Skip to main content

SARAUNIYAR KYAU - Hausa Novels

💓*SARAUNIYAR KYAU*💓


 

 *_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️
───────────────────────
```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.}``` ✏️
     ____________(✪)______________
https://www.facebook.com/profile.php?id=100069755834980
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•


💓*SARAUNIYAR KYAU*💓
       
   👑_(The Glam Queen)_ 👑
       
         ```Takun Farko```

Story & Written By:

              *_The Nainarh KD_*

_In dedication to my dear Classmate Science G.S.S.S BELE ROAD._


*_Special Thanks to:_*

  - Official Muhammad Aufan Mahmoud
  - Afeefarth Abubakar Mai Kyau
  - Zaynerb Abubakar Mai Kyau
  - Aasief Mai Waje
  - Bardia Fazzan
  - Jieddarth Juraej Komai Naga
  Love you all 💞💖💘💗💝


*بسم الله الرحمن الرحيم*

*Page 1&2*


Abuja, Nigeria

Mai Kyau  District

Doguwa ce dirarra ƙyaƙyawa ajin farko wacce idan aka ce kyau to fa ana zuwa kanta an rufe ƙofar kyau. A shekaru ba za ta haura twenty years or twenty one years ba a duniya.

Akwai ta da diri wanda a Turance ake kira da Coca Cola Shape, tana da manya-manya kuma dara daran kyawawan fararen idanu masu shining, masu egg shape. Yanayin launin kwayar idon nata su ba blue color ba, haka ma ba green color ba sannan kuma ba ash color ba. Su dai ga su nan yanayinsu sky purple masu matuƙar shining da ɗaukar hankalin duk wani mahaluki.

Akwai ta da wasu kalar laɓɓa ƙanana sirara jajayen gaske da su, ga shape nasu gwanin ban sha'awa da burgewa. Daɗi da ƙari ga ɗaukar hankali.

Hancinta kuwa wani kalar dogon hanci ne wanda ya zauna daidai a kykkyawar fuskarta ga shi ɗan daidai. Tsayawa bayyana yanayin kyawunta ya zama kauyanci. Ta hada dukkan wasu suffofi da mace ke bukata don jan hankalin namiji.

Tana sanye cikin wasu dakakkiyar doguwar gown ƙirar Malaysia, wacce ta kama jikinta ɗas ta zauna. Gown ɗin mai gajeren hannu ce saboda haka sai ta ɗaura after dress sky purple mai adon stones masu bala'in sheƙi, ita kanta rigar da ke jikinta sky purple ce doguwa har ƙasa.

Dogon gashin kanta wanda yake asalin dark brown, ya sha gyara ta tufke shi da wasu shegun ribbon masu masifar kyau da tsada guda uku wanda hakan ya ba dogon gashin damar zubo mata har tsakiyar gadon bayanta.

Ga wani yalolon mayafi da ta yafa gefen kafaɗarta, fuskarta kuwa tasha light make-up, ta yi kyau sosai. Ga wani haɗaɗɗen Wrist-Watch da ke saƙale a  hannunta. Yanayinta ta fi kama da mutane marasa hayaniya.

Tsaye take gaban dress mirror tana ƙoƙarin fesa wani perfect perfume mai masifar kyau da daɗin ƙamshi mai sanyaya ran bil-adam. Turo ƙofar katafaren haɗaɗɗen bedroom ɗin da take ciki aka yi. Ba tare da ta juya ba sanin da ta yi kowace ce ta shigo, ta ce cikin wata kalar murya mai masifar daɗin sauraro ga ta siririya yanayin sautin ta kamar ana busa sarewa.

"Oh my lovely dad mister mai kyau, ɗiyarka tana so ta fa takura mini. Yanzu zan iya cewa fa na fasa zuwa wajen birthday party ɗin nan kuma ta zauna, kin san da wannan tunda da ma can satar hanya za mu yi zuwa birthday ɗin saboda an ga daddy ba ya nan."

Ta yi maganar like a little girl kuma cike da tsabar shagwaɓa wacce ba ƙaramin kyau hakan ya ƙara mata ba, sannan kuma maganar duka da ta yi tana yi tana hutawa ne.

Dariya mai sauti wacce ta shigo bedroom ɗin tayi, sannan ta ce, "My Feefarh! Ba na son rashin mutunci fa, sai da aski ya zo gaban goshi za ki ce kin fasa haba ɗiyar mister mai kyau! Kar ki yi wa Zahra haka mana, ko dai kin manta wace ce ita gurinki?"

Mayar da perfect perfume da ke hannunta ta yi zuwa ma'ajinsa saman haɗaɗɗen dressing mirror ɗin sannan ta juyo gabaɗayanta tana fuskan tar budurwar da ta kammala yi mata magana.

Kawar da zancen zuwa birthday ɗin ta yi da faɗi, "To ya ya na yi kyau kuwa kamar SARAUNIYAR ƘYAU ta duniya?" Ta yi maganar cike da mafificin nishaɗi tana dariya.

Wannan karon ƙayataccen murmushi mai ɗauke da sauti mai cike farinciki da nishaɗi, budurwar ta kuma yi a karo na biyu tun da ta shigo sannan ta zauna gefen gado tana fuskantar ta....

A hankali ta fara magana ita ma cikin lallausar muryarta, "My Feefarh tawa ta kaina kin san ai shi mai kyau ba ya buƙatar tambaya a kan kyansa, da ganin shi kai ka san mai kyan ne shi, yanzu kamar ke dube ki. Kamar sananniyar jarumar India 'Anu  Emanuel', dogon hanci mai kyau da tsari kamar Chinese actress 'Janine Chang'. Ga ɗan ƙaramin siririn baki naki kamar a gurin wannan ɓarumar Korea 'Kim Sohyun'. Gashinki tsayi da yawa ga shi asalin dark brown kamar na fittaciyar jarumar Korea ɗin nan mai suna 'Park Shin Hye'. Ga fatarki mai masifar sheƙi da ɗaukar hankali kamar na..."

Ai tun kafin ta ƙarasa faɗin abin da take niyyar faɗa budurwa ta yi saurin tarar numfashinta da fadin, "Auntie Leesarth, ina ga wannan yabo kamar wata SARAUNIYAR ƘYAU ta duniya ya yi yawa gare ni."

"E, sarauniyar kyau ce mana tunda dai all most one month ya rage daga nan za a ga sarauniyar ce ko kuwa dai..."

"Oh bari  dai na yi shiru kawai tunda naga kamar Ba a so na yi maganar." Cewar wata ƙyaƙyawar matashiyar budurwa da ta shigo bedroom ɗin, ita ma tana rufe bakinta sannan ta canza maganar da cewa, "Ku yi ku fito mu tafi birthday party ɗin nan tun kafin daddy ya dawo fa."

Ta yi maganar ne tana zare manyan idanunta, wanda ba komai ya sa ta yi saurin sauya maganar da ta yi niyya ba, fa ce hararar da Haleesarth ta antaya mata, ba tare da ɗayar budurwar ta ankara ba.

Miƙewa Haleesarth ta yi tana faɗin, "Ai duk ga wacce duk ta bi ta ɓata mana Lokaci nan da kwalliyarta nan sai ka ce wacce za ta je wajen gasar BRITISH QUEEN."

Ta yi maganar ita ma tana antaya wa budurwar da still har yanzu tana nan tsaye gaban mirror wata uwar harara amma fa ta wasa.

Dariya ta yi sannan ta ce' "To mu je ba don halayenku ba, tunda dai na riga da na shirya." Ta faɗa tana yafa veil ɗinta da ta cire tare da ɗaukar haɗaɗɗiyar handbag ɗinta mai shige da kayan jikinta wato sky purple. Gabaɗaya waje suka yi, har sun fito ƙayataccen falon daya gaji da haɗuwa ta ko,ina fes-fes.

Wannan budurwar ta tsaya tana bin ko'ina na falon da kallo ko za ta hangi wacce take nema, sai dai har ta yi waige-waigenta ta ƙare ba ta ga wacce take da muradin gani ba a katafaren falon.

Juyowa suka yi suna kallon ta cike da ƙosawa Haleesarth ta ce, "To yanzu kuma mene ne ya faru kika tsaya kina ƙare wa falon kallo kamar baƙuwarsa?"

Ba tare  da ta kalle ta ba ta ce, "Ina anti Zainab  take? Kash damn it oh my God!"

Da sauri ta juya gabanta na mugun bugu, ba ta tsaya jira ko saurarar amsar da za su ba ta ba, ta nufi wani ɗan madaidaicin korido bedrooms biyu ne gurin, hannu ta kai da niyyar knocking ɗaya ciki wanda yake ɓangaren dama abin mamaki a buɗe ƙofar take.

Shiga ciki ta yi da sallama ɗauke saman laɓɓanta, ba ta ga kowa ba a ciki, saboda haka sai ta nufi hanyar bed. Tsayawa ta yi cak tana ƙarewa bedroom ɗin kallo sama da ƙasa gabas da yamma kudu da arewa, gabaɗaya a mugun hargitse yake kamar ba mutum ke rayuwa ciki ba, sai ka ce ba ɗazun nan yake tsaf-tsaf ba.

Pillows a ƙasa shi kansa bedsheet ɗin a ƙasa shi ma yake da alama an sha bidiri cikin bedroom ɗin. Daga can ƙarshen bangon ɗakin kuwa wata ƙyaƙyawar budurwa ce baje saman tiles na ƙofar shiga toilet, ga kwalabe a gabanta sun kai kala uku duka na Whiskey.

Da sauri ta ƙarasa kusa da ita, "Zainab, Zainab, anti Zainab! Please tell me! What happening to you? Kwalba kuma me kike yi da waɗannan kwalaben haka?"

Gabaɗaya ta bi ta ruɗe ta fita hayyacinta sabodaa tashin hankali, sam ƙwaƙwalwarta ta gaza tuna mata cewa yau ɗin ranar da suke ranar Valentine's Day ce, ranar da ta kasance wacce Zainab ba za ta taɓa mantawa da ita ba har abada kuwa a rayuwarta.

Zainab ba ta amsa mata ba sai ma  kokarin kafa kwalbar Whiskey da ke hannunta take a baki, da sauri ta kwace kwalbar cikin kunar rai.

Ta fara magana, "Wai anti Zainab sau nawa zan faɗa miki cewa Shannon giya na da matukar hadari ga lafiya? Amma ba kya ji. Ba ma wannan ba, shin ba kya tsoron fishin Allah ya sauka kanki?"

Cikin muryar mashaya Zainab ta ce, "Haba my kanwa Afeefarh, na faɗa miki ba yin kaina ba ne gabaɗaya jikina ji na nake kamar ba ni ba. Ni ma fa so nake na daina wannan mummunar halayyar ta dabbobi, amma hakan ya ci tura na kasa. Please Afeefarh ki rabu da ni wannan rayuwa ta ce kuma kaddarata ce."

Cike da tsabar tausayawa, matashiyar budurwar wacce Zainab ta yi mata kira da Afeefarh take kallon yayarta Zainab wacce kaddarar soyayya haɗe da son zuchiya ya jefa ta cikin wannan mummunan halin.

Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta miƙe tsaye tana bin ƴar uwar tata da kallon tausayi ta ce, "Anti Zainab ɗita! Bari na kira anti Sa'adah ta gyara miki bedroom ɗin amma please kafin ta zo ki taimaka ki tashi ki kwashe wadannan kwalaben kuma a kullum ina kara tuna miki cewar ki kasance mace mai yawan yarda ya kaddara a duk ta inda ta zo miki sannan ki kasance mai juriya kin ji my anti? Ni yanzu zan tafi saboda za mu ta fi Birthday Party na Zahra da navyi miki maganar tun last sai mun dawo."

Tana gama  faɗin haka ba tare da jiran ta bakin Zainab ɗin ba ta fita daga bedroom ɗin.

Katafaren aljannar duniyar falon ta dawo sannan ta karisa gurin Haleesarth da ke tsaye tsakiyar falon, gabaɗaya ta gama tunzura da ɓata musu lokacin da Afeefarh ɗin take.

Ba tare da Afeefarh ta kula complain ɗin Haleesarth ɗin ke mata ba ta fita daga falon zuwa farfajiyar katafaren gidan ta karisa parking lot da ke shaƙare da manya-manyan motoci na alfarma a fake..

*SARAUNIYAR KYAU*♥


_(The Glam Queen)_👑




           ```Takun Farko```



Story & Written By:


       Khadeejarth Sabi`u Yahyah


               *_The Nainarh KD_*




_In dedicated to my dear Classmates Science G.S.S.S BELE ROAD_



*Page 3&4*


Sautin dariyar da ake ɓaɓɓakawa ne yasa ta tsaya cak da tafiyar da takeyi,a hankali ta juyo gefan damarta ta saitin da dariyar take fitowa,ɗan zaro kyawawan idanunta tayi waje baki a hangame da mamaki ganin wa`inda suke wannan dariya haka kamar babu gobe..

Su bakwai ne,dukansu sanye cikin kayan ma`aikata Launin black and white suit,daga inda kowannen su yake tsaye akwai rata da ɗan uwansa,domin suna tsaitsaye ne tsayuwa irinna ma`aikatan tsaro wato {ESCORT} wasu daga cikin su ma Jami`ai ne na ƴan sanda wa`inda aikin su shine tsaron gidan,Dariya kawai suke ɓaɓɓakawa kamar masu cutar hauka,domin wasu daga cikin su ma harda hawaye saboda tsaban dariya,saidai da ganin yadda suke dariyar zaka fahimci na dole ne..


Hii Afeefarh wai menene kike kallo haka ne,ma`aikatanne baki taɓa gani ba,ko kuwa dai akwai sabo ne cikinsu,da kika tsaya haka Like a Gunki kina kallon su?....

Da sauri afeefarh ta juyo tana kallon haleesarth da tayi maganar hankali kwance tana ƙoƙarin buɗe tsadaddiyar mota ƙirar Bugatti, launin sky purple ta shiga..


Zuwa yanzu ta fahimci komai ajiyar zuciya ta sauke sannan tace  "a`a bawai kallon su nake ba dan ban gane wani ba,ko naga sabo cikin su, kallon su nake ganin yadda suke wannan dariyar da alama ɗaya daga cikin ku kodai ke,ko kuma LAILAH wata ta aikita haramci."

Eh kina da gaskiya wannan dariyar da sukeyi da akwai dalilinta kuma lailah ce sila bawai ni ba.Haleesarth tayi  maganar tana mai ya mata nuni da lailah data iso wajen tana baza ƙamshi cikin takun isa da gadara...

menene kuma naji ana Lailah ce sila gani nayi ba zasu taɓa bari mu fita cikin daɗin rai ba shiyasa kawai nayi abinda ya kamata dasu....

Abinda ya kamata fa kikace hakanne abinda ya kamata lailah are serious,mutane ne fa,waima tukunna menene abinda kika musu ne?. Afeefarh tayi maganar tana danne ɓacin rai dama cikin sa take tun lokacin da taga halin da zaynerb take ciki....

Haba  afeefarh menene na ɓacin rai da fushi kuma?,naga ma`aikata ne kuma a ƙarƙashin uba suke samun na ci da sha, da kike maganar menene abinda nayi musu,naga kema likita ce kama ta saboda haka kinsan abinda nayi,  kawai LAUGHING_GAS na fesa musu mintuna ƙalilan zasu ɗauka suna dariyar bazai cutar dasu ba nayi miki alƙawari...

Ɗan jim afeefarh tayi tana kallon lailah da tayi maganar hankalinta kwance tana ƙoƙarin shiga motar gidan gaba, daya ke  itace zatayi driving nasu. ..


Allah ya shirya ki lailah muguwar gidan mu,afeefarh tayi maganar cikin ƙyaɓe fuska da ɗan hararar lailah ɗin domin kuwa batasan abinda zatace mata ba,tasan wannan kaɗan daga cikin halin lailah ne, wato mugunta..

Madam nace ina zaku tafi ba tare da kunyi min magana ba mu shirya motoci kinsan dai fitarku ku kaɗai babu guards akwai hatsari ko?..

Fasa shiga motar afeefarh tayi ta juya tana kallon mahalukin da yayi maganar,saida gabanta yaɗan faɗi ganin wanda ke tsaye cikin black suit yana kallonta,ba kowa bane fa ce SALSA ɗaya daga cikin manyan ma`aikatan gidan zama`a iya kiransa da shugaban gabaɗaya ma`aikatan gidan.SALSA dai wani jibgegyan qaton Arne ne ɗan asalin ƙasar Philippine  qato ne mai qirar samudawa,wanda wannan ƙirar tashi ne tasa gaban afeefarh bugu, ai dole domin kuwa jinsa yake  shida qirar sa kamar basamude...

Rasa abinda zatace mishi tayi tsawon minti ɗaya,ajiyar zuciya ta sauke sannan ta fara magana kamar haka...

"Kaga mai ƙirar  samudawa tun wuri ka bari mu tafi tun muna mu kaɗai,kafin raina ya ɓaci"tayi maganar cikin haɗe gira kuma da hausa dama da gangar tayi sanin da tayi bayajin hausa,domin maganar da yayi mata da farko ma da turanci yayi..

Kinga madam koma menene zakice saidai ki faɗa dole tare zamu tafi domin alhakin kula da lafiyarki Boss ya damƙa a hannun mu,saboda haka koma miye zakice saidai ki faɗa dan tare zamu.....

Tunda haka ne, na fasa tafiyar kuma kasa ido zakaga abinda zai biyo baya, badai ka hanani fita ba,daddy zan kira na faɗama kasani daga yau,kabar aiki a gidannan tunda dani zakayi compromise.....

Tayi maganar tana kashewa lailah ido ɗaya sannan ta fara yunƙurin saka hannu a handbag ɗinta tana ƙoƙarin ciro wayarta...

Murmushi lailah tayi sannan cikin ɗan zaro ido da ɗaga murya ta fara yima salsa magana.
Kai amma fa baka da hankali yanzu ka gummace data kira da daddy ta faɗa mishi,kai kuma ka rasa aikin ka,kayi sauri ka ceci aikinka ta hanyar daya dace kafin ta kira daddy a waya,muddin ba so kake ka koma ƙasar philippine ba.....

Cikin tashin hankali yana share zufar data tsitato mishi salsa,cikin rarrabewar murya yace,"totto madam lailah meya kamata nayi banason rasa aikina oh jesus".....

Ya Allah abinda suka iya kenan kiran wannan suna chioooo cewar haleesarth tana jan tsakin takaici......

Hidden dariya lailah tayi ganin yadda lokaci guda gabaɗaya salsa yabi ya ruɗe daga kira masa rasa aiki,tana dariyar tace."kawai hakuri zaka bata sannan kace bazaka ƙara ba sannan kuma karka ƙara koda wasa,kana kasan yadda zakayi wa`incan baƙaƙen dake tsaron gate na farko su barmu mu fita,domin gate na biyu isah da sauran mutanen bamu da matsala dasu..

Da sauri cikin rawar jiki salsa yayi abinda lailah ta bugata ta hanyar bawa afeefarh hakuri da kuma yima jami`an dake tsaron gate na farko magana akan su barsu su fita sannan kuma yana mai ƙara basu hakuri duka...


Ɗan nema yaji maganar rasa aiki harda rawan jiki ah lallai na sama abin fakewa dashi dan ubansa da wata jar fatarsa a gurin kamar na akuya,cewar afeefarh tana dariya bayan ta shiga motar,dama can ba burinta ne ta kira daddy ta faɗa mishi ba,kawai dai kafce ne....

Hhhh aini tun four months back na fahimci raunin sa wato dai aikinne  bayaso ya rasa,to banda abinshi ma,ai momy ce ta ɗaukeshi aiki nan gidan bawai daddy ba,saboda haka ita kaɗai keda ikon korarsa lokacin dataso bawai daddy ,cewar lailah tana kuma dariya..

Itadai afeefarh murmushi kawai tayi tana lalubo lambar Auntie Sa`adah a wayarta domin umartanta da gyara bedroom ɗin zaynerb !!!


Wuraren ƙarfe Biyar dai dai na maraice suka isa wajen birthday ɗin wanda ya qawatu iya qawatuwa haɗuwa iya haɗuwa..

Fitowa daga tsadaddiyar motar nasu sukayi a tare kuma ko waccensu tana baza ƙamshi mai class ..
Afeefarh wacca babu abinda takeyi sai faman baza idanu tana ƙarewa gurin kallo babu abinda takeyi,indai ba idonta bane mai matsala gani take kamar dai "MASHAYA!" Sukazo da sauri ta juya tana binsu haleesarth da kallon mamaki da al`ajabi tsaban takaici tama kasa magana.....

Ganin ɓacin rai haɗe da mamakin dake saman kyakyawar fuskarta ne yasa da sauri haleesarth ta nuna lailah dake qumshe dariya dan kuwa da gangar taqi faɗa mata gurin da za`ayi birthday ɗin saboda bataso ta ɓata musu budget...

Da sauri lailah ta kama kunnenta alamar ta tuba tun kafin afeefarh tace wani abu...

Girgiza kai kawai afeefarh tayi tasan halin lailah farin sani akwaita da tsokana,barkwanci, saurin fushi ji_ji_da kai ɗaukar komai ba komai ba,sai tsoro kamar ƴar fari😁..

Qarisowar zahrah gurinne ya hana afeefarh faɗin abinda tayi niyya shiru tayi tana kallon zahrah ɗin...

Cike da farin ciki zahrah ta qariso gurin su tana washe baki dan kuwa batayi tunanin afeefarh zata yarda tazo  "MASHAYA!" Gurin birthday party ɗinta ba..

Hi!! Feefarh mai ƙyau Ashe zakizo birthday na zahrah ta faɗa tana kamo hannun afeefarh cike da farin cikin zuwanta...

Murmushi mai Bayyana dimples tayi sannan tace gani kuma nazo gurin  birthday party ɗin aminiyata zahrah...

"Wato dai  Ansama aminiya  an manta damu ƴan karere ko to kisani da ƙƴarma muka samu tazo birthday ɗin naki ae da kike wannan rawar jikin",cewar haleesarth tana antayawa zahrah harara,dan kuwa taji haushin ganin yadda zahrah ɗin duk  tabi ta firgice da ganin zuwan afeefarh ɗin saikace ba da ƙƴar aka samu tazo ba..


Oh sorry my friend banma kula dake ba,murnar ganin feefarh mai kyau ne,yasa ban gankiba wallahi,zahrah ta faɗa tana kama kunnenta alamar ban hakuri. .

Haleesarth zatayi magana lailah ta rigata da cewa "kunga kuzo muje anata kiran birthday girl fa,wani lokacin a ƙarisa wannan topic ɗin..

Murmushi zahrah tayi sannan tace "okay  shall we" ɗunguma sukayi dukansu ukun suka shiga wajen birthday party da yake cike da manyan yara maza da mata masuji da tashen quruciya da dukiya ta iyayensu...


An kammala komai an shirya komai ,anzo wajen yanka cake ,yanka cake ɗin zahrah tayi da wani madaidaicin ATM card  dake hannunta sannan taci taba saurayinta abdul a baki shima ya bata nan wajen ya ɗauka sowa samari da ƴan mata ana faɗin "happy birthday to you zahrah. ..

Hakadai abin nasu wallah👯


Ita dai afeefarh tana daga gefe burin ta ayi a gama su koma gida kafin daddy  MISTER MAI ƘYAU ya dawo basunan domin kuwa idan ya rigasu komawa da akwai ƙura over highly.


"Assalamu Alaiki Yake ƙyaƙyawa cikin kyawawa, tauraruwa cikin ƙyawawan taurari wacca take haske duk wani waje"

Wannan Maganar ne ya dira mata a kunnenta wanda hakan yasa saida tsigar jikinta ya miƙe saboda batayi tsammani ba taji muryar mai maganar ya dira a kunnenta.

Wata Sansanyar murya ta bayanta akayi mata  sallama da yabo lokaci guda.

Bata Juya ba kuma bata amsa sallamar ba saidai ta amsa cikin zuciyarta...

Sallamar aka ƙarayi mata still,a fusace ta juya da niyyar yima ko ma waye masifa,sai kuma me?.

Ido huɗu sukayi dashi yana kallon ta,itama tana kallon shi.

Zata iya cewa gaban ta ya ɗan faɗi kaɗan,sakamakon ƙyawawan idanun shi daya kafe ta dasu..

Shiru tayi tana ƙare mishi kallo from head to toe. ..

Fari ne shi amma ba fari cancan ba,bashi da tsayi highly highly,irin can ɗinnan amma fa,he`s so cute nd beautiful obaa..
Launin kwayar idanun shi Brown color kamar na mage,ya tara suma akanshi baki sidiq irinna  fulanin usul gata tasha gyara in stylishly...



SARAUNIYAR KYAU* 💓
       
   _(The Glam Queen)_ 👑
       
         ```Takun Farko```

Story & Written By:

              *_Ⓣⓗⓔ Ⓝⓐⓘⓝⓐⓡⓗ ⓀⒹ_*

_In dedication to my dear Classmate Science G.S.S.S BELE ROAD._

*ℙ𝕃𝔼𝔸𝕊𝔼 𝕊ℍ𝔸ℝ𝔼 𝕀𝕋 𝔽𝕆ℝ 𝔼𝕍𝔼ℝ𝕐𝕆ℕ𝔼*

*Page 5&6*

Sanye yake cikin ƙananan kaya T-shirt fara da wando crazy Jeans ash color, kansa ba hula, kunnensa ɗaya manne da ɗan kunnen barima irin wannan wanda maza suke sakawa na gayu, shi ɗin cikakken gaye ne mai ji da kuruciya da gayu ga kuma naira.

Cikin sakanin da ba za su wuce uku zuwa huɗu ba, ta gama ƙare mishi kallo ta cikin glashin dake fuskarta, kai ba za ka ce shi take kallo ba saboda yadda ta tsare gida. Shekarun shi baza su wuce ashirin da huɗu zuwa da biyar ba a iya lissafinta.

Muryarsa ce ta dawo da ita daga duniyar tunanin da ta lula.

"Hey babe am Sabbir Salis Mai Naira, amma an fi kira na da S.S Gidan Naira."

Ya faɗi hakan yana miƙa mata hannu alamar su gaisa. Hannun nasa take bi da kallo ita ba ta ba shi nata ba, kuma ba ta masa magana.

Ɗan sosa sumar kansa ya yi ganin ba ta kulashi ba. Sannan ya cusa hannunsa ɗaya cikin aljihun wando, ya gyara tsayuwarsa sannan ya ce, "Please beautiful! A taƙaice dai za mu iya zama abokai?" Ya faɗa yana wani kanne mata ido ɗaya irin na tatattun ƴan duniya.

"Oh da gaske amma saboda me za mu zama abokai?" Ta tambaya ba tare da ta bari sun haɗa ido ba, don kuwa sai ya sa ta ba shi eleven ɗinta ba tare da ta sani ba, da wadnnan shegun idanun nasa.

Murmushi ya yi, "Because you are so beautiful!" Ya ba ta amsa yana ƙara kashe murya.

Za ta iya cewa ya ba ta dariya wannan kashe murya haka, haka ko mace albarka. Ba tare da ta kuma kallon shi ba ta ce, "Hmmm! I'm Lailah Abubakar Mai Kyau!"

Ta faɗa tana yamutsa fuska don ya ta kura mata shi ya sa ta faɗa masa sunan Lailah komai ta fanjma fanjam.

"Lailah, wow nice name! Am so Amazed meeting you."

"Me too!" Ta ba shi amsa  tana kokarin barin gurin domin kuwa ta gaji da tsayuwar, da sauri ya sha gabanta sannan ya ce, "Sorry ba ki ba ni eleven naki ba?" Ya faɗa yana marairaicewa tamkar maraya.

Ganin dai zai tara mata mutane ne ya sa ta ba shi lambar Lailah da yake duka wayoyin har da ma na Haleesarth suna hannunta.

Da sauri ya kwashe lambar data karanto masa cikin dankareriyar wayarsa, don bala'i saboda ya tabbatar sai da ya kira ya ji ko tatan ce ko kuwa, ɗauko wayar ta yi a handbag ɗinta ta nuna masa sannan ta ce,"Shi ke nan ko da wani abu?"

Murmushi ya yi ganin ya sama lambarta, ita kuwa Afeefarh ba ta tsaya jin surutun da yake koarin yi mata ba tabar gurin.

Jin an dafa shoulder ɗinsa ne yasa shi jujowa, "Ah Haydar, kai ne ashe."

Murmushi Hydar ya yi sannan ya ce, "To ya an samu nasara ko kuwa?" Ya tambaya yana kallon Sabbir da fuskarsa take ɗauke da ƙayataccen murmushi.

"An samu da ƙyar amma fa..." Ya faɗa yana dafe saitin zuciyarsa.

"To kai Shar Shar, tunda ka samu Haydar." Ya faɗa cikin murmushi sannan ya ci gaba da cewa, "Amma na ji kamar ƴar uwarta ka ce kana so fa, to ya haka?"

AFEEFARH

Ɓangaren  Afeefarh fita waje ta yi wajen da suka parker motocinsu, tana jiran su Haleesarth.

A taƙaice dai su Afeefarh ba su suka bar gurin Birthday ɗin ba sai wajen takwas na dare.

Burin su bai wuce ace daddy bai dawo ba,dan sunsan idan ya dawo kashin su ya bushe..

"Oh  my God !!  Rashin sa`a cewar Haleesarth Lokacin da security gate man ya wangale musu wagameman gate ɗin katafaren Gidan nasu,idansu bai sauka Ko`ina ba sai a parking space...

Da Jerin Motocin MISTER MAI ƘYAU da suke a pake  suka yi arba. Ko gama daidaita parking haleesarth datayi driving nasu yanzu batayi ba suka fito dukansu.

Palo suka shiga da Mister mai kyau suka fara cin karo yana kaikawa da qaton palon hankali a tashe....

A hankali suka fara taku saɗan saɗab kamar mara sa gaskiya cikin palon aikuwa kamar ance mister mai ƙyau juyo sukayi four eyes da afeefarh dama itace a gaba.

Da sauri  ya qariso gurin hannunta dake rawa kamar mazari ya kamo.

A hankali ya fara magana kamar mai jin tsoron wani abu ya raba shi da ita shalelensa.

"Shalelena ba abin da ya same ki please tell me. Gabaɗaya na shiga damuwa na dawo gida bakunan".
Murmushi Afeefarh ta yi tana kara jin ƙaunar mahaifin nata da wannan  ƙauna da yake nuna  mata da kulawa.

"Ah Daddy karka damu indai ni ce babu abin da zai same ni muddin kana tare da ni lovely daddy, yanzu birthday party ɗin zahrah classmate ɗinmu muka je mun yi tunanin bazaka barmu bane shi yasa muka yi satar hanya amma muna ba da haƙuri our apologize."

"To amma shalele mai ya sa ba ku tafi da guards ba, kun fa san yadda ƙasar nan ta lalace." Mister mai Kyau ya kuma faɗa.

"Dad! Mu fa ba ma son hayaniya ne shi yasa ba mu tafi da escort ba."

Tun kafin ya kuma cewa komai ta riga shi da kara faɗin, "I need to take shower, na gaji sosai daddy."

Murmushi Mister Mai Kyau ya yi sannan ya ce, "To shi ke nan shalelena, yi sauri ki je ki yi wanka ki huta kin ji?" Ya faɗa yana duban inda su Haleesarth suke sai dai me? Wayam babu ba su sun gudu, ya girgiza kai cikin murmushi irin na manya.

Dariya Afeefarh ta yi ta ce "Daddy ke nan ai tun ɗazu suka shige bedroom nasu ta faɗa tana kuma murmushi.

Daddy Bai kuma cewa komai ba ya wuce dining table wajen Matar Gidan Haj. Rafi'at  {Mrs Mai Kyau}Sai dai yaranta sun fi kiran ta da Momy Ko kuma Momy Rafi'at, musamman Zaynerb da Afeefarh sun fi kiran ta da haka a matsayinta na kishiyar mahaifiyarsu Hajara da ta daɗe da rasuwa tun haihuwar Afeefarh.

Momy Rafi'at ta kasance kyakyawar Bafulatana ce kyakyawar ƙarshe ajin farko, ta kasance mace mai son a girmama ta na ɗaya, ta kasance mace mai son mijinta Mister Mai Kyau fiye da komai a rayuwarta na biyu, ta kasance mace mai bala'in saurin fushi da gaza fahimta kuma ita tana so a fahimce ta na uku, ta kasance mace mai Bala`in iya ɗaukar wanka da shiga na kece raini domin kuwa sometimes idan ta ɗauki wanka ta saka mayafi da glass kai ba za ka yi tunanin shekatunta Hamsin da ɗauriya a duniya ba, tunani za ka yi ba ta wuce 30yrs ba, na huɗu ta kasance babu wasu wadnda ta taɓa tsana a duniya ko na ce ta tsana sama da Zainab da kanwarta Afeefarh ta tsane su, sama da mutuwarta, sai dai ba ta taɓa nunawa ko a fuska ba, tun shekaru goma sha daya" baya da ta yi kuskuren yi wa Zaynerb  da Afeefarh dukan mutuwa a kan dalilin da bai kai ya kawo ba, ai kuwa lokacin ta ga masifa da bala'i domin sai da mijinta ya sake ta a lokacin, kuma ya ɗauki yaransa Zaynerb da Afeefarh ya bar ƙasar da su tsawon shekaru shida sannan da ƙyar aka samu ya dawo, tun lokacin  ba ta ƙara yunƙuri ko gigin sake dukan su ba, sai dai ba wai don tsanar su ta bar zuciyarta ba, a'a sai dai don ba ta so mijinta ya ƙara sakin ta, domin wancan lokacin da ya sake ta ta sha matukar wahala kafin ya dawo da ita don sai da ta shekara guda cur sannan aka samu ya haƙura aka mayar da aurensu.

Shi ya sa take danne tsanar tasu a zuciyarta ba wai don ta ƙyale su ba, a'a ɗaurin talala ta yi musu ya gama nuna musu ƙaunar.

Da yake tana da katafaren asibiti nata na ƙashin kanta a tsakiyar garin Abuja, tana aiki a can shi ya sa mafi yawan lokuta take cikin busy da yake asibitin nata Pediaric ne.

Yau ma around 6:pm ta dawo asibiti a gajiye ta sama mijinta Mister Mai Kyau cikin tashin hankali wai ya dawo gida bai ga shalelensa ba hankalin shi ya tashi yake faɗa mata.

Abin ba ƙaramim sosa mata rai da ba ta haushi  ya yi ba, kawai ba yadda ta iya ne ta danne ɓacin ranta ta ki kula shi, sai dai abin yana nuƙurƙusar ta ƙasan rai. To ban da latsinsa ma da rashin son gaskiya, Afeefarh ce kaɗai ba ta gidan, ai har da su Lailah da Haleesarth amma Afeefarh ya tuna saboda ita ce ƴar gold sauran ko oho.

Da ta gaji da abin nasa bayan ta yi wanka ta shirya cikin jallabiya ruwan madara da mayafi shi ne fa ta fito palon ƙasa inda yake tsaye har yanzu, ba ta kula shi ba ta karasa haɗaɗɗen dining room ma'aikata suka yi serving nata ta fara cin abinci hankali kwance.

Tana nan zaune Afeefarh suka shigo palon  kuma tana jin duka abin da suka tattauna sai dai ba ta kula su ba, har Mister Mai Kyau ya dawo dining room ɗin ya zauna cikin washe baki.

Ma'aikaciyar  ce cikin rawar  jiki ta fara kici-kicin serving ɗinsa, ai kuwa cikin zafin nama Momy Rafi'at ta yi saurin miƙewa tana mai daka wa 'yar aikin tsawa a kan za ta yi serving mijinta abinci abin da ko da gigin wasa ba su taɓa ba, tana mata tsiya dan bala'i gefe guda kuma tana antayawa Afeefarh da za ta wuce ta side ɗin hararar tsana.

Ita ma Afeefarh ba ta kuma magana ba ta nufi bedroom ɗinta ko kula momy Rafi'at da ke antaya mata harara ta gefan ido ba ta yi ba.

KANO

Da gudu ta shigo bedroom ɗin tana ƙwala wa Jieddarh kira, "Jieddarh, Jieddarh. Ke Jieddarh!" Hango ta ta yi saman gado ta yi ɗai-ɗai tana ƙwasar barci.

Da sauri ta hau kan bed ɗin tana kiran sunanta, "Jieddarh ki tashi takardar ki ta fito nan da wata ɗaya za ki fito gasar SARAUNIYAR KYAU matakin Jaha.

𝔗𝔥𝔦𝔰 𝔦𝔰 𝔐𝔶 𝔉𝔦𝔯𝔰𝔱 𝔑𝔬𝔳𝔢𝔩 𝔖𝔥𝔞𝔯𝔢 𝔦𝔱 𝔣𝔬𝔯    𝔢𝔳𝔢𝔯𝔶𝔬𝔫𝔢 𝔭𝔩𝔢̨𝔞𝔰𝔢🙏


SARAUNIYAR KYAU* 💓
       
   _(The Glam Queen)_ 👑
       
         ```Takun Farko```

Story & Written By:
                          🅣🅗🅔 🅝🅐🅘🅝🅐🅡🅗 🅚🅓

*page7&8*

A hankali ta buɗe fararen idanunta ta ware su akan fuskar ʜumaira dake mata magana.

maƙalƙale ʜumaira tayi ta miƙe tsaye tana rawa da juyi saman bed ɗin ita ma ʜumaira tana taya ta.

Da sauri ta dira daga saman bed ɗin. ᴛa fita daga bedroom ɗin gabaɗaya. ɪta ma ʜumaira ta rufa mata baya. ᴅa gudu ta ɗare jikin wata ƴar ƙyaƙyawar dumadumar mata baƙa,ᴅake palon wacca ba za ta wuce shekaru arba'in da huɗu zuwa da biyar ba.

Tana faɗin "Auntie nayi nasara zan fito gasar SARAUNIYAR KYAU matakin jaha nanda one month"...
Da sauri ƴar dumadumar matar da jieddarh ta kira da "Auntie tayi saurin yin, rijecting ɗin wayar da takeyi sannan ta juyo da jieddarh gabanta tana tambayarta,abinda ke faruwa.

Cike da farin ciki jieddarh ta ce "Auntie an zaɓeni, zan fito gasar SARAUNIYAR KYAU matakin jaha fa"..
Ƙayataccen murmushi Auntie Tayi,ba tare da tace komai ba.

Ita ma jieddarh bakinta washe yake kamar gonar auduga, ᴢama tayi saman two sieter kusa da ʜumaira tana faɗin "Auntie yau ina cikin farin ciki burina Ya kusa cika zan zama SARAUNIYAR KYAU" ta faɗa tana rungumo hannun ta a ƙirji Tana lumshe kyawawan idanun ta kamar mai jin bacci.

"murnar mai akeyi ne BRITISH QUEEN?" muryar ʜeesham taji yana magana da sauri ta juya tana kallon ƙofar palon ta wajen da ta jiyo muryar shi, tsaye yake jikin ƙofar ya rungumo hannun shi ta baya yana sakar mata ƙayataccen murmushi.

Da gudu ta miƙe tsaye ta ƙarisa gurin shi, ʏi tayi kamar zata rungume shi, sai kuma ta fasa ta tsaya a gaban shi tana sauke ajiyar zuciya, cikin murya mai sanyi tace "Yaa .H. yau ina cikin farin ciki burina zai cika an zaɓeni a cikin waɗanda zasu fito gasar SARAUNIYAR KYAU matakin jaha.

"Da gaske take, ku rantse mana" ya tambaya yana kallon ʜumaira dake murmushi ɗaga mishi kanta tayi alamar haka ne.

Gyara tsayuwar sa sayayi a gaban ta kamar wani soja yayi saluting ɗinta yana dariya.

Ita ma salute ɗin shi tayi tana murmushi ta ce "Yaa .H. kaga daga na zama SARAUNIYAR KYAU ta jaha sai ta ƙasa daga ta ƙasa saina duniya ko", ta tambaya tana kallon shi.

Dariyar da ba shiri Auntie Tayi ta na faɗin "yarinya kenan waya faɗa miki daga na jaha saina ƙasa akwai wasu gaba"..

"Wanne da wanne kenan jieddarh ta tambayi Auntien tana zama a kujera, ʙayan ta dawo gurin.
Dukansu gyara zama sukayi suna kallon Auntie murmushi Auntie ta yi a zuciyar ta ta ce "anzo gurin Yarinya Jieddarh GO AHEAD Muje zuwa"...

Muskuɗawa tayi sannan "ta ce na farko dai da ace a ƙauye kike to saikin fara cin na local government sannan azo na State idan shima na state kinci sai azo.
Na state`s talatin da shida na ƙasar nan, shima sai kinyi winning sannan kuma azo na ƙasa, Bayan wasu ƙananu da za`ayi waɗanda su ba dole,bane domin ko anyi ko ba`ayi ba za`a iya shiga na ƙasa.
Kana azo a haɗa ƴan waɗannan ƙasar da wacan ƙasar shima idan kinyi winning akwai wasu da yawa sannan kuma azo uban gayyar na DUNIYA!.

Jikin jieddarh ne yayi sanyi jin waɗannan uban lissafi ita awa na state ɗinma ya aka ƙare balle na duniya Allah yasa taci na jahan ma tukunna, Toh dama Haka Abin Yake Idan akazo maganar sai taji jikinta Yayi sanyi laqwas....

"Aini nasan indai jieddarh ce zata cinye waɗannan tuni, wae bakuga wannan kyau ɗin bane ae ko wata ƴar american albarka come on mana Jieddarh yane wae da rasa qwarin gwiwa haka, haba mana keɗin fa, kece SARAUNIYAR KYAU ta gidan mu", Humaira ce duk tayi waɗannan maganar a domin kwantar ma da jieddarh hankali, fuskarta ɗauke da ƙayataccen murmushi, "Ko ba haka ba Yaa .H. da sauri yace Haka ne mana na yarda  highly.

Ganin yadda jikin jieddarh ɗin har yanzu  Yake a sanyaye yasa Auntie faɗin "kuma ae nasan yarinyar tawa kyakyawace zata ciyo mana kyauta na musamman,nasan da wannan.

Washe baki jieddarh tayi dan kuwa a kullum tanaso taji ana yabon ta, ana ƙara mata ƙarfin gwiwa, ana ƙara zugata kanta na hayaƙi😇.

"Kinga yanzu sai a fara shirya shirye ko?" cewar ʜumaira, Da sauri jieddarh ta ce "eh Haka ne to amma dame za'a fara?.
"Ku shirya kawai na kaiku kuyi shopping tun yau kuma yanzu ku zaɓo duk abin da ranku ke so, nauyin payment na ɗauka", Heesham ya faɗa yana kallon Humaira ɗin da ita Jieddarh.

Da sauri suka miƙe tsaitsaye harda ruga ruge  "kabamu minti biyar kawai Yanzu zamu shirya no wasting time suka faɗa a tare suna nufar hanyar staircases  domin shiga bedroom  don shiri domin kuwa a kullum Burinsu a fita shopping basa gajiya sam ko kaɗan da outing🥰.
Sallama suka ma Auntie Bayan sun shirya suka fita shopping mall aikuwa dai sun jido kaya kala kala a gurare daban daban Wani ma, ba amfani zayyi ba,kawai don a kashe kuɗaɗe suka jido.
Basu suka dawo ba sai da suka biya suka sha ice cream cheese Burger e.t.c.

Daga ƙarshe ma sai da aka biya dasu sukayi salon sannan suka dawo gida.
Aikuwa dai a gajiye suka dawo gidan,domin kuwa ko gurin Auntie basu biya ba don ko ba ƙaramin gajiya suka kwaso ba.zuwa lokacin Dare ya lula kowannen su  wucewa bedroom ɗinsa yayi domin samun Hutuu...

WANNAN KENAN

       
           

   ABUJA!

___Lailah

Ɓangaren Lailah tsaf ta shirya cikin sleeping dress payjamas pink color mai taushi, har zata kwanta ta tuna bata amsa wayarta wajen Afeefah ba,don haka hijjab ta sanya jikinta sannan ta fito daga bedroom ɗinta sai da ta fara biyawa kitchen ta haɗa black coffee mai kauri sannan ta nufa bedroom ɗin Afeefah, knocking ɗin ƙofar tayi, Daga ciki Afeefah ta bata izinin shiga.

Kwance tasa meta tayi daidai saman Royal Bed ɗinta tana ibadar da aka saba wato chatting😅.

Zama tayi kan stool na dress mirror sannan ba tare da ta kalleta ba Ta ce "malamar chatting bani wayata".

Ita ma Afeefah Ba tare da  ta kalleta ba saboda yadda gabaɗaya hankalin ta yana kan tsadaddiyar wayarta dake hannun ta, chatting da ƙawaye ya ɗauke mata hankali, Ta mata nuni da kan bed daga gefanta, ƙarisawa Lailah Tayi sannan ta ɗauka handbag ɗin ta ciro wayarta a ciki kana ta koma ta zauna saman wata doguwar softened stool dake ɗakin kana ta kunna Wayar dayake a kashe take.

Aikuwa kamar jira ake ta kunna saiga saƙonni nata tururuwar shigowa,Can kuma saiga kira ya shigo unknown number ne.
Dan haka batayi picking call ɗin ba saboda tsarinta kenan, sai da aka jera kira wajen uku sannan da ta gaji da kiran ta saka Wayar a silent..
Ganin taƙi ɗaukar kiran da ake mata ne gashi kuma shi mai kiran yaƙi haƙura Yasa Afeefah da ringing ɗin wayar ya isheta ta ɗago tana kallon Lailah kana Ta ce "Lailah ta ana kiranki fah ko bakiji bane?."

Tsaki Lailah taja sannan Ta ce "kinsan dai bana ɗaukar unknown number ko?", "Ki ɗaga kiji ko waye mana tunda anƙi dena kira kikasani ko wani abu mai muhimmancine?",
Ya mutsa kyakyawar fuskarta Lailah tayi "banajin haka kawai dai mara aikin yine".

Saukowa Afeefah tayi daga kan bed ɗin tana shirin ɗaga kiran wayar ta yanke saboda haka Komawa tayi ta zauna ta ci gaba da latsa wayar ta, Lailah zatayi magana wani kiran ya sake shigowa, Picking Tayi amma batayi magana ba, ta dai saka wayar a hands Free.

Jin ba'ayi magana ba sai Faman ajiyar zuciya da ake saukewa yasa Tayi kamar zata katse kiran,da sauri Afeefah tayi mata alama da karta katse ta Jira tukunna.
Cikin wata irin murya mai sanyi daga can ɓangaren mai kiran wayar Yayi sallama.
Cikin ƙyawawan yaran mister mai ƙyau dake bedroom ɗin wato Afeefah da Lailah rasa wanda zai amsa sallamar akayi, Sai can Lailah tayi ƙarfin halin amsawa da...

Wslm ta faɗa a gajarce kuma a taƙaice sannan a fusace,wata kalar ajiyar zuciya aka kuma sauke wa ta can ɗayan ɓangaren mai kiran,Sannan aka fara magana kamar haka.

"Lailah ta to ya kike kin isa gida lafiya, inata kira baki ɗauka ba har na karaya fah, sai naji kamar bansama shiga ba. Hala dai duk gajiyar birthday ɗinne?."

Shiru yayi da maganar Jin kamar hankalin ta Baya kanshi Tunda batayi magana ba. "Hello Lailah ƙawa ta did you hearing me?, please say something mana!.

Da sauri Lailah da mamaki ya kusa kasheta ta ce "wrong number, Malam kai waye kuma sannan miye haɗina da kai?",

Jin tana ƙoƙarin katse kiran ya sa shi faɗin Lailah Abubakar Mai Kyau koh ko ba ita bace?,
A mugun fusace Lailah Ta ce "ni ce sai akayi Yah Yah,huh Nace sai akayi YahYah zaka takumin fa, Tayi maganar a fusace domin kuwa akwaita da saurin hawa,kamar momy Rafi`at Mahaifiyarta.

Oh baki gane mai maganar ba kenan,Bangane ba,Oh sabbir salis mai Naira ne, Da muka haɗu dake wajen birthday party ɗin classmate ɗin ku, ɗazunnan.

Dariya ne ya kusa kama Afeefah amma tayi saurin ƙumshe wa,Ita kuwa Lailah mamaki ya hanata cewa komai,"Kinajina kuwa sabbir ya faɗa daga ɓangarenshi.

Uhhhm ta faɗa a taƙaice tana hamman gajiya da wannan futile maganar.
"it's okay My friend Bacci kikeji bari na barki kawai,kiyi mafarkina fah kinji ko friend ɗita bye bye!!
Tana shirin yin magana ya katse kiran..
Baki sake Lailah take bin wayar da kallo tana mamakin yaushe har suka haɗu dashi wai har ta bashi numbar ta, ita da ko lambar namiji ɗaya, babu a wayarta daga na dady saina uncle's ɗinta da kuma YaYYinta maza na Dangi shikenan.

Ganin yadda Lailah take bin wayar da kallo kamar wacca bata cikin hayyacin yasa Afeefah taɓota....
Firgigit ta dawo hayyacin ta tana kallon ta, "menene Haka kuma ba saurayin ki bane zakiyi wani pretend a gaba na" Afeefah ta faɗa tana cin magani kamar da gaske....

Da sauri Lailah ta ce "ni wallahi banma sanshi bah kema dai kinsan ba abinda yake haɗa ni da maza hasali ma tsoron su nake saboda namiji ba abin yarda bane, ki duba saboda namiji zaynerb ta koma wata kalar Rayuwa Wanda Farin ciki Yayi ƙaranci a ciki."
Shiru tayi tana tunani,ita ko Afeefah ta zuba mata ido tana kallon ta gaskiya Lailah ta faɗa wasu mazan abin tsoro ne tunda gashi a dalilin ɗa namiji zaynerb ta faɗa mummunar hali amma ae ba duka aka haɗu aka zama ɗaya ba.

"Oh ohoo Yes na ganoshi" Lailah ta faɗa tana bin Afeefah da kallon tuhuma...
"Kin gano shi wayeshi?".  Kuma meyasa kikemin wannan kallon kamar nayi miki sata Afeefah ta faɗa cikin tsare gida.

"Bashi bane wannan guy ɗin dana ganku ɗazu wajen birthday ɗin zahrah Lailah" Ta faɗa tana kallon Afeefah.
Sannan ta ci gaba da faɗin "wato idan na fahimta ya takura miki saikin bashi lambar ki shine kika bashi nawa kamar yadda kika saba ko?."

Shi kuma harda kira na da murya like a sweet... mtsshhooiii taja tsaki.
Ita dai Afeefah dariya kawai takeyi tana mamakin kaifin tunani irin na Lailah  tanajin yadda Lailah ke ƙarewa sabbir cin mutunci.

"Kiyi dariya da kyau daga ke har shi saina koya muku hankali daga kaina bazai ƙara takurawa mata ba".
Lailah ta faɗa a kufule ganin yadda Afeefah ta mayar da ita abin dariya
Tsayawa Afeefah tayi da dariyar da takeyi tana kallon Lailah saikuma ta kuma fashewa da dariyar.
Tana nuna Lailah da yatsa Ta ce "kalleki yanzunnan kika gama cewa kina tsoron maza fa.
Saikuma kice zaki koya mishi hankali?". Shiru Lailah tayi ba ta  ce komai ba sai Faman muzurai da takeyi da hura hanci 👃.

Ganin haka yasa Afeefah ta miƙa mata wayarta.  
Duba ki gani na samo zazzafan dress ne, mai zafi fa,sosai zai taimakamin wajen shigata na gasa, Afeefah ta faɗa tana miƙawa Lailah wayar dan taga alamar kamar ranta ya baci.
Ko kallon wayar Lailah bata yiba ta miƙe zata bar ɗakin tana faɗin bani da Lokaci yanzu,amma wata gila gobe, dama dai kayan make-up ne toh wata ƙila na duba amma fah idan anci mugun sa'a.
Afeefah ba tace komai ba har Lailah ta fita. Ita ma tashi tayi ta fita, bedroom ɗin Zaynerb ta wuce.

Saman sallaya ta hango ta da alama sallah takeyi dan haka bata ƙarisa shiga ba ta juya bedroom ɗinta tana mamakin halin Zaynerb wani lokacin tana abu kamar mai hankali wani lokacin kuma kamar mai taɓin ƙwaƙwalwa ko kuma mai shafin aljanu 👹

 DAGA ALƘALAMIN {𝔗𝔥𝔢 𝔑𝔞𝔦𝔫𝔞𝔯𝔥 𝔎𝔡♥}
 

 
Washe gari Afeefah kamar yadda ta saba bayan ta iddar da sallah tayi azkhar fita tayi, ɗakin Zaynerb ta shiga ta tashe tayi sallah sannan ta shiga na Haleesat da Lailah ta tashe su.

Sannan Kitchen ta wuce acan ta sama Auntie sa'adah tana aikin haɗa breakfast dayake ainihin ma'aikatan gidan mata Biyu ummi da Elina da Suke Aikin haɗa recipe na Gidan sun Tafi Gida hutun shekara,basu riga sun dawo ba.
Gaisawa sukayi cikin mutunci kamar yadda suka saba.

Sannan Afeefah ta kama mata suka ci gaba da haɗa breakfast ɗin domin Afeefah ta qware highly highly ta koya girki kala kala wajensu Elina da ummi,sannan kuma har makaranta na koyon girki suka shiga ita da Haleesat.

Ita dai Auntie sa'adah tana mamakin hali irin na Afeefah ganin yadda dukiyar mahaifin ta ko kuma yanayin gidansu baisa ta ɗauki girman kai ta ɗaurawa kanta ba.

Nisawa Auntie sa'adah tayi tana kallon Afeefah dake aikinta cike da qwarewa sannan ta fara kama kame irin dai tanaso Tayi magana batasan ta inda zata fara bah "uhnm ahmm nace bah",
Juyowa Afeefah tayi tana kallon Auntie sa'adah dake kama kame ta rasa abin cewa.
"A hankali ta ce Auntie sa'adah akwai Wani abu ne?", murmushi Auntie sa'adah tayi sannan ta ce "eh dama ina so naje ƙauye ne naga yarinya ta da kuma sauran jama`an ƙauye da Ahalina" sai kuma ta tsaya tana kallon Afeefah sannan ta ci gaba da cewa "kuma zan ɗan daɗe ban dawo ba shine nakeso a ɗan yiwa hajiya Rafi`atu magana a kan albashi na."

Cike da takaici Afeefah ta girgiza kanta tana mai mamakin hali irin na Momy Rafi'at ace house maid baza'a basu salary ba sai sun tambaya, Allah ma kaɗai yasan iya waɗanda tayi wa wannan halin, no wonder wani lokacin sai dai a nema ƴan aiki sama da ƙasa a rasa.
Nisawa tayi tana kallon Auntie sa'adah dattijuwar da ba za ta wuce shekaru arba'in ba.

Sannan a hankali ta ce "shikenan zuwa yaushe zaki tafi ?, Da sauri Auntie sa'adah ta ce "zuwa da yamma ne",Okay ba damuwa zan mata magana cewar Afeefah
Daganan ba wanda ya kuma cewa wani abu acikin su har suka kammala

Tuwon shikafa ne miyar wake sukayi da lemon abarba da kwakwa sannan sai meat balls and potato sauce da kuma health spinach mix da farfesun kayan ciki sai kunun gyada😘 e.t.c

Sai Afeefah tayi ɗan wake mai rai da lafiya dan kuwa tace shi take jin yin breakfast dashi.
Jerewa sukayi a dinning table..
Afeefah ta kalla Auntie sa'adah dake shirin barin wajen ta ce "uhmm dama miye ma sunan garin naku ne?", juyowa Auntie sa'adah tayi tana kallon Afeefah da mamakin tambayar da tayi mata..
Ganin mamaki a fuskarta yasa Afeefah cewa "dama kawai na tambaya ne fah amma no problem".

Da sauri Auntie sa'adah ta ce "Jaji ne sunan garin."  "JAJI " Afeefah ta maimaita a hankali tana tunanin a wani state ma yake.....
Kamar Auntie sa'adah tasan abinda take tunani ta ce "a kaduna garin yake".
Murmushi Afeefah tayi bata kuma cewa komai ba ta koma bedroom ɗinta wanka tayi ta shirya cikin abaya dark green tayi rolling da mayafin abayar batayi make-up ba powder kawai ta shafa a kyayawar fuskarta sannan ta sa lip gloss a red lips ɗin ta kana ta fito.

Afeefah matashiyar budurwa ce da bazata wuce shekaru ashirin zuwa da ɗaya ba a duniya, doguwa ce sosai highly gata akwai yalwar gashi har gadon baya yanayin fatar ta ita ba za'a kirata da fara ba, amma tafi ƙarfin a kirata da chocolate color ko Black beauty wata kalar fata gareta mai shinning gunin burgewa ga hancinta dogo mai tsini da yayi daidai da yanayin fuskarta bakinta ɗan ƙarami mai ɗauke da lips red gata da diri tabara kalla masha Allah, shalelen daddy wato MISTER MAI KYAU kenan, a hankali zamu tsunduma cikin wannan labari mai suna S⋆A⋆R⋆A⋆U⋆N⋆I⋆Y⋆A⋆R⋆♥︎K⋆Y⋆A⋆U⋆, domin jin wacece SARAUNIYAR nan, labari mai ɗauke da cin amana yaudara zamba cikin aminci chakwakiya hargitsi maƙirci danasani nishaɗantar wa game da zazzafar soyayya😜😜

A♥f♥e♥e♥f♥a♥h♥

Part ɗin mister mai ƙyau ta wuce kanta tsaye ta wuce bedroom ɗin sa knocking tayi.. "Yes come in"! Daga ciki aka bata amsa shiga tayi ciki akan Royal sofa ta sameshi zaune da al qur'ani mai girma a hannun shi da alama dai karatun Yakeyi ko kuma ya kammala, zama tayi akan carpet ta kwantar da kanta akan laps ɗinshi sannan cikin murya mai cike da shagwaɓa tace "daddy".

"Daddy na sabah*ul khairi!!

Murmushi daddy yayi sannan yace kin Tashi lafiya shalele na, "lafiya qlau daddy na" ta faɗa tana murmushin ƙaunar mahaifin nata.
Ɗan waigawa tayi tana dube dube, ganin haka yasa daddy faɗin lafiya kuwa me kike nema ne ?, Daddy wae Momy Rafi'at fa ta faɗa duk da tasan matar ba ƙaunar ta take ba amma matsayinta na matar daddynta ya kamata ta bata girman ta.

Tana part ɗinta daddy ya bata amsa fuskar sa ba walwala, lura da Hakan da Afeefah tayi ne yasa ta canza topic ɗin da faɗin  "ah daddyna our breakfast is ready".
Ta faɗa tana murmushi ta ci gaba cewa a yau ƙarfe goma sha ɗaya na safe muke da lectures ni da Lailah" ta ƙarishe tana ɗaukar al qur'ani da daddy ya aje akan glass center table da ke a palon ta mayar dashi mazunin shi.

Sannan suka fito daga part ɗin nasa a Tare suna fira Cike da farin ciki kana kallon su kasan uba da ɗiyarsa ne wa'inda ba ƙaramin shaƙuwa bace tsakanin su.

Zaynerb suka samu a dinning room ɗin ita kaɗai tana kai Loma, tana hango daddy fara'ar fuskarta ta ƙaru da sauri ta ƙariso gurin tayi hugging ɗinshi sannan ta manna mishi sumba a gefan fuska tana dariya ta ce "good morning daddy".

Murmushi ɗauke a fuskar daddy ya ce "morning daughter amma ya naga idanun ki sunyi jajur bakiyi bacci bane jiya hala, nifa banaso kina takura kanki da karatu fa,ki dinga bawa kanki hutu kinji ɗiyata"..
Murmushin da yafi kama da na yaƙe zaynerb tayi sannan ta ce "eh  toh dayake muna da exam yaune" ta faɗa a gajarce tana komawa ta zauna idonta na kan Afeefah dake serving daddy addu'a take a ranta Allah yasa kar Afeefah ta tona mata asiri a gurin daddy, tunda baisan tana harkar shayashaye ba.

Aikuwa dai addu'ar ta bata amsu ba dan kuwa gyaran muryar Afeefah taji tana faɗin "a dai dinga jin tsoron Allah a komai please."
Bata kulata ba ta ci gaba da cin breakfast ɗin ta.

Lailah ce ta ƙariso gurin tana ɓata fuska da alama tashin ta akayi tana bacci bayanta Haleesat ce tayi shirin ta cikin english gown marron color ta ɗaura hula akanta dogon gashin kanta ya fito dayake hular rigar jikinta ne bata rufe gashin ba fuskarta ba make-up sai lip gloss.

ita kuma Lailah sanye take cikin abaya peach color wanda yayi daidai da kalar fatar ta, ta yafa veil ɗin abayar a akanta fuskar nan tasha heavy light make-up ta ƙarisa gurin daddy ta rungumeshi ta baya ta manna mishi sumba a gefan fuska tana faɗin "good morning Lovely dad!."

"Morning daughter how far?".
 I'm fine daddy ta faɗa tana zama a kusada shi ƙarisowa gurin ita ma Haleesat tayi tana murmushi take faɗin "good morning Daddynmu".

Murmushi Daddy Yayi yana kallonta sannan shima Ya ce "Morning daughter how are You?,am okay daddy ta faɗa tana zama Kusada da Zaynerb.

Sannan Suka ci gaba da cin breakfast ɗin su, can saiga Momy Rafi'at ta sauko ƙasa daga Upstairs dayake can bedroom yake, bata kula kowa ba ta zauna a kujerar dinning  ɗin da sauri Auntie sa'adah ta ƙariso gurin tayi serving ɗinta.

Ina kwana momy!!. Afeefah ta faɗa tana kallon abincin gabanta, ba ta re da da Momy Rafi'at ta kalleta ba ta ce lfy a taƙaice ita ma, suma su Lailah gaisheta sukayi ta amsa da sakin fuska.

Kallon zaynerb Afeefah tayi ta mata alama da ta gaisar da Momy Rafi'at, Zaynerb tana sane taƙi kulata ɗan gyaran murya daddy Yayi yana kallon zaynerb ɗin a hankali ya ce "daughter bakiga momynki bane?",.

Zaynerb tana kallon Momy Rafi'at dake mata kallon ƙasan ido tayi smile ta ce "oh oho ae daddy karka damu, har ɗaki nabi ta muka gaisa fa", ta faɗa tana kashe wa Momy Rafi'at ido Wanda Hakan daya faru ba wanda ya gani ko ya lura.

Kallon Momy Rafi'at Daddy Yayi cikin murmushi yace haka akeso daganan ya cigaba da cin breakfast ɗinshi.

Ita kuwa Momy Rafi'at da ɗumbin mamaki Take kallon Zaynerb data shirga ƙarya amma ko'a jikinta Domin kuwa basu haɗu ba sai yau kuma yanzu, amma shine harda iya cewa tazo ɗakinta sun gaisa qwafa taja bata ce komai ba, ta ciga ba cin abincin ta.

Gyara zama Zaynerb tayi tana fuskan tar daddy cikin murya irinna zumuɗi ta ce "daddy nanda wata ɗaya  fa, za'a gudanar da zaɓan   S͓̽A͓̽R͓̽A͓̽U͓̽N͓̽I͓̽Y͓̽A͓̽R͓̽♥︎K͓̽Y͓̽A͓̽U͓̽ matakin jaha kuma sannan sunan Afeefah ya fito ma ina tunanin baka sama Labari ba,ko na ce SARAUNIYAR Gidan namu bata faɗa  maka ba" Zaynerb tayi maganar ne  tana kallon reacted ɗin  gabaɗaya mutanen dake a dining ɗin aikuwa dai tana lura da yadda saura kaɗan Momy Rafi'at ta qware da juice ɗin da take sha saboda tarin da yazo mata yi take ba qaqqautawa.

Da sauri Zaynerb ta miƙa mata ruwa tana mata sannu, ko kallon ruwan da zaynerb ke miƙa mata Momy Rafi'at batayi ba dan takaici gorar ruwan ever dake kusada da ita ta ɗauka sai da ta kwankwaɗe shi tas sannan ta aje gorar tana ɓallawa Zaynerb harara kamar idonta zai fito waje tsaban takaici  da tsanar da tayi mata.

   
Ita ko Lailah kasa haɗiye abincin bakinta tayi Dan kuwa maganar da Zaynerb ta faɗa a bazata ya zo mata da Ƙyar ta iya haɗiye abincin bakinta tana kallon daddy dan jin abinda zaice.

To Bangaren Haleesat ma Hakane sai dai ita ko a fuska bata nuna ba balle ka zargi wani abu ita ma dai zuba ma daddy ido tayi dan jin abinda zaice.

Afeefah kuwa murmushi kawai take saki tana kallon ko wannensu kana ta sauke idonta akan daddy ita ma.

Qayataccen murmushi na musamman daddy ya saki yana kallon kyakyawar Yarinyar tashi Afeefah daya ci buri akanta, sannan a hankali ya ce "na sama labari  tun last week kawai dai ina jira kuda kanku kuyimin tuni sannan,yanzu saiku fara shiri ko.

fuska washe Zaynerb take faɗin Hakane daddy zamuyi list ɗin abubuwan da ake buƙata duk da dai ita Afeefah ɗin bamusan ko wani kalan kaya zatayi amfani dashi a gurin ba Zaynerb tayi maganar tana maida hankalinta akan Afeefah.

Murmushi tayi sannan ta canza zancen da faɗin nayi waya da xixi tace min nan Nijeriya zata dawo da karatunta ba za ta iyayi a abroad ba.

"Zinaru ɗin ce ta faɗi hakan da kanta?", daddy ya tambaya cikin kaɗuwa suma dai su Haleesat baki wanga me suke kallon Afeefah xixin da ko one Year ba ta cikasa ba da zuwanta faransa karatu, zatace zata dawo bayan ita ta takura a paris take son yin karatu wajen Uncle Yunus harda su rashin lafiyar ƙarya dan daddy yaƙi Yarda daga farkon Lamarin....

Afeefah ta cigaba da cewa ta ce idan ta dawo zata faɗa dalilinta fa, inaga kawai Kewar mu Takeyi highly shiyasa.

Shiru sukayi jin abinda da ta ce ita ko Momy Rafi'at takaici ya isheta wai ace ɗiyarta guda zata dawo ita bata sani ba sai a bakin wata banza Afeefah waya sani koma ita Afeefah ɗinnne ta zugata tabar karatun a acan.

Ba wanda ya kuma cewa komai a cikin su har suka kammala cin breakfast ɗinnasu.
Ta re da Lailah Afeefah suka fita dayake school ɗaya sukeyi Suna karantun likitanci M.B.B.S. a Babbar university dake birnin tarayya ɗin wato madinatul Abuja😎.

Haleesat bata fita ba dan yau batada lecture ita micro biology take karanta tana matakin ƙarshe.
Zaynerb kuma itama ba ta da lecture gabaɗaya satin dan kuwa Shari'a take karanta tana matakin kusada Ƙarshe.

{ 𝔹𝕪 𝕋𝕙𝕖 ℕ𝕒𝕚𝕟𝕒𝕣𝕙 𝕂𝕕 }

*💋SARAUNIYAR KYAU💋*

*ⓟⓐⓖⓔ 9&10*

🄺🄰🄽🄾

    
🅹🅸🅴🅳🅳🅰🆁🅷♥︎🅚🅞🅜🅐🅘♥︎🅝🅐🅚🅐

A gurguje take shirin tana jin Humaira na ƙwala mata kira zasu tafi airport ɗauko "ABBA" zai dawo daga ƙasar Australia. Da sauri ta ƙara murza Jan baki a laɓɓanta tana kallon kanta a dress mirror saida tayi juyi sannan ta ɗauki wayoyinta  da handbag ɗinta ta fito tana yafa scarf ɗinta.

A palo kuwa Humaira ta cika tayi fam fam domin kuwa saura kaɗan ta fashe, da sauri ta ƙarisa saukowa downstairs ɗin da sassarfa ta ƙariso wajen Humaira bata tsaya jin abunda Humaira za ta ce ba ta jawo ta tana faɗin "afuwan my sis zo muje" ba yanda Humaira zatayi haka tabi bayan Jieddarh suka fita dan tuni Auntie tana jiransu a mota ita da Heesham da yake shi zai kaisu airport ɗin.

***
Sun isa airport lokacin saura five minutes jirgi Yayi Landing, dan haka suka tsaya jira basu wani daɗe suna jira ba jirgi ya sauka, a hankali fasinjoji suke saukowa duk gabaɗaya su jieddarh sun bada hankulansu suna jiran fitowar sa.

A hankali farin dattijo wanda akalla bazai wuce shekaru Hamsin zuwa da uku ba yake taka mattatakalan jirgi yana saukowa, Humaira ce ta fara hango shi aikuwa da sauri ta ƙarisa gurin shi bata tsaya jiran wani Abu ba ta rungumeshi tana faɗin "welcome Abba we miss you highly."

Murmushi kawai yake saki yana bubbuga bayan ta, lokacin ne su Jieddarh suka ƙariso gurin fuskar ko wannensu ɗauke da walwala.

"To ae saiki sakeshi ya huta ko, kin wani maƙalƙale shi, Like a baby girl!, Jieddarh ta faɗa cike da barkwanci dan kuwa duk, wanda yasan Jieddarh yasan ta da barkwanci,She`s flirting girl.

Dariya Humaira tayi tana faɗin "nayi kewar ABBA obaa highly shiyasa", ta faɗa lokacin da take sakin shi.

A haka dukansu suka yi hugging ɗin shi cike da farin ciki da Nishaɗi, Auntie ce ƙarshen yi da akazo kanta sai taƙi yin hugging ɗinshi wai tayi fushi saida aka gama da yara sannan za'a tuna da ita?.
Dariya sukayi dukansu hadda Abba Jieddarh ta ce "haba Auntie ae yanzu ba take akeyi ba tamu Abban mu yake ke kinyi tsufa kalli yadda kike tafiya kamar zaki yi kasa fah,  habah Auntyn mu kinyi zamanin ki fah wannan ƙarnin mune fah."

Dukan wasa Auntie ta kai mata da sauri ta ɓuya a bayan Abba tana dariya qwafa Auntie taja tana faɗin "zan kama ki ae fitinanniyar Yarinya kawai hmm hmm."

Dariya Abba yayi ya ce "ba ganewar da zatayi ae gaskiya ta faɗa dan haka a qyale min ɗiyata.

Heesham ya ce "da kunzo antafi gida a ƙarishe drama ɗin acan."
"Aikuwa dai da zaifi armashi" cewar Humaira Ita ma.
Gabaɗaya suka ɗunguma gurin mota suka ƙarisa Heesham ya shiga mazaunin driver, Humaira kuma a gefan mai zaman banza, Yayinda Jieddarh dasu Auntie suke a kujerar baya Jieddarh tana nanuƙe da Abba a Haka har Gida.

     

           

   ⒶⒷⓊⒿⒶ

🅷🅰🅻🅴🅴🆂🅰🆃♥︎🅜🅐🅘♥︎🅚🅨🅐🅤

Bayan fitan su Lailah school ɗaki ta koma kai tsaye Wayarta ta ɗauka ba tare da Wani ɓata lokaci ba, ta lalubo lambar xixi na ƙasar faransa ta danna kira, Sai dai a kashe wayar take.

 Yanzu ma Bayan tsawon mintuna Talatin, ta kuma kiran tana mai addu'ar Allah Yasa xixi ta ɗauka, saboda akwai maganar da take so ta mata, shin ko akan meyasa takeson dawowa Nigeria da karatunta bayan kuma ita ta zaɓa karatu a Abroad.

Cikin sa'a kuwa wannan karon xixi ta ɗaga kiran.

Wata nannauyar ajiyar zuciya Haleesat ta sauke tana mai zama akan Royal bed ɗinta.

"Hello!! xixi," Haleesat ta faɗa Cike zaquwa.
On the Other hand ƙasar faransa, xixi ta amsa da....
"Hello!! Aunty leesat ya kike?"....
"Am so Normalcy," "kefah naji muryar ki kamar ta mai kuka meke faruwa?", aikuwa kamar ta ce ma xixi ta ƙara volume ɗin kukan ta ne, ƙara sautin kukunnata tayi, cikin kukan take faɗin "Aunty leesat ni gida kawai zan dawo na gaji da wannan ƙasar ta faransa,muguwar ƙasa,ni kawai Nijeriya zan dawo soon.

cikin rarrabewar murya Haleesat tace "xizzixi! xixi!! calm down just relax, natsu ki faɗamin abinda ya sameki kinji,"
Still cikin muryar kukan xixi ta ce "ni kawai gida nakeso na dawo, na gaji da wannan muguwar ƙasar wallahi." ta ƙarishe maganar  tana mai fashewa da kuka higher.

"Tofah" Haleesat ta faɗa tana furzar da huci tunda taji xixi na kuka tasan abin ya cutura, a hankali cikin muryar lallashi ta ce "xixi shiga video call kawai domin zamufi enjoying na maganar okay!!."

"Tom" xixi ta ce tana kashe wayar sannan ta shiga video call ɗin ita ma Haleesat kan sofa ta koma ta zauna sannan ta shiga video call ɗin ita ma, nan take wata kyakyawar matashiyar budurwa ta bayyana wacca ba za ta wuce shekaru goma sha tara ba, tana kwance saman royal bed jikinta sanye da top red color da wando jeans pencil dogo black color ta ɗaure dogon gashin kanta da red nd black Ribbons tayi style in ponytail idanun nan nata kuwa sun koɗe sunyi jajur, fuskarta ta kumbura alamar dai taci kuka ta godewa Allah, dogon hancinta shima har wani ja, yayi saboda matsan da yasha. pillow rungume a chest ɗinta ta ƙanƙame shi cikin muryar kuka ta ce "Aunty leesat!".

Zaro ido Haleesat tayi tana bin xixi da kallo ganin yadda duk tabi ta rame tayi zuru zuru da ita. "xixi kece kuwa?"xixi Menene meke faruwa dake haka ne duk kinbi kin rame". Haleesat ta tambaya cikin shiga tsananin violence.

Qara ƙanƙame pillows ɗin dake ƙirjinta xixi tayi ta rufe bakin ta da duka hannayenta ta kasa cewa komai saima kukan dake ƙara taho mata.

"Okay natsu kwantar da hankalinki sai kimin magana" Haleesat ta faɗa tana ƙara waro ido tana bin xixin da kallo gabaɗaya ta fita hayyacinta kamar ba ita ba, ajiyar zuciya ta kuma saukewa a karo na babu adadi sannan ta kira sunanta.

A Hankali "xixi! faɗamin abinda ya faru kinji?, kodai baƙyajin daɗin zaman gidan Uncle Yunus ne?, girgiza kai xixi tayi alamar a'a, "to menene ko a school ne?", nanma girgiza kanta ta kumayi alamar dai a'a. "to kin gaji da paris ɗinne kinaso ki dawo Nigeria gurin mu?.

Girgiza kai tayi, sai kuma da sauri ta ɗaga kanta alamar eh Hakane, murmushi Haleesat tayi sannan ta ce "wato kewar mu kike yi ko?", eh xixi ta faɗa tana sauke ajiyar zuciya to yanzu me kike nufi Haleesat ta Tambaya tana jiran amsa.

Dan kuwa tasan xixi ɓoye mata kawai tayi wannan dalilin bashi zaisa ta rame haka ba akwai dai wata a ƙasa.
"Okay kinsan menene ki daure ki kwantar da hankalinki ki samu ki ƙarisa wannan term ɗin kinga yanzu kina level one going to level two ki daure ki ƙarisa kin san dai daddy baya tolerating nonsense ki daure ki ci gaba karatun ki nasan ba gaskiya kika faɗamin ba amma na miki uzuri duk time ɗin da kikaga ya miki zaki iya faɗamin abinda ke damun ki, kinji ko Tawan," Da to xixi ta amsa tana sakin murmushin ƙarfin hali.

"Okay to sharre hawayen naki kinji baby xixi na Autar momy kuma Autar gidan mu daga ke ba ƙari ko anaso ko ba`aso," Fashewa da dariya xixi tayi, ita ma Haleesat ɗin dariyar takeyi.

Muryar Labiba taji ta bayanta da sauri ta juya tsaye take, ta harɗe hannayenta ta baya tana sanye cikin Turkish gown riga doguwa milk color bata sa mayafi ba sai veil da ta yafa a kanta  fuskar nan nata a ɗaure tawau.

Qarisowa tayi saman gadon ta zauna sannan ta ce "Aunty leesat karki bi ta wannan yarinyar tunda ta iya zurfin ciki tun one week da ya wuce take wannan kukan anyi lallashin duniyar nan ta faɗa abinda ke damunta taƙi faɗa," Labiba ta ƙarishe tana hararar xixi.

Dariya Haleesat tayi sannan ta ce "ae kunfi kusa ko kin manta saboda ke ta dawo nan ƙasar da karatunta ta barmu Anan,"

Dariya Labiba tayi ta ce "gashi kuma taƙi faɗamin abinda ke damunta gabaɗaya na shiga damuwa,"  "ae rabu da ita kawai idan taji wuya zata faɗa ne" Haleesat ta faɗa tana murmushi, "ke dae Aunty Leesat barta kawai karma ta faɗaɗin zamuga wanda zai bari ta dinga yin ƙunci a gidanan," Labiba ta faɗa tana ƙara tamke fuska alamar bada wasa take bah, nan dai Haleesat da Labiba suka ci gaba da fira tsakani,ita kuwa xixi idan taga dama ta saka musu baki idan kuma bata ga dama ba sai dai tabi su da ido, sun ɗauki lokaci suna wayan kafin suyi sallama Haleesat ta kashe wayarta a hankali ta lumshe kyawawan idanun ta.

Tunani ta faɗa lokacin da xixi ta kammala secondary school ɗinta, lokacin xixi dagewa tayi sai ta koma paris da karatu wajen Uncle Yunus ɗinsu wai tare takeso su ci gaba da karatun tareda Labiba ɗiyar Uncle Yunus a paris dayake, Age mate Suke Labiba taba xixi wata biyu a duniya, alokacin har ciwo ta kwanta dan daddy ya hanata zuwa paris karatu saida ƙyar aka samu ya barta ta tafi shine yanzu wai kuma zata dawo itama tasan ba'a take dan daddy ba yarda zayyi ba har saita kammala degree tukunna, murmushi Haleesat ta saki a fili tace xixi rigima silly girl kawai kuma autar gidanmu😝

Tashi tayi ta faɗa wanka takai tsawon mintuna talatin kafin tafito ɗaure da towel White color.
Gaban dress mirror ta tsaya tana busar da dogon gashinta da handDrier saida ta busar da gashin, sannan ta aje Drier ɗin a mazaunin shi.

Shiryawa tayi cikin indian dresses gown iya gwiwarta pink mai adon stones purple da wando jeans pencil dogo pink and purple shima, ribbons tasa ta tufke sumarta da ƙyar don yawan da sumar take dashi domin kuwa kaf gidan daga Zaynerb sai Haleesat sune masu tsayi da yawan gashi over highly,ita dai Afeefah sai dai ta nuna musu yawan gashi sosai domin gashinta akwai yawa sosai don ya wuce gadon bayanta ya sauka har mazaunanta.
Ɗaukar mayafin kayan tayi ta yafa akanta ba tare da tasa hula ba tana shirin ɗaukar wayarta domin kiran Wata Maryam classmate ɗinta domin su tattauna akan Bikin maryam ɗin daya kusa, Ta tajiyo muryar momy a palo tana ƙwala mata kira.
Palon ta fito ta sama guri ta zauna a saman two siter ita ma momy Rafi`at ɗin guri ta samu ta zauna tana fuskan tar Haleesat ɗin "Haleesat".

Momy ta kira sunan ta ba tare da ta ɗago daga latsa wayar da takeyi ba ta amsa da "na'am momy akwai wani abune?"

Gyara zama Momy Rafi'at tayi bata damu da yanayin yadda Haleesat ta amsa mata ba ta fara magana.
Haleesat ki natsu magana mai muhimmanci nakeso muyi dake Yanzunnan.
Mayar da wayar dake hanunta gefanta Haleesat tayi sannan ta fuskan ci momy Rafi`at ɗin "Yeah! inaji wata magana ce wannan ?".
"Haleesat yanzu haka zamu saka ido a Gidannan wannan shegiyar Yarinyar nan ta dinga juya kowa yadda takeso kamar wasu bayinta ki duba ki gani ɗazu da zata fita a gaban mu taba wancan kucakar House maid ɗin can  sa'adah dubu ɗari biyu, to wallahi idan muka bari irin haka ta ci gaba da faruwa tofa wata rana Gidannan sai yafi ƙarfin mu gashi ɗazu naji wai ana maganar an zaɓe ta a gasar 𝐒𝐀𝐑𝐀𝐔𝐍𝐈𝐘𝐀𝐑 𝐊𝐘𝐀𝐔 matakin jaha kuma naji ana maganar saura one month.....
Ɗan tsagai tawa da maganar Momy Rafi'at tayi tana kallon yadda Haleesat ta mayar da hankalinta gabaɗaya kanta tana sauraronta.

Murmushin gefan fuska Tayi sannan ta ci gaba da cewa "Kuma tana cin gasar nan nasan ba za ta tsaya ba saita je na ƙasa daganan kuma saina duniya,mu kuma Zuwa Lokacin baƙin ciki Ya kashe mu"😱

"Yanzu na yanke shawarar kota halin qaqa bazan bari taci gasar nan ba gobe zanbi  Flight zuwa China gobe."
"Na Rantse da Allah Mai girma indai ina numfashi a duniya bazan bar yaran haajarah su huta a duniya ba yaran da mijina ya fifitasu sama da nawa yaran" ta ƙarishe maganar tana huci kamar wata kububuwa..

Miskilin murmushin gefen baki Haleesat tayi sannan ta ƙara gyara zaman ta akan Royal sofa ɗin kana ta fara magana, momy kenan wani lokacin kina bani mamaki saiki dinga abu kamar yarinya yanzu wannan ƙaramar alhakin ne saikin Tafi har can China akanta, irinsu makirci ma kaɗai ya ishesu yanzu ga YaYarta Zaynerb duk da bansan ko Menene ainihin abinda ya sakata a Halin shayashaye ba amma nasan da saka hannunki ciki sabosa nasan wacece ke sama da kowa right, ɗan shiru Haleesat tayi yayinda suka shiga kallan kallo tsakanin ta da mahaifiyartata Momy Rafi`at,wai akuya ta mari kura, wani ƙayataccen Murmushin gefan fuska Halessat ta kuma saki sannan bata damu da kalar fitinannen kallon da Momy Rafi`at take mata ba ta ci gaba da cewa,  "Ae koshi kaɗai ya ishesu a Rayuwa ma ba sai an ƙara musu da komai ba,Haleesat ta ƙarishe maganar tana kuma sakin shu'umin murmushin gefen baki...

Wata Kalar Dariyar Bosawa Momy Rafi'at ta fashe da ita tana tafa hannu tace yanzu nasan na haifa ƴa duk sauran yarana duk wawayene yanzu nasan na haifa Yarinyar da zata maramin baya a duk shirina. Haleesat ɗiyata Allah Ya suburbuɗa miki Blessed highly highly kuwa.

Dariya Haleesat tayi ita ma harda ba momy hannu suka tafa kamar wasu yara ba ƴa da uwa ba { T⨳o⨳f⨳a⨳h⨳ T⨳o⨳ A⨳l⨳l⨳a⨳h⨳ y⨳a⨳ k⨳y⨳a⨳u⨳t⨳a⨳ }

A hankali Zaynerb dake laɓe a bakin ƙofar bedroom ɗin ta fara Ja da baya tana rufe bakin ta da duka hannayenta jin wani irin kuka nason qwace mata, Yayinda gabaɗaya Jikinta babu inda baya rawa na tsananin tashin hankali data shiga, Da gudu ta shige ɗakinta ta rufe da key.

Ta faɗa saman bed tana sakin wani marayan kuka ta na ƙarajin mamakin hali irin na Momy Rafi'at, ita batasan me ita da ƴar uwanta suka tarema matar nan ba tabi ta tsanesu a Rayuwa duniyar su, share hawayenta tayi ganin ba kuka ne abin yi ba tashi tayi ta zauna a saman bed tana ƙara tuno yadda taji firan Momy Rafi'at da Haleesat ɗin, Farkon Abin ta fito da niyyar tafiya ɗakin Haleesat suyi magana akan matsalar xixi taji magana ƙasa ƙasa shine ta tsaya dan taji me ake cewa dan ita da farko ta ɗauka Haleesat ɗince take waya da ƙawayenta ashe abin ba haka bane, Gashi taji abinda yafi ƙarfin tunanin ta ashe Haleesat kallon kishe akema rogo muguwar makira ne ba'a sani ba, murmushi tayi sannan a fili furta China ko zanga yadda za'aje china kuwa, Ubangiji Allah ya kaimu goben da rai da Lafiya😇.

Miƙewa Tayi sannan Takai dubanta ga agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunta ƙarfe ɗaya da kwata na rana.

Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta nufa gaban dress mirror ta cire agogon hannun ta sannan ta shiga bathroom, Alwala ta ɗauro ta fito ta shimfiɗa sallaya sannan tayi sallar azahar bayan ta iddar da sallar ba tare da ta cire hijjab ɗin da tayi sallah ɗin ba ta fito daga bedroom ɗinta, kai tsaye kitchen ta wuce Auntie sa'adah ta samu tana aikin abincin Rana, Da murmushi ɗauke a fuskar ta ta ce "Auntie  sa'adah sannu da aiki baki wuce ba kenan?",  Ita ma murmushi tayi ta ce "sai zuwa ƙarfe uku na rana zan wuce insha Allah.

"Okay aunty akwai wani Abu na musamman a kitchen ɗinnan kuwa wanda mai ƙaramin ciki zata iya buƙata na marmari?".

Murmushi Auntie sa'adah tayi sannan ta ce "eh mana Zaynerbu Abuuu akwai, baza`a rasa ba. "Yawwa Auntie a haɗomin akwai mai buƙata cewar Zaynerb tana murmushi, "Ae inaga zatafi son kwaɗo ko bari nayi  ma ta shi kinsan mai ciki akwai son kwaɗayi, "Aikuwa dai Auntie sa'adah ita wannan cikin nata wata huɗu ne shigan na biyar, Zaynerb tayi maganar tana zama a ɗaya daga cikin chairs ɗin dining da aka qawata kitchen ɗin dasu.

Aikuwa kwaɗon dafaffen zogale da quli yaji kayan hadi tayi sannan ta zuba a kula ƴar daidai taba Zaynerb dake kallonta tana murmushi ta ce "gashi an kammala" Amsa Zaynerb tayi tana yima Auntie sa'adah godiya sannan ta fita daga kitchen ɗin.
Auntie sa'adah ta bita da kallon tausayi dan kuwa sosai take tausawa Rayuwar Yarinyar ita da ƴar uwanta Afeefah basu da wata matsala saina Rashin uwa ga mahaifin su shiba mazauni ba gashi sun haɗu da kishiyar uwa mace mai son kanta da Yawa, kai kurum ta girgiza sannan ta ci gaba da aikin ta tana mai musu addu'ar samun ingantaciyar Rayuwa cikin zuciyar ta.

{𝔗𝔬𝔣𝔞𝔥 𝔍𝔞𝔪𝔞'𝔞 𝔐𝔢𝔫𝔢𝔫𝔢 𝔄𝔟𝔦𝔫𝔡𝔞 𝔐𝔞𝔥𝔞𝔦𝔣𝔦𝔶𝔞𝔯 𝔰𝔲 𝔄𝔣𝔢𝔢𝔣𝔞𝔥 𝔱𝔞𝔶𝔦𝔴𝔞  𝔪𝔬𝔪𝔶 ℜ𝔞𝔣𝔦`𝔞𝔱 𝔫𝔢 𝔡𝔞 𝔷𝔞𝔣𝔦 𝔥𝔞𝔨𝔞, 𝔡𝔞 𝔱𝔞 𝔡𝔞𝔲𝔨𝔦  𝔞𝔩𝔴𝔞𝔰𝔥𝔦 𝔪𝔞𝔦 𝔤𝔦𝔯𝔪𝔞 𝔥𝔞𝔨𝔞 𝔞𝔨𝔞𝔫𝔰𝔲 𝔷𝔞𝔶𝔫𝔢𝔯𝔟 𝔡𝔞 𝔄𝔣𝔢𝔢𝔣𝔞𝔥, 𝔄𝔫𝔶𝔞 𝔨𝔲𝔴𝔞 𝔨𝔲𝔫𝔞 𝔱𝔲𝔫𝔞𝔫𝔦𝔫 𝔴𝔞𝔫𝔦 𝔞𝔟𝔲,𝔨𝔲𝔴𝔞 𝔨𝔬𝔡𝔞𝔦 𝔫𝔞 𝔟𝔞𝔨𝔦𝔫 ℌ𝔞𝔩𝔢𝔢𝔰𝔞𝔱 𝔡𝔦𝔫𝔫𝔢,𝔐𝔬𝔪𝔶 ℜ𝔞𝔣𝔦`𝔞𝔱 𝔱𝔞𝔫𝔞 𝔡𝔞 𝔰𝔞 𝔥𝔞𝔫𝔫𝔲 𝔞 𝔰𝔥𝔞𝔶𝔞𝔰𝔥𝔞𝔶𝔢𝔫 𝔡𝔞 𝔷𝔞𝔶𝔫𝔢𝔯𝔟 𝔱𝔞 𝔱𝔰𝔦𝔫𝔠𝔦 𝔨𝔞𝔫𝔱𝔞 𝔠𝔦𝔨𝔦 𝔨𝔲𝔪𝔞 𝔱𝔞𝔨𝔢𝔶𝔦 𝔱𝔬 𝔨𝔬 𝔪𝔦𝔶𝔢 𝔞𝔪𝔰𝔞𝔯 𝔡𝔲𝔨𝔞 𝔴𝔞𝔡𝔞𝔫𝔫𝔞𝔫 𝔗𝔞𝔪𝔟𝔞𝔶𝔬𝔶𝔦𝔫 𝔰𝔲𝔫𝔞 𝔠𝔦𝔨𝔦𝔫 𝔴𝔞𝔫𝔫𝔞𝔫 𝔡𝔞𝔡𝔡𝔞𝔡𝔞𝔫 𝔏𝔞𝔟𝔞𝔯𝔦 𝔪𝔞𝔦 𝔰𝔲𝔫𝔞 🅢🅐🅡🅐🅤🅝🅘🅨🅐🅡♥︎🅚🅨🅐🅤  𝔨𝔲 𝔟𝔦𝔶𝔬 𝔞𝔩𝔨𝔞𝔩𝔞𝔪𝔦𝔫 𝕋𝕙𝕖 ℕ𝕒𝕚𝕟𝕒𝕣𝕙 𝕂𝕕 𝔡𝔞𝔫𝔧𝔦𝔫 𝔴𝔞𝔫𝔧 𝔦𝔯𝔦𝔫 𝔡𝔞𝔯𝔞𝔰𝔦 𝔩𝔞𝔟𝔞𝔯𝔦𝔫 𝔶𝔞𝔷𝔬 𝔡𝔞𝔰𝔥𝔦, 🄺🄷🄰🄳🄴🄴🄹🄰🅁🅃🄷 🅂🄰🄱🄸`🅄 🅈🄰🄷🅈🄰🄷, { 𝕋𝕙𝕖 ℕ𝕒𝕚𝕟𝕒𝕣𝕙 𝕜𝕕 ✍️👑👸📲 }♥︎💖💝 }

Zaynerb bedroom ɗinta ta koma ta canza hijjab iya gwiwa fari dama doguwar rigar pakistan ne a jikin ta blue black sai wando shima na pakistan Red color mai adon stones blue black, kular ta ɗauka sannan ta fito daga gidan gabaɗaya ta nufa gidan maƙwabciyar su mai suna ⓈⓊⓃⒶⒾⓃⒶⓇⒽ!.

🅛🅐🅘🅛🅐🅗♥︎🅜🅐🅘♥︎🅚🅨🅐🅤
 

Ɓangaren Lailah kuwa suna zaune a lecture Room suna ɗaukar lecture ita da Afeefah ne bencinsu a gaba sai bencin su zahrah a bayan nasu sai kuma sauran student, nan wayar Lailah Tayi ƙara alamar shigowar kira waƙar mawakiyar korean  "J.Fla" na Tashi mai taken { Attention }

Gabaɗaya hankulan mutanen dake cikin lecture Room ɗinne ya dawo kanta hadda lecturer ɗin dake musu lecture gabaɗaya sun zuba mata na mujiya har Afeefah dake gefenta suna kallo, Da sauri tayi checking excuse. Lecturer ɗin ya bata dama sanin wacece ita da kuma mahaifinta badan haka ba a ƙa`idar makarantar ba`a zuwa da phone idan ba aiki da ita bane ya taso,amma sanin waye mahaifinta a ƙasar yasa, ba ko musu bai mata ba,balle kuma kallon banza ya bari ta fita ɗaga kiran, kuɗi kenan😇

Fita daga lecture Room ɗin tayi tana sauke ajiyar zuciya tana shirin ɗaga wayar kiran ya tsinke tsuka taja Cike da Takaici, To dama da unkown number aka kirata,don batasan ko waye ba,To koma ta sani indai Laila ce,ba bin kiran zatayi bah.

Zata koma wani kiran ya ƙara shigowa wayar sai dai wannan karon momy ne mai kiranta ba wancan ba.
Ɗaga kiran tayi da sallama.
Daga can Ɓangaren Momy Rafi'at dake zaune saman Royal sofa nata ta kira sunan ɗiyartata "Lailah!", amsawa tayi da "na'am momy da wani abu ne ina class Yanzu please zan kiraki anjima Bye bye, Love you, Bata tsaya jin mai momyn zata ce ba ta katse kiran tana jan tsuka sannan ta kashe wayar gabaɗayanta.
Sannan ta koma Lecture Room ɗin basu daɗe ba Lecturer ɗin ya fita dama daga shi ba wani sai kuma gobe, dan haka fitowa sukayi suka nufo Gida Gabaɗaya.

A mota Afeefah sai tsokanar Lailah takeyi dan tasan bazai wuce sabbir bane ya kirata😇

Ita dai Lailah bata kulata ba driving ɗinta kawai takeyi tanajin yadda Afeefah ke tsokanar ta taƙi kulata har suka iso Katafaren Gidan nasu Wanda Ya gaji da haɗuwa ta kowani ɓangare securities ne..
Horn tayi gate man ya wangale musu wagameman gate ɗin gidan, sannan Lailah ta cusa hancin motar cikin Katafaren Gidan a parking lot tayi parking sannan suka fito dukansu a gajiye suke, Don Haka koda suka shiga cikin palon bajewa sukayi saman Royal sofa's da aka qawata qaton palon dasu kuma sukayi ƙyau.

Zaynerb kuwa tana fita Gidan Kai tsaye Gidan wata Neighbor ɗinsu sunainah ta nufa, Da isarta ƙofar wagameman gate na gidan ba tare da ɓata lokaci bah.

Knocking ɗin ƙaramar ƙofar gate ɗin Tayi, sannan mai gadi ya buɗe mata bayan Na`urar tsaro dake jikin gate ɗin ta gama bincikarta, fuskar sa ɗauke da fara'a yake amsa gaisuwar da Zaynerb ke mishi domin kuwa Ya santa highly, ah ae dole yasanta sosai kodan na ce fa ne datake bashi huh🤣😂😅.

Shiga cikin Gidan Tayi sannan ta tura door ɗin palon a buɗe yake dan haka shiga palon tayi da sallama saidai ba kowa ciki..

A tsakiyar palon ta tsaya tana ƙwaɗawa matar Gidan kira, faɗi Take  "Ummyn farhana", "Ummyn farhana!",  Da sauri wata ƴar dattijuwar mata wacca ba za ta wuce ƴar aikin gidan bane ta fito daga kitchen. Da sauri ta ƙariso gurin Zaynerb.....
Ganin ta Yasa Zaynerb ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ce "Yawwa Babah dije matar Gidan tana nan kuwa?", Zaynerb ta tambaya Babah dije data fito daga Kitchen na Palon, ,Eh madam ki sama guri ki zauna bari na kira ta inaji Bacci ne ya ɗauketa kinsan masu juna biyu sai da hutawa", Babah dije ta faɗa tana nufar wani korido dazai sadata da bedroom ɗin matar Gidan.

Zama Zaynerb ɗin tayi tana latsa wayar ta kafin matar Gidan ta fito ilai kuwa bata daɗe da zama ba, Babah dije ta fito tana faɗin "gatanan zuwa bacci ne ya ɗauketa, amma fah batayi nisa ba domin kuwa ina magana ɗaya ta farka duk nisan bacci  irinna masu ciki,"  cewar babah dije lokacin data ƙariso gurin da Zaynerb ɗin take, Godiya Zaynerb ta mata da sauri dan ta fahimci tsohuwar shegen surutu ne da ita,dan wannan surutun da tayi ya fahimtar da Zaynerb ɗin haka domin ita ɗin ɗalibai lauyanci ne kuma zaqwaqwura don tasan makamar karatunta shiyasa da zarar ta haɗu mutun mai surutu ko wani abin take fahimta.
Ita kowa babah dije ta koma kitchen ta cigaba da abinda takeyi.

Zaynerb tana zaune can saiga wata ƙyakyawar mata wacca ba za ta wuce shekaru ashirin da bakwai ba, ta fito tana faɗin "ah ah Yau manyan baƙi ne a gidan namu ashe"  Ta faɗa tana zama a three sieter, Dariya Zaynerb tayi ta ce "uwan Triple yau kuma mune baƙin kodai cikin ne yasa ba'a gane mutane Yadda Ya kamata?"..
Dariya ita ma tayi sannan ta ce "ras nake gani kece dai kikayi nisa kinfa kai one week baki zo ba wallahi, Afeefah tafi ku kirki dukanku harsu Lailah ɗin don tafiku son zuwa nan alamu yana nuni da nan gaba ma saita fiku rike zumunci Yarda ya kamata.

"Okay tuba muke uwan Triple" Zaynerb ta faɗa tana miƙa mata kular hannun ta, Karɓa tayi tana faɗin "harda su tsaraba ne Allah yasa dai na'iya ci,"  Ta faɗa tana buɗe kular aiko tana arba da kwaɗonnan ta fara suburbuɗawa  Zaynerb godiya tana faɗin "dama yau da Wani irin kwaɗayin zogale na tashi gashi Allah ya aikomin ke Zaynerb ɗiyar Albarka dashi.

Ita dai Zaynerb latsa wayar ta take tana dariyar kwaɗayin masu ciki, "Ae kigama min dariya Allah kaimu ranar da zangan ki da ciki zan rama nima," sunainah ta faɗa ganin yadda Zaynerb ke mata dariyar kwaɗayi.
 
Da sauri Zaynerb ta ce "tuba nake Ummyn farhana kinsan Waya ne a hannuna, Don Haka ita ce ta bani dariya obaa  highly bawae keba."

Sunainah bata kulata ba ta ƙwalawa Babah dije mai aikinta kira, Da sauri dattijuwar tazo tana faɗin gani maman Ferhane!!😝😝.

Dariya Zaynerb tayi ta ce "babah dije ba "Ferhane" ake cewa ba "Farhana" ake cewa."
Dariyar ita ma Babah dije tayi tana faɗin "ae wannan suna sai ku ƴan zamani ni ina zan iya cewa wani ferhane."
Sunainarh tana dariyar maganar Babah ta ce "Babah rabu da Zaynerb kawai, Plate zaki ɗaukomin a kitchen",  "To" Babah dije ta ce sannan taje kitchen ta ɗauko special plate ta kawo mata aikuwa ta ansa ta juye kwaɗonnan a plate ɗin nan ta hauci kamar ba gobe, Hannu baka hannu plate, Saida ta cinye tas ta sha Ruwa tana mai miƙa Appreciation to Allah.

Da mamaki Zaynerb ke kallon ta ganin ko minti biyar ba'ayi ba harta cinye,  "Lallai "Ummyn farhana" wannan ci haka anya ba Triple bane bamu sani ba," Zaro ido sunainarh tayi ta ce,  "Triple kuma Zaynerb na kaisu ina? ɗaya ma ya aka ƙare balle kuma har ƴan uku.

Dariya Zaynerb tayi ta ce "ainaga cikin minti biyar harkin cinye Kwaɗo cikin plate ba dole nace ƴan uku bane."
Murmushi sunainarh tayi ta ce "idan ma ƴan ukunne Allah ya bada masu albarka, ae Albarka ake nema ba wani abu ba." Zaynerb ta amsa da ameen, nan dai suka ci gaba da fira irinnasu na ƙawaye.

IN BRIEFLY
Zaynerb dai ba ita ta bar gidan ummyn farhana na ba sai wajen biyar na yamma acan tayi la'asar sai da taga mijin sunainarh ɗin ya kusa dawowa sannan ta mata sallama ta nufi gida.

🅆🄰🄲🄴🄲🄴_🅂🅄🄽🄰🄸🄽🄰🅁🄷_?
    

Sunainarh dai itaɗin makwabciyar su Zaynerb ce, Kuma  asalinta ta kasance ƴar bauchi ce, Aure ne ya kawota Abuja "Sohail" Shine sunan mijinta ɗan gidan ministan ilimi ne shiɗin, haihuwar ta ɗaya sunan Yarinyar FARHANA shekaran ta uku a duniya, Shiyasa Zaynerb take ce mata "Ummyn farhana" suna mutunci obaa highly da Zaynerb harda ma su Afeefah.

🆆🅰🅽🅽🅰🅽 🅺🅴🅽🅰🅽.


💋SARAUNIYAR KYAU💋

💄The Fashion Show💄

*page 11&12*

Tun kafin ta ƙarisa shiga palon take jiyo muryar su Lailah da alama gardama sukeyi ko makamancin haka.

Shiga tayi ciki a palo ta samesu su duka Afeefah, Lailah,da Haleesat saikuma wasu ƴan mata su biyu da alama ɗaya daga cikin su da ita akeyin gardaman, guri ta samu saman one siter ta zauna ba wanda ya lura da shigowar sai Afeefah hannu. Afeefah ta ɗaga mata daga inda take zaune a dinning Room tana cin abinci, alamar gaisuwa ita ma Zaynerb ɗin ta mayar ma da Afeefah martanin murmushi tana gyara zamanta a kujerar da take tana sauraron firansu Lailah tanason gano inda firar tasu ta dosa.
Abin dariya wai gardama suke akan film Yayinda Lailah take faɗin film ɗin, "TILL THE END OF MOON" yafi kyau ita kuma ɗayar matashiyar budurwar da aka kira da Ameenah take faɗin, ina ae film ɗin "THE LEGEND OF ZU yafi kyau👌

Ikon Allah Zaynerb ta furta ganin gardaman nasu yaƙi ƙarewa "wai akan menene ake wannan gardaman Zaynerb ta Tambaya kamar bata fahimci komai ba.

Da sauri ɗayar budurwar wacca bata saka musu baki a firan nasu ba ta ce "kema dai Sister Zaynerb ƙya tambaya wannan abu haka kamar wasu Yara wai akan film sukeyi fa" Ta faɗa tana taɓe baki alamar dai abin bai dameta ba.

Ohooo akan film ake wannan tada jijiyon Neck haka ashe, Zaynerb ta maimaita kamar irin tun farko bata fahimci abin ba.
"E` wai Haka matashiyar budurwar ta kuma bata amsa still Baki a kyaɓe dama gashinan kamar na hmm umm a gurin😇

"Yawwa Aunty Zaynerb raba garma dan Allah wanne yafi" cewar Ameenah cike zaƙuwa. "E to inaga dai "THE LEGEND OF ZU,"  Yafi kyau saboda ana zuba Love ciki koba haka ba?", Zaynerb ta faɗa tana yiwa Lailah dariya ganin yadda ta ɓata fuska ba'a yabi film ɗin da take supporting ba.

"Ato dama ni na sani wama zai haɗa, Ae kai dama daga ji kasan wanda yafi"  Cewar Ameenah cike da farin ciki  wai ita anyabi film ɗin da take supporting.
A fusace Lailah ta ce "ae shima dai  "TILL THE END OF MOON," ɗin ana zuba soyayyar,"
"Eh dan soyayya anayi amma kuma ana magic ciki, Dan Haka ni nafi supporting "THE LEGEND OF ZU!, Ameenah ta faɗa lokacin da take ɗaukar handbag ɗinta tana gyara tsayuwa.

"Ah badai tafiya zakuyi ba dan Allah," cewar Lailah, eh tafiya zamuyi Ameenah ta bata amsa, ita ma ɗayar budurwar da suke tare da Ameena ɗin miƙewa tayi tana faɗin "To sai wataran kuma Ƙyawawan Ahalin Mister mai ƙyau.
miƙewa Lailah tayi dan ta musu rakiya zuwa gurin motar su, sallama sukama su Zaynerb sannan suka fita Lailah na take musu baya suna ɗan taɓa fira suka fita.

Dawo da hankalinta Zaynerb tayi kan Haleesat dake kwance saman three siter da littafin koyon ITALIAN COOK a hannunta tana karantawa dayake Haleesat akwai sun karance karance especially na koyon girki amma badai ka ganta a kitchen ba, ɗan gyaran murya Zaynerb tayi tana gyara zama, Hakan da tayi ne yasa Haleesat kallon ta dan kuwa tasan indai Zaynerb tayi gyaran murya to gulma zatayi, Ganin Haleesat ta maido da hankalinta kanta ne yasa Zaynerb ɗin yin murmushi sannan ta ce "duk kin buɗe jiki gida ya cika da baƙi ke jiki ba suturan kirki ba" ɗan kallon jikin ta Haleesat tayi taga ta inda ta buɗe jikin, Sanye take cikin Riga t-shirt dark green sai wando jeans pencil dogo baki ta ɗaure gefen Rigar da wani bakin gyalle ta gefa Wajen waist ɗinta, sai hula dark green akanta an rubuta benz ajiki saita fito Like a indian actress Krithi_shetty.

"To menene a jikin nawa da yake a buɗe?", Haleesat tambaya dan kuwa ita iya dubawan ta bata ga wani aibun shigar jikinta ba, Lailah ce da shigowar ta yanzu kenan ta ca fe canzen da faɗin  "a'a kidai duba ki gani ke baki ji alamar ana kallon ki ba tun ɗazu?",  "Kallona kuma kamar YaYah kallo na ban fahimta ba" Haleesat ta Tambaya cikin ɗaurewar Kai da shiga confused.

"Eh ina nufin bakiji a jikin ki ana kallon ki ba" Lailah ta faɗa tana zama a two sieter ta ci gaba da faɗin "wannan ƙawar Ameenah ɗin tunda suka shigo idonta yana kanki ke bakiji alama ba?,"
Ɓata fuska Haleesat tayi dan kuwa sai yanzu ta gano abinda su Lailah keson ganar da ita cike da takaicin ƙare mata kallon da aka ce ƙawar Ameenah tayi ta ce "ni ina zan sani naje na saki baki ina karatu ashe ita tananan tana bina dana mujiya,"

Zaynerb tana cire hijjab ɗin dake jikin ta take faɗin "ae shiyasa ma dana shigo ko cire hijjab ɗin jikina banyiba yanzu duniya ta lalace mata ma bin mata suke Allah Yasa mu da ce kawai da ameen su duka suka amsa.

Afeefah da ƙarisowar ta gurin kenan hanunta ɗauke da ɗan tray ciki snacks da drinks ne.
Ajewa tayi a saman Glass center table ɗin dake a palon sannan ta ɗiba snacks ɗin a plate ta zauna a two sieter kusada Lailah tana faɗin  "Jama'a ga Valentine's cooking fah idan akwai mai buƙata tunda dukanku ba mai boyfriend balle ayi mishi."

 Afeefah ta tayi maganar tana kai kallonta ga Zaynerb dan taji mai zata ce, suma dai su Haleesat ɗin kallonta suke dan jin abinda zata faɗa.
Ga mamakin su sai sukaji ta ce, "Eh akwai wanda muka haɗu dashi a social media munyi dashi gobe zaizo mu haɗu karku damu ba zan mishi yadda nake ma sauran ba," Zaynerb tayi maganar tana miƙewa ta zuba  lemon abarba da kwakwa ɗin da Afeefah ta haɗa cikin mug sannan ta zauna tana shan juice ɗin.

Haleesat da maganar Zaynerb na saurayi ya bata mamaki ta buɗi baki ta ce "Saurayi kuma Zaynerb kodai wasa kike?,"

Zaynerb da dama can da biyu tayi maganar tai murmushi kana ta ce "a'a da gaske ne gobe ma zaizo idan Allah ya kaimu zaku ganshi."
"Allah ya kaimu cewar Lailah da ta ɗauki remote control tana canza tasha zuwa korean drama [NO TURNING BACK ROMANCE].

A haka suka ci gaba da fira sama sama wanda yawanci Zaynerb ce mai janyosu da firan Yayinda da take ƙarewa Haleesat kallo tana nazarin ta da karantarta har can wajen shida na marece Momy Rafi'at ta dawo daga HOSPITAL dayake likitace babba ma dan kuwa har hospital gareta na Ƙashin kanta. {Mrs Mai ƙyau Pediatric Hospital}.

WANNAN KENAN

**

🅰🆁🅾🆄🅽🅳 9:20🅿🅼

Da dare Afeefah fitowar ta daga wanka kenan ta tsaya gaban dress mirror tana busar da doguwar sumar kanta da hand Drier saida ta busar da shi sannan ta nufi cloth set shiri tayi tsaf cikin kayan bacci riga fara mai taushi sai wando shima fari dogo kana ta ɗauki ribbons ta tufke gashin ta daya zubo mata har gadon baya, hula ta sa fara dayake ita ba ma'a bociyar sa kallabi bane, Saman doguwar softened stool ta zauna sannan ta ɗauki wayarta tana karanta Wani £nglish Novel.

Lailah ce ta shigo bedroom ɗin tana jan tsaki saman doguwar softened stool ta hangota a kwance ga waya a hannunta sai faman murmushi take ƙarisawa tayi ta zauna kusada ita.

Afeefah tana riƙe da waya tana zuba murmushi taji an wabce wayar, a firgice ta dubi Lailah dake sakin huci, malama bani wayata Lailah bata kulata ba ta koma ta zauna saman softened stool ɗin gefe tana dafe kanta.

Ganin haka yasa Afeefah tashi zaune tana kallon Lailah "what's wrong with you?", Afeefah ta tambaya Lailah lokacin da takai hannu goshinta da wuyanta tana so taji ko batajin daɗi ne Lailah bata kulata ba still.

Ganin haka yasa Afeefah ɗin dawowa kusa da ita ta zauna a ƙasa tana kallon ta a hankali ta kira sunan ta "Lailah!"

Kamar ba za ta kulata ba sai kuma a hankali Lailah ta ɗago tana kallon Afeefah amma har lokacin bata ce komai ba, cikin muryar kwantar da hankali Afeefah ta ce "Lailah pleased faɗamin meke damunki please Lailah tawa, Ajiyar zuciya Lailah ta sauke kana a hankali ganin yadda Afeefah duk tabi ta shiga damuwa da halin da take ciki.
Ckin murya mai sanyi kamar ba Lailah da Afeefah ta sani ba ta ce.
"ina cikin damuwa....
"Damuwa kuma?", Afeefah ta tambaya da sauri, girgiza kai Lailah tayi sannan ta ci gaba da cewa "ina cikin damuwa sosai, wallahi sister na rasa ya zanyi...
Shiru Afeefah tayi tana kallon ta ganin haka yasa Lailah ci gaba da faɗin "ina cikin damuwa guda biyu na farko akan family na kinga YaYa Maleek har yanzu ba'a san duniyar da yake ba gashi Daddy yaƙi sawa a nemo shi tunda ya bar gida har takai ta kawo ko maganar shi Daddy bayaso ayi mishi ga matsalar xixi ya kunno kai ta nace saita dawo gida gashi nayi nayi ta faɗamin abinda ke damunta taƙi ga shi ɗazu ɗazunnan munyi waya da Aunty Nailah faɗamin take wai zata dawo gida cuz sunyi rigima da mijinta, kuka fa ta kirani tanayi, A lokacin saina koma kamar ni ce YaYar ita kuma ƙanwar da kyar nasamu ta haƙura amma ta ce saita dawo gida gashi kinsan halin Daddy ba barinta zayyi ba tunda ga yadda tun farko yanayin auren nata ya kasance dama Daddy ba wani son auren yayi ba kin sani, ita kuma Aunty Nainarh munyi waya ita ma dai ba daɗi abin, wai dangin miji sun saka ta a gaba da maganar rashin haihuwa gashi ita kuma Momy ce matsalar Dan tun farko bata amince da Auren Aunty Nainarh ba, Toh kinji dai...
Lailah ta ƙarishe maganar tana mai jan dogon numfashi.
Tunda ta fara maganar Afeefah bata dakatar da ita ba saida taji tayi shiru.

Ajiyar zuciya Afeefah ta sauke tana kallon Lailah kallon mamaki dan kuwa gani take kamar wannan Lailah dake zaune a gabanta ba Lailah da ta sani bane, Lailah dai mace mai son kanta wacca bata damu da damuwar kowa ba sai nata kuma ba ruwanta da sha'anin kowa sai nata, Lailah da ake mata Kallon Haughty lady, Amma yau gata a gabanta tana faɗa mata damuwar wasu,Lallai.

Da wani ne ya faɗa mata wai cewa koda nan gaba ne Lailah zata damu da damuwar wani, ba zata yadda ba amma yau gashi taji kuma ta gani Lailah ce a gabanta tana koro mata damuwar wasu, Yaran Momy Rafi'at shida ne Abdulmaleek ne Babba, Sai masu bi mishi Nainarh nd Nailah twins ne, Sai kuma Haleesat wacca rana ɗaya aka haifesu da Zaynerb, Haleesat da safe ita kuma Zaynerb da Yamma aka haifeta sai kuma Lailah mai bima Haleesat, Sai Zinaru Auta sakamakon taci sunan kakar su ne mahaifiyar Momy Rafi'at Yasa ake ce mata xixi Yaran Momy Rafi'at Ba wasu shekaru masu Yawane a tsakanin su ba Haleesat da Lailah shekara biyu ne a tsakanin su, suma sauran Yaran duk shekara biyu biyu ne a tsakanin su kuma ko wanne halin sa ya banbanta, especially ma Lailah da halinta yafi banbanta dana sauran Yayyinta ana cewa halin Momy Rafi'at tayo a wasu lokutan.

Ganin kamar Afeefah ta shiga duniyar tunani ne yasa Lailah ɗan tafa hannu a fuskar Afeefah ɗin, "Hey my friend menene kina jina ma kuwa?,"  Lailah ta faɗa tana kallon yadda Afeefah ta zuba mata ido tana kallon ta.
Firgigit Afeefah ta dawo hayyacin ta daga duniyar tunanin da ta faɗa ajiyar zuciya ta kuma saukewa a karo na biyu tana kallon Lailah sannan ta ce "indai akan wannan ne kika shiga damuwa ki kwantar da hankalin ki, Domin zanyi ma Daddy maganar da na tabbatar da zai fahimce ni akan su Aunty Nainarh harma da YaYa maleek ɗin insha Allah zai fahimta kuma zaisa a nemo YaYa maleek ɗin a duk inda ya shiga, Kinga saiki saki ranki ko saiki faɗamin damuwar naki na biyu muji ko zan iya yi miki solving ɗinta,"  Afeefah ta ƙarishe maganar tana murmushi.

Ita ma Lailah ɗan murmushin tayi tana kallon Afeefah ƙaunar ƴar uwan na ta na ƙara shiganta, "A'a shi wannan ba wani matsala bane sosai kawai dai Uncle Al'ameen ne ya takura min da maganar soyayya kuma ni kinsan tsarina ba soyayya a tafiya ta, Dariya Afeefah tayi "kina bani mamaki Lailah wani lokacin saiki ce wai ba soyayya a tsarin ki to haka zaki dogara ba aure ina tausayin ki duk ranar da soyayya ta shige ki ba zata miki shigan sauƙi ba Allah, Kuma da kike maganar Uncle Al'ameen ae naga ya daɗe yana ƙaunar ki kawai ki bada kai musha biki sister, Afeefah ta ƙarishe maganar tana dariyar shaqiyanci ganin yadda Lailah ta haɗe rai.

"Ke sis feefah bana son wulaƙanci fah, kisani ae idan ma maganar gaskiya za'a bi kece zaki fito da miji musha bikin tunda naga kullum sai an miki layi wajen zuwa fira,"  Tamke fuska Afeefah tayi ta ce "amma dai kinsan aure lokacin ne ko zan fito da miji soon amma sai buri na cika dan kuwa ae amfanin soyayya aure,"  Murmushi Lailah tayi dan kuwa tasan babban burin Afeefah shine zama SARAUNIYAR KYAU👰👸

"Sha re wannan topic ɗin kinji ga wani Special Dress fa na samo amma naga alamar nuna tsiraici zayyi yawa ciki amma duba ki gani", Afeefah ce mai maganar tana nunawa Lailah Dress ɗin da ta yi searching  a wayarta, Karɓa Lailah tayi tana faɗin "Okay sis let me it, Sannan ma ana bedroom ɗin zan kwana".
Baki da damuwa madam Lailah Mai ƙyau, Cewar Afeefah cikin murmushi.
Murmushi Lailah tayi ita ma haka suka ci gaba da fira har can Afeefah ta ce bacci take ji sannan  ta kwanta, Saida Afeefah ta ɗan daɗe da kwanciya da alama ma bacci yayi gaba da ita, sannan ita ma Lailah ta kwanta tana ɗan murmushi a zuciyar ta furta ina ƙaunarki ƴar uwata duk da cewa ba ciki ɗaya muka fito ba amma muɗin JINI ƊAYA NE tunda dai mahaifin mu ɗaya, addu'a tayi ta shafe jikinta sannan ita ma sarkin ɓarayi yayi gaba da ita

🅷🅰🅻🅴🅴🆂🅰🆃♥︎🅼🅰🅸♥︎🅺🆈🅰🆄

Misalin ƙarfe goma sha ɗaya da rabi na dare ta shirya tsaf cikin wasu ƴan iskan kaya doguwar riga maroon color mai hannu ɗaya anyima rigar tsagu tun daga cinya zuwa ƙasa, sannan ta ɗauki takalmi heel mai tsini shima maroon color tasa ta ɗaure igiyoyin jiki, Ga gashin kannan nata ya sha gyara  in Braid style, Ɗaukar dogon hijab har ƙasa fari tayi tasa da niƙab sannan ta ɗauki jakarta ta fito, A hankali take sanɗa saɗab saɗab saida ta tabbatar da ba kowa a palon sannan cikin sauri ta nufi kitchen ta buɗe ta ƙofar kitchen ta fita sannan tabi ta garden ko tsoron dare bata yi tabi ta ƙofar dake garden ɗin wacca aka mata ado da wasu flowers masu shaining a qawace ta fita.

A hankali Momy Rafi'at wacca akan idanunta Haleesat tayi duka abinda tayi tun daga kan fitowarta daga bedroom ɗinta bin da tayi ta ƙofar kitchen fitarta ta garden, duka abinda ya faru ta gani daga tsayen da take, Zuge curtain ɗin window ɗin tayi sannan ta koma ta zauna a saman Royal bed ɗinta na alfarma, Wayarta ta ɗauko ta kira lambar Haleesat amma a kashe, Murmushi tayi tana gyara zaman ta saman Royal bed ɗin, Still tana kuma sakin murmushi mai ɗauke da ma'anoni kala kala.
Kwanciya tayi abinta kamar ba uwan da taga ɗiyarta ta fita ba cikin dare baccinta tayi hankalinta kwance..............{ Ikon Allah sai kallo 🏃🏃}

🆉🅰🆈🅽🅴🆁🅱♥︎🅼🅰🅸♥︎🅺🆈🅰🆄

Tana so tasha whiskey ko kwalba ɗaya ne amma kuma tana tuna alƙawarin da tayi ma Afeefah na bazata ƙara shan wani abu daya danganci maye ba, Wanda wannan dalilin ne yasa ta  tashi ta ɗauro alwala a Bathroom, nafila tayi raka'a huɗu sannan tayi sallama Al qur'ani mai girma ta ɗauko tayi tilawa sannan Batareda ta cire hijjab ɗin dake jikin ta ba.
Ta tsaya gaban window tana shaƙar fresh air, Kamar da wasa ta hango mutum yana sanɗa ya nufi hanyar garden.
Tuni ta fahimci ko wacece Haleesat ce domin kuwa two months da suka gabata ta fahimci Haleesat tana satar hanya tana fita da dare, Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta koma ta zauna saman bed tana mai yima Haleesat addu'ar shiryuwa a ƙasan ranta don banda wannan ba abinda zata iya mata.

Ita kuwa Haleesat tana fita ta nufi wata Jar mota ƙirar BMW dake a pake acan gefe, shiga tayi cikin motar ƴan mata ne aciki su uku biyu a gaban mota, Ɗaya a baya duk da Haleesat suka zama su huɗu.

Cire dogon hijab ɗin dake jikin ta tayi tare da Niƙab ɗin tana faɗin, "Oh God zufa huh", Budurwar dake kusa da ita tayi dariya tana faɗin "Baby leesat yau fa kin ɓata mana lokaci wannan tsayawa ɓadda kaman da kikayi".
"Ke dai rabu dani kawai, Kinji ki Zuree babe yanzu ma da ƙyar na fito, Samu nayi ba kowa a palo ma shiyasa kuka ganni, Cewar Haleesat lokacin aka tayar da motar suka bar gurin suna taɓa fira da budurwar da ta kira da Zuree babe da kuma sauran ƴan matan biyu dake gaban motar Feenah da kuma ɗayar budurwar Jenny.

𝔻𝔸𝔾𝔸 𝔸𝕃Ƙ𝕃𝔸𝕄𝕀ℕ✍️ 𝕋ℍ𝔼♥︎ℕ𝔸𝕀ℕ𝔸ℝℍ♥︎𝕂𝔻📲

Isarsu Night club ɗin suka fito a tare, Haleesat ce a tsakiya hannunta riƙe da hannun Zuree sai kuma Feenah ita ma hannunta riƙe da hannun Jenny shiga ciki sukayi, wa'iya zubilla ƴan mata ne kawai ciki kamar yaran arna ba wata suturar kirki bane a jikin su, abin dai ba ƙyan gani ga samari nan iri iri kuma abin da zai kuma ba mutum ta kaishi da mamaki shine zallah gurin Yaran Hausawa ne birjiq😭

Shigarsu wajen keda wuya, nanfa kiɗa ya canza manyan Yaran sun iso nan wajen ya ɗauki sowa da tafi faɗi, Suke ga manyan Yaran masu ji da lokaci sun iso ae dole a basu guri, don masu guri sun ƙariso, haka suke ta faɗi Cikin Yanayi irinna su.

Kujeru masu arnen kyau suka zauna akai Haleesat tare Zuree a kujera mai mazaunin mutum biyu sai Feenah tare da Jenny a ɗayar kujerar ita ma mai mazaunin mutum biyu sai fasa musu kai ake da yabo su kuma suna ƙarajin ba kamar ya su lokacin sune bawai bane😎

Wani ƙayatacen Tray na glass mai ɗauke da whiskey kala kala ma'aikacin gurin ya kawo ya aje saman glass table ɗin dake a gaban su sannan ya koma ya kawo wani tray ɗin kuma daban mai ɗauke da glass cups na zinare ya aje, Sannan cikin nutsuwa yake zuba musu whiskey ɗin acikin cups ɗin Haleesat ya fara miƙa ma dan kuwa ita ce jigon abun mahaifin ta yafi mahaifin su Zuree kuɗi nesa ba kusa ba shiyasa suke girmama ta ba kaɗan kaɗan ba shiyasa ta zama kamar ita ce shugaban su sai abin da ta faɗa ake bi.

Wani irin tsawa Haleesat ta bugawa ma'aikacin wanda yasa saida ya kusa zubar da whiskey ɗin dake hannun shi tsaban firgita da tsoro.
"Bala'i amma Kai wani kalan bagi dajen mutum ne ka taɓa ganin nasha whiskey a gurin nan, Ko shashancine da rashin kulawa yasa zaka bani whiskey saboda ka mayar dani nonsense wacca batasan abinda take yi ba.
Cike da masifa da kuma gadara Haleesat take maganar tana girgiza ƙafa, Game da sakin huci dan ƙiris ya rage ta kai mishi mari...
Gabaɗaya hankulan wasu daga cikin maza da mata na gurinne ya dawo kansu domin ganin abinda ke faruwa.

Shi ko ma'aikacin mai suna Vinood sai faman bata hakuri yakeyi duk yabi ya haɗa uban zufa jikin shi sai faman rawa yakeyi tsoron shi ɗaya shine karya ya rasa aikin shi a gurin.

Ganin Haka yasa Feenah wacca duk cikin su tafisu sanyin hali kuma bata cika san hayaniya ba, Alama tayiwa ma'aikacin daya tafi ya bar gurin, da sauri kuwa ya bar gurin har yana tuntuɓe.

Kamo hannun Haleesat Feenah tayi tana faɗin "please baby leesat ki kwantar da hankalin ki yanzu zai kawo miki abin da kike buƙata kinji?",  Feenah ta faɗa hakan ne saboda tasan Haleesat bata shan whiskey ko kuma Wani Abu daya danganci kayan maye...Tafi ganewa ta busha shisha ko wani abun, Amma bata shan kayan ruwa ma'ana abin da ya danganci maye.
Ajiyar heart Haleesat ta sauke sannan ta ce "ba damuwa kawai dai ya ɓata min raine amma ba komai "forget about the pass".
Murmushi Feenah tayi "shiyasa nake son ki ta waje na akwai ki sauƙin hali", Feenah ta faɗa tana komawa ta zauna.
Feenah ƴace ga Alhaji Sulemanu  canji, shahararren ɗan canji ne a garin Abuja da kewaye, Yana da kuɗi obaa highly dan kuwa bayan harkar canji da yakeyi ɗan kasuwa ne shi na bugawa a jarida, Feenah itace ƴar shi ta biyar mahaifiyar ta ta rasu tun tana da shekaru sha biyu a duniya a gurin kishiyar uwanta take.

Yayinda Zuree take ƴa ga malam Adamu jama'are mahaifin ta shahararren malami ne a garin Abuja asalin shi ɗan garin jama'a re ne na jahar Bauchi, Kasuwanci ne da kuma malimta ya dawo dashi garin abuja har ya gina family ɗinshi anan yaran shi tara,  Zuwairiya wato Zuree ita ce ta fita zakka a yaran malam Adamu dan kuwa ƴar malam ce wacca taƙi halin malam.

Sai kuma Jennifer lopez, wato Jenny mahaifin ta cikake kuma shahararren mai dukiya ne a garin Abuja sannan kuma pastor ne wanda akeji dashi Jenny ta kasance, Ƴar shi ɗaya tilo tsoka ɗaya a miya shiyasa take abin da taga dama saboda a sangar ce iyayen ta suka raine ta bata san wani abu waishi wahala ba a rayuwa dukansu ajin su ɗaya a University sannan kuma course ɗaya suke karanta wato Microbiology.

Dogon tsaki Zuree taja tana faɗin, "Wallahi Baby Leesat kina Bani mamaki da takaici bansan ranar da zaki waye ba wallahi ke ba shan wannan kayan ruwa ba, Bakya taɓa harkar nan ke gabaɗayanki sai aslow wallahi", Tayi maganar cike da takaici.

Haleesat bata kulata ba da dan kuwa idan da sabo yaci ace ta saba da wannan tsoki burushun na Zuree.
Saima cewa da tayi, "Okay guys kuzo mu motsa Jiki mana,"
Gabaɗaya su ukun tashi sukayi gabaɗayan su suka hau kan dandamali nanfa akayi changing ɗin wakar speakers ɗin CLUB ɗin zuwa wani korean song na zamani, habba nanfa suka fara dancing kamar ba gobe cike da kwarewa suke rawan su abinsu ba ruwansu.

Tsaye take can ɗaga wani ɗan korido na club ɗin, Yayinda take ƙarewa club ɗin kallo dama society ɗin dake ciki.

Pin-up dress ne a jikin ta, Riga black color sai belt golden color da ta kama ƙugunta ta ɗaureshi, Rigar iya gwiwar ta tsaya sannan kuma ta kama ta ɗam, ga wani tsinannen takalmi hill a ƙafafunta kanta kuwa yasha kitson attach mai masifar tsada,  Hannunta na hagu kuwa zanen tattoo ne brown color.
Doguwa ce sosai dan kuwa a shekaru ba za ta haura ashirin da uku zuwa da huɗu ba, Idonta yana sanye cikin wani arnen glass no respect launin eye balls ɗinta kuwa abin burgewa ne ga mai kallon tsakiyarsu launin Blue color suke.

Hannyenta rings na diamond masu masifar kyau da tsada ne,  Ga wata arniyar chain na diamond a neck ɗinta siririya mai kyau da kuma tsada, Ear ɗinta kuwa ba`a magana wasu kalan earings ne a kunnenta na diamond amma kuma Yanayin shape ɗinsu cross ne, Fuskar ta kuwa tasha light make-up launin hair ɗin ta kuwa brown color ne dogo, ta fito sak Like a indian actress RAKUL PREET SINGH fara ce tas fatar ta har wani shaining takeyi saboda haske gashi kuma ya haɗe da jindaɗi Yanayinta tafi kala da mara sa son Hayaniya obaa highly.

Hannu tasa a pocket ɗin rigarta ta ciro wayar ta ƙirar iPhone 14promax daga inda take a tsaye take ɗaukar Haleesat a hoto, Tayi sunkai kala biyar sannan ta turawa wata number wanda akayi saving da MR. AMIGO sannan ta kira lambar cikin sa'a kuwa ringing ɗaya aka ɗauka magana ta fara cikin Harshen
farasanci, "Hello Mr. Amigo ga wasu pics nan na turo maka nan da gobe nakeso a samomin taƙaitaccen tarihin Yarinyar cikin pics ɗin in Tomorrow please."
On the other hand mutumin shima cikin Harshen farasanci ya ce "shikenan madam amma nace!,"
Bata tsaya jin abinda zai kuma cewa ba ta katse wayar ta mayar cikin gown pocket ɗin ta sannan ta fito daga cikin club ɗin gabaɗaya motar ta ƙirar bugatti ta shiga taja motar da gudu ta bar gurin.

A takaice dai su Haleesat basu suka bar club ɗinnan ba sai wuraren ƙarfe biyu da rabi na dare kamar yadda suka saba sauke ta sukayi a gurin da suka ɗauke ta ɗazu har zata fita a motar ta tsaya jin abinda Jenny take faɗa.
"Wai guys baku kula da wata red ɗin mota da take binmu ba tun ɗazu na lura da'ita fah, Tunda muka fito daga club Take binmu."

Ɗan juyawa sukayi a tare suna kallon inda Jenny ke nuna musu motar a daidai lokacin kuma motar dake binsu ƙirar Benz tayi ribas tabar gurin da speed, Tsaki Haleesat taja irin she don't care ɗinan "koma waye ne matsalar shine fa ba wai namu ba" Ta faɗa hakan yayin da take barin gurin bata tsaya jin abunda suke faɗa ba da sauri ta buɗe ƴar ƙaramar ƙofar da take bi ta gurin ta wuce.
Kai idan baka lura ba bama zakace da hanya a gurin ba balle har a sama ƙofar wucewa saboda gurin akwai wasu flowers da suka rufe ƙofar sai suka zama kamar kwalliya.

Cikin sanɗa take taku harta shigo palon gidan sannan in rushing ta wuce bedroom ɗinta.
Zaynerb da har gyangyaɗi ya fara ɗaukar ta, Baiwar Allah ajiyar zuciya ta sauke ganin Haleesat ta dawo cikin ƙoshin lafiya, Miƙewa tayi ta shige bathroom tanajin zuciyar ta ba daɗi, It's Necessary gareta ta sama Haleesat akan wannan satar hanyar da take tana zuwa Night Club, Ba tare da sanin ƴan gida ba.
Bayan wasu mintuna ta fito ɗaure da brown towel a chest ɗinta ko lotion bata tsaya shafawa ba cikin sauri sauri ta shiga cloth set ta shirya cikin sleeping dress riga na saka maroon color doguwa, Saman bed ta hau tayi addu'ar bacci sannan ta lumshe kyawawan idanun ta bayan wani lokaci bacci yayi awon gaba da ita.

Haleesat kuwa tana shiga bedroom ɗinta kai tsaye bathroom ta shige bayan ta cire dogon hijab ɗin dake jikin ta da niƙab da ta qwaqwama.
After some minutes ta fito jikinta sanye cikin bathrobe gaban dress mirror ta tsaya tana ƙara goge sumarta, da ɗan ƙaramin towel ɗin dake hannunta zama tayi akan stool na madubi tana shafa lotion Bayan ta gama busar da gashin kannata saida ta kammala shafa lotion ɗin, Sannan ta miƙe ta shiga cloth set ta shirya cikin pyjamas mai taushi milk color, System ɗinta ta ɗauka ta koma saman mattress ta zauna tana sarrafa system ɗin ta ɗauki lokaci tana amfani da system ɗin sannan ta mayar da system ɗin ma'ajiyar ta, Kana ta koma saman bed ɗin ta kwanta, Pillows ta rungumo a chest ɗinta tana sauke ajiyar zuciya ba batun addu'ar bacci a haka har sarkin masu iya sata yayi gaba da ita.

Can cikin baccinta mai daɗi taji ana tashin ta ana jijjigata ana kiran sunanta.
A hankali take buɗe lumtsatstsun idonta mai cike da bacci, Biji biji ta fara ganin mutum a gabanta kafin idanun ta suka buɗe duka.
 Afeefah ce tsaye a gabanta tana sakin murmushi, riga ce short a jikin ta iya ka gwiwar ta sai dogon wando ga apron blue color da ta ɗaura a saman rigar jikinta, Kanta kuwa hular apron ɗinne shima blue color da alama kitchen zata shiga.

"Aunty Zaynerb"  "Aunty Zaynerb!! ki tashi mana tun ɗazu naketa faman tashin ki, kitchen zamu shiga kinsan yaufa Aunty sa'adah bata ta tafi garinsu,"  Afeefah ce ke maganar tana tashin Zaynerb.

A Hankali ta sauko daga saman mattress ɗin miƙa tayi tana karanto addu'ar tashi daga bacci clock ɗin dake manne a wall na ɗakin takalla ƙarfe bakwai na safe da sauri ta diro daga saman gadon tana faɗin "Yah Allah yaushe lokaci ya tafi haka ban tashi nayi sallah ba,"  Bathroom ta shiga da sauri bayan wani lokaci ta fito ɗaure da towel fari a ƙirjinta dubawa inda tabar Afeefah tayi, Bata da alama ta fita ne, Cikin sauri ta zura doguwar riga, A jikin ta sannan ta saka hijab ta tayar da sallan asuba bayan ta iddar cire hijjab ɗin tayi sannan ta fito kitchen ta Shiga.

A can ta samesu da Lailah suna kici kicin haɗa breakfast.
"Yauwa Aunty Zaynerb please ɗan kira Haleesat tazo muyi mu kammala haɗa breakfast ɗinnan tare", Cewar Afeefah ba tare da kalla Zaynerb ɗin ba.

Fita Zaynerb ɗin tayi ɗakin Haleesat ta shiga bata ciki dubawa bathroom tayi nanma bata,  Fitowa tayi zata koma kitchen ɗin a palo sukayi karo da Haleesat Jogging suit ne a jikin ta da alama daga morning Exercise take.
"Good Haleesat ki shirya Yau dai kitchen za'a shiga dan haka ki shiga ki shirya muna kitchen muna Jiranki, Kinsan dai Yau Aunty sa'adah bata nan kuma su Ummi da Elina Basunan".
Zaynerb ta ƙarishe maganar tana bin ta gefan Haleesat zata wuce, Da sauri Haleesat ta sha gabanta a ɗan hasale ta fara magana "waime? ni Haleesat ni ce zan shiga kitchen ɗin huh to akan wani dalili?".
Murmushi Zaynerb tayi sannan ta ce "akan dalilin da yasa kike cin abinci mana" tayi maganar tana kuma bi ta gefan Haleesat zata wuce, "Yauwa kuma kiyi sauri fa, dan kinsan umarnin shalelen Daddy ne ba'a sanya ko jin kiri, Idan kuma akayi tofa rai yana ɓaci kinsan da wannan.
Tana gama faɗin haka tayi gaba abinta.
Tabar Haleesat da cizon yatsa tsaki taja tana bin Zaynerb ɗin da kallon banza dama can basa ga maciji da Zaynerb ɗin cuz indai zasu zauna guri guda tofa saisun raba hali.
Ɗakinta ta shige dayake ɗakunan nasu a jere suke ɗakin Afeefah ne a farko sai na Lailah sai kuma na Zaynerb dake ɗayan Wall side ɗin sannan sai na Haleesat a ƙarshe.


_(The Glam Queen)_ 👑
       
         ```Takun Farko```

Story & Written By:
                 𝔗𝔥𝔢 𝔑𝔞𝔦𝔫𝔞𝔯𝔥 𝔎𝔡

*Page 13&14*

Zaynerb kuwa tana koma wa kitchen, Guri ta samu ta zauna a ɗaya daga cikin chair's na dinning ɗin dake a kitchen ɗin dayake kitchen ɗin babba ne highly.

Kallon Lailah tayi ta ce "Ke Lailah ba haka ake yanka cabbage ba kinje kinayi manya manya keda zaki yanka ƙana na haba, duh Allah ki dinga kula mana.

A hasale Lailah ta juyo, dama da Yayah Afeefah ta samu ta shigo kitchen ɗin gashi tun ba'ayi nisa ba Zaynerb ta fara kushe ta don jan ayi tsiya, ta ce "dan Allah sister Zaynerb zo ki yanka da kanki mana, Haba ni dama na gaji wallahi," Ta faɗa tana dafe goshi duk tabi ta haɗa uban zufa kamar mai amfani da ita ce.

Dariyar ƙetah Zaynerb Tayi sannan ta ce "a'a ba ruwana ae girki sai dai ku Lailah ni dai barni anan inda nake" Ta faɗa tana latsa tsadaddiyar wayar ta, Lailah zata ƙara magana Afeefah tayi mata inkiya da ido alamar tayi shiru qwafa taja kawai ta ci gaba da yayyanka cabbage ɗin da take cikin nutsuwa da rashin qwarewa a fannin.

Jin shiru Haleesat bata zo ba yasa,  Zaynerb miƙewa tsaye saboda tsaban rigima irinna ta, Ita ba aikin takeyi ba, Amma don neman magana zata je kiran wata, Tana shirin fita daga kitchen ɗin, Saiga Haleesat ta shigo kitchen ɗin sanye cikin riga doguwa da dogon wando jeans.

"Yauwa ɗiyar albarka kin shigo, To ga rigar girki ki sanya ko sister"  Zaynerb ta faɗa tana miƙa mata apron karɓa Haleesat tayi zata ɗaura, Da sauri Zaynerb ta ƙarisa ta bayan Haleesat ɗin ta ɗaure mata igiyar rigar,  "Yauwa sis a fara aiki"  Cewar Zaynerb tana komawa ta zauna.

Ita dai Haleesat bata kula ta ba, Hasali ma earpiece ta maƙala a kunen ta duka biyun, Kama sumu aikin tayi suka ci gaba da fafatawa dama can ita Haleesat gwana ce wajen iya girki kala kala domin har lecture na koyon girki take zuwa kawai dai shiga kitchen ɗinne ba ra'ayinta ba, A haka suka ci gaba da yi Zaynerb na zaune sai dai idan taga sunyi ba daidai ba tasa baki kuma fah kar kuyi tunanin ta iya ne a'a ko ɗaya ba wani girkin azo a gani ta iya ba kawai tonon tsiwa ne irin nata, Daga  ƙarseh ma ɗaukar wayarta tayi tana musu video wai zata ɗaura a Yanar gizo ga ƴaƴan MISTER MAI KYAU guda a kitchen suna girki NEW UPDATE  kenan🤣😂😅.

Lailah ce da surutun Zaynerb ya isheta ta juyo tana kallon Zaynerb ɗin ta ce "sister Zaynerb dan Allah zaki iya fita ki bamu guri keba aiki ba sai surutun tsiya haba,"
Zaynerb bata kulata ba ta ci gaba da nuna ma Haleesat wai yadda ake ɓare Maggi mai star, "ke Haleesat na faɗa miki ba haka ake ɓare Maggi ba kin ƙi ganewa, A haka ae zubewa yakeyi haba sis a dinga kula mana," Zaynerb tayi maganar tana miƙewa bayan tayi saving video ɗin data gama ɗaukarsu, Ƙarisawa tayi gurin Haleesat ta karɓa ɓare maggin, "Yauwa to ɗauka wani aikin bari na tayaki wannan🤔.

