Alhamdulillah Allah kara mana Lafiya.."Suka amsa da Ameen sun Dade yana ta Jansu da Hira Yana da Barkwanci da Hira Har Balaraba ta gama Dambum Masara ta Zubo musi sai Diza ta Mike tace ta Koshi ita kuma Rumana Ganin bazasu ji Dadi ba in Basu ci ba sai tace ta saka mata a kwano Zata Tafi Dashi Gidan su Hajja taci achan da Farinciki kuwa ta saka mata Cikin Sabuwar Samira ta Basu Har Kofar Gida ta Rakasu Tana Godiya ganin haka yasa Rumana ta bata 3k,gashi Daman basuzo da komai ba Dakyar ta amsa Tana ta Godiya.

Suna Fita Daga Gidan Diza ta kalleta Ta Tabe baki Tana Fadin"Iyayi...!Daga haka kuma sai ta saki Dariya ta Juya tana Tafiya Tak Rumana batace mata ba Domin tayi ma kanta alkawarin ta Daina Biye ma Diza da Duka Abunda take Nufi akanta Daga Gidan Inna Balaraba Diza bata koma Gida wajen su Hajja ba ta Shiga Motarta ta karisa Shiga Gidansu ita kuma Rumana ta koma wajen su Hajja da Dambunta nan Hajja ta Kara mata mai Mai da Magi Taci Ta Rage ma Hajja Ayya kuma Abincin da Rumana Ta kawo Take ci Tana Korawa da Zobo Tana Santi.
Rumana tayi ma Hajja mganar Tana son zuwa Duba baban Mansur Gobe in zasu Tafi Ayya tace Daman har da ita akace wayar Mastur ne akayi ta Nema ba"a samu ba Balle agayamai Gobe Zasu Tafi Harda Mommy da Hajja da Ayya Direban Daddy zai kaisu Shima da Hardashi Zai je Sai Tafiya ta Kamashi Zuwa Lagos Gobe kan Motocinsu ne Da sukayo Oder suka samu mtsala Daga Chan Shine zai je ya gani,Rumana na Jin haka tace Zata je in ta koma Gida Zata Kira Mastur ta gayamai Hajja tace Shikenan.
Nan ta wuni Sallar La"asar Duk anan Tayi kama ta Share ma Ayya Dakinta ita da Hajja ta gyara Ta Share Falon Tas Ayya da Hajja sai sakamata albarka suke Bayan Haka ta Tattara wanke wanke Tayi Hajja nata bari taki Ta kuma Zage Tayi ma Hajja Miyar Jajjage Aturmi Ta Jajjagashi Ta soya Miyar Ta hana Hajja Komai ta Dafa Farar Shinkafa Sai Ana Kiran Sallar mangariba ta Gama Ta kwashe komai ta Zuba A muhallinsu Adakin Hajja Tayi alwala Tayi Salla Tana zaune taji Shigowar Baba Habibu Sai da tagama Azkar dinta ta Fita Falo ta Rusuna ta gaiaheshi ya amsa Cikin kulawa Ayya na gefe Tana Koramai irin Dawainiyar Rumana garesu Shi kuma yana ta Saka mata albarka kunya ya kamata ta kasa zaman Falon sai ta Shige dakin Ayya bata Fito ba Har sai da Taji Shigowar Mansur da Diza kana ta Fito Baba Habibu na cin Abinci Hajja ke Fadamai Girkin Surukarsa ce Rumana Mansur na jin haka yace ma Hajja Shima zai ci anan aka Zubomai ya Baje yana ci Diza kuma da akayi mata Tayi tace ta Koshi Rumana kuma tace a kula Zata saka sai taje gida Zataci,Hajja kuwa ta saka mata Cikin kularta data kawo musu Abinci.
Diza dai na Falon Rumana dai Dakin Ayya ta koma ta zauna Tana Jin an Fara Kiran Sallar Isha"i ta Mike Tayi sallarta Bayan ta Idar ne Ayya ta Shigo Dakin nan ne take Tambayarta Inda Zata kai wanki Ayya tace Gobe Tazo Dashi Akwai wani mai wanki Chan gabansu,Itama Ayya Sallar Tayi sai da ta Idar kana Rumana ta Mike Tayi Shirin Tafiya,ta nada gyalenta Ta Dauko Jakarta ta Fito Falo Mansur da Baba Habibu sun Fita Sallah Diza ce kadai Zaune tana Latsa waya Rumana sai da ta jira Hajja ta Idar da Salla Ta Fito sai ga Su Mansur sun Dawo nan dai Mansur yace ya yi ta Kiran Mastur bai samu ba Baba Habibu yace bakomai Ruman Tunda Tana son Zuwa ta Shirya kawai Daganan sukayi musu sallama Suka Fice Bayan Rumana ta Dauko kwandonta Sai da suka kara Shiga wajen Mommy Rumana Tayi mata Sallama har Lokacin Daddy bai Dawo ba Bata barta Haka ba sai da ta bata kyauta awarwaron mata mai kyau Diza sai jin Haushi Take Tare suka Jera su ku Motar Diza na Gaba Rumana Tsakiya Mansur na Bayansu Har gida Suna Zuwa kowa ya Faka Motarsa Rumana Sama sama Tayi musu sallama Mansur ne ma ya amsa ta banda Diza.

Rumana bata Gwada kiran Mastur ba sai data gama Duka Abubuwan da Zatayi Tayi Shirin kwanciya Wajen karfe 10pm kana ta Kirasa Har ta katse bai Daga ba sai da Ta kara Kira ya Katse Kiran sai gashi yabi Bayan Kiran nata Cikin Dakiya ta Daga Kiran Lokaci Daya da Sallama.

*******

Mastur Dake Kishingide kan Daya Daga Cikin kujerun Dake Falon Apartment dinsa Gajeren wando ajikinsa ko Riga babu,Mug ne a Hannunsa yana Shan Tea Kafarsa Tana Mike Sambal kan Center Table din Dake Falon Gefensa kan kujera Filet ne Shake da Cake da Donut yana Dauka yana ci Daya bayan Daya yana Korawa da Tea din Tsakani ga Allah Rumana ba karamin Taimakon ta yayi ba Tunda yazo bai Siya abinci ba Abubuwan Data Taimake shi dashi yake Rage Zafi dasu Miyar Datayi mai kuwa ki yaci Da Buredi ko kuma ya Dafa Farar Shinkafa Takaichinsa Daya Dambun Nama ya kare Jiya ya Cinyeshi Duka,Saura Cake da Donut Su yake shan Tea dasu da Safe ko da yammah in ya Dawo alokacin Daya ga kiranta yana ta Ayyana yadda Zai Tura mata Sakon Godiya ne ammh kuma sai ya Rasa Me zai Rubuta kuma ta Ina Zai Fara..!

Lokacin Dayaa Kirata ta Dauka yaji Tayi sallama sai da yaji kunya yasan ko kiran Dazu kila tagani Rashin Kirkinsa yasa Tayi Banza Dashi Eh mana baida Kirki Tunda ya Tafi fa sau Biyi sukayi mgana kamar ba Matarsa ba Shi kuma ya rasa yadda Zai iya karban wannan abu wai yau Rumanace Matarsa Game Da duka Ahalinsa Baya waasa ammh Game da Rumana bashi da Kirki Sam ya kasa ya kasaDaurewa ya Dubeta a matsayin Datake kai Zuciyarsa Mace Daya take so kuma Bayan ita ba wata Ba Laifinsa ba Yana Jin wani Nauyi matukar ya Zauna da Rumana yana Yaudaranta alhalin ba ita yake so ba..!

Rumana Taji wani irin Jin Tayi sallama Mastur yayi mata Shuru bai amsa ta ba sai da ta kara Duba wayar taga yana kan Layi sai Tayi Tunanin Kila Rashin Daga wayar Dazu ce Shiyasa da Sauri tace"Am sorry dazu ka Kirani ban gani ba..Munje mu gaida gaida Kawu din ne.."Tafada Tana Gyara zamanta,Mastur Dake Sauraranta yayi gyaran Murya Kafin yace"Kada ki Damu..Kina Lafiya..? Rumana ta amsa da Cewa"lafiya lau ya aiki..? Mastur yace"Alhamdulillah Hp komai da Lafiya.."Sai Tambayan nashi ya bama Rumana Dariya Cikin Ranta Tana Danne Takaichinta,Tunda ya Tafi bai taba Kiranta ya Tambaueya ya take ba..? Ya aikin data Fara Zuwa..? Asibitin sun karbeta ko yaya..? Bai taba Damuwa da hakan ba Ita Me zata ce..? Wa zata Fadama kukanta..? Alhalin Awajen kowa Mastur mai kula ne mai Daraja mai kima ne Kullum sukayi waya da Umma sai tace Mastur ya kirasu ya gaishesu Sai tace ita baya kiranta..? Wazai yarda da ita..!? Babu Shiyasa gwara Tayi kukanta ta Share Hawayenta Tana ganin Tabbas Tayi kuskuran Fara Furtamai kalmar so..Ammh kuma ai bata Tursasashi auranta ba Kuma Ai Da kansa yace yana Ra"ayinta Toh in Hakane mayasa ya Rataye ta yana mata wannan Rikon Sakainar kashin..?

Yadda Ta Dauke Wuta Haka Shima ya Dauke mata shidai yana Sauraranta Bai da ta Cewa Kalamansa Duka sun kare,Dakyar Rumana tayi yaken Mgana Tace"Dama..Dama kan mganar Zuwa gaida Baba Sule ne gobe Su Mommy zasu tafi Harda Hajja da Ayya Shine nace zan Bisu ance ana ta kiranka ba"a samu ba.."
Sai da yagama Jinta Tas kana ya Muskuta yace"I know..Allah ya Kiyaye Hanya.."Mamaki ya kamata Shi komai ya sani ne..? Daganan tace mai da Safe suka yanke Kiran Tana kara Nazarin Wasu abubuwaj abunda bata sani ba Ba Dadewa suka gama waya da Baba Habibu ya gayamai Komai Shi da bama sai an Nemi izininsa ba Bashi da Wata Mtssla sai dai kuma Hakan Datayi yasa yaji Girmanta Dayake gani Ya kara ninkuwa Sosai Tana da Hankali Da Tarbiya..








*Shakira...*
1/1/22, 18:54 - Maryam Badmsi: *SS...27*

*Kibiya ki karanta cikin Salama 09069067488 Mace mai aji mallakan komai nata take yi bata jiran Abun Sata*

"Rumana ita kadai ta Dinga Tunanin bai kamata atafi hakanan ba babu abunda Zata Rike ma mara Lafiya ba,,Tayi Tunanin kara kiran Mastur sai kuma ta fasa Gari na wayewa Bayan ta Idar da sallar asuba bata koma ba ta Shiga Kitchen Dankalin Turawa ta Fere mai Dan yawa Daman Tana Sauran Alaiyahu sai Kuma ta Duba Taga Tana da Sauran Hantan Data siyo a kasuwa Duk da bashi da yawa sai tace bari ta kara da Nama.
Kafin kace me ta kamallah Fanten Dankali mai Ruwa Ruwa da Alaiyahu yaji Hanta da Nama Daidai na Mara Lafiya Tana gamawa ta Kwasheshi a wata Sabuwar kularta Ta Dauko kwandon Data Dawo Dashi Daga Gidan su Hajja ta saka aciki kadan ta Rage wanda Zata Karya Dashi kafin su tafi.
Sai da tagama Komai ta gyara Kitchen din Bayan ta Dafa Ruwan Tea kana ta koma Bedroom Dinta ta Shiga wanka Agurguje ta Fito ganin 7:30am ta wuce Shirin nata ma Agurguje Tayi Shi Wata Atamfa ta saka super mai kalan baki baki sai tayi amfani da Bakin mayafi da Bakar jaka da Takalmi
Kitchen ta koma ta samu Filet ta Zubo Fenten Dankalin ta Zubo Ruwan Tea din A wani karamin mug wanda yaji Citta da Ganyen Na"a Na'a Daman taji Kamar mura na son kamata Saman Dining ta Zauna Tana Sha tana kurban Tea dinta ta gama kenan ta tashi Zata maida kayan Kitchen taji kiran wayarta Wacce ke Cikin Jakarta nan Falo sai da takai komai Ciki Ta Daureye Ta Kifesu kana ta Fito Tana Zuwa Ta Fito da Wayar tana Duba mai Kiran sai Taga Diza ce Batayi mamaki ba Sanin kila ana Jiranta ne Tana kokarin Sanya Mayafinta wani Kiran ya kara Shigowa sai ta Daga Tana Sallama.
Diza Da Mansur dake Haraban Gidan ta Dake Murya Tana Fadin"Mansur yace ki fito.."Daga haka bata Jira cewar Rumana ba ta Datse kiranta Mansur bai jita ba Domin Yana Gaban Mota yana Duba wani abu ita kuma Ta Baya Tana Latsa wayarta.

Rumana bataDamu ba ta Saka Mayafinta Ta Dauki Jakarta Daman kwandon Abincin ta kawo Shi nan Falon sai kawai ta Sunkuta Ta Fito,Sai da ta Tsaya ta Kulle Shashenta kana ta Karisa garesu Daidai Lokacin da Mansur ya Fito nan suka Fara gaisawa Rumana tace"Dakai zamu je Ranka ya Dade..? .Mansur Dayaji Dakakkiyar Farar Shadda Harda Babbar Riga yace"Kai Antynmu Harda ke..? Dani za"a je saboda akwai yan Tawagarmu ta party mu da zamu je Tare suna son gaida Baba.."Rumana ta gyada Kai Tana Fadin"Ba Shakka Honourable Mansur..Chairman sai kayi Tun yanzu ma na gama baka Kujeran.."Tafada Tana yar Dariya Shima Mansur din yana Tayata Diza Dake gefe Sai Hararan Mansur tske ta gefen ido Yake Shi kuwa bai ma ganta ba Rumana kuwa Yi tayi kamar bata ganta ba.
Rumana ta kalli Mansur Tana Fadin"Budemin Both na saka wannan Basket din. "kallon Abun Hannun nata yayi kafin yace"Anty Dr.Rumana wannan fa... ? Rumana ta wuce Tana Fadin"Nidai Budemin..Abun Mara Lafiya ne..'Mansur ya Murmusa Yana kara ganin girman Rumana ya shiga Motar ya Bude mata Booth wanda Diza na wajen ne da Farko jin haka yasa Ta tashi Daga wajen ta Zagaya ta Bude gaban Mota ta Shige Tana karamin Tsaki Ita kuwa Rumana bata ma san Tanayi ba Ta Bude Booth din ta saka Basket din tazo Mansur ya Bude mata Gidan Baya ta Shiga yana mata Tsiyan Matar Dcp ce Dole a girmamata.
Diza ta shaka Haka ta Hade rai kamar Tayi Kuka Sai da Rumana suka Fice Daga gidan ne suka Dauki Hanya Rumana ta kalli Diza Tana Fadin"Amarya Diza an tashi Lafiya..? Dakyar Diza ta amsa mata Shima Saboda Mansur ne Da ace su kadai ne wlh ko kallonta bazatayi ba yanzu anan Duniya ba wacce ta Tsana take jin Haushi irin Rumana..
Mansur Dake tuki ya Kalli Diza yana Fadin"Daman baku gaisa ba Firstladyta..? Ya kamata ki Rika Bata Girmanta a mtsayinta na Matar Babban Yaya,ki bita Har Shashenta ki gaisheta da kwana Ita din Antynm ce."Ya karishe Fada yana yar Dariya Diza Dataji Haka sai taji kamar ta Gunduma ma Mansur Ashar sai kuma ta Fasa kawai ta bame bakinta ta kauda kai Rumana kuwa yar Dariya Tayi batace komai ba Shina Mansur din Hankalinsa ya bar wajensu wayarsa aka Kiran ya Dauka suna mgana.

Koda suka isa Hanwa Tuni yan Tawagar Mansur sun iso mota Biyu 4matic Dayan kuma Doguwa ta Party ce irin ta Fita kamfe din nan sun iso suna ta Jiransa Sagir yana Ciki sai wasu Maza Har da magidanta wadanda suka Girmema Mansur din Diza Da Rumana Wajen Mommy suka Fara Shiga suka isketa itama ta gama Shirinta Harda Ferfesun kayan Ciki Dayawa ta saka mama Fadime tayi ma Mara Lafiya,Daddy bayanan Tun Safe ya Tafi Sokoto Direba ya tukasu Tunda yanzu Mansur zai kaisu Bayan sun gaisa Rumana ta barsu ta Fita Zuwa Gidan Hajja Duk da Mommy bata da masaniyar Rumana ta Riko wani abu ammh sai da Tayi ma Dizan Fada Taya zata je gaida Uban Mijinta bata Dafa Komai ba Sai Diza ta Tura Baki ta kalli Mommy tana Fadin"to ni Mommy me zan Dafa Don Allah..?gani nayi ba gari Daya ba kuma ai mansur yayi musu Siyayya gashi chan a Booth zamu tafin musu Dashi.."
Mommy Tana kallonta wani Takaichi na Cikata ta Sakarmata Dakuwa Tana Fadin"Kaniyarki nan..Ke bakisan Dubarun mata ba Khadija..Gidan fa Uban Mijinki Zamu.Mansur?  Haka zaki je hannu sake kina Matarsa ai ko bakonai kyauta nada Dadi balle Kina sane basu da Karfi sosai Tallafinsu Mansur da Mastur sai iyayanku Nidai kam ba Halina kika Dauko ba ba kuma na Alhaji ba Chan kika Roro wannan Mugun Halin Shiyasa Bazan Fasa gaya miki ba Sai dai kiji Haushi Rumana Tafi ki wayau da Sanin Mu"amalan yau da kullum..Ki Duba ko nan Zata zo bata Taba zuwa mana Haka Hannun Rabbana ba sai ke sakara mara wayau.."Diza data kusa Fashewa da kuka Ta Mike Tana Fadin"Mommy kenan..Shiyasa naganta da Basket kenan.Itama ba Don Allah take ba Son a sani ne..'Mommy tace"Eh koma son asanin ne tayi dai Tafiki dai..Ai Daman na sani ba yadda Yarinyar Zata Taho hakanan.."Diza bata kara Jinta Mommy ba ta Fito Daga Dakin Cikin Fushi ta Sauko kasa Fuu ta Fice Daga Falon kamar ta Fashe da kuka komai sai ace Rumana ce kan gaba akanta Rumana ta kwace mata Masoyi ta kwace mata Dangin Miji ta kwace mata Iyayenta Komai Rumana Ta Tsaneta Har Abada.

Tana Fita Waje taga su Hajja da Ayya har sun Fito Allah Sarki Hatta Hajja da Kulan Abuncinta da Dafo ma mara Lafiya,Dole ta saki Fuska ta karisa suka gaisa Baba Habibu kuma yana wajen Mansur suna gaisawa da Mutanensa sai ga Mommy ta Fito Mama Fadime na Bayanta Dauke da Basket,Amotar Mansur aka saka komai Mommy suka gaisa dasu Hajja da Baba Habibu Mansur ma suka gaisa da ita da Sagir Shiga Mota sukayi Diza ko kunya ta Shige gaba Duk kuwa da Kyfta mata idon da Mommy take yi ta Nuna bata gani ba Rumana da Mommy da Ayya da Hajja suka zauna abaya..
Sune akan gaba Sauran Tawagan suka Bi bayansu,Baba Habibu na Tsaye yana Daga musu Hannu da Fatan Allah ya kiyaye Hanya.

Dayake Sun Fito da wuri Shiyasa 11am suna Tsakar Dakin Inna Zainaba Don ma basu yi Gudu Sosai ba Inna Zainaba duk ta Rude Ta rasa Ina zata saka kanta Ta Riga ta gama Sakewa Mansur kam ya mata Nisa,Tawagar yan party dinsu Mansur basu wani Dade ba Bayan sun Duba mai Jiki su ka bashi Alheri Sosai Masu 5k,Masu 10k azahar kadai sukayi suka Juya ko abinci basu Tsaya ci ba sun sha dai Fura da Lemo Su kuwa su Rumana Danwake da mai da yajin Daddawa Maryama Tayi musu sai gashi suna Ci cikin marmari Duka abinci da suka zo Dashi sun bama Inna Zainaba Baba Sule sai Maimaita Godiya yake musu Har yana kwalla Da Ayya ta Nuna mai Rumana amtsayin Matar Mastur ya kalleta Sai kawai ya Bude baki yana Fadin"Allah yayi Miki albarka yar nan..Keda Mijinki Allah ya Duba ku..Kina mai addu"a ko..? Wlh Na Tabbata Mansur kadai na Haifa ammh Habibu ya bani Ya"ya Biyu Duka Maza Mastur Mutum ne Matashi ne mai kima da Daraja da Sanin ya kamata,Koda yauahe yana Tafe hidima Dani ni da Iyalaina Kowani Sati yana Turama Maryama kudi ta Bankinta yace acire ayi amfanin Gida Dashi Baya wuni ya kwana Bai Kirani yaji yajikina ba..Aduka Sallolina Biyar ina saka sa Ina Fatan yadda sukaji kaina Shi da Dan"uwansa Mansur da Habibu da Alhaji Makocinku Allah yaji kansu suma.."Ya karishe Fada Hawaye suna Zubomai Sharr Sai Ayya ta Fara Sharan Hawaye itama Jin yana Hawaye yana Fadin"Allah ya jikan ki Maryama..Kin Tafi da Burin ganin kwanki aduniya gashi kin Haifi ko abunda kika Haifa baki gani ba Macen kirki kuma Tagari Tunda nake batataba Sabamin ba Yau gashi bakya Raye da kin ga Yadda Mansur ya koma Da kin ga Yadda Mastur Dinki Yaron da kika so shi kamar Ranki ya koma adalilinki Kaunarki ga Mastur Nima ya Shafeni yau bakya Raye Hatta da Yayanki bai Yarda Dani ba Suna kula dani da Ahalina Gabadaya Allah yayi Miki Rahma Allah ya sadaki da Mala"ikun Rahma Maryama...'
Ya karishe Fada yana kuka Sosai gabadaya Dakin suka amsa da Ameen Ameen Kowa Dake Dakin sai da yaji Tahowar kwalla,Mansur tashi yayi ya Fice kada yayi kuka gaban Matarsa Rumana ma sai da Tayi kwallah Mommy ma haka Hajja ne da Ayya kamar yanzu Akayi Rasuwar,Kewar Maryama da Rashinta ya Dawo musu Sabuwa Sai da suka Share kwallah,Inna Zainaba na gefe kanta na kasa bata da Cewa Domin tasan Ko ita ba tace ga abunda Maryama Tayi mata ba sai ma itace Tayi mata gashi yau Rayuwa wacce suka kira Juya,ta Haihu ta Rasu ta bar Abunda ta Haifa gashi yau Yana ta Dawainiya dasu da shi da Yan"uwan Maryaman gabadaya ai bata da ta cewa
Momny ce ta saka baki Tana ta bama Baba Sule baki kana yayi Shuru,sai kuma aka koma Hira Rayuwa da Shekarun Baya Matan Yayyinsa duk sunzo sun gaishesu da Mazajensu wasu da suke nan,Harda kwanukan abincinsu,Sakina ma Tazo Daga Gidan Mijinta,Zuwa 3pm sukayi Shirin Tafiya Tunda zasu Biya Ririwai,Kafin su tashi Tafiya Sai da Inna Zainaba ta Kwanke musu Kololinsu ta bada aka saka musu a mota,Mansur kuma ya Sauke musu kayan abincin Dayazo Dashi bayan ya bama Inna Zainaba 20k yace ta Rike na Cefane ya bama Baba Sule 20k yace na komawa asibiti da zasu yi wani Satin in ya samu Lokaci zai Shigo in bai samu ba zasu yi mgana ta waya Sauran Baffanin nashi ma Duk ya bisu da kudi wadanda basa nan yabama Matansu,Haka suka tafi suna Daga musu Hannu da saka Albarka Mardiya kuma tace Zata zo Insha Allahu Ashe Mansur ne yace tazo Domin sunyi mgana da Mastur ta Dawo nan Wajen Hajja ta zauna ta Shiga makarantan Boko,Tunda ga maryama na Tare da Inna Zainaba.

Ririwai sukayi Sallar La"asar gidan Inna Karime,Sun iske Tayi Dambun shinkafa basu Tsaya ci ba ta Zuba musu suka Dauki Hanya Dashi,Karfe 7:40pm na Dare suka Shigo Zaria sai da suka kai su Hajja dasu Mommy gida kana Sukawuce gida Gabadayansu agajiya suke Tun ballatana ma Rumana tun ahanya ta Fara barci bata saba Doguwar Tafiya amota ba Tafi yin Tafiyan Jirgi in zata Lagos Sama sama Tayi ma Mansur da Diza sai da Safe ta Shige Shashenta Sallar Mangriba tayi da Isha"i Ta Dibi Ruwam Zafi a Fulas ta Sha Tea tayi Shirin kwanciya ta kwanta Saboda Gajiya Washegari ma Allah ya Taimaketa ba aiki sai ta Huta Maryama ta kirata awaya tamata bangajiya har ta bata Baba Sule suka gaisa yana ta Godiya da Saka musu albarka Da suka yanke Kiran Rumana sai ta kara Tsinkewa da Lamarin Mastur kowa Kaji ya Bude baki badai kaji ya fadi Sharrinsa ba sai da alhrrinsa ta Fahimci a wajen kowa Shi mai Kirki ne awajenta ne Bashi da Kirki da kulawa ko kadan.



*****

*Bayan wata Hudu..*

Bayan shudewar Wattanin Hudu,Abubuwa suna ta Faruwa yadda Allah ya tsara,Anyi Zaben su Mansur Wata Daya Da ya gabata kuma Alhamdulillah Mansur ya samu Nasaran Hawa Kujeran Chairman na Sabongarin Zaria Local goverment,Farinciki babu kama Hannun yaro Mutanen Dogowa sun zo kwansu da kwarkwatansu Domin Taya Mansur Murna,Abba da Umma ma sunzo Daga Sokoto Taya Mansur Murna anyi Walima A Haraban gidansu Dake nan Hanwa Locost,Har katon gida Mansur ya kara mallaka a Gaskiya Layout ammh yace bazai iya Tashi ya bar Dan"uwansa ba Suna Tare Har Abada Mastur ne kadai bai samu Zuwa ba alokacin Ba ma wanda ya Damu da Rashin Zuwan nashi sai Mansur din wanda yayi Fushi sai da Mastur din yadinga Ban Hakuri kana ya Hakura Mardiyaa kuwa Daman Ta nan Zaria ta Dawo wajen Hajja da Zama Mansur ya Daukan mata lesson Teacher yana Koyamata Darasin Turanci da lissafi,Sai kuma Islamiya Tana zuwa nan gaba dasu Kafin a sakata a makaranta Maryama Tana Chan maruka Mansur din ya Sakata makaranta Achan,Baba Sule kuma Alhandulillah jiki yayi kyau,Su Diza an zama matar Chairman Sai kuma Daga kai da Fifiko ya karu Rumana take mawa kuma ita bata gabanta Mansur yanzu ya zama Babban Mutum mai girma Honourable ne Yana Tafe da Excort dinsa Guda Daya Mota Daya na Take masa Baya Domin kafin Zaben Motocin da Abba ya Siya musu duka sun iso ta nan Kamfanin Daddy suka iso ssi gasu har Gida Guda Biyu iri Daya Biyu iru Daya ta su Mansur Benz ce kirar Toyota,sai tasu Diza accord ce kowa yayi Murna ammh banda Diza wanda ko Abba bata kira tamai Godiya ba sai da Mommy ta mata Fada Dayake gidan nasu Haraban nada Girma duka Motocin sun Dauke Rumana tana Hawa nata in wannan Satin ta Fita asibiti da Sabuwar wani Satin ta Dauki Tsohowar nata Mansur ma yana Hawa Tashi Sosai Duk yanzu ya mallaki Motocin Hawa sun fi Biyar Diza ma Bayan ta Abba Mansur ya Siyamata Sabuwa ta yayi 350 prado ana ta Fafa da ita Mastur ne kadai bai Hau Tashi ba Tunda bai zo ba Rumana sai dai Tayi kukanta ita kadai ta Share Hawauyenta bamai Lallashinta Saukinta Daya asibitin Datake zuwa
Su Diza an zama Manya mata Tuni Catering dinta ya kara Suna Kowa yasan na Matar mai Girma Chairman ne,Kodomin Ta sanka sai kayi Odering,Har Kwakwaryan party ta Shirya itama ta gayyaci kawayenta da abokam kasuwancinta ammh bata gayyaci Rumana ba kuma itama  bata yi Shishshigi ba,ta Debeta ta watsar bata gabanta koda yaushe yanzu gidansu na Jama"a ne Kofar gida Maza masu Jiran Chairman Cikin gida mata yan Siyasa ko yan Maula,Rumana bata ma cika zama agidan ba In bata asibiti Tana gidan su Hajja sai yamma take dawowa Balle ma Da suka Fara yin Seminar a asibitin nasu na yan Intenship.

Mansur ya kara siyan Filin gaban gidansu an shigar dashi Cikin Gidansu ya kara Fadada Haraban Gidan anyi Sabon Fentin an sauya Get Habibu kuma ya sauyamai mashin Tunda anyi anyi ya karbi mota yaki yafi son Mashi Har chan Gidansu na Maruka ya Bigeshi ya gyarashi Kowani Shashi na Gidan ya Fitar ma da Baba Sule da Inna Zainaba Flat dinsu na Musamman ya Zuba musu kayan More Rayuwa sai gashi inna Zainaba ta zama Cele A maruka tana mtsayin Uwa ga Chairman Baba Sule Uban Honourable Shi kuma Mastur ya Turo da kudi aka Siyama Baba Sule Sabuwar Mashin,Duk da Shawaran Mastur Mansur ya Taimaki Mutane sosai ya rabama Baffaninsa Jari ya siya ma Kanwarsa Sakina keken Dinki da Injin Nika ba anan kadai ya Tsaya ba Anan Zaria ma ya Fara iya Kokarinsa Domin duk da Mastur ba Siyasa yake ba yana Kokarin bana kaninsa Shawara kan yadda Zai gyara Lahirarsa.


Kwana arba'in da Tabbatar da Mansur a matsayin Chairman Aka kira Daga sokoto Cewa Ciwon Sugar din Abba ya tashi har an kwantar dashi a asibitin Uduth Hankalin Daddy ya Tashi matuka,Rumana ma Tana asibiti ba"a gayamata ba Mastur Dake parthercourt Har yaji Labari ita bata sani ba Sai Daga Baya Taji Labari,Tun alokacin ta Fara kuka Ranar basu samu Tafiya ba sai Washegari suka Tafi ita da Daddy da Baba Habibu da Mommy,Su Hajja zasu Taho Daga Baya sun je sun samu jikin nashi yadan Motsa Sosai Rumana Tayi kuka sosai ganin Abbanta bai san wanda ke kansa ba wannan Dalilin yasa Baba Habibu ya kira Mastur ya gayamai Halin da ake Ciki kwanansu Daya da Zuwa da yammah ya iso Garin Jirgi yabiyo ba wanda yasan da Zuwanshi,Ko Baba Habibu bai gayama yana Tafe ba Tun Bayan Bikinsu Daya Tafi sai Lokacin suka kara Ganin juna da Rumana tayi mamakin ganin ya Rame duk Yayi Baki sai Dan wuya kowa ma ya kara ganin Ramarsa,ammh Hankula ba kawance suke ba,aranar kam Jikin Abba da Sauki har Yana gane Mutane,Tunda Mastur yazo yana asibitin bai Tafi ba duk yadda Umma taso su koma Gida da Rumana yayi wanka ya Huta yace bakomai Shi yace su umma su koma Gida hardasu Daddy Shi zai kwana da Abba,Dole suka koma Gida suka barsa nan ya kwana ai kuwa sun kusan Raba Dare suna Hira da Abba da Safe da su Umma suka Dawo suka iske Abba garas dashi Farinciki ya kamasu sosai sai da sukazo kana Mastur ya tafi shima ba Gida ba Hotel yaje ya kama yayi wanka ya Sauya kaya ya Huta yaci abinci sai yamma ya Dawo Ranar ma anan ya kara kwana Washegari kuma aka Sallami Abba ya Dawo gida akuma Ranar Daddy da Baba Habibu suka Dawo Zaria,sun tafi ba Dadewa sai ga Mansur da Diza sun iso suma Sukace su Hajja na gaishe da mai Jiki,sun zo ba Dadewa sai ga Alhaji Yusuf da Matarsa Hajiya Laure Iyayan Mus"ab,Duka har su Diza duk nan suka kwana Mastur dai da Mansur Hotel sukaje suka kwana Harda Excort dinsa ma da Safe suka Dawo su Mansur suka Dauki Hanyar komawa Su suka wuce da Mommy ganin kanwar Umma Anty Saratu ta iso,Daman itama Mommy agidansu ta kwana Diza ce ta kwana nan Gidan su Rumana Taso taje gidan kakaninta Mansur ya Hanata Dakin Rumana ta kwana Rumana kuma ta kwana Dakin Ummanta,Duk da Diza tazo Gidansu har yau har gobe Zamansu bai sauya Zani ba,Rumana kuma da Mastur basy samu kebewa ba sai da Mastur ya kwana Biyar agarin Sokoto kana yayi Shirin Biyowa ta Zaria kana ya Koma wajen aikinsa Rumana taso tayi Sati kafin ta koma Ammh Abba yace Maza ta Shirya Tabi Mijinta Dole ta Shirya suka Taho Tare Jirgi suka Shiga zuwa kaduna Taso da ita kadai ne ta Biya Gidansu Basma ammh kuma ba Dama kiran waya yayi Daganan Headquater su na kaduna aka basu Mota da Sargent ya karisa dasu Zaria gida suka wuce Direct sai da yayi wanka ya Huta Da Daddare ya Dauki Mota Yaje Chan Hanwan sai Chan Dare ya Dawo.
Rumana kuma tana gida Tana Barcin gajiya Allah yasa ta saka Aisha Bala tayi mata aikinta akwanakin da bata gida ammh Monday zata koma aikinta Insha Allahu.

Zuwan Mastur yasa Mansur ya Hada musu wani Dan get Together,Ranar Lahadi da Daddare sukaje Reataurant sukaci abinci sukayi Raha yawancin Hiran Mansur ne sai Mastur dake Binsa da Eh ko A'a Rumana ma tana Tsoma bakinta Diza kam na gefe ta kara kiba ta zama wata so Classis so ba kowa take kulawa ba,Alokacin tagama Sadaukar da Duka Soyayyarta ga Mijimta Mansur ba Domin komai ba Saboda Shima ya Sadaukarmata da komai nashi Ta Fara sonshi da kaunarsa Sai dai bazata iya Daina son Mastur ba Shiyasa Duk Lokacin da suka Hadu sai taji Mikin Baya ya taso mata,shiyass Har yau har Gobe Bata kaunar Rumana kuma Har Mutane sun Fara Fahimtar haka Har Mansur din ya Fahimci ba wata Alaqa mai karfi a tsakaninsu yayi mata mgana ta Fitttike Dole ya Kyaleta Mastur kuma ba mazauni bane bai Damu Da yasan meke Faruwa ba.
Duk da Shima yana Kokarin yayi yaki da Zuciyarsa kan Soyayar matar kaninsa sai dai ba yin kansa bane ya kasa Cire Diza acikin Rayuwarsa gabadaya ya Tusa Rumana Shiyasa bayason Zuwa Zaria saboda gujema abubuwa guda Biyu na Farko Haduwa da Diza wacce ke Famo mai wani gyambon Dayake kokarin Yaki Dashi na Biyu ganin Rumana da Haduwata da ita kamar Zunubi ne,baya mata adalci baya kyautamata yana so yayi kokarin Cusata acikin Ransa ammy ya kasa.
Shiyasa wannan Fitan Mansur ne kadai da Rumana sukaji Dadinta ammh Mastur da Diza kam sam basu ji Dadi ba an fama ma kowa Sirrin Zuciyarsa sai da suka Biya suka siya Kayan kwalama kana suka Dawo Gida amotar Mastur Sabuwa sukayi Fitan wacce Abba ya Siya musu.

Washegari kuma ta kama Monday ne Tun Safe Mastur ya Tafi Anzo an Daukesa zuwa kaduna,ta chan zai hau Jirgin zuwa Porthercourt itama Rumana Ranar ta koma asibiti,Dayake ta sanar Babanta ba Lafiya Shiyasa tana Zuwa ana ta yi mata ya mai Jiki Dayake yanzu ta Daina Call,sai na Safe zuwa yammah Suna nan suna Mutumci da Dr.Yahaya sun zama kamar Yaya da kanwa,har zuwa wannan Lokacin ba wata kyakyawan alaqa tsakanin Mastur da Rumana sai dai abu Daya daya Sauya Dawowar nan har ya koma abincinta yake ci Safe da yammah Har tama Tambayesa me yake Bukata ya Fadamata kuma ya Rage zaman Daki zasu zauna afalo suyi kallo koda ba wanda zai tankama wani ahakan ma Rumana tana kallon abun awani Cigaba da aka samu.











*Shakira...*
1/1/22, 18:55 - Maryam Badmsi: *SS....28*

*Ki biya ki karanta Cikin Salama 09069067488 Mace mai aji mallakan komai nata take yi bata jiran abun sata*

"DIZA kudi sun shigo kuma sun zauna mata bama domin tana matar mai girma Chairman ba Daman chan ta Tara abun Duniya Sai tayi amfani da yadda Tayi suna sosai ana ta Rubibinta Sai ta Kara Fadada wajen aikinta aka Fitar da Bangaran Saloon ta Zuba kwararrun ma"ikata Aka Fara aiki ba kama Hannun yaro yanzu bata Cika zuwa ba bai wuce a sati ta Je sauBiyu ba Ta kara Zuba Ma"aikata sosai wadanda ke kula mata da komai Ammh Tana nan tare da Yan Amanata Meery da Hauwa Sun kasance Tamkar sune Idanuwanta kan Duk Abubuwan Dake Faruwa Merry ta kasance Idanuwanta da Komai yana kan bangaran Catering ne na Snaks ita kuma Hauwa Bangaran Makeup da Saloon din Gabadaya Domin Hauwa itace Ta rika ma Mtsama Diza har sai ta Ta Bude Saloon a wajen Mai suna DIZA BEUTY SALOON..!
Alhamdulillah kuma kwalliya ta Biya kudin Sabulu,Mutane Daga ko"ina suna zuwa wajen Domin aikinsu na kwararru ne kuma Diza Bata Daukan Ma"aikatanta haka kurum sai kana da Shaidar kwarewa kan aikin da Zata baka bayan haka kuma sai ta Jarabaka ta gani kafin ta baka aiki A ma"aikatanta.

Yanzu kokarinta Daya ne so take Ta Bude Class na Masu koyon Snaks na Online da kuma Na Gani da ido,Ta fara ma Mansur mganar basu gama ba Tafiya ta kamashi zuwa Abuja,Shiyasaa basu karisa mganar ba kuma Bayan ya Dawo wata Sabgar tasha gabansa basu kara mgana ba,Ssi dai ta Fara Gudanar da Class dinta ta Online kuma Maaha Allah abubuwa suna Tafiya yadda suka kamata Dayake tayi suna kowa ya santa so ana Rubibin Shiga Duk Abunda Diza ta Bude balle kowa yasan Diza Macece Data san aikinta ta kuma san me Tayi.


*******

Zaman Doya da Manjan Dake gudana Tsakanin Rumana da Diza har yau bata sauya zani ba sai ma abunda yayi gaba kamar ma Zaman nasu ya kara Tabarbarewa ma yayi Domin sai suyi Sati basu hadu da juna ba Diza ko Bataje ko"ina ba Tana Shashenta bata Fitowa wanda ke Nemanta anan zai sameta Rumana kuwa Tana zuwa asibiti aikinta ya Dauke mata Hankali Sosai Balle ma ta Riga tayi ma kanta alkawarin Fita Sha"anin Dizan gabadaya Shiyasa bata Taba mauda kai da ita ba.
Wani Lokacin itace ma mai zuciyar Imani in ta Fito da Safe Akaci Sa"a Ranar Diza zata Fita sukaci karo da juna Rumana na mata sallama ammh kamar Diza bata Taba sanin Rumana ba sai ta ga Dama zata amsa Rumana bata Damuwa ta Riga ta gama ijiye Diza a wani Shashi na Jahilai wadanda basu san Inda ke musu Ciwo ba.
Rumana Tana da Tarin Zurfin Ciki ba Taba Fadama Umma ko Abba yanayin Zamanta da Mastur ko Diza ba koda yaushe alheri take Fada akansu Ballatana su Hajja da basu Taba Takowa Gidan ba gwara ma Aiya Mansur ya Daukota tazo sau Daya Mommy ce da Mansur suka Ankare da irin Zaman Rumanan da Diza Mansur bai da tacewa wajen Diza Domin ko ya mata mgana bata Cemai kanzil Rumana  ma haka sai tace bakomai Hakuri kawai yake bata kawai Haka ma Mommy Hargidan Tazo a karo na Farko ta Kira Diza Har Shashen Rumana ta Hadasu tayi musu Fada sosai Duk yadda taso Rumana tayi mgana Batayi ba sai ma Nuna ma Mommy Datayi itace bata Fahinci wani abu ba Bawata mtsala Tsakaninta Diza ita kuwa Diza Har aka gama Mganar bata Tanka ba Abunda ke kara mata Haushin Rumana Munafuncinta komai akace sai dai Tayi Mirmishi tace bakomai da wannan Take Siyan Zuciyan Mutane Mommy ta ja ma Diza kunne ta kan ta gyara Halinta ammh sai ta Nuna ba wani abu Tayi ba kawai bata kaunar Doguwar Mu"amala Tana Hadata da Rumanan ne.
Mastur dai Yana Chan Porthercourt bai san Wani Hali suke Ciki ba Mansur ya kirashi ya Faramai mganar bai bi takai ba Kuma Bai kara Neman Mansur din da mganar ba Shima bai Kara Tadamai mganar ba Rumana ce ya Janye Jiki da ita Tun lokacin da mganar auransu ta Bayyana Ki ayanzu in ya Kirata Daga gaisuwa sai Tambayan Lafiyan Juna Shikenan ba wata Shakuwa Ballatana Fahintar juna atsakaninsu Tun Rumana na Damuwa Har tazo Abun ya Zame mata Jiki Ta Daina Damunta sai dai ta Dauki Darasi Guda Daya na zamanta da Mastur kada ta Cika Zakewa kada watarana yayi mata Abunda bazata Taba mantawa ba Shiyaasa taja Jikinta Dashi in bashi zai kirata ba Bazata kirashi ba In kuma ta Kirashi Tabbas Bukatar Fitace ta wani Uzuri ya Taso mata Gidan Hajja ko Gidan Mommy ma yace bata da Shamaki Duk Sanda Taga Dama taje kawai Shiyasa in daiBata da Zuwa asibiti chan take Tafiya da Wuni wajen su Hajja ko kuma in Taje asibiti ta Dawo sai ta Biyo a wannan wattanin Shakuwa ce mai Karfi ta Shiga Tsakaninsu da Rumana da ta zama yar gida Tamkar Diza kowa Yabonta yake yi Wannan Abu ma ya kara Jawo mata Tsananin Kiyayya Tsakanninta da Diza Uwa Uba ga Mardiya da suka Saba da Rumana Sosai Har yanzu ba"a sakata makaranta sai ta gama Iya wasu abubuwan Tunda Mastur yace SSCE yake so Tayi Shiyasa lesson Teacher din zai koyae da ita na wata Goma ne kafin a sakata a makaranta.
Dalilin Sabon da sukayi yasa Mardiya ke kaunar Rumana Saboda Bata da mtasla Gashi Tana Koyamata abubuwan Rayuwa Sosai Ta bangaran Girki ma ba Dama Shiyasa takan je Ranar weekend su Wuni Tare Tana Koyon wasu abubuwan gashi Rumana bata da kyashi komai Tagani da kudinta Zata saka Ta Siya ma Mardiya Sabanin Diza da Bata da wannan Hausan sam itace sai Bakin Kishi Bata da Dubaran kanta Zuwan da Mardiya take ashe konama Diza rai yake yi Tana Dannewa Tunda Wani Lokacin sai Mardiya ta Fara Sauka Shashen Rumana take Shiga wajen Diza su gaisa,Lura da haka sai ta Fara Dauke ma Mardiya in ta Shigo sai ta Hade Fuska ta bata rai tun Mardiya bata gane ba Har ta Fara Fahimta ta Kawo ma Rumana Complain ita da ta Fahimta sai tace mata ta Dinga Sauka wajen Diza kafin ta Kariso wajenta Mardiya batayi gaddama ba ta Dawo tana Fara isa Shashen Diza sai ta ga Chanji Sai kuma Dizan ta Bullo da wani Taku Bata bari Mardiya din taje Shashen Rumanan Tayi ta janta da Hira ko Ta sakata wani aikin da Har sai Lokaci ya Tafi Mardita bata leka wajen Rumana ba Har Tatafi,Mardiya ita bata Fahimci komai ba in Rumana ta kirata sai ta bata Hakuri Tana gayamata Diza ce ta Sakata aiki Har Lokaci ya Tafi Bayan Ta gama kuma ta saka Direba yakai ta gida Tunda yanzu Diza Mansur har Direban Dake Tukata ya Daukan mata arziki yaci Uban nada.
Rumana Tagama Fahimtar Diza Tsab Abun ya bata mata rai ammh Bata Nuna ba ta Bari sai Ranar da Dizan Ta Fito Sak a Mutum Sai tayi mganinta Ranar Zata Fahimci Shuru ba Tsoro bane gudun mgana ne.
Kamar Mardita ta sani sai ta Dauke kafa da gidan Sai dai In Rumanan taje Gidan Hajja sukan Hadu kuma bata Taba Tambayanta me yaasa ta Dauke musu kafa Ashe Mgana Diza ta gayamata kan Rumana Ranar suke nemi Fada ma Diza tace Mardiyaa ta kusa Zaginta kan Rumana Mansur ya Shiga mganar.
Diza ce tace ma Mardiya ta Daina Zuwa Shashen Rumana me suka Hada..? Ai itace Dolenta itace Matar yayanta Ba Rumana ba Mardiya tasha mamaki Dataji kalaman Diza Shine ta Bude Baki tace mata ai da Mansur da Mastur Duk Dayane sai Diza ta Fara Fada tana Bambamin fada Mardiya zata mata Rashin kunya da Mansur yazo Mardiya sai ta Boye gaskiyan mgana Tanajin kunyan Mansur yaji Haka Daga bakin Diza Shiyasa Har yayi ma Mardiyan Fada bai ji asalin Abunda ya Faru ba ita kuna ta Boye hakan ne gudun samun wani mtsala Sai ta Yanke Shawaran Dauke kafa Daga gidan Batare data Ko Hajja Tayi ma Zencen ballatana Rumana.


*******

Anyi haka da Sati Daya Diza ta tashi da zazzabi Har sai da Sukaje asibiti Shi da Mansur Rumana bata gida Tun Safe tatafi asibiti,Dalilin haka yasa Bayan sun Dawo Daga asibiti ya kira Hajja ya gayamata Diza Bata da Lafiya sunje asibiti an yi mata Text Zuwa gobe zasu je su karbo Tana Fama da Zazzabi mai Zafi da Ciwon kai tazo ta Taimaka mata Rumana bata nan,Hajja batayi kasa a gwiwa ba ta Ce ma Mardiya ta Shirya ta bata kudin Mashin tace taje Gidan su Diza Yayanta na Nenanta Jin haka yasa ta Shirya Tatafi ta iske Diza na kwance ba Lafiya Bayani yayi mata yace ta Zauna ta kula da ita kuma ta gyara Gidan Tayi Girki Shi zai Fita Fatan dawowa Lafiya Tayi mai ya Fita.
Maryama ita tayi komai Har girki Ita tayi Domin ta kware Rumana ta Koyamata komai,Diza Tashi kawai Tayi Taga Mardiya Tagama Komai taji Sauki Wanka Tayi tazo taci Abinci ta Dauki wayarta Tana kiran Missedcalls.
Rumana bata Dawo ba sai da yammah kuma Gidan ta Biya ta gaida su Hajja nan nema Ayya ke Fadamata Mardiya na Gidansu Wajen Diza ba Lafiya Tana jin haka bata Tsaya ba Tayi musu Sallama ta Wuce gida Ko Mommy bata biya ta gaidata ba Tana zuwa Gidan ko Shashenta Bata Shiga ba ta Shiga Shashen Diza ta Iskesu Dukkansu ita da Mardiya afalo suna kallo Mardiya na ganin Rumana Ta tareta da Fara"a Tana ta Rawan Jiki akanta Diza na zaune kamar ta Fashe Rumanan na mata ya ajiki Dakyar ta amsa,Saboda Rumanan ta Tura mata Haushi ta Dinga Jan Mardiyan da Hira wacce har abinci ta Zubo mata da lemo Jin ita ta Dafa yasa Rumana taci aikuwa Diza kamar ta Mutu tatashi Fuu kamar Zata tashi Sama ta Shiga ciki ba Dadewa ta Kwalama Mardiya kira Tana zuwa tace wai Ta mata Fentin Dankali Shi take Sha"awa Saboda bata son ganinsu Tare Mardiya na Fitowa ta Fadama Rumana Abunda Diza tace batayi mamaki ba sai ma Tayi Dariya Ta Mike ta mata sallama ta Fice Zuwa Shashenta Duk da Mardiya din ta mata akawarin Zuwa Wajen bayan ta gama Girkin bata zo ba Har washegari sai bata Damu ba Ranar Ta kama Lahadi bata da zuwa asibiti Barcinta taci sai chan bayan azahar tatashi Tayi gyaran Gida Ta Hada Tea ta sha ta zo Falo ta zauma Tana kallo,Sai La"asar ta Shiga Kitchen ta Dora Girki Dambu Take Sha"awa Daman Tazo da Bushashiyar Zogalenta da Aisha Bala ta zo mata dashi Daga gidansu Kuma Tana da Barjen Shinkafa wacce ta Kai gidan Hajja aka Kai mata Barje Shine yau tayi Dambu Dashi Domin shi take Sha"awa.
Bayan Ta gama komai Tayi wanka Tayi sallar mangariba ta Shiga wajen Diza ta Dubata da Jiki Sai Ta iske tana Salla Nan suka zauna suna Hira da Mardiya ta gayamata Tayi Dambu tace Za taci bata Tafi ba sai da Diza ta idar da Sallah har Cikin Bedroom dinta ta Bita ta gaisheta ta amsa tana wani cin ngani ita dai Rumana bata Tsaya bi ta kanta ba ta Fice ta barta.
Ashe tunda Diza taji Mardiya tace zata shiga wajen Rumana ta kasa ta Tsare ta Shiga sakata aiki Ta Hanata sakat Rumana kuma Tagaji da jiranta taji Shuru sai ta yanke Shawaran kiran Mardiya din Taji Lafiya Tajita Shuru.
Lokacin da Wayar Rumana ya Shigo Wayar Mardiya suna zaune afalo ita da Diza Tana shan Faten Dankalin Datayi mata Taji kiran wayar Kallo Ta sakarma Mardiya din Cikin alamun Zargi Dayasa ta kasa Daga wayar cokalin Hannunta ta ijiye Kafin Tace"Rumana ce ke kiran ki ko..?