Ita dai Afeefah sai daɗi takeji Zaynerb ta fara dawo walwalarta kamar da, Bayan lokaci mai tsayin gaske don shekaru biyar baya da Rayuwarta ta shiga tasko farin ciki yayi ƙaranci ciki kuma ya rushe, Bata irin waɗannan abun, Amma yanzu da takeyi hakan na nufin ta manta komai kenan ta barma Allah zaɓinta?.

Haka suka ci gaba da aikin su Zaynerb nayi musu gyara kamar itace boss.
Cikin ɗan ƙanƙanin lokaci suka kammala haɗa haɗaɗɗen breakfast mai rai da lafiya sannan na Alfarma.
Jerewa sukayi a dinning Room sannan ko wace ta shige haɗaɗɗen bedroom ɗinta domin shiryawa.

Zaynerb tana shiga bedroom ɗin ta bathroom ta shiga takai minti talatin sannan ta fito ɗaure da towel blue color a chest ɗinta, Cikin sauri sauri ta shirya cikin kayan hausawa Atamfa pink mai ratsin fari anyima Atamfar zanen flowers doguwar riga ce mai dogon hannu, Sannan ta kafa ɗaurin ture kaga tsiya kayan sunyi masifar yi mata kyau kamar kamar me, Dama kuma gata mai kyau, Ɗiyar mai kyau, Jikar kyawawa, Feshe Jikin ta tayi da perfumes kala kala masu tsada da sanyin ƙamshi.
Sannan ta fito daga bedroom ɗinta tana baza ƙamshi, dukansu suna zaune a dinning room ɗin suna cin breakfast hadda Daddy MISTER MAI KYAU da Momy Rafi'at, ƙarisawa tayi taja kujera ta zauna tana greetings ɗin Daddy da Momy Rafi'at fuska sake Daddy ya amsa mata gaisuwar har yana tambayar lafiyarta duk da kasancewar lafiyarta ƙalau.
Ita kowa Momy Rafi'at da kyar ta amsa kamar anyi mata dole wai danma taga mijinta MAI KYAU yana gurin ne,  Zaynerb kuwa ko a jikin ta da irin amsa gaisuwar ta da Momy Rafi'at tayi, Murmushi ma tayi dan kuwa ita kaɗai tasan irin tsiyar da ta shirya mata, Jira take taga yadda za'ayi aje china a Yau.

...

Bayan sun kammala cin breakfast ɗin palo suka dawo suka zazzauna dayake yau su Lailah basu da lectures Haleesat ce ma take da lectures ɗin a yau amma sai zuwa ƙarfe uku na Yamma.
Lailah da Haleesat ne a palon sai Afeefah suna jiran Mister mai kyau ne dayake zasu rakashi airport zai wuce  germany a yau.
Yayinda Zaynerb ta koma ɗakinta bayan ta ce tana fama da headache sama sama,  Sai da Zaynerb ta tabbatar da sun fita raka Daddy airport ɗin, Sannan ta fito palon ba kowa dan gabaɗaya Ma`aikatan gidan da masu gyara palon ma sun gama sun koma ɓangaren su, Wanda hakan ba ƙaramin daɗi yayima Zaynerb ba, Don zatafi samun aiwatar da shirinta in carefully.

Upstairs ta hau bedroom ɗin Momy Rafi'at ta nufa kanta tsaye ɗan buɗe ƙofar bedroom ɗin tayi, Ta leƙa kanta a ciki ba kowa shiga tayi dukanta, Ƙaran ruwa taji a toilet da alama wanka takeyi dube dube ta fara a ɗakin amma bata ga komai ba jin alamar an taɓa ƙofar toilet ɗin za'a fito ne yasa ta fita da sauri daga ɗakin.

Kitchen dayake anan Up ɗin ta shiga da sauri sauri bayan wani lokaci ta fito hannun ta ɗauke da robar mai.
A bakin ƙofar ɗakin Momy Rafi'at ta tsaya, Aje robar man tayi a gefe sannan ta ɗauko mopper ta aje a gefe shima,  wannan robar man data fara ajewa, ta ɗauko ta juye shi tas a ƙofar ɗakin momyn sannan ta ɗauko moppern ta fara gogewa ta yanda ba za'aga alamar mai ba a gurin ba.
Cikin sauri sauri take aikin don bata buƙatar Momy Rafi'at ta fito ta sameta gurin, Saida ta kammala tas sannan ta mayar da moppern ma'ajiyar ta, roban man ma ta mayar kitchen da sauri sauri ta koma bedroom ɗinta.

AFTER SOME MINUTES

Jin Ƙarar shigowar motar su Afeefah da alama dai har sun dawo daga airport ɗinne.

Palo suka zauna suna ɗan taɓa fira ita ma Zaynerb ɗin ta sauko Down ta dawo palon ta kwanta a saman three sieter tana dafe kanta kamar ciyon kan gaskiya su Afeefah sai sannu suke mata cike da tausayi dan kuwa suna ƙaunar junan su highly.
Haleesat ce ta kalli Zaynerb cike da kulawa ta ce "ki shiga medical room mana ki ɗauki magani kinji sis,"  
Ƙasa ƙasa Zaynerb take kallon Haleesat ɗin sannan ta maƙale murya ta ce "karki damu sister nasha fa", T a faɗa da kyar kamar mai ciwon baki, Lailah ta ɗan yi murmushi ta ce "Lallai su Aunty Zaynerb an buɗe file kenan baki ya mutu kamar ba kece mai surutu game da ɗaukar video ɗazu ba,"
Zaynerb bata kulata ba don tafi kowa sanin halin Laila da tsokanar ta, "Sannu kinji sister" cewar Afeefah tana taɓa goshin Zaynerb ɗin taji koda zafi, "Yauwa ƙanwata"  Zaynerb ta amsa tana lumshe ido.

𝔐ℜ𝔖_𝔐𝔄ℑ_𝔎𝔜𝔄𝔘

Momy Rafi'at ta gama shirinta tsab na zuwa china da mummunar ƙuduri ta shirya tsab cikin expensive material fari tas da mayafi mai tsada, Ga jakarta shima fari tas ta fito sai baza ƙamshi takeyi, Tafiya takeyi bata kallon gabanta sauri take don saura mintuna goma jirgin su ya tashi ita bata masan ya akayi ta ɓata lokaci haka bata shirya ba.
Cikin tafiyarta batasan ya akayi ba haka zalika bata lura da mai ta taka ba, Sai dai kawai taji wani uban zamiya game da zantsi ya kwashe ta, Aikuwa sai dai tim tittim tim akeji ta faɗi saman tiles, Bata dandara ba ta miƙe da kyar tana dafe ƙuƙurunta saboda wani uban azaba da takeji aikuwa miƙewan data kuma yi santsi ya kuma ɗibarta fiye da farko, Saiga Momy Rafi'at tana faɗowa daga saman staircases gabaɗaya bata dena juyi ba saida tayo kasa tun daga saman bene saida ta dangana da ƙasa.

Da gudu su Haleesat sukayo kanta suna kiran sunan ta amma ina Momy Rafi'at tayi sumar wucin gadi, Dan kuwa ba ƙaramin buguwa tayi ba, Ƙunƙurunta da bayan ta dama sauran jikin ta sai faman kiran sunanta suke cikin tashin hankali,  Amma ina Momy Rafi'at bata ma jinsu dan a sume take.
Dq sauri Lailah ta ɗauko ruwa a fridge ta yayyafa mata shiru bata farfaɗo ba,  Haleesat hadda kukanta ganin haka yasa Afeefah ƙara yayyafa mata ruwan sai gashi ta farfaɗo tana ihu tana faɗin bayan ta zai ɓalle jikinta ciwo maganar take kamar bata hayyacinta.
Ganin ta kasa tashi yasa Afeefah ta kalli Lailah "Sister mu kaita hospital kawai zaifi, don na fahimci ba ƙaramin buguwa tayi ba,"  Cewar Afeefah tana kuma kallon yadda Momy Rafi'at take ihu kamar wata karamar yarinya, Da sauri suka taru su ukun banda Zaynerb wacca take kwance a three sieter tana baccin ƙarya, Da kyar suka iya cicci ɓarta suka nufa waje da ita a mota suka sakata sai faman haki suke, Ko tsayawa jiran driver da escort basuyi ba, Afeefah ce taja motar da gudu suka bar gidan zuwa hospital dan ma sunsa mayafan su tun kafin su fito.

Zaynerb kuwa tana tabbatar da sun bar gidan ta fashe da dariya hadda riƙe ciki, A fili ta furta Allah ya ƙara Yasin banji tausayinta ba, Don bata da imani wannan matar har kisan kai zata iya yi tama yi bama zata iya ba, Tsaki taja tana tuna yadda tasha azaba a hannun Momy Rafi'at kafin abin ƙaunar su mahaifin su MISTER MAI KYAU ya ɗaukesu ya mayar dasu Germany.

Zama tayi tana tuna wani lokaci shekaru GOMA SHA ƊAYA baya da Momy Rafi'at take dukan Afeefah, Zaynerb tana kuka tana roƙonta ta dena duka mata ƴar uwanta amma Momy Rafi'at taƙi ji tohm ana cikin haka saiga Daddy yayi dawowar bazata yayi kyakyawar gani kuwa Momy Rafi'at tana dukan shalelen shi da wayar wuta aikuwa a lokacin saida ya saki Momy Rafi'at, Sannan ya ƙwace Yaran shi duka amma banda su Lailah ya bar ƙasar dasu a lokacin sai da kyar aka samu ya mayar da Momy Rafi'at.

Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta tashi ta hau Up da sauri sauri ta goge duk gurin da ta tabbatar tasa mai sannan ta dawo palo tayi kwanciyar ta abinta.

Koda su Afeefah suka isa asibiti an duba Momy Rafi'at an tabbatar da ta samu goje war ƙashi da wasu gurare a jikin ta da ta sama karaya basu suka baro asibitin ba sai wajen ƙarfe biyu, Gida suka dawo da ita tayi jinyar anan don ita ta zaɓa hakan, Nanfa ƴan uwa da abokan arziki da suke a kusa suka fara zuwa duba jikin ta, Gashi daddy baya ƙasar dole sai Afeefah ce ta kira shi a waya a faɗa mishi Halin da ake ciki.

*°°*

Kwance take saman royal bed ɗin ta, Daga ita sai riga shirt na bacci pink color sai wando short shima pink color.
A hankali ɗan bakinta yake motsawa da alama mafarki takeyi murmushi ta saki ta kuma gyara kwanciyar ta kafin wani lokaci kuma ta buɗe kyawawan idanun ta.
Saukowa tayi daga zaman bed ɗin toilet ta nufa, Tun kafin ta ƙarisa shiga toilet ɗin ta cire short ɗin jikin ta tayi jifa da dashi ita ma rigar cireta tayi, ita ma tayi wurgi da ita gabaɗaya gashin kanta mai uban yawa da tsayi ya rufe mata fuskar ta ya warwatse,  Toilet ɗin ta shiga takai minti arba'in ciki.

A hankali ta turo ƙofar toilet ɗin ta fito chest ɗinta ɗaure da towel White color, Da sauri ta ƙarisa gurin expensive wayarta dake kawo wuta, Alamar kira ne ya shigo, Ganin mai kiran nata yasa saida ta fara zauna saman mattress, Sannan tayi picking call ɗin ta kara a kunen ta, Daga cikin wayar mai kiran ya fara magana cikin harshen hausa.

"Hello  Madam ansamo brief history na Yarinyar hotunan nan kamar yadda kika nema, Sunanta "Haleesat Abubakar Mai Kyau! Shekarunta Ashrin da uku a duniya, Ita ce ƴa ta hudu a gurin mahaifin su Alhaji Abubakar mai kyau wato dai {Mister mai kyau} wata gila zaki sanshi saboda shi ba ɓoyayyen mutum bane a ƙasar nan, Dama duniya baki ɗaya, Sannan kakanta shine mamallakin wannan shahararren company na magani wato S.L pharmaceutical industry!,"

Ɗan lumshe idanun ta tayi tana jinshi ya civgaba da cewa "tana karantar micro biology anan American University dake a nan Abuja, Sanin da yayi ba sosai take fahimtar hausa ba, Yasa ya ɗanyi full stop da maganar nashi sannan ya ci gaba da cewa.

"Ƙawayenta huɗu ne kacal, Feenah, Zuree, Sai Jennifer, Sai kuma wata da ake kira da Maryam ita ɗin Irregular Friend ɗinta ne.

A halayya kuma ta kasan mace mara son surutu sosai kamar dai ke madam, Ya faɗa cike da zolaya, Ɗan murmushi tayi a gajarce "uhumm"  Ina jinka tayi maganar tana kuma gyara zaman wayarta a kunen ta.
Magana ya ci gaba, Sannan kuma bata shan kayan maye sai dai kuma tana busa shisha da sauran su, Amma banda sigari, kana bata kula maza dan zan iya ce miki ma bata da saurayi ko ɗaya, Nan dai ya ci gaba da kwararo mata bayani akan Haleesat yadda zata fahimta da kyau.
Mayar da expensive wayar tayi saman mattress bayan sun kammala wayan ta aje.

Cikin nutsuwa take shirinta tsab ta shirya cikin business suit pink color, Sannan ta ɗauki space pink color shima tasa, Kana ta ɗauki shoes glitter stilettos shima pink color tasa, Hair ɗinta kuwa ta gyara shi in straight style, Hular ta mai wani kalar style da kuma qwal biyu ta saka, Wanda hakan yaba dogon gashin kanta mai tsayi da santsi ga yawa damar fituwa ya sauka a gadon bayanta sannan ta ɗauki coat ɗinta pink wanda aka qawata gaban ta da wasu buttons Golden color masu shaining komai pink color, Tayi kyau highly highly harta gaji kyau gata kamar a wanke hannu a taɓa.

Fitowa tayi harabar hotel ɗin data ke, Zata shiga motar ta ƙirar BMW pink color kenan taji ankira sunanta a bazata.

"ⒽⒺⒶⓇⓉ_ⒸⒽⒺⓃⒼ_ⒿⓊⓃⒼ!!

Fasa shiga motar tayi, A hankali ta juyo domin ganin mai kiran nata, Ɗan waro ido tayi da tsananin mamaki ɗauke saman kyakyawar fuskar ta, Na ganin wacca take a gabanta, Sam  bata manta ta ba duk da cewa sun ɗauki shekaru masu ɗan yawa basu haɗu ba.
"Harper David" ce classmate ɗinta da sukayi karatu tare a ƙasar "MALAYSIA" da sauri Harper ta ƙariso gurin ta, "HEART kece kuwa kodai idanuwa nane basa gani da kyau" Ta faɗa tana murza eye ɗinta dan tabbatar da wacca take gabanta.
Sannan kuma duk cikin turanci take mata maganar. Murmushi "HEART" tayi ta ce "ni ce mana,"
"Ohoo to me ya kawo ki Nijeriya nidai nasan baki da wata connection da ƙasar" Cewar Harper, "Business mana" Heart ta bata amsa cikin Hausa, Wannan karon ƙara waro ƙanan idanun ta Harper tayi "oh gosh Ashe har Hausa kike ji?,

"E' mana highly highly ma,  Ae ko wata bahaushiyar bata faɗamin Hausa ba"  Heart tayi maganar da hausa a bakinta raɗau.
"Harper David ke to meya kawo ki Naija tunda dai kema nasan baki da wata alaqa da ƙasar."

"Yawon buɗe ido mana,"  Zaro ido HEART tayi cike da mamakin Jin abinda Harper ta faɗa mata "yawon buɗe ido kuma?,"
"E' mana Harper ta bata amsa, "Yanzu dai ba wannan ba, Sauri nakeyi Anyway ga Room card ɗina kawai," HEART tayi maganar tana miƙawa Harper card, Karɓa Harper tayi ta ce. "Okay ni ma dai yanzu akwai gurin da zani dama".
"Okay to shiga motata na rage miki magana mana HEART ta ce ma Harper.

"Ok let's go" cewar Harper shiga motar sukayi suka bar hotel ɗin suna taɓa fira.

[Menene asalin su Afeefah, shin wata kalar ƙiyayya ce a tsakanin Momy Rafi'at da mahaifiyar su Afeefah ne, wacca bata ma a duniyar. Wacece "HEART" wacece Harper ga Jieddarh a gefe duk amsosin waɗannan tambayoyin suna a cikin wannan ƙayataccen Labarin mai suna SARAUNIYAR KYAU]💋👰💋

🅜🅐🅛🅛🅐🅚🅘🅝

🄺🄷🄰🄳🄴🄴🄹🄰🅁🅃🄷
ⓉⒽⒺ ⓃⒶⒾⓃⒶⓇⒽ ⓀⒹ}

         
🅺🅰🅽🅾

Zaune suke a dinning room suna lunch, Yayinda ƴan aikin gidan ke jere musu lafiyayun Abincicika kala kala masu rai da lafiya wasu kuma na aikin serving ɗinsu cikin nutsuwa, dukansu ƴan gidan ne suke a dinning ɗin, Jieddarh, Humaira sai Heesham da Auntie sai kuma Abba wato Alhaji Jafar Komai Naka.
Dayake dinning table ɗin mai mazaunin mutum takwas ne, cikin nutsuwa suke yin lunch ɗin abinsu.

Bilkisu ce ƴar aikin su budurwa mai kimanin shekaru sha tara ta ƙariso da saurinta har ta kusa faɗi saboda sauri gurin Heesham ta ƙarisa cikin rawan jiki take serving ɗinshi yayinda ta kafeshi da ido kamar zata cinyeshi ɗanye saboda so da ƙauna, Shi kuwa baima kula da irin kallon da take mishi ba gabaɗaya yafi mayar da hankalin shi wajen kaima cikin shi haƙƙin da.
Ganin ta gama serving ɗinshi amma bata bar gurin ba yasa shi dakatawa da cin abinci da yakeyi ya ɗago da kanshi yana kallon ta.
Ae bilkisu sai da ta kusa sumewa ganin yau ta ciri tuta ya kalleta, "malama baki gama bane ko dai kina jiran wani abinne?,"
Ya tambaye ta cikin tsare gida da ɗan faɗa ganin yadda ta ƙureshi da ido, Da sauri ta ce "na gama oga,"  gurin Jieddarh ta ƙarisa tana serving ɗinta amma gabaɗaya hankalinta yana kan Heesham wanda shi baimasan tanayi ba.

Kaf gurin ba wanda ya kula da irin kallon da take mishi sai Jieddarh cikin zuciyar ta ta ce " Wow kaga wani kalan love aikuwa sun dace da juna ,Allah ta biyo ta hannuna zan taimaka mata", Ganin yadda Bilkisu ta wani ƙurawa Heesham ido kamar yau ta fara kallon shi dama ta lura da take taken Bilkisu kwana biyu akan YaYannata Heesham tunda ya dawo daga karatu ta ganshi gabaɗaya bata cikin nutsuwar ta.
Ɗan gyaran murya jieddarh tayi sannan ta kalli Bilkisu ta ce "please  Bilkisu ɗan ɗaukomin maltina mai sanyi a fridge mana,"  Kallon Jieddarh Bilkisu tayi kawai saboda, ta katse mata jindaɗinta shine zata wani ce, Ta ɗauko mata maltina mai sanyi a  fridge bayan ga wasu drinks ɗin a gabanta daɗin daɗawa kuma ae tafi ta kusa da fridge ɗin.
Tana ƙunƙuni taje ta buɗe fridge ɗin ta ɗauko mata, "gashi" ta miƙa mata ba tare da ta buɗe mata ba, "Ɗan buɗe min mana" jieddarh ta faɗa tana kallon yadda Bilkisu ta ɓata fuska ga Heesham ya kusa barin gurin bata gama ƙare mishi kallo san ranta ba😂.

"Buɗe mata mana Bilki ko ba ƙyaji ne" Cewar Auntie ganin yadda Bilkisu ta zuba ma jieddarh ido tana kallon ta kamar bata fahimci mai take nufi ba.

Da sauri ta buɗe miƙa mata tayi tanaji kamar ta mari jieddarh ɗin dan haushi, Tana shirin barin dining Area ɗin Jieddarh tayi saurin cewa "please Bilki ɗan dafamin noodles mana na kasa cin wannan abincin na gaba na," Tayi maganar tana ture plate ɗin gabanta.

"Ba Ƙya jin daɗine mamana naga yanayin ki kamar baki da lafiya" Abba ne ya tambayi jieddarh cikin kulawa, Lafiya qalau Abba kawai bana cin wannan abincin ne gwara a dafamin ko noodles ɗin naji ko zan iya ci.

"Okay Toke Bilki kinji don haka jeki dafa mata noodles ɗin mana kin tsaya kina kallon ta kamar baki santa ba," Auntie tayi maganar tana hararar Bilki danta tsana talaka.

Jieddarh fah ta rantse saita hana Bilki kallon Heesham cike da takaici Bilki ta wuce kitchen tana tsaki cikin ranta sai dai ba yadda ta iya, Cikin minti biyar ta kammala girka mata noodles ɗin zubo mata shi tayi a plate ta kawo mata, A lokacin Auntie bata a gurin ta kammala Humaira ita ma ta tashi jieddarh ne da Abba sai Heesham a gurin, Aje mata tayi a gabanta " To gashi nan.
Ɗan murmushin rainin wayo jieddarh tayi ta ce "to gashi naga kamar kinajin yunwa malama Bilkisu mai gadon zinare zauna muci kawai dan naji na ƙoshi."
Ɗan waro ido Bilki tayi jin abinda jieddarh ta ce, Yo ae ita ko karen hauka ne ya cijeta ba zataci wannan girkin ba, "kici mana naga fa tun safe kike zurzurga baki samu kinci abinci ba" muryar jieddarh ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta lula, Ganin yadda Abba Alhaji Jafar Komai Naka da kuma, masoyinta Heesham suka zuba mata ido ne yasa ta zauna a zuciyar ta ta ce "yau na mutu sai dai kuma gawata Yau dai jieddarh ta Rantse saita kasheni🤔.

Aje mata plate na noodles ɗin jieddarh tayi a gabanta "gashi Bilkisu mai gadon zinare muci ko,"  ƙara gyara zaman ta tayi sannan ta ɗauki spoon ta ɗi ba takai bakinta tana rumtse ido, ae ba shiri ta fito dashi jin wani uban yaji ga gishiri game da uban maggi da yayiwa abincin yawa tari ta fara ba qaqqautawa kamar zata shiɗe, Da sauri jieddarh ta miƙa mata gorar ruwa na Mr. V.

Hannu na rawa ta karɓi ruwan saida ta shanye ruwan tas sannan ta sauke gorar daga bakinta tana sauke ajiyar zuciya da sauri ta ɗauki maltinar data ɗaukowa jieddarh bata shaba, ta kafa a bakinta tas ta shanye maltinar harda karkaɗe kwalbar, Dariya ma taba su jieddarh ganin yadda take karkaɗe robar , na gode Bilki ta faɗa da sauri lokacin da ta ɗauki plate ɗin indomie ɗin tabar gurin kitchen ta shiga da sauri.

jieddarh na kiranta amma ina tayi gaba ko juyowa batayi ba, dariya jieddarh takeyi dama shiyasa taƙi cin indomie ɗin dan kuwa tasan da wuya idan Bilki bata shirya mata mugunta a ciki ba gashi abinda take zargi ya tabbata, Ita ko Bilki koda ta shiga kitchen ta ƙofar kitchen ɗin ta fita ta koma sashen su na ƴan aiki cike da takaicin jieddarh da ta sa ta shan yaji ba tare tayi shiri ba, gashi ko gama kallon masoyinta Heesham ba tayi ba, A fili ta ce Allah ya isa na Jieddarh'

****

Da yamma wuraren ƙarfe biyar dai dai jieddarh na zaune a wasu ƙayatattun kujeru na hutawa daga gefan compound ɗin gidan tana karanta wani  English Short Novel Mai Taken The Power Of The Silent, Gown ce doguwa a jikin ta na atamfa brown mai ratsin milk sai mayafin da ta yafa akanta milk color gabanta kayan mar mari ne kala kala sosai takejin daɗin karatun saboda yanayin weather na garin iska na kaɗawa kaɗan kaɗan gashi garin yayi luf luf💔

*Hauwa'u Ma`ana ☆🄺🅈🄰🄺🅈🄰🅆🄰🅁 🅈🄰🅁🄸🄽🅈🄰 🄼🄰🄸 🄹🄰🅁 🄵🄰🅃🄰☆ shi ne cikakken sunanta kyayawar budurwa ce mai kimanin shekaru goma sha tara zuwa ashirin a duniya.
Fara ce sosai hasken ta mai haɗe ja ne, Don zan iya cewa ma Jan yafi yawa akan farinna fatarta, Kyakyawa ce ajin farko duk wani qualities na kyau jieddarh tana dashi gashin kanta dogo mai tsayi highly highly...domin kuwa har mazaunan ta ga santsi sumar kanta mai kala biyu ne daga sama BAƘI ne suɗuq daga kasa kuma brown color ne mai haske idanun ta farare tas gasu dara dara masha Allah ga hancin ta mai tsini wanda Yayi daidai da kyakyawar fuskar ta, Bata da faɗin fuska don  fuskar ta is Normalcy ne, Ga ɗan ƙaramin bakinta mai ɗauke da launin dark pink tana da gashin gira highly highly gashi baki ga gashin idonta gazar gazar gunin ban sha'awa tana da tabon Allah a kasan gemunta baƙin ƙirin wanda ya ƙarama kyakyawar fuskar ta kyau highly highly😍.....Doguwa ce dirarra gata da duri ba'a magana saboda akwai ta da kayan alatu....Akwai ta da Yawan murmushi gata da dimples a duka gefe da gefen fuskar ta koyaya tayi magana saiya lotsa, Jieddarh akwai ta da son wasa da dariya ba ruwanta...Ta kammala  Primary da secondary school ɗin ta a private schools masu masifar tsada a ƙasashe daban daban na duniya, Don bazai yiwu na ce ƙasa ɗaya ba...saidai kuma har wannan Lokaci bata shiga University ba ace war ta secondary School ma ya isheta tunda ta iya turancin ta Shikenan, Jieddarh tun tana da shekaru sha shida tayi saukan alqur 'ani mai girma tana da hazaqa highly highly🤓

Abba Yaya ne agurin mahaifin ta mahaifin ta ya rasu tun tana ciki ba`a haifeta ba..Jieddarh bata taso tasan mahaifiyar ta ba, ko'a hoto mahaifin ta dai wannan ta sanshi a hoto sannan tasan sunan shi "JURAEJ" amma mahaifiyar ta ko tayi ma Auntie ko Abba maganar ta sai suce mata mahaifiyarta bata sonta ta tsaneta bata ƙaunarta tunda ta haifeta ta bar gidan basu sake sannin inda take ba.

Saboda haka ko`a wani lokaci tayi musu magana akan mahaifiyar ta haka suke faɗa mata, Wannan ne yasa bata ma musu maganar mahaifiyarta ta saboda ta lura idan tana musu maganar ta ransu ɓaci yakeyi, Jieddarh ta taso sam batasan Menene soyayyar iyaye ba duk da cewa su Auntie ba takura mata suke ba amma soyayyar iyaye na daban ne, Burin Jieddarh ɗaya a rayuwa shi ne a wayi gari ta zama SARAUNIYAR KYAU sannan kuma tana son wasan golf obaa da kuma gasar tseren🤐.
.......................................................................................................................

𝕎𝕒𝕟𝕟𝕒𝕟 𝕜𝕖𝕟𝕒𝕟 𝕒 𝕥𝕒𝕜𝕒𝕚𝕔𝕖 𝕟𝕒𝕟 𝕘𝕒𝕓𝕒 𝕫𝕒𝕞𝕦 𝕛𝕚 𝕕𝕒𝕝𝕚𝕝𝕚𝕟 𝕕𝕒 𝕪𝕒𝕤𝕒 𝕞𝕒𝕙𝕒𝕚𝕗𝕚𝕪𝕒𝕣 𝕁𝕚𝕖𝕕𝕕𝕒𝕣𝕙 𝕥𝕒 𝕥𝕒𝕗𝕚 𝕥𝕒 𝕓𝕒𝕣𝕥𝕒 𝕕𝕒 𝕜𝕦𝕞𝕒 𝕕𝕒𝕝𝕚𝕝𝕚𝕟 𝕕𝕒 𝕪𝕒𝕤𝕒 𝕁𝕚𝕖𝕕𝕕𝕒𝕣𝕙 𝕓𝕒𝕥𝕒 𝕤𝕠𝕟 𝕜𝕒𝕣𝕒𝕥𝕦 𝕕𝕒𝕞𝕒 𝕕𝕒𝕚 𝕤𝕒𝕦𝕣𝕒𝕟 𝕤𝕦
.......................................................................................................................

{ 🅺🆄 🅳🅰🅸 🅺🅰🆆🅰🅸 🅺🆄 🅱🅸🆈🅾 𝕿𝕳𝕰 𝕹𝕬𝕴𝕹𝕬𝕽𝕳 𝕶𝕯 }

***

Ji𝖊ddarh Bilkisu ta hango zata shiga ɓangarensu na ƴan aiki da alama daga garden take ƙwala mata kira tayi da ƙarfi juyowa Bilki tayi jin ana kiran ta kuma tasan ba kowa bane sai Jieddarh, ƙarisowa gurin tayi, " Malama Bilki zauna mana" Jieddarh Ta ce tana murmushi, zama Bilki tayi a ɗaya daga cikin kujerun gurin harda ɗaukar Tufa tana ci.

"Gani kiran me kikamin aiki zanyi fah bakiga ɗakina ba kacaca saboda haka faɗi abinda da zan miki ko nayi gaba abina" Bilki tayi maganar tanacin tufa ɗinta hankali kwance, aje tsadaddiyar wayar dake hanunta Jieddarh tayi tana kallon Bilki ta ce "kinason YaYa Heesham ko?."

Da sauri Bilki ta kalli Jieddarh jin abinda ta faɗa dan kuwa batayi tunanin wannan kalan tambayar zata mata ba, ɗan gyara zaman ta tayi tana sosa kanta kamar wata mara gaskiya, Ita kuwa Jieddarh ta zuba mata ido tana kallo, Ɗan ɗagowa Bilki tayi zatayi magana saita fasa ganin yadda Jieddarh ta zuba mata ido tana kallo "ina jinki fah, kiyi magana nifa zan taimaka miki wajen YaYa Heesham ɗinne," ɗagowa Bilki ta kumayi jin abinda Jieddarh ta kuma cewa magana ta fara cikin inda inda "ni nnifa Jieddarh kin zuba min waɗannan idanun naki mai kalar Ash bazan iya magana ba ae."

Dariya Jieddarh tayi ta ce "miye kuma idanu na suka miki da bazaki iyamin magana ba idan ina kallon ki?,"

"Hhmmm bazaki gane bane Yasin Jieddarh,"  "to ki ganar dani mana cewar Jieddarh.
Hm hum hum hmm Bilki taja doguwar ajiyar zuciya sannan ta fara cewa "kinga idanun naki kalar su Ash dasu su suke hana mutane haɗa ido dake dan kuwa ina faɗamiki ko mijin kine kika zuba ma wannan idanun naki mai kalar Ash mai Shaining to Yasin ina faɗamiki baisan lokacin da zai baki kuɗin  Lalle ba kona anko ba Yasin."

Dariya Jieddarh tayi har jejarrun teeth ɗinta farare tas suka bayyana cikin dariyar take cewa "Allah da gaske kike ki rantse Bilki ta ce kicema ya mallaka miki gabaɗaya dukiyar shi tofah da gudu zayyi hakan.
Bilki hadda kuma gyara zaman ta a kujera ta ce "Allah kuwa ae ina faɗamiki keɗin mai sa'a ce a rayuwa."

Jieddarh ta ce "to mudawo topic ɗin mu kinason YaYa Heesham ko a'a?.

Bilki ta ce "kema dai Jieddarh kinsan ba kunyar ki zanji ba, ko E' ina son shi," ta faɗa hadda rufe ido wai kunya bayan kuma yanzu ta gama cewa bata jin kunya ta ci gaba da cewa amma fah karkiga na rufe fuska kije ina jin kunyar ki a'a duk acikin soyayyar da nake mishi ne, To in ma ji kunyarki akan me bayan nasan ke sa'a tace dan kuwa nasan bazaki girmeni ba sai dai muzo sa'anni amma dai yanzu ba wannan maganar ce agaba na ba.

"Na Menene" Jieddarh ta tambaya "ah ae kema kinsani kawai dai ni bansan ta yadda zan janyo hankalin YaYa Heesham ya dawo kaina bane gashi ɗan gayu ina faɗamiki idan naje kusa da shi har wani shiɗewa nakeyi na manta kaina na manta wacece ni gabaɗaya a duniya."

"Tofah kice abin ya girmama?," cewar Jieddarh Bilki ta ce kedai Jieddarh ba zaki gane bane kawai amma na miki uzuri saboda baki taɓa soyayya ba, Bakisan Love bah amma duk ranar da kikasani zaki tuna abinda nake faɗa miki amma yanzu mu aje maganar ki a gefe aji da matsala ta ki faɗamin abinda yafi so da kuma wanda bayaso da sauransu.

Jieddarh ta ce "na farko dai abinda zan faɗa miki ki dena mishi wannan mayen kallon da kike mishi kamar zaki cinyeshi idan kinganshi saboda bayason kallo, Ke bamashi kaɗai ba akwai mutane da yawa basu cika son a kalle su ba haka suke su, Na biyu kuma ki dinga tsafta highly highly saboda YaYa Heesham yana son tsafta highly highly ke bama shikaɗai ba duka maza suna son mace mai tsafta daɗin daɗawa kuma tsafta cikon addini ne.

Jieddarh ta ɗan yi shiru tana ganin yadda Bilki ta zuba mata ido tana kallo "kina fahimta kuwa?," Jieddarh ta tambaya, ajiyar zuciya Bilki ta sauke ta ce "ina fahimta sosai ma",  "yauwa haka akeso ae" cewar Jieddarh nan dai Jieddarh ta dinga koyawa Bilki yadda zatayi Heesham ya sota acewar su.

Wasu danƙararrun motoci ne masu kyau da tsada suka shigo gidan guda biyu Yayinda Bilki ta saki baki da hanci tana kallon mutanen da suke fitowa daga motocin a fili ta ce "cabɗi jan yau muke ganin ƴan gayu anan gidan nan Yasin Yasin😇.

"Kalle su Mata su huɗu masu kama da Hajiya Jamila Wato Auntie da alama ƴan uwanta ne" cewar Bilki ta ci gaba da cewa gasu da yaransu suma ƴan gayu kamar su saidai ɗaya ce naga ba Yaro a tare da ita wata gila bata haihu ba ta tsaya tsarin iyali aikuwa za'a tsareta da kishiya duk ranar da mahaifarta ta sama problem "😅😂🤣.

Ɗan murmushi Jieddarh tayi bayan matan sun shiga ainihin gidan ba tare da sun kula su Jieddarh dake zaune a gurin ba, Bilki ta kalli Jieddarh da fuskar ta ya nuna alamar rashin jindaɗi ta ce "Jieddarh su kuma wa'innan fah kamar basu ga mutane a guri ba suka wuce hadda binmu da kallon banza hala ƙanin Hajiya Jamila ne naga suna kama da ita.

"E' ƙanin Auntie ne," Jieddarh ta bata amsa a gajarce "To ikon Allah amma kuma bansan suba ae gashi ina shirin zama IN LAW ɗinsu na miki na turawa.
Cewar bilki, "Oh Bilki ke komai sai kin sanine wai" cewar Jieddarh, Bilki ta ce "eh mana ba dole na sansu ba ƙannin suruka tace fah ae dole na sansu Yasin," Dariya Jieddarh tayi ta ce "to dai na farkon mai sanye da shigar hausawa YaYar Auntie ce uwa ɗaya uba ɗaya sunan ta Hajiya Nusaiba sai kuma ɗayar mai ƙaramin yaro sunanta sister Na'ima ɗayar kuma wanda kika ga ta riƙe hannun wannan kyakyawar yarinyar sunanta pretty Nafisah bazawara ce mijin ta ya rasu tun kafin Ta haifa ɗiyarta khausar, Duk tafi su kirki Yaranta biyu, Sai kuma na ƙarshen budurwace ita batayi Aure ba sunanta Ni'ima beauty shekarun ta Ashirin da biyar ita ce Babbar ƴar Auntie Nusaiba a mata YaYa Heesham takeso shiyasa batayi Aure bah🤣😂😅.


💓*SARAUNIYAR KYAU*💓
*Page 15&16*

Da sauri Bilki ta kalla Jieddarh hadda dafe ƙirji ta ce "wani YaYa Heesham ɗin, Badai masoyina ba?,"
"Of course yes, shi fa," cewar Jieddarh, miƙewa Bilki tayi zata bar gurin, Da sauri Jieddarh ta ce "ina zaki je ne, Haka?," "Hmm ke dai Jieddarh barni kawai zanje naga mai son masoyinane," Da sauri Jieddarh ta ce "to ki tsaya na faɗamiki wani abu mana.

Dawowa da baya Bilki tayi to gani faɗamin halayenta ina sauraronki,"  "haba malama Bilki toki nutsu mana saina faɗa miki yadda kema zaki fi fahimta," zama Bilki tayi cikin ƙosawa ta ce "to faɗamin ina sauraro," Ajiyar zuciya Jieddarh ta sauke sannan ta ce "kedai Bilki na farko dai ko shekara bakiyi a gidannan kina aiki ba watan ki bakwai ne, dan haka baki gama sanin halayyar ƴan gidannan ba ma balle kuma ƴan waje," ɗan shiru Jieddarh tayi sannan ta ci gaba cewa "ita wannan Ni'ima beauty da kika ganta ba'a shiga harkar ta, saboda bata da kirki ko kaɗan sannan kuma tanason YaYa Heesham highly highly kuwa," Jieddarh tayi maganar tana dariya, Ɗan kallon ta Bilki tayi cike da takaici da kishin Ni'ima ta ce "Yasin Jieddarh da nasan wannan shirmen zaki faɗamin da ban tsaya ba, Yo ni Allah na tuba kar tayi kirkin mana ina ruwa na da ita," Da sauri ta miƙe ta shige palon, Jieddarh ta bita da kallon tausayi kawai, Eh mana dole ta tausaya mata saboda wannan makauniyar soyayya da takewa Heesham, Jieddarh tasan halin Auntie yadda ta tsani talaka fiye da yadda ta tsani mutuwar ta da wuya wannan Auren ya yuwu gashi kuma soyayyar ɓangare ɗaya ne sai dai kawai Bilki ta sha wahala.

Bilki tana shiga palon ta samesu zaune sunyi ɗaiɗai saman Royal sofa's ɗin dake palon sai fira sukeyi da Auntie.
Kai tsaye kitchen ta shiga bayan wani lokaci ta fito hannun ta riƙe da Tray mai ɗauke da cups guda huɗu a saman, ciki juice ne mai sanyi, Ƙarisowa gurin su tayi ta bisu ɗaya bayan ɗaya tana raba musu wannan juice, Saida ta gama raba musu tas sannan ta dawo gurin Yarinyar Nafisah tana mata wasa ita kuwa Yarinyar sai ɓangale baki takeyi tana dariya, Dama ance mai ɗa wawa ganin haka yasa Nafisah cewa "Hi young lady what is your name?,"  Da sauri ita ma Bilki ta harhaɗa ɗan turancin da ta koya a makarantar gwamnati da tayi ta ce "year Aunty My name is Bilkisu Adam Mai gazon Zinare."
Dariya Nafisah tayi ta ce "aikuwa sunan ki mai ɗadi it's deserved to you beauty.
"Na gode highly highly" cewar Bilki a lokacin da take ɗaukar Yarinyar zata fita da ita, Harta kai ƙofa taji Ni'ima na faɗin "Yanzu fisabilillah Mamy Nafisah wannan bagidajiyar Yarinyar zaki bari ta ɗaukar miki ƴa kamar bakisan zafin haihuwa ba kwata kwata Yarinyar nan naki ko shekara batayi ba haba adai duba lamarin," Nusaiba ta amsa da faɗin barta Allah yasa a kwaso mata cutar talakawa babu ruwanmu ciki," ita dai Bilki fita tayi tanajin Nafisah na basu amsa ita kuwa tayi tafiyar ta a zuciyar ta ta ce "wannan Ni'imar anyi shegiya tayi da baki kamar mariƙin lema saina koya mata hankali soon na lura bata da wani cikakken hankali akanta.

Ƙarisawa gurin da Jieddarh take zaune Bilki tayi ita ma ta zauna kallon Jieddarh Tayi ganin Yadda gabaɗaya ta Mayar da Attention ɗinta akan tsadaddiyar Wayarta ƙirar SAMSUNG GALLAXY dake hannunta, Ta ce "lafiya kuwa Jieddarh wannan ƙurawa Salulah ido fah bakya tsoron Ya shafa lafiyar idanunki?".

Ajiyar zuciya Jeiddarh ta sauke Still idonta Yana kan Wayar hannunta Ta ce "kedai Bilki Bari kawai domin kuwa Wani ƙayatacce kuma haɗaɗɗen Labari Nake karantawa shiyasa Banma san Lokacin da kika ƙariso bah," Murmushi Bilki Tayi sannan ta ce "ato ae dama daga ganin Yadda kika Mayar da gabaɗaya hankalin ki akan wannan tsadaddiyar Wayar hannun ki nasan da wata a ƙasa, Toh dai Yanzu Zan iya Sannan Sunan wannan ƙayataccen labari Wanda Ya Tafi da gabaɗaya hankalin ki, Idan akwai dama, ma sai kiyim ƙarin bayani akan Yadda zan samu na siya nima na karanta cikin nutsuwar zuciya."
Ƙayataccen murmushi Jieddarh Tayi sannan ta ce "Tabbas akwai dama highly highly mah Yanzunnan zanyi miki dogon Bayani akan wannan shahararren Labari Wanda Yazo da salo na daban.........
Da Farko dai Sunan Wannan Katafaren Labari shine 🅂🄰🅁🄰🅄🄽🄸🅈🄰🅁 🄺🅈🄰🅄 sannan ya sama rubutu ne daga Alƙalamin sabuwar marubuciya 🄺🄷🄰🄳🄸🄹🄰🅁🅃🄷 𝕎𝕒𝕥𝕠 🆃🅷🅴 🅽🅰🅸🅽🅰🆁🅷 🅺🅳, sannan kuma wannan labari zaki iya samun shi a kafar yanar gizo kamar irinsu, FACEBOOK WHAT'SAPP TELEGRAM WATTPAD, ke idanma kina da buƙata zan iya baki phone number na wannan marubuciyar domin tayi adding ɗinki a what'sApp Group nata da take Tura SARAUNIYAR KYAU ciki fah.

Washe baki Bilki Tayi Sannan Ta ce "ah gaskiya daga Jin wannan Bayani Naki Nasan Wannan Novel zai Bada Jitta obaaaaa ae ina faɗamiki Jieddarh Yanzunnan Zan kwashe What'sApp lamba Nata domin na dunga samun updates wannan ƙayataccen labari don kar a barni a baya🤓
Murmushi Jieddarh Tayi sannan ta ce "aikuwa dai ya kamata don kema ki ƙaru da abinda yake ciki.

Bilki Ta ce ohoo kaji ƴar gari kuma ƴar birni, yanzu abinda za'ayi kawai phone number na wannan Marubuciya zaki bani yanzu na lalubota, "Zan baki amma ba yanzu ba", "to sai yaushe Bilki ta tambaya jin abinda Jieddarh ta faɗa.
Murmushi Jieddarh tayi ta ce "saima gama ja miki aji sannan " Humm amma Yasin Jieddarh kina da wulakanci sai dai ya na iya da saurayin ummata haka zanyi haƙuri ki gama jamin ajin" Bilki tayi maganar Like a orphan tana mai yin alamun tausayi murmushi kawai Jieddarh tayi ba tare da ta ce komai bah.

Haka dai suka ci gaba da fira da Jieddarh sun daɗe suna fira kafin wani lokaci su Nafisah suka fiffito, Da alama tafiya  zasuyi gurin su Nafisah ta ƙariso karɓar ɗiyar ta sai dai kuma me aikuwa Yarinya ta fara kuka ba za ta je wajen ta ba, Wai ita harta saba da Bilki dariya Bilki tayi ta ce "Yau na sama ɗi ya ɓagas gashi kuma banma san sunanta ba amma ta maƙale min" Nafisah na murmushi ta ce "sunanta khausar", "wow nice name shiyasa take sona ashe taga ɗiyarta ne" cewar Bilki tana washe baki "da gaske haba kice sunan mama ce da ita Nafisah ta tambaya cikin murmushi, "Yasin kuwa sis" cewar Bilki tana jijjiga khausar ɗin dake kuka, "gashi kuma taƙi ta yarda dake yanzu ya za'ayi gashi kuma jiran ki akeyi Jieddarh ta faɗa ganin yadda Yarinyar kamar wata mai wayo taƙi zuwa wajen mahaifiyar ta😕.

Ni'ima ce ta ƙariso gurin cikin isa da gadara Like a ɗiyar Gwamna "lafiya kuwa Mamy Nafisah kizo mu tafi mana kin tsaya magana da wannan dirty girl ɗin."
"To Ni'ima yarinya dai taƙi yadda dani fah"
"Taƙi yadda dake kuma ban gane taƙi Yarda dake ba, kar dai ace an asirce miki ƴa ne daga raino" Ni'ima tayi maganar tana ɓalawa Bilki harara dan haka kawai taji bata mata.
Ba wanda ya kulata a cikin su, saima bawa kurma da blind da mara aikin yi, Ajiyar ta da sukayi😇.

"Please Mamy Nafisah ki karɓa ɗiyar ki mu tafi mana, dare nayi fah, Ni banma san dalilin da yasa mukazo gidan Mamy Jamila da Yamma ba gashi garin hadarine highly" Ni'ima tayi maganar da iya gaskiyar ta, Da ƙarfi ta karɓa Yarinyar a hannun Bilki tana faɗin "aikin kawai, ke Mamy Nafisah sai ki zo muje ae", tayi gaba abinta haƙuri kawai Nafisah taba Bilki jin an fara ruwan sama, ta ce "karki damu Bilkisu ina nan dawowa wata rana zan dawo, kuma a gurin ki khausar zata wuni, kuma ke zanba yayenta idan lokaci yayi tunda naga tana sonki insha Allah," Murmushin jin daɗi Bilki tayi ta ce "ba komai sis Nafisah, kuma ina sauraron ranar da za'a kawomin lovely Khausar momyna yaye," "Lallai ma wato har kin saka mata suna Lovely momy ko?," cewar Jieddarh cikin murmushi, ita ma Nafisah murmushi kawai tayi sai dai ba ta ce komai ba saboda rashin lokaci, sallama sukayi su Nafisah suka tafi, su kuma Jieddarh suka koma ciki jin ruwa ya tsinke kamar da bakin ƙwarya.

🅱🅰🆈🅰🅽☆🆂🅰🆃🅸☆🅱🅸🆈🆄

         

ABUJA

Kwance take tayi ɗaiɗai, Tana kallon sararin samaniya kamar mai ƙirga taurarin dake a sararin samaniyar, Ta saka hannun ta ɗaya tana murza dogo kuma baƙin gashin kanta wanda ya baje a saman koranyen ciyawu wato Grass carpet dake a cikin garden ɗin da take ciki kwance, wanda aka qawata da shuke shuke da kuma bishiyu kala kala kamar su  mangwaro,gwaiba,taura ayaba. Da dai sauran su, da sauran su.
Headphone ne manne a kunen ta tana sauraron lyrics na mawaƙiwa celline Dion mai taken "A New day has come" ta lumshe idanun ta Yayinda take bin waƙar a hankali cikin ranta.

Gefen ta kuwa Afeefah ce, zaune a kujera mai lilo dake a garden ɗin Al qur'ani ne a hannunta tana tilawa.
Riga ce top fara a jikin ta sai wando crazy jeans black kanta kuma Baby hijjab ne black shima, shiga kala ɗaya ne a jikinsu su biyun kammala karatun nata ne yayi daidai da haske da wayarta tayi alamar dai kira ne ya shigo, waƙar shani'a Twain, "Forever and for always," ya karaɗe gurin hannu tasa ta ɗauki wayar dake a gefenta, nan sunan  SISTER NAINARH, ya bayyana saman screen ɗin wayar, sallama tayi bayan tayi picking call ɗin.
Zuba mata ido Lailah dake Kwance saman Grass carpet Tayi, shiru taga tayi da alama magana ake ta ɗayan ɓangaren, Can sai kuma taga Afeefah ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ce "eh da sauƙi dai......Shiru ta kuma yi can ta kuma cewa "a'a nima dai ba na ce ba kawai dai muna zaune a palon ƙasane mukaga ta faɗo daga saman step's na staircases mu kuma muka kaita asibiti kuma koda muka dawo mun duba bamu ga komai a ta gurin da ta faɗon ba, sannan mun tambaye ta ta ce ita ma bata san meya faɗo da ita ba kawai dai abin ya faru ne in insticnt.."
Ɗan shiru ta kuma yi alamar sauraron maganar da mai kiran nata takeyi, Zumbur ta miƙe tsaye fuskar ta cike matsanancin farin ciki take faɗin "Please sis ki rantse, yaushe kuma a wani airport ɗin gamu nan zuwa Yanzunnan," sai kuma ta katse wayar tana kallon Lailah data zuba mata kyawawan idanun ta tana kallo.
Ta ce "Hello babe Aunty Nainarh ta shigo ƙasar fah, Yanzu take faɗamin, don haka ki taso mu tafi airport mu ɗaukota kawai ba saimun tsaya jiran drivers ko escort bah."
Ɗan waro ido Lailah tayi alamar mamaki ta ce "sister Nainarh kuma ita kaɗai ce, ko kuwa dai." Cike da ƙosawa Afeefah ta ce "ke dalla malama ki taso mu tafi mana, ita kaɗai ne mana dan  kema kinsan wannan mijin nata mai kama da zabiya ba zuwa zayyi ba.
Ɗan taɓe baki Lailah tayi "well koma miye ae ita taja ma kanta ace mahaifiyar ta guda ta sama karaya amma sai da akayi sati biyu shine zata wani ɗauko ƙafa ta taho" Lailah tayi maganar cike da takaici, tana miƙewa, suka shiga cikin gidan su fara shiryawa sannan su wuce airport ɗin.

****
💓💔💓
****
"Wai kuwa gwaggo na nace yanzu muna sauka a motar nan shikenan mun shiga birni ko kuma ma a birnin garin habuja ko?, daga yau shikenan bani ba ƙauyenmu,bah su delu babu ƴan ƙauyenmu balle kuma na rama abinda sukamin shikenan sun shani a musilla."
Wata kyakyawar matashiyar Budurwar Yarinya ce duk take wannan zubo zancen ga gwaggon ta a cikin motar da suke zaune a gidan baya ga sauran mutane nan a motar gaba da baya.
Ta ci gaba da cewa "waima gwaggo na yanzu aikin me zan dinga yine idan munje gidan aikin da zaki kaini?, bata tsaya ba ta ci gaba da cewa "kuma shikenan kina kaini zaki dawo gida kiyi auren ki, abin ki, Ki barni a Habuja ni kaɗai bansan kowa ba kowa bai sanni ba, kawai saita fashe da kuka, Gwaggo ta kalleta cike da takaici ta ce "au yanzu dije tun kafin na kaiki gidan aikin zaki faramin kuka kamar na dake ki faɗamin na dake kine ko kuwa gidan aikin kikeyi ma kukan ban sani bah."

Cikin muryar kuka budurwar ta ce "toh gwaggo ba kece kika ce a birni zaki barni ba ni kaɗai ba, kuma ae nace miki kiyi hakuri bazan ƙara faɗa dasu hanne ba, kuma fah su suka fara tona na shine ni kuma na rama kuma ke gwaggo ma ae kinsan sarkin yawa yafi sarkin ƙarfi shine sukamin duka, gefe ɗaya kuma ga dukan da wannan matar tayimin gashi jiki na baigama warkewa bah, fuska ta ma haka shi ne kika kawo ni aiki don a ƙarisani."

Ɗan tausayinta ne ya kama gwaggon nata, a hankali gwaggon ta ce "ae ke ce dije na hanaki wasan banza dasu hanne amma ba kyaji sannan kuma da kike cewa na kawoki aiki birni ae mahaifin ki shine ya ce a kawo ki aiki birnin bani ba.".

shiru budurwar tayi tana kallon gwaggon sai kuma tayi murmushi ta ce "toh gwaggo makaranta na fah zan ci gaba da zuwa anan abujan kuwa?, ɗan shiru gwaggon tayi kamar mai tunani sai kuma can ta ce "eh to idan kika nutsu highly, ƴan gidan suka ga irin nutsuwar ki wata ƙila su iya saki a makarantar.

Dariya tayi cike da farin ciki da yarinta kamar ba ita ce mai kuka yanzu ba ta ce "shikenan yanzu sunana ya tashi daga dije sai dai Nanah ko kuma ace min Deejarth ko Deejarh irinna ƴan birni, na bar su hanne da wahalar ƙauye da sunan ƙauye," ta kuma gyara zaman ta a motar tana kallon cikin garin abuja ta glass ɗin motar, sannan  ta kuma juyowa tana kallon gwaggo ta ce "gwaggo yanzu fah, su ƴan birni sunan su bah irin na ƙauye bane koh?," gwaggo tayi dariya ta ce "sosai ma, aisu ƴan  birni sunan su na daban ne, special ne in miki na turawa.

Dije ta ce "ae ina faɗamiki gwaggo na muna zuwa gidan aka tambaye ni sunana zance Deejarh ta faɗa tana nuna yadda zatayi wajen faɗan sunan nata idan aka tambaye ta, wannan karon ba iya gwaggo ne tayi dariyar ba hadda sauran ƴan motan wata mata a motar ta ce "Deejarh aikuwa suna mai daɗi, it's nice name."

Dije tana yanga ta ce "tnx" wai irinna ƴan birni matar ta kuma cewa "hala daga ƙauye kike, Ah ah su Dije an sama guri ga abokiyar hira ta samu ta ce "Yasin kuwa kamar kin sani, daga ƙauye nake amma yanzu na shigo birni ae," matar da alama ita ma "A" ce a gurin surutu ta ce "to su sunan ƴan ƙauyen da naji kina faɗa ya suke?.
wannan karon kallon matar Dije tayi highly, ta dai ga alama gilama ko sunan ƙauye matar bata sani ba.

Hadda sauke Ajiyar zuciya tayi sannan ta ce "sunan ƴan ƙauye yanzu kamar dai ace sunan ki Hafsat a birni tofah a ƙauye ina faɗamiki sai dai a kira ki da hanse ko kuma ace hansi ko kuma hansatuwa 🤣😂😅.
 
ko kuma sunan ki sa'adatu a birni tofah ina faɗamiki idan a ƙauye ne sai dai ace miki sa'ade ko kuma a kira da sa'a duk da dai sunan gwaggo nane sa'aden amma Yasin na faɗa.

Gwaggo dake gefe ta ce "ae dama kin rainani shiyasa kike kiran sunana haka gatsal"  Dije tayi dariya ta ce "gwaggo kenan ae wannan bayani nakeyi shiyasa kikaji na faɗa sunan ki a haka,"  Dije ta kuma kallon matar ta ce "ni kuma yanzu kamar ni sunana "khadeejah" amma a ƙauye kinsan me ake cemin kuwa?, matar tana dariyar Dije ta ce "a'a saikin faɗa ae zan sani ko?."
Dije ta girgiza kai alamar takaici sannan ta ce "wai fah Dije ake cemin, wasu ma har magajiya suke cemin, a birni kuwa ae sai dai kiji ance deejarth Deenah ko kuma ace Nanah ko Nainarh koma hadiza ga sunan nan dai kala kala sai wanda mutum ya zaɓa a birni.

Wata budurwa ce ta ce "ni kuma sunana AYSHA idan a ƙauye ne, me ake kiran mai sunan?... Dije ta kalli budurwar da ta kira kanta da AYSHA gata ƴar gayu kyakyawa da ita, sannan tayi murmushi ta ce "ae Yasin ina faɗamiki Yadda kike da kyau ɗinnan a ƙauye ba ruwan su sai dai kiji ankira ki da a'i ko kuma indo ko esha ko ma shatu, bah wani sunan ki AYSHAN NAN Yasin, AYSHA tayi dariya ta ce "amma za'a iya cemin Humaira ko A`ishatu acan ɗin ko?," Dije ta ce "idan kinci sa'ah ba."

KUYI HAƘURI DA WANNAN PAGE ƊIN, BANA JIN DAƊI NE SHIYASA.
SARAUNIYAR♥ƘYAU♥FAN`S♥GROUP♥LOVE♥U♥ALL💝

✍️𝖙𝖍𝖊 𝖓𝖆𝖎𝖓𝖆𝖗𝖍 𝖐𝖉 𝖈𝖊📲

*💋𝑆𝐴𝑅𝐴𝑈𝑁𝐼𝑌𝐴𝑅 𝐾𝑌𝐴𝑈💋*

𝑀𝐴𝐿𝐿𝐴𝐾𝐼𝑁☆☆𝐾𝐻𝐴𝐷𝐸𝐸𝐽𝐴𝑅𝑇𝐻
     
                 

                            {𝑇𝐻𝐸 𝑁𝐴𝐼𝑁𝐴𝑅𝐻 𝐾𝐷}

*Page 17&18*

Haka dai Dije ta ware da ƴan motar sunata kwasan fira kamar dama can sunsan juna dayake ita haka take bata da wuyar sabo da mutum, kowa ya faɗamata sunan shi saita faɗa yadda ake kiran sunan nashi a ƙauye a haka har suka sauka a tasha, sannan  suka hau napep izuwa gidan da gwaggon nata take aiki.
A napep Dije ta kalla gwaggo ta ce "wai gwaggo na miye sunan unguwan da gidan aikin naki yake ne?,"  gwaggo tayi murmushi, tambayar da Dije ta mata, tuno mata da ƴan gidan da tayi musamman ma Afeefah, cike da fara'ar da ya bayyana saman fuskarta ta ce "MAI KYAU DISTRICT" a taƙaice.
A hankali Dije ta maimaita sunan a ranta a fili ta ce "kilama unguwan zatayi kyau tunda naji sunan da daɗi fa, kai Yasin ma daga ji bama KYAU kaɗai ba, harda kyan gani."
Ita dai gwaggo bata ƙara kulata ba har suka isa unguwan, zare ido kawai Dije takeyi ganin fantsama fantsaman gidajen da suke wucewa sunƙi su ƙare.

Dije ta ce "lah lah lah gwaggo Yasin gidajen masu shegen kyan kyawu ne, Allah kai sai kace fadar aljannar duniya," ta faɗa tana ƙanƙame gwaggon nata kamar za'a ƙwaceta daga hannun gwaggon nata, Humm ae Dije bata ƙara tsurewa ba, har sai da taga ƙaton Jibgegen katafaren gidan da mai napep ɗin ya saukesu a bakin gate ɗin shi, numfashin ta ne ya kusa tsayawa cak saboda tsantsan kyan gidan wai danma dare ne shiyasa amma ae ba ta ga komai ba. A fili ta ce "aljanar duniya kenan wannan ƙato kuma gandameman gidan haka Yasin ni Dije ta ƙauye naga gurin zama🤣.

Ƙwanƙwasa ƙaramar ƙofar gate ɗin gidan gwaggo ta fara, gate man ne ya leƙo ganin gwaggo ne yasa shi ya buɗewa, da sakin fuska da alama sun saba da gwaggon.

Shiga gidan sukayi ita dai Dije sai ƙarema gidan kallo takeyi ga hasken lantarki da expensive lights ya haske ko'ina da ina na gidan, ga kuma shuke shuke gashi gidan ƙato gaske "ae yasin gobe da safe saina fito na ƙarewa gidan kallo, kai ina zan bari kallon daular aljannar duniya ya wuce ni, Dije ta ƙarishe maganar nata, a dai dai lokacin da suka ƙarisa bakin ƙofar palon katafaren gidan, don ita ma kanta ƙofar palon na glassa ne, kuma glass ba wai irin normal glass ba, a'a glass ne irin highly expensive glass ɗinnan wanda ba'a ko'ina ake samun kalar shi ba,sai gurin da naira ta zauna aci asha sannan aka tada kai da ita abar da take juya duniyar wato  ita 𝑁𝐴𝐼𝑅𝐴💸💲💰

Dije a zuciyarta ta ce ita kanta ƙofar ma abin kallo ne harda Wani Glass, ga kuma gurin danna lambobin sirri, oh ni Dije ta ƙauye yau dai ina ganin ikon Allah da abin mamaki a birni,kuma a gidan shugaban ƙasa. Dije ita duk a tunaninta fah gidan president take,don tun lokacin da ta ga waɗannan jibga jibgan jami'an tsaron dake tsaron gidan ta sadaƙar da cewa nan fa gidan shugaban ƙasa ne, gwaggo ta kawota.

Kallon gwaggo dake knocking ɗin ƙofar palon tayi saboda ta gaza riƙe abinda ke ranta ta ce "gwaggo hala wannan gidan shugaban ƙasa ne ko?," dariya tambayar Dijen yaba gwaggo tayi sannan ta ce "a'a me kika gani?,"  Dije ta saki baki da hanci ta ce "lah wai dama nan ba gidan shugaban ƙasa bane, to gidan waye?," gwaggo ta ce "ko kaɗan ba gidan shugaban ƙasa bane,"  Dije ta ce "tabɗijan aikuwa dai...Dije tana shirin yin wata maganar taga alamar ana buɗe ƙofar palon, nutsuwa tayi a zuciyarta kuma cewa tayi bari na natsu saboda aji daɗin sakani a makaranta da wuri.
Wata haɗaɗɗiyar ƴar Gayu ce ta buɗe musu ƙofar, Dije tana shirin gaisheta taga ta juya ta koma bayan ta bisu da kallon banza, baki sake Dije tabi ta da kallo ganin gwaggo na shirin shiga ciki ta barta ne yasa tabi bayan gwaggon da saurinta.

 
Ae Dije baki,hanci, kunne,ido, ba abinda bata saki ba ganin irin haɗuwar palon na fitar sense ƙarewa palon kallo ta shiga yi kamar wata sakarya komai na palon sky purple ne and white color gashi ƙaton gaske 100by100.

Jin murya ana magana ne yasa ta dawo hayyacin ta tana bin ƴan palon da kallo kamar yadda suma suke kallon ta.
Muryar gwaggonta ta tsinkayo tana gaishesu, baki ta kuma saki jin wai gwaggo ne take gaishesu su kuma ba kunya sun amsa a zuciyarta ta ce "bala'i Yasin ba shegiyar da zan gaisar tunda ba'a haifeni ba caɓɗijan, gyara tsayuwar ta tayi tana kuma bin mutanen palon da kallo a zuciyarta ta ce wa'innan suba turawa suba larabawa sannan kuma ba chanistawa bah🤣😂😅.

Afeefah dake saukowa downstairs ta hango mutane tsaye a palo kamar masu jiran kota kwana ga wasu abubuwa hannunsu kamar tsummokara🤣.
Ita batama gane su ba saida ta kusa saukowa sannan ta gane kosu waye cike farin ciki ta ce "laha'ila Auntie sa'adah kece?," da ɗan saurinta ta ƙarisa saukowa sannan ta ƙariso gurin su tana faɗin "Auntie sa'adah yaushe kika dawo ne?, yana ganki a tsaye ki zauna mana please, kallon Dije tayi wacca ta zuba mata ido kamar zasu zubo ƙasa saboda kallo.
"Lah Auntie sa'adah wannan fah?, ta tambaya bayan su Dije sun zauna a two sieter ita kuma ta zauna a one sieter. murmushi Auntie sa'adah tayi sannan ta ce "wannan ƴar yaya tace nazo da ita zata dinga tayani girki da wasu ayyukan. tayi maganar a gajarce.
Murmushi Afeefah tayi Sannan ta ƙara kallon ƴar kyakyawar baƙauyiyar yarinyar dake kallon ta har yanzu kamar ta sama television, ta ce "barkanki dai please may i know your name?,"

"Sunana die dee deejarth, eh deejarh." Dije ta faɗa cikin inda inda, game da daburcewa na ganin tsantsan kyau irinna wannan kyakyawar halitta dake gabanta.
"Hala dai kina inn inane" Afeefah ta tambaya.
 Da sauri Dije ta ce "a'a banayi 'Balarabiyar india'.
 Murmushi Afeefah tayi ta ce "Wacece kuma 'Balarabiyar indiyar?." Dije ta ce "ke mana ae kece 'Balarabiyar india' don naga kinfi wa'incan kyau, ne sa ba kusa ba Yasin. Ta faɗa tana nuna mutanen palon da suke harkar gabansu kamar basusan da wata hallitar a gurin ba inma sun sani to basu damu dasu bah🙄.

Kallon su duka Afeefah tayi yaran ƙanwar Momy Rafi'at ne Hajiya Sailiba, su biyu fareeda da fadeela twins ne sai kuma Lailah dake kwance a Three sieter da alama karatu take bacci ya ɗauketa sai kuma can dinning table  Nainarh da Nailah ne suke cin dinner ɗinsu.

"To Ke ma miye sunanki" Dije ta tambaya.
"Sunana Afeefah Abubakar Mai ƙyau", "wow nice name" cewar Dije hadda haɗawa da ɗan turancinta da ta kowa a makarantar ƙauyensu. Ta kuma cewa "i'm very pleasure to meet you.
A wannan karon ba iya Afeefah ba hatta su fadeela, fareeda,su Nainarh da Nailah dake dinning room saida suka juyo suna kallon Dije da tayi maganar dan kuwa basuyi tunanin tanajin turanci ba, tun daga yanayin shigar dake jikin ta, huh to akan mema zasuyi tunanin tana jin turanci bayan kallon irin shigar jikinta,duk wanda ya kalleta lokacin kai tsaye da Villager girl zai kirata.
Dije tayi murmushi dan kuwa da gangar tayi turanci dan ta kankarowa kanta daraja, a zuciyarta ta ce jisu sun ɗauka kowama dusa ne taja qwafa🤓.

Afeefah ta ce "wow you are so cute and adorable."

 Nanfa ɗaya Dije ta fara zarar ido tana rabawa dan bataji abinda Afeefah ta faɗa a ƙarshen maganar ta ba, turancin ma da tayi yanzu da yaya ta haɗasu, da kyar ta iya cewa "na gode," amma a ranta ta riƙe kalmar "adorable" ƙam saita bari daga ita sai Afeefah ɗin, zata tambaye ta fasarar kalmar.

Afeefah ce tayi magana, Dare fah nayi ta kallesu ta ce "Aunty bari da safe ma ƙarisa maganar yanzu kije ki kwanta kawai," sannan ta kalla Dije ta ce "follow me na rakaki ɗakin da zaki zauna," tashi sukayi dukansu Auntie sa'adah ta wuce ɓangaren su na ƴan aiki ita kuma Afeefah ta nuna ma Dije wani bedroom dake kusada kitchen, tana murmushi ta ce "bedroom ɗinkine shigo nanuna miki ciki," binta ciki Dije tayi hannun ta riƙe da jakar kayan ta, ɗakin yanada girma sosai ba lefi komai na ɗakin milk and Brown color ne.
Yanayin komai na ɗakin yayima Dije kyau sai faman washe baki takeyi ɗakin tsaf da alama kullum ana gyarashi bathroom suka shiga Afeefah ta nuna mata yadda ake amfani da wasu abubuwan dake ciki wasu kuma ta ce sai gobe, sai da Afeefah ta tabbatar da ta nuna ma Dije yadda ake amfani da komai sannan ta fita ta rufo mata ƙofar.

Afeefah na fita Dije ta daka tsalle ta haye saman gado a fili ta ce "huh saini Dije ta ƙauye a birni kuwa deejarh nake Yasin.
Tashi tayi tana kuma ƙara bin ɗakin da kallo iya yinta saida tayi iyayinta sannan ta cire  yamu shashshe hijjab ɗin jikinta wanda yaga jiya yaga yau.

Toilet ta shiga jin ana kiran sallan isha'i alwala ta ɗauro as a muslim girl, bata tsaya ƙarewa toilet ɗin kallo ba ta fito, jakar kayanta ta buɗe ta ciro sallaya da hijjab sabo.
Gurin da taga an tanadar domin sallah taje tayi, bayan ta idar da sallan ta cire hijjab ɗin, jakar kayanta ta ɗauka ta fito da kayan ciki duka waje tayo dasu, saboda tsaban iyayi irinna Dije a wardrobe ta jeresu tas bayan tayi musu ninki irinna guga.
Sannan ta tashi toilet ta koma tana kuma bin ko'ina da kallo yayi kyau sosai gaban mirror ta tsaya tana kallon kanta saman mirror ta kalla taga abubuwan wanke kala kala sai wanda mutum ya zaɓa.
Ae ba shiri Dije ta zaro ido ganin abubuwa na ƴan gayu iri iri ba'a magana, kayanta ta cire, ta ɗaura towel ɗin da taga anyi hanging ɗinshi in toilet wall.
Ɗaya daga cikin abin wanke kai ta ɗauka taga an rubuta "shampoo" buɗewa tayi tatso a saman hannunta sannan ta murza zuba saman gashin kanta saida ta gama sawa Sannan ta kunna famfo tasa ruwa ta wanke tas, wani ta kuma ɗauka taga an rubuta "All hair conditioner" ba tunanin komai shima ta wanke kanta dashi bayanta gama wanke sumar kanta da shampoo's ɗinne, tayi wanka ta fito ɗaure da towel fari ga wani a hannunta tana tsane sumar kanta dashi hand Drier ta gani da sauri ta jona a charge sannan ta fara bushar da gashinnata bayan ta kammala ko shafa lotion batayi ba ta je wardrobe ɗin data jere kayanta riga doguwa na material ta ɗauka duk taji duniya ta saka bayan ta gama komai ta haye saman bed sai bacci. {Dije anya kuwa wannan daga ƙauye take?, E mana gani nayi ae ta iya komai daya danganci bathroom sai kace wacca dama can ta saba shiga🤔}.




NKD ✍️ ✊

Khadeejarth Nainarh Kd.




𝐴𝑓𝑒𝑒𝑓𝑎ℎ 𝑚𝑎𝑖𝑘𝑦𝑎𝑢

Ɓangaren Afeefah kuwa tana fita daga ɗakin da ta sauke Dije kai tsaye bedroom ɗinta ta koma, system ɗinta ta ɗauka tana karatun exam dayake sun fara ne.
Tana zaune saiga Lailah ta shigo ita ma hannunta riƙe da littafai irinna su na likitoci, zama tayi tana faɗin "a gaskiya na gaji wannan karatun, wallahi karatun likita ba sauƙi saina Allah....kai ina, ni da ma a soke karatu kwata kwata adena a duniya."
kallon Afeefah tayi dake faman aiki da system da alama ma batasan ta shigo ɗakin ba. "Hey miss feefah, duk karatun ne haka ba'asan ma lokacin da na shigo ba." Lailah tayi maganar tana tafa hannunta a fuskar Afeefah ɗin, ɗagowa Afeefah tayi tana kallon Lailah fuskar ta ɗauke da murmushi ta ce "yane likita karatun exam ɗinne, yayi zafi ko?," Aiyar zuciya Lailah ta sauke ta ce "ana fama wallahi, ni fa ko, wani lokacin sai naji kamar nabar wannan karatun likatancin fah." Waro ido waje Afeefah tayi tana ɗan murmushi ta ce "lah lah Lailah aikuwa wannan maganar sai a kunnen daddy, ko dai duk karatun exam ɗinne ya kawo hakan kike saɓa lamba haka."
 "Hummm kedai ba zaki gane bane kawai Miss feefah sai dai kawai abar zancen anan," cewar Lailah, "haba zan gane mana idan kika ganar dani Afeefah ita ma ta bawa Lailah amsa tana dariya.ɗaukar littafin karatunta Lailah tayi ba tare da ta ce ma  Afeefah ɗin ci kanki ba😂.

**

Sai wajen sha ɗaya na dare, sannan suka kammala karatun nasu wai nanma Lailah ce ta dage bacci takeji shiyasa suka haƙura.

**
Kiran sallah ne da sanyin asuba dake kaɗo curtains ɗin ɗakinne ya tashi Dije daga bacci tashi tayi tana miƙa alamar dai baccin bai isheta ba. Kai tsaye bathroom ta shiga ta ɗauro alwala ta fito ta tada kabbarar sallar asuba bayan ta shimfiɗa sallayar ta da ta zo dashi daga ƙauye.
Tana cikin raka'ar ƙarshe ne aka turo ƙofar ɗakin aka shigo Afeefah ne jikin ta sanye da hijjab fari tas har ƙasa na sallah zama tayi saman bed tana jiran Dije ta idar da sallah.

Juyowa Dije tayi bayan ta idar tana kallon Afeefah ta ce "lah Balarabiyar india kece ashe ina kwana,"  murmushi Afeefah tayi ta ce "lafiya ƙlau Deejarh ya kike ya baƙunta kuma fatan kina cikin ƙoshin lafiya.
Washe baki Dije tayi ta ce "ae Balarabiyar india ina faɗamiki babu baƙunta don tuni yabi gado, amma wai Balarabiyar india na tambaye ki mana idan babu damuwa?," cewar Dije.
Afeefah ta ce "ina jinki Allah yasa na sani," washe baki Dije ta kuma yi cike da farin ciki wannan kyakyawar Balarabiyar india tana mata magana ta ce, " ah dama Balarabiyar india wannan ɗakin hala na ƙanwar kice?." Dariya Afeefah tayi ta ce "a'a ko ɗaya bana ƙanwa ta bane, amma me kika gani ne?," Dije ta ce "ae naga akwai komai da komai ne, a ciki hadda man wanke gashi fah na gani kala kala a can wajen ta nuna bathroom.
"Okay ae ɗakin baƙi ne idan suka zo sai suke zama anan, kamar dai ace ƴan mata kamar ki, aikin ga ɗakin irinna ƴan mata ne waɗanda basu wuce 15years ba ko," Dije ta ce "E, mana gashi ɗakin mai kyau kuwa, Balarabiyar india wai Menene ma sunan ki na gaskiya sunan akwai daɗi amma kuma sai wahalar faɗa ko miye ma "AFEEF" ne ko "AFFAF" ta tambaya tana kallon Afeefah ɗin.

Yauwa na tuna Afeefah hakane ko?,"  'E,' Afeefah ta bata amsa sannan ta ce "follow me muje kitchen Auntie sa'adah na kiran ki zamu haɗa breakfast okay,"  tashi Dije tayi tabi bayan Afeefah bayan ta cire hijjab ɗin jikinta ta ɗaura ɗan kwalin rigar dake a jikinta.

Dije sai faman kallon kitchen ɗin takeyi tana kallon kyau da tsaruwa, muryar gwaggon ta taji suna gaisawa da Afeefah da sauri ta kalla gurin da gwaggon nata take ta ce "lah gwaggona kece wai, to ina kwana ni yasin na manta dake mah," gwaggo ta ce "toh dama tayaya zaki tuna dani kina can kin sama a.c kina kwasar bacci harda minshari.......washe baki Dije tayi tun kafin gwaggonnta ta ƙarisa maganar da takeyi Dijen ta rigata da faɗin, "Yasin kuwa gwaggo bakiji ba kamar karna fito daga ɗakin domin wani irin madarar daɗin bacci ɗakin yake dashi.
Dariya Afeefah tayi ta ce "to malama deejarh mai ɗaki, ga wannan juyo in ɗaura miki, kallon abinda Afeefah take miƙo mata Dije tayi ta ce "laha'ila wannan kuma Menene wai ku nan birni idan za'ayi girki sai an saga wannan abunne?."
Afeefah ta ce "E, mana ta yadda bazai ɓata kayan ki ba" Dije ta kuma washe baki ta ce "to Balarabiyar india! au Adda Afeefah miye sunan wannan ɗin shi kuma muji idan akwai daɗi.
 Saida Afeefah ta gama ɗaura mata sannan ta ce "cikin murmushi sunan shi apron.

Dije ta ce "aikuwa daga yau na riƙe sunan shi don fita kunya, apron ko kika ce ae,"
Gyaɗa mata kai Afeefah tayi Sannan ta bata kayan vegetables ta ce "ina fatan dai kin iya yankawa ƙanana ƙanwata?," Dije ta ce "E, mana Balarabiyar india sosai ma, na iya a ƙauye.
"Okay to yanka mu gani tunda kince kin iya," ɗauka Dije Tayi ta fara yankawa iya qwarewarta, Afeefah tana lura da'ita tana mamakin yadda yarinyar ta iya aikin highly, don ita da farko ma tayi tunanin yarinyar ba za ta iya aikin komai ba, sai kuma gashi yanzu yarinyar ta bata mamaki.
Kallon Auntie sa'adah Afeefah tayi Sannan ta ce "Auntie jiya naji kamar kince zaki faɗamin wani abu koh, ɗan juyowa Auntie sa'adah tayi tana kallon Dije sannan ta nuna ma Afeefah, Dije ɗin ta ce.
"Ita wannan sunan ta khadijatu kuma ɗiyar  YaYa na da muke uwa ɗaya uba ɗaya dashi ne, mahaifiyarta ta rasu tun tana da shekaru biyu a Duniya, a lokacin naso YaYa na wato mahaifin ta ya bani ita na ci gaba da rainonta tunda kamar yadda aka sani ne ban taɓa haihuwa ba amma Allah bai nufa ba.

A hannun kishiyar uwanta ta taso, matar ba ƙaramin wahalar da'ita tayi ba, don  da kyarma aka samu ta bari aka sakata makaranta na arabic da na boko, to haka rayuwa ta ci gaba da tafiya Dije tana hannun kishiyar mahaifiyarta har ta kawo wannan lokacin sati ɗaya baya, daya wuce ne wai su isu isu ƴan matan ƙauyen wai suka haɗa gasa wai suna gasar SARAUNIYAR KYAU ? sannan tsarin gasar shine, duk wacca tafi kyau to zasu haɗa kuɗin da ƴan kallon gasar suka haɗa, su ba wacca tayi nasara, to ana haka shine fah, ita ma Dijen ƴar ƙaniya da ita, ta shiga kuma taci shine da aka bata kuɗinta a matsayin wacca taci nasarar, ita kuma ba ta ba Ladidi ba, ta yi harkar gabanta dasu, Ladidi wato matar babanta da take riƙonta, shine ita kuma Ladidi taji haushin hakan wanda dalilin kenan da yasa ta kamata ta ɗaure a ɗaki ta mata dukan mutuwa kuma taƙi ta kwanceta abinci ma taƙi bata saida YaYa na wato mahaifinta ya dawo gidan yaga halin da take ciki, a lokacin ranshi ba ƙaramin ɓaci yayi ba, nan dai ya kwanceta ya kawota gurina shine ni kuma na yanke shawarar na kawota nan aikatau saboda na kusa Aure nanda sati ɗaya ne InshaAllah shiyasa jiya kika ganmu da dare, Auntie sa'adah ta ƙarishe maganar tana sauke ajiyar zuciya, duk da cewa yankan kaɗan daga cikin tarihin rayuwar Dije tayi ta ba Afeefah a taƙaice kuma a gajarce don ba duka bane, hasali ma iya labarin da ta ba Afeefah kaɗanne ko na ce kamar talla ne daga cikin labarin rayuwar Dije.

Ita ma Afeefah ajiyar zuciyar ta sauke tana bin Dije da kallon tausayi sannan ta mayar hankalinta kan Auntie sa'adah ta ce "to amma dai hukuma ta hukunta matar ko, dubi yadda duk jikin ta yake a farfashe fa. Tayi maganar tana kuma kallon yadda wasu gurare ajikin Dije suke duk wounds ne.
Hucin takaici Auntie sa'adah ta sauke tana faɗin, "wani hukunci ae ba abinda aka mata hasali ma, shi YaYan nawa da kanshi, ya kasa ko mata kallon banza balle azo maganar hukunci.
Da tsananin mamaki a wannan taƙin Afeefah take kallon Auntie sa'adah ta ce "kamar yaya bayyi mata komai ba kenan kinaso kice min babu abinda aka mata, aka barta ta ci gaba da rayuwa a haka. "E' haka nake nufi" cewar Auntie sa'adah.

A fili Afeefah ta ce "amma wallahi mutumin ƙauye bayyi ba wani lokacin haba dan Allah," Auntie sa'adah tayi murmushi ta ce "gwara dai da kika ce wani lokacin", "sorry for say so, kawai dai abin ne ya bani takaici, Afeefarh ta faɗi hakan ganin yadda yanayin fuskar Auntie sa'adah ɗin ya sauya. Sannan ta ci gaba da cewa.
"Auntie sa'adah amma wallahi, matar nan ta bani haushi sosai, duka duka ita Dijen ɗin nawa take da har zatayi mata abin da tayi," Auntie sa'adah ta ce "ba za ta wuce shekaru goma sha biyar ba, da haihuwarta a duniya," Afeefah taja qwafa tana faɗin, "dama da gani ba za ta haura hakan ba nasani. Oh naji ma kamar kince zakiyi Aure ko?, Yanzu shikenan zaki tafi ki barmu da kewarki?," tayi maganar cike da shagwaɓa da rashin jin daɗi, Auntie sa'adah tayi murmushi tana faɗin "to ba ga Dije ba, ae zata zauna mada dina."
Ita ma Afeefah murmushi tayi ta ce "ae munfi sonki akan ita Dijen ɗin cuz mun daɗe dake highly, don ina ganin kusan six years muke tare dake, ita kuwa kwata kwata jiya tazo, kuma muka fara ganinta.
Da sauri Dije dake yanka onion akan chopping board ta ce "au yanzu, Balarabiyar india kinfi son gwaggo na akaina kenan?," Afeefah ta ce "E, mana nafi sonta akanki sosai ma, kuma sannan  sunan ta ba gwaggo bane, ki dinga kiranta da "Auntie sa'adah" daga yau," Dije ta ce "shikenan naji, kuma nima ta dena cemin Dije sunana Deejarh ko kuma ta ce Nanah, ko kuma dai suna mai daɗi, amma ba irinna ƙauye ba. Afeefah ta ce "Okay, to dai kinji Auntie sa'adah, Deejarh ta ce ki dena kiranta da Dije, sai dai kice Nanah ko Deejarh." Auntie sa'adah ta ce "to to shikenan na dena Dije na," Dije kamar zatayi kuka ta ce "kuma dai kin ƙara faɗar Dijen, Afeefah tana dariya ta ce "to ae ba tashi ɗaya bane zata iya dena faɗa, dole sai da kaɗan kaɗan sannan.
Dije ta ce au bari dai alƙalamina ✍ ya kiyayi rubuta wannan Dijen tunda bataso kar tayimin kuka 😢😂.

Deejarh ta kalla Afeefah ta ce "Balarabiyar india, amma dai zakije ƙauye bikin gwaggona Auntie sa'adah ɗinki ko?," Afeefah tayi murmushi tana faɗin,  idan Allah ya nufa kafin lokacin mun kammala exam a school zani Insha Allah.
Tun kafin Deejarth ta ƙarayin wata maganar Auntie sa'adah ta rigata da faɗin "a'a, ae bama sai kinje ba abin da ba mutane za'a tara ba kawai ɗaurawa ne da tarewa, rana guda, Afeefah ta ce "Okay to Allah ya kaimu musha biki, kuma Allah ubangiji yasa gurin zama ne," Deejarh ta amsa Ameen Ameen Balarabiyar india ta kuma Allah yasa tana shiga wata tara kuma koma suna.
Dukan wasa Auntie sa'adah ɗin ta kaima Deejarh tana faɗin "na shiga tara na ni, Dije yanzu da tsufa na ne zanje ina wani  haihuwa, ae haihuwa yanzu sai yara.
Dariya kawai Afeefah takeyi yayinda take kare Deejarh da ta ɓoya a bayan ta, bakinta bai mutu ba take cewa "ae Yasin gwaggona baki wuce haihuwa ba, kwata kwata shekarunki nawa ne, ae rannan ina jinki lokacin da kike faɗawa Dillaliyar da zaki saya kayan ɗaki gurinta, cewar shekarunki Talatin da tara da watanni ne baki ci ke Arba'in ba, kuma ae ance sai mace takai shekaru arba'in ne ko fiye da haka take dena haihuwa."

"Au kenan ba za kiyi shiru ba ko?," cewar Auntie sa'adah tana hararar Deejarh ɗin.
"A"a Yasin nayi shiru bazan ƙara cewa komai ba, tunda na lura bakya so ina faɗar gaskiyar" ita Deejarh ta ba gwaggon nata amsa tana ci gaba da yanka Albasar hannunta.
Ita dai Afeefah tana jin yadda Deejarh gwaggon nata suke kwasar drama, ita kuma tana kwasar dariya, kwando kwando🤣.

Haka dai suka ci gaba da aikin, suna taɓa fira kuma shan dariyar Dije ta ƙauye da ta rikiɗe ta koma Deejarh a Birni🤓.
Har suka kammala haɗa haɗaɗɗen breakfast  ɗin tare suke jerewa a dinning room har suka kammala jerewa duka sannan  Afeefah ta wuce bedroom ɗin domin yin wanka da Shirin school, ita kuwa Deejarh a faffaɗan plate ta ɗi ba duka kalolin abincin breakfast da suka haɗa, babu kalar da bata ɗi ba  san ranta ba, sannan takai ɗakinta, kana ta dawo ta kuma ɗiban juice ɗin da Afeefah ta haɗa ta koma ɗakinta dashi.

Sai da ta cinye abincin data ɗi bo tas ta kora da ruwa game da sassanyar juice sannan ta tashi ta shiga bathroom wanka tayi ta fito ɗaure da towel, kalolin expensives lotion ɗin da ta gani a saman dress mirror ta shafa abinta ba ruwanta, bayan ta gama shafa lotion ɗin wardrobe ta buɗe inda ta shirya kayanta ta ɗauki wasu riga da zani na atamfa da suka ga jiya suka ga yau, ta saka sannan tasa hula da alama kayan basu da kallabine.
Ɗukar plate ɗin da taci abinci a ciki tayi, ta fito haɗaɗɗen palon gidan da bata gajiya da kallon shi, kitchen ta shiga ta wanke plate ɗin, sannan ta mayar dasu ma'ajinsu ta fito daga kitchen ɗin tana bin palon da kallon ƙauyenci.
Sam bata lura da mutanen dake a dinning table suna cin breakfast ba, don a nata shirmen bedroom ɗin Afeefah take nema, amma batasan ko wannene ba ciki ƙerarrun bedroom's dake zagaye da palon, zata wuce ta koma ɗakinta kenan tunda bata ga ɗakin Afeefah ɗin ba, saidai me?, turus taja tunga ganin mutane a dinning room suna cin abinci, cikin nutsuwa da rashin hayaniya, lura da tayi kamar basu lura da'ita ba yasa tayi sauri zata wuce zuwa ɗakin, karaf taji muryar Afeefah tana kiran sunan ta.

A hankali ta juya ta nufa dinning ɗin, ƙarisawa tayi, gaisar da mutanen gurin tayi, bata jira sun amsa ba, ta kalla Afeefah tana washe baki ta ce "Balarabiyar india gani, naji kamar kina kira na ko?," Murmushi Afeefah tayi ta ce "kinci abincin kin ƙoshi kuwa?," "E, naci sosai plate ɗin ma, na mayar kitchen na wanke tas don nasan gidan ƴan gayu nake, Deejarh ta bata amsar amma hankalin ta yana akan kallon Haleesat da Zaynerb da suke mata mugun kama, bata ganesu ba dan jiya bata gansu ba tadai gane Lailah da su fareeda da fadeela.

Mister mai kyau, Daddyn su Afeefah ne ya kalla Deejarh kallon nutsuwa da nazari irinnasu, sannan ya ce cikin muryarsa mai sanyi da taushi da kuma girma, "ɗiyata ya sunan ki, kuma daga wani gari kike?," A hankali kamar mai tsoron magana ta ce "sunana 'Nanah khadijatu' amma ana cemin Dije a ƙauye a birni kuma Deejarh😅.

Ɗan murmushin manya Daddy yayi sannan ya kalla Afeefah ya ce "wato dai ita ce kenan?, yayi ma Afeefah tambayar ne, don tuni tayi mishi faffaɗan bayani akan Dije ɗin yadda zai fahimta, kuma ya fahimta ɗin highly.
Afeefah ta ɗaga mishi kai alamar 'E, sannan ta kalla Deejarth tana murmushi ta ce "Malama Deejarh, Let me explain my family to you.
Nuna Nainarh tayi sannan  ta ce "wannan sunan ta Auntie Hassana, amma muna kiranta da sister Nainarh ita ce Babba cikin mu, tanada Aure, amma bata haihu ba tukunna, Deejarh ta ce "Allah ya kawo Yaran masu amfani, suka amsa da Ameen, hadda Nainarh wacca da farko ɗaure fuska tayi, amma tanaji ance Allah ya bata Yara ta saki fuska hadda murmushi, don a duniya bata da wani buri da ya wuce ganin ga ta da yaro ko yarinya wata rana, wannan shine burin Nainarh Abubakar Mai Kyau a Duniya.
Afeefah ta nuna Nailah ta ce wannan kuma sunan ta Auntie Hussaina, ita ma muna kiranta da sister Nailah, twins ne ita da Auntie Nainarh ita ma tanada Aure da yaro ɗaya watan shi bakwai a duniya.
Deejarh tayi murmushi ta ce "ae dama daga ganin su anga ƴan biyu yasin, Afeefah ta kuma yi ma ta nuni da Haleesat ta ci gaba da cewa "ita kuma wannan sunan ta Auntie Haleesat ita ma muna ce mata sis leesat a wani lokacin."  Da sauri Deejarh ta ce "Yasin kuma tana kama ƴar indiyar nan miye ma sunan ta ne kuwa?,  Yauwa na tuna sunan ta 'Krithi Shetty, wannan mai dimples din gata kyawawa, Yasin komai nasu iri guda da na wannan Haleesa ɗin."  Dariya sukayi hadda Haleesat ɗin Afeefah ta ce "haka da yawan mutane suke cewa.
Sannan ta nuna Zaynerb tana murmushi ta ce "ita kuma wannan ƴar kyakyawar da kike gani, ita ce my Lovely Aunty sunanta Auntie Zaynerb sannan rana ɗaya aka haifesu ita da Auntie Haleesat."
Deejarth ta ce " ato kice shiyasa naga suna kama, amma sai dai ita wannan, ta nuna Zaynerb ta ce "tafi kama da meliz ta wannan turkish film ɗin 'Elimi Birakma' wato Rayuwata wannan Turkish actress 'Cemre Baysel' Yanayin gashin kanta mai tsayi da sheƙi iri ɗaya da komai ma, Deejarh tayi maganar ne hango gashin kan Zaynerb da ya leƙo ta Hular dake kan Zaynerb ɗin, da tayi.
Sukayi dariya kafin Afeefah ta kuma cewa wani abu Deejarh ta ce "suma sunada Aure ne?," Afeefah ta zaro ido ta ce "Aure kuma?, a'a basu da, Deejarh da mamaki ya kusa kaita zaune ta ce "cabɗi jan ae wa'innan da'ace a ƙauyen mune da yanzu sun kusa Aurar da Yaran su, ma yasin huh, lallai ƴan birni a gaiaheku.
Dariya Zaynerb tayi ta ce "sai dai kuma nan birni ne ba ƙauyen ku ba.

Afeefah ta ci gaba "wannan kuma ta nuna Lailah ta ce sunan ta Lailah kuma ita ɗin, my sweet sister ta ce, kuma ƙanwata ce don na bata wata biyu,  Lailah tayi murmushi ta ce "amma kuma idan aka ganni aka ganki sai dai ace ni ce Babba ko, tayi maganar tana yima Afeefah ɗin  gwalo.
Deejarh  da bakinta baya shiru ta ce "Yasin Auntie Lailah!.
Lailah ta maka mata harara, Deejarh taja bakinta ta ɗinke da allura😬.
Afeefah tayi dariya ta ce "saikuma wa'innan ta nuna su Fadeela sannan ta nuna Fadeelan  ta ce sunan ta Fadeela ita kuma wannan ta kuma nuna Fareeda ta ce sunanta Fareeda suma twin's ne suma, kuma yaran ƙanwar momyn mune." Deejarh ta ce "to amma ina momyn naku take banganta ba?,"  Da sauri Zaynerb ta ce bata jindaɗi ne shiyasa, tana upstairs, Deejarh ta ce "inane kuma upstairs?," Wannan karon Haleesat ce ta magana ta hanyar cewa, "tana nufin tana bedroom ɗinta acan saman bene," Deejarh ta ce "ohooo, au yanzu na fahimta ae. Afeefah ta ce "saini kuma Shalelen Daddynta da Auntie Zaynerb ɗina, Sunana Afeefah Abubakar Mai Kyau,"  Deejarh ta ce "suna mai daɗi, Afeefah ta ce "ga kuma Daddyn mu, Mister Mai Kyau."
Deejarh ta kalla Daddyn tana murmushi ta ce "ina kwana Daddyn mu, nima ka zama Daddyna.
Lailah ta ce "ba kun gaisa ba ɗazu?,"  Deejarh ta ce "E' mana mun gaisa amma wannan gaisuwar ta musamman ce😍.

🆂🅷🅰🆁🅴 🅸🆃 🅿🅻🆂🙏



𝑳𝒐𝒗𝒆💘𝑮𝒍𝒂𝒎𝒐𝒖𝒓💋𝑫𝒆𝒔𝒕𝒊𝒏𝒚😼𝑻𝒐𝒍𝒆𝒓𝒂𝒏𝒄𝒆😥𝑹𝒐𝒎𝒂𝒏𝒊𝒛𝒂𝒕𝒊𝒐𝒏_𝒉𝒊𝒈𝒉𝒍𝒚🌹𝑫𝒆𝒂𝒕𝒉😭𝑴𝒂𝒔𝒕𝒆𝒓_𝒅𝒆𝒗𝒊𝒍👹𝑪𝒉𝒂𝒎𝒑𝒊𝒐𝒏𝒔𝒉𝒊𝒑👑𝑪𝒉𝒆𝒂𝒕𝒆𝒅🤕𝐁𝐞𝐚𝐮𝐭𝐢𝐟𝐢𝒄𝒂𝒕𝒊𝒐𝒏💅𝑳𝒂𝒖𝒈𝒉𝒆𝒅😆𝒂𝒏𝒅_𝒑𝒆𝒓𝒇𝒆𝒄𝒕_𝒄𝒐𝒖𝒑𝒍𝒆𝒔_𝒓𝒆𝒍𝒂𝒔𝒉𝒊𝒐𝒏😇__𝑨𝒍𝒍_𝒊𝒏_S♥a♥r♥a♥u♥n♥i♥y♥a♥r♥K♥y♥a♥u♥____T⋆a⋆k⋆u⋆n⋆_F⋆a⋆r⋆k⋆o

*💋💋S̑̈Ȃ̈Ȓ̈Ȃ̈Ȗ̈N̑̈Ȋ̈Y̑̈Ȃ̈Ȓ̈ K̑̈Y̑̈Ȃ̈Ȗ̈💋💋*

           
*💥𝑇ℎ𝑒 𝐺𝑙𝑎𝑚 𝑄𝑢𝑒𝑒𝑛💥*

Đ₳₲₳ ₳Ⱡ₭₳Ⱡ₳₥ł₦

*💘𝐾ℎ𝑎𝑑𝑒𝑒𝑗𝑎𝑟𝑡ℎ 𝑆𝑎𝑏𝑖'𝑢 𝑌𝑎ℎ𝑦𝑎ℎ💘*

*☆𝑇ℎ𝑒 𝑁𝑎𝑖𝑛𝑎𝑟ℎ 𝐾𝑑☆*

°°°°°°°°°°°°

*💝LAFAZI WRITTER'S ASSOCIATION💝*🤙®
<><><><><><><><><><><><><><><><><><><><><><><><><><><><><

*page 19&20*

Sannan ta kalla Afeefah ta ce "Balarabiyar india, bari na  koma ɗaki, anjima zan fita in ƙara ganin wannan ƙaton ƙerarren gidan, kamar na shugaban ƙasa." Ko kafin Afeefah tayi magana, tuni Haleesat ta riga ta faɗin, "wannan sunan kuma fa?," Deejarh ta ce "wai Balarabiyar india kike magana?,"  Haleesat ta ce "E,Shi fa,"  Deejarh tayi murmushi ta ce "sunan Aunty Afeefah ne, ae nina saka mata, Jiya da dare kuma ya kamata a yanka rago gaskiya."  Lailah ta ce "Yau nake ganin ikon Allah ganin ido na, wai ma dakata, to ae naga babu larabawa a ƙasar india ko?,"  Deejarh ta ce "ae saboda tafi ƴan ƙasar indian kyau ne shiyasa, nake ce mata Balarabiyar india, ko sunan bayyi ba, na canza ya koma Balarabiyar America ko London?," "Aikuwa dai sunan  yayi mata kyau obaa highly, inaga a barshi a Balarabiyar India ɗin kawai zaifi," cewar Zaynerb, tana ƙumshe dariya.
Deejarh ta ce "kunji ƴar gari, Lallai Auntie Zaynerb zamu je ƙasar India dake," Nainarh ce da surutun Deejarh ya fara isarta ta ce, " wannan kyakyawar baƙauyiyar yarinyar akwai surutu kamar xixi, baki kamar radio cicihhh ceee basa gajiya,  Deejarh ta ce "laha'ila wacece xixi?, hala ita ƴar nan gidan ne, Nailah ta ce "E, mana, ƙanwar mu ce ae," "to tana ina?," Deejarh ta tambaya, Afeefah ta bata amsa da faɗin, "tana karatu a outside," "oh oh inane kuma outside?," Deejarh ta kuma tambaya tana qwalalo ido. Lailah wacca Ƙauyancin Deejarh ya dena bata haushi sai ma dariya, ta ce "tana nufin tana karatu a ƙasar waje ne, are you clear," Deejarh ta ce "au au yanzu na fahimta ae, kallon Afeefah tayi ta ce "Balarabiyar india zan tafi," Afeefah ta gyaɗa mata kai, ba tare da ta ce komai ba, don ta fahimci yarinyar akwai surutu obaa.
Ita kuwa Deejarh barin  dining room ɗin tayi ta koma bedroom ɗin da yake matsayin nata a halin yanzu.
Bayan Deejarh tabar gurin Fareeda sarkin gulma, ta ce "gata ƴar kyakyawa abin ta," ita ma Fadeela ta amshe da faɗin "gata bata da duhun kai irinna wasu ƴan ƙauyen, sannan abin da na fahimta da ita shi ne, tana da saurin sabo, Nainarh ce wacca surutu, bai dameta sosai ba, ta ce "barin ma dai idan tana zubo turancin ta na ƴan koya, abin har dariya yake bani, sai dai ta burgeni, don tafi wasu."  "turanci kuma, ita ɗin?," Haleesat ta tambaya a mamakance, "E, mana"  Nailah ta bata amsa, Haleesat ta ce "yaushe tayi turancin, ban sani ba?," Afeefah tana dariyar ganin yadda Haleesat tayi tambayar idanu waje, ta ce "jiya ne fa, da dare,"  Fareeda ce yanzu tayi magana, "ae wallahi ina faɗa muku, nasha mamaki, duk da cewa ba turancin azo a gani tayi ba, sai dai, nima ta burgeni, ba ƙarya."  Fadeela ta ce "ah gaskiya kam, tayi ƙoƙari, ba laifi."

Deejarh kuwa tana komawa ɗakin ta, kai tsaye bathroom ta shiga, brush tayi kamar yadda tasa ma ranta, sannan ta fito ta kwanta a saman gadon da yake matsayin na ta, kamar da wasa bacci ya kwasheta saman bed ɗin.
Bata fi minti goma da kwanciyar ba, Afeefah ta shigo bedroom ɗin, ganin tana bacci ne yasa tayi murmushi sannan ta rufe mata ƙofar ta fita, da ma school zasu wuce ta ce, bari ta shigo ta ga baƙuwar tasu.

Deejarh ba ita ta tashi daga baccin daya ɗauke ta ba, sai wuraren karfe ɗaya na rana.
Addu'ar tashi daga bacci, ɗauke a bakinta lokacin da ta farka, kai tsaye ba tare da wani ɓata lokaci ba, bathroom ta shiga tayi wanka haɗe da alwala, bayan fitowarta doguwar riga tasa a jikinta, bata tsaya shafa kalolin lotions da suke a saman dress mirror ba, sai da ta idar da sallan sannan ta shafa lotion ɗin da ta shafa da safe, bayan kammala shafa lotion ɗin, hular rigar jikinta ta ɗauka ta saka.

Sannan ta fita waje can farfajiyar gidan garden ta fara zuwa tasha kallon bishiyun kayan mar mari kala kala, kuma ko wata bishiya ta gani indai taga zata iya sai ta hau, saman bishiyar ta cinka ƴa ƴan bishiyar saboda tsaban ji da ƙauyanci, daga garden kai tsaye haɗaɗɗen swimming pool ɗin, gidan ta wuce, aikuwa tasha kallon ikon Allah, dan lokacin da ta ga yadda ruwan waterfall da yake launin sky blue, na gurin yake spray yana zuba ƙasa abin ba ƙaramin burgeta yayi ba, nan ba tare da wani ɓata lokaci ba, ta ƙarisa gurin ta shiga cikin ruwan tana wanka, tafi ƙarfin sama da mintuna ashirin a haka, sannan ta wuce can wani keɓantaccen guri cikin gidan, gabaɗaya gurin haɗaɗɗun kejuna ne wanda cikin ko wannen su, wasu irin wild animals ne, na cikin daji ake kiwon su, a gurin, tun daga kan, Tsuntsaye masu kyau da ban sha'awa, sai faman karkaɗa wing's nasu suke, ga kuma, wasu karnuwa da launin su yake sky brown irinna turawa, da dai dabbobi kala kala, da yawa a gurin waɗanda lokaci bazai bari nayi bayanin su ba.

Daga nan kaf girman gidan da faɗin shi, ba inda Deejarh bata leƙa ba, tasha kallon tsaruwa da kyau, sai dai tasha ƙauyanci, dan baki wangale take kallon komai.
Bayan ta gama ƙauyancin nata da ƙarewa gidan kallo san ranta sannan ta wuce BQ wajen gwaggon ta, Auntie sa'adah ta ɗan daɗe a gurin gwaggon na ta har wajen la'asar, sai da tayi sallan sannan ta bar ɓangaren.
Ta dawo cikin katafaren palon gidan, ko ɗakinta bata shiga ba ta ƙarisa main palon inda ta hango mutane zazzaune, su Nainarh ne suke kallon wani indian drama "Nannaku prematho" can gefe kuma Afeefah ce ita da Lailah karatu sukeyi, da sauri ta ƙarisa gurin su tana faɗin, "lah Balarabiyar india, yaushe kuka dawo gidan bansani ba?."
"Ah to dama, yaushe zaki sani, bayan kina can wajen yawo, da nuna ƙauyanci, nasan zuwa yanzu kaf ma'aikatan gidan nan babu wanda baisan da zuwan ki ba." Lailah ce tayi ma ta maganar tana ɗan hararar ta.
Washe baki Deejarh tayi ko'a jikinta da irinna maganar da Lailah tayi ma ta, taja wata uwar ajiyar zuciya irinna ƙauyanci, ta ce "hum hum humm, ae ina faɗamiki Auntie Lailah yau nasha kallo, ni ce gurin ruwan feshi, ni ce gurin sam pool, {wai fa swimming pool, take nufi} ke na ƙare miki zance ma, ni ce har gurin bishiyar mangwaro na hau na  tsinkosu da yawa," kallon ta Lailah tayi da tsakanin mamakin yarinyar da ya kusa kai ta ƙasa, badin ta na zaune ba, ta ce "bishiya fa, kikace kin hau ?," Deejarh ta kuma Washe baki ta ce "sosai ma, Auntie Lailah dan ma na shanye mangwaron ne, lokacin da na je gurin gwaggona da kuke kiranta da "Auntie sa'adah" da kin gansu jajaye ga daɗi, gasu nunnanu yasin."

Lailah ta ce "amma dai kinyi wanka da kika dawo ko?," tayi ma ta tambayar tana bin ta da wani irin kallo. Deejarh ta ce "a'a banyi ba, yanzu fa na shigo, kuma ae nayi wanka ɗazu kafin nafi ta,"  Lailah da takeji kamar takai ma ta mari, ta daure ta ce "naji to jeki ki ƙarayi indai kinaso mu shirya ni dake."
Tashi tayi saboda bata so ta ɓata musu rai aƙi sakata makaranta, zata bar gurin ta kalla Afeefah ta ce "hala yau Balarabiyar india tana a zumin magana ne?," murmushi Lailah tayi ta ce "wai Afeefah kike magana, rabu da wannan intern ɗin kawai, don karatun exam ya ɗau wuta, obaa highly." Deejarh da bata jin magana ta ƙyale ba tayi magana ba, tana shirin shiga ɗakinta ta ce "Auntie Lailah Menene kuma intern?," Lailah ta ɗaga murya yadda Deejarh ɗin zataji ta ce "ɗaalibar kwalejin likita,"  Da sauri Deejarh ta tsaya daga shiga ɗakinta da zatayi ta ce "dama Balarabiyar india likita ce?,"  Lailah ta ce bata riga ta zama likitan ba, tukunnan tana dai karatun," Deejarh ta ce "Yasin kuma likitanci zai mata kyau,"  ta faɗa lokacin da take shiga ɗakinta.

Lailah tayi murmushi ta ce "wannan yarinyar ƙauyen, aku kenan mai bakin magana, wai ace daga zuwanta gidan nan, jiya har na ɗan fara sabo da surutunta."

Suna zaune can sai gata ta fito yanzu riga ce na material ash doguwa a jikinta, sai hular saƙa irinna sanyi, da ta saka Ita ma ash color rigar taji duniya ba laifi, don harda faji gefan ta, wannan karon ba gurin su Lailah taje ba ƙarisawa cikin palon tayi wajen su Nailah tayi sannan ta zauna a saman kujera mai ɗaukar mutum biyu, ba ruwanta, kallon Nainarh tayi ta ce "Auntie Nainarh ina ne ɗakin momyn naku na gaisheta naji ɗazu Antie Zaynerb ta ce bata jindaɗi."
Nainarh da surutun yarinyar baya burgeta ta ce "sama zaki hau room na biyu zaki shiga," ta bata amsa a gajarce. "to" ta ce tana miƙewa ta nufa benen sai kuma ta tsaya tana kallon twin's staircase ɗin dake gaban ta ga kuma wani staircase daga right ɗin ta wanda shi ɗaya ne, bawai twin's ba.
Rasa wanne zata bi tayi, juyowa tayi tana kallon, Nainarh ta ce "Auntie wanne zanbi ne?, naga abin naku kashi uku ne," Nainarh ta ce "kibi Right kawai."

'To ta kuma cewa sannan ta fara taka staircase ɗin, har ta hau sama, "Yauwa yanzu, na wuce room na ɗaya, ta faɗa a lokacin da ta wuce gurin, ɗaki na biyu ta shiga.
Da shigarta wani irin ƙamshi wanda tunda take a duniya bata taɓa shaƙar mai kala dashi bama, balle shi, ya ziyarci duka ƙofofin hancinta, ae ba shiri ta lumshe idanun ta tana kuma shaƙar ƙamshin da kyau, huh mutumiyar taku fa, ita da tazo duba mara lafiya sai ta ɓige da kallon irin kyau da tsaruwar bedroom ɗin, a fili ta ce "cabɗijan wannan ɗakin yasin kona matar shugaban ƙasa albarka, wannan kyau da tsaruwa haka, ah lallai birni ana murewa," haka dai ta dingi sambatu, tana ƙarewa ɗakin kallo, san ranta, Sannan ta fito ganin da tayi matar tana bacci.
Ƙasa ta sauko ta zauna a kujerar da ta fara zama, Nailah ta ce "duba mara lafiyar ne kika daɗe haka?," Deejarh tana ƙumshe dariya ta ce "na tsaya na tayata fira ne ae."

Ta farka ne?, Lailah ta tambaya, Deejarh ta ce "E, mana, amma ta koma, lokacin da zan fito," sannan ta kalla Nailah ta ce "Aunty wai ina waɗannan ƴan biyun?, naga bangansu ba." Nailah ta ce "wai Fareeda da Fadeela kike nufi?," ta ce "E, su," "Allah sarki ae sun tafi gida, tun ɗazu," Nailah ta bata amsa.
Deejarh ta ce "Allah sarki anan garin suke ne?," Nailah ta ce "E,

Afeefah ta kalla Deejarh ta ce "wai kina ganesu ne, ko kuwa kawai kina cinkai sunan nasu ne?," Deejarh ta ce "waisu Auntie Nainarh kike nufi?, ina gane su sosai ma," "Okay tunda kince haka, to nunamin Auntie Nainarh, a cikin su, cewar Lailah, dan ta ƙure ta.
Deejarh ta miƙe ta ƙarisa gurin Auntie Nainarh tana karɓar jaririn Nailah dake hannunta, ta ce "wannan ita ce Auntie Nainarh," Afeefah da ɗan mamaki a fuskar ta, ta ce "ya akayi kika ganeta?," Deejarh tayi murmushi ta ce "ae ita Auntie Nainarh tanada tawadar Allah a gefen fuskarta ta gurin kunen ta na hagu, ita kuma Auntie Nailah a akan hancinta tawadar nata yake, wannan shine abin da yasa, na gane ko waccensu." Lailah ta ce "aikuwa kin cinka dai dai, sai dai kuma!, maganar dake bakinta da take ƙoƙarin fito dashi waje, ne ya tsaya cak sakamakon mutanen da taga sun shigo palon kamar an korosu..
Zaynerb ce ita da Haleesat suka shigo palon a tare suna sauke haki da alama sun sha gudu, Zaynerb ta zube a saman sofa 1sieter tana faɗin "Huh sister mun tsira," Nailah ta ce "lafiyar ku, kuwa kuka shigo ba sallama kamar an je foku?."
Haleesat ta ce "ae gwara ace jefomu akayi, da dai wannan uban gudun da muka sha, kamar marasa gata."
"Ikon Allah meya faru ne wai," Afeefah ta tambaya. Zaynerb tana jire hijjab ɗin jikinta ta ce "kedai barmu kawai, ina wannan karen gidan Sunainah ɗin, tofah shine ya biyomu, unfortunately.
Lailah tana gyara zama ta ce "ah ah yau kuma, ita Sunainarh ɗin, ta tashi daga Ummyn Farhana ne, ta koma 'Sunainah' ga tsau, ko dai duk cikin wahalar ne, nifa wallahi wannan, shegen karen ne, yasa banason zuwa gidan, kare kamar zai cinye mutum ɗanye wai ma, ya akayi ma karen ya biyo ku ne, ba an ɗaureshi ba?,"

Zaynerb tana galla mata harara ta ce "wani an ɗaureshi?, to mudai a kwance muka ganshi kuma fa, a ƙofar gidan, shine shi kuma bawan Allah, bamu kulashi ba, ba muyi komai ba, ya biyomu shine fa, ita kuma wannan matsoraciyar, Haleesat tayi gudu nima na mara mata baya, shima kare ya mara mana baya, nan aka shiga tsere."

"Kin ji ki, bake ki ka fara gudu ba, ni kuma da naga zayyo kaina, na biyo ki a tamanin?."

Haleesat ta faɗa Ita ma tana cire zumbulelan hijjabin jikinta.
Lailah tana dariyar shaƙiyanci ta ce "wai waya ga, su Auntie Zaynerb ana gudun kare, ga wannan zumbula zumbulan Hijjaban da kuka saka, ae dole kare ya biyo ku."

Haleesat tana dariyar abin da ta tuno ta ce "hahaha saima kinga yadda Zaynerb tayi lokacin da muka iso nan gidan, ƙofar gate a rufe, yi tayi kamar zata tashi sama, dan tsoro, aikuwa ina baki story, gate man yana buɗewa ta kusa haɗawa dashi wajen shigowa."

Zaynerb taja qwafa tana faɗin "ae kuma dai, ni da ƙara zuwa gidan Sunainah sai wani jiƙon wallahi....

Sudai su Nainarh ba abin da sukeyi sai dariya, Deejarh saboda tsaban dariya sai da ta kusa yarda jaririn Nailah dake a hannunta, yi take ba ƙaƙƙautawa.
Gabaɗaya suka zuba mata ido suna kallon ikon Allah, Lailah ta ce "wannan fa?, kodai tanada aljanu ne bamu sani ba?, "ke Deejarh lafiyar ki qalau kuwa?," cewar Afeefah a ɗan tsorace dan duk a zaton ta, kodai aljanun Deejarh ɗinne na dariya, suka tashi...

Saida tayi ma'ishi sannan ta dakata, dan kanta....
"kingama, nace kingama?,"  Lailah ta tambaye ta, tana galla mata harara...
aikuwa kamar ta ce ta ci gaba ta kuma fashewa da dariyar, Lailah ta ce "Auntie Nailah ki karɓa ɗan ki, a gurin wannan susuwar yarinyar idan kuma ba, haka ba tom."
Sai a lokacin ta dakata da dariyar, Afeefah ta ce "miss laugh, to dariyar me kikeyi?," Deejarh ta ce "kawai na tuna lokacin da karen gidansu habbulle ne, ya taɓa biyomu ni da ƙawata Hameeda, ranar sallah lokacin munje gidan kaimusu abincin sallah, ƙarshe abincin nan a jikin Hameeda ya zube tass, shikuma kare yace wana kama a lokacin saida ya ciza Hameeda mugun cizo...."
"Ke kuma ya kika ƙare kenan?,"  
Lailah ta tambaye ta, Deejarh ta ce "na zomo mana na ranta a dubu na bar gurin, sai gida....

Zata kuma magana sukaji ana knocking ƙofar palon tun kafin wani ya miƙe Deejarh ta miƙe taje ta buɗe, mai gadi ta gani "lafiya kuwa," ta tambaye shi, jaka ya miƙo mata yace "wannan na Madam Zaynerb ne tayar garin gudu," karɓa tayi sannan ta mishi godiya ta dawo palon ta miƙama Zaynerb tayi ta ce "gashi Auntie Zaynerb kinyar garin gudu, inji mai gadi."

Karɓar jakar Zaynerb tayi tana faɗin "aikuwa dai, garin gudu na manta nayar da ita wallahi naga mutuwa.
Haleesat ne ta kalla Nailah ta ce "Auntie yaushe zaki koma ERITREA ɗinne?."

Kai tsaye Nainarh ta bata amsa da "bayan gasar su Afeefah mana," su duka kallon ta sukayi Lailah ta ce bayan gasa kuma, Nainarh ta ce "E. mana ko akwai matsala ne?,"
"Kema dai kinsan Daddy bazai barki ki zauna ba, bayan ga mijin ki can a wata uwa duniya ƙasar ERITREA ko?," cewar Zaynerb, Nainarh ta ce "to ya ya kukeso nayi sucan sunce tunda ni juyace aure zasu ƙara mishi, wacca zata haifa musu jika,"
"aure kuma, auran lafiya kwata kwata shekaru nawa ne da bikin naku da za'a ƙara mishi mata haba, sufa larabawan nan shiyasa ba burgeni suke ba, don sun cika nuna ƙabilanci."
Lailah tayi maganar da alama ranta ya ɓaci highly. .

"Shekaru uku ne kacal da auren," Nainarh ta bata amsa, Nailah ta ce "dama can sunada niyyar su ƙara mishi matar ne, ƴar ƙabilansu da zasu wani ce saboda bakya haihuwa inaga aishi haihuwa lokaci ne ko,"
Ajiyar zuciya Afeefah ta sauke sannan ta ce "yanzu ba wannan maganar ya kamata ayi ba,"
"to maganar me za'ayi Haleesat ta tambaye ta, ta ce "kamata yayi ta samu ta koma ta gyara zaman ta da mijinta, tunda suna son junansu, wannan zuwan da tayi shine zaisa suji daɗin aura mishi balarabiya ƴar uwarshi ae a nawa tunanin."

"Ba laifi kin kawo shawara," cewar Zaynerb..
 Lailah ta ce "ni dama shiyasa soyayya bata dameni ba kiga anyi auren soyayya daga baya anzo ana samun matsala kamar da ba'ayi soyayya ba kamar ba gobe.

Nailah ta ce "au wai har yanzu Lailah kina ɗauke da wannan ra'ayin naki naƙin soyayya?,"

"of course yes,"

Lailah ta bata amsa, Nailah ta kuma cewa "anya ke macece kuwa?, gaskiya ina tantama," zaro ido Lailah tayi ta ce "ni macece mana me kika gani?," ɗan jim Nailah tayi sannan ta ce "banga alama ba, ke bakyajin irin wannan feeling ɗinne da akeji?."

Kwashewa da dariya Lailah tayi harda clapping finger's, sai da tayi ma'ishi sannan buɗar bakinta ta ce "banaji ni banma sanshi ba, Yasin.......
Gabaɗaya palon suma suka kwashe da dariyarta, Zaynerb ta ce "anya kuwa Lailah kina lafiya qalau kuwa, Nailah ta ce

 "yauwa sis tambaya mana ita dai."
Lailah ta ce "kai mai kuka mayar dani Yasin lafiya ta qalau ba zaku fahimta bane kawai, Afeefah ta ce "kece dai bazaki fahimtar damu ba," Nainarh ta ce "ke Afeefah ai inaga idan ana maganar masu lafiya baza'a sakaki ciki ba," tayi maganar tana ɗaukar remote ta canza channel zuwa wani chinese drama LOVE DESIGNER....

Afeefah ta ce "saboda mene baza'a sakani a ciki ba?,"  Nailah ta bata amsa da "saboda gwara Lailah ma akanki ke ko maganar soyayya ni bantaɓa ji ko ganin kinayi ba,"

Ajiyar zuciya Afeefah ta sauke sannan ta ce "hakuri nasara ne! haka zalika aure lokaci ne!, Soyayya kuma sai nayi thinking akai😝..

Lailah ta ce "akwai wanda kike hakurin jira ne, Afeefah ta amsa da "a'a."
Lailah ta ce "ae na ɗauka sabbir kike jira,"
"Wanene sabbir kuma?," Zaynerb da Haleesat suka haɗa baki wajen tambaya, da sauri Afeefah ta ce "ah shiɗin saurayin Lailah ne."
"Saurayin Lailah kuma?, Nainarh ta tambaya da ɗan mamaki sai kuma tayi murmushi ta kalla Afeefah ta ce "bamu ruwan labari mutsa ƴar uwa," Afeefah ta gyara kwanciyar ta a saman two sieter da take sannan ta fara magana.....
"a birthday partyn wata Zahrah c.m ɗinmu muka haɗu dashi shi kuma yaga Lailah ya faɗa kogi,"

"Amma Afeefah kina ruwa wallahi," cewar Lailah jin ƙaryar da Afeefah ta zubo.
"kusada breaker ma kuwa🤣"
Afeefah ta bata amsa hadda mata gwalo, Lailah tayi murmushi, "aikuwa da gaske ne tunda kukaga tana murmushi cewar Nailah, da sauri Lailah ta ɓata fuska ta ce "Allah kuwa,  bada gaske bane."
"ba wani nan kedai kawai kin faɗa gaskiya," Haleesat ta faɗa, shiru kawai Lailah tayi dan tasan koda ta faɗa musu gaskiya ba yadda zasuyi ba tunda Afeefah ta riga da ta mata sharri, haka suka cigaba da fira abin gunin ban sha'awa suna haɗawa da flirting.

🅺🅰🅽🅾

   

*

𝑊𝑢𝑟𝑎𝑟𝑒𝑛  𝑘𝑎𝑟𝑓𝑒 𝑏𝑖𝑦𝑎𝑟 𝑛𝑎 𝑚𝑎𝑟𝑒𝑐𝑒

Zaune take a bakin swimming pool, yayinda kyawawan ƙafafunta duka biyun suke cikin ruwa, tana lilawa a hankali da alama yanayin da ake ciki yana mata daɗi, kamar ko yaushe sanye take cikin ƙananan kaya Riga top white color, mai zanen stairs c.green sai wando shima crazy jeans c.green, sai hular vani ita ma white color saman hular anyi rubutu da zare c.green an rubuta  '𝐺𝑙𝑎𝑚' da ƙananan baƙi, wayarta ne a hannunta na dama tana tsalawa.

Can gefe kuwa Bilki sai faman safa da marwa takeyi takai mari takai goho, doguwar rigar atamfa ce a jikinta mai dogon hannu gaban rigar kuwa anyi ado da flowers masu kyau wa'inda suka ƙarawa ɗinkin kyau, sai kuma ɗan kwalin rigar datayi ɗaurin ture kaga tsiya.

Da ta gaji da safa da marwan saita ƙarisa gurin da Jieddarh, take ita ma ta sama guri ta zauna sannan ta kalla Jieddarh ta fara magana a hankali kuma cikin damuwa.

"Jieddarh na kasa nafa kasa, Jieddarh Yasi  na kasa," haka kawai Bilki take ta faman faɗa tana ƙarawa kamar mai bitan karatu.

Kallon ta Jieddarh tayi da ta isheta ta ce "malama kinfa isheni da surutu, waima miye kika kasa ɗinne?,"
Ajiyar zuciya Bilki ta sauke sannan ta ce "nakasa shawo kanshi, mana," dariya Jieddarh tayi ta ce "au ni sai yanzu ma na fahimci abinda kike nufi, ae kece bakiyi yadda zai kulaki ba, kuma ai nace ki dena kallon shi idan yana guri, amma kinƙi ji, Bilki taja ajiyar heart sannan ta ce "wallahi Jieddarh ba zaki fahimci yadda nakeji bane amma kamar kullum yauma na miki uzuri saboda bakisan Menene Love bah💘

"Toki faɗamin Menene Love ɗin mana," cewar Jieddarh, Bilki ta ce "nidai ba take nake ba, yanzu nasan ya kusa dawowa daga office kuma inaso na ganshi amma ba dama,"

Jieddarh ta ce "akwai dama mana kala kala ma saidai idan kece bazaki iya amfani dashi ba,"  Bilki ta ce "kamar yaya bazan iya amfani dashi ba, ki faɗamin nikuma zanyi iya bakin ƙoƙarina, don naga nayi amfani dashi."

Jieddarh ta ce "da gaske kikeyi, Bilki ta ce "of course kuwa," Jieddarh ta miƙe ita ma Bilkin miƙewa tayi.
Saida Jieddarh tasa flat shoes ɗinta sannan ta riƙo hannun Bilki tayi gaba ita ma Bilkin tabi bayanta kamar raƙumi da akala....

Cikin palon gidan ta nufa da ita saida ta tsaya ta canza shoes ɗinta da na shiga palon, a gurin da aka tanadar domin ajewa kafin a shiga palon sannan suka shiga cikin main palon ba kowa saida suka tsaya a tsakiyar palon sannan Jieddarh ta saki hannun Bilkin.
Ita dai Bilki tana kallon ikon Allah daga cewa a bada shawara.....

White curtains ɗin Window's na palon Jieddarh ta yaye ta hango motar Heesham Benz Ash color ana parking ɗinta a parking lot, da alama shine ya dawo daga office, da sauri ta saki curtains ɗin ta koma wajen da ake aje mopper ta ɗauko ta miƙawa Bilki ta ce
"riƙe na faɗa miki kalar dramar da za'a shirya," karɓar mopper ɗin Bilki tayi, da sauri Jieddarh ta raɗa mata abin da zatayi a kunne, murmushi Bilki tayi takai ma Jieddarh duka tana murmushi Ita ma Jieddarh murmushi takeyi ta kauje da sauri ta koma wani korido ta tsaya sannan ta lalubo wayarta ta shiga camera.
.

Ita kuma Bilki ta fara mopping tana raira waƙa kamar da gaske😅

A daidai lokacin kuma Heesham ya turo ƙofar palon ya shigo bakin shi ɗauke da sallama, da sauri Bilki ta amsa ta tsuguna zata gaisheshi daidai lokacin kuma wutar lantarki na palon ta ɗauke, ihu Bilki ta kurma ta ɗafale a ƙirjin Heesham Like a little baby dai dai lokacin da wutar ta dawo ita kuma Jieddarh ta fara zuba musu pictures kala kala saida tayi wajen kala biyar sannan ta tsaya.

Ita kuwa Bilki ƙara ɗafale Heesham tayi ta rumshe idanun ta tana faɗin.
"wayyo duhu yaya heesham ka taimakeni duhu banason duhu zan mutu." Haka kawai take faɗa tana ƙarawa-Shikuwa bawan Allah Heesham gabaɗaya jikin shi ya mutu ƴar gajiyar daya kwaso sayya nemeta ya rasa, ga Bilki ta ɗafale mishi a ƙirji gabaɗaya sayya tsinci kanshi cikin wani hali wanda ba'a faɗa.
A hankali yake ɗan shafa bayanta alamar rarrashi kamar yana lallaɓa karamar yarinya cikin kunen ta ya raɗa mata.
"ki buɗe idonki wutan ta dawo kinji?,"  yanayin yadda ya mata maganar ba ita ba hatta Jieddarh dake laɓe ta korido tana leqen su saida tsigar jikinta ya miƙe, ai ba shiri Bilki ta sauka ƙasa tana sunkayar da kai da gudu ta ɗauka mopper ɗin ta bar gurin a three sixty 360😃

Murmushi yayi yana shafa sumar kanshi sannan ya ɗauka briefcase ɗinshi da ta faɗi tun lokacin da Bilki tayi hugging ɗinshi, kana ya fara taka staircase's in twin's ya nufa part ɗinshi..

Saida ya ƙule sannan Jieddarh ta fito daga muɓoyarta, ɗaura hannu biyu ƙugu tayi tana bin staircase's ɗin da kallo kamar mai neman wani abu.
Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta fita daga palon  swimming pool ta nufa dan tasan acan zata sama Bilki.
Ilai kuwa tana ƙarisawa taji an rungumo ta baya da sauri ta juya sai taga Bilki bakin nan kamar gonar auduga saboda fara'a, dariya kawai Bilki takeyi tana faɗin Jieddarh "nagode nagode sosai, highly obaaa."

Tureta Jieddarh tayi tana faɗin "zaki ɓallani fa," dariya Bilki ta kuma yi ta ce "kece Jieddarh akwai basira yasin,"
Ɗan murmushi Jieddarh tayi tana miƙama Bilki wayarta ta ce "ai ina faɗamiki daga yau kisa ido kawai zakiga canji," karɓar wayar Bilki tayi tana faɗin "Menene zanyi da wannan wayar da kike bani", ai bata rufe baki ba ta daka tsalle ganin pictures ɗinsu ita da masoyinta Heesham kala kala ƙara hugging ɗin Jieddarh tayi tana faɗin wayyo Jieddarh "na nagode miki sosai, kai gaskiya kinyi a rayuwa."
Murmushi Jiedarh tayi ta ce "kedai Bilki wannan duk a cikin soyayyar ne?,"  ta tambaya  a lokacin da ta koma ta zauna akan ɗaya daga cikin resting chairs dake a gurin...

*💋💋𝑆𝐴𝑅𝐴𝑈𝑁𝐼𝑌𝐴𝑅 𝐾𝑌𝐴𝑈💋💋*

*👑𝑇ℎ𝑒 𝐺𝑙𝑎𝑚 𝑄𝑢𝑒𝑒𝑛👑*

*𝑊𝑟𝑖𝑡𝑖𝑛𝑔 & 𝑆𝑡𝑜𝑟𝑦 𝐵𝑦*

*𝐾ℎ𝑎𝑑𝑒𝑒𝑗𝑎𝑟𝑡ℎ 𝑆𝑎𝑏𝑖`𝑢 𝑌𝑎ℎ𝑦𝑎ℎ*

{♥︎𝑇ℎ𝑒 𝑁𝑎𝑖𝑛𝑎𝑟ℎ 𝑘𝑑♥︎}

💘*𝘓𝘈𝘍𝘈𝘡𝘐 𝘞𝘙𝘐𝘛𝘛𝘌𝘙𝘚 𝘈𝘚𝘚𝘖𝘊𝘐𝘈𝘛𝘐𝘖𝘕*💘🤙

<><><><><><><><><><><><><><<><><><><><><><>><><><><><><

*page 21&22*

...A hankali ta lumshe idanun ta tana faɗin "oh Allah ko nima yaushe zan haɗu da masoyina na gaskiya ne?."
"Nan bada daɗewa ba Insha Allah, zaki haɗu da Yariman ki, ƴar uwa,"
Taji muryar Bilki tana faɗar haka, ɗan waro ido tayi dan batayi tunanin a fili tayi maganar ba, a hankali Bilki ta dawo kusada Jieddarh ta zauna a ɗaya daga cikin kujerun tana faɗin.
 "Insha Allahu nan bada daɗewa ba inaji a jikina, kema zaki haɗu da naki Jarumin bi'iznillah, ɗan dariya Jieddarh tayi ta ce "Bilki kenan bazaki fahimta bane kawai," Bilki ta ce "ki fahimtar dani mana?,"
Gyara kwanciyar ta tayi a kujerar sannan ta ce "abar maganar kawai,"  Bilki tana dariya ta ce "a'a wallahi da dai an ci gaba saboda inajin daɗinta,"
Murmushi Jieddarh tayi ta ce "Bilki anya kuwa an taɓa faɗamiki kin zare?," dariya Bilki ta kwashe da shi sannan ta ce "a'a gaskiya ba'a taɓa faɗa ba, amma yau anfaɗa,"
 Murmushi Jieddarh ta kuma yi, "Bilki kenen YOU CRAZY IN FALL IN LOVE ❤.

"Kinsan miye kuwa?,"  Bilki ta tambayi Jieddarh, a hankali Jieddarh ta girgiza mata kai alamar a'a.
Bilki ta ce "yau sai naga kamar ba ƙya cikin special mood fa," "saboda me kika ce haka?,"  Jieddarh ta tambaya, Bilki ta ce.

"Hausawa sukace maganar zuciya a tambayi fuska, alasa nayi hausar dai dai, kinsan hausan nawa sai aslowly fa, abinki da bafulatana,"
Fashewa Jieddarh tayi da dariya, "wai maganar zuciya a tambayi fuska wannan hausan fa, cewar Jieddarh still cikin dariya.
Ita ma Bilkin dariya tayi dama tayi hakan saboda taga fara'ar Jieddarh ɗin ne kuma tayi winning tunda ga Jieddarh tana dariya harda ƙyaƙyatawa.

Gyara zamanta tayi a kujerar tana fuskan tar Jieddarh ta ce

"kinsan wani abu kuwa?,"

"a'a saikin faɗa,"

Bilki ta ce "ina faɗamiki a lokacin da zaki haɗu da yarimar ki zaizo miki yana akan farin doki fuskar shi ɗauke  da ƙayataccen murmushi idanun shi ɗauke da kallon ƙauna zuwa gareki, zai ɗaukeki ya ɗauraki saman farin dokin sa, kuyita zagaye fili sirdi, abinku cike da farin ciki kuma.....Da sauri Jieddarh ta dakatar da ita ta hanyar faɗin "wait a minutes  tsaya_tsaya yarima kikace fa, please faɗamin a wani film kika kalla, hala dai indian film ne nasan sune suke irin wannan labarin soyayyar........Jieddarh tayi ma Bilki tambayar tana zaro ido haɗe da jiran amsa.

Dariya Bilki tayi tana faɗin, "a'a ba'a film na kalla ba, inaji ajikina dake zai faru, haka kawai nakeji a jikina ɗan sarki zaki aura dan dashi kika dace, domin keɗin matar saraki ce, haka zalika matar manya,"  wayyo Allah na harna fara hangoki a gidan sarauta kina zuba mulki, kuma zakiyi kyau da zama gimbiya yasin.....

Dariya Jieddarh keyi tsaban dariya hadda riƙe ciki jin abin da Bilki take faɗi.
Bilki ta ci gaba da cewa "dama kawai ranar gasar nan kiyi shigar sarauta nasan zakiyi kyau, ba kaɗan kaɗan ba."

"to za'ayi kamar yarda kika faɗa your highness, cewar Jieddarh cike da nishaɗi tana sakin murmushi a lokacin da tayi imagine gata cikin kayan sarauta wow abin ba'a magana is so sweet.

Jin ana kiran sallan magarib ne yasa suka tashi a tare suka nufa ciki, yayinda Bilki ta wuce BQ ita kuma Jieddarh ta shiga ciki a main palo ta sama ƴan gidan gabaɗayan su amma banda Heesham, Auntie ne sai aAbba (Alhaji Jafar Komai Naka) da kuma Humaira, magana suke amma tana shigowa sukayi tsit, bata kawo komai ba, ta gaisar da Abba ta haye sama Bedroom ɗin ta domin yin sallah.

________________________~~~~
ɯαʂԋҽ ɠαɾι
-----------------------

ɯαʂԋҽ ɱιʂαʅιɳ ƙαɾϝҽ ɠσɱα ʂԋα ԃαყα ɳα ʂαϝҽ

ʝιҽԃԃαɾԋ

Zaune take a palo saman kujera mai ɗaukar mutum ɗaya gefenta kuwa, Bilki ce tana mopping a palon suna taɓa fira kaɗan kaɗan don Jieddarh tafi mayar da hankalinta akan tv tana kallon wani ƈԋιɳҽʂҽ ԃɾαɱα ~ρɾιɳƈҽʂʂ αɠҽɳƚ~ 𝚗𝚊 𝚓𝚊𝚛𝚞𝚖𝚊𝚛 𝚌𝚑𝚒𝚗𝚊 𝚐𝚠𝚊𝚗𝚊 𝚐𝚞𝚛𝚒𝚗 𝚓𝚒𝚎𝚍𝚍𝚊𝚛𝚑 𝚠𝚊𝚝𝚘  *z̟h̟a̟o̟ l̟i̟y̟i̟n̟g̟*

Gidan ba kowa sai su biyu Auntie ta fita company gurin aiki Abba ma haka shi ma Heesham office, ita kuma Humaira bata daɗe da fita ba, tana karatu a University tana karantar mass.com.

Sai gidan ya kasance su biyu ne ciki, sai kuma mai gadi da sauran masu aiki.

Bilki jin tana magana ba'a kulata ba yasa ta kalla ɓangaren da Jieddarh take a zaune gabaɗaya hankalinta yana kan tv sai faman sakin murmushi takeyi, ganin haka yasa ita ma Bilkin gwanar soyayya, mayar da kallon ta, akan tv dan taga abin da ya ɗaukewa Jieddarh hankali a ciki, ba shiri ta saki murmushi  ganin stars ɗin film ɗinne ake caskalewa.

Jieddarh cike da nishaɗi ta ce "inason wannan jarumar obaa, ta iya faɗa kala kala especially ma kung fu, ga iya acting.

Bilki ce ta tambayeta hanyar cewa, "miye sunan ta," Jieddarh ta ce sunan ta, *ȥԋασ ʅιყιɳɠ* Bilki ta ce cabɗijan ana suna a duniya wani irin sunane kuma 'chao liying ' ko me, ni bama zan iya faɗa ba.

Jieddarh tayi murmushi tana gyara mata sunan ta ce "Zhao liying' ake cewa fa, "jinki fa, wai 'zhao liying' taɓɗi, Bilki ta jajanta tana ya mutsa fuska, ta ci gaba da cewa, "ina faɗamaki ɗazu fa, har wani kallon ƙauna mutumin yamin dana gaisheshi."

Jieddarh harta buɗe baki zatayi magana sukaji door bell, Bilki ce taje ta buɗe ƙofar.

Baki da hanci ta saki ganin wacca take a ƙofar palon Ni'ima ce gabanta kuwa akwatuna ne masu kyau guda biyu, mai gadi ya kawo mata da alama hutu tazo.
Matsa ma ta Bilki tayi don ta sama hanyar shigowa, ganin tana ƙoƙarin tureta ta shiga, ko sallama babu Ni'ima ta shigo palon yayinda mai gadi ya biyota da akwatu nanta, bata kula Jieddarh dake binta da kallon mamaki ba, ta saka key ta buɗe wani bedroom anan palon ƙasan da alama anan take sauka idan tazo tunda ga key a hannunta, buɗew tayi ta shiga in.

Bilki dake riƙe da baki tunɗazu a fili ta ce "jar bala'i yau nake ganin abin mamaki kare da tallan tsire.

Jieddarh tayi murmushi ta ce !Bilki kenan akwai ki da neman magana fa,"
Bilki tayi dariya tana faɗin "ai abinne yafi ƙarfin kaina da ɗan tunanina, inaga ai koda sallama ta mana tunda dai duka musulmai ne, amma na mata uzuri saboda batasan Menene fa`idar sallama ba, da alama."

"Kedai kiyi aikin baganki kawai malama," cewar Jieddarh tana gyara kwanciyar ta saman 3sieter, tana rufe baki saiga Ni'ima ta fito daga ɗakin data sauka, sanye cikin £nglish wears riga brown color, hannun rigar anyanka ta wajen kafaɗarta sai skert pencil black iya gwiwar ta  mai adon stones brown,  kannan nata ko arzikin hula bai samu ba yatsa kitson attach mai tsadar gaske brown, ta zubo kitson ta gaba tayi kyau ba ƙarya sai baza ƙamshin turaren white gold takeyi zama tayi a saman 2sieter, ta ɗauka remote control ta canza channel zuwa na waƙoƙi.

Ba ido kaɗai ba hatta baki da hanci saida malama Bilki ta saki tana kallon ikon Allah, ita kuwa Jieddarh ko a jikinta da alama ta saba da ganin haka.

Saida ta gama shan ƙamshinta sannan ta kalla Jieddarh ta ce "hala dai surukata batanan ne?,"
Jieddarh yi tayi kamar bataji mai ta ce ba, a zuciyarta ta ce "idan ma zaki buɗe baki kiyi magana ki buɗe malama," ganin alamar Jieddarh ba ta jita ba, yasa ta ɗan ɗaga muryar ta ce,

"Jieddarh,  Jieddarh magana fa nake, nace hala dai suruka ta batanan ne?,"
Murmushi Jieddarh tayi sannan ta buɗe idonta da ta rufe kamar bacci ta ce "oh wai Auntie kike magana, ta tafi wajen aiki bata faɗamiki bane hala?,"
"Bata faɗamin ba wallahi, kuma tasan zanzo may be ta manta ne."
Ni'ima ta faɗa tana mai da akalan kallon ta kan Bilki cikin ya tsine fuska ta ce "Bilki kike ko, please dafa min indomie guda ɗaya kwai biyu saiki haɗomin da juice mai sanyi cuz i'm hungry obaa.

Ajiye moppern dake hannunta Bilki tayi sannan ta nufa hanyar kitchen tana faɗin "ba ki da damuwa Auntie beauty wato surukar hajiya jamila."

Tana shiga kitchen ɗin ta ɗauka pot ƙarama, dai dai one indomie, ta wanke sannan ta kunna gas, ta ɗaura tukunyar, kana tasa ruwa kaɗan saida ruwan ya tafasa sannan ta zuba indomie guda ɗaya ta ɗauko mai tasa sannan tasa maggie's kala kala batasan adadi ba ita kanta, tana murmushi hadda ɗan raira waƙanta "yau za'aci indomie, a ƙoshi highly, indomie wanda ba'a taɓa cin kalan shi ba, badai yau anzo kwaɗayi ba, gidan mutane hadda shigan arna to yau za'a gane kure highly highly.
Tana girkin tana raira waƙar abinta spicy's ta ɗi bo a spoon ba adadi ta zuba, sannan tayi twisted.

Tsayawa tayi tana tunanin wani muguntar zata ƙara kuma, "yes na tuna" ta faɗa sannan ta ɗauko onion ta yayyanka a chopping board,  ko wankewa batayi ba ta zuba a haka saida indomie ɗin ya nuna sannan ta juye a plate.

Da sauri ta haɗa lemun abarba da kwakwa, ita da zatasa sugar a juice ɗin amma saboda iya shege salt ta ɗi bo a cokali ta zuba, ta juya saida ta kammala komai sannan ta zuba juice ɗin a cup, Tray ta ɗauka ta ɗaura plate ɗin indomie a ciki sannan ta ɗauka juice ɗin shima tasa a tray ɗin, ɗauka tayi ta nufo waje.
Palo ta fito a lokacin Ni'ima tana waya, ita kuma Jieddarh tana kwance a inda ta barta da alama ma bacci yayi gaba da ita, saman center table ta ɗaura tray ɗin sannan ta matso dashi gaban Ni'imar ta yadda zataji daɗin meal.

Tana aje Tray ɗin ta ce "Auntie beauty gashi nan, na kammala fa," tana gama faɗar haka ta ɗauka mopper ɗinta da sauran abubuwan ta  tabar palon tana dariya lols😂

Ni'ima tana kammala wayar ta matso da table ɗin gaban sosai ta yadda zataji daɗin kai loma, tana buɗe plate ɗin wani ƙamshi da tururi yayi mata sallama lumtse ido tayi tana ayyano yadda indomie ɗin zayyi daɗi.
Ɗan waro ido tayi ganin bata soya mata eggs ɗin da ta sakata ba, qwafa taja tana faɗin wannan yarinyar batada hankali, na sakata aiki taƙiyi."
Ta faɗa a daidai lokacin da takai indomie cokali ɗaya bakinta,  wani uban yaji ne da magi yayi ma ta sallama, ai ba shiri ta dawo da shi waje, da sauri ta ɗauka juice ɗin takai bakinta domin ya ma ta maganin raɗaɗin azabar da ya ziyarci bakinta.
Tana sakawa a memakon taji sasauci ina, ai saima wani uban gishiri da taji har wani ɗaci ɗaci game da bauri bauri yakeyi.

Ihu ta kurma wanda yayi Sanadin tashin Jieddarh a tsorace, saboda azaba Ni'ima tama kasa magana sai hawayen wahala take zubarwa gashi ta riga ta haɗiye juice ɗin da ta kafa a baki maƙogwaronta har wani qurjine ya fito dan azaba lolz.😳

Da sauri Jieddarh ta miƙe ta ɗauko mata ruwan gora ever, a fridge ta bata, hannunta na rawa ta karɓa ta kafa a baki saida ta kwankwade shi tass, sannan tayi jifa da gorar tana sauke haki na wahala, ido jajur.
Jieddarh sai faman ƙumshe dariya takeyi ganin yadda kwalliyar Ni'ima ya tashi aiki jam baki har kumatu tasan wannan kaɗanne daga aikin Bilki 😀

Zama tayi a kujera tana kuma kallon yadda Ni'imar take faman kakarin amai, amma yaƙi zuwa, "sannu kinji Ni'ima beauty sannu fa,"  Jieddarh ta faɗa tana kuma umshe dariyar ta,
Ko kallon ta Ni'ima batayi ba ta shige ɗaki ta banko ƙofar, jikake garamm.
"a'a ai bani na kar zomon ba, rataya aka bani Auntie Beauty,"  cewar Jieddarh tana fashewa da dariya a fili ta ce "Bilki kin taho march wallahi, Allah yasa kinada ƴan wasa lol 😂
Remote ta ɗauka ta sauya tashar waƙoƙin da Ni'ima tasa zuwa korean drama MY STRANGE HERO.