Kai Mardiya ta Daga mata Lokaci Daya Tana Daga kiran Kafin Takai ga Karata a kunnenta Diza ta saki wani Dogon Tsaki Ta Fara Fadin"Wai ni binbin nin na miye Matar nan ke miki ne Mardiya..? Tafada Cikin gatsala da wani Rainin wayau wanda ya Dakatar da mardiya daga mgana da Rumana awaya sam ta manta ta Dauki wayar ta Bude baki Tana Fadin"Kamar ya Anty Diza..? Anty Ruma ce ke kirana Kuma Dambu tacemin Tayi nace mata Zan zo naci Hakan laifi ne..?

Dawani kallon ke baki isa ba Diza Ta Narkama Mardiya Haushinta ya kara kamata Kamar Rumanan ne ke gabanta tace"Aikin banza..Munafunci dai in Dambun kike Sha"awa bani da kayan yinsa ne ko kuwa Tsabar ita akomai sai ta Nuna Tafi kowa..? Daman ta saba nuna min Iko kan Komai nawa ina kyaleta Yanzu ai sai ta Kyale min ke ko banza Nice Dolenki Matar Yayanki Shakiki nake ita fa..? Matar Mastur ce ita ba Matar Mansur Sulaimam Doguwa bace.."
Ta KarisheFada kanta Tsaye ko ajikinta Mardiya ta saki baki Tana kallon Diza Cikin Firgici tace"Innalillahi yanzu sai kika sake maimaita wannan mganar..?
Tafada tana waige waige ko Mansur ya shigo sai idonta ya Fada kan wayarta daidai Lokacin Da Rumana tagama jin komai ta Datse kiran da Sauri Mardiya ta Dauki wayan ta Duba Kiran Minti 1har da wani abu Mikewa Tayi ta Dora Hannu akai Tana Fadin"Na shiga uku ni Mardiya Diyar Sule..!
Diza ta Datacigaba da Shan Fenten ta ta Dago Tana kallonta Bata samu Zarafin mgana ba Kamar Yaki sukaci Buga Kofar Shashen Falon Diza Sai mardiya ta Zabura Tana Fadin"Shikenan ta Faru ta kare..Gata nan ta zo.."Diza ta kalleta da mamaki kafin tace"Ke wai lafiyan ki kuwa..?ita waye tazo kuma?
Mardiya da Idamuwanta suka kawo kwallah tace"Anty Ruma ce..Itace wlh.Duk taji mganar da kikayi ashe na Dauki kiran ban sani ba ita kuma Bata kashe ba.."Gaban Diza ya fadi ammh sai ta Dake ta Mike tsye Tana kare Hade ranta kafin tace"Bude mata Kofa..Daduk Abunda Tazo. Dashi.Diza Diyar Sunusi Tureta na Daidai da ita.."Tafada tana Kara Tamke Fuska Tana kara Bude Hamci duk mardiya ta Rude Bata kaunar Wata Fitina tatashi ace sanadinta ne Ta karisa Jikin Kofan Tana addu"an Allah sa ba Ruman bace sai dai Bata karbu ba Domin Tana Budewa taci karo da Rumana wacce Fuskarta ba Annuri ko kadan kana Hango Tsabar Bacin rai da Fushi atare da ita Ko Gyale bata Yafo ba Daga ita sai Wata Doguwar riga da mayafinta Mardiya Tayi kasake Tana kallonta Kafin ta Bude baki Tace"Tsaya kiji Anty Ru."Bata karisa ba Rumana ta Tureta ta Shige Ciki,Tana Fadin"Ina Dizar Take..? Nazo ne ta kalli Idanuwana ta kara Maimaita min Mardiya Kanwar Mansur ce kadai ban da Mastur in gani in kina da kunya.."Ta Karishe Fada Cikin Fushi da Daga Murya Mardiya taja Salati bata karisa ba Ta karisa ga Diza Zata tare ta wacce ta Tsaya gaban Rumana kyam suna aika ma da juna kallon kallon Mardiya Zata yi mgana Rumana ta Daga mata Hannu Tana Fadin"Koma gefe Mardiya..Ba Fada nazo nayi da ita ba so nake naji da kunnena ta maimaita abunda ta Fada Domin awaya sai naji kamar ban ji Daidai ba."
Wata yar iskar Dariya Diza tasaki Kafin tace"Kunnen ki na Ciwo ne..?ko ke kurma ce Dr Rumana...?Tobari na gayamiki da amon Muryata yaddazata kiji Dakyau cewa nayi da kike wani Shishshigewa Mardiya kamar yadda kike Shigema kowa kanwar Mijin kice..?Ko kun Hadawani abu ne..? Inace Mardiya Kamwar Mansur ce kuma Nice nan Matarsa ba ke ba.."Rumana ta Sanadare Tana kallon Ikon Allah bata Taba zaton Diza bata Hankali ba sai yau.
Mardiya ce ta Fashe da kuka Tana Fadin"Haba Diza..Meyasa kike tamaimaita mgana Daya ne..? Ina kika Tabaganin Bambamcin Tsakanin ya Mansur da Ya mastur..?waya baki ikon Nuna wannan Bambamcin..?

Wani Dogon Tsaki Diza Taja Tana Fadin"Dole nagayamata..Naga ta Fara wuce iyaKarta.."Rumana ta Katse ta Da Fadin"Mardiya kanwar Mansur ce banda Mastur ko..?Diza ta karkace kai tace "Me suka Hada..? Goggonsa ce Mahaifiyar mansur kuma ta Rasu..? Mardiya Tatsaon Inna Zainabace sai ki gayamin ta inda kuka Hada dasu Rahma Sarkin Zumunci Ke..."
DIZA..."Bata karisa ba taji Muryan Mansur Cikin kaushi ya kirata Da amo mai karfi Dukkansu sai da suka Rude suka juya suna kallonsa Ashe ya Dade Tsaye yana jinta Idamuwansa sun yi Jajir Tunda takeda Mansur bata Taba ganinsa Cikim wannan yanayin ba bai tsaya neman Mgama ba ya Taka Cikin Zafin Nama gabam Diza bai yi wata wata ba ya Cira Hannu ya Zabga mata Tafin Daya Rudata ya Ruda Rumana da Mardiya suka ja baya suna Rawan Jiki Diza kuwa Hannunta Dafe da kunci Tana Shatatan Hawaye Mansur ya nunata Cikin wani irin Fushi yace"Akul dinki...Kada ki kuskura ki kara Fadin wannan mganar Daga bakin ki..Mastur Shakikin Da yake ga BabaSule..Haka Zalika Tsayayyen yaya yake ga Mansur da Maryama da Mardiya da Sakina..Ina nace Tsayayye wanda ko Bayan Raina zai iya Rike ki Da kedasu gabadaya.."Daga haka bai kara cewa komai ya Taka ya Shige Ciki kamar zai tashi sama.
Diza kuwa kunya Nadama Da komai sun Rufeta ganin marin ma gabam Rumana uwa uba ga Mansur wanda bata Ta aganinsa haka ba Yasa takwashi kuka zuwa Dakinta Key din Motarta ta Dauko da Mayafi ta bar su Rumaman nan Tsaye afalonta ta Fice koda suka Fito Tuni ta tsshi Mota Tayi Ribas tayo Hon megadi ya Bude mata ta Fice Rumana suka Kalli juna ba wanda yayi mgana Rumana tawuce Shashenta Jikinta yayi sanyi ita kuma Mardiya ta koma Cikin Falon Diza Tana jin Kamar kafafunta Bazasu iya Daukamta ba.
Tana shiga Mamsur na Fitowa Tana neman kwaso Rantsuwa ya Dakatar da ita da Fadin'"Basai kim ce komai ba..Naji komai..Gwara Datafi Gida Ta Fada ma su Mommy abunda ta aikata da kanta Domin ni kaina ina jim kunyar Fada kamar diza ta Fara Shaye Shaye.."
Yafada Lokaci Daya yana Ficewa bayan yasauya kayan jikinsa tana ji Shima ya Fice Daga gidan ta koma ta zauma kan kujera Tana Fadin"Allah ya kyauta..."











*Shakira...*
1/1/22, 18:55 - Maryam Badmsi: *SS....29*

*Ki biya ki karanta cikin Salama 09069067488 Mace mai aji mallakan komai nata takeyi bata jiran abun sata*

"Diza Tana Fita Gida ta wuce Tana kuka sosai,Mommy Hankalinta ya tashi gsshi kuma Tayi Tambayan Duniyanan Diza taki mgana sai dai kuka Ranta ya baci ta fita Batunta,ta kama Harkan Gabanta.

Ita kuwa Diza sai daga Baya kunya da Nadamar abunda ta aikata ya shigeta Tasani bata kyauta ba Uwa uba sai yau taga ta kure Hakurin zama da ita da Mansur yake Tunda take Dashi Bata Taba ganin Fushinsa ba Komai Tayi mai baya maida kansa Iyakata dai kawai yayi mata Mirmishi,Sai gashi yau ta batamai rai har yakai ga Marinta Bata san me ya Shiga kanta ba Kishi ne mai Zafi take ji akan Rumana Wanda bata iya Controling kanta Sai alokacin Taji kunyar abunda ta aikata Meyasa Har yanzu take son Mastur bayan kuma Tana auran Kaninsa..? Dame Mansur ya Rageta..? Babu tunda sukayi aure Shi yake Wahala da Dawainiya da ita Ita me ta sakamai..? babu sai mugun Hali da Rashin Tsausasawa ya kamata ta Mafarka Daga mafarkinta da bazai Taba Tabbata ba aure ya Haramta Tsakaninta Mastur ya kamata ta Fahumci Gaskiya ta Rumgumi Mijinta,yanzu bata da karfin gwiwan Fadama Mommy wani abu Ta Tabbata itace bata da Gaskiya.

Kukan datayi Shi ya kara Dawo mata da Zazzabin Jikinta mai Zafi,Ta na kwance Kan gadonta tana Rawan sanyi ahaka Mommy ta Shigo ta Tarar da ita sai Hankalinta ya tashi ta Kira Daddy ta gayamai Shi kuma yace Takai ta asibiti hankali a tashe Mommy ta tuka Diza zuwa asibitin da suke da Fayel Almadina Suna zuwa aka Karbeta saboda ta galabaita suna Hanya Tana ta Kwarara amai,Taimakon gaggawa aka bata Bayan an Dibi Jininta Domin gwaje gwaje sai aka Saka mata Drip,aka kawota Daki na Musamman Likita yayi ma Mommy Bayanin sai zuwa Gobe zasu koma gida Har sai an gama gwaje gwaje kana Lokacin ita Dizan ta Dawo Cikin Hayyacinta jin Haka yasa Mommy ta kira Mansur ta gayamai Halin da ake Ciki Lokacin yana Gida ne afalon Hajja Shi yake Fada musu ma Diza na asibiti.

Adaran ya Dauko Ayya da Hajja suka je suka Dubata Tana Barci Daga Gidan kuma Mama Fadime Tayi abinci Direba ya Daukota ya kawota suna asibitin Sai ga Daddy da Baba Habibu sun zo Har suka Tafi Diza bata Farka ba Tana ta Barci Mommy aka bari ta kwana da Diza,Su Rumana kuwa sai da safe Taji labari Domin sai Chan Dare Mansur ya Dawo Gidan Mardiya ta kwanta koda ya Dawo Rumana ma na Shashenta sai da safe bayan ya Shirya zai tafi asibitin yake gayama Mata ita ta Shiga Shashen Rumana ta gayamata ta Isketa ta Shirya Zata tafi Asibiti,Hankalinta ya tashi Mansur ya Rigasu yin gaba Rumana ita ta Dauki Mardiya suka Tafi asibitin Bayan ta kira Mommy ta gayamata asibitin da suke da Lambar Dakin.

Sanda sukaje Diza ta Farka Tun Cikin Dare kuma Alhamdulillah Jikin nata da Sauki sai duk tayi wani iri Tun Safe da Likita ya kawo Takardan gwajinta ya Tabbata Tana da Shigar Ciki na Tsawon Wata uku To meya Rage mata..? Ta riga ta zama na Mansur har Abada ya kamata ta Dawo Cikin Hayyacinta Lokacin da Mamsur yazo yaji Labari kamar zai suma saboda Dadi da Farincikin Tun alokacin Taji komai ya kwace mata Taji Duk wani Nauyin Zuciya ya saketa Tsananin Son Cikinta ya kamata Lokaci Daya da Burin Haihuwa da Mansur ko Allah zai bata D"a irin Mansur mai Hakuri da Dadin Zama,so take ta samu kebewa da Mijinta ta bashi Hakuri kuma Tamai alkawarin Zata bama Rumana Hakuri insha Allahu komai ya wuce.

Rumana Tayi mamakin yadda ta gaishe da Diza ta amsa Cikin Sakin Fuska kamar ba ita ba,Saboda ganin wannan Chanjin yass tace Mommy tabi Mama Fadime data kawo Abun karyawa ta koma Gida ita da Mardiya zasu zauna da Dizan har ta Dawo Shine ma Har Diza Ke fadin ba Asibiti zata tafi ba.? Rumana tace ta kira Aisha Bala Zataje tayi mata aikin ta na yau gobe itasai ta Rama mata,Sai Diza Tayi Shuru bata kara mgana ba Mommy tabi Mama Fadime ta koma Gida Mansur ya Tafi suna da Taro anan Sabongarin Zaria Shiyasa ya Tafi.
Rumana ita ta taimaka ma Diza tayi wanka atiolet din Dake Dakin ta Sauya kaya wanda Mansur ya Taho mata dashi ta Hada mata Tea tasha sosai da Buredi,Ta koma ta kwanta Har tana ma Rumana Godiya,Ita kuma sai dai Tayi Mirmishi batace komai ba,Dayake Mommy ta gayamusu Zencen Cikin Dizan Farinciki ya Cika Zukatansu,Ita ta kira Umma Daga chan Sokoto Ta Fadamata ita kuma ta kira Mommy Ta mata yamai Jiki da kuma Murnan karuwa da Diza ta samu suka Rabu Cikin Farinciki.
Su Rumana suna asibitin Har yammah kana Likita ya basu Sallama Lokacin Mommy na nan da Hajja,su suka Tarkato Diza da kayayyaki suka Taho gida Direct gidanta suka wuce da ita,Domin da Farko Mommy taso ta Wuce da ita gida Har ta kara jin Sauki ammh Diza taki tace a kaita Gidan ita taji Sauki Likita ma ya bata mgungunan karin Jini ne kawai sai Shawarwarin yadda Zata kula da Lafiyarta.
Mansur sai dai Mommy tamai waya suna gida Shiyasa daya tashi bai Je asibitin ba ya Dawo gida nan ya iske su Hajja da Mommy da balaraban kawu Usman sai Rumana da Mardiya Tunda suka Dawo Rumana bata Zauna ba ita da Mardiya su sukayi Girki,Diza tace Fate zata sha,Rumana Tayi mata shi Mai Hanta kuma taci sosai yaji Alaiyahu,ganin su yasa su Mommy suka koma gida suka bar Rumana ita da Mardiya itama bata koma Shashenta ba Har sai da Mansur ya Dawo Lokacin Diza ma tasha mgungunanta ta samu Barci Wajen 10pm na Dare Mardiya ta Rakata Shashenta.

Washegari kuma Diza da kanta tace mata Tatafi wajen aikinta Taji Sauki kuma ga Mardiya ba Mtsala Shiyasa Rumana tatafi Bayan Tafiyanta ne sai ga Yan maruka Ashe mardiya ta kirasu ta gayamusu Inna Zainaba da Mariya suka zo Duba Dizan,Kuma Mansur yaji Dadi sosai Domin ance Naka daman naka ne kwana Daya sukayi suka koma Tunda Jikin Diza yayi Sauki sai dan Abunda ba"a rasa ba na Laulayin masu Ciki.
Yan ma"aikatan Diza sun zo Duba Merry da Hauwa sune gaba gaba,Bata da mtsala Dasu su san aikinsu Ragamar komau yana Hannunsu koda bata da Lafiyan nan bata da Damuwa Tunda Kamar tana Wajen indai Merry da Hauwa suna tare da ita.

Mansur da kansa ya Kira Mastur ya gayamai Diza nada Ciki ya Tayasa Murna sosai har yana mai Tsiyan Allah yasa ya Girma yanzu Bayan sun gama Wayar Mastur Kamar zai yi kuka yana Jin Takaichi da Rugugun wani Daci acikin Zuciyarsa Na yadda ya kasa Cire Soyayyar Diza acikin Zuciyarsa Gashi har tana Dauke da Cikin kaninsa Shi kuwa wannan wani irin So ne..? Allah ya waddan wannan Soyayyar batamai amfani ba sam,Ranar bai iya barci ba kwana yayi yana Sallah Tare da addu'an Allah ya Cire mai Soyayyar Diza acikin Zuciyarsa Allah sakamai Soyayyar Rumana ko zai samu ya Sauke Nauyin Dake kansa nashi ya sani In ya Mutu a wannan Halin Allah sai ya Tambayeshi Hakkokin Rumana Daya Danne mata yana Rokon Allah ya bashi Iko da karfin Zuciyar da zai iya Sauke Nauyin Rumana Daya Rataya a Wuyansa.

*****
Bayan Sati Daya Da Kwantar da Diza a asibiti Alhamdulillah Ta samu Sauki Sosai sai dai Amai ne bai Saketa ba,Mardiya ta koma Gida wajen Hajja,Sai dai in Tana Bukatar wani abu ta kira Mommy ita kuma ta saka Direba Ya kawo mata,Rumana ma Tana iya Bakin Kokarinta akan Dizan Ballatana ganin yanzu ta saki Tunda Har yar Hira sunayi Tana Tambayanta wajen aikinta kuma In ta Dafa wani abun kwadayi na masu Ciki Tana kawo ma Dizan Ta karba Taci Tana Godiya Har acikin Ran Rumana taji Dadi sosai,Kuma abunda ya Faru dukkansu basu Furtama kowa ba Hatta shi Mansur din.

Yau din ta kama Lahadi ne Rumana na gida bata je asibiti ba tatashi da Kwadayin Cin Alalen Leda shi Tayi wanda ta Sakamai Kwai da Hanta,da alaiyahu da kanta ma Ta fita tayi Cefenan ta Dawo Shine ta shiga Wajen Diza ta isketw kwance kasala Duk ya Rufeta batayi komai ba Rumana bata koma Shashenta ba sai da ta gyara Ma Diza Dakunanta ta Hada mata Ruwan wanka Ta tasheta tace taje tayi,ta gyara gadon da Bedroom din gabadaya Bata tafi ba Har sai da Diza ta Fito Daga wanka ita kunyar Rumanan take ji kuma ta kara yardan ma kanta ba wai iyayinta bane ke saka ana Yabonta ba ta yardan ma kanta Rumana Tana da kyawun Hali.
Da zata tafi ne take gayamata Alele zatayi sai Diza tace Zataci Don Allah ta kawo mata Shine Dalilin Dayasa bayan Tagama Tayi wanka ta Dauki Kulan Alalen da Yajinta na Tafarnuwa wanda Balaraban Kawu Usman ta Daka mata itama bataci Alalen ba Tace sai taje Shashen Diza su ci Gabadaya.

Diza taji Dadin zuwanta Daman Tana zaune ita kadai ne sai kallo take yi Mansur Tun Safe ya Fita Sai kuma Dare ita sai yanzu take jin Haushin ma Siyasar tashi,Mutim ba Hutu ko Mganar data ke so suyi basu samu Dama ba to in ya Dawo tayi barci Saboda magungunar akwai mai saka Barci da Safe kuma bama takai ga Tashi zai Fice Shiyasa bata samu Lokacin da zasuyi mgana ba ammh yau ta kudiri Niyar yin mgana da Rumana ta bata Hakuri.

Rumana ita ta shiga Kitchen din Diza ta Dauko musu Babban Filet ta Bare musu alalan Ta saka musu Yaji ta kalli Diza Dake kan kujera tace"Ko zaki sauko ne muci kamar kasan zai fi mana Dadin Zama.."Diza ta ijiye wayar dake Hannunta Tana Fadin"Wlh kuwa zai fi Dadin ci..Balle ga yaji kana ci kana jan Yajin ka.."Ta karishe Fada tana yar Dariya Lokaci Daya tana Saukowa kasa Rumana ta mike Tana Fadin"Kin Tuna min bari na Dauko mana Ruwa.."Diza tace"Kai..Hanzarta
."Frigde din dake Falon Rumana ta Bude ta Dauko musu Goran Ruwa guda Biyu masu sanyi tazo ta ijiye ta koma Kitchen ta Dauko kananan kofuna tazo ta ijiye kana ta Zauna sukayi Bismillah suka Fara cin abinci ba wanda yayi mgana.
Chan Diza Data Tauna Alalan a bakinta tace"Uhm..Kai gaskiya Alalen nan yayi Dadi ban taba cin Alalan Dayayi min Dadi irinsa ba.."
Rumana na Dariya tace"Allah ko..?Kodai na saka miki waigi ne..!
Diza na Dariya tace"Bafa santi ne..Ina dai Fatan akwai Ragowa Domin ni anjuma shi zan ci.."Rumana tace"Akwai Har mai girma Honourble ma zai samu.."Diza tace"Daya saka miki albarka..Yana son Alale Koyaushe yana Min gorin ban taba mai Alale ba.."
Rumana tace"Su gori manya..Ina Ruwan Mansur.."
Diza ta gama Shan ruwa tace"Wai ni kam nace Ya Mastur Laifin me nayi mai..? Ko awaya bai kirani ba.."Rumana Tace"Kinsan baida Aikun kiran waya fa..Sai dai yayi mgana ma Mansur kema kin sani.."Diza tace"Daman mana..Rashin zaman Mansur ne kila da kinji Zencen sunyi waya yana gaisheni abakinsa.."Rumana tace"Eh kam haka din ne.."
Daganan basu kara mgana ba Har sai da suka gama cin Abincin Diza tayi Gyatsa da Hamdala Tana Fadin"Alhamdulillah..Naci na Koshi..Allah yasa kar nayi amai..'Tafada Cikin Bayyana Damuwa.

Rumana tace"Kada kidamu insha Allahu bazaki yi Amai ba.."Diza tace"Allah yasa hakan"Daganan Rumana ta Tattara abunda suka Bata zuwa Kitchen,ta Dawo Diza na zaune nan kasa Ta rasa ta ina Zata Fara ma Rumana mgana sai da Taga tana Shirin saka Mayafi kana takalleta Tana Fadin"Wai har zaki Tafi..?
Rumana tace"Wlh..karatu zan je nayi..Gobe Seminar gareni Shiyasa.."

Diza ta kada kai Tana Fadin"Da kuma mgana nake son nayi Dake in bazaki Damu ba.."Rumana ta Tsaya Bayan ta saka mayafinta Lokaci Daya ta koma ta Zauna Tana Fadin"Bakomai ina jinki.."Diza ta Dukar dakai ta rasa Ta ina zata Fara Dakyar tayi karfin Halin Fara fadin"Daman Hakuri zan baki Rumana kan abubuwan da sukayi ta Faruwa Tun Farkon zaman mu acikin Gidanan Don Allah ki yafemin Rashin Fahimtane Abunda ya Faru Ranar nan kiyi Hakuri komai ya wuce hakan bazai kara Faruwa ba..!
Diza ta karishe Fada tana wasa da Zoben Hannunta ita kuma Rumana sai Mirmishi Take yi Cikin Jin Dadi ta tashi ta karisa ga Diza ta Durkusa ta Dafa Kafadarta Tana Fadin'"Haba Diza..Miye na bani Hakuri ai bakomai zaman tare daman yagaji haka..Naji Dadi kwarai Insha Allahu komai ya wuce..Allah ya zaunar damu Lafiya..ke kuma Allah ya kara Miki Lafiya ya kuma Sauke mana ke Lafiya musha Shagali.."
Ta karishe Fada Tana Dariya Diza Taji kunya ta Sunne kai Tana amsawa da Ameen Ameen.
Daganan Rumana ta Koma Shashenta bayan ta barma Diza Sauran Alalan Data zo Dashi tace taci da Daddare sauran Kuma ta Rage ma Mansur Dizan Tayi ta Godiya..
Ita kuwa Rumana Tayi Farimcikin wannan Daidaitawar tasu ita da Diza ko bakomai Shi Zaman lafiya wani abu ne,mai matukar amfani bata da Damuwa game da Mastur Domin ta Tattarashi ta watsashi gefe Daya,ta Dauki auranta Dashi a mtsayin wata kaddara Ta rayuwarta wanda bazata iya Tsallake hakan ba.

Diza kuwa Kin yin barci Tayi saboda Tana son yau tayi mgana da Mansur yasa taki kwanciya Barci,Sai Allah ya taimaketa ya Dawo da wuri,Around 9pm koda ya Shigo yayi mamakin ganinta a Falo zaune kan kujera Tana kallo Lokaci Daya kuma wayace a Hannunta Tana Sarrafata duk don Saboda kada barci ya Dauketa.
Sanye take da wani Wando mai kama da plazo sai wata Shirt mai Ruwan Zuma Data lame ajikinta kanta ba Dankwali ta kama gashunta a tsakiyar kanta ssi Baza kamshin Turare take Zubawa kuma Duka adon yau tayi Shi Saboda Mansur ne Abunda bata Taba mai ba.

Da mamaki ya karisa gareta Lokaci Daya yana Sabule Babbar Rigar Shaddar dake jikinsa Tare suka isa ga Jikin juna itama Mikewa Tayi ta tarbeshi Fuskarta ya Tallafa da Hannaye Biyu yana mai kura mata ido kafin yace"My Firstlady..Meyasa Har yanzu baki kwanta ba kuma kinsan Yanayin da ki ke ciki ko  ?
Lumshe ido Tayi ta Bude kafin tace"Taya zan iya Barci Alhalin kana Fushi dani..?
Ido ya Zuramata kafin yace"Ni bana Fushi Dake Matata..!
Wani Sanyi Taji yana Ratsata Wanda bata san Lokacin data kwantar da kanta Saman kirjinsa  Tana Sauke Numfashi ba Abun ya bashi mamaki sai Jikinsa ya saki ya Tallabeta zuwa Jikinsa Yana Fadin"Kinyi sallah..? Kinci Abinci..,?
Kanta na saman Kirjinta tace"Nayi Sallah kuma..Naci na koshi..Rumana Tayi mana alale mai Dadi shi naci da Rana har daranan..."Cikin mamaki ya Dagota yana Fadin"Rumana kuma..? Kai ta gyada mai Tana Fadin"Eh..Kaima ta ijiye Maka naka.."Yana so ya Tambayeta sai kuma ya fasa ya Tallafeta Zuwa Cikin Bedroom dinsu kan gado ya Zaunar da ita yana Fadin"Nagaji..Bari naje nayi wanka...Duk da na Biya wajen Hajja naci Tuwo zan ci Alalan nan Tunda naga kina Santi nasan yayi Dadi sosai.."
Tana kallonsa batayi mgana ba har ya Ture kofar Tiolet ya Shige ya barta nan zaune kawai sai Taji Hawaye ya cikamata ido da Tsausayin Mansur ta Godema Allah Data gane gaskiya da Wuri kafin Lokaci ya kure mata data mutu Cikin wannan Halin batasn me zata gayama Allah ba.


Har Mansur ya Fito bata sani ba Sai da taji Dumin Ruwan Wankansa Saman Fuskarta yana Share mata Hawaye Tana Bude ido ta gansa Durkushe saman Gwiwoyinsa agabanta Yana Dafe da Cinyoyinta Cikin wani yanayi ganinta Tana Hawaye yace"Meya Faru ne Naga Hawaye a Fuskar Firstladyta..?yafada yana Bayyana Damuwarsa Kura mai Ido Tayi Cikin wani yanayi kafin taji kukanta ya karu kawai sai ta sakamai kuka nan da nan ya Rude ya mike ya Tarairayota Jikinsa yana Tambayanta ki me ya Faru..? Kasa mgana Tayi saboda bata san ta ina Zata Fara ba Kawai sai ta samu kanta da Fadin"Don Allah kayi hakuri ka yafemin..Duk Abunda ya Faru ba Laifi na bane..Wlh bansani ba.."Ta karishe fada Tana gunjin kuka kamar Zata Shide Dagota yayi Daga Jikinsa Cikin Rawan jiki yake share mata Hawaye yana Fadin"Wlh banta Rike ki da wani Laifi ba Diza..Na Dade da yafemiki Duka Laifin da kikamin da wanda ma zaki min nan gaba Diza..Ina sonki soyayyar da Bansan yaushe ta Fara ba..Kuma bansan Ranar da zata yanke ba kila sai Ranar da na Daina Numfashi Diza..'Ya karishe Fada cikin Sanyin murya da karaya Da Sauri Diza ta Dago tana kallonsa Cikin Zubar kwallah Kafin ta samu Zarafin mgana taji yace"Ko da bazaki Taba sona ba Diza..Ni na yarda nacigaba da sonka Har karshen Numfashina.."Da wani irin Gudu ta Fada Jikinsa ta kamkameshi Cikin kuka take Fadin"A"a..Nima Wlh INA SONKA...'!Ina sonka...! Tafada cikin gunjin kuka da Sauri ya Dagota yana Girgirzata cikin mamakin kalamanta yace"Da gaske kike Diza kin Daina son Ya Mastur ni kike so..? Ya tambayeta Cikin Wani irin Rauni da muradi mai girma.

Cikin Zubar kwallah idanuwanta na Runtse tace"Wata irin Matace ne da zan rika Begen wanda ya Haramta gareni..? Wata irin Bakar Zuciya gareni da zan juyama wanda ke sona da Duk Zuciyarsa baya..?Bani da wannan karfin gwiwan Mansur Wlh ina sonka..Ina kaunarka da Duka Zuciyata.."Cikin wani irin azama ya Dora Bakinsa kan bakinta nan nan da ta Bashi Dama ta Hanyar Budemai bakinta ta Cafki Harshensa suka Fara bama Junansu Sumba mai Tsawo Cikin Muradi da kauna Alokacin Diza ta Rude Madamai martani kawai Take ita ta karbi Ragamar abun Sai Mansur ya koma dan kallo Haka ta Rika Sarrafashi Har suka samu Natsuwa Mansur ya Gigice sosai Yana ma Diza kuka da  idanuwansa yana Fadin kada ta barshi in ta barshi Zai iya Mutuwa itace Rayuwarsa,Karo na Farko Tun Bayan Auransu da Diza Tataba Bashi Hadin kai 100%shiyasa abun yazo mai cikin wani yanayin da bai Taba Zato ba.
Tare sukayi wanka Suna yi suna kara Tabbatar da soyayyar junansu bayan sun yi wankar Tsarki suka Fito suka shirya Cikin Kayan barci kana Diza ta gabatarmai da Alalansa suka taru sukaci Cikin Soyayya da kaunar da suka Tsinci kansu acikinta.

Awannan Daran Dare ne Masu Daraja da Tsada wajen Diza da Mansur domin tafi Daran Farkonsu Dare ne msi Cike da muradi da soyayya wanda suka kwana yima juna alkwarurruka da Sadaukarwa mai Tarin yawa Har garin Allah ya waye Dokin junansu bai sake su ba Ranar Mansur  bai iya Fita ko kofar Gida ba Duka ya Kashe wayoyinsa yana Enjoying din Sabuwar Duniya da Diza ta Rika Tafiya Dashi Har Abada bazai Taba juyama wannan Sabon al"amarin Baya ba.







*Shakira...*
1/1/22, 18:55 - Maryam Badmsi: *SS...30*


*Kibiya ki karanta Cikin Salama 09069067488 Mace mai aji mallakan komai nata take yi bata jiran Abun sata*


*2 Month Later*


"Abubuwa Dadama sun Faru ayadda kowa yake so Domin a wannan Lokacin Zaman Diza da Rumana sai dai ace son Barka sun Hade kansu Tamkar wata Baraka bata taba Shiga Tsakaninsu ba Dama Diza ce Mtsalan kuma yanzu ta Zubar da makamanta.
Mansur yafi kowa jin Dadin haka sai Mommy da mardiya da yanzu Take jin Dadin zuwa gidan Fiye da Baya,in yau suka wuni Shashen Diza gobe Shashin Rumana zasu wuni indai Rumana na Gida girki kuma indai Tana nan ita take musu Gabadaya bata barin Diza Tayi wani aikin Wahala saboda Cikin Jikinta da yanzu yake Cikin Watansa na Biyar har ya Fito Dayake Diza Zatayi Girman Ciki.

Mastur yazo gida yayi Sati Biyu ya koma sai dai wannan zuwan Shima abubuwa sun Fara  Daidaita Sanadin zuwan nashi Baba Habibu ne ya samu Hatsari akan Hanyarsa ta Dawowa Gida Mota taTureshi yaji Raunika sosai sai dai Ba karaya asibitin Abu Tudun wada suka kaishi,Washegarin Ranar Bayan Mastur yaji Labari ya Hayo Jirgi ya Taho hankalinsa yayi matukar Tashi Dawowarsa ne yasa ya Sauya ma Baba Habibu asibiti Zuwa ABU chika Dake Samaru.

Wannan Dalilin Shi yasa ya Dade agida bai koma ba Har sai da Baba Habibu yayi sati Daya a asibitin aka sallameshi,suka Dawo Gida zuwa Lokacin Hatta yam Maruka sun so gaisheshi Baba Sule da yan"uwansa Umma da Abba ma Daga Sokoto sun Taho sun Dubashi Inna karime ma Tazo ita da Mijinta Mommy da Daddy kuma Koda yaushe suna asibiti Tare dashi Diza ma Haka Rumana kuma Daman anan take aiki Haka abokan aikinta keta zuwa gaishe shi Domin ta sanar dasu Baban Mijinta ne sai alokacin wasu suka ga Mijin Rumana Mastur,Shima Din alokacin ne yaje Har bangaran Datake aiki yagani Abunda yabama Rumana mamaki Batayi mamaki ba sai Taga in ya Dawo gida yayi wanka Da Safe saboda Achan yake kwana Tare da Baba Habibu,Mansur yayi nacin ya Dinga kwana ya Hanashi In Tana gida bata Fita ba sai yace ta Jirasa su koma tare in sun koma yammah Tayi zata koma gida sai ya Dauketa ya maidata watarana kuma Mansur ya maida su Gida ita da Diza haka sukayi tayi Har yaji Sauki ya koma gida Hajja da su kansu suna kara Kula dashi.

Abunda ya kara bama Mastur Tsoro da mamaki Abu Daya ne zuwa Biyu,alokacin da Baba Habibu ke asibiti Rumana bata zuwa Hannu Rabbana sai tayi abinci Tazo dashi haka bayan ya koma gida ma haka bata zuwa Hakanan abunda ya bashi Tsoro bai Taba ganin alert din ta Cire ko Naira Biyar Daga cikin kudinsa ba,To da wani kudi take amfani..? Yaji Tsoro ya Shigesa kada fa yazo ya mutu ya shiga Wuta saboda Hakkin Rumana Dake kansa sai ya yanke Shawaran yi mata mgana.

Aranar tare suka Dawo Daga Gidan su Hajja dukkansu,Ita taje wajen aiki sai da ta Dawo ta Biyo,ta iske ma su Inna Zainaba sunzo da Maryamu da Mariya Harda Sakina,Diza kuma Daman anan ta isketa,nan aka Hadu ana ta Hira anan ne ma take jin Maryama ta samu Miji Zatayi aure acikin garin Kano kowa ya Tayata Murna sosai,Har anyi mgana an sska Ranar auran nan da wata Biyu,ita kuma Mardiya Daman an Biya mata Jarabawan Da Jamb saboda Achan maruka tayi karatu har matakin Jss3,Shiyasa bayan tazo nan din Mastur yace sai dai Tayi Tsallake zuwa gaba saboda ta girma Shiyasa ya saka Mansur ya samar mata lesson Teacher Shiyasa abun yazo da sauki.

Achan suka kai Dare sai Wajajen 10pm kana suka koma Gida Dukkansu Diza Tana Motar Mijinta ita kuma Rumana Da Motarta taje asibiti sai ta barta nan Gidan Hajja Mastur ya Dauketa a nashi Zuwa Gida suna zuwa Kowa ya nufi Bangaransa Hakance ta Faru da Rumana Domin Dakinta ta Shige Shima Mastur ya Shiga Dakinsa sai da yayi wanka ya Sauya kaya zuwa na Barci Riga da wando masu Ruwan Toka,kai Tsaye Bayan ya Fito Daga Dakinsa ya Nufi Dakin Rumana jin bai ji Motsinta ba Bayajin yunwa Domin Dukkansu sunci Abincin da Hajja ta Dafa musu.

Tana Tsaka da Karatu Domin Tana da wata Seminar gobe din Sanye take da Riga Doguwa mai Budadiyar gaba wacce keda madaurin Gaba Bata saka Dankwali ba Sai dai ta Tufke gashinta,Fuskarta Sanye da Siririn gilashinta mai kara mata karfin gani System ne agabanta akan gado Tana karatu Taji Sallamarsa da Shigowarsa Dakin Da mamaki ta Dago Tana kallonsa kamar yadda Shima yake kallonta Ganin bata bsshi Izinin karisowa ba yasa ya Coge Daga Kofar dakin Hannunsa Saman Kirjinsa yace"Baki bani Izinin Shigowa ba Madam..?
Mamakin kalamansa Taji Da Sauri ta muskuta kunya Take ji Saboda Rigar jikinta Gaban Nonuwanta suna Bude ne shi bai ma lura da Kirjin nata ba Dayake ba Kodayaushe yake kula da irin wadanan Abubuwan ba Tunda ya Rasa Diza.
Da sauri tace"Ah Haba..Har sai na baka izinin zama kaima ai Dakin ka ne..!

Karisowa yayi har gefen gado kana ya zauna yana kallon System din gabanta kafin yace"Kina wani aiki ne..! ? Rumana tace"A"a karatu nake..Cikin wannsn satin zan gama Seminar ta.."Kai ya Rausaya kafin yace"Allah ya bada sa"a..!
Ta amsa da Ameen a kasan Ranta sun Kara Daukan tsawon Lokaci kafin ya kalleta yana Fadin"Duk iya Tsawon wannan Lokacin meyasa baki Taba taba ko Sisi Cikin Katin Bankin da na baki ba..?
Daga sama Taji Tambayar shiyaasa ta Dago Tana kallonsa acikin Ranta Tana Ayyana Daman yana Sane da bata taba Taba ko Biyar dinsa ba"Kinyi Shuru..?
Ya katse mata Tunani da Sauri ta Sauke Numfashi kafin tace"Ina da kudi a Hannuna ne..Abba yana Turomin kudi duk wata kuma akwai Kudin da gwannati Take Biyana duk wata na Intenship din da muke yi Shiyasa kaga ban Taba amfani da kudin Daka barmin ba..!
Yana kallonta Har ta gama Bayaninta sai yaji ssm bai kyauta ba Shiyasa ya kara Tausasa Murya yana Fadin"Duk na sani..Ai ba Abba ke da iko akan ki ba..ni ke da alhakin Baki komai na Rayuwar nan Rumana Duk da auranmu  ba yadda mukayi Tsammani bane ammh ai Aure sunansa aure kuma Hakkin kowannenmu yana Rataye ne a Wuyanmu Ko bakomai ki bani Damar sauke wannan Nauyin naki Don Allah.."Har yagama Jawabinsa kanta na kasa Bata Dago kanta mamakinsa ya Cikata Daman wai yasan da ita Matarsace ko kuwa yau kawai Dadin Bakin su Maza ne ya Motsa..?
Jin tayi Shuru yasa ya mike tsaye yana Goye da Hannayensa kan Kirjinsa yace"Kada ki kara amfani da wani kudi in ba Cikin Katin Bankin da na baki ba Kinji ko..? Bata da Zabi illah ta Dagamai kai Cikin Gamsuwa kai ya gyada kafin yace"Gud..Kuma Komai kike Bukata ki kirani ki Fadamin Plz.."Cikin mamakinsa tace"Insha Allahu.."Daga haka yayi mata sallama ya Fice Ta Bishi da kallon mamakinsa Bata iya Dora wannan al'amarin nashi a komai ba sai a Dadin bakin Namiji kawai.
Haka kuwa akayi Domin Kafin ya Tsfi sai da ya Dauketa suka Shiga kasuwa yayi Cefene kuma suka Shiga Shop ya siya mata abubuwan amfani sosai su pad ne,da kayan kwalama Duk dai yaji ya Sauke Nauyin Dake kansa Ba Laifi Rumana taji Dadi Sosai ko Bakomai Zakaji Dadi yau wanda bai Damu da Damuwarka ba ya Damu dakai koda Sau Daya ne.
Bai tafi ba sai da yaga Jikin Baba Habibu ya samu kana ya koma Bayan ya tura ma Baba Sule kudi kan Hidiman Bikin Maryama ita ma Maryama din ya bata kudi yace ta Siya abubuwan da Zata kara Koda Mansur yaje chan maruka ya iske komai ya kamallah daga Taimakon Dan"uwansa kuma Yayansa haka Baba Sule keta kwararamai addu"a Shi kanshi Mansur yana alfahari da samun Dan"uwa kamar Mastur Domin Dayane shi acikin Dubu abunda ya kara musu kadan ne Domin Yayan nashi ya gama yin komai.

Ba Laifi Mastur yayi kokarin gyara Zamantakewarsa da Rumana yana kiranta Bayan kwana Biyu zuwa uku yaji Lafiyanta da kuma Tambayanta in akwai wata Damuwa,Hakan ba karamin Farantama Rumana rai yayi Shiyasa itama takan Kirashi kafin ya kirata in taji Shuru,Saboda kada yaga kamar Bataji mganarsa ba yasa taje ta Cire 30k acikin kudinsa Ta Siyama mardiya kaya su Atamfa da leshi Da Sauran kayan amfani Saboda ita babu abunda bata dashi Ta Taba kudin ne saboda ya samu Sukuni acikin Ransa kuma Yaji Dadin haka sai yaji kamar Rumana ta Sauke mai wani Nauyi ne.

Shiryan shiryan Bikin Maryama suke yi Daga ita Har Dizan Dayake Maryaman Datazo bata koma Tare da Su Inna zainaba sai ta Tsaya ta kwana Biyu da wannan Damar Diza da Rumana suka samu suka gyarata,Rumana ta Siya mata su Turarukan gyaran Jiki,Mommy kuma ta Hada mata kayan gyaran mata na Sokoto,Bata koma ba sai da Tayi Fes da ita Domin har Dika da Halawa Diza ta kaita akayi mata bayan ta Zage da kanta tayi mata Saloon mai kyau,Ta kuma saka aka yarfa mata Kitso mai kyau da yarari Tana Zaria su Mansur sukaje suka Dauro auren ta da angonta Jabir wanda ya kasance Civil Defence ne yana da mata Daya da Yara Biyu wani Operation ne ya kawosa nan Maruka har suka Hadu da Maryama din yaji ta kwantamai arai Daman an saka Za"a Fara Daura auran ne Daga Baya sai ta Tare,wannan karon Mastur yayi kokarin ya samu Daurin auran Domin yaji matukar kunya ace wannan karon ma bai samu Zuwa ba kamar na Sakina ammh bai Biyo ta Gida ba kwana Daya yayi ya juya Abuja Daganan zasu yi Taro ne da IG Na kasa Gabadaya suma su Mansur din kwana Dayan sukayi suka Dawo,Baba Habibu da Daddy da Kawu Usman Abba bai samu zuwa ba sai dai yayi ma Baba Sule sako.
Sai bayan Daura auran da kwana Biyu angon Maryaman da kansa yazo ya Dauketa Dauke da Sha Tara na arziki,da Diza da Rumana suka Hada mata uwa uba Mommy kaya Dinkakku bata san iyakarsu ba da kuma kwance wadanda zata kaima Matan Baffaninsu da ya"yansu kannensu kenan,koda ta koma ta Bude kayan arziki Inna Zainaba sai kuka Tana mai kara Nadaman abubuwan Data aikata ma Maryama da Zuru"arta ssi gashu yau bata Duniya abunda ta Haifa da Ahalinta sune jigonsu ayau Kayan Data Rabama Matan Baffaninta da ya"yansu kuwa kamar Zasu Goyata saboda Murna kayan Diza da Rumana ne Sabbi ne bai wuce sawa Daya zuwa Biyu sukayi ba sai kayan Mommy harda na Hajja ita don ma ta kwashe ma Inna Karime Datazo.
Tun da Tariyan ta gabato Rumana ta samu Diza sukayi Shawaran zasu yi anko na Fitar Biki Tunda angon ya yarje in ankai Maryama baki su kwana anan Gidansa Dake kano sai Washegari su koma Zasu yi ankon kala Biyu Leshi da Atamfa Rumana tace Mastur zai Dauki Ragamar Siyan ma kowa Less din Ita kuma Diza kuma tace Mansur sai yayi Atamfa,Rumana cikin Bankin Mastur ta Cira kudi mai yawa gaske Daya ga Alert din bai wani Damu ba Domin koda Baya son Rumana ya yarda da ita Dari Bisa Dari ya Tabbata bazata taba yin wani abu na Batanci ba ko kuma wani abu wanda bai kamata ba yana da kyakyawan Zato a kanta.
Shiyasa koda sukayi waya batayi mai mgama ba Shima bai mata ba Itama Diza Batare da sanin Mansur din ba Ta Cire mai kudi ta Bankinsa yagani Shima din bai bai da kai,Shima din dai ya yarda da Diza Sosai Fiye da kansa yana da kyakyawan yakini akanta Ballatana Harkan nasu ta Siyaasa ta kara Dauke mai Hankali.

Kano suka Tura sakon kayan wannan aikin Diza ne domin tana Harka da Dilolin Kaya Dake kano Ita da Rumana suka Zauna Sukayi Selecting kala da kuma Iya adadin wadanda za"a kawo Guda Goma Sha Biyar sukace akawo Both,Sukace koda yayi yawa ba"a rasa wanda za"a Bama wa ba cikin kwana Daya Sakon ya iso Direban Diza yaje ya karbo Sakon,Dinki ma waje Daya suka kai Telan Diza suka bama Dukkansu sun san Size din wadanda zasu bama kayan Shiyasa basu wani Wahala ba Size din Hajja akayi ma Inna Zainaba da Inna Balaraba sai Size din Rumana akayi ma Sakina da Mariya tunda suna da Dan kauri Sai Maryama akayi musu Kai Daya Dana Mardiya Tunda tace Jikinsu Daya Mommy kuma Diza tasan nata haka Umma Rumana ta Fadi nata Tunda itama tace Insha Allahu Zata zo.