~~~~

𝙳𝚊 𝚢𝚊𝚖𝚖𝚊 𝚠𝚞𝚛𝚊𝚛𝚎𝚗 𝚔𝚊𝚛𝚏𝚎 𝚋𝚒𝚢𝚊𝚛 𝚍𝚊 𝚛𝚊𝚋𝚒 𝚗𝚊 𝚖𝚊𝚛𝚎𝚌𝚎.

ʝιҽԃԃαɾԋ☆ʝυɾαҽʝ

Kamar yadda ta saba Jieddarh tana kwance a garden saman lallausar carpet ɗin da ta shimfida, laptop ne a gabanta tana search na  'ρɾιɳƈҽʂʂ ԃɾҽʂʂ' kala kala a youtube.
Gefenta Bilking ce zaune a ɗaya daga cikin resting chairs na garden ɗin  taci ado cikin riga da zani na atamfa, ga ɗan kwalin nan tayi ɗaurin zarah bahari dashi, tayi kyau ba ƙarya Fuskar nan tasha light make up da Jieddarh ta ɗanɗasa ma ta.

Hannunta kuwa yasha jan henna lalle, wanda ya ƙarawa farar fatarta kyau, Bilki kyakyawa ce ita ba laifi.

Kallon ta Jieddarh tayi tana ɗan murmushi ta ce "wai duk wannan kwalliyar kamar zakije gasar SARAUNIYAR KYAU ta duniya, duka na yaya 'H' ne?, gaskiya anaji dashi sosai fa,"

Ƙayataccen murmushi Bilki tayi tana wani fari da ido ta ce "to ya san ranki, yauwa Jieddarh dama inaso kifaɗamin abinda zance mishi ne, idan ya dawo, kinga yanzu ya kusa dawowa fa,"
"ke Bilki kifa dinga bi aslowly, idan ba haka tom, shawara ce,"
cewar Jieddarh dan ta lura idan ba tana dakatar da Bilkin a wasu abubuwan ba, tofah ita Bilkin ita ce zata sha wuya ba kowa ba.
"kedai malama kawai ki faɗamin abin dana tambayeki kinji,"  Bilki ta faɗa ko'a jikinta da abin da Jieddarh ta ce ma ta.

"inaga kawai kice mishi welcome yayi,"

"haba Jieddarh wani 'welcome' kuma?, ai welcome ya zama tsohon yayi gaskiya."
Cewar Bilki tana kyaɓe fuska.
Jieddarh ta ce "toni kinga dai ba soyayya nake ba, balle nasan me zance miki ko,"  Bilki ta ce "amma kuma, ai kinyi karatu kinfi ni nida na tsaya iyaka secondary school,"
Jieddarh tayi dariya tana faɗin "ai duk kanwar ja ce, don nima dai iya kana secondary school ɗin."
Waro ido Bilki tayi ta ce "haba yanzu kamar ke haka kin kammala secondary shine  saboda jin daɗi, kika tsaya a haka baki ɗaura ba,  ni ina mamakin abin da ya hanaki shiga University, gaskiya da walaki,"
Jiiddarh ta ce "bana ra'ayine kawai, that's why, ba wani abu ba,"
Bilki tana ya musta fuska alamar ita bata yarda da abin da Jieddarh ɗin ta ce ba, ta ce.
"haka kawai saboda iya shege kice bakya ra'ayi kawai dai da wata a ƙasa ki yarda da wannan madam,"

Zata kuma magana taji durar motar Heesham zumbur ta miƙe tsaye, ɗaukar gyalenta tayi ta nufi cikin gidan babu magana.

Girgiza kai Jieddarh tayi kurum a fili ta ce "gaskiya ni bansan wani kalan soyayya Bilki take ma Heesham ba, sai kace aikin sihiri?."

Ita kuwa Bilki da sauri ta ƙarisa parking lot a daidai lokacin da Heesham ya fito daga motar hannun shi riƙe da briefcase, har zai wuce ya jiyo muryar ta tana faɗin.

"yaya Heesham,"  juyuwa ya ɗanyi, aikuwa sukayi four eyes da Bilki zuba mata kyakyawan idanun shi yayi yana jira yaji mai zatace, gabaɗaya sai taji ta ruɗe ta duburburce da kyar ta iya haɗo kalmomi ta haɗasu guri guda.

Tana ɗan inda inda ta ce "amm uhm yaya Heesham 'welcome back home' ya gajiya?, umm dama nace kawo jakar naka na riƙe maka kaji?," da kyar ta iya haɗa kalmomin ta faɗa saboda yadda ya zuba mata ido ba ko kyaftawa.

Baice komai ba ya miƙa ma ta briefcase ɗin, hannun ta na rawa tasa ta karɓa, shikuma yayi gaba tabi bayan shi hadda ɗan saurinta.

Gabaɗaya Bilki ta manta da babin wata Ni'ima da irin laifin da ta mata har, saida suka shiga palon sukayi ido huɗu da ita, zaune saman 2sieter ta ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya, tana taunar cingum
Hango shigowar  Heesham ne yasa ta wani taso da saurinta zata rungumeshi.

Da sauri ya matsa gefe yana kwaɗa mata harara sannan ya fara magana  kai daga jin maganar kasan ranshi ya fara ɓaci da irin halinta.

"Ni'ima meyasa bakyajin magana ne, dubi shiga ki fa, ya miki kala da shigar yaran musulmai?, kuma na faɗa miki ba sau ɗaya ba, akan, ki dena ƙoƙarin hugging ɗina, cuz keba muharrama ta bane, amma ba kyaji ko, so this is the last warning da zan miki akan wannan ugly ɗabi'ar taki.

Cike da shakwaɓa Ni'ima ke faɗin, "haba my world, mana yanzu miye laifin wannan shigar tawa?, sai kace baka waye ba, come on mana, ka shigo zamani mana,"
Ta faɗa tana kuma yin juyi a gaban shi. cike da takaici ya kalle ta.
Ya juyo ya kalla Bilki da tayi tsuru tsuru, yace "duba nan, dubeta, a tsakanin ita dake wacece tayi shigar rashin da'a fisabilillah faɗamin?,"  kallon Bilkin ita ma Ni'imar tayi taga shigar jikinta ya mutsa fuska tayi tana faɗin, "haba my world dubeta fa, wannan ai shigar ƙauyawa tayi.

Da sauri Bilki ta kalla Ni'ima jin abin da ta ce lallai ta latsa ta, ita Ni'imar sanye take cikin €nglish gown black color, mai hannun vest ko gwiwar ta rigar bata kaiba gashi ta ɗameta ɗam numfashi ma, da kyar takeyi.

Bai tsaya jin abin da zata kuma cewa yayi gaba abin shi, da sauri Bilki tabi bayanshi, suka bar Ni'ima a tsaye kamar gunki.
Suna shiga bedroom ɗinnashi dake upstairs ta aje mishi briefcase ɗin a palo ta dawo down ta sauko bataga Ni'ima ba dan haka batama damu ba garden ta koma gurin Jieddarh zuciyarta qhal💦

D̬̂â̬ĝ̬â̬ Â̬l̬̂k̬̂â̬l̬̂â̬m̬̂î̬n̬̂

*🌼ƚԋҽ ɳαιɳαɾԋ ƙԃ🌼*

🅰🅱🆄🅹🅰

**
Yau juma'a wanda yayi daidai da kwanakin Dije {Deejarh} biyar da zuwa gidansu Afeefah kuma yaune gwaggon ta wato Auntie sa'adah zata koma ƙauye, Zuwa yanzu Deejarh ta fara fahimtar kaɗan daga cikin halayen mutanen gidan, farko dai kamar:

'𝑵𝒂𝒊𝒏𝒂𝒓𝒉' ta fahimci mace ce ita, mai masifar rashin son shiga jama'a bawai kuma miskila bace, a'a ita haka halinta yake, sannan kuma ta fahimci tana masifar ƙaunar ƴan uwanta sannan kuma tana da kirki sai dai bata nuna kirkinnata kamar   AFEEFAH ita NAINARH nunawa take kamar bata da kirki, amma idan ka zauna da ita zaka fahimci ko wacece ita.

'𝑵𝒂𝒊𝒍𝒂𝒉' ta fahimci itaɗin mace ce ƴar bin ra'ayin kanta kamar mahaifiyarsu MOMY RAFI'AT sannan kuma kirkinta ragagge ne bisa kowa na gidan.

'𝒁𝒂𝒚𝒏𝒆𝒓𝒃' ita kuma Deejarh ta fahimci ZAYNERB mace ƴar komai saina shiga ma'ana ita dai ZAYNERB akwaita da neman rigima amma ga ƴan uwanta kuma rigima irin wacca za'ayi wasa da dariya.

'𝑯𝒂𝒍𝒆𝒆𝒔𝒂𝒕' cabɗi sarkin miskilanci kenan yadda Deejarh ta mata laƙani, don ta fahimci a rana guda ma za'a iya ƙirga adadin magana da HALEESAT tayi, sannan ta lura Haleesat mayyar Bacci ce, sannan kuma na lura Haleesat tana tafiya Club, sai dai bata yi gigin faɗawa kowa ba, sakamakon dalilai.

'𝑳𝒂𝒊𝒍𝒂𝒉' ta fahimci ita kuma ƴar Ji_ji da kai ce, ga kuma mugun iyayi, da alfahari da dukiyar iyayenta, sai dai ita ma tanada kirki iya nata, sannan kuma ta iya yaɓa magana babu taunawa ko wata kala ce kuwa.

'𝑨𝒇𝒆𝒆𝒇𝒂𝒓𝒉' uwar gayya kenan, a gaskiya Deejarh ta kasance tanajin daɗin zama da AFEEFAH fiye da kowa a cikin gidan MISTER MAI KYAU har shi kanshi dama matar sa MOMY RAFI'AT
Deejarh ta fahimci Afeefah mace ce ita mai masifar kirki highly domin kuwa ba ruwanta da kowa bata faɗa da kowa, haka zalika kowa nata ne ba ruwanta, sannan bata ɗaurawa kanta Ji_ji da kai ba sam, sosai akwai bambanci mai yawa tsakaninta da ƴan uwanta especially ma LAILAH, sam Afeefah bata wulaƙanta kowa akan dukiyar da mahaifinta yake dashi. ko kuma wai irin ta nuna bambanci tsakaninta da ƴan uwanta akan ƙaunar da mahaifinsu MISTER MAI KYAU yake nuna ma ta sama da kowa sam bata haka, sannan tun zuwan Deejarh gidan bata taɓaji Afeefah tayima wani ko wata daga cikin ƴan aikin gidan tsawa ko masifa ba. ba kamar Lailah ba da a gaban Daddynsu ta mara ƴar aiki akan 'As depleted ta zubo mata tea a jiki ba tare da ta sani ba.

Afeefah tana da kirki fiye da tunanin mai tunani, sannan Babban mafarkinta a duniya shi ne zama SARAUNIYAR KYAU ta duniya gabaɗaya, Burinta kuma shine zama Babbar Likita da ƙasarta zatayi alfahari da ita, Fatan ta kuma shi ne zama House Wife ta gari💃

________________________________________________________________________________

Tun safe ake abu ɗaya da Deejarh, ta maƙale akan sai tabi gwaggon ta ƙauye ita kuma gwaggon ta ta ce, ba za ta koma da ita ba, yanzu ma haka abin da ake ciki kenan da ita.

Tsaye suke a parking lot Afeefah, Deejarh, Auntie sa'adah sai kuma Zaynerb da Lailah dake gefe suna kallon ikon Allah.

"Deejarh ki bari ta shiga mota, mana driver yaja su tafi, kinga lokaci yana ƙurewa fa, ko kinaso tayi dare a hanya ne?,"
Duk wannan maganar Afeefah ne takeyi ma, Deejarh a hankali kuma cikin rarrashi.
Deejarh tana sha re hawaye ta ce "to zata dinga zuwa dubani, a koda yaushe, da yaushe 😳.
Da sauri Auntie sa'adah ta ce "E, mana Dije na, ai duk wata zandinga zuwa duba ki ba fashi,"
"toki rantse min," cewar Deejarh iya gaskiyar ta.
Dariya Afeefah tayi ta ce "ai ba seta rantse ba, idan ma bata zoba nida kaina zan kaiki ƙauyen, ki ganta ko," da kyar dai akasamu Deejarh ta bari Auntie sa'adah ta shiga motar driver yaja, suna ɗagama juna hannu har suka fice daga gidan.

Su kuma suka koma ciki suna shiga Deejarh ta ɗare saman 3sieter kamar ba ita bace ta gama kukan rabuwa yanzu, zama Afeefah tayi a gefan Deejarh tana faɗin "dubeki kamar ba kece mai kuka yanzu ba,"
Dariya Deejarh tayi ta ce "to ai ni haka nake, yanzu zakiga ina kuka anjima kuma dariya."

Zaynerb ta kalla Afeefah lokacin da ta zauna a kujerar kusada ita ta ce.
"ni banga kina wani shirye shiryen gasa bane fa, kallon Zaynerb Afeefah tayi ta ce "shirya shirye kuma sai kace wacca zatayi aure?,"
Lailah tana shafa wayarta ta ce "bawai haka ba, amma ai ya kamata ko ɗan gyaran jiki kiyi ko?."

Baki Afeefah ta saki tana kallon Lailah sai kuma tayi dariya, "lallai Lailah bakiji da kyau ba, kawai saboda wahala sai naje ina wani gyaran jiki saboda gasa, a'a to bada ni ba,"
 Lailah ta ce "Wallahi da gaske nake fa,"

 Afeefah ta ce "nima ai da gaske nake,"

"nifa yau banga wulƙawan Auntie Nailah ba kwata kwata, Zaynerb tayi maganar.

Deejarh ta ce "ai lokacin da kika tafi makaranta ne suka fita ita da wannan ƙawan nata mai kama da jarumar india 'Pooja Hegde' ɗinnan, ni banmasan sunanta ba,"

"amma wallahi baki da kirki sadiqqa ce take kama da Pooja ɗin?," cewar Zaynerb tana dariya.

Dariya ita ma Deejarh tayi ta ce "Yasin Auntie wannan ƙawar Auntie Nailah ɗin, da pooja take kama har tsayin da hasken ɗaya, yanayin  gashinta ne, kawai bansani ba."

"ke kuma a'ina kikasan tsayin pooja ɗin?, uwar ƴan sanin kamanni?,"
Lailah ta tambaya, Deejarh ta ce "a cikin film mana,"
"wanne a ciki?,"  Lailah ta kuma tambayarta.

Ta ce "wannan wanda tayi ita da allu arjun ɗin mana na dai manta sunan shi ne."
"wai 'Alavaikunthapurramuloo' kike nufi?,"  Afeefah ta tambaye ta bayan ta faɗa sunan film ɗin, da sauri Deejarh ta ce "E, shi nake nufi.

Zaynerb ta ce "ai tafi jaruman india na yankin telugu kyau gabaɗaya."
Lailah tace "a'a wasa dai kikeyi ko amma me za'ayi da wata 'pooja' bayan gasu 'kajal aggarwal' a gefe,"

Zaynerb ta ce "wake maganar kajal, ai wannan ta tsufa,"
" a gurin ki ba, cewar Lailah, Afeefah ta ce "to Ladies a'ina kuka bar Rashi Khanna ɗin, gasu Tamannah Bhatia, Mehreen dasu Samantha duka a gefe,"
"faɗa ma ta dai sister," cewar Lailah ta ci gaba da cewa "ga kuma Shruti Hassan madam ina faɗamiki idanun nata kamar kamar me kyau da kyau aka haɗa fa."

Deejarh ganin suna magana suna haɗawa da turancine, gashi ita ba komai take fahimta ba, a zuciyarta ta ce "bari dai nima nayi turanci nan na haɗa da indian ci😎

Gyaran murya tayi sannan ta kalla Lailah dake kwance a  2sieter ta ce "Auntie Lailah na tambaye ki wani mana?,"
"inajinki da sauraronki cewar Lailah.
Deejarh ta ce "karfa kice bakyajin yaren da zan miki maganar dashi,"
Lailah ta ce faɗa mana baki da problem, to banda abinki Dije ta ƙauye yaruka goma nake ji fa, kuma duka na qware akan jinsu highly.

Deejarth ta kuma gyara zaman ta alamar za'a fara sannan ta ce.
"Menene is poonakaalu ahora?,"

Tashi zaune Lailah tayi tana faɗin, "ban fahimci me kike nufi ba, please ɗan maimaita muji, maimai tawa Deejarh tayi.

"Menene is poonakaalu ahora."

A hankali Lailah ta kuma maimai tawa ita ma, girgiza kanta tayi, "ke bansani ba, wannan ai hauka kawai kika haɗa."

"Ba hauka bane fa, tambaya tayi miki,"
Cewar Zaynerb kallon Deejarh Zaynerb tayi murmushi ta ma ta sannan ta ce.

"na farko dai da ta ce 'Menene' hausa tayi, na biyu kuma da ta ce 'is' turanci tayi, na uku kuma da ta ce 'poonakaalu' yaren telugu tayi, na huɗu kuma da ta  ce 'ahora' yaren spanish tayi."

"Nifa wannan dogon bayanin, ba ganeshi nakeyi ba jeki gundarin magana kawai kai tsaye," cewar Lailah.

Da sauri Afeefah ta ce "tana nufin ta ce 'ƙarfe nawa ne' fa, shine ta haɗa yare kala huɗu ko ba, haka bane?,"  tayi maganar tana kallon Deejarh ɗin, dariya tayi ta ce "E, mana Balarabiyar india haka nake nufi."

Fashewa da dariya Lailah tayi har tana faɗowa daga saman sofa.
Duk suka zuba mata ido, ita ma Zaynerb dariyar takeyi ba laifi.
Saida Lailah tayi dariya ma'ishi sannan ta dakata. Kallon Deejarh tayi cikin dariyar take faɗin, "amma fa, kinyi ƙoƙari waima, ke a'ina kika koya, wannan yarukan kala kala haka?,"

Deejarh ta ce "nima kawai naji na iya ne fa," dariya Lailah ta kuma fashewa da shi.

Afeefah da abin ya isheta buɗar bakinta cewa tayi, "Lailah kodai kin sama taɓuwa ne?,"  

Lailah ta ce "lafiyata qalau, kawai dai na manta rabon da, a sakani dariya kalar haka ne,"
"ai saikiyi da kyau an baki aiki cewar Afeefah.

"Lailah zoki rakani gidan Sunainah mana?," cewar Zaynerb tana miƙewa tsaye.
Tsayawa Lailah tayi da dariyar da takeyi ta kalleta "amma dai wasa kike ko?,
Zaynerb tana ƙoƙarin shiga bedroom ɗinta, ta juyo ta ce "da gaske nake, don akwai abin da nakeso ta koyamin, kinsan course ɗin da nake karanta shi ta karanta ko?,"
 
Tana faɗan haka ta shige ɗakinta, bata daɗe ba, ta fito sanye da hijjab blue black har ƙasa ga folder's rungume a chest ɗinta, kallon Lailah tayi ta ce
"zo mu tafi mana."
"Inason zuwa, amma wallahi ina tsoron karen gidanta,"  Lailah ta faɗa iya gaskiyar ta.
"ke matsoraciya, indai saboda kare ne, ba zaki ba to kisa ranki a inuwa domin karen yana ɗaure ma kaca."
"ke tayaya kikasani?,"
Lailah ta tambaya, Zaynerb ta ce "ita ta faɗamin, kinsan kuma ba zatamin ƙarya ba ko,"
Tashi Lailah tayi ta ɗauka gyalenta dake a gefen kujera ta yafa a kafaɗarta.

"Nima zan biku kinji Auntie Zaynerb, tunda na shigo gidannan, ban fita ba,"
Cewar Deejarh iya gaskiyarta, "idan bakyajin tsoron kare, kizo muje,"  cewar Lailah tana dariya, "banajin tsoron shi,"
"to zo muje," Zaynerb ta amsa ma ta.
Da sauri ta miƙe tsaye ɗakin da yake matsayin nata, ta shiga ta ɗauko hijjab ɗinta iya gwiwa fari.

"ke yanzu nanda maƙwabtan ne, saikin saka wani hijjab," cewar Lailah tana kallon Deejarh da koɗaɗɗen hijjabinta. Zaynerb ta kalla Deejarh ta ce "rabu da Lailah kawai don ta iya tonon tsiwa kala kala, ɗunguma sukayi wajen fita daga palon su ukun.

Suna taɓa fira a hanyar su har suka ƙarisa gidan, ƙwanƙwasa ƙaramar kyauren gate ɗin gidan, Zaynerb tayi shiru taji hannu tasa ta tura ƙofar tajita a buɗe.
Shiga gidan sukayi basuga mai gadi a kujerar shi, ta zama ba, basu kawo komai ba suka nufi cikin gidan a tsakiyar palo suka tsaya suna kwaɗa sallama, amma ba amsa.

"Kai kodai bata nan ne?," Deejarh ta tambaya, Zaynerb ta ce wata ƙila, wata ƙila kuma.....zata kuma magana saiga Babah Dije mai aikin ta fito, "yauwa Babah wai Ummyn Farhana tana nan kuwa?,"
Zaynerb ta tambaya, Babah Dije ta ce "aikuwa Ƴar nan bata nan ta fita ita da mai gidan, wato Alhaji Sohailu."
"to bata faɗa miki inda zata ba?," wannan karon Lailah tayi tambayar.
Babah Dije ta ce "eh inaga gidan surukanta suka tafi," "okay ba damuwa, idan ta dawo kawai kice mata munzo bamu sameta ba, Zaynerb ta faɗawa Babah ɗin hakan.
Da 'to' Babah Dije ta amsa musu, su kuma suka fito.

Lailah ta ce "danasani ma, ban biyoki ba, tunda dai batanan....Zaynerb ta ce "ai kin motsa jiki koba komai inagaa!....kasa ƙarisa maganar tayi ganin abin da ke gabansu, "kinaga mene?,"
Lailah ta tambaya jin Zaynerb ɗin ta kasa ƙarisa maganar bakinta.
A hankali takai kallon ta inda taga 𝑍aynerb ɗin ta saki baki da hanci tana kallo.

*~𝑺𝒉𝒊𝒏 𝒌𝒐 𝒎𝒂𝒊, 𝒁𝒂𝒚𝒏𝒆𝒓𝒃 𝒕𝒂 𝒈𝒂𝒏𝒊 𝒅𝒂 𝒚𝒂 𝒉𝒂𝒏𝒂𝒕𝒂 𝒌𝒂𝒓𝒊𝒔𝒂 𝒎𝒂𝒈𝒂𝒏𝒂𝒓 𝒅𝒂 𝒕𝒂𝒌𝒆𝒚𝒊?~*
*~𝒔𝒉𝒊𝒏 𝒅𝒂𝒎𝒆 𝑳𝒂𝒊𝒍𝒂𝒉 𝒛𝒂𝒕𝒂𝒚𝒊 𝒊𝒅𝒐 𝒉𝒖𝒅𝒖 𝒊𝒅𝒂𝒏 𝒕𝒂 𝒋𝒖𝒚𝒂?~*
*~𝒎𝒆𝒚𝒂𝒔𝒂 𝒎𝒂𝒊 𝒈𝒂𝒅𝒊 𝒃𝒂𝒔𝒉𝒊𝒏𝒂𝒏 𝒈𝒖𝒓𝒊𝒏 𝒛𝒂𝒎𝒂𝒏 𝒔𝒉𝒊?~*

*ᴋᴏᴍᴀ ᴍɪʏᴇ ᴍᴜ ʜᴀᴅᴜ ᴀ ɴᴇxᴛ ᴘᴀɢᴇ's ᴊɪʙɪ ɪɴsʜᴀ ᴀʟʟᴀʜ, ᴅᴏᴍɪɴ sᴀɴɪɴ ʏᴀᴅᴅᴀ ᴢᴀᴛᴀ ᴋᴀsᴀɴᴄᴇ, ᴅᴀsᴜ ᴢᴀʏɴᴇʀʙ, ᴅᴇᴇᴊᴀʀʜ, ʟᴀɪʟᴀʜ, ᴀ ɢɪᴅᴀɴ sᴜɴᴀɪɴᴀʀʜ*

👑🩸ɢʟᴀᴍ ǫᴜᴇᴇɴ🩸👑
       💝ᴛᴀᴋᴜɴ ғᴀʀᴋᴏ🤙


*~💅ᴛʜᴇ ɢʟᴀᴍ ǫᴜᴇᴇɴ, ᴡᴀɴɴᴀɴ ʟᴀʙᴀʀɪɴ ᴍᴀʟʟᴀᴋɪɴᴀ ɴᴇ, ɴɪ ᴋᴀᴅᴀɪ ɴᴀᴋᴇ ᴅᴀ ᴅᴀᴍᴀʀ sᴀʀʀᴀғᴀ ᴀʙɪɴᴀ ʏᴀᴅᴅᴀ ɴᴀᴋᴇsᴏ, ᴡᴀɴɴᴀɴ ʟᴀʙᴀʀɪɴ ɴɪ ɴᴀʏɪ ᴋᴜᴍᴀ ɴᴀsʜᴀ ɢᴡᴀɢᴡᴀʀᴍᴀʏᴀ ᴡᴀᴊᴇɴ ᴋɪʀᴋɪʀᴀɴsʜɪ, ᴡᴀɴɴᴀɴ ʟᴀʙᴀʀɪɴ ᴋɪʀᴋɪʀᴀɴsʜɪ ɴᴀʏɪ, ᴅᴏᴍɪɴ ɪʟᴍᴀɴᴛᴀʀᴡᴀ ᴅᴀ ғᴀᴅᴀᴋᴀʀᴡᴀ ʜᴀʀᴍᴀ ᴅᴀ ɴɪsʜᴀᴅᴀɴᴛᴀʀᴡᴀ, ɴɪ ɴᴇ ɴᴀsᴀɴ ɪʀɪɴ ᴡᴀʜᴀʟᴀɴ ᴅᴀ ɴᴀsʜᴀ ᴋᴀғɪɴ sᴀᴍᴀʀ ᴅᴀsʜɪ, sᴏ ɪɴᴀ ᴍᴀɪ ɢᴀʀɢᴀᴅɪ ᴅᴀ ᴋᴀᴋᴋᴀᴜsᴀʀ ᴍᴜʀʏᴀ ᴀᴋᴀɴ, ʙᴀɴ ʏᴀʀᴅᴀ ʙᴀ, ᴋᴜᴍᴀ ʙᴀᴢᴀɴ ʟᴀᴍᴜɴᴄᴇ ᴡᴀɴɪ ᴋᴏ ᴡᴀᴛᴀ sᴜʏɪᴍɪɴ, ᴀᴍғᴀɴɪ ᴅᴀ ᴡᴀɴɪ sᴀsʜᴇ ᴋᴏ ʙᴀɴɢᴀʀᴇ ɴᴀ ᴄɪᴋɪɴ ᴡᴀɴɴᴀɴ ᴋɪʀᴋɪʀᴀʀʀᴇɴ ʟᴀʙᴀʀɪ '𝐒𝐀𝐑𝐀𝐔𝐍𝐈𝐘𝐀𝐑 𝐊𝐘𝐀𝐔' ʙᴀ, ɪᴅᴀɴ ᴋᴜɴɴᴇ ʏᴀᴄɪ ᴍᴀғɪʏᴀ ʏᴀᴡᴀɴ ᴍᴀsᴜ ɪʏᴀ ᴍᴀɢᴀɴᴀ, sᴜᴋᴀ ᴄᴇ ɢᴀɴɢᴀɢᴀʀ ᴊɪᴋɪ ʏᴀ ᴛsɪʀᴀ, 👑ᴛʜᴇ ɢʟᴀᴍ ǫᴜᴇᴇɴ💅 ᴍᴀʟʟᴀᴋɪ ɴᴀ ɴᴇ, ɴɪ ᴋᴀ𝙳ᴀɪ🤙~*

^ɴᴏᴠᴇʟ ᴡʀɪᴛᴇʀ ᴏғ✦

💓sᴀʀᴀᴜɴɪʏᴀʀ ᴋʏᴀᴜ💓

♥︎ғɪʀsᴛ sᴛᴇᴘ

*💋💋ʂαɾαυɳιყαɾ ƙყαυ💋💋*

*~ƚԋҽ ɠʅαɱ ϙυҽҽɳ~*

*☆ʂƚσɾყ & ɯɾιƚιɳɠ Ⴆყ☆*

*~ƙԋαԃҽҽʝαɾƚԋ.         ʂαႦι'υ.         ყαԋყαԋ🤙~*

{~✦ƚԋҽ ɳαιɳαɾԋ ƙԃ~}😇

*page 23&24*

Waro dara daran idanun ta waje Lailah tayi ganin abin da ke gabansu, wani ƙaton kare ne, irinna turawa wanda yasha training ya gaji sai faman hura fala falan kunen shi yakeyi ga mai kula dashi a gefe hannun shi riƙe igiyar da ya ɗaure ƙafan karen ɗaya.

Ita Lailah sam bata lura da ƙafan karen dake a ɗaure da sarƙa ba, gabaɗaya a mugun tsorace take ga wani guntun fitsari da ya matseta a mara.

Tattare skirt ɗinta ta farayi, ganin zata ruga ana kare yasa Iliya dake riƙe da karen saurin faɗin.
"hajiya karki gudu karki gudu fa, a ɗaure yake da sarƙa," Amma ina Lailah tayi nisa bata jin kira a three sixty 360 ta ranci na kare.

Shikuma kare dayaga haka ya rama mata baya, Toh abin yazoma Iliya a bazata ne, dan haka baima san lokacin daya saki igiyar hannun shi ba, shikuwa kare yace dama haka nakeso.

Hannu biyu Iliya ya ɗaura aka yana mai faɗin " yau ina ganin bala'i ganin ido na, dan Allah madam ki tsaya ki dena gudu, amma ina wanda yayi nisa bayajin kira.

Jama'a ba saiga Lailah da kare ana zuba tsere a compound ɗin GIDANMU ba, gabaɗaya Lailah ta rikice batama san inda take jefa ƙafafunta ba, ga kare da shegen gudu duk inda ta cire ƙafa nan yake jefa nashi.

Ganin Lailah tasha kwana shima karen ya mara mata bayane yasa su Zaynerb da Deejarh dake faman hawaye da ma Iliya gabaɗaya suma suka mara musu baya.

Lailah idonta ya rufe kawai gudu take ba ƙaƙƙautawa, fitsarin da take riƙewa batasan lokacin da ta kusa saki ba.
Tazo wuce swimming pool santsin gurin ya kwasheta, saiga Lailah saman ruwa kace kace, kare dayaga haka sai juyo zai koma inda ya fito a daidai lokacin kuma Deejarh dasu Zaynerb sukayo kwanar kawai sai aka tsaya kallan kallo a tsakanin Deejarh da kare yayinda Zaynerb da Iliya suke a daga baya ko  wannen su ido a zazzare tsaban tashin hankali.

Deejarh kuwa yi tayi kamar zata ruga da gudu, sai kuma taja wawiyar kwana ta zube a ƙasa tayi pretend kamar irin ta suma ɗinnan, shikuma karen daidai lokacin ya taho jama'a saiga kare ya tsallake Deejarh ya wuce, wata wawiyar kuma doguwar ajiyar zuciya Deejarh ta sauke a lokacin da karen ya tsallake ta.

Da sauri Iliya ya lallaɓa a hankali cikin sanɗa da kuma dabara wajen da karen yake dayake ya bashi baya ne, da sauri ya riƙo igiyar da ya ɗaure ƙafar karen.

Gabaɗayan su suka sassauke ajiyar zuciya hadda Lailah dake cikin ruwa tsundum har yanzu, da sauri Zaynerb ta ƙarisa bakin swimming pool ɗin ta riƙo hannun Lailah suka samu ta fito Lailah tana riƙe qugunƙumi  ita ma Deejarh tashi tayi daga kwancen da take.

Lailah ko kula Iliya dayake mata sannu batayi ba tsaban takaici, saima kallon ka cuceni da ta jefa mishi tayi gaba abinta, su Zaynerb suka mara maba baya.

A hanya tafe suke bamai magana sun zama kuramen ƙarfi da yaji, sai ajiyar zuciya da kowanen su yake saukewa, wani wawan shura Lailah takai ma ƙaramar ƙofar gate ɗin gidansu,  ba shiri gate man yazo ya buɗe don ganin wani mahaluki ne, wata wawiyar dariya ce ta tahoma Isah mai gadi ganin fuskar Lailah da tayi kamar wacca aka qwato daga bakin kura.

Aikuwa bai iyayin juriyar riƙe dariyar ba, dan saida yayi abinshi.
Wata uwar harara Lailah ta galla mishi cike da balbalin bala'i ta ce "wannan dariyar da kamin to, a bakin aikin ka kayita😨

Tana faɗa mishi haka tabi bayan su Zaynerb da sukayi gaba kamar zata tashi sama saboda sauri.

A tare duka su ukun suka kaima ƙofar palon duka su uku ae ƙofar ba shiri ta buɗe suka shiga ciki.

Afeefah, Nainarh da Nailah da suke kallon wani Chinese Drama 'Intrepreneurial age.'

A tare suka juyo dan ganin mahalukin da ya turo ƙofa kamar zai ɓalla haka, sunayin ido huɗu dasu Lailah a tamanin Auntie Nailah tayi jifa da jaririn dake hannunta zata gudu ganin fuskar Lailah da tayi tunaninta gamo tayi da ZOMBIE ko HORROR ko kuma FATALWA 👽, Allah ne kawai, ya tsare Nainarh tayi saurin cafe yaron cike da tsoro.

Su Zaynerb basu kula Afeefah da Nailah da suke rige rigen haye staircase's don neman gurin ɓuya ba, suka sama guri su duka suka zazzauna a saman 3sieter.

"Zaynerb lafiyar ku kuwa, kuka shigo ko sallama babu, sai kace ku ɗin  duka ba yaran musulmai ba," cewar Auntie Nainarh tana zama a 2 sieter babu alamar tsoro a tare da ita, don bata ma kula da fuskar Lailah ba, kallonta ta mayar kan Deejarh sannan cike da mamaki ta mayar kan Lailah zumbur ta miƙe tsaye, tanabin Lailah da kallon tsoro da mamaki.

"Lailah kece kuwa, miye haka ya sameki?, kodai faɗa kikayi da kura ne?,"
Nainarh ta jerowa Lailah tambayoyin ko tsayawa batayi ba saida takai aya.

A hankali Afeefah da Nailah suka fara dawowa da baya jin abin da Nainarh take faɗa.
Da sauri Afeefah ta ƙariso tana kallon Lailah "to kodai faɗan taje tayi da kuran bamu sani ba," cewar Afeefah da ta tsaya a gaban Lailah tana ƙare mata kallo cike da tsoro game da mamaki.

Buɗe baki Deejarh tayi zatayi magana sai kawai ta fashe da dariya tunowan da tayi lokacin da Lailah take tafka TSEREN MUTUWA tsakanin ta da kare.

"ah ah menene haka kuma, qalau kuwa kike ke Deejarh?,"
Nailah tayi tambayar tana kallon Deejarh ganin yadda take dariyar na ta na hauka tsakanin ta da Allah, "rabu da wannan mental ɗin kawai, ke Zaynerb menene ya faru ne wai na ganku haka 'So Bleak ne'," cewar Nainarh.

Zaynerb ta buɗe baki kenan da zummar zata musu bayani, ita ma ta tuno abin da ya faru ba shiri, ta fara ƙyaƙyata dariya harda riƙe ciki, ganin haka yasa Lailah dake harare harare ita ma ta fashe da dariyar.

Gabaɗaya su ukun suka haɗu suna ƙyaƙyata dariyar su sai yanzu ma abin da ya faru yake tariyo kanshi a kwakwalwar ko wannensu.

Uban tagumi Afeefah ta rafka hannu biyu biyu tana kallon ikon Allah, idan ta kalla Deejarh sai ta kalla Lailah idanta kalleta saikuma ta mayar da akalan kallon nata kan Zaynerb, dayake akwai kaifin kwakwalwa da basira, kafin ta ankara tuni wani tunani yazo kanta, kawai ita ma saita fashe da dariyar.

Nainarh ta ce "wa'innan yaran fa, sun sama mental illness  nake gani,"
"ae ki bari kawai suyi mai isansu, idan suka gaji su da kansu zash dena," cewar Nailah tana karɓar yaron ta.

'𝑭𝒊𝒗𝒆 𝒎𝒊𝒏𝒖𝒕𝒆𝒔 𝒕𝒐 𝒈𝒐'

Saida sukayi dariyar ta ishesu sannan suka tsaya suna sauke ajiyar zuciya a tare kamar wa'inda suka sha gudun fanfalaƙe.

"Okay kun kammala?, yanzu zaku iya faɗa mana abin da ya faru?," Nainarh ta tambaya tana jiran amsa.
Fashewa da dariya Deejarh ta kumayi kamar wata zautacciya.

Da kyar Zaynerb ta samu ta saita nutsuwar ta sannan ta fara basu labari kamar haka.

"Ɗazu ne fa, mun fita mu uku, ni da Lailah da kuma Deejarh zasu rakani gidan Sunainarh, domin ta kowa min wani topic,  tohm munje gidan batanan, ta tafi gidan surukanta ita da mijinta, to shine fa, mun fito zamu dawo gida, a daidai compound ɗin gidan muka haɗu da karen gidan, shida mai kula dashi da alama sun dawo daga £vening exercise ne, shine fa, ita Lailah gabaɗaya saboda ruɗewar da tayi na ganin wannan karen, batama lura karen a ɗaure yake da sarƙa ba, ina faɗamuku da ta tattare skirt ɗinta ta ranta da gudu, shi kuma kare yabi ta a three sixty 360.

Nan suka dinga zagaye gidan Lailah tana gudun ceton rai, sai daga ƙarshe ta samu, ta faɗa swimming pool 'In indistinctely, sannan ta samu ta tsira sai kuma kawai ya dawo kan Deejarh dayake tanada wayau sai tayi kamar ta suma shikuma kare da yaga haga yayi gaba abinshi, sannan ne fa, Iliya ya samu ya ɗaureshi da dabara."

*'𝑫𝒂𝒅𝒂 𝒂𝒍𝒌𝒂𝒎𝒊𝒏'*

*~☆ƚԋҽ ɳαιɳαɾԋ ƙԃ☆~*

Tunda ȥaynerb ta fara rattaɓa bayani,  Nailah da Afeefah suke ɓaɓɓaka dariya kamar taɓaɓɓu, ita kuwa Nainarh, baki ta saki tana kallonsu su duka cike da mamaki, saida taji Zaynerb takai aya, sannan ta sauke ajiyar zuciya.

Kallonta ta mayar kan Lailah, ɗan murmushi tayi ganin yadda gabaɗaya hallitar Lailah ya canza dan wuya, don komai mazewar ka idan kaga fuskar Lailah a lokacin kuma aka baka labarin abin da ya faru dole kaji dariya tazo maka 😀

Still cikin ɗan murmushi Nainarh, ta ce "au ashe dama Lailah har yanzu kinanan da wannan shegen tsoron karen naki?,"

Lailah tana shafa fuskarta dake ma ta raɗaɗi raɗaɗi ta ce "wallahi Auntie Nainarh bazaki gane bane kawai, dan bakiga yadda karen nan ya biyoni bane kawai, ni harna sadaƙar ma wannan mayen karen sayyayi Bitten ɗina, sai kuma Allah ya tsare, na faɗa pool.
Afeefah tana ɗan saita nutsuwarta ta ce "yanzu tunda kin tsira, sai kije kiyi wanka, ki gurje duka dattin da ƙuran da kare yasa kika kwaso ko?," Afeefah ta ƙarishe maganar da alamar tsokana.
Harara Lailah ta maka ma ta sannan ta ce "ai ko baki faɗa ba, madam yanzu zan wuce."
Kallon Zaynerb tayi ita kanta Lailah ɗin, dariya yana zuwa ma ta amma ta maze ta ce, "wai kuwa Auntie Zaynerb nace ina folder's ɗin, dana gani ɗazu a hannun ki ne, waɗanda sanadin su na shiga halin nan?,"

Ajiyar zuciya Zaynerb ta sauke tana mai ƙoƙarin ta tuna inda ta zubar ta ce.

"ni kaina, banmasan a gurin dana zubar ba, inaji garin gudun ceton rai ne, na zubar."

"Gashi fa, a hannuna na riƙe, ɗazu garin gudu kika zubar, ni kuma na kwashe na riƙe miki, a hannuna,"  Deejarh ta faɗa tana miƙawa Zaynerb folder's ɗin.
Karɓa Zaynerb tayi tana faɗin, "gaskiya kinyi abin kirki nagode miki obaa highly."
Lailah ta ce "aini da komawa gidan Sunainah kuma sai wani ikon Allah ɗin, dan bazan har abada ba, kuma bazan ce nan nan kusa ba."
Lailah tayi maganar a lokacin da ta miƙe tayi hanyar bedroom ɗinta, tanaji su Afeefah suna kuma ma ta dariya amma ko tsayawa batayi ba.

________***___🎀

𝑾𝒖𝒓𝒂𝒓𝒆𝒏 𝒌𝒂𝒓𝒇𝒆 𝒕𝒂𝒓𝒂 𝒅𝒂𝒊 𝒅𝒂𝒊 𝒏𝒂 𝒅𝒂𝒓𝒆💫

Afeefah ta tura ƙofar bedroom da Deejarh take kwana, a hankali ta shiga, kamar yadda tayi hasashe, kwance ta sameta saman bed tana fuskan tar stylish ceiling na bedroom, idonta a buɗe kamar mai  tunanin wani abu ko ƙarisowar wani abun.

Guri ta samu a gefen bed ɗin, ta zauna tana kallon Deejarh wacca alamu ya nuna har yanzu batasan ma da shigowar ta ba.

A hankali ta kira sunan ta 'Deejarh'," juyowa Deejarh tayi tana kallon ta ba ta ce komai ba, murmushi Afeefah tayi Sannan ta ce "mekike tunani ne haka?, na shigo bakisani ba."

"Tunanin abubuwa da yawa, Balarabiyar india ina tunanin abubuwa da yawa da yawa sosai fa," tayi maganar tana kallon Afeefah ta ci gaba da cewa, "ina tunanin Ummata da ta rasu ta barni, ina tunanin Abbana da ya fi son yaran matar shi akaina, ina tunanin gwaggona da take matuƙar ƙaunata, ina tunanin komai da kowa, ina tunanin yadda GOBE NA zata kasance, ina cikin kaɗaici sosai, Balarabiyar india."

"Tunda ta fara maganar Afeefah take kallon ta, tana mamakin ashe tana da hankali haka, da har zata tsaya tunanin iyayenta, da gobenta, ta wani ɓangaren kuma tana kuma tausayawa Deejarh ɗin yarinyar ta taso batasan Menene soyayyar iyaye ba, kuma a irin labarin da Auntie sa'adah ta bata ta fahimci yarinyar ba wani shaƙuwace a tsakanin ta da mahaifin ta ba, daɗin da ɗawa kuma ta fahimci yarinyar gabaɗaya ba'a ma ta training irinna na uwa ba, sannan kuma tana da matuƙar wauta.

Ajiyar zuciya ta sauke tana kuma kallon Deejarh ɗin sannan ta fara magana.

"Deejarh kenan, Ni ma a baya, a lokacin ban wuce shekaru irinna naki ba a duniya, haka nake ƙurewa can cikin bedroom  nasha kukana idan na tuna mahaifiyar mu, wani lokacin kuma idan Momy Rafi'at ta siyoma su Lailah kayan wasa banda, ni da ƴar uwata Zaynerb, haka zan shige ƙasan bed nasha kukana idan Auntie Zaynerb tana nan ta rarrasheni, idan kuma bata nan haka zantayi har saina ba uku lada." badan komai nake wannan kukan saidan irin ƙiyayyar da Momy Rafi'at take nuna mana ni da Zaynerb ƙiri_ƙiri."

Da sauri Deejarh ta ce "dama ba Momyn bane ta haifeku ke da Aunty Zaynerb ɗin?,"
Dariya Afeefah tayi tana share hawaye ta ce "E, ba ita ta haife mu ba ni da Auntie Zaynerb, Mahaifiyarmu ta rasu ranar da ta haifeni sunanta HAJARA ina matuƙar kewarta da begenta."

"Lah Balarabiyar india, kuka kikeyi ne?," Deejarh ta tambaya tana miƙewa ta dawo kusada Afeefah ɗin ta zauna.
Ba shiri Afeefah tayi dariyar pretending sai dai maganar da tayi niyyar faɗa ba ita ce, ta fito daga bakinta ba, tun daga ƙasar zuciyarta maganar ta fito, cewa tayi.
"E, mana kuka nakeyi, kukan tuna mahaifiyar mu nakeyi,"

"To tana inane mahaifiyar taku?,  Deejarh ta tambaya dan bataji lokacin da Afeefah ta ce ta rasu ba.

"Ta rasu a washe garin ranar da ta haifeni," Afeefah ta faɗa tana kuma share hawaye ta ci gaba da cewa "ni da ƴar uwata Zaynerb mun taso kwata kwata bamusan Menene soyayyar mahaifiya ba, mahaifin mu kawai muka sani kuma dashi kaɗai muka shaƙu sai kuma kakarmu AMMA Zaynerb ce ma ta shaƙu da ita fiye da dani,"
"to ita AMMA ɗin tana ina ne, halin yanzu?," Deejarh ta tambaya.
"Tana KANO STATE," Afeefah ta bata amsa, Deejarh ta kuma cewa.

"to meyasa bata dawo nan ba, ta zauna tare daku," Afeefah ta ce "tana zaune a gidan ƙanin mahaifin mu Uncle sagir ne da yake zaune a KANO ɗin shida iyalan sa, shiyasa bata dawo nan ba, kumaa, shiru tayi ganin Deejarh tana hawaye "Menene kuma ya sakaki hawaye?,"
Afeefah ta tambaya, cikin kuka Deejarh ta ce "ba komai kawai dai na tuna kakanni nane dukansu sun rasu Ummata ma ta rasu, Abbana kuma baya sona,"
Janyota zuwa jikinta Afeefah tayi tana rarrashi ta ce "addu'a zaki musu ba kuka ba, kuma Abbanki yana sonki, kawai dai ki bashi lokaci shida kanshi zai nemeki kinji ko?," gyaɗa ma ta kai tayi alama taji.

"Good girl haka nake so" Afeefah ta faɗa tana miƙewa ta nufa wardrobe dake bedroom ɗin, tana faɗin "bari muga kayan ƙawantawa ƙilama sunfi nawa kyau da tsari highly," 😍

Ba shiri Deejarh ta fashe da dariya tana faɗin "kai Auntie Afeefah,"
Dariya ita ma Afeefah tayi ta ce "E, mana da gaske nake wata ƙilama sunfi nawa kyau, ta ce kuma gobe ki shirya zamu fita  shopping, Daddy yace gobe muje ki zaɓa duk abin da ranki yakeso, kijido baki da wata damuwa koma duka kayan SHOPPING MALL kikace kinaso yace a kwaso a kawo miki gabaɗaya😂
Haka Afeefah ta ci gaba da janta da fira saboda ta mantar da ita damuwarta.

*~💅💥💅~*

*𝑯𝑨𝑳𝑬𝑬𝑺𝑨𝑻*

Fitowar ta daga bathroom kenan, jikinta sanye da bathrobe, ta hango wayarta dake saman mirror tana haske alamar shigowar kira, dayake a SILENT wayar take.
Da sauri ta ƙarisa ta ɗauka ganin 'JENNY' ce mai kiran nata yasa tayi murmushi, picking tayi sannan ta kara kunenta shiru tayi domin jin abin da Jenny zatace, sai kuma taji bata jin abin da Jenny ɗin take faɗa hayaniya yayi yawa a gurin.

"Hello Jenny, banaji fa, akwai hayaniya a gurin da kike," shiru taji, da sauri ta duba wayar gani tayi Jenny ta katse kiran.

Taɓe baki tayi a fili ta ce "wata ƙilama suna jira na a waje ne, duba clock ɗin dake manne a wall na bedroom ɗin tayi, taga ƙarfe sha ɗaya saura na dare "Kan ubancan ashe lokaci yaja haka huh,"  ta faɗa tana zama akan stool na dress mirror lotion ta shafa sama sama sannan ta miƙe closet ta nufa ta zaɓo kayan da zata saka, sannan ta dawo ta aje saman bed, zama ta kuma yi kan stool ɗin, light make-up tsantsara sama sama.
Sannan cikin ƙanƙanin lokaci ta shirya cikin Floral Dress Gown blue black mai zanen flowers pink color, sai belt pink color da ta ɗame Tummy ɗinta dashi, rigar hannun vest ce da ita saita gyara hair ɗinta in 'punky ponytail' 'straw hat' ta ɗauka pink color ta riƙe a hannunta sannan ta ɗauko zundumeman hijjab blue tasa ta ɗauka ƙaramar handbag ɗinta blue black.

*~𝑻𝒐𝒅𝒂𝒚 𝒊'𝒎 𝒊𝒏 𝒔𝒊𝒄𝒌, 𝒚𝒐𝒖 𝒔𝒉𝒐𝒖𝒍𝒅 𝒎𝒂𝒏𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓 𝒕𝒉𝒊𝒔 𝒍𝒊𝒕𝒕𝒍𝒆 𝒑𝒂𝒈𝒆, 𝒔𝒐𝒓𝒓𝒚 𝒇𝒐𝒓 𝒊𝒕 😎~*

*~✦𝑲𝒉𝒂𝒅𝒆𝒆𝒋𝒂𝒓𝒕𝒉.  𝑺𝒂𝒃𝒊'𝒖. 𝒀𝒂𝒉𝒚𝒂𝒉✦~*

🥳𝑻𝒉𝒆 𝑵𝒂𝒊𝒏𝒂𝒓𝒉 𝑲𝒅🤙


*💋💋SARAUNIYAR🎀KYAU💋💋*

______________________________________________________________________💥👑𝑻𝒉𝒆 𝑮𝒍𝒂𝒎👑💥____________________𝑩𝒚:𝑻𝒉𝒆 𝑵𝒂𝒊𝒏𝒂𝒓𝒉 𝑲𝒅____𝑲𝒉𝒂𝒅𝒆𝒆𝒋𝒂𝒓𝒕𝒉.  𝑺𝒂𝒃𝒊'𝒖.  𝒀𝒂𝒉𝒚𝒂𝒉🤙

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆
💦𝑳𝒂𝒇𝒂𝒛𝒊 𝑾𝒓𝒊𝒕𝒕𝒆𝒓'𝒔 𝑨𝒔𝒔𝒐𝒄𝒊𝒂𝒕𝒊𝒐𝒏💦🤙

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆

*𝑷𝒂𝒈𝒆 25 & 26*

Sannan ta fito daga bedroom ɗin, cikin sanɗa kamar yadda ta saba take wuce palon duk girman shi, a hankali ta tura door ɗin kitchen ta shiga, haka kawai taji gabanta na faɗauwa, da sauri ta buɗe ƙofar kitchen ɗin ta fita, da sauri sauri take tafiya har ta dan gana da ƙaramar ƙofar garden ta fice da sauri.

Ajiyar zuciya Zaynerb ta sauke daga inda take a bakin window na bedroom ɗinta, zuge curtains ɗin tayi, a zuciyarta ta yanke shawarar gobe kawai koma miye zai faru, sai tayi ma Haleesat maganar wannan satar hanyar da takeyi tana tafiya Night Club, koma miye zai faru ya daɗe bai faru ba, wani yanki na zuciyarta kuma faɗa ma ta yakeyi kawai ta sama Momy Rafi'at ta ma ta Bayanin komai, yayinda wani ɓangaren yake gargaɗinta akan idan tayi haka Haleesat ba zataji daɗi ba.

Da tunanin ya isheta a fili ta ce, "toh kartaji daɗin mana miye nawa tunda bani na sakata fitar dare ba ae."

Haleesat kuwa tana fita tun kafin ta ƙarisa gurin motar ta cire hijjab ɗin jikinta, sannan ta saka straw hat ɗin hular hannunta, akanta, sam bata lura da wata farar mota acan gefe dake fake ba, saboda duhun dare da gurin da motar yake dashi.

Tana shiga motar Zuree taja suka bar gurin, saida ta saita nutsuwar ta sannan ta kalla motar da kyau, bataga Jenny ba 'dum dadam' taji gabanta ya faɗi na rashin dalili, gabaɗaya motar mutum uku ciki, hadda ita Zuree dake driving sai Feenah dake gefenta tana shafa wayarta sai kuma ita Haleesat ɗin ta uku.

*__🏪__*

'𝑷𝑨𝑹𝑻𝒀 𝑨𝑳𝑳 𝑵𝑰𝑮𝑯𝑻'

A hankali Haleesat ta furta sunan saman laɓɓanta tana ɗan murmushi ganin irin tsadadden club ɗin da sukazo a yau.

Night club ne wanda yayi  ƙaurin suna cikin garin Abuja kuma da kewaye, guri ne na manyan yara, don masu zuwa girin sai wane da wane don ba guri ne na ƙananan qwari ba, shi kanshi kuɗin parking mota na da ake biya a Club ɗin ya ishi wani talakan Najeriya jari mai ƙarfi, don zunzurutun kuɗaɗe ne bana wasa ba, aƙalla ana biyan kuɗin parking mota a haɗaɗɗen parking lot na Club, sama da Dubu ɗari uku parking kawai, sannan yanayi yanayin mota ake bi, don idan motar ka/ki mai masifar tsada ce tofah kuɗin da mutum zai biya sai haure hakan 😎

Har yanzu ƙayataccen murmushin fuskar ta bai ɗauke ba, ta kalla Zuree da ta ƙariso gurin bayan tayi parking a gurin da aka tanadar domin yi.

Ta ce "it's pleasure babe muna wuta fah highly higher kuwa, Yau kuma nan akayo damu ne?,"
Dariya Zuree tayi tana karkaɗa car key's ɗin dake hannunta ta ce, "Yeah I you enjoy this ko kuwa a canza wani Club ɗin?,"  ta tambaya Haleesat ɗin tana ma ta nuna da gabaɗaya  haɗaɗɗen Club ɗin.

Dariya ita ma Haleesat tayi sannan ta ce "Yeah Yeah I enjoy this special Club, 'PARTY ALL NIGHT',"
Kallon Feenah tayi tana faɗin.
"yane wai Feenah yau kamar bakya walwala fah, what happening to you?,"
Tun kafin Feenah tayi magana Zuree ta rigata da faɗin, " ae barta kawai kinsan halin ta fah, ko'ince kinsan halin ku guda na miskilanci."
 
"Toh ina kuma Jenny take?," Haleesat tayi tambayar tana kallonsu su duka, Still Yanzu ma  cikin sauri Zuree ta ce "Yau batajin daɗi shiyasa fah, that's All ta faɗa tana ɗan sosa fuska game da inda inda.
"Alright kuzo mu shige fah guys, don anayi bamu," cewar Haleesat.

Ba wanda ya kuma magana acikin su suka shiga ciki, Haleesat cikin tafiyar ta juya tanayima  Feenah magana, sam bata lura ba, taji tayi karo da mutum gamm, a tsiwace ta juyo dan taga wani shafaffe da mai ne ya bugeta, bai iya bada hakuri ba, maganar da tayi niyyar yine ya tsaya cak a maqwogwaronta sakamakon ganin irin mutumin dake tsaye gabanta, dum dadam daram taji gabanta ya tsananta bugu a dalilin haɗa kwayar idanu da sukayi.
She was very Thither shocked, saboda yadda taga yanayin shi dogo fari, ga faffaɗan ƙirji, ga kyakyawan suffa irinna asalin jaruman sadaukai, ba za ta iya cewa ga yanayin fuskar shi ba, sakamakon sanye yake da face mask.

A hankali ta lumshe kyawawan idanun ta, in few secs, sannan ta buɗesu tana mai addu'ar sake kallon kyakyawan surar dake gabanta, sai dai me?.
Da buɗe idanun da zatayi, wayam ba kowa a gurin sama da ƙasa, da sauri sauri cikin zafin nama ta juya bayanta, can ta hangoshi a ƙofar fita zai fita da alama wani yake nema ko yake bi.

Da ƙarfi ta ciji pink lip ɗinta na ƙasa har saida ya fashe, da sauri  Feenah ta ƙariso gurin tana tambayar ta, ko lafiya ta tsaya a gurin.
Bata ce mata komai ba, ta kama hanyar fita daga gurin, harabar Club ɗin ta fita, amma bataga kowa ba, koda kuwa mai kama dashi ne.

Wannan karon hadda Zuree suka ƙariso gurin da take, ita taƙi gaba haka zalika taƙi baya.
Zuree da ɗan mamaki ta ce "wai Baby Leesat lafiyar ki kuwa, menene kike nema haka?,"

Sai lokacin Haleesat ta ɗan dawo cikin nutsuwar ta, kallon ta tayi cikin lumshe idanu ta ce.
"me kika gani ne, kika ce haka?," Zuree ta ce "naga kina abu kamar wata mai iska mana,  gashi yau naga kamar akwai abin da ke damunki ko?,"
Murmushi Haleesat tayi ta ce "ba komai, kawai dai yanayin garin ne, amma ba komai, So no need to worry your self, nagode da kulawa fa."

Ciki suka koma Zuree na faɗin "gabaɗaya sai naji Club ɗin yau babu, daɗi dukanku bakwa cikin walwala," Feenah ta ce "share kawai."

Suna shiga basu tsaya komai ba, kai tsaye suka haye wajen Rawa dama ba'a rabasu da ita rawar, yi suke kamar ba gobe, kuma kamar basa gajiya da ita rawar 😇

IN BRIEFLY

A taƙaice dai basu suka fito daga club ɗinnan ba, sai wajen ƙarfe biyu na dare.

A mota Haleesat ta kalla Zuree dake driving cike da nishaɗi ta ce "Babe ya naga baki ɗauka hanyar gidanmu bane, naga kin miƙa wata hanyar daban, ko dai kin manta dani a motar naku ne?."

Ƙin kulata Zuree tayi saima ƙure volume da tayi, ganin haka yasa Haleesat ta mayar da kallonta kan Feenah zatayi magana.

Da sauri kamar tana jira ta kalleta, ta jefa mata wani farin handkerchief a fuska, ko sakan bata ƙara ba, wani bacci mai nauyi ya ɗauketa.

Dariya suka sheƙe da ita a tare hadda tafawa, Zuree tana murza steering ta ce.

"yau Haleesat saita gane aya zaƙine mai masifar ɗanɗano da ita, badai ta shigo hannu ba a yau, hadda wani cewa Feenah ya naga yau bakya cikin hayyacin kine?, tayi maganar tana kwaikwayon irin muryar Haleesat.
Suka kuma fashewa da dariyar shaƙiyanci a tare, Feenah tana taunar cingum tass tass ta juya idanu ta ce.

"ae kedai, batta kawai, da shegen zaƙin murya Like a sweet," taja qwafa.

Zuree taja qwafa ita ma ta ce, "ae barta shegiya, gata da kyau, gasu  duka ƴan gidansu masu kyau kamar ƴa ƴan aljanu."

Feenah ta ce "kedai bari ina faɗamiki, barinma wannan ƙanwar nata, duk tafisu kyau da komai, miye ma sunan ta, wannan wacca ta shiga takarar gasar  𝐒𝐀𝐑𝐀𝐔𝐍𝐈𝐘𝐀𝐑 𝐊𝐘𝐀𝐔  ɗinnan?,"
Zuree ta ce wai 'Afeefah',"

Feenah ta amsa ma ta da "E, mana ita fa, sunan ma kanshi mai daɗin faɗane, gashi na LARABAWA.
Zuree ta ce "danma bakisan duka ƴan gidannasu bane, shiyasa ga gashi, ga kyau, ga diri ga komai da komai na more rayuwa haba madam,"

Haka suna gossip ɗin ƴan gidansu Haleesat  iyalan MISTER MAI KYAU.
Har suka isa wani madaidaicin flat home, irin ƙerarunnan waɗanda ƴan haya ƴan makaranta sunfi zama a irinsu.
Horn sukayi, mai gadi ya wangale musu gate ɗin gidan, suka shiga da motar, a parking lot Zuree tayi parking, sannan suka fito a tare.
Feenah ce ta buɗe back seat ta ɓangaren da Haleesat take kwance.
Zuree ta kamo hannun Haleesat ɗaya ita ma Feenah ta kamo ɗayan, a haka suka nufi cikin gidan da ita.

A wani madaidaicin bedroom suka sauketa sai da suka tsaya suka ɗan huta, sannan suka ƙara cicciɓarta suka ɗaurata saman bed ɗin.
Feenah ta kalla Zuree tana murmushin winning ta ce, "kira kice aiki ya kammala,"
Wayarta Zuree ta ciro a cikin trouser pocket ɗin jikinta wata special number ta lalubo sannan ta danna ma ta kira, ringing ɗaya aka ɗauka.
"Sir aiki ya kammala," haka kawai Zuree ta faɗa aka katse kiran, daga ɗayan ɓangaren.

Dariya Feenah ta fashe dashi tana faɗin "zamu kwashi gara wallahi,"
"ai yau sai ta kasa tafiya, raping ɗinta zanyi yadda ya kamata, Babe ɗinnan ta taramin kwaɗayi da yawa fa, yau saina korar da kwaɗayina gabaɗaya."
Zuree tayi maganar tana suɗe baki, Like a old prostitute😰

Sunkai akalla Ten minutes, suna zaune a bedroom ɗin can sukaji alamar shigowar mota gidan, da sauri Feenah ta zuge curtains, sannan ta buɗe glass window ɗin bedroom ɗin tana dubawa, wata bakar range rover ce tayi parking, sannan wata kyakyawar budurwa ta fito daga ciki.
Da sauri Feenah ta koma ta zauna daɓasa saman bed, "lafiyar ki kuwa?,"  Zuree ta tambaya ganin yadda ta dawo ta zauna jiki ba laka.
"Babu komai,"  Feenah ta bata amsa.
Ƙamshin sassayan turaren white gold ne ya fara baƙuntar hancinsu sannan mamallakiyar ƙamshin ta bayyana, kyakyawar gaske sanye cikin €nglish Gown mai shaining,  marron color iya gwiwar ta, fuskar ta rufe da face mask, mai rubutun 'GLAMOUR'.

Gabaɗayan su suka zuba mata ido, harta sama guri saman doguwar sofa dake a bedroom ɗin, zama tayi ta ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya.
"bana buƙatar kallo ya cika yawa fa, don hakan yana haddasamin  Headache."
Ta furta a hankali kamar mai ciwon baki, cikin sassanyar muryarta.
Da sauri suka janye idonsu akanta cike da kunya,. Zuree ce tayi ƙarfin halin faɗin.
"Gata mun kawo ta, kamar yadda kika buƙata, amma please zamu iya ganin fuskar ki kuwa?,"

"Because Of What Reason?,"

Ta tambaya tana kallon su da kyawawan Blue £yes ɗinta masu shaining.
Shiru ɗakin yayi, sai can Feenah ta kore shirun da faɗin, "ba damuwa, ae basai munga fuskarki ba, yanzu dai gata, sai ki bamu cikon kuɗin mu,"

Tun kafin Feenah  ta rufe baki sukaji Alert a duka wayoyin su, dake hannayensu, da sauri suka ciro wayoyin nasu suna dubawa, "kan bala'i two million's" Zuree ta faɗa da ƙarfi kuma a fili tana zazzare idanu,  kallon Feenah tayi tun kafin tayi magana Feenah ta ce.
"Kwarankwatsa nima haka ne, Two million's, na gani kamar a mafarki."

Gabaɗayan su suka mayar da kallonsu kanta cikin rawar jiki da baki, Zuree ta ce "madam duka waɗannan  kuɗaɗen nawa ne, two million's fa?,"

Sha re maganar tayi, ta kalle su ta ce "ku fara aikin da yake a zuciyoyin ku."
"Mu fara aikin da yake zuciyoyin mu, kuma, kamar ya ya?,"

Zuree ta tambaya da ɗan mamaki.
"aikin fini sa ni, oya ku fara domin nima naga yadda akeyi,"

Tuni Feenah ta ramfo menene budurwar take nufi, da sauri ta ce "mu fara fa, kikace ke banda ke?,"

"E, ta bata amsa, ta ci gaba da cewa "inaso na koya ne, shiyasa na ce ku fara ae,"
Wannan karon Zuree ce, ta ce "to a gabanki kikeso muyi, kike nufi?,'
tayi ma ta tambayar tana fito da ƙananan idanun ta waje, ita sai yanzu ta fahimci abin da take nufi.
"E, haka nake nufi, ko bazaki iya bane, na nemi wasu, ko kuwa dai rashin kunyar naku bai kai nan bane?,"
Da sauri Feenah ta ce "iyawa ma kuwa, yanzu zakiga iya aiki, tashi tayi ta haye saman bed ɗin, kallo ɗaya ma zaki fahimci yadda ake harkar, madam kyakyawa, cewar Feenah ɗin sannan ta fara kici_kicin😬

Kamar a mafarki taji ana shafata, ana kuma ƙoƙarin rabata da tufafin jikinta😳

A hankali take buɗe idanun ta da suka ma ta nauyi, biji biji ta fara ganin mutane akanta, ga wani shafa da ake ma ta kamar za'a yaga mata fatar jiki, ba shiri ta buɗe idanun ta gabaɗaya, abin da ta gani ne, yasa ta ƙara rumtse idanun ta, tana fatan idan ta kuma buɗewa taga mafarkine, ba gaske ba, amma ina tana kuma buɗewa abin da ta fara gani da farko shine ta kuma gani yanzu ma.
Da sauri ta yunƙura zata miƙe tsaye, ganin haka yasa Feenah ta mayar da ita da ƙarfin gaske.

Matsananicin kokawa suka farayi Haleesat tana ƙoƙarin qwatar kanta, yayinda su Zuree suka dage, baji ba gani, akan saisun rabata da tufafin jikinta, ita kuma taƙi ta basu damar hakan😫

Da Allah ya ba ta sa'a ta buga kan Feenah da headboard da ƙarfin gaske, amma kamar ta bige dutse, saima wani gurnani da Feenah takeyi ta kuma dawowa har tana tsinka ma ta mari a fuska.

Jama'a saiga Haleesat tana ihun neman taimako, wani cizon da Zuree tayi ma ta a cinya ne yasa, ba shiri Haleesat ta saki ihun da yasa budurwar dake zaune gefe tana kallon komai rufe kunenta da duka hannun ta tana rumtse idanu.

Da ƙarfi ta faɗin "ku rabu da ita, I say Stop It Please,"

Amma ina kamar tanayi da dutse, buɗe murya tayi da wani tsawa take faɗin.

"ku rabu da ita nace," ku wasu kalan dabbobi ne wai, mace ƴar uwanku kuke ƙoƙarin yima fyaɗe, anya kuwa kuɗin mutane kuwa?,"

Da sauri Zuree dake wuya, ta juyo zata ma ta magana a zafafe, wannan juyawar da tayi, yaba Haleesat dama, aikuwa bata tsaya jiran komai ba, ta dage iya ƙarfin ta na bara dana bana ta haɗa ta gannawa Zuree cizo a damtsen hannu😂

ihun azaba Zuree ta saki tana rumtse ido, dan kuwa cizon ya shigeta yadda ya kamata, ko kafin Feenah tayi wani yunƙuri, Haleesat ita ma tayi kukan kura ta buga kan Feenah da headboard na gado da masifar ƙarfi ta ƙara bugawa saida tayi hakan fin sau huɗu, Wanda hakan yasa Feenah sakin ihun azaba nan take ta sume a gurin😅

Huci kurum haleesat take tana faɗin "Shegu ƴan iska kawai, maciya amana condemned kawai Allah yayi wadaran hallinku, ƴan kutmarrr  😳🏃

Gabadaya Haleesat bata cikin hayyacin ta, ga dogon gashin kanta ya rufe ma ta fuska.

Juyowa tayi kan budurwar dake gefe tana kallon ta babu alamar tsoro tare da ita.
A hankali ta sauko ƙasa ta zauna tayi tagumi hannu bibbiyu, tana kallon budurwar, a hankali budurwar ta takai hannu ta cire face mask ɗin dake rufe da fuskar ta.
Nan kyakyawar fuskarta ta bayyana, wanda sai da tasa Haleesat lumshe ido, duk da har yanzu bata gama dawowa hayyacinta ba, sannan ta buɗesu kar akan budurwar da bata taɓa ganin ta ba, ko haɗuwa da ita ba, tsawon rayuwarta sai yau kuma yanzu, a wannan taƙin da suke ciki.

"wato dai idan na fahimta, kece kika sakasu ko?," "to amma meyasa?,"
Haleesat ta jerowa budurwar waɗannan tambayoyin, shiru ta ma ta, kamar ba zata bata amsa ba, sai kuma can ta nisa sannan.
Buɗar bakinta sai cewa tayi, "haka kawai, na sakasu,"

Da mamaki Haleesat take kallonta, sai kuma tayi murmushi ta ce "badai haka kawai ba akwai dai dalili, kuma wannan dalilin nakeson sa ni."

Ɗan murmushi budurwar tayi sannan ta ce "ki yarda dani haka kawai, naji inaso nasan yadda akeyin abin, don naga Al'ummar yanzu ko nace matan yanzu sunfi raja'a akan yin hakan,"

"oh wato shine kuma, kikace bari ki gwada akaina ko?,"

Haleesat ta tambayeta cike da takaici, sannan ta ci gaba da cewa "amma sha re wannan, kinamun kama da wata, amma kuma na manta ko wacece, to komadai wacece matsalar ta,  yanzu ki faɗamin, a inda kika taɓa ganina, da har kikaji sha'awar gwada hakan akaina,"

kai tsaye budurwar ta bata amsa da "a Club ne, wata ranar Sunday, idan bazaki manta ba, kinyi ma wani ma'aikacin Night club, ɗin faɗa akan ya kawo miki whiskey ko?,"

"oho kice anan kika ganni ko, yanzu  na fara fahimta," cewar Haleesat.

Budurwar ta ci gaba da cewa, shine ni kuma tun daga ranar na saka miki ido, har taƙaitaccen tarihin ki na sa mo."

Ajiyar zuciya Haleesat ta sauke, duk wannan maganar fa, da sukeyi cikin nutsuwa sukeyi kamar ƙawaye ko kuwa waɗanda suka san juna.
sannan ta ce "shin zan iya sannin sunan ki?,"

"𝖧𝖤𝖠𝖱𝖳 𝖢𝖧𝖤𝖭𝖦 𝖩𝖴𝖭𝖦"  budurwar ta bata amsa, Nice name, Haleesat ta faɗa, ta kuma cewa zan iya tambayar ki wani abun kuma?,"

Jinjina mata kai Heart tayi alamar 'E', haleesat ta ce "kin taɓayin lesbian ne?,"

Da sauri Heart ta ce "a'a,"
Haleesat tayi nodding kai, ta kuma cewa "kin taɓayin zina?,"

Yanzu ma da sauri Heart ta girgiza ma ta kai alamar dai 'a'a' sannan ta fara magana.

"Ban taɓa aikata zina ba, ko lesbian, amma anso asakani a hanyar yi,"

"a'ina kuma suwa?,"

Haleesat ta jero mata tambayar, Heart ta ce "a school kuma ƙawayena," ta cigaba da cewa "baso ɗaya ba, ba kuma sau biyu ba ƙawayena sunsha ɗaureni, suce sai sunyi raping ɗina amma basu taɓa samun dama akaina ba, abin har mamaki yake bani,"

"Saboda me" cewar Haleesat ido waje, Heart ta ce "nima dai bansani ba, amma dai wasu suna cewa saboda kyawuna ne, yayinda wasu suke faɗin saboda diri,"

Dariya Haleesat tayi ta ce "ai sun faɗa gaskiya, shiyasa akeso mace ta dinga suturta jikinta da hijjabi a koda yaushe."

"Menene kuma hijjabi?," Heart ta tambaya, ɗan murmushi Haleesat tayi tama, manta ko wacece a gabanta, ta ce.

"Sanya hijabi bin umarnin Allah ne da annabin sa, kariya ne daga fitina, alamace ta tsarkin zuciya, kyakkyawan ɗabi'a ce, garkuwa ne daga faɗawa halaka, sutura ce daga al'aura, kariya ne da ga mazaje marasa mutunci fasiƙai, kariya ne daga aljanu, kariya ne daga shiga cikin azabar Allah da fushinsa, bautar Allah ne sanya hijabi."

Ajiyar zuciya Heart ta sauke jin Haleesat takai aya, sannan ta ce "to zan iya saka hijjab ɗin?,"  murmushi Haleesat tayi ta ce "zaki iya mana."

Juyawa tayi tana kallon su Zuree da Feenah da sukayi tsuru tsuru dasu ta ce "me kuka yima Jenny?,"
Da sauri Zuree ta ce "Feenah ce ta saka mata qwayar bacci a lemu."

Girgiza kai Haleesat tayi sannan ta ce "kunyi ma kanku, kuma ban yafe ba, ta faɗa tana miƙewa saman bed ɗin, tahau ta ɗauko ribbon's ɗinta da hularta ta saka.

Kallon Heart tayi bayan ta dawo ta zauna a ƙasan ta ce, "sunana 'Haleesat Abubakar Mai Kyau', am very amazing to meet you," ta ɗanyi shiru sannan ta ci gaba da cewa.

"zamu iya ƙulla ƙawance dake?, tayi ma ta tambayar tana miƙa ma ta fresh hand ɗinta.

Hannun Haleesat kawai Heart take kalla sannan ta sauke ajiyar zuciya ta ce.

"yanzu bakiji haushin abin da naso ayi miki ba?,"

Haleesat tayi dariya sannan ta ce "ko kaɗan banji haushi ba,  saima darasin rayuwa dana koya, da ma can tun farko laifi nane da nake zuwa Night club, amma yanzu, na fahimci wani abu a rayuwa, wannan abun shi ne bada kowa ake yadda ba, a duniya, komai dangantakar ka da mutum kuwa."

Murmushi Heart tayi sannan ta miƙawa Haleesat hannunta tana faɗin "kamar yadda na faɗa miki a farko sunana HEART CHENG JUNG' Naji daɗin haɗuwata dake."

Murmushi ita ma Haleesat tayi sannan tasa hannunta cikin na HEART suka ƙulla ƙawance.

Clock ɗin dake manne a wall na ɗakin ta kalla lokaci yaja sosai ƙarfe huɗu na asuba saura.

Kallon su Feenah tayi ta galla musu harara kamar qwayar idonta zai fito, sannan ta kalla Heart ta ce inaga fa saidai mu kwana ana gidan, saboda lokaci yaja sosai,"

"Okay baki da damuwa Heart ta bata amsa, tana murmushi.

Tashi Haleesat tayi ta shiga toilet bata daɗeba ta fito, kan bed ta haye abinta kallon Heart ta kuma yi, tayi murmushi sannan ta ce "saida safe, sabuwar ƙawa,"

Heart da ɗan mamaki ta ce "bakyajin tsoron su kuma yunƙurin yi miki wani abun?," tayi ma ta tambayar iyakar  gaskiyar ta, dariya Haleesat tayi ba shiri sannan ta ce.

"Idan na amince da mutum na gama nawa, saura ya rage nasa ya kyautatamin ko ya ha'inceni, Nikam banada matsala shida Allah."

Heart ta ce "kina burgeni sosai fa,"

Haleesat tayi dariya, "da gaske nake fa" cewar Heart, "ai na sa ni," Haleesat ta bata amsa.

Murmushi Heart tayi sannan ta kwanta a saman doguwar kujerar da take.

Lumshe ido Haleesat tayi tana tuno kyakyawan mutumin da ta haɗu dashi ɗazu da kyakyawar surarshi, mutumin da ko ainihin fuskarshi bata sa ni ba, balle kuma sunan shi.

*🩸ʂαɾαυɳιყαɾ ƙყαυ 🩸*

*☆ƚԋҽ ɳαιɳαɾԋ ƙԃ☆🤙*

Kiran sallah ne ya tasheta da ga baccin da ya fara ɗaukarta, a hankali ta buɗe kyawawan idanunta, bakinta ɗauke da addu'ar tashi daga bacci saukowa tayi daga kan bed ɗin toilet ta shiga ta ɗauro alwala, sannan ta fito, dagewa tayi iya ƙarfinta ta ɗakawa Zuree duka, a firgice kuma ta gigice ta tashi zaune tana zare ido.

"Bani key ɗin motar ki,"  Haleesat ta faɗa a dake kuma fuska a ɗaure, ba musu Zuree tasa hannu a trouser pocket ɗinta, ta ciro key ɗin sannan ta miƙa ma ta.

Karɓa Haleesat tayi sannan ta fita can parking lot motar Zuree ta buɗe ta ciro hijjabinta da kuma handbag ɗinta.

Cikin bedroom ɗin ta dawo bata ga Heart ba, da alama toilet ta shiga handbag ɗinta ta buɗe ta ciro wani madaidaicin scarf shimfiɗa shi tayi bayan saka hijjabinta ta tayar da sallah, tana idarwa bata tashi daga wajen ba saida tayi azkhar.

Wall Clock ta kalla ƙarfe bakwai da rabi na safe, kallonta ta mayar kan Heart da tun fitowar ta daga toilet taga tana sallah ta zuba ma ta ido ba ko gyaftawa.

Ɗan murmushi tayi sannan ta ce "barkanki dai madam yanzu zan iya tafiya gida?,"  murmushi Ita ma Heart tayi sannan ta amsa da  "yauwa barka, zaki iya."

Tashi Haleesat tayi ta ɗauka handbag ɗinta, bayan ta saka scarf ɗin aciki.

Waje suka fito dukansu hadda su Feenah da Zuree waɗanda ko sallah ma saida rana ta fito gatsau sannan suka gudundura.

"Ko zan iya rage miki hanya" Heart ta tambaya tana kallon Haleesat ɗin.

Haleesat bata ce ma ta komai ba ta nufi motar Heart ɗin, har zata shiga kuma saita juyo, ta kalla su Feenah ta ce "daga yau nida ku anyi baram baram kar ɗayanku tayi gigin koda kirana a waya ne daga yau nida ku  b.s.b.s.,"

Tana gama faɗin haka ta shige motar Heart taja suka bar gidan, ba wanda ya iya magana acikin har suka iso unguwan su Haleesat ɗin, sai kuma lokacinne Haleesat ta fara jin faɗuwar gaba daurewa kawai takeyi.

Guri Heart ta samu a gefen wata tree a unguwan tayi parking, fitowa Haleesat tayi ta zagaya ta ɓangaren da Heart take, ɗan kwankwasa glass ɗin window tayi.

Buɗewa Heart tayi tana kallon Haleesat ɗin, murmushi Haleesat tayi sannan ta ce "nagode fa, amma please karki ƙara tunanin sannin wannan abun,"
"saboda me?," Heart ta tambaya, "saboda babu kyau,"  Haleesat ta bata amsa ta cigaba da cewa "zan iya samun phone number ɗinki?,"
Heart ta ce "sosai ma, why not,"  wayarta ta ciro a cikin handbag ɗinta tana rubuta lambar wayar da Heart take karanto ma ta.

Ƙurawa wayar ido tayi bayan ta gama rubuta lambar da Heart ɗin ta karanto ma ta ganin lambar bana Nigeria bane yasa ta kalla Heart ta ce "wannan lambar fa?,"

"Number nane na ƙasata, Ƙasar France yau zan koma na gama abin da ya kawoni nan ƙasar,"

 Heart ta bata amsa.
Qura ma ta ido Haleesat tayi ita sai yanzu ma take ƙarewa Heart ɗin kallo yadda ya kamata.

Kyakyawa ce sosai, don bata mayi kalar ƴan nigeria ba, da gani ma bata da wata alaqa da ƙasar, amma kuma meyasa taga kamar tana mata kama da wata?, amma kuma ta kasa tuna koda wa Heart ɗin take kama.

Sha re tunanin tayi, sannan ta kalla Heart ta ce "okay Allah ya tsare hanya, bari na shiga gida," ta faɗa bata jira amsar taba tabar gurin.
Ganin haka yasa ita ma Heart taja motar ta tabar haɗaɗɗiyar unguwan.

Kwankwasa ƙaramar ƙofar gate ɗin Haleesat ta farayi zuciyarta na harbawa jin ba'ada niyyar zuwa a buɗe ma ta ne, yasa ta ƙara ƙarfin bugun amma shiru, can taji alamar za'a buɗe, ɗan matsawa tayi gefe.
Isah ne ya buɗe gate ɗin yana faɗin "bama za'a bar mutum ya samu koda baccin sa fe yayi ba, anzo an takura da bugu nasan ma bazai wuce ƴan maula ba, to ai sai aja please a rungumi sorry  domin Alhaji Abubakar Sameer Lamiɗo  bayanan kuma ma.......

Sauran maganar da yayi niyyar gasa ma koma waye ne, ta maqale a bakin shi, sakamakon ganin wacca take tsaye a ƙofar, da sauri ya matsa gefe yana goge zufar da ta fara wanke mishi fuska, dan kuwa bai manta wahalar da ya sha ba a lokacin da yayi ma Lailah dariya ba, da tasa aka kusa korar shi daga aiki saida ƙyar ya samu Lailah ta haqura.

Haleesat ko kula sannu da zuwan da Isah yake ma ta batayi ba ta shige ciki gabanta na bugu da qarfin gaske.

Knocking ɗin ƙofar palon ta shiga yi baji ba gani, a zuciyarta kuwa tunanin yadda zazu kwashe da ƴan gidan take, dan ma sauƙinta ɗaya taji Isah na faɗin Daddynsu Mister Mai Kyau  baya nan.

Jin an buɗe ƙofar ne, yasa ta ɗago daga tsugunawar da tayi, domin har wani ciwon mara takeji.

Ajiyar zuciya ta sauke ganin ERINA ce mai gyara palo, hanya Erina ta bata ta wuce ciki, shiga palon tayi bakinta ɗauke da addu'o'i kala kala.
Bata ga kowa a palon ba, dan haka da saurinta ta nufi hanyar bedroom ɗinta, har ta saka ƙafa zata shiga ɗakinta taji muryar Auntie Nainarh tana kiran sunanta.

Rumshe idonta tayi da ƙarfin gaske sannan ta juyo dahm da dahm taji zuciyarta ta bada bugu saboda tsananin tsoro.

Duka Ƴan gidan ne zaune a dinning table hadda Momy da ta warke tsaf tana tafiya abinta.

A hankali ta fara taka ƙafafunta tana ƙarisawa dinning ɗin, yayinda gabaɗaya sassan jikinta babu inda baya rawa kamar mazari, cak taja tunga ta tsaya a tsakiyar palon taƙi gaba taƙi baya, kamar suna jira ta tsaya gabaɗayan su suka taso sukayo kanta da tambayoyi kowa da kalar tambayar da yake jefo ma ta.

Ganin haka yasa Momy Rafi'at ta daka musu tsawa cikin faɗa ta fara magana.
"wai ku wasu kalan mutane ne, a haka ne zata baku amsa koya da kalar tambayar da yake ma ta, taya zata iya baku amsa, ku sama guri ku zauna mana."

Umarnin ta suka bi gabaɗayan su suka zazzauna Nainarh, Nailah, da kuma Zaynerb a Three sieter, sai kuma Afeefah, Lailah a two sieter, sai Deejarh one sieter, sannan momyn ta kamo hannun Haleesat ta riƙe suka zauna a three sieter a tare da ya ke kujeru set biyu ne a palon.


*💋💋𝑆𝐴𝑅𝐴𝑈𝑁𝐼𝑌𝐴𝑅 𝐾𝑌𝐴𝑈💋💋*

*👑𝑇ℎ𝑒 𝐺𝑙𝑎𝑚 𝑄𝑢𝑒𝑒𝑛👑*

*𝑊𝑟𝑖𝑡𝑖𝑛𝑔 & 𝑆𝑡𝑜𝑟𝑦 𝐵𝑦*

*𝐾ℎ𝑎𝑑𝑒𝑒𝑗𝑎𝑟𝑡ℎ 𝑆𝑎𝑏𝑖`𝑢 𝑌𝑎ℎ𝑦𝑎ℎ*

{♥︎𝑇ℎ𝑒 𝑁𝑎𝑖𝑛𝑎𝑟ℎ 𝑘𝑑♥︎}

💘*𝘓𝘈𝘍𝘈𝘡𝘐 𝘞𝘙𝘐𝘛𝘛𝘌𝘙𝘚 𝘈𝘚𝘚𝘖𝘊𝘐𝘈𝘛𝘐𝘖𝘕*💘🤙

<><><><><><><><><><><><><><<><><><><><><><>><><><><><><><

*Page 27&28*

Kallon Haleesat dake hawaye, Momy Rafi'at tayi, sannan murya ƙasa ƙasa ta fara ma ta magana, "Haleesat ina kika shiga ne?,  yau ba'a ganki ba a gidannan ba, gabaɗaya lungu da saƙo na gidannan babu inda bamu duba ba, amma bamu ganki ba, faɗamin Menene ya faru dake kuma daga ina kike yanzu?, please tell me, everything my dear."
Duk a lokaci ɗaya Momy Rafi'at ta jerowa Haleesat waɗannan  tambayoyin kuma ɗaya bayan ɗaya.

Shiru Haleesat tayi taƙi tayi magana sai faman matsar qwalla takeyi.
"wai nace bada ke ake magana bane, da zaki tsaya kina ma mutane kukan banza da hofi," a wannnan taƙin Nainarh ce tayi maganar ranta a mugun ɓace, dan ji take kamar ta tashi ta shaƙe wuyan Haleesat ɗin, har saita faɗa ma ta gidan uban da ta kwana, ta tabbatar da Haleesat ba'a gidan ta kwana ba.

A hankali Haleesat ta buɗe bakin da tsaban tsoro har kakkarwa yakeyi, ta ce "Kidnapping ɗina, akayi jiya da dare."

Tayi maganar a gajarce, kuma ta  faɗa ne, tana tauna laɓɓanta na ƙasa.

Gabaɗayan su suka haɗa baki cike mamaki gurin faɗin "what kidnapping, fa kikace, anyi naki, to a'ina kuma su waye."

Dukansu suka haɗa baki wajen yi ma ta wannan tambayar, amma banda mutum biyu, cikin waɗanda sukayi tambayar, wato Zaynerb da Momy Rafi'at.
Zaynerb kwata kwata bata yarda da abin da Haleesat ɗin ta faɗa ba, musamman ma da taga yadda take tauna laɓɓanta na ƙasa, tasan Haleesat farin sa ni bata iya qarya ba, inma tayi sai an gano ta, saboda indai tayi qarya saita dinga cizan laɓɓanta na ƙasa da ƙarfi, shiyasa ma Zaynerb ɗin kwata kwata bata yadda da abin da Haleesat ɗin ta faɗa ba.

Momy Rafi'at kuwa bazan iya cewa ga ainihin abin da ke ranta ba, saboda yadda tayi act, komai qwaqwafin mutum sai dai ya batta kawai😇

"Ki bamu amsar, mana ana tambayar ki, kinyi shiru su waye sukayi kidnapping ɗin naki?, kuma mai suke nema, sannan kuma garin yaya kika kuɓuta idan ma sacekin akayi da gaske?."
Wannan karon Nailah ce tayi maganar ranta a mugun ɓace, da rainin wayon da Haleesat ɗin takeso tayi musu.
Afeefah kuwa kasa cewa komai tayi dan mamaki, haka ma ita  Lailah, sai zubawa sarautar Allah ido kawai.

"Dan Allah kuyi hakuri, zan faɗa muku, amma please kubarni, ba yanzu ba, please ku bani lokaci dan Allah na roƙeku," tana  maganar ne, cikin haɗa hannaye alamar roƙo,  tashi tayi da gudu ta shige bedroom ɗin ta, ta rufo ƙofar da key sannan  tabar key ɗin ajikin ƙofar.
Saman bed ta faɗa tana kuma fashewa da wani sabon kukan, saida tayi ma'ishi sannan ta miƙe ta shige bathroom, wanka tayi sannan ta fito wardrobe ta buɗe, ta ciro wata doguwar Gown ta Abaya ash color nd red, ta saka sannan tayi rolling ɗin mayafin Abayar akanta, ko lotion bata shafa ba, ta kwanta saman royal bed ɗinta.
Lumshe idonta tayi tana tariyo abin da ya faru gabaɗaya daga jiya da dare zuwa yanzu, rayuwarta ta sauya akala, cikin  brain ɗinta take tuno komai, tamkar lokacin komai ya faru.

Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta buɗe beautiful eyes ɗinta,  zumbur ta miƙe tsaye, tana zazzare idanu, ganin wacca take gabanta, a tsorace ta ce "ta ina kika shigo ɗakin nan?,"

Guri Zaynerb ta samu ta zauna fuska a turɓune, sannan ta bata  amsa da faɗin.

"Ba wannan tambayar ya kamata kiyimin ba, kamata yayi kice meya kawo ni, bawai 'ta ina na shigo ba."

Gyara zama Haleesat tayi, ita gabaɗaya tension ɗin da take ciki yasa, ta manta da akwai wata ƙofar ta bedroom ɗin Zaynerb, wanda kai tsaye zata kawoka bedroom ɗin Haleesat ɗin.

Ajiyar zuciya Zaynerb ta sauke, da niyyar zatayi magana, da sauri Haleesat ta ɗaga ma ta hannu, sannan ta ce "ba yanzu ba, dan Allah Zaynerb ki rabu dani, nayi alƙawari zan faɗamiki abin da ya faru, amma ba yanzu ba please please please.

Kallon ta Zaynerb tayi da kyau sannan tana nodding kai, alamar gamsuwa, ta ce "na yarda dake Haleesat, kuma nasan kinsan haka, ni nasan ba zaki bamu kunya, Sannan karki manta Daddy yana ƙaunar mu, yana sonki sosai, dan Allah karki bashi kunya Haleesat, shawara na baki a matsayin ƴar uwa ta gari, kuma mai ƙaunar ki, fatan zaki fahimce ni."

Da sauri Haleesat ta kalle Zaynerb ɗin, jin abin da ta ce, ɗa ga ma ta kai Zaynerb tayi sannan ta ce "ki fito zamu tafi shopping kuma yanzu."

Tashi Haleesat tayi ta sauko daga kan bed ɗin, wardrobe ta buɗe ta ciro wani zumbulelan hijjab ash color, ta saka sannan ta juyo tana kallon Zaynerb ɗin  ta ce.

"na shirya, zamu iya tafiya,"

Da ɗunbin mamaki Zaynerb take kallon Haleesat ɗin, ganin wai yau kuma hijjab tasa da kanta, a yau, ba'a tilas ta ma ta ba.
Gaza jurewa tayi saida ta kalla Haleesat ɗin sannan ta ce tana murza idanu " anya kuwa, Haleesat ce a gaba na?,"  

Murmushi Haleesat tayi ita kanta mamakin sauyawarta lokaci guda take.
"Ni ce mana, me kika gani, kikamin wannan tambayar?,"

"naga kin canza, sosai fa, Zaynerb ita ma, ta bata amsa tana murmushi, Haleesat ta ce "a hakan, na canza ko?,"  Zaynerb ta ce "E, mana."

Fitowa palo sukayi anan suka tarar da gabaɗaya ƴan matan gidan duka, Afeefah, Lailah, Deejarh sai su Auntie Nainarh da Nailah.

Gabaɗayan su sanye suke cikin tufafi iri ɗaya dukansu, Abaya ne ajikin su farare sai kuma mayafin Abayar, shi kuma baƙi hadda Zaynerb, da take tare da Haleesat ɗin.

Deejarth ne kawai sanye cikin doguwar rigar atamfa sai kuma hijjab da ta saka iya gwiwa fari.

Gabaɗayan su kallon Haleesat suke wanda hakan yasa tasha jinin jikinta, Lailah ce ta kasa hakuri ta ce "Auntie Leesat, yau kuma kece kika saka hijjab, hijjabin ma dogo haka, lallai yau akwai story na ɗaurawa a status😀

Ko kula Lailah dake suruntu irinna tsokana, Haleesat batayi ba, saima hannun Zaynerb da ta kamo suka fita daga palon.

Ganin haka yasa suma suka mara musu baya, Afeefah ce take faɗin "yau dai muna ganin sauyi da yawa a gidannan."

Gabaɗayansu a parking space suka hallara, Haleesat da Zaynerb suka shiga mota ɗaya driver yaja.
Yayinda  Nainarh da Nailah suka shiga mota ɗaya suma driver yaja.
Sai kuma Afeefah da Lailah da kuma Deejarh suka shiga mota guda suma da driver yaja suka bar gidan a nutse.

Momy Rafi'at dake kallon su, ta saman balcony na ɓangarenta, ta sauke ajiyar zuciya tana gyaɗa kai fuskar nan a haɗe kamar hadari yayi baƙi.
Bedroom ta koma da sauri ta ɗauka wayarta dake gefan drawer, wata privet number ta lalubo wanda akayi saving da rubutun chinese sannan ta danna ma ta kira.

__🎀____

A bakin wani kata faren shopping mall motocin nasu guda uku duka farare sukayi parking, a tare ko wannensu ya fito daga motar da yake hanyensu cikin na juna.

Habba nanfa kallo ya koma sama wai akace shaho ya ɗau giwa, gabaɗaya hankalin ƴan mata da samarin, dake wajen ya dawo kansu, kyau iya kyau malam, To dayake ita ma Deejarh farace saita haɗe dasu kai sai kace ƙaramar ƙanwar su ce ita saboda yadda sukayi similar.

Cikin nutsuwa da wayewa irinna cikakuna ƴan boko, kuma waɗanda ilimin addini ya ratsasu highly, suke tafiya abinsu a tare.

'MAI KYAU ABBAN FEEFAH SHOPPING MALL'

Deejarh ta karanta abin da taga an rubuta a saman Ƙaton shopping mall ɗin da suka nufa, babban plaza ne mai kimanin hawa ashirin da biyar ciki, kusan komai na glass ne a gurin, ga security nan, masu kula da shige da fice.

Shiga ciki sukayi, baki da hanci kawai Deejarh ta saki, ganin irin kyau da tsaruwa irinna na gurin, gabaɗaya ma'aikatan gurin sun taru guri guda suna kawo gaisuwa, ga ƴaƴan 'MISTER MAI KYAU' idan wannan ya kawo gaisuwa aka wuce gurin da yake, wanda akazo kanshi shima yayi, Deejarh bata gama shan mamaki ba, har saida taga wasu daga cikin ma'aikatan gurin sun jero kekunan da ake zuba siyayya a ciki in  Aisle, sun taru guri ɗaya suna jira su Afeefah su fara zabar abin da suke so, su kuma suke turo kekunan suna binsu a baya, har sai sun kammala.

Hannun Deejarh da ta dage tana nuna ainihin kalar ƙauyanci a gurin, Afeefah taja ganin yadda ta saki baki da hanci tana kallo.
Ɓangaren kayan sawa ta kaita, kallon Deejarh ɗin Afeefah tayi, murmushi ta ma ta sannan ta ce.

"ki zaɓi kalar  abin da ranki keso kinji, baki da matsala,"  
"to shikenan,"  Deejarth ta ba Afeefah, amsa sannan ta fara ruwan ido, tsaban haɗuwar gurin rasa dame zata fara tayi, sai faman ruwan ido take tama rasa me zata zaɓa, gane hakan ne, yasa Afeefan tayi murmushi sannan ta fara jidan ma ta kaya kala kala iri iri.

Tun daga kan abayoyi, atamfofi, materials masu tsada, laces, shadoji, £nglish wears, jakun kuna, gyalulluka, takalma, sarƙoƙi na gold, abin hannu.
Zobe, kayan kwalliya, da dai sauran su.

Kallon Haleesat da tayi shiru, Zaynerb ta kuma a karo na ba adadi, tana ƙara karantar yanayinta, ta lura tunda suka shigo gurin Haleesat bata ɗauka favorates ɗin ba, wato €nglish wears ko wasu ƙananan kaya ba, saima atamfofi da yadin hijabai dama hijaban da kuma abayoyi da taga tana faman jido ido rufe.
Sosoi mamaki ya kamata highly, sai dai bata ma ta magana ba,  ta rabu da ita.

Hango wani perfect perfume, irin na musamman ɗinnan kuma wanda ta daɗe tana neman kalan shi, bata samu ba, sai yanzu, yasa ta saki murmushi sannan in over rushing, ta nufa gurin, ta kai hannu kenan zata ɗauka, taga wani hannun da ba nata ba, yayi gaggawan ɗauka kafin nata hannun ya ɗauka.
Da sauri ta ɗago dan ganin wani mahaluki ne, haka.

"Tabarakallahu ahsanul khalin😍 Masha Allah😎 Anya kuwa wannan mutum ne tsaye a gabana a wannan TAKUN?,"

Wato tsaban kyau da irin haɗaɗɗiyar surarar, jikin wannan kyakyawan Mutumin dake gabanta ne, yasa tayi wannan maganar, tare da yiwa kanta wannan tambayar, yayinda kyawawan idanunta, suke kafe ta ƙure wa, mamallakin haɗaɗɗiyar kyakyawar surarar dake gabanta😇

Ganin tsantsan kyau da kamala daɗin daɗawa, ga wani uban kwarjini da ya ma ta, wannan bawan Allah dake a tsaye gabanta, sanye cikin  Expensively GUCCI higher  Dress, tun daga kan p-cap brown color, dake nutse cikin sumar kanshi wacca jelar ta, tsaban tsayin da take dashi, ta leƙo ta waje.

Har izuwa Cost  shoes ɗin dake special kyawawan ƙafafun shi, komai na companyn 'GUCCI' ne, hatta tsadadden watch ɗin dake ɗaure a tsintsiyar hannun shi.

Ta sani kuma tasan sannan tanaji ana faɗin tanada kyau na nunawa a television kyau irin highly ɗinnan, amma yau kuma a yanzu sannan a wannnan taƙin, taga wanda ya damata a kyau nesa ba kusa ba, ya shanye.

Tsayawa tayi da kallon ƙurillan da take mishi, saida ta saita nutsuwar ta sannan ta kuma kallon shi ta ce "please bawan Allah, ka barmin wannan perfume ɗin, ka nemi wani."

Tun kafin ta ƙarisa mishi maganar ya jefo ma ta tambaya da faɗin.

"Because of what reason"

Yayi ma ta tambayar a gajarce, ɗan jim tayi sannan ta ce "saboda ina sonshi sosai fa, kuma dani yafi dacewa, bawai dakai ba." Ta bashi amsar a ɗan tsiwace.

Gyara tsayuwar shi yayi yana lumshe kyawawan idanun shi, sannan ya ce "amma kuma, na ga maza ne ko, And naga ke macece, So bakya buƙatar amfani da abin da, ba naki ba."

Kallon shi tayi jin abin da yace, sai kuma tayi murmushin rainin wayo ta  bashi amsa.

"E, na sani akwai wanda nakeso naba ne shiyasa, sorry dan Allah ka bani, ka nemi wani, rayuwata zan ba, kuma kasan rayuwa yadda take ko?,"

Yi yayi kamar zai bata, sai kuma ya fasa ya jefa cikin kwandon dake gaban shi nasa kayan siyayyar, har zai tafi, sai kuma ya juyo ya kalleta sannan yace.

"ki nemi wani fa, wannan ya zama nawa."

Yana faɗin haka yayi gaba abinshi ya barta da bin bayan shi da kallo tana cizan yatsa.

Jin an taɓota ne yasa tayi saurin juyawa tana kallon wacca ta taɓeta.
Deejarh ce tana murmushi ta ce "Auntie Afeefah ina kikaje ne,  inata neman ki, amma banganki ba, sai yanzu?,"

share maganar Afeefah tayi Sannan ta kamo hannun Deejarh ɗin.
"zo mu tafi gida angama siyyayar, na yau,"

Bin bayan Afeefah Deejarh tayi, suka nufa wajen dasu Nainarh suke, saida suka jira su, Nailah suka kammala sannan suka ɗunguma suka fito a tare ma'aikatan gurin suka biyosu da niƙi niƙin shopping thing's ɗin da sukayi suka saka a wata mota na Mall ɗin, zata kai musu gida.

Kamar ance Afeefah ta juya, aikuwa tana juyawa ta hangoshi cikin abokanshi suna tsaye daga gefan kwalta, da alama wani suke jira, ɗan taɓo Lailah tayi, sannan ta ma ta nuni da shi, a daidai lokacin shima ya juyo....

Murmushi Lailah tayi domin ta ganeshi,  'SABBIR SALIS MAI NAIRA'.

cikin sauri ya ƙariso gurin da suke a tsaye, kallon Afeefah yayi sannan ya mayar da kallon shi akan Lailah, ya fa ruɗe ya kasa gane wacece ma Lailah a cikin su saboda yanayin shigar dake jikin su kala ɗaya ne, baya da hakan kuma Afeefah da Lailah suna ɗan kama, normally irin wanda ake samu tsakanin ƴan uwa da suka haɗa uba ɗaya😍

Ganin haka yasa Lailah tayi murmushi sannan ta ce "barkanka dai, aboki ya kake?,"

 In rushing  ya juyo yana kallon ta, sai kuma yayi murmushi yana amsawa da.
"Yauwa barkanki dai, Ƙawata, amma fa, ina cikin ruɗu na kasa gane wacece Lailah Mai Kyau ac ikin ku biyun?,"

Har  Lailah ta buɗe baki, zata bashi amsa, Afeefah ta rigata da faɗin "Allah sarki, ae ga Lailah Mai Kyau nan, a gabanka, ko dai, baka gane ta bane?,"

Da sauri Sabbir yace "E' ita fa."

Afeefah ta kuma murmushi ta ce "to gata tsaye a kusada kai," ta faɗa hakan tana, kuma nuna mishi Lailah wacca tsaban mamaki yasa, ta saki baki tana kallonsu su duka, daga Sabbir ɗin har ita Afeefah ɗin da ta shirya komai.

Afeefah ta ci gaba da cewa "idan kuma baka yadda ba, ka kira wayanta, ae kanada number ɗinta ko?,"

Aikuwa ba musu Sabbir ya ciro ƙatuwar wayar shi, a trouser pocket ɗinshi, ya lalubo lambar Lailah ya latsa ma ta kira. saigata wayar Lailah dake cikin jakarta tana ƙaran shigowar kira.

Murmushi Afeefah tayi Sannan ta ce "bari na tafi mota, na jira ku, kafin ku kammala."
Ta faɗa tana kallon Lailah dake galla ma ta harara ba ta bi takan Lailah ba, tayi gaba abinta.

Shiru ko wannensu yayi, kowa da inda yake kalla, da irin tunanin da yakeyi.

Shafa sumar kanshi irinna fulanin ainihi, yayi yana fuzar da iska, daga bakin shi.

"Ko kinsan kinada wani abu?,"

"Me kenan?," Lailah ta tambaya.

"ko kinsan kinada kyau, irin sosai ɗinnan, nasan ance miki kinada kyau, sai dai nasan ba'a taɓa ce miki kina da kyawawan idanu ba 😂

Kiyi haƙuri fa, rasa abin faɗa ne, yasa na faɗamiki hakan fatan banyi laifi ba, a gurin wannan kyakyawar jinin kyawawa mai kyawawan idanu."

Dariya Lailah tayi, domin kuwa ya bata dariya ba kaɗan ba.

"babu matsalar komai,"

Ta bashi amsa, still cikin murmushi.

"kai aikuwa dai kwara da kikayi dariya, don na kusa mantawa da wannan, a gaskiya dariya tana yi miki kyau highly highly😅

ᴀғᴇᴇғᴀʜ

Da barin gurin, direct Motarsu ta shiga, tana hangosu suna taɓa fira can kuma taga Lailah tana dariya, abin ba ƙaramin ɗaure ma ta kai yayi ba, a fili ta ce "ikon Allah Lailah kuma da dariya ga saurayi, Lallai abu ya girmama, haka tana zaune a motar saiga bayan wani lokaci  Lailah ta taho bayan sunyi sallama da Sabbir.

Shiga motar Lailah tayi driver yaja suka bar gurin, a hanya Afeefah gaza jurewa tayi, ta kalla Lailah ta ce.

"wai kuwa menene ya faɗa miki, naga kina dariya ne, haka harda ƙyaƙyatawa?,"
ƙin kulata Lailah tayi, saima tambayar da ita ma ta jefo ma ta,  ta ce "wai kuwai nace ina Deejarh take, naga banganta ba?,"

Afeefah tayi murmushi tana faɗin, "ah wannan karon motar su Haleesat ta shiga, ba tamu motar ba, domin cewa tayi saita shiga ko waca mota, taji irin  ta😝.

Sannan bata ƙyale maganar farko ba, ta kuma cewa "wai me muka tattauna, da shi Sabbir ɗin naga kina fara'a haka?."

Lailah tayi murmushi sannan tana cewa, "shiɗin akwai shi, da  barkwanci sosai fa, ina faɗamiki highly."

Afeefah ta tambaye ta da cewa "iya barkwancin gareshi, ko kuwa da wani abu ƙasa, da bamu sani ba?,"

Ta faɗa tana murmushi, "meyasa baki tsaya kinji, da gani ba?

Lailah tana maka ma ta hararar ta bata amsar, Afeefah ta ce "gani nake kamar bai kamata, na tsaya tsakanin masoya ba, shiyasa nayi gaba abina."😯

Da sauri Lailah ta kalleta ta ta ce "wani munafikin ne ya faɗamiki soyayya muke?."

Afeefah ta bata amsa "ke malama ni ba, wani munafikin da ya faɗamin, tunani ne ya faɗamin hakan."

Lailah ta ce "akwai ki barkwanci, wani lokacin fa, to wannan karon tunanin ki, bai faɗa miki gaskiya ba,"
Afeefah ta ce "da gaske nake, wata rana saikin sameni kina kuka, kina faɗin kinason Sabbir fa."

Dariya Lailah tayi irin hakan bazai taɓa yiwuwa ba, for Ever. sannan ta bata amsa, "your challenge is failed Insha Allah,"
Afeefah ta ce "Yarinya kenan, ai ba ke zaki faɗa, haka ba lokaci ne zai nuna mana."

Haka dai suka ci gaba da firan, har suka ƙarisa haɗaɗɗen gidan su, driver yayi horn, securities suka wangale gate motocin suka shiga gidan a tare.

Parking driver yayi, a gurin da aka tanada domin yi, suka fito a tare suka shiga ciki.

A palo suka tarar da Momy Rafi'at wacca bata fita asibiti ba, zaune ita da ƙanwar ta Momyn su Fareeda da Fadeela, da ta kawowa ƴar uwar tata ziyara.

Gaisar da ita su Afeefah sukayi kafin kowa ya nufi bedroom ɗin shi cike da gajiya, Afeefah ɗakin Deejarth ta wuce ta tayata shirya kayan da sukayi shopping a gurin da ya kamata.

"Ina da wata ƴar jan kunne gareki, kar ki ga, kin tsinci kanki cikin gidan Mister Mai Kyau, shahararren Billoniya, kiyi tunanin yin ko aikata wani abu ba daidai ba, zan iya cewa, kyakyawar ƙaddarar ki ce tasa, cikin lokaci ƙanƙani kika haɗe da ahalin Mai Kyau, tamkar dama can tare kuke, ina yi miki wannan ƴar jan kunne ne, badan komai ba, sai dan saboda gaba, wata ƙila zakiga wasu abubuwan da suke ba daidai ba, cikin gidannan, to ina mai jan kunnen ki, da kar kiyi gigin shiga cikin lamarin, ko kuma shiga abin da bai shafeki ba, domin haɗari ne babba ga rayuwarki, fatan zaki kiyaye, sannan akwai form da ake cikewa kafin a ɗauki ko wani ma'aikaci da yake aiki cikin gidannan.

Sai dai ke, ban baki form ɗin, domin ki cike ba, wanda nima bansan dalilin hakan ba, sai dai zan iya cewa saboda tun ganin farko da nayi miki, kika shiga raina highly, kuma na ɗaukeki matsayin ƙanwa gareni.

Khadeejah ina miki fatan nasara a raywarki, sannan barkanki da shigowa Ahalin Mai kyau, kyakyawan Ahali, waɗanda ba iyakar kyawun sura dana jiki ko fuska gare su ba, harda kyawun zukata, Ahalin Mai Kyau, Ahali Mai ɗauke da sirrika kala kala, daban daban, ma banbanta.

Zan baki form ɗin, zuwa wani lokaci domin kiga yadda tsarukan aiki a gida Mai Kyau yake, da kuma sharaɗin da ake cikawa da alƙawura, sannan badan komai zan baki ba, sai dan ki kasance mai taka tsantsan cikin gidannan, domin kamar yadda na faɗa miki ne, kyakyawar ƙaddarar kice ta kawo ki gidan Mai Kyau.

Fatan kin Fahimci bayanin da nayi miki kuma, zakiyi aiki da wanda ya kamata, malama Khadeejah?,"

Afeefah ta kammala wannan doguwar maganar kuma bayani game da jan kunne, ga Deejarh, daga inda take a tsaye gaban window tana shaƙar fresh air, yayinda kyawawan idanun ta suke kallon, can waje ɓangaren da swimming pool yake.

Ajiyar zuciya Deejarh ta sauke, tana tuna shekaru uku baya, kamar haka aka zaunar da ita ana, faɗa ma ta irin waɗannan kalaman da Afeefah tayi ma ta yanzu.

"Insha Allah Zanyi Amfani da Jan kunnen ki, gareni Balarabiyar india, sannan nagode tuna tarwarki gareni."

"You are welcome Dear"

Afeefah ta amsa ta.

ᴀ ᴘᴀʟᴏ ᴋᴜᴡᴀ~

Bayan shigansu Afeefah ɗaki, ƙanwar MomyRafi'at mai suna Hajiya Sailuba, ta kalla Momyn ta ce "wannan kyakyawar yarinyar, da na ga sun shiga ɗaki da Afeefah fa?, kodai ita ma dangin mijin naki ke, bansan ta ba?,"

Momy Rafi'at ta ce wani dangin miji ƴar aiki ce fa,"

Riƙe baki Haj. Sailuba tayi cike da mamaki ta maimaita, ƴar aiki fa, kikace shine naga ta shiga cikin yaran gida, ta saje dasu, kekuma kina ina lokacin da hakan ya faru?."

Cike da takaici Momy Rafi'at ta ce "a lokacin ina jinyar targaɗen da nayi, to ko ina da lafiya ma, mai zan iyayi, tunda ƴar gaban goshin babanta tana sonta?,"

Haj. Sailuba ta ce "a gaskiya Auntie Rafi'a kina ƙoƙari wallahi, wannan zamanin wake riƙe yaran miji ma, balle wata ƙasƙantacciya ƴar aiki."

Momy Rafi'at ta ce "da dai kinbar zancen nan kawai, inaga baki manta ba, saboda wannan Yarinya mijina uban ƴaƴana ya taɓa ratta ɓamin saki har biyu ko?."

Haj. Sailuba ta ce cike da takaici, "inafa zan manta ae banmanta ba, sam."

Girgiza kai kurum Zaynerb tayi, dan kuwa duka abin da suka tattauna, taji a kunenta, dama ta fito ne domin ta shiga bedroom ɗin Haleesat, Sai kuma taji ana wannan zanje, "to kodai sun manta a palo suke ne?," ta tambaya kanta sai kuma taba kanta amsa da ayyana "wata Ƙila sun manta a palo suke, palon ma na ƙasa.

*~💅ᴛʜᴇ ɢʟᴀᴍ ǫᴜᴇᴇɴ, ᴡᴀɴɴᴀɴ ʟᴀʙᴀʀɪɴ ᴍᴀʟʟᴀᴋɪɴᴀ ɴᴇ, ɴɪ ᴋᴀᴅᴀɪ ɴᴀᴋᴇ ᴅᴀ ᴅᴀᴍᴀʀ sᴀʀʀᴀғᴀ ᴀʙɪɴᴀ ʏᴀᴅᴅᴀ ɴᴀᴋᴇsᴏ, ᴡᴀɴɴᴀɴ ʟᴀʙᴀʀɪɴ ɴɪ ɴᴀʏɪ ᴋᴜᴍᴀ ɴᴀsʜᴀ ɢᴡᴀɢᴡᴀʀᴍᴀʏᴀ ᴡᴀᴊᴇɴ ᴋɪʀᴋɪʀᴀɴsʜɪ, ᴡᴀɴɴᴀɴ ʟᴀʙᴀʀɪɴ ᴋɪʀᴋɪʀᴀɴsʜɪ ɴᴀʏɪ, ᴅᴏᴍɪɴ ɪʟᴍᴀɴᴛᴀʀᴡᴀ ᴅᴀ ғᴀᴅᴀᴋᴀʀᴡᴀ ʜᴀʀᴍᴀ ᴅᴀ ɴɪsʜᴀᴅᴀɴᴛᴀʀᴡᴀ, ɴɪ ɴᴇ ɴᴀsᴀɴ ɪʀɪɴ ᴡᴀʜᴀʟᴀɴ ᴅᴀ ɴᴀsʜᴀ ᴋᴀғɪɴ sᴀᴍᴀʀ ᴅᴀsʜɪ, sᴏ ɪɴᴀ ᴍᴀɪ ɢᴀʀɢᴀᴅɪ ᴅᴀ ᴋᴀᴋᴋᴀᴜsᴀʀ ᴍᴜʀʏᴀ ᴀᴋᴀɴ, ʙᴀɴ ʏᴀʀᴅᴀ ʙᴀ, ᴋᴜᴍᴀ ʙᴀᴢᴀɴ ʟᴀᴍᴜɴᴄᴇ ᴡᴀɴɪ ᴋᴏ ᴡᴀᴛᴀ sᴜʏɪᴍɪɴ, ᴀᴍғᴀɴɪ ᴅᴀ ᴡᴀɴɪ sᴀsʜᴇ ᴋᴏ ʙᴀɴɢᴀʀᴇ ɴᴀ ᴄɪᴋɪɴ ᴡᴀɴɴᴀɴ ᴋɪʀᴋɪʀᴀʀʀᴇɴ ʟᴀʙᴀʀɪ '𝐒𝐀𝐑𝐀𝐔𝐍𝐈𝐘𝐀𝐑 𝐊𝐘𝐀𝐔' ʙᴀ, ɪᴅᴀɴ ᴋᴜɴɴᴇ ʏᴀᴄɪ ᴍᴀғɪʏᴀ ʏᴀᴡᴀɴ ᴍᴀsᴜ ɪʏᴀ ᴍᴀɢᴀɴᴀ, sᴜᴋᴀ ᴄᴇ ɢᴀɴɢᴀɢᴀʀ ᴊɪᴋɪ ʏᴀ ᴛsɪʀᴀ, 👑ᴛʜᴇ ɢʟᴀᴍ ǫᴜᴇᴇɴ💅 ᴍᴀʟʟᴀᴋɪ ɴᴀ ɴᴇ, ɴɪ ᴋᴀ𝙳ᴀɪ🤙~*

*🩸ᴋʜᴀᴅᴇᴇᴊᴀʀᴛʜ.   sᴀʙɪ'ᴜ.   ʏᴀʜʏᴀʜ. ᴄᴇ ᴡᴀᴛᴏ🩸*

☆ᴛʜᴇ ɴᴀɪɴᴀʀʜ ᴋᴅ😇☆

✦ɴᴏᴠᴇʟ ᴡʀɪᴛᴇʀ ᴏғ✦

💓sᴀʀᴀᴜɴɪʏᴀʀ ᴋʏᴀᴜ💓

♥︎ғɪʀsᴛ sᴛᴇᴘ♥︎

𝗔𝗿𝗼𝘂𝗻𝗱 5:39𝗣𝗺

αϝҽҽϝαԋ💅

"Haba soyayya kuma wai kuma ni, kawai wahalar da kanku zakuyi, domin ni ban taɓa soyayya ba kuma banayi,"

ʅαιʅαԋ😍

"E, Munsan da hakan, amma burin mu kawai ki karɓa wannan challenging ɗin, ta haka muda kanmu, zamu saka ki antaya soyayya, burin mu kawai ki amince."

ȥαყɳҽɾႦ😇

"Ke malama ki amince kawai, da challenging ɗinnan da muka baki, kokuwa kiyi rashin nasara👎,"

ԋαʅҽҽʂαƚ😉

"Ke Afeefah idan fa, baki yarda da wannan challenging ɗin ba, tofah kinyi rashin nasara a wannan gasar,"

ɳαιɳαԋ🤐

"Ke Afeefah inaga fa, kawai ki karba wannan challenging ɗin idan kinaso, kiyi nasara, bayan hakan bazan kara cewa komai ba, akan wannan challenging naku,"

ɱσɱყ ɾαϝι'αƚ🤓

"To ke Afeefah mana ki amince da wannan challenging ɗin, kodan kiyi winning akansu mana,"

Shiru Afeefah tayi tana nazari akan ta karɓa ƙalubantar da duka ƴan uwan nata, suka ma ta, ko kuwa karta karɓa, a barshi tayi rashin nasara.

Dama sun saba duk lokaci bayan lokaci, sukan zauna idan basu da aikin yi, ko school, haka zasu zauna suna challenging tsakanin junan su, duk wacca aka ƙalubalanta akan wani abun, idan tayi daidai yadda akeso, ta cike duka ƙa'idoji, tofah tayi winning, kuma tanada gwagwaɓar kyauta da mutum biyu, wato Momy Rafi'at [Mrs Mai Kyau] da kuma shi kanshi uban gayyan, wato Alhaji Abubakar Mai Kyau [Mister Mai Kyau].

Gwaggwaɓar kyautar ita ce.

Na Farko

Kyautar zunzurutun kuɗaɗe Dalar America Bundles Uku da kuma canjin Mota zuwa na yayi daga gurin Momynsu Rafi'at Mrs Mai Kyau

Na Biyu

Kyautar Tsadaddiyar Waya da kuma zuwa duk inda mutum yakeso, in free ba tare da securities ba, sannan da ƙarin kuɗaɗe.

To shine fa yau suka canza tsarin abin, ya koma zasu ƙalubanci Afeefah akan zasu haɗa lambobi dukaninsu, za'a kira waya tofah duk wanda ya ɗauka wayar, idan ta macece zasu ƙulla ƙawance da Afeefah, kuma Afeefah zata kasance ta faɗi sunan Yarinyar da kuma garin da state ɗin da take, ba tare da yarinyar ta faɗa ma ta ba.

Idan kuma Namji ne, tofah salon na daban ne, domin zata kasance a duk bayan kwana ɗaya, tana kiranshi a waya ne, kuma zasu ƙulla soyayya, mai ƙarfi tsakanin su, ba kuma tare da sunsan fuskar  junan su ba, kuma zata kasance mai tura mishi massage's in daily, sannan a yanzu idan ya ɗauka wayar zata faɗi sunan shi ba tare da an faɗa ma ta ba, baya da waɗannan ma akwai sauran sharuɗa daban daban, akan challenging ɗin.

{ᴛᴏғᴀʜ, sʜɪɴ ʀᴇᴀᴅᴇʀ's ᴋᴜɴᴀ ᴛᴜɴᴀɴɪɴ ᴀғᴇᴇғᴀʜ ᴢᴀᴛᴀ ʏᴀʀᴅᴀ ᴅᴀ ᴡᴀɴɴᴀɴ ᴋᴀʟᴜʙᴀʟᴀɴᴛᴀʀ ᴅᴀsᴜ ʟᴀɪʟᴀʜ sᴜᴋᴀ ʙᴀᴛᴀ, ᴋᴏ ᴋᴜᴡᴀ ᴢᴀᴛᴀʏɪ ʀᴇᴊᴇᴄᴛɪɴɢ ᴛᴀ ʀᴀsᴀ ᴅᴀʟᴀʀ ᴀᴍᴇʀɪᴄᴀ ʙᴜɴᴅʟᴇs ᴜᴋᴜ ᴅᴀ ᴋᴜᴍᴀ ᴍᴏᴛᴀ ɢᴀ ᴛsᴀᴅᴀᴅᴅɪʏᴀʀ ᴡᴀʏᴀ ᴅᴀ ᴋᴜᴍᴀ ʏᴀᴡᴏ ɪɴ ғʀᴇᴇ ʙᴀ ᴛᴀʀᴇ ᴅᴀ sᴇᴄᴜʀɪᴛɪᴇs ʙᴀ?, -ᴛᴏ ᴋᴏᴍᴀ ᴍᴇɴᴇɴᴇ ᴍᴜ ʜᴀᴅᴜ ᴅᴀ ᴀɴᴊɪᴍᴀ ᴋᴀᴅᴀɴ ᴀ ᴄɪ ɢᴀʙᴀɴ ᴡᴀɴɴᴀɴ ᴘᴀɢᴇ's ᴅɪɴ ᴢᴀɴᴊᴇ ɴᴀsʜᴀ ᴄᴏғғᴇᴇ ɴᴀ ᴅᴀᴡᴏ ᴅᴏᴍɪɴ ᴊɪɴ ʏᴀᴅᴅᴀ ᴢᴀᴛᴀ ᴋᴀʏᴀ😆}

☆ᴛʜᴇ ɴᴀɪɴᴀʀʜ ᴋᴅ🤙

*💓sᴀʀᴀᴜɴɪʏᴀʀ ᴋʏᴀᴜ💓*

    `☆`ғɪʀsᴛ sᴛᴇᴘ`☆`

Wannan ci gaban page's 27&28 ne, bawai next page's bane, Jᴜsᴛ Fᴏʀ Yᴏᴜ Sᴀʀᴀᴜɴɪʏᴀʀ Kʏᴀᴜ Fᴀɴ's Cʟᴜʙ💅

"Tunda haka kukeso, to na amince, da za'a haɗa lambobi ayi kiran sannan abi yadda abin yake,"

Afeefah tayi maganar tana kallon su gabaɗaya, murmushi ko wannensu yayi sannan.

Lailah da ta fi kowa zaƙewa a abin ta ce, "Yauwa sis ƴar gari, yanzu tunda kin amince, sai a haɗa lambobin ayi kirar, Ni dai na fara da sifli {0} da kuma Tara {9} sai wata sifli {0} ɗin, saura ke sister Zaynerb, ae a ƙa'idar abin, ita Afeefah ba za ta faɗi lambar ba ko?,"

Lailah tayi tambayar tana kallon ƴan uwannata, su duka suka amsa da "E, haka ne, ita Afeefah ba za ta faɗa ba,"

Zaynerb ta gyara zama tana faɗin, "ni kuma na gaba kenan zan faɗa ko, tunda kin faɗa guda uku, to na zaɓa 'guda'  sai ke Haleesat,"

Zaynerb tayi maganar tana kallon Haleesat ɗin, alamar turn ɗin ita Haleesat ɗinne yanzu.

"ke Zaynerb menene kuma wani 'guda' karfa ki mana irinna 'MUFEEDA' mai cewa tayar mota takwas tayar mota takwas fa, ke da zakice 'ɗaya'😀

Gabaɗaya palon dariya sukayi harda ita kanta Zaynerb ɗin, wato kar tayi musu irinna 'MUFEEDA' ta littafin 'ASMABAFFA' mai taken 'KASUWANCINA'😅😇

"Kai sis Nainarh, to bari na canza, na zaɓa 'ɗaya' {1} gaban wanda Lailah ta faɗa," cewar Zaynerb ɗin tana dariyar maganar da Aunty Nainarh ɗin tayi.

"Okay, ae gaskiya na faɗa ni kuma na zaɓa 'ɗaya' {1} ɗin again a gaban naki," ita ma Nainarh ta faɗa sannan ta ce, "Haleesat saura ke,"

ita ma Haleesat zaɓa tayi ta faɗa, sannan Nailah, wacca duk drama ɗin da ake kwasa, tana can tayi, baƙuwa wata ƙawarta 'Saddiqa', to sun fito palon da 'Saddiqan' zata ma ta rakiya, ita ma ta tsaya akayi da ita, hatta saddiqa ɗin ita ma, sai da ta faɗa na ta, sannan Deejarh sai kuma Momy Rafi'at, da sukaga saura ragowar lamba ɗaya lambobin su cika, shine kawai Afeefah ta faɗa ɗayan lambar sannan lambar wayar ya cika Goma Sha Ɗaya cifffff😛

Taruwa sukayi guri ɗaya wayar Afeefah na hannun Lailah da ta latsa kiran wannan lambobi da suka haɗa, sai dai da privet number ɗin Afeefah, Lailah ɗin ta danna kiran, dan Afeefah ɗinne ta buƙaci hakan.

*ᴀʙᴜᴊᴀ, ɴɪɢᴇʀɪᴀ*

*ʜɪɢʜᴇʀ ʙɪʟʟɪᴏɴɪᴇʀ's sᴛʀᴇᴀᴍ Qᴜᴀᴛᴇʀ's*

Sunan Unguwan kenan, a farkon shiga Area ɗin, aka rubuta hakan jikin wani tsadadden 'sign board' wanda shi kanshi alamu ya nuna ba ƙananun kuɗaɗe, aka zubar wajen samar dashi ba, in fonts akayi rubutun da launin sky purple sannan kuma in stylish.

A gaskiyar lamari ita wannan haɗaɗɗiyar unguwa, ba irin na ƙananu ƙananun masu naira bane, wannan unguwar, tsadaddiyar unguwa ce, wacca sai kaci ka tada kai da naira sannan kake shiga irin ta, har ka kai ga zama cikinta, sannan ba'a zama cikinta haka kara zube, sai anyi register sannan kuma akwai takardu da lasisin zama cikinta.

Gabaɗaya gidajen Area ɗin, yanayi da tsari na ginin su da komai kala ɗaya ne, hatta yanayin haɗaɗɗun gate's ɗin kala ɗaya ne, da alama company ɗaya ne yayi, ko kuma ma gabaɗaya Area ɗinne mallakin wani companyn😎

Can Cikin Takuna Na Farko, Domin Son Kawowa Fan's Of Sarauniyar Kyau, Update's Na Hango Wani Hatafen Gida, Wanda Kai Tsaye Da Ganin Farko, Za'ayi Mishi Laƙani Ko Kira Da 'Daular Aljannar Duniya', Tsaban Tafiya Da Hankalina Da Kyawu Da tsarin Gidan Yayi Dani, Yasa Ban Wata Wata Ba, Da Gudu Na, Na Bara Da Bana, Anya Ciki💃💃

________________________________________________________________________ᴛʜᴇ ɢʟᴀᴍ ǫᴜᴇᴇɴ♥︎____ʙʏ:_ᴋʜᴀᴅᴇᴇᴊᴀʀᴛʜ sᴀʙɪ'ᴜ ʏᴀʜʏᴀʜ______ᴛʜᴇ ɴᴀɪɴᴀʀʜ ᴋᴅ💅

A gaskiya ganin cikin gidan daga ciki, yafi gani daga waje, domin komai na gidan abin burgewa ne, so thrilling, securities ne cikin gidan ta ko'ina sai dai yawan securities na gidan baisa gidan yana da wata haniya ba.

A gaskiya tsayawa faɗamuku irin tsari na ginin gidan, lokaci bazai bamu damar gudanar da hakan ba, sai dai kawai Just muyi manage da abin da ya samu.

Domin hatta ƙasan gidan, bawai inter log bane kamar yadda kuka saba gani a wasu gidajen, a'a wasu expensive tiles ne bawai irin masu cutarwa ba, no just tiles masu tsada da tsari, daga cikin katafen palon gidan kuwa, ma'aikata ne, wajen guda goma, ke kai kawo ciki.

Daga tsakiyar palon yake lumtse saman tattausar stool irin na sarauta, wanda ake zama ko kwanciya ciki.

Dogo ne shi, sannan mai kyakyawar haɗaɗɗiyar surar jiki ga qwamji, ga ƙira irinna mazajen sadaukai.

Yana da Jar fata, irinna larabawan ƙasar Ethiopia, sannan kuma yana da kyau irin na musamman ɗinnan, sumar kanshi, ba wata doguwa bace can irinna larabawa, sai dai tasha aski irinna haɗaɗɗun gayu in stylish, da ganin irin gyaran da aka ma sumar kasan ba ƙaramin, ji da ita ake ba.

Sanye yake cikin wata tsadaddiyar jallabiya ƙirar Saudi, hannayenshi gabaɗaya tallafe da Tablet {kwamfutar hannu} sakin tablet ɗin yayi ta koma saman lap's ɗinshi.

Yayinda yayi tagumi hannu bibbiyu, yana kuma waro fararen idanun shi, yana watsa su saman wannan tablet.

Murmushi tayi tana yiwa mai ɗaukarta video nuni da hannu alamar ta dena, sai dai da alama mai ɗaukar nata video ɗin, ƴar rigima ce domin taƙi ta dena abin da takeyi, saima juyawa da camara ɗin da take ɗaukar da ita gefe da tayi, nan fuskar wani matashin saurayi ya bayyana, kusan sakin camara ɗin, tayi tana waro ido, dan batayi tsammanin zataga mutum tsaye ba, ƙoƙarin jefar da camara ɗin, tayi tsaban firgici.

Da sauri wannan budurwa da batason a ɗauketa video ɗin, ta  miƙe tsaye cikin zafin nama, ta taro camara ɗin sannan ta saita camara ɗin fuskar wancan budurwar tana dariya, ta kuma juyo da camara ɗin, tana fuskantar fuskarta, dariyar nishaɗi kawai takeyi tana bin sautin waƙar dake tashi a gurin,  a hankali cikin zazzaƙatar muryarta, gefe guda kuma tana ɗaukar videon dramar da ake kwasa tsakanin budurwar farko mai ɗaukar video da wannan saurayi.

Murmushi yayi mai bayyana dimples, dai dai lokacin ita ma, tayi nata ƙayataccen murmushin, da ya bayyana dimples ɗinta duka biyun.

Daga can haɗaɗɗen dining area, dake can keɓantaccen guri cikin palon kuwa.

Cikin nutsuwa ya kammala lunches ɗin nashi, sannan yakai hannu ya murɗa sink dake jikin table dining ɗin ya wanke hannun shi, duk bada hannu yaci abincin ba, goge hannun yayi da expensive tissues.

Dai dai taƙin kuma, tsadaddiyar haɗaɗɗiyar wayarshi, wacca kai tsaye ba nace ko ƙirar wata company bane, domin banga tambarin ko wani company ba, sai wani haɗaɗɗen tambarin rubutu da akayi wanda ya tafi dan.

'ᴏғғɪᴄɪᴀʟ'  haka akayi tambarin rubutun jikin wayar, rurin da tayi ne a lokacin, ya tabbatar mishi da kira ne ya shigo.

"Okay, Pick up,"

Ya furta ba tare da ya kallah, tsadaddiyar wayar, nashi dake saman table dine ɗin ba.

Nan take wayar tayi picking call, ɗin da kanta, ba tare wani ko wata daga cikin jerin ma'aikata mata mazan dake tsai tsaye a dining ɗin, ya sarrafa ko taɓanta ba.

Shiru yayi baice komai ba, kamar yadda ɗayan ɓangaren na kiran ma ba'ayi magana ba.

To shi dama ɗabi'arshi kenan, dalilin da ya sa ma, yayi picking ɗin, tunanin shine ya bashi wata ƙila ɗaya daga cikin privet securities na shi ne ya kirashi.

"Hello, 'Official,"

On the other hand, abin da aka faɗa kenan, da ɗan mamaki gabaɗaya ma'aikatan gurin suka saki baki suna kallon wayar, jin mace ta kira 'Boss' ɗinsu kuma ta kirashi da sunan shi wanda ba kowa ne, yake kiranshi da hakan ba.

Wato 'Official,' gabaɗaya suna da tabbaci da yaƙinin cewa ba, ɗaya daga cikin ƙannin shi mata bane, ta kirashi.

Shi kuwa 'Boss' ɗin nasu in slowly ya juyo karo na farko ya kalla wayar.

"Hello, 'Official on line, and who is on the line too?."

Tsintar kanshi yayi da faɗin hakan, a lokacin da ya ɗauki wayar, ya dawo da ita saman right hand ɗinshi, kare a kunneshi again.

'Smile' wacca ta kasance ƴar asalin ƙasar china ne, kuma ɗaya daga cikin manyan ma'aikatan 'Official', tsaban mamaki da ya isheta ganin 'Boss' a yau ya amsa kiran wata budurwa, kasa haɗiye gulmarta tayi, ɗan gyaran murya tayi tana yima sauran ma'aikatan su biyar maza huɗu mace ɗaya, alama da suka kalla 'Boss'.

"humm dama sunana, eh sunana 'RISHITAH' daga mai diguri najeriya, amma kaifa?, oh na manta, sunanka 'Official' ko?,"

Shiru yayi yana mazarin abin da zaice jin irin amsar da ta bashi.

Alama yayi ma gabaɗaya ma'aikatan da su tafi, 'Smile' badan taso ba, haka tabar gurin, ranta babu daɗi dan taso taji yadda 'Boss' 'Official' zai ƙare da wannan budurwa da ta kira kanta, da 'RISHITAH' 😀

"Official, yau cikin farin ciki nake, domin naga muradin raina fa,"

haɗaɗɗen kyakyawan saurayin yayi maganar ne yana zama kan kujerar dake gefan wanda Official yake zaune saman ta, bayan ya ƙariso dining ɗin.

"To shikenan, Allah ya kawomu lokaci,  zaka fara surutun  naka kenan,"

Official ne yayi maganar bayan ya aje tsadaddiyar wayar nashi gefe, bayan budurwar da ta kirashi ita da kanta ta katse kiran, bayan tayi mishi introducing kanta, sannan yayi maganar yana kallon saurayin nan mai sanye cikin jallabiya ne.

Ƙayataccen murmushi yayi yana shafa ɗan gemun shi na gayu  yace.

"Official a yau da gaske nake, na ganta, kuma a video na ganta, a pajin wata wai 'ƴar rigima' ka yarda,"

Baya Official yayi sannan jingina da kujerar dining ɗin, hannayen shi biyu, harɗe a saman faffaɗan ƙirjinshi, so yake yayi magana, sai dai da ya buɗe bakinshi babu muryar da yakeji sai zazzaƙar muryarta, 'Rishitah' haka sunan yake ƙara tariyowa a kwakwalwar shi, ganin abin zayyi yawa, {Official da tunanin mace 😂}  yasa ya lumshe kyawawan idanun shi ba tare da ya furta komai ba.

"nasani, daga jin yadda yayi shirun nan baice komai ba, nasan bazai wuce tunanin ta yake ba," Saurayin ya furta ƙasa ƙasa yana kuma kallon picture's na ta, dake saman dekstop na tablet dake hannun shi.

"Bardiaa!"

Official yaja sunan idanun shi a lumshe still.

"E, sunana ne hakan, wanda ka raɗamin shekaru Ashirin da wani abu baya, challenging ɗinka nake, shin zaka ce min ba tunanin ta kake ba?,"

"Tunanin ita wa kenan?,"

Official ya tambaya yana buɗe Blue shines £yes nashi ya watsasu kan 'Bardia'.

"Ita mana, wacca ku ka haɗu ɗazu a shopping mall, har tana baka kyautar perfect perfume, ko zakace ba tunaninta kake ba, sannan ma ae ita ce, ta kiraka yanzunnan, 'Official' babu wani pretend da zakamin kawai dai 'KYAKYAWA' zatayi suruka ƴar Nijeriya nan da wani lokaci 😍

"Bardia na lura yau, ka zauce na ganinta fa, bari na baka guri, ka gama tukunna."

Official yayi maganar yana miƙewa tsaye ya ɗauki tsadaddiyar wayar shi, ya nufa haɗaɗɗen palon ya zauna abin shi. Murmushi Bardia ya raka Official dashi.

Official dogo kuma kyakyawan matashin baturen saurayi da ya haɗa jini da larabawa, yana da kyau obaa highly, ga kwanji jikinshi a mugun murɗe yake sosai, yana da yalwar sumar kai tamkar mace, don saboda yawanta har takai ga sayya ɗaureta ta sauka ta gadon bayanshi.

Gabaɗaya su biyun daga 'Official' ɗin har shi kanshi 'Bardia' ɗin ba kalar samarin da mace mai ji da kanta first class lady, zata gani kallo guda taƙi ƙara kallo bane.

Dukaninsu su biyun kyawawan samari ne ajin farko a kyau kuma jinin larabawa, domin shi 'Bardia' gabaɗayanshi balarabe ne, gaba da baya, iyaye da kakanni, yayinda shi kuma 'Official' have case ne domin ya haɗa jini da larabawa sannan ya haɗa da turawa.

ᴀ ʜᴀɴᴋᴀʟɪ ɪᴅᴀɴ ᴍᴜᴋᴀ ᴛsᴜɴᴅᴜᴍᴀ ᴄɪᴋɪɴ ʟᴀʙᴀʀɪɴ ᴢᴀᴍᴜ ғᴀʜɪᴍᴄɪ ᴋᴏᴍᴀɪ ᴅᴀ ɪʀɪɴ ᴅᴀʀᴀsɪɴ ᴅᴀ ʟᴀʙᴀʀɪɴ ʏᴀᴋᴇ ᴛᴀғᴇ ᴅᴀsʜɪ🥰

𝒀𝒂𝒏𝒛𝒖 𝒅𝒂𝒊 𝒌𝒂𝒘𝒂𝒊, 𝐉𝐮𝐬𝐭 𝐦𝐮𝐲𝐢 𝐜𝐞𝐥𝐞𝐛𝐫𝐚𝐭𝐢𝐨𝐧 𝐧𝐚 𝐛𝐚𝐲𝐲𝐚𝐧𝐚𝐫 𝐉𝐚𝐫𝐮𝐦𝐚𝐧 𝐋𝐚𝐛𝐚𝐫𝐢𝐧 𝐦𝐮🤩

𝙺𝚄𝙳𝙰𝙸 𝙺𝙰𝚆𝙰𝙸 𝙺𝚄 𝙺𝙰𝚁𝙺𝙰𝙳𝙴 𝚉𝙰𝙽𝙸, 𝚂𝙰𝙽𝙽𝙰𝙽 𝙺𝚄 𝙶𝚈𝙰𝚁𝙰 𝚉𝙰𝙼𝙰, 𝙳𝙾𝙼𝙸𝙽 𝙺𝚄𝚆𝙰 𝗦𝗔𝗥𝗔𝗨𝗡𝗜𝗬𝗔𝗥 𝗞𝗬𝗔𝗨 𝚈𝙰𝙽𝚉𝚄 𝙰𝙺𝙰 𝙵𝙰𝚁𝙰,T̥ͦḀͦK̥ͦU̥ͦN̥ͦ_F̥ͦḀͦR̥ͦK̥ͦO̥ͦ_____ 𝚈𝙰𝙽𝚉𝚄 𝙽𝙴 𝙲𝙷𝙰𝙺𝚆𝙰𝙺𝙸𝚈𝙰𝚁 𝚉𝙰𝚃𝙰 𝙵𝙰𝚁𝙰, 𝙱𝙰𝙳𝙰𝙸 𝚂𝚄 𝙻𝙰𝙸𝙻𝙰𝙷 𝚂𝚄𝙽 𝚂𝙰𝙺𝙰 𝙹𝙰𝚁𝚄𝙼𝙰𝚁𝙼𝚄 𝚃𝙰 𝙺𝙸𝚁𝙰 𝙹𝙰𝚁𝚄𝙼𝙸𝙽 𝙼𝚄, 𝙰 𝚆𝙰𝚈𝙰 𝙱𝙰, 𝙱𝙰𝚈𝙰 𝙳𝙰 𝙷𝙰𝙺𝙰 𝙺𝚄𝙼𝙰 𝙰𝙸 𝚂𝚄𝙽 𝙷𝙰𝙳𝚄 𝙰 𝚂𝙷𝙾𝙿𝙿𝙸𝙽𝙶 𝙼𝙰𝙻𝙻_______𝙺𝙰𝚆𝙰𝙸 𝙺𝚄 𝙱𝙸𝚈𝙾 𝙽𝙸__K̬̂ĥ̬â̬d̬̂ê̬ê̬ĵ̬â̬r̬̂t̬̂ĥ̬_Ŝ̬â̬b̬̂î̬'û̬_Ŷ̬â̬ĥ̬ŷ̬â̬ĥ̬🤙☆тнє✦n҇a҇i҇n҇a҇r҇h҇✦к∂💅




____💓𝑻𝒉𝒆 𝑮𝒍𝒂𝒎 𝑸𝒖𝒆𝒆𝒏💓___________________________________________________________________☆☆☆☆☆Ⴆყ☆ƙԋαԃҽҽʝαɾƚԋ☆ʂαႦι'υ☆ყαԋყαԋ




*𝑷𝒂𝒈𝒆 29&30*






  'ᴋᴡᴀɴᴀᴋɪ ʙɪʏᴜ ɢᴀʙᴀ'




 𝑴𝒂𝒊_𝑲𝒚𝒂𝒖_𝑺𝒄𝒊𝒆𝒏𝒄𝒆_𝑪𝒐𝒍𝒍𝒂𝒈𝒆_𝑺𝒆𝒄𝒐𝒏𝒅𝒂𝒓𝒚_𝑨𝒏𝒅_𝑼𝒏𝒊𝒗𝒆𝒓𝒔𝒊𝒕𝒚💝




Ta furta sunan da taga an rubuta, a saman makarantar, akan laɓɓanta sai kuma ta kalla uniform ɗin dake jikinta skirt pencil iya gwiwa ash color, sai riga white color, sai kuma rigar sanyi a sama maroon color, tana sanye da safa doguwa wanda takai ma ta har gwiwa, ga takalmin ƙafafunta shima ash nd maroon color, mai igiyoyi.

Babu hijjab a jikinta sai dai wata hular saƙa, mai ɗauke da launi ash nd maroon color's, ga sumar kanta mai yawa wanda tasha gyara ya zubo ta bayanta.



Da sauri ta kalla Afeefah da tayi parking a cikin makarantar, tun kafin ta ce wani abu Afeefah ta rigata da faɗin.

"Surprised" tana dariya, ita ma Deejarh ɗin dariya ta fashe dashi, sannan ta ce.
"Balarabiyar india, wai yaushe kika san inasan makaranta ne?,"
Afeefah tana dariya ta bata amsa da faɗin, "a mafarki naji kina faɗa wani lokaci, da nazo bedroom ɗin ki, naji kina faɗin, 'wayyo makaranta ni a sakani a makaranta, kona gudu daga gidannan,"



Fashewa Deejarh tayi da dariya, Afeefah ta ce "koba haka bane?," rufe fuska Deejarh tayi tana dariya, Afeefah ta kuma cewa "shine, ni kuma nace bari nama Daddy magana ya sakaki a school, tun kafin,"  sai kuma tayi shiru tana murmushi bata ƙarisa ba.



Buɗe back seat tayi ta ciro wata haɗaɗɗiyar backpack ta miƙawa Deejarh.

Da sauri Deejarh ta karɓa tana murmushi ta ce "kai Balarabiyar india kina surprising ɗina highly, yau fa, thank you so much, Allah ya ƙarawa Daddy Mister Mai Kyau ake cewa ko?, to Allah ya ƙarawa dukiya albarka, kuma ta kasance mai amfani, da kuma yawa fiye da cikin duniyar nan💴💶😅




Ba shiri Afeefah tayi dariya tana amsawa da Ameen Ameen dear, hannun Deejarth ɗin ta kamo suka nufa office ɗin principal, Deejarh sai kalla kalle takeyi, na ƙauyanci, don har yanzu abin bai saketa sosai ba.



Kwankwasa glass door ɗin office ɗin principal ɗin Afeefah tayi, daga ciki aka bada umarnin shiga, da sallama suka shiga ciki hannun Deejarh cikin na Afeefah.






Yana Zaune a Royal chair inshi tana juyi dashi, yaba ƙofa baya, saida ya gama shan mulkin shi, sannan ya juya kujerar ta juyo dashi.
Ganin wacca take tsaye tana kallon shi ga wata beautiful Girl kusada ita, yasa ba shiri ya miƙe tsaye.
Gabaɗaya ya da burce, ganin Afeefah wata ƙila bayyi tunanin ita bace, rasa mai zayyi yayi sai kawai ya ɗaga hannun shi dake rawa yayi salute ɗinta 😂



Ƙumshe dariya Deejarh tayi ganin wannan matashin dattijon wanda akalla ya kai shekaru arba'in da biyar yana saluting Afeefah abin gunin ban dariya.


Cikin Rawar jiki da na murya yake faɗin, "ah um madam, ah wai kece, dan Allah zazzzauna mana, ga guri ki zauna hajiya madam mai kyau," gabaɗaya cikin zare ido da inn ina yayi maganar in violence.



Zama Afeefah tayi a kujera, sannan ita ma Deejarh ta zauna kusada ita.
Sai lokacin shima ya zauna yana goge zufa amma fa na tashin hankali.
Murmushi Afeefah tayi dan ta fahimci abin da yasa yake duk  wannan rawar jikin, toh kuwa yayi a banza.


Gyaran murya Afeefah tayi Sannan ta gaisar da shi, yana murmushi ya amsa sannan ya nuna Deejarh yace " ah madam wannan kyakyawar fa, kodai ƙanwar kice?,"

"E, Afeefah ta bashi amsa a taƙaice sannan ta cigaba da cewa "sunanta Khadeejah,"

Sai kuma tayi shiru batasan miye sunan mahaifin Deejarh ɗin ba.
Kallon Deejarh tayi dan taji mai zata ce, da sauri Deejarh tace "My name is Khadeejah Abubakar mai kyau."


Da sauri Afeefah ta kalleta sai kuma tayi murmushi ta mayar da kallonta kan principal.
Cikin washe baki yace "aikuwa gashi kuma kuna kama, ita ma ɗin kyakyawa kamar ku."


Afeefah ta ci gaba da cewa "na kawota ne yanzu, ya za'ayi za'a ma ta interview ne, sannan a sakata a class ɗin da ya kamata da ita ko kuwa?."

Da sauri principal yace "ai duk abin da kikace, shi za'ayi madam,"
Maida kallon shi kan Deejarth yayi yana kuma washe baki yace "Nanah khadeejarthu, makarantar da kika fito a wani class kike?."

Ɗan jim tayi sai can ta ce "j.s.s two, na kammala, yanzu zan shiga j.s.s Three ne."
Principal yana murmushi ya ce "yauwa Nanah Khadeejarthu, yanzu idan na tambaye ki wasu abubuwa zaki iya bani amsarsu kuwa?."

Deejarth ta ce "in Allah ya yadda."

Principal ya fara "a darasin £nglish, wato Turanci zaki iya faɗamin, How many part of speech?,"

Shiru tayi sai can ta ce "guda Takwas {8} ne,"

"Da £nglish zaki faɗa,"  cewar principal.

Gyara zaman ta tayi ta ƙara ƙanƙame backpack ɗinta sannan ta ce.

"£ight  ne,"

"Good" cewar principal sannan ya kuma cewa "and what and what."

Ta ce

"Noun, Pronoun, Verb, Adverb, Adjective, Conjunction, Interjection, Prepositions,"

"Good, and What is Noun?,"

Gyara zamanta ta kumayi sannan ta ce.

"A Noun is a Name of Anything.,"

Murmushi principal yayi sannan ya cigaba da jefo ma ta tambayoyi akan £nglish language. Tana bashi amsa, wasu tayi daidai wasu kuma, yana ma ta gyara.



"Angama da £nglish saura basic science" cewar principal.
Ya kalla Deejarh yace.

"a darasin basic science, What is digestion ?,"

Yanzu ma saida tayi jim kafin ta fara kwararo masa bayani,  wanda yasa Afeefah da ke gefe zaune, ta saki baki tana kallonta cike da mamakin ilmin yarinyar.


"Digestion is the process, by which injested food, material are broken down in to similar particle's."

"Wow, good, and Define what is Brain?,"

Ta ce, "The part inside your head, that controls your thoughts, feelings, and movements."


Haka principal ya ci gaba da jerowa Deejarh tambayoyi daban daban akan subjects kala kala kamar su.

National Value, Agriculture, £conomic, Computer Science, I.r.s, Civic £ducation, £.t.¢.

Daga ƙarshe ya rufe da faɗin, give me the Ten, word's of £nglish.

T@ ¢£!
1.perfect,
2, Dream,
3, Table,
4, Challenge,
5,Get,
6, Offer,
7, School,
8, chair,
9, office,
10, salute🤭😇






Tunda ta fara Afeefah ta saki baki tana kallonta tasha mamaki sosai, da Deejarh ta iya wannan.
Ashe abin ba haka bane da ake ganin wasu mutanen da ke ƙauye ko kuma waɗanda suke zuwa government school ake musu kallon, jahilai, kodai adinga musu wani kallo na dabam abin ba'a zuwa government school bane, maida hankali da kuma jajircewa ne, dan ba wanda ya taɓa yin ilimi yana zaune sai an tashi an zage damtse, an shiga rana sannan da wuya koda daɗi 👍

Amma tana tunanin ko'a haka ita Deejarh ɗin tana cikin wa'innan mutanen da ake kira da Geniuses a turance kennan, sannan ita ɗin gifted ce.




Murmushi principal yayi yana kallon Deejarh  ta burgeshi sosai da hazaƙarta.

"Nice good girl, kin amsa duka tambayoyi sai dai Wanda ba'a rasa ba."

Sannan ya mayar da kallon shi akan Afeefah yana murmushi yace "ta cinye interviewing, duka dan haka za'a sakata a j.s.s.three, she deserved it."

Afeefah tayi murmushi ta ce "okay sir."

Telephone ɗin dake ajiye kusada dashi, ya ɗauka ya danna wasu lambobi sannan ya kira, cikin harshen turanci yake maganar har ya gama, sannan ya kalla Deejarh yace "Nanah khadeejartu, taso na kaiki class da kaina,"

Murmushi tayi sannan suka miƙe dukansu suka fita a ƙofar office ɗin.
Afeefah ta kalla Deejarh tana faɗin,  "to Deejarh ayi karatu da kyau, idan an tashe ku, Moses driver zaizo ya ɗaukeki kinji,"

"To shikenan babu damuwa," Deejarh ta amsa, sannan Afeefah ta nufi motar ta, Deejarh na ɗa ga ma ta hannu.



Kana tabi bayan principal elevator taga ya nufa, ita ma tabi bayan shi suka shiga a tare hawa na uku taga ya danna bayan sun shiga.

Ba'a daɗe ba taga ɗofar ta buɗe sannan suka kuma fita.