Haka kuwa akayi Cikin Kwana uku aka gama Duka Dinkuna Dayake sun saki Kudi iyayen Dinki Iri Daya akayi musu,Yan matan kuma da Matan auran Iri Daya ne Dukkansu,basu Fito da kayab ba sai ana Gobe Tafiyarsu Ranar da Umma ta Diro Daga Sokoto wajen Mommy ta Sauka Ranar Diza da Rumana suka je da kayan suka bama Kowa nashu Harda Aiya ba"a barta abaya ba Sukace Kowani Kala Daya Daga Mansur da Mastur,Hajja ma suka bata nata Haka ma Mardiya sai Umma da Mommy sai na Inna Balaraba Daman tana Gida Ita Harda kwallah Tana jera ma su Mansur addu"an gamawa da Duniya  Lafiya,sauran kuma sukace na yan Maruka ne har Raran Guda Biyu sukace zasu bama Matan Baffanin mansur manya guda Biyu su umma sukace hakan yayi Daidai.
Ana Gobe Tariyan suka Daga zuwa Maruka Dukkansu Harda Ayya ba"a bari ba Baba Habibu kadai aka bari da Daddy sai Mansur Sai Kawu Usman Daya samu Lafiya Shima har ya koma kasuwa Irin Baba Habibu Wata Motace mai cin Mutum goma sha Biyu Mansur ya kawo musu na Siyasan su ne Direbansa yakai su shi kuma zai jirasu ya Dawo Dasu.
Suna sauka suka iske Kara da kuma Tarban da akayi musu,sai wanda yagani nan suke iske Inna karime Maryama sai murna Take ita dasu Sakina Taja Lallenta ja da Baki, sai da suka Ci abinci sukayi Sallah kana Rumana ta Fito da kayan ta bama Kowa nashi Inna Zainaba haka take kuka Tana kwarara su Mansur addu"a ita da Matan yayin Baba Sule hakama Inna Karime Domin har da ita Daga Mansur Har Mastur basu da Masaniyan komai sai dai kiran waya kadai suke amsawa Daga yan"uwan da iyayanau suna Gode musu da sska musu albarka,abun ya basu mamaki Mansur ma Hajja ya kira yana Tambaya ta Fadamai mganar kayan shi ya kira Mastur ya gayamai,Mastur bai yi mamaki ba ya Tabbata wannan Tunanin Ruma ce domin Haka take mai kyakyawan Zuciya Koyaushe Yana jin Alherin Datake kaima su Hajja abakin Aiya Tana gayamai kuma Har ga Allah yana jin Dadin Har cikin Zuciyarsa yaji ya bata wani Matsayin Dazai yi Zaman aure da ita Tunda wacce yake son tayi mai Nisa Nisa na Har Abada Tunda Har gata Dauke da Cikin Dan"uwansa Rabin Jikinsa,bazai ce ya Cire Diza Daga Ransa ba, sai dai ya Dakushe Tasirin Soyyar nata ya Fara Karkata kansa Inda Halas dinsa yake ya Riga yagama Gudiri Niyar in yayi wannan Dawowar zai kara gyara Mu"amalansa da Rumana komai ya wuce da yardan Allah.

Washegarin Ranar da suka zo sun Tashi Da Hidiman Biki ne,kowa ta saka Atamfanta da su Rumana suka zo dashi leshi sai Gobe in sunje kano,Abunda yasa Zasu kwana Saboda Jere ne,Mommy ce ta Wakilta wata kawarta achan kano ita aka Turama kudi tayi Siyayyan komai kuma sai aranar ta kira Mommy tace ita da kannenta suna Gidan Maryama din Inda Zata zauna ita da Abokiyar Zamanta sun Fara gyara Dakin Mommy taji Dadi tace suna Hanya Komai fa achan achan kayan su Soye Soye Diza ta saka ma"aikatan ta sukayi komai Duk Dasu suka zo karfe 1pm na Rana ango ya kawo Mota Biyu aka Dauki Amarya da yan"uwanta Su Umma kuma motarsu da suka zo da ita suka Shiga sai kano suna zuwa suka Fara gyaran Dakunan Maryama din mai Ciki da Falo da Bedroom sai Kicchen,sun samu Tarba wajen Danginsa da Matarsa,sun kai Dare suna gyaran kafin su gama Gari na wayewa karisawa ne kawai Kowa yaga Daki sai Masha Allah aikin Mastur ne Shi yayi komai ma wannan karon,Tum Safe suka gama Shirin Komai su Mommy da Matan Baffaninsu Baba Sule suka Mikata Wajem abokiyar Zamanta suka Hadasu karfe 11am na Safe suka Dauki Hanya Bayan sun bar Maryama na kukan Rabuwa dasu a anguwan Dorayi suke da Zama gidan mai kyau dashi Masha Allah Maruka suka koma suka Kara kwana Washegari Litini suka Juyo Zuwa Zaria Cike da kayan arzikin da Inna Zainaba da kuma Yan maruka suka basu irin su Daddawa kuka,Kubewa,garin kunu da Sauransu
Suna Dawowa kwana Daya Umma ta kara ta juya Sokoto.
Sai bayan da suka Dawo ne Mastur ya kira Rumana yayi mata Godiya Abunda dataji kamar amafarki Bangaran Diza kuwa Godiyar data amsa mai Girma ce kuma mai Tsadace kuma mai wuyar mantawa ce..Ita kadai in ta Tuna Mansur sai taji kamar Daman ce Shi take so Kawai Mastur burgeta yake yi Tunda gashi a Duk Duniya yanzu Bata da wani Sanyin idanuwa irin Mansur Tana jinsa acikin Bargonta da Ruhinta Gabadaya Yadda take Bama Mansur madaran kauna yasa ya Barka wata Kiba saboda kwanciyar Hankali da Natsuwa.

*****


Hulansa ta Daukomai kalan Sararin Samaniya wacce ta Dace da kalan Shaddan Jikinsa Dake maiko da yarari ta aza mai Bisa kansa Bayan tayi Dage da Turtstsen Cikinta Daya Fito Sosai Turare ta Dauko ta Shiga Fesamai Tana kauda kai Lokaci Daya bata so Su Hada ido Dashi.
Kugunta ya Riko Lokaci Daya da Hannunwanta Yana so su Hada ya Kalli Fuskarta ammh sai ta kawar da kanta ganin Haka yasa ya Rumgumota gabadaya acikin Jikinsa yana Fadin"Haba Firstlady dita Duk Fushin ne na Kada na tafi na barki yasa kika kasa Hada ido dani..?
Tura Baki Tayi Lokaci Daya taji wani Rauni ya Shigeta Ta Dago Tana kallonsa a raunane tace"Nidai kada Fita Yau don Allah.."Abun nata sai yaso bashi Dariya ya Dafa kafadunta Duka Biyu yana Fadin"Meyasa yau kika Chanza Dizata..? Na saba Fita Har Tafiye Tafiye ma ammh baki Taba cemim kada na Fita ba sai yau..?Umh gayamin meke Damunki ne...?
Yafada Lokaci Daya yana Saka Hannunsa Guda Daya ya Dago Habarta Dashi kamar al"amara sai ga Hawaye Sharr Cikin Tsoro ya tsaya yana kallonta kafin yace"Subhanallah Diza..meyake Faruwa ne..? Cikin kuka Diza Ta Fada Jikinsa Tana Fadin"nidai Kawai ka Fasa Tafiya kadunan nan.Haka kurun nake ji araina in ka Tafi kamar bazan sake ganin ka ba..!ta karishe Fada Cikin gunjin kuka.
Kalamanta sun sakashi yaji wani Farinciki da karin Kaunarta bai Dagota ba sai ma Dukan Bayanta Dayake Cikin alamun Lallashi.
Sai da yaji ta samu natsuwa kana ya Dagota yana Share mata Hawaye Lokaci Daya yana Fadin"in jiwa yace in na Tafi bazan Dawo ba ehe..? Insha Allahu zam Dawo Gareki Firstladyta.."Yafada yana mai kura mata ido Cikin wani yanayi da kauna da Muradi mai Girma.
Kwalkwal Diza Tayi kafin tace"Nidai naji..Ammh kafasa Tafiyan nan Don Allah."Kansa ya Dafe kafin yace"Bazai yuyu na Fasa ba Diza..Taron na gwanna nefa..In ban je ba akwai mtsala yanzu haka nasan yan Tawagata suna nm....! Kir...kir...kir..!
Kiran wayarsa ya Katsesa da Mgana da Sauri ya Dauketa Tunda Cikin aljihunsa Take ganin mai kiran Sagir ne P.A Dinsa Da Sauri ya Daga,Shuru yayi bai yi mgana sai chan yace"Kuna wajen get din ne..? Sai chan kuma yace"Shikenangani nan Fitowa..!
Daga Haka ya yanke kiran yana kallon Diza agogonsa na Fata ya Dauka ya Daura a Tsitsiyan Hannunsa Lokaci Daya ya Duka yana Zura Takalmin da Diza ta Fitomai Dashi Sahu Ciki,sai da ya gama Sakawa kana ya Dago yana kallon Diza kafin yace"Ba Rakiya Uwar Biyu..?
Kasa Mgana Tayi Domin ita kadai taji me takeji Ganin taki Takowa garesa yaasa yayi Mirmishi kawai ya Juya yana Fadin"Sai na Dawo..Ki kula da kanki Kin ji ko..?
Sai da yakai kofa taji kuka yazo mata ta Runtuma da gudu ta isa Garesa sai dai yaji ta Rumgumoshi Ta Baya Tana kuka sai Lokacin Jikinsa yayi sanyi ya Waigo ya juyo da ita yana Share mata Hawaye Lokaci Daya yana Fadin"Ki daina kuka kin ji ko..? Zan Dawo da yardan Allah..!
Kai ta gyada mai kafin tace"Kayi min alkawari..? Shima kan ya gyada mata kafin yace"Nayi miki.."Mirmishi ta sakarmai kafin ta Kara Rumgumeshi Shima sai ya Riketa yana Fadin"Kinga Dauki mayafinki na ijiyeki wajen Mommy ko Hajja..Tunda Anty Rumanan bata nan Tana asibiti..!
Da musu ta koma ta Dauko Mayafinta wayarta suka Fice Tare  amotarsa ta Shiga Direba na Jansu suna Fitowa Tawagarsa na waje suka Rufa musu baya amotar ma har suka kai kofar gidansu Hajja Kuka Diza take yi Tun Mansur na Daukan abun Wasa har shima Jikinsa yayi sanyi Shi ya karata Har Falon Hajja suka gaisa Lokacin Aiya na Ciki Tana Barci har yakai Kofa ya Dawo ya Tsugguna gaban Diza ya Sumbaci Cikinta kana ya Dago ya Sumbaci Goshinta ya Fice da Sauri Hajja dai na Daga Dakinta sai dai itama Haka kurum taji Zuciyarta ba Dadi tama kasa Cema Dizan kala.

Tun Bayan Tafiyarsa bata Minto Goma sai ta kirashi Taji Lafiyansa Haka shima,ta kasa Samun natsuwa sai da yace mata sun kusa isa Kaduna kana taji ta Dan sake,Hajja na Kitchen tana wanke wanke taso ta karba ta Hanata ganin Abunda take Dauke dashi sai ta Dawo Falon ta zauna Tana Cin wainar Fulawar da Hajja ta Soya mata yanzu da yaji.
Ko Minti Talatin basu yi da mgana da Mansur ba sai ga Kiransa wannan karon sai taji Mugun Faduwar gaba Har Hannunta na rawa wajen Daga kiran.

"Hello...Daga Hukumar Road Safety ne..Honourable Mansur Doguwa ya samu Hatsari a Hanyarshi ta Zuwa Kaduna yanzu haka muna Hanya zamo kawosa nan asibitin ABU dake Chika sai ku isa Asibitin Domin karin Ba....!
Iya abunda ta iya ji kenan wayar ta Subuce Daga hannunta ta Fadi kasa ita kuma ba inda Jikinta baya bari Gabadaya taji Numfashinta ya tsaya Cak Dan Cikinta ya Wani Wuntsila Lokaci Daya Taji Jinta ya Dauke da ganinta sai dai ta samu nasaran Yabka wani Razanannen Ihu Lokaci Daya Tana Fadin"Na shiga uku na Lalace Shikenan Mansur ya Tafi ya barni..Sai da nace kada ya Tafi..Shikenan ya Tafi ya barni..!





*Shakira..*
1/1/22, 18:55 - Maryam Badmsi: *SS...31*

*Ki biya ki karanta cikin salama da aminci 09069067488*

"Hajja dake Kitchen ne ta Rugo da gudu zuwa Falon jin ihun Diza atare suka Iso falon da Aiya wacce ke barci Ihun Diza ya Tada ita,Hajja ce ta Duka ta Rike Diza Tana Girgizata Lokaci Daya Tana Fadin"Hadiza meya ke Faruwa ne..? Lafiya.meya samu Mansur din..?
Take Fada Cikin Razana da Firgici jin kalaman da Diza ke Fadi.
Cikin kuka da Tsayawar Numfashi Diza ta Dago Tana kallon Hajja Lokaci Daya ta Riko Hannunta Tana Fadin"Hajja Mun bani mun Lalace..yanzu akakirani awaya ana Fadamin Mansur ya samu Hatsari a Hanyarsa ta zuwa kaduna..!
Dam gaban Hajja da na Aiya Bugawa Lokaci Daya Hajja ta Zabura ta saki Hannun Diza ita da Aiya suka Bude baki suka Furta Innalillahi wa"inna ilaihirraju"un Lokaci Daya cike da wani Firgici da Tashin Hankali Da ya bayyana a Fuskarsu Lokaci Daya.
Baya Hajja Taja cikin Tashin Hankali take fadin"Hasbunallahi wani"imal wakeel..Mansur..Allah yasa yana Lafiya Allah yasa wani Abu bai samu D'ana ba.."Tafada Lokaci Daya Hawaye suna wanke mata Fuska haka kurum Take jin wani Tsoro Daga kasan Ranta Diza kuwa kuka take yi kamar Ranta zai Fita Aiya ma Haka ga Rikicin Tsufa sai kuka Take Tana kiran Sunan Mansur Hajja Data Rasa ina Zata Nufa waje kawai Tayi ba Takalmi a kafarta ta Rarumi Zaninta data wanke saman igiya ta yafa ta Fice da Gudu sai Gidan Mommy Domin ta Shaida mata Abunda ke Faruwa.
Tana Shiga Falon Farko taci karo da Mama Fadime yadda Ta ganta ne yasa tace"Hajja Lafiya kuwa..?Hajja na Sharan kwallah tace"Ina Hajiya..?Mama Fadime tace'Tana Sama.."Ai batama gama Rufe baki ba Hajja ta Fara Taka Benen Da Gudu kamar Zata Kifa Mommy Dataji Kamar mgana Daga Sama ta Fito Daga Dakinta sukayi Kicibis da Hajja Cikin Tashin Hankalin ganin yadda Hajja ke kuka ne ya kusa saka Zanin Dake Jikin Mommy Sabulewa Cikin yanayin Firgici Tace"Mun Shiga uku Hajja Lafiya..? Wani abu ya Faru ne..?
Hajja ta Fashe da kuka cikin Raunin Zuciya tace"Yanzu aka kira Diza Aka gayamata Mansur ya Samu Hatsari a Hanyarsa ta Zuwa Kaduna..!
hannu Mommy ta dora akai Tana Fadin"Innalillahi wa"inna Ilaihirraju"un
Innalillahi wa"inna ilaihirraju"un
Tafada Lokaci Daya Cikin Tashin Hankali kafin ta Rike kafadun Hajja Tana Fadin"Yanzu yana ina..? Hajja tace"Bansani ba..Dizan bata min wani bayani ba sai kuka take.."Mommy tace"Ita Dizan tana ina..?
Hajja ta kara saka kuka Tana Fadin"Ko Minti Arba"in ba"ayi ba Dayazo ya kawota yayimin Sallama da zai je kaduna Taron su na Siyasa ya Dawo ga Diza ta zauna waje na Tunda gidan ba Kowa Ruma na asibiti..!
Ta karishe Fada Cikin karaya da Raunin Zuciya.
Juyawa kawai Mommy Tayi Zuwa Daki Tana Fadin"Bari na Kira Alhaji..Hasbunallahi Allah yasa Mansur yana Cikin kyakyawan yanayi ya Allah.."Take Fada itama Tana Gabda Fashewa da kuka jin Haka yasa Hajja itama ta Runtuma Zuwa Gida Domin ta kira Baba Habibu koda ta dawo ta iske ba yarda suke,Diza Tana ta kuka kamar Zata Shide,Aiya kuwa tama Gama Shiga rudani.
Ganin Halin da Diza take Ciki ne yasa Hajja ta Rikota Tana Fadin"Tashi..Tashi..Bar kukan nan Diza..Insha Allahu Babu Abunda zai samu Mansur..!
Diza kallon Hajja kadai take yi Tana jin kanta kamar ba Nata ba Cikin Juriya Hajja tace"A ina suka ce Mansur din yake yanzu..?
Diza ta Dafa Hannun Hajja Tana Fadin"Sunce suna Hanya zasu kai shi Asibitin ABU chika.."
Cikata kawai Hajja Tayi ta Nufi Daki Tana aro Jarumta wayarta ta Dauka ta kira Baba Habibu yana Tsakiyar kasuwa ta sanar mai Labarin Daya kusa sashi ya Fadi kasa Cikin Matsanancin Tashin Hankali ya Furta"Gare ka muke muka garekazamu koma ya Allah..Mu hadu a asibitin yanzu zamu tafi ni da Usman..'Yana gama Fadin haka ya Yanke kiran yana kiran Sunan Allah Kawu Usman Dake gefensa ke Tambayansa me ya Faru cikin Tashin Hankali nan yake gayamai Shima sai Salati Daman Baba Habibun ne yazo Sabon Shagon da Mastur ya tankamai Jari ya Farfado,nan da nan suka Hau Mashin din Baba Habibu suka Dumfari asibitin Chika Hankula tashe.
Haka ta Faru Daga Barayin Daddy Lokacin da Mommy ta kirashi,take gayamai shima Duk sai Hankula suka tashi yace yana Sabon gari ne yanzu haka Shima zai wuce asibitin In Mommy Zata iya Tuki ta tukasu Zuwa asibitin Haka kuwa akayi Mommy ko Duba mayafi ma batayi ba Hijabin Sallarta ta Zumbula ta Dauko key din Mota ta Zo Haraban Gidan ta Fito da Mota waje Bayan ta Sanar da Megadi da Mama Fadime Halin da ake Ciki.
Cikin gidan su Hajja ta Shiga ta iskesu Zukata sun Raunana Gwiwoyin sun yi Sanyi Diza ba yarda Take tun Tana iya kukan da Baki ta koma na Zucci sai Hawaye Hajja ce ma ta Zama mai Juriya tana Lallashinta Aiya kuma sai mganganu take Tana Fadin"Wayyo Mansur..Allah yasa yana Lafiya Allah ya karemana shi.."
Da Farko Mommy taso tace Diza da Aiya su zauna agida ammh ganin Irin yadda Suke ne yasa bata samu Damar yin mgana ba Suka Dumguma Dukkansu Zuwa asibitin Mommy ke karfin Halin jan Motan Su kuma zukata nata Salati da Ambaton Allah.

Sanda suka isa asibitin sai suka Rasa ina zasu gashi asibitin ta Cika da Motoci basu san Lokacin Tuni har tawagar mansur din sun iso dashi Tare da yan Sanda,Mommy ce ta kira Daddy ya Daga nan take gayamai gasu sun iso Cikin Tashin Hankali yace yana Hanya bai kariso ba Ammh Yanzu sunyi mgana da Baba Habibu yace Sagir P.A din Mansur ya kirashi suna Emergency Harda shi Baba Habibun da Usman din Balaraba sun iso Suna Tare."
Jin haka yasa da Tambaya suka isa Kofar Emergency din Tunda  wajen suka Tabbatar da Ba Lafiya Domin gasu Sagir nan sai Sharan kwallah suke da Sauran Matasa ga yan Siyasa nan Abokan Mansur da kuma Yan Partynsu Gefe kuma Baba Habibu ne da Usman Tsaye kowane yana Kokuwa da Numfashinsa Hajja ce ta Fara Tunkarasa Sai ji kawai yayi ta Rikosa Tana Fadin"Ina Mansur din..? Babu abunda ya Sameshi ko?
take fada Cikin matsannancin Damuwa da kuma Zubar kwallah sai da ya Dago kai ne ya Ci karo da Mommy da Diza da Aiya Idanuwa sunyi Jajir Cikin Jarumta yace"Hajiya gabadaya kuka Taho..? Harda Hadiza Tana wannan halin ai da kun barta agida ita da Aiya..!
Mommy tace"Bazasu Zauna ba Baba Habibu..Yanzu dai ya ake Ciki..? An kawo Mansur din..? Kuma wani Hali yake Ciki..?
Baba Habibu ya saki Numfashi kafin yace"To bazan iya cewa komai ba Hajiya koda muka kariso an riga an iso Dasu har an Shiga dasu Ciki..Sagir ne ya Kirani ya gayamin sunaa Emergecy Hatsarin Shida Direbansa ne suka yi karo da Mitar Bua..!.
Dukkansu suka Hada Baki wajen Fadin"Innalillahi wa"inna illaihirraju"un.."Sai kuka Diza da Aiya Hajja kuma sai Hawaye Baba Habibu na Jin Abun aranshi yace"Mummunan Hatsari ne ya Faru sukace..Dayake Motarsace akan gaba Yanzu dai Tunda Likitoci suka Shiga Ciki basu Fito ba..Sai dai mu jira muga Abunda Allah Zai yi kuma.."Mommy na Sharan kwallah Tana Fadin"Allah ya Tashi kafadunka Mansur..'
Daidai Shigowar Daddy Hankali Tashe ganinsu Cikin wannan yanayin yasa Duk ya Razana Cikin Tsoro yace"Ya jikin Mansur din Habibu..? Bayanin Daya yi ma su Mommy Shi yayi ma Daddy wanda yasa Dole ya Cire Hula yana Fifita Cikin Tashin Hankali yace"Hasbunallahi wani"imal Wakeel Allah ka kawo ma wannan bawa naka da Sauki.."Yagama Rufe baki kenan sai ga Babban likitan Daya Jagorancin Sauran Likitocin Daga Emergency din ya Fito yana Cire Safar Hannunsa Duk Jini ya Jefa Cikin Abun Shara Da Sauri Su Daddy suka Nufeshe da Duka Jama"ar Dake wajen kowa Tambayansa yake Ya ya Mansur din yake..?
Dr. Din ya kallesu Daya Bayan Daya kafin yace"Su waye Ilayan Honourable Mansur acikin ku..? Da sauri Daddy da Baba Habibu suka Bayyana Gabansa Cikin Nazarinsu yace"Shi Dayan fa da aka kawo su Tare..'?Sagir ne yace"Direbansa ne Tare suka samu Hatsarin..!
Dr din Cikin Tsausayawa ya Dafa Kafadan Daddy ganin Duk yafi su Rudewa yace"Sai Hakuri..Dukkansu sun amsa Kiran Allah..Shi D'anku ma Tun kafin su iso nan ya Cika kansa ne ya Fashe..Dayan ne sai bayan da muka Shiga dashi Ciki..We are Sorry Mun kasa Ceton Rayuwarsu..yanzu wani Cikin kuzai Biyo ni Office Domin Cike Takardu Za"a baku gawarwarkinsu.!
"Daidai da kalma Daya na mganarsa Tamkar wata Dalmace ko nace Wuta A zukatan Ahalin Mansur Sai Ihu da kuka ya Tashi Baba Habibu Dashi da Daddy suka Tallafi juna Domin Dukkansu suna Neman Faduwa Diza Dataji komai acikin kunnunta ta kwala kara Ta Zube ajikin Mommy Data Tallafota Tana Girgizata Cikin kuka Take Fadin"Innalillahi Wa"inna Ilaihirraju"un..Allahu Akbar Allah ya jikan ka Mansur Allah yayu maka Rahma.."Take Fada Tana Rumgume Diza Ta Fashe da kuka Hajja kuwa ba Domin garun Dake gefenta ba sai ta Fadi kamkame Hannun Aiya Dake gefenta Tayi Lokaci Daya Taji kamar ta Daina Fahintar komai Sai da taji kukan Aiya Tana Fadin"Innalillahi yanzu Shikenan Mansur ya amsa kiran Allah..? Kai Innalillahi wa"inna Ilaihirraju"un zukata bazasu iya Daukan Wannan Rashin ba..!
Sai alokacin Hajja taji bakinta na Furta Salati ta Dire da Hasbunallahi wani"imal wakel Kafin ta Fashe da wani kuka mai Fitowa Daga karkashin Zuciyarta.
Baba Habibu yayi kokarin Danne kukansa ya Dafa Daddy yana Fadin"Sai Hakuri..Allah Shine ya Hallesa kuma yafimu Sonsa ya karbi Abunsa..Allah ya jikan ka Mansur."
Daddy sai Hawaye Sharr haka Kawu Usman Baba Habibu kuwa Wajen Su Sagir ya Nufa yana Fadin"ku kira Iyalan Direban nashi ku sanar dasu..Suzo sai su karbi gawarshi..Allah yayi musu Rahma.."Gabadayansu kallonsa suke suna ganinsa a mtsayin mai Jarumta da Dakiya Shi ya kara Tausan Daddy Dake kuka suka Tafi Office din Likita suka Cike Takardu nan da nan aka Fara Cukun Cukun Basu gawar Mansur Ba Dadewa sai ga Iyalan Direban sun iso Dan Cikin Zaria ne sai kuka suke Abun Tsausayi Matansa Biyu alokacin Hawayen Mommy Dake Diga kan Fuskar Diza ya Farkarta da ita sai bata mgana bata kuka sai Hawaye kadai Dan Cikinta na Har bawa kamar zai Fito aranar.
Zuwa Lokacin Tuni Mutuwar tayi Tambari ta Fara Yaduwa ta kafafen yada Labarai ta Internet gidajen Radio dai basu Fadi ba Tukunnah Gawan Direban aka Fara Fita da ita mansur Shi a Ambulance din asibiti za"aFita Dashi Saboda Jini Dake Zuba ta kansa.
Baba Habibu da kansa ya Kira Yayan Baba Sule ya Fadamai Rasuwar Mansur Allahu akbar Zukata Daga Chan maruka sun Raunana Maryama da Mardiya haka suka sume gau Daman Mardiya Tana chan Tun Biki Chan suka barta Baba Sule kuma sai Ciwo ya Tashi ya Fadi Allah yasa An Tareshi,Cikin Tashin Hankali suka kamo Hanya kwansu da kwakwatansu suna kuka kukan Fadin wani majingini kuma Bango Garesu Zuwa Lokacin Duk wanda ya kamata yaji Rasuwar yaji Daddy ya kira Abba ya Fadamai haka ya koma Gida yana Fadama Umma sai kuka nan da nan ya Fara musu Shirin Tahowa ta Jirgi.
Mastur ne kadai ba'a samu wayarsa  ba Ana ta kiransa wayarsa Tana Kashe sai Rumana da kwata kwata Tashin Hankalin da suke ciki ya mantar dasu ita.


****

Rumana Da suke Zaune da Abokiyar aikinta Aisha Bala a Femele word na cikin asibitin Abu Chika,waya ce a Hannun Aisha Tana ta Danne Danne Lokaci bayan Lokaci Tana Sakin Mirmishi ita kuma Rumana Zaman ta kenan ta Dawo Daga Roud din Ta Duba wasu marasa Lafiya ne,Tazo ta zauna nan kujeran Dake Fuskatan Aisha a kebentattacen wajen da aka Tanada musu Domin irinsu.

Tsuru kawai Tayi ta kura ma Kofar Shigowa ido haka kurun tun Safe yau take jinta Cikin yanayi mara Dadi ta rasa gano Dalilin Haka Taji mganar Aisha a Sama Tana Fadin"Nifa yau naga Asibitin nan ta Cika da Mutane..Anya Lafiya..?
Rumana ta Dago Tana kallonta tace"Kinsan ai ita wannan asibitin kullim Cikin Jama"a take bata Rabo da mutane..!
Aisha bata kara mgana ta Mike Dauke da wayarta ta Fice Rumana ta Bita da kallo Tana Fita Batayi Nisa ba sai gashi ta Dawo ta iske Rumana  Dauke da Jakarta Tana kokarin Fito da wayarta Cikin kulawa tace"Nifa nace..Yanzu na gamu da Dr.Yahaya shi yake Fadamin wani Dan Siyasa ne suka samu Hatsari a hanyar kaduna aka kawoshi nan asibitin kamar ma ya Rasu yace gawarsa ne ake kokarin Tafiya da ita..!
Sanda Aisha ta Fadi haka sai da gaban Rumana ya Fadi da Sauri taDago Tana kallonta Dauke da waya a Hannunta Cikin karfin gwiwa tace"Allah Sarki..Allah ya jikan Musulmi.."Ganin yadda Tayi ne yasa Aishan Tace mata"Ruma Meke damun ki..?
Ruma Data koma ta Zauna Tana Fadin"Meke kika gani Aisha Bala..?
Aisha tace"Na ganki so Cool..Kinyi wani Sukuku dake kamar ba Dr.Rumanan Dana sani ba mai Kazar kazar da Kuzari sosai..!
Wani Mirmishin Fatan baki Rumana ta saki kafin tace"Ni kaina haka na Tsinci kaina..Bansan meke Damuna ba..!ta fada kamar Zatayi kuka Aisha na Shirin mgana wayarta tayi kara sai ta Fice Domin ansa wayar Fitarta yasa Rumana ta maida Hankalinta kan wayarta Tana Dubawa sai abun ya bata mamaki ba Bata ga kiran Mastur ba Alhalin sunyi waya jiya da Daddare yace mata da Safe zai kirata ganin haka yasa ta Kirashi ammh wayarsa Tana kashe sai taji Zuciyarta ta tsinke Sanin Bashi da Dabi"an kashe waya duk Tsiya zaka Sameshi sai dai in bazai Daga bane.
Tana cikin kara kiran Wayar nashi ne Aisha ta Shigo a Razane Cikin Haki Kamar Zata Shide wanda ya Firgita Rumana ta Mike Cikin kaduwa Tana Fadin"Aisha Bala lafiya..?
Aisha ta karisa ga Rumana ta Riko Hannunta Tana Fadin"Taho Ruma inaga wannan kanin Mijin nakin ne ya rasu..Yanzu nabi ta Wajen Emergency naga Baban Mijinki Daya Taba kwanciya anan asibitin da kuma Matar gidan nan naku suna ta kuk.."
Ai Rumana bata gama jin mganar Aisha ba Ta Fincike Hannunta Daga na Aisha Wayarta Dake hannunta Ta Subuce Allah yasa Aishan Tayi Saurin Tare wayar Rumana ta Fita Tana Haki da gudu Tana Salati Lokaci Daya tana Fadin"Lahaula walakuwatu Illah Billahi..!
Haka take ta Fada tana Kuka Lokaci Daya kowa ya ganta yasan Bata Cikin Natsuwarta Rumana ganin Sauri bazai mata ba yasa ta Fara Hadawa da gudu Cikin Lokaci sai gashi ta iso Emergency din Daidai Lokacin da aka Fito da gawan Mansur Zanin da aka Rufeahi Dashi Zanin Hajja ne wanda tayi mayafi dashi ta bada Har ya Jike saboda Jini,Nurses ne maza suka Daukosa akan gadon da aka Daukan Matattu dashi.
Mommy na gefe Tana kuka Diza na Jikinta tana Zubar kwallah masu Zafi Hajja ma na gefe Tana kuka ita da Aiya Baba Habibu ne da Daddy sai Kawu Usman ke Biye da gawan zuwa Wajen Motar Ambulance din da asibitin ta bada zasu Kaishi gida,Sauran Tawagan Marigayi mansur suka Rufa musu baya Cikin wani yanayi.
Rumana Dataji tamkar gangar Jikinta bazai Dauketa ba ta kasa ma karisawa ga su Hajja,Tana Tsaye kamar an Dasata Tana jin kamar kanta na Juyawa da ita Bayanta Aisha ce data Biyo bayanta da Jakarta da wayarta Cikin wani yanayi Baba Habibu ne ya Dawo bayan an gama Saka Mansur a mota yazo yace su Hajja su Fito su tafi gida yaci karo da Rumana Cikin yanayin kuka na Fitar Hayyaci.
Ganinsa Yasa Rumana ta samu kwarin gwiwan yin mgana Cikin Muryan Kuka da Sarewa tace"Ba.Ba..Me samu Mansur..?
Baba Habibu Daya ke nuna Dakiya da Jarumta yace"Rumana ashe kina cikin asibitin..? Rudanin da muke ciki ya mantarmu Dake..Sai Hakuri Allah ya Dauki Ran Mansur..!
Da wani irin karfi Rumana ta Dora Hannu aka ta saki wani Razanannen Kuka Lokaci Daya Tana Zubewa akasa Domin kafafunta sun gaza Daukanta.
Baba Habibu Dayake jin shima kamar ya saka kukan yace cikin Lallashi"Ash..Tashi Rumana..Tashi..Mansur ba kukan ku yake Bukata ba addu"a kadai ce Zamu yi mai mu nunamai Soyayyarmu.."Yake fada cikin Dauriya kafin ya karisa wajen su Mommy yana Fadin"Hajiya kuyi hakuri ku Fito muje..ni zan bi Motar gawan Ku kuma Alhaji ya kiran Drebansa yana waje yana jiranku zai Tuka ku shi Alhaji Zai Taho atashi Motar,Usman kuma zai Taho da Babur dina sauran jama"a kuma zasu bi bayanmu da Motocinsu.."Fadin haka Da yayi yasa kukan Hajja ya karu Kallonta kawai yayi yana Fadin"Hajara Ba kuka Mansur ke Bukata ba yanzu..Ahalin Dayake Ciki addu"anmu itace Soyayyarmu garesa Don Allah ku Daina mai kuka Allah ne fa ya bamu Shi kuma shi ya Dauke abun Shi Domin yafi mu sonshi..Hu hanzarta ku Fito mu Tafi..Saboda asallaceshi da wuri a kaishi Gidansa na gaskiya.."Yana mgana ya Kama Hajja Data kusa Fadi ya kuma Riko Hannun Aiya Mommy ta Tallafo Diza Dake Zubar kwallah ta Zama kamar Mutum mutum kawai Rumana Data ga Ta yunkura ta mike Aisha ta Taimaka mata Suka Rufa musu Baya Cikin Alhini da Rauni.
Kamar yadda aka Tsara hakan ce ta Faru Baba Habibu Shi ya Bi Motar Gawan Su kuma Matan Direban Daddy ya Tukasu Rumana kuma Aisha ta karbi Key din ta tukasu Sauran Jama"ar Mansur suka Rufa musu Baya Irin su Sagir Cikin Tashin Hankali.

Zuwa Lokacin da suka isa anguwan Tuni Rasuwan ta isa kunnen Mutane Tunda Gidajen Radio sun Watsa Labarin,Daddy kuma Tun yana asibitin sukayi mgana da Baba Habibu kan Lokacin Jana"iza karfe 4:00pm na yammah Tunda Hatsarin ya Faru ne wajen karfe 9:30am na Safe da kawo su asibiti da karban gawan da komai 11am na Safe ma ya wuce suka Dawo saboda Sauran Mutane da kuma Uwa Uba Mastur Da ake ta kira akashe Za"a Jingirta Domin yazo ya Sallaci gawan Dan"uwansa kafin kace kwabo anguwa ta Cika da al"umma kama Daga Abokan Siyasan Mansur matasa yan makaratansu Yan maruka ma sun iso Cikin Raunin Zukata Sai aka Hade Falon Hajja ana ta kuka Kamar me,Ba iya Cikin Gida ba Har waje magidanta kuka suke na Rashin Mansur haka Matasa,Inna karime ma ta iso Ita da Mijinta Tana kuka,Sai ga Maryama itama ita da mijinta da Kishiyarta ajaran majaran Ita bata ma ji Ba Mijin nata ne yaga Labarin na yawo A social media yazo ya gayamata Tunda yasan Yayanta ne, Shine fa Hankula suka Tashi Ajaran majaran suka Taho.
Tana Shigowa sai kuka kuma ya Karu Gawan Mansur Tana Uwar Dakin Hajja ne,chan aka kaisa Hajja na gefe sanye da Hijabi da Carbi Tana ja kuka ya Dauke mata Mommy na gefenta itama Cikin Hijabi da Qur"ani a Hannunta Tana karatu sai Daga Chan Gefen Diza ce Zaune tana Jingine da Bango Tana Sanye da katon Hijabin Hajja sai Carbi Dake hannunta ta kura ma gawan Mansur ido Dake Lullube da Zani tana Zubar kwallah Shaa!!! Kamar famfo Gefenta kuma Rumana ce itama Cikin Hijabi Itama kuksn take sai Kawarta Aisha itama sai Sharan kwallah take sai mardiya,Sakina dasu Mariya suna Falon Hajja suna ta kuka dasu Balaraba da Sauran matan Baffanin Baba Sule,da sauran Makota da suka Shigo,Ana cikin hakane sai ga Umma ta iso ita da Anty Saratu itama Tana shiga taga gawan Mansur sai ta Fadi Tana Kuka Hawaye na Zubar mata take Fadin"Allahu akbar..Allah jikan ka Mansur Allah ya maka Rahma..Allah ya sadaka da Mala"ikun Rahma..Allah Sarki Rayuwa kenan..'Take Fada Tana kuka Anty Saratu na Riketa itama Tana Sharan kwallah Dagata tayi suka koma Gefen Hajja suka Zauna Cikin kuka take Fadin"Hajja ya muka ji da Hakurin wannan Babbar Rashin..?
Hajja ta Bude baki Cikin Shakkiyar Muryan Dataji kuka tace"Hakuri..Namu ne Duka Hajiya sannunku da zuwa. mansur ya tafi ya barmu..Shima yazo ya tafi kamar yadda Mahaifiyarsa Maryama Tatafi ta barmu.."
Umma na kuka take Fadin"Allah ya musu Rahma..Allah ya sadashi da mala"ikun Rahma..An gayama Shi Dan"uwan nashi..? Har muka iso Abban Ruma nata kiransa Wayarsa Tana kashe..!
Wannan karon Mommy ce Tayi mgana cikin Zubar kwallah Tace"Duka an kira wayoyinsa a kashe..Ba'a samesa ba..Su Alhaji sunce baza"a jira sa ba..Gwara ayi a Sallacesa Zuwa Gidansa na gaskiya..Tun dazu ma da suka Shogi nan har sun kira Chan dambom makabarta an Fara Hakan kabari nan kuma Usman Mijin balaraba ya tafi Hado likafani da kayan wanka..!
Tana Fade tana Sharan kwallah Umma ta gyada kai tana Fadin"Allahu akbar..Rai bakon Duniya.!.
Rumana ta mike tsam ta Fice Daga Dakin Bata kuka sai dai idanuwanta sun yi Jajir Saboda kuka kitchen ta Shiga ta Zaro wayarta Cikin Haban Sikat din ta Kara Nenan Layin Mastur bata shiga Kawai sai ta yanke Shawaran Turamai sako.

*Ya Mastur kana ina ne..? Ko a ina kake kazo gida ba lafiya..*
Daga haka ta Turamai kana ta Fito Daga kitchen Dakin Aiya ta Shiga Aiya tana Falo kamar ma ta Rude sai mganganu take,Dake da Tiolet ta Shiga ta Dauro alwala tazo ta Dauki Aqur"ani Ta koma Dakin ta koma inda tatashi Ta Bude Qur"ani ta Fara karatu Cikin Sanyi da Rauni Duk Sai Dakin ya Dau Shuru kowa yana ji Bugawar Zuciya da Rauni mai Tsanani.

*****

Shigowarsa Office dinsa kenan yau tun safe bai zauna ba wani Operation suka Tafi kuma Abun Farincikin Operation din is Sessufull,Sai da ya zauna kan kujeransa ya Tuna daya kashe wayoyinsa tun Safe bai ma Tafi dasu ba nan Cikin Office din ya watsar dasu Tun Shigowarsa da Safe.

Cikin kasala dayake jin ya sameshi Lokaci Daya ya Jawo Wayoyin ya Bude su,sai da suka gama Daidaita Network kana personal Phone dinsa tayi alamun Shigowar Sako ya Dagata yana Dubawa Jerin mutanen da suka Nemeshi ne, saboda wayarsa irin mai nuna mai Duk wanda ya Nemeahi bai samu bane,Abunda ya Bashi mamaki Shine ganin Abba ya nemeshi,Baba Habibu,Daddy,Baba Sule,Ruma,sai yaji Jikinsa bai Bashi ba ganin bai ga kiran Mansur ba Alhalin da Asuban nan ma sai da sukayi mgana yace zai kirashi da Safe su karisa mgana kan yadda Zasu kai iyayansa Sauke Farali wannan Shekaran
Bai gama mamaki ba yaji Shigowar Sako daga Rumana Jikinsa na rawa ya Shiga ya Bude Abunda ya gani ne yasa ya mike da Sauri bai Shirya Lokaci Daya yaji Zuciyarsa na Duka da karfi da karfi.
Bai tsaya ba ya kwashi Wayoyinsa ya Fice daga Office din,yana Fitowa ya Hadu da Sargen Inuwa Cikin bada Umarni yace"Sargent Dauko Mota ka kaini Filin Jirgi..Zaria Zani Now.!
Sargent inuwa yayi mamakin wannan Gaggawa sai dai ba"ayi ma oga Gardama

 Da Uniform din Dake jikinsa da wayoyinsa,gidan Dayake Zaune kadai ya shiga ya Dauko Atm dinsa da Walet dinsa Daya manta da Safe bai dauka ba ya Fito ya Shiga Mota sai Filin Jirgi Abunga ga Masu fada aji kuma abu in aka ce maka akwai Naira nan da nan komai ya kamallah ko Awa Daya Mastur bai yi a Filin Jirgi ba Jirgunsu ya Daga Zuwa Kaduna da Misalin karfe 11:30am Hankalinsa kwata kwata ba"a kwance yake ba Shiyasa bai yi Tunanin kiran wani ba suna Shiga Jirgi ma kuma ya Kashe Duka Wayoyinsa sai dai kuma Tuni Zuciyarsa ta Daina Bugawa Daidai yana ji ajikinsa Tabbas wani Abu na Faruwa mara dadi a Zaria.








*Shakira..*
1/1/22, 18:55 - Maryam Badmsi: *SS....33*

*Ki biya ki karanta cikin Aminci da Salama 09069067488*

"Yadda suka ga Rana haka suka ga Dare,Mastur bai Runtsa ba Duk Tsawon Dare hakama su Baba Habibu su Diza kuwa Daga cikin gida ba mgana Barci sai dai Barawo ya iya sace Daidai ku Daga Cikinsu,Domin zukata Tuni sun gama raunana,Kuka ya bar Fito musu sai Jiki da Zuciya ke ta Faman Turiri da Zafi Dacin Rashin da sukayi mai Girma atare dasu.

Washegari ma haka ma Mutane basu yanke ba sai zuwa suke kamar ba gobe Mastur bai yi mamakin ganin Abokan aikinsa sun zo mai gaisuwa basanin Kaninsa Sananne kuma Mutuwar ta Zaga Duniya Harta da Headquater su na Porthercourt sun zo mai gaisuwa sai ga Abokinsa Acp Saleem kumo da Matarsa Hajiya Malika sun zo ma Mastur gaisuwa ba Shakka yaji Dadi sosai nan da nan akayi ma Malika iso Cikin gida wajen su Diza,Duk Ba wanda yasan ta a ido ammh Suna jin Labarin Saleem kumo abokin Mastur abakinsa.
Malika ta Tsausayama Diza sosai da Rumana Duk sun Fita Hayyacinta Dayake daga ita sai Saleem din sukazo ta bar su Hajiya wajen Ummi suna Abuja Tayi amfani da Iliminta ta Rika Lallashin Diza da Rumana da kalamai na kwantar da Hankali Tana musu misali da Ranar data Rasa Mahaifinta da irin Tashin Hankalin Data shiga sai gashi Dalilin gwarzom Mijinta gashi yanzu bata Cikin wani Rashi Da Damuwa ssi ma Godiya Allah Datake yi.
Rumana ce kadai ta Fahimceta banda Diza da take kallon kasa kawai batare data Motsa ba Tun Jiya bayan an kai Mansur gidansa na Gaskiya Diza bata kara mgana sai dai ta kan amsa gaisuwa in anyi mata Kowa yazo ya ganta sai ya Tsausayamata Da kuma Addu"an Allah ya Sauketa Lafiya.
Sai washegari Saleem kumo da Matarsa Malika suka koma Cike da Tsausayin Mastur da Ahalinsa.
Tunda akayi Rasuwan Gidajen Biyu suke Cike da Jama"a wasu na Zuwa wasy na Tafiya Lalle ya Tabbata Mansur mai Jama"a ne kuma mai Mutane,Sun ga Zahiri Lokacin da kasa ta Rufe idanuwansa kuma Duk wanda yazo Alherinsa yake Fada ba wanda ya Taba ganin Abokin Fadansa Mus"ab ma yazo Shi da Iyayansa Yayi kuka sosai kamar Ransa zai Fita yaje har kabarin Mansur yayi mai addu"a sai Ranar da akayi uku suka koma Sauran Bakin maruka da yan Ririwai da sukazo kuwa wasu Ranar Shida wasu kuma sai da akayi addu"an bakwai wasu kuma Sai Washegari kamar sun kannen Mansur Sakina da maryama da mariya masu Auran sai Inna Zainaba da Matan yayyin Baba Sule dashi kanshi da Sauran yan"uwansa Duk aranar suka Koma,Sun yi kuka kamar Ransu zai fita sai Mutuwar ta Dawo Tamkar Sabuwa aranar Washegari Ranar takwas Umma da Abba suka koma Dayake duk yan uwansu na Tureta dana wamako duk sunxo gaisuwa Mota Guda da yan Gidansu Mommy Tun Ranar da akayi uku suka zo suka koma
Har Inna karime da iyalanta Ranar ta koma gida duk ya watse Daga Rumana sai Diza sai Mardiya dasu Hajja Mommy ma ta koma Gida sai dai nan take Wuni Waje kuma Daddy ne kadai ke karban gaisuwa Dayake Mutane na Zuwa Jefi Jefi.
Zuwa Lokacin Mutuwar ta Gama shiga Jikinsu Sun Riga sun Tabbatar da Mansur ya Tafi ya barsu har Abada kowa kagani ya Rame yayi Dan wuya Barin ma Mastur da Diza tamkar basu Taba Fuskantan wani Farincikin acikim Rayuwarsu ba gwara Mastur yakan sha Ruwan Lipton arana ita kuwa Diza sai anyi Daga da ita da Mommy najan Ido kama take yarda ta saka wani Abu acikinta bata Damu da Wani Hali Abunda ke Cikinta Zai Shiga ba kawai taji aranta Tafi kaunar itama ta Mutu tabi Mansur Chan da Zamanta a wannan Duniyan.