Ita dai nata ido, don sai ƙarema makarantar kallo, takeyi sosai makarantar ta burgeta ga ɗalibai kala kala farare da baƙaƙe hausawa dama waɗanda ba hausawa ba.


Wani haɗaɗɗen class taga principal ɗin ya shiga, kafin ta ankara, da sauri tabi bayan shi sai kuma ta tsaya cak ganin class mai kyau da tsari gashi duka ɗaliban ciki basu wuce su ashirin ba kai bama sukai hakan ba.


Gaisar da principal ɗin, taga student's ɗin sunyi bayan sun miƙe, ya amsa musu fuska a tsume kamar bashi ke washe baki yanzu a office ɗin shi ba 😅



Nuna musu Deejarh yayi sannan yace "kunyi sabuwar New comer, kallon Deejarh yayi yace, "gabatar musu da kanki, a matsayin sabuwar ɗaliba duk cikin turanci yake maganar.

Ta fahimci wani abu dan haka kallonta ta ɗauke daga kanshi,  ta mayar kan students na class ɗin da suka zuba ma ta ido suna kallo.



Qara Riƙe backpack ɗinta dake bayanta tayi sannan ta fara magana.

"Hello class,  am Nanah khadeejah Abubakar mai kyau, am New comer, kamar yadda mai girma principal ya faɗa da farko."

Da turanci take maganar tana haɗawa da hausa fa.

Ta ci gaba da cewa "am very Gladness to see you, ina fatan zaku karɓeni hannu biyu biyu ko?,"

Ɗan shiru tayi tana kallonsu, sai kuma ta ce "ina fatan dai ƴan uwan nawa ɗalibai suna fahimtar abin da nake faɗa, saboda ni ɗin ma ƴar koyo ce, ba komai na iya ba."


Gabaɗayan su students ɗin suka haɗa baki wajen faɗin "munajin ki, kuma muna fahimtar ki, sannan kuma muma muna masu Farin cikin haɗuwa dake kuma muna fatan zaki kasance damu har lokacin da zamuyi Candy."

Dariya Deejarh tayi {Ɗalibai kenan, basu daɗe da shiga j.s.s Three ba amma suna tunanin fita daga school ɗinma gabaɗaya, ae haka muke ɗalibai akwai mu da Buri kala kala 🥰🇳🇬}





Ta ce "Nima haka, ina muku fatan nasara a rayuwa, sannan kuma, ku cinye jarabawar j.s.c.e. hadda ma s.s.c.e. gabaɗaya😇


Dariya sukayi hadda ita, principal yace "yanzu tunda kun gaisa kunsan juna saiki sama guri ki zauna."


"To," ta amsa masa, sannan ta nufi gurin zama, da sauri wata kyakyawar matashiyar budurwa ta ce "baki faɗamana wani abu ba."


Lokacin da tayi maganar principal ya fita kuma dama can ba teacher a class ɗin.


Deejarh ta tambayeta, "Menene abun?," budurwar tana dariya ta ce "baki faɗamana, Menene burinki ba, sister,"

Dariya Deejarh tayi sannan ta ce "burina shine naga wata rana, an wayi gari na zama babbar likita wacca take taimakon talakawa da marasa ƙarfi, SO I WANT TO BE A DOCTOR.




Tafi class ɗin ya ɗauka rafraf suna faɗin munayinki wallahi our new comer { kuma kunsan students idan malami baya class 😁 }





Deejarh tayi murmushi a takaice sannan ta ce "nima dai zanso naji Burin ko wannenku ko?,"

Budurwar da tayi magana ne ta miqe dama bencin farko take kuma ita kaɗa ce.

Ta tsaya gaban blackboard kusada Deejarh, Sannan ta miƙawa Deejarh ɗin special hand ɗinta ta ce. "AM FALILAT KHAM££S, AND I WANT TO A DOCTOR TOO."




Murmushi Deejarth tayi sannan ita ma ta miƙa ma ta hannunta dake sanye cikin handglove ash color ta ce "nice to meet you miss Falilat,"


Falilat ta koma ta zauna, wata ma tazo sukayi kamar yadda sukayi da Falilat, haka suka dingi yi har aka gama da ɓangaren mata.



Wani saurayi ya fito ya miƙowa Deejarh hannu, wai su gaisa, murmushi tayi sannan ta juya hannunta ta baya ta karkaɗa mishi ta ce "haka akeyi saboda ni ba muharramarka bace."


Murmushi yayi yana faɗin "na gode da tuni, And am Farhad Khamees, i want to be a perfect £ngineer

Deejarh tana dariya ta ce "amma dai ku, twins ne da Falilat ko?,"
 
Amsa ya bata da faɗin, "E, haka ne, tayi murmushi haka suka ci gaba da yi mazan suma ba'a gaisawa sai dai a karkaɗa hannu. inji Deejarh.


Bayan sun gama ta sama guri a bencin farko, ta zauna kusada Falilat suna taɓa fira sama sama akan karatu, suna haka saiga wani malami ya shigo, miɗewa sukayi aka gaisar dashi, bayan ya amsa suka zauna.

Deejarh ta kalla Falilat dake ciku cikun ciro littafi a jakarta ta ce "wani darasi wannan malamin yake koyarwa?,"

Falilat ta amsa "£nglish language," jin haka yasa Deejarh ta ciro book ɗinta a jakarta ita ma.
Saida ta tsallake pages ɗin da aka wuce ta sannan ta fara copyn writing ɗin da malamin yakeyi a blackboard.

Bayan ya kammala ne yayi musu dogon explaining saida period ɗinshi ya fita sannan ya bar ajin.

Wani ma ya shigo bayan ya fita, aka kaɗa bell lokacin Break, ganin kowa yana fita, Banda su yasa Deejarh ta kalla Falilat ta ce.

"nace ke banda kene a fita Break ɗin?,"

Murmushi Falilat tayi sannan ta bata amsa, "ki tsaya kiga ikon Allah mana."
Jin haka Deejarh tayi gum, can saiga Farhad da snacks da kayan maqulashe kala kala ya duresu a gaban su, sannan ya kalla Falilat yana faɗin.

"Auntina waɗannan hadda qawarmu," yayi maganar yana kallon Deejarh da ta saki baki tana kallon su, yayi murmushi sannan yace "mamaki kike ko?,"

"Sosai ma," cewar Deejarh, yace "to ai ba abin mamaki bane, auntina ce ita idan kuma baki yadda ba, ki tambaye ta yana faɗin haka ya fita waje, wajen abokanshi.





Deejarh ta kalla Falilat zatayi magana, Falilat ta rigata da faɗin  "haka ne ni ce babba awa ɗaya tsakanin mu, kuma yana girmama ni, nima ina bashi girmanshi."

Deejarh ta ce "amma kuma ana ganin shi, aka ganki za'a ce shine babba,"

Falilat ta ce "Eh mana saboda shi namiji ne ae."

Haka suka cigaba da fira suna taɓa snacks ɗin gaban su har aka dawo class.


Wannan karon macece ta shigo ta koyar dasu Hausa language,  'Malama Fateema' bayan ta gama ta fita wani ma ya shigo a haka har aka tashi sallah bayan sunje sunyi, sun dawo islamic aka koyar dasu dayake haka tsarin makarantar yake.


Ƙarfe uku dai dai aka tashe su, a tare Deejarh da Falilat da kuma Farhad suka fito.


Tsaye suke a bakin gate na makarantar, Falilat ta kalla Deejarh tana faɗin.
"to kodai zamu rage miki hanya ne, tunda drivern naki bai ƙariso ba?."
Murmushi Deejarh tayi sannan ta ce "an karki damu fa, kuje kawai nasan nan bada ɓata lokaci ba zai ƙariso,"

"to shikenan,"

Falilat ta amsa ta sannan ta shiga motar su driver yaja suka tafi.
Akalla takai minti biyar a tsaye sannan ta hango wata farar mota ta parker, a kusa da ita, da sauri Moses driver ya ƙariso yana faɗin.
"am sorry ma'am Mrs mai kyau ce ta aikeni shiyasa ban ƙariso da wuri ba."
Murmushi Deejarh tayi sannan ta ce "ba komai Moses yanzu shiga mu tafi gida, dan Yunwar da nakeji ba za ta faɗu ba, shiga motar tayi bayan shi ma ya shiga yaja suka bar gurin sai gida.








KANO




Da Gudun tsiya ta taho saboda tsananin saurin da takeyi, in twin's take taka staircases ɗin da sauri ta ƙarisa tsakiyar palon tana sauke haki.

"Ke Jieddarh lafiyar ki kuwa?,"

Auntie da Humaira suka haɗa baki wajen tambayar ta ganin yadda ta sauko kamar wani abu ya biyota.
Tana sauke haki ta musu nuni da haɗaɗɗiyar princely gown dake hannunta.

Cike da farin ciki take faɗin Auntie na kammala, a yau na kammala haɗa gown ɗinnan.

Da sauri Humaira ta karɓa rigar tana faɗin.

"nicely Jieddarh barkanki dai, wannan aiki haka, shimfiɗa rigar tayi a tsakiyar palon tana bin haɗaɗɗiyar rigar da kallo ta haɗu sosai ba ƙarya.

Ɗinki ne irinna ƴa ƴan sarakuna, yaran sarakunan ma ba ƙanana ba.


Da wani kalar tsadadden yadi aka tsara ɗinkin rigar, yadi mai masifar kyau da tsada, sky blue color mai haske.

Rigar bata da hannu, daga sama wajen ƙirji an matse rigar,  daga ƙasa kuma ta buɗe, amma ba sosai ba, yanayin tsarin dai irinna ɗinkin yaran sarakai.
Wasu kyawawan stones farare da kuma sky blue color da aka jeresu jikin yadin, da aka ƙawata saman rigar dasu sai sukayi kamar sarƙa.
Daga tsakiyar rigar kuma ta wajen ƙirji wasu haɗaɗɗun flowers ne, sirara sosai aka taho dasu har izuwa ƙasa, yayinda wasu guda bibbiyu kuma aka jasu ta baya ko wani ɓangare biyu.
Sai kuma wani haɗaɗɗen yadi fari ta bayan rigar, doguwa ce rigar sosai, dan sai taja ma ta ƙasa, duk da cewa ita ma Jieddarh ba baya ba akwai ta da tsayi ba ƙarya.

Sai kuma wani haɗaɗɗe kuma kyakyawan yadi fari da aka ƙawata shi da stones sky blue color, sannan aka ɗinke, shi aka  zagaye ma'ana dai zayyi kamar shine hannun rigar amma shi daban yake ba haɗe da Rigar ba.

Gefe ma ga wasu Beautifuls hand Gloves farare suma masu ɗauke da adon stones sky blue color, suma sak, ko ince fiye da na yaran sarauta suma daban a gefe ba'a jikin Rigar ba.


Kallon Jieddarh Humaira tayi Bayanta kammala ƙarewa gown ɗin kallo obaa highly.
Tana murmushi ta miƙawa Jieddarh hannunta tana mai faɗin "a gaskiya na yaba da wannan haɗaɗɗiyar Rigar tayi ɗari bisa ɗari 100%. Jieddarh tawa sannu da ƙoƙari fa."


Sannan ma zatayi ma wacca ta ɗinka kyau ɗari bisa dubu, dariya Jieddarh tayi tana faɗin.
"wayyo Humaira bakiji yadda nakeji ba, jina nake kamar nayi tsuntsuwa, naje na yanjo Ranar gasar nan ya dawo yau, kuma yanzu sannan kuma adai dai wannan lokacin  a wannan gaɓar" 😝


Humaira ta ce "kisa ranki a inuwa kamar kinyi, babban baƙo ya mutu da dare.

Championship day ɗin aita kusa nan da jibi ne ae."

Kallon Auntie Jieddarh tayi tana washe farare kuma ƙananan teeth ɗinta ta ce.
"Auntie ya kika ga wannan Rigar tayi kuwa?,"
Auntie dake zaune a saman three sieter ta ce, "sosai ai saima Ranar gasa ɗiyata zata fito a cikakiyar princess ta fasa Taro da kyawunta mai ban mamaki."


Fashewa Jieddarh tayi da dariya tana faɗin "wayyo Auntie kuna fasamin kai fa, da wannan ya bawar,"

"Yoo ai gaskiya ake faɗa keɗin kyakyawa ce, a cikin kyawawa ina faɗamiki, mutumiyar keɗin, tauraruwa ce, a cikin kyawawan taurarin dake haske guri," Humaira ce take kwararo wannan zancen a yayinda da take ninke haɗaɗɗiyar gown ɗin.



Jieddarh ta ce "wow it's so very very amazing oh my glamorous Time."


Please Humaira can you imagine, yadda zan kasance a ranar gasar kuwa?."
Ta faɗa tana yin zaman ƴan bori a tsakiyar palon tayi tagumi hannu bibbiyu tana lumshe ido, ga fuskar ta har yanzu a sake take, wanda hakan yaba kyawawan dimples ɗinta duka biyun damar bayyana, dama kuma can koda tayi murmushi ko batayi ba a haka fuskarta take koda yaushe dimples ɗinta a bayyane suke.



Humaira ta ce "komai yayi  zam zam, sai dai abu ɗaya da kika manta da shi."

Da sauri Jieddarh ta ce "Menene shi wannan abun?,"

Murmushi Humaira tayi sannan ta ce "banga kin nuna mana, wannan ƴar sandar da yaran sarakuna suke riƙewa ba."

Jieddarh ta bata amsa "ina nan da ita, tana bedroom gata ita ma launin ta sky blue ne, nd White color,"
 
Humaira ta ce "na lura da gaske kike wannan shirin fa,"

"sosai ma," cewar Jieddarh tana washe baki kamar gonar auduga.

Tashi Humaira tayi ta koma saman two sieter tana faɗin "da kikace 'glamorous' ma tunomin da wani chinese drama mai suna 'OUR GLAMOROUS TIME', kikayi, inason dramar sosai,"

Jieddarh ta ce "ni kuma wacca take cikin dramar nake so, Humaira ta ce 'Zhao liying' kike nufi?,"

"E, mana ta iya act sosai da sosai take burgeni I LIKE HER SO VERY MUCH." Jieddarh ta faɗa tana nufar staircase hannunta riƙe gown ɗin.





ABUJA


Da sallamarta ta shiga palon tana cillah school bag ɗinta sama ta cafowa.
Amsa ma ta sallamar Lailah dake zaune saman two sieter gabanta laptop tayi.
Ɗa go da kanta tayi daga kan laptop ɗin, ta sauke akan Deejarh daketa faman washe ma ta baki.

"ah ah barkanki dai ƴar school, to ya ya school ɗin?, ina fatan dai anyi karatu sosai da sosai?," cewar Lailah cike da fara'a kamar ba ita ba.


Zama Deejarth tayi a tsakiyar palon tana amsawa da "yauwa Auntie Lailah, hala ke kaɗai ce a gidan?,"


"Me kika gani?,"

Lailah ta tambaya tana kallon Deejarh ɗin, dan kuwa ba ƙaramin kyau yarinyar tayi ma ta cikin school uniform ba.


"naga kamar banga kowa bane sai ke, " ta bata amsa, Lailah ta ce "Auntie Zaynerb da Haleesat suna school, sai zuwa anjima zasu dawo, su kuma Auntie Nainarh da Nailah suna up, Momy kuma ta fita hospital kinsan bata cika zaman gida ba."


" toh Balarabiyar india fa, tana ina Deejarh ta tambayeta, murmushi Lailah tayi sannan ta bata amsa.

"Balarabiyar indian ki tana garden tana hutawa, yanzu sai ki tashi ki shiga kiyi wanka ki canza kaya sai ki fito kici lunch ɗinki yana jiranki, shalelen Balarabiyar india😃




"To shikenan,"  

Ta amsa sannan ta miƙe ta shige ɗakinta, tana shiga aje jakarta tayi a saman bed, sannan ta cire uniform ɗin jikinta, ta ɗaura towel ta shiga bathroom wanka tayi da brush sannan ta fito ko lotion bata tsaya shafawa ba, ta buɗe wardrobe ta ciro kayan da zata saka.

Cikin ƙanƙanin lokaci ta shirya cikin English wears, riga doguwa wacca bata wuce gwiwarta ba purple color, sai wando pencil fari, Ribbon tasa ta kamo doguwar sumarta kanta na ainihin fulani baki siqiq ta ɗaure ta, in cute ponytail, sannan tasa p-cap fara.


School bag ɗinta ta buɗe ta ciro wasu littafai guda uku, ɗaya £xercises Book na subject ɗin Basic science, biyu kuma Note Books ne.

Palo ta fito ta sama Lailah bata da alama bedroom ɗinta ta shiga wata ƙila.

Dinning room taje ta zauna a kujerar dinning ɗin, sai da taci abinci ta ƙoshi sannan ta miƙe hannunta riƙe da Books ɗin ta fita waje.



GARD£N ta nufa, a hankali ta Tura ƙofar garden ɗin ta shiga akan wasu haɗaɗɗun kujeru, na hutawa ta hango Lailah da Afeefah zaune, Afeefah tana karanta wani £nglish Book 'HOW TO MAKE FALL IN LOVE,' yayinda Lailah take sarrafa system ɗin dake saman lap's ɗin ta.


Akan kujerar dake lilawa ta zauna tana faɗin "Auntie Lailah ashe Nan kika taho?,"
Lailah ta bata amsa "ae nan na gudo nima,"

Kallon littafan hannun Deejarh ɗin, tayi sai kuma tayi murmushi tambayarta tayi, "wa'innan fah ?.

Dariya Deejarth tayi sannan ta ce "kai Auntie Lailah karatu fa, zanyi da Rubuta, kuma akwai wani Assignment da aka bamu yau a school zaki koyamin."

Lailah tana murmushi ta ce "ah lallai Ƴan makaranta daga zuwa yau har an fara baku Assignment?, to wani subject ne?,"

"Hausa language ne fa, kuma zasuyi wahala sosai," cewar Deejarh tana ya mutsa fuska.

In rushing Lailah take faɗin "to tunda Hausa ne, ki bari in anjima kya ba Auntie Nainarh, tunda ita Hausa ta karanta,"

Deejarh ta ce "ke bazaki iya bane?,"
Lailah ta ce "rabani da wahala, Hausa ai akwai wuya yafi Turanci wahala sosai fa."

Dariya Deejarh tayi ta ce haka Ƴan class ɗinmu suketa faɗa,  lokacin da malamar ta bada Assighment ɗin,  gata akwaita sauƙin kai ga fara'a🤓



*💋💋SARAUNIYAR🎀KYAU💋💋*

______________________________________________________________________💥👑𝑻𝒉𝒆 𝑮𝒍𝒂𝒎 𝐐𝐮𝐞𝐞𝐧👑💥____________________𝑩𝒚:𝑻𝒉𝒆 𝑵𝒂𝒊𝒏𝒂𝒓𝒉 𝑲𝒅____𝑲𝒉𝒂𝒅𝒆𝒆𝒋𝒂𝒓𝒕𝒉.  𝑺𝒂𝒃𝒊'𝒖.  𝒀𝒂𝒉𝒚𝒂𝒉🤙


☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆
💦𝑳𝒂𝒇𝒂𝒛𝒊 𝑾𝒓𝒊𝒕𝒕𝒆𝒓'𝒔 𝑨𝒔𝒔𝒐𝒄𝒊𝒂𝒕𝒊𝒐𝒏💦🤙

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆





*Page 31&32*






"E gaskiya suka faɗa hausa akwai wuya ga wanda bai iya ba, ni kenan" cewar Lailah.

Saidai kuwa idan mutum bai mayar hankali ba," Afeefah ta bata amsa tana mayar da kallonta kan Deejarh.

Lailah ta ce "nidai ban iya ba, "shine kuma kikeyi yanzu?,"


Deejarh tayi ma ta tambayar tana ƙureta da idanu, murmushi Lailah tayi sannan ta bata amsa.

"ae faɗan Hausa a baki daban, haka zalika rubutawa daban, sannan kuma koyan harshen Hausa shima daban ne."

Deejarh ta ce "oho shiyasa ake cewa hausan baka, hausan adabi 😳
Ko miye da miye dai, gasunan kala kala,"
"kinjiki bazaki iya lissafowa ba kenan?," Afeefah ta tambaya.

Lailah ta karɓe da faɗin "ai tamayi ƙoƙari tunda har tana ganewa,"
Da sauri Deejarh ta ce "au ke bakya ganewa?, a lokacin da kike a secondary school kenan?,"

Dariya tayi ta ce "jerk kawai akwai ki da surutu fa,"  Deejarh ta ce "haka ake faɗa, to idan mutum bayyi surutu ba, ɗinke bakinshi zayyi da zare da allura?,"
Lailah ta ce "bawai haka ba, kawai wani lokacin ki dinga yima bakinki linzami."








💅𝐓𝐡𝐞 𝐅𝐚𝐬𝐡𝐢𝐨𝐧 𝐒𝐡𝐨𝐰 𝐒𝐭𝐨𝐫𝐲💅







ʜᴀʟᴇᴇsᴀᴛ



A gajiye ta fito daga practical lab. Chest ɗinta rungume da ma'ajin bayanai.

Tsayawa tayi da tafiyar da takeyi jin ana qwala ma ta kira, bata juya ba saima duba wristwatch ɗin dake ɗaure a tsintsiyar hannunta tayi ƙarfe huɗu saura na Yamma...


Sannan ta ɗago tana kallon Jenny da ta ƙariso gurin tana sauke haki alamar tasha gudu ba laifi.


"Menene sauri nake faɗa abin da zaki faɗa zanyi gaba,"

Da tsananin mamaki Jenny take kallon Haleesat, sai kuma tayi murmushi ta ce "haba Leesat ai bani na kar zomon ba, dama akwai abin da nakeso na tambaye ki, idan babu damuwa?."

"Okay, ina sauraronki,"  Haleesat ta faɗa tana gyara tsayuwa cike da gajiya.


"Wai mene ya faru ne, a tsakanin ki da su Zuree naga kamar baku ga maciji, yanzu kuma naga kin dena zuwa Night club,  shine nakeso naji ko lafiya?,"

Jenny ta dire maganar tana kallon Haleesat, murmushin takaici Haleesat tayi sannan ta bata amsa "au su basu faɗa miki abin da ya faru bane, kokuwa zakice baki san komai ba?."

Da sauri Jenny ta ce "ba wani abu da na sani,"

"Okay yanzu dai kinaso kicemin bakisan sunyi kidnapped ɗi na ba kenan?, kuma sunyi attempting raping ɗina😓



Qwalalo madaidaitan idanunta Jenny tayi waje baki da hanci sake take faɗin.

"what, mekike nufi kinaso kicemin dai sunyi abin da naji suna shiryawa kenan...." ta faɗa cike da mamaki.



"Of course not! Sunyi attempt haka amma basu sama nasara ba,"
Jenny da taji tsayuwar da take bai isheta ba, ta zauna daɓas zaman ƴan bori a ƙasa, ta kuma miƙewa sannan ta koma ta kuma zama, babu abin da bakinta yake furtawa fa ce.

"jesus oh amma fa, su Zuree sun bani mamaki ba kaɗan ba,"  Haleesat tana murmushin abin da Jenny tayi ta ce.

"ashe dai kinsan wani abu,"

Kallonta  Jenny tayi har yanzu bakinta bai bar faɗin 'jesus' ba ta ce "nasan dai wani abu daga ciki, amma zamu iya zama saboda maganar ba za ta yuwu a tsaye ba,"

"Okay to ga guri can ai, Haleesat ta bata amsar, tana gaba, ita ma Jenny tabi bayanta kamar wacca kwai ya fashewa a ciki.




A wasu kujerun hutawa farare ƙasan bishiya suka zazzauna, suna fuskan tar juna sunyi shiru na ɗan lokaci, kafin Jenny ta katse shirun da faɗin.



"Wata Ranar Saturday misalin ƙarfe uku na Rana. Muna zaune a hostel."

[da yake a hostel suke zaune Jenny, Zuree, Feenah, a tare a]


"Lokacin idan banmanta ba, ni ina daga saman bed ina karanta wani £nglish book 'SAY NO TO CORRUPTION' yayinda Zuree take kwance a saman doguwar sofa mai ɗaukar mutane biyu, tana chatting a wayarta, ita kuma Feenah tana goge wasu kayanta da iron, a lokacin munayi muna ɗan taɓa fira sama sama.
Har ɗan hayaniya yaso ya kaure a tsakanin Zuree da Feenah akanki, saboda bakya shan kayan ruwa ko wani abin da ya dangance maye daɗin daɗawa kuma bakya kula ko wani kalan Namiji balle kuma wani abu ya shiga tsakani.

Zuree ta ce 'ai saboda taba waye bane shiyasa,' ita kuma Feenah ta ce 'ba wani waye wa, ai waye ba shine shashaye ba, ko kuma bin maza da mata kamar busuruwa ba,'  jin haka yasa Zuree ta fusata ta miƙe tana nuna  Feenah da yatsa, tana faɗin, 'ai qwara ita, kowa yasan tanayin abinta a fili wata kuma bin matan ma a ɓoye takeyi,' da faɗar haka ita ma Feenah ta fusata a miƙe tsaye ita ma tana faɗin, 'ai qwara ita watan, saboda iya mata take bi, wata kuwa har maza tanabi saboda rashin sanin ciwon kai.'



"HABBA!.


Nanfa aka fara bankaɗe bankaɗe kowa yana faɗar sirrin kowa idan wannan ta faɗa wannan ta faɗa.
Nidai ina daga gefe sai haƙuri nake basu ba abinma da yafi ɗauremin kai sai jin da nayi Zuree na faɗin Feenah tana bin jinsinta mata, kamar yadda ita ma Zuree take, abin ya ɗaure min kai, sosai.
Ni aga ganina ba haka abota ko ƙawance yake ba, A ZATO NA idan akace aboki ko ƙawa ana nufin wanda komai ya sameka tamkar shiya sama ne, A ZATO NA idan aboki yana cikin matsala ko wani abun aboki shi zai jajirce da ƙarfin shi ko da wani abu daya mallaka har sayya ceto wannan aboki nashi.

A TUNANINA idan aboki ya faɗi ƙasa da sauri shima ɗayan abokin nashi zai bishi su faɗi tare, ashe nayi kuskure ba haka abin yake ba, ashe abotar yanzu anyinta ne kawai amma ba'a san Menene ainihin 'KALMAR ABOTA YAKE NUFI BA.'



Haka sukayita yi har saida suka gaji dan kansu, sannan suka saurarawa juna, nidai ina daga gefe nayi tagumi hannu bibbiyu ina kallon abin mamaki, tun lokacin da naje janye Feenah na sama nabon naushi a ciki daga Zuree nayi gefe😂




Can wuraren Ƙarfe huɗu da rabi wata 'Hanifa Falalu' wacca ɗakinsu yake ƙasan namu ta shigo tana faɗa mana wai munyi baƙo a waje, kuma mu dukan mu yake kira, da mamaki mu duka muke kallonta, jin abin da take faɗa, Zuree ta ce 'mu kuma?, kodai bamu bane, amma ta ya za'ace mu duka yake kira?, Hanifa ta ce 'haka yace ma ta', Zuree da Jenny da kuma Feenah, sannan kuma mutumin yana daga wajen gate yana jiranmu gate man yaƙi bari ya shigo.'

Jin haka yasa Feenah da Zuree suka miƙe ko wacce ta zara gyalenta suka fita, nidai cewa nayi ba inda zani tunda bansan ko wanene mutumin ba.




 'T£N MINUT£S AGO'




Sai gasu sun shigo suna fira hadda shewa kamar basu suke harare harare a lokacin da zasu fita ba.


Nidai ban bi ta kansu ba, saima saukowa daga kan bed da nayi na shige bathroom domin nayi wanka, bayan nayi ne zan fito daga bathroom ɗin kenan harna saka hannuna dake ɗigar ruwa, zan murɗa ƙofar bathroom ɗin naji Zuree tana faɗin.

"yanzu saimu san lokacin da ya kamata mu ɗana ma ta tarko, domin kuwa wannan aikin da aka bamu mai tsokane sosai,"

Feenah ta karɓe da faɗin "kedai bari kawai, a wannan lokacin wazai baka two million's akan wannan ƙaramin aikin, kai kuma ka tsaya wasa, ai da gudu zan amsa, ko kisan kai ne, ai sainayi badai akwai masu motsi ba, suka kuma kwashewa da dariya.


Nidai tsananin mamaki ma ya hanani koda motsi, sai da naji suna ci gaba da tattauna war, sannan na samu na kwashi ƙafafuna waɗanda sukayi sanyi na jin abin da suke faɗa haka na fito daga bathroom ɗin a raina ina saƙe saƙen abubuwa da yawa sosai sosai.


Ganin na fito daga bathroom ne yasa Feenah tayi shiru da faɗin abin da tayi niyya ni kuwa ko kallonsu banyi ba, har na ɗaga kafafuna na nufi closet a domin shiryawa, naji ina ai gwara kawai na taresu a fili ba ɓoye ɓoye, domin naji abin da suke shiryawa budurwar da ko saninta banyi ba, domin a lokacin basu ambaci sunanta ba, idan ma na rabu dasu tsoro ma kenan, bayan kuma naji suna shiryawa wata gadar zare,  banga amfanin zaman tare, babu amana ba, indai ban fito na musu magana akan hanyar da suke su jefa kansu ba.





Cike da gwarin gwiwa na juya ina kallonsu dukansu, da idanuna da suka rine da ɓacin rai, wanda ban taɓa shiga ba tsawon rayuwata, domin naji abin da yafi ƙarfin tunanina da lissafina.



Cikin faɗa da hargowa nake faɗin, 'kundai ji kunya wallah, kuna mata bakusan ciwon ɗiya mace sai ɗiya mace ba, akan wata banza two million's zaku jefa kanku cikin masifa.


Shin ko kunsan abin da shi mutumin zayyi da ita budurwar da ya baku umarnin samota?.

Ko kuwa ya faɗamuku ne?, kuka sani ko kasheta zayyi ko kuma yayi Raping ɗinta ko kuma yayi wani aikin asiri da ita,  ko ko duka dai bakusani ba, kawai dai akan wata banza two million's kunzo nan kunata wani cika baki menene da menene ku ba Ruwanku. Tur da zama da ƙawaye irin ku, tir da halinku kaico wallah.



Tunda na fara maganar na fahimci jikin Feenah ya ɗanyi sanyi, ko kuwa yanayin hallitar ta ne ya motsa, na yawan sanyi, nidai bansani ba, na nufe ido ina zazzaga ruwan  masifa.

Yayinda Zuree ta cika tayi fom fam ƙiris take jira ta fashe duk surutun da nake yana shiga right ear ɗinta ne ya fita ta left.

Aikuwa ban rufe baki ba ta tashi a fusace, dama bahaushe yace da hauka ake naɗe tabarman kunya, aikuwa nanta hau yi kamar bakinta zai tsage dama gata da saurin baki kamar me faɗi take, "to ke ina ruwan ki koma miye zayyi da ita ba abin da ya damemu mudai munji dumus, kuma zamuyi aiki sai naga uban da ya isa ya hanamu banza dake a gurin."




Nima cikin masifa na hayayyaƙo ma ta nace "dubeki shashasha dake a gurin, ke a cikin shashashu ma sai dai a kira ki 'DANKALI' yasin, saboda tsananin shashanci da akuyanci, ki rasa wacca zaki cuta sai ƴar uwanki mace, aikuwa anyi asara."


Cike da kumfar baki Zuree ta ce "E, naji koma miye zakice kin daɗe baki faɗa ba, kuma anjima da dare saina kai mishi 'Haleesat' ɗin idan ma kasheta zayyi ko Raping ɗinta yayi, kawai dama ta isheni a rayuwa."



Tun a lokacin data kira sunan 'Haleesat'  jina da ganina na wani lokaci ya ɗauke sakamakon banyi  tunanin ke ba ce, ashe ɗan Adam ba'a bakin komai yake ba.


Da ƙyar na samu na dawo da nutsuwata, na kalleta a ƙasƙance nace.

"aikuwa sai dai aniyar ki ta biki domin Haleesat tafi ƙarfin ki nesa ba kusa ba, domin 'she was very £xtraordinary lady' ita ba kalarki bace, ko zuwa Night Club da takeyi jarab tane kuma kema kinsani Haleesat batayi kalar mata masu yawon ta zubar ba."



Shiru tayi domin kuwa a yanzu bata da amsar da zata bani, ganin haka naja tsaki ina faɗin "idiot kawai kina mace bakisan ciwon kanki ba, wai kuma a haka kike yarinya a gurin babban malami shahararre, andaiji kunya ƴar malam taƙi halin malam.



Duk sunaji na amma daga ita har Feenah dake kwance saman bed, sun kasa tankamin, na kuma jan tsaki sannan na nufi wardrobe na ciro kayan da zan saka.
Harna kammala shiri suna ɗakin sunyi gum kamar ruwa ya shanye su.




Dare misalin ƙarfe goma saura a lokacin wayata tayi full charge, ina zaune saman doguwar kujerar ɗakin, ina sipping coffee, na lalubo lambar ki na kira duk a zato na, sunyi bacci shine fa, kina ɗagawa Feenah ta ƙure volume na speakers, ke kuma daga wajen ki bakyaji sosai, na miƙe da niyyar fita waje, nan wani jiri ya kwashe ni mug dake hannuna ya tarwatse a ƙasa, daga nan nima na bishi bansan tayaya kuma meya faru ba.



Kawai dai da safe na farka ne na ganni a saman bed, ɗakin ba kowa alamar dai ba'a anan suka kwana ba, a lokacin kasa tashi nayi saboda kaina dake matuƙar sarawa haka kuma ga jikina ba qwari.



Nafi ƙarfin two hours a haka sai daga baya na samu na tashi da kyar na shiga bathroom nayi wanka na fito, har lokacin ba ɗayarsu da ta dawo a gurguje na shirya cikin sauri sauri.

Bayan na shirya ne fa, wuraren ƙarfe biyu na rana har lokacin dai ba wacca ta dawo, zuwa lokacin hankalina ya fara tashi ina nan zaune, saiga ƙanwar Zuree ta shigo ɗakin wai tazo gurin Zuree yayarta, kuma tarema suke da babban yayansu.

Aikuwa ba tare da ɓata lokaci ba, ma ta bayanin abin da ke faruwa tun daga farko har ƙarshe.
Ita kuma tanajin haka ba ɓoye ɓoye taje ta faɗama babban yayansu dake waje cikin mota yana jira, shima dai kamar ƙanwar yasha mamaki, amma sayya dake ya ciro phone ɗinshi a trouser pocket ɗinshi ya lalubo lambar Zuree, ya danna kira amma waya a kashe ya kira yakai sau goma amma dai abu ɗaya waya a kashe.




TASHIN S£NS£!


Muna tsaye a bakin gate munyi cirko cirko muna jiran tsammani, saiga wata arniyar mota black color ƙirar R.R. ROLLS ROYC£.
Tayi parking a can gefen mu saiga ƙanwar Feenah, wato Fannah ta fito daga ciki da sauri ta ƙariso gurin da muke tana tambaya na ko lafiya, sannan kuma Feenah tanan sun kawo ma ta ziyara ne.

A lokacin duk da bani ce nayi laifin ba, amma wallah saida naji wani fitsarin tsoro ya cika marata.

Da kyar na samu na ce ma ta "Feenah bata nan,"  zatayi magana saiga Dadynsu da kuma Momyn su matar da Feenah take a hannunta, da kuma wani saurayi da alama yayansu ne sun ƙariso gurin.



Hannu yayansu Feenah yaba Babban yayansu Zuree sukayi misa baha, sannan suma suke tambaya ko lafiya suka ganmu cirko cirko dayake na ɗan saba da ƴan gidansu Feenah ba laifi.

Nanfa babban yayansu Zuree ya gyara tsayuwarshi, yaba su labari kamar yadda na bashi.



Nanfa naga ɓacin rai kalar wanda ban taɓa gani ba, dan kuwa yayansu Feenah yafi Babban yayansu Zuree nuna tsantsar ɓac
cin ranshi akan abin da yaji su Feenah sun aikata ko ince suke akan aikatawa.


Cikin tsananin ɓacin rai yake faɗin "yaushe kuma ta yaya Safeenah, dama haka sunan Feenah yake na gaskiya.


Ta zama haka, kuma mu muna ina, a wannan lokacin da ƙarfi ya damɗe hannun shi yana futar da huci, shikuwa Dadynsu Feenah tsananin mamaki ya hanashi faɗin komai, haka dai munkai kusan minti talatin muna tsaye a gurin kowa da abin da yake saƙawa aranshi.



Can saiga Motar Zuree ta nufo gate ɗin bamu sani ba, sun hago mutane ne a gurin ko miye ya faru, da sauri dai mukaga motar tayi reverse zata bar gurin.


Ai a three sixty 360 yayansu Feenah shida Babban yayansu Zuree suka bi motar wata kalar super Babban yayansu Zuree yayi yasha gaban motar, yayinda yayansu Feenah ya fasa glass ɗin motar da hannun shi, bai damu da jinin da hannun shi yake ba, ya finciko Feenah waje bai tsaya komai ba, ya dingi ball da ita yana marinta ta ko'ina dukanta yakeyi, don koda yaga ta suma ruwan roba ya ɗauko a mota ya kwara ma ta, ba shiri ta farfaɗo shi kuma ya ci gaba daga inda ya tsaya,  ganin zayyi kisane yasa ƙanwar Feenah, Fannah ta ruga da gudu tana kare Feenah tana bashi haƙuri, amma ina kamar ma cewa take ya ci gaba, aikuwa ya haɗa da ita yana jibga baya ma gajiya ga mutane har an fara taruwa ƴan kallon qwaqwaf hadda masu ɗaukar video.

Ganin zai kashesu su duka ne yasa Momyn su ta tafi da sauri ta shiga tsakani, sannan fa ya dakata, shikuwa Dadynsu yana gani yaƙi magana sai ma mota daya koma abinshi.




Shikuma Babban yayansu Zuree tun lokacin da ya kamota wani farin gam yasa ya rufe mata baki dashi, sannan ya ɗauko igiya ya ɗaure m ata hannu da ƙafafu duka biyu sannan fa yahau dukanta yana kwallo da ita haɗe da marinta, fuskar nan nata da tasha bleaching tayi wani irin jajir kamar kamar me.
Bai dena dukanta ba sai da yaga bata motsi sannan ya ciciɓeta a haka ya jefa a mota kamar kayan wanki sannan ya dawo wajen yayansu Feenah suka sakeyin misabaha, ya min godiya sannan ya shiga mota ita ma ƙanwar Zuree ta shiga yajasu suka bar gurin.
Shima yayansu Feenah kaɗasu yayi suka shiga mota suka bar gurin suma daga nan kuma kowa yayi gaba, nima haka jiki ba gwari na koma ciki.



Ajiyar zuciya Jenny ta sauke da ta kawo nan sannan ta kalla Haleesat da tunda ta fara maganar ta zuba ma ta ido, murmushi tayi ta ce "in taƙaice miki dai Zuree a ranar mahaifinta ya aurar da ita sadaka ga wani almajirinshi, sannan kuma yace karatun ma an barshi ba ita ba ƙara zuwa school forever...ita kuwa Feenah taci wuya amma dai ita ba'a katse ma ta karatu ba saboda Dadynsu cikaken ɗan boko ne, gaba da baya amma dai yanzu bata kwana a hostel sai dai ana tashi driver yazo ya ɗauketa su tafi gida thats is all.


Ajiyar zuciya Haleesat ta sauke, sai da ta nisa sannan ta ce "duk da abin da suka min banji daɗin hukuncin da aka yankewa Zuree ba, aure bashi zaisa ta nutsu ba, nasan halin Zuree gaba da baya."

Da tsananin mamaki Jenny take kallon Haleesat ta ce "ae na ɗauka zanga kina farin ciki ne, a lokacin da nake baki labari,..sai kuma kika bani mamaki...a gaskiya Haleesat bazan ɓoye miki ba, kina burgeni sosai fa over, sannan kuma zuciyarki mai kyau ce, ina alfahari dake a matsayin ƙawata, am so very proud of you, ashe akwai mutane irin ki a duniya lallai ne, yau na yadda da kalmar na 'INDA RANKA KA SHA KALLO.'


Ɗan murmushi Haleesat tayi aiƙaice sannan ta ce "Jenny kenan akwai ki da sonyin karin magana, gashi baki wani iya ba," ta ƙarishe maganar tana kuma sakin murmushi, Jenny ta ce.


"saura kuma abu ɗaya, da ban faɗamiki ba,"


"Menene shi?,"


Haleesat ta tambaya, Jenny ta ce "na sama Admission a Beijing China, acan zan ɗaura master's ɗina."

Ta faɗa cike da farin ciki, washe baki Haleesat tayi sannan ta miƙawa Jenny hannu tana faɗin.
"congratulations Dear, yanzu shikenan zaki tafi, ki barmu da kewar ki ko?."
Jenny tana dariya ta ce, "toya za'ayi duk acikin neman ilimi ne.."

Dariya sukayi a tare Haleesat ta ce "kuma fa kinyi gaskiya," tashi sukayi a tare Haleesat ta nufi motar ta shiga taja, ita ma Jenny ta nufa nata ta shiga.





HAL££SAT



Tana driving amma gabaɗaya hankalinta baya jikinta, ta faɗa duniyar tunanin hali irin na mutane zaka haɗu da mutane kala kala a Rayuwar ka sannan kuma zakaga kowa da kalar halinshi.



Horn tayi a ƙofar gate ɗin gidansu bayan ta iso, wangale ma ta gate ɗin mai gadi yayi, sannan ta shiga da motar ciki.

Saida ta daidai ta parking a wajen da aka tanadar domin yi sannan ta fito, back seat ta buɗe ta ciro handbag ɗinta da wasu files, sannan ta nufa ciki, gabaɗaya jikinta a sanyaye.




Wasu lambobi ta danna a jikin glass door ɗin nan take ƙofar ta buɗe da kanta saida tsaya a bakin ƙofar ta canza takalman kafafunta izuwa slippers na shiga, sannan ta shiga ciki bakinta ɗauke da sallama.

Gaba ɗaya mutanen dake zaune a palon suka amsa ma ta Zaynerb tana daga saman doguwar kujera tana kallon wani indian drama 'THOLI PREMA' na varun tej da Raashi Khanna, yayinda Nainarh takeyi ma jaririn Nailah wasa. Ita kuma Nailah tana baje a tsakiyar palon tana duba wasu takardu, ƙarisa shiga ciki tayi.
Zaynerb ta ce "yau baki dawo da wuri ba, fatan komai Normalcy?,"
Kallon Zaynerb dake magana Haleesat tayi sannan tana murmushi ta ce "komai lafiya sister, kawai dai yanayin garinne,"
Zaynerb ta ce "haka akeso komai ya kasance lafiya a kullum kuma a ko yaushe,"

Haleesat tayi dariya Zaynerb akwai ta da barkwanci wani lokacin bedroom ɗinta ta wuce bayan tama su Auntie Nainarh barka.




Tana shiga ta aje handbag ɗinta da sauran files ɗin dake hannunta a saman glass center table, sannan ta fara kici kicin rage kayan jikinta, bayanta gama ɗaura towel tayi sannan ta shiga bathroom, wanka tayi da brush dayake bata da tsarki.

Fitowa tayi chest ɗinta ɗaure da towel White color, sama sama ta shafa lotion saboda yanayin garin sannan ta shirya cikin kayan shan iska, riga fara mai hannun vest sai wando crazy jeans ash color, sannan ta ɗauko Ribbons white color nd ash color guda biyu, ta tufke doguwar suman kanta, ya zubo har gadon bayanta, wani siririn gyalle ash color ta ɗauka sannan ɗaura akanta tayi kyau ba ƙarya. Ta fito sak RAASHI KHANNA, gaban dress mirror ta ƙarisa ko powder bata tsaya shafawa ba, ta ɗauki man baki ta saka a siraran laɓɓanta jajaye dasu.


𝑳𝒐𝒗𝒆💘𝑮𝒍𝒂𝒎𝒐𝒖𝒓💋𝑫𝒆𝒔𝒕𝒊𝒏𝒚😼𝑻𝒐𝒍𝒆𝒓𝒂𝒏𝒄𝒆😥𝑹𝒐𝒎𝒂𝒏𝒊𝒛𝒂𝒕𝒊𝒐𝒏_𝒉𝒊𝒈𝒉𝒍𝒚🌹𝑫𝒆𝒂𝒕𝒉😭𝑴𝒂𝒔𝒕𝒆𝒓_𝒅𝒆𝒗𝒊𝒍👹𝑪𝒉𝒂𝒎𝒑𝒊𝒐𝒏𝒔𝒉𝒊𝒑👑𝑪𝒉𝒆𝒂𝒕𝒆𝒅🤕𝐁𝐞𝐚𝐮𝐭𝐢𝐟𝐢𝒄𝒂𝒕𝒊𝒐𝒏💅𝑳𝒂𝒖𝒈𝒉𝒆𝒅😆𝒂𝒏𝒅_𝒑𝒆𝒓𝒇𝒆𝒄𝒕_𝒄𝒐𝒖𝒑𝒍𝒆𝒔_𝒓𝒆𝒍𝒂𝒔𝒉𝒊𝒐𝒏😇__𝑨𝒍𝒍_𝒊𝒏__S̟A̟R̟A̟U̟N̟I̟Y̟A̟R̟ K̟Y̟A̟U̟__T⋆a⋆k⋆u⋆n⋆_F⋆a⋆r⋆k⋆o⋆









*💋💋S̑̈Ȃ̈Ȓ̈Ȃ̈Ȗ̈N̑̈Ȋ̈Y̑̈Ȃ̈Ȓ̈ K̑̈Y̑̈Ȃ̈Ȗ̈💋💋*

           
*💥𝑇ℎ𝑒 𝐺𝑙𝑎𝑚 𝑄𝑢𝑒𝑒𝑛💥*




Đ₳₲₳ ₳Ⱡ₭₳Ⱡ₳₥ł₦




*💘𝐾ℎ𝑎𝑑𝑒𝑒𝑗𝑎𝑟𝑡ℎ 𝑆𝑎𝑏𝑖'𝑢 𝑌𝑎ℎ𝑦𝑎ℎ💘*


*☆𝑇ℎ𝑒 𝑁𝑎𝑖𝑛𝑎𝑟ℎ 𝐾𝑑☆*






*page 33&34*







Fitowa tayi Drawing-Room ta shiga ta ɗauko wani board wanda akeyin zane akanshi da kuma Drawing-paper da sauran kayan zane.
Sannan ta fito palo daga can gefe ta shirya kayan zanen da ta ɗauko, komawa tayi ta ɗauko wata royal chair ta zauna akai yadda zataji daɗin yin zanen yadda ya kamata.
Sudai su Nainarh sun zuba ma ta ido suna kallon ikon Allah, yau kuma Haleesat ce da zane, aikuwa akwai kallo, ita kuwa tanayi tana ɗan tsayawa tunani.

Lailah, Afeefah, Deejarh sune suka shigo palon bakin su ɗauke da sallama, duk suka amsa musu Nailah na faɗin "har andawo daga garden ɗin kenan?,"

Afeefah ne kawai ta iya bata amsa, domin Lailah da Deejarh hankalin su yana kan Haleesat da ta taƙarƙare tana zanenta ba abin da ya dameta.



Da sauri Deejarh ta aje Books ɗin dake hannunta a saman center table sannan ta nufi wajen da Haleesat take, faɗi take



 "Auntie Haleesat zane kikeyi kenan?,"

Juyowa Haleesat tayi tana goge uban gumin da ta haɗa da wani handkerchief ash color, tana murmushi ta ce "you know kinsan abin da zan zana ne."

Deejarh ta ce "a'a zandai sani idan kika gama zanawar,"

"Okay, saka ido kiga ikon Allah," dariya Deejarh tayi sannan ta zauna a saman carpet tana faɗin "to Auntie Haleesat ɗinmu,"

Tanayi Suna taɓa fira sama sama da mutanen palon da duka suka zubo ido suna jira ta kammala suga abin da ta zana.

Lailah ta ce "da alama wannan zanen is very very special tunda har naga an ɓata lokaci ba'a gama ba,"


Zaynerb ta amshe da faɗin kika sani ko Brother In law ɗin mune?,"

"Kudai kawai ku zuba ido kusha kallo, koma waye ai dai zata gama, kuma zamu gani."
Cewar Nailah da duk tabi ta ƙosa Haleesat ɗin ta kammala zanen suga ko wani kala ne.




"Yes yasin ta kammala wallahi ta kammala."

Deejarh ta faɗa hakan cike da farin ciki, da sauri su duka suka taso banda Nainarh.

"Kun gani yasin yayi kyau sosai sosai fa."

Deejarh ta kuma faɗa tana juyi a gurin, dukansu dariya sukayi ganin abin da Deejarh takeyi.

"To a bamu mu gani, mana a nata ja mana rai fa,"  Lailah tayi ƙorafin tana kuma cusa kanta danta hango zanen, yayinda Haleesat taƙi bari kowa ya gani.


Ganin zasu iya qwata ta ƙarfi tunda sun fita yawa ne, yasa da sauri ta aje zanen a saman center table na tsakiyar palon.


"Kinyiwa kanki gata da kika aje." Zaynerb ta faɗa tana ƙarewa zanen kallon ƙurilla, kamar yadda suma su Afeefah sukayi suna kallon zanen.


Wani haɗaɗɗen cute guy ne, dogo sanye cikin trouser jeans da t-shirt, fuskar shi rufe take da wata haɗaɗɗiyar face mask. Ba'a iya ganin komai a fuskar shi, sai manyan idanun shi farare kyawawa dasu, sai kuma dogon hancin shi da face mask ɗin bai gama rufewa ba, kanshi kuwa p_cap ce wacca ta kusa rufe mishi fuska, yasa hannun shi ɗaya cikin trouser pocket ɗinshi yayinda ya riƙo saman p-cap ɗinshi da ɗayan hannuna shi, kafafun shi sanye cikin back-shoe irinna jami'ai.


Ajiyar zuciya ko wanen su ya sauke bayan sun kammala ƙarewa mutumin da Haleesat  ta zana kallo, kafin suka dawo da kallon su akan Haleesat da sai faman sakin murmushi take kamar wata zautacciya.


"Shin zaku iya cinka ko waye wannan ɗin?,"
Haleesat ta tambayesu dan tasan tambayoyin dake a bakunansu kenan, shiyasa ta riga su.

Qara kallon zanen ɗin Afeefah tayi da kyau tana nazari. "a tunanina yanayin falsafar tsayuwar shi, ya nuna kamar detective ne shi, especially idan ku ka lura da yadda ya zura right hand ɗinshi cikin trouser pocket, zai iya yuwuwa bindiga zai ciro, sannan kuma ku duba da kyau, yanayin yadda ya rufe fuskar shi, da face mask da kuma yadda yasa hannun shi yana kuma janyo p-cap ɗin, sannan kuma da alama wani yake nema, ko kuma yake shirin bi, sannan kuma ku ƙara duba yanayin shigar shi, yafi yanayi da shigan jami'ai, jami'an ma na sirri."



Ganin yadda suka zubo ma ta ido suna kallo ne, yasa tayi saurin faɗin, "amma fa, hasashe ne bawai nasani bane, kawai dai yadda zuciyata ta hasasomin ne."

Ajiyar zuciya dukansu suka sauke sannan suka juya Suna kallon Haleesat da tayi shiru kamar mai tunani, tabbas idan bata manta ba, kamar wani taga yake bi a lokacin.




Deejarh ta ce "to har yanzu dai ba'a faɗamana ko wanene ba," Zaynerb ta amshe da faɗin "nidai nasan Brother In law ne, kawai tana kunyar faɗane."
Harararta Haleesat tayi tana faɗin duk cikin ku, banga wacca zanji kunyar ta ba."

Lailah ta ce "to idan abin haka ne, faɗamana ko wanene tunda dai ba haka kawai zaki zauna ki ƙera drawing wannan handsome guy ɗin ba."


Lumshe kyawawan idanunta tayi, sannan ta buɗe a hankali ta wani juyasu in styling, ta kallesu su duka ta ce.


"MY SOUV£NIR."


Kwashewa sukayi da dariya su duka Afeefah ta ce "aha kice shiyasa naga ake wani jin kunyar mu, ashe our Brother In law ne."

Duka Haleesat ta kai mata da sauri ta matsa gefe tana dariya, Lailah ta ce "ah lallai Auntie Haleesat, kin kamu da yawa, irin wannan special handsome haka, wai damma a zane muka gani ina ga ace a fili ne, ai dole ma kiyi nisa."



Nainarh ta ca fe da faɗin "ah banga laifinta ba, soyayya daɗi bakuji ana faɗin, Love is sweet like a lollipop ba?."


"Yanzu dai our sister, finally she's fall in love, dan haka dole mu haɗa shagali, ko ba haka ba sister's?."

Zaynerb tayi maganar tana kallon su, gabaɗayan su suka haɗa baki, hanyar amsa ma ta da "haka ne ƴar uwa."

Ba tare da ɓata lokaci ba, Afeefah ta danna wasu lambobi a telephone ɗin dake a palon tayi ordered na pizza dasu shawarma, burger, cake e.t.c.


Sannan ita da Lailah da Deejarh, sai Zaynerb ko wacce ta ɗaura apron suka shiga kitchen aka fara aiki😃



Cikin ƙanƙanin lokaci suka jere komai a dining table zuwa lokacin, ma'aikacin boutique ya kawo ordered ɗin da Afeefah tayi gabaɗaya suka haɗa suka jere a dining.



Tun daga kan snacks juice kala kala ba kalan da babu.
Gaba ɗayansu suka hallara a dining table, su duka.


Zasu fara kenan sukaji door Bell, tashi Lailah tayi ta nufi ƙofar domin buɗewa, saida ta fara duba ƴar qaramar portable computer dake manne a wall na palon, da sauri ta ɓude ƙofar ɗin ganin mutanen dake tsaye a bakin ƙofar.



Da gudu tayi hug ɗin Momy Rafi'at dake tsaye cikin shigar cikakkun manyan likitoci, sai da ta rungumi Momy sannan ta juya kan Daddynsu dake gefe yana murmushi sanye cikin Business suit black, shima rungume shi tayi tana faɗin.

"oyoyo Daddy kayi surprised ɗinmu sosai, shine baka faɗa mana yau zaka dawo ba ko?."

Momy Rafi'at ta ce "tunda dai ya dawo lafiya, ai sai ki bari ya shiga daga ciki, sannan sai kiyi shagwaɓar yadda kikeso." Momy tayi maganar fuskar ta a washe.



Ɗunguma sukayi suka shiga ciki, hannayen Lailah cikin nasu su duka, Afeefah da taji Lailah shiru ta taso domin ganin abin da ke faruwa, saukayi ido huɗu da Daddynsh, ai batasan lokacin da ta taka da gudu ba, ta rungumeshi tana dariya shima Mister Mai Kyau, dariya yakeyi.

"zaki ɓalla mana Daddy fa, wannan abu haka kamar ƙaramar yarinya."
Zaynerb da suka ƙariso gurin ta faɗa hakan, Daddyn yace "abarmin shalelena ta wataya abinta, aini zanso ta karyani ma."

Nainarh tana murmushi ta ce "mu kuma ba zamuji daɗi ba, idan aka karya mana Daddynmu."



"Ya naga kamar ana wata qwarya qwaryar party, ba'a gayyacemu ba?."

Mister Mai Kyau, daya hango abubuwan maqulashe a dining, yayi maganar.


Zaynerb ta buɗe baki zata bashi amsa, da sauri Haleesat dake kusa da ita ta rufe ma ta baki da hannayenta, ganin haka yasa Lailah faɗin.


"ah dama Haleesat ce ta antaya soyayya fa, shine muka shirya wannan ƴar qwarya qwaryar partyn, domin tayata murna ta ƙarishe tana qintse dariya, ganin yadda Haleesat take antayo ma ta harara, tana raba ido kamar baiwar da tayiwa sarki ƙarya😝



"Okay shine ba'a gayyacemu ba, zakuyi ku kaɗai, to qwara da Allah yasa muka dawo yanzu sai ayi damu."

Momy Rafi'at tayi maganar tana ajiye Lab coat da jakar ta saman center table.







KANO




💘JIEDDARH💘





Daga kwancen da take a saman bed ɗinta, ta jiyo knocking sama sama, amma a yanayin gajiyar da takejin kanta, tana tunanin koma waye wannan mai knocking sai dai ya haƙura sai gobe koma miye.
Saboda baccin dake a idanunta sai dai me, jin da tayi mai buga ƙofar yaƙi haƙura, yasa ba shiri ta sauko daga saman gadon tana ya mutsa fuska alamar bacci takeji over.

Palon dake a bedroom ta fito sannan ta nufa ainihin ƙofar ɗakin ta buɗe ƙofar.

Da mamaki take kallon wacca take a bakin ƙofar, tana sakar ma ta murmushi. Ni'ima ce sanye cikin sleeping dress, dogon wando fari sai riga blue color, kanta da hula fara mai haɗe da blue.


Martanin murmushin ita ma Jiddarh ta mayar ma ta sannan ta matsa gefe, domin Ni'imar ta sama damar shigowa, shiga ciki tayi, wannan shine karonta na farko da ta shigo bedroom ɗin Jiddarh shiyasa batasan lokacin da ta saki baki tana kallon kyau da tsaruwa irinna na bedroom ɗin ba.



Wani kalar zallar kyau ne a bedroom ɗin, na nunawa a television tundaga kan fenti na ɗakin da yake ruwan grey, shikanshi wall na ɗakin ba'a ganin shi, an rufe shi da wasu haɗaɗɗun glass grey color, ga wasu frames na Jiddarh guda biyar da aka jere a jikin bangon.

Tayi kyau a hoton sosai, dama kuma itaɗin mai kyau ce, daga ɗayan gefe na bangon kuwa, wata ƴar ma daidaiciyar plasma tv ne, mai kyau da ita, gefe da wasu dogayen glass vases masu ɗauke da flowers kala kala, masu fidda wani ƙamshi na musamman.
Daga can gefen bangon kuma mirror ne, na dogon yaro wanda yake manne da Wall ɗin.
Gefen bangon kuwa shima wasu frames ne, wasu ɗauke da hoton Jiddarh ita da Humaira a cikin qanqara da alama ba'a Nigeria sukayi hoton ba, yayinda wasu kuma hotunane masu kyau.




Kallonta ta mayar a tsakiyar madaidaicin palon wanda aka kashe naira wajen tsara shi, kujerune set ɗaya suma grey nd milk color, yayinda sofa's ɗin suke grey color, su kuma cushions ɗin suke milk nd grey colors, haka zalika suma curtains na ɗakin grey nd milk color ne, hatta da Droplight na ɗakin hasken grey nd milk color suke bayar wa.
Ga kuma wasu kyawawan wind chime masu bada iska suma still grey nd milk color.



Kamar ance ta kalla can gefe aikuwa ta hango wasu haɗaɗɗun stools, na zama grey color masu faɗi an jeresu, guda huɗu tsakiya ga kuma wani Glass coffee table daga tsakiyar stools ɗin.



Daga saman wani madaidaicin table kuwa 'FISH TANK' ne ga wasu ƙanana kyawawan kifaye ciki, ruwan cikin kuwa yana bada launin sky blue ne.


Ni'ima batasan lokacin da ta koma ta zauna saman 1sieter ba, saboda kaɗuwar da tayi, da ganin palon Jiddarh.

Yes tasan mahaifin ta cikaken mai dukiya ne, wanda ba iya Nigeria kaɗai sunanshi ya zagaya ba, hadda ma ƙasashen waje, amma ita tunda take a rayuwar ta, bata taɓa ganin palon da ya tafi da imanin ta ba, irin palon Jiddarh, ya haɗu ƙarshe, idan akace haɗuwa to azo palon Jiddarh kawai magana ta ƙare🤗.




Tanan a zaune tana kuma bin ko'ina na palon da kallo gabaɗaya ta manta abin da ya kawota ɗakin, saboda tsananin kyan palon da ya kasheta, da sauran ranta a duniya😅

Jiddarh ta yaye wani curtains dake a can gefe, ta fito hannunta riƙe da mug na coffee sai faman steam yakeyi, tun lokacin da Jiddarh ta buɗewa Ni'imar ƙofa ta shiga wani ɗan korido da aka rufeshi da curtains, kai ba za ka taɓa cewa da wani abu a gurin ba, ashe wani ɗan ƙaramin kitchen ne, na dafa shayi a gurin.


Da sauri Ni'ima ta miƙe tsaye tana bin Jiddarh da kallo kamar na tsoro, bata jira komai taje ta yaye labulayen da taga Jiddarh ta fito ta ciki, sai kuma ta tsaya cak, wani mamakin yana kuma kamata wai still dai ga wani abun mamakin kuma, kitchen ne a palon daga ke ɓantaccen guri.


Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta koma ta zauna tana kallon Jiddarh ɗan murmushin yaƙe tayi ta ce "ina fatan dai ban takura miki ba?."

Jiddarh ta girgiza kai alamar a'a sannan ta bata amsa da "ko ɗaya dama bacci nakeji kuma yaƙi zuwa...Sai kuma gaki, af ga coffee fa, kar yayi sanyi, miƙa ma ta tayi, Ni'ima ta karɓa yawunta har wani tsinkewa yakeyi, batasan lokacin da ta lumshe ido ba, sanda takai coffee ɗin a baki cikin ƙanƙanin lokaci, sai ga Jiddarh da Ni'ima sun ware  suna zuba fira, dama Jiddarh gata gwanar surutu.


Ni'ima ta ce "nifa rigar da kika ɗinka ne, nazo gani kinsan lokacin da kika fito da ita, kika nunawa su Humaira bana gidan."
Jiddarh tayi murmushi tana amsa ma ta da "ai ba damuwa tana bedroom ɗi na, zoki ganta mana."

Miƙewa sukayi tare suka nufi wannan mirror na dogon yaro dake cikin bedroom ɗin, wani waje Jiddarh ta danna a jiki saiga ƙofa ta bayyana, shi kuma mirror ya matsa gefe, ita dai Ni'ima sai zare ido take tana kuma kallon ikon Allah, "wato abin mamaki baya ƙarewa a duniya, yanzu wazayyi tunanin akwai wata ƙofa anan, balle kuma har a shiga bedroom ta gurin." Ni'ima take faɗan hakan a ranta.


Shiga ciki sukayi Jiddarh a gaba, Ni'ima kuma tana binta a baya.
"oh Allah yau dai, bazan gaji da ganin abin mamaki ba ashe," Ni'ima ta kuma faɗa a zuciyarta ganin tsantsan kyau da tsari da kuma burgewa na bedroom ɗin Jiddarh ashe ma ba komai ta gani a palo ba, a nan bedroom kallo yake.


Wani haɗaɗɗen glass sif dake manne a bango, taga Jiddarh ta buɗe ta ciro wata haɗaɗɗiyar riga ta shimfiɗe ta saman mattress.


Da sauri Ni'ima ta ƙarisa tana bin rigar da kallo kamar idanunta zasu zubo ƙasa, gabaɗaya kyan rigar ya tafi da ita, don ji take kamar ta ɗauki rigar ta ruga a guje, amma ina ba damar haka, akalla takai mintuna talatin tanabin ko'ina da ina na rigar da kallo.



Kallon Jiddarh tayi bakinta na rawa wajen faɗin "Jiddarh dan Allah na roƙeki ki faɗamin a wani company kika siya wannan special princely gown ɗin, wallahi tamin zan siya ko million nawa ne, koda kuwa companyn ba'a nan ƙasar yake ba🤩."


Dariya Jiddarh tayi ta bata amsa da "haba sister Beauty matar yaya H to be, ki kwantar da hankalin ki ba'a company na siya ba, ni ce ɗinka abina da kaina."

Waro ido Ni'ima tayi waje, ba shiri ta miƙe tana kallon Jiddarh cike da zaƙuwa take cewa.

"wai dan Allah da gaske, ke ce kika haɗa wannan, ko wasa kike."
Tambaya tana nuna rigar, murmushi Jiddarh kawai tayi ta bata amsa  "of course ni ce na ɗin ka, amma nakai a kalla watanni bakwai ina ɗin kawa idan ban manta ba."


Ni'ima ta ce "a gaskiya Jiddarh bazan ɓoye miki ba, kinyi ƙoƙari sosai sosai, wannan zamanin dai, banga telan dazai tsaya ya ɓata lokaci har watanni bakwai domin ɗinka riga ɗaya ba, koda yake ba abin mamaki bane, tunda ɗinkin, ke zaki saka abinki."

Jiddarh tayi murmushi ta ce "haba, baki dai binkcika bane, amma ai ko telolin kowa da halin shi, ai baza'a taru a zama ɗaya ba, dole akwai na gari masu ƙoƙarin cika alkawari."


"E, wata ƙila baza'a rasa ba, amma wai meyasa bakya ɗinkin mutane ne, zafa ki sama kuɗaɗe sosai."
Dariya Jiddarh tayi sannan cikin nutsuwa ta ƙarisa wajen labule ta yaye curtains, ashe nan ma gabaɗaya wall ɗin gurin, glass ne.
Sai ga babban titin birnin Kano ya bayyana, kana ta juyo tana kallon Ni'ima da ta kuma sakin baki tana kallon ikon Allah, wato titi kuma yanzu, abin yayi fa, ba laifi tunda glass ɗin irin wanda mutumin da yake waje bazai hango komai bane, sai dai na ciki ya hango na waje.




Kafin Jiddarh ta ce wani abu, Ni'ima ta rigata da faɗin, "indai zaki dinga yi ni kuma zan dinga nemo miki customers kala kala, har saikin gaji dasu kedai kawai kice kin amince,"

Murmushi kawai Jiddarh tayi Ni'ima ta tono ma ta gurin dayake ma ta raɗaɗi, ita batasan menene matsalar ta ba, a baya can, ta fara ɗinki mutane suna kawo ma ta tanayi abu kamar wasa har sunanta ya fara zagaye gari qwararriyar tela lamba ɗaya a cewar mutane, saikuma batasan meya faru ba aka wari gari ko mutum ɗaya an dena kawo ma ta ɗinki haka kawai.

Ajiyar zuciya ta sauke tana mai amsawa da "shikenan ba damuwa zaki iya,"

Wani tsallen murna Ni'ima tayi kamar wacca aka ma ta bishara da aljanna, da sauri ta matso ta rungumo Jiddarh tana faɗin.

"nagode sosai Jiddarh thank you so much."

"Never mind, haba Aunty Beauty wannan godiya haka, ni zaki ɓallani fa."
Dariya Ni'imar tayi tana faɗin, "ai dole, yanzu kafin a samu tela irinki a wannan zamanin ai sai an tona😉


Jiddarh ta ce "to ai sai a tona ina ga za'a samu,"

Ni'ima ta ce "gaki ma ansamo, da aka tona ɗin😀

Dariya sukayi duka nan Ni'ima ta taimakawa Jiddarh sukayi fold ɗin rigar, sannan suka mayar sif, cikin ƙanƙanin lokaci saiga su suna fira kamar dama can sunsan juna.
Ita dai Jiddarh tana mamakin Ni'ima ashe ta iya surutu haka?, to meyasa da batayi, 'oho' taba kanta amsa.










ᴡᴀsʜᴇ ɢᴀʀɪ



Kamar kullum alarm clock dake a saman locker, a gefen bed ɗin ne, ya tasheta.
A hankali take buɗe dara daran kyawawan idanunta, tana mai furta addu'ar tashi daga bacci, yaye tattausar blanket ɗin da ta lulluɓa tayi sannan ta sauko daga saman mattress ɗin, tana miƙa hannu ta ɗauki ribbons da hularta dake can gefen mattress.
Saida ta tufke dogon gashinta da ribbons ɗin sannan ta saka hular ta shiga bathroom.

Wanka tayi haɗe alwala ta fito a gurguje ta saka doguwar riga da hijjab dogo sannan ta shimfiɗa sallaya a gurin da aka tanadar domin yin sallah.

Raka'atainul fajir ta farayi raka'a biyu, sannan ta jira aka kira sallan asuba, kana ta miƙe tayi, Bayan ta idar, bata miƙe daga saman sallayan ba, har sai da tayi azkhar bayan ta kammala tayi folded sallayar ta mayar ma'ajiyar ta.





Shiryawa tayi cikin wando three Quarter white color, da riga t-shirt mai garejen hannu fara, sai hula p-cap fara, sannan ta saka safa doguwa har gwiwarta ita ma fara, earpiece ta ɗauka shima fari ta maƙala a kunenta duka biyun, tayi connecting ɗinshi da wayarta, sannan ta saka wayar a trouser pocket ɗinta.
Ɗauko takalman ta trainers farare a hannayenta tayi, ta fito palon ɗakinta Club ta ɗauka /wato sandar wasar golf/.


*💋💋ʂαɾαυɳιყαɾ ƙყαυ💋💋*


*ƚԋҽ ɠʅαɱ ϙυҽҽɳ*


*☆ʂƚσɾყ & ɯɾιƚιɳɠ Ⴆყ☆*

*~ƙԋαԃҽҽʝαɾƚԋ.         ʂαႦι'υ.         ყαԋყαԋ🤙~*



{ƚԋҽ ɳαιɳαɾԋ ƙԃ}😇




*page 35&36*







Palon sama ta fito ba kowa, dama ba tayi tunanin ganin kowa ba, tunda safe ne yanzu.
Cikin sauri take taka staircases ɗin harta sauko palon ƙasa Ajiyar zuciya ta sauke, hango Humaira da tayi tsakiyar palon  ita ma cikin shigar wasan golf irinna ta.



"Good morning Humaira, hope kintashi lafiya?."

Jiddarh tayi maganar a lokacin da ta ƙariso gurin ta, murmushi Humaira tayi ta amsa da "lafiya qalau nake, fatan kema hakan.?"
Tayi maganar a yayinda suke fita daga palon. Jiddarh ta amsa ma ta, "lafiya nake garau ma."

Suna tafe suna taɓa fira har suka ƙarisa filin buga wasanni dake a can gefan gidan, ɓangaren buga wasan golf suka ƙarisa nan suka fara.
Jiddarh dayake qwararriyar ce, a ɓangaren sai cinye Humaira take ta fita sai ti.



Gefe Humaira ta koma tana sauke haki ta ce "a gaskiya yau, ba sa'a gabaɗaya sai faman cinyeni kikeyi, na hakura kawai."

Tayi maganar tana ɓalle murfin gorar ruwan ever dake a hannunta, ta kafa a baki.

Jiddarh tana dariya hadda tsalle ta ce "kiyi a hankali fa, karki qware, kuma ki gama ki nemo mana ball, don ta shige a tsananin bishiyu."

Harara Humaira ta galla ma ta ta ce "banayi, ko bakiji na ce yau ba ranar sa'ata bane?, dan haka, ja gefe kije ki Nemo ball ɗin ki da kanki."

"mutane suna bani mamaki, sai kiga idan mutum yayi wata gasa ko kuma dai, yayi rashin nasara a wani al'amari, sai kaji yana faɗin wai ranar ba ranar sa'a bane, ko nasara a gareshi, sai kace shi yake zaɓawa kanshi abin da zai faru a ƙaddararshi...A gaskiya mutane da yawa suna irin wannan kuskuren na faɗin haka wai ba ranar sa'a ba, da'ace nasara fa, yayi bazaka ji bakinshi ba, sai dai yayi gum hum."

Jiddarh ce duk takeyin wannan maganar cike da takaicin halin wasu mutanen.

Ajiyar zuciya Humaira ta sauke ta ce "a gaskiya Jiddarh you are right, saboda da yawa mutanenmu na yanzu, haka ake ba godiyar Allah sai dai kawai Allah yasa mudace. gabaɗaya su biyun suka amsa da Amin.





ᴍᴀɪ ᴋʏᴀᴜ, ғᴀᴍɪʟʏ



Zaune suke a dinning table suna karin kumallo da ya ke glass dinning  room ɗin yana ɗaukar kimanin mutane sha biyu ne, sai ya kasance Daddyn yana kujerar da take a miƙe, yayinda Momy Rafi'at ita ma take a ɗayar kujerar wacca ita ma take a miƙe saiya kasance Daddyn da Momynsuna suna fuskantar juna ne 😁.



Sannan kuma sauran kujerun ya kasance Nainarh tana daga ɓangaren hannun dama, ita kuma Nailah tana daga hannun hagu, saiya kasance suma suna kallon juna, gefan Nainarh kuwa Haleesat ce, ta ɓangaren hannun hagu, kuma Zaynerb ce suma kallon juna kenan.
Sannan kuma gefan Haleesat, Lailah ita ma suna fuskan tar juna ita da Afeefah, dake a hannun hagu sai kuma Deejarh a gefan Afeefan tana zaune ita ma.


Saiya kasance sauran kujerun dining ɗin guda uku, babu mutane wayam suke.

Daddy ya kallesu gabaɗaya, kowa ya mayar da hankali ana kai loma, yayi murmushi wani abu yana tsaya mishi a qahon zuciya, kamata yayi ace akwai yaro Namiji koda ɗaya ne, a gurin, amma haka Allah ya tsara kaddarar ta kasance.


Yana ina?, yana cikin ƙoshin lafiya, ko a kasin hakan, shin yana ma duniyar, idan ma yana raye a halin yanzu, wata kalar rayuwa yake gudanarwa, shin ya dena halayyar sa wacca ita ce sanadiyar da yasa shi barin gidan, ko kuwa bai dena ba, shin yaci abinci kuwa, shin akwai iyayen da suke kula dashi ne, shin yayi kewar Daddyn shi da Momyn shi da ƙannin shi kuwa, shin yana tunawa dasu a kullum.
Kamar yadda a  koda yaushe yake maƙale a zuciyoyin su, shin zai dawo gida kuwa, kamar yadda suke fata.

shin shin shin kalar waɗannan tambayoyin sune cike da koda yaushe a zuciyar shi, bai sani ba, amma yanaji yana da kaso tamanin cikin ɗari na halin da Babban ɗanshi, ɗaya tilo Namiji ya fa ɗa.


Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya kore tunane tunanen da suke so, su rinjayo zuciyar shi daga dogon fushin da yake a ciki, ɗago da kanshi yayi karaf suka shige cikin na sahibar Matar shi /Momy Rafi'at/ da tun lokacin da ya faɗa tunanin, take an kare dashi, dama jira take ya ɗa go da kanshi..Girgiza mishi kai tayi alamar a'a.
Murmushi ya sakar ma ta kawai, ita ma ta mayar mishi da martanin murmushin.



Kallon shi ya mayar akan ƴa ƴan shi ma ta, farin cikin ko wani uba nagari😘

Ɗan jim yayi yana ƙare musu kallo kana yace, "ni banga hoton surukin nawa ba daɗin daɗawa, kuma ba'a faɗamin koda sunan shi ba, kodai rowan shi a keyi min?."

Ya ƙarishe maganar yana kallon Haleesat, fuskar shi cike da Annuri.

Wani irin tari ne mai haɗe da qwarewa yazo ma Haleesat, aikuwa nan tahau yi ba qaqqautawa.
Da sauri Zaynerb dake fuskantarta ta miƙa ma ta ruwa a cup, tana ma ta sannu.

Karɓa tayi ta kaba a baki ta shanye tas, sai faman sannu mutanen gurin sukeyi ma ta.

Ajiyar zuciya ta sauke tana kallon Daddyn nasu da ya zuba ma ta ido yana binta da kallon tambaya.

Da sauri ta ce "Daddy!," sai kuma tayi shiru, ta rasa abin cewa, dariya Zaynerb tayi ta ce.
"Allah Daddy komai za ta ce karka yadda saita faɗa maka sunan shi, sannan kuma ta baka hoton shi, mu ma mu gani, jiya ba kalar roƙon da ban ma ta ba, akan ta faɗamin ko da sunan shi ne. Amma taƙi."

Zaynerb ta ƙarishe maganar tana jefawa Haleesat hararar wasa.





Kafin wani ya kuma cewa komai, sai ga Lailah wacca ba wanda yasan lokacin da ta bar gurin, ta dawo hannunta riƙe da doguwar paper.


Gurin Daddyn ta ƙarisa da saurinta, ta tsaya ta gefan shi, sannan ta warware paper ɗin, sai ga zanen kyawawan matashin saurayi Gentle dashi, ya bayyana.

Lailah tana dariya tana faɗin "Daddy ga hoton surukin ka, wanda ɗiyar ka Haleesat ta zana shi, jiya jiyan nan."

Ƙurawa zanen ido Mister Mai Kyau yayi, yana yima zanen kallon kamar ya san fuskar a wani guri.

Yayinda duk kallo ɗaya da zayyima zanen, sai zuciyar Haleesat ta buga da ƙarfi, tayi tsuru tsuru tana jiran tsammani, ita da ko magana ta fatar baki bai taɓa shiga tsakaninta da mutumin ba, amma aje ta zana shi, har tana nunawa su Lailah masu bakin surutu, gashi yanzu tajama kanta Daddyn ya gani.



"To ba'a faɗamin sunan shi ba, ko shima saina roƙa ne?."

Taji muryar Daddyn yana faɗar hakan, da sauri ta ɗa go kanta tana kallonsu, gaba ɗaya sun zuba ma ta ido suna kallo, don suji abin da za ta ce.

Cike da in ina ta ce "sunan shi, wai sunan shi?, ohoo sunan shi, ae sunan shi 'MAHMOUD' ne fa." Tayi maganar tana cizan laɓɓanta na ƙasa da ƙarfi.


Gaba ɗayansu basu kula da halin da take ciki ba, sai Zaynerb ita kaɗai.
Lailah ta ce "suna mai daɗi, ashe shiyasa kike mana rowar faɗa." Tayi maganar cike da zaulaya.

"Anfa takura wa yarinyata, gabaɗaya kunsa sai kunya takeji haba dai."
Cewar Momy Rafi'at tana ɗan dariya. Suma dariyar sukayi Lailah ta kuma faɗin.
"Allah Momy ba wani kunya, hadda ma miskilanci." Tayi maganar tana komawa ta zauna gurin zamanta.
Ta ci gaba da cewa "ni ina mamakin a inda Auntie Haleesat ta samo miskilanci, nasan dai Daddyn mu ba miskili bane, haka zalika Momy."

"kika sani ko'a cikin dangi ta gado?."

Nailah ta faɗa tana dariya, kallon bakusan komai ba Momy Rafi'at tayi musu, sannan ta ce, "abar kaza cikin gashinta kawai..."


Afeefah ta kalla Daddynsu ta ce "Allah Daddy ita ma Auntie Zaynerb, saita faɗa mana saurayinta, nasan dai ba za ta rasa saurayi ba, duk da ba kulasu takeyi ba..." Harara Zaynerb take ta faman jefawa Afeefah, amma tayi kamar bata gani ba, ta ci gaba da faɗin. "ina mamakin ki Auntie Zaynerb da kwata kwata bakyasan ayi miki maganar saurayi, koma aure gaba  ɗaya...Bakya kallon Momyn da Daddyn ne, gasu Auntie Nainarh da Nailah, duk gabaɗaya suna cikin farin ciki ae. soyayya da daɗi, ko ba haka bane?."

Tayi maganar fuskarta washe tana kallon su, duk ba wanda ya kulata saima  fuska da taga su Auntie Nainarh sun ɓata daga bisani ma tashi Nailah tayi ta bar gurin.
Baki sake Afeefah ta bisu da kallo, mai yayi zafi ita dai tasan iya kar gaskiyarta ta faɗa, a gurinta rayuwar aure farin ciki ne ciki gabaɗaya, a gurinta idan a kace ma'aurata, tofa anzo ƙarshen soyayya. Amma fa a nata silly tunanin😻

Ta miƙe zata bi bayanta, ta jiyo muryar Daddyn yana faɗin.

"dawo ki zauna?."

Da sauri ta kuma kallon shi, baki a sake sai tabi umarni ta koma ta zauna jiki ba gwari.






JIDDARH



"Ke kuma ina zaki da safiyar nan?."

Juyowa tayi dan ganin mai maganar, ganin su tsaye yasa ta saki fuska.
Ita batama lura da mutane ba, cikin sakin fuska ta ce "Jiddarh, Humaira kune ni?, harna ji tsoro banyi tunanin da mutane a bayana ba, sai kawai naji murya?."

Dariya Jiddarh tayi ta ce "ah mudai mun hangoki, tun daga nesa kinci kwalliya da safiyar nan, ina zakije haka?."
Ni'ima ta ce "gida zanje na dawo, daganan zan wuce gidan Auntie Nafeesah, ta ce naje na karɓo yarinyarta khausar, na kawowa wannan ƴar aikin naku, wai ita zata yaye ma ta ita."

"Badai Bilki ba?, ita Bilki ta ina ta iya wani raino, da har zatayi yaye?."

Humaira tayi maganar da mamaki. Dariya Jiddarh tayi ta ce "aikuwa zakusha mamaki indai Bilki ce, dan kuwa ta iya raino sosai.."
"oho dai koma miye ita Auntie Nafeesar tunda dai taji kuma ta yadda shikenan, mudai namu kallo ne."
Ni'ima tayi maganar tana shiga motarta tayi horn mai gadi ya buɗe ma ta gate ta fita. Bayan sunyi sallama.



Juyowa Jiddarh tayi tana murmushi ta kalla Humaira ta ce.

"kinsan wani abu kuwa?."

" a'a saikin ae faɗa.

Humaira ta bata amsa, Jiddarh ta ce "muyi tseren gudu, zuwa ƙofar palo, duk wacca ta riga zuwa, za'a bata wani abu."

Kamar mene kenan?."
Humaira ta tambaya, Jiddarh ta ce "idan na cinye ki, zaki bani wannan ƴar ƙaramar garayar taki, wato 'guitar' ah turance."

"Dube ki to india jita nane sai dai ki hakura domin kuwa bazaki taɓa samu ba." Humaira tayi maganar tana galla ma ta harara. Jiddarh ta ce "to ai sai ki tsaya na ƙarisa ko."

"Okay, inajin ki ai."

Humaira ta kuma bata amsa, Jiddarh ta ci gaba, "idan kuma kece kika cinyeni, wato kika rigani ƙarisawa, sai ki zaɓa abin da kikeso a kayana, ni kuma zan baki, ba tare da wani musu ba."
Murmushi Humaira tayi tana faɗin, "nidai wannan ƙaton frame ɗin, dake manne a bangon bedroom ɗin ki, zaki bani idan naci, don shi nakeso."
"wanne kenan?." Jiddarh ta tambayeta tana ma ta kallon 🤬.



Humaira ta ce "wannan dai mai ɗauke da hoton Babban birnin Indonesia 'JAKARTA',"
Jiddarh ta ce "kima dena sa ranki akan wannan a bun Tarihin a gurina, dan ba samu zakiyi ba,"
Humaira ta ce "to a gwada mana, a gani, ai sai da kira karen bebe yake gane gida." jiddarh ta ce to a gwadan mana."

Humaira ta fara ƙirƙe, "One Two Three Go.!"
Da gudu suka nufa ƙofar palon, nanfa aka fara daga ƙarshe dai da Jiddarh taga alamar dai, Humaira da gaske take zata wuce ta.
Ta dage iya ƙarfinta ta qwala ihu, wanda hakan yasa Humaira juyowa slowly tana kallonta, wannan juyowar da Humaira tayi, shiya ba Jiddarh damar kwasa da gudu, ta isa bakin ƙofar palon, tana sauke haki.

Ganin kalar wayon da Jiddarh ta haɗa, yasa Humaira ta sadaƙar kawai sai ta dena gudun ta tsaya ta huta, sannan ta ƙariso bakin ƙofar ta tarar da Jiddarh sai faman ihun murna takeyi, tana faɗin "nayi winning na cinye, dan haka dole a bani guitar."

Ita dai Humaira bata kulata ba, ta buɗe ƙofar ta shiga ciki, ganin haka yasa ita ma Jiddarh tabi bayanta tana faɗin ta jirata.




Suna shiga a palo suka tarar da Auntie da Abba zaune daga can gefe, suna cin breakfast a ƙasa. Da sauri Jiddarh ta ƙarisa gurin, tana faɗin.
"Abba, yau kuma anan ake karin kumallon?."
Alhaji Komai Naka, yana murmushi ya shafa kanta yace. E, Mamana, angama wasan golf ɗin kenan?."
Murmushi tayi ta ce "E, Abba, yanzu ma wanka zanje nayi,"  kallon Auntie tayi ta ce "ina kwana Auntie," fuska cike da fara'a Auntie ta amsa ma ta.
 Sannan ta ce "ai ina jira ku gama gaisawa ne, tukuna." murmushi Jiddarh tayi.
"Auntie kenan, bari na haura sama nayi wanka, na dawo akwai labari fa."
Tayi maganar tana hawa bene bedroom, ta shiga tun a palo ta fara rage kayan jikinta, tana shiga bedroom ɗin kuwa kai tsaye bathroom ta shige.



Takai tsawon mintuna talatin, sannan ta fito sanye cikin bathrobe milk color, ga wani ƙaramin towel milk tana goge sumar kanta dashi, zama tayi a kan swivel chair na dress mirror, sannan ta ɗauki hairdryer ta busar da dogon gashin kanta, kana ta ɗauki hair brush ta tace gashin, lotion ta shafa kala kala kana tayi light make up.

Ba wani sosai tayi kwalliyar ba, hoda kawai ta shafa sama sama sai kwalli da ta saka a idanunta, sai kuma lip gloss da ta shafa a saman siraran laɓɓanta.


Cikin ƙanƙanin lokaci ta shirya cikin riga da skirt na a tamfa mai launin kore da ruwan hoda, rigar tayi ma ta ɗass a jiki haka ma skirt ɗin ribbons ta ɗauka mai launin kore da ruwan hoda suma, sannan ta kamo dogon gashin kanta ta ɗaure da kyar saboda tsayin gashin, kallabi ta ɗauka babba ne sosai dan sai yafi rabin falle.


A hannunta ta riƙo kallabin ta fito palon bedroom ɗin ta, a gaban madubin dogon yaro ta tsaya, tana kici kicin ɗaura ɗan kwallin, amma ta kasa, haka dole ba yadda ta iya ta fito palon ƙasa.
Da sauri ta ƙarisa gurin su Auntie dake saman 3sieter ita da Abba suna kallon wani Indian Drama 'Bruce Lee The Fighter'.{ Na Ram Charan Da Rakul Preet Singh.} dayake ranar saturday ne ɗarshen mako ba zuwa office.


Da sauri ta ƙarisa gurin Auntie ta miƙa ma ta ɗan kwallin sannan ta ce  "Auntie ayi min taimakon muslunci, kallabi yaƙi ɗauruwa min fa 😂.


Karɓar ɗan kwalin, Auntie tayi tana mita faɗi take, "ni dai Jiddarh banga ranar da zaki girma ba, koda yaushe baki iya ɗaurin kallabi ba, haka za'ayi auren baki iya komai ba?."
Tayi maganar a yayinda take ɗaura ma ta kallabin. Dariya Jiddarh tayi ta ce.
"Auntie kenan, ana zaune lafiya, zaki kawo wani zancen aure kuma."

"au kina nufin dai bazakiyi ba, sai dai ki ƙare a nan gidan, to baki isa ba, don rana ɗaya zan haɗaku da Humaira na aurar."  Alhaji Jafar ne, yayi wannan maganar  cike da zaulaya.



Dariya kawai Jiddarh takeyi, bayan Auntie ta kammala ɗaura ma ta ɗan kwalin, ta dawo kusada Abban ta zauna a tsakiyar su, sannan tace "Abba kenan, ae  Aure lokaci ne dashi ba'ayin shi lokaci bayyi ba dole sai an jira. ka sani lokaci ɗaya wani zayyi wuff dani 😄."




"Kuma fa, kin faɗa gaskiya sister shiyasa nakeson ki, domin akwai ki da faɗin gaskiya, a koda yaushe, sannan komai rintsi."
Humaira ce tayi maganar a yayinda take saukowa downstairs hannayenta ƙiqe da wani abu ta ɓoye a baya, ita ma kalan kayan jikin Jiddarh ne a jikinta ƙarisowa palon tayi, sannan ta zagayo da hannunta dake riƙe da guitar waje.


Miƙawa Jiddarh tayi tana faɗin, "ga kyautar gasar da kika ci fa, duk da dai kinyi zamba ciki."
Da sauri Jiddarh ta karɓa tana ma ta godiya cike da farin ciki.

"keda kika ci gasar tsere, miye na min godiya, ai keya kamata ayima godiyar."
Cewar Humaira tana zama a 1sieter. "Wani ƙoƙarina ba wani ƙoƙarin da nayi, nida nayi cuta a wasar."
Jiddarh tayi maganar tana komawa ta zauna ita ma saman 2sieter, Humaira ta ce "a kullum Jiddarh ƙara burgeni kikeyi, saboda akwai ki da faɗin gaskiya.

Alhaji Jafar yace "ai haka a keso koda yaushe mutum ya kasance mai faɗar gaskiya a rayuwar sa🤳.




ƚԋҽ ɠʅαɱ ϙυҽҽɳ

                 Ⴆყ

💅тнє ɳαιɳαɾԋ ƙԃ💅





𝚖𝚒𝚜𝚊𝚕𝚒𝚗 𝚔𝚊𝚛𝚏𝚎 𝚝𝚊𝚔𝚠𝚊𝚜 𝚍𝚊 𝚛𝚊𝚋𝚒 𝚗𝚊 𝚍𝚊𝚛𝚎

Afeefah tana zaune a palo saman doguwar kujera mai mazaunin mutum ɗaya.
Hannunta riƙe da Alqur'ani mai girma, tana karatawa cikin zazzaƙar muryarta.
Yayinda Deejarh dasu Lailah suke zazzauna a sauran kujerun suma alqur'ani mai girma ne, a hannunsu suna tilawa a kalla sunkai mintuna talatin sunayi, kafin suka idar a tare sannan Afeefah tabi duk ta karɓa alqur'anan dake a hannayensu, ta mayar ma da kowa bedroom ɗinshi, sannan ta dawo suka ci gaba da fira.

Suna cikin yi saiga Mister Mai Kyau, da Mrs Mai Kyau, sun shigo palon a tare, da alama daga ɓangaren Daddyn suke.

Guri suka samu suma suka zauna a saman 3sieter ganin haka yasa su Zaynerb suka koma ƙasa suma suka zazzauna, sai ya kasance Daddyn da Momy Rafi'at suna daga saman kujera su kuma.
Nainarh, Nailah, Haleesat, Zaynerb, Afeefah, Lailah sai Deejarh suna daga ƙasa cikin girmamawa suka gaisar dasu suka amsa cike da kulawa.

Daddy da yake cikaken ɗan boko ne, na bugawa a mujalla, gashi kuma mai dukiya lamba ɗaya akaf faɗin Nigeria. Ga kuma Momy Rafi'at ita ma cikakkiyar likata ce, wacca take da hospital nata na ƙashin kanta a garin Abuja, ga ilimin boko da ya ratsata ciki da wajen ta.


Kallon su Daddyn yayi yana murmushi, sannan ya mayar da kallonshi akan Afeefah.

"Shalelen Daddynta."
Ya kirata dq sunan da yafi yawan kiranta dashi, tana murmushi ta amsa da, "na'am Daddyna,"

Daddyn yace

"Tomorrow is championship day, toh a halin yanzu ya ya kike jin kanki?."

"Cike da farin ciki Afeefah ta ce "ai Daddyn ina faɗamaka, jina nake a sama, sai naji kamar gari ya waye na buɗe ido, na ganni a filin gasar, jina nake a sama can ƙololuwa fa."

Da sauri Deejarh ta ce "shine kuma muke ganin ki anan, kuma naji kince jinki kike a sama?."


Dariya sukayi gaba ɗaya Lailah ta ce "Deejarh kenan idan mutum yace yana jinshi a sama, yana nufin bazai iya bayyana irin farin cikin da yake ciki ba. Misali idan wani abu na farin ciki ya sameshi kuma sayya kasance wannan abun yana da muhimmanci sosai a gurin shi, toh ina fata dai kin fahimta?."

Dariya Deejarh tayi tana cewa, "sosai ma, Auntie Lailah nima jina nake a sama fa."

"Saboda me?,"

Nainarh ta tambaya, Deejarh ta ce "saboda gobe Balarabiyar India zataje gasar sᴀʀᴀᴜɴɪʏᴀʀ ᴋʏᴀᴜ😆.


Dariya suka kuma yi, nan dai suka ci gaba da fira sosai, basu suka tsagaita ba, har sai da Daddyn ya du ba, wristwatch ɗin dake manne a tsintsiyar hannun shi, yaga lokaci yaja da yawa sannan yace, a tashi domin a  kwanta, sannan sukayi wa juna sallama ko wacce ta shige bedroom ɗinta.





AF££FAH



Tana shiga bedroom ɗin ta wanda ya gaji da haɗuwa, kai tsaye bathroom ta shige a kalla takai fifty minutes tana wankan sannan ta ɗauro alwala ta fito sanye da bathrobe light blue.

saman stool na dress mirror ta zauna, tana goge sumar kanta mai yawa da kuma tsayi santsi game da taushi ga wani ƙamshi na musamman da yake fitarwa, da wani farin ƙaramin towel, dake hannunta takai minti goma tana kuma gyara gashin, sannan ta shafa lotion sama sama a fatarta mai taushi da santsi har wani shaining takeyi da glowing, saida ta kammala shafa lotion ɗin, sannan ta saka lip gloss a red lips ɗinta...


https://chat.whatsapp.com/FlMq3Ol15mlBd3nRTr9c1t





*💋💋SARAUNIYAR🎀KYAU💋💋*

______________________________________________________________________💥👑𝑻𝒉𝒆 𝑮𝒍𝒂𝒎 𝐐𝐮𝐞𝐞𝐧👑💥____________________𝑩𝒚:𝑻𝒉𝒆 𝑵𝒂𝒊𝒏𝒂𝒓𝒉 𝑲𝒅____𝑲𝒉𝒂𝒅𝒆𝒆𝒋𝒂𝒓𝒕𝒉.  𝑺𝒂𝒃𝒊'𝒖.  𝒀𝒂𝒉𝒚𝒂𝒉🤙


☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆
💦𝑳𝒂𝒇𝒂𝒛𝒊 𝑾𝒓𝒊𝒕𝒕𝒆𝒓'𝒔 𝑨𝒔𝒔𝒐𝒄𝒊𝒂𝒕𝒊𝒐𝒏💦🤙

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆





*Page 37&38*







Wardrobe ta buɗe ta ciro sleeping dress, shiryawa tayi cikin vest red color, sai kuma wando crazy iya gwiwa red color, ribbons red colors ta ɗauko ta tufke gashinta. Bayan ta gama ta saka hula ita ma red color.

Saman bed ta koma ta kwanta cike da zumuɗi pillow ta rungumo a chest ɗinta, ta kwantar da kanta saman mattress, bacci takeso yazo ya saceta, kodan gobe ta farka da wuri amma ina baccin yaƙi zuwa.

Ganin baccin yaƙi zuwa yasa ta janyo wayar dake gefe, ta shiga £nglish stories ta fara karanta wani english novel TH£ KING AND HIS HAWK.




Labarin yana nishadantar da ita sosai, har lokaci yaja bata sani ba, sai da taji ta fara gyan gyaɗi sannan ta haƙura ta mayar da wayar a ma'ajiyar ta, kana ta janyo blanket ta lulluɓa addu'a tayi kana ta safe jikinta tabi lafiyar bed😎








Gaba ɗaya gurin haske ne, na fararen drop light's, tafiya take sanye cikin farar doguwar riga, kanta ba hula dogon gashin kanta ya zubo ta gaba da bayanta.
Daga can nesa ta hango wasu ƙofofi guda biyu, ƙofar farko haske ne da ita kamar yadda wajen yake cike da haske na ban mamaki.
Yayinda ƙofa ta biyu duhu ne da ita sosai. Tsayawa tayi cak ta rasa waca ƙofa zatabi daga ta cikin ƙofa ta biyu mai duhu

Ta hango hannayen mace, da alama taimako take nema, da sauri ta ƙarisa gurin. Domin ta taimakawa matar.

Sai kuma ta tsaya cak a gaban matar tana bin ta da kallon tsoro, fuskar matar ta kalla.
zaro fararen idanunta tayi cike da tsoron ganin ba kowace ke neman taimakon ba, fa ce Haleesat, yayinda daga cikin ƙofar mai duhun gaske wata mata sanye cikin baƙaƙen kaya, ba ka ganin fuskar ta saboda duhun gurin, ta dake sai janyo Haleesat take ciki da ƙarfi.

Yayinda Haleesat taƙi yadda, ita kuma matar taƙi hakura kuka Haleesat take tana miƙo ma ta hannu alamar ta taimaketa, ita kuma saboda tsoro ta kasa komai, da ƙarfi taji wata murya a ta bayanta tana ma ta magana.

A sanyaye ta juya tana kallon matar dake sanye cikin fararen kaya fuskar ta a lulluɓe da mayafi, matar faɗi take "ki taimaki ƴar uwanki, idan ba haka ba waccan azzalumar zata cutar da ita kamar yadda takeso ta cutar dake, ki taimakawa ƴar uwanki, karki baki wancan muguwar matar ta cutar da ita kamar yadda ya cutar dani."

tana gama faɗin haka ta ɓace ɓatt, a firgice ta fara waige waige cikin gurin mai haske amma sama ko ƙasa bataga wannan matar da tayi maganar ba.
Da wata iriyar jarumta ta juya ta fara janyo hannun Haleesat tana ƙoƙarin fitar da ita daga cikin baƙin ɗakin da wannan matar takeso ta shigar ciki.

Amma ta kasa wata kalar jar wuta matar dake a cikin baƙin ɗakin ta jefo ma ta, da sauri ta kauce, wannan kaucewar da tayi shiya ba matar damar tura Haleesat da take kuka kamar ranta zai fita cikin wannan baƙin ɗakin take ƙofar ta rufe ruf matar da Haleesat suna ciki.


A firgice kuma a gigice ta farka daga baccin da ya ɗauke ta har tayi wannan mummunar mafarkin, gaba ɗaya tabi ta haɗa uban zufa, ba abin da take furtawa a bakinta sai, "a'uzu billahi mina shaytanirrajeem."

Saukowa tayi daga saman mattress ɗin agogon bedroom ɗin ta kalla, ƙarfe uku da rabi na dare, hularta ta ɗauka a saman gadon sannan ta shiga bathroom, bakinta ɗauke da addu'a, gaban sink ta tsaya tana sauke haki.

A gaggauce ta ɗauro alwala sannan ta fito, sallaya ta shimfaɗa tayi sallah raka'a huɗu, kana tayi sallama, ta daɗe akan sallayar tana addu'o'i har taka kira sallar asuba, sai da tayi sannan ta miƙe ta ninke sallayar bayan tayi azkhar ta mayar ma'ajiyar ta.

Bathroom ta shiga akalla takai one hour tana wanka sannan ta fito sanye cikin bathrobe, knocking taji daga ƙofa sai da ta saka hijjabi dogo sannan ta nufa ƙofar ta buɗe.

Murmushi tayi ganin Deejarh sanye cikin doguwar rigar atamfa ta saka hijjab blue iya gwiwarta, hanya ta bata ta shigo bedroom ɗin, zama tayi saman wata kujera na karatu sannan ta ce.
"Balarabiyar India ta ina kwana kuma da yaushe za'a tafi ne dan na ƙosa sosai sosai?."

Afeefah ta ce "ae tuni na ɗauka kin fara hankali, ashe ashe ba haka bane, to yanzu wanne kikeso na amsa miki daga cikin tambayoyin da kike faman antayomin hunm?."


Dariya tayi ta ce "duka nake so ki bani amsar su,"

"ashe dai har yanzu da sauran Deejarh."

Cewar Afeefah tana murmushi, Deejarh ta kuma faɗin "amma dai Balarabiyar India yau ba za ki shiga kitchen ba, ko?,"

"Saboda me fa?."

Afeefah ta tambaya, Deejarh ta ce "saboda yau Babbar rana ce....Yauwa baki faɗamin ko ƙarfe nawa za'aje ba."

Afeefah tana dafe goshi alamar gajiya da surutu ta ce "misalin ƙarfe tara zamu tafi, za'a fara ƙarfe goma sannan a kammala karfe sha ɗaya mu dawo gida sha biyu."

Deejarh tana murmushi ta ce "kuma fa wannan tsarin yayi highly highly na miki na Anty Lailash."

Ƙin kulata Afeefah tayi saima closet da ta nufa ta shirya cikin rigar Abaya dark green sannan ta ɗaure igiyar rigar ta baya, mayafin tayi rolling dashi akanta.

Agogon ta kalla ƙarfe takwas dai dai na safe, zaro ido tayi waje ganin lokaci ya tafi.

Deejarth ta ce "idan ma tunanin shiga kitchen kikeyi sai dai kiyi haƙuri, dan tuni mun kammala komai, nida su Auntie Nainarh."
Juyowa Afeefah tayi ta ce "ni banma san lokaci yaja haka ba, wallahi.."
Tayi maganar a yayinda suke fita daga bedroom ɗin, a dining area suka hango duka ƴan gidan, suna karin kumallo ƙarisawa sukayi suka zauna Afeefah ta gaisar da Daddyn da Momy Rafi'at sannan suka fara cin breakfast ɗinsu.







**


Misalin ƙarfe tara dai dai na safiyar ranar litina, gaba ɗaya Ahalin Mai Kyau suna tsaitsaye a parking lot tun daga kan Uban gayyar Abubakar Mai Kyau, da matar tashi Momy Rafi'at Mrs Mai Kyau, Auntie Nainarh, Auntie Nailah, Haleesat, Zaynerb, Afeefah, Lailah sai kuma Deejarh dukansu matan sanye cikin Arabian gown dark green yayinda mayafin su yake fari takalman su ma iri ɗaya fancy ballerina, ko wacce da bag ɗinta na gayu a hannu, hadda Momy Rafi'at sunyi kyau sosai, dama gasu Ahalin Mai Kyau, Daddyn kuma sanye cikin suit blue black.


Kallon Lailah Deejarh tayi sannan ta ce "Auntie Lailah nifa ban gane wani abu ba, zan iya tambaya kuwa, domin anyimin ƙarin bayani?."

Murmushi Lailah tayi ta ce "Menene baki gane ba, mai bakin tambaya?."

"ah kinga laifinta, batta kawai tayi tambayarta, san ranta, domin ma tambayi baya ɓata." cewar Auntie Nainarh.

Deejarh ta kuma cewa "dama tambayar ita ce, naga Balarabiyar India batayi shigar gasar ba, naga ita ma kalar kayan jikin mu shine a jikinta?."

Zaynerb ce ta bata amsa da faɗin, "Deejarh kenan to ki bari muje can zakisha mamaki ai ba'a nan zata shirya ba, sai anje can, domin abin akwai tsaruka bawai kara zube akeyi ba."

"ohoo ai sai yanzu na fahimta dama haka ne." cewar Deejarh bakinta a sake cike da ƙauyanci.

Gaba ɗayansu suka nufi motocin suka shiga Auntie Nainarh da Zaynerb da Lailah a mota ɗaya, sai kuma Auntie Nailah da Haleesat sai Deejarh a mota ɗaya, Mrs Mai Kyau, Mister Mai Kyau, Afeefah a mota ɗaya.

Gaba ɗaya motocin sun kama guda uku masu kyau da tsadar gaske na nunawa a B.B.C, tun kafin su ƙarisa bakin gate mai gadi ya wangale musu wagameman gate ɗin gidan suka fita a tare.












 
💞WOND£RFUL_HALL_ABUJA_CITY💞









Qaton gurin taron ya tsaru sosai, tsaruwa iya tsaruwa yanayin tsarin haɗuwa da zanen gurin dai shine, da farko dai ga wasu kujeru irin na zaman ƴan kallo mutane ne zazzaune akai suna fuskan tar floor ɗin wanda, masu gasa (SHOW) zasu dinga fitowa ta ciki suna tsayawa akai daga sama kuma can gefe Alƙalan gasa ne mata turawa biyu sai kuma baƙaƙen fata biyu suma zazzaune saman kujerun alfarma, daga saman floor na gasar kuwa wata kyakyawar budurwa ce wacca akalla ba zata wuce shekara talatin da biyar ba wato dai mai gabatar wa (Introducing Lady).

Hallau kuma daga can gefe masu ɗaukar hoto ne wato (Photographers), gefan su kuwa ƴan jarida ne maza da mata gaba ɗaya sun saita abubuwan ɗauka (camera) suna jira lokaci ya cika a fara kafta wasan gasar SARAUNIYAR KYAU (The Fashion Show).


Daga first kujerun gurin na zaman ma ta kuwa su Lailah da Zaynerb da Momy da Haleesat sai Auntie Nainarh, da Auntie Nailah sai kuma Deejarh sune a first chairs na gurin da suke daga ɓangaren hagu, ɓangaren dama kuma maza ne.

Akalla gaba ɗaya mutanen gurin zasu kai su ɗari biyar gaba ɗaya hadda alƙalan gasar da kuma sauran jama'a dake a gurin.



Duk wucewar sakan ɗaya sai Zaynerb ta kalla agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunta, baiwar Allah gaba ɗaya ta ƙosa a fara, haka ma sauran jama'an gurin.

Wata wawiyar ajiyar zuciya ta sauke a lokacin da ƙarfe goma ta cika dai dai kuma a dai dai lokacin baturiyar budurwar dake saman floor na gasar take faɗi cikin harshen turanci.


"A halin yanzu lokaci ya cika dan haka ba tare da ɓata lokaci ba za'a fara kafta gasar Allah yaba mai rabo sa'a. Daga ni taku SANDRA nake muku fatan alkhairi kuji daɗin kallon FASHION SHOW, lafiya..!"

Tana gama faɗar hakan ta sauka daga wajen ta koma, saman wata hamshaƙiyar kujera na alfarma ta zauna.

Gaba ɗayan su mutane da ƴan kallo kowa da kowa na gurin suka mayar da hankulan su a ta saman floor na gurin suna jira suga shahararriyar da zata fara fitowa. Toh nima dai 𝑵𝒂𝒊𝒏𝒂𝒓𝒉 𝒌𝒅 da nake ɗauko muku rahoto juyawa nayi aslowly domin naba kyawawan idanunta haƙƙin su😎


Sanu a hankali dogayen labulayen launin jajaye na gurin mai haɗe da fari suke yin sama a hankali, tohm kamar yadda curtains ɗin suke launin ja da fari haka sauran abubuwan gurin suke ja da fari hatta da tiles na saman gurin shima red color nd White color ne.



In slow motion curtains ɗin sukayi sama a take salon bugun zuciyoyin mutanen gurin ya canza😂

Saboda tsananin kyan kyayawar hallitar da ta bayyana, kyakyawar budurwa ce kyakyawar gaske na bugawa a jarida sanye cikin wasu arnayen kaya na Allah tsine uwar mai ƙarya a kyau, budurwar akalla ba za ta haura shekaru ashirin ba a duniya, cikin taku irinna wacca tasha training na salon tafiya, take taku tana juya jiki abin dai sai an gani, oh Allah wannan budurwa ta haɗu qwarai sai da ƙariso dai dai tsakiyar filin sannan ta juya ta kuma juyowa, taba masu ɗaukar hoto damar ɗaukarta da kyau, aikuwa nan suka shiga yi ma ta ba qaqqautawa bakajin ƙarar komai a gurin sai ƙarar flash flash minti biyar dai dai tayi sannan ta juya ta koma ta wajen da ta shigo bayan wasu sakanni.



Saiga wata kyakyawar matashiyar budurwar ita ma dai wacca shekarunta ta ba za su haura ashirin da biyu zuwa da uku ba, still ita ma dai cikin shigar kece raini ga gashinta nan yasha gyara ba'a magana.
Ita ma dai sai da tayi minti biyar sannan ta koma sai gata uku ta fito ita ma.


A hankali Zaynerb ta koma ta kwantar da bayanta a jikin kujerar da take zaune. Kallon ta Deejarh tayi dama kujerun su neighbors na junane ta ce "Auntie Zaynerb nifa harna fara gundura har yanzu Balarabiyar India bata fito ba, gashi har biyu sunyi ta uku ma ta fito fa."

Murmushi Zaynerb tayi ta ce "Deejarh kenan kamar yadda kika ƙosa ta fito nima dai na ƙosa, wata ƙilama nafiki ƙoss...!!


Sauran maganar bakinta ne ya tsaya cak kamar yadda tunaninta ya tafi hutun wani lokaci saboda tsananin ruɗewar da tayi na ganin wacca ta fito.
Deejarh ganin tana yima Zaynerb magana ne amma hankalinta baya akanta, yasa ita ma ta mayar da kallonta inda Zaynerb ɗin take kalla, ba shiri ta murza idanunta ta buɗe domin gasgata abin da take gani, wani ihun murna ta saki tana miƙewa tsaye har batasan lokacin da ta fara whistle (fito)  ba, da bakinta saboda tsananin farin ciki game da zumuɗi.




 

 ❤𝔞𝔣𝔢𝔢𝔣𝔞𝔥❤
    
    
    
Sanye take cikin wata kalar shiga wanda kafin kaga mai irin shigar akalla sai ga cike files dubu a kwanaki dubu lokaci dubu komai dubu😜

Wayyo Allah yau nake ganin kyau (Huh The Fashion Show) masu karatu ina ma kunanan a gurin nan sannan kuma a dai dai wannan lokaci da kunga kyau iya kyau da gaske Afeefah kyakyawace cikin kyawawa ku yarda da hakan💃😍




Sanye take cikin dresses gown wanda kai tsaye da Pink Fairy za'a kira dresses ɗin da take cikin😎


Gown ɗin mai hannun vest doguwa har ƙasa ga wasu butterfly ta bayan masu launin rigar sky purple, haka ma waɗannan butterfly ɗin na baya.

Brown wavy gashinta kuwa wanda ya zubo ma ta har mazaunai an ɗauroshi da wasu flowers sky purple wanda hakan ba ƙaramin kyau da burgewa ya ƙarawa gashin ba👸


Hannayenta cikin wasu kyawawan handgloves sky purple suma, sannan ga kyawawan ƙafafunta cikin wasu arnun tsadaddun takalma Glam Boots sky purple masu tsini ga wani shaining da sukeyi humnm👄💥👄



Ga kuma wasu Beautifuls bracelet (munduwa💍) sky purple a hannayenta duka biyun.

Kyawawan idanunta kuwa cikin wani haɗaɗɗen fancy sunglasses sky purple💞



Hallau ga wata beautiful fashion hand bag (Jakar hannu) a hannunta na dama. Ita ma kanta jakar hannun nata sky purple ne ga wasu stones kyawawa da aka ƙawata ƴar ƙaramar jakar dasu.

Wuyanta (Neck) kuwa wata haɗaɗɗiyar Diamond necklace chain ne, doguwa wacca ta sauko har ƙasan chest ɗin ta, Sarƙar mai launin sky purple.


Haka zalika earrings ɗin dake maƙale a kunneta duka biyun kalar sarƙanne sky purple, daga yatsarta na hannun hagu kuwa wani haɗaɗɗen diamond ring ne, na zamani.

Fuskar ta kuwa wa'iya zubilla kyau kenan Natural beauty fuskarta tasha make up abin ba'a magana hatta blush on na fuskar ta sky purple ne.


💋COME ON GUYS💋


𝔄𝔣𝔢𝔢𝔣𝔞𝔥𝔯𝔪𝔲 𝔣𝔞

Tayi kyau so cute. Tayi kyau so sassy so steady so sexy so mature so chic so perfect so casual nd so normal so so so much over💔❤💔

Ta fito as a Natural beautiful Afeefah Mai kyau ɗinta. Gata Afeefah Mai Kyau, ɗiyar Mai Kyau, Jikar Kyawawa, Jinin Turawa da Larabawa game da kannuri da hausa fulani duka 💄💃💄



Taku take irinna cikakkiyar wayayyar ƴar gayu (The Glamouristlelly 👄💋👄)...... fuskar ta a Washe take tana ɗagawa mutane (Fan's ɗinta) hannu kamar yadda suma suke ma ta bakajin komai a gurin sai ihun murnar da mutane maza da mata sukeyi. Toh ata can gefe kuma ga alƙalan gasa (Championship Leader's👀✨)....Ɗayan gefan kuwa manyan ƴan jarida ne, da masu ɗaukar hoto suke aikin su.


Sai da ta ƙarisa dai dai tsakiyar filin tsayuwar sannan ta tsaya a memakon tayi juyi da rairaye rairaye game da malƙwashe malƙwashe da dai sauran abubuwa, kamar yadda sauran sukayi ita nata salon tayi daban sumba (Kiss💋👄💋) ta watso wa mutane tana dariyar da ta bayyana kyawawan fararen haƙoranta...
Idan akace kyau a farko, tofah ana zuwa kan Afeefah Ɗiyar Mister Mai Kyau, an rufe ƙofa ita ɗin  kyakyawa ce na first class, a ko'ina ta gama haɗuwa ni dai (Ɗiyar Mutanen Kd💃) nayi shiru a gefe ina zare ido da kallon zallar kyau.


Wani ƙayataccen abu tayi wanda ya daɗa burge mutane, hannu tasa a cikin ƴar ƙaramar tsadaddiyar jakar dake a hannunta ta ciro tsaleliyar wayarta wacca akalla ba'a kasara ba zatakai Ten million's naira a kuɗin Nigeria, camera ta shiga ta juya ta ɗauka selfie tare da mutanen da suke akan kujeru sannan ta kumayiwa kanta ita kaɗai sai da takai tsawo mintuna biyar ɗinta dai dai, sannan ta juya zata koma aikuwa nan gurin yayi tsit kamar mutuwa ta gifta da alama mutane basu so ta koma a yanzu ba, sai da takai dai dai wajen da zata koma ciki sannan ta juyo ta kuma watso musu sumba sannan ta shige ciki, cike da farin ciki bayan wasu sakanni sai ga wata ma ta fito.


Haka aka din gi yi idan wannan ta zo taci mintuna biyar ɗinta sai ta koma wata ma tazo taci mintuna biyar ɗinta a haka har mutane goma sukayi dama kuma su goma ne chas chass Ƴan Tawagar Gasar na Abuja.








Sai da cikon ta gomar ta koma sannan, Sandra ta dawo ta tsaya a tsakiyar floor ɗin, yanzu ma cikin harshen turanci ta fara magana kamar hakan👇


"Hi Hello Welcome Namaste (Da ya ke ita ɗin haifaffiyar Indiyace shiyasa yaren ta na TELUGU ya zauna a bakinta).. Barkanku dai masu kallo muna fatan wannan gasar na 𝔖𝔞𝔯𝔞𝔲𝔫𝔦𝔶𝔞𝔯 𝔎𝔶𝔞𝔲 𝑚𝑎𝑡𝑎𝑘𝑖𝑛 𝐽𝑎ℎ𝑎,  tana burgeku da nishaɗantar da ku yadda ya kamata?."


Mutane gaba ɗaya aka amsa, sannan ta ci gaba da cewa "a halin yanzu duka ƴan matan gasa zasu fiffito a tare, ko waccensu ta tsaya a tsakiyar floor kamar yadda aka saba duk shekara, daganan kuma alƙalan gasa su fidda gwana zaqwaqwura ma'ana dai wacca ta sama nasarar (win) lashe wannan gasar na bana wato SARAUNIYAR KYAU💅





Ihu game da sowa na murnar maganarta mutane suka kuma saki maza da mata abin sai wanda ya gani.
Bayan wani lokaci gurin ya kuma yin tsit kamar ba wata hallita mai motsi a gurin, Sandra ta fara da ''one, two, three.!!"


Kafin ta rufe baki saiga ƴan matan su goma rhass sun fito a tare sun tsai tsaya a tsakiyar filin gasar.

Nan fa guri ya kuma tsit mutane ana jira aji hukuncin alƙalan ƙasa.





Akalla an  kwashe sama da mintuna goma a haka sannan wata Kyakyawar Baturiya daga cikin alƙalan gasan ta miƙe tsaye  cikin shigarta na tsadaddun suit na mata kuma na alƙalan fashion show, da alama ita ce chairlady, sannan ne kuma ɗayar baƙar fatar dake a kusada ita, ita ma ta miƙe tsaye ɗaukar abin magana (Micro Tone) baƙar fatar tayi sannan ta fara magana cikin harshen hausa, yawancin maganar nata akan dai gasan ne sai kuma ɗan flirting (Barkwanci) da take sakawa a zancen nata, daga ƙarshe dai ta rufe da faɗin.




"yanzu dai, bari na barku haka na koma mazaunina domin na bawa. Ƴar uwa Mrs William damar bayyana mana wacece zaqwaqwurar da tayi nasara a gasar SARAUNIYAR KYAU na bana😍




Dariya akayi sannan ta koma ta zauna..
Nan wannan Baturiyar ta ɗauki abin maganar sannan ta fara da nuna murnar ta akan gasar da dai sauran su, sannan ɗaura da faɗin.


"dai dai wannan lokacin zamu bayyana muku zaqwaqwurar wacca taci wannan gasar na SARAUNIYAR KYAU matakin jaha. Wannan Shahararriyar zaqwaqwurar dai  ita ce! ita ce!! ita ce...!!"

Shiru tayi tana kallon mutane fuskar ta cike da murmushi kamar yadda zuciyoyin ƴan matan gasa take bugu da ƙarfi, haka ma zuciyoyin ƴan kallo maza da mata har dama ƙananan yara, zuciyoyin suke bugun wuce ƙima, hatta sauran mutane na duniya daga kan masu kallo a t.v show, da masu wayoyin hannu da dai sauransu, gaba ɗaya jira ake aji ko wacece tayi nasara ta zamo zaqwaqwurar shekara, {☆ nima dai ƚԋҽ Nαιɳαɾԋ ƙԃ da nake gefe nayi tsuru tsuru zuciyata bugu take na wuce ƙima saboda tsoro💔®}





Murmushi Mrs William tayi ta kuma kallon doguwar paper ɗin dake a hannunta, sannan ta ɗago kanta, ta kuma kallon duka kyawawan ƴan matan gasa waɗanda duka suma idanunsu yake akanta, amma banda Afeefah da tayi kamar batasan a halin da ake ciki ba, saima magana ta ido da takeyi ita da Zaynerb sai faman murmushi suke sakarwa juna.





Gyaran murya Mrs William tayi sannan ta kuma gyara zaman medical glass ɗin dake a fuskarta, sannan ta ce.
"ba kowa bace wacca taji gasar SARAUNIYAR KYAU matakin jaha ma'ana tazo ta ɗaya kuma zaqwaqwurarmu fa ce 'MISS F££FAH MAI KYAU..." [dayake shine real name na ta a gasar😘].



Wani irin ihun murna gaba ɗaya mutanen gurin suka saka hadda masu fito (whistle) da masu rawa (dance) Deejarh saman kujerar da take kai ta hau tana faɗin.

"Kai yasin sai Balarabiyar India, Huh Huh ta zama SARAUNIYAR KYAU ta jaha Allah ya kaimu na ƙasa ma, yaƙini nake dashi akan cewa ita ce zata cinye huh hu oh sai Balarabiyar India😛."

Haka kawai Deejarh take faɗa cike da farin ciki, wayyo masu karatu kuzo kuga murna a wajen su Auntie Nainarh, Auntie Nailah, Haleesat, Zaynerb, Lailah abin ba'a iya cewa komai Mrs Mai Kyau kuwa komai faƙonka baka isa kace ga abin da ke a zuciyarta ba, ta dage tana taya murna😆






 

💋SARAUNIYA  F££FA  MAI  KYAU💋


Kuwa wani irin rumshe idanunta tayi da ƙarfi, tana sauke ajiyar zuciya sam ko'a a tunani batayi tunanin zataci wannan gasar ba, tun daga lokacin da ta ɗaura idonta akan kyawawan ƴan matan gasan, a gaskiya wannan ranar ta zama ranar tunawa a rayuwar ta, ba za ta taɓa manta wannan ranar mai cike da tahiri a gurin ta ba, har abada. Habba ai abin akwai farin ciki kalan wanda alƙalami bazai iya rubutawa ba SARAUNIYAR KYAU fa ta jaha aiko anan kasuwa ta tashi ɗan koli yaci riba ba kaɗan ba. [sai dai mu zamu so kasuwa ta cigaba da ci domin sanin mai zai faru gaba, anan dai ga Afeefah taci gasan to ita Jieddarh fa😃]…





A hankali ta buɗe kyawawan idanunta waɗanda suka kawo ruwa saboda tsananin farin ciki, jin da tayi ana nemanta domin a bata kyauta, "au dama hadda wata kyauta ne, da za'a bada?." Ta tambaya kanta, sai kuma taba kanta amsa da "gashi kuma ana kirana nazo karɓa😇."



Sannu a hankali take taku yayinda zata ƙarisa gurin Sandra wajen karɓar kyauta, cikin takun jan aji da nutsuwa irinnata ta ƙarisa gurin sai da suka gaisa da Sandra, sannan Sandra ta ɗauko wani secret box wanda aka nannaɗeshi da wasu kyawawan igiyoyi na flowers ta miƙa ma ta, sannan kuma ta miƙa mata wani haɗaɗɗen fure mai fidda sassanyan ƙamshi na musamman. Afeefah harta juya zata tafi, Sandra ta ce

"bakiji ba."

Juyowa tayi tana kallonta fuskar ta cike da fara'a ta ce "ina jinki." Sandra ta ce "am very so sorry amma please zamu iya hoto a tare?."
Tayi maganar tana marairaicewa duk a tunanin ta Afeefah ba za ta yadda ba, sai kuma ta bata mamaki da cewa "ba damuwa zamu iya."

Murmushi Sandra tayi sannan ta ciro tsadaddiyar wayar ta a aljihun dogon crazy jeans ɗin dake a jikinta suka kafta selfie kala biyar da Afeefah sannan ta juya tana nunawa mutane kyautar da ta samu sannan ta koma gurin ta cike da farin ciki, sai dai wani ɓangare na zuciyarta bugu yake na rashin dalili, tun lokacin da magana ta haɗa ta da Sandra.





Mrs william tayi gyaran murya sai da ta jira mutane aka nutsu kowa ya koma ya zauna a mazaunin shi, sannan ta ce "malama Feefah Mai Kyau, gaba ɗayan mu alƙalan gasan muna tayaki murnar cin gasar SARAUNIYAR KYAU matakin jaha, muna fatan zamu haɗu a gasar SARAUNIYAR KYAU matakin ƙasa nan da one month ko?."

Ƙayataccen murmushi Afeefah  tayi daga gurin da take tsaye ta ɗaga kanta alamar 'E,👏💪💃







Mrs william tayi murmushi sannan ta ce "haka nakeson ji." sannan ta kuma nutsuwa ta ce "yanzu kuma zamu ji wacca tazo ta biyu."
Ƙara kallon doguwar paper ɗin dake a hannunta ta kumayi sannan tayi murmushi tana mai cewa.

"ba kowa ce wacca taci gasar SARAUNIYAR KYAU na jaha tazo ta biyu ma'ana dai zaqwaqwurar mu ta biya fa ce 'SAMEEHAH SALIS MAI NAIRA'...


Ihun murna masoyan Sameeha suka saka suna tayata murna, a hankali kyakyawar matashiyar budurwar da ba za ta wuce shekaru ashirin da haihuwa ba, take taku cike da farin ciki ta ƙarisa wajen Sandra suka gaisa, sannan ita ma aka bata kyautar secret box wanda aka rufeshi da igiyoyi, amma bai kai girman na Afeefah ba, sannan sukayi pictures kala biyar ita da Sandra kana ta juya tana nunawa mutane cike da farin ciki, sannan ta koma matsayarta ta tsaya kusada Afeefah murmushi Afeefah tayi ta ce cikin ƙasa da murya.

"Hi ina tayaki murna sosai, sannan naji daɗin haɗuwa dake highly."

Murmushi ita ma Sameeha tayi sannan ta ce "me too dear Feefah Mai Kyau." Dariya sukayi a tare.


Bayan gurin yayi tsit Mrs William ta kumayin gyaran murya sannan ta ce "malama Sameeha Salis Mai Naira, muna tayaki murnar zuwa ta biyu a gasar SARAUNIYAR KYAU na jaha."

"I really Appreciate highly Madam William." cewar Sameeha cike da farin ciki.💞


*💋💋𝑆𝐴𝑅𝐴𝑈𝑁𝐼𝑌𝐴𝑅 𝐾𝑌𝐴𝑈💋💋*


*👑𝑇ℎ𝑒 𝐺𝑙𝑎𝑚 𝑄𝑢𝑒𝑒𝑛👑*



*𝑊𝑟𝑖𝑡𝑖𝑛𝑔 & 𝑆𝑡𝑜𝑟𝑦 𝐵𝑦*

*𝐾ℎ𝑎𝑑𝑒𝑒𝑗𝑎𝑟𝑡ℎ 𝑆𝑎𝑏𝑖`𝑢 𝑌𝑎ℎ𝑦𝑎ℎ*



{♥︎𝑇ℎ𝑒 𝑁𝑎𝑖𝑛𝑎𝑟ℎ 𝑘𝑑♥︎}





💘*𝘓𝘈𝘍𝘈𝘡𝘐 𝘞𝘙𝘐𝘛𝘛𝘌𝘙𝘚 𝘈𝘚𝘚𝘖𝘊𝘐𝘈𝘛𝘐𝘖𝘕*💘🤙

<><><><><><><><><><><><><><<><><><><><><><>><><><><><><><

/𝐓𝐡𝐢𝐬 𝐏𝐚𝐠𝐞 𝐈𝐬 𝐃𝐞𝐝𝐢𝐜𝐚𝐭𝐞𝐝 𝐓𝐨 𝐙𝐢𝐞𝐞𝐲 𝐌𝐮𝐜𝐡 𝐋𝐨𝐯𝐞🥰/


💄The Fashion Show💄




*Page 39&40*






"Zaqwaqwurar mu ta uku, kuma ta ƙarshe a wannan gasar na SARAUNIYAR KYAU matakin Jaha, ba kowa bace fa ce ABHI GAIL ELIAS, so that, muna gayyatar miss Abhi Gail, izuwa saman floor, domin ta karɓa gift nata na mussaman kuwa."



Da takun ƙasaita take tafiyar kyakyawar budurwa har ƙarisa gurin Sandra, sannan ta tsaya fuskar ta cike da annuri.
Haɗaɗɗen Diamond ring da chain ɗin shi suna shaining da ƙalli, Sandra ta miƙa ma ta tana mai tayata murna, cike da murna Abhi Gail ta karɓa gift ɗin sannan sukayi pictures kala biyu da Sandra kana ta koma ta tsaya kusada su Afeefah da Sameeha.  (💋ZAQWAQWURAN MU💋)





Mrs William ta ci gaba da faɗin "munataya ku murna sosai kyawawan ƴan matan da suka sama nasara a wannan gasar, hakama sauran da basu sama nasara ba, muna tayasu jaje, sannan ku sakama ranku shekara mai zagayo daku za'yi."


Nan ta ɗan basu baki da tausasan kalamai. Dan kuwa babu daɗi mutum ya shiga gasa ko waca kala ce, ace bayyi nasara ba.

Tana kammalawa ta koma ta zauna, sannan ɗayar Baturiyar ita ma ta miƙe tayi taƙaitattun maganganu.


Sannan ita ma baƙar fatar cikon ta huɗun su, ta miƙe ta ɗanyi ƙarin bayani daga ƙarshe ta rufe da faɗin "muna yiwa kowa da kowa duka waɗanda suka halarci wannan special gasar muna godiya sannan kuma muna fatan kowa zai koma gidajensu lafiya kamar yadda kukazo lafiya."


Tana gama faɗin haka ta koma ta zauna daga haka taron gasar SARAUNIYAR KYAU matakin jaha ta shekarar yazo ƙarshe, daganan mutane suka fara tashi ana watse wa, daga ɓangaren ƴan matan gasa kuwa, suma komawa sukayi ta gurin da suka shigo sannan jajayen labulayen gurin suka koma da kansu su haɗe.






💗Ahalin Mai Kyau💗





Tsaye suke gaba ɗaya a gurin da sukayi parking tsadaddun motocin su, daga harabar Hall ɗin na taron, suna jiran ƙarisowar Daddyn da kuma Sarauniyar wato Afeefah 😍



Lailah ta ce "a gaskiya wannan gasar ta ƙayatar dani sosai, da ace ina da account na Tik Tok ko kuma Facebook da Instragram dana ɗaura ɗaukar, saboda abin ya tafi yadda nakeso, especially ma da Afeefah tayi NASARA a gasar ga Kalar dressing ɗin da tayi ya tafi da mutane highly."


Zaynerb ta amshe da cewa "aha ƴar uwa, ai Lailah ina faɗamiki abin yayi yadda ya kamata Allah ya kaimu Gasar na matakin ƙasa, akwai ɗaukar SHOW kuwa, huh wayaga Afeefah Mai Kyau As Sarauniyar Kyau ta ƙasa huh The Glam Queen."

"Ina da tambaya, wai shin a'ina ne, za'ayi na ƙasa ɗinne, naji wannan Baturiyar ta ce 'nanda one month' amma bata faɗa ko'a ina za'ayi ba."




Deejarh tana dariya tayi musu tambayar, Lailah ta bata amsa da, "inaga a Lagos za'ayi, nanda wata ɗayar kamar yadda kikaji ta faɗa, muna fatan shima na matakin ƙasa ɗin ƴar uwanmu Afeefan mu ta lashe gasa."



Wani ihun murna Zaynerb ta saki da ƙarfi, a lokacin da ta duba wayarta taga abin da ke faruwa ciki faɗa take "muje zuwa Guys, aha ai yanzu aka fara gasar akwai na matakin Ƙasa yana nan tafe, ku saka ranku a inuwa."  Ta ƙarishe faɗar hakan tana tsalle abin ta Like a Little Kid.😎









Har rige rigen ƙarisawa gurin ta sukeyi domin ganin abin da ke cikin wayar nata da ya sakata ihun murna a cikin mutane haka.

Tsakanin Haleesat, Lailah Deejarh.
Haleesat ce ta rigasu ƙarisawa don haka, wani cafka takaima wayar dake a hannun Zaynerb ɗin, saiga wayar a hannunta da sauri tayi unlocked na wayar tana dubawa, lokacin Lailah da Deejarh suma sun ƙariso gurin Lailah cikin haki abin ka da ba'a saba ba 😅



Cikin Tik Tok Account na Zaynerb ɗin, ta tsinci wayar, da sauri ta shiga duba videos na Show ɗin da Zaynerb ta ɗaura a  Tik Tok Account ɗin nata, videos ne kala kala kusan kala goma. Na farko daga ciki ta shiga ta fara dubawa, cikin ƴan mintunan da Zaynerb ta saka Videos ɗin, har ta sama Likers kusan mutune fiye da dubu ɗari, ga ruwan Comments kala kala kusan na mutane dubu goma, Kai bama iyaka ƴan Najeriya ba kowa yaba wannan gasar SARAUNIYAR KYAU na garin Abuja yake kowa da abin da yake faɗa akai.💃💃







Kakkaurar ajiyar zuciya Haleesat ta sauke ta ce "A gaskiya wannan Fashion Show, Championship ya karɓu a gurin mutane sosai, duba fa, ki kalla yadda mutane maza da mata suke zuba ruwan like da comments kala kala a wannan videon."
Tayi maganar tana ƙarisawa gurin Momy Rafi'at ta miƙa ma ta wayar Zaynerb ɗin.
Da sauri Momyn ta karɓa wayar kamar mai jira ai nan take tahau washe baki tana yabawa.

Ita dai Zaynerb tana daga gefe tana kallon ikon Allah sannan kuma idan angama a bata wayarta.😂


"Kema Auntie Haleesat ina ce kin saka a Instagram Account ɗin ki ko?, ki duba mana domin muga halin da ake ciki."


Lailah ce tayi maganar cike da zaƙuwa game da farin ciki. Da sauri Haleesat ta saka hannunta a cikin handbag ɗinta ta ciro wayarta da ya ke babu Password kai tsaye Instagram ɗin ta ta shiga bayanta kunna Data.



Zaro ido tayi waje ganin uban likes da comments da take samu suna shigowa babu qaqqautawa. Dalilin ganin yadda Haleesat ta kasa magana ne gaba ɗaya,  yasa Lailah ta karɓa wayar tana dubawa. Murmushi tayi ganin ashe anan Instagram manyan qwarin suke likes ne da comments kawai ake zubowa ta wayar Haleesat kamar kamar me.
Shiga tayi cikin wani Video akalla likes ɗin da Video ɗin ya samu sunkai one million a iya tunanin ta fa.😎




Ɗagowa tayi cike da farin ciki zatayi magana ta hango Afeefah da Daddyn suna tahowa Afeefah sanye cikin kayan Gasar amma yanzu ta saka mayafi fari tayi rolling kanta dashi sai dai ta cire Fancy Glass ɗin fuskar ta.


Da sauri Lailah ta ƙarisa suka rumgumo juna da Afeefah cike da farin ciki, bayan sun gama Deejarh da ta ƙariso ita ma tayi hug ɗin Afeefah tana faɗin   "Balarabiyar Indiata ina ta ya ki murna sosai sosai, sannan ina cikin farin ciki mara adadi fa"

Murmushi Afeefah tayi sannan ta ce "Ina godiya sosai nima Deejarh tawa Allah ya bar ƙauna mara adadi tsakanin mu."

Mister Mai Kyau ya ce cike da zolaya "Yanzu dai a barmin Shalele taje ta shiga mota driver yaja mu tafi gida, sannan ayi taya murnar a gida can ina ga zaifi. Dariya sukayi sannan babu musu suka ɗun guma cikin motocin su cike da farin ciki sai gida.









KANO





HUMAIRA



Humaira zaune suke a ƙaton wajen gunadanar da gasar SARAUNIYAR KYAU matakin jahar Kano, wanda ya sama hallatar manyan mutane maza da mata da ƙananan yara hadda ma Larabawa da Turawa da kowa da mutane, gurin ya haɗu sosai sosai. Especially ma saman floor ɗin gaba ɗaya launin komai na gurin sky blue and White color ne,  jama'a ƴan kallo gaba ɗaya an nutsu ana jira a fara gunadar da Gasa. Daga gefe gasu Photographers nan birjik,  ga ƴan gidan T.V nan, ƴan jarida ne da sauransu ana sai ta camerori ana jira lokaci ya cika da.


Daga ɗayan gefan kuwa Alƙalan Gasar ne kamar yadda aka saba mutane huɗu Baƙaƙen fata biyu, sai Baturiya ɗaya sai kuma wata Kyakyawar Balarabiya suna zaune saman wasu haɗaɗɗun kujeru irinna zaman manyan mata masu jida kansu, ga wasu uban littafai da papers a gaban kowannensu, mutane an cika gurin ba masa tsinke gurin yayi tsit ana jira lokaci ya cika a fara kafta Gasa.






MISALIN ƘARF£ GOMA SHA ƊAYA DAI DAI...






Humaira suna zaune a first chairs na gurin ita da Ni'ima dake a gefanta na hagu sai kuma Auntie Mrs Komai Naka, daga gefan dama, sai su Auntie Nafeesa da su Na'ima.

Gaba ɗayansu sun bada hankulansu suna jira suga kyakyawar da zata fara fitowa. ah domin kuwa taron na kyawawa ne.



TOHM


Ta wani dogon korido wata haɗaɗɗiya kuma kyakyawar budurwa ta fito tana takun gayu, tana sanye cikin shigarta na Gasar tayi kyau harta gaji da yin kyau ɗin, duk taku ɗaya da zatayi sai ta tsaya masu ɗaukar hoto sunyi ma ta sannan...



Da sauri Humaira ta ciro tsadaddiyar wayarta a jakarta, ta fara ɗaukar Video ana gudanar da Gasar, ita kuma tana ɗaukar duk wacca tazo sai ta ma ta Video idan ta koma  kafin wata tazo sai tayi saving ɗin Videon a wayarta, idan wata ta fito ita ma ta ma ta nata ɗaukar daban.




TOFAH


Gasa ta fara ɗaukar ɗumi fa, a domin kuwa ƴan matan Gasar biyar har sun fito saura biyar kenan.

Gaba ɗaya gurin ya kuma yin shiru ana jira budurwa ta shida ta fito. domin ganin nata salon kyawun😘




WOW


Daga ganin irin shigar Princely Dresses ɗin da take ciki sai ka rantse ƴar sarkin ETHIOPIA ce, saboda tsananin kyau irin kyawun da tayi.
Tayi irin kyan nan na bugawa a kowani irin takarda da kuma bayyanawa game da nunawa a  gidan talabijin na duk duniya.
Irin kyawun nan wanda samari suke poster su dinga liqawa a unguwa unguwa fa, tayi kyau as Diamond.



So Casual and Perfect take cikin wata arniyar Gown sky Blue irinna ƴa ƴan sarauta. Har ƙasa rigar ta sauka ma ta.
Pastel twist hair ɗinta lulluɓe da wata kalar mayafi sky Blue mai adon stones,  fuskarta tasha make-up abin sai wanda ya gani, hannayenta cikin wasu handgloves sky Blue irinna Princely Princess, hannunta na dama riƙe da wata ƴar siririyar sanda mai launin sky Blue and purple color, shima dai irinna na yaran sarauta, kai idan nace zan tsaya lissafo kalar kyan da tayi sai a kwana ba'a kai ko rabi ba, saboda haka just kuyi imagine kawai guys 🥳



Kyawawan ƙafafunta kuwa cikin wani haɗaɗɗen Crystal Princess Heels mai shaining, launin shi white and blue color, ga kyawawan idanunta masu launin Ash color cikin wani arnen glass no respect mai launin sky Blue.


Tafiya take a dogon koridon Hall na Gasar har ta ƙariso tsakiyar floor ɗin. So Casual and Perfect Jiddarh ta gama haɗuwa tako ina abin dai hmm hummm sai mai iya imagine,  gata kyawun ta Natural ne babu ƙarin na kanti ko kaɗan fa.


Fuskar ta cike da fara'a take kuma taku mai cike da salo na musamman, tunda Jiddarh ta fito gurin ya ɗauki ihun murna anga kyau kamar a wanke hannu sannan a taɓa.



Daga ɗayan ɓangaren kuwa gaba ɗaya Photographer's sun tattare hankulansu guri ɗaya suna ɗaukar hoton Jiddarh domin takai a ɗauketa hoton, harta wuce matsayin tuni.
Sai da tayi mintuna biyar dai dai sannan ta koma ciki, wata ta fito haka abin ya dingi tafiya har akazo kan ta goma kuma ta ƙarshe wacca daga ita shikenan Bye Bye Gasa😊


Ita ma dai ta haɗu babu ƙarya sam z tsarin, sai da ta goma tayi five minutes kamar sauran ta koma, bayan mintuna goma ansamu dai gurin yayi tsit sannan...





Miƙewa ɗaya daga cikin Alƙalan Gasar tayi tana magana cikin harshen Turanci magana take akan yadda su duka suka nuna farin cikin su akan hallatar Gasar da mutane sukayi sannan suka bada gudun mawa wajen ganin Gasar ya tafi yadda ya kamata, kana ta gangaro da maganar nata akan ƴan matan Gasa, ta ɗanyi bayani a taikace sannan ta bada dama duka ƴan matan Gasar su goma suka hallara a tsakiyar gurin Gasar.






Madam Miracle ta ci gaba da cewa "A halin yanzu zamu ji kuma mugani sannan musan wacca ta sama nasarar lashe wannan Gasar ma'ana dai tazo ta ɗaya."

Tayi maganar tana duba wata white paper doguwa dake a hannunta na dama tayi murmushi sannan!.

Ta ci gaba da faɗin "Ya kamata mu taya Malama Jiddarth Komai Naka, murnar lashe wannan Gasar na SARAUNIYAR KYAU matakin jaha...Dan haka cikin girmamawa muna gayyatar Malama Jiddarth izuwa saman floor domin ta karɓa gift ɗinta na musamman da ta cancanci samu."

Ta ƙarishe maganar a yayinda take kallon kyakyawar Diamond Lady ɗin da sunanta yake a matsayin Jiddarth har cikin zuciyarta ta yaba da kyawu da komai na Jiddarh, don ita Jiddarh  ake kira one in Dollars bama
 million ba eheee . 🤗😁












🎀J££DD@RH🎀



Fuskarta kawai idan mutum ya kalla zai fahimci tana cikin farin ciki ba ɗan ƙarami ba, farin ciki irin wanda mutum baimasan taya zai bayyana shi ba.
Tafiya take cikin nutsuwa a yayinda zata ƙarisa ta karɓa gift a matsayinta na wacca ta lashe Gasar SARAUNIYAR KYAU matakin jaha. A garin Kano Najeriya.

Sannu a hankali take tafiyar yayinda duk taku ɗaya da zatayi sai kaji ƙarar Crystal Princess heels ɗin dake a kyawawan ƙafafunta.




Ɗoss,  Ɗoɗɗos, Ɗas, Ɗas.


Haka sautin yake bayarwa, gaba ɗaya gurin yayi tsit hankulan mutanen gurin gaba ɗaya  yana akanta.






Qarisawa tayi saman floor ɗin sannan taja ta tsaya a gaban Madam Miracle, murmushi Madam Miracle tayi sannan ta ɗauko wani haɗaɗɗen box Blue color an nanɗeshi da wasu kyawawan igiyoyi Yellow color and other's ta miƙa ma ta tana faɗi cikin ƙasa da murya.


"Malama Jiddarth ina tayaki murnar lashe wannan Gasar ina fatan zamu haɗu a gasar SARAUNIYAR KYAU matakin ƙasa?."


Washe fuska Jiddarh tayi sannan ta ce.

 "In Allah ya yarda."


Ta faɗa hakan a lokacin da Madam Miracle ta miƙa ma ta box ɗin, harta juya zata koma, Madam Miracle ta ce


"Baki ji ba,"

 
Juyowa Jiddarh tayi tana kallon ta, murmushi Madam Miracle ta kumayi sannan ta miƙawa Jiddarh wani haɗaɗɗen Diamond Ring ta ce "Wannan dagani ne, na baki kyauta saboda kyanki kawai." 😃




Ihun mutane da sowa gurin ya kuma ɗauka kamar kamar mene.
Dariya kawai Jiddarh takeyi a lokacin da Madam Miracle ta kammala zura ma ta Diamond ring a yatsarta na Ƙarshen hannun damar ta, godiya tayiwa Madam sannan ta juya tana nunawa mutane gift ɗinta da kuma tsadadden Diamond ring ɗin bayan komai ya lafa ta koma ta tsaya a gurin ta.





Haka aka ci gaba da kiran sunayen ƴan matan Gasa har aka zo kan ta uku, aka bata kyautarta sannan ta dawo kusa dasu Jiddarh da budurwar da tayi ta biyu ta tsaya.



Madam Miracle ta ci gaba da jawabi cike da qwarewa da sanin takan abin, ana cikin haka ana shirin tufe taron kenan wata kyakyawar matashiyar budurwa daga cikin sauran ƴan matan Gasan bakwai ta zube a gurin a sume.






Da sauri wata kyakyawar budurwa daga cikin ƴan kallo ta hau saman gurin tana kiran sunan budurwar da ta suma da alama budurwar Ƴar uwanta ce, duk yadda akaso wannan budurwa ta farka daga suman da tayi abu ya cutura, haka aka kwasheta ranga ranga zuwa asibiti.
Daga haka kuma taron dai ya tashi jikin kowa yayi sanyi laqwas.












Da gudu Jiddarh ta ƙarisa wajen su Humaira da suke tsaye curko curko a harabar Hall ɗin taron, bata damu da tarin mutanen dake kallonta da ɗaukar Video da kuma hotunan ta ba.

Rungumo Humaira da Auntie tayi a tare tana dariya.
"Oh Allah wai ke Jiddarh bakya girma ne?, ai wannan sai ki karyani fa." Cewar Auntie tana dariya.

Dariya Jiddarh takeyi ta ce "Auntie na ina farin ciki da murna yau, kawai dan ma abin da ya faru yanzu ya ɗan sanyaya min jiki ne, don da alama yarinyar ta gaza jure rashin nasara ne shiyasa harta suma ko?."

Humaira ta ce "E, gaskiya abin akwai taɓa zuciya wata ƙila tayiwa Gasar dogon buri ne, sai kuma Allah yasa ba ita zata sama Nasara ba, sai ita kuma ta saka jure hakan ta sume."


"Koma miye matsalar ta can taje taji dashi ba damuwar ku bane, kuji da abin da yake a gaban ku yarana."

Cewar Auntie tana ya mutsa fuska. Da tsananin mamaki su biyun suke kallon ta jin abin da ta ce Jiddarh mamaki ya hanata magana, sai Humaira ce tayi ƙarfin halin cewa.

"Auntie wai mane naji kina faɗane?,  mutum ce fa ita, kuma mace dole zataji babu daɗi kinsan zuciyoyin mu ma ta akwai rauni."


Ɗan dafe goshi Auntie tayi tana cizan harshenta ganin tayi sakin layi a gabansu.😳


"Auntie dake fa nakeyi, kin min shiru?." Humaira ta faɗa a hasale tana fitar da numfar fashin ɓacin rai.

Gane yanayin da Humaira ta shiga ne yasa Auntie saurin kamo hannunta tana faɗin.
"Am so sorry my Dear, it's all my fault, na yadda bai kamata nayi wannan maganar ba. Amma ki yafeni kuskuren baki ne."


Da ƙarfi Humaira ta qwace hannunta daga cikin na Auntie, ta buɗe mota a fusace ta shiga ciki.
Ajiyar zuciya kawai Auntie take saukewa cike da tsaban tsoro, kamo hannunta Jiddarh tayi idanunta sun cicciko tab da qwalla ta ce "Dan Allah Auntie karki saka wannan abun a ranki, saboda ke mahaifiyarta ce kinsan dai ba halinta bane raini, bata cikin hayyacinta ne shiyasa.

Ɗan murmushi Auntie tayi sannan ta ce "Ba komai Jiddarh na sani gaskiyarta ne duka laifina ne, da banyi wannan maganar ba, da ranta bai ɓaci ba, har waɗannan mutanen su leƙo kuma a fusace."

Magana Auntie takeyi tana leƙen motar da Jumaira take ciki.

Hakan da tayi da kuma maganar da tayi duka ba ƙaramin dariya taso ta ba Jiddarh ba. Amma ta danne ta ce "Auntie wai ina su Sister Ni'ima ne suzo mutafi gida, lokaci yana ƙurewa fa, naji da wannan ɗaukar Video da hotunan da ake min."

Murmushi Auntie tayi ta ce "Su Ni'ima akwai gurin da zasu biya, ki shiga mota kawai mu tafi gida zamu haɗu dasu acan.



"To" Jiddarh ta ce sannan ta nufa motar da Humaira take ciki. Da sauri Auntie ta ce "A'a Jiddarh inaga kizo wannan motar da nake mu tafi tare naga kamar mutanen basu koma ba."

Qumshe dariya Jiddarh tayi tana rufe baki ta ce "A'a Auntie barni na shiga wannan kawai, ai sun sanni Abokai nane, babh abin da zasumin fa domin mun saba."

Tayi maganar tana buɗe motar zata shiga, Auntie ta ce

"Ni dai ba ruwa na, Jiddarh tunda kince wannan motar zaki shiga su waɗannan mutanen ba ruwan su da wata Abota ko ƴan uwan taka uban mutum zasuci da gayya." 😝



Dariya Jiddarh tayi sannan ta shige motar ta zauna gefan Humaira dake waya abin ta. Daga ɓangaren hannun hagu ta zauna sannan driver yaja suka fita daga gate ɗin gurin motocin nasu guda huɗu rass, sannan suka ɗauki hanyar gida ɗoɗar.






A hanya Jiddarh ta ɗan kalla Humaira sai kuma da sauri ta kauda kanta tana karanto duk addu'ar da tazo bakinta,  ƙara kallon Humaira tayi a zuciyarta ta ce "Wata ƙila sun koma."

Ɗan taɓo kafaɗun Humaira tayi cike da tsoro, wani irin juyowa Humaira tayi gaba ɗayanta tana kallon Jiddarh da idanunta waɗanda suka canza kala izuwa dark maroon.





Wani irin fitsarin tsoro ne yazo ma Jiddarh amma ta maƙale shi tana zare ido, so take tayi ihu koda driver zaiji ya tsayar da Motar kota samu ta tsere, amma ta kasa daga ta buɗe baki sai taji kamar an mayar dashi da ƙarfi an rufe.  Ba abin da takeyi sai zufa ƙoƙari take tayi hawaye koda zasuji tausayinta. amma mandaƙas idanunta suke ko ɗan qwalla babu.





Matsawa jikin murfin mota take yayinda Humaira take biyota kamar wata 😘.


Wata dabara ce ya faɗo ma ta da sauri ta lalubo wayarta, a cikin jakarta dake a hannunta, cikin rawar hannu ta lalubo lambar Humaira ta danna kira.


Kai tsaye kiran ya shigo wayar Humaira dake saman cinyarta sautin zazzaƙar muryar Ahmad Sulaiman yana karanto suratul Ma'ida ya karaɗe motar.



Firgigit Humaira ta dawo hayyacinta, wata wawiyar ajiyar zuciya Jiddarh ta sauke sannan tayi rejected kiran, kallon Humaira tayi tana murmushin yaƙe ta ce "Uhm sannu Humaira kin farka daga baccin kenan.?"



Ya mutsa fuska Humaira tayi  tana faɗin "Wai ya akayi ma na ganni a mota ba'a tsaye muke ba munajiran ƙarisowar Ni'ima.?"


Da sauri cikin sarƙewar murya Jieddarh ta ce "E, e mana kwarai, ai a tsaye muke sai kikace muzo mu tafi gida bacci kikeji, wannan ne abin da ya faru fa."


Qura ma ta ido Humaira tayi tana kallonta sannan ta ce "Ya naga kina inda inda kodai ƙishi kikeji ne.?"

Da sauri Jiddarh ta fara tari kamar da gaske tana faɗin "Ruwa, a bani ruwa please, dai dai lokacin da driver ya shiga da motar gidan.




Fitowa tayi daga motar tana riƙe baki kamar mai jin ƙishin da gaske da sauri Auntie ta ƙariso gurin tana tambayar ba'asi.

Cike da damuwa Humaira ta ce "Wai ƙishi takeji shiyasa take tari fa."

Kallon Jiddarh Auntie tayi zatayi magana Jiddarh ta kashe ma ta ido ɗaya, tuni Auntie ta ramfo abin da take nufi. Dan haka kallon Humaira tayi ta ce "mu shiga ciki ko."




Da gudu Jiddarh ta taye sama bayan sun shiga palon saboda sauri in twin's take taka staircases ɗin hannunta na rawa tasa key ta buɗe Bedroom ɗin ta.




Da ido Auntie da Humaira suka bita da kallo Sannan Auntie ta dawo da kallonta kan Humaira cike da tuhuma ta ce "Menene ya faru a mota naga kamar bata cikin nutsuwar ta.?"


Fuskarta da alamar Rashin jindaɗi Humaira ta ce "Nima dai bansan abin da ya faru ba, farkawa kawai nayi na tsinci kaina a cikin mota driver yana tuƙi ga Jiddarh a gefena, shi ne na tambaye ta abin da ya faru tahau inda inda, bayan na tambaye ta ko qishi takeji sai ta hau tari ba ƙaƙƙautawa."
Humaira tayi maganar tana zama a two sieter.

"To Allah ya kyauta gaba."

Cewar Auntie a lokacin da tayi picking call ɗin da ya shigo wayarta, sannan tayi hanyar kitchen tana magana.
Da ido Humaira ta bita sai kuma ta taɓe baki tana gyara kwanciyar a saman kujerar da take akai.





Jiddarh kuwa tana shiga haɗaɗɗen palon ta wanda ya gaji da haɗuwa, jifa tayi da handbag ɗinta saman kujera sannan ta ɗauki ruwan roba a fridge tasha, kana ta dawo ta zauna akan kujera tana kici kicin rage kayan jikinta.



 
Sai da ta kammala cire doguwar gown ɗin jikinta sannan ta miƙe ta shige Bedroom a saman bed ta aje gown ɗin sannan ta shiga bathroom.
Sai da ta kwashe mintuna Ashirin tana wanka kana ta fito ɗaure da towel White color a chest ɗinta.



Gaban Dress Mirror ta tsaya tana kallon kanta tayi murmushi afili ta ce "Saini Jiddarth ɗiyar Ahalin Komai Naga, yau na cinye Gasar SARAUNIYAR KYAU matakin jaha saura na ƙasa, ina fatan kamar yadda na lashe wannan shima na lashe shi." 😎


Sai tayi shiru da sauri ta ɗauki red jam baki ta buɗe, sannan ta zizara a saman jajayen laɓɓanta kana ta mayar da jam bakin saman Dress Mirror.

Kallon kanta ta kuma a madubi washe baki tayi a fili ta kuma cewa "Amazing Masha Allah sai ni Jiddarh kuma fa wallahi ina da kyau  sosai. Ya Allah wannan baiwar ta ka Jiddarh tana godiya da wannan hallitar da aka ma ta bada wayonta ko dabara ba."
Kwance Ribbons ɗin da ta ɗaure dogon gashin kanta tayi aikuwa gashin ya zubo ta gabanta da bayanta duk yabi ya rufe ma ta fuska.



Gefe ta matsa da gashin da ya rufe ma ta fuska, kallon kanta ta kumayi a madubi ta ce "Wash sai ni Jiddarh SARAUNIYAR KYAU a garin kano, wannan kyau haka aiko Larabawa da Turawa saina cinyesu a Gasa bansani ba."

Dariya tayi sannan ta ɗauki kwalli ta kuma zizarawa a dara daran kyawawan idanunta, bayan ta gama haka ta ci gaba da yaba kanta da kanta har sai da gaji dan kanta sannan ta hakura dan kanta.


https://chat.whatsapp.com/LUPynCNbwwKFbvnBmQ504P



*💋💋𝑆𝐴𝑅𝐴𝑈𝑁𝐼𝑌𝐴𝑅 𝐾𝑌𝐴𝑈💋💋*


*👑𝑇ℎ𝑒 𝐺𝑙𝑎𝑚 𝑄𝑢𝑒𝑒𝑛👑*



*𝑊𝑟𝑖𝑡𝑖𝑛𝑔 & 𝑆𝑡𝑜𝑟𝑦 𝐵𝑦*

*𝐾ℎ𝑎𝑑𝑒𝑒𝑗𝑎𝑟𝑡ℎ 𝑆𝑎𝑏𝑖`𝑢 𝑌𝑎ℎ𝑦𝑎ℎ*



{♥︎𝑇ℎ𝑒 𝑁𝑎𝑖𝑛𝑎𝑟ℎ 𝑘𝑑♥︎}



*_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️
───────────────────────
```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.}``` ✏️



𝐓𝐡𝐢𝐬 𝐒𝐭𝐨𝐫𝐲

_In dedication to my dear Classmate Science G.S.S.S BELE ROAD._



Page *41&42*




Shiryawa tayi cikin kayan shan iska wando jeans black color, sai riga Top mai gajeren hannu milk, sannan ta saka Ribbons milk da black ta kamo doguwar sumarta kanta ta tufke da kyar, hular bat saka akanta black color.



Palo ta fito ta ɗauki handbag ɗin ta a saman kujera sannan ta saka flat shoes black color fitowa tayi daga Bedroom ɗin, sannan ta fara taka staircases tana saukowa ƙasa.


Downstairs ta sauko can saman 2sieter ta hango Humaira tana kallon wani Nigerian Drama 'The Best Friend In The World.'

Qarisawa tayi ta zauna a saman 3sieter ita ma tana mayar da kallonta akan Tv.
Shiru sukayi gaba ɗaya suna kallon, can sai ga Auntie ta sauko Downstairs ɗin cikin shigar alfarma sai baza ƙamshi take, zama tayi a 2sieter tana kallon su gaba ɗaya da alama ba wacca tasan lokacin da ta ƙariso gurin.



Remote ta ɗauka sannan ta danna pause, gaba ɗaya su biyun suka juya suna kallonta a firgice.


Dariya Jiddarh tayi sannan ta ce "lah Auntie yaushe kika ƙariso nan bamu sani ba?."
Harara Auntie ta galla ma ta tana faɗin "To dama yaushe zakusan nazo gaba ɗaya hankulanku yana akan Tv."

Jiddarh ta ce "Allah Drama ɗin akwai kyau ne shiyasa,"

"Uhm ba wani nan, yanzu ina kyautar naki yake mugani." cewar Auntie fuska washe.


Dariya Jiddarh tayi sannan ta miƙawa Auntie jakarta tana cewa "Box ɗin yana ciki du ba mana muga abin da ke ciki."

Karɓar jakar Auntie tayi sannan ta zuge zip ɗin ta ciro ɗan box ciki.


"Wannan box ɗin da gani ba wani abun kirki bane a ciki, to wai dama haka akeyi gurin Gasar idan anyi Nasara a bada secret box?." Humaira ta tambaya.


Jiddarh ta ce "Ni ma dai bansani ba, amma wata ƙila su wannan ne salon su, sai dai hakan ya ƙayatar dani matuƙa."

Tayi maganar tana kallon box ɗin da Auntie take warware igiyoyin da aka ɗaure dashi, Humaira ta kuma cewa "Ni fa gaba ɗaya na ƙosa a buɗe domin ganin ko menene a ciki, so samu ace wannan buɗewar a gaban su Abba da Yaya Heesham dasu Ni'ima za'ayi da zaifi armashi over."


Jiddarh ta amsa da faɗin "Barsu kawai gaba ɗayansu nayi fushi dasu, har Abban sai da yaga ranar Gasar shine ya gudu Spain, shima Yaya Heesham ya bishi ko, zasu dawo su gamu dani ae." Jiddarh tayi maganar ne tsakaninta Allah tana ɗaure fuska, alamar rashin jin daɗi.


 Humaira tayi dariya zatayi magana ne, amma cak maganar ta tsaya a bakinta ganin danƙareran Diamond Wrist Watch da Auntie ta ciro daga cikin box ɗin.


Ajiye shi Auntie tayi a gefe sannan ta kuma ciro wasu haɗaɗɗun Diamond Chain and Earings da kuma Diamond Ring.


Suma dai ajiyesu a gefe tayi, kana ta kuma ciro wani Check na kuɗi.

Har rige rigen karɓan Check ɗin ake a hannun Auntie a tsakanin Humaira da Jiddarh.


Humaira ce ta riga karɓa tana dariya ta buɗe. a fili ta ce




"Two Millions Naira fa."





Tayi maganar tana kallon Jiddarh, ai ba tare da wani ɓata lokaci ba, ta rungumo Jiddarh tana faɗin "Congratulations My Dear, Jiddarh a gaskiya keɗin mai sa'a ce a cikin masu nasara a wannan rayuwar."

Sakin Jiddarh tayi sannan ta ɗauki Diamond Wrist Watch ɗin, ta riƙe a hannunta sannan ta kallesu su duka tana faɗar.
"Shin ko kunsan wannan Watch ɗin akalla ba'a kasara ba saiya kai Ten Millions, ga wannan sarƙar da kuma zobe da ƴan kunnaye kuɗaɗensu na badanne fa, dan bazai lissafu ba."

Magana take amma gaba ɗaya kamar hankalinta baya a cikin jikinta, saboda tsananin mamaki da kuma farin ciki.

Zama tayi a saman 3sieter sannan ta kalla Jiddarh dake ta faman washe baki kamar gonar auduga saboda tsananin farin ciki tama kasa magana.



Murmushi Humaira tayi sannan kuma mayar da kallonta akan Auntie da ta lula duniyar tunanin.

Zatayi magana tsadaddiyar wayarta dake gefanta tayi ƙara alamar shigowar kira, gaba ɗaya suka sauke ajiyar zuciya na dawowa hayyaci hadda ita.


Ganin bata da niyyar picking call ɗin yasa Auntie cewa.


"Ki ɗa ga mana ko dai ba kiran ki ake ba, ajiyar zuciya Humaira ta kuma saukewa a karo na bar ka tai sannan ta ɗauke kallonta daga kansu ta mayar kan wayarta dake faman sowa.


Murmushi tayi ganin Abokiyar aikinta Hameeda Sagir ce mai kiran nata, da sauri tayi picking sannan ta kara a kunenta bakinta ɗauke da sallama, daga can ɓangaren Hameeda Sagir ta fara magana.


"Ke Komai Naka Girl, aje sallamar nan a gefe kiji abin da zan faɗamiki."

"Okay inaji ai."

Humaira ta bata amsa tana saita nutsuwarta, Hameeda Sagir ta ci gaba da cewa.
"Yanzu yanzu ki kunna T.v domin sanin halin da Birnin Kano Najeriya take ciki, dan da alama baki kunna ba, kuma baki sani ba."


Da sauri Humaira ta tambayeta "Menene yake faruwa ne, a garin haka da na ji ki So Anxiety ne?"


Hameeda Sagir ta ce "Kedai kawai ki kunna T.v zaki ga komai." Da faɗar hakan tayi rejected.


Ganin yadda Humaira take bin wayar da kallo batayi magana bane yasa Jiddarh tambayar, "Lafiya kuwa Humaira meke faruwa ne, wacece ta kiraki, kuma mai ta faɗa miki."


Kallonta Humaira tayi ta ce "Hameeda Sagir ce Abokiyar aikina ta kirani."



Auntie ta ce "Oho Hameeda dai nan Neighbor ɗin mu ko, to menene ta faɗa  miki.?"

Humaira ta bata amsa da, "Cewa tayi wai na kunna T.v zanga wani abu fa."



Tun kafin ta ƙarisa Jiddarh ta ɗauki Remote Control ta kunna T.v dake a palon gaba ɗaya suka zuba ma T.v ido domin ganin abin da zai faru."




ᴀʙɪɴ ᴅᴀɪ sʜɪ ɴᴇ.
Da farko hoton Asibiti aka fara nunawa sannan kuma aka nuna wannan Shararriyar ƴar jaridar da tasan  makamar aiki, wato Hameeda Sagir.
Magana take kamar haka.



"Assalamu alaikum jama'ar duniya masu kallon mu da sauraron mu,  kamar yadda kuka sani sunana Hameeda Sagir ina tare da Abokin aikina  mai ɗaukar bidiyon abin da ke faruwa, wato Omar Uthman Gaya, yau muna tafe muku da wani rahoto ne, akan wannan dai budurwar Gasar SARAUNIYAR KYAU matakin jaha, da ta faɗi a lokacin da ake tsakiyar gudanar da Gasar SARAUNIYAR KYAU na jahar Kano, ana tsaka da Gasar."


A halin yanzu muna cikin Asibitin da aka kwantar da ita, kamar yadda kuke gani zamuji ta bakin ita wannan budurwar mai suna Juwairiya Jabir Bici.
Domin sanin dalilin da ya sa ta faɗi a tsakiyar filin Gasar a sume."


Ƴar jaridar Hameeda Sagir tayi maganar tana nufar cikin Ɗakin da aka kwantar da Juwairiya Jabir Bici yayinda mai ɗaukar bidiyo yake take ma ta baya.

Kyakyawar budurwar tana daga kwance saman Bed irinna na masu jinya jikinta sanye da kayan marasa lafiya ana ma ta ƙarin ruwa.


Zama Hameeda Sagir tayi daga gefanta sannan taba mai ɗaukar bidiyon damar mayar da na'urar ɗaukar akan Juwairiyar.


Murmushi Hameeda Sagir tayi ma Juwairiya Jabir Bici, ita ma ta mayar ma ta sannan Hameeda ta fara magana.


"Sunana Hameeda Sagir kuma niɗin ƴar jarida ce, sannan ga Abokin aikina Omar a halin yanzu wannan ɗaukar da kikaga anayi ta kai tsaye ne. Don haka Malama Juwairiya Jabir Bici zaki iya faɗa mana muda ɗumbin mutanen da suke kallo ainihin abin da ya saka kika suma a tsakiyar filin Gasar.?"

Hameeda Sagir tayi ma ta tambayar tana mayar da abin maganar dake hannunta a sai tin fuskar na Juwairiya.



Miƙewa Juwairiya tayi ta zauna da kyau, sannan tayi gyaran murya kana ta fara magana kamar haka.



"Da farko dai,
Sunana Juwairiya Jabir Bici.
Mahaifina Alhaji Jabir cikakken ɗan garin Bici ne ta jahar Kano.
Mahaifiyata kuma Asalinta ƴar Nijar ce, a maraɗi, zaman aure ya kawota Najeriya kuma Kano, mu biyar ne a gurin iyayen mu yayyina uku duka maza, sai ƙanwata mace Auta kenan, sai kuma ni.
Tunda na taso a rayuwata burina ɗaya  ☝, shine naga wata rana an wayi gari na zama SARAUNIYAR KYAU koda kuwa ta jaha ce.
Ko'a Makaranta ne aka tambaye ni abin da nakeso na zama a rayuwa sai nace burina ɗaya shine na zama SARAUNIYAR KYAU, haka ƴan class ɗin mu zasuyita min dariya, suna cewa tayaya zan zama SARAUNIYAR KYAU bayan kuma ni baƙace?.😭

A lokacin sai dai kawai nayi murmushi nace musu, ai abin ba haka yake ba, zama SARAUNIYAR KYAU, ba dole sai farar fata ba, baƙaƙen fata ma zasu iya zama."👍





Shiru tayi sannan tayi murmushi tana goge siraran hawayen da suka zubo ma ta, ta kalla Hameeda Sagir da tayi shiru tana kallonta, murmushi Juwairiya ta kuma yi sannan ta tambayeta da.



"Kinsan wani abu kuwa?."


Girgiza kai Hameeda tayi alamar a'a.
Juwairiya ta ci gaba da cewa "Akwai wani lokaci, wata rana da bazan taɓa mantawa da ita ba tsawon rayuwata, a lokacin na kammala Secondary School, ina shirin shiga University, a ranar da ta kasance Lahadi kamar yadda yake a al'adata ina zaune a palo ina abin da na saba, wato bincikar yadda ake gudanar da Gasar SARAUNIYAR KYAU. da kuma irin abuwawan da ya kamata wacca ta  shiga Gasar tayi.
A Laptop nayi nisa sosai akan abin da nakeyi, najiyo muryar Yayana abin alfarina wanda kaf gidan mu shikaɗaine yake bin bayana akan ra'ayina na zama SARAUNIYAR KYAU.

Yana qwalamin kira tun daga waje, da sauri na miƙe tsaye na fita waje gurin shi, ina tambayar shi abin da yake faruwa, a lokacin cike da farin ciki Yayana yake faɗamin abin da na daɗe ina jiran ji a rayuwata.

Cewa an saka sunana acikin jerin ƴan matan da zasu shiga Gasar SARAUNIYAR KYAU matakin jaha na shekara.

A lokacin na shiga farin ciki da zaquwa kalar wanda ban taɓa shiga ba, tsayin rayuwata haka zan zauna na dinga qwada kaya kala kala ina neman kalar da zansaka ranar Gasar.


Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya har akazo saura kwana ɗaya a gudanar da Gasar ranar ko bacci na kasa, saboda zaquwa a saman sallaya na sallah na kwana ina jira gari ya waye mutafi wajen Gasar.


Haka ma da gari ya waye ko abinci ban ci ba saboda ƙosawar da nayi.

A TUNANINA idan mutum yana da wani  buri nashi, mutanen gidansu sune first waɗanda zasu fara qarfafa mishi gwiwa akan burin shi kafin mutanen waje.

Amma ni banyi wannan sa'ar ba, domin kuwa kaf gidan mu ba mai ƙarfafa min gwiwa akan burina, sai Yayana abin alfarina shikaɗaine yake son abin da nakeso.

Babban abin da ya sanyaya min jiki a karo na farko shine.
A Ranar da zamuje Gasar ko mutum ɗaya daga cikin ƴan gidan mu babu wanda yazo domin ganin yadda Gasar zai kasance, sai Yayana shikaɗai.

Haka mukaje wajen Gasar gaba ɗaya jikina a sanyaye, sai dai kuma wani Babban abin da ya ƙara kashemin jiki shine.

A lokacin da akayi Gasar nayi rashin Nasara, domin kuwa koda ta Uku kasa zuwa nayi.
Haka muka koma gida jiki ba qwari, amma ko mutum ɗaya a gidanmu an kasa samu wanda zayyimin koda tambayar yadda Gasar ta kasance.




Sai Yayana shikaɗai a kullum yake ƙara ƙarfafamin gwiwa akan nayi hakuri akwai shekara mai zuwa, karna damu kaina domin haka rayuwar take.

Rayuwa ta ci gaba da tafiya harna shiga University na fara karatu shekara ta zagayo.
Haka wannan shekarar ma Yayana yayi ƙoƙari ya samu aka saka sunana a cikin ƴan matan Gasar.

Haka cike da farin ciki yazo yake faɗamin, sai dai wannan karon na rage zaƙuwar, dan lokacin da ya faɗamin ma ban wani nuna farin ciki na sosai ba,  kawai dai cewa nayi Allah ya kaimu lokacin.
Na cigaba da aikin da nakeyi, a lokacin sam Yayana baiji daɗin abin da nayi ba,  amma bai ce dani komai ba.
Sai washe gari ya sameni yamin nasiha sosai akan yadda da ƙaddara.

A lokacin jikina yayi sanyi sosai kuma na ƙarajin ƙaunar Yayana sosai fiye da baya, sannan fiye da komai a Duniyata gaba ɗaya 💓


Haka rayuwata ta ci gaba da tafiya har akazo ranar Gasar a ranar nida Yayana mun fito harabar gidanmu zamu shiga mota mu tafi, saiga ƙanwata ta ƙariso gurin da gudunta, gaba ɗaya muka juyo muna kallon ta, Yaya ne ya tambaye ta abin da ya sakata gudu, sai cewa tayi tanaso ta rakamu gurin Gasar ne.🙂

Umma bataso Ummanmu ta sani saboda zata hanata🙃.
Duk da jikina yayi sanyi amma haka na daure nace ma ta ta shiga mota mu tafi, haka muka tafi da ita ba tareda Ummanmu ta sani ba, muka tafi wajen Gasar."








Shiru Juwairiya ta kuma yi tana kallon Hameeda Sagir, kamar yadda ita ma Hameedar ta zuba ma ta ido tana kallo cike da tausayi.

Sai da tayi mintuna biyar a haka sannan ta sauke ajiyar zuciya ta ci gaba cewa.

"Muka ƙarisa gurin Gasa an fara gudanar da Gasar nayi Round ɗina nima cike da gwarin gwiwa irin wanda bantaɓa samun kaina a ciki ba.

Ba komai ya ƙaramin gwarin gwiwa ba sai ganin yadda ƴan uwana har uku sun zo kallon Gasa na domin kuwa ɗayan Yayan nawa yazo shima.



Anyi Gasa an gama gaba ɗayanmu ƴan matan Gasa mu goma muna daga saman floor muna jira muji waɗanda suka ci Gasar, wato sama Nasarar zama winner's na shekara.


Haka munaji aka kiran wacca tazo ta ɗaya aka kira ta biyu, haka ma aka ta uku amma ba'a kirani ba.

A lokacin kasa jurewa nayi, domin ni macece ina da rauni sosai musamman ma akan abin da nakeso, kuma na sanya a gaba.
A lokacin zuciyata tamin nauyi na gaza jurewa.
Dalilin ne yasa na zube a gurin a sume, sai farkawa nayi na ganni a gadon Asibiti, That's All."


Ta ƙarishe maganar tana kuma goge hawayen fuskarta, Hameeda Sagir harta buɗe baki zatayi magana, Juwairiya ta rigata da kuma faɗar.

"Sai dai kuma yanzu komai yazo ƙarshe na haƙura da zama SARAUNIYAR KYAU, a baya idan mutane suna cewa bazan taɓacin Gasar SARAUNIYAR KYAU ba, saboda ni baƙace bana yadda amma yau na yadda ɗari bisa ɗari 100% baƙaƙen fata basa samun Nasara a Gasa sai dai fararen fata amma yanzu na fahimci komai."



Ta rufe da faɗar

"Inayiwa sauran ƴan matan da suka sama Nasarar lashe wannan Gasar na SARAUNIYAR KYAU matakin jaha fatan Nasara.

Sannan ina taya ira irena waɗanda suka faɗi a Gasar baƙin ciki da jaje."


Tana faɗin haka tayi shiru, gaba ɗaya ɗakin ya ɗauki shiru ana kallon kallo tsakanin juna.



Can ƴar jarida Hameeda Sagir ta katse shirun da ɗakin ya ɗauka da faɗin  "Malama Juwairiya Jabir Bici nida sauran jama'ar dake kallo da sauraro muna tayaki jin babu daɗi, akan wannan al'amari kuma muna fata hakan ya zama mafi alkhairi a gareki dama sauran waɗanda suka sama failure a Gasar."


Tana gama faɗin haka ta juyo tana fuskan tar na'urar ɗaukar bidiyon, sannan ta ci gaba da cewa "Yanzu dai mutane gaba ɗaya munji dalilin da ya saka Malama Juwairiya ta faɗi a gurin Gasar daga bakinta, dama Hausawa sukace magana daga bakin mai ita tafi sugar."😋




Ta ci gaba da cewa "A halin yanzu muna jiran ƙarisowar Madam Miracle wato ɗaya daga cikin manyan alƙalan Gasar, domin muji ta bakinta akan wannan al'amari mun sama labarin yanzu yanzu tana akan hanyarta zata ƙarisowa wannan Asibiti domin duba jikin Malama Juwairiya Jabir Bici, sannan kuma ta amsa mana wasu ƴan tambayoyi."




Tana kai maganar suka turo ƙofar room ɗin suka shigo, securities ne mata guda biyu ɗirka ɗirka dasu, suka fara shigowa sai Madam Miracle sai kuma wasu matan biyu suna take ma ta baya.


Da sauri ɗan jaridar mai ɗaukar bidiyon ya mayar da na'urar akan Madam Miracle da ta zauna akan wata farar kujera kusada Juwairiya Jabir Bici tana ma ta ya jiki, cike da farin ciki Juwairiya take amsawa.



Sai da Madam Miracle ta kammala duba jikin Juwairiya Jabir Bici, sannan ta juyo da kallonta akan Hameeda Sagir ƴar jarida dake zaune a gefanta saman wata farar kujera hanunta riƙe da abin magana.




Murmushi Madam Miracle tayi sannan ta ce ma kyakyawar ƴar jaridar dake zaune a kujerar kusada ita.

"Go ahead."

Sai ta abin maganar ƴar jarida Hameeda Sagir tayi shima mai ɗaukar bidiyon ya sai ta nashi akansu, su duka ukun hadda Juwairiya Jabir Bici.


Gyaran murya ƴar jarida Hameeda Sagir tayi sannan ta kalla sai tin na'urar ɗaukar bidiyon ta ce 'Barkanku dai masu kallon mu  da sauraron mu, kamar yadda kuke gani ga Madam Miracle ta ƙariso fa."


Dawo da kallonta tayi kan Madam sannan ta ce "Barka dai Madam Miracle fatan kin ƙariso lafiya.?"

Madam ta amsa da "Yauwa barkanki dai, lafiya ƙlau."

Ƴar jarida ta ci gaba da cewa "Masha Allah, shin Madam zamu iya sanin ainihin dalilin da yasa ba'a zaɓi Malama Juwairiya Jabir Bici ba a Gasar SARAUNIYAR KYAU matakin jaha?, ko kuwa dai kamar yadda ita Malama Juwairiya ɗin ta faɗane, cewa ba'a zaɓan baƙaƙen fata sai farare?."



Murmushi Madam Miracle tayi sannan ta gyara zaman Medical glass dake fuskar ta kana ta ce "naji duka tambayoyin ki Malama Hameeda Sagir amma mudai a tsarin Gasar SARAUNIYAR KYAU na ko wani mataki ba'abin hasken fata, domin kuwa ba'akan haka aka gina Gasar ba.
Sannan da kika tambaya akan Miss Juwairiya.
Yes baƙar fatace ita. Amma ba wannan dalilin ne ya hana a zaɓeta a Gasar ba ae.'

Cikin sauri Hameeda Sagir ta kuma tambaya, "Shin Madam zamu iya sanin dalilin da ya sa ba'a zaɓeta ba kuwa."

"Of course, zaku iya sani ae, babu damuwa "

Cewar Madam Miracle.

"Babban dalilan da suka saka ba'a zaɓa Miss Juwairiya ba, guda biyu ne zuwa uku, na farko shine batada idanu😳

Ma'ana dai idanunta sunyi ƙanana da yawa wanda hakan yasa ba'a zaɓeta ba.
Na biyu kuma shine tsayinta bai kai yadda akeso ba."


Da mamaki Hameeda Sagir take kallon Madam sannan ta ce Madam bamu fahimci abin da kike nufi ba?.  Kenan dai har tsayi ana dubawa wajen Gasar. Ko ince ana buƙata ko?."

Murmushi Madam Miracle tayi kana  ta bata amsa da "Sosai ma,  ana duba tsayi.  Misali ita Juwairiya Jabir Bici, it's her Height is _1.49m take, kinga kuwa babu  yadda za'ayi tayi Nasara."

Hameeda Sagir ta ce "Okay, Madam ko zaki iya faɗamana yadda akeso tsayin ya kasance?."




Madam ta ce "anaso ya kasance kamar_1.55m zuwa sama da hakan."



Hameeda ta ce "Madam tambayoyi biyun ƙarshe please. Na farko shin zaki iya faɗamana dalilin da yasa kikazo duba lafiyar Juwairiya Jabir Bici?."

"Na biyu shin zaki iya faɗamana dalilin ki naba budurwar da ta lashe Gasar tazo ta ɗaya kyautar tsadadden Diamond Ring?. Domin mutane da yawa suna so susan dalilin ki nayin hakan."


Wannan karon dariya Madam Miracle tayi har farare jerrarun haƙoranta suka bayyana sannan ta bata amsa da "Duka waɗannan tambayoyin naki Miss Hameeda Sagir amsa ɗaya ne dasu, wannan amsar kuma ita ce saboda naji ina ra'ayin hakan ne, cause it's the personal secret thing."




Hameeda Sagir zata kuma magana, Madam Miracle ta miƙe tsaye tana faɗar



"It's okay, lokaci yaja zan tafi."


Miqewa ita ma ƴar jarida Hameeda Sagir tayi tana faɗin  "Okay Madam Miracle sosai munji daɗin wannan taƙaitaccen firan da ya gudana tsakanin mu, muna fatan nan gaba zamu sake zama domin firar kalar wannan?."


Murmushi Madam Miracle tayi sannan ta ce "Babu damuwa, domin a koda yaushe ina mai maraba daku, na barki lafiya."


Juyowa ƴar jaridar Hameeda Sagir tayi tana fuskan tar na'urar ɗaukar bidiyon tana faɗin "Toh jama'a masu kallon mu, da sauraron mu, kamar yadda kuka gani mun tattauna da Madam Miracle kuma munji dalilin da yasa ba'a zaɓi Miss Juwairiya Jabir Bici ba a cikin Gasar SARAUNIYAR KYAU matakin jaha ba."





# MASU KARATU, IDAN BAKU MANTA BA, DUK WANNAN TATTAUNA WAR KALLON SHI SU JIDDARH SUKEYI A TV.




Kashe T.v ɗin Jiddarh tayi sannan ta kalla su Humaira tana faɗin "Abin akwai ban tausayi fa, ace mutum bai samu ya cika burin da ya sama rai ba, a gaskiya yarinyar ta bani tausayi ba kaɗan ba."

Ajiyar zuciya Humaira ta sauke tana mai faɗin "Ni ma dai hakan ne, amma ya zatayi wannan ita ce ƙaddarar ta gashi abin ya yayatu a social media ta ko'ina maganar ta akeyi fa."

Auntie ta ce "ai kunji irin matsalar yanzu tajama kanta da iyayenta tonon qwaqwaf kenan fa."

Ci gaba da tattaunawa akan lamarin sukayi gaba ɗaya jikin Jiddarh yayi laqwas duk tausayin budurwar yabi ya addabeta a zuciya.



Suna cikin haka sai ga Bilki ta shigo bugujin bugujin da ita ga yarinya a hannunta tana tsotsar madara a fida.

A tsakiyar palon ta zube sannan ta kalla Jiddarh tana faɗin "Sannu SARAUNIYAR KYAU ta jahar Kano, gaskiya ina tayaki murna sosai."

"Ke tayaya kika san ita tayi Nasara a  Gasar bayan kuma bakije Gasar ba?."

Auntie ta tambaya tana kallonta, dariya Bilki tayi ta ce "Hajiya kenan Auntien mu kin manta ina da waya ne.?"

Humaira ta saka baki, "Malama Bilki mai raino, to ya ya yarinyar taki take,?"

Bilki tana washe baki ta ce "Ga yarinyar bata da rigima sam, inajin daɗin wannan yayen da nakeyi, ni dama mutane zasu gane su dinga kawomin raino ai dana zama Auntyn Yara."


Jiddarh ta ce "Aikuwa zaki dace da Autyn Yaran highly."

Bilki ta bata amsa da "Kedai bari ai abin ba'a iya cewa komai wallahi."

Jiddarh ta kuma cewa "To ya zakiji idan akazo tafiya da Khausar ranar da kika gama rainonta?."

Bilki ta ce a gaskiya abin babu daɗin faɗa ko'a baki, dan zanyi kewar ta sosai banama fatan ranar da zata zo karɓanta tazo, dan idan tazo sai nayi zazzaɓin yini ɗaya yasin."

Tayi maganar tana zuba uban tagumi.
Humaira ta ce "Ba kewar ta zakiyi ba kenan, tunda dai zazzaɓin yini ɗaya zakiyi kacal?."

Bilki ta amsa da "To ai na yini ɗayan yafi daɗin faɗane a baki fa, shiyasa nace hakan."

Dariya sukayi jin irin wautar Bilki fira suka ci gaba dayi sama sama Bilki tana basu dariya da shirmen ta.





*SARAUNIYAR KYAU* 💓
       
   _(The Glam Queen)_ 👑
       
         ```Takun Farko```

Story & Written By:

              *_The Nainarh KD_*

_In dedication to my dear Classmate Science G.S.S.S BELE ROAD._







*THE ONGOING BOOK'S*


 1. *SONKI NE ƘADDARA TA*
 
          MALLAKAR
FATIMA ABDULLAHI
          _Batool Kamba_





 2.  *ZAN JIRA KA*

        MALLAKAR
     A'ISHA ALƘALI
         _Mrs Aysib_








Page *43&44*



ABUJA_NIGERIA



M.M.K, FAMILY💓



Sun isa gida lafiya, cike da farin ciki dukaninsu suka fito daga cikin motocinsu sannan suka miƙa hanya, palo suka shiga bayan Momy Rafi'at ta danna lambobin sirri ta buɗe.
Gaba ɗaya saman kujeru matan suka zube cike da gajiya, dama shi M.M.K tuni yayi part ɗinshi.



Lailah ta nisa tare da faɗin "A gaskiya mun kwaso gajiya, ba kaɗan ba, domin kuwa jina nake kamar anyimin dukan tsiya fa."



Tayi maganar tana kwance igiyoyin takalmin ƙafarta da bata samu ta cire ba, saboda tsaban gajiyar da tayi.


Zaynerb ta ce "Kedai bari kawai, dan gajiya akwaita kam sosai, dan yanzu banajin zan iya zama, har saina ji ni ina take shower ko zanji daɗi."



Ɗagowa lailah tayi tana shirin yima Momynsu magana taga ta nufi staircase's ta fara takawa saboda sauri da bibiyu ma take taka staircase's ɗin.


Dukansu da kallo suka bita baki sake, amma basu kawo komai a ransu ba, dan kuwa sunfi tunanin gajiya ne, da kuma tunanin Asibiti wata ƙila za'a iya nemanta a ko wani lokaci yasa tayi hakan.
Sai dai banda Zaynerb wacca kanta kawai ta girgiza sannan ta shige Bedroom ɗinta tana saƙa abubuwa da yawa a zuciyarta.







Wani wawan bugu ta kaima ƙofar Bedroom gaba ɗaya tama manta a kulle ƙofar take, har sai da taga ƙofar taƙi buɗuwa, sannan ta zuge zip ɗin jakarta dake rataye a kafaɗarta ta ciro key's ta buɗe ƙofar ta shiga ciki a mugun fusace,  zuciyarta har wani tafasa take saboda tsaban ɓaccin rai.







Tana shiga bata tsaya komai ba tayi jifa da jakar hannunta a saman gado mayafin kanta ma cireshi tayi shima tayi throwing ɗinshi saman mattress, gaba ɗaya perfumes da cosmetics ɗin dake saman mirror tayi watsi dasu  har ƙasa, nan masu tarwatse suka farfawashe a ƙasa, hakan ma bai ma ta ba ɗaukar wani kwalbar turare tayi da ƙarfi ta jefa shi saman Dress Mirror, aikuwa nan take Dress Mirror ɗin ya tarwatse a gurin.




Huci kawai take fitarwa tana zagaye Bedroom ɗin, da sauri ta ƙarisa gurin da ta jefar da jakarta, buɗe jakar tayi sannan ta ciro wayarta, kai tsaye contacts ta shiga ta lalubo wata lamba wanda akayi saving da rubutun CHINESE, kira ta danna amma abu ɗaya wannan Baturiyar mai baƙin jini take faɗa shine, wayar da take kira a kashe take.




Bugun zuciyarta ne ya ƙaru fiye da kima, wai meke shirin faruwa ne?, kardai ace wannan matar yaudaranta tayi bata ma ta aikin da ta sakata ba,  aikuwa bazai yiwu ba, ita bama uban kuɗaɗen da ta bawa matar takeji ba, a'a wahalar da ta sha kafin ta samu ta sama..."Kai bazai yiwu ba wallahi, No Way.! wallahi bazan yadda ba, ina! sai dai kuwa idan ba ni ce Rafi'atu Rafiq Rayyan ba.




Gaba ɗaya maganar takeyi idanunta a rufe kuma a fili take maganar cikin hargowa saboda mugun ɓacin ran da take ciki.

Wani irin jifa tayi da wayar hannunta a jikin bangon ɗakin sai ga wayar a ƙasa tayi tatsatatsa ta tarwatse a ƙasa, da gudu ta ƙarisa gurin wayar faɗin take "Ina bazai yiwu ba, bai kamata nayi haka ba, wannan wayar tana da matuƙar muhimmanci a gurina."







Gaba ɗaya saboda tsananin tashin halin da take ciki, saya tana abu kamar wacca bata cikin hayyacinta faɗi take "Please an  waya ki kawo, karki yimin haka ina buƙatar amfani da ke, please please..."



Ganin dai wayar ba kawowa zatayi ba, yasa ta kuma jifa da ita, ba abin da takeyi a Bedroom ɗin sai faman kai kawo daga nan zuwa can.
Tsayawa tayi cak da kai kawon da takeyi, juyawa ƙofa baya tayi, sannan daga tsayen da take ta fara magana a fili cikin ɗan ɗa ga murya take faɗin "Wallahi bazai yiwu ba, ace yarinyar nan ta sama Nasara, to wai ina inane lokacin da hakan ta faru?..."

Ɗan shiru tayi kamar mai tunani, sai kuma can bayan wasu mintuna a fili ta kuma cewa "Na rantse da wanda raina yake hannunsa sai naga ƙarshen zuri'ar Hajarah mudin ina raye a duniya koda kuwa zanyi yawo tsirara ne, waɗannan mutanen guda uku bazan bari su sama sa'ida ba a rayuwa, indai ni ce Rafi'atu Rafiq Rayyan tabbas anwuce gurin."





"Da gaske kike zaki iya yawo tsirara akan cikan burinki, ko kuwa faɗa kawai kike na kuri.?"

Da mugun sauri ta juya tana kallon wacca tayi ma ta wannan tambayar.


"Ke kuma tun yaushe kike anan?."

Tayi ma ta tambayar tana zama saman Bed ta ci gaba da cewa "Menene ya kawoki nan.'

Qarisa shigowa Haleesat tayi ita ma ta zauna a saman bed ɗin tana fuskan tar ta sannan ta mayar da kallonta kan bedroom da yayi kaca kaca, tana ƙarara ko'ina kallo, har sai da ta gama nazartar Bedroom ɗin tsaf, sannan ta ce fa idanunta zuwa ga kallon Momy Rafi'at dake faman huci, da alamu har yanzu ɓacin ran da take ciki, bai gama sakinta ba.




"Na tambaye ki kinyi shiru, shin zaki iya yin yawo tsirara a domin cikar burin ki?, sannan naji kina faɗin mutane uku zaki ɗauka fansarki akansu, nidai nasan mutum biyu shin wanene ko kuma wacece ta ukun?."


Shiru Momyn ta ma ta kamar ba zatayi magana ba, sai kuma ta ce "Lokacin da zakisan ko wacece ta ukun bayyi ba, amma duk ranar da burina ya gama cika, tabbas zan faɗa miki ko wacece ta ukun, a ranar zakisha mamaki kalar wanda baki taɓa sha ba tsayin rayuwar ki Haleesat."

Tayi maganar tana sakin shu'umin murmushi kamar ba ita ce wacca ta haɗe rai ba, sannan kuma idanunta qur akan Haleesat kamar yadda ita ma Haleesat ɗin ta zuba ma ta nata kyawawan idanun tana kallo ba tare da ta ce da ita komai ba.


Ajiyar zuciya ta sauke har yanzu idanunta akan Momy Rafi'at suke, da kyar ta iya haɗiye yawun bakinta domin kuwa yanzu Momyn ta dena bata mamaki, sai dai tsoro, sannan ta ce "Shin Momy zan iya tambayar ki wani abu kuwa?."



Ɗan murmushi Momyn tayi sannan ta ce "Go ahead,"

Haleesat ta ce "Wai shin menene ainihin abin da yasa kika tsana maragayya Mamy Hajarah, bayan kuma ba abin da tayi miki, kuma naga ai ta mutu ko, amma baki rabu da yaranta biyu ba, da Allah ya azurtata dasu kafin rasuwarta, sannan kuma naga Daddyn har da kowa a cikin dangi harke kanki ba wanda ya taɓa faɗar hallayar ta mara kyau, kowa sai dai ya faɗi alkhairinta. Shin ko zaki iya faɗamin dalilin da yasa kika tsaneta haka?."




Haleesat ta ƙarishe jero ma ta jerin tambayoyin, tana kuma kallon Momy Rafi'at ɗin da kyau tana jira taji ta bakinta.


Ajiyar zuciya kawai Momyn take saukewa tana kuma ɗaure fuska, tuno abubuwan da suka faru fiye da shekaru Ashirin baya. Tunosu take kamar yanzu suka faru, tana tuna yadda Hajarah taci amanarta ta aure ma ta miji, yayinda take tuno hakan zuciyarta take ƙara ma ta zafi.




Sun ɗauki fiye da mintuna biyar a haka suna kallon kallo.


Kafin can Haleesat ta katse shirun da faɗin ''Ina jinki fa Momy, ko dama ba wani abu da tayi miki, kawai kinaso ki ɗauki fansa ne, ba tare da ta yi miki wani Babban laifi ba?."


Da sauri Momy Rafi'at ta katseta da faɗin "Dakata Haleesat badai kinaso na faɗamiki abin da Hajarah tayimin ba, to yanzu zakiji komai, zakiji kalar cin amanar da tayimin. Sannan sai ki tantance wacece mai gaskiya tsakanin ni da kuma ita."



Gyara zamanta Momyn tayi sannan ta fara magana haka.

"Hajarah tayi min abin da ban taɓa tunani ba a rayuwa.
A shekarun baya fiyeda shekaru Ashirin da huɗu baya.
Wata rana ni da Mahaifin ku, mun dawo daga unguwa, muna cikin motar shi, a lokacin ban haifeki ba, daga Nainarh sai Nailah sai Babban Yayan ku Maleek na haifa.
A lokacin muna tafiya cikin mota mun biyo ta yankin daji daji can gefen titi muka hango kamar mutum a kwance cikin jini. Ni ce na fara hangowa da nayiwa Daddyn ku magana akan ya tsaya domin a taimakawa matar domin na lura macece.
Da farko yaƙi yadda ya tsaya har sai da nayita roƙon shi sannan ya tsaya muka fito a tare muka bar yaran a mota..."


Katse Momyn Haleesat tayi da faɗin "Ki gajerta labarin kawai ki faɗamin abin da ya faru gaba, domin jiranmu ake a Downstairs."

Kallon Haleesat Momy tayi da kyau tana faɗin "Kin canza sosai, ba yadda na sanki ba ko dai..."



Share maganar tayi, ta ci gaba da cewa "A wannan lokacin ba kowa bace matar da muka taimakawa fa ce 'Hajarah' daga baya kuma tazo taci amanata 'TA AUREN MIJI' uban ƴaƴana, sannan abin ƙaunata akaf faɗin duniya, kuma abin alfarina, wanda ban haɗa son da nake mishi da kowa ba, hatta iyayena, Hajarah ta aura miji na ta janyeshi daga gareni, ya zama baya jin maganar kowa sai nata sai abin da ta faɗa shi ake bi a gidannan, bata tsaya anan ba ta ƙara da janye yarana daga gareni sai na dawo dani da babu duk ɗaya, a gidannan, fadar kowa hadda mai gidan ya koma a tafun hannun Hajarah..."


Qara katseta Haleesat tayi da cewa "Momy kinata maganar taci amanarki ta aure miki miji, amma ni banga wani cin amana ba, dama can Allah ya nufa zata zama matar Daddyn mu ne fa, That's All."





Haleesat tayi maganar tana miƙewa tsaye, don bata da lokacin ɓatawa wajen sauraren wannan maganar na mahaifiyar tasu. kallon Momyn tayi sannan ta ce "Momy ki sauko ana jiranmu a Downstairs, domin kuwa su Haseeya sunzo daga Kano, haka ma ƴan Adamawa da ƴan Mai Duguri duk sun iso, ke kaɗai ake jira fa."




Tana gama faɗar hakan ta buɗe ƙofa ta fita daga bedroom ɗin.






Baki sake Momyn tabi bayan Haleesat da kallo saboda tsananin mamaki ma ta kasa magana, can ƙasan ranta kuwa tunanin ake wai shin yaushe raini ya shiga tsakanin ta da Haleesat ne, bata sani ba, wato ita Haleesat zata kalla tsakiyar idanunta saboda fitsara ta ce ma ta bataga cin amanar da Hajarah tayi ma ta ba, lallai ya zama dole ta kuma zage damtse domin wankin hula zai iya kaita dare bata sani ba.😏






Qwafa taja a fili ta ce "Tabbas zanyiwa tufkar hanci sooner."


Miƙewa tayi ita ma ta fito waje Downstairs ta sauko tun daga nesa take hango mutane zazzaune saman kujerun palon ana fira.




Qarisa saukowa tayi sannan ta sama guri ita ma ta zauna saman 2sieter gaba ɗaya ƴan matan palon suka gaisheta, amsawa tayi fuska a sake sannan ita ma ta shiga gaisawa da manyan suna taɓa fira, ta lura babu Afeefah da Lailah da Deejarh a wurin, domin daga Haleesat sai Zaynerb da kuma su Nainarh da Nailah da suka shiga cikin ƴan mata ƴan uwansu suna fira.








 





💅D££JARH💅








A hankali ta turo ƙofar bathroom ta fito, chest ɗinta ɗaure da towel white color, ga wani ƙarami tana goge sumar kanta dashi.

Janyo swivel chair na Dress Mirror tayi sannan ta zauna akai tana fuskantar Mirror, Hairdryer ta ɗauka bayan ta jona a charge ta fara drying hair ɗinta cike da jindaɗi.
Ta ɗauki lokaci tana hakan, sannan ta ɗauki Hair Brush bayan ta mayar da Hairdryer ɗin ma'ajiyar shi, sai da ta ta je sumar kanta yadda zata iya sannan ta shafa lotion, bayan ta gama bata tashi daga wajen ba, sai da ta tsaya tayi make-up sama sama, domin kuwa ba wani iyawa tayi ba, danma Afeefah tana ɗan koya ma ta ne.

Powder ta fara shafawa sannan ta zizara kwalli a idanunta, sai kuma ta saka jam baki Maroon color, harta ɗauka Masraca zata saka a idanun ta sai kuma ta fasa, a fili ta ce "Ba sakawan da zanyi Natural gashin ido nawa ma ya isheni Blush ta ɗauka wato barbaɗa kumatu a hausance😘 ta barbarɗe kuwa a fuskar ta da ya ke fara ce sai yayi ma ta kyau sosai.




Tashi tayi ta nufa Wardrobe ta buɗe sannan ta ciro tufafin da zata saka cikin ƙaramin lokaci ta shirya cikin £nglish Gown Maroon color mara hannu iya gwiwa, sannan ta saka Dogon wando shima Maroon color wanda ya matseta Ribbons ta ɗauka guda uku Maroon color da fari sai black color.
Gaban Dress Mirror ta dawo kana ta kamo dogon gashin kanta na fulanin ainihi ta tufke da Ribbons ɗin da kyar.


Ɗaukar after dress na Gown ɗin dake jikinta tayi Maroon color mai adon flowers pink and stones sky Maroon tayi, ta saka sannan ta ɗauki flat shoes glitter stilettos mai shaining launin sky Maroon ta saka a madaidaitan ƙafafunta.


Komawa tayi ta buɗe Wardrobe ta ciro wani abu a ciki sannan ta rufe, cikin trouser pocket ɗinta ta saka abin da ta ɗauka.


Bakin ƙofar Bedroom ɗin ta dawo ta tsaya tana so ta fita amma tana jiyo muryoyin mutane kala kala a palo gashi batasan kowa ba a ciki dan bataji muryar ƴan gidan ba, a cikin muryoyin da take iya jiyowa daga gurin da take a tsaye.





Daurewa kawai tayi ta murza key ɗin dake a jikin ƙofar sannan Door ɗin ta buɗe.

A hankali ta zura kanta ta waje tana leƙen palon, ganin da tayi kamar hankalin mutanen palon baya ata wurin da take, yasa tayi shahadar fitowa gabaki ɗayanta.



Cikin sanɗa take taku a palon duk dan kar a ganta, kai tsaye Bedroom ɗin Afeefah ta nufa, cikin sanɗa takai hannu zata buɗe ƙofar Bedroom ɗin kenan.

Tajiyo wata murya ta bayanta, cak ta tsaya ta kasa juyowa sai da taji an kuma magana sannan ta juyo da kanta a hankali tana fuskan tar mai maganar, amma kuma idanunta a rufe ƙam.



A hankali ta buɗe kyawawan idanunta ta saukesu saman fuskar wata kyakyawar matashiyar budurwa dake tsaye a gabanta tana binta da kallon rashin sani.
Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta ce "Sunana Khadeejah bawai 'Ke! ba."


Da tsananin mamaki budurwar take kallonta sai kuma ta ce "Khadeejah kuma dama akwai budurwa kamar ki,  anan gidan?,"

Murmushi Deejarh tayi sannan ta bata amsa da "A'a ni baƙuwa ce ae, shiyasa baki sanni ba."

"Ohoo, to meyasa kike sanɗa kamar mara gaskiya.?"



Budurwar ta tambaye ta tana kallonta, dariya Deejarh tayi ta ce


"Balarabiyar India nakeso naba tsoro ai,"

"Balarabiyar India kuma, wacece ita. Kodai Auntynki ce?."


Budurwar ta kuma tambayarta tana dariya dan da alama ita ma gwana ce wajen surutu.


Cike da gajiya Deejarh ta ce "E, mana Balarabiyar India ae yayata ce sosai ma, uwa ɗaya uba ɗaya muke da ita."



Tayi maganar tana juyawa ta buɗe ƙofar Bedroom ɗin Afeefah, ta shige ciki tabar budurwar tsaye a wurin.



Tana shiga Bedroom ɗin ta sauke Ajiyar zuciya, sannan ta ƙarisa shiga ciki, can saman doguwar kujera ta hango Lailah zaune taci ado iya ado, ga tsadaddiyar wayarta a hannunta tana kafta selfie, daga gefe kuma Afeefah ce tsaye gaban mirror tana goga kwalli a kyawawan idanunta.
Suna taɓa fira da Lailah ɗin sunyi kyau sosai cikin the same shiga komai kala ɗaya, sai dai kalar ɗinki da ya banbanta, domin kuwa Lailah tana sanye ne cikin riga da skirt na atamfa ga ɗaurin ɗan kwali nan da tayi ɗaurin ture kaga tsiya mai style, fuskar ta tasha make-up, sai kuma Afeefah sanye cikin doguwar riga atamfar irinna Lailah rigar atamfar ammata ɗinki mai style na eshap wacca ta ma ta kyau sosai, sai dai saɓanin Lailah, ita Afeefah hular bat ce akanta golden color, saman hular an rubuta beauty ga atamfar jikinsu golden mai tsadar gaske, gaba ɗayansu sunyi kyau kai saika rasa wacca tafi ƴar uwanta kyau a ciki.








Cikin sanɗa Deejarh tabi ta bayan kujerar da Lailah take akai, taje ta tsaya ta bayan Afeefah tana dariya, ta mirror Afeefah ta hangota, murmushi tayi ma ta tana faɗin "Ke kuma yaushe kika shigo bamu sani ba?."



Juyowa Lailah tayi domin taga wacca ta shigo, daidai lokacin Deejarh take faɗin "E, mana cikin sanɗa na shigo, dan naga mutane da yawa a palo, kuma duka bansan su ba, shiyasa nazo nan fa."




Dariya Afeefah tayi tana cewa "Indai kinaso ki sansu yanzunnan zaki sansu duka Insha Allah."



Da zaƙuwa Deejarh ta amsa "E, inaso na sansu dukansu gaskiya."


Juyowa Afeefah tayi tana fuskantar Deejarh ta ce "To Ƴan Mata ya ya nayi kyau kuwa?."

ai ba Deejarh ba hatta Lailah dake zaune batasan lokacin da ta miƙe tsaye ba, ta ƙariso wurin Afeefah ɗin, bakinta tana mai furta kalmar



"Masha Allah."




"Nima dai yau bari na qwada kiranki da wannan sunan gaskiya, cikin washe baki Lailah ta ce

"Balarabiyar India kinyi kyau sosai sosai, idan nace sosai to ina nufin over fa, a gaskiya wannan kyawun bazai wuce a banza ba, dole sai munyi pictures kala kala da *SARAUNIYAR KYAU* ta Garin Abuja."


Tayi maganar tana kuma shiga camera ta wayarta.


Dariya kawai Deejarh da Afeefah sukeyi ganin yadda Lailah duk tabi ta ruɗe na ganin tsantsan madarar kyau wajen Afeefah.

Ƙarisowa wurin Lailah tayi sannan ta ce "To ku shirya muyi pictures na tarihi domin wannan kyawun dole saida pictures zafafa."


Gyarawa sukayi gaba ɗaya za'a fara kafta hotuna, da sauri Deejarh ta ce "Nifa kunsan bani da tsayi bazan kai tsayin ku ba, ya ya za'ayi kenan?."🤣



Dariya Lailah tayi ta ce "To ki hau kan kujerar mirror mana,"


Aikuwa Deejarh bata jira komai ba, ta kwantar da stool na Dress mirror sannan ta hau kai, suka fara kafta selfie's kala kala iri iri, mai kyau, da mara 😏 sai da sukayi ya ishesu.


Sannan Afeefah ta ce "A barshi haka ana jiransu a waje, ɗaukar scarf ɗinta mai adon stones tayi ta yafa, ita ma Lailah ta ɗauki nata golden color ta yafa a gefan kafaɗarta, sannan suka nufi ƙofa a tare zasu fita.

Kallon Deejarh Afeefah tayi tana faɗin "A haka ne zaki fita da gashi a waje kai ba hula. kamar wata 🤥?."



Dariya Deejarh tayi tana mai bawa Afeefah amsa da
"Balarabiyar India mana, nafa saka Ribbons har guda uku na tufke, ae shikenan sun isa."


"To dan kin saka Ribbons kin tufke sai akace ki fita a haka, ko bakisan akwai maza ba a palon?."


Wannan dai dariyar ta ƙauyanci Deejarh ta kumayi ta ce
"To ai naga ni yarinya ce, ba dole sai na saka mayafi ba."



''Ta ina kike yarinya bayan kin fara Breast haka ki ji ki fa."




Lailah tayima Deejarh tambayar iya gaskiyar ta.

Cike da kunya Deejarh ta rufe ido wai kunya, kana ta ce

"Auntie Lailah mana,! bakyajin kunya wai?,"
Lailah ta ce
"Kunyar mai zanji ko zakice baki fara bane, kujimin yarinya kam da wani pretending."





Qara rufe fuska Deejarh tayi ta ce 'Kai Auntie Lailah Allah kina bani kunya da yawa fa "

Dariyar mugunta Lailah tayi "Ashe dai kinada kunyar."



Dawowa wurin Afeefah tayi hanunta riƙe da hular bat sky maroon, miƙawa Deejarh tayi tana faɗin

"Oya saka mu tafi."


Amsar hular Deejarh tayi ta saka, Lailah ta kuma gyara ma ta gashinta da ya sauko har gadon bayanta sannan suka fita a tare.



Tun kafin su ƙarisa palon ƙamshinsu ya isa hancunan mutanen da ke zazzaune a palon.


Habba ae nan kallo ya koma sama wai shaho ya ɗau giwa.🤐




Gaba ɗaya mutanen palon suka juyo suna kallon su fuskar ko wannensu su cike da fara'a da walwala, wata daga cikin ƴan matan ce tayi magana

"Amazing kunga *SARAUNIYAR KYAU* ta iso tana baza ƙamshi."



Gaba ɗayansu su ukun suka sama wuri a 3sieter suka zazzauna nan suka shiga gaisawa da mutanen palon cike da farin ciki suke amsawa amma yawancinsu idonsu yana akan Deejarh wacca take zaune kusada Afeefah tayi tsumu da ita kamar tsumma a randa 🤓





Afeefah ta lura da irin kallon neman ƙarin bayanin da mutanen n palon sukeyiwa Deejarh, amma ta sha re suka ci gaba da fira yayinda Deejarh take buga game na *Streetchaser* da wayar Afeefah.



Suna zaune sai ga mazan sun shishshigo dama can suna part ɗin Daddyn ne gaba ɗaya suma suka sama wuri suka zazzauna dayake palon Babba ne sosai kuma kujeru set biyu ne, yasa duk ya ishesu suka zazzauna nan suka shiga sabon gaisha gaishe yayinda Deejarh take buga game ɗinta hankali kwance tunda ta gaishesu suka amsa.



Wata ce daga cikin ƴan matan ta gaza haƙuri ta kalla Haleesat tana tambayarta

"Wai Leesat a'ina kuka samo wannan Beautiful Baby ɗin, ƴar Kyakkyawa da ita?."

Tayi tambayar tana nuna Deejarh sai kuma hankulan gaba ɗaya mutanen palon ya dawo kan Haleesat ɗin suna jira suji mai za ta ce, ganin ta kasa magana ne sai dai ta kalla Deejarh ta kalla mutanen palon.

Yasa M.m.k gyaran murya sannan yace "Ɗiyata ce sunanta Khadeejah."

Kallon Afeefah yayi yana murmushi yace "Shalele yima ɗiyata Khadeejah bayanin kowa da kowa."



Cike da taikaci Momy Rafi'at take jefawa Daddyn hararar ƙasan ido, tana jan qwafa wato dai Hajarah ta mutu ga Ƴarta ta gaji sarauta ko, yanzu fisabilillah gata zaune a palon, amma ya tsallaketa yace ma wannan yarinyar mai kamada uwarta wani wai shalele yima ta bayanin kowa da kowa, ta kwaikwayi muryar Daddyn a zuciyarta cike da haushi qwafa ta kuma ja sannan ta mayar da kallonta kan Afeefah kamar yadda duka sauran jama'ar palon suke kallonta.



Murmushi Afeefah tayi Sannan ta kalla Deejarh ta ce "Dama ba kinaso kisansu ba ko?."

Dariya Deejarh tayi ta ce "E, mana Balarabiyar India,"

Afeefah tayi dariya sannan ta ce "Yauwa to yanzunnan zakisan kowa da kowa Insha Allah."

Tayi maganar tana kuma kallon jama'ar palon.
Sannan ta nuna wata kyakyawar mata ta ce "Sunanta Mamy Zuwaira tana aure a Jigawa State yaranta huɗu maza biyu, mata biyu ga matan anan ta nunasu, Zakiyya da  kuma Fateemah, mazan kuma Zaid da Yusuf, amma basu zo ba.


Gyaɗa kai kawai Deejarh take alamar tana ganewa sannan ta kalla matar da aka kira da Mamy Zuwaira ta ce "Sannu Mamyn mu."

Hajiya Zuwaira tana murmushi ta ce

"Yauwa sannu Khadijatu."

Kallon Zakiyya da Fateemah ta kumayi ta ce "Barkanku dai yayyina."

Suma suna murmushi suka amsa ma ta da
"Yauwa kema barkanki."




*_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️
───────────────────────
```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.}``` ✏️
     ____________(✪)______________
https://www.facebook.com/profile.php?id=100069755834980
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•


*SARAUNIYAR KYAU* 💓
       
   _(The Glam Queen)_ 👑
       
         ```Takun Farko```

Story & Written By:

              *_The Nainarh KD_*

_In dedication to my dear Classmate Science G.S.S.S BELE ROAD._



*THE ONGOING BOOK'S*


 1. *SONKI NE ƘADDARA TA*
 
          MALLAKAR
FATIMA ABDULLAHI
          _Batool Kamba_





 2.  *ZAN JIRA KA*

        MALLAKAR
     A'ISHA ALƘALI
         _Mrs Aysib_






Page *45&46*


.
Afeefah ta ci gaba ta nuna wata matar dake hakimce saman kujera ta ce "Sunanta Mamy Jawaheer ita ma tana aure a Jigawa State ne, yaranta uku maza biyu mace ɗaya, sannan ta nuna wasu kyawawan matasan samari da suke zaune kusada Daddy tana faɗin "Gasu nan da Yaya Omar da kuma Yaya Umer, sai ta nuna wata matashiyar budurwa dake zaune gefan Zaynerb ta ce "Sai wannan sunanta Husnee."


Deejarh ta gane budurwar ita ce wacca suka haɗu da zata shiga Bedroom na Afeefah ɗazu, dan haka cikin sakin murmushi ta musu sannu duka suma suka amsa.




Ci gaba da magana Afeefah tayi Bayanta nuna wata matar

"Sunanta Mamy Jummai ita ma dai aure take a Jigawa State, yaranta uku duka mata ga ɗaya anan wacca taci sunan Mamy Jawaheer muna kiranta da 'Ƙarama' sauran biyun kuma suna karatu a Abroad.

Sai kuma Mamy Sakina tana aure a mai Duguri amma ita bata sama damar zuwa ba, gadai wakilanta wato yaranta su biyu Yaya Salim da kuma Saleemarh."


Suma suka gaisa da Deejarh cikin sakin fuska abunka da ƴan boko wayayyu.

"Sai kuma Uncle Yusuf."


Ta nuna wani magidanci da yake zaune kusada da Daddyn sannan ta nuna wata mata da yara biyu mata ta ce "Ga matarshi Auntie Yusra da yaranshi Yasira da Yasmin, akwai Yaya Yasir amma shi baizo ba yana ƙasar Australia yana karatu, suna zaune a Adamawa State ne."

Suma suka gaisa da Deejarh tana washe baki.


Afeefah ta ɗanyi shiru sai can ta ce "Akwai Uncle Saminu yana zaune a Lagos da iyalansa, amma suma basu sama damar zuwa ba, sai kuma Uncle Yunus yana zaune a ƙasar France shida iyalansa."




"Sai wannan da kike gani Mamy Suwaiba matar Uncle Sagir ce."

kana ta nuna wasu kyawawan ƴan mata biyu da wani saurayi tana faɗin

"Yaranta ne Haseeya da Mah'eesha sai Yayah mahfuz."



Ajiyar zuciya Deejarh ta sauke tana kallonsu su duka a zuciyarta tana mai faɗar "Lallai ma, wato su kowa yanada twin's ne a familynsu?, babu inda basu ko'ina suna nan."


Ta kalla Afeefah ta ce "Lah Balarabiyar India.!  Baki faɗamin garin da suke ba, dukansu."


Afeefah ta bata amsa da "Ki cin ka mana."

Ɗan shiru Deejarh tayi tana kallonsu kana ta ce

"Ina ganin Kano ne ko?."



Afeefah ta amsa ma ta da "E, haka ne."



Da sauri Deejarh ta ce "To wai ina Ammah ne, naga basu zo da ita ba?."


Wannan karon Zaynerb ce ta ce "Kedai Deejarh rabu da Amman nan rigima take ji  taƙi zuwa, wai sai dai mu muje can fa."


Nainarh ta karɓe da faɗin "Ai ni nayi fushi da ita, tunda taƙi zuwa a taya Afeefah murna da ita."


Nailah ma ta ce "Mu ai sai muje can mu sa me ta, idan mun tashi tafiya gida ko?."


Deejarh ta kalla Afeefah ta na faɗin "Balarabiyar India kema zakije na bi ki?."


Kafin Afeefah tayi magana wata daga cikin ƴan matan wacce Afeefah ta kira da suna 'Husnee' ta ce



"Ni fa ina da tambaya?."


Kallonta sukayi Haleesat na cewa "Muna jin ki, go ahead."

Husnee ta ce "Wai meyasa naji wannan yarinyar..." ta nuna Deejarh. "Tana kiran Afeefah da Balarabiyar India ne?."


Lailah ta bata amsa da "Muma hakan muke ce ma ta ai wasu lokutan."



Wannan karon Umer ne yayi tambaya da faɗin "To saboda me kenan?."


Deejarh ta amsa "Saboda ita kyakyawa ce."


Yasira ta ce "To amma ae naga babu Larabawa a Indai ko?."

Yasmin ce taba Yasirar amsa da "Kika sani ko akwai su, kece baki sani ba?."





"Ni dai nasan ba wasu Larabawa a ƙasar India, dama dai Qatar ta ce ko kuma Sudan ko Egypt da dai sauransu dai, dana yarda."



Cewar ƙarama. Ɗiyar Mamy Jummai.

Deejarth ta ce "Ai saboda babu Larabawa a India ne, yasa nake ce ma ta Balarabiyar India fa."



"Because of what?."


Haseeya ta tambaya


Deejarh ta ce "Saboda duka Indiyawan tafisu kyau."



Dariya aka saka Mahfouz yana faɗin "Ni dai banga laifinta ba, ai gaskiya ta faɗa, domin Afeefah kyakyawa ce, ni ma daga yau Balarabiyar India zan dinga kiranta dashi gaskiya."


Nan ma aka kuma saka dariya Mamy Zuwaira ta ce

"Nima dai hakan."

Fateemah da Zakiyya suka haɗa baki wajen faɗar

"Muma haka gaskiya."

Nanfa kowa ya shiga faɗin shima haka, daga haka dai aka dasa sabuwar fira a tsakanin familyn cike da farin ciki da fahimtar junan su, suke firan nasu gunin burgewa abin nasu.😎





Can suna cikin fira sai ga Elina da Ummi ma'aikatan gidan masu girka lunch suka ƙariso wurin sanye cikin kayan ma'aikata, sun ɗaura apron blue a saman kayan jikin su, wurin Momy Rafi'at Elina ta ƙarisa cike da ladabi ta ce


"Madam the lunch is ready, shin a jeresu a Dining Room ne, ko kuma a kawo nan?."



Tayi maganar cikin harshen turanci, tana jira a bata amsa, ɗan murmushi Momy Rafi'at tayi sannan ta amsa da


"Ah inaga a kawo nan kawai domin za'a fi enjoying da kyau."



Cike da ladabi Elina ta amsa ma ta, sannan ta juya ita kuma Ummi ta shimfaɗa lodojin cin abinci daga can gefe a wuri biyu ma'ana da wurin maza dana mata mabanbanta.

Cikin ƙanƙanin lokaci suka kammala jere komai akan lodojin, sannan Elina ta dawo ta faɗawa Momy Rafi'at sun kammala, kana ta koma ciki.





Magana Momy Rafi'at ta musu gaba ɗaya mutanen palon suka tashi suka nufa wurin cin abincin, kowa ya zauna a wurin da ya dace dashi, yayinda Ummi take binsu ɗaya bayan ɗaya da roba da ruwa a hannunta suna wawwanke hannayensu a ciki, sai da suka kammala tsaf sannan ta koma ciki.
Su kuma suka fara ɗu'amun sannu a hankali cikin nutsuwa.🥳





A hankali Deejarh dake zaune gefan Afeefah, ta matsa da bakinta sai tin kunnen Afeefah ɗin tana faɗin "Balarabiyar India, shin zan iya tambayar ki wani abu?."

Afeefah ta ce "Inajin ki."

Deejarh ta ce "Waɗannan matan da suka raba abinci, su kuma daga ina suke?, Naga ma harda arniya a cikin su😏."