Ranar da Mansur yayi kwana Goma da Rasuwa duka Kafafuwa suka Dauke Baki da Nesa Dana kusa sun gama komawa Gidajensu Lafiya da Fatan Allah ya Jikan Mansur yayi mai Rahma Akuma Ranar ne Dadaddre bayan Sallar Isha"i Dukkansu suka Zauna afalon Hajja,Daddy ne ya Bude Taron da addu"a Bayan Doguwar addu"an da sukayi ma Mansur da Fatan Dacewa kana Daddy ya gangaro kan makasudin zaman nasu Nasiha kan yarda da Kaddara da kuma Tunatarwa cewa Allah Dayane kuma Mutuwa Zahiri ne inda Mansur yaje chan Zasu je suma Yayi Nasiha sosai Hakama Baba Habibu ya Dora da nashi,Diza Hawaye kawai take Zubarwa hakama Rumana da Mardiya Ayya kuwa Daman ta koma Shuru Shiru Mutuwar ta Tabata sosai Mastur na Gefe Yana Nazarin Diza gabadaya yaji Duk Duniya ba abun Tsausayi irin Diza Ko Shekara basu yi da aure ba Mansur ya Tafi ya barta da Cikinsa Shi kuwa yayi alkawarin Sai inda karfinsa ya kare wajen ganin ya Inganta Rayuwar Diza da Abunda Zata Haifa Bazai Taba bari Tayi kuka ba.
Hajja ma na gefe Tana Sharan kwallah Ita Uwa ce..Kuma Shakikiya wajen Mansur ta Shaku Dashi Kamar Danta Tunda ta Shayar dashi da Cikinta,Dole tayi kukan Rashin Shalelen Danta wanda bata da Kamarsa,Kafin a tashi wannan zaman anyi mganan Kan A ina Dixa zata zauna Har ta Haihu..?Cikin Sauri
Mommy ta Nemi da Zata Tafi Diza ta zauna wajenta ta kula da ita Har ta Haihu,Ba wanda yayi gaddama kowa yayi Na"am Sanin Halin da Dizan take Ciki Uwa ce kadai Zata iya Juriyan Da ita da kuma Kula da ita Daga karshe Daddy ya Umarci Mastur ya Dauki Matarsa Rumana su koma Gidansa yau din Ba yadda ya iya Illa Bin Umarinsu a Koda yaushe rumana ta Rumgume Diza tana kuka sai da Mommy ta Rabasu,sai da ta raka Diza da Mommy Gida Har Dakin Dizan kana ta Dawo suka Tafi gida ita da Mastur Cike da Tsausayi da Wani Acikin Zuciyarta na Tsausayin Diza da Mastur suna Zuwa gida Megadi ya Fara musu gaisuwa Mastur kadai ya amsa Rumana kuwa Haraban gidan Take kallo Tana ganin Motocin Mansur dake wajen guda 3,gata Diza itama Guda uku ta juya ta Kalli Shashensu sai kuka ai da Gudu ta Shige bata ma Jira Mastur din ba,Shima a wannan Lokaci Wani kafada yake nema inda Zai yada kansa yayi kukan Rashin Dan"uwanasa,ammh bai Samu ba.
Shima cikin gidan ya Rufa mata Baya kai Tsaye Dakinsa ya wuce,Yayi wanka ya Sauya kaya ya koma ya kwanta yana ganin kamar abun mafarki ne yau wai ba Mansur ya Tafi ya barsu Tafiya na Har Abada
Yafara Tunanin Rayuwa ba abakin komai bawa yake ba yau kana Raye gobe baka Ya Tuna yadda suka Turbune Mansur acikin kasa Dagashi sai Halinsa sai Allah,Me zai ce ma Allah in ya Mutu yau..? Wani amsa Zai bama Allah in ya Tuhumeshi da Rashin Sauke Nauyin Rumana Dake kansa..! Bashi da wani Uzuri Ballatana wani abun cewa ya kamata yaji Tsoron Allah ya gyara Lahirarsa kafin Shima yau ace ya bar Gidan Duniya.
Wannan Tunanin yasa ya Tashi Zumbur ya Fada Tiolet ya Dauro Alwala,yazo ya sauya Jallabiyan Jikinsa zuwa wata Mai ruwan Madara bata da Tsawo sosai Turare ya Fesa kai Tsaye ya Nufu Dakin Rumana da yakini da Niyyar gyara komai Shi kansa bai san meyasa Zuciyarsa keJansa ba sai dai kawai ya san Shi din Abun Tsausayi ne

Tana Kokarin kwanciya Mastur ya Shigo Dakinta Tana Sanye da Rigar barci iyakarta Gwiwa mai karamin Hannu,Idanuwanta sun kumbura tayi kuka Har tagaji Tayi mamakin ganin Mastur acikin Dakinta Cikin wani yanayi Take kallonsa Tama manta a wani Hali Take Ciki Shima Din kallonta yake Tundaga Sama Har kasa Cikin Wani yanayi wanda bazai iya Fassara shi ba.
Cikin Sanyinsa ya fara Takowa Zuwa gabanta Sai da suka zo Gabda kana ya Dakata yana Sauke Numfashi Cikin Dakiya da Raunin muryab Data kamashi Bayan Rasuwar Mansur yace"Kiyo alwala muyi Sallah..!
Yafada Lokaci Daya yana Nufar ma"ajiyar Dardumanta ya Dauka ya Daidaici gabas ya Shinfida kana ya waigo yana kallon Rumana Data kasa Motsi Idanuwanta ya Ciko da kwallah ita duk a Tunaninta,Salla da addu"an neman ma Mansur Gafaran Allah yau zaku kwana yi ita da Mastur.
Shi kuwa ganinta Tsaye yasa ya kara gyaran Murya yana Fadin"Baki ji bane Rumana..?
Sai alokacin Ta iya Motsawa tana Fadin"Ina da alwalata.."Lokaci Daya Tana juyawa ga Wardrope dinta ta Bude ta Dauko Dogon Hijabinta ta isa garesa ganinta yasa ya Daidaita Sahu ya Tada Sallah itama ta Daidaita ta Bishi Basu Tsawaita ba abun mamaki Raka"a Biyu sukayi Yayi musu addu"an Zaman Lafiya Daga karshe ya Rokar ma Mansur Gafara da Rahma wajen Allah.
Kana ya Juyo yana kallon Rumana Cikin wani yanayi da kuma Rasa ta ina Zai fara ita kuma kanta na kasa Tana wasa da gefen Hijabinta ganin sun Zauna Shuru yasa ta Dago kanta Ta gansa yayi Zuru kawai yana kallon Gabansa kamar mai nazarin wani abu Tun bayan Rasuwar yau suka samu kadaicewa su kadai yasa ta Bude baki Cikin Wani irin Rauni tace"Ya hakurin Hakuri kuma..? Allah jikan Mansur Allah yamai Rahma..!
Tafada Lokaci Daya Kwallah Suna Zubo mata.
Cikin wani irin Sarewa ya Bude baki yace mata"Hakuri namu ne Duka Rumana..Bamu kadai muka yi Rashin Mamsur ba Mutane Da Dama sun yi Rashi..Allahu albar..Allah ya Rahamaheka Mansur Allah ya Kyautata makwancinka..!
Yake fada Cikin karaya kamar zai Fashe da kuka Cikin kuka Rumana ke amsawa da Ameen Mastur Cikin Wani irin Duba ya Dubi Rumana yana Fadin"Gani nake kamar ba gaskiya ba..Gani nake kamar Mansur yayi Wata Tafiya ne zai Dawo Watarana..Na ji Rauni ya kamani na Tsorata Rumana naji kamar na Fadi kasa ina Birgima Lokacin Dana ga gawan Dan"uwana Cikin Jini..Wlh kullim sai nayi mafarkinsa Bana iya barci bana iya Runtsawa Rumana na Rasa kanina Dan"uwana mafi Soyuwa gareni Na kasa Duka na kasa Wannan Dauriyan ina Neman wata Kafada inda Zan kwanta nayi kuka..Kuka na Dacin daya Kwanta acikin Zuciyata yana Sukani Tamkar Nima zai yi Sanadiyar Ajalina haka nake ji Rumana..Taba kirjina kinji yadda Zuciyata ke Bugawa da Sauri da Sauri ko..? To wlh Tana Bugawa da ambaton sunan Mansur na kasa yarda Mansur ya Tabi ya Barmu Ru...ma...na..!
Mastur ya karishe Fada muryansa ta karyewa Lokaci Daya kuma ya Damki Hannunta Guda Daya ya Damke Saman kirjinsa Tana jin irin Bugun Zuciyarsa Cikin Sauri da Sauri Bata ankara ba Taga Hawayensa Masu Zafi suna Zuba saman hannunta Cikin Razana take kallonsa ganinsa yana kuka karon Farko a Rayuwarta sai taji itama bata da karfin gwiwan Rike Rauninta bata san sanda ta Karisa garesa da Rarrafe ba sai ji Tayi ta Fada Jikinsa ta Rumgumesa kamkam Tana Fadin"Yi kuka..Ka Zubar da Hawaye ya Mastur..Kayi kuka a kafadana ni Rumana har sai kaji Zuciyarka Tayi Sanyi.."Take Fada Cikin kuka itama Da karfi ya Kamkameta kamar wani Zai kwaceta ya Saki kukan Dayake ta Rikewa Wajen kwana Goma Haka ya Dinga kuka yana kamkame da ita,itama kukan take tana Shafa Bayansa alamun Lallashi Tun Suna Zaune har dai basu san Lokacin da sukayi malale Saman Cafet din Bedroom din ba Mastur Tusa kansa yake saman Kirjin Rumana yana kuka kamar wani karamin yaro ita kuma Tana Shafa Sumar kansa Cikin Tsausayi da Soyayyah mai Tsanani.
Rumana bazata iya Fadin yaushe ne Da wani Lokacin ne Lamarin ya Fara ba..? Sai da ta Tsinci kanta Hannun Mastur Dumu Dumu yana Sarrafata Cikin Zafi Lokaci Daya kuma Idanuwansa na Zubar kwallah Tana cikin Dimuwa na karon na Farko Jin wannan bakon Lamarin ga kuma Jikinta da ba karfi ga Yanayin Mastur Daya kara Sakata ta Sakamar Duka Ragaman Rayuwarta ta Mika wuya ita dai baxata iya cewa komai ba Tadai jita Saman Kafadan Mastur ya Mikar da ita kafin taji ya Dagata sama Lokaci Daya kuma Taji su sun Fada Saman gado Abubuwan da suka Faru Dukkansu sun Faru ne yadda Basu yi Tsammani ba Mastur ya karbi Budurci Rumana Cikin Fitan Hayyaci da kuma Dacin Mutuwa da Nadaman hakkinta Dake kansa ita kuma Rumana bazata iya Dora komai sai dai Abu Daya ta sani Lamarin yazo mata A bazata Domin batayi Tsammani ba, bata Zata ba kuma bata ma kawo ma kanta nan kusa ba sai ta Sanya hakan a wani Lamari da Allah ya Kaddara Zasu zamonta Daya ita da Mastur koma yane Koma wani yanayi ne abun ya Faru ta Daukeshi ta kuma Rikeshi a ranta ta kuma sakashi Cikin Jerin Ranakinta masu matukar Muhimmanci a Rayuwarta.
Mastur kuwa wani irin yanayi yajisa acikinsa wanda bai taba Shiga ba iya Tsawon Rayuwarsa Daman Tuni Rauninsa ya Bayyana Shiyasa yayi ta kuka Tunda Farkon Dare har Zuwa asubahi yanayin da baki Baxai iya Fadansa ba sai dai Zuciya ta Kisima ko ta auna ko ta kwatantan Bayan komai ya Lafa Haka Mastur ya kamkame Rumana yana kuka,kukan Farinciki Rahma da Raunin Rashin Tade tare dashi ammh Hakan bai Hanasa Tashi ya Taimaka ma Rumana ta Tsabtace Jikinta ba Shima haka ya Sauya musu Zanin gado suka koma suka kwanta Duk da Zazzabin Dake jikinsa da asuba ma Dakyar ya iya tashi yayi Salla ya koma sai gashi Rumana ce ta Mike Tana Taimakamishi ta bashi mgani yasha ya koma ya kwanta Duk da Halin Datake Ciki haka ta Rarrafa ta sama musu abun karyawa Gabadaya Ranar daga ita Har Mastur wuni sukayi suna Jinyar Juna Shi Jinyar Zuciya da na Rauni Hade da na gangar Jiki,ita kuma Rumana Jinyar Jikinta wanda Mastur yayi Sanadiyar Faruwarsa
Daga chan gida ba wanda ya Nemesu sai washegari ne Baba Habibu ya kira Mastur din awaya Lokacin ne yace baya jin Dadi Nan Baba Habibu yamai Sannu yace Daman Zasu je gaisuwa Gidan Direban Marigayi Mansur ne Mastur yace su tafi kawai in yaji sauki zai je kafin ya Tafi da yardan Allah.
Haka kuwa akayi Cikin kwana uku yaji Sauki Tunda Rumana na kula dashi Itama taji Sauki Tunda Tana kula da kanta Bakin aiki ne bata koma ba Har yanzu ammh Takai Report.
Ranar sukaje gaisuwan Shida Rumana Daganan suka yada Zango wajen Diza Allah Sarki Ta na nan Jiya iyau Mommy Dai ke kula da ita da komai nata Diza bata mgana sai kuka kawai Abun Tsausayi,Mastur ne ya Zauna yana ta Lallashinta da Nasihu Duk da Shima yana Bukatar hakan sai dai gwara shi Rumana ta Zage dantse wajen ganin Mastur bai Raunana Da yawa ba Duk da Ramin Dayake Cikin Zuciyarsa mai Zurfi ne Lokaci Daya Rumana bazata Taba Cikeshi ba.
Mastur ya sauya kamar bashi ba Ya Roki Rumana gafaran Abubuwan suka Gudana Bayan auransu kuma ta yafemai,Sun Fara Shimfida Rayuwarsu cikin Kyautatama Juna,da kuma Kiyaye Hakkin Juna Duk Kokarin Rumana na Mastur ya samu karfin Gwiwa sai dai Abunda bata sani ba Tuni ya Sare kuma ya gama Raunana Tun Lokacin Daya Tabbatar da ya raasa Mansur..

Haka Rayuwa ta Cigaba da gangarawa har Tsawon Sati Biyu da Rasuwar Mansur,Duka makusantan sun fara Saduda sai dai banda Diza hankula suka Fara komawa kanta Domin ta Lalace ta Fita Hayyacinta bata cin Abinci bata mgana bata wanka sai Mommy Ta matsa mata Tun Abun ana ganin Radadin Mutuwar ne har dai aka Fahinci Diza na Bukatar Taimako Sosau Mastur Dayaji haka Shi ya Dauki Diza da kansa zuwa asibiti aka Dubata batare da tayi gaddama ba Domin shi batamai gaddama,ko Abinci ne taki karba Mommy na kiransa yazo Yana cewa ta karba Zata Fara ci,kuma bata iya Hada ido Dashi Shikuwa yanzu duk Duniya tafi kowa bashi Tsausayi.
Likita ya Dubata har awon Ciki anyi mata Cikinta watansa Biyar Zata Fara zuwa awo nan da Lokaci kadan,shawarwari ya bata Domin ya aunata jininta ya yi sama Sosai ta saka Damuwa ga Cikin jikinta ya bata Shawarwari sosai na cin Abinci domin karin Lafiya ga ita kanta sa Jaririnta.
An bata mgangunan karin jini Dana Sanya Cin Abinci kana suka Dawo Gida Mastur ya Zaunar da ita yayi mata Lallashi tare da Rokonta ta Rika cin Abinci ta kuma Rika shan mgani Ta Daina yawan Tunani da kuka ko Saboda Jaririn Cikinta Zata Rasshu In tacigaba da yin haka Tamkar yadda ta rasa Mastur Diza sai Kuka ba mgana Daman Gobe zai koma bakin aiki nan yayi musu Sallama bai kuma Tafi ba sai da ya Tabbatar da Diza bata raasa komai ba taci abinci Rumana ta Taimaka mata tayi wanka Tasha mgani Har Tayi barci.
Gida ya isa nan ma yayi ma su Hajja Sallama sai kukan Mutuwan Mansur ta Dawo Sabuwa Allahu akbar,Koda suka koma Gida Mastur ya kara Damka Amanar Diza a hannun Rumana ta kuma mai alkawarin Kulawa da Diza da Abunda ke Cikinta da yardan Allah sun kwana suna Raya wannan Daren mai Cike da Tarihi Washegari Tun Safe ya tafi kaduna ya Hau Jirgi Cikin Rauni da wani Sarewwa Itama Aranar ta koma Bakin aiki ko yaya akayi mata gaisuwan Mansur sai taji kwallah Ballatana Mastur da har yakai Headquater dinsu baya Cikin Natsuwarsa Tabbas ya Sare..Wannan karon Rauninsa ya Bayyana Rashin Mansur garesa Tabbatar Rashin wani Gibi ne garesa Babba.
Sai washegarin Daya koma ya kira Chan Maruka Domin jin Jikin Baba Sule Tunda suka koma yake kwance bayajin Dadi jinJikin Har yanzu yasa ya Tura kudi a acctount din maryama masu yawa yace su kai Baba Sule asibitin Sauran suyi Hidiman Gida Hakika Baba Sule yayi kukan Rashin Dansa Mansur sai dai ya Fada afidi Da"ansa Daya ya Rasa Ammh bai Rasa Dayan D"an nashi ba wato Mastur.




*Shakira...*
1/1/22, 18:55 - Maryam Badmsi: *SS....32*

*Kibiya ki karanta cikin Salama da Aminci 09069067488*


"Da wurin misalin 2:30pm na Rana Jirgi ya sauke Mastur a kaduna Daganan bai ma yi Tunanin kiran wani Sargent dinsu Daganan Reshensu na kaduna ba ya Fita ya samu mai Mota yace zaria zai kaishi Shi kadai Tasha,nan da nan kuwa ya samu ammh basu Fita Daga kaduna ba sai da sukayi Sallah Domin Direban ne yace zai yi sallah kafin su mika jin haka yasa Shima yayi Sallar azahar ya Hada da La"asar sanin da yayi kafin su isa Zaria La"asar ta gabato Saboda Zullumin Dayake Ciki baya ta Cikinsa ma.
Arude yake shiyasa bai ma Tuna daya kunna wayarsa balle ya Nemi wani Daga gida ba,Kuma Saboda Baya Cikin Natsuwarsa adaidai wajen Barrak na Jaji Hatsarin ya Faru kuma sunce Lokacin ko Kauda Motar Mansur din Datayi Dameji ba"ayi ba da Motar Bua din da sukayi karo sai dai Motoci sun Rika Zagayesu suna wucewa Allah ya gani yaga Motar ammh Sam Hankalinsa bai basa ya Tantance Motar ba Duk da ta Lalace ta Gabanta da Bayanta.

Sai 4:10pm Mai Motar Daya Dauka ya Shigo Layinsu na Hanwa Irin Tarin Motocin Da Mansur ya gani ne Tundaga Farkon Layin nasu abun ya kara Bashi Tsoro Allahu Akbar Mansur akwai Jama"a Shi din mai Masoya ne zuwa Lokacin Tuni Mutane sun cika anguwan Tasu Tunda Daga Taron da Za"a gudanar achan kaduna Taro ne na Charmo mi da kuma Yan Majalisun Jaha,wanda gwanna ne ya Shirya Taron da kansa To daga chan suka samu Labarin rasuwar Mansur Taron bai Samu ba Suka Tarkato zuwa nan Zaria Domin samun Jana"iza Gwamna bai zo ba ammh ya aiko Wakilinsa,Shiyasa wajen ya kara Cika da Motoci sai Taron matasa Wanda Daman Kowa ya sani Mansur na Jama"a ne.

Mastur ganin Cinkoson Ababan Hawa Data Mutane yasa ya Umarci Direban Daya sauke sa Daga Chan gefe,koda ya Fito Daga Motar kamar kafafunsa baza su iya Daukansa ba Haka yake ji Walet dinsa ya Ciro ya Mika ma Mai motar nan kudi wadanda bai san wayan adadinsu ba Hankalinsa yayi gaba Direban nata mgana ganim kudi wajen 10k ammh bai ma san yaanayi ba jefa kafarsa kawai yake yi Hannunsa Dauke da Walet dinsa da bai ma da karfin maida ita inda ta Fito ko wayoyinsa Dake jikinsa ji yake sun mai Nauyi Tuni Rauni ya gama Bayyanamai ya Fara Tunanin kodai Baba Habibu ne ya Rasu..?ko Hajja ce..?ko dai Aiya ce..? Sam Hasashensa da Tunaninsa bai taba kawo masa Dan"uwansa bane Ko acikin zuciyarsa bai Shirya Rabuwar tasu yanzu ba.
Ya fara Dumfaro Kofar gidan nasu da kafarsa Abunda ya Bashi mamaki ganin Mutane haka yana ganinsu ammh bazai iya ma gane suwaye ba Kuma sai Nunashi akeyi Cikin Tsauaayawa,bai nemi Tsayawa ba Burinsa yaji ya jingina da Abunda Zai Taresa Faduwa yadda yake jin Kafafunsa na rawa.

Bai kara jin wani Dum a tsakar kansa ba sai da ya kariso Kofar Gidan nasu yaga an Wangale get ga Mutane nan aciki da waje Cikin wani yanayi wasu kuma suna alwala Idanuwansa sun Hangi masa Baba Sule Dake kuka Hawayensa Bibbiyu bai gama Farfadowa ba kawai yaga Wani Kamar Baba Habibu da wani Wanda bai sani ba sun kamo makara Zasu Shiga gidansu Dashi Daidai Lokacin da Daddy ya Fito idanuwansa Jajir alamun yasha kuka yana Fadin"mu Hanzarta..Lokacin Janaza din Har cika..!

Kamar Daga sama sukaji Muryansu saman kansu Cikin wani irin Amo da Firgici yace"Dad...Ddy..Waye...ya rasu..?yana Rarrabe mganar kamar mai In"ina sai Alokacin ma aka Lura Dashi Gabadaya sai aka Zubamai Ido Baba sakin makaran yayi da Sauri Sagir Dake gefe ya karbeshi Suka Nufi Cikin Gida da ita Hankulan Mutane duk ya Dawo kan Mastur,Baba Habibu Da Daddy suka kalli Juna kafin su karisa ga Mastur din Dake Tsaye kikam kamar an Dasashi.
Dafa kafadarsa Daddy yayi yana Fadin"Alhamdulillah..Ashe ka samu Labari..?
Mastur Tsuri yayi ma Daddy da ido,,in ya kalleshi sai ya juya ya kalli Baba Habibu kamar bai Fahimcesu ba,Sai dai ya samu kansa da bakinsa da Fadin"Ba..ba.meya faru ne..? Bangane wannan Taron ba..? Naga makara ne an shiga da ita cikin gida waye ya rasu..!? Hajja ce ko Aiya.?
Kallon kallon aka Shiga yi Tsskanin Baba Habibu da Daddy,an rasa wanda zai Fara yima mastur mgana acikinsu Su azatonsu ya samu labarin Rasuwar ganin Mutuwar ta Zaga ko"ina Tunda dai basu same sa ta waya ba,
Bakinsu yayi nauyi matuka Kowa bashi da wannan Jarumtar ganin haka yasa Mastur ya karisa ga Baba Sule Dake tsaye kusa da yan"uwanshi yana ta Sharan kwallah,gabansa ya Tsaya Cikin wani yanayi yace"Baba sule wai koken koken me kuke yi.? Nace a Fadamin meyake Faruwa ne..? Waye ya rasu..?ko so akeyi sai Zullumi da Tashin Hankali ya saka Zuciyata bugawa ne..?

Ya karishe Fada Cikin Tsawa da Hargagin irin mutum baya cikin Hayyacinsa Da Sauri Baba Sule ya Dafa kafadarsa yana Fadin"Sai Hakuri Mansur Kai akayi ma Rashi bamu ba..Allah yayi ma Dan"uwanka Rasuwa..!
Alokacin Kwakwalwar Mastur ta Dole ne bai ma Fahimci wani abu ba,Kalmar Dan"uwan ne ma ya Bace mai sam acikin Kwalkwalwarsa,Ya kasa ma kama wani Dan"uwan nashi ake Nufi Saboda Tsabar Firgici ko Sunan Mansur bai kamo ba Cikin Rawan baki ya Furta"Wa...ni Dan"uwan nawa..?
Yafada gabadaya Idanuwansa suna Waje ganin haka yasa Baba Habibu yayi Saurin Rikosa Daddy ma ya Riko Gefen kafadarsa ganin Mutanesuna kallonsu basu Tsayar dashi ba sai da suka Shiga Haraban gidan kana Baba Habibu ya Dago yana kallon Cikin Idanuwansa yace"Mastur Kayi hakuri...Allah yayi ma Mansur Rasuwa Sakamakon Hadarin Mota..Sai dai muyi Fatan Allah ya jikansa da Rahma Allah ya sadashi da mala"ikun Rahma"
Daddy yana ta amsawa da Ameen Lokaci Daya yana Bubbuga kafadan Mastur din alamun Lallashi.

Mastur Dayaji kalaman Baba Habibu Tamkar saukan aradu acikin kansa Cikin wani irun yanayi yaji Zuciyarsa Tayi nauyi,Kafafunsa sun yi Wani rin Sanyi kamar wanda Harshashi ya Shigesa,Gangar Jikinsa kuma kamar ba Nashi ba Miyan bakinsa sun kafe,Idanuwansa suna Fari Fari saboda irin yanayin Daya shiga kamar wanda yake Cikin Coma kunnuwansa suna ijiyemai amsa kuwwa na Cewa Mansur yarasu Sakamakon Hadarin Mota.
Ganin yanayin Dayake Ciki ne yasa Baba Habibu riko Hannunsa yana Fadin"Mu je..Adauko Gawan Dan"uwanka Da Hannunka Mutane sun Hallara Jana"izan damam karfe 4:00 ne.."Shidai Mastur kamar baya jin ma mgana Saboda Kunnuwansa kamar sun Nane sama sama yake jin mgana Shidai Kamar wani Rakumi da akala,Sai tsintan kansa yayi Cikin Tsakiyar Falon Hajja yaga Mata Zazzaune suna kuka suna Kallonsa suna kara Karfin kukansu yadda Yake alokacin Baya ma Bambamce Fari da baki Kamar irin wanda ya Mutu kafin akai shi Kabari yana ji ammh bazai iya mgana ba Ballatana Tantance matan Dake Falon
Bai kara Jin kamar Yana Cikin wata irin Rayuwa ba sai da Baba Habibu ya sadasa da Uwar Dakin Hajja bai sakesa ba ssi Daya dangantasa da gaban Gawan Mansur da aka Riga aka Hadashi Cikin likafi kuma Har am Sanyashi Cikim makara an Rufeshi da Zanin Hajja,ga Jini Duk ya wanke likafin Saboda Fashewar kansa Jinin Har alokacin bai Tsaya ba.

Daddy ne ya Durkusan da Mastur gaban gawan Mansur yana Fadin"Kayi ma Dan"uwanka Addu'a kafin afita Dashi..Kayi Hakuri kada kayi mai kuka kaine Komai nashi Tun yana Duniya yau ma da zai yi bankwana Damu ka Zama komai nashi.."Yafada Lokaci Daya Shima Hawaye na kawo mai da Sauri ya juya ya Fita yana Sharan Kwallah Hakama Baba Habibu,Rumana Data ke kallon Mastur haka take Toshe Bakinta Saboda kuka Hajja ma kallonsa take ji Rauninta ya kara Bayyana Mommy da Umma suma sai Sharan kwallah Diza dai ido kawai ta sakamai Har yanzu din nan Kanzil Diza bata Bude baki tace ba Kuma Tunda ta Zauna awajen bata Motsa ba,har aka Fita da Mansur akayi mai wankan gawa wanda Baba Habibu ne da limamin masslacin anguwan sukamai wanka suka Shiryashi
Mastur Durkushe yake yana Bin gawan da akace ta Mansur ne da kallo Hawaye koDigo bai Sauko Daga Cikin kwarmin Idanuwansa sai dai Radadi da Zafin Dayake Fitomai Daga kasan Zuciyarsa sai ya Gummaci Dama Faduwa yayi a kasa yayi ta Birgima yana kuka kila zai samu wani Sauki.
Mansur fa..?Mansur dan"uwansa Dayafi Kowa Shakuwa Dashi Duk Duniya ,Mansur kaninsa wanda suka Taso Tare..? Mansur wanda ya kasance Farincikinsa madubinsa,Komai nashi Yau Shine ake so ace mai Cikin Likafini acikin makara Za"a kaishi Kabari..?
kai Innalillahi wa"inna Ilaihirraju"un sai alokacin Yaji acikin Zuciyarsa ya iya ambaton Haka Sai ya samu kansa da Sulalewa ya Zauna Dabas gaban gawan Hannuwansa na Rawa ya saka ya Jaye mayafin Fuskar Mansur mai Cike da Mirmishi a kullim ta Bayyana Cikin Likafi an Daddaueshi gam,Sai Mastur ya saki Zanin yanaji kamar wani Duhu zai mamaye Cikin Idanuwansa Lokaci Daya ya kurama Mansur ido Yana Turo Rayuwarsu Daki Daki Tun suna yara Har matakin Girmansu   baisan sadda ya Fada kan gawan fa yana so ya Fashe da kuka ne ammh kuma kukan yaki Zuwa sai dai Soya da Radadi Daga kasan Ransa kamkame gawan Mansur yayi yana ji kamar mafarki ne Mansur zai Tashi yace Dagani Ya Mastur Dagani da Rai na.
Gabadaya su Umma sai suka Fashe da kukan Tsausayin Mastur Rumana kuwa Kasa Zama Tayi sai ta mike ta Fice da Gudu Tana kuka Hajja ta Mike Cikin ganin Jiri ta isa kusa da Mastur ta Durkusa ta Dafashi Tana Fadin"Kada kayi mai kuka Mastur..Tashi ka Dago kanka kayi mai addu"a..Mansur ya Riga ya Tafi ya barmu..Ya tafi ya barmu Cikin Tsananin kewa Sai dai muyi Fatan Allah ya jikansa da Rahma.."Ta karishe Fada Tana Danne kukanta kafin ta Mike Tsaye Jiri ya kwasheta Tayi kamar Zata Fadi Umma ta Mike da Sauri Ta tarota ta Fado Jikinta suka Fashe da kuka da Sauri tajata suka Fita Falo suna kuka.
Jin kalamam Hajja yasa kamar Wani Allura tayi ma Mastur ya Dago kansa yana kallon Fuskar Mansur ya Dafashi yana Fadin"Allah ya jikan ka Kanina..Allah ya Rahamsheka..Allah yayi maka Rahma..Allah ya kyautata zuwanka..Allah ya sadaka da Mala"ikun Rahma Allah ya sa Kyakyawan Hallayanka su Bika..Allah Allah ina Rokonka Allah ya jikan Mansur Allah Allah ka Tsausayamai..Allah..Ya Allah.."Kawai yake Fada yana jin wani karyewan Zuciya Lokaci Daya Wasu Hawaye masu Dimi Suka Biyo Kuncinsa Baba Habibu da Daddy da Abba da Baba Sule Dake Tsaye Bayansa Tun Dazu suka rika amsawa da Ameen kafin Abba ya Duka ya Saka Zanin ya Rufe gawan Mansur Daddy kuma ya Saka Hannu ya Dago Mastur yana Fadin'"Ameen Mastur...Tashi..Tashi..Ka kama gawan Dan"uwanka mu Tafi mu Sallacesa Mu mikasa gidansa na Gaskiya.."Kamar Rakumi da alaqahaka ya Mike sai Alokacin ya ga Diza Zaune gaban gawan ta kura ma gawan ido Tana jam Carbi Bakinta na Motsi da karfi kamar wacce ta Tabu Tsuri yayi mata da ido yana kallonta suma su Abba ita suka maida Hankali suna kallo Baba Habibu ya Girgiza kai yana Fadin"Tun da aka Fadi Rasuwar take Cikin wannan Halin..Ina Rumana tazo ta kamata zuwa Falo tasha Iska.."Yafada yana lekawa Falon yace akira Rumana wacce ke chan Bakin kofa Durkushe Tana kuka Aisha Bala ce ta Rikota Zuwa Dakin Abba ne yace mata ta kama Diza,su Fita Falo Za'a Fitar da gawan Mansur Zuwa Waje Cikin kuka da Hawaye ta isa Gareta ta kamata Tana Fadin"Taso muje Falo Diza..Taso..'Kamar wata Yarinyar haka ta kalleta kafin ta juya ta kalli gawan Mamsur Cikin Wata Murya tace"In je inyi me a falon Ruma..?Ga Mijina kwance anan ai ba inda Zani..!
Tafada Tana kwace hannuwanta Da Sauri Rumana ta sake Rikota Tana Fadin"Eh na sani Falo Zamu je..Shima chan za "a Fito da shi yanzu nan..'Sai da tayi Kamar ba zata tashi ba kafin Rumana ta Kamata ta Mike Dakyar da Cikinta Daya Bayyana Mastur yana kallonta yana kallon Cikin Jikinta sai yaji kamar Ya Fadi a wajen ya Dinga Rusa kuka.
Dakyar Rumana ta Fita da Diza Falo Lokacin Tuni kowa ya mike jin Z"a Fita da gawa ne zuwa Waje Diza bata ankara ba Taga an Dauko Gawan Mansur za"a Fita Dashi Waje Mastur ne ke gaba yana Rikeda Makaran Saman kafadansa yana jinsa Tamkar Bashi ba yana ji kamar acikin Barci ne komai ke Faruwa.
Diza Data ga Fita Za"ayi dashi Ta Nemi bin bayansu Tana Fadin"Na Shiga uku ina zaku kaimin Mijina kuma.?
Tafada Cikin Rauni da wani Sarewa Rumanace ta Rikota Tana Fadin"Diza ki bari..Mansur ya Tafi ya barmu..ki bari aje sallacesa Zuwa gidansa na gaskiya.."Da wani karfi ta Fizge hannunta Tana Fadin"uban na barin ne..?nace na bari yaci kaxa kaxansa Rumana Mijina za"a Daukemin shi araba ni dashi kuma kice na bari..?kina Haukane ko Kin Fara Shaye Shaye ne..? Tafada tana kwalalo mata Ido Cikin Kuka ta Fizge kanta ta Rumtuma da gudu Tana Fadim"Mijina..Kuna gani..Zasu FitaDashi..Wayo Allah na Shiga uki wani ya Taimakamin mana"Take Fada Tana kuka Gabadaya Falom sai ya Gauraye da kuka masu addu"a nayi masu Surutai nayi Umma ce da Mommy suka Rike Diza tana kuka Tana Tirjiya Tana kiran Mijinta Itama Rumana Kamar ta Shide ganin an Fita Dashi Daga Falon gabadaya yasa Diza ta saki kara ta Zube kasa asume Alokacin itama Rumana ta Sume,Hajja ma Ta Sume,haka su Maryama dasu Mardiya suka Sume suma sai Waje ya Rude mata na Gujen Gujem Dauko Ruwa suna Sheka musu inda akaci Sa"a Duk wacce aka Sheka ma Ruwa sai ta Farfado Tana Gunjin kuka Diza sai da Mutane suka Rirriketa Tana ta kuka da Ihun abarta Tabi Mijinta Aiya kuwa Tama Rude ga Jikin Tsufa ga Mutuwa Mutuwa ma irin Mutuwar Mansur Dole ta Dimauce,Inna karime ne ke Riketa da ita itama kukan take sosai kamar Ranta Zai Fita.

A Kofar gidansu aka Sallaci gawan Mansur ko awajen Sallar Tsaye kawai Mastur yake ammh Baya Fahimtar komai har aka Idar aka Fara Shirin Tafiya Allahu Akbar Mansur ya Dace Allah ya bamu irin nashi Dan"adam din da suka Sallaceshi sunfi 400 ba adadi kuma Dasu aka Rankaya Rakasa Gidansa na Giskiya a Makabarta Dambo Mastur a Motar Daddy sukaje Dukkansu,kuma Dashi da Baba Habibu da Baba Sule da Daddy suka Saka Mansur Cikin Kabarinsa Suna ji suna gani suka saka kasa suka Binneshi ta ko"ina Baba Habibu sai alokacin Yaji yana ta kuka ba Tsayawa Harda Shessheka sai da Baba Sule ya Rikosa yana Bashi Baki Mastur kadai ya Rage gaban gawan Mansur ya Duke ya Dafa Kasam kabarin yana ta mai addu"an Saduwa da mala"ikun Rahma yana Zubar kwallah,kwallah mafi Zafi da Ciwo acikkn Rayuwarsa,Dakyar Su Baba Habibu suka iya Janyensa Daga Kabarin Bayan an saka Budo awajen anjera Domin Shaida gane kabarin koda watarana anxo Ziyarsa.
Har suka Dawo Gida Mastur bai ma kowa mgana ba Shidai gashi nan ne kawai abubuwan ne yake ganinsu kamar mafarki suna zuwa aka Firfto da Manyan Dardume da Tabarmu Daga waje kuma aka Saka kujeru da Tantuna Saboda Rana Mastur Suna Daga Cikin Haraban suna Zazzaune su da su Daddy dasu Abba dasu Baba Sule Daddy Shi ya sanya aka Sauke Motocin Ruwan Gora dana Lemuka abincin kuwa Oder ya bada Dago Restaurant Har na Tsawon kwama bakwai nan da nan akayi ta Shiga da komai Cikin Gida ana Raba mutane Daganan waje haka yan Siyasan su Mansur suma suna ta Sauke Lemuka da Ruwa da su Snacks haka ana Ta Rabama Mutane masu ci daai sun Faraci ammh wadanda Mutuwar ta Shafa ko kallon Lamarin ma basayi ba Mastur dai gashi nanne yana amsa gaisuwan mutane Daga saman Lebensa kawai ba Domin yana Cikin Hayyacinsa ba nan da baki sai zuwa suke gaisuwa mata da Maza sai ga Zuga guda Daga ma"ikatan Diza da kuma wadanda Rumana take aiki Dasu asibitin Chika da kuma abokan aikinta yan Intemship duk sunzo gaisuwa Dayake Aisha Duk ta Kirasu ta gayamusu Mansur Sulaiman Doguwa kanin Mijin Rumana muhammed wamako ne.
Koda suka shiga Cikin Falon Hajja Zukata sun gama Raunana Gabai sunyi Sanyi,Idanuwa sun gaji da Zubar kwallah sun komaa ma na Zucci Zuwa Lokacin Tuni Diza ta Daina kuka da Ihu sai Tayi Shuru kawai Duk wanda yayi mata gaisuwa ta amsa ta gama Shaida cewa Mansur ya Tafi ya Barta Tafiya ta Har Abada hakama Hajja Ta saka ma Ranta Rumana ma haka kannensa ma sai kukam Zucci kawai suma ga ababen sha da ci ammh ba wanda ya Kalleshi Sai Dai Dai,basu Tashi Daga wajen ba sai da sukaji kiran Sallah kana masu Kuxarin suka Mike Domin gabatar da Sallah Harda wadanda basu da Kuzarin sun mike Domin sun yarda kuma sun amince cewa Allah Daya Hallicesu Shi ya karbi Mansur suma din basu yi Tsaiko kuma basu jinkiri ba Ballatana gaggawa akowani Lokaci suma Zata iya Riskansu suna masu kai kukansu ga Allah da kuma Rokan ma Mansur Yafiya da Gafara wajen Allah.
Haka ta Faru su Mastur shima yayi addu"an neman gafara ga Mastur acikin Sujjadansa kamar Zai Cire bakinsa Tsoron Allah ya karama Kamashi yau ga watarana da Mansur zai yi kwanan kabari ba Diza ba Mastur a gefensa ba Hajja ba Baba Habibu Lalle Rayuwa Bawa ba abakin komai yake ba Allah ya Jadaddama Rahma gareka Mansur Allah ya jikan iyayanmu da suka Rigamu gidan gaskiya Allah yasa in tamu tazo mu cika da kyau da imani Ameen ya Allah.






*Shakira.*
1/1/22, 18:55 - Maryam Badmsi: *SS...34*

*Ki biya ki karanta cikin Salama da Aminci 09069067488 Mace mai aji mallakan komai nata take yi bata jiran abun sata*

"Zuwa Lokacin da Mansur yayi wata Biyu da Rasuwa Zukata ta Fara saki,raunin ya fara Barin gangar jikin sai dai bai bar Zuciya ba,har kuma alokacin Mutanen arziku da basu samu zuwa gaisuwa ba Suna ta zuwa musu gaisuwa sosai.
Ita Duniya Daman da Zarar ka Tafi Shikenan za"a manta Dakai Lokacin dake Raye ne kake da Amfani,hakan ce ta Faru Domin Daman ance ita Siyasa Tankar Riga ce yau tana wuyan wane gobe ma Tana wuyan wane hakan ce ta Faru Domin kujeran Mansur Tuni har anyi Nada wani zuwa Lokacin da Tenua su zai Cika asake Sabon Zabe..Allah Sarki Daman Haka Rayuwa ta gada sai dai mu yi Fatan Allah yayi mana kyakyawan karshe.

Zuwa Lokacin kuma an Tattara Duka Abunda Mansur ya Mutu ya bari Gidaje,Motoci da Tsabar kudi za"a jira Har Diza ta sauka Lafiya kafin araba komai,Bangaran Iyayen Mansur kuwa Mastur ya Debe musu wannan Raunin Duk Sati Biyu Zai Tura ma Maryama kudi,saboda Hidimansu Da kuma Hidiman Baba Sule na asibitin Tunda Tun bayan Rasuwar mansur din Jikin nashi yaki Dadi hawqn Jini Yakwanta asibiti yaji Sauki aka Sallameshi ammh yana Zuwa ganin Likita Lokaci Bayan Lokaci Baba Sule yana Da Raunin Rashin Dansa Mansur ammh Mastur ya Cike Gibi mai yawa na Rauninsa,Kullum sai ya kirashi sun gaisa yakuma Ji yaya Lafiyar Jikinsa Gabadaya Dangin Mansur Suna Fadin ya Tafi ammh kuma bai Tafi ba Domin Mastur bai barsu sunyi Rashin komai ba sai dai ita Mutuwa Dayace kuma Yaya Ta Shafeka bazaka taba mantawa da ita ba.
Duk da shi kanshi Maatur din Lallashin yake Bukata yana Bukatar Hutu da kuma Karfin Zuciya bai Samu ba kuma bai Damu da kansa ba Ballatana Lafiyansa Damuwansa Tana ga Raunin Rashin Dan"uwansa Diza itace Damuwarsa ta Farko sai su Hajja sai Dangin Mansur,A koda da yaushe Cikin kiran su Hajja yake yana kara kwantar musu Da Hankali Sai kace nashi Hankalin yana kwance ne,Baya Taba Nuna Rauninsa a kan idonsa Sai dai in ya kasance shi kadai yayi ta kuka kamar Ransa zai Fita.

A koda yaushe Cikin kiran Mommy ke Ko Rumana yana Tambayansu Lafiyan Diza Rumana saboda Mastur yasa Kullun ta Dawo aiki wajen Diza take Zama sai Dare ta koma Gida wani lokacin ma nan take kwana Weekend ma Haka nan take shan Wuninta wani Lokacinma anan tske musu Weekend duk Domin Diza ta saki Jikinta sai dai kuma Ta nan Yarda take bata mgana sai Dai tayi shuru chan kuma sai Hawaye sai kuma karatun Qur"ani ko wajen aikinta bata kara mganarsa bama,Sai dai Dayake Merry da Hauwa yan Amana ne suna kula da komai kuma sukan zo su Dubata Lokaci bayan Lokaci su mata Bayani bata cewa komai sai dai ta Dora Meena Kawarta kan ta rika kula da komai yanzu takan ci Abinci saboda Lafiyan Jaririnta Rumana ta kaita asibiti ta Fara zuwa awo anan asibitin Abu na Tudun wada Ranar da zasu Fara zuwa Diza ki tayi ta Fara kuka sai da Rumana ta Kira Mastur ta Fadamai aka ba Diza wayar ya mata Mgana kana ta yarda sukaje ko achan asibiti achan ma Haka Likita ya Dinga Fadan Rashin cin Abincu da kuma Damuwa Tunda Jininta yana ta Sama Rumance tayi mai Bayani Rasuwar Mijin Dizan ammh Duk da Haka yace a kiyaye saboda Lafiyan Abunda ke Cikinta

Da suna Hanya Zasu koma Gida Rumana ke Driving din Motar ta Juyo tana kallon Diza da ta kura ma Window ido kawai Tana kallon Wucewar Motoci,Kai ta Girgiza Tana fadin"Don Allah Diza ki Rage wannan Tunanin..Kinji dai abunda Likita yace..In kina son wani abu ya Samu Cikin jikin ki Shikenan..!
Har ta Fidda rai da Diza Zata Tankata sai taji Muryanta Cikin Sanyi da Rauni Tana Fadin"Ruma Mijina fa na rasa..Mijina Mansur ne ya Tafi ya barni Daidai Lokacin da nafi Bukatarsa alokaci  Daya kamata mu zauna Dani,Dashi mu reni cikin nan Har Zuwa Ranar da zai zo Duniya..Munyi ma juna alkwarin Zamu Reni Abunda muka Haifa Dani Dashi muji dashi muyi mai gata da Tarbiya atare..Sai Lokaci Daya Mansur ya Tafi ya barni Alhalin ko Cikin ma bai Fito Duniya ba Taya ya kike Zato ko Tsammanin Zan iya kwantar da Hankalina Ruma..? Mijina fa na rasa Uban Cikin Jikina kice bazan yi Tunani ba to in ban yi Damuwa So kike nayi ta Farincikin Tunda na zama karamar bazawara wacce Mijinta ya rasu..ki Dubeni Ruma Takaba nake yi ina Cikin Takaban Mijina ne Ya kike so nayi ehe..Ki Fadamin..!
Ta karishe Fada Cikin gunjin kuka kamar wata karamar yarinya Gabadaya Jikin Ruma ya kara sanyi Cikin Alamun Lallashi Tace"Hakane Diza..Ammh Hakuri zakiyi..Allah daya baki Mansur Shi ya Dauke abunsa in kina haka Tamkar kina ja da Hukuncin Allah ne..Kuma hakan da kike yi bzai taba saka Mansur ya Dawo wannan Duniyan ba ya tafi kenan Har Abada..!
Diza na Sharan kwallah Tace"Na sani ya tafi bazai bata Dawowa ba..Ammh ni kuma ku barni naji Radadin mana .Ku kyaleni Naji wannan Radadin..Radadin danake da Tabbacin Har na koma ga Allah bazai gushe Daga Raina ba..Saboda ku daina Damuna da Zencen Damuwata ku barni Ni kadai nasan yaya Dacin Rashin Masoyi kuma Miji irin Mansur yake komai Zan Fada miki Ruma bazaki Taba ganewa ba sai wanda Abun ya Faru dashi.."Ita dai Rumana bata kara mgana ba Har suka koma Gida Ranar kuwa Mutuwar ta koma ma Diza sabuwa,tayi kuka sosai Har sai da ya saka mata Zazzabi Diza kadai Abar kayi mata kuka ne Tayarda Mansur ya Tafi ya barta ammh bata yarda tayi yaki da Raunin Dayake Cikin Zuciyarta ba.

Bangaran Mastur kuwa ya Dauki Aniyar gyara Zamantakewarsa da Rumana kuma ya gyara sai a yanzu yake kara Fahimtar Rumana sosai kuma yasa ta Cikin mata nagari Abun alfaharin Wanda ya samesu Abunda ke Burgesa da ita Hakurinta da kawaicinta Hade da Sanyin Halinta gata da Ladabi da Biyayyah bata Taba Tsallake Umarninsa ba,komai yace Tayi ko Bata so ba sai dai ta Bishi da To kawai Gata da kokarin kwantar mai Da Hankali da kalamai Sanyaya Duk Domin taga ya Saki ya Daina Damuwa koda bai Rage Damuwarsa ba ammh Rumana ta samu Wajen Zama sosai aransa Ko bai kirata ba Zata kirasa,wani Lokacin in Damuwa tayi mai yawa ita yake kira Tayi ta bashi Labarin wajen aikinta makaranta da Sauransu duk Domin taga ya saki Jikinsa Abunda bata sani ba Ramin Zuciyar Mastur babumai iya Cikesa nan kusa,aammh ko bakomai Yana godema Rumana da kular Datake Nuna mai Ta kirashi Sau nawa arana saboda Taji yaci Abinci ya kwanta yayi Salla..?me yake yi..? Duk Domin Taji Lafiyarsa kuma Hakan nayi mai Dadi har ya sama mata wani Matsayi acikin Ransa bata sani ba.

*******

Yau tunda ya tashi yake ji kansa yayi masa Nauyi fiye da kowacce Rana Ga kirjinsa na Ciwo ga Jiri wanda yake Fama Dashi Tun Bayan Dawowarsa ammh bai maida kai kan Lamarin ba ahakan ya Shirya ya Fita Zuwa Office saboda zasu Shiga Meeting baya so ya kwanta agida kada Cutar Dayake jin ta kamasa ta Samu Rauninsa ta kwantar Dashi Gabadayansa.

Mastur Dayasan Haka zata Faru Dashi da bai Je wannan Taron ba Domin ya Shiga Dakin Tattaunawar bai ma kai ga  Zama ba Jiri da Duhu suka Mamayeshi ya Zube kasa bai san inda kansa yake ba Cikin Gaggawa suka Daukeshi Zuwa Wani Babban asibitin kudi na garin Porthercourt abunka da masu Mikami Cikin Lokaci aka karbeshu aka Shiga Dashi Domin bashi Taimakon Gaggawa.
Dakyar Likitoci suka iya Samo Numfsshin Mastur shi din ma sai da suka sanya mai Oxygen Abun Taimakom Jawo Numfashi kana suka samu kansa,Dakin Hutu aka kaisa Daki na Mussmman,Domin ya Huta Duk da har zuwa Lokacin Bai Farfado ba.
Likita ne yace yana Bukatar ganin wani Ahalin Yallabai din Saboda mganace mai Muhimmanci zai Sanar dasu game da Ciwon Ogan nasu Tunda su Sargent Inuwa ne suka Daukosa Zuwa asibitin.
Jin haka yasa Sargent Inuwa yayi amfani da Daya wayar Mastur Dake Hannunsa tun Bayan Faruwan lamari ya kira Layin Daddy ya sanar Dashi Halin da ake Ciki alokacin Daddy baya Gari yana Abuja Harkan Kasuwanci takaisa Hankali Tashe ya kamo Hanya Bai ma gama Abunda ya kaisa ba Tun a Hanya ya Kira Baba Habibu ya sanar mai da Halin da ake Ciki Zukata sun Raunana jin wannan Labarin Musamman ma Da Daddy ya Dawo da Baba Habibu mganar takai kunnin mata,sai Suka fi Rudewa da Tashin Hankali Musamman Rumana Da tayi ta kuka Ganin Haka yasa Daddy ya yanke Shawaran Washegari Zasu Bi Jirgi zuwa Porthercourt din Shi da Baba Habibu Rumana na jinhaka tace zata je Daddy bai hanata ba Ko bakomai Mijinta ne Tabbasa yana Bukatarta.
Washegari kuwa haka akayi kaduna Direban Daddy ya kai su suka Hau Jirgi zuwa Porthercourt,karfe wajen 3pm na Rana suka sauka agarin Daganan Tashar Mota sukayi har zuwa asibitin Tunda Daddy ya kira Sargent Inuwa ya Turomai adireshin Asibitin.
Asibitin Babba ne wanda ake ji Dashi agarin suna zuwa Suna Fadin sunan Mastur aka fara musu masauki Office din Babban Likitan Daya ke Duba Mastur din Suna Zuwa Daddy yamai Bayanin sune iyayan Mastur yanzu suka Sauka agarin.
Likitan ya kalli Rumana yana Tambayan itafa..? Daddy yace Matar Mastur ne,kai ya kada kafin ya Dauko File din Mastur din yadan Duba kadan kana ya Dago ya Fara yi ma su Daddy Abunda ke Damun Mastur.
Sun Razana sun kuma Tsorata da Jin Mastur ya kamu da Ciwon Zuciya wanda Har ta Fara kumbura kadan Saboda yawan Tunani da kuma Damuwar Daya ke Ciki Kana yana da Hawan jini wanda shi ya Haddasamai ganin Jiri da Faduwar da yayi Allah ne ma ya Taimakeshi Bai yi Shanyewar Barin Jiki ba anyi Saurin kawosa asibiti sun bashi Taimakon gaggwa ya gaya musu Har yanzu bai Farfado ba,Domin Abun Zukan Numfsshi ke Taimakamai Domin sanda aka kawosa Numfashi yayi Nisa sai da Dakyar suka Samosa.
Tashin Hankali wanda ba"a saka musu Rana Duk Dauriyan Baba Habibu sai da yayi ma Mastur kwallah da suka Shiga inda yake yana kwance Sambal kan gado Hancinsa da Oxygen Ta nan yake Fitar da Nunfashi Duk ya Rame ya Lalace kamar ba Mastur ba, Dukkansu sun Danganta Ciwom Mastur da Rashin Dan"uwansa Mansur basu San Daman Mutuwar ta Iske Raunin Rashin Diza ba Daman rashinta ta gina Katon Ramin Sai Raunin Rashin Mansur yazo ya kara yi ma Ramin Zurfi.
Rumana ma Sai kuka ganin Halin da Mastur yake,har sargent Inuwa yazo ya Daukesu zuwa Gidan Mastur na cikin Headquatersu bai Farka ba Domin asibitin ba"a kwana suna da Masu kula da Majinyata.
Rumana yau ce Rana ta Farko Datazo wajen aikin Mijinta Daddy da Habibu sun Taba Zuwa Sau Daya Marigayi Mansur ne yasha Zuwa sosai har kwanaki ma yanayi wajen yayan nashi.
Rumana ainihin Bedroom Din Mastur ta sauka Ciki su Daddy kuma suka Sauka na kusa Dashi Sai Bayan sun Rama Salolinsu ne Sargent Inuwa ya kawo musu Takeway din Abinci basu wani ci da yawa ba,sai dai sun kira Chan Zaria suka kwantar musu da Hankali Sanin suna chan Cikin Damuwa Rumana kuwa Abun mamaki Har Diza sai da ta kira ta Tana Tambayanta ya Jikin Mastur..? Tace da sauki yana asibiti sai gobe zasu koma,Umma ma ta kirata da Abba Ashe Daddy ya kira Abba ya gayamai Sun ce in Jikin yayi Tsanani zasu Taho Rumana tace suyi Zamansu da Sauki.
Haka suka kwana Cikin Zullumi Tun Safe suka Shirya Sargent Inuwa ya maidasu asibitin Alhamdulillah sun iske Mastur ya Farka Har an Ciremai kakakin Numfashi kamar Daga Sama yaga su Daddy Domin Cikin Dare ya Farka Ba wanda yayi mai wani Bayani.
Abakin Daddy yaji Labarin Kiran da Sargent Inuwa yayi mai na Likita nason ganin wani nashi Tunda yaji haka yasha Jinin Jikinsa sai dai ya barsa Rumana kuwa sai kafa kafa Take dashi Yana Binta da kallo ko bai Fada ba yaji Dadin zuwanta ko bakomai Zata Debemai kewa na wani Lokaci.