Murmushi Afeefah tayi dama tuni ta rubuta ta aje cikin zuciyarta sai Deejarh ta ma ta wannan tambayar. Ita ma cikin ɗan ƙasa da murya ta bata amsa da cewa "Ma'aikata ne su, wa'innan da kike ganin su Degree, garesu akan fannin girge_girge anan gidan namu suke aiki ana biyansu Salary mai tsoka, duk wata."



Deejarh da mamaki ya kamata ta ce "To meyasa kusan kwanana goma anan, amma ban taɓa ganin su ba sai yau kuma yanzu?."



Afeefah ta bata amsa da "Saboda sun tafi gida hutun watanni har biyu ne, yau suka dawo shiyasa bakisan su ba."


Deejarh tana gyaɗa kai alamar gamsuwa da bayanan Afeefah ta ce "Ooho kice ba'a nan garin suke ba kenan?."






Murmushi Afeefah ta kumayi, ita fa Wallahi bata gajiya da shirmen tambayoyin da Deejarh take ma ta, saima sakata nishaɗi da suke yi🤣



Ta ce "E, ita Ummi anan kusa take amma dai bansan sunan garin su ba, sai dai wata ƙila ma, anan Abuja suke zaune. Ita kuma Elina Ƴar Lakwaja ce, ita ma dai bansan sunan ainihin garin da take ba..."





"Wai kam nace gossip ɗin wa akeyi ne haka, naji anata qus qus fa?."



Cewar Husnee tana kallon su Afeefah ɗin.
Dariya Deejarh tayi ta ce "Sirri ne, tsakani na da Balarabiyar India ta."🤥



"Oh tunda haka ne, bari na barku ku ci gaba, ayi gulma da kyau guy's."


Husnee tayi maganar tana mayar da hankalinta wajen cin abincinta.





Hayaniyar da suka ji, yana tashi ne daga can waje yasa duk sukayi shiru, suna so su fahimci abin da ke faruwa.


Jin da sukayi hayaniyar ba mai ƙarewa bane, yasa ba shiri gaba ɗayansu, suka mimmiƙe suka nufa waje domin ganin abin da ke faruwar.




Gaba ɗayansu fitowa sukayi waje, don ganin komai. Daga can tsakiyar compound ɗin gidan suka hango gaba ɗaya ma'aikatan gidan sunyi curko curko dasu, ga wani saurayi ya juya baya yana zuba musu ruwan masifa kamar wanda baya cikin hankalin shi.


Da sauri suka ƙarisa wurin su duka Daddy yana tambayar Peter mai bawa flowers ruwa abin da ke faruwa. Cike da girmamawa Peter yake faɗi cikin hausar sa wacca bata gama karyewa a harshen shi ba.



Yace.



"Sir wannan ne,"

Ya nuna saurayin dake faman zabga masifa kafin ƙarisowarsu wurin amma suna ƙariso yayi tsit sannan kuma yaƙi juyowa.


"Sir tun ɗazu yake ƙoƙarin shigowa ciki, yana faɗin gidan sune wai, mu kuma bamu sanshi ba, munƙi bashi dama, shi kuma ya dage, ya dage akan sai ya shigo, har yana marin Moses fa, shi ne mu kuma muka dage muka hanashi shigowa Sir."

Peter yana maganar ne, yana gwada musu yadda saurayin yakeyi wai. { kuma dai masu karatu kunsan yadda Yare suke Especially ma idan suna so a Yarda da abin da suke faɗa 😆 }.





Ɗan murmushi Daddyn Yayi ganin yadda Peter ya dage yana bayani, bayaji baya gani, ba kuma ƙaƙƙautawa.

Sannan Mister Mai Kyau ɗin, ya mayar da kallon shi akan saurayin wanda
yake sanye cikin riga Top blue mai gajeren hannu, sai kuma wando Crazy Jean's wanda ya tsaya mishi iya gwiwa black color, ya saka p-cap black akanshi ga kuma face mask black, shima dai. Ya goya Backpack irinna na masu tafiya a bayanshi, ƙafafunnshi kuwa Boots ne blue color, ga kuma wani akwatu yashe a gefansa.


Cikin jin ɗan faɗuwar gaba, wanda baisan dalili ba, Daddyn ya fara magana kamar haka.
"Yaka ɗan saurayi, shin zaka iya jiyowa domin muga fuskarka da kyau kuwa?."



Shiru saurayin yayi kamar ba zai juyo ba, sai can ya juyo gaba ɗayanshi tare da cire face mask ɗin dake a fuskarshi nan take kyakyawar fuskarshi ta bayyana.



Tundaga kan Momy Rafi'at wacca ko'a mafarki ba za ta taɓa manta wannan kyakyawar fuskar ba...
Da Nailah wacca gaba ɗaya tsananin mamaki da ruɗani ya bayyana a kyakyawar fuskarta.

Ga Haleesat wacca ko daga bacci ta tashi ba zata taɓa mantawa da wannan fuskar ba.
Ba re Lailah wacca kullum take kwana take tashi da tunanin wannan saurayi da kyakyawar fuskarsa a kullum.

Zaynerb kuwa, ita bama za'a iya cewa komai ba, domin kuwa, she was very thither shock.


Gaba ɗaya suka haɗa bakunan su wajen faɗar


"BUDDY."



Afeefah da ƙarisowar ta wurin kenan ita da Nainarh da kuma Deejarh, taji maganar a kunnuwanta tamkar saukar adu.



Da wani irin sauri take wuce mutane harta ƙarisa gaban shi ta tsaya cak tana kallon shi kamar yadda shima yake kallonta.



Cikin sarƙewar murya da wahalar fitar numfashi take faɗin

"YaYa Maleek..! kaine kuwa..?"



Lallausar murmushi ya saki, sannan yace

"Ni ne dai Yaya Maleek ɗinki mai ƙaunar ki, yau gani na dawo gareki, shin ba za ki zo kiyi Hugging ɗina ba kamar yadda kika saba a koda yaushe?. MY sweet Blood 6ter?."


Yayi maganar yana buɗe ma ta duka hannayenshi.




Da gudun tsiya Afeefah ta nufa gurin shi, da niyyar zata rungumeshi, kamar yadda ya buƙata.
Sai dai kafin ta ƙarisa wurin sa, ta zube a ƙasa sumammiya.🤕






🔥ᴛᴀsʜɪɴ sᴇɴsᴇ🔥



Ai da wani irin sauri Maleek ya jefar da Backpack dake rataye a kafaɗunshi, Yayo kan Afeefah da gudu yana kiran sunanta da ƙarfi ya kai Hannu kenan zai taɓa ta.



Cikin mugun buga tsawa Nainarh ta dakatar dashi da faɗin

"Kar ka sake ka taɓamin Ƴar uwata da wannan ƙazamin hannun naka.🤨


Cak Maleek ya dakata da niyyar taɓa Afeefah da ya yi.

Ya juyo da rinannun idanun shi waɗanda sukayi jajir lokaci guda, saboda tsananin ɓacin rai, yana kallonta.


Qarisawa wurin Nainarh tayi tana tafa hannu ta ce

"Sai Yau?, na ce yau ne ka tuna damu Buddy?."
Nuna Afeefah dake yashe maga shiyan a ƙasa tayi da hannayenta waɗanda suke tsananin rawa tana faɗin

"Dube ta baiwar Allah yau tana cikin farin amma da zuwarka kalla yadda ta ƙare fa. Yanzu ka Faɗamin meyasa zaka zaɓa wannan ranar. This is only our glamorous Day, not yours, Amma... duba ka gani, daga zuwanka duba baiwar Allah yadda ta ƙare a sume fa."


Maganar take cikin hargowa da tsananin ɓacin rai gaba ɗaya ta manta wanda yake tsaye a gabanta, ta manta Buddy ɗinsu ne mai ji dasu, ta rufe ido tana zazzaga mishi masifa, tana fitar da duka baƙin ciki da damuwar da suka daɗe suna caccakar zuciyarta.😰




Zubewa Maleek Yayi gwiwo winshi duka a ƙasa yana zubar hawaye.

Hawayen da bai zubar dasu ba ranar da yabar gidan, Hawayen da ya daɗe yana jiran fitowarsu sai yau suka ƙari so. Saboda tsananin kuka ya ma kasa magana.



Shikuwa Daddyn su wato Mister Mai Kyau, Ashe tuni ya daɗe da yin sumar tsaye ba'a sani ba tun lokacin da Maleek ya juyo, da kuma tun lokacin da Shalelen shi ta zube a ƙasa sumammiya alamar ciwonta ne yakeso ya taso.




Ganin za'ayi to ne to ne ne, a tsakiyar gida yasa Uncle Yusuf kallonsu gaba ɗaya yana faɗin

"Ku shiga daga ciki a ƙarishe maganar zai fi."

Yayi maganar yana kamo hannun Daddyn wanda ya zama kamar mutum-mutumi, sannan ya kalla Auntie Yusra yace da ita.

"Ku kamo Afeefah ku shigo da ita ciki,"


Kallon shi ya mayar kan Maleek da har yanzu yake a durƙushe, cikin sanyin murya Uncle Yusuf Yace

"Ka  ɗauko kayanka ka shigo ciki." sannan ya yi gaba.😞



{*Tofah.! masu karatu, wai shin Menene ainihin abin da yake faruwa ne, a wannan labarin, gadai Maleek ya dawo gida, kuma ga Daddyn Ya zama kamar baya cikin hayyacin shi, gefe guda kuma ga Jarumar mu tana sume cikin wani hali, shin dama akwai wani ciwo ne da Afeefah take dashi  ba'a sani ba🤔 koma dai menene yanzu zamuji asalin labari }... INSHA ALLAH 💘*}



*SARAUNIYAR KYAU*💓

          
   _(The Glam Queen)_ 👑
       
         ```Takun Farko```

Story & Written By:

              *_The Nainarh KD_*


____________________________________________👑

*THE ONGOING BOOK'S*


 1. *SONKI NE ƘADDARA TA*
 
          MALLAKAR
FATIMA ABDULLAHI
          _Batool Kamba_





 2.  *ZAN JIRA KA*

        MALLAKAR
     A'ISHA ALƘALI
         _Mrs Aysib_





___________________________________________👑






*TH£ B£GINNING OF THE STORY*
          *MAFARIN LABARI*




 
*SOM£ Y£ARS £ARLI£R*




*AL_HAJI SAMEER LAMIƊO*



Page*47&48*

Shararren mai dukiya ne, wanda duniya ke ji dashi, a domin kuwa ba iyaka ƙasar Nigeria sunanshi ya tsaya ba, hatta da ƙasashen waje sunanshi ya zagaya, yana da tarin dukiya mai yawa, Wanda shi kanshi baisan adadi ba, ga companies kala kala gareshi, kaf faɗin Nigeria ba State ɗin da babu companynshi, sannan kuma shine mamallakin wannan shahararren Industry na sarrafa magani wato S.L__ Pharmaceutical Industry. Dake Babban birnin Nigeria Abuja.







__AL_HAJI SAMEER LAMIƊO.





Asalin shi cikakken ɗan garin Jigawa State ne, gaba da baya, sai dai mahaifiyar shi da ta kasance cikakkiyar ƴar Adamawa state ce.


Matan shi na Aure uku, matar shi ta farko ta kasance Hajiya Harirah wacca aka musu auren gida, Hajiya Harirah bata taɓa haihuwa ba tsawon zamanta da AL_HAJI SAMEER LAMIƊO.

Sai kuma matar shi ta biyu Dr_Raheemah wacca ta kasance Balarabiya ce ta ƙasar Sudan.
AL_HAJI SAMEER LAMIƊO, ya haɗu da matar shi ta biyu Dr_Raheemah ne, a wani taron manyan Likitocin duniya da ya hallarta a ƙasar Sudan Babban Birnin ƙasar wato KHARTOUM, a lokacin kallo ɗaya yayima Dr_Raheemah yaji ta kwanta mishi.
Aikuwa bayyi wata wata ba bayan kammala taro ya sameta da zance.
Tom da ya ke ita ma Dr_ Raheemah tun daga kallon farko taji ta kamu, sai ba'aja zancen da nisa ba, duk da dai da farko Ahalinta sunso su bada matsala kasancer AL_HAJI SAMEER LAMIƊO baƙar fata.

Amma daga baya komai ya wuce ansha biki.
Sai matar shi ta uku Hajiya Zuwairiya wacca ta kasance ƴar Mai Duguri Ita ma dai Babbar Likita ce.






  _AL_HAJI SAMEER LAMIƊO

Yaran sa biyar da Dr_Raheemah, huɗu  da Hajiya Zuwairiya Tara kenan.

Yunus shine Babba a kaf yaran gidan wanda ya kasance ɗa ne ga Dr_ Raheemah, sai kuma Zuwaira wacca ta kasance ɗiya ta biyu a gidan kuma ƴa ga Dr_ Raheemah.
Sai Yusuf ɗa na uku ga AL_HAJI SAMEER LAMIƊO, shi kuma ya kasance Hajiya Zuwairiya ce ta haife shi.



Sai Abubakar na huɗu shi kuma Dr_Raheemah ce ta haife shi, tsakanin shi da Yusuf sati ɗaya ne, domin kuwa a ranar sunan Yusuf Dr_ Raheemah ta haifa Abubakar.


Sannan sai Sameen na biyar wanda ya kasance ɗane ga Hajiya Zuwairiya.

Kana sai Sakeenah ɗiya ta shida ga AL_HAJI SAMEER LAMIƊO sannan kuma Dr_ Raheemah ita ce mahaifiya a gareta.

Sai Jawaheer ta bakwai da Jummai ta takwas waɗanda su kuma ƴaƴa ne ga Hajiya Zuwairiya, tsakanin Jawaheer da Jummai shekara ɗaya ne kacal, saiya  kasance Jawaheer ce Babba sai Jummai mai bi ma ta.

Sai Auta sagir yanda ya kasance gaba ɗaya gidan shine ƙarami, domin kuwa tsakanin shi dasu Jummai shekaru biyu ne, Dr_Raheemah ita ce mahaifiya a gareshi.

Sai ya kasance Yunus, Zuwaira, Abubakar, Sakeenah, Sagir. Sune Yara ga Dr_ Raheemah.


Yayinda ya kasance. Yusuf, Saminu, Jawaheer, Jummai. Su kuma sune Yaran Hajiya Zuwairiya.



Yaran AL_HAJI SAMEER LAMIƊO
Sun kasance kyawawan gaske na bugawa a mujalla ne, domin kuwa kaf cikin su babu munana tabbas {kuma dai masu karatu, You can imagery mana Yadda jinin Larabawa Hausa Fulani Kanuri e.t.c. zai kasance 😁. }



Gaba ɗaya Yaran sun taso da kyawu na musamman daɗin daɗawa gasu da wani abu da ya yi ƙaranci a wannan zamanin wato haɗin kai.

Suna ƙaunar junan su sosai, domin kuwa idan kai baƙone kazo gidan, to bafa zaka gane ga ɗan wannan ɗakin ba, musamman ma da ya kasance Yusuf da Abubakar a gurin Hajiya Harirah suke zaune, sai ka rantse ita ta haifesu, domin kuwa abin da take musu ko iyayen su mata da suka haifesu ko su iyakar abin da zasu musu kenan.








Sai dai wani abu duk, kyawun Yaran AL_HAJI SAMEER LAMIƊO, ba fa komai bane idan aka haɗa da kyawun Abubakar.


Domin wani irin madaran kyau ne dashi na musamman wanda kafin a sama mutum mai irin kyawun shi a wannan lokaci sai an tona.


Sannan kaf yaran AL_HAJI SAMEER LAMIƊO, shine son kowa ƙin mara sa'a, domin kuwa kowa a gidan har dama kaf Ahali son shi suke kamar me, domin Allah ya mishi wannan Farin jinin Sanadin haka har suna aka saka mishi a family da abokan shi suna kiran shi da 'MAI KYAU'  domin kuwa shi ɗin mai kyau ne.






Gaba ɗaya yaran gidan maza suna karatun degree ɗinsu ne a Birnin London, yayin da Yunus yake karantar Sociology ma'ana Ilimin hallayar zaman jama'a.



Abubakar da Yusuf kuma suke karantar £ntrepreneurship, ma'ana harkokin kasuwanci.


Sameen kuma yake karatun Likitanci ɓangaren Surgery.

Shi kuma Auta Sagir yana karantar Biology ma'ana Ilimin halitta.



Matan kuwa a ƙasa Nigeria sukayi karatun su a wancan lokacin, Yayin da Zuwaira da take Babba ta gaji mahaifiyar su Dr_ Raheemah, tana karatun Likitanci ita ma a Babban University dake Jigawa State na wancan lokacin.



Sai kuma Jawaheer ƴar qwalisa ita Fashion and Love affair's take karanta.
Sai Jummai da Sakeenah suna karatun Likitanci suma ɓangaren E.N.T.


A haka rayuwa ta ci gaba da lulawa, har bikin Yunus Babban Yaya da kuma matan gidan duka Zuwaira, Sakeenah, Jawaheer, Jummai ya taso.





_

Yayinda da Yunus zai aura Yaganah ɗiyaga ƙanwar Hajiya Zuwairiya auren soyayya, Zuwaira kuma zata aura wani ɗan unguwan su mai Suna Jamil wanda tsohuwar soyayya ce domin kuwa tun suna yara suke son juna, ita da shi Jamil ɗin ɗa ga Alhaji Jalaludeen Aboki ga AL_HAJI SAMEER LAMIƊO.



Sai Sakeenah wacca ita kuma wani ɗan Adamawa State zata aura ɗa ga Yayan Hajiya Harirah, Auren muna son junan mu.🥰



Sannan Jawaheer da Jummai suma duka anan Jigawa State mazajen da zasu Aura suke suma duka Auren so da ƙauna ne.


Haka akasha shagulgulan biki aka gama lafiya, daganan kuma aka kai amare ɗakunan mazajensu.


Shi kuma Yunus ya ɗauki amaryarsa Yaganah ya wuce da ita ƙasar France inda ya sama aiki a ofishin jakadancin Nigeria dake a ƙasar.




Haka Rayuwar ta ci gaba da tafiya, har Abubakar da Yusuf harda Sameen suka kammala karatun su, ya rage saura Sagir ya kammala.






Wata Ranar Saturday zaratan samarin Ƴaƴan AL_HAJI SAMEER LAMIƊO..!  suka sauka a ƙasa Nigeria, anan international airport dake Jigawa State.


Basu faɗawa kowa a gida dawowarsu ba, sai dai kawai ganin su akayi gida, a lokacin AL_HAJI SAMEER LAMIƊO. An fara tara jikoki ta wajen su Zuwaira bayan haka ma tsufa ya fara zuwa ba laifi.



Haka akasha murnar dawowar su sosai, barin ma dai Hajiya Harirah kamar ta goya twin's ɗinta kamar yadda ake faɗa Abubakar da Yusuf dan murna kamar me.





___
Satin su Abubakar ɗaya da dawowa Nigeria zuwa lokacin Abubakar ya sama aiki a Abuja. Yayin da Sameen ya samu a Lagos.
Yusuf kuma a Mai Duguri ya zaɓa ɗaya daga cikin company na AL_HAJI SAMEER LAMIƊO.
Zai ci gaba da kula dashi acan Mai Dugurin wannan abu ba ƙaramin daɗi Yayiwa Hajiya Zuwairiya ba.


___

Wata Ranar Saturday gaba ɗayansu jama'ar gidan suna zazzaune a palon gidan, hadda su Zuwaira, Sakeenah, Jawaheer, Jummai da suka zo ganin gida da Yaran su.
Yunus ne kawai babu da ya ke yana zaune a France ne, da Iyalanshi.





Ana cikin fira sukaji Door Bell, Sakeenah ce ta miƙe, taje ta buɗe don ganin waye.




Galala ta tsaya tana kallon kyakyawan matashin saurayin dake tsaye gabanta. Yana sakar ma ta murmushi jikin shi sanye cikin t-shirt Red color and trouser jeans Ash color. Ya ɗaura rigar sanyi a saman t-shirt na jikin sa, ga sumar kanshi mai tarin yawa a waje baisa hula ba.



Da sauri yayi throw away da trolley ɗin dake hannun shi, bai tsaya komai ba ya rungumota yana faɗin, "Yayi kewar su baki ɗaya,"

Da sauri Sakeenah ta tureshi daga jikinta tana dariya ta ce "Haba Sagir kai baka girma ne wai, ai sai ka shigo daga ciki."

Tayi maganar tana ɗaukar trolley ɗinshi da ya jefar


Gaba ɗaya mutanen dake zazzaune a palon suka mimmiƙe tsaye, suna kallon Sagir cike da mamaki, shi kuwa ko'a jikin shi sai ma ƙarisawa da ya yi ya ɗauki jaririn Jawaheer yana mishi wasa.





Yusuf da mamaki ya ɗan sake shi, ya buɗe baki yace




"Kai kuma daga ina haka?."



 Juyowa sagir ya yi yana kallon su gaba ɗaya, da sauri ya ƙarisa ya rungume AL_HAJI SAMEER yana faɗin


"Abbhee.! ka gani ko wato Ƴaƴan ka basa ƙaunar Autarta, duka suka gudo Nigeria suka barni.

Shine nima kawai na gudo nan, kaga sai na ƙarishe karatun anan, tunda na kusa kammalawa."


Yayi maganar hankali kwance yana zama a kujera.




Suma komawa sukayi suka zazzauna sai kuma aka shiga gaisawa, bayan komai ya lafa Zuwaira ta kalla Sagir tana cewa

"Uhum munaji sai kuma akai mene, kawai ka ɗauko ƙafa ka dawo gida, yanzu me kakeso ayi maka?."



Kai tsaye ya bata amsa da

"Aure.!"


Gaba ɗaya palon suka zubo mishi ido suna kallo, Dr_Raheemah ta kalleshi da kyau, tayi murmushi sai dai bata ce komai ba, dan ita macece mara san hayaniya sosai.




"Kaga naka, nace ungo naga kaji?."

Cewar Sameen yana jefa mishi daƙuwa. Su kuwa Abubakar da Yusuf mamakin ƙanin nasu ya hanasu magana.





Dariya Sagir ya yi yana ciro phone ɗinshi a trouser pocket, sai da ya ciro sannan ya lalubo wani picture na wata matashiyar budurwa.



Ɗaga wayar ya yi a tsakiyar palon yadda kowa da kowa zai gani, sannan Yace
"Ga ta sunanta Suwaiba Ƴar Kano ce, karatu ya kai ta London, shine muka haɗu acan muka fara soyayya fa, nikuma naji ina son Aure shine kawai na yanke shawarar na sameku na faɗa muku, a domin aje Kano a nemomin aurenta."

Yana maganar ne yana kuma musu zooming na picture ɗin ta yadda zasu gani yadda ya kamata.




Baki sake wannan karon gaba ɗaya suke kallon shi, sunma kasa magana dan mamaki.

Miƙewa Yusuf ya yi ya ƙarisa wurin da yake, ya kamo hannun shi ya nufa ƙofa dashi, bayyima kowa magana ba.
Da sauri Hajiya Harirah ta ce "Ina zaka kaishi ne?."




Juyowa Yusuf ya yi yana kallon duka Ƴan palon kana ya yi murmushi kai tsaye yace
"Naga alamar ya sami mental illness. wannan ne dalilin da yasa zan kaishi psychiatric hospital, kinsan akwai wani friend ɗina acan, sai ya taimaka ya duba mana lafiyar shi, idan akwai mai zuwa a cikin ku falil lahil hamdu sai yazo mu tafi, tun kafin abin nashi ya yi nisa fa."


 Yayi maganar yana gimtse dariya.
Miƙewa Jawaheer tayi tana faɗin

"Allah sarki Autar mu. Ashe shiyasa naga yana abu kamar wanda baya a cikin hankalinsa. Ashe kuma imagine da nakeyi ne ya zama gaskiya, aikuwa muyi sauri Yah Yusuf dan kasan yamma ta fara, kar su tashi a hospital ɗin."🤣




Ita ma tayi maganar tana ɗaukar handbag ɗinta da jaririyarta a hannu. Kamar da gaske.






Ganin dai da gaske suke kallon mahaukaci suke mishi, yasa ba shiri ya qwace hannun shi daga cikinna Yusuf.
Ya ruga wajen AL_HAJI SAMEER ya zauna kusa dashi yana faɗin

"Allah Abbhee. waɗannan yaran naka ba sona sukeyu ba, kana dai gani wajen psychiatrist zasu kaini fa."  Yayi maganar cike da shagwaɓa.




Su kuwa mutanen palo mai zasuyi idan ba dariya ba, aikuwa nan suka shigayi babu qaqqautawa Happy family 🤪.



Bayan sunyi shiru aka ci gaba da fira Abubakar ya kalla Sagir yace "Au yanzu haka zaka zauna ba za ka shiga ɓangarenka ka huta ba?."




Dariya Sagir ya yi sannan ya dawo ƙasa ya zauna, yana kallonsu gaba ɗaya kana yace


"Kun san wani abu kuwa?."



Duk a tunanin su wani abun kirki zai faɗa.
Saboda haka duk suka haɗa baki wajen cewa
"A'a sai ka faɗa."

Jummai ta gyara zama tana faɗin "A'a ƙaninmu sai ka faɗa, sannan zamu sa ni.'



Murmushi ya yi sannan yace "Da gaske nake fa, Allah Aure nakeso, wannan ne ma Babban dalilin da ya sa na dawo."


Sakeenah ta ce "Kai Sagir yanzu a gaban su Hajiya da Abbhee kake wannan maganar, bakajin kunya, daɗin daɗawa ga yaranka a wurin fa."😅

Tayi maganar tana mishi nuni da ƙananan yara dake palon, ƴan dugui dugui dasu, su na wasannin su.


Murmushi ya kumayi yace "Aha to ai wannan dalilin ne ma yasa nake maganar a gurin, saboda naga suna wurin, kawai dan bakuga Suwaiba ta ba ce, da sai kun fini ƙosawa na Aureta kafin wani yamin snatching ɗin ta."😎




Ko kunya babu yake maganar yana kuma nuna musu pictures kala kala na Suwaiba, zai kuma magana kenan.

Sameen ya ɗauki cushion na sofa ya jefa mishi yana faɗin

"Yi mana shiru ɗan nema baka da kunya ko kaɗan, gashi kaje London ka kuma koyowa salo salo."





Dariya kawai Sagir ya ke yi yana faɗin "Wallahi Yah Sameen kai ma kasan yadda London ɗin nan take, gaba ɗaya sun mayar da bawan Allah kamana kullum sai dai nayita ɗaukar azumi fa kuma....!"



"Au badai zakayi shirun ba ko, ka ci gaba ne ko?."

Cewar Sameen yana dariyar "Tu no wani drama da ya taɓa faruwa tsakanin Sagir da wata Baturiyar London 😍.



Sagir ya kalla duka mutanen palon yana faɗin

"Kunga ni ko tunda kukaga yana dariya shima Auren yakeso, saboda haka kawai a haɗamu dasu Yah Yusuf ayi lokaci guda."




Tashi Sameen ya yi daga zaunen da yake ya nufa Sagir zai kama ya naɗa.

Ai da sauri Sagir ya miƙe tsaye yana faɗin "Yah Sameen na fa taimaka maka ne, tunda naga kanajin kunyar faɗa fa."

 Ya yi maganar yayin da suke zagaye palon shi da Sameen yana binshi zai kamo ya daka, shi kuma yaƙi bari hakan ta kasance, sai faman zagaye ƙaton palon suke cike da farin ciki kamar wasu ƙananan yara ko dama ba wasu shekaru na azo a gani bane a tsakanin su.





Saminu ganin Sagir wahalar dashi kawai yake ba tsayawa zayyi ba, yasa shi ya koma ya zauna yana faɗin

"Tunda haka ne sai na faɗa, kowa ya sa ni."

Sagir dake can gefa tsaye yana sauke haki yace

"Ka faɗamana so what.?"



Sameen yana dariyar mugunta Yace "Kai kyakyawar African Nigeria ka ce na faɗa komai ko?."


Jin abin da Sameen yake cewa ai Sagir bai san lokacin da ya yi wata super ba, sai gashi a gaban Saminu ya rufe mishi baki da duka hannayen shi, faɗi yake


"Haba my Yah Sameen ba kace ba zaka faɗawa kowa ba, indai ni ne na dena maganar Aure indai ba zakayi wannan maganar ba, to daga yauma zan dinga kiranka da YaYah Sameen shikenan, daga Yau haka zan dinga kiranka kaji ko my Yah Sameen?."



Gaba ɗaya Sagir Yana maganar ne a ruɗe tsoron shi Allah kar Sameen ya faɗawa su Abbhee dasu Yah Yusuf abin da ya taɓa faruwa a tsakanin shi da wata Baturiyar London.🤣




Murmushi kawai AL_HAJI SAMEER LAMIƊO. Yakeyi ganin yadda family ɗinshi suke cike da farin ciki, ga haɗin kai, wannan ya nuna mishi kenan ko da bayan ranshi Ahalinshi ba zasu tarwatse da rashin zumunci ba.


Kallon matan shi dake zagaye gefan shi ya yi yana kuma sakin murmushin nishaɗi can cikin zuciyar shi kuwa tasbihi yake yana kuma godiya ga Allah da ya azurtashi da wannan kyakyawan Ahali abin kwantance fa ɗin Birnin Jigawa State dama ƙasa Nigeria baki ɗaya hadda ƙasashen waje.😘
 
*SARAUNIYAR KYAU*💓

          
   _(The Glam Queen)_ 👑
       
         ```Takun Farko```

Story & Written By:

              *_The Nainarh KD_*


____________________________________________👑

*THE ONGOING BOOK'S*


 1. *SONKI NE ƘADDARA TA*
 
          MALLAKAR
FATIMA ABDULLAHI
          _Batool Kamba_





 2.  *ZAN JIRA KA*

        MALLAKAR
     A'ISHA ALƘALI
         _Mrs Aysib_





___________________________________________👑


Page*49&50*



Sameen dai ganin Sagir ba kyaleshi zayyi ba, yasa shi ɗa ga hannu alamar surrender.


Ganin haka yasa Sagir ya koma tsakiyar palon ya zauna yana faɗin

"Amma Yah Sameen nagode sosai dan kuwa idan ka faɗa bansan ina zankai kunya ba Allah kuwa "


Ya yi maganar yana dariya sosai, shima dai Sameen dariyar yakeyi.



"Wai wannan wata kalar magana ce, da ba'a so muji ne?."


Cewar Zuwaira cikin murmushi, "Kedai bari, wata ƙila ba gaskiya a lamarin tunda kikaga yaƙi bari a faɗamana muji."





Jummai ta amshe zancen ita ma fuskar ta washe da farin ciki.

Abubakar ne yace "Tunda dai ba'a so muji shikenan mun haƙura, idan tayi wari maji ai."



Haka suka ci gaba da fira cikin fahimtar juna da maɗaukakiyar ƙaunar junansu, can wajajen magarib mazajensu Jawaheer suka zo suka ɗaukesu suka koma gida bayan sun shiga ciki an gaggaisa.





_____👑





Rayuwa ta ci-gaba da tafiya tana lulawa da mutane cikin ƴan watanni da suka gabata, komai ya daidaita Abubakar ya koma Abuja da zama, domin kuwa a can yake kula da companies na AL_HAJI SAMEER LAMIƊO.


A yayin da shi kuma Yusuf ya wuce Borno State shima ya fara gudanar da.
S.L__ GROUP OF COMPANIES dake can BORNO STATE.


Shima Sameen ya yi nashi gurin Lagos yana gudanar da aikin na shi Likitanci a Babban Asibitin ƙasa dake Birnin Lagos.

Tuni aka saka ranar bikin Sagir da kyakyawar shi Suwaiba sakamakon yadda ya qwazzaba shi fa aure yake Buƙata, harda kwanciya rashin lafiya na ƙarya, duk dan saboda ah farko AL_HAJI SAMEER LAMIƊO Yaƙi Yarda, haka dole ba yarda aka saka ranar bikin nashi da Suwaiban shi, wacca ta kasance ɗiya ga Alhaji Saleh Sama'ila a Birnin Kano ta Dabo koda me kazo anfika Aha, wanda take cikin AREWA cin Nigeria yankin Africa.






Sameen shima da zankaɗeɗiyar shi Sadeeyah wacca ta kasance ƴar Gombe State ce ita, sai Yusuf da tashi gwanar Yusra ƴar asalin Kaduna State garin governor, mazauniyar Borno State.


Kaf cikin su Abubakar ne kawai bandashi a auren, shima dai lokacin da aka zaunar dashi ana tambayar shi ko yanada tashi gwanar, sai cewa ya yi bai isa Aure ba ai.🤣




A lokacin dariya AL_HAJI SAMEER da ƴan uwanshi maza biyu dake wurin sukayi, sannan Alhaji Yahya da yake Yaya a gurin AL_HAJI SAMEER LAMIƊO.


Yace "Abubakar kenan ai shi Aure da kake ganin shi lokaci ne dashi, idan lokacin ya yi kai da kanka zaka nememu, amma tunda yanzu kace baka isa auran ba, mu zamu baka lokaci nanda watanni biyar, ka ga lokacin ya yi daidai da Auren su Yusufa wata biyu da yi kenan, tunda wata uku aka saka, lokacinzamu sameka da magana idan lokacin ya yi kace mana baka samu ba.  Ka yarda mu aura maka ko wacece?."






Murmushi Abubakar ya yi sannan cike da girmamawa Yace "Na amince Alhaji sannan ina godiya."


Murmushin manya kawai sukayi sannan aka ƙulla Deal.


Rayuwa ta ci-gaba tafiya yayin da kullum kwanan duniya lokaci yake kuma raguwa, wanda hakan ke ƙara ƙarfin imani ga masu shi.




A can ɓangaren kuma hakan ya yi daidai da saura sati biyu, bikin mutane uku daga Babban Ahali yara ga shahararren mutumin da duniya ke damawa dashi AL_HAJI SAMEER LAMIƊO Jigawa State.




Gaba ɗaya ɓangarori biyun shiri suke ba kama hannun yaro, ba ga dangin amare ba, haka zalika baga dangin angwaye ba, shirin shan shagalin biki ake sosai waɗannan suna nunawa waɗancan wane ku ta fannin mutunta juna da nuna abin Alkhairi ga juna.




Lokaci naja sosai har aka wayi gari a ranar wata laraba, an ɗaura Auren Sagir Samir Lamiɗo, da zankaɗeɗiyar amaryarsa Suwaiba Saleh Sama'ila a Birnin Kano ƙarfe sha ɗaya na safe, Auren da ya sama hallartar duban jama'a na fa ɗin Nigeria dama wajenta.



Sai kuma Sameen Samir Lamiɗo, shima da tashi gwanar a Babban masallacin jumma'a na Birnin Gombe State, misalin ƙarfe biyu da rabi na rana.



Sannan Yusuf Samir Lamiɗo, shima a Kaduna State ƙofar gidan mahaifin amaryar sa Yusra, Alhaji Nazir Sani Sidi, misalin ƙarfe huɗu da rabi na yamma aka ɗaura Auren.



Daganan kuma ƴan ɗaurin Aure da kuma matan da sukazo tare, aka wuce da amarya Yusra Jigawa State wurin dangin ango, kafin daga baya ita da angonta su wuce Borno State wurin da yake zaune.





Sun isa Jigawa State can cikin dare wajajen ƙarfe sha ɗaya, dan haka ba'a tsaya jiran komai ba, aka musu tarba na ban girma sannan aka saukesu a masauki ɓangarena musamman.



Washe gari da ta kama Alhamis sannan kuma ranar cikan biki, aka tashi da sabon shagali wanda aka nuna ainihin al'adar mutan garin, ansha shagulgulan biki sosai kuma jama'a da dangin amare sun ƙayatu matuƙa.
Sai da aka kwashe kwanaki uku ana shan shagulgulan biki sannan komai ya lafa.




Zuwa rana ta biyar da bikin, gaba ɗaya jama'a sun watse gida ya rage daga amare da angwayen su sai kuma surukai iyayen angwaye.



Zuwa dare bayan isha'i Alhaji Samir Lamiɗo, da matan shi Hajiya Harirah da Dr_Raheemah da kuma da Hajiya Zuwairiya.


Gaba ɗaya suna zazzaune a ƙaton palon gidan, wanda ya gaji haɗuwa yasha kayan more rayuwa kala kala abin ba'a magana sai wanda ya gani.


Sai ga Yusuf ya shigo amaryar shi na take mishi baya, fuskar ta lulluɓe da lufaya mai shigen kayan jikinta, wuri suka samu daga can gefe a ƙasa, suka zazzauna, sai ga Sameen shima da tashi amaryar sanye cikin shiga kala ɗaya suke, ita himar ne dogo har ƙasa a jikinta, wuri suma suka samu suka zazzauna Sameen kusa da Yusuf yayin da da amaryar shi ta zauna kusa da Yusra matar Yusuf suma suka gaggaisa dasu Hajiya Zuwairiya.



Can sai ga Auta Sagir da kyakyawar amaryar sa Suwaiba suma sun shigo bakinsu ɗauke da sallama cikin shiga iri ɗaya, suka shigo sai faman baza ƙamshi da gyalli irinna amare sabbin suke.🥰





Kusa da Alhaji Samir Lamiɗo  Sagir ya ƙarisa ya zauna, ganin hakan yasa Suwaiba ita ma ta ƙarisa wajen su Sadeeyah ta zauna tana Suna sakarwa juna murmushin yaƙe na rashin sabo.




Buɗe taro akayi da addu'a sannan AL_HAJI SAMEER da matansa suka shiga jero nasihohi akan zaman Aure da ladan dake ciki, muddin za'a daure ayi haƙuri to akwai riba a gaba, domin shi Aure akwai farin ciki a ciki sannan kuma akwai akasin hakan, daga ƙarshe dai aka kuma rufe taro da addu'o'i sannan aka sallami kowa.











WASH£ GARI

Gaba ɗaya amare da angwaye duk suka watse yayin da Yusuf ya yi Borno State da matar shi.


Sameen kuma ya yi Lagos da nashi matar, su kuma Sagir da Suwaiba amarya sai wajen ƙarfe shida na yamma sannan suka bi jirgi izuwa London domin su a can ɗin zasu ƙarishe karatun su.




Gida ya rage daga Abubakar wanda shi sai zuwa gobe zai wuce Abuja, sai kuma sauran jama'ar ciki suma dai su Zuwaira, Jawaheer, Jummai, Sakeenah  waɗanda sukazo rakiya ga angwaye sai zuwa dare duk suka koma gidajen su cike da kewar ƴan uwansu.





*AURE KENAN*







 




*WASH£ GARI*





Shima Abubakar mai kyau 😁

Yabi jirgin Safe izuwa Babban Birnin Nigeria Abuja City.



Da isarsa Abuja ya ɗaura da harkokinsa daga inda ya tsaya, sam baya ma saka maganar Aure a ranshi, domin kuwa ba shine a gabanshi ba, a halin yanzu Babban abin da ke gabanshi, shine gudanar da Aikin shi cikin nasara da kuma kyautatawa na ƙasa dashi.




_*
Rayuwa ta ci-gaba da tafiya tana lulawa da mutane cikin sauri sauri lokaci ke wucewa.

Har aka kwashe tsawon watanni biyar gaba, cikin lokacin harkoki sun ƙara buɗewa Abubakar Mai Kyau ta ko'ina kuɗaɗe shigowa suke yi gare shi, dama kuma akwai su waɗanda ba'asan a dadi ba ma, sunan Abubakar Mai Kyau ba iyaka family da Abokan shi waɗanda suka saka mishi sunan ya tsaya ba, a'a sunan Abubakar Mai Kyau ya zagaye gaba ɗaya ƙasa, harma da wajen ta.




Abubakar Mai Kyau shi sam yama manta da wata Agreement dake a tsakanin shi dasu Alhaji Yahya akan batun Aure, gaba ɗaya yafi mayar da hankalinshi akan gina gobenshi.


Wata Ranar Saturday da ta kasance weekend yana kwance saman 3sieter a dake ƙaton palon shi, yana tunanin yanayin Rayuwa ya yi nisa sosai.


Yaji ƙarar ringtone na wayar shi dake saman center table, cike da kasalar da baisan ta miye ba, ya miƙa hannun shi na dama ya ɗauki wayar, ba tare da ya duba mai kiran ba, domin kuwa idanun shi a rufe suke ruf ya yi picking call din, Sannan ya yi sallama a kasalance.



Bai san lokacin da ya miƙe daga zaune ba, ƴan sauran baccin da yakeji da kasala, gaba ɗaya ya nemesu ya rasa.

Cikin tsananin girmamawa da ladabi yake gaisar da mahaifin shi da ya kira wayar. Tamkar yana a gaban shi, cike da ladabi ya amsa da
"To Abbhee Insha Allah nanda gobe ina hanya."

Yana faɗan hakan sukayi sallama ya kashe wayar.


Aje wayar ya yi gefe sannan ya yi tsuru, yana tunanin abin da zaisa mahaifinsa ya mishi irin wannan kiran na gaggawa,  Amma duk iya tunanin shi bai hasaso komai ba, dan haka miƙewa ya yi ya koma Bedroom tun a lokacin ya fara shirya shirye domin zuwa gobe ya wuce Jigawa State.

 



__WASHE GARI
    

JIGAWA STATE__



Ƙarfe ɗaya na rana tayi mishi a ƙofar gate na gidansu, horn driver ya yi, gate man ya wangale gate sannan slowly jerin motocin suka shiga cikin gidan.

Sai da driver ya daidaita zaman motar a filin ajiye motoci na gidan, sannan Abubakar ya fito jikin shi sanye da suit Ash color, ciki ya shiga yayin da escort ɗinshi suka tsaya a waje.



Wurin Hajiya Harirah ya fara zuwa mariƙiyar sa, bayan sun gaisa sannan ya wuce gurin mahaifiyarsa Dr_Raheemah, nanma sai da ya daɗe kana ya wuce Wurin Hajiya Zuwairiya, ita kam sunsha fira sosai, sannan daga ƙarshe ya wuce ɓangaren shi a gidan, domin ya huta kafin lokacin dawowar Alhaji Samir Lamiɗo ya yi.




*_*

Da yamma wuraren ƙarfe biyar Abubakar Mai Kyau yana zaune saman lallausar carpet, ya yi zaman cin tuwo yayin da ya yi tsit ya mayar da gaba ɗaya hankalin shi yana sauraron nasihar da mahaifinshi ke mishi.

Sai yanzu ma da Abbhee ya ɗauko mishi wannan maganar sannan ya tuna dalilin kiran da aka mishi zancen dai ɗaya ne shine maganar Aure.!






Ɗan ɗagowa ya yi ya saci kallon mahaifinsu jin tambayar da ya yi masa


"Wai ina matar Aure?."

Sai kace matan a rami ake samowa, cikin ƙasa da murya yace "A'a Abbhee har yanzu dai bansamu ba, ina dai lalube cikin duhu ne."



Murmushin manya Alhaji Samir Lamiɗo, ya yi sannan yace "Abubakar kenan to ai ita mace rufe ido kawai ake a lalubo, idan ba haka ba sai dai ka ƙare a tuzuru baka sani ba."



Ƴar dariyar da bayyi shirin yi ba ne ta kufce masa kana ya amsa da faɗar "Abbhee da gaske nake, ko budurwa ban taɓa yi ba."🙃



AL_HAJI SAMEER yace "Kenan dai kana nufin kace ka amince ni na zaɓa maka wacca ta cancanta, da kai ko?."


Cike da ladabi Abubakar ya amsa da "To shikenan Abbhee na amince, Allah ya zaɓa mana abin da yafi alkhairi a garemu."


Cike da alfahari Alhaji Samir Lamiɗo, yake kallon yaron nashi kana ya amsa mishi da "Ameen.!"



To daga nan dai maganar tasu ta tsaya, dama ita ce mussababin haɗuwar tasu a ranar zuwa bayan isha'i Abubakar ya bar Jigawa State ya dawo Abuja City, ya ci gaba da harkokin sa, cike da nasara, maganar Aure da mace kuma ya Aje a gefe ɗaya, domin kuwa shi a nashi ra'ayin har yanzu bai ga macen da ta masa ba, duk da dai akwai su kala kala da masu bibiyanshi, amma ko kallon kirki basu isheshi ba, abin da ya saka a gaba shine dai gina gobenshi a farko.

A yi maganar koma miye daga baya a cewar shi...





Ranar ta kasance Litini a gajiye ya dawo daga company dan haka bayan ya yi wanka ya huta, palo ya sauko ya zauna saman 3sieter yana karanta wani £nglish Book 'Nigerian Poverty.'


Wayar shi dake ajiye gefe ce, tayi ƙara alamar shigowar saƙo, ɗaukar wayar ya yi yana dubawa, saƙo ne daga Abbhee abin da ke cikin saƙon.


Da farko dai pictures ne guda biyu na wata kyakyawar matashiyar budurwa, ɗaya tana sanye cikin shigar Likitoci ta ɗaura Lab coat a saman kayan jikinta, babu hijabi a jikinta, sai wani Farin scarf da tayi rolling kanta dashi, tana murmushi.

Na biyun kuma tana a ɗakin kula da yara ne, cikin Asibitin da alama likitar yara ce, shima dai tana murmushi akayi hoton, sannan shima ba hijabi a jikinta, sai mayafi da tayi rolling dashi.



Kyakyawa ce Ajin farko, dan kuwa ta mallaki dukkan wani abu da ya kamata ace mace wacca ta amsa sunanta mace tana da shi, kuma da alama zatayi fara'a da kirki tunda gashi duka murmushi take lokacin da aka ɗauka pictures ɗin...😘




Murmushi ya yi yana shafa sumar kanshi mai tarin yawa, bawai yana murmushin kyawunta bane, a'a yana murmushin Abbhee ne, wato harda pictures dan karma daga baya yace "Ba ya yi, to wai yaushe ne Abbhee yasan ra'ayin sa, nason Auran mace Likita?.




Murmushi ya kuma yi sannan ya ɗauko wayar ya fara karanta rubutun dake a ƙasan pictures ɗin..

"Sunanta Rafi'atu Rafiq Rayyan.
Ta kammala karatun likitanci fanin pediatrics.
Yanzu ta kasance cikakkiyar likitar Yara sannan🩺.
Shekarun ta Ashirin da biyu, ita da Ahalinta suna zaune anan garin Abuja.

Mahaifin ta Alhaji Rafiq Rayyan, ya kasance Amini ne a gareni🤼.

Ga address na gidansu daga ƙasa 💒.

Zuwa gobe nakeso kaje ku haɗu da ita, bayan kun haɗun, idan kun dai dai ta, sai ayi tunanin shafa fahita. Domin kuwa ta mi ƙe za'ayi.
Ba batun wani saka rana da waye waye.
Ga Number ɗin ta, shima daga ƙasa.
Da Fatan zaɓinnawa zayyi maka. Ya ka Abubakar🤗
Saƙo daga Mahaifin ka mai ƙaunar farin cikin Ƴaƴan shi, a kullum💝.
Good look🙏."





Ya karanta wannan saƙo yafi a ƙirga, ba abin da yakeyi sai murmushi, wato dai iyaye iyaye ne, babu kamar su a kaf faɗin duniya, wanda ya kyautata musu ya huta.
To Allah yasa mu rabu da namu iyayen lafiya Ameen.🙏






WASHE GARI

Bayan ya dawo daga company, kamar yadda Abbhee ya buƙata shiryawa ya yi cikin shigar hausawa wanda ba ƙaramin kyau ya yi ba, sannan ya ɗauki mota shi kaɗai, ba tare da securities ba, ya nufa Address ɗin da ya gani, a saƙon.



Isar sa gidan keda wuya gate man ya wangale masa gate da alama ansan da zuwan sa.

Shigar da motar shi ya yi ciki sai da ya daidaita zaman motar a filin ajiye motoci na gidan, sannan ya fito yana ƙarewa ƙaton gidan kallo.
Gidan Babba ne sosai, mai ɓangarori uku, ga ma'aikata sai faman zirga zirga sukeyi.


Tunani yake shin ya lalubo wannan saƙon da Abbhee ya turo masa ne, don ya duba lambarta ya kira ta, ko kuwa ya tsaya jiran tsammani?.


Yana nan tsaye jin gine da mota, bai san abinyi ba, sai ga wasu kyawawan yara maza biyu mace ɗaya su uku waɗanda ba zasu wuce shekaru biyu a duniya ba, da alama Triple ne, ga wata kyakyawar budurwa tana binsu a baya yayin da su kuma suke faman gudu sunƙi bari ta kama su.





Hango mutum suka yi jikin mota, aikuwa ba tare da sun tsaya duba ko waye ba gaba ɗaya suka Ɗafalfale shi, suna dariya, bayan sun ƙarisa wurin.

Tsugunawa ya yi yana musu wasa shima domin kuwa akwai shi da son yara sosai.


Qarisowa wurin budurwar da ke binsu a baya tayi tana sauke haki, ta kira sunan ɗaya daga cikin yaran.



"Kai.! Aleem ƙariso wurina, kunga baƙone wannan, kar ku ɓata masa kaya ko.?"

Tayi maganar tana marairaice wa Yaran yayin da su kuma suketa faman ɓuya a wayanshi, suna ƙara ɗafal fale shi, suna dariya, ɗaya daga cikin yaran macen ta ce cikin gwarancinta

"Lah lah siz jaki jekemu e, idan ukazo urin ki."

 Ita ma yarinyar ta bata amsa tana kuma ɗafalfale shi.



Ganin Yaran ba zuwa zasuyi ba, yasa budurwar ta kalla baƙon dake tsaye gabanta, yana ta wasa da yaran abin shi gunin burgewa, cikin faɗuwar gaba mara dalili ta ce

"Barka dai Mister Mai Kyau, dan Allah ka shigo daga ciki, Auntie Rafi'at ɗin tana ciki fa."

Tayi maganar tana yunƙurin kamo Yarinyar amma ta kasa.



Murmushi Abubakar Mai Kyau ya yi sannan Yace
"Barta kawai, ba zuwa wurin ki zatayi ba, tunda tayi sabon Yaya a yau."


Ita ma tana murmushi ta kuma cewa "Am sorry Mister mai kyau, Yaran duk sunbi sun ɓata maka kaya, akwai su da ƙiriniya sosai."

Maganar take cikin kulawa da kuma nuna girmamawa a gare shi.



Abubakar Yace "Ai Yaran kenan, karki damu kinji 'precioso'."


Da sauri ta ɗago tana kallon sa duk da ba jin yaren Spanish take sosai ba, amma ta fahimci sunan da ya kira ta dashi yanzu wato *KYAKKYAWA*


Murmushi tayi da ya bayyana kyakyawan dimples ɗin ta sannan ta ce "Shigo ciki please, na barka a rana kayi haƙuri fa."


Gaba tayi yabi bayanta, du ka hannayen shi riƙe dana Ƴan uku sunƙi bari ya yi ko nesa dasu, kamar dama can sun saba dashi ne.


Palon baƙi ta kai shi sannan ta fita, bata daɗe ba, ta dawo da Tray a hannunta saman Tray ɗin, an rufe da wani ƙayataccen gyalle Like a Indian People.🤔



Saman center table ta aje sannan ta kamo hannun Yarinyar suma sauran ta kamo da wayau da dabara, kana ta kalle shi cikin murmushi take faɗin "Am sorry Mister Mai Kyau ga Auntie Rafi'at ɗin nan ta kusa ƙarisowa."


Ah maimakon ya bata amsa, sai ya tsinci kanshi da faɗin "Por favor! cuàl  esta vuestra nombre.?"

Ma'ana  { "Please! what is your name?."

"Dan Allah! Menene sunan ki?." Da Hausa kenan, shi kuma da Spanish ya ma ta maganar.





Kallon sa tayi da kyau, tana mamakin abin da zai sa ya dinga ma ta harshen Spanish bayan kuma Hausa take masa.

"To kodai yasan a ƙasar Spain nayi karatu ne?."



Ta tambaya kanta sai kuma ta share, bata kawo komai ba a ranta cikin sakin fuska ita ma ta bashi amsa da


"I'm Haleesat Rashid Rayyan."



Tana faɗin haka ta nufa ƙofa zata fita, sai kuma ta tsaya a hankali ta juyo zata saci kallon sa, aikuwa karaf suka haɗa ido, ai a tamanin ta ƙarishe fi cewa daga palon hartana buge kanta da ƙofa.





Ajiyar zuciya Abubakar ya sauke yana jin bugewar da tayi kamar shi ne ya buge, shafa sumar kanshi ya yi yana sakin murmushin da bai san dalili ba.


"A ah kai Mister Mai Kyau.! dakata mana da wannan Nonsense tunanin, wai wannan 'Babe" ɗin ba ƙanwa bace a wurin Yarinyar da kazo gani bane?."

"Eh mana haka ƙanwar Yarinyar da nazo gani ce."

 "To me yasa kake ɗarsa wa zuciyar ka tunanin ta bayan ta kasance ƙanwa ce, ga Yarinyar da ake shirin Aura maka?."

"Ni ma dai bansani ba."😞

"To dakata, tukunna wai ma, me yasa naji ita wancan Yarinyar da nazo wurinta an kira ta da Rafi'at Rafiq Rayyan. Ita kuma wannan ta kira kanta da 'Haleesat Rashid Rayyan'.  Toh yanzu wacece ta kasance Asalin Ƴar gidan kenan?."🤨






Duk wannan uban surutun shikaɗai yake abin shi, a can cikin zuciyar shi, shi da zuciyar ta sa.🤣🤣

Ajiyar zuciya ya kuma saukewa sannan a fili yace

"Ooho dai."


Ciro tsadar diyyar wayarsa ya yi a aljihun doguwar Rigar shaddar dake jikin sa, ya fara latsawa a hankali.



Wani ƙayataccen ƙamshi ne ya fara baƙuntar hancin sa, sannan wacca ta kasance mamallakiyar ƙamshi ta bayyana.

Shigowa palon tayi bakinta ɗauke da sallama.
Amsa ma ta ya yi ba tare da ya ɗago kansa daga kan phone dake a hannun sa ba.




Wuri ta samu a kujerar dake fuskantar sa, ta zauna sannan cikin kashe murya ko kuwa dama can haka muryar take ohoo ta ce "Good afternoon Mister Mine Mai Kyau."🤓






Bai amsa ma ta gaisuwar da take antayo masa ba, sai kallon da yake ƙare ma ta ta ƙasan idanu.
"Yes she is so very Beautiful, domin kuwa ganin ta a fili yafi ganin ta a pictures, kyakyawa ce sosai fi ye da tunanin mai tunani, ba za'a kira ta da siririya ba, haka zalika bata da ƙiba na azo a gani, tana tsaka tsaki ne. Yanayin fuskar ta kuma is normalcy circle, domin kuwa bata da fa ɗin fuska, haka ma fuskar ta ba tsayi, tana nan dai ba yabo balle kuma 🤫.


https://whatsapp.com/channel/0029VaEZtE15a2429vfcpf20




*SARAUNIYAR KYAU*💓

          
   _(The Glam Queen)_ 👑
       
         ```Takun Farko```

Story & Written By:

              *_The Nainarh KD_*


____________________________________________👑

*THE ONGOING BOOK'S*


 1. *SONKI NE ƘADDARA TA*
 
          MALLAKAR
FATIMA ABDULLAHI
          _Batool Kamba_





 2.  *ZAN JIRA KA*

        MALLAKAR
     A'ISHA ALƘALI
         _Mrs Aysib_





___________________________________________👑








Page *51&52*




Tana sanye ne cikin doguwar riga ƙirar Saudiya, fara mai adon stones ash color, tayi rolling kanta da veil fari, fuskarta kuwa tasha light make-up, ta fito sak Shilpa Shetty Indian Actress, sai faman baza ƙamshi takeyi.



Ganin da tayi kamar bai ji abin da take faɗa ba. Yasa ta kuma kashe murya cike da kwarkwasa da kisisina ta ce



"Mister Mai Kyau good afternoon."



"Barkan ki, ya kike, ya gida?."


Ya tambaya ba tare da yana kallon ta ba.

Qara kashe murya tayi cike da yanga ta amsa da "Ina lafiya ina. Fatan kaima hakan?."


Ah maimakon ya Biye ma ta su ci gaba da fira, kamar yadda ya fahimci tana buƙata, a'a sai ma tambayarta da ya yi da faɗin.



"Ya kuke da ita?."


"Ita wa, kenan?."

Ta tambaya da mamaki



Ɗan jim ya yi sannan yace "Haleesat Rashid Rayyan..!"


Zaro ido tayi waje bata san lokacin da ta saki asalin munafukar muryar ta ba, tana cewa.
"Wata Haleesat Rashid Rayyan ɗin ke nan?, ni bansan ta ba..."



A je wayar dake a hannunsa ya yi a gefe, bayan ya kashe, sannan ya ɗa go aslowly yana kallon ta, ya ƙura ma ta manyan fararen idanunsa yana kallon ta bai ce da ita komai ba.





Ganin irin kallon da yake ma ta da fararen idanunsa yasa ta hau kama kame cikin ɗan daburcewa ta ce "Uhmm Au wai ita Haleesat.! kake nufi?."

"Eh sunanta 'Haleesat Rashid Rayyan' kamar yadda ka faɗa mahaifin ta ƙanine a gurin Daddyn mu, tun tana ƙarama ta rasa iyayenta, sanadin hatsarin mota, a wurin Mamyn mu ta taso, saboda ba'asan a salin mahaifiyar ta ba da ya ke TUBABBIYA ce, shiya sa muka taso tare a nan gidan mu, kafin daga baya ta wuce Spain karatu.
Shekarunta Ashirin da ɗaya ƙanwa ce a wurina, tayi karatun Likitanci fanin Dentist, wannan shi ne taƙaitaccen bayani akan ta."




Tana faɗin haka tayi shiru domin taga yadda Reacted nasa zai kasance, sai dai bata ga komai saman kyakyawar fuskarsa ba, sai ma miƙewar da ya yi yana kallon agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannun shi.



Ita ma ta miƙe ta marairaice murya kamar mai shirin kuka tana faɗin "Please Mister Mai Kyau ka ɗanci wani abu mana, kaga idan baka ci ba muda su Haleesat ba zamuji daɗi ba sam."


Bai san me yasa ba, amma tana kiran sunan Haleesat ya tsinci kanshi da sakin murmushi sannan a hankali cikin nutsuwa ya koma ya zauna, amma bai ce ma ta komai ba.
Ganin haka yasa tayi murmushin gefan baki sannan ta ƙarisa wajen Tray ɗin ta ya ye gyallen da aka rufe saman da shi,  sannan tayi saving ɗin shi a plate, meat balls and potato sauce, ɗayan plate ɗin kuma ta saka masa fish and boiled eggs sauce, sai kuma savoury stuffed Yam balls a wani plate daban, sannan kuma ta zuba masa zoɓo wanda yasha kayan haɗi a glass cup.



Kallon shi tayi cikin ƙayataccen murmushi ta ce "Mister Mai Kyau please Bismillah."


Tayi maganar tana masa nuni da saman center table, sannan ta koma ta zauna kana ta zuba masa ido kamar ta sama television ko gajiya babu.


Shi kuwa kaɗan ya tsakura, daga tilin uban abinci da ta jide a gaban shi, cokali ɗaya biyu ya yi sannan ya kora da juice yasha ruwa kana ya goge bakinsa da tissue.

Miƙewa ya yi tsaye yana kuma kallon agogon hannun shi, lokaci yaja sosai shikuma idan akwai abin da yafi bawa muhimmanci fi ye da komai na Rayuwarsa to shi ne lokaci.


Kallonta ya yi fuska a tsume yace "Ina ga kiyiwa Mamy magana, domin na shiga mu gaisa."


Da sauri ta miƙe tsaye ita ma tana faɗin "Okay Mister Mai Kyau."



Sannan ta fita zuwa wani lokaci ta dawo fuskar ta washe da murmushi ta ce "Za ka iya shiguwa."


"Okay."

Ya furta saman laɓɓansa.
Kana yabi bayanta suka shiga ƙaton palon da ya gaji da kyau da haɗuwa.

Cikin mutunci suka gaisa da Hajiya Zinaru wacca ta kasance mahaifiyar su Rafi'at.


Har wajen Mota ta rako shi bayan sun fito sallama suka yi sannan har zai shiga motar sa, sai kuma ya fasa ya juyo ya kalleta tana tsaye inda take.

Hannu ya zura cikin trouser pocket ya ciro bundles na ƴan ɗari biyar biyar ya miƙa ma ta.
Ƙin karɓar tayi, sai ma cewa da tayi "Ka barshi kawai, iya abincin ma daka ci ya wadatar."

Murmushi ya yi wanda tunda suka haɗu fuskar shi a tsume take, sai yanzu ya yi murmushi wanda ya ƙara fito da ainihin kyawun shi na musamman da hakan yasa Dr-Rafi'at ƙara mutuwa a kogin ƙaunarsa.




Maganar da ya yi ne ya sata dawowa hayyacinta daga kogin ƙaunarsa da ta lula.



Yace
"Ai ni ba ke naba kuɗina ba, Haleesat Rashid Rayyan da kuma Triple ɗina na bawa."






"Hhhh amma dai wasa kakemin ko?."


"A'a da gaske nakeyi, ko kinga alamar wasa ne, a tare dani?."


Murmushin yaƙe tayi masa tana faɗin "A'a, shikenan dai kawo na kai musu, sun gode sosai."


Tayi maganar tana karɓar kuɗin ranta na ƙuna. Shi kuma ya shiga mota, tana ɗaga masa hannu har gate man ya wangale masa gate yabar gidan.



Ajiyar zuciya ta sauke tana fitar da huci mai zafi, wato dai wannan zabiyar Yarinyar ba zata rabu da Rayuwarta ba, ke nan shima dai wannan kaman sauran sai da ta janyo hankalin shi da kyanta ko?.


Da ƙarfi ta ciza laɓɓanta na ƙasa tana kuma ra ya yadda zata shayar da Haleesat mamaki, don kuwa wannan Mister Mai Kyau ɗin ba za ta bari ya kufce ma ta ba, kamar sauran mazan, ai kodan wannan tsantsan kyau da dukiya mai tarin yawa da yake dasu ba za ta bari ya kufce daga hannunta ba, bayan haka ma wani mugun son sa da ƙaunar sa da takeji yana bin magudanar jini da jijiyon jikinta fa, tayi ya ya dasu?.

Qwafa taja sannan a fili ta ce "Haleesat Rashid Rayyan You are die.! Wallahi."


Cikin gidan ta koma tana kuma imagine yadda zata ɓullowa wannan guy ɗin dan ta lura He was arrogant a nata tunanin.










___KWANAKI UKU GABA





Tun a ranar da Abubakar yaje gidansu Rafi'at, bai sama damar komawa ba, saboda bai ga amfanin komawar tashi ba, domin kuwa tun a ranar da yaje bayan ya koma gida, a maimakon ya yi tunanin Rafi'at, a'a sai dai kyakyawar fuskar Haleesat Rashid Rayyan take masa yawo a fuska, wannan dalilin yana daga cikin dalilan da ya sa bai koma ba.

Yau ta kama Sunday weekend Misalin ƙarfe biyar dai dai na marece. Ya shirya tsaf cikin shigar alfarma sai dai yau a maimakon ya yi shigar manyan kaya kamar yadda ya yi a ranar farko, a'a shiryawa ya yi cikin suit ash color.

Yauma dai shi kaɗai ya ɗauka motarsa mai kyau da tsada ba tare da escort ba, ya nufa gidan su Rafi'at, domin kuwa ya kasa jurewa, burinsa kawai ya yi tozali da kyakyawar fuskar Haleesat Rashid Rayyan, a dalilin da shi kanshi bai sani ba.



Cikin Motar ya tsaya bai fito ba bayan gate man ya wangale mishi gate isarsa gidan.

Wayarsa ya a trouser pocket sannan ya dannawa Rafi'at kira, bugu ɗaya ta ɗauka da sallama, amsawa ya yi sannan a taƙaice yace da ita


"Na ƙariso."



Kana ya kashe wayar ya fito ya jingina da motar yana latsa wayarsa sannan kuma yana ayyano yadda zai samu ya ganta a yau.



Yana tsaye jikin motar ya hango ta yauma kamar kullum sanye cikin Arabian gown white color mai adon flowers coffee color tayi rolling kanta da mayafi coffee color, tayi kyau sosai kamar a sace.






Qarisowa wurin tayi tana murmushi ta ce "Barka dai Mister Mai Kyau, ina Fatan kazo lafiya."

"Yeah am normal."


"Good please ga wurin zama daga can gefe fa."

Tayi maganar tana masa nuni da wani ƙayataccen balcony na hutawa wanda daga ciki kujerune na zama farare, ga glass table a tsakiya saman shi kayan marmari na alfarma ne kala kala.



"Okay shall we."
Qarisawa wurin su kayi a tare sannan taja masa kujera ya zauna, ita ma ta zauna tana ɗan janshi da fira.
Amma shi gaba ɗaya hankalinsa baya a kanta waige waige kawai yake ta inda zai hango Haleesat Rashid Rayyan sai dai Rashin sa'a, dan kuwa duk iya waige waigen shi ko mai kama da ita bai gani ba.





Duk waige waigen shi Rafi'at tana ankare dashi.

Murmushi tayi a fili a zuciyarta kuwa cewa take "Ai Malam Mai Kyau ka gama waige waigen ka, indai Haleesat Rashid Rayyan ce, ko mai kama da ita ba gani zakayi ba, a domin kuwa tana ciki na rufe ta a Bedroom."


Qayataccen murmushi ta kuma yi tana cizan laɓɓanta na ƙasa.


A hankali sannan cikin kashe murya ta ce "Mister Mai Kyau, please idan bazan takura ka ba, zaga iya ragemin hanya izuwa gidan Uncle Riyaz a domin na amso wani saƙo wajen matar sa Auntie Ramlat kuwa?."


Murmushi ya yi ke nan dai zai sama dama na ganin hasken Ranshi.🥳



"Okay babu damuwa shiga ki kira ƙannin naki, mu tafi tare."

Da wani irin mugun sauri ta kalleshi bakinta har wani rawa yake wurin faɗin

"Mene are You kidding me?."

Ta sauke ajiyar zuciya tana kuma danne abin da yake caccakar zuciyarta, cikin ɗan sanyin murya ta ce

"Alright it's okay. Bari kawai na shiga na kira su, sai mu tafi taren."

Tayi maganar a ɗan daburce sannan ta bar wurin cikin sauri sauri ta shige cikin gida.










AFT£R F£W MINUT£S


Su uku suka fito a tare Rafi'at Rafiq Rayyan, sai Haleesat Rashid Rayyan, sai kuma wata kyakyawar matashiyar budurwa wacca ba za ta kaisu a shekaru ba, Rafi'at da budurwar a tare sai Haleesat tana bin bayansu hannunta janye da wani madaidaicin Akwati.


Dukkansu suna sanye cikin shiga kala ɗaya wato Arabian gown white color mai adon flowers coffee color, sai ma yafi coffee color da suka yi rolling kansu dashi.
Ƙari sawa wurin shi sukayi yana jingine da Motarsa yanzu kuma waya yake yi da alama abin da ya shafi harkokin kasuwancin sa ne.




Rafi'at babu abin da take saƙawa cikin Ranta fa ce duk yadda zata yi Haleesat Rashid Rayyan karta shiga cikin Motar Abubakar Mai Kyau, dan kuwa ba shi kanshi ba hatta da abin da ya shafeshi bata ƙaunar Haleesat ta raɓa.





𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮𝗿𝘁𝗵 𝗦𝗮𝗯𝗶'𝘂 𝗬𝗮𝗵𝘆𝗮𝗵


𝗪𝗿𝗶𝘁𝗲𝗿 𝗢𝗳




Ŝ̬Â̬R̬̂Â̬Û̬N̬̂Î̬Ŷ̬Â̬R̬̂ K̬̂Ŷ̬Â̬Û̬
fιяѕт ѕтєρ







Ganin ya kammala wayar da yake yi ne, yasa cikin washe fuska ta ce dashi "Barka dai Mister mai kyau 2days Fatan kana lafiya?."



Murmushi ya yi cike da jindaɗin jin muryar ta na rashin dalili ya amsa ma ta da
"I'm very Normal, Fatan kema hakan, Ina Ƴan uku na?."

Murmushi Haleesat Rashid Rayyan tayi ta ce
"Oh Ƴan uku suna gidansu. Yanzu haka can zamu wuce ai."
"Okay harna ƙosa a ƙarisa domin kuwa nayi kewar Rashin jin su sosai."


Abubakar ya yi maganar cike da zoyala da nishaɗi kamar ba shike tamke fuska ɗazu ba.




Kallon ɗayar budurwar dake tsaye gefe ya yi Yana faɗin
"Barkan ki ƙanwar mu kina lafiya?."



Ɗan sosa kai budurwar tayi cike kunyar bata gaisheshi ba, sai shi ya gaisheta, ta amsa da
"Lafiya qalau Mister Mai Kyau, Fatan kaima hakan?."


Tayi maganar ne a Yayin da suka shiga Motar sa ita da Haleesat Rashid Rayyan a baya, sai Rafi'at a gaba, sai kuma shi bayan ya amsa ma ta sannan ya tada motar suka bar gidan.





A hanya a tsakanin Haleesat Rashid Rayyan da Abubakar Mai Kyau sai kuma wannan Budurwa mai suna Sailuba ne ake taɓa fira.




Yayin da gefe guda kuwa Rafi'at ta mayar da kanta tana kallon hanya amma can ƙasan ranta ji take kamar ta harbe Haleesat Rashid Rayyan kowa ma ya huta, daurewa kawai takeyi tana kuma ba kanta haƙuri, sai dai ta yanke a ranta suna komawa gida zata sama Dadynsu Alhaji Rafiq Rayyan da maganar Auren ta da Abubakar, kuma batason ya wuce sati biyu.



A haka har suka ƙariso gidan Uncle Riyaz! gaba ɗaya fitowa suka yi bayan ya yi parking a ƙofar gate na gidan.



Haleesat Rashid Rayyan da Sailuba suka yi gaba ita kuma Rafi'at ta tsaya suka yi sallama da Abubakar sannan ita ma tabi bayan su, shi kuma Yaja motar sa ya yi gida.




Haka abin dai ya ci gaba da tafiya kullum Abubakar sai yace gidan su Rafi'at fira, amma fa bawai dan ya yi fira da ita ba a'a.




Sai dai idan yaje ya saka ta kira masa Haleesat Rashid Rayyan suyi ta fira abin su, ita kuma a barta da kwasan Haushi.



 Haleesat tun tana jin kunya harta ware sai abin ya zama idan zai zo ita take masa girki na musamman domin kuwa ita qwararriya ce ta fanin, shi kuwa haka zai ware ya kwashi gara.



Ana cikin hakan kuma aka saka Ranar Auren Rafi'at Rafiq Rayyan da Abubakar Mai Kyau, sati biyu a Ranar Rafi'at tayi kwanan farin ciki sosai, dan jinta take kamar wata amaryarsa ma.🤣



Shi kuwa ta ɓangaren Abubakar ba zai ce yana farin ciki da wannan Aure ba, haka zalika ba zai ce baya Farin ciki ba, abin dai ba yabo balle kuma wani Abu wai shi fallasa.





Haka Rayuwar ta ci gaba da wucewa ta ko wani ɓangare shiri suke, abin babu kama hannun yaro ta can Jigawa State ɓangarensu Hajiya Harirah ma duk shirya shiryen bikin Abu lele suke😘




Mutanen Lagos, France, Mai Duguri, Adamawa States harda ma mutanen Birnin London su Sagir da matarsa duk sun ƙariso, gaba ɗaya sun taho da matayen su haka su Zuwaira, Sakeenah, Jawaheer, Jummai.
Sai shirin bikin Abubakar Mai Kyau suke yi dama abu harka na masu Naira, ko da ba wani lokaci aka saka ba.
Abuja City nan ma dai shirin biki sukeyi amarya Rafi'at saboda tsananin farin ciki sai da ta zuba Ruwan sanyi a ƙasa tasha🤔.



https://whatsapp.com/channel/0029VaEZtE15a2429vfcpf20




*💋💋𝑆𝐴𝑅𝐴𝑈𝑁𝐼𝑌𝐴𝑅 𝐾𝑌𝐴𝑈💋💋*


*👑𝑇ℎ𝑒 𝐺𝑙𝑎𝑚 𝑄𝑢𝑒𝑒𝑛👑*



*𝑊𝑟𝑖𝑡𝑖𝑛𝑔 & 𝑆𝑡𝑜𝑟𝑦 𝐵𝑦*

*𝐾ℎ𝑎𝑑𝑒𝑒𝑗𝑎𝑟𝑡ℎ 𝑆𝑎𝑏𝑖`𝑢 𝑌𝑎ℎ𝑦𝑎ℎ*



{♥︎𝑇ℎ𝑒 𝑁𝑎𝑖𝑛𝑎𝑟ℎ 𝑘𝑑♥︎}





💘*𝘓𝘈𝘍𝘈𝘡𝘐 𝘞𝘙𝘐𝘛𝘛𝘌𝘙𝘚 𝘈𝘚𝘚𝘖𝘊𝘐𝘈𝘛𝘐𝘖𝘕*💘🤙

<><><><><><><><><><><><><><<><><><><><><><>>






Page *53&54*

____*


Tun ana saura kwanaki takwas a ɗaura Auren, Abubakar ya dena zuwa gidansu Rafi'at domin kuwa bai ga amfanin zuwan nashi ba, ita ma dai Rafi'at ta wani ɓangaren jindaɗinta ne hakan, tunda dai wata magana zata dena shiga tsakanin shi da Haleesat Rashid Rayyan.


Rayuwa ta ci gaba lulawa kwanaki suna raguwa a kullum kwanan duniya lokaci daɗa ja yake yi domin shi baya jira sai dai a jira shi.






_____*


"An ɗaura Auren Abubakar Sadeeq Sameer Lamiɗo da zankaɗeɗiyar Amaryarsa Rafi'atu Rafiq Rayyan akan sadaki mafi daraja da cancanta lakadan ba Ajalan ba.'



Wannan maganar da wani maroƙi yake yi yana ƙarawa, ita ce ta dura a kunen Haleesat Rashid Rayyan tamkar Saukar Aradu.



Dafe kanta dake faman sara ma ta tamkar zai rabe gida biyu tayi da duka hannayenta babu abin da take furtawa a bakinta fa ce kalmar.

"Inna-lilahi-wa-inna-illahir-raji'un. Alhuma-la-sahla-illa_ma-ja'altahu-sahlan,wa-anta-taj'alu-l-hzana-idha-shi'ta-sahlan.

Ya Allah! Babu wani abu mai sauƙi sai abin da ka sanya shi ya zama mai sauƙi, kuma kai kana sanya tsanani idan ka so ya zama sauƙi.''



Haka kawai take iya furtawa a bakinta zubewa a ƙasa tayi tsakiyar Bedroom ɗin.
Wai meke shirin faruwa da ita ne?. wannan wata kalar makauniyar kaddara ce, ta rasa wanda zata so sai Saurayin Yayarta, a halin yanzu kuma miji a gareta...


"Kai! Kai!! Ya Allah! Allah na tuba, wannan wata kalar makauniyar soyayya ce?."😭


Ta furta a fili cikin matsanancin kuka, baiwar Allah gaba ɗaya tabi ta fita a hayyacin ta, komai abin mutum ya ganta cikin halin da take ciki sai ya tausaya mata.


Ta daɗe a wurin tana gurzar kuka kamar ranta zai fita. Kafin daga baya jin an fara knocking bedroom ɗin, yasa ta miƙe tsaye da kyar, ta shiga bathroom wanka tayi sannan ta fito zuwa lokacin kumburar da idanunta suka yi, sun ɗan ragu ba laifi.


Cikin kayanta na Anko ita ma ta shirya tsaf, sannan tayi kwalliya sama sama ba domin ya ƙara ma ta kyau ba sai dan ya rufe kumburin idanunta.






Ɓangaren da Amarya da ƙawaye da Ƴan uwa suke ta wuce kai tsaye.

Ita ma aka ci gaba da shagalin biki da ita, amma gaba ɗaya jikinta a sanyaye Yake.
{Allah sarki macen fah ke nan, komai tana iya shanyewa, tana iya sadaukar da farin cikin ta akan farin cikin wani mutum daban, zaka samu a koda yaushe fuskarta a washe take da fara'a, amma kuma can ƙasan zuciyarta ita kaɗai tasan abin da takeji. Mata na gari Allah ya ƙara ɗaukaka ku, sannan kuma Allah yasa kuci ribar haƙuri duniya da lahira Ameen}...🙏








Zuwa ƙarfe huɗu da rabi na marece, masu ɗaukar Amarya suka zo domin sai an fara kaita Jigawa State wurin dangin ango, sannan bayan kwana uku zuwa lokacin sun gama shagulgulan biki da na al-ada.
Sai a dawo da ita danƙareran gidan mijinta wanda Abubakar ya gina anan Abuja.


Tayi sallama da Ƴan uwa da Abokan arziki, sannan suka kaita wajen Dadynsu ya ma ta nasihar da ko wani uba na gari yake yiwa ɗiyarsa kafin a wuce da ita ɗakin miji.

Sannan aka fito da ita, suka shishshiga motoci aka nufa Jigawa State.
Amma har lokacin da aka fita da ita daga gate na gidansu ko gudan hawaye babu a idanunta.🌚










*JIGAWA_STATE_NIGERIA_*



Sun isa Jigawa State da Amarya Rafi'at wuraren ƙarfe takwas da rabi na dare, dangin Amarya sun sama tarba na mutun tawa da dajara a wurin dangin ango manyan mutane.




Haka ma sauran kwanaki uku da suka yi suna ganin yadda aka sha shagulgulan biki dana al-ada. Lafiya aka watse sannan kuma a rana ta huɗu aka juya da Amarya Abuja izuwa gidan mijinta abin alfarin ko wata matar kirki.









Sun isa Abuja City wuraren ƙarfe biyar na yammaci da yake ba fitowar wuri suka yi ba.



Da isarsu tanƙameman gidan Abubakar Mai Kyau, kai tsaye aka wuce da amarya ɗakinta bayan ansa tayi addu'a kafin shigarta cikin gidan, haka ma da zasu shiga ɗakin sai da tayi addu'a, kana ta saka kyawawan ƙafafunta na dama wa'danda suka sha jan lalle ta shiga cikin haɗaɗɗen Bedroom nata a gidan mijinta Abubakar Mai Kyau.




Zuwa ƙarfe tara na dare kowa da kowa an watse, an barta ita kaɗai domin kuwa ba ango ba labarinsa.
Ganin haka yasa bata wani damu ba a nata tunanin tunda dai an ɗaura aure tofa anyi mai wuyan, bathroom ta shiga tayi wanka haɗe da ɗauro alwala.



Sannan ta fito ta shimfiɗa darduma a wajen da aka tanadar domin yin sallah, sannan tayi magarib da isha'i waɗanda bata samu tayi ba tunɗazu.



Shiru shiru dai Amarya Rafi'at Rafiq Rayyan tana jiran ƙarisowar angonta Abubakar Mai Kyau har wajajen ƙarfe sha ɗaya na dare, amma shiru kakeji ba ango ba labarin sa kamar yaro yaci shirwa.




Harta fara gyan gyaɗi tajiyo ƙarar mota, alamun ƙarisowar angonta Abubakar Mai Kyau. Abin ƙaunar ta.

Cikin sauri ta miƙe ta ƙarisa wajen window, sannan ta ya ye labulayen sannan ta buɗe gilashin, tana leƙen farfajiyar gidan.



Hango shi tayi sanye cikin suit Ash and White color wa'danda ba ƙaramin Kyau, suka masa ba.


Karɓar Briefcase ɗin sa ya yi a wajen P-A. Ɗin sa sannan cikin sauri sauri ya shige ciki a dalilin Ruwan sama da ya tsinke kamar da bakin qwarya.








Da sauri ta saki labulen sannan ta mayar da gilashin ta rufe, kana ta dawo gaban madubi tana kallon kanta.



Murmushi tayi sannan ta cire hijjabin jikinta ta a je saman bed saboda ta fita ta tarbe shi.





Tana fita shi kuma a daidai lokacin yasa hannunsa ya buɗe ƙofar Bedroom ɗinsa da key, sannan ya shiga kana ya dawo da ita ya rufe.

Rafi'at tana masa magana amma ko kulata bayyiba, kuma tanada tabbacin ya ganta, tunani ta shiga yi shin taje ta masa knocking ne kuwa?.



Ko kuma ta kira shi a waya ya buɗe ma ta ƙofar?.


Ƙaramin tsaki taja sannan a fili ta ce "Idan ma na kirasa a waya, ko kuma naje na masa knock GIRMA YA FAƊI ke nan sha re shi tayi ita ma, ta wuce bedroom ɗin ta tabi lafiyar gado.








*WASHE GARI*


Amarya Rafi'at bata tashi da wuri ba, sai wuraren ƙarfe bakwai da rabi na safe.



Wanka tayi sannan tayi sallah a gaggauce ko kwalliya batayi tunanin yi ba, da saurin ta ta shirya cikin doguwar rigar atamfa, ta saka hula mai shigen kayan jikinta kana ta fito ƙasa ta sauka palo.






Kai tsaye kitchen ta wuce cikin sauri sauri ta kammala haɗa breakfast sannan ta jere a Dining Room kana ta koma Bedroom ɗin ta ta kuma yin wanka.
Bayan ta fito ta tsaya ta tsara kwalliya sannan ta shirya cikin shadda milk color mai adon stones coffee color kana ta ɗan ɗa sa ɗaurin ture kaga tsiya.




Tana fitowa daga Bedroom ɗin ta kai tsaye Bedroom ɗin mijinta Abubakar Mai Kyau, ta wuce ta kwankwasa ƙofar Bedroom ɗin dake garƙe.

Ta ɗan daɗe tana knocking sannan ta ciki taji ance ta shigo.

A hankali tasa hannunta wanda yasha jan lalle, ta tura ƙofar Bedroom ɗin a buɗe ta jita.




Kutsa kai ciki tayi tana mai masa sallama, sai da ta jira ya amsa sannan ta ƙarishe shiga ciki.



Tsaye ta hango shi can gaban madubi yana gyara zaman neck-tie ɗin Blue black suit dake jikinsa.



Da sauri ta ƙarisa wurin sa sannan ta karɓa tie ɗin, tana saka masa, sai da ta kammala gyara masa.




Ɗagowa tayi zata masa magana karaf suka haɗa ido, cike da kunya ta ce "Am so sorry Mister Mai Kyau dama kawai saboda naga ka kasa sakawa ne shiyasa, amma ina mai bada haƙuri."


Tayi maganar tana ɗan ɗagowa domin ganin Reacted ɗin sa.

Ga mamakin ta murmushi ya ma ta sannan cikin kamilalliyar Muryar sa yace da ita


''Thank You."




Ɗan murmushin samun nasara tayi, can ƙasan zuciyarta kuwa ta yanke zata biyo masa duk ta yadda ya buƙata, don taga alamar, yanasan mace mai kunya.


A fili kuwa kallon shi ta ɗanyi sannan cikin ƙasa ƙasa da murya ta ce


"Good morning Mister Mai Kyau, da fatan ka tashi lafiya. Dama nazo ne na faɗa maka breakfast ya kammala, please idan babu damuwa zamu iya Karin kumallo tare?."





Ga tsananin maɗaukakin mamakinta gani tayi ya yi gaba yana faɗin.


"It's okay babu damuwa."


Ya yi maganar ne a yayin da ya nufa ƙofar bedroom zai buɗe.



Da sauri tabi bayan sa tana kuma murmushin samun nasara.

"Ashe dai wannan Bawan Allah ba shi da wani girman kai, kamar yadda nayi zato. Ashe dai HE IS VERY NORMALCY PERSON.."


gaba ɗaya wannan zancen a can cikin Ranta takeyi 🤓.








A tare suka sauko Downstairs suka ƙarisa Dining table.

Yanzu ma cikin sauri ta ƙarisa tayi saving ɗin sa, duk irin Abin da yake buƙata.
Sannan ita ma ta zauna suka yi karin kumallon a tare.




Bayan sun kammala ta riƙe masa Briefcase ta raka shi har Bakin motarsa dama kuma akwai scarf akanta.

Sallama suka yi sannan ya shiga mota driver yaja, ita kuma ta koma ciki, cike da farin ciki, saman bed ɗin ta ta faɗa tana sakin ihu a fili ta ce

"Muje zuwa Malam Mai Kyau a tsakanin ni da kai a ga wanda zai sauke girma kai aha."



Haka ma da Rana ta tsara masa Lunch mai rai da motsi, ta zuba a food flask guda biyu sannan kuma ta haɗa lemun kayan marmari na musamman ta zuba a goruna duka ta jeresu a basket, ta haɗa da plate's da kuma cups ƙanana, sannan ta fito farfajiyar gidan ta sama driver ta bashi ya kaima Boss nashi office.








Da marece wuraren ƙarfe Bakwai da rabi ta kammala haɗa dinner, sannan gaba ɗaya ta jere a dining room, kana ta wuce bedroom nata.





Wanka ta fara yi sannan ta tsara kwalliya, kana ta shirya cikin shigar atamfa riga da skirt pencil wa'danda ba ƙaramin kyau shigar tayi ma ta ba.
Ta lura yafi son kalar shigar, to ita kuma ta ɗauki niyyar biyo masa duk ta inda ya buƙata.


https://chat.whatsapp.com/CVLsMqJthIoKIGGGaYlw8j



*💋SARAUNIYAR KYAU💋*
*Takun Farko*


______________________________________________________________________💥👑𝑻𝒉𝒆 𝑮𝒍𝒂𝒎 𝐐𝐮𝐞𝐞𝐧👑💥____________________𝑩𝒚:𝑻𝒉𝒆 𝑵𝒂𝒊𝒏𝒂𝒓𝒉 𝑲𝒅____𝑲𝒉𝒂𝒅𝒆𝒆𝒋𝒂𝒓𝒕𝒉.  𝑺𝒂𝒃𝒊'𝒖.  𝒀𝒂𝒉𝒚𝒂𝒉🤙


☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆
💦𝑳𝒂𝒇𝒂𝒛𝒊 𝑾𝒓𝒊𝒕𝒕𝒆𝒓'𝒔 𝑨𝒔𝒔𝒐𝒄𝒊𝒂𝒕𝒊𝒐𝒏💦🤙

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆



🎀🎀ϝιʋҽ ʂƚαɾ'ʂ ɯɾιƚҽɾ'ʂ🎀🎀

ᵀᴴᴱ συɾ σɾԃιɳαɾყ  ᴼᴺᴳᴼᴵᴺᴳ ᴮᴼᴼᴷ'ˢ


1:ȥαɳ ʝιɾα ƙα
       ɳα
A'isha Alƙali
            /ɱɾʂ αყʂιႦ/


2:ιɳ Ⴆα ƙαι
         ɳα
Fateemah .M. Kabeer
               /συɱ αϝɾҽҽɳ/



3:ɾαʂԋιɳ ʂαɳι
             ɳα
 Fatahiyya Moh'd Yakasai
                  /συɱ ყαʂɱҽҽɳ/


4:ʂσɳƙι ɳҽ ƙαԃԃαɾα ƚα
                   ɳα
          Fateemah Abdullahi
                    /Ⴆαƚσσʅ ƙαɱႦα/


5:ʂαɾαυɳιყαɾ ƙყαυ
                ɳα
 Khadeejarth Sabi'u Yahyah
                   /ƚԋҽ ɳαιɳαɾԋ ƙԃ/







Page *55&56*



Tana fitowa daga bedroom ɗin ta kai tsaye bedroom na mijinta Abubakar Mai Kyau ta wuce batare da tayi knocking ba, dan a tunanin ta yanzu kuma shikenan sun haɗe.


Tasa hannu ta tura ƙofar a hankali, ta shiga, baya nan a palon bedroom ma  hakan.

Can ciki ta wuce a hankali ta tura kanta ciki tana leƙen sa.


Zaune ta hangoshi saman wata doguwar sofa mai mazaunin mutum biyu dake manne da bed ya ba ƙofar yaba, domin kuwa yana kallon bed ne, ga waya manne a kunenshi.


Shiru tayi tana so ta fahimci hanyar da wayar da yake yi ta nufa, duk da cewa a nutse yake yi daɗi da ƙari kuma a hankali yake abin sa.
Amma wannan bai hanata jiyo abin da yake faɗa ba.

Abin ya gigita ta sosai, sannan yasa ka dukkanin jikin ta ɗaukar rawa kamar mazari

Duk da yanayin tashin hankali da maganar da taji suna fitowa daga bakinsa suka je fata, hakan bai hanata gyara tsayuwar ta ba, tana kuma jin maganar da yake fitarwa waɗanda suke nema su saka zuciyarta ta tarwatse, ba tare da ta shirya ba.





"Haba dai, ya zaki dinga faɗar hakan bayan kin san cewa baku haɗa iyaye da ita ba, kodai bakya sona ne?."





Ɗan shiru ya yi domin ya sama damar jin abin da zata ce.
Ajiyar zuciya ya sauke sannan cikin ƙara ƙasa da murya ya kira sunan ta



"Haleesat Rashid Rayyan..!'

Bai jira ta amsa ba ya ci gaba da cewa "Muddun kin yarda da ƙaunar da nake miki, kuma kema ɗin kina sona.! To kawai ki bari na turo magabata na  nanda five months, nasan zuwa lokacin na gama duka wasu shirya shiryen da suka kamata sannan idan ma bakya so ku zauna a gida ɗaya da 'Rafi'at, wannan ba damuwa bane zan iya a je ki a ɗayan gidana."




Shiru ya kuma yi sannan ya ciro wayar daga kunen shi yana dubawa.
"Ta kashe wayar da gaske fa. Katse min kira tayi fa."

Ya faɗa a fili kuma yana sauke hucin ɓacin rai.



Ganin yana shirin juyowa ne yasa Rafi'at da tayi suman tsaye, tun a lokacin da taji ya kira sunan 'Haleesat Rashid Rayyan'.
Saurin rufe ƙofar tayi ta juya da sauri sauri tabar bedroom ɗin.




Tana fita daga bedroom ɗin a maimakon tayi hanyar bedroom ɗin ta, bin hanyar ɗan ƙaramin kitchen ɗin dake anan upstairs ɗin tayi, ta shiga ciki.
Zama tayi a d`aya daga cikin kujerun dining dake kitchen a maimakon taji hawaye sun zubo mata kamar yadda tayi tsammani.
Neman su tayi ta rasa ashe dai hawaye ma rahama ne a wasu lokutan, domin ita gashi yau tana neman su ruwa a jallo amma ta rasa.





A kalla takai mintuna goma a haka bata sani ba, ta riga da ta faɗa a duniyar tunanin yadda zata yiwa tufkar hanci.




Ajiyar zuciya ta sauke tana sakin murmushin nan dai nata mara tabbas.


Ganin zama a wurin babu abin da zai ƙara ma ta illa ciwon kai, yasa ta miƙe ta fito daga kitchen ɗin.



Bedroom na mijinta Abubakar mai kyau Abin ƙaunar ta a kullum ta kuma komawa sai dai wannan karon tsayawa tayi cak a bakin ƙofar sannan ta saka hannun daman ta tayi knocking, kusan sau uku sannan yazo ya buɗe ma ta, murmushi tayi sannan cikin tsananin girmamawa da ƙanƙan da kai ta ce.


''Good evening Mister, dama cewa zanyi ne Dinner ya kammala a Dining room…"



Shiru tayi bayanta faɗan haka tana jira taji abin da zai ce.


"It's okay je ki ina zuwa."



Ya bata amsa a yayin da yake komawa ciki.

Rafi'at ji tayi tamkar ya watsa ma ta ruwan zafi a duka jikin ta, amma sai ta daure ta shanye kamar yadda ta sha alwashi.


Murmushin takaici ta saki a fili cikin ƙasa da murya ta ce


"Zaka shigo hannu ne, duk ranar da ka sake ka shigo hannuna. Ni Rafi'atu Rafiq Rayyan. Na Rantse da Allah mai girma zaka ɗanɗani kuɗar ka..."



Ta kumayin dariyar bosawa Like a zararriya, sannan tayi gaba Downstairs ta sauko ta ƙarisa Dining room ta ja kujera ta zauna, kana tayi saving kanta duk abin da zata buƙata shima tasa masa abin da ta fahimci yana so.



Komawa tayi ta zauna sannan ta ɗauki fork tana caccakar pounded Yam dake gabanta tamkar ta sama Haleesat Rashid Rayyan take gani.

Ta ɗauki tsawon mintuna biyar a haka, sannan ta jiyo sassayan ƙamshin turaren sa yana hallartar duka ƙofofin hancinta.


Kana daga baya mamallakin wannan sassayan ƙamshi mai haskaka zuciya ya bayyana cikin kyakyawar shiga.


Murmushi tayi sannan cikin kashe murya ta ce Bayan ya zauna ke nan "Barka da ƙari sowa Mister Mai Kyau."




"Yauwa Barkan ki dai fatan kin wuni lafiya?."


"Lafiya qalau Wallahi."



Ta bashi amsa cikin sauri, ya kuma tambayarta

"Ya baƙunta kuma?."



Murmushin jindaɗi tayi kana ta amsa da

"Awesome."



Ci gaba da fira sama sama sukayi, suna cin Dinner ɗin su, har suka kammala a tare, tashi ya yi ya bar wurin da alama bedroom nasa zai koma.




Kallon murmushi tabi bayansa dashi bayan ya ƙule tayi dariya a fili ta ce "Abubakar Sameer Lamiɗo mijina Mai Kyau, ni kaɗai ba tare da wata mace ba, muddun kuma wata mummunar makauniyar kaddara ta saka wata mace tayi kuskuren zama mata a gare shi, hmn hmmm hhhhh ina tsoron kaina, dan ban san abin da zai biyo baya ba Wallahi..."🔥





Tayi maganar tana kuma sheƙewa da dariyar bosawa Like a zararriya woman.😅


Sai da ta kammala gyara Dining table ɗin tsaf sannan ta kwashe plates da suka yi amfani dasu, kana ta wuce kitchen ta wanke su gaba ɗaya ta jeresu a ma'ajiyar su."




Fitowa tayi ta haye Up kai tsaye bedroom nata ta nufa, tana shiga kamar yadda tasa barwa kanta bathroom ta shige tayi wanka da Brush da alwala sannan ta fito, cikin ƙaramin lokaci ta shirya cikin sleeping dress.




Sannan ta hau saman mattress, ita batayi bacci ba, ita batayi wani abu ba.

Kawai dai tunanin mijinta take duk da cewa basu taɓa kasancewa a tare ba, amma tunanin shi takeyi sosai.
Wani lokaci?. A'ina?. Da yaushe?. Saboda wani dalili?.

Gaba ɗaya bata sani ba, abu ɗaya kawai ta sani shine tana son mijinta Abubakar Mai Kyau. tana ƙaunarsa da duka zuciyarta.

Tana masa son da batayi wa kanta, tabbas ta sani ƙaunar da take masa tayi yawa, ta sanie tana masa son da yafi a kira shi da, 'MASEEFAR SO' sai dai a kira shi bala'in ƙauna.

Tana ji a ranta da duka zuciyarta zata iya yin kisa akan shi, idan ta ce "Kisa tana nufin kashe mutum ɗan Adam har lahira."🙄




Tana cikin wannan tunane tunanen ne ta jiyo knocking a hankali sama sama.

Kasa kunenta tayi a domin taji shin da gaske ne, ita ake wa wannan knocking haka?.

Ilai kuwa tabbas ƙofar bedroom nata taji ana bugawa, du ba agogo tayi ƙarfe sha ɗaya na dare. Ta ga agogon ya nuna.





Saukowa tayi daga saman mattress ɗin kana ta nufa ƙofar ta buɗe.
Tsuru tayi tana kallon mutumin dake tsaye gabanta sanye cikin sleeping dress na maza, hannayen sa, gaba ɗaya cikin trouser pocket ɗin sa.



Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta bashi hanya ya shiga ciki.

Ita kuma ta mayar da ƙofar ta rufe, saman bed ya zauna yayin da ita kuma ta zauna daga saman wata doguwar stool, tana kallon shi cike da mamaki can ƙasan zuciyarta kuwa ba za ta iya kwatanta irin farin cikin da take ciki ba.





Ajiyar zuciya ta sauke tana kuma kallon sa cikin ƙasa da murya take faɗin


"Mister Mai Kyau, me kazo yi nan, a wannan daren, kuma a daidai wannan lokaci wurina?."



Ta jero masa tambayoyin tana zuba masa manyan idanunta.
Murmushi Mai Kyau ya yi kamar yadda shima yake Mai Kyau kana Yace
"Wai ni kam, wannan sunan ba za'a canza min bane, ko dai har yanzu ba'a ɗaukeni a matsayin miji ba ne?."


Shi ma ya yi maganar yana zuba ma ta kyawawan idanun shi yana kallo.



Ɗan murmushi tayi, Aha lallai ba shakka, sai yau, kuma yanzu sannan dai dai wannan lokacin ta yadda cewa Namiji ba shi da kunya ko kaɗan kuwa, domin ko bata tunanin mijinta Abubakar Mai Kyau yana da kunyar, mutumin da ya gama waya ɗazu ɗazunnan da ƙanwar ta yana faɗa ma ta irin son da yake ma ta amma yanzu saboda lokacin da ake raba kunyar yana kwance saman royal bed, shi ne zai zo ma ta da wani ƙauli da ba'adi.
Ita sai yanzu ma ta fahimci abin da yake nufi.
Wato dai wannan Bawan Allah yana nufin yace haƙƙin sa yazo karɓa.🙃




Murmushi tayi, ita ba shashasha ko kuma sakaryar mace ba ce, tunda haƙƙi yazo nema aikuwa zai sameta sabuwa fil a leda, shi zai ɓare abin da. 🤐








A fili kuwa ƙasa tayi da kanta wai kunya kana cikin kashe murya da kisisina ta ce




"Toh ni kuma mai zance?."


Tayi maganar kamar wata sakarya, murmushi Abubakar ya yi sannan yace "Ki zaɓa mana, ga sunaye nan kala kala."

Qara ƙasa tayi da kanta tare da faɗin "To My Lawful..."




Wani haɗaɗɗe kuma ƙayataccen murmushi ya kuma saki sannan Yace "Okay aikuwa naji daɗin wannan suna da aka sakamin, wato Your halal. To yanzu dai your lawful yana da buƙatar SARAUNIYAR KYAU ta shiga bathroom tayo alwala a domin suyi sallar godiya ga Allah. Ya yi maganar ne cike da zaulaya kamar... 🤓


Da sauri ta miƙe ta shige bathroom tana rufe fuska wai kunya, tana shiga a maimakon tayo alwala ta fito a'a, tsayawa tayi tana kallon kanta a jikin madubi dake a bathroom ɗin, dogon tsaki taja tana sakin murmushi kamar ta zare, cikin hura hanci ta ce "Wani wai sallar godiya ga Allah."


Ta kwaikwayi muryar shi, taja qwafa sannan ta fara alwala, bayanta kammala ta fito tana rufe da fuska, hijabi ta ɗauka dogo ta saka sannan ta shimfiɗa musu sallaya a wurin da aka tanadar domin yin sallah, kana yaja su Raka'a biyu kamar yadda addini ya hukunta.



Bayan sun idar kamar yadda aka saba tambayoyi ya yi ma ta akan addininta ta bashi amsa fi ye ma da tambayar sa, murmushin jindaɗi ya yi sannan sannan...🔥

Daga wannan Ranar, daga wannan dare, daga wannan lokaci sabuwar Rayuwar Aure suka buɗewa juna, duk da cewa ba wani soyayya da kulawa yake nuna ma ta ba.

Amma kuma a kullum kwanan duniya a saman faffaɗan ƙirjin shi take kwana, Rungume da juna sannan kuma a bedroom ɗin sa.🙄

    






   




 __*BAYAN_SATI_BIYU*
    
    
    
   


A Ranar da suka cika sati biyu da Aure Abubakar Mai Kyau shi da Amaryarsa Rafi'atu suka je gidansu Rafi'at a domin duba iyayenta.

A  Ranar kuwa Hajiya Zinaru mahaifiyar su Rafi'at da kuma Alhaji Rafiq Rayyan mahaifin su Rafi'at ba ƙaramin daɗin ziyarar da suka kawo musu suka ji ba, daɗin daɗawa ganin yadda Rafi'at har wani haske na jindaɗi tayi.

A Ranar duk wani motsin Haleesat Rashid Rayyan da Abubakar Mai Kyau a idon Rafi'at yake faruwa, tana kallon yadda Abubakar yake so su haɗa ido da Haleesat, amma ita kuma taƙi bashi dama.

Qwafa taja kawai tana ƙara matsawa jikinsa sosai, ta yadda zata fahimci idan Haleesat Rashid Rayyan tana son mijinta Abubakar Mai Kyau.

Aikuwa ta fahimci komai, dan kuwa tashi Haleesat Rashid Rayyan tayi ta bar musu wurin idanunta sun cicciko da qwalla.


Bayan barin Haleesat Rashid Rayyan  wurin ne Alhaji Rafiq Rayyan yake faɗa musu cewa, "Ai ita ma Haleesat ta sama miji, kuma sunansa Abubakar yanzu ma yana shirin zuwa gidanne a domin su ganshi daga nan a saka biki.

A ranar ba ƙaramin farin ciki Rafi'at tayi ba jin cewa Haleesat Rashid Rayyan ta sama mijin Aure ke nan dai zata rabu ma ta da mijinta ta huta, a Ranar har suka koma gida cikin farin ciki take.





🎀🎀ϝιʋҽ ʂƚαɾ'ʂ ɯɾιƚҽɾ'ʂ🎀🎀
💦💦ɯҽ αɾҽ ƚԋҽ ρҽɾϝҽƈƚ ɯɾιƚҽɾ'ʂ💦💦
           ✍️αʅƙαʅαɱι ყαϝι ƚαƙσϝι🤙



https://whatsapp.com/channel/0029VaEZtE15a2429vfcpf20




*💋 SARAUNIYAR KYAU💋*


______________________________________________________________________💥👑𝑻𝒉𝒆 𝑮𝒍𝒂𝒎 𝐐𝐮𝐞𝐞𝐧👑💥____________________𝑩𝒚:𝑻𝒉𝒆 𝑵𝒂𝒊𝒏𝒂𝒓𝒉 𝑲𝒅____𝑲𝒉𝒂𝒅𝒆𝒆𝒋𝒂𝒓𝒕𝒉.  𝑺𝒂𝒃𝒊'𝒖.  𝒀𝒂𝒉𝒚𝒂𝒉🤙


☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆
💦𝑳𝒂𝒇𝒂𝒛𝒊 𝑾𝒓𝒊𝒕𝒕𝒆𝒓'𝒔 𝑨𝒔𝒔𝒐𝒄𝒊𝒂𝒕𝒊𝒐𝒏💦🤙

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆


🎀🎀ϝιʋҽ ʂƚαɾ'ʂ ɯɾιƚҽɾ'ʂ🎀🎀

ᵀᴴᴱ συɾ σɾԃιɳαɾყ  ᴼᴺᴳᴼᴵᴺᴳ ᴮᴼᴼᴷ'ˢ


1:ȥαɳ ʝιɾα ƙα
       ɳα
A'isha Alƙali
            /ɱɾʂ αყʂιႦ/


2:ιԃαɳ Ⴆα ƙαι
         ɳα
Fateemah .M. Kabeer
               /συɱ αϝɾҽҽɳ/



3:ɾαʂԋιɳ ʂαɳι
             ɳα
 Fatahiyya Moh'd Yakasai
                  /συɱ ყαʂɱҽҽɳ/


4:ʂσɳƙι ɳҽ ƙαԃԃαɾα ƚα
                   ɳα
          Fateemah Abdullahi
                    /Ⴆαƚσσʅ ƙαɱႦα/


5:ʂαɾαυɳιყαɾ ƙყαυ
                ɳα
 Khadeejarth Sabi'u Yahyah
                   /ƚԋҽ ɳαιɳαɾԋ ƙԃ/







Page *57&58*




_____*


Rayuwa ta ci gaba da tafiya yau da daɗi gobe a kasin haka, to dama haka duniyar take, ba koda yaushe ake cikin jin daɗi ba.


Auren Abubakar Sadeeq Sameer Lamiɗo da Rafi'at Rafiq Rayyan nada wata biyu Rafi'at ta koma bakin aikin ta, zuwa lokacin sunje Jigawa State sun duba su Dr_Raheemah dasu Hajiya Harirah, Hajiya Zuwairiya daga nan suka wuce wurin Zuwaira, Jawaheer, Jummai, duka anan Jigawa State ɗin, daga nan kuma Adamawa State suka yi wurin Sakeenah nan ma suka sha murnar ganin juna, basu yi ƙasa a gwiwa ba, suka wuce Mai Duguri wajen Yusuf da matar sa Yusra, daga Mai Duguri kuwa Lagos suka antaya wajen Sameen da matar sa Sadiya.




Bayan sun kammala ziyarce ziyarce suka dawo Abuja City, waɗanda kuma basa a ƙasar sai dai ta waya suka gaisa, zuwa lokacin Yunus dake a ƙasar France ya zama ambassador na ƙasar.



Auren su nada watanni uku Rafi'at ta fara laulayin ciki, aikuwa koda aka gwada a kaga ciki ɗan wata biyu da satikai nanfa sabuwa, domin kuwa gaba ɗaya kulawar Abubakar akan Rafi'at ada da yake baifi kashi Ashirin cikin ɗari ba, albarkacin cikin dake jikinta kulawar da yake bata sai ta ninku ta koma kashi sittin cikin ɗari.


Rayuwa ta ci gaba da tafiya cike da nasara a ta kowani ɓangare, amma banda ɓangaren Haleesat Rashid Rayyan, domin kuwa Rayuwa tayi ma ta zafi musamman ma da ta fahimci Rafi'at suna zaune lafiya da mijinta Abubakar Mai Kyau, ta taya Rafi'at murna sosai domin kuwa ba Burin ta raba su ba, amma kuma ta yanke ba ita ba aure har duniya ta naɗe, domin kuwa zuciyarta ɗaya ce kuma ta riga da ta mallakawa wanda yafi cancanta a gareta, sai dai kuma tasan koda zata mutu ta dawo Abubakar Mai Kyau ya yi ma ta nisa,  saboda yana Auren ƴar uwanta Rafi'at, tana ƙaunar ƴar uwanta, ba zata so suyi zaman kishi ba, a dalilin haka ta sadaukarwa da Rafi'at Rafiq Rayyan duka soyayyar da take yiwa Abubakar Sadeeq Sameer Lamiɗo har qarshen duniya kuwa ta haƙura dashi.😰





      

 



__*BAYAN WATANNI HUƊU*




Cikin Rafi'at Rafiq Rayyan ma ta ga Alhaji Abubakar Sadeeq Sameer Lamiɗo nada watanni bakwai kenan.

**
Ɓiit! Ɓiit...!!!

Haka sautin yake tashi gaba ɗaya yankin a yayin da jerin motocin suke buga horn a ƙofar ƙerarren gidan.


Da sauri gate man ya ƙarisa bakin gate sannan ya wangale gaba ɗaya, sannu a hankali motocin suka shiga gidan, sannan a jere suke tafiya har suka ƙarisa wajen da aka tanadar domin ajiyar motoci, shikuma gate man ya mayar da gate ya rufe.


A hankali ya zuro ƙafarsa waje daga cikin Motar kana ita ma ɗayar ta biyo baya, daga ƙarshe kuma gaba ɗayansa ya fito daga motar, kamar yadda yasa ba sanye cikin Business suit black and White color.


Tafiya ya fara sannu a hankali a yayin da da escort service nasa suke take mishi baya, wasu kuma suka tsaya suna ciro trolleys a boot na Mota.


A dai-dai bakin ƙofar palo escort ɗin suka dakata, shikuma ya shige ciki yayin da waɗanda suka ɗauko jakunku nan na tsaraba suka biyo bayan shi a palo suka jere wuri ɗaya sannan suka fice abun su.


Staircases ya hau yana qwalawa matar sa kira, amma yaji shiru shi dai yasan yana dawowa zai sameta a Palo tana jiransa amma yau tsit kakeji, babu ita babu alamar ta.


Qara ɗa ga muryar sa ya yi yana kiran sunan da ya raɗa ma ta

"Matar Mai Kyau.!"

"Matar Mai Kyau.!!"



Still shiru dai, da sauri ya tura ƙofar bedroom nata ya shiga tun daga kan mattress bathroom wardrobe babu inda bai duba ba, amma ba Rafi'at ba labarin ta, da sauri ya kuma fitowa wannan karon bedroom nasa ya nufa yana tunanin ko tana can ne bacci ya ɗauketa shi yasa bata fito ba.

Sai dai abin mamaki bedroom ɗin nasa ma, ba inda bai duba ba, still dai babu Rafi'at.

Zuwa lokacin fa hankalinsa ya fara tashi danma shi ɗin Namiji ne.

Fitowa ya kumayi ya shiga duba gaba ɗaya gidan, amma ba Rafi'at ko alamar ta

Zuwa lokacin ya fara gajiya da nemanta domin kuwa shi ba Engine bane.




Dawowa palon ƙasa ya yi ya zauna ya zuba uban tagumi yana kallon tilin kayan wasan yara da ya bada ordered ɗin su aka kawo.
Can gefan zuciyar sa kuwa tunani yake wai shin yaushe ya fara son Rafi'at Rafiq Rayyan ne da zai damu haka da rashin ta?.
Ko dai ya manta ita ɗin Likita ce wata ƙila ma tana can anyi ma ta kiran emergency shi yasa ta fita ba tare da ta faɗa masa ba.
Wani ɓangare na zuciyarsa kuma cewa yake

"To dama kasan da haka shine zaka dama kanka kodai ka fara son matar mai kyau ne?."




Da sauri ya ba kanshi amsa da faɗi a fili "A'a ba sonta nake ba, unborn ɗina  dake a cikinta nake so, ba ita ba, zuciya ta ɗaya ce, kuma na riga na mallakawa wacce ta cancanta da samunta..."



Shiru ya yi daga hakan. Ya daɗe zaune a palon yana tunane tunane a cewarsa ba Rafi'at yake jira ba.

A kalla yakai mintuna talatin da biyar a wurin yana jira, can ɗa go kansa da zayyi suka yi ido huɗu da ita, a Yayin da take ƙoƙarin wuce shi, da alama bata lura dashi ba.


Da sauri ya miƙe ya ƙarisa wurin ta yana kiran sunan ta

"Rafi'at.! Rafi'at..!! Lafiyarki kuwa daga ina kike haka?."


Tambayar yake hankali a ɗan tashe, ganin kamar ba'a cikin hayyacinta take ba yasa ya ɗauketa gaba ɗaya bai damu da cikin dake jikinta ba, ya wuce sama da ita.

A ranar Rafi'at gaba ɗaya jikinta kamar a sanyaye yake, saboda haka Abubakar bai takura ta da tambayar inda taje ba, saboda yasan yana yin aikinta daɗi da ƙari kuma ita ɗin mace ce mai ɗauke da  juna biyu.
Wata ƙila a can Asibitin da take aiki ne taga abin da ya firgita ta saboda haka ya yanke shawarar ba zata ƙara zuwa wajen aiki ba har sai ta haihu.

Koda ya sameta da maganar bata wani damu ba saima cewa da tayi "Allah yasa hakan shine mafi alkhairi."

Zuwa daren Ranar kuma ta ware kamar ba ita bace jiki sanyaye da rana.













__*GAB@  KWANAKI  BIYU*
           {_TWO DAYS LATER_}



Suna zaune a palo Rafi'at kwance saman 3sieter Yayin da Abubakar yake zaune gefanta yana karanto mata wani £nglish story.
THE MOST BEAUTIFUL HEART.

Gaba ɗayan su labarin yana ƙayatar dasu yadda ya kamata.

Wayar Rafi'at dake gefe ne ta farayin ƙara alamar shigowar kira.
Da sauri takai hannu ta ɗauka, sannan ta tashi zaune da taimakon mijinta, kara wayar tayi a kunne bayan tayi picking.



Shiru tayi tana sauraron abin da ake faɗa ma ta ta ɗayan ɓangaren.

Ko ƙaramin motsi ta gaza yi da alama ta fita daga hayyacinta, ganin kamar bata hayyacinta yasa Abubakar tambayar ta Abin da ke faruwa.
Kallon sa tayi kamar wata zautacciya batasan lokacin da ta saki Wayar hannunta ba, aikuwa ta faɗi a ƙasan tiles ba ta tarwatse.



Da sauri Abubakar ya janyo ta jikinsa yana rarrashi, ganin yanda hawaye yake zuba daga idanunta tamkar an buɗe famfo.


Sai da ya tabbatar ta sama nutsuwa sannan ya sake ta yana tambayar abin da yake faruwa.
Cikin shashsheƙar kuka Rafi'at take faɗin


"Haleesat Rashid Rayyan."

"Haleesat....

Haleesat ce wai wai ita ce..."



Sai kuma tayi shiru tana kuma fitar da siraran hawaye.



A mugun tsorace Abubakar yake kallonta sannan cikin tsananin matsanancin tashin hankali da murya wacca bata fitowa sosai saboda rarrabewar da takeyi wajen furta maganar yake faɗin



"Haleesat Rashid Rayyan. Kuma to Menene abin da ya sameta, ki faɗamin mana kinji Rafi'at Please..."


Ya yi maganar yana jijigata tamkar ta  faɗa mishi Haleesat ɗin rasuwa tayi.





Cikin tsananin kuka Rafi'at ta ci gaba da cewa

"Haleesat ce wai aka sace ta tun kwanaki huɗu da suka wuce shine, Sailuba ta kirani tana faɗamin...."


Bata ƙarishe maganar ba ta kuma fashewa da matsiyacin kuka kamar zautacciya.


Shi kuwa Abubakar za'a iya cewa suman zaune ya yi jin abin da Rafi'at take faɗa Tamkar shock na wutan lantarki haka maganar tazo mishi a ba za ta sannan kuma ta dake shi yadda ya dace.



Sun ɗauki tsawon lokaci a haka ba wanda ya iya qwaqwqwaran motsi cikin su.

Sai can Abubakar da yake Namijin gaske ne, ya kalla Rafi'at bayan ya dawo hayyacinsa daga duniyar tunanin da ya lula yana faɗin


"Ki kwantar da hankalinki in Allah ya yarda za'a ganta nanda bada ɓata lokaci ba, kinji. bata bashi amsa ba, sai ma faɗawa jikinsa da tayi tana kuma fashewa da kuka.




Da yake a lokacin wuraren ƙarfe shida na yamma ne.

Yasa sai da aka kira sallar isha'i sannan suka shirya suka wuce gidan su Rafi'at.

Can ma dai banda kuka babu abin da Rafi'at take yi gaba ɗaya Ahalin Alhaji Rafiq Rayyan sun taru anata faman addu'o'i ana fatan bayyanar Haleesat Rashid Rayyan cikin gaggawa daga hannun wa'innan kidnappers da ake tunanin sune suka sace ta.



Sai can cikin dare wuraren ƙarfe sha ɗaya sannan Abubakar ya ɗauki Rafi'at suka koma gidan su, gaba ɗaya jikin ko wannensu a mugun sanyaye.






🎀🎀ϝιʋҽ ʂƚαɾ'ʂ ɯɾιƚҽɾ'ʂ🎀🎀
💦💦ɯҽ αɾҽ ƚԋҽ ρҽɾϝҽƈƚ ɯɾιƚҽɾ'ʂ💦💦
           ✍️αʅƙαʅαɱι ყαϝι ƚαƙσϝι🤙





_https://chat.whatsapp.com/DP2UrllaLb34m7nsvgeNEd




__*💋 SARAUNIYAR KYAU💋*___________________________________________________________________💥👑𝑻𝒉𝒆 𝑮𝒍𝒂𝒎 𝐐𝐮𝐞𝐞𝐧👑💥____________________𝑩𝒚:𝑻𝒉𝒆 𝑵𝒂𝒊𝒏𝒂𝒓𝒉 𝑲𝒅____𝑲𝒉𝒂𝒅𝒆𝒆𝒋𝒂𝒓𝒕𝒉.  𝑺𝒂𝒃𝒊'𝒖.  𝒀𝒂𝒉𝒚𝒂𝒉🤙


☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆
💦𝑳𝒂𝒇𝒂𝒛𝒊 𝑾𝒓𝒊𝒕𝒕𝒆𝒓'𝒔 𝑨𝒔𝒔𝒐𝒄𝒊𝒂𝒕𝒊𝒐𝒏💦🤙

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆




Page *59&60*


__*

Rayuwa ta ci-gaba da tafiya kwanaki suna ja yayin da gaba ɗaya hankulan Ahalin Alhaji Rafiq Rayyan yake a tashe na Rashin Haleesat Rashid Rayyan babu ita babu labarin ta.



To abin ma haka ne ta ɓangaren Rafi'at Rafiq Rayyan da mijinta Abubakar Mai  Kyau gaba ɗaya sun ɗauki damuwar duniya sun ɗaurawa kansu.


Har takai ta kawo ma Rafi'at bata iya cin abinci sai dai idan Abubakar yana gidan ne, to shine yake takurawa sai taci kodan unborn ɗin su, wani lokacin sai dai ta saka masa kuka tana bashi labarin kyawawan halaye irin na Haleesat Rashid Rayyan gata da haƙuri ga son mutane.







Kwanaki sun ci gaba da tafiya har ya kasance an ɗauki tsawon sati biyu da sace Haleesat Rashid Rayyan amma har yau waɗannan masu kidnapping basu kira sun faɗi abin da suke buƙata ba,  zuwa lokacin jikin kowa ya kuma yin sanyi lakwas, wasu ma sun fara tunanin kashe ta aka yi yayin da har zuwa lokacin wasu basu cire rai ba, domin kuwa INDA RAI DA RABO.








____

Zaune yake a tsakiyar palon, saman tattausar carpet sanye cikin jallabiya fara ga hula ita ma fara akan shi hannunsa riƙe da alqur'ani mai girma yana karantawa, daga gefansa kuma Rafi'at ce ita ma zaune saman lallausar carpet ita ma sanye cikin Arabian gown white color ga mayafi fari shima tayi rolling kanta dashi, hannunta riƙe da alqur'ani mai girma ita ma tana karantawa.



Sun ɗauki tsawon lokaci a haka sannan a tare suka kai aya, kana suka rufe alqur'anan dake a hannun su.

Wanda hakan Ya yi dai dai da shigowar kira a Wayar Abubakar dake gefansa cikin nutsuwa irin nashi yakai hannun daman sa ya ɗauki wayar kana ya yi picking, a tunaninsa wata magana ce akan ɓatar Haleesat Rashid Rayyan da yasa ana binkcike na musamman, shiyasa bayyi tunanin komai ba ya saka Wayar a free sannan ya a je gefe ta yanda zasu ji abin da mai kiran zai faɗa.



Sallama suka ji mai kiran ya farayi, amsa masa Abubakar ya yi sannan Wanda ya yi kiran cikin girmamawa yake cewa

"Mister Mai Kyau wannan budurwa mai suna Haleesat Rashid Rayyan da aka bamu report na ɓatar ta ita ce aka samu can cikin forest {gandun daji} yayin binkcike, a halin yanzu an ɗauke ta izuwa Asibitin..."

Tun kafin ya ƙarisa cikin sauri Abubakar da Rafi'at har suna haɗa baki wajen tambayar sa wani Asibitin?.

Faɗa musu sunan Asibitin ya yi sannan Abubakar ya kashe Wayar basu tsaya jiran ko escort ba, ya ɗauki Rafi'at a mota ita kanta bata damu da tsohon cikin dake jikinta ba, suka bar gidan sai a hanya ne ma Abubakar ya samu damar kiran su Alhaji Rafiq a waya ya musu bayanin abin da ke faruwa, sannan ya basu Address na asibitin da aka kwantar da Haleesat Rashid Rayyan.




**

A tare Motar su Abubakar dana su Alhaji Rafiq Rayyan suka ƙari sa Asibitin da aka kwantar da Haleesat ɗin, saboda tsananin tashin hankalin da suke ciki yasa basu tsaya gaisawa ba, gaba ɗaya suka ɗunguma ciki.



Zama sukayi a kujeru amma banda Rafi'at da Abubakar domin kuwa a miƙe suke, duk yadda akaso Rafi'at ta zauna ƙi tayi, haka aka rabu da ita.

Suna Zazzaune zaman jiran tsammani sai ga wasu ma'aikatan aikin jinya mata biyu sun fito tare da wata Likita mace.


Gaba ɗayansu suka miƙe suka ƙarisa wurinta kowa da irin tambayar da yake ma ta akan lafiyar Haleesat Rashid Rayyan.


Ajiyar zuciya Dr_Salahah Gashwa, ta sauke tana kallon su cike da tausayawa sannan cikin sanyin murya take faɗin

"Mun samu an tsayar da zubar jinin da take yi, amma raunukan jikinta sune matsala, saboda haka dole akwai wani Babban Likita da muke buƙatar taimakon sa a halin yanzu..."


Shiru tayi tana kallon yadda gaba ɗaya suka yi shiru suna sauraronta.
Sannan ta ci gaba

"Please zamu iya maganar a office ɗi na kuwa?."


Ajiyar zuciya Alhaji Rafiq Rayyan ya sauke sannan yace


"Ba damuwa muje."

Da sauri Rafi'at ta ce

"Dr_Salahah zamu iya shiga nida Sailuba da Mamyn mu a domin duba ta?."


''Eh zaku iya shiga amma banda hayaniya domin ta sama bacci ne."


Dr tayi maganar sannan tayi hanyar office ɗin ta Alhaji Rafiq da ƙaninsa Alhaji Riyaz sai Abubakar suna take ma ta baya.






A hankali ta tura ƙofar ɗakin sannan ta shiga tafiya sannu a hankali irin na masu cikin da ya kusa fita.

Ƙarisawa tayi wajen gadon kana ta zauna gefan gadon a hankali Yayin da Hajiya Zinaru da Sailuba suka tsaya a tsaye suna kallon Haleesat wacca ke sanye cikin doguwar riga sky blue irin Wanda marasa lafiya suke sakawa, Baiwar Allah gaba ɗaya tayi baƙi ta rame duk tabi ta fita hayyacinta da alama masu kidnapping ɗin basu bata abinci ba, saboda yadda duk tabi tayi ƙashin wuya ga jikinta gaba ɗaya raunuka ne, da alama sosai aka gana ma ta a zaba wasu wuraren ma a jikinta shedan bulalu ne. Lallai waɗannan masu kidnapping basu barta haka ba😞




Fuskar ta kuwa abin ba kyan gani domin ko gaba ɗaya bakinta a fashe yake, idanun ta kuwa duk da a rufe suke amma ana iya ganin yadda suka kumbura ga shedan cizo ba ɗaya ba kuma biyu ba a wuyanta da fuskar ta gaba ɗaya fuskar ta a kumbure take manyan idanun ta kuwa jajir suke gasu sunyi ƙanƙanta na Rashin cin abinci.😭







Da sauri su duka suka ɗauke kallon su daga kanta gaba ɗaya hawaye suke yi, a fili Sailuba take faɗin


''Allah sarki Rayuwa tabbas INDA RANKA KA SHA KALLO a ƙasƙantacciyar Rayuwar nan da muke ciki, yanzu dan Allah dubi Auntie Haleesat, Mamy ku duba kuga inda waɗannan azzaluman mutane suka mayar da ita, ta koma tamkar wata skeleton, ina tsoron ace min Raping ɗinta aka yi domin kuwa bazan lamunta ba Wallahi..."


Gaba ɗaya maganar takeyi cikin kuka ta ci gaba da cewa in Allah ya Yadda wa'innan mutanen da suka yi ma Auntie Haleesat wannan abu sai sunga mummunar ƙarshe a Rayuwar su in Allah ya Yadda ba zasu taɓa ganin mai kyau a duniya da lahira ba. Ni Sailuba na Rasa abin da mutane suke nema ne a duniya wannan marainiyar ban san laifin da tayi musu ba, da suka saka ma ta da wannan mummunar uquba Duniyar mu da mutanen cikin ta sun koma tamkar sheɗanu saboda tsananin Rashin imani..."



Da sauri ta ƙarisa bakin gadon ta tsaguna sannan ta kamo hannun Haleesat dake saman mattress ɗin ƙara fashewa da kuka tayi tana kallon ikon Allah, wato a hannun ma ba'a Rabu da ita ba sai da aka gana ma ta wani salon a zaba.

"M_M_R_D_L."

Sune kalmomin da aka Rubuta a hannun Haleesat Rashid Rayyan da manyan baƙi sannan kuma a wawware.


Juyowa tayi tana kallon su Rafi'at da Hajiya Zinaru dake ta faman share hawaye wasu na ƙara fitowa Sailuba tayi sannan cikin kuka ta buɗe baki zatayi magana taji alamar hannayen Haleesat Rashid Rayyan dake cikin nata sun fara motsi...






🎀🎀ϝιʋҽ ʂƚαɾ'ʂ ɯɾιƚҽɾ'ʂ🎀🎀
💦💦ɯҽ αɾҽ ƚԋҽ ρҽɾϝҽƈƚ ɯɾιƚҽɾ'ʂ💦💦
           ✍️αʅƙαʅαɱι ყαϝι ƚαƙσϝι🤙



https://whatsapp.com/channel/0029VaEZtE15a2429vfcpf20




___*💋 SARAUNIYAR KYAU 💋*___________________________________________________________________💥👑𝑻𝒉𝒆 𝑮𝒍𝒂𝒎 𝐐𝐮𝐞𝐞𝐧👑💥____________________𝑩𝒚:𝑻𝒉𝒆 𝑵𝒂𝒊𝒏𝒂𝒓𝒉 𝑲𝒅____𝑲𝒉𝒂𝒅𝒆𝒆𝒋𝒂𝒓𝒕𝒉.  𝑺𝒂𝒃𝒊'𝒖.  𝒀𝒂𝒉𝒚𝒂𝒉🤙


☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆
💦𝑳𝒂𝒇𝒂𝒛𝒊 𝑾𝒓𝒊𝒕𝒕𝒆𝒓'𝒔 𝑨𝒔𝒔𝒐𝒄𝒊𝒂𝒕𝒊𝒐𝒏💦🤙

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆

🎀





Page *61&62*




A can ɓangaren kuwa

Zama Dr_Salahah tayi kana suma suka zazzauna a kujerun dake Kallon wanda ta zauna shiru office ɗin ya ɗauka gaba ɗaya sun zuba ma ta ido suna jira suji abin da zata faɗa, a kalla sunkai mintuna biyar a haka.

Sannan Dr_Salahah ta ɗago daga rubuce rubucen da take yi tana kallon su, ta cire farin glass dake saƙale a fuskar ta fararen idanunta suka bayyana kana ta  fara magana cikin harshen hausa yadda gaba ɗaya zasu fahimci abinda takeson faɗa musu da kyau.





"Wato Abin da Rahoton binkciken da muka gabatar akan Dr Haleesat Rashid Rayyan shi ne, akalla an ɗauki tsawon kwanaki biyar ana gana ma ta a zaba sannan binkciken mu ya nuna cewa an ɗauki tsawon kwanaki goma a kullum sai anyi Raping ɗinta sau biyu, bayan an gama kuma ana saka wani abu mai tsatsa kodai sanda ko ƙarfe ana goge duk wata alama ko hujja wacca zata nuna anyi ma ta fyaɗe.😭



Daɗin daɗawa kuma binkcike ya nuna ba iya maza ne kawai suka yi amfani da ita ba hadda ma mata sannan ta ƙarfi suke yi wanda hakan ne yasa duk taji ciwuka a jikinta da bakinta sai kuma hannunta da aka Rubuta wasu alphabet guda biyar.



"M_M_R_D_L."

Sune abin da aka Rubuta a hannun daman ta sai kuma tsakiyar hannun hagunta nan ma aka Rubuta "X" da alama ɗaukar fansa ne yasa aka sace ta ba wai saboda kuɗi ko wani abun ba."

Tana faɗin haka tayi shiru tana kallon su.




Tun lokacin da Dr Salahah ta fara magana gaba ɗaya shiru suka yi suna kallon ta Alhaji Rafiq ashe suma ya yi ma lokacin da Dr ta ce anyiwa Haleesat ɗiyar ɗan uwanshi fyaɗe, shi kuwa Alhaji Riyaz ba abin da yake iya furtawa sai kalmar inna lil lahi har ƙarshe.




Abubakar ne kawai ya yi ƙarfin halin yin magana cikin murya wacca alƙalamin 'Nainarh Kd' bazai iya bayyana yanayin da yake ba.

"Yanzu Dr Salahah kina ganin Haleesat zata iya ci gaba da Rayuwa kuwa?...'



Shiru Dr Salahah tayi sannan ta bashi amsa da


"Gaskiya bani da amsar wannan tambayar naka Mister Mai Kyau sai dai kawai abin da na sani shi ne bamu da kayan aikin da zasu taimaka wajen kulawa da Lafiyar ta yadda ya kamata, sai dai akwai wani Babban Likita da muke buƙatar taimakon sa amma a halin yanzu baya ƙasan nan."




"Za'a iya fita da ita Abroad kuwa wannan taƙin da ake ciki?.''


Abubakar ya tambaya a dabke, Dr Salahah ta ce

"Mister Mai Kyau ke nan wannan ai ba'a ridaga anzo maganar fita da ita Abroad ba tukunna, saboda Yanzu abu ɗaya muke tsoron faruwar sa."

"Menene shi wannan abun?.''


Abubakar ya kuma tambaya, Dr Salahah ta ci gaba da cewa

"Wannan abu ɗayan shi ne, muna tsoron kar ta sama Abrogating, ko kuma mental illness, da sauran su saboda abin da ya same ta."




Abubakar har ya buɗe baki zayyi magana ke nan aka banko ƙofar aka shigo, Sailuba ce hankalin ta a Mugun tashe da alama taji abin da suke tattaunawa ne, ƙarisowa wurin su tayi cikin kuka take faɗin

"Auntie Haleesat ce take buƙatar ganin ku dukan ku hadda Yaya mai kyau...''





Wata ɓoyayyiyar ajiyar zuciya Dr da Abubakar suka sauke fahimtar da suka yi bataji komai daga abin da suke tattaunawa ba.



Da sauri Abubakar ya miƙe tsaye ya fice daga office ɗin a 360 ita ma Sailuba tabi bayan shi, hannun Alhaji Rafiq, Uncle Riyaz ya kamo ganin yaƙi tashi amma sai ji ya yi hannun ya biyo shi. Da sauri ya juyo yana kallon shi a mugun tsora ce.




Kallon Dr Salahah ya yi a tsorace yake tambayarta.

" Dr duba min ya mutu ko?.."


Ya yi ma ta Tambayar Like a Little kid sannan kuma hawaye yake yi.

Da sauri Dr Salahah ta ƙarisa wurin ta shiga duba Alhaji Rafiq bayan tayi abin da zata iya ta ɗago tana kallon Alhaji Riyaz da ya zuba mata ido sannan cikin hawaye da murmushi ta ce


"Bai mutu ba ya dai faɗa doguwar suma ne."








Wani wawan burki yaja daga ƙofar ɗakin yana hango yadda Haleesat Rashid Rayyan ta koma wata abun tausayi.
A hankali kamar kazar da kwai ya fashe ma a ciki ya fara taku a hankali yana ƙarisawa wurin gadon da take kwance.


Durƙusawa ya yi da duka ƙafafunsa yana kallon ta yayin da yake tariyo abubuwan da suka taɓa faruwa tsananin sa da ita, tun farkon ganin ta da ya yi a gidan su, da son ta da ya ke ma ta daga kallon farko, da ma yadda ya bayyana ma ta soyayyar sa a gare ta, amma saboda wani dalili nata tayi rejection nasa, da kuma yadda tasa ya ɗauka ma ta alƙawarin dashi kansa yasan bazai yuwu ba.
Na ya taimaka ya cire ta daga zuciyar sa domin kuwa ita ɗin ba wani tsawon rayuwa ne zatayi ba a doron duniya.




Komai dawo masa yake sabo fil a zuciyar sa, bai san kuka yake yi ba, har sai da yaga tana girgiza masa kai, alamar a'a sannan yasa hannunsa wanda yake faman rawa saboda tsananin tausayinta da ƙaunarta dake zagaye dukanin ilahirin jikinsa da ruhin sa.



Ya share hawayen fuskarsa amma wasu ƙara zubowa suke hannun damansa yakai ya kamo nata hannun yana kallon ta cike da tausayawa game da tsananin ƙaunarta.

Zayyi magana, tayi saurin girgiza masa kai tana murmushin ƙarfin hali.


Sannan ta kalla su Hajiya Zinaru da Sailuba dake tsaye gefe sunyi curko curko sai share hawaye suke yi, murmushi tayi kana ta mayar da kallonta kan Rafi'at dake durƙushe can jikin gadon tana hawayen tausayin Ƴar uwan nata, da hannu Haleesat Rashid Rayyan tayima Rafi'at alama da ta ƙariso wurin, ko damuwa da cikin jikinta Rafi'at batayi ba ta ƙarisa wurin da sauri.


Har yanzu murmushin dake saman fuskar ta bai gushe ba, ga fuskar nan tata tayi wani haske na musamman sai faman shaining take yi, ga wani kyau na musamman da ta ƙara, amma kana ma ta kallon gurilla komai Rashin imanin ka saika tausaya ma ta wata ƙilama saika zubar da hawaye saboda Abin bakyan gani, tana jin jiki sosai sosai. 😭



Kamo hannun Rafi'at tayi sannan ta kamo hannun Abubakar tana murmushi ta haɗa wuri ɗaya kana cikin murya irin wanda daga ji kasan mai ita ba ƙaramin jin jiki yake ba ta fara magana.


"Kamar ko yaushe anaso mutum ɗan adam ya kasance mai kyautatawa ɗan uwansa zato ko ya ya ne, amma wannan zamani mutane masu kyautata zato sunyi ƙaranci a wannan Rayuwa...
Mister Mai Kyau ga Ƴar uwata kuma Auntie ta Rafi'at Rafiq Rayyan please ka taimaka ka riƙe ta da amana, ka sota ka ƙaunace ta kamar yadda na tabbatar da cewa ita ma tana ƙaunar ka fiye da Rayuwarta please Mai kyau ka taimaka ka riƙe mana ita amana. ir vosotros oír mí u cuál ?.. { did you hear me or what ? }...."




Tayi maganar tana dariya duk da cewa cikin ciwo take, murmushin yaƙe kawai Abubakar yake yi yama kasa magana sai faman girgiza ma ta kai yake yi alamar yaji kuma ya yadda zai riƙe alƙawari, kallon Rafi'at tayi kana cikin murmushi ta ce


"Auntie Rafi'at please ga your lawful naki ki riƙe shi amana kin san fa yana ƙaunar ki ko?, dan Allah zaki riƙe shi da amana tunda kin san yana ƙaunar ki."





Cikin hawaye da murmushi Rafi'at ta shiga girgiza kai kana ta ce


"Nasani Haleesat nasani sister..."



Kallon su Hajiya Zinaru da Sailuba tayi kana tayi musu alama dasu ƙariso da saurin su suka ƙariso wurin gadon har rige rigen riqe hannunta sukeyi.



Murmushi Sailuba tayi kana cikin hawaye da dariya ta ce


"Auntie Haleesat kin warke zaki tashi mu ci-gaba da girka abinci tare muna wasanni kuma, Daddynmu yace za'a kama mutanen da suka miki wannan ba za'a gyalesu ba har sai sun faɗa Wanda ya saka su kinji ko?."





Tayi maganar tana kuma kamo hannun Haleesat dake cikin nata, dariyar ƙarfin hali Haleesat Rashid Rayyan tayi kana cikin muryar marasa lafiya ta fara magana.



"Sailuba kinji ki rabu da mutanen da suka min haka kinji?."



"Saboda mene Auntie Haleesat?."


Sailuba ta tambaya cikin sauri hawaye na zuba, Haleesat ta bata amsa da "Saboda Allah ya fisu, kuma Allah yana tare da masu Haƙuri."





Mai da kallonta kan Hajiya Zinaru tayi kana ta fara magana bayan ta kamo hannunta.



"Hajiya! please! Yau ɗaya dai zan iya kiranki da wannan Babban suna wato Mahaifiya?, domin kuwa kin cancanta da na kiraki da wannan suna, a dalilin kin riƙe ni da amana da gaskiya kinyi min riƙon da ko iyayena sai haka, amma ni kuma ina ganin baki kai na kiraki da wannan suna ba, dan Allah Hajiya zaki iya yafewa wannan Ɗiyar taki sannan ki bata damar kiranki da wannan sunan Mahaifiya?..."





Hawaye Hajiya Zinaru take amma hakan bai hanata murmushin farin ciki ba, jin yau Ɗiyar da ta Raina da hannunta wacca tsawon shekarun da suka yi tare bata taɓa kiranta ko tayi ma ta kallon uwa Mahaifiya ba sai yau gashi tana roƙon ta.



Da kyar ta iya buɗe bakinta dake tsananin rawa ta ce


"Eh na yadda Haleesat ɗita kullum kiyita kirana da sunan mahaifiya domin hakan ba ƙaramin farantamin raina zaiyi ba kinji?."



Cikin kuka da dariya Haleesat Rashid Rayyan ta buɗe bakinta a hankali kana cikin dabara ta furta a saman laɓɓanta



"UMMA NA, MAMA NA, MAMY NA..
 Hakan ya yi daga yau zan dinga kiran ki da UMMATA...''




Da sauri Hajiya Zinaru ta amsa ma ta da sosai ma hakan Ya yi tana maganar ne kamar bata cikin hayyacinta tsoro take karta rasa Haleesat kamar yadda suka rasa iyayenta Sanadin hatsari mota.




"Ummata ina Abbana Yake da Uncle Riyaz bangansu ba wai suna ina ne?."





Haleesat Rashid Rayyan tayima Hajiya Zinaru tambayar tana Ƴan waige waige, murmushi Hajiya Zinaru tayi kana cike da zaulaya take faɗin


"Yau wannan nema neman haka sekace kina mana bankwana kodai kinaso Dr Salahah tayi sauri tayi Discharged namu tunda kin warke ne?..."




Murmushi Haleesat Rashid Rayyan tayi Yayin da fuskar ta take ƙara wani haske da shaining gunin burgewa kana ta ce

"Ummata ba bazaki fahimci abin da nake ji bane, ina kallonsu cikin fararen kaya sunayi min murmushi Yayin da wasu suke miƙo min hannu, kin san miye kuwa?."



Bata jira Hajiya Zinaru ta amsa ma ta ba ta ci-gaba da cewa.



"Ummata dan Allah keda Abban mu dasu Rafi'at da Sailuba da kowa duk Wanda nayi wa wani laifi a Rashin sani kuya femmm..."


Tarin da ya taho ma ta ne yasa ta kasa ƙarishe maganar da zatayi nan ta shiga tayi ɓaɓɓaka tarin tambar kayan cikin ta zasu yo waje.😞




Tana mai furta kalmar shahada su duka suna tayata sun ɗauki lokaci a haka kana can suka ji tayi tsit hannunta dake sarƙe cikin nasu ya sage ga fuskar ta ɗauke da qayataccen murmushi.😓




Ganin tayi shiru yasa Rafi'at ƙara kamo hannunta tana mai kiran sunanta amma ina rai ya yi halin sa Wanda yafi su ƙaunar ta ya amshi abin sa.




Ganin da gaske dai batayi magana ba yasa Abubakar dake gefe ƙarisowa wurin cikin sauri ya shiga duba ta, duk da cewa shin ɗin ba Likita bane amma kuma yasan cewa Haleesat Rashid Rayyan bawai tayi bacci ba ko kuma zata farka zuwa anjima ba, a'a bata duniyar gaba ɗaya shikenan TAFARU TAƘARE Haleesat Rashid Rayyan ta tafi inda muma muna nan ƙarisawa idan lokaci ya yi domin kuwa kowa lokacin sa yake jira, lokaci nayi ba jira za'a tafi tafiyar da babu dawowa har abada har duniya ta naɗe shikenan kuma.😭😭😭




Ja! da baya ya farayi cike da matsanancin tashin hankali babu abin da yake iya furtawa sai kalmar inna lil lahi har ƙarshe yana mai rumshe idanunsa Yayin da wasu siraran hawaye suke zubowa akan kyakyawar fuskar sa.



Fahimtar abin da yake faruwa wai Haleesat ta tafi, tafiya na har abada yasa Rafi'at ta yanke jiki ta faɗi a wurin sumammiya.




Ita kuwa Sailuba kusan zaucewa za'a iya cewa tayi saboda tsananin tashin hankali, Yayin da Hajiya Zinaru ta koma Tamkar mutum mutumi.


/Yau abin dai Alƙalamin Nainarh kd bazai iya rubutawa Yanda yake ba saboda is very vThither Ban tausayi over 😭😭😭....Kuyimin Afuwa....😓😓😓/







Gaza jurewa Abubakar ya yi domin kuwa zai iya cewa tunda yake a tsayin Rayuwar sa bai taɓa shiga tashin hankali irin wannan ba.



Fita ya yi daga ɗakin kai tsaye office na Dr Salahah Gashwa ya wuce ashe camma wani tashin hankalin zai kuma tarar wa domin kuwa Alhaji Rafiq Rayyan ne ciwon zuciyar sa ya tashi Ashe ma har gado aka bashi anan Asibitin.





Tashin sense.!😫




Tashin Hankalin Wanda ba'a saka masa Rana zuwa Yammacin Ranar gaba ɗaya dangin Alhaji Rafiq Rayyan suka hallara a wannan Asibitin zuwa lokacin kuma Sailuba ta fara dawowa hayyacinta amma ba gaba ɗaya ba.


Yayin da ita kuma Rafi'at abin yazo da sauki ta farfaɗo shima dai Alhaji Rafiq Rayyan abin sai godiyar Allah sai dai shi Asibitin sun riƙe sa saboda tsaron lafiyar sa.



Saboda haka bai sama damar Raka maragayya Haleesat Rashid Rayyan izuwa makwancinta ba.




Da yake a wancan lokacin waya tayi ƙaranci yasa ba kowa ya sama damar zuwa ba cikin Ahali wa'inda suke da nisa, sai washe gari suma mutanen Jigawa State suka ƙariso.



Rafi'at gaba ɗaya ta ɗauki damuwar duniya ta sakawa kanta domin kuwa koda abinci bata iya ci sosai ta saba kafin suyi aure da Abubakar Mai Kyau a kullum tare suke da Haleesat Rashid Rayyan koda wani wuri zasuje to tare suke zuwa, bama ita kaɗai ba gaba ɗaya ɓangarorin abin sai a hankali.



Satin Haleesat Rashid Rayyan biyu da Rasuwa Rafi'at ta koma gidan mijinta Abubakar zuwa lokacin kuma an sallami Alhaji Rafiq Rayyan daga Asibitin.




/RAYUWA KE NAN😭/






_*BAYAN_WANNI_BIYU*_





Rayuwa ta ci gaba da tafiya sumuluquii ta wasu ɓangarorin amma banda ɓangaren Rafi'at da mijinta Abubakar domin kuwa zama suke zaman doya da manja tun rasuwar Haleesat Rashid Rayyan komai ya taɓarɓare tsakanin su ko ɗan kulawar da Abubakar yake bata a Sanadin cikin jikinta Yanzu babu, domin kuwa wani miskilanci Yake ji dashi haka suke zaman abin sai addu'a.





Ranar wata litina Rafi'at ta tashi da naƙuda ba'a ja lokaci ba da yake da wata tsohuwa Babah Ladii ƙanwar Kakansu a gidan saita taimaka ma ta zuwa Yamma lokacin Abubakar ya dawo ya tarar da halin da ake ciki, bai ɓata lokaci ba, ya kira Hajiya Zinaru ta waya ya sanar da ita abin da ke faruwa.




Ko kafin Hajiya Zinaru ta ƙariso Rafi'at ta haifo kyakyawan Jaririn ta ƙato mai kama da ubansa kamar an tsaga kara komai iri ɗaya sak, Like father Like son 🤓





Koda suka ƙariso ita da wata ƙanwar ta sai kuma Sailuba nan suka haɗu da Babah Ladii suka shiga kula da mai jego da kuma Jaririnta.




Zuwa kwana uku da haihuwa gaba ɗaya Ahalin Alhaji Sameer Lamiɗo dana Alhaji Rafiq Rayyan ba Wanda baizo duba lafiyar mai jego da kuma Jaririn da ta haifa ba, kowa yazo sai ya yaba da kyau irin na wannan jariri.






Ranar suna Yaro Yaci suna


ABDUL'MALEEK.!


/THE KING/


Mutane na kiran sa da Maleek Yayin da iyayen sa suke kiran shi da


BUDDY

Wato Aboki
Duniya sabuwa fil a wurin Rafi'at da Jaririn ta Abdulmaleek domin kuwa tun a Ranar da ta haihu wani kulawa na musamman Abubakar Yake bata ita da Jaririn su sunyi ƙiba sunyi ɓulɓul abinsu.




ABDUL'MALEEK Ya taso Yaro ne shi mai ƙiriniya sosai da sosai domin ko Asibiti Rafi'at ta tafi dashi tofa Ya dingi dukan Yaran mutane ke nan gashi ita kuma Likitar Yara ce, gashi daga ita har uban sa suna ƙaunar shi sosai ƙaunar da ta sa basa ganin laifin sa koya yake.









___*💋 SARAUNIYAR KYAU 💋*___________________________________________________________________💥👑𝑻𝒉𝒆 𝑮𝒍𝒂𝒎 𝐐𝐮𝐞𝐞𝐧👑💥____________________𝑩𝒚:𝑻𝒉𝒆 𝑵𝒂𝒊𝒏𝒂𝒓𝒉 𝑲𝒅____𝑲𝒉𝒂𝒅𝒆𝒆𝒋𝒂𝒓𝒕𝒉.  𝑺𝒂𝒃𝒊'𝒖.  𝒀𝒂𝒉𝒚𝒂𝒉🤙





Page *63&64*



Duk da cewa shiɗin ɗan fari ne amma wannan bai hana Rafi'at da Abubakar nuna masa soyayya ba koda kuwa a gaban waye ba ruwan su ƙaunar ɗan su suke kamar Rayuwar su.



Tun Bayan Haihuwar Abdulmaleek Rafi'at bata kuma haihuwa ba sai da Abdulmaleek yakai shekaru uku a duniya sannan kuma ta haifa twin's duka mata Ranar suna, aka raɗawa Yara suna Hasana Babbar taci suna Nainarh Yayin da ita kuma Hussaina ƙaramar taci suna Nailah.



Sai kuma lokacin Sabuwar ƙauna da kulawa ta ninku fi ye da baya saboda Yadda Abubakar Yake ji da Yaransu uku a duniya shi da matar sa Rafi'at.



Abdulmaleek, Nainarh, Nailah Rayuwa ta ci-gaba da tafiya ko wani ɓangare hankali kwance sai dai abu ɗaya dake tokarin Rafi'at Rafiq Rayyan mata ga Abubakar Sameer Lamiɗo uwa ga Abdulmaleek Nainarh Nailah shi ne.

Tunda suka yi Aure har izuwa Yau da Yaran su uku.
Abubakar bai taɓa yi ma ta kallon soyayya ba, ko kuma ya furta ma ta kalmar so, wannan abu ba ƙaramin ci ma ta tuwo a qwarya yake ba.
Kawai dai haƙuri takeyi a kullum tana masa uzuri saboda ita ɗin mai ƙaunar shi ne, shiyasa bata ganin laifin sa ko kaɗan.







_______**


Rayuwa ta ci-gaba da tafiya ta ko wani ɓangare abin masha Allah.

Ana cikin haka su Rafi'at suka sha bikin Sailuba da mijinta suma anan Abuja suke zaune da yake mijin nata ɗan kasuwa ne.





____*

Tafe suke cikin motar Abubakar, Rafi'at da Yaran Yayin da Abdulmaleek Babba Yake a back seat Yana wasa ga Nainarh na kusa dashi, sai Nailah a hannun Rafi'at da take zaune gaban mota ita da mijinta Abubakar Mai Kyau.


Tafiya sukeyi ta gefa gefan titi suna ɗan taɓa fira sama sama daga gidan Sailuba suke sun dawo daga kai ma ta ziyara zasu koma gidan su.






Suna firan ne Yayin da Rafi'at take kallon gefan titi cike da Nishaɗi kamar ance ta kalla can gefe wajen wasu bishiyu aikuwa tayi kyakyawan gani, domin kuwa kamar mutum ta hango cikin jini.



Ba tare da fargaban komai ba ko tunanin wani abu ba, ko ɗarsawa zuciya tunanin komai.



Rafi'at ta kalla mijinta Abubakar Mai Kyau cikin murmushi ta ce

"My lawful naga kamar mutum ne fa kwance cikin jini a can gefan wasu bishiyu, please ka tsayar da Motar nan muƙarisa domin mu taimaka ma ta naga kamar macece fa."



Tayi maganar cikin Rarrashi domin kuwa tasan halin abin ta.


Duk da cewa cikin Rarrashi tayi maganar sannan kuma cike da shgagwaɓa amma hakan baisa Abubakar tsayawa ba, saima cewa da ya yi

"Ba wani mutum cikin jini kawai dai idanun kine basu gani dai dai ba."




"Wallahi Ras idanuna suke gani, please ka tsaya mu taimake ta domin naga alamar jini take zubarwa sosai."


Rafi'at ta kumayin maganar kamar zatayi kuka.



Habba jama'a ai fa nan aka shiga ja'inja a tsakanin Abubakar da Rafi'at shi yana faɗin "Ba wani mutum kawai idanunta ne basu gani dai dai ba."


Yayin da ita kuma ta Rantse masa ta kuma Rantsewa akan tabbas mutum ta gani.


Ganin dai bazai saurareta ba idan bata haɗa masa da wani hadisi ko Ayya ba, yasa Rafi'at tayi gyaran murya sannan ta kalleshi da kyau yana tuƙin sa hankali kwance ta ce




"My Lawful a kullum muka zauna zaman fira da Daddynmu abu ɗaya yake faɗa mana, wannan abu ɗayan shi ne "Ku taimaki wanda yake neman taimakon ku, ba tare da tunanin samun wani abu daga garesa ba." Ko kuma Yace mana "Ku taimaki wanda baku sani ba, batare da sa ran wani sakamako ba daga gare shi ba wannan shi ne mutun taka."



"Shin baka mana kwaɗayin samun ladan wannan taimakon da zamuyi a wurin Allah, tunda nake a Rayuwata banajin na taɓa taimakon wani na ƙasa da ni, shin Yau ba zakamin kwaɗayin samun lada ba?.
Yau ɗaya nayi niyyar taimako ba zaka goyamin baya ba, haba mijina haba jarumin jarumai miji a wurin Rafi'at ita ɗaya ka taimaka please pleased..."






Ba ƙaramin sanyi jikin Abubakar Ya yi ba, jin abin da Rafi'at take faɗa shima tunani ya fara shin wai Yaushe Rabon shi da ya Taimakawa wani ɗan adam?. a gaskiya shi kanshi bazai ce ga tsawon lokacin da ya ɗauka ba.






Ba shiri Ya yi Reverse sannan ya yi baya da Motar ya juyo dama tuni sun wuce wurin.
Murmushi Rafi'at tayi tana sauke ajiyar zuciya batasan dalili ba, amma kawai Yau taji tanaso ta taimakawa budurwar da ta hango cikin jini, wacca ko fuskar ta bata hango sosai ba.






Tsayar da Motar Ya yi a dai dai sai tin budurwar dake kwance cikin jini kayan jikinta da suke farare suma sun koma ja saboda tsananin jinin da ta zubar.






Fitowa suka yi shi da Rafi'at daga cikin Motar suka bar Abdulmaleek da Nainarh.

Rafi'at ta Riƙo Nailah a hannunta sannan cikin sauri gaba ɗaya suka ƙarisa gaban budurwar dake kwance.




Sai kuma lokacin tsoro ya fara kama Rafi'at, wannan tsoro bana komai bane saina ganin wani kalar masifaffen kyau da wannan budurwa wacca ta gama yin kaca kaca cikin jini duk da cewa cikin jini take amma wannan bai hana Rafi'at hango tsantsan kyau na musamman da wannan budurwa ke da shi ba.


Cikin zuciyarta tana mai tabbatar wa koda za'a bar wannan budurwa a haka ba tare da tayi wani kwalliya ba a haɗasu Gasar kyau Rafi'at tana da tabbacin duk da itaɗin tana da masifar kyau tofa wannan budurwa sai tayi ma ta zarra.








A fili Abubakar ya furta kalmar


"Masha Allah."


"Allah mai hallita yarda ya so..."


Ya yi maganar yana kuma ƙarewa kyakyawar fuskar ta kallo domin kuwa zai iya cewa tunda Yake a duniya bai taɓa ganin macen da kyau ya yi mata kyau ba sai wannan budurwa dake kwance gaban sa, cikin jini ga idanunta a rufe da alama suma tayi.

Ita ɗin mai kyau ce cikin masu kyau. 🤠🏃👑




Ganin Yadda mijinta Abubakar mai kyau ya tsuguna yana ƙarewa wannan budurwar dake kwance cikin jini dake gabansu kallo, ya sa Rafi'at jan ɗan ƙaramin tsaki cike da jin haushi na Rashin dalili ta ce

"Malam Mai Kyau ka taimaka mu kamata a sakata a mota domin a kai ta Asibitin saboda naga jini take zubarwa fa."


Rafi'at tayi maganar cikin ƙunƙuni ganin kamar bai jita ba yasa ta dage iya ƙarfinta ta ɗaka masa duka a baya tana kuma maimaita masa abin da ta faɗa.



A maimakon taga Yaji haushin dukan da tayi masa, a'a sai ma tsadadden murmushi Ya yi ma ta kana ya miƙe yana gyara hannun rigar sa, ganin haka yasa ta aje Nailah a gefe ita ma ta fara kici kicin gyara mayafin kanta.




"Ke kuma mai zakiyi?."


Taji Abubakar ya tambaye ta, murmushi tayi kana ta ce

"Zan tayaka ne mu cicciɓeta a kaita Asibitin ai."


Tayi maganar tana dariya.🤣


"Saboda kin mayar dani Rago ko me?."


 Ko kafin ta nema amsar da zata bashi tuni taga ya ɗauki wannan budurwa da duka ƙarfin da Allah ya bashi ya nufa motar shi da ita🧐.



Baki wangame 😨 Hanci sake 👃 ido warwaje 👁️👁️fuska ɗauke da matsanancin mamaki 🤔 Rafi'at tabi mijinta Abubakar da kallon ikon Allah.




Ai bata tsaya tunanin komai ba ita ma ta mara masa baya, har ta kusa motar, ta jiyo kukan Jaririyarta Nailah da sauri ta juya Ashe wai saboda tsananin mamaki da matsanancin kishi ne yasa ta manta da jaririyarta a wurin.🤣





Fin ciko Nailah tayi saboda baƙin kishi ko gabanta bata gani da sauri ta ƙarisa jikin motar tana haki, shikuma Abubakar daidai lokacin ya gama daidai ta ma wannan budurwa kwanciya a back seat kusa da Yara.




Fito da kansa Ya yi daga cikin Motar kana Ya kalleta cikin murmushi Yace


"Ina trolley ɗin ta dana gani gefe kin ɗauko kuwa?."




Cike da takaici Rafi'at ke kallon mijinta Abubakar Mai Kyau saboda takaici da kishin da ya zo ya danne ma ta maƙoshi, ta rasa amsar da zata bashi, sai kawai ta tsinci kanta da faɗin!


"A'a ban ɗauko ba dama umarni nake jira a bani aii 😬."




Murmushi ya yi baima kula da Yayin da take ciki ba. To koya kulama Sharewa Ya yi sannan Ya ce

"Okay to your lawful ya bada umarni maza Kije ki ɗauko ma ta trolley ɗin wata ƙila akwai abubuwan ta masu muhimmanci a ciki."





Murmushin yaƙe kawai Rafi'at take yi cikin zuciyarta kuwa tana jinjina wannan ƙarfin hali na Abubakar wai ɓarawo da sallama.

Amma banda ya Raina ma ta wayo wato ita ce zata je ta ɗauko trolley ko ba komai ae.




Ajiyar zuciya ta sauke kana ta gyara Riƙon da tayima Nailah ta nufa wajen da trolley ɗin yake ta ɗauko kana ta dawo, ko kallo Abubakar bai isheta ba taje ta buɗe boot ta saka sannan ta dawo ta buɗe Motar gidan gaba ta shige ta zauna tana faman huci da hura hanci.






Shigowa shima Abubakar Ya yi sannan ya tayar da Motar suka ɗauki hanya firan da sukeyi ɗazu ma ko shi ba'ayi Yanzu. Tafiya suke tsit Abubakar ne ma da ya gaji da tsit ɗin ya kunna karatu a Radio na Motar.

Su kuwa Yaran tuni sunyi bacci amma banda Abdulmaleek da ya zubawa wannan budurwa ido yana kallo kamar ya sama TV.


Rafi'at tana lura dashi ta madubin mota qwafa taja tana kuma tamke fuska.





Wani emergency suka iso da ita ba tare da da ɓata lokaci ba Abubakar bayan ya fito ya buɗe back seat ta ɓangaren da ya kwantar da wannan budurwa sannan ya fito da ita.

A lokacin wasu Nurses biyu sun turo gadon ɗaukar marasa lafiya, dan haka cikin sauri ya kwantar da ita saman gadon sannan aka ja suka nufa ciki tare da shi.






Ita kuwa Rafi'at zama ta gyara a motar tana jan tsaki.


Abubakar ya daɗe ciki bai fito ba sai da ya kammala duka abin da ya kamata dan ma shiɗin sananne ne daɗi da ƙari ga Naira shiyasa ba tare da wani ja'inja ko ɓata lokaci ba likitocin suka karɓa budurwar, sai da ya tabbatar da an shiga da ita ɗakin hutu bayan likitoci sun gama bata taimakon da ya kamata sannan ya fito da niyyar zuwa anjima idan ta farfaɗo sai su dawo ganin ta da yake lokacin dare ya fara kawo kai.





Tana zaune harta fara gyan-gyaɗi ta hangoshi Yana nufo motar, ajiyar zuciya ta sauke ta ƙirga a dadin lokacin da ya ɗi ba a ciki kusan awanni biyu.

Gyara wa Nailah kwanciya tayi a saman jinyarta sannan Ita ma ta sai ta zaman ta kana ta rufe idanunta kamar mai bacci.




Buɗe motar Ya yi sannan ya shiga bayan ya kammala abin da ya kamata ya tayar da Motar suka bar emergency ɗin sannan ya ɗauki hanyar gidan sa.




A hanya jin shiru taba yi masa magana ba, yasa ya ɗan juyo da fararen idanun shi yana kallonta duk a tunanin sa tayi bacci ne.

Ya yi murmushi a fili Yace

"Mata iyayen kishi."



Tana jin sa tayi muluqwiii kamar mai bacci.



Har suka ƙariso gida Ya daidaita faker motar a wurin da aka tanadar domin yi bayan gate man ya wangale masa gate.




Bata koyi motsi ba, hakan yasa Abubakar ɗan bugun kafaɗunta yana kiran sunan ta.

Ƙin motsi tayi shi kuma yaƙi denawa haka ba yadda ta iya, ta buɗe idanun ta tana hamma ta Kalle sa cike da ƙissa ta ce


"Oh My Lawful am sorry har mun ƙariso gida ban samu na tayaka fira ba bacci ya yi gaba dani."





Murmushi Abubakar ya yi ma ta sannan yace


"Aah karki damu kinji, matar mai kyau,  nasan akwai gajiya fa sosai."




Fitowa suka yi gaba ɗaya shiya taimaka ma ta wajen kwashe Yaran suka shiga ciki.
Shi Maleek aka kai shi ɗakinshi Yayin da suma sauran ta wuce dasu nata bedroom ɗin, shima Abubakar ya wuce nasa dukanin su a gajiye suke over.


 



___*💋 SARAUNIYAR KYAU 💋*___________________________________________________________________💥👑𝑻𝒉𝒆 𝑮𝒍𝒂𝒎 𝐐𝐮𝐞𝐞𝐧👑💥____________________𝑩𝒚:𝑻𝒉𝒆 𝑵𝒂𝒊𝒏𝒂𝒓𝒉 𝑲𝒅____𝑲𝒉𝒂𝒅𝒆𝒆𝒋𝒂𝒓𝒕𝒉.  𝑺𝒂𝒃𝒊'𝒖.  𝒀𝒂𝒉𝒚𝒂𝒉🤙


Page *65&66*




*WASH£ GARI*






Tana tsaye a kitchen sanye cikin kayan shan iska ta ɗaura apron saman kayan tana haɗa musu Breakfast cikin nutsuwa take komai abinta.



Alamar taku da ta jine yasa ta tsaya da abin da take yi sannan ta juyo.

Da tsananin mamaki take kallon mijinta dake tsaye gabanta sanye cikin doguwar jallabiya Brown tunani take shin ko ya yi makuwa ne ko me, amma in banda haka mai zai kawo shi kitchen bayan tunda suka yi Aure shekaru wajen nawa ko tunanin shiga baya yi, ko irin yace zai taya ta girki, a'a sai dai wani ba Abubakar sai dai ta girka yaci ba godiya balle 🥰....




A je tunanin tayi a gefe sannan cikin murmushi ta ce

"Barka da safiya My Lawful Fatan dai ba neman wani abu bane ya kawo Babban mutum kamar ka kitchen, kai da kanka baka nema wannan servant naka ba a domin ka bata umarni ba."



Murmushi Abubakar Mai Kyau Ya yi sarai ya fahimci abin da take nufi wato dai gatse tayi masa ko ba damuwa, gyara tsayuwar sa ya yi kana Yace


"Ko ɗaya dama nazo ne na faɗa miki ki girka abinci daban saboda..."

Da sauri ta katse shi da faɗin

"Baƙi zamuyi hala, ai karka damu Yanzu zan kammala sai na saka a kuloli, kaje kayi shirin office kawai oga."


Tayi maganar tana juyowa ta ci-gaba da aikin da take yi, bai kuma cewa komai ba ya fice shima daga madafar.





__*

Wuraren ƙarfe Takwas da Rabi a Ranar tana zaune saman mattress bayan sun kammala breakfast ne tayi wanka tayi shirin zuwa asibiti, shi ne ta zauna a gefan mattress tana jiran shigowar mijinta Abubakar ɗakin.




Jin shiru bashi ba labarin sa yasa ta miƙe sannan ɗauki lab-coat ɗinta da kuma jakar ta dama tuni ta yafa mayafin ta.



Fitowa tayi kai tsaye ta wuce bedroom ɗin sa tura ƙofar tayi bakinta ɗauke da sallama daga can ta hango sa tsaye sanye cikin shigar alfarma na manyan kaya.

Ɗan dafe kanta tayi ita ta manta Yau Laraba wacca ta kasance first October babu aiki sam.


Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta ƙarisa shiga ciki tana faɗin

"Oh amma a gaisheni, gaba ɗaya na manta da cewa Yau ɗin a Free muke Ranar zagayowar Ƴan cin ƙasarmu abin alfaharin mu."


Tayi maganar tana dariya.
"Karki damu kinji kin kusa samun Abokiyar zama kinga saita dinga tayaki wasu ayyukan inaga idan kika sama Abokiyar zaman zaki rage samun tention da yawa ko kuwa?.."


Tunda Abubakar ya fara maganar Rafi'at take faman antaya masa harara.

Lura da hakan da ya yi ne ya shi canza topic ɗin ba shiri.🤣




Murmushi Abubakar Mai Kyau Ya yi sannan Yace


"Okay to ai babu damuwa a haka ma Yadda kike zaki iya Rakani izuwa unguwa tare da Yara."



"Unguwa kuma to wurin wa."


Rafi'at ta tambaya cikin suɓutar baki.



"Kedai kawai ki shirya zaki gani ai."


Abubakar ya bata amsa, bata kuma cewa komai ba ta miƙe tana kallon sa sannan ta ce

"Ka bani mintuna biyar Yanzunnan zan shirya shaf-shaf."


Tayi maganar tana nufar ƙofa ta buɗe sannan fita.



Tana fita bedroom ɗin ta ta wuce tana shirya wa tana tauna maganganun Abubakar wato Abokiyar zama, kuma ita hmmm, murmushin Takaici tayi a fili ta ce

"Rafi'at Rafiq Rayyan tafi ƙarfin ayi ma ta kishiya har duniya ta naɗe forever Wallahi."




Tsaf ta gama shirinta sannan ta ɗauki jakar ta da mayafinta ta fito waje har lokacin bata gama dawowa dai-dai ba domin kuwa har wani zazzaɓine taji Yana shirin kamata jin maganar kishiya, wai danma da wasa ya yi ma ta maganar, imagine take yi to da'ace da gaske Abubakar Yake wannan maganar ya zatayi ke nan."


A fili ta ce "Sai dai idan bani a duniyar."





Downstairs ta sauko daga can saman kujeru ta hango mijinta Abubakar ga Yaranta suma a shirye cikin shigar alfarma suna fira da mahaifinsu Abin gunin ban sha'awa.


Murmushi kawai take yi tuni ta manta da maganar wata banza kishiya, hango mijinta da tayi da Yaranta cikin farin ciki.



Sai ita ma ta tsinci kanta a cikin matsanancin Farin ciki taji gaba ɗaya baƙin cikin da Abubakar ya ƙunsa ma ta na maganar kishiya ya gudu.



Qarisowa wurin tayi fuska ɗauke da ƙayataccen murmushi tana faɗin

"Oh My Lawful ayi haƙuri dani na ɓata muku lokaci daya wa ko?."


Tayi maganar cike da ƙissa, murmushi Yayi Yace

"Oh no Yaranki sun qwace ki saboda sun zagaye mahaifin su suna masa tatsuniya."



Tana dariya ta ce "Ai haka ake so."


Abdulmaleek Yaron da bazai wuce shekaru huɗu da watanni ba a lokacin ya kalla mahaifiyar sa kana ya mayar da kallon sa akan mahaifin nasa dariya ya yi cikin qwaranci irin na sa Yace


"Daddy! Mommy!!."


Gaba ɗaya suka juyo suna kallon shi Yace
"Momy Daddy Yafi ki kyau cocai cocai."🤣



Dariya suka yi baki ɗaya kana Rafi'at ta ce

"Aha ai kowa ma haka ake cewa harni ma na sani saboda shiɗin kyakyawane a cikin kyawawa."


Tayi maganar cike da nishaɗi, miƙewa suka yi ita ta riƙe Nailah Yayin da Abubakar Ya ɗauki Nainarh sannan Ya riƙe hannun Abdulmaleek suka fita waje, motar sa suka shiga baki ɗaya sannan ya tayar da Motar, gate man ya wangale masa gate ya fita sai unguwa🚗..../This is the happiness family/....🚗







***





Cak murmushin dake akan kyakyawar fuskar ta ya gushe fuskarta ta koma Tamkar bata taɓa murmushi ba, saboda tsaban mamakin wurin da taka mijinta Abubakar ya dawo dasu "this is unbelievable."

Wato shiyasa taka jiya da dare ya fita bai dawo ba sai wuraren sha ɗaya Abin da bai taɓa ma ta ba.


Kallon sa tayi dai dai lokacin da shima ya juyo da kallon shi akanta, cike da tsaban takaici ta ce

"Haba My lawful yana ga ka dawo damu wannan emergency kodai wani ne aka kwantar ban sani ba?."


Tayi maganar cike da sa ran ya bata amsa ba kalar wanda take tunani ba.




Gimtse kyakyawar fuskar sa ya yi alamar ba wasa kana ya ce

"Wurin Ƴar uwanki muka zo domin tafiya da ita gida."


Ya mutsa fuska tayi cike da alamar tambaya take kallon sa sannan ta ce


"Wacca Ƴar uwata kuma Sailuba ba ko wa?."





Girgiza ma ta kai ya yi alamar a'a kana Yace


"Fito mu shiga zakiga ko wacece ai."


Babu musu ta buɗe motar ta fito shima bayan ya fito suka riƙe Yaran sannan suka nufa ciki Yayin da wasu Nurses ma ta ke bin bayan su da kulolin abincin da suka zo dasu.





Ita dai Rafi'at tafiya take kawai amma gaba ɗaya hankalin ta baya a jikin ta tunani take shin ko wurin waye haka Abubakar ya kawo su, ita ko kaɗan bata kawo wannan budurwa da suka taimakawa jiya a tunanin ta.


To akan me ma zatayi tunanin ko ita ce bayan cewa taimakon ta kawai suka yi bawai zasu kasance da ita bane.






Har suka ƙariso Ward ɗin bata ankara ba, har sai da taga waɗanan Nurses dake gabansu sun shiga wani Room kana ta fahimci nanne Room ɗin da wacca suka zo wurinta take.



Tura ƙofar Room ɗin Abubakar ya yi ya shiga Bakin sa ɗauke da sallama yayin da ita ma Rafi'at ta take masa baya.





Zaune take a saman gadon marasa lafiya jikinta sanye da kayan asibiti gaban ta kuma tufa ne take ci a hankali, kanta a duƙe tana kallon ƙasa, sai da ta cinye Wanda yake a bakinta sannan ta amsa sallamar da taji anayi a daidai lokacin da ta ɗago da kanta tana kallon mutanen dake shigowa ɗaya bayan ɗaya take binsu da kallon Rashin sani.





Wani irin bugawa ƙirjin Rafi'at Ya yi ganin kyakyawar fuskar budurwar dake a ɗakin zaune saman bed.



It's unbelievable menene kuma haka me yasa Abubakar ya dawo dasu wurin wannan to su mata Mene?.





Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta sama wuri ta zauna a saman wata farar kujera kusa da mijinta Abubakar da shima ya zauna.




"Sannun ku fa please Mister and Mrs kune kuka taimake ni. In Yesterday?."




Budurwar ta musu tambayar fararen haƙoran ta duka a waje saboda murmushin dake akan kyakyawar fuskar ta.



Har Rafi'at ta buɗe baki zata bata amsa ke nan, likita ya turo ƙofar room ɗin ya shigo yana mai musu sallama.




Shiru Rafi'at tayi kamar mai tunani tana ji lokacin da su Abubakar da wannan budurwa suka amsa masa sallamar amma ita tafasar da zuciyarta take bai bari ta amsa ba.




Bayan wannan likita da Abubakar sun gaisa ne, budurwar ta kuma antayo musu tambayar ɗazu.


Murmushi likita ya yi sannan yace


"Kedai Wannan patient nawa kinaso ki gano mutanen da suka taimake ki ko to ai sune waɗannan a gaban ki."




Dariya tayi cike Farin ciki ta kalla su Rafi'at da kyawawan Yaran dake a gaban su ta ce


"Barkanku dai."


Amsa ma ta suka yi da faɗin


"Yauwa kema barka."



Nan kuma suka shiga gaisawa da ita tana musu godiyar taimakon ta da suka yi.


Rafi'at murmushin yaƙe kawai take bin wannan kyakyawar budurwa dashi amma na ciki na ciki.




Kallon kyawawan Yaran tayi cikin shauƙi ta miƙawa Nainarh hannu alamar tazo, aikuwa Yarinyar ta ɓangale baki kana ta ɓanɓare hannunta daga cikin na Rafi'at ta rarrafa da saurinta irin na Yara, ta ƙarisa bakin gadon da budurwar take zaune sannan ta kama gadon tana kici kicin hawa.



Dariya kawai gaba ɗaya suke ma Nainarh wato shi dai Yaro ba Ruwan shi ƙaunar kowa Yake ba abin da ya dame shi.




Da sauri budurwar ta kamo hannun Nainarh tahau da ita saman gadon tana ma ta wasa, aikuwa ganin haka suma Nailah da Abdulmaleek suka ƙarisa wurin da saurin su aikuwa duka ta haɗa tana musu wasa da alama tana ƙaunar Yara sosai obaaaaa.



Kallon Abdulmaleek tayi da yake Babban cikin su sannan ta ce


"My friend please Tell me, what is your name?."


Dariya Yaron ya yi sannan cikin qwarancin sa na yara Yace



"Body."

/Buddy/

Dariya tayi cike da nishaɗi ta ce "Okay wato dai 'Buddy' kake so kace ko?."



Girgiza ma ta kai Yaron ya yi alamar "E," yana dariya.

Ta kuma cewa "To ai na gaskiyar nakeso ka faɗamin."




Ɗan shiru ya yi kamar mai tunani sai kuma can Yayi dariya yace "Abdulmaleek naji Aya Aleem iya kiyana."




"Oh suna mai daɗi."🙂


Ta faɗa tana dariya.

'Kema Menene sunan ki, ko baki da suna ne?."



Yaron ya antayo ma ta tambayar wacca tasa ta yin murmushi sannan ta bashi amsa da


"Maleek ke nan ai kowa yana da suna a duniya kamar nima dai suna na, suna na...."


Shiru tayi kamar tana tunani sai da kyar ta iya faɗi cikin in'ina

"Suna na Ha-Ja-ah..."

Tayi maganar tana dafe qwoqwon kanta da taji kamar zai rabe gida biyu saboda raɗaɗin da yake ma ta.





"HAJARAH."

Rafi'at ta maimaita sunan cikin ranta tayi murmushi a fili ta ce


"Sunan ki mai daɗi kuwa?."


Murmushin ƙarfin hali budurwar mai suna Hajarah tayi tana kuma dafe kanta ta ce da kyar


"Nagode."




"Ah ah kodai kan yana miki ciwo ne,  naga kina riƙewa?."


Rafi'at tayi ma Hajarah tambayar a yayin da take ƙarisawa wurin da take zaune saman bed.


"Eh Auntie sosai yake mugun rasamin jina nake kamar bani ba."


Hajarah ta bata amsa tana rumtse idanun ta.



Jin haka yasa likita ya yi ma Abubakar alama da su fita.

Ba musu Abubakar ya miƙe suka fita daga room ɗin, suka bar Rafi'at tana ma ta sannu haɗe karanto ma ta addu'o'i dan ta fahimci kamar hadda jinnu a zancen.





Kai tsaye office na likita suka wuce bayan sun zauna ne, Abubakar da ya gaza jurewa ya kalla likita cikin son jin ƙarin bayani yace

"Please Dr Khasim ko zan iya samun bayanan Rahoton lafiyar Hajarah kuwa?, danna fahimci akwai abin da yake damunta sosai."





Ajiyar zuciya Dr Khasim ya sauke sannan Ya fara magana


"A gaskiya Mister Mai Kyau akwai abin da yake damun wannan patient Hajarah abubuwa da yawa ma ba abu ɗaya ba."




"Okay Inajin ka kamar mai da mai ke nan?."


Abubakar ya tambaya yana kuma gyara zaman sa sannan ya mayar da gaba ɗaya hankalin sa akan Dr Khasim yana jira yaji abin da zaice.




"To kamar dai Yadda kaji na faɗa Malama Hajarah tana fama da matsaloli daban daban na Farko dai shi ne....


A binkciken da muka gunadanar akan kwakwalwarta shi ne na farko ta manta da gaba ɗaya Ahalin ta da kuma ainihin State da take, sai dai abu ɗaya da ya ba kowa mamaki shi ne....."




Katse sa Abubakar ya yi yana goge zufar da ta karyo masa kana cikin wata kalar murya yake faɗin

"Bangane ba Dr Khasim ban fahimci abin da kake nufi ba kwata kwata wai kana so kace min mutum zai iya mantawa da Ahalin sa ne a dalilin wani hatsari ko kuma taɓin kwakwalwa?."






Murmushi Dr Khasim ya yi sannan ya amsa da


"Of course wannan mai sauƙi ne, amma ka fara dakatawa kaji sauran abubuwan da suke damunta kafin kayi wasu tambayoyin."


Jin haka yasa Abubakar nutsuwa amma zuciyar sa bata bar bugu ba.





Dr khasim ya ci gaba da cewa


"Kamar yadda kaji ne, tabbas ta mance gaba ɗaya memory nata da ya taɓa faruwa a tsakaninta da Ahalinta, sannan kuma ta manta da sunan State da take gaba ɗaya a Brain nata...
Sai dai abu ɗaya shi ne bata manta ko wacece ita ba, ma'ana dai shi ne bata manta sunan ta ba, ko kuma karatun ta ko kuma wani burin ta bata manta dasu ba, sai dai kuma ɓangaren Ahalin ta dai...
A bisa binkciken da muka gabatar shi ne zata iya tunawa da Ahalinta da kuma sunan State nata kamar nanda shekara ɗaya ko fi ye da haka a bisa hasashen wasu manyan likitocin duniya...
Amma idan shekara ɗaya tazo ta wuce wata shekarar ta zagayo bata tuna komai ba, tofah sai dai ayi haƙuri domin kuwa har abada ba zata taɓa tuna komai ba...."





Ido waje wannan karon Abubakar yake kallon Dr Khasim saboda tsananin mamaki ma kasa cewa komai ya yi kawai yana tauna maganganun Dr Khasim ne.






Sun ɗauki tsawon lokaci a haka ba Wanda ya iya cewa komai, sai can bayan kamar mintuna biyar.
Abubakar ya nisa sannan yace


"Dr Khasim ina da wata tambaya ɗaya fa."


Murmushi Dr Khasim ya yi kana Yace


"Okay Go ahead Inajin ka."



Abubakar Yace "To wai dama can an taɓa samun kalar wannan matsalar ne, mutum ya manta memory nasa da ya taɓa faruwa a tsakanin sa da Ahalin sa a dalilin hatsari ko wani Abun?."



"Eh an taɓa samu a ƙasar China Babban Birnin ƙasar wani mutum ya yi hatsarin mota sai gaba ɗaya ya manta da Ahalin sa da sunan garin sa abin da bai manta ba kawai shi ne shiɗin ɗan kasuwa ne, sannan kuma ƙarin abin mamakin bai manta da harkokin kasuwancin sa ba."







___*💋 SARAUNIYAR KYAU 💋*___________________________________________________________________💥👑𝑻𝒉𝒆 𝑮𝒍𝒂𝒎 𝐐𝐮𝐞𝐞𝐧👑💥____________________𝑩𝒚:𝑻𝒉𝒆 𝑵𝒂𝒊𝒏𝒂𝒓𝒉 𝑲𝒅____𝑲𝒉𝒂𝒅𝒆𝒆𝒋𝒂𝒓𝒕𝒉.  𝑺𝒂𝒃𝒊'𝒖.  𝒀𝒂𝒉𝒚𝒂𝒉🤙


☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆
💦𝑳𝒂𝒇𝒂𝒛𝒊 𝑾𝒓𝒊𝒕𝒕𝒆𝒓'𝒔 𝑨𝒔𝒔𝒐𝒄𝒊𝒂𝒕𝒊𝒐𝒏💦🤙

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆






Page *67&68*



"A ƙasar India an taɓa samun irin haka ba iya nan ba a wasu ƙasashen ma anyi ta samu, amma ni dai a Nigeria wannan ne karo na farko dana tsinci wannan al'amari."

Nan dai Dr Khasim ya ci gaba da yima Abubakar bayani akan matsalolin da suke damun Hajarah.



A taƙaice dai su Abubakar basu suka bar wannan Asibitin ba sai wuraren ƙarfe ɗaya na rana.
Washe gari ma haka suka sake dawowa wurin Hajarah sannan Abubakar ya kuma komawa wurin Dr Khasim ya masa ƙarin bayani akan lafiyar Hajarah.



Sai da suka kwashe tsawon sati ɗaya suna zuwa duba lafiyar Hajarah, zuwa lokacin taji sauƙi sosai, sannan kuma ba ƙaramin shaƙuwa bace ta shiga tsakanin ta da family ɗin Abubakar Mai Kyau dashi kansa dama matarsa Rafi'at, ai ba'a ma maganar Yara su Abdulmaleek domin kuwa wata kalar shaƙuwa ta ban mamaki tayi da Yaran a sati ɗaya kacal.




Zuwa lokacin kuma Abubakar ya gama binkcike akan Hajarah ya gano cewar.
Ita ɗin Ɗalibar psychology ce a wata University dake a nan Abujan, sannan kuma ta kammala karatun gaba ɗaya a Ranar murnar kammala karatun nasu ne ma, bayan an gama, kowa ya watse ita ma tana hanyar ta komawa gidan da take zaune da yake ba'a hostel take zaune ba, shi ne fa wannan hatsari ya auku da ita, Motar da take ciki wasu Ƴan fashi suka tare, ta fito a domin ta gudu wata mota ta bigeta shikuma mai mota yaji tsoron kota mutu ne shi ne ya gudu bai taimaketa ba, shi ne fa su Abubakar suka tsince ta a wurin da abun ya faru hadda jini a jikinta that is all.






To koda Abubakar ya tambaya Hajarah abin da ya faru, anyi sa'a bata manta komai ba, ita ma dai haka ta faɗa masa, a lokacin Rafi'at ta tausaya ma ta sosai domin kuwa abin akwai ban tausayi ace mutum ya manta gaba ɗaya memory nasa wanda ya faru a tsakanin sa da Ahalin sa daɗin daɗawa kuma ace hatta sunan State da yake ya manta abin akwai ciwo obaaaaa.








___*_____*

Satin Hajarah biyu a asibiti mutanen Jigawa State, suka diro Abuja sakamakon kiran su da Abubakar ya yi a waya ya faɗa musu halin da ake ciki.


Kai tsaye Asibitin da aka kwantar da Hajarah suka wuce suma dai bayan isansu suka kuma tabbatar da abin da Abubakar ya faɗa sun tausaya ma ta sosai, musamman da ya kasance suɗin likitoci ne sun san matsalar abin Especially ma Hajiya Zuwairiya da ya kasance ita ɗin ɓangaren ta karanta wato Brain.




___*


Kwanan su biyu suka juya Jigawa State da Hajarah a bisa shawarar da gaba ɗaya suka yanke na qwara ta koma hannun su da zama, kafin asan abin yi tunda ba za ta iya tuna komai ba, indai ɓangaren da ya shafi Rayuwar ta da family nata ne.


Wannan konawa Jigawa State da zama na Hajarah ba ƙaramin faranta Ran Rafi'at ya yi ba, domin kuwa a da sosai ta damu da inda Hajarah ɗin zata zauna tsoro take kar ta barta a gida ita gata ba mazauniya ba wani abu yazo ya shiga tsakanin ta da mijinta. 🤦




Su kuwa ta ɓangaren Yara ba ƙaramin kewar Auntyn su Hajarah suke ba domin kuwa a ɗan sati biyu da suka yi a tare da ita, shaƙuwa ce sosai ta shiga tsakani domin ko Ranar da su Hajiya Harirah zasu koma Jigawa State da ita ba ƙaramin daru aka sha dasu ba.


Shi kuwa ta ɓangaren Malam mai kyau ni dai Nainarh kd ban ma san abin da zan iya rubutawa da alƙalamina ba, saboda Rayuwar sa ya ci gaba da gudanar wa kamar ko yaushe cike da Nasara ta gefe ɗaya kuma ga Ahalin sa.





Sai dai kuma me?.


Sati ɗaya ya wuce, aka zo sati biyu, ita ma ta wuce sai kuma a lokacin Abubakar ya fara jin kewar ta amma dai ya daure, sati ɗaya ya kuma wucewa abu ya kuma girmama, aikuwa ba shiri ya kwashi matar sa Rafi'at da Yaransu suka bi jirgin yamma sai Jigawa State a cewar sa ganin gida zasuje, aikuwa anyi murna da Farin cikin zuwan su sosai barinma dai Hajarah da tayi kewar Yaranta kamar yadda take faɗa, a lokacin kuma Sagir da matar Suwaiba sun daɗe da kammala karatun su, da farko a Rivers State suka fara zama sai kuma daga baya suka koma Kano ɗungurun gun da zama, suma dai sunzo ganin gida da Yaran su biyu a lokacin aikuwa nan aka haɗu.
Kwanan su Abubakar uku a Jigawa State suka koma Abuja saboda yanayin aikin su.







***

Rayuwa ta ci gaba da tafiya Yayin da da Abubakar ya tsiri sabon abu duk bayan wata ɗaya ko sati biyu sai ya uzzurawa Rafi'at sun tafi Jigawa State haka take haƙura suje su dawo.
Da dai taga abin nashi bana ƙarewa bane, wata Ranar lahadi da dare da ya same ta da maganar zuwa Jigawa State gobe sai ce masa tayi.

"Ita fa Wallahi wannan zuwa Jigawa ta gaji dashi, wai tukunna mai yake zuwa yi ne da yake uzzurawa sai an tafi?."


A lokacin murmushi Abubakar ya ma ta sannan Yace

"Nan da lokaci kaɗan zaki sani ko menene..."
Daga haka kuma ya sha re maganar suka dauko wata.



Washe gari kuma ya same ta da maganar zuwa Jigawa aikuwa kai tsaye ta ce masa "ita da Yaranta ba inda zasu sun yafe."




Rayuwa ta ci-gaba da lulawa yau da daɗi gobe babu yayin da Mister Mai Kyau a duk ƙarshen wata sai yaje Jigawa State abin da bayayi a baya.


___*

A wani zuwa da ya yi ne wata Ranar Saturday mahaifin sa Alhaji sameer Lamiɗo ya yi masa wata tambaya, lokacin da suka kaɗaice a palon Alhajin tambayar da ta saka shi yin murmushin jin kunya yana yin ƙasa da kansa

A lokacin kallon Ɗan sa Abubakar Alhaji Sameer Lamiɗo ya yi cike da kulawa sannan ya nisa bayan ya kira sunan Abubakar ya amsa ya ce.

"Wai kuwa nace wannan zuwa da ake mana ba hutu anya ba wani abu ake nema a wurin mu ba kuwa?."


Ya yi maganar mai harshen damo cikin kulawa yana ƙarewa ɗan nasa kallo.



A lokacin ƙasa da kai Abubakar ya yi cike da kunya tabbas maganar Abbhee haka ne daga ƙarshen ƙarshe dai bayan Haleesat Rashid Rayyan yaga wata Ɗiya mace da yaji yana ƙaunar ta fi ye da komai na Rayuwa yana son ta yana ƙaunar ta fi ye da komai idan yace komai tofa koman komai yake nufi.







Ajiyar zuciya ya sauke a karo na ba adadi sannan ya ɗago yana kallon mahaifin su Alhaji Sameer Lamiɗo kamar yadda shi ma shi ɗin yake kallo, ko kafin ya sama zarafin yin magana Alhaji Sameer Lamiɗo ya riga sa da faɗin


"Iyalinka tasan da maganar kuwa?."


Ɗan waro ido Abubakar ya yi sannan kai tsaye Yace

"A'a bata sani ba, amma dai zata sani nan bada jimawa ba."


Murmushi Alhaji Sameer Lamiɗo ya yi sannan ya kuma cewa ita ɗin ta sa ni kuwa ko kuwa soyayyar ɓangare ɗaya ne?."





"Eh tasani amma dai ta ce wai tana jin kunyar ku, da kuma mata ta."


Abubakar yaba mahaifin nasa amsa Yana dariya ƙasa ƙasa.

Shi ma dai Alhaji Sameer dariyar yake cike da jin daɗi domin kuwa ya yaba da Tarbiyar Yarinyar obaaaaa.



Suna cikin haka saiga Hajiya Harirah ta shigo da yake ita keda turaka, ƙarisawa ciki tayi tana faɗin

"Ikon Allah kace zance ya yi daɗi tunda naga ana faman sheƙa dariya."




Kallon matar nasa Alhaji sameer ya yi "Bayan ta sama wuri ta zauna, har yanzu fuskar sa a washe take yace

"To dai Ɗanki ya sama mata."

"Ɗana kuma wanne a ciki, kuma wacece matar?."


Tayi tambayar tana binsu da kallon jiran amsa.
"Ɗan ki dai Abubakar Wanda yake zaune a gaban ki a halin Yanzu shi ne ya sama mata kuma ita ɗin Ɗiyarki ce."



Alhaji sameer ya bata amsar tambayar ta.



Cike da farin ciki fuska washe Hajiya Harirah ta kalla Abubakar sannan ta rangaɗa buɗa tana faɗin


"Aikuwa muna ta yashi murna, sai dai kuma abu ɗaya har yanzu ban fahimci wacece matar da ya samu ba fa."




"Toh tunda har yanzu baki fahimta ba kawai kije ki kira mana Ɗiyarki Hajarah zaki fahimci komai ai."


Cewar Alhaji sameer, aikuwa ba musu ta miƙe ta fi ce daga palon ba'a daɗe ba.


Sai gata ta dawo Hajarah na take ma ta baya, wuri ta samu ta kuma zama ita kuma Hajarah ta zauna a ƙasa daga can gefe, sannan ta kuma gaisar da Alhaji sameer ya amsa cikin kulawa sannan
Ya kalle ta cikin kulawa ya fara magana



"Hajarah Ɗiyata kinji haka ake yi, kawai sai muji batu waje. Ashe Ɗiyata tayi miji bamu sani ba."


Ya yi maganar ne cikke da Zoyala.


Qasa da kai Hajarah tayi cike da kunya sai dai bata ce komai ba, ganin haka yasa Alhaji sameer ya ci gaba da cewa

"To Yanzu dai Ɗiyartawa tana son Yayan nata ko kuwa dai..."


Sai ya yi shiru bai ƙarisa ba.

Tun daga kan shi kanshi da ya yi maganar har Abubakar mai neman Auren 😋 da kuma Hajiya Harirah dake gefen mijinta gaba ɗaya suka mayar da kallon su akan Hajarah suna jiran amsar da zata bada.






Tsuru tayi idanun ta na kallon lallausar carpet da da take zaune akai Yayin da zuciyarta ke tariyo ma ta abubuwan Alkhairi da wannan family mai tarin albarka suka ma ta tun daga kan rescue nata da Abubakar ya yi shi da matar sa, da kuma ɗaukota da Alhaji sameer shi da kanshi da kuma iyalansa sukayi daga Abuja zuwa Jigawa State, duk da cewa ta manta da memory nata akan Rayuwar ta da gaba ɗaya Ahalinta hatta sunan State da take ba zata iya tunawa ba.

{ kuma dai masu karatu nasan da yawa daga cikin ku zasu ce to me yasa ba'ayi cigiyarta a gidajen Radio ba, to ku sani cewa wancan lokacin ba ɗaya yake da wannan lokacin ba. Yanzu zamani ya sauya ci-gaba yazo sosai, amma kuma wancan lokacin da babanci nesa ba kusa ba🤳 }
 **The Nainarh Kd 🔥
                           Writer 🔥**






Suka ɗaukota daga Abuja suka dawo da ita Jigawa cikin su, suka ci gaba da riƙe ta da gaskiya da amana ba tare da saran zata biyasu da komai ba, wannan shi ne mutun taka ta gaskiya waɗannan Ahali sun kasance masu mutunci.
Ita kuwa idan taƙi Auren Abubakar to ai tayi musu mugun butulci kuwa.


Murmushi tayi tunawa da tayi wancan zuwan Abubakar yadda yake roƙonta akan ta amince ta Aure sa, koma ba haka ba, ai ita ɗin ta daɗe tana ƙaunar sa dama kunya ce kawai ta hanata, kuma dama ta yanke shawarar samun sa ta faɗa masa. Ra'ayin ta a kansa ehee. 🥰







Kallon su tayi cike da farin ciki a zuciyarta a fuskar ta kuwa cike da kunya ta amsa da


"Eh na amince Abbhee ko dan saboda rescue nawa da ya yi aiya cancanta da ya zama shield a gareni na tsawon har Abada."




Tayi maganar ne a lokacin da ta tashi da gudu ta bar palon tana Rufe fuska.🤦

Gaba ɗayan su dariya sukeyi hadda Abubakar ya yi murmushi Mai Kyau kamar yadda shi ma yake Mai Kyau.



Hajiya Harirah ta ce

"Ƴar nema dama can ana so ake kaiwa kasuwa, to dama wata mara sa'arce za'ayi wa tayin wannan haɗaɗden Lu'u'lu'un Mai Kyau taƙi. ai Abubakar ɗina ɗaya cikin Dalas.😎




Dariya suka yi ai nan aka dasa sabuwar fira a tsakani, domin kuwa Abubakar Mai Kyau jinsa Yake ya gama sa'a tunda har zai mallaki wannan kyakyawar fure haka.




Domin kuwa Hajarah kyakyawa ce first class ta haɗu ta ko'ina tunani Yake anya tuwa bata haɗa jini da turawan Yamma ba kuwa, koda kallon Yanayin gashin kanta mai tsayi da sheƙi ga launin shi abin burgewa shi ba baƙi ba kuma ba Brown ba kai duk Yadda kake tunanin kyau tofa Hajarah ta wuce wurin obaaa...




A Ranar Alhaji Sameer Ya kira duka Ƴan uwansa dake kusa. Ya faɗa musu kyakyawar Albishir sannan kuma a Ranar aka saka Ranar Auren Abubakar Sameer Lamiɗo da Hajarah nan da wata Ɗaya tak domin kuwa Alhaji Sameer cewa ya yi "Gwara ayi ayi."






___*💋 SARAUNIYAR KYAU 💋*_________ƚαƙυɳ ϝαɾƙσ__________________________________________________________💥👑𝑻𝒉𝒆 𝑮𝒍𝒂𝒎 𝐐𝐮𝐞𝐞𝐧👑💥____________________𝑩𝒚:𝑻𝒉𝒆 𝑵𝒂𝒊𝒏𝒂𝒓𝒉 𝑲𝒅____𝑲𝒉𝒂𝒅𝒆𝒆𝒋𝒂𝒓𝒕𝒉.  𝑺𝒂𝒃𝒊'𝒖.  𝒀𝒂𝒉𝒚𝒂𝒉🤙


☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆
💦𝑳𝒂𝒇𝒂𝒛𝒊 𝑾𝒓𝒊𝒕𝒕𝒆𝒓'𝒔 𝑨𝒔𝒔𝒐𝒄𝒊𝒂𝒕𝒊𝒐𝒏💦🤙

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆








Page *69&70*



Abubakar bai sama damar komawa Abuja ba, sai Washe gari ya bi jirgin Safe izuwa Babban birnin Nigeria Abuja, koda ya koma bai sama matar sa Rafi'at da maganar Auren Hajarah da zayyi ba, sai ma harkokin gaban sa ya shiga yi ba ruwansa.




*SATI_ƊAYA_GABA.*



Wata Ranar Sunday wacca Rafi'at ba zata taɓa mantawa da ita a Rayuwar ta ba, ita ce wata Ranar lahadi da Yammaci Abubakar yazo ma ta da maganar ƙarin Aure.

Abin da dai da ya faru shi ne...


A wata Ranar lahadi Rafi'at tana zaune a ƙayataccen palon gidan Wanda yasha kayan ado na duniya ba'a magana, tana sanye cikin shiga ta alfarma hannunta Riƙe da wani Book na Likitoci tana karantawa ga Yaranta a gefe duka sanye jikin shigar Yaran manya suna wasannin su.


Daddaɗar ƙamshin turaren shi ne ya fara kawo wa dogon Hancin ta ziyara, bata iya jurewa ba, sai da ta ɗaga kanta tana kallon kyakyawan mijinta abin alfaharin ko wacce mace ta gari.🥰

Wanda yake tsaye daga tsakiyar staircases sanye cikin kayan shan iska ya ɗaura hannu a waist yana kallon Yaran su cike da Nishaɗi, sannan a hankali ya ƙarisa saukowa daga saman Floor ɗin kana ya ƙariso wurin ta yana sakar ma ta ƙayataccen murmushi Wanda yasa sai da gabanta ya faɗi.

Zama ya yi a 3sieter gefanta ke nan Yana kallonta kamar yadda ita ma ta zuba masa ido tana kallo Like a ta sama TV.


"Matar Mai Kyau Yane ya da wannan kallo haka?."


Abubakar ya yi ma ta tambayar yana dariya.
Murmushi tayi tana faɗin "Mijina Mister Mai Kyau ina son ka, ina ƙaunarka fi ye da Rayuwa ta."

Tsura ma ta ido ya yi yana kallo ya fahimci maganar dake fitowa daga bakinta, ba iya fatar bakinta ya tsaya ba, a'a tunda ga ƙasan zuciyarta take masa maganar, Ajiyar zuciya ya sauke tunani yake anya kuwa ya faɗa ma ta maganar dake a bakin sa kuwa, ko ya fasa sai gaba?.

Kai ina gwara kawai ya faɗa a yau kuma yanzu saboda a kullum lokaci ƙara ja yake yi obaa.




Gyara zamansa ya yi a kujerar yana kuma matsawa kusa da ita, sannan ya kamo hannunta duka biyun kana ya kira sunan ta da wata murya wacca Alƙalamin Nainarh Kd ya yi kaɗan wajen rubuta sufar ta.😘




Amsa wa tayi ita ma cikin faɗuwar gaba maras dalili, ci gaba da cewa ya yi

"Ina so zamuyi wata magana mai muhimmanci dake, shin zamu tsaya anan ne ko kuwa?."


Ya yi maganar idonsa a kanta, murmushin ƙarfin hali ta masa kana ta janye hannunta daga cikin nashi, ta ƙarisa wajen center table ta ɗauko juice a glass cup ta dawo ta zauna ta miƙa masa tana faɗin

"Oh Allah My Lawful ke nan yi maganar ka kai tsaye kawai ba tare da wani shakka ba, kaji nawan."


Ƙin amsar juice ɗin da take miƙa masa ya yi saima cewa da ya yi

"Ina ga ke yafi kamata ki sha wannan Ruwan Ƴaƴan ita cen ba ni ba, ni dai kawai hankalin ki nake buƙata a tare dani."


Wannan karon gyara zama ita ma tayi sai da ta kurɓa juice ɗin hannunta sannan cike da ƙissa da kisisina tana kashe murya ta ce



"Okay My Lawful ina jin ka."



Tayi maganar tana riƙe glass cup na hannunta da kyau.


"Rafi'at Aure zan ƙara nanda sati uku shi ne dama maganar da nakeso muyi dake..."

Ya yi maganar yana zuba ma ta kyakyawan idanunsa kamar mai tsoron ta, bawai fargaba yake ba, a'a kawai Yana tsoron Halin wasu matan....🌚





"Damn All wai Rafi'at Aure zan ƙara nanda sati uku shi ne dama maganar da nakeso muyi dake..."


Ta maimaita wannan maganar a cikin zuciyarta Yafi sau dubu a cikin sakanni uku kacal.

"Damn it..."


Da ƙarfin gaske ta damƙe glass cup ɗin dake a hannunta har sai da glass cup ɗin ya tarwatse aikuwa nan hannunta yahau zubar jini kamar an bude famfo, amma ita ko a jikinta maimaita maganar ƙarin Aure kawai take cikin ranta. "Kaico Wallahi, kaico da Halin wasu mazan,"

To wai ma dakata tambaya ɗaya take dashi wai shin Menene bata yiwa wannan Bawan Allah da zai saka ma ta da maganar ƙarin Aure idan fanin kula dashi a bed ne, tasan tana iyakar bakin ƙoƙarin ta kuma ta tabbata ita ɗin ba raguwa bace, idan kuma a kace ta fannin mutunta shi ne, ko kuma mutunta dangin shi da duk waɗanda suke a Ahalin sa, tasan dole a bata kyautar oscar ta wannan ɓangaren, idan kuma a kace ta ɓangaren kula da Gida da kuma Yarane, wannan ma ajin farko take.

"Kai  kai! No.! No! Way..!!

Bazai yiwu ba, bazai taɓa yiwuwa ba Wallahi..."



Ta faɗa da kuwwa a can ƙasan zuciyarta Yayin da idanunta suka yi jajir na ɓacin rai, tana ji Abubakar ya tashi da sauri can ya dawo da first aid box a hannun sa ya shiga bata treatment a hannunta da ya fashe amma ko motsi ta kasa.


Har ya kammala ya mayar first aid box ma'ajiyar shi sannan ya dawo ya zauna kusa da ita Yana kallonta kamar yadda ita ma ɗin shi take kallo, buɗe baki ya yi zai ma ta magana.


Katse sa tayi da sauri

"Abubakar please ina buƙatar na kasance ni ɗaya ko zan iya samun wannan damar?."



Tayi maganar tana kallon yadda ya saki baki da hanci yana kallonta jin abin da take faɗi iya kar sannin shi da ita bata taɓa kiran ainihin sunan shi ba, sai yau


 "Lallai kuwa an ta ɓota obaaaaa..."

Ya faɗa a ƙasan ranshi yana jin jina kai.


Ganin ya mayar da ita tamkar hoto ne yana kallo yasa taja mugun tsaki sannan ta miƙe da gudu ta haye staircases tana ji Yana kwala ma ta kira amma taƙi tsayawa, domin ji take idan ta ci gaba da kallon sa sai ta kai masa mari bata sani ba.

Ita kanta tasan tana da bad temper obaaaaa, shi yasa take kiyaye wa daga abin da zai ɓata ma ta rai, domin tasan ƙarshen bazai yi kyau ba, gashi a yau mijinta Abubakar yana so ya tayar ma ta da hawan Ruwa.🙆





Wani wawan bugu ta kaima ƙofar bedroom nata, aikuwa ba shiri ƙofa ta buɗe dama babu key a jiki, shiga bedroom ɗin tayi sannan ta mayar da ƙofar ta rufe hadda murza key.




Dafe kanta dake faman sara mata Tamkar zai rabe gida Biyar tayi, tana huci da gudu ta ƙarisa wurin Dress Mirror ta ɗauki wani kwalbar turare iya ƙarfinta ta jefa wa Mirror ɗi wannan kwalbar aikuwa nan take Mirror ya tarwatse, hakan ma bai ishe ta ba, nan ta shiga watsi da kayan bedroom ɗin faɗi take

"Wallahi Abubakar baka isa ba, kayi kaɗan, ba macen da ta isa ta aure ka muddun ni Rafi'at Rafiq Rayyan mata ga Abubakar Mai Kyau, ina Raye a doron duniya wallahi babu macen da takai wannan matsayin..."



Ihu take tana surutai tana watsi da kayan bedroom ɗin.

Ta ɗauki tsawon lokaci tana haka sai da ta tarwatsa komai na ɗakin bata bar komai ba, sannan ta dakata dan kanta.


Komawa gefe tayi ta zauna tana faman haki tanaji Abubakar yana buga ƙofar amma taƙi ta buɗe, duk da magiyar da yake ma ta tana ji taƙi buɗe wa, can kuma taji shiru da alama ya gaji ya koma inda ya fito.🤨



Dogon tsaki taja sannan ta duba a gogon bangon ɗakin ƙarfe Takwas na dare wani tsakin ta kuma ja sannan ta ce a fili

"Ashe ma lokaci ya tafi haka, tashi tayi ta haye saman bed da yake bata da tsarki shiyasa bata damu ba.

Duk yadda taso bacci ya ɗauketa a wannan daren ƙin zuwa ya yi to, ta ya ya ma zai zo bayan taji abin da duk duniya tafi tsana maganar kishiya.



Haka ta kwana bedroom ɗin a hargitse idanunta a buɗe tana kallon ceiling, kiran sallan farko a kunenta a kayi amma ta kasa tashi saboda gajiya sai lokacin ta fara jin gajiyar haukar da tayima Ɗakin.



Ba ita ta tashi daga saman bed ɗin nan ba, sai wuraren ƙarfe bakwai da rabi, sannan ta sauko daga saman mattress ɗin kai tsaye bathroom ta shige tayi wanka bata damu da yanayin bedroom ɗin ba, ta shirya cikin ƙananan kaya bayan ta fito daga bathroom ɗin.




Fitowa tayi daga bedroom ɗin kai tsaye bedroom na Yara ta wuce, sai Yanzu kwakwalwar kanta ta fara dawowa kan sai ti tunani take shin ko a wani hali mijinta da Yaranta suka kwana Ooho.😏




Buɗe bedroom ɗin tayi ta shiga wayam babu kowa, du ba du be ta fara, amma ba Yara ba Sanadin su, hankali a ɗan tashe ta fito waje tana du ba ko'ina, amma ba Yara ba ubansu har bedroom nasa ta duba ba kowa tuni ta fara da ta sanin rufe ƙofar da tayi.






Da sauri ta nufi staircases ta fara taka wa saboda tsananin tashin hankalin da take ciki yasa da bibbiyu take taka benen saukowa Downstairs tayi, ta fara dubawa amma wayam kamar ance ta mayar da kallon ta a ɓangaren da Dining room, aikuwa ta hangosu Zaune gaba ɗaya Yaran da uban suna Karin kumallo.





Da sauri ta nufi wurin har tana tun tuɓe amma bata damu ba, ta ƙarisa wurin tana haki ta ja kujera ta zauna, aikuwa da ganin ta ƙananan Yaran suka fara miƙo ma ta hannu suna dariya.




Ajiyar zuciya ta sauke tana binsu da murmushi, ɗan satar kallon mijin nata tayi, aikuwa tayi kyakyawar gani fuskar nan a Tamke ya haɗe girar sama da ta ƙasa.


Ajiyar zuciya ta kuma saukewa sannan da kyar ta iya haɗiye lomar abincin da takai bakinta kallon Ɗanta Abdulmaleek Tayi ta ce

"Yane Buddy baka ganni bane naga baka min magana ba?."




Kallon mahaifiyar tashi Yaron ya yi yana ɓa ta fuska sannan cikin qwarancin sa Yace

"Momyn ina fici da ke, jiya kin sha Daddy a fyacin lai cocai cocai, kuma a bedroom naca muka kwaya, nida su Nailah kuma ya yi mana wanka Nainarh sai kuka take yi, wai taya emanki, kuma fa Nailah bata futa ba cabulu ya ciga mata idooo..."





Tunda Yaron ya fara magana Rafi'at ta saki baki tana kallon shi cike da tsananin mamaki ashe haka Yara suke da kula tsaf.
Har sai da yakai aya sannan ta sama zarafin yin magana.


"Am so sorry My Buddy jiya Momyn bata da lafiya shiyasa bata kula daku ba, amma ba zata ƙara ba, kaji?."


Tayi maganar tana kama kunne, a maimakon taga Yaron ya sausauto, a'a sai ma ƙara Tamke fuska ya yi kamar yadda ubansa ya yi sannan yace

"Toh melaca aki gayawa Daddy ba ya siyo miki agani?."



Wannan karon baki sake take kallon sa a zuciyarta kuwa ayyana irin zuciya na wannan Ɗa nata take yi

"Aikuwa akwai Babban aiki a gaba na."

Ta faɗa a hankali sannan ta ce

"Toh ai Daddy yana fushi dani shiyasa..."




"A'ina ki kaga ina fushi dake?, ni bana fushi dake, to akan me zanyi fushi dake, bayan ma ni na kar zomon?."


Taji muryar mijinta Abubakar yana faɗin maganar kuma har lokacin bai juyo ya kalleta ba.

Shiru tayi bata bashi amsa ba, sai ma Tamke fuska da tayi, tuno maganar kishiya.
Murmushi ya yi

"Good ke nan dai har yanzu fushi ake da ni ko?."

"A'ina kaji na faɗa hakan?."


Yanzu mana shin zaki iya faɗa mana Abin da kikayi ke kaɗai a bedroom kuwa?."


Taji ya kuma antayo ma ta tambaya.
Kallon sa tayi har lokacin fuska a tamke sannan ta ce

"Aljanuna ne suka taso."

Kofin shayi mai zafi da yake ƙoƙarin kaiwa baki ne ya kusa suɓucewa daga hannun sa jin abin da take faɗa, da sauri ya a je tea cup ɗin a gefe sannan ya juyo da kyau yana kallon ta kamar yadda ita ma take kallon sa.




"Me kikace aljanu kuma, to me suka ce da suka zo?."



Ya tambaya yana murmushin tura haushi.


Aikuwa ta shaƙa, gyara zama tayi sannan ta ce

"Cewa su kayi karkayi wannan Auren da kake shirin yi idan kuma ba haka ba Tom tabbas za'aji a jiki...."



Dariya Abubakar yake hadda Riƙe ciki wato aljanu, sai da ya yi ma'ishi suma Yaran da basu san me yake wiya dariyar ba, suna taya shi sannan ya dakata yana kallon ta Yace

"To waye kuma zai ji a jiki idan ban fasa Auren ba?."



"Jikin magayi mana."



Ta basa amsa, dariya ya kuma yi wannan karon Ita ma tana tayasa sai kuma abin ya koma musu na nishaɗi.



Tun daga Ranar Rafi'at bata ƙara gigin tado maganar kishiya ba, tunda taji shima ya yi shiru anata silly tunanin wata ƙila anfasa Auren ne tunda taji shiru.






______*_____*

Rayuwa ta ci-gaba da tafiya Yayin da a kullum Bikin Abubakar Mai Kyau da Hajarah ƙara matsowa yake Yayin da Amarya take can gidan su ango.




Ɓangaren Rafi'at kuwa zuwa lokacin ta sadaƙar mijinta Abubakar Abin ƙaunar ta, Aure zayyi da gaske, musamman ma da taga anata gyara gyare a gidan sai dai kuma har zuwa lokacin bata san wacece matar da zai aura ba.

Kuma bata Fatan ta san koda sunan wannan mace da zai Aura ne, domin kuwa shi kanshi Auren da Auren ƙaddara ta kira shi acewarta in banda shiga shara ba shanu irin na Abubakar yana da mace kamar ta a ajiye a gida ai bata ga abinda zayyi da wata macen ba




\\hmm hmm ni kuwa da nake a gefe nace Rafi'at ke nan ana nuna miki gabas kina Yamma zaki bi in banda abinki to su mazan aka faɗa miki kamar dutse suke indayyi shiru kawai kafin su wance suyi waje dani 🤫//



Haka Rayuwar ta ci gaba da antaye ta ko wani ɓangare shirya shirye ake, harya kasance saura one week a ɗaura Aure zuwa lokacin kuma mutanen France, Lagos, Kano Mai Duguri, Adamawa State, gaba ɗaya sun hallara gida ana shirya shirye dasu gasu Zuwaira ma dasu Jawaheer da Jummai gaba ɗaya Ahalin Alhaji Sameer Lamiɗo dama sauran dangi antaru ana gudanar da shirya shiryen biki.



___*💋 SARAUNIYAR KYAU 💋*_________ƚαƙυɳ ϝαɾƙσ__________________________________________________________💥👑𝑻𝒉𝒆 𝑮𝒍𝒂𝒎 𝐐𝐮𝐞𝐞𝐧👑💥____________________𝑩𝒚:𝑻𝒉𝒆 𝑵𝒂𝒊𝒏𝒂𝒓𝒉 𝑲𝒅____𝑲𝒉𝒂𝒅𝒆𝒆𝒋𝒂𝒓𝒕𝒉.  𝑺𝒂𝒃𝒊'𝒖.  𝒀𝒂𝒉𝒚𝒂𝒉🤙


☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆
💦𝑳𝒂𝒇𝒂𝒛𝒊 𝑾𝒓𝒊𝒕𝒕𝒆𝒓'𝒔 𝑨𝒔𝒔𝒐𝒄𝒊𝒂𝒕𝒊𝒐𝒏💦🤙

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆





Page *71&72*



To abin ma haka yake ta ɓangaren uwar gidan Abubakar Rafi'at da taga abin dai bana wasa bane ita ma sai ta tashi tsaye ta fara shirya shiryen bikin domin kuwa da shawarar mahaifiyar ta Hajiya Zinaru da kuma ƙanwar ta Sailuba tayi amfani na ta kwantar da hankalin ta ta ɗauki komai ba komai ba dadai ira iren su.




Gaba ɗaya kayan dake cikin gidan Abubakar sai da ya canza su bai bar komai ba, hatta da kayan bedroom na Rafi'at kala ɗaya ya ma ta dana Amarya Harajah.


Ita dai Rafi'at tana daga gefe tana kallon ikon Allah yadda Abubakar yake kashe kuɗaɗe kamar bai san zafin su ba, to dama taya zai san zafin su abin da akwai ba'asan a dadi ba, an tara masa shi ma ya tarawa kanshi.



Tun ana saura kwana biyu ɗaura aure, gaba ɗaya dangin ta na nesa da na kusa suka iso aka fara shirin biki Yayin da dangin miji suma suke nasu a can Jigawa State.



Rafi'at ta kwantar da hankalin ta bata tayar da hankalinta ba, ko kuma na mijinta tun daga ranar da yace zai ƙara Aure ta kulle kanta a ɗaki bata kuma Gigin maimaita hakan ba, ko ma ta ɓata Ransa a'a.

Sai ma dagewa da tayi ta danni kanta da zuciyarta  ita ma tana bada gudun mawar da ya kamata a wannan Aure. Wanda hakan ba ƙaramin kima ya ƙara ma ta ba a idanun mijinta Abubakar. shi dai bazai yi wannan Aure a domin baya ƙaunar matar sa Rafi'at ba, a'a ai sai da so ake zama wuri ɗaya ballanta ma zaman Aure na har abada.



Yana son ta yadda ya kamata, sai dai har wa Yau da ta kama Jumma'a Ranar ɗaura Aure Rafi'at bata san wacece amaryar da mijinta Abubakar zai auro ma ta cikin gida ba, kuma bata damu da ta sani ba, sai ma Sha'anin gaban ta take ba ruwanta tamkar ba ita bace wacca za'ayi wa kishiya.





A tunanin ta Amaryar Ƴar can Jigawa State ce, tunda taga dangin mijin nata suma suna shagalin Bikin a can basuzo nan Abuja an haɗe ba.

"Wata ƙilama Amaryar Ƴar dangi ce suka haɗu dashi shiyasa."


Haka kawai Rafi'at take kawowa cikin tunanin ta sam bata tunanin Amaryar Ƴar wata State ɗin ce ba Jigawa State ba, dalilin ta na wannan tunanin kuwa shi ne tun ana saura kwanaki uku biki mijinta Abubakar ya koma can Jigawa State ana shagalin biki dashi.



Uwar gidan Abubakar Rafi'at da Yamma wuraren ƙarfe biyar na Ranar ɗaura Auren.

Taci kwalliya ta cakare cikin wata Ɗanyar lace golden color ɗinkin Yayi na wancan lokacin, ta cakara ɗaurin sangaya, gaba ɗaya shigar jikinta Ruwan golden color ne, ga wasu arnen Ƴan kunne sarƙa abin hannu komai nata gold, tayi kyau ba'a magana gata dama kyakyawa sai aka ƙara haɗewa, sosai tayi kyau.🥰




Gaba ɗaya ita da ƙawayenta da dangin ta suna zazzaune a ƙayataccen palon gidan suna jiran ƙarisowar Amarya da muqarrabanta, sai faman surutu suke irin na gidan biki, sai dai wannan yasha banban domin kuwa komai cikin nutsuwa irin na cikakkun ƴan boko masu ji dukiya suke yi.🙃




Sai dai kuma me?, wani abin mamaki tun ana jiran ƙarisowar Amarya da muqarrabanta da wuri, har aka kai can cikin dare, amma abu shiru ba Amarya ba dangin ta.



Abu dai kamar wasa har gari ya waye babu alamar dangin Amarya da ita kanta.
Tun Rafi'at tana ɗaukar abin wasa har hankalinta ya fara tashi, ganin har an kwashe kwanaki biyu da biki, amma dangin Amarya ba labarin su, ga kuma mijinta Abubakar shima dai bai dawo ba, gashi a wancan lokacin bama waya kaɗai ba, hatta cibiyar sadarwa ƙaranci yake.





Tsoron ta Allah abu ɗaya take tsoro karfa ace Abubakar ya raba musu gida ne ita da wannan amaryar da ya ƙara ma ta aikuwa da bai kyauta ma ta ba.




A Rana ta uku da ɗaura Aure ne, zuwa lokacin gaba ɗaya dangin ta da ƙawaye sun watse sai dai ƙanwar ta Sailuba ce da kuma wata Yayarta Badi'atu sai kuma wasu dangin ta su uku kacal, suka rage basu tafi gidajen su ba.

Suma dai shirye shiryen tafiya suke zuwa dare.


Gaba ɗaya suna zazzaune a palon gidan sunyi jigum jigum, barin ma dai ita Rafi'at da abin duniya ya ma ta yawa a kai.
Tunani take shikenan fa yanzu mijinta Abubakar yana can tare da Amaryar sa a wani gidan suna shan shagali an barta anan jigum gum. 😭






Suna cikin haka kowa da tunanin da Yake yi, suka ji dirar motoci ba ɗaya ba biyu ba.
Sai shigowa suke yi, ba bu wacca tayi gigin tashi daga cikinsu, har zuwa can mutane suka fara shigowa, suna nan zaune.

Ba ƙaramin mamaki Rafi'at tasha ba, ganin dangin mijinta Abubakar sune suke shigowa ga kuma wata lulluɓe da mayafin da ya rufe ma ta fuska da jiki da alama ita ce amaryar.


Ko waccensu da buɗa ri-ri-ri take shigowa, har suka wuce ɗan wani korido Wanda kai tsaye zai sadasu da ɓangaren Amaryar.



Ita dai Rafi'at da sauran dangin ta da suke zaune a palon ikon Allah kawai suke kallo.

Sailuba ce da ta gaza haƙuri ta kalla Yayarta Rafi'at ta ce