Ranar nan suka wuni Cikin asibitin sai dare suka koma Gidan Mastur,Washegari ganin Jikin nashi da Sauki Daddy yace Zasu koma Shida Baba Habibu Mastur da kansa ya Roka kan su bar masa Rumana ta kwana Biyu Daddy yace Daman ba da ita Zasu Wuce ba kafin su Tafi sai da suka Tasaahi da Nasihu da Shawarwari Sai alokacin yake jin Sabon Ciwon Daya kamu Dashi na Ciwon Zuciya ya Illahi,sun Hankalarta dashi Mutuwa Dole ce Saboda haka yayi Hakuri yayi musu alkawarin Insha Allahu zai kula da kansa Kafin su wuce sai da suka kira chan Zaria duka Matan sukayi mgana Dashi suka mai Sannu da Jiki sai Lokacin Hankula suka kwanta Abba ma da Umma suna kira ko yauahe Domin jin Jikinsa Haka Mutanen Maruka ma sun kira jinsa Shuru Rumana ta amsa wayar ta Fada musu Halin da ake Ciki,Dayake Sargent Inuwa ya bata Duka Wayoyinsa,Suma Hankalinsu Duk ya Tashi Barin ma Baba Sule,Sai da sukayi mgana da Mastur din ya Tabbatar musu Dayaji Sauki kana Suka Kwantar da Hankali Aranar su Daddy suka Juya suka bar Rumana wajen Mastur Zatayi Sati Daya in ya karajin Sauki An Sallameshi Sai ta Dawo.
Duk da ba"a barin majinyaci ya kwana sai Rumana takai Dare Sargent Inuwa ke maidata Gida ita da kanta Tayi ma Mastur mgana Tana so tarika yimai Girki da kanta ba sai an siya ba,ta Duba Kitchen din ba Cefene jin haka yasa yayi ma Sargent Inuwa mgana Shi yayi mata Cefanan komai da komai,Arana ta Hudu Tayi ma Mastur Ferfesun Kayan Ciki da Dankalin Turawa Sai Lomon kankana wanda kuma yaji Dadin Lemon Har yana Ce mata Gobe ma irinsa Zatayi masa Ferfesun kuma yaci Sosai Kadan ya Rage,Rumana tayi Wahala da Mastur ita ke Taimakamai yayi wanka Ya gyara Jikinsa Abincinsa Shansa da Taimaka mai yayi alwala ya gabatar da Sallolinsa, da komai ita ke kula Dashi Sai alokacin Ma"aikatan Da suke aiki Tare dashi suka Taba ganin Matarsa nan take Wuni asibitin Tare dashi sai Dare Kana Sargent Inuwa ke maidata gida Mastur yana ta Tambayanta ko Zata iya kwana agida ita kadai..? Tace Zatayi ai akwai Mutane a Kusa da ita apartment din dayake kusa da Na Mastur akwai Mutane.
Gani yake kamar bazata iya ba,Shiyaaa Data koma Gida Zai kirata suyi waya Tayi ta Jansa da Hira Dayake Rumana Allah yayi mata baiwar Iya sarrafa kalamai,Shiyasa Suyi ta mgana da Mastur bai gaji ba sai tace yaje ya kwanta kana zasu Rabu.
Da safe kuma kafin ta Fito ssi tayi mai Abinci,mai rai da lafiya da Lemukan da zasu rika Taimakamai wajen Dawomai da Jikinsa da Kuzarinsa kuma yana jin Dadin haka Zaman Rumana Tare Dashi Tamkar wani garkuwa ne gareshi koda yaushe suna waya da Chan Zaria suna jin Lafiyarsu hankula sun kwanta Jin Mastur din yaji Sauki sai Abunda ba"a rasa ba.
Satin Mastur Daya asibiti kana Likita ya yarda ya Sallameshi Inda ta Mastur ne Ranar Dayake da Kwana Biyar yaso a Sallameshi Likitan yaki,Kafin su Tafi ssi da ya gayama Rumana ta kula da Mastur adaina Barinsa Cikin Damuwa ko Tunani Duk wani Abunda Zai batamai rai agujesa A kuma rika yin Duk Abunda zai sakashi Farinciki ya Daina Zama shi kadai Balkatana yayi Tunani ya Zama koda yaushe wani na kusa Dashi Domin gujema Damuwa,Daga karshe ya Rubuta mgunguna Wanda asibitin ta basu kafin su Tafi Duka Bill din Asibitin Headquater dinsu keda Alhakin Biyan komai ko nace Nigerian police din Gabadaya.
Sargent Inuwa ya kwashe su Zuwa Gida,shi da Rumana Wanda Taso tatafi aranar ammh ganin ba"a sallamesa ba sai Ranar yasa ta Fasa zata kwana Kwana Uku Saboda Asibiti Daman Aisha Bala ke mata Ranar Data ke da Duty,kuma yanzu Ranakun aikinsu sun Daina Fadowa Rana Daya kamar baya.
Rumana tabi Shawaran Likita Sosai kuma Tana Kokari kan Mastur Ranar Tare suka kwana Rumgume da juna Washegari Rumana Tatashi da gyaran Duka Dakunan Har tana ma Mastur Tsiya gidansa dai baya ganin Shara yana Zaune afalo Sanye da Jallabiya baka Saman Cafet ya gama Shan tea kenan da Dankali Rumana ta Bashi mgangunansa sai ta Mike ta Fara Sharan Sharan Tace Zata fara da Dakinsa in ta gama Sai ya koma Chan tazo ta gyara Falo da Sauran Dakunan zuwa Kicthen.
Mirmishi kadai yake yi acikin Ransa kuwa yana Fadin Tabbas Mganar Hausawa ne gida sai Mace in bata Ciki kuma ba Gida bane Kango ne Zuwan Rumana Gidan ya Sauya kamshi na Tashi na Dakuna dana Girki,abaya kuwa Shi bai ma san wani Turara  Daki ba sai dai na kaya dana Jiki Girki kuwa baiyi Sai dai ya Siya in yayi wuta ne ya Dafa Ruwan Tea ammh Zuwanta Har Kitchen din yasan da Mace tazogidan.

Tashige Dakin Tana gyarawa Ta gyara ko"ina,Har Cikin Wardrope dinsa ta gyara mai kayansa Tana Cikin gyarawan ne saboda Ta Lura in zai saka kayan Duk sai ya Barbaaza goggun Dake wajen ta Gyara wajen ta Sagale na Hanger Sauran su gajerun wandona da Vest ta kwashe takai Tiolet ta Jika Cikin Botiki da Niyar in Tagama Shara Ta wanke
Tana kokarin Rufe Wardrope din Wani littafi ya Fadi a kan kafarta ta Duka ta Dauka Tana Dubawa kamar Zata mayar mai ta Rufe wajen sai taji kamar Zuciyarta Tana Rinjayanta Data karanta sai ta samu kanta da Bude Littafin abun mamaki Rubutun Mastur Tagani acikin Littafin yayi Rubutu da Harshen Hausa da kuma Turanci wanda yaja Ra"ayinta ta Fara karantawa.
Rumana data san me ke Cikin wannan Diary da bata karanta ba Tun Tana Tsaye har takai ga Zama Hawaye ya gama wanke mata Fuska,rubutun ya kare ne Daga Lokacin da akayi Bikinsu aka gama sai yayi wani Rubutu Daga karshe da Cewa.

_Soyayyaata ba Rayayiya bace..Allah ya kaddara cewa Daman chan matattaciyace..Diza ta Haramta gareni Har Abada Tunda Ta zama Halastattaciya wajen Kanina..Nayi Sadaukarwan Abun mafi Daraja a Rayuwata sai dai Hakan yafi yemin da in bude ido naga Dan"uwana Mansur Cikin Wani Hali Alhamdulillah nagode ma Allah da Tarin Ni"imarsa sai dai Soyayyar Diza bani na saka ma kaina ba Har gaban Abada bana ji Zan daina sonta.Sai dai zan Rumgumi Abunda Allah ya Zabamin Wato Rumana itama Din Mace ce mafi soyuwa azukatan wanda ya Zauna da ita Allah ka bani Ikon yi mata adalci.._

Wannan Shine karshen Rubutun Gabadaya sai ga Rumana ta Kwanta a kasa tana kuka,Kukan Tsausayi,Nadama da kuma Wani Rauni Dayake ta Fitowa Daga kasan Ranta Dama Ashe Mastur Diza yake so ba ita ba? Daman ashe Sadaukarwa yayi da abunda yake so ga Dan"uwansa Marigayi Mansur..? Daman Dalilin Ciwon Zuciyarsa kenan..? lalle ta yarda ma kanta komai Allah yake Tsarashi Daki Daki Ta Tabbata Rabo ne yasa Diza ta auri Mansur Rabon Cikin Jikinta,Kuma kila Diza Zata Dauwama karkashin Mastur ne yasa Allah ya Dauki Ran Mansur Allahu akbar Allah mai girma ne.
Ashe Mastur ba ita yake so ba..? Allah sarki ta Shigo Rayuwarsa Cikin Halin Dayake Ciki Ita kuwa wani irin Zuciya Mastur yake da ita..? Tabbas Shi din na Dabam ne.
Tana cikin kuka da wannan Zencen ne taji muryansa yana Kiranta da Sauri ta Tashi ta Maidamai mai Diary dinsa inda ya Fado ta Fada Tiolet ta wanke Fuskarta kana ta Fito,yana ganin ta Sai dai yaji Jikinsa yayi wani iri,Saboda ganin kamar Tayi kuka Daya Tambayeta tace Kura ne ya Shiga idonta.
Sauri tayi ta koma ta gama gyaran Dakin ta wanke Bayin Ta Hada da Boxers din ta wanke ta Shanya anan Tiolet din Kana ta Fito tace ma Mastur ya koma Ciki ta karisa gyaran Gidan Bayan ya koma Haka ta Zage tana gyaran Tana kuka Tana Sharan kwallah ita kadai ta yanke wani Shawara acikin Zuciyarta Ta yarda ta Amince Zatayi Sadaukarwar so Domin ta Tsamo Wanda Take so daga Halin Dayake ciki da yardan Allah..!













*Shakira..*
1/1/22, 18:55 - Maryam Badmsi: *SS....35*

*Kibiya ki karanta cikin Aminci da Salama 09069067488*

"Kwata kwata bata bari ya Fahimci ta karantamai Diary ba,Bayan ta gama gyaran Gidan Ta koma Kitchen ta gyara ta Dora Girki,Shi kuma Mastur ya Dawo Falo Saboda yan Sanda wadanda ke kasansa dama wadanda ke samansa suna ta Shigowa Dubasa ,kuma In sukazo yakan Kira Rumana tazo ya Nuna ta matsayin Matarsa Abun yayi ma Rumana Dadi yau ko da bai aureta Don yana Sonta ba akallah ya Darajata Sosai fiye da kima.

Har ta kara kwana uku Tana kula Dashi bata bari ya Fahimci komai ba,Ranar da Zata tafi da kansa ya kaita Filin Jirgi Tunda yaji Sauki Sosai,Rumana ta kula dashi Tun Ballatana Bangaran Abinci Shiyasa Cikin Lokaci Ya Dawo Daidai.
Sallaman Masoya sallama ne mai Cike da kewa Mastur Bai so Rumana ta koma ba ammh bashi da yarda Zai yi Saboda aikinta Yana Filin Jirgin har sai da Jirgin su Rumana ya tashi kana ya koma Gida Daman already ya kira Headquater dinsu na Kaduna da Ta isa za"a je a Dauketa akaita Zaria hakan kuwa akayi Tana Sauka ta Kira Mastur ta gayamai Shi kuma yayi waya ba Dadewa wani Sargent yazo da Mota ya Dauketa Bai direta ko"ina ba sai Kofar gidan su Hajja sukayi sallama ya juya Tana Shiga da Hajja ta Fara cin kari Saboda Murna sai da ta Rikota Tana mata Maraba.
Ita da Mardiya Ayya ma sai da ta Fiti suna ta Tambayan Jikin Mastur ta Tabbatar musu daya warke Ta na nan har Dare wajen Diza ta Shiga ta Dubata Ta isketa Zaune tana karatun Qur"ani Cikinta ya Turo gaban nan ta Zauna suna ta Hira da Mommy kan dai yanayin Ciwon Mastur ne, Sai da Baba Habibu ya Dawo Daga kasuwa ta koma suka Gaisa Ta Jaddamai Mastur yaji Sauki Kana ta Hau Kekenapep Zuwa Gida.
Haka Rayuwar ta cigaba da gangarawa Da Dadi ba Dadi,Agefe Daya komai yana Tafiya yadda Allah ya Tsara Bangaran Mastur yana zuwa Gida Duk bayan Sati Biyar,Saboda Nauyin Daya hau kansa yanzu in abaya Mansur yana Raye Yau an wayi gari babu Shi Dole ne yanzu
 ya Dinga kula da Ahalinsa Tunda Babu Mansur.
Uwa uba ga Diza kuma Daya kasance yana Kula da ita Sosai ita da Abunda ke Cikinta,Balle Mutanen maruka sai Godiya Tsakaninsu da Mastur Mardiya kuwa Har tayi Jarabawa Mastur ya Dauki Nauyinta ta Fara Zuwa Poli Dake nan Zaria.
Diza kuma Tana Cigaba da Zuwa awon Cikin Jikinta gefe Daya kuma Rumana na kula da ita Domin ita take Kaita awon Ta jira agama ta Daukota ta maidata Gida Koda Tana da aiki a asibiti sai Bayan ta kaita ta Dawo Kana Take Tafiya.
Zukata sun Fara Saduda da Rashin Mansur sai dai basu Taba mantawa Dashi ba Koda yaushe suna mai addu"an Gafara da Rahma Wajen Allah sai kuma Hankalun Mutane ya koma kan Diza da Abunda ke Cikinta ko bakomai Shine zasu Rika kallah su Tuna da Marigayi Mansur.
Rumana Tana iya bakin Kokarinta Shiyasa kowa ke Yabonta Hatta Shi Mastur din bazai Taba Juyama Alherinta Baya ba Shiyasa koda wasa bai Taba Nuna mata Saboda Diza yake Zuwa Zaria akai akai ba Kwata kwata Bashi da Natsuwa da Zarar ya koma Porthercourt Tunanin Halin da Diza ke Ciki da Abunda ke Cikinta,ko Daman chan Diza ce Rabin Ransa yazo kuma ga Rashin Mansur ga kuma Ciki sai abubuwan suka karu ba wanda yake ganin Kulawar da Yake bama Diza a matsayin wani abu Ana Duba Yadda suke da Mansur da kuma Cikin Datake Dauke Dashi Rumana ce kadai ta Sani Shima Batare Daya san Ta sani ba.
Wani Lokacin Kishi na Kamata ammh Sai ta Kori Shedan Saboda acikin Zuciyarta Bata son ta saka maRanta wani abu kan Diza Saboda Tana da wani Kuduri acikin Ranta Datake Fatan yuyuwarsa ko Tabbatuwarsa in ko Har Tana son Hakan ya Tabbata sai ta Cire komai acikin Ranta.

Shiyasa Wani Lokacin sai ta Rika Nuna kamar batasan komai ba komai ya kirata ya Umarceta Batamai gaddama,Ballatana Musu Shiyasa Lokaci kadan Rumana ta Shiga Ran Mastur ta samu wani Matsayi Wanda Har yake jin da bai karbi Auranta ba Dayayi Babbar asara ba shi kadai ba Kowa yabonta yake Ko Diza acikin Ranta Tana Girmama alherin Rumana.

*****

*After 3 Month*

Bayan watannin Uku,Tuni Cikin Diza yashiga watansa na Takwas ya Girma Sosai har yana Rinjayanta Duk ta Rame Kafafuntaa sun kumbura da Fuskarta ta Sauya kamar ba Diza,Sai dai an samu Sauki Zuwansu awo na Baya Jininta ya Sauka sosai Kowa yaji Dadi da Rumana tazo Tana Fada Zuwa Lokacin kowa Jiran Haihuwan Diza yake ita kuma Rumana Tana gabda Gama Intenship dinta Saura Service.
Mardiya kuma Tana Cigaba da Zuwa makarantar ta Su Sakina suna zuwa Lokaci Bayan Lokaci Duba Diza Har Baba Sule da Inna Zainaba sun zo sau Wajen uku Duba ita Dizan Allah Sarki Har sai da Daddy yace suyi Zamansu Diza Tana nan Lafiya suyi mata Fatan Allah ya Sauketa Lafiya.
Mastur Yana Kirge da wattanin Cikin Diza kilama ya Fita liasafi Tunda yaga Cikin ya Shiga watan Haihuwansa ya Fara Lissafinsa azuwa Lokacin kuwa abubuwansa sun Fara bama Rumana mamaki sai Mastur ya Biyo Jirgi yazo yaga Diza ya koma Aranar,ammy bazai jira ta Dawo Daga wajen aiki ba Sai dai in Ta dawo Taji Labarin yazo Tun Abun baya Damunta Har ya Fara Damunta,Ganin Yanzu Diza tafita Kusanci da Mastur waya kuwa kowani Lokaci sai ya kirata yaji ya take..? Taci abinci..?ta samu Barci Itama kanta Diza Duka Umarnin Mastur din take bi Tun Shedan bai samu galaba kan Rumana ba Har ya samu Zuciyarta ta Fara gayamata Daman ita yake so Tun Farko bake ba Saboda haka kada ki bari Wani chanjinsa ya Rudeki Da wannan Tunanin ta kame kanta Gefe yanzu ba kowacce Rana take Biyowa in ta Dawo daga aiki ba ganin yana Chan ma kamar yana nan ne..Kuma yakan Taso Daga Chan Saboda Ita,Shiyasa sai ta kama kanta ta koma Gefe ta zama yar kallo.

Mastur bai yi Shawara da kowa ba yayi ma Sarget Inuwa mgana Matarsa Tana Harkan kasuwanci na Kaya kala kala ita ya bama Kudade masu kauri,tayo Mishi Siyayyar kayan Haihuwa na Jarirai Both Wanda za"a saka ma Mace ko Namiji,Da Siyayyan Atamfofi da lesuna na Diza akwati Biyu nata Daya na Abunda ke Cikinta Daya kuma ya Shirya Ya kawo su Har Zaria da kansa Batare da Rumana ma ta sanu ba Har yazo ya Tafi sai da ya wucen ne ya Kirata ya Fadamata yazo,ammh ya koma to me zata ce mai..?Bata da Abun cewa Tunda Hakan ya Zaba kuma yaga yafiyemai.
Tana Tashi Daga wajen aiki ta wuto nan Direct,Gidan Hajja ta Fara Biyawa suka gaisa ita ce ma Take Fara Fadamata abun Arzikin da Mastur ya kawo ma Diza tace ta Shiga gidan tagani Rumana sai taji Abun ya Daketa Sosai Ammh bata Nuna ma Hajja ba Tayi mata Sallama ta Shiga Wajen Diza.
Mommy bata nan taje gaisuwan Rasuwan Mijin kawarta ya Rasu Diza ce Kadai agidan sai Mama Fadime.
Afalon kasa suka gaisa da Mama Fadime Tana Tambayanta Diza tace Tana Dakinta Daganan ta Nufi Dakin Diza Zuciyarta Cike da Sake Sake.
Tana Shiga da Sallama Ta iske Diza zaune kan gado Akwatunan Duka Zube agabanta abude Tana Ta Dubawa Tana Mirmishi ita kadai Dagani Kila Tun zuwansa da kayan ne bata Rufesu ba..
Cikin Fara"a Ta Dago Tana amsama Rumana Sallaman nata Fara"an da Tun bayan Rasuwar Mansur batayi irinsa ba sai yau Cikin mamaki da Dariyan yake Rumana ta kariso Cikin Dakin Tana Fadin"Uwar Biyu..Me ake kallo ana Ta Sakin Mirmishi haka..?
Tafada Lokaci Daya tana Zama gefen gadi kuma Tana kare ma Tsadaddun kayan kallo Ranta na Suya wanda bai Rasa nasaba da Kishi..
Cikin Fara"a Diza ta Dago Idanuwanta ta Sauke kan Rumana Tana Fadin"Kedai bari Ruma..Daman yanzu nake Shirun Kiranki..Kalli ki gani Abun arzikin da ya Mastur ya kawomin Hatta komai na Bby ya siya Haihuwan kadai yake Jira.."Ta karishe Fada Tana Daga mata kayan Rumana ta karba Tana kallo Cikin yake tace"Kai Masha Allah Kaya sun yi kyau..Kinsan Uba ne shi..Shiyaa kamata ya Fara Tarban wannan Haihuwan.."Diza na Dariya tace"Ko..? Shima haka yace..Bai jima da Tafiya ba ina ta mamakin ina yasan Kaya nace ko kike kika Siyo sai yacemin A"a Matar yaronsa ne Achan Porthercourt ya bama kudi tayi Siyayyay ki Duba Harda Nima fa yamin kaya Akwati Guda na Fitar suna.."Ta karishe Fada tana Dago ma Rumana wasu atamfofi.
Rumana Tana kallo Tana yabawa Cikin Farinciki ko alama Bata Nuna ma Diza wani abu ba Har Mommy ta Dawo ta isketa itama sai alokacin Taga kayan Tunda bata Gida Tun Safe ta Fita
Rumana bata Dade ba Tayi musu Sallama ta koma gidansu Hajja suma Tayi musu Sallama ta wuce Gida Ranar dakyar ta iya Barci Abun ya Dameta Tana ganin Anya Abunda take ganin yana Faruwa in har tace Zatayi Gudurinta anya watarana Mastur bazai manta da ita Ba matukar Diza na gabansa ba Ta Fara Sarewa da Tunanin Anya..? Gabadaya gwiwanta yayi Sanyi ta rasa wannan karfin Gwiwan Datake Dashi Tun Farko.
Da safe da sukayi waya da Mastur din bata nuna mai komai ba sai ma Godiya Data Taya Diza yace kada ta Damu Diza da Abunda ke Cikinta suna Wuyansa ne koda Mansur yana Raye Ballatana Baya Raye,Da ace bata karanta Diary dinsa ba Data yarda da Shi ammh yanzu Jinsa kawai take ta Riga tagama Sanin Karfin Soyayyar da Mastur kema Diza bazai barsa yayi Sukuni ba sai yaga ta Sauka Lafiya.

******

Rumana ta kare Intenship dinta Har Tayi Cukun Cukun Tafiya Service dinta Anyi Posting dinta Camp din Kano,Data kira Mastur ta gayamai yace ba Mtsala sai ta Kwana Gidan Maryama haka kuwa akayi Dataje Kanon Bayan Taje Camp din Tagama abunda Zatayi Dayake Komawa Zatayi Tayi Marriage Certifcate Daganan Mijin Maryama yazo ya dauketa taje gidansa ta kwana Maryama itama Cikinta Har ya Fiti Ashe tun zuwanta Rasuwa da karamin Cikinta,nan ta kwana Maryama na ina ta saka da ita Washegari bata Tsaya ba ta Koma Zaria,Taje Abu Asibiti takai Takardunta nan Zatayi Service dinta Nan da Sati Hudu Zasu Fara kafin su Fara sai Ta Roki Mastur Tana so Taje gida Sokoto ko Sati Tayi ammh kafim ta Wuce Zata Biya kaduna Gidansu Basma ta duba mamarta bata da lafiya,Kuma Dayake Ita da iyayanta sun zo mata gaisuwan Mansur,Mastur bai Hanata ba ya barta da Cewar zai zo Nan Sokoto sai su Dawo zaria Tare da haka suka Rabu Tafiyar Mota Tayi bayan Taje kaduna ta kwana Daya Gidansu Basma Daganan ta Hau Jirgi Zuwa Sokoto Bayan tayi sallama dasu Hajja da Mommy da Diza wacce Cikinta ya shiga watan Haihuwansa.

Rumana Taje Sokoto ta Huta sosai ta samu kyakyawan Lokaci Tare da iyayanta,Allah Sarki Tana chan Sokoto Jikokin Goggo Jummai suka zo suka Tafi da ita Jikin yaki Dadi ba yadda Abba bai yi ba su barta Anan ya kaita asibiti suka nuna a"a Ashe Ajali ne ke kiranta da Tafiyarsu da kwana Daya Allah yayi mata Rasuwa Rumana taji Mutuwar nan ba ita kadai ba Hatta Umma da Abba Daman Jume Da ita suka Tafi Kwanan Rumana Biyar da zuwa suka Tafi wamako Gaisuwa suka kwana Daya suka Dawo Ranar Datayi kwana Shida da Zuwa sai ga waya Daga Zaria Mommy ta kira Umma Tana gayamata Diza ta sauka Lafiya ta samu Da Namiji Umma Tana ta Murna ita take Fadama Rumana Diza ta Haihuwa itama Tayi Murna Jin Lafiya ta Sauka Duk da a asibitin Abu Tudun wada ta Sauka inda take awo,Sai da ta Kira Mommy ne take Fadamata Tun Jiya Dizan ke Naguda asibiti suka kwana Tana ta kuka tace a Kira mata Mastur Shine aka Kirasa,yau da Safe ya Biyo Jirgi ya Taho yana asibitin ma Diza ta Sauka yanzu haka yaje Biyan Bill Dim asibitin ne an basu Sallama Zasu koma gida.
Rumana Taji mamaki,Ganin ga yadda suka Rabu da Mastur Meyasa bai kirata ya gayamata ba..? Wata Zuciya ta ankarar da ita Diza tafiki Muhimmanci Shiyasa,Ranar tayi kuka Sosai kukan Rashin Samun Zuciyar wanda take so.
Ko washegari da Umma taga batayi Shirin Tafiya ba Data Tambayeta sai tace zata jirata su koma Tare Umma tace Shikenan

Rumana ta kira Diza a waya Tayi mata Barka tace Ta na nan Dawowa ita da Umma Zasu zo Daga nan sokoto Ashe kanwar Mommy Taje chan tana kula da Dizan Anty Hadiza,Mastur bai kira Rumana  ba sai Da aka kwana aka wuni kana ya Kirata yana Tambayanta yaushe Zata Dawo tace Umma take jira Daganan bai ce mata komai ba sai itane ma Tayi barkan Haihuwan Dizan.
Sai ana Jibi suna suka Dira zaria Ita da Umma da kayan Sunan Umma Niki Niki ita da Abba,Rumana Taga abun mamaki Babu Abunda Mastur bai siya ba na Suna Kama Daga Raguna Guda Biyu sai Sa Guda Daya kayan abinci Komai da komai ya Tanada,Ya kuma bama Dizan 200k yace ta Rike a Hannunta in tana Bukatar wani Abu Ita da kanta Dizan take Fadamata Ranar da suka zo ita da Umma,Bata Damu ba kuma Bata Nuna Bakincikinta ba Domin Shine komai yanzu.
Nan yazo ya sameta suka gaisa da Umma Kana ya Dauketa suka Tafi Gida sai adaran ne yake Shawartatan me ya kamata ya Siyama Hajja da Aiya da Mommy da Mutanen maruka Rumana tace Lokaci ya kure sai dai In zasu je Kasuwa su suyi Atamfofi Su kai Dinki a sakarmai kudi Za"a samu kafin Safe Shine fa da Safe ya Bata kudi ta Nemi Rakiyan Mardiyan Sukaje ta Siyo Atamfofi na adadin Mutanen Ta kai Dinki ta kuma bada kudin Dinki Wajen Telan Diza ne wanda ta Hadata da ita,Kuma Daman ya bata 50k yace itama Tayi ma kanta Siyayyah sai ta Siyan ma kanta less Daya da Atamfa guda Daya sai ta Siyan ma Mardiya less Daya ta kara musu da Material ita da Diza sukayi anko.
Ana gobe sunan su Inna Zainaba suka iso Harda inna karime da Maryama Daga kano,Sakina ce kadai tazo Mariya nada Tsohon Ciki,Sai matan yayyin Baba Sule su Biyu da suka zo sai Balaraban kawu Usman da makota da akayi ta Hidima dasu
Bangaran ruwa da Lemuka Mota aka Sauke agidajen Biyu Su Snaks kuwa Daga Catering din Diza akayi Merry ita da Sauran Ma"aikata suka zo Dashi Lalli kuma Wata ce Hauwa ta kawo Tayi ma Diza Harda kitso itama Rumana Tayi gyaran kai itama an Zirara mata Kunshi Aranar Da daddare Telan ya kawo Kayan Rumana ta Damka ma kowa nashi tace in ji Mastur ,Inna Zainab dasu maryama da Sakina sai Inna karime Balaraba,Umma Mommy Anty Hadiza da Ayya Tsohuwa mai Ran karfe sai na Mardiya sai nasu da tayi musu anko Ita da Diza,Diza ta karba Tana ta Godiya.
Basu yi wani aiki ba Tunda abincin ma aikatau suka kai,Shiyaasa washegari Tun Safe Bayan Mahauci yazo ya yanka Raguna Kowa ta Tsala wankanta,Sai Da Safen Mastur yazo yayi ma Jarrin Huduba da Mansur wanda Daman ba inda ya bar Babansa,Kowa sai Fadi yake Mansur ya Tafi ga wani Mansur din yazo.
Hauwa tazo Tayi ma Diza kwalliya Sama sama itama Rumana anyi mata,Diza ta Shiga ta Fita Cikin Tsadaddun kayan da Mastur ya Dinkamata ita da Little Mansur sai da yammah ta Saka Material din da Rumana ta Dinkamusu,sai suka saka atare,Sosai jama"a suka zo musu Wannan Taron,Anci ansha Sosai Kuma anyi kuka da Tuna Mutuwar Mansur Musammsn Diza,Taron Diza agidan tayi shi Taron sauran Mutane kuma Gidan Hajja nan aka gyara Naman Sa da na Ragunan ma su Inna Zainaba suna aikinsu.
Mastur kuma yana Gida,Daddy kuma yana wajen aiki hakama Baba Habibu yana kasuwa duk sai Dare suka Dawo.
Anyi suna Lafiya an watse Lafiya Baki Duk sun koma Gidajensu Lafiya Rumana kuwa sai bayan suna da kwana Biyu Mastur yazo ya Dauketa suka koma Gida Shima a washegarin ya koma ammh Sai da ya Biya Ta gida Yaga Diza da Little Mansur Dayaji Duk Duniya ba wanda yake so da kauna irin yaron nan gabadaya soyayyar Mansur ya Dawo kansa ne Kowa gefe ya koma ya bar masa Domin Dan nashi ne
Umma ma Ta koma Sokoto Anty Hadiza ce kadau bata koma ita keyi ma Diza wankan Jego Ta kuma Kula da little Mansur.
Sai bayan suna da Sati Daya Baba Sule yazo yaga Jikansa ya Daukeshi ya sakamai albarka Yayi kuka sosai kwana Daya yayi ya koma Bayan ya koma Abba ma yazo yaga Little Mansur bai kwana baya koma,Haka Abokan Siyasan marigayi ke ta zuwa barka suna bama Diza abun Arziki Duk Sagir ya gaya musu Haihuwan Dizan aikuwa suna ta Zuwa kuma kowa yazo da abun Arzikinsa Har Chairman din da aka Dora yazo yaga Little Mansur ya bama Diza100k,kyauta Diza fa ta samu kudi bata san adadinsu ba In Ta tasa Little Mansur tana kallo Bata sanin sadda take Fashewa da kuka sai kuma ta kamashi Ta Rumgume tana kuks sai Anty Hadiza tayi ta Fada kana take yin Shuru.
Rumana ta Fara Service dinta anan asibirin Abu dake Zaria,sai dai Itama Lokaci Bayan Lokaci Tana Zuwa Duba Diza da Little Mansur Daya gama Shiga Ran kowa Hatta Baba Habibu Takawa yake ya Shiga Saboda ya gansa ya Daukesa yana ji kamar Mansur ne ya Dawo.




*Shakira.."*
1/1/22, 18:55 - Maryam Badmsi: *SS....36*


*Ki biya ki karanta cikin Salama da Aminci 09069067488*



"Anty Hadiza da Mommy suka Hada Hannu wajen Cigaba da kula da Diza da Little mansur wanda Mastur yace baza"a sskaya sunansa ba da Mansur dinsa za"a rika kiransa.
Cikin kwanciyar Hankali Diza take Jegonta Tayi Bulbul Tayi kiba ta Fara maida kibanta,Su hajja ma ba"a barsu abaya ba kowa yana iya bakin kokarinsa wajen kula da Diza da Mansur karami
Babu abunda Diza ta nema ta rasa na Rayuwa ba Daddy ko Mommy ba,Mastur shi ya Dauke duka Dawainiyar Diza da Mansur karami,madaransa kayan waasansa,kayansa pampers komai nashi Mastur ne,Hatta da ita Dizan Nauyinta Duka ya maidashi kansa arana sau ya kirata yafi a Kirga yana Tambaysn Mansur karami Ta sskamai kukansa yaji ko kuma Numfashinsa Kowa yasan Kaunar Dake Tsakanin Mastur da Mansur ne ya Dawo dashi kan Mansur karami.
Baya wata Daya bai ijiye duk abunda yake yi yazo gida ganin Mansur karami ba,kuma baya zuwa Hannu Rabbana da Sha tara na arziki na Mansur karami,in yazo har ya Tafi Mansur wajensa yake wuni ssi in yayi kuka ne ya bada akaima Diza ta bashi Nono kowa dauka yake saboda Mansur Mastur ke Zarya Tsakanin Zaria da Porthercourt,Sai Rumana wacce gabadaya ta la"kanta Abun a Saboda Diza yake zuwa Duk da Hakan take a zuciyar Mastur din ammh kuma Yaana zuwa ne Saboda Mansur karami,da kuma amfani da wannan Damar wajen Samar da Shakuwa a Tsakaninsa da Diza wanda bai wanzuba a tsskaninsu ba abaya kuma Ba Laifi Shakuwa ta Fara Shiga Tsakaninsu ance mai Da wawa kuma mai baka Kulawa yana Samun Wata Daraja akan ne ta  Faru da Diza Gabadaya Mastur ya zame mata wani al"amari wanda batasan yaushe ya Farfado ba Soyayyarsa Data Binne Shekarun Baya itace ta Fara Bayyana kanta Batare data sani ba,Yawan kiranta Dayake akoda yaushe da Kula da ita da yake yasa Zuciyarta taFara kwadaita mata Cikar Burinta nan kusa da kuma Tunanin Kila hakan ne yasa Allah ya karbi Ran Mansur Saboda ta auri Mastur sai dai duk da haka Rana bata Taba Fitowa ba ta Fadi bata Tuna da Mansur tamai addu"a ba Shidin wani Jigo ne nata Wanda bazata taba mantawa Dashi ba Har gaban Abada.

Anty Hadiza bata koma Sokoto ba sai da Diza Tayi arba"in kana ta koma Bayan Daddy da Mommy sun cikata da abun arziki harda Mastur ma,Bayan Tatafine ba Dadewa Mommy ta Raka Diza sukaje Sokoto Har Tureta sai da sukaje ta kai Mansur karami Har gidansu Rumana sai da sukaje ta kaima Umma da Abba mansur Karami Wajen kwanansu Goma kana suka Dawo bayan sun Dawo Suka Shirya ita da Mardiya suka je Maruka wanda Duka Dawaniyar Tafiyar Mastur ne ma yayi shi Direban Daddy ya kaisu.
Agidansu Mansur tayi Sati Daya Cur Tare dasu kuma sun ji Dadi kwarai an Zagaya Dangi da ita ana Nuna cewa matar marigayi Mansur ce Kamar su Lasheta ita da mansur karami Har gidan Sakina Taje da mariya,Maryama kuma ita tazo Dataji Labarin zuwanta Daganan Ririwai suka Sauka gidan Inna karime suka kwana kans suka juyo zuwa Gida Zuwa Lokacin Diza tayi kiba tayi Bulbul da ita ta kara Haske Daga gani Hankalinta ya Fara kwanciya.
Bayan Dawowarta ta natsu agida ta cigaba da kula da Mansur karami Wanda take jinsa aranta bama ita kadai ba Kowa da Rana wajen Hajja yake wuni har ya saba Baya yawan kuka akwai Hakuri kamar Babansa,Mardiya in Tana gida Tayi ta Reno in Tana makaranta Hajja ta Goya Tana Jijjiga,Diza ita dashi Sai dare Tunda In Baba Habibu ya Dawo Shima ya Dauka yana mai wasa Hakama Daddy daya Dawo Diza Zata Hawo mai da Mansur karami Sama sai Dare ya Tsala Mommy zata Dawo mata dashi yayi Barci Ita Renon Mansur karami Baya hannunta yana Hannayen su Mommy ne Tsskaninta Dashi Kawai bashi Nono ne ko wanka da Shiryashi Aikin Mommy ce ko Mama Fadime wani lokacin kuma Hajja.
Su Daddy sunyi zama wajen Rabon gadon Dukiyar Mansur Mastur ya bada shawaran saida Motocin Mastur Duka da Sauran kadarori Sai dai yace abar Gidaje Saboda Mansur karami in ya Girma an samu kudi Miliyoyi Masu yawa,An raba gadon Yawancin Dukiyan Rabi da kwatanta na Mansur karami ne sai Baba Sule Dayasamu gado sai Diza ita Ta samu Gida da kudi Sai Baba Sule shima Daya mallaki gidan Mansur na Gra.
Duka Dukiyan Mansur Karami Mastur aka Damkamawa bai karba ba,ya Umarci Diza da taje ta Bude accout da sunan mansur Karami ta ijiyemai kudinsa ita keda alhaki a mtsayinta na uwa Garesa haka kuwa akayi taje ta Budemai banki ta adana mai Dukiyarsa Ta Hada duka da Kudaden da ta samu Lokacin Haihuwarsa Da Rasuwarsa wadanda abokansa yan Siyasa sukayi ta bata,Bata da wani Abunda Zatayi Dasu komai na Rayuwa Mastur ya Dauke mata Uwa uba ga Catering dinta ba Laifi ta samu kudin da Bata san iyakarsu ba.

Diza da kanta ta Nemi Izinin Daddy Akan tana so ta koma Wajenta aikinta Hakan zai Rage mata Zaman kadaici,Daddy bai yi Gaddama ba ya yarda Daman Abunda suke nema ne gashi ya Tabbata su ga Diza ta saki Jikinta ta Dawo kamar Baya,Data gayama Mastur bai ce komai ba Illah Jadadda mata ta kula da Mansur karami,Ta Fara Zuwa Catering dinta Ranar awajensu Hauwa kamar Salla,haka aka Dinga Daukan Mansur karami kamar Za"a Lashesa Saboda ya Saba da Mutane bashi da kiyuwa Sosai Ammh Saboda Daukansa da Bashi Ruwa yasa Diza tayi ma Mommy mgana kan Tana so ta Dauki nanny wacce Zata rika Taimaka mata in sun Fita Mommy Balaraban Usman Tayi ma Mgana ita ta samo musu yar nan kusa dasu Wata yarinya Hanne yar Shekara Sha uku,Diza ta Dauke Zata rika Biyanta Duk Wata akan Lokaci Daman iyayan nata ba wani Hali sai sukaji Dadin hakan.
Da hanne take Tafiya wajen aiki Tana Tayata kula da Mansur in kuma suka Dawo gida shikenan yana wajen Mommy ko kuma yana Gidansu Hajja wajen mardiya ko Ita Hajjan da kansa,Sai ko abunda ba"a rasa ba Daman da sun dawo Diza ke Sallaman Hanne ta koma Gida sai kuma Gobe in zasu Fita in kuma bazata Fita ba sai dai tazo Gida Tazauna Haka ta Daukeshi Zuwa Chan kuma Diza sai ta Sallameta ta koma gida.
Haka suka Cigaba da Tafiyar da Rayuwarsa aduka Bangarorin Rumana Tana Cigaba da zuwa wajen aikinta kuma Lokaci Bayan Lokaci Tana Biyo nan ta gaida su Hajja ta Biya taga Mansur karami da Diza,wacce Manema suka Fara mata ja,Kamar ana jiranta Ciki harda P.A din Marigayi Mansur Sagir,mastur yana chan bai ji Labari ba kuma bawanda ya sanar dashi Diza ma basa gabanta Domin ta Tabbatar musu baxatayi aure ba sai Mansur karami ya Girma.
Sagir dai shine ya Rike wuta da Cewarsa Zaman Amanan da sukayi da marigayi Shi ya Dace ya aureta ya Rike Mansur Karami Tamkar shine ya Haifesa Diza bata amince dashi ba ammh kamar su Daddy sun karbeshi Domin Taga sunyi Na"am Dashi Duk da itama bama wannan ba awannan karon in ba Burin Ranta bazata yarda ta Kara wani Aure ba sai dai ta Hakura.

Rumana bata da Labarin Abubuwan da suka Faru saboda Kwana Biyu bata leko ba aiki yayi mata yawa a asibiti Sai Ranar Lahadi Data Leka Mommy ke mata Zencen Tana Umartatan Data Bama Diza shawaran Sagir Ya Dace da ita Duk da Saurayi ne bai da mata ammh Iyayensa kansu sunyi Na"am da Batun na Diza Rumana Mamaki ya Hanata mgana data samu Diza da mganar ta Fasa mata kuka Dole ta Rabu da ita ammh Taje gida ta kwana tana Tunani ta rasa mafita.
Diza tayi kokarin ta Kaucema Mganar Sagir ammh hakan ya gagara Domin har su Hajja sun yi Na"am dashi yana zuwa Lokaci Bayan Lokaci Hidima kuwa Yana yinta da Jikinsa da Aljihunsa Mansur karami Dan gatane ta ko"ina Har Mastur yazo ganin gida ya koma ba wanda yamai Tadin Sagir,Shima Sagir din baya gari alokacin sai da ya koma yazo
Daddy daya Lura Diza na Karar Sagir da kansa ya kirata ya bata Shawara Akan bazai Tursasata ta auri Sagir ba ammh kuma in ta Zabesa zai ji mata Dadi da karin Shawarwari sosai wadanda suka karya Lagon Diza sosai su Mommy sun Wahala da ita tayarda ta kara rasa Burin ranta akaro na Biyu Tunda shi bai sonta kuma bai Furta mata ba Dadai ta Tsaida wannan Alhazan masu katon Tumbi gwara Tayi Maneji da Sagir din..
Da kanta take Sanar da Rumana Abunda ta yanke game da Sagir ita kuma Tace mata Tayi mgana da Mastur Diza tace A"a sai Abun yazo ba yanzu bane sai ta yaye Mansur karami.


*******

Bayan Shudewar wani Lokaci.
Tuni Mansur karami yana Tafiyarsa ko"ina Lokacin yana watansa na goma da Haihuwa,yana gudunsa ko"ina,yana kara yawo kamaninsa da Marigayi Mansur na kara Bayyana Tare da kwaramiyansa,ya Fara mgana irin nsu na yara ya iya kiran sunan Hajj,da Baba Habibu,da Aiya sai Daddy Dayake kira Baba Diza kuma Mama,Rumana ma Mamace ,Mardiya kuma Anty,Mastur kuma Baba Daman a kansane ya iya kiran sunan Baban
Mansur karami yana ganin gata kowa nan nan yake dashi yan maruka Musamman suke zuwa ganinsa kan Uban kowa su Sakina Lokaci Bayan Lokaci suna zuwa da abun arzikinsu ga Dansu Mansur da suke ganin Tanmkar Dan"uwansu.
Baba Sule kuwa saboda yanayin Tsufa,Diza ke kaimasa Shi ya gansa in ta samu Lokaci Zuwan Datayi na karshe Yana ta mata Nasihan da Lallashin ta Cire komai aranta Tayi auranta Dagajin haka tasan Daddy ne ko Baba Habibu wani yayi Zencen dashi.
To me zata ce..,? Bata da abun cewa Domin wanda takejira bazata samesa ba,kuma ayanzu bata da wani Zabi tunda ta rasa Mansur Taa Cire wani Buri acikin Ranta Tasan bata auri Mansur Domin Tana sonsa ba ammh kuma akwai Shakuwa mai karfi a Tsakaninsu,Ya rasu ya barta da Ciki alokacin Data Fara sonshi Take jin Dadin Zama dashi Har Abada bazata manta wannan Rasuwar ba,mutuwar mansur gareta Tamkar wani gyambo ne acikin Zuciyarta wanda bazai goge ba.
Ashe Sagir ne yazo har nan maruka ya samu Baba Sule da mganar Diza Akan ya Rokar mai ita ta bashi Daman ya Turo mgabatansa Tunda su Daddy sunce bazasu Tursasama Diza Duk Abunda ta yanke Daidai ne,Yazo musu da Kayan abinci kuma ya Zube ma Baba Sule kudade masu yawa ba wannan ne Zuwansa na Farko ba yana zuwa Lokaci bayan Lokaci yace Alherin da Marigayi yayi mai bazai Taba Biyansa ba Dalilinsa gashi Shima yayi Nisa a Siyasa Dashi kuma yake Tsaye da Kafafunsa.

Har wannan Lokacin Mastur bai san Sagir na Neman Auran Diza ba yasan dai Zawara sun mata Chaa,Tunda sun Taba mganar da Daddy bai maida kai ba Tunda Daddy da kanshi ya sanar dashi Diza bata bama kowa Fuska kuma Shi bazai Takura mata ba,Dayake yanzu yakan Dade bai zo gida ba,Saboda yanayin aiki Daya musu yawa in kuma yazo kwana Daya yake yi,ko Biyu ya juya kuma koda yazon Wani Lokacin in yaje ya Dauko Mansur karami Gida yake Dawowa Dashi shi da Rumana suyita Hidima Dashi,Sai yamma ko Dare suke maidashi gida wajen Diza Shiyasa Lokacin da Sagir yake zuwa bai sani ba itakuma Rumana ta sani ammh kuma bata yarda Tayi mganar da Mastur Domin batasan me Zata gayamai ba.

Diza ta kan kula Sagir Darajan iyayenta,Shiyasa in yazo ta kan Saukeshi nan Falon Farko Mama Fadime ta cikamai gabansa da kayan Ciye ciye da Shaye Shaye,Takan zauna suyi hira wanda yawan Hiran mganar Sagir itace ta bashi Izini ya Turo mgatansa,,Batace mai komai ba Saboda bata da tacewa ta kasa Bashi Damar Dayake so har yanzu Domin bata Taba son Sagir ba Akwai dai Tana Kulashi ne Saboda Yadda yake wajen Marigayi Mansur da kuma Darajan su Daddy da Baba Habibu Kowa yanuna mata Sagir ne ya Dace da ita.
A irin wannan Zaman ne Mastur ya Cimmusu ya Dawo jiya Cikin Dare,sai ya sauka agida sai da Safe bayan ya kai Rumana asibiti ya Dawo sai ya Fara shiga wajen su Hajja suka gaisa Daganan yashiga gidan yagaida Daddy da Mommy sai kuma yaga Diza da Mansur karami.
Sai dai yana Shigowa yayi kyakyawan gani Sagir Zaune afalon Farko Yana Dauke da Mansur karami Yana ta wasansa Dauke da Chaculate a Hannunsa,Diza na gefensa Tana Sanye da Riga da Siket na wata Atamfa mai kalan ja sai Tayi amfani da jan Mayafi batayi kwalliya ba sai dai Fuskarta tayu wasai da ita.
Dukkansu basu Lura da Shigowarsa ba Sagir ne ta ma Diza mgana ko nace Roko kan ta Bashi Dama yana so yayi Tafiya ta kamashi Zuwa Abuja sai nan da Sati Biyu zai dawo yana so Ta bashi Dama kafin ya Tafi ya Turo magabatanss,Diza shuru Tayi kanta na kasa Tana jinsa Basu san da Wanzuwar Mastur a Falon ba wanda Zuciyarsa ta Buga Sau uku alokaci Daya kansa ya Sara Kafafuwansa suka Fara rawa kamar bazasu iya Daukansa ba ya Juya Cikin karfin Hali da Niyar barin Falon.
Mansur karami Daya gansa ya Fara Zillo ajikin Sagir yana Fadin"Baba..Baba.."
Wanda ya jawo hankalim Diza suka juya inda suka ji Mansur karami na kallo yana kiran Baba suka ga Mastur ya juya baya yana Shirin Tafiya gaban Diza ya Fadi Ras Sagir kuma sai ya Mike ya Saki Mansur karami yana Fadin"Wayon Little Mansur akwai yawa..Jibi yaga Babansa ya ganesa..Jeka wajen Baba Mastur.."yafada yana Sakinsa da gudu kuwa ya Tafi garesa Mastur ya Jiyo yana Boye Halin Dayake Ciki ya Durkusa ya Tarbi Mansur ya Rumgumesa yana Sakin Numfashi.
Shima Mansur din haka ya Lafe ajikinsa kamar wani mage Mikewa Mastur yayi ya Daukesa Tsab ya Daga sama yana mai wasa Shi kuma yana Bangala Dariya Daga Sagir din ne har Diza suna Tsaye ne suna kallonsu
Mastur ya kalli Sweet din Hannun Mansur karami yana Fadin"Waya siya maka Sweet My Son.? Mama ce..?
Kai ga girgiza ya nuna Sagir yana Fadi Cikin gwarancinsa"uncu ne..! Wato Uncle ne sai da Mastur yayi Dariya Lokaci Daya ya shafa Kumatunsa yana Fadin"My Son ya Girma"Shima kumatunsa ya shafa yana Dariya da gwarancinsa
Sagir ya karisa gaban Mastur Lokaci Daya ya bashi Hannu sukayi Musabaha.
Sagir yace"Tun bayan Rasuwar nan bamu kara Haduwa ba Yaya mastur ba sai yau.!
Mastur yace"Hakane..Kasan yanayin aikim mu sai a Hankali ko nazo gida bama wuce kwana Daya zuwa Biyu..!
Sagir ya jinjina Kai yana Fadin"Hakane Allah ya Taimaka.."Mastur ya amsa da Ameen yana Satan kallon Diza da Duk tayi wani irin Zuciyarsa Bugawa takeyi bayaso Abunda yake Hasashe ya zama Haka din ne To in ba haka ba me zai kawosa Har Cikin Falo kuma suna Zaune Shi da Diza ayanayi na Masoya.
Bai gama mamaki ba yaji Sagir na Fadin"Yaya Neman iro muka zo..Kasa baki Diza ta amincemin Na turo mgabatana tun bayan Haihuwam Mansur karami nake Binta taki Bani Dama kuma su Daddy sunce bazasu yi mata Dole ba a Taimakamin Baban yaya..!
Ya Karishe Fada yana Sosa Keya irin na kunya din nan Shi kuwa Mastur ji yayi kamar Sagir ya Bigamai Guduma atsakar kansa Bai san sadda ya Dago kansa yana Bin Diza da wani Kallo ba wanda itama Ta Dago tana Ganin yanayim Kallon Da bai taba mata ba kenan mganar ta Dade ba wanda ya Taba gayamai?
Dakyar ya iya Sarrafa kansa ya Bude baki yace ma Sagir"Haba kada ka damu..Indai Tana sonka Zata baka Dama kada ka Saremana Tun yanzu..!
Yafada Lokaci yana kallon Diza da wani yanayin da sai da ta Sadda kansa kasa bai kara bi ta kansu ba yayi ma Sagir sallama ya Fice Dauke da Mansur Karami wanda ke tamai gwaranci bai ma Jinsa Zuciyarsa da gangar Jikinsa sun Tafi yanayi wanda ya Dade bai jisu ba.
Har ya kai Falon Hajja baya Cikin Hayyacinsa,Sai da yaji Hajja nama Mansur Wasa cikin wani yanayi ya Dago ido yana kallon Hajja Cikin Muryan sanyi yace"Hajja wai da gaske ne Sagir na Nemam auran Diza Tun Tuni..?
Hajja Data dauke da Mansur ta ijiyeshi Tana Fadim"Eh Wlh..Tun Haihuwan Mansur karami yake ta Bin Diza ammh Taki bashi Daman yayi mgana da Babanka da Alhaji sukuma sumce Zabi na wajenta nasu kawai Shawara ne da addu"a Wlh yaron Kirki ne Koda yauahe baya gajiya da Hidima bamu nan ba Har Cham maruka yana Zuwa Lokaci Bayan Lokaci ya Duba Sulen kuma nidai aganina ya Dace da Khadija da Zaka saka baki kila ta Amimce Baban Mutum!
Zuru kawai yayi ma Hajja da ido Har sai da ta Tsorata Cikin Firgita Tace"Lafiya kuwa Babban Mutum..? Ganin  irin yadda ya Saka mata ido ne abun ya bata Tsoro.
Mirmishin Dayafi kuka Ciwo yayi mata Kawai ya Mike yana Fadin"Bakomai Hajja.."Daganan ya sa kai ya fice Hajja da ta Bisa da kallon mamaki Kafin ta gyada kai Tana so ta Fahimci Meya samu Dan natane Lokaci Daya haka bata da mai bata wannan amsan.
Daga nan gida ya koma Yana Tuki yana ji Zuciyarsa kamar Zata Fashee saboda Radadin Datake yimishi Allah ne ya kawosa Gida Lafiya.
Bedroom din Rumana yaje ya kwanta yana jin kamar Sanyi zai kamashi Zazzabi sai Ciwon kai,nan ya wuni yana Fama da Zuciyarsa ko abinci bai iya Sakama Cikinsa ba yana ci wayarsa na Neman agaji ya kasa Tashi ya Duba salla ma Azahar da La"asar ya Hada lokaci Daya

Rumana Da tashi Daga wajen aiki Tayi ta kiransa bai Dauka ba sai Tayi Tunanin bai kusa da wayar ne saisuka Hau Motar Haya ita da Aisha Bala Tunda batazo da Motarta ba,gabda mangariba ta Shigo Gidan shuru Tasan Mastur yana nan Tunda Taga Shashennata a Bude kuma taga Motarsa sai dai Tayi mamakin ganinsa agida,Bata kara mamaki ba Sai ta shiga Bedroom dinta tagansa kwance Cikin Blanlet Yana rawan sanyi Cikin Tashin Hankali tayi wurgi da Jakar hannunta ta Fada kansa Tana Tambayansa Meya samesa..?
Jinta kusa dashi da Muryanta yasa Rauninsa ya kara Bayyana ya tashi Zaune Lokaci Daya ya Rumgumeta sai yaji Hawayensa sun kawo Cikin wata irin Murya yace"Na kara rasata Rumana..Na kara rasata akaro na Biyu..!
Yafada Lokaci Daya Hawayensa na gangarowa abayanta.
Cikin Rudewa Rumana take jin Mastur yana kuka wanda Kukansa Da Tataba gani Rasuwar Mansur sai gashi yau yana kuka Saboda Diza Ta Tabbata akanta yake mgana Saboda Tana asibitin Dizan ta kirata Tana gayamata bata san yadda Zatayi ma Mastur din Bayani ba Yaganta da Sagir Daman tasan haka Zata Faru Shi Tayi ta Gudun Faruwarsa.
dago kansa Tayi Tana Fadin"Ita wacece ka kara rasawa kuma.?
Ta tambayeshi Tana kallonsa Runtse ido kawai yayi ya koma ya kwanta yana Kokarin Goge Hawayensa baisan ta Rika tagani ba.
Cikim karfin Hali yace"Dafamin Ruwan Zafi nasha Tea..Duk wunin yau banci komai ba..!
Yafada yana kokarin Saita kansa Daga Barambaraman daya kusa yi.
Rumana sai tayi Mirmishim Dayafi kuka ciwo ta juya ta Fice,Tana Sharee kwallar Data Taho amata afili ta Furta.."Ina son Mijina..So na gaskiya bazan bari saboda Soyayyar Diza yasa rasashi ba..Zan yi kokari naga ka samu Cikar Burinka Mastur..Insha Allahu Zan Sadaukar da Soyayyar danike maka wajen ganin ka mallaki Zabin Ranka Diza da yardan Allah..!








*Shakira...*
1/1/22, 18:55 - Maryam Badmsi: *SS....37*

*Ki biya ki karanta cikin Salama da Aminci 09069067488 Mace mai aji mallakan komai nata take yi bata jiran abun sata*

"Ranar haka Rumana ta kwana  Hidima da Mastur wanda ya kwana bai yi barci ba ga Ciwon kai ga jiri ga Ciwon da kirjinsa keyi yadda suka ga Rana haka sukaga Dare Rumana Tun Tana Daurewa sai ta saka kuka,Domin yaki yarda ta kaishi asibiti Ballatana ta kira wani Daga chan Hanwa..
Washegari ma ko Sallar asuba sai a zaune yayi ta,dakyar shima da Taimakon Rumana Ta Fita ta Hado mai Tea Ganin Tun jiya bai ci komai ba Kuma yace bazai iya cin Wani abu ba Rabonsa da wani abu Tun Tea din Data Hadomai jiya,Shima kadan ya sha Cikin Dare kuwa sai da ya amayar dashi.
Ta kawo mai Tea din Tana ta Faman Lallashinsa yasha yaki sha Sai ta saka mai kuka Kukanta na Dagamai Hankali Cikin karfin Hali ya Mike Zaune kan gado yama jin kamar kansa zai tsage gida Biyu ya Dafe kan nashi da Hannu Daya kafin ya kalleta Cikin Lumsassun Idanuwansa da suka Chanza Launi Tun jiya yace"Ruma..Wannan kukan fa..? Kina so ki kashe ni ne..,?
Yafada yana Sakin Nishi Nishi Sama sama ta kalleshi Cikin wani yanayi Lokaci Daya taji Kishi Ya Turniketa acikin ranta Tace"In ni ban kashe ba ai Ita Zata kasheka.."Bata sani ba afili Tayi mganar kuma ya jita shiyasa ya Sakarmata ido yana kallonta Cikin mamakinta bai kawo ma Ransa ta san Damuwarsa ba Shiyasa bai Hasasho ma kansa ba sai ya Tunanin kila kalamansa na Jiya Tayi amfani ta Fadi haka.
Hannu ya mika mata ya karbi Mug din Tea,Filet din Soyayyan Dankalin Turawan Dake hannunta ta nuna mai kai ya girgiza yana Fadin"Bazam iya ci ba..!
Kallonsa tayi kawai kafin ta kada kai ta koma Kichen Ta Fito kenan Taji wayarta na kara Aisha Bala ce ta Dauka sukayi mgana Daman ta kiratane da Safe ta Fadamata yau bazata samu zuwa ba Mastur ba Lafiya tayi mata aikinta na yau Zata Rama mata Aisha tace ba mtsala Dayake ma sun kusa gama Service dinsu Rumana Tariga ta Fadama Abba Ba aiki Zatayi ba Residency take so tayi Ta samu kwarewa kan Abunda ya shafi yara,Har Mastur din Tayi mgana Dashi kuma ya bata Goyon baya Zata Nema ko Uduth ko Atbu,inda ta samu anan Zatayi Sai dai tana Fatan Samu Zaria Saboda Auranta.

Tana Cikin wayar ne taji kamar kakarin Amai da gudu ta Jefa wayar nata kan kujera ta Rumtuma Zuwa Dakinta anan gefen gado yake Durkushe yana Kakarin Aman bai iya karisawa Tiolet ba,da Sauri ta karisa gareshi ta Rikeshi tamai sannu Makogwaronsa ya Tushe Numfashi ma Dakyar yake Fitarwa ga Tari Daya Sarkeshi Ya farayi ba kakkautawa Sai ga Jini yana Biyo dan Ruwan Tea din Dayasha Rumana ta Tsorata Cikin Firgita ta kurama Jinin Ido kafin tace"Mun shiga Uku..Jini fa..,?
Tafada Lokaci Daya Cikin wani irin Rudewa shi kanshi Mastur,ya Rude Daya ga Jini yana Fita Daman Likita ya Fadamai in Zuciyarsa takai wani mataki ko Tari yayi ssi jini ya Fita to ganin haka yasa yasan Abubuwa sunyi Nisa kuka Rumana ta Fashe dashi Tana kuka ta Taimakamai ya Tashi taRakashi Tiolet ta taimakamai yayi wanka Ta barshi ya karaasa wankan ta Fito ta gyara wajen Daya bata Tanayi Tana Sharan kwallah acikin Ranta Tana Fadin ya Zama Dole Tayi wani abu.
Ita takoma Cikin Tiolet din ta taimaka masa ya Fito yana Fitar da Numfashi Sama Sama,ita ta taimaka mai ta shafa mai mai ta kuma sakamai Saukakkun kaya ya saka Yana kallonta ta Saka Hijabin Sallarta Ta Dauki key din Motarta Yana kallonta Yafara Kokarin yi mata mgana Ganin haka yasa tace"Zan je na samo maka mganin Mtsalarka..Bazan bari ka Mutu saboda wata ba Ahalin ina da yadda Zanyi..!
Tafada Idanuwanta Taf da kwallah mamaki ya kamashi Cikin Sarkewar murya yace"Wata..?wata wa..?
Bata tsaya ma bashi amsa ba ta kada kai ta Fice Tana Fadin"Ka kula da kanka..yanzu zan dawo..!
Daga haka ta Fice tana Sharan kwallah Allah ne ya kawota Hanwa Lafiya a gidan Daddy ta Sauka Ta zuba Hon megadi ya Bude mata get ta sulala zuwa Ciki,ko parking din ma ba Daidai Tayi ba,Bata cikin Natsuwarta Tana Fitowa Tayi hamdala ganin Motar Daddy Gudu Gudu Sauri Sauri ta Nufi Cikin gida.
Afalon kasa Taci karo da Mama Fadime ita kanta Mama Fadime Ta tsorata da ganin yanayin Rumana Tana Daga Tsayen ko Zama ta kasa yi bayan sun gaisa tace tayi mata mgana da Mommy,ta amsa da Toh da Sauri ta Haura sama aranta Tana Fatan Allah yasa Lafiya.
Diza Dake Cikin Dakinta Taji kamar mgana afalon kasa Daman Hankalimta Tun Jiya ba"a kwance yake ba Tun Tafiya Mastur kuma Tayi ta kiran wayarsa bai Daga ba Mansur karami bayanan wajen mardiya ya kwana da Safen ta kawo mata shi yasha Nono ita ta wuce makaranta Ta bashi Nonon kadan yasha,daman Mardiya tayi mai wanka sai barci Tana Zaune ne tana Tufka tana warwara kamar taje Chan Lowcost tagani ko Lafiyasa yasa ta kasa Zama Waje Daya ko Sagir din Dayake ta Kiranta bata Daga ba jin mgana Sama sama afalo yasa ta tashi da Sauri ta Fito Daidai Lokacin da Mommy ta sauko kasa Tana Kallon Rumana cikin mamaki Tace"Ah Rumana lafiya dai ko...
Rumana najan majinan kuka tace"ba lafiya Mommy ina kwana..? Don Allah kimim mgana da Daddy ina son mgana dashi Cikin gaggawa..!
Mommy ta Rude Cikin Tashin Hankali tace"Rumana meyafaru..? Wani abu ne ya samu Mastur din ne..?
Kai ta girgiza ssi kuma ga Hawaye Diza dake tsaye Kofar Dakinta sai taji Zuciyarta ta Fara rawa,Mommy kuma Tashin Hankalinta ya karu taja Hannun Rumana Tana Fadin"Muje Sama..Daddy na chan..!
Tafada Lokaci Daya suna Haura Steps din Bene Diza Data Daskare a Tsaye ta kasa Daga kafafuwanta Ballatana Ta bi bayansu haka kurum take jin kasala ya Rufeta Dakyar ta samu Damar Ciran kafa tabi Umarnin Zuwanta wajen Bin bayansu Taji meke Faruwa..? Allah yasa ba wani Rashin zasu sake yi ba.

Afalon Mommy Ta zaunar da ita ita kuma ta Shiga Cikin Bedroom din da Sauri Ta taso Daddy jin Rumana tazo tana kuka yasa Jallabiya kadai ya Zura ya Fito Cikin Tashin Hankali Rumana na ganinsa ta Mike Tana kuka Shar Hawaye suna ta Zubo mata kamar an Bude Famfo Daddy ya kalli Mommy itama ta kalleshi Cikin wani yanayi wajenta ya karisa Cikin Wani Hali yace"Subhanallah Rumana Lafiya kike kuka..?
Jin haka yasa ta kara saka kukanta Lokaci Daya ta Zube gabam Daddy Tana Fadin"Don Allah Daddy..Ka Rufamana asiri..Ka Aura ma YA MASTUR Diza in ba so kake mu rasashi kamar yadda muka rasa Mansur Ba Daddy..!
Tafada Cikin gunjin kuka da wani Kishi Hade da Soyayyar Mijinta,Ba Daddy da Mommy sukaji Mganar kamar Daga sama ba Hatta Diza dake bakin kofar Shigowa Sai ta Taji wani Dum! Dum! Sau Biyu kanta ya wani Sara mata Sai ta kasa Shiga Dakin ta Dakata tana jin wani Bakon Lamari yana Ratsa gangan Jikinta me Rumana take so ta Fada?
Metake Nufi ne..? Wata mgana ce take so ta Furta...?
Bata gama mamaki ba Taji Daddy na Fadin"Rumana wata irin mgana kike Fadi haka Rumana..?
Yafada Lokaci Daya yana Dagota Daga Durkushen ya Zaunar da ita kan kujera Mommy ma ta ksa Mgana Saboda yadda Taji mganar.
Rumana ta gyada kai Tana Fadin"Eh Daddy..Im kukayi kuskuran barin Diza ta auri Sagir ina mai Tabbatar muku Zamu rasa Ya Mastur Shima zai barmu har Abada Kamar yadda Mansur ya barmu..!
Daddy ya kura mata ido Cikin wana yanayi Gefenta ya Zauna yana Dafa kafadarta lokaci Daya yana Fadin"Naji duk mganarki Rumana ammh meyasa kika ce haka..?kuma shi Mastur din ne ya aiko ki..?
Rumana na Sharan Hanci Tace"Bashi ya aiko ni ba Daddy ni na aiko kaina..Asali ma baisan na san Halin Dayake Ciki ba!
Mommy ta kalli Daddy shima ya kalleta kafin ta maida kallonta kan Rumana tace"Wani Hali yake Ciki.?
Rumana ta gyara zama Cikin Zubar kwallah da Shasshekan kuka ta Fara Fadin"Nasan Abunda ke Damun ya Mastur da ba wanda ya sani Daga shi sai Allah suka sani..Nima ba gayamin yayi ba Sanda mukaje wajensa baida Lafiya ne na Samu ganin Diary dinsa na karanta anan nasan Komai..!
Nan ta Fara Basu Labarin Abunda Tagani Rubuce a Diary din Mastur wanda ya Rubutu Tu daga Farkon Fara son Diza da Bullowar mganar Mansur da yadda ya Sadaukar da soyayyarsa ga Dan"uwansa uwa uba kuma da yadda ya Nuna ma Diza bai taba sonta ba ya Roketa ta so Marigayi mansur Saboda Soyayyar datake yimai da Auransa da Rumana da abubuwan da suka Faru Rumana tana mgana tana kuka ta Karishe da Fadin"Hatta da Hawan jinin Daya samu da Ciwon Zuciyarsa Dalilin Diza ne Daddy..Ya mastur ya wahala saboda Soyayyar Diza,saboda Mansur yasa ya Boye abun a ransa bai Taba Fadama kowa ba, Kada wannan karon ya rasata in ya kara rasata zamu rasa gabadaya ne kamar yadda muka rasa Mansur kuma Faruwar haka tamkar bayyanar wani wawaken Rauni ne wanda har Abada bamai iya Cikeshi Daddy..!
Ta fada cikin kuka sosai kamar Zata Shide ba ita datasan Labarin ba Mommy da Daddy da yau suka taba ji haka suke Sharan kwallar Tsausayin Mastur da Dattakonsa,Ballatana Diza da kafafunta suka kasa Daukanta ta Sulale nan kofar Falon Mommy Tana Kuka Lokaci Daya tana Toshe bakinta da Hannayenta kada kukanta ya Bayyana ammh Labarin da Rumana ta bada yasakata cikin wani yanayin da bazata iya Fassarashi nan take ba.
Bata sani ba na Tsausayin Mastur ne ko matsananancin Soyayyarsa.?kawai ita dai taji Zuciyarta na Bugawa da Sauri da Sauri kanta na wani Sarawa.
Achan falon kuwa Daddy ne ya Mike da Sauri yana Share kwallar Tsausayin Mastur yace"Lalle ya cika sunan da iyayensa ke kiransa BABBAN MUTUM..Ku taso..Maza mu je gidan Habibu kowa yaji wannan al"amarin..Al"amarin da ko a mafarki bamu Taba Tsammani ba Asiya sako mayafinki ki kubiyo keda Rumana ki ma Diza mgana ta taho itama..! Yake fada yana kama Hanyar Ficewa saboda Halin Dayake ciki Diza tayi kokarin Mikewa Dakyar suka Kusan cin karo da Daddy ganinta Tana kuka yasa ya gane taji komai kai ya gyada mata yana Fadin"Ki kibiyo su ku taho Tare..!
Daga haka ya sauka kasa a Sarssaafa kamar zai tashi Sama Diza Dakyar ta Rufamai Baya zuwa Daki ta iske Mansur karami bai tashi Daga barci ba ammh bata Cikin Hayyacinta haka ta Daukesa yana barcin ta saba shi a Bayanta ta Goya tana ta Sharan kwallah sai ga Mommy ta Shigo Ganinta Tana ta Faman Sharan kwallah sai ya bata mamaki kafin Tayi mgana Diza ta gyada mata kai Tana Fadim"Naji komai Mommy..Naji komai..!
Take Fada Tana Hawaye,Mommy ta Riko Hannunta Dake Dauke da mayafinta tace"Ki daina kuka Diza..Taho mu tafi Rumana na jiranmu da Daddy..!
Ita ta jawo hannuwanta Har Falon inda suka Tadda Rumana Tsaye Tana jiransu kallon kallon sukayi Tsakaninta da Diza alokacin Kowa yaji kishin kowa Musamman Diza da Rayuwarta Daman Rumana abokiyar kishinta tace,Ita kuma Rumana wani iri taji acikin Ranta na Diza Mastur yake so ba ita ba Akwai wannam Kishin acikin Idanuwanta.
Haka suka karisa gidansu Hajja Jiki a sanyaye koda suka je har Baba Habibu ya Fito yayi ma Daddy Jagora zuwa Cikin Falon,Hajja na gefe zaune Ayya ma Haka su kadai ake jira suna Shigowa zama kawai Sukayi Daddy ya kalli Rumana yana Fadin"Rumana maimaita Abunda kike zomin dashi yanzun nan..!
Rumana bata yi kasa a gwiwa ba ta Shiga maimaita komai Daki Daki,kafim ta gama Hajja ta Fashe da kuka Tana Fadin"Biri yayi kama da Mutum..Baban Mansur ka Tuna Bayan Bikin yaranan nayi maka Zencen Babban Mutum..?
Baba Habibu da gabadaya Jikinsa yagama yin sanyi yace"Tabbas..Kin min Zencen gabadaya ya sauya ya Rame.
yanzu ya kara zama mara som mgana da Hayaniya kikacemin kina ganim kamar wani abu na Damunsa nace miki kada ki Damu kanki Lafiyansa lau..Wlh nima alokacin nace miki Hakane kawai ammh ni kaina nasan ya Chanza ammh Tunda har ni da kaina na Tambayeshi meke Damunsa yace bakomai sai kawai acikin Raina na Cigaba da Tayasa addu"a Allahu Akbar Allah ya jikam Mansur da Rahma..Tabbas Mastur yayi Rashi..da sun Rayu da juna da An samu Nagargartattun yan"uwa masu Sadaukar da komai nasu Domin junansu na Tabbata da Mansur yasan Mastur na son Hadiza Wlh Tallahi shima bazai aureta ba zai ce ne ya bar ma Dan"uwansa sai dai shi Lamarin Ubangiji muna namu Allah na nashi ne..Tabbas Rabon samun Mansur karami yasa akayi wannan Auran Rasuwar mansur kuma wata aya ce nacewa Akwai Rabon Zama Tsakanin Mastur da Hadiza Tabbas bazamu ja da Hukuncin Allah ba..,!
Ya karishe fada yana Saurin Dauke Hawayen Daya kawo masa Ayya ma da Jikin Tsufanta Tana Sharan kwallah tana Fadin"Allah yayi maka Rahma Mansur..Habibu Alhaji ku aura ma Megidana Hadiza ko bai ce yana Sonta ba Duk Duniya shi kadai zai riketa ita da mansur karami Cikin aminci kuma na Tabbata Mansur zai samu salama Cikin kabarinsa sanin Hadiza da Mansur karami bazasu Tagayyara ba!
Kowa sai da kalaman Ayya ya sakashi kuka barin ma Diza da Tunda aka Zauna take kuka,Mansur karami ya tashi ganin Mamansa na kuka shima sai ya Fara Saukoshi Tayi ta Rumgume Tana kuka,Rumana kuwa kanta na kasa Cikin Dashewar murya tace"Ayanzu haka yana nan gida na barsa Ba yadda yake..Tun jiya Daya ga Diza da Sagir..Yau da safe har Aman jini sai da yayi..!
Gabadaya Falom aka Dauki Salati Daddy ya Mike da Hanzari yana Fadin"Habibu ku tashi muje Chan gidan nasu Kada shima mu Rasashi indai Hadiza ce na bashi ita Halak malak..Ku tashi mu Tafi Gabadaya muje mu Hada hannunshi da na Hadiza Domin ya Tabbatr da ita din kaddara ta Riga ta Hadasu waje Daya..!da sauri kowa ya mike Hajja batama Tsaya Daukan Hijabi ba Zanin atamfanta ta yafa ta kama Ayya datake kokarin mikewa ta saka mata Hijabi suka Bi bayansu Daddy da suka Fita Tuni.
Rumana ita ta Tuka matan Shi kuma Daddy da Baba Habibu da Mansur karami Dake hannunsa suna Motar Daddy.
Basu ci burki ko"ina ba sai Haraban Gidan Su Rumana Dake Lowsoct,Suka paka Motocinsu Cikin Hanzari suka Firfito Rumana ne kan gaba ta Jagorancesu zuwa Shashensu ba wanda yayi Tunanin Tsayama a Falo Gabadayansu Cikin Bedroom din suka Nausa Rumanace ke gaba suna Binta Sahu sahu a baya bamai mgana ammh kowa kagani Kirjinsa na Bugawa.
Suna Shiga suka iskeshi kwance ya Lumshe idanuwansa ba barci yake ba Yaji Sallaman Rumana sauran Sallaman ne bai ji ba saboda ba suyi sallama ba Hankalinsu baya jikinsu gabadaya su Gaban gadon suka Tsaya Banda Diza Dake Chan gefe Tana kallon Mastur yadda rame dare Daya ya koma haka.
Rumana ce ta Durkusa ta Dafa Hannayensa Tana Fadin"Ka Bude idonka..Naje na samo maka mganin Mtsalarka tare nake dasu Daddy har da ita kanta Dizan Daka ke kwance saboda ita..!
Kamar a mafarki yaji kalaman Rumana cikin mamaki ya Shiga Bude idanuwansa Karaf ya fara saukewa kan Daddy da Baba Habibu,sai Mommy da Hajja, da Ayya Dake gefe Tana Sharan kwallah sai Daga gefe kuma Diza ce Take ta kuka ya kasa Sauke idanuwansa Daga kanta yana jinsa kamar Zuciyarsa Zatayi Tsalle ta Fito waje gefe Daya kuma yana Jin mganar Rumana kamar a mafarki.
Daddy ne ya zauna gefen Mansur din ya saka Hannu ya Dagosa yana Fadin"Tashi Tashi..Ba a son Namiji kamar ka da Ragwanci..Abokan aikin ka zasu yi maka Dariya in sukaji Labarin Saboda mace kake kwance Zaka Mutu.Maza ka Mike indai Hadiza ce na baka ita Halak malak..Zan Daura muku aure yau bayan Sallar azahar da yardan Allah..!
Shidai gashi nan zaume ne yana bin kowa da kallo mganganun Daddy da Rumana kamar bai Fahimci ina suka Dosa ba sai dai kawai yayi shuru bakinsa yayi Nauyi Mansur karami ne yake ta mikamai hannu yana kiran Baba sai Baba Habibu ya mikamai shi ya karbeshi,kana Baba Habibu ya Dafa kan Mastur din yana Fadin"A gaishe da Babban Mutum..Banda abunka ai Hadiza Takace meyasa bakayi mgana ba Tun Fari..? Tunda Kaddara ta Dauke Dan"uwanka kai ya Dace ka aureta Daman ka zama Bangonta Mastur.!
Mastur da sai yanzu ya samu Damar mgana Cikin wani Nauyin baki yace"Baba..Waya fada muku wannan mganar..?
Kafin yayi mgana Rumana tace"Nice..Na karanta komai acikin Diary dinka Daka Rubuta Lokacin Danaje Porthercourt na Zauna Dakai..Tun lokacin nayi alkawarin wa kaina Zan samo Sillan da zaka samu Abunda kake so..So yayyata dakai bazatayi Sillar da zan kasa Taimaka ka samu Abunda kake so ba..!
Kura mata ido kawai yana kallonta Lokaci Daya Zuciyarsa na Budewa da Kofofi kofofin yarda da Aminci da Soyayyar Rumana wanda bai san Daga ina hakan yake Faruwa ba Hawayenta ta Share tana Fadin"Insha Allahu yau Zaka Zama angon Diza...Daga barayina nayi maka alkawarin bazaka Taba Samun wata mtsala ba sai dai Kuskure na Dan Adam..!
Gabadaya sai ta bama kowa Tsausayi a wajen Mommy ta Rumgumota Jikinta Tana Fadin"Allah yayi miki albarka Rumana..!
Acikin Zuciyar Mastur kuma yace"Ameen..Allah ya Biyaki Rumana..Allah kada ya kamani da Hakkin Sabamiki koda da Rana Daya..!
Yake fada Cikin Ransa Lokaci Daya yana kallonta itama shi take kallo Tana Dariya sai Lokacin ta waiga taga ba Diza Mastur yaga Lokacin Data Fita su Hajja Falo suka Fita suka bar Shi da Baba Habibu da Daddy suna ta mai Nasiha da nuna yadda Al"amarin Allah yake.
Diza kuma suna Falo tare dasu Mommy,Kuka kawai take yi kowa ya kasa gane inda ta dosa Su Daddy Basu dade ba suka Fito sai ga Mastur Kan kafafunsa ya Rakosu yana Rike da Mansur Karami har bakin mota suka Rakasu shi da Rumana inda Daddy ya kara Jadadda Bayan Sallar Azahar za"a Daura auran Diza ta Fara shiga Mota Mastur bai tsaya Fahimtar yanayinta ba Rumana kawaiyake kallo yana aika mata Godiyarsa da ido Mansur karami yaki Bin su Mommy sai Rumana tace abarshi in zasu zo zasu zo dashi.

Sai da Motarsu ta Fice daga Haraban gidan kana suka koma Cikin gida suna Shiga Falon Mastur ya kama Rumana da Mansur Tare ajikinsa Kamkam Lokaci Daya yana sakin Numfashi Cikin wata murya yace"Kada Allah ya kamani da Laifin kuntata miki Rumana..Allah ya bani ikon kwatanta miki Dimbin Alherinki gareni..Nagode..!
Yake fada sai ga Hawaye Itama Kukan take ammh Jinsa yana kuka yasa ta Dago Tana Share masa Hawaye tana Fadin"Soyayyar da nike maka ta gaskiya ce..Shiyasa nake Zaban Farincikin ka saman nawa akoda yaushe..!
Kara riketa kawai yayi ya kasa mgana har na tsawon wani Lokaci,kafin ta Zare Jikinta Tana Fadin"Muje ka Shirya Lokaci ya kusa..!
Daganan bedroom suka Nufa,duk yadda taso ta Zille bai barta ba sai da yaja Ra"ayinta suka Mori junansu Aranar Rumana Tayi kuka sosai
Soyayyar da Mastur ya nuna mata bata Dauketa anata ba,ta Dauketa a Saboda samun Diza ne ya Raba Farincikinsa da ita ayau shiyasa tana wanka Tana kukan,kukan tsausayin kanta da kishin Diza.
Ammh haka ta Daureshi ta Tayashi Shiryawa cikin Sabbin Kaya Shadda Fara Tazarce Dinkin Zamani,Da Hula zanna Bukar sai Agoginsa baki na Fata,da Rufaffan Takalminsa na Fatar Damisa baki,Ita ta Feshe shi da Turaransa na azzro Visit.
Tana kokarin maida kwallarta Ta shirya Mansur karami Cikin Kananan kaya masu kyau wanda ta Siyamai da kudinta,itama taci Wani Rantattsen Leshi Riga da Zani Tayi kyau duk da batayi kwalliya ba.
Duk kokarin Mastur Daya Fahinci Halin da Rumana take ciki bata bashi Dama ba Har suka bar gidan zuwa Hanwa.
Koda sukaje sunga abun mamaki Yan maruka har sun iso su Sakina da Mariya da Inna Zainaba da Baba Sule da yayyinsa guda Biyu ashe Daddy ya kirasu ya gaya musu Mutane anguwa ma duk sun Taru saboda Baba Habibu ya kira Kawu Usman ya gayamai shi kuma ya dunga gayama Mutane.
Gidan Mommy ma Makota duk sun Shigo Mommy ta kira kawar Diza Meena ita ta Taimaka mata tayi wanka ta kira Hauwa tazo Tayi mata Simple makeup,Diza gani take kamar karya ne,yau ita Zata zama matar Mastur Rumana sai da ta shiga ta gaida yan maruka kana ta kariso gidan Mommy kowa ya ganta sai sska mata albarka yake yi,Ta saki Jikinta Ita ke ma kara Lallashin Diza Ta Fuskarta bata nuna wani Hali take ciki ba.
1:30pm na Ranar Laraba aka Daura auran Mastur da Diza kan Sadaki Dubu Hamsin Daddy ya zama Waliyin ango Baba Habibu ya zama waliyin Diza abun mamaki hatta da Sagir ya Hallaci Daurin auran kuma ya mikama Mastur hannu sukayi musabaha ya tashi murna yana Fadin"Daddy ya kirani yana bani Hakuri..Yana gayamin kai ne..Nace na janye zaka fini Xama wani Jigo ga Hadiza Allah baku zaman lafiya..!
Ya amsa mai da Ameen Daganan Cikim gida kuwa Rumana tana jin an Daura aure ta shige Tiolet din Diza Tana Boye kukanta itama Dizan sai ga hawayen Farinciki suna kwaranyomata,
Kiran Umma ne ya Sa ta Fito Daga Tiolet bayan ta wanko fuskarta ta Daga kiran Umma Nasiha tayi mata tare da alfahari da ita sun Dade suna mgana kafin suyi sallama tace zata zo In Dizan zata tare nan da Sati Daya Inji Daddy daya kira Abba ya Fadamai komai Rumana sai taji ta cire komai aranta Tana da yakinin Abunda Tayi shine Daidai.
Wayarta ta Duba taga sakon Mastur

*Tanque..Thanks so Much Mrs Dcp Mastur Habib Dogowa..Zuciyata tana Girmama Karaminciki..Allah yayi miki albarka Rumanata..*

Sakon ya sakata Dariya da kuka Lokaci Daya acikin Ranta ta Furta.."Naji Dadi..Ko bakomai nasami Albarkacin Diza..!




*Shakira..*
1/1/22, 18:55 - Maryam Badmsi: *SS....38*

*Kibiya ki karanta Cikin Salama da Aminci Mace mai aji bata jiran Abun sata mallakan komai nata take yi,09069067488*

"Rumana Tayi kokarin Danne Abunda take ji yana kokarin Taso mata acikin zuciyarta,Ta nuna komai ba komai ba ta Fito aka Cigaba da Hidima da ita ta Rumgume Diza Tana Share mata Hawaye Kowa awajen Sha"awan Rumana yake yana saka mata albarka.

Ba laifi anyi Sha"ani Sosai duk da ba Ranar Diza zata tare ba ammh yan"uwan da suka zo an taru an Taya Diza da Mastur Murna Mommy da Hajja duk sun gayyaci Makota saboda Daddy yace Biki Daya za"ayi daga wannan bazaka akara Taruwa ba Ko Mutum Dayane zata raka Diza Dakin Mijinta Sati Dayan ma Dayace Kafin ta taren Shi Mastur din ne ya roka saboda yana soyayi ma Dizan kaya ya kuma bata Lokaci Tayi nata Shirin sai kuma mganar inda Zata Zauna wanda Tunda ya kawo mganar Daddy yace Sashenta zata zauna inda Ta zauna da Mansur ba Bukatar wani abu kuma
Daddy ya riga ya yanke Hukunci bamai jadashi..Mastur ma bai ce komai ba Sanin baida wani Muhalli a Hannunsa ammh yana saka Ran nan gaba Zai mallaki gidansa Inda Zai Hada matansa waje Daya da yardan Allah.
Aranar anan ya bar Rumana ta kwana tunda tace ya barta ta kwana Duk da yaso su tafi gida ammh Ta Nuna ya kyaleta ta kwana sai ya barta ita kuma ta Gujemai ne saboda bata son Gangar Jikinta da Zuciyarta ta saba da wannan Sabon Mastur din Bata son ta Rika Raban Alfarman Soyayyar Diza Zuciyarta tana Raunana sosai.
Tare da Diza suka kwana,Mansur karami kuwa yana gidan Hajja wajen su Sakina Tunda suka zo yana Hannunsu.
Sai washegarin Rumana ta koma Gida ta Shirya Mastur ya kaita Wajen aiki ssi nan nan yake da ita ko Kuda baya so ya Tabata Mgana Daya Biyu sai yace Nagode Rumana Allah yayi miki albarka Sai dai Tayi Mirmishi kawai tace Ameen.
Bata san a ina Aisha bala ta samu Labari ba Tana zuwa tayi mata Zencen abun ya bata mamaki sai kuma batayi mamaki ba abun Duniya Baya Boyewa Data Tambayi Aishan a ina taji ba, sai tace mata a Social media Tagani Matar marigayi Honourble Mansur Sulaiman ta Sake Auran Dan"uwansa Dcp Mastur Habib Doguwa,Rumana batayi mamaki ba Tunda yanzu komai ya koma Social media.
Bata gama mamaki ba sai da Basma ta kirata Tana Fadin"Ruma me nake gani haka.
? Mastur mijinki ya auri Diza Matar marigayi..?
Rumana Tayi kokarin Danne Abunda ke Damunta tace"Ke kuma a ina kika ji Labari...?
Basma Tace"A shafin Diza na gani kinsan ina Following dinta a Intergram,yanzu naga posting dinta ta saka Alhamdulillah Finally Mrs Dcp Mastur Habib   Doguwa..!
Rumana ta Runtse ido Tana kokarin Daidaita kanta bata ji mamaki ba saboda Taji labarin Daman chan Diza Mastur taso ba Mansur ba kuma Ta karanta a Diary din Mastur Daman kukan Datakeyi ai ta sani na Farinciki ne bana Bakinciki ba ammh bakomai ita Tayi haka ne saboda Soyayyarta da Mastur in batayi haka ba kila Daga ita Har dizan Zasu iya rasa Mastur din.

Rumana tace"Da gaske ne..Jiya aka Daura auran Zata tare nan da kwana Shida ina Fata zadai ki zo ko Kawata..? Wani Dogon Tsaki Basma Taja Kafim tace"Allah ya kyauta..Ke kam kiyi ta wani abu kamar wata sakara..Yanzu kika yarda akayi miki kishiya ko Haihuwa baki Taba yi ba Rumana... ? Gaskiya hatta da iyayen Dizan basu kyauta ba da iyayensa da suka kasa Nuna mai hakan bai dace ba..!
Rumana na jin haka Tayi saurin Dakatar da Basma Tana Fadin"Eh naji ni Sakaryace..Saboda na bama Mijina Dama yayi abunda Allah ya Hallitamai..? Ba ruwansu Mommy a wannan mganar ballatana su Hajja Kuma kada ki manta Bayan Mastur banga wanda ya Chanchanta Ya auri Diza ba shine yafi Dacewa..Koda ace yau Mansur Zai Dawo Duniya zuciyarsa Zata fi samun Salama akan Diza ta auri wani na waje..!
Daga haka kawai Rumana ta Datse kiran Tana kokarin maida kwallarta Bata so Tayi kuka Saboda Aisha na wajen ita kanta sai kallon Rumanan take batadai yi mata mgana ba ammh ita,kanta taga Wautan Rumana da zata bama Namiji goyon bayan yayi mata Kishiya.
Har ta tashi bata bama Aisha Fuskan da Zatayi mata wata mgana ba Ko Mastur Dayace ta kirashi in sun tashi bata kirashi ba Motar Haya ta hau zuwa gida.
Koda ta koma Baya gidan acikin Ranta tasan yana Hanwa Wata Zuciya tace yana wajen Diza dai Rumana ta kasa Sarrfa kanta bata san sadda Ta fada kan gado Tana gunjin kuka ba Zuciyarta TaRaunana sai take jin Nadaman meyasa ma ta Fadi mganar Batayi Shuru da bakinta ba Tunda Shi yaki ya Furta..?Shedan nata saka mata Wasi wasi Ganin haka yasa ta Daga waya ta kira Umma ta saka mata kuka,Umma tasan Zafim Kishi ita kanta Datake uwar Rumana Har kawo yanzu ba"ayi mata Kishiya ba Tana matukar Tsausayama Rumana Sai bata nuna mata ba Ta Shiga Lallashinta da bata baki da Nasihu har tayi shuru Zuciyarta Tayi sanyi Tayi ma Umma alkawarin bazata kara Sakama kanta Damuwa ba.
Wayar da sukayi da Umma ita ta Taimaketa taji ta Wasai Tashi Tayi ta Shiga Kitchen Tayi Dinner kana tazo Tayi wanka ta Fito kenan Taji kiran Mastur Har ta katse sai tabi bayan kiran Tana Dagawa yace yana Asibitin Chika ta Fito su tafi yana ta kiranta Bata Daga ba sai kuma taji bata kyauta ba Cikin Sanyin murya tace Ta dawo Gida Tunda bata jin Dadi Dan jim yayi kafin ya kada kai ya yanke kiran duk sai taji ba Dadi.

Sai bayan mangariba ya Shigo Gidan,yanayin yadda yaga Rumanan sai Fargabansa ya Ragu Tun jiya yake Tunanin bai kyauta mata Ba Tahowar datayi Bata kirasa ba sai yaji ba Dadi ammh Yadda ta tsala kwalliya ta Tareshi sai ya kara Sanyayamai Jiki yana Tunanin mata irin Rumana sai an Tona Har ta rakashi Yayi wanka ya sauka Saukakkaun kaya suka Fito Falo sukayi Dinner Bai daina kallon Rumana ba yana saka mata albarka Har taji kunya ma duk ya Isheta Taji duk wani Fargaba ya saketa ko da wannan albarkan ta Tsira ta Tabbata ta Rabauta.
Tare sukayi Sallar Isha"i yajasu Jam"i da Shafa'i da wuturi,kana suka Saka kayan Barci suka kwanta Mastur na kamkame da Rumana kamar wani zai kwace mishi ita Yana Shafa kanta zuwa Bayanta yace"Ruma..!
Bata Dago ba sai ta amsa Kiransa Muskutawa yayi yana Fadin"Shawara nake so muyi game da Kayan da zan yi ma Diza..? Ya kike ganin Tsarin zai tafi..?
Rumana ta gyara Zaman kanta Saman kirjinsa Tana Fadin"Kawai ka bata kudi ta Siya abunda take so..!
Mastur yace"Kina ganin hakan zai fi..?
Ruma tace"eh nifa aganina Ammh dai kaje ka sameta kuyi mgana kaji Ra"ayinta..!
Kara riketa yayi kafin yace"is ok..Basai na sameta ba Hakan za"ayi..Kema kudin zan baki kenan.?
Rumana ta Dago kanta Tana kallinshi kafin tace"Ni basai ka bani komai ba..Soyayyarka kadai da yardanka nake nema in ka bani wannan kagamamin komai..!
Kallon Juna suke ido Cikin Ido ta Dan Hasken Dake Shigowa ta window,dayake sun kashe Hasken Dakin,Rumgumeta kawai yayi yana jin wani yanayi na Shigarsa Cikin sanyin murya yace"Indai wannan ne kin gama kuma kin Samu..Ammh kada kice bazaki karbi Komai ba Zan ba ku Miliyan Daya ku Raba keda Diza kowacce Dubu Dari Biyar..!
Da sauri Rumana tace"A'a ni bazan karbi Dubu Dari Biyar ba Tayi yawa..Me ka Rageni dashi..?
Ai ni ba Amarya bace Saboda haka Dubu dari Biyi zan karba Shima don ka mtsa ita Dizan sai ka bata Dubu Dari Biyar din..!
Kamar bazai tanka ba sai da tace"Kaji...?
Kai ya gyada mata yana Fadin"Shikenan itama Dizan Dubu Dari Biyun zan bata.."Tasotayi mgana ya hanata Lokaci Daya ya Hade bakinsu Waje Daya yana kokarin mantar da ita Duniyar da suke Ciki itama Batayi kasa a gwiwa ba ta mikamai Ragamar Rayuwarta.
Abunda ke saka Rumana kuka Tana Kishin Diza tazo ta Dandani Zumar Mastur wacce ya Fara Dandanamata mai saka ta kamar Tayi Hauka tana Kishin Diza tazo ta san wannan Zumar ta so ace ita Zata Cigaba da Dandanan zumar har karshrn Rayuwarta sai dai ina Kaddara ta riga ta kawo Diza cikin Rayuwarsu.
Kwana sukayi Farantama Ransu Kamar wadanda suka Shekara Cikin Mayen son juna.
Yau ma shi ya kaita asibitin ya kuma Bata Atm dinsa yace ta Cira kudin Tayi amfanin da Zatayi Dashi bata so Tana mai gardama Ta karba ta saka Cikin Jaka tace sai ta Dawo anjuma Tare zasu Shiga kasuwar ya Taya ta Zaban kayan yaji Dadin haka yace in tatashi ta kirashi a waya Ta sauka Tana Dagamai Hannu Shima yana Dagamata.
Daganan Hanwa ya tafi sai daya Shiga ya gaida su Hajja itama Dubu 100k ya Zube mata ita da Ayya yace su siya abunda suke Bukata,ya bama yan Maruka 50k yace su kai ma Baba Sule Tunda ya koma shi Tun washegari su sakina ma haka ya basu kudi Inna Zainaba bazata koma ba sai Takai Diza Daki Sakina ne da Mariya suka koma Shi yakai su Tasha suka hau Mota Daganan ya shiga gidan Daddy Mansur karami na Hannunsa Daman wajen Mardiya ya karbeshi Koda ya Shiga Mommy bata nan ta Fita ita da Daddy zasu gaisuwan Rasuwar matar mai Taimaka ma Daddy a Campanysa Diza kadai ya Iske itama Tana Shirin Fita ne Ta kira Mastur din da Safe Tace mai Tana so ta Leka Catering dinta Tunda Mommy tace sai ta Kirasa yace mata ta jirashi gaahi nan zuwa.
Basu tsaya ba yace ta Fito ya kaita Diza kanta yayi girma sosai taji Dadin haka Duk da Tun bayan auran nasu basu sami kebewa ba sai yau.
Suna tafe Cikin Mota bamai mgana Mansur ne ke wasansa kan Cinyar Mastur din da Hamkalinsa ke wajen Tuki,baya so ya rika yawaita Kallonta kada ya takura ammh duk wani Motsinta yana kallonta ta gefen idonsa.
Har suka iso Haraban Catering din bai ce mata komai ba abun da ya bata mamaki ya akayi yasan Catering dinta..? Abunda bata sani ba Tun Kafin Daddy ya Bude mata yayi Shawara dashi kuma atakaice ma shi yace Daddy ya Siyan mata wajen.
Sai da yayi parking kana ya Dago yana kallonta ita kuma Duk sai taji wani iri Jikinta na wani kyarma wanda bata Taba jin irinsa ba
Cikin Sanyin muryansa yace"Menene Shirin ki  game da Tarewar..?
Diza Tayi shuru kamar bazatayi mgana ba sai chan ta Numfasa tace"Bani da wani Shiri...Shashena Kawai su Anty Hadiza zasu zo suyi gyara da abubuwan da ba"a rasa ba..!
Kai tsaya yace mata"Bangaran kaya fa..?
Sai da ta kalleshi kafin ta Dauke kai Lokaci Daya tace"Bana Bukatar wasu kaya..Duka Duka yaushe ka dinkamin Sabbin kaya..? Bata Numfasa ba ya bata amsa da cewa"Wanchan Dabam...ki Duba wayarki na Tura Miki 200k kiyi amfani Dashi..!
Dagowa tayi tana Kallonshi Tama rasa bakin mgana Shima Kallonta yake yi Cikin wani yanayi yana ji kamar mafarki ne Diza ba matarsa bace Cikin karfi Hali yace"Kada ki makara..!
Yunkurawa Tayi da Jakarta Tana Fadin"Nagode Allah ya kara Budi..!
Da Ameen ya amsa Lokacin Data Bude Murfin Mota zata Fita Taji yana Fadin"Karfe nawa Zaki tashi..?
Dan jim Tayi kafin tace"Kamar 2pm haka..! Kai ya kada kafin yace"Ki kirani.."Daga haka ta amsa mai kafin ta Fice Daga Motar mansur karami na Daga mata Hannu bai ma Damu da ita ba Tana Wajen har ya juya ya Fice Daga Haraban haka Diza ta Fara takawa Zuwa Cikin Catering dinta Mirmishi na Subuce mata Tana jinta kamar Tana yawo kan gajimare Saboda Farinciki.
Haka take cikin Farimciki Ma"aikatan ta Kowa ya ganta yasaan Diza tana Cikin Farinciki Saisuka Danganta hakan da Auran Datayi Domin suma sunji Labari sai Faaman Tayata Murna suke sai dai Tayi Mirmishi kawai.
Karfe uku na Rana ta Kira Mastur bai ma Daga kiranta ba Sai bayan Wasu Mintina ya kirata yace yana Waje koda ta Fito wannan karon Tare da Mansur karami suka Dawo Daukanta Basu yi mgana ba Har yakai ta Gida ya ijiye Daganan ya juya zuwa gida zai yi wanka ya jira kiran Rumana Daaman bayan ya Dawo Daga kai Diza Shashensu shi da marigayi Mansur ya Shige shida Mansur yana ta Debemai kewa da gwarancinsa.

Karfe biyar da wani abu Rumana ta kirasa yaje ya Daukota Mansur karami Wajen Hajja ya kaisa yace Mardiya tayi mai wanka,Yaje ya Dauko Rumana Daga nan kasuwa suka Shiga sabon gari suka samu Shagon Kayan mata kama Daga Atamfofi zuwa lesuna da Takalma Mastur ya taya Rumana zaban kaya masu kyau da Takalma da Jaka da Mayafai masu Tsada Daganan suka Shiga Shagon kayan kwalliya shima ta Siya,harda Shagon sai da kayan maza ta siya ma Mastur Boxers da Singlet da kayan barci da Turare,sai Mansur karami data Siyama kaya ta kashe kudi sosai Mastur yace ta Biya acikin Kudinsa Duka tace kudin kayan data Siya zata Biya da kudin Daya bata ammh wanda ta Siyamai da Mansur karami ita zata Biya ta siyama Hajja da Aiya da Mommy,Duk cikin kudinta wanda Abu ke Biyanta Mastur natayi mata Dariya yana Tsokananta da tafisa kudi ita dai Mirmishi kadai take yi basu Dawo gida ba sai Dare har Cefanan kayan Girki Duk Rumana ta siyo abunta Shi dai Mastur Binta yake kamar Rakumi da akala,yana Rike da wasu ledoji Sauran kuma yan Dako suka Daukan musu.
Ana kiran Isha"i suka Shiga gida Basu yi komai ba Salla suka Fara Gabatarwa kana Rumana ta Shiga Kitchen ta sama musu Abunda Zasu ci Tana da Miya sai ta Dafa Musu Farar shinkafa ta Hada musu Salat,da lemon kankana kusan Rabin aikin tare Sukayi da Mastur Duk da ta Hanashi ya nace yaki Fita Tare sukayi aikin suka Dungumo saman Dining suka ci abinci Mastur ya Ciyar Da Rumana itama ta Ciyar dashi bayan sungama Tare suka Shige Bedroom dinsu sukayi wanka Tare suna ta Soyayyarsu,Sun manta da Wata Diza.
Bayan sun Fito sukayi Shirin barci Suka kwanta suna ta Hira Domin Shakuwa Ta shiga Tskaninsu Sosai da kaunar junansu Basu sani ba,Sun Dade suna Hira kafin su gangara da jumansu wata Duniya Bayan sun natsa ne suka je suka Tsakarkake Jikinsu suka kamkame juna Barci mai Tarin Dadi ya kwashesu.
Washegari hana Rumana zuwa asibiti yayi sai da ta kira waya Wuni sukayi suna cin Soyayya Rumana ta gama yardan ma koda ki taci albarkacin Diza ta godema Allah ta samu kulawar Mastur koda ba Soyayyarsa ba.
Sai yammah suka Fita Takai Dinkuna har da nasu Hajja kana suka Dawo Ranar Diza ko Motsin Mastur bata ji ba ta Damu ta kirashi Sau Daya bai Daga ba sai ta Kyaleshi shi kuma yaga kiranta ammh Suna Tare da Rumana bayaso yayi abunda zai bata mata Rai kwata kwata Shiyasa ya sa wayar a Silent.

Ana saura kwana Biyu Tariyan Anty Hadiza ta iso ita da Umma Tafiyan Jirgi sukayi Daga kaduna suka Hawo Motar Haya suka kariso Zaria Umma tazo ma da Rumana Kayan gyaran Da kuma Turaruka Harda Diza Gabadayansu,Koda suka iso Rumana na asibiti sai dai Data Dawo nan Ta sauka,sai Dare Mastur ya dauketa suka koma Gida Washegari kuma Umma da Anty Hadiza da Inna Zainaba da Balaraban Usman suka zo suka gyara Shashen Diza suka Share suka gyara ko"ina Cikin Kitchen suka Tsaftace suka Fitar da abunda ya Lalace Daddy ya bada kudi Aka yo Cefene aka Cika su a Fridge komai da yaji Diza kuma Ranar taje ta amso dinkunanta Daga Online ta siya kayanta nata dana Mansur karami Nata takai Dinki kwana Biyu har an Dinka mata Masu kyau dataje ne ma Taga Dinkunan Rumanan telan nata yake Fadamata kayan Rumana ne tare suka kawo da Mastur sai gashi Diza taji Haushi Saboda Tun Ranar daya kaita Catering dinta bata kara ganinsa ba Sai Jiya Shima sanda ya Shigo Gaida su Umma da kiran Rumana Lokacin ta gansa Daga Nesa Abun na Damunta ammh sai ta Nuna komai ba komai bane bata so Shedan ya Fara Tasiri akanta Tasan Tana da Kishi sosai ammh Bata so Ta kara Nunashi kan Rumanan.
Washegarin aka tashi da Tariyan Dizan ba wani Taro akayi ba ita kanta Dizan bata gayyaci kuwa ba sai yar"uwarta Meenal ko kwalliya hana Hauwa zuwa Zatayi Tadai saka kaya masu kyau Tana shiga Tana Fita Rumana nan gidan ta Dawo itama akayi Sha"anin da ita,itama ta Shiga ta Fita ita da Mansur karami Diza ma bata sakamai kayan Data siyamai Rumana ce ta Sakamai nata wanda ta siyamai haka Mommy da Hajja da Umma wanda Rumana ta siya musu suka saka.
Bangaran kayan gyaran da Umma tazo musu dashi Diza Tasha nata,Harda wadanda Anty Hadizan tazo mata dashi Rumana tana shan nata ammh a hamkali sanin Diza zata karbi Ragamar Miji Tukunna Rumana tayi gayyah Aisha Bala tazo mata sai yammah Tatafi,Ango Mastur kuwa yana Chan sai aranar ya kira Acp Saleem kumo ya gayamai Halin da ake Ciki ya Dinga zaginsa yana Cemai bai da kirki Mastur dai ya bashi Hakuri Daga karshe suka Rabu kan sai sunzo Shi da Madam bayan yayi mai Fatan alheri,wuni yayi acikin Gida yana kewar Dan"uwansa Yayi kuka sosai Lokaci Daya yayi mai addu"an Rahmar Allah Gashi Rumana taki zama Tatafi ta barsa da kewa abinci kadai tayi mai kafin ta Fita saboda kada ya Zauna da yunwa.

Karfe 6pm na Rana da Daddy da kansa ya kawo Diza Dakinta a karo na Biyu,Tare da Rakiyar Umma da Anty Hadixa sai Rumana data Taho a Motarta ita Dauko Meenal da Inna Zainaba da Mardiya ssi Balaraba,Har shashen suka shiga bayan Daddy yayi ma Diza da Rumana addu"an zaman lafiya kana ya Fita ya barsu anan su kansu su Umma nasu Nasihan suka Dora Duk da sunyi Daga Gida Diza kuka Rumana kuka Ba wanda yasan Dalilim kukansu Rumana Tana kukam Wani Nauyi ne Daya Tokare mata Kirji Na yau Zata bar ma Diza Mijinta ita kuma Dizan Tana kukan jin wani iri da kuka Rashin Mansur,Sai kuma Nauyin Rumana Tana Fatan Kada Allah ya Kara Doramata Kishin Rumana,Tun ada ma da basu Hada Miji ba Ballatana yanzu da Zasu Zauna karkashin Ihuwa Daya.
Kafin Isha"i duka sun watse Fita sukayi bakin Titi suka samu Motar Haya,suka Hau zuwa Hanwa Tunda daddy ya koma Mastur kuma yana Shashen Rumana bai Fito ba yadai ji Shigowarsu,Ya kira Rumana yace tazo tace ba yanzu ba,Zata Shigo ba sai Baki sun Tafi,Mansur karami yana Hannun Mommy ba"a zo dashi ba Sai da suka Tafi kana Rumana Tayi ma Diza Sallama tace Zataje ta Shirya angon nata Zata Rako mata shi yanzu..Diza Mirmishi kawai Tayi Tana Danne Abunda ke Cikin Ranta.

Koda Rumana ta koma Shashenta cikin Bedroom dinta ta iske Mastur Lullube Cikin bargo Data shigo kin kulata yayi wai yayi Fushi sai da tayi ta Lallashi Ta Lura Rigima yake ji Domin Haka ya Tarota ta Fado gadon ya Turmusheta yana Fadin"Ni ko.?ni kekiranki kina jamin aji ko Rumata..?
Mirmishi ta saki Tana kokarin Daidaita kanta take Fadin"Taya zn iya barin su Umma na taho wajenka? Tab salon ace bani da kunya kuma Diza bazata ji Dadi ba yau Tana Amarya nazo na Rike mata ango..!
Kura mata ido yayi itama Idon ta Kuramai Kafin tayi Saurin Janyen Idanuwamta Tana kokarin maida kwallarta ya Shagala da kallonta ta Shammacesa ta Kwace kanta ta Diro Daga kan gadon Tana Fadin"Tashi ka Shiga wanka..Kafin ka Fito na Fito maka da kayan da zaka saka yau ni da kaina zan Shiryaka na Rakaka Har Dakin Amarya Diza Harta Kazan amarci baka da Damuwa na Tanadar maka kaidai kawai Biyayyarka nake nema..!
Yana kallonta Cikin wani Shauki ya Mike tsaye Cikin kasala ya sara mata yana Fadin"Yes Mah..ammh da Sharadin ke Zakimin wankan ko..? Yafada yana Daga mata Gira Dariya Tayi kafin tace"Ok Sir..As you wish.."Kama Hannunsa Tayi ta Turasa Cikin Tiolet yana kokarin Juyiwa ta saki hannunta ta Juya ta Fice da gudu tana Rufomai kofa da Mirmishi ya bita yana Fadin"Zan kamaki ne..!
Tana Fitowa ta Bide Wardrope dinta ta Dauko Sabuwar Farar Shaddan Data Dinkamai Riga da wando da Babban Riga Gezner ce mai kyau dubu 100 ta siyeta,Ta kuma bada aka Dinkamai Batare Daya sani ba ta Siyamai Sabon Agogon na Kamfanin Rado Takalminsa Rufaffae na Fatar Damisa da Hula zanna Bukar,sai Boxers da Singlet sai Turaren da zai Fesa Duka ta ijiyemai ta Fita Zuwa Kitchen ta Dauko kazan ta Dake Cikin Frigde wacce ta Tafasa tun safe ta Gama Hadata Tun Safe Cikin Oven ta sakata ta Fara gasawa Ta Fito da Babban Lemon Holladian mai sanyi Guda Biyu da Kilishin Data Bama Aisha kudi ta Siyo mata Yanzu data Dawo ta Shigo Dashi.
Sai datagama gasa kasan Tsab ta Nannadeta Cikin Poul Paper,Ta Hada Harda Kilishin,ta samu wani kyakyawan kwando ta Sakamai ta jera Harda Lemukan kana ta koma Cikin Bedroom din
Ta iske shi Tsaye yana Duban kayan bai saka ba Yana Sanye da Towel a kugunsa..
Tsayawa Tayi rike da kugu Tana Fadin"Me kake jira baka Shirya ba?lokaci na Tafiya..?
Kallonta yayi kafin yace"Wadanan Kayan fa is for Who..?
Karisowa Tayi Tana Daga kayan Lokaci Daya Tana Fadin"Is Urs..Gudummuwata kenan bazaka je  Dakin kanwata da Tsoffin kaya ba..Oya maza Daga hannu ka saka Singlent bana son gaddama Lokaci na Tafiya..!
Shidai kallonta yake yi bai iya ngana ba da Taimakonta ya gama Shiryawa Sai gashi ya Fito Ras ango,Ta jashi gaban madubi ta Fesheshi da Turare Tana Kallonsa kafin ta juya tana Fadin"Kayi kyau ango Diza..!
Rumgumeta yayi Lokaci Daya yana Fadin"Kuma Mijin Rumana ba.."Mirmishi ta saki kafin Tayi mgana yace"Kiyo alwala muyi Sallar Isha"i Tukunnah..!
Batayi gaddama ba Daman Tana neman Hanyar Guduwa kai ta Gyada Kafin ta Sabulr Jikinta ta Shige Tiolet tana Sharan kwallah.
Tana wanka tana kuka Ta Dade kafin ta Fito koda ta Fito ta ganshi Xaune yana jiranta Mirmishi ta sskarmai Kamar yadda Tayi mishi shi ya Taimaka mata ta Shirya itama cikin Shadda Doguwar riga ya jata gaban madubi ya Daura mata Kallabi Lokaci Daya ya Rumgumeta yana Fadin"Thanks So much..Allah ya saka Miki..Allah yayi miki albarka..!
Da ameen take amsawa Tana kokarin saita kanta.
Sallar Isha"i yajasu Jam"i sukayi Suna Idarwa Tara Tayi Rumana ta Mike da Hijabin Jikinta tace"Ka taso na rakaka..Dare yayi kada Diza Tajimu shuru..!
Mikewa yayi ita kuma ta Riko Hannunsa suka Fito Falon tace ya Jirata ta Shiga Kitchen ta Dauko kwamdon ta Fito ta kama Hannunsa Dayake Binta da kallo Zuciyarsa ta kasa Fassara wani mtsayi Rumana gareta acikin Zuciyarsa.

Bata Dire Hannunsa ba sai da ta Rafka sallama Bedroom din Diza Bayan ta Sadashi da Gefen Diza Dake Zaune kan gadon Cikin mayafinta Bata Dago ba sai da ta amsa Sallamansu.
Rumana ta zauna gefen gado Tana Fadin"Amaryanmu..Kiyi Hakuri na Dauki Lokaci..Na Tsaya Shirya angon naki ne kamar yadda nayi miki alkwari Gashi kuma na cika ga angonki nan na kawo Miki Sai ki Rikemin shi Amana .Allah ya baku zaman lafiya da Zuru"a Dayyiba..!
Diza ta amsa da Ameen Mastur ma aransa ya amsan kwamdon ta ijiye gefen gadon Tana nuna ma Mastur da ido kafin ta mike tana Fadin"Asha Amarci Lafiya..Sai da Safe..!
Tafada tana kokarin juyewa jin Hawaye suna kawo mata da Sauri Mastur ya mike ya Rikota Cikin Jikinsa Sai kawai ta Rumgumeshi tana Fidda Numfashi Zuciyarta na Zafin Kishi kamar yadda na Diza ke yi Data Hangensu ta cikin mayafinta kamar Zuciyar ta Zatayi Tsalle ta Fito waje haka take ji saboda Kishi.
Rumana ce ta Fara Zare Jikinta Tuna inda suke ta Ja kumatunsa Tana Fadin"Ka kula da Diza..!
Shima kumatunta ya shafa yana Fadin"Kema ki kular min da kanki..Matata..,!
Kai ta jinjinamai kafin ta Daga kafa Zata wuce yana Kokarin Binta ta Dakatar dashi.."Ka koma wajenta..Zan iya komawa da kaina..!
Daga haka bata tsaya jiransa ba ta Fice da Sauri jin hawayenta suna neman zubowa.
Allah ne yakaita Shashenta Lafiya bata Zube ba saboda Kukan Daya kwace mata Dakyar ta kai kamta Bedroom ta kwanta Tana ta Rusa kuka Lokaci Daya tanaji kamar Zuciyarta Zata Faso waje Innalillahi kawai take maimaitawa acikin Ranta.






*Shakira..*
1/1/22, 18:55 - Maryam Badmsi: *SS....39*

*Kibiya ki karanta cikin Salama Mace mai aji mallakan komai nata take yi bata jiran abun Sata 09069067488*


"Har Rumana ta Fice Mastur bai iya Motsawa Daga inda yake ba Gabadaya Jikinsa yayi sanyi Kirjinsa ya cika da Karamcin Rumana da Alherinta Gareesa sai yake ganin kamar bai kyauta mata ba Tamai komai a rayuwa TaRufamai asiri ta zauna Dashi Ahalin da bai taba kallonta a mtsayin matarsa ba Bata taba kai karansa ba,bata taba kuma Bude baki Tayi mai mgana ba,Shiyasa yake girmama Hallayarta acikin Zuciyarsa.
Diza Dake zaune Cikin mayafi Tana kallonsa Gabadaya sai ta Raina kanta ganin irin yanayin Daya shiga ya kurama Kofar da Rumana ta fita Tun dazu ya kasa Motsi sai taji kirjinta yayi nauyi Kishi ya Lullubeta har bata san Lokacin da Hawaye suka Ciko idanuwanta ba Ta Shirya ma Kanta Rayuwa da Mastur ita kadai a ton Farkon Fari sai dai ina Allah ya gama nashi Tsarin Dole Zatayi Sharing dinsa da Rumana.
Tana cikin wannan Halin ya juyo yana kallonta Hannayensa Goye a Bayansa Bai zauna ba illah Kwandon da Rumana Riko ne yake kallo Zuciyarsa na Harbawa waje Daya,Kamar kwallah Zata Zubomai saboda Tsananin Tsausayinta,da wani irin yanayin Da Har yau ya Kasa gane wani yanayi ne yake ji game da Rumana sai dai abu Daya ya sani ita din ta Cika Kirjinsa da karancinta da kyakyawan Dabi"unta wadanda suka sama Mata Gurabe masu Girma da Matsayi acikin Zuciyarsa.
Har yanzu Bai gama yarda ma kansa Diza ta zama matarsa ba Gani yake kamar a mafarki,Allah Sarki Rayuwa Ashe Rabon Mansur karami ne ya Tabbatar da Auranta da Mansur ashe shi din bamai Zama bane
Allah ya jikan Mansur da Rahma Rana bazata Fito ta Fadi bai ji Dacin Mutuwarsa ba, bai ji Hawaye sun kawo Idanuwansa ba Ya Tabbata Har gaban Abada bazai Taba mantawa Dashi ba Duka Khamsun Salatmwatul dinsa Baya mantawa Dashi yana Rokamai adddu"an Rahma da Gafara a wajen Ubangiji.
Kallon Bedroom din yake da alama Sabo ne ba"a Taba amfani Dashi ba kamar ya sani Diza ta Bukaci a Dayan Bedroom zata Zauna wanchan da sukayi Rayuwa da Mansur ba zata iya kara wata Rayuwa da waninsa ba,Haka kurum take ji kamar bata kyauta ma Marigayi ba,Shiyasa Datayi mgana kowaya yarda da ita Dayake Ita da Mansur Lokacin Bedroom Daya sukayi ta Sharing har bayan Rasuwarsa sai ya kasance Dayan ne suka barma Baki Dayan kuma Basu Taba amfani dashi ba Shi aka gyara Daman akwai komai na Bukatar Rayuwa sai dai an kara Abunda ba"a rasa ba.

Mastur Dake Tsaye gaban Diza ya saka Hannu ya kwabe Babbar Rigar Jikinsa ya Ijiyeta nan Saman gadon Lokaci Daya ya Duka yana Sabule Takalmin kafarsa kana ya Dago yana kallon Diza Lokaci Daya yace"Ki tashi kiyi alwala muyi Salla Hadiza...!
Daman haka yake kiranta Sai Lokaci Bayan Lokaci ne zakaji ya ambaci Diza.
Muskutawa Tayi ta Zuro kafafunta ta Sauko Daga kan gado Tana Rike mayafinta Cikin Sanyin Murya tace"Ina da alwala..Kuma nayi Sallar Isha"i..!
Sau Daya ya kalleta ya kauda kai Jin yadda Zuciyarsa ta Gaba ganin ta yaye mayafinta,Da Sauri ya karisa Saman Cafet din Dake bakin gadon ya Daidaita Sahu yana Fadin"Nima nayi isha"in aie..!
Ganin haka yasa ta Bude Wardrope ta Dauko Hijabinta Dayake Duk Anty Hadiza tazo mata da akwatunan kayanta Sauran dai suna gida,Takowa tayi ta Tsaya abayansa itama ta Daidaita Tabishi Sallar Raka"a Hudu yayi musu kafin su Sallame yayi addu"o"i sosai na Zaman Lafiya garesu daga karshe ya Rokama Dan"uwansa Gafara Dukkansu sun Shafa addu"an ne da Raunin Zuciya da Sanyi Jiki Gefe Daya Idanuwansa ya kawo Ruwa Saboda Tunawa da Mansur wanda Har Abada Zukata bazasu Manta dashi ba.
Shuru ya Biyo bayan Shafa addu"an nasu kowa da Tunanin Daya addafeshi,Diza Tana Gefe kanta na kasa Tana wasa da Gefen Hijabinta Yayinda Da Mastur yake gefe shima kansa na kasa ya Rasa ta ina zai Fara,Shi dai ba wata Shakuwa Tsakaninsa da Diza yau yanzu ma Bayan Rasuwar Mansur da Sauki Sauki kan Abaya Ganin ya raasa me zai ce mata ne ya Dago yana kallonta Cikin Sanyinsa yace"Kina jin yunwa..? Bai bata Zarafin mgana ba ya Cigaba da Fadin"Dauko ga kwandon Chan Rumana ta kawo muga Abunda ke Ciki..!
Ita dai Ranta ne ya baci jin Abunda ma zai riko mata Rumana ce ta kawo sai taji Duk Ta Raina kanta bazata mai gaddama ba yasa ta Mike Jikinta Sanyaye ta Dauko kwandon zuwa Gabansa Dayake a Zuge yake da zif Tana Shirin zama ya kalleta yana Fadin"Open it..!
Batayi musu ba ta Duka ta Budeshi,Sai ga Hollandian masu sanyi guda Biyu da kilishi da kazan Tayi Rapping dinsu Kura ido yayi yana kallonsu kafin ya Murmusa yace"Allah yayi miki albarka Rumana..!
Yafada yana Bayyana Jin Dadinsa ita dai Diza kanta na kasa Ta kasa Fassara wani Hali take Ciki Cikin Hakane taji yana Fadin"Ki samo Filet ki Dibi kici..!Batasan sadda tace"Ni fa a koshe nake.."
Tafada Cikin Kishi Daya taso mata Daga kasan Zuciya na yau Daran Farkonsu ammh kuma Mijinta na gabanta yana saka ma Wata albarka ita kuma ko Oho..!
Yana kallonta Ido Cikin ido Kafin yace"Ban yarda ba..Me kika ci..?
Yafada yana Tsareta da ido sai ta kasa mgana ganin haka yasa shi ya yunkura ya mike ya Fice Batare Daya tankata ba yana Fita ta Sauke Numfashi Tana kokarin Daidaita kanta Kada ya Fahimci Halin Datake Ciki.
Bai dade ba ya Dawo Dauke da Filet da Mug,sai Pork guda Daya shi ya Bude kazan ya Gutsiran ma Diza ya kuma Diban mata Kilishi da Dayawa Tunda shima yana son Kilishi,Sai ya Tsiyayamata Madaran Duka ya Turo gabanta bai mata mgana ba sai shi ya matso gabanta suka saka Filet din a Tsakiya yana Fadin"Oya Matso..!
Batayi gaddama ba ta Matso batare da wani Tunani ba ya saka Hannu yago Cinyar Kaza,ya Nufi Bakinta Dashi,Cikin mamaki Take kallonsa Sai ya Hade rai yana Fadin"Oya open ur Mouth..!
Dole ta Bude ya Tura mata yana Fadin"Nasan yunwa kike ji..ki Bude Ciki kici sosai..Rumana ta gasa kazan nan da kanta naji Test din gashinta..!
Tunda ya ambaci Rumana taji Dandanon Naman ya koma mata Daci Turawa kawai Takeyi ba wai Domin Tana jin Dadi ba,Dakyar ta karba sau Biyu ta kauda kai sai ya Girgiza mata kai yana Fadin"Ki bude Ciki fa..Ga Kilishi ga Madara..!
Dole bata da yadda Zatayi tayi mai gaddama haka ya Dinga bata Kilishin sai da yaga ta kusa Amai ya kyaleta,Ya mika mata Madaran ta karba tasha kadan ta Mikamai shima ya karba yasha,Ya ci Kilishin sosai ya Cinye Duka,Diza bata barsa ya Tattara komai shi kadai ba ita ta Tayashi suka maida komai Kirchen Sauran kilishin da kazan kuma ta sanya Cikin Fridge.
Kana suka Dawo Daki,Tiolet Mastur ya Shiga ita kuma Diza sai ta Bude Wardrope dinta ta Fito da kayan Barci itama Tana son Shiga Tiolet din Zatayi Brush ta wanke bakinta
Bai dade ba sai gashi ya Fito shima bakin ya wanke Yana Fitowa ya Kalleta irin kallon nan na wani yanayi da Sauri ta Raba ta Gefenshi ta Shige Tiolet,Kansa ya Dafe Tunanin bai Dauko kayan Barci bs ko Jallabiya bai iya kwana da kayan Jikinsa sai ya Cire Rigar yabar da Singlet din wandon Jikinsa ya Zauna nan gefen gado sai ga Diza ta Fito Sanye da Wata Rigar Barci mai Ruwan Madara bata da kauri Sosai Domin yana Hango Farin pant din Jikinta da kuma kan Nonuwanta Da bata Sanya Bra ba,Rigar ko gwiwa bata kai mata ba kunya yakamata taji kamar ta koma Tiolet din sai dai ya Riga ya ganta Ita da ba domin Anty Hadiza ta matsa sai ta saka wannan Rigar ba wlh bazata iya sakata ba Lokacin Mansur bata da wata Damuwa ba Ko ba aure Sun Shaku da juna bata wani jin Nauyinsa To Mastur ne fa akwai jim kunya da Nauyin juna a Tsskaninsu sosai.
Shi kuwa Daskarewa yayi a zaune yana kallonta Zuciyarsa na Harbawa yana jin yana yanayi na Sha"awar diza da matsananciyar Soyayyarta na kara Fizgansa wlh da Farko bai shigo da niyar yi mata wani abu ba ammhZuwa yanzu Daya ganta Cikin wannan yanayin Tunaninsa ya Sauya wanda Har bai san sadda ya Taso ya kariso gabanta ba daga ita Har shi basu Fargaba sai da suka jisu sun samu Muhalli a Cikin Kirjin junansu kana kowa ya Ssuke ajiyar Zuciya Diza sai ga Hawaye na kukan daman zata ga wannan Ranar da zataji tasaman Kirjin Mastur shima anashi Tunanin haka din yana Rike da ita yana Tunanin yau ga Dizan Daya kusa mutuwa akanta ta Zama mallakinsa sai da Hawaye suka Cika Idanuwansa kamkam ya Rumgumeta yajata Gefen gado ya Zauna Lokaci Daya yayi mata Masauki kan Cinyarsa kunya ta kama Diza sai ta kasa Dagowa ta Noke Bisa Kirjinsa.
Wani Kayattacrn Mirmishi ya saki kafin ya Dago Habarta suka Hada ido,Ido Cikin ido suke kallon Juna suna karantar yanayin da suke Ciki Diza Tana kallon Idanuwan Mastur tana jin kamar su dauwama ahaka yayinda Shi kuma yake kallonta Cikin Soyayyarta da kaunarta Hade da matsananciyar Sha"awarta Daya kamashi Loksci Daya.
Cikin Shakewar murya yace"Alfarma Daya zan Rokeki Hadiza ina Fatan zakimin..?
Kanta na kasa ta Dagamai kai Tana Fadin"Insha Allahu indai batafi karfina ba..
Jinjina kai yayi yana Fadin"Bata fi karfinki ba..Rokon ki zan yi Don Allah..Da Darajan iyayanmu Ki zauna Lafiya da Rumana..Ki Tayani Mutumta ki Tayani Girmamata ki Tayani yi mata alheri koda Rana daya kika Kalleta da wani Duba bazan ji Dadi ba..Ni kaina ina Girmamata ina kuma Ganin Darajanta ki Taimakamin kema ki Darajata ki girmamata Shi kadai nake Rokon ki.!
Diza tayi Jagale tana kallonsa Kai ya gyada mata alamun Tabbatarwa kafin ya Cigaba da Fadin"Eh Diza..Rumana ba irin Sauran mata bane..Tayi min Karamci da alherai masu Dimbin yawa wanda bazan iya mantawa dasu ba..Ba auran ki bane Alherinta gareni Rumana ita Ce Rufin asiri na Ta Dade tana Nuna Min Halin Girma Shiyasa bana son naga An batamata rai ko kuma Naga kunci ko Damuwar a saaman Fuskarta ta Chanchanci Tayi Farinciki har Karshen Rayuwarta..!
Yafada Kamar zai mata kuka,Ganin haka yasa Diza ta Danne abunda ke taso mata tace"Nayi maka alkawarin zan Tayaka Girmamata Har karshen Rayuwarmu.."
Ido ya sakar mata kafin yace"Are u sure..? Da sauri tace"Yes Very Sure..!
Ai batasan sadda yabata Wani Rumguma ba kamar zai Tsaga Kashinta,yana Tusa kansa Cikim Kirjinta yana Fadin"Tanque..So much..Allah yayi miki albarka.!bai bata Damar amsamai ba Taji yana Kaita wata Duniyar da ba wai bata sanda da ita bane sai dai kuma Bata tsammaceta alokacin ba kuma Diza bazata iya juyama Salon Mastur baya ba Balle bukatarsa ba Bata san ya akayi ba Tadai tsincesu Tsakiyar gado Cikin Bargo Dukkansu Naked Fatar su na Gogan na Juna Diza ta Haukace ta Rude jin Ta hannun gwarzon maza Wanda ya sata ta Fita Daga Hayyacinta Tana kuka Sharban batare Data sani ba Bazata iya Dora komai ba Abubuwan da suka Faru ba sai dai abu Daya ta sani Duniyar da Mastur ya kaita tasha Bambam da wanda ta saba zuwa abaya wannan wata Duniya ce ta Dabam
Shi kanshi Hakan ce ta kasance a wajensa baxai iya Dora komai ba,ba kuma zai Furta komai ba Sai dai zai iya cewa ya samu gamsuwa da Diza 100% ,Mata suna suka Tara,kuma duka mace sunanta Mace Shidai yasan mai Sa""a ne Duka matansa yan Baiwa ne Rumana zumarta na Gigitashi Har ya Fice Daga Hayyacinsa yau ga Diza itama Daya sami Gamsuwa da ita sosai Wanda yaasa Har bayan sun yi wanka sun koma sun kwanta Da suka Tashi sukayi sallar asuba bai iya Kyaleta ba Sai da ya kara maimaitawa yana kara Godema Allah da Tarin Ni"imar Daya yi Mishi na Zuka zukan mata masu Lafiya Da Kuruciya.

A bangaran Rumana kuwa Ganin kukan ta yaki tsayawa ne Shedan Tana kisi ma mata wasu abubuwa kan Diza da mastur yasa tamike da Hanzari  ta Fada Tiolet tayi wanka Lokaci Daya da Dauro alwala Tana Fitowa ta Daidaita Sahu a gabas ta Tada Sallah tanayi tana Sallamewa Tana Mikewa bazata iya kirga Raka"a nawa tayi ba Bata kuma Dakata ba sai da barci ya Jika idanuwanta Gwiwanta yayi sanyi kana ta Sulale saman Darduma Barci ya kwasheta da Taimakon Allah kuma bata Farka ba sai Dataji kiran Sallar asuba ta farka kuma Cikin yardan Allah ta Samu natsuwar Zuciya Shiyasa ta mike da Kuzarinta Bayan Ta idar da Salla ta gama azkar dinta ta Fada Kitchen domin sama ma Ango da amarya abunda zasu ci Gefe Daya Tayi Shirin zuwa asibiti Domin suna Shirin Tattara ina inasu su yi sallama da Abu Gabadaya sauransu Wata Daya su gama Service dinsu.

Karfe 8am na Safe Dr.Rumana ta Fito Cikin Shirinta Tsaf na Doguwar Rigar material Ta yane mayafi Bisa kanta da Karamar Jakarta sai key din motarta Da kwaton kwandon Data jera ma su Diza Abun karyawansu wanda ta Bata Lokaci wajen Hada musu ita batama jin cin komai,tea kadai tasha Ta Fito Adaidai kofar Shashen Diza Bayan ta Rufe Shashen nata ta Tsaya tana Duba agogon Fatan Dake hannunta karamin Tsaki Taja ganin ta makara kamata yayi by now tana Cikin Asibitin Chika..
Kofar Shashen Diza ta isa ta Fara Knooking a hankali kada Buga kofar ya Takura musu.
Mastur Dake Nannade da Diza Suna Sharan Barci yaji kamar Bugun kofa sai kuma yaji kamar ba Bugun ba,Ssi ya kara Nannade Diza acikin Jikinsa,suka kara Lamkwamewa Cikin Bargo.
Rumana Dataga bzasu jita ba sai ta ijiye kwandon Abinci ta Bude Jakarta ta Dauko wayarta ta kira Mastur kira Daya Cikin na Biyu ya Daga kiran nata Cikin Kasala da Idanuwan Barci yace"Hello Ruma..!
Yafada Cikin wata Murya mai cike da amo da Zati,Rumana ta gyara Tsayuwarta Tana Fadin"Gud Mrning...am sorry na tada ku Daga barci..Gani kofar Shashen ku Dauke da Breakfast dinku ina Sauri zan wuce asibiti..Ko na ijiye muku ne in kun Fito ku Dauka kada na saku Tashi baku gama barci ba..!
Tafada Cikin mirmishin karfin Hali,Mastur Daya watsake Daga Barcinsa ya Mike Zaune ya Raba Diza Daga Jikinsa yana Fadin"No..Gani nan Fitowa kada ki Tafi plz..! Daga haka ya Datse kiran Daidai Lokacin daya Sauko Daga kan gadon Diza Data ji ya Rabata da Ni"imantattacen Jikinsa mai Dadin zama kamar ta Dauwama ahaka haka take ji.
Ta kalleshi yana Kokarin saka Rigarsa tace"Ina zaka kuma..?
Waigowa yayi yana Sakar mata Mirmishi Lokaci Daya yana Fadin"Rumana ke kofa tana Jiran mu da Breakfast dinmu..kema ki Tashi ki Sanyo Hijabi ki Fito ku gaisa Asibiti zata wuce..!
Daga haka bai Tsaya ba yana Rawan Jiki ya Fice ta Bisa da kallo Zuciyarta Tana Tukiki a jiyan Tana jin Kishinsa ammh Daga Daran jiya zuwa wayewar garin yau sai taji Kishinsa Datake ji ya Ninka Dari Bisa Dari,Ashe ma bataji komai ba sai yanzu da suka Zama Daya taji Ambaton sunan Rumanan da yayi sai taji kamar takasheta saboda Tsanarta Balle ma ganin yadda yake wani rawan jiki akan Rumanan Daga ta kira waya tace Tana Kofar Shashe karamin Tsaki Taja Kafin ta yunkura ta Mike ta Fada Tiolet.

Mastur kuwa da Hanzari ya isa Kofar Shashen nasu ya saka Hannu ya Bude,sai ga Rumana ta Bayyana tana mai mirmishinta mai kayatarwa Cikin Girmamawanta tace"Mrning...! Tafada Lokaci Daya tana Daukan kwandon Ta Nufi cikin Shashen nasu Bayan ya bata Hanya A tsakiyar Falon ta tsaya saman Center Table ta Ijiye Kwandon Tana Fadin"Ina Amarya Diza..? Fatan Tatashi Lafiya..!
Bai bata amsa ba illah karisowa da yayi ta bayanta ya Rumgumota Lokaci Daya yana Sagala kansa ta wuyanta yana Shinshinata kamar wani Mage,Ita kuma Rumana sai ta Sauke ajiyar zuciya kafin ta sami Zarafin mgana tajisa yana Fadin"Uhm..wannan itace irin gaisuwan tawa Ruma..?
Yafada cikin wani sanyin murya Lokaci Daya Yana kai Hannayensa wani waje acikin Jikinta da Sauri ta rike hannunsa  tana Dariya Lokaci Daya da kokarin Zillewa Tana Fadin"Kaifa sabon ango ne..Kada Diza ta Fito ta ganmu..bazata ji dadi da..!
Bata gama Rufe baki ba Diza ta Bayyana afalon Cikin Dogon Hijabinta Tana Binsu da wani Kallo acikin idanuwanta na Takaichi da Bakinciki wanda ta kasa Controling kanta da Kishinta.
Rumana ce tayi saurin kwace Jikinta Tana Daidaita kanta Take Fadin"Amaryanmu. kin tashi Lafiya..?
Tafada Tana bayyana Mirmishinta Mastur kuwa yana Gefe goye da Hannayensa Abayansa yana kallon yanayin Diza da yadda Ta hade rai taki sakarma Rumana Fuska sai yaji bai ji Dadin hakan ba Shiyasa ya isa gareta yana Riko hannunta Lokaci Daya yake Fadin"Baki ji bane Rumana na Tambayan ya Amarya ta kwana bane..?
Diza saboda Takaichi Zare Hannunta Tayi Cikin nashi Tana Zama Cikin Daya Daga Cikin kujerun da sukayi ma Falon kwanya Lokaci Daya tana Tattaro Sauran Mirmishin Daya rage akan Labbanta ta ara ta yafa kafin ta Rausaya tana Fadin"Lafiya..!
Daga haka ta Dauke kanta ta kasa Cigaba da mgana saboda tasowar wani Takaici da kishin Rumana Daga kasab Ranta na ganin irin kallon da Mastur ke Bin Rumana da ita kamar zai lasheta.
Rumana Data ga haka sai ta Rausayar da kai itama tana Nuna ma Diza kwandon Abuncin Lokaci Daya Tana Fadin"Daman Breakfast dinku na kawo muku..Ni zan wuce asibiti..!
Dakyar Diza ta iya cewa"Mungode..!
Daga haka ta Dauke kanta Tana kokarin maida kwallar daya kawo mata,Rumana kuwa sai ta Sagala Jakarta Tana kallon Mastur tace"Zan tafi..!
Takowa yayi zuwa gabanta kamar zai rikota sai taga Idanuwan Diza na kansu sai taja Baya Tana Duba agogon Hannunta Lokaci Daya tana Fadin"Na makara fa Ya Mastur.."
Ta karishe Fada Cikin Shagwaba.
Kai ya kada yana Fadin"kun kusa gama wa ko..? Tace"Eh sauran mu wata Daya mu gama Insha Allahu..!
Mastur yace"Allah ya kaimu..Munyi wata mgana da Abba! Da sauri Rumana tace"Allah yasa ba kan mganar komawata Resendency bane yayi maka Domin naga Abba yana Neman yace na Dakata hakanan..!
Bai ce mata komai ba illah cewa da yayi"Koma miye zamu yi mgana in kika Dawo..!
Kai ta Kada kafin ta juya tana yi musu Sallama Diza dai Tana ganin ikon Allah Domin agaban Idonta Mastur ya Fice yayi ma Rumana rakiya bai dawo ba sai da Motarta tabar Haraban Gidan kana ya Dawo bai iske Diza ba taShiga wanka ya Lura da ita da yanayinta Shiyasa shima ya kwabe ya Bita Tiolet din sukayi wankan Tare duk Kamewar Diza Kasawa Tayi Domin Mastur ba irin Mazan da zasu mika ma matansu Hannu suki karba bane Bata da yarda zatayi dole ta Mika kai Bori ya hau shi ya Nadota a Towel zuwa Bedroom dinsu ya kuma Shafamata mai ya Shiryata Tsab Itama ta taikamai ya shafa mai ya maida kayansa na Jiya suka Fito suka karya da kayattacen Abun karin da Rumana ta Shiryamusu Suka Cinyar da juna Cikin soyayyah Kana Mastur yayi amfani da makulin Dake wajensa ya Bude Shashen Rumana ya Dauko kayansa da Zai Bukata kafin ya bar Bangaran Diza.
Wuni sukayi agida Mastur bai fita ko"ina ba wayoyinsa ma kashesu yayi ya Dauki Duka Hankalinsa da Soyayyarsa ya Mikama Diza wacce a wuni Daya Taji kamar tafi kowacce mace sa"ae samun Gwarzon miji irin Mastur Har taji Tana Fatan su Dauwama aahaka su kadai har Abada Kada Rumana ta Dawo gidan Domin in Mastur na Bata Soyayyarsa Dauka take ita kadai ne ta mallakesa Data Tuna da Rumana sai taji Komai ya Fitar mata a ka,
Rumana kuma tana asibiti Umma ta kirata tace sun wuce ita da Anty Hadiza Rumana tayi ta Bata rai kan me Umma Tatafi bata jira sunyi sallama ba Hakanan Umman ta bata Hakuri sai da tatashi da Zata Dawo ta Biya ta Hanwa ta iske Inna Zainaba ma ta koma da Safe Mardiya ta Bita zata kwana Biyu sun samu Break amakarata.
Saboda tabama Diza da Mastur Lokacin nan wajen Hajja tasha Zamanta Illah ta shiga ta gaida Mommy tama jima tana yi mata Nasiha kafin ta Dauko mansur ta Dawo Dashi Gidan Hajja Tunda ya makalemata Tun shigarta Gidan.
Nan takai dare har sai da Ta taya Hajja suka yi tuwon Shinkafa Miyar alaiyahu,Taci ta Koshi Ta Fara Tunanin su Mastur mai zasu ci wata zuciya tace ina Ruwanki..? Sun fiki sanin Cikin su in suka ji yunwa zasu neman ma kansu mafita da wannan Ta kauda Tunaninsu taci ta Koshi bata ma Jira Dawowar Baba Habibu Ta yi Shirin Tafiya saboda bata son Driving din Darw da Zata tafi Mansur karami ya Fara kuka sai ya Bita ita kuma tace Zata tafi dashi ta Biya Mommy ta hada mata kayansa ta saka sa a Mota suka Dawo gida..
Daman ta san Mastur bazai Fita ba Tunda taji Hajja tace bai leko ba tasan ba inda zaahi Tunda shi ba irin Mansur marigayi bane baya yawo Daga gida sai gida.
Basu ji Dawowarta ba suna chan suna Soyewarsu ko yunwa ma basaji Sai zuwa chan da suka ji yunwan suka sha Tea suka Hada da Sauran Dankalin da Rumana ta Soya musu da Safe sai Lokacin Mastur yaji bai kyauta ba ya Kunna wayarsa ya kira Rumana Lokacin Tagama bama Mansur karami abinci tamai wanka ta sakamai kayan Barci suna Shirin Barci Tunda tayi sallar Isha"i Harda Shafa"i da wuturi taji kiran Mastur Duk da Taji ba Dadi Da Sharetan da yayi ammh bata Nuna mai ba,Ta Daga suka gaisa Tace mai ta Dawo gida Tunda Dazu ita da Mansur Karami ya biyota yaji Dadin haka yace zai Shigo tace ya bari sai da safe su zasu zo da haka sukayi sallama da juna.
Awannan Daran ma Kwana Sukayi suna Farantama juna rai Diza taji ta Raina kanta da Saninta Gabadaya saboda Mastur ya Riga ya gama Goge mata Duka Saninta acikin kwana Biyun da sukayi tare Diza ta Tabbatar ma kanta Mastur na sonta ko a washegarin ma Rumana tayi ta Dawainiya dasu ta kawo masu abun karyawa kafin ta Fice zuwa Wajen aiki Tare da Mansur karami Tatafi domin koda Mastur ya nuna ta bar shi Sai yaron yaki yarda sai ta tafi Dashi Diza kuma Daman bai Damu da ita ba Bayan tatashi yau ma din a Hanwa ta wuni tafi son ta basu Lokaci su gama Cin Amarcinsu.
Bayan Mastur ya gama kwana ukunsu na al"ada adakin Diza Rumana tace ta karamai Kwana Hudu yayi ma Diza kwana Bakwai Mastur ya kasa mgana da Karamcin Rumana garesa Duk da yaji Dadi ammh bai nuna mata ba sai ma Rumgumeta da yayi yana Korafin ta yanke mgana batayi Shawara dashi ba ita dai sai ta bashi Hakuri tace tayi Niyyar har ga Allah.....
Koda ya koma Diza sai taji kamar an sakata a aljannah Damar tun Daya Tafi ya barta take kwance Tana kuka Zuciyarta Cike da Tsanar Rumana da Kishinta wanda Daman akwai shi Dalili yasa Komai ya sauya yanzu kuma komai ya sake Bude mata balle yanzu Data Dandanin Zumar Mastur take jin Dama ita kadai ta mallakesa.
Cikin Satin Dayan da Mastur yayi Tare da Diza Rayuwarta ta Sauya ta kara Fari da Kiba ta Cika da Farinciki Shima haka Mastur dim Lalle Diza ce Rayuwarsa ya Tabbata,Domin a satin Daya sukayi tare ya samu Dukkan Farinciki kuma ya Nemi Ciwonsa ya Rasa Batare Dayaje asibiti ba ko ya Nemi mgani ba.
Bayan ya Dawo wajen Rumana da kwana Daya yayi Shirin komawa Bakin aikinsa a kuma Daran ya Daukesu dukkansu zuwa Hanwa Daman mansur karami yana wajen Rumana yaki yarda ya koma wajen Hajja ko Mommy.
Gidan Daddy suka Fara zuwa Allah yasa Daddy yana gida ya Hadasu dukkansu yayi musu Nasiha sosai,mommy ma ta Tofa albarkacin Bakinta,har anan ne Daddy ke Ma Rumana mganar Cigaban karatunta Cikin Ladabi tace"Abba ina so na samu kwarewa kan Abunda ya Shafi yara..Karatun Shekaru Shida ne ammh naji Abba yana mganar na Dakata hakanan Saboda Aurena..!
Daddy yace"Nima yayimin wannan mganar..sai nace ya Tuntubi Mijimki yaji in ya barki sai nayi ma Dr Hambali mgana sai kiyi karatunki anan Abu din..
Rumana ta Dago Tana kallon Mastur wanda ke Latsa wayarsa Mansur karami na kan jikinsa yana ta tsallensa
Daddy ya juya yana Kallonsa yace"Alhaji Muhammed ya kira ka..?
Mastur ya maida wayarsa aljihu yana Fadin"Eh ya kirani munyi mgana Nace mai ni banga Wani Abun Damuwa ba ai abu ne mai kyai bai kamata mu ki bata Dama ba Tunda Tana da Ra"ayin hakan na gayamai in ni yake ji ya Daina ko ba Mijin Rumana nake ba wlh yayanta nake ni mai Biyamata kudin Karatu ne bama anan gida Nageria ba Duk kasar sa Datake so zan bata izinina da Taimako na da aljihuna da yardan Allah naga ta Cika Burinta!.
Ya karishe Fada yana Kallon Rumana Dake kallonsa Cike da wanni Annuri tana aikamai da kalmar Godiya ta ido Shima ya gane ya Shiga make mata kafada yana Girgiza kai alamun bayason irin wannan Godiyar.
Duk Diza na ankare dasu Bakimciki kamar tatashi ta Shakesu haka take ji Daman ga Ranta ya gama baci da Cigaban karatun Rumana haka kurum taji itama Tana Sha"awar ta koma makaranta Bata kaunar Rumana ta Darata a komai
Mastur kuwa Bazai iya Hana Rumana Burinta ba yayi alkawarin Bata Dukkam Farincinki Tunda Tayi sanadiyar samuwae nashi Farinciki itama zai sanyata Farinciki har karshen Rayuwarsa.
Daddy da Mommy kuwa sai sska albarka suke sun Dade agidan kafin su fito su yada Zango Gidan Hajja nam duka Nasihun ne Daga Bangaran Baba Habibu da Hajja da Ayya nan sukayi Dinner sai Mastur ya gayama su Hajja mganar Cigaban karatun Rumana suma sunyi na"am sosai suma sakamata albarka sukeyi Tuni Diza taji itama Tana jin Lokacin Da zata  koma makaranta ya kusa
Sai pass 9pm suka koma Gida amota ma sai Hira Rumana suke da Mastur kan tsarin Karatun da Zatayi kan bangaran yara Shi kuma yana bata goyon baya.
Suna isa Gida ko Raka Diza Shashenta bai yi ba nan sukayi Sallama Mansur karami ya makale ma Rumana Dole ta wuce Dashi Shashenta.
Awannam Daran Rumana taga Soyayya da kauna wanda ya kusa Kama na Daran Farkonta ta Zage ta Nuna na Mastur Godiyarta da Goyon bayan Daya bata suka kwana suna Faratama juna rai Tafiyar Safe zai yi shiyasa Bata kwanta ba Bayan sunyi Sallar asuba Ta tashi ta Tayashi Shirya kayansa ta Hada musu abum kari tace ya Kira Diza  su karya Tare
Haka kuwa ya Daga waya ya kirata kamar tace bazata zo ba sai dai bata isa tamai gaddama ba,hakanan tazo suka karyawa Tare ita dai Sai Binsu da ido take Ganin yadda suke kafa kafa da Juna Diza Sai taji ta Raina kanta ta Guduri niyar ilimin da Rumana Ta fita ne yasa Mastur ya fi Darajata sosai Shiyasa ta guduri Niyyar in ya Dawo zata mai mganar komawar ta makaranta.
Tare suka rakashi Har wajen Mota Daman tun jiya ya sallami Iyayan naashi sukayi Fatan Dawowa Lafiya da Fatan Nasara.
Duka ya Hada matan nasa ya Rumgume yana Jadadda musu zai yi kewarsu Cikin ransa kuma ya gama Yanke Shawaran in ya sake Dawowa in zai koma sai da Daya Daga Cikinsu bazai yarda yana da mata Har Biyu ba ya zama gauro a parthercourt ba.
Mansur ma ya Rumgumeshi yana Gayamai zai yi kewarsa Shima ya lafe ajikinsa yana gaurancinsa Katin Bakinsa Rumana ya bamawa Tunda itace Babba yace in Wani Bukata ya taso suyi amfani Dashi Ya bar amanan Gidansa da Iyayensa duka Hannun Rumana haka ya Dinga Nanatamata Har taji Jikinta yayi sanyi Tana Tunanin kodai Mutuwa Gogan nasu zai yi..?
Diza Shashenta ta koma Bayan Tafiyarsa Duk yadda Rumana taso su Zauna tare sai tace Zatayi wani abu ne zata Shigo bayan ta gama nan kuwa so take ta kebe Tayi kuka kukan irin girma da mtsayin da Rumana ta samu a wajen Mastur duk da ita yake so sai gaahi Rumana ta samu nasaran Samun Matsayin da ita bata samu ba.
Ta Kara yardan ma kanta Rashin ilimi mai zurfi ne ya jamata ta Dauki Damaran komawa makaranta itama tayi karatun Ta goga Kafada da Rumana.




*Shakira...*
1/1/22, 18:56 - Maryam Badmsi: *SS...40*

*Kibiya ki karanta Cikin Salama Mace mai aji mallakan komai nata take yi bata jiran abun sata 09069067488*

"Har Mastur ya koma porthercort yayi kwana Talatin da Biyar ya Dawo ko sau Daya Diza bata taba Tambayan Rumana wani abu ba bawai domin bukatar kudin bata taso ba,A"a sun taso mata sai dai Tayi ma kanta alkwarin bazata Sadda kanta ta koma tana Bin Rumana ba Tunda ba ita ta aura ba.
Sai dai Tana ragamata saboda abubuwa Dadama kulawarta akanta da kuma Danta Mansur karami Daya koma wajenta itace komai nashi,Diza sai dai in sun shigo gaisheta wanda Rumana bata taba Fita wajen aikinta batare da ta Shiga Shashen Diza ta Dubata ba Domin sauke Nauyin da Mijinta ya Damkamata.
Diza kuma tana ragamata ne saboda hakan da kuma dan kunyar Rumanan Datakeji in ta tuna Nuna yadda ta Kula da ita da Rasuwar Marigayi mansur,Ammh Kishinta Damkam yana nan acikin Zuciyar Diza duk iya kokarinta nata Danneshi wani Lokacin baya Boyuwa Tun Ballatana yanzu data kara sanin wanene Mastur.
Yana kiran kowacce a waya a kowacce rana saboda yaji ya Lafiyansu,Duk a iya kokarinsa na ya dawo Da wuri hakan bai samu ba saboda ayyukan da sukayi masa yawa yasa sai da Yayi wata Daya da kwana Biyar kana ya samu Dawowa,Da kuma karin Cuku cukun Karatun Rumana Zata Dora Tunda sun gama Service dinsu tun wanchan Satin sunyi Lonching,Rumana har Diza ta gayyata bataje mata ba bata Damu ba Tunda Mommy da Daddy sun je mata da Hajja da Mardiya Baba Habibu ne bai samu zuwa ba Rumana taji Dadi sosai Hatta su Umma Dake sokoto sun ji Dadin wannan karan da akayi ma Rumana.
Wannan Dawowar da yayi yana Dakin da Diza ne Tunda da zai Tafi Adakin Rumana ya gama kwana 2 dinsa kafin ya Tafi Dayake da Kansa ya Raba musu kwanakin.
Diza daman Tasan ita keda Miji Tunda yayi yawa yana kan Hanya ta kasa Zama ayi wannan ayi wannan a Dafa wannan a sauke wannan,Bayan ta gama aka Tsala wanka akayi Shigan alfarma bayan an Rangada Kwalliya Daman Daga chan Ciki anyi ta Gyare gyare,Saboda tana so yau ta Haukatashi ya Manta da kowa da kowa sai ita kadai kuma yau take da Burin tayi mai mganar Cigaban Karatunta.

Tafiyar Mota yayi shiyasa sai Wajen 10pm na Dare ya iso Duka Zaratam matan nashi ba wacce ta Runtsa suna ta kiransa Tun yana Hanya Domin suji ko ya kusa karisowa,Tunda sukaji Hon da Budewar get kowacce ta Fito Daga Shashenta Cikin kayattaciyar kwalliyarta Diza Tayi mamakin ganin Rumana itama Cikin adonta na wani Less Riga da sikat ya kamata karma ma sabo ne Tayi Daurinta Zahra Buhari Tayi matukar kyau Ita kadai ta Fito kila Mansur Karami yayi barci ne.
Abun ya sosa ran Diza ganin ai ita kadai ya kamata ta Tari  Mastur saboda ita kedashi ayau din ammh Sai Rumana tazo Zata mata mata ranta ai Diza bat taji Kamar ta Mutu ba  sai da taga Rumana ta Rigata isa ga Motar Mastur din Tun kafin ya gama parking ta Bude mai Murfin Mota Tanayi mai wannan Munafukin Mirmishin nata wanda Diza ta Tsana Da farko taso ta jure itama ta Kariso sai ta kuma Kafafuwanta suka gaza Daukanta ganin Mastur na Fitowa ya jawo Rumana jikinsa ya Rumgume kamkam Cikin Shauki da wani Farinciki da Muradi mai girma
Wannan Mugun ganin da Diza Tayi yasa ta tsaya Cak Ta kasa gaba ta kasa Baya Ta kuma kura musu ido Tana jin Zuciyarta na Bugawa ganin in ta Cigaba da kallonsu Zatayi samun Bugawar Zuciyasa yasa ta juya kawai Zata koma Shashenta sai taji an Riko Hannunta ko daga yanayin Zafin Hannun ta Fahimci ko waye Mastur ne,juyo da ita yayi Lokaci Daya yana Fadin"Taya zaki juya alhalin baki zo kin min Oyoyo din ba Uhm Amarsu..!
Yafada Cikin Zolaya,Lokaci Daya Ya Rumgumota jikinsa Har Lokacin yana Rumgume da Rumana itace ma ta Zame Jikinta tana yar Dariya ganin yadda Sam Diza Fuskarta ba Fara"a.
Rumana Tayi saurin Saita kanta Tana Fadin"Bari na Shiga Ciki..Sai da Safe..!
Tafada Tana Sakin Mirmishi Lokaci Daya Tana mikama Diza Karamar jakar data Dauko Daga Motan Mastur,Diza kamar bazata karba ba sai dai ta karba Fuskarta ba Fara"a Tayi gaba kawai ganin Mastur din ya Riko kafadan Rumana suna mgana kasa kasa bata san me suke cewa ba ita dai ta Shige da Sauri Har Tana Tuntube ganin in ta Tsaya ta Cigaba da kallonsu Zuciyarta Zata sakata aikata abunda bata yi Niyya ba.
Diza tafi Minti Biyar da Shigowa Kafin ya Shigo Shima a  gajiye yake sosai ga yunwa yana ji,Kamar Ta Sharesa sai taga Rashin Dacewar haka Ita ta Taimakamai yayi wanka ya Rama Salollinsa Kafin tajashi Saman Dinning ta Zubamai abincin Data Wuni tana Shiryamai yaci yana santi wanda Duk cin nashi ma ita ta Rika bashi a bakinsa,shima Bayan yaci ya koshi ya ci da ita sai da ta koshi kana ya kyaleta Daganan ya Dauketa Cak sai Cikin Bedroom dinsu,a tsakiyar gadonsu ya Direta Cikin Lokaci Ya Fara Nuna mata irin Zalamarsa da kewar ta da yayi itama a kage take Da sauri ta Rika Taimakamai Da Zafi Zafi suka Rika aikama juna Sakonnin junansu,Cikin Lokaci kankani suka Rikita juna bakajin komai sai Tashim Numfashinsu Lokacin da suka gama Raba junansu da Suturun Jikinsu.
Shudewar Awanni uku Bayan Lafawar komai sun yi  wanka Mastur ya Sanya karamin Wando 3quater,Ita kuma Diza Ta sanya wata Yaloliyar riga karama mai Budadden Kirji,Ta manne a jikinsa kanta na kan kirjinsa Tana wasa da kananun gashin Kirjinsa Shi kuma Yana Shafa gashinta kanta zuwa Bayanta Kowannensu yayi Shiru suna Sauraran Bugawan Numfashin juna.
Diza Kuma acikin Ranta tana ta auna irin yadda Zata Tsara kalamanta Wajen Tambayan Maatur izinin Cigaban karatunta,Har dai ta samu matsaya Shiyasa ta muskuta Tana Fadin"Ya Mastur..!.
Cikin sanyin muryanta Shima amsa mata yayi da Fadin"Ban yarda ba..Bana son wannan yaya..Ko ki sauya min suna kamar yadda Ruma ta sauyamin ko kuma ki rika kirana da Sunana kawai..!
Yafada Cikin Rada in ba ita Datake kusa dashi ba bazata jisa ba Saboda Salon muryan Daya sa yayi mganar.
Ranta Tuni yayi bakikirin Da jin sunan Daya ambata sai taji Bama zata iya Sauyamai sunan ba,Duk a abaya tasha Auna irin sunayen da zata Rika kiransa Dashi ammh a yanzu Daya ambaci Rumana ta Rigata sai taji abun ya Fita kanta.
Cikin Haka ne taji yana Fadin'Umh ina jinki..!
Sai alokacin ta Daidaita kanta Tana Kara Shafa Kirjinsa Ta Fara Fadin"Daman ina so na Tambayeka ne ko nace neman izininka..!
Sai ta dakata Tana jan Numfashi Yana Kara Riketa yace"Izinin me Hadiza..?
Dakyar ta samu jarumtar Cigaba da Fadin"So nake ka barni na koma makaranta..Nima ina so na Cigaba da Karatu In ka amince zan yi Jamb in na samu sai Daddy ya Min Hanya na samu ko nan Abu ne..!
Tunda ta Fara mgana ya Cika da mamaki bai katseta ba sai da ta gama kana yayi Mirmishi kawai batare da yayi mgana ba,Sai da Tagaji ta Dago Tana kallonsa ta Dan Hasken Dumlight din Dake Dakin tace"Kaji..!
Ajiyar rai ya Sauke kafin ya Mike Zaune Lokaci Daya ya saka Hannu ya kunna Hasken Wutar Dakin,Haske ya bayyana Suna kallon Fuskokin juna shi da ita.
Wani irin kallon kin makara yayi mata kafin ya karkace kai yace"Ki bar wannan mganar bamai yuyuwa   bace..!
Yafada kai tsaye da Sauri Diza tace"Saboda mene..?
Kura mata ido yayi kafin yace"Saboda ke kika zabi hakam Tun Farko..Lokacin da akayi ta baki Zabin karatun ai kince bkya Ra"ayi sai yanzu da Lokaci ya kure miki..? Ki bar mganar komawa makaranta hakan bazai Taba yuyu ba..!
Yafada Lokaci Daya yana komawa ya kwanta Diza da wani Kololin bakinciki ya taso mata,yasa Hawaye ya Cika mata ido har ya Zuraro mata,Cikin Takaici tace"Saboda nace bana Ra"ayi a baya..? Ai ba Hujja bane..Tunda yanzu nace ina Ra"ayi sai abarni nayi in fa adalci Zakayi..!
Yana jinta Kamar bazai Tamka ba sai chan yace"Wannan shine adalcin bakisan ance Apportunity Comes ones in Life ba..Kin samu Dama kin yi wasa da ita yanzu kuma ta Riga ta wuce ki Har Abada bazata Dawo ba..!
Jin haka yasa ta Fashe da kuka Cikin kukan Take Fadin"Dole kace haka..Ni ka hanani Nayi karatu ammh ga Rumana nan ka barta Tayi karatu ta zama Likita bai isa ba yanzu hakama wani karatun zaka kara Biyamata Tayi Har sai ta gaji ita baka ce Damarta ta wuceta ba sai ni..Daman ba Tun yau ba na Fahimci baka min adalci Tsakanina da Rumana akomai ita kake ambata kafin ni kada dai ka manta Nice ka so Tun Farko ba ita ba..Ko yaya Matar sotafi Matar Chuse Daraja..!
Ta karishe Fada tana wani Gunjin kuka Duka kalamanta Daki Daki suka Shiga kunnuwansa Lokaci Daya yaji bacin rai ya Rufeshi Zuciyarsa ta Fara zafi wanda yasa yayi saurin Mikewa yana bin Diza da wani kallon irin Kada ki kara mgana in ba Haka ba Ranki ya Baci.
Bayason Bacin rai Shiyasa ya Mike Daga kan gado zai barmata Dakin ganin haka yasa Diza ta Dago Tana Fadin"Meyasa kayi Shuru..? Kayi mgana mana ai kasan gaskiya na Fada..Kuma indai Zata Cigaba karatu acikin Gida nan Nima sai na koma makaranta..!
Yadda ta Fadi mganar ne yasashi Dawowa Cikin Dakin agabanta ya Tsam yana Binta da kallo kafin ya Fara mgana Cikin bacin Rai"Rumana zata Cigaba da karatun ba iya anan Gida Nageria ba in kasar waje take son Zuwa zan kashe mata Daga naira Daya har Miliyan Dari tayi karatunta..Ammh ke Biyar dina bazan kashe akan ki koma makaranta ba Infact ma bada Izinina ba Ballatana yardata ba..Sannan mganar Matar so ko ta Chuse kin Jahilci Lamarin Soyayyah Diza yes ban yi miki karya ke na Fara so kuma ke Zuciyata taso har yau har gobe..Na yarda An aura min Rumana ba domin bana ina sonta ba ammh Tafi karfin matar Chuse a wajena Domin ita din wata kaddara ce mai Daraja da kima awajena..Tunda nake da ita Bata Taba maidamin mgana ba bata Taba fada na Fada ba,Bata tabamin Korafi ba,Bata taba Ganin Laifina ba Ita din mace ce mai Uzuri Biyayyah kyawawan Hali da sanin yakamata Tarbiya natsuwa da Yakana Shiyasa Cikin Lokaci ta Shiga Raina ta mamaye Fili mai girma acikin Zuciyata Ta samu girma mai girma acikin Zuciyata wanda Wlh Tallah zan iya Rantse Miki ke Dana so baki Samu ba..Ki Kama kanki da Harshenki akan Rumama Tafiki Daraja awajena Zuciyarta mai kyau ne a kan kowa bata Taba Nuna Kishi ko kyashi akanki ba Ammh ke ba Tun yanzu ba na Nadade dalura da Take takenki akan Rumana Ke banda ma Sakarci Matar datake kula da Danki Taci kashinsa da komai nashi bata Yarda ta samu Cigaba ita kadai ba sai dake ammh ki na Mganar Komai sai nace ita? Kada ki manta itace Matata ta Farko Uwargidata,Kuma bari na gayamiki wani abu guda Daya ko abaya Ba kin Rumana nake ba sai dai ke Zuciyata take so..Ammh Wlh Tallahi Zuciyata na Daraja Rumana tana Burgeni har wani Lokacin In yi ta addu"an Dama ace Dama ace Rumana ta Zama ke Diza Saboda yadda komai nata yayimin a Tsagin danake son mace ta kasance kuma karatu Rumana Shine Burinta Bani na Fara sa mata Burin Tayi Karatu ba ita din da Abunta na ganta ita ta sani na kara Tabbatar ma kaina Duk wanda yasa abu a ransa zai iya to Tabbas zai iya..Ki shiga Hankaliki Diza na Fadamiki..!
Ya karishe Fada Cikin Zafin Zuciya kafin yaja Blanket da Filo ya Fice Fuu Lokaci Daya yana Rufo mata KofarBedroom din da karfi kamar zai Balla nan ya barta ta Baje akan gado Tana kuka da Ihu Tana Fadin"Rumana
.!Rumana!kin gama Dani kin gama da komai nawa..!
Haka Diza Take Fada tana Rafzan kuka Kamar ance Uwarta ta Mutu.
Haka Mastur ya Fito Falo ya kwanta kan kujera yana Sauke Numfashi Bacin ransa na Raguwa Lokaci Daya yana mamakin Diza bata da Kirki ko kadan Tunda Har zatayi iya Fadin haka Rumanan Data Shige gaba wajem Tabbatuwam auransa da ita ammh yau itace take Fadin komai sai yace Rumana..?kalaman sun batamai rai kuma mganar karatu bazatayi shi ba,ba Domin bai da kudin da zai Biya mata ba sai Domin ya nuna mata Darasin haka a rayuwa sai dai ta Cigaba da abunda ta zabar mata kanta.
Ranar Suka kwana A bambamta waje,Diza a Bedroom ta kwana Sai shi kuma afalo Diza kwana Tayi kuka da wani Tsanar Rumana acikin Ranta,Shi kuma Barcinsa yasha bayan Ya watsar da Sha"anin Diza Tana ciki da asuba ya Shigo yayi wanka ya saka Jallabiya ya Fita kuma Tunda ya Fita bai Dawo ba sai Wajen 10pm na Safe Ran Diza kamar Tayi Bindiga saboda Takaichi Domin Tana Da Tabbacin Shashen Rumana yaje yayi zamansa Taga shaida Domin Tare da Mansur karami yashigo,Duk da abunda ya Faru Tsakaninsu Jiya bataki tashi Tayi Breakfast, ba ammh Jibi abunda yayi mata Domin Data gabatar mai da Breakfast din a Dakile yace mata ya koshi,ga wani karin abun Haushi Mansur karami kiri kiri yaki zuwa wajenta ya makalema Mastur Daga Baya ma sai ya saka kuka yana kiran Anty Anty,Ran Diza ya Baci bata san Sadda ta Dugure mai kai ba Tana Fadin"Ba Anty ba Anto..Don Ubanka ba itace bace Uwarka nice nan na Haifeka..!
Tafada Cikin bayyana Kishinta ganin bayan Mijin ma Har Danta Rumana Take shirin Kwace mata Mastur na wajen kallomta kawai yayi kala bai ce mata ganin Diza ta Fara Fita Daga Hayyacinta.
Daukansa yayi ya maida ma Rumana shi kuma ya Dawo yayi wanka ya Sauya Kaya Riga da wando na kanfanin Armani batare da yace ma Diza ci kanki ba ya Zari key din Motarsa ya Fice Tana ta bakin Window din Shashenta ta gansa ya Fito Dauke da Mansur karami Rumana na Bayansa Cikin Shigan alfarma kamar sun san Tana kallonsu Suna ta Hiransu suna Dariya Cikin Begem juna agaban idonta Mastur ya Bude ma Rumana Mota ta Shiga kana ya Rufo ya koma ya Shiga bangaran Direeba ya tada Mota yayi Hon megadi ya Bude mai get suka Fice.
Sai sulalewa kawai Diza Tayi anan wajen tana kuka,Kukan Data rasa na Wani Dalili ne na kwace mata miji da Rumana Tayi ko na kwace mata D"a ko na Mganganun da Mastur ya yabamata ne duk ta rasa Dalili ita dai kuka take da Dukkan Zuciyarta Ta kuma rasa mafita ko madafa.
Ayayinda Ta bangaran su Mastur basusan Halin da Diza take ciki ba Domin tun safen nan suna Cikin Abu Samaru Mastur nayi ma Rumana Cuku cukun Fara Resedency dinta wanda Daddy ya kira Dr.Hambal shine ya wanci yayi musu Shige da Fice Basu Dawo ba sai yammah abinci ma a Cafteria suka Ci,Basu gama Komai ba sai zuwa gobe Za"a karisa Duk da Dr.Hambali yace ba mtsala Mastur ya Fitar da kudi Sosai kan karatun Rumana Abunda ya kara Girma acikin Idanuwanta,Anan asibitin Chika Zata Fara Karatun nata.
Da suka dawo ma Hanwa suka yada Zango sai 9pm suka Dawo kana Mastur ya Raka Rumana Shashenta kafin ya iso Shashen Diza ya isketa Tayi kwalliya ammh Tayi Dama Dama da ita da Hawayen da kuka da majina Saboda Bakincikin Abunda Mastur yayi mata yau Tun dazu tagama Girki Tayi kwalliya Tana zaman jiran Sa ammh don Wulakanci sai yanzu ya Dawo gidan kuma ko kallo bata ishesa ba Ballatana wani abincinta haka ya Shige Bedroom yayi wanka ya Sauya kaya Daman yayi Sallar sa a Hanwa ya kuma ci Abincin Hajja.
Shiyasa bai kara bi ta kan Diza yayi kwanciyarsa Hankalinsa kwance,bai san ya ta kare ba Domin bata kwana adakin ba da Safe ma wajen Rumana yaje ya karya ya Bige da ce mata Diza ce bataji Dadi ba ta ce zata je ta Dubata ya hana yau ma kamar Jiya Samaru suka wuni basu Dawo ba sai da komai ya kamallah nan da Sati Biyu Rumana Zata Fara karatu kan Bangaran yara wato paediatric Doctor kenan,Saboda Dr.Hambali yasa aka makala sunanta Cikin wadanda zasu Fara a Shekarar.
Diza kuwa ba ita keda Mastur ba Sshiyasa da suka Dawo bata sakashi a Ido ba Cikin kwana Daya da yini Duk ta Fige ta Rame kamar ba Diza ba yar kwalliya,Rumana kuwa kwana sukayi Farantama juna rai ita da Mastur da Safe suna karyawa yace ta Shirya da ita zai Tafi porthercourt sai ta Dawo bayan Sati Biyu.,kafin ta fara karatunta
Rumana Tayi mamaki ta Dago Tana kallonsa Domin ta gama Lura da akwai abunda ke Faruwa Tsakaninsa da Diza duk da batasan ko miye ba kuma bata so ta sani Tunda ba Huruminta bane taso tayi magana ammh bai Bata Damar haka ba Taga ya Dauke kansa bayan ya Hade Fuskarsa bayaso tayimai wani korafi.
Rumana Tayi alkawarin zama da Diza Lafiya cikin Aminci bazata karya alkawarinta ba itace Amarya da ita ya kamata ya Tafi,Wata zuciyar tace mata ai yasan da itan ya nemeki..? Wata kuma ta kwabeta da Kada kiyi Haka Rumana ko bakomai kece Babba Wannan girman da Allah ya baki ki Rikesa.
Da wannan Tunanin ta Shiga Shashen Diza da yammah Bayan Fitan Mastur da Mansur karami Koda ta Shiga Diza na Cikin Bedroom Dunkule cikin bargo Ta gama kukanta Barci ya kwasheta sai da Rumana Tayi ta sallama da Knooking kana ta jita Kafin ta taso Tazo ta Bude mata yanayin da Rumana Taga Diza sai ya bata Tsoro Cikin mamaki take Tambayan Diza ko Lafiya ganin yadda ta wani Yi iri da ita kamar ba Diza yar kwalliya ba.
Diza Bata so tayi ma Rumana wani Rashin Mutumci Saboda Tana ganin Girmanta kadan Shiyasa ta kauda kai kawai batace mata komai ba ganin haka yasa Rumana ta taka zuwa ga Dizan ta Riko hannunta Tana Fadin"Don Allah Diza ki daina Daukana amtsayin Kishiyarki kiDaukeni a mtsayin yar"uwarki Kamar yadda na Dauke ki Don Allah..!
Kalaman Rumana sun kashe ma Diza Jiki idanuwanta suka Ciko da kwallah ta Duba Irin Halin Rumana ko abaya Duk irin cin kashin Datayi mata bata Taba Daga ido ta kalleta ba Ta yarda da mganar Mastur Rumana ta Dabam ce kuma kyawawam Hallayarta su suka Sayo mata girma da kima wajen kowa ta Tuna Sanda Take Cikin Halin Rashin Mansur Rumana Tayi ta Dawainiya da ita Bata ko Damuwa da kanta koda yaushe Tana Tafe hanwa saboda ita uwa uba ga D'anta Da Rumana ta Daukeshi Tamkar ita ta Haifeshi ko Saboda Haka ya kamata ta Raga mata ta Daina jin Haushinta da kishinta,Mace ce wacce ta Sadaukar da komai nata saboda ita da Mastur bai kamata Rumana ta Chanchanci haka ba Sam.
Ammh ba laifinta bane Laifin Zuciyarta ne Da kuma Halittarta na Mugun Kishi,Sai dai zata yi yaki Da hakan ko ta samu Zuciyarta ta samu Salama da Sukuni,nan da nan Nadama ta kama Diza ta fashe da kuka ta Fada Jikin Rumana tana Fadin"Ki yafemin Rumana don Allah..Ni bam chanchanci ki rika Kallona yadda kike kallona ba..Ni ban Chanchanta ba Zuciyata bata d...!
Bata bari ta karisa ba ta Dagota ta Rufe bakinta Tana Fadin"A"a kada ki sake Fadin haka Diza..Ni wlh har acikin Raina banta Rike ki da wani abu ba..Haka nake Diza ko abokin Fada bani dashi Tundaga Rayuwar kuruciyata Har zuwa Girma na..Sai yanzu da na zama matar aure mace mai Daraja zan Chanza Daga yadda nake..? Kada ki Damu Diza na Fahinceki kowacce mace da yanayin Kishinta,Sai dai zan Baki Shawara ki yi kokarin Koyin yadda Zaki Sarrafa naki..Wlh Tallahi zaki sameni mai kiyayewa kuma mai aikin da Hadisin nan na Manzon sallalahu alaihi wasalam dayace Kaso ma Dan"uwanka Abunda kake so ma kanka..!
Diza Sai ga Hawaye Sharri sun zubo Mata ta Riko Hannayen Rumana Tana Fadin"Nagode da Shawaranki kuma Insha Allahu Zaki Sameni yadda baki Zato ba..!
Rumana Cikin Jin Dadi ta saka Hannu ta Share ma Diza Hawaye Tana Fadin"Yauwa ko kefa..? Ki je kiyi wanka Diza Amaryace kefa..Ki kalleki kin zauna ba kwalliya ba gyara,Ki kuma Shirya kayanki gobe Tare da Angon naki zaku wuce porthercourt..!
Da mamaki Diza ke kallon Rumana kafin Tayi mgana Rumana ta Rigata da Fadin"Karki ce komai..Kedai kawai ki Shirya..!
Kai Diza ta Kada Tana yi ma Rumana Godiya bata jima ba ta Koma Shashenta ita kuma Diza da karkashinta Tayi wanka Tayi kwalliya Tana kokarin yaki da Zuciyarta ta zauna Tana Dakon Jiran Dawowar Mastur sai chan Dare taji Dawowarsa Daman ta Guduri Niyar gyara Shiyasa ta saka Mayafinta ta baro Shashenta zuwa Shashen Rumana ta iske su suna Dinner Rumana taji Dadin ganinta nan ta tashi ta Tarbeta Mastur kallo Dayayayi mata bai kara ba,Kan Dinnig din Rumana ta kariso da Diza ta Ja mata kujera ta Fara Kokarin Serving dinta Mastur na ganin haka ya Ture kujera ya Mike Rumana na mgana yace ya koshi Zai wuce Daki Mansur karami ya saka Rigima sai da ya Daukesa suka Shiga Ciki Duk sai Diza taji ta Muzanta,Rumana ta gama yadda akwai Wata baraka Tsakanin Ma"auratan sai dai bazata ce komai ba Tunda Daga Dizan Har shi ba wanda ya Fadamata bazata shiga Abunda ba Huruminta bane,sai dai Tana Yi musu Fatan su Daidaita kansu.
Rumana ita tayi ta jan Diza da Hira Bayan sun gama Cin Abinci suka Dawo Falo Tun Diza bata saki Jiki ba Har ta saki Jikinta da Rumana suna ta Hira Har bata san Dare yayi bama
Sai wajen 10pm Rumana ta Rakata zuwa Sheshenta Tana kara Jadaddamata ta Shirya Tare zasu wuce da Mastur da to kawai ta Bita ammh ita kan Jikinta yayi Sanyi Tagama yin Nadamar Abunda ta aikata.
Rumana koda ta Shiga Ciki Mastur da D'ansa sun Dade da yin Barci itama wanka tayo tayi Shafa"i da wuturi,kafin itama tazo Cikin takwanta,Ta shiga Tsakiyarsu Mastur ya Rumgumota Daga ita Har Mansur din Ya Hadesu waje Daya suka Shige Cikin Blanket Cikin Soyayyah da Muradi mai girma.
Da asuba Mastur yana ta Shirin Tafiya yaga Rumana bata Shirya kayanta ba,Daman ya Fadama Hajja mansur karami zai dawo wajenta kafin su Dawo,Kuma har Mommy ya Fadama da Rumana zai Tafi wannan karon kuma sunyi Na"am da hakan Domin ko bakomai Zamanshi da matarsa yafi ya Rika Tafiya shi kadai Tunda Yana da Muhallin da zata zauna.
Tana Tayashi saka Tektie dinsa ya Kalleta yana fadin"Kin Hada kayanki ne..? Kai ta Girgizamai Tana Fadin"A"a..! Cikin mamaki yace"ammh kinsan da wuri zamu wuce ko..?Rumana na Mirmishi Tace"Nasani Ta Shirya ai wacce zaku Tafi taren..!
Cikin mamaki ya kallonta kafin yace"Ita wa..?
Kai tsaye tace"Diza mana..itace Amarya da ita zaka Tafi..In na samu Hutu sai muje tare..!
Mastur ji yayi Rumana ta gama Raina mai wayau da Hankali Saboda Haushi ko kara kallonta bai yi ba yana ji tana mai mganar Breakfast ya Dauki Jakarsa Yana Fadin"Bana Bukatar Abincinki.Tunda kema bazaki ba ba sai kin gayyatomin wata ba..Ai nasan da ita nace ke din ko..?gud dukkanku ku sha Zamanku..Nagode..!
Daga Haka ya Figi Key din Motarsa ya Duka yayi ma Mansur karami Kiss wanda ke Barci ya Fice Rumana ta Bishi da Sauri Tana Bashi Hakuri bai Tssya Sauraranta ba
Suna Fitowa sai ga Diza ta Fito Itama Cikin Shirinta Harda Trolley dinta agabanta Komai ya Faru ya Shige Motarsa Bayan ya saka Jakarsa yayi Hon megadi ya wangalemai get ya Fice abunsa,Rumana sai taji bata ji Dadi ba Diza kuwa Daman ta Dai Shirya ne ammh,Tasan hakan zata Faru Dukkansu ba wacce Tayi ma yar"uwanta mgana kowacce ta Shige Shashenta Cikin Sanyin Jiki.
Rumana tayi ta kiran Wayar Mastur yaki Dagawa Har Washegari bai Daga kiranta ba Daga karshe ma sai ya kashe wayarsa Ita kadai ta yanke wani Shawara tace Diza ta Shirya kwana daBiyu ta Tafiyarsa,Kaduna sukaje Da Cuku cuku da komai Diza ta samu Jirgi zuwa Porthercourt,Diza Tayi ta mamakin Rumana sai da taji Taruwan Hawaye Daman tace mata Tazo da Shirinta ammh batace mata ga inda Zata ba..Bata bar kaduna ba sai da Jirginsu Diza ya Daga bayan ta Jadadda mata bayan sun Sauka ta Kira Mastur ta gayamai Tana Filin Jirgi ta Tabbata bazai kyaleta Daga karshe ta bata Shawaran ta bashi Hakuri ita kuma in ya Dawo sai su karishe dashi,ita da Mansur Karami ne Dare yayi mata sai ta Biya Gidansu Basma ta kwana Bayan ta Kira Mommy ta Fadamata Ta Rako Diza kaduna gata zata kwana Gidansu Basma.
Mommy tayi mamakin jin Diza ta Bi Mastur alhalin shi yace da Rumana zai tafi ganin Rumanan bata mata wani bayani ba yasa Mommy bata nemi taji ba"asi ba.
Bangaran Diza kuwa sai Bayan mangariba ta sauka a Porthercourt,Saboda Jirgin bai taso da Wuri ba Tana Sauka ta Kira Mastur sai da tayi mai kira Biyar ajere kana ya Daga Daman Yaga Text din Rumana ta Fadamai Diza na Hanya bai yi mamaki b Illah Jinjina Karamcin Rumana da yayi Yana Dagawa yace mata Sargent Inuwa zai zo yanzu ya Dauketa.
Haka kuwa akayi shi yazo ya Dauketa Har Heaquater su acikin Gidan da ya zama mallakin Mastur shi din yana wajen aiki bai Taso ba Diza wannan ne zuwanta karo na Farko,Ammh Duk da Haka bata zauna ba Tayi amfani da Shawaran Rumana ta Zage ta Fara Tsabatace gidan ta Saka Turaran Kamshi  Daganan ta Fada Kitchen akwai komai na Cefane, tayi Girki mai rai da Lafiya Bayan tagama ta Fada Bedroom dinsa Inda Tayi ma kanta Muhalli tashiga wanka taxo ta Tsantsara kwalliya Cikin wata Arniyar Rigar barci wacce bata Boye komai ba kuma tayi ma kanta wankan Turaran Humra mai kamshi
Sai 11pm Mastur ya Shigo Gidan ya Zata ma Diza ta kwanta Ya shigo mata da Takeway,Sai dai kuma ya Tarar da gidan Cikin Ni"ima kamshin Turaran Daki Dana Abinci na Tashi bai gama mamaki ba sai da Diza ta bayyana agabansa Duk Dauriyan Mastur kasa Dauke ido Yayi Daga kanta ganin Tarkonta ya kama yasa ta Fada Jikinsa Tana kukan Shagwaba Lokaci Daya tana Bashi Hakuri bai ki karbanta ba Haka ya Zubar da Abunda ya Shigo Dashi ya Chachumeta zuwa Cikin Daki suka Fada kan gado Daganan zencen yasha Bambam da sunan  Hukuncin Dayake Bama Diza na Laifin data aikatamai sai da suka ntsa sukayi wanka suka Fito Cin Abinci Shi yayi Feeding dinta itama tayi nashi Bayanan kuma aka sake Kwakwuman junan Mastur yana ta Famshen Bashin da Diza taci.
Sai Washegari da Mastur yaje Office Ya kira Rumana yana Mata Fada ita dai Hakuri kawai ta bashi Shima din ma Taku ne irin na Maza ammh wane shi yaki Godema Rumana kan wannan alfarman Datayi mai..? Ya saka mata albarka yafi Cikin Botiki.
Tunda ga Lokacin komai ya Daidaita wani Sabon Honey moon ne Diza da Mastur suka Bude a porthercourt,Daman ba wanda ya san ya kara aure sai Sargent Inuwa shine ma yake Fada musu ganin Dizan da Mastur suna Fita yawom Shaqatawa da yammah ko da Dadaddare yanzu su Yallabai an Daina kaiwa Dare a office an samu wajen Hutawa Yan sandan Dake kasansa suna ta Gulmansa,Ganin yanzu ya Daina Cika ma kansa aiki kamar baya Tunda ya Samu Diza a kusa Dashi,Rumana suna yawa dasu sosai koda yaushe ta Fara zuwa Makaranta sai take barin ma Hajja Mansur karami in ta taso Taje ta Daukesa su dawo gida shi ke Debemata kewa shi kanshi yasan waya in Mastur ya kira yayi ta Tsalle yana mai gauranci bai Damu da wata Diza ba itama sai take ma Rumana kara.
Wannan Tafiyan Mastur yadan Jima sai da ya kusa wata Biyu kana suka Dawo Dukkansu sun Sauya sunyi Kiba Dagashi Har Diza,ita Har da Tsaraban Cikin Porthercourt wanda ta dawo Dashi ba wanda ya sani sai da yayi Sati Daya ya koma Shi kadai Bayan Tafiyarshi Diza ta Fara Laulayi Har da su kwanciya asibiti Dole ta koma gida Wajen Mommy Tunda Rumana na zuwa makaranta Farinciki wajen Mastur da Rumana ba"a mgana ashe itama tana Makale da nata ba wanda ya sani sai ranar a makaranta ta Fadi ana gwadata itama sai ga Ciki da Mastur ya samu Labari kamar ance ya Shiga Aljannah bai iya zama ba sai da ya Tattaro ya zo ya yi jinyar Matan nashi da kansa Mardiya sai ta Dawo nan tana Taimaka musu Sati Daya yayi ya koma Lokacin sun warware har Rumana ta Cigaba da zuwa makarantar ta Diza kuma bata zuwa Ko'ina Cikinta yafi na Rumana Laulayi Catering dinta sai ta ga Dama ta leka komai Tana Gudanar dashi ta wayanta.
Iyaye da yan"uwa kowa sai taya Mastur Murna yake kyautan Allah a lokaci Daya Alhamdulillah Umma da Abba suma sai son barka zasu samu Jika akaro na Farko.

******

*MURFI..*


*After 10 Years..*
Bayan shekaru goma da suka Gabata.

Dr.Rumana Muhammad wamako Yar kimamin Shekaru Talatin da Biyar a Duniya zaune take Cikin Babban Office dinta Dake cikin Asibitin Specialist Hospital Abuja,Bangaran yara paediatriction Inda anan take aiki Shekaru Uku da suka Gabata.
In ka kalleta Dole ka kara kallonta Kamar ba itace ta mallaki wannan Shekarun ba Har yanzu yarintarta da wannan Mirmishin nata mai karamata kwarjini da kima Sanye take da Doguwar riga kirar Armani Tayi Rolling din mayafin Rigar sai wani Siririn glass din Dake idanuwanta mai kara mata karfin gani ta ko"ina Rayuwa ta yi kyau Sai son barka.
Ashekarin da suka Shude abubuwa Dadama sun Faru an samu rashi,an kuma samu karuwar abubuwa Dadama acikin Rashin da akayi sun Rasa Ayya Shakarun baya Allahu akbar Allah ya jikanta da Rahma
Sun samu karuwa Domin tayi Haihuwan Farko ita da Diza  Diza ta Rigata Haihuwa da Sati Biyu kafin itama ta Ssuka Dukkansu mata suka Haifa sai suka ci Hajja da Mommy,Wato Hajara da Asiya kenan kuma suna kiransu da Hajja da Mommy ne suna Boye sunansa,Bayan Mommy,Rumana ta kara Haihuwan Habib wanda yaci Sunan Baba Habibu sai Diza Data kara Haihuwan mai sunan Umma,suna kiranta da Ummanti,Rumana sai ta Dakata da Haihuwa saboda Karatunta sai Diza ce ta samu mai sunan Daddy Sunusi,sai da Rumana ta gama karatunta tayi ma Mastur Takwara Shima,Wanda Dagashi bata kara Haihuwa ba sai Diza ce ta Kara Haihuwan Mace taci Ayya suna kiranta da Ayya,Gidan Mastur Ya cika da ya'ya Alhamdulillah,Ahalin Dayake Ciki yanzu ya tashi Daga Dcp Mastur ya koma IGP Nakasa Gabadaya Shekaru Biyu da suka Gabata,Suka Tattaro suka Dawo nan Abuja da Zama,Cikin katon Gidansu da Mastur ya mallaka mai Dauke da Shashi masu Girma da tsari,
Mastur ya cika Burin marigayi Mansur yakai Duka iyayansu Makka,Daddy mommy,Hajja Baba Habibu da Baba sule da Inna Zainaba sai Kawu Usman da Inna Balaraba wadanda Mastur ya sa aka gyara musu Gidansu ya koma na Zamani.
Sai bayan sun dawo ne Shima Dashi da Iyalansa Gabadaya sukaje sukayi Hajja,Daganan suka wuce India sukayi sati Biyu suka Dawo gida saboda Yara da karatunsu.
Lokacin kafin su koma Abuja yawanci Diza tafi zaman porthercourt,ita kuma Rumana tana Zaria saboda Karatunta sai ya zamana sai ta samu Hutu take zuwa ma Mastur,Yawanci yaran Diza duk ita ta Reno su ita dasu Hajja Diza dai ta kan Haifa Ta barma Rumana Shiyasa ko taki ko taso Rumana mace ce mai Girma da Daraja acikin Idanuwan kowa.
Gabadaya Mastur ya inganta Rayuwar iyayansa ya Dawo da Baba Sule da iyalansa nan Zaria agidansu,da suka bari Rayuwa tayi Dadi Mardiya tayi aure a kaduna har ta Haiyayyafa haka su Maryama da su Sakina kowacce ta zama uwa sosai,Basma kawar Rumana tayi aure anan zaria ta auri Sagir Allah yace shine mijinta yaransu Biyu,Haka ma Aisha bala tayi aure a lagos Ashekarar Data gabata itama Dayake ta tsaya Cigaban karatunta bangaran mata wato Gyneacologist

Rayuwa tayi Dadi sai son Barka Mastur ya Riga ya Dauke Dukkan Nauyin Dake kansa wanda abaya Dashi da Mansur suke Daukesa Albarka iyaye da yan"uwa bazata bar Zagaye dash ba.
Mansur Karami Dayake amsa sunan Mansur S.Mansur Doguwa yana Bording school anan Abujan sai sun samu Hutu yake zuwa Sauran yaran kuma suna Day ne anan garin Abujan Direba kai kaisu ko Diza ta kai su ta Dawo dasu Ita ta zama Hajiya yanzu manya Cateing gareta Har Abuja Da kaduna,Mastur ya Tallafa mata sosai ta Bunkasa aikinta da kasuwancinta yanzu bama Nageria ba Harta Kashashen waje sun san Labarin Diza Catering and Makeup da Diza Beuty Saloon.
Yanzu da suka Dawo waje Daya Diza ce ke kula da yaran duk da Rumana ta Dauko Juma jikar Goggo Jumai sun taho da ita nan Abuja Tana Taimaka musu,Ita daman Tun Safe take Fita sai yammah ita da Ogan da kansa Sai Diza agida in ba an kirata ta Fita yin wani bane wajen Catering dinta Tana gida Tana Hutawa.

*****

Rumana Tana tsaka da Duba patient Misalin karfe 6pm na yammah Sauri take ta tashi bata son Tukin Dare kuma Yallabai Mastur sam bayaso Fada yake mata,Tana Haraman Tashi ne kiran Diza ya Shigo wayarta ta Daga Tana Fadin"Ga ni nan a Hanya..Yanzu na Tashi Mamin yara..!
Haka take cemata Tunda haka yaran ke kiranta ayayinta ita kuma suke Cemata Mama Diza Dagachan Bangaran Tace'Mamansu Gida fa yau ba kowa..Duka yara basa nan..!
Rumana cikin mamaki tace"Bangane ba? basu Dawo Daga School bane..!
Diza tace"Sun dawo kin mata yau suka samu Hutu..suna Dawowa suka Iske Direban Daddy yazo suka Hau Shiri sai sun Bishi na Kira Yallabai na gayamai yace na Tattarasu duka ya kaisu Wajen su Hajja.."
Rumana Tayi Dariya Tana Fadin"Daman ance wannan karon Zaria za"aje Tunda wanchan Hutun Umma akayi ma shi.."Diza tace"Aikuwa su Mommy nachan na Murna yanzu muka gama waya da ita Har sun isa .Ban kira ki bane sanin kina aiki..!
Rumana tace"Yayi kyau muma ma Huta ina..Megidana..!
Diza tace"Dashi aka tafi..!
Rumana ta waro ido Tana Fadin"Na shiga uku..Yaron nan ya Cika Rigima mamin yara..!
Diza tace"Kuka ya Dinga yi Dayaga zasu tafi..Yallabai najin haka yace a hadamai kayansa a kaima Hajja Babban Mutum dinta..!
Rumana tace"Shikenan sai na kariso..!
Daga haka suka yanke kiran Lapcot dinta ta Dauka da wayarta sai Jakarta ta Fito Tana Amsa gaisuwan Likitoci da Nurse din Dake kai da kawo Tana Fita Haraban asibitin ta Shiga Motarta Kirar Prado ta Fice Daga asibiti.
Anguwan Maitama suke da zama nan ta Nufa ana Bude mata Wagegen get din ta Sulala ciki ne nan Motar IGP Mastur Habib Doguwa ta sawo kai Shima yana Daga Baya Direba na jansa,Kusan Lokaci Daya suka Shigo Gidan.
Rumana Data Fito sai da ta jira Mastur wanda Direba ya Budemai ya Fito Dan kimamin Shekaru 50 da wani abu Duniya ammh jin Dadi da Hutu sun Boye haka sanye yake da Uniform dinsa Domin Daga Villa yake sunyi ganawar Sirri da Shugaban kasa Tunda ga nesa suke sakin ma Juna Mirmishi kafin su Fara taku zuwa ga junansu.
Rumgume juna sukayi Cikin Shauki Mastur na Fadin"Dr na..!Rumana na..!
Itama Rumanan din Cikin farinciki take fadin"Yallabaina..Mastur dina..!
Dariya suka saka Gabadayansu Kafin su Nufi kofar da zata sadasu da Babban Falon gidan
Wani Dan Sanda na Binsu da wayoyin Yallabai.
Suna Shiga Falon da Sallama Kamshin ya Dakesu a tare suka Lumshe ido Lokaci Daya suka Furta.."Mamin yara..!
Suka Fada Lokaci Daya suna kallon juna Shi dai Dan sandan nan shiga yayi ya zube Wayoyin saman Wani Tamgamemin Glass Dake Tsakiyar falon ya sara kafin ya Fice.

Sun Fara takawa zuwa Tsakiyar Falon hannunsu Rike da juna Juma ta Fito Daga Kitchen Tana yi musu maraba da sauri ta koma Kirchen ta Hado Abun sha da Lemi ta kawo musu Lokacin har sum samu matsugunni a kan Daya Daga cikin kujerin Falon Rumana ta Tsiyaya Ruwa a glass cup Cup ta mikama Mastur itama ta Zuba Tana sha Tana mamakin ina Diza taShiga Juma ta kwalama kira Bayan tazo tace mata Ina Diza kafin ma ta bata amsa sai ga Diza tana Fitowa Daga Kitchen Tana Turo wani Katon tubur na glass Dauke da wani katon Cake taci kwalliya sosai da ka ganta kaga Dizan Mansur Dizan Mastur sai dai ta kara Girma da cikar Haihuwa data Hutu da jin Dadi.
Baki sake suke kallonta Tana Karisowa gabansu ta ja ta tsaya Tana Fadin"Happy 15 years Marrige Annivesery...Dr.Rumana muhammad wamako and ur Lovely Husband IGP Mastur Sulaiman Doguwa..!
Tafada Lokaci Daya wasu Fulawars na Zubowa ta saman kansu Cikin Sha"awa ta juya tana Dagama juma Hannu alamun jinjina itama ta Dagamata Domin tare suka Shirya komai.
Bakinsu yaki Rufuwa saboda Murna Gabadaya sun ma manta,Yau ne suke cika Shekaru goma Sha Biyar da aure Matakin Rayuwa kala kala sun taka da Farinciki.
Rumana sai Hawaye ya Ciko Idanuwanta Ta Rumgume Diza Tana mata godiya Dukkansu Mastur ya Hada ya Rumgume,Tuni Juma ta kawo Wukan yankar Cake karama Rumana da Mastur suka Rike hannu zasu yanka Cake Rumana ta Jawo hannun Diza ta Dora saman nasu ta Dagamata kai suka yanka gabadaya,Mastur shi ya Fara basu Dukkansu abaki kafin kowacce ta bama Yar'uwanta Lokaci Daya suka Tarovsuka Turama Mastur Cake abaki kamar zai yi amai yana Haki yace"Kai kai..Ku mugaye ne ko..?
Suna jin haka Diza da Rumana suka kalli juna kafin su Lakuti Cake din suka Laftamai a Fuska ya Kwabe Fuska yana kallonsu kafin yace'Lala..Mamansu da maminsu sai fa na Rama nima..!
Fadar haka yasa shima ya lakuti Cake din ya Dumfaresu da gudu suka Dare suna Darewa suka Fara Zagayen Falon Shi kuma yana Binsu yana Fadin"Mugaye sai na Rama..!
Juma Dake Kitchen Tana kallonsu ta Girgiza kai Tana Fadin"Ya Allah ka Cigaba da Dauwamar da Farinciki a wannan gidan da Zuru"arsu gabadaya..!
Ammh har gaban Abada bazasu Taba mantawa da Rashin da sukayi ba Rashin Mansur Sulaiman Doguwa wani Rashi ne daHar Abada wanda wannan ahalin bazasu mantashi ba,kaf yaran ba wanda baisan labarin Marigayi Baba Mansur ba Daga bakin Daddynsu ba haka kuma Office dinsa da Dakin barcinsa makale da Hotunan Mansur din da suke Dauka Lokacin suna raye.
Mansur karami ya san ba Mastur ne ya Haifesa ba ammh kuma Bashi da maraicin wani bango
Rumana ce uwarsa har gobe Mastur Ubansu Diza kuma Anty take awajensa..!


*Tammat Bihamdullahi*

*Alhamdulillah nan na kawo karshen wannan Labarin nawa..Abunda na Rubuta Daidai Allah ya bani ladansa Kuskuran Dake ciki kuma Allah ya yafemin ina Godiya Masoya da kuka Nunamin kauna wajen Siyan Littafaina Allah ya saka muku da alheri Sai mun hadu a Sabuwar Shekara Cikin wata Tafiyar..!*








*Shakira*
*Janafty*
*Intelligent writer"s asso*
*23/12/2021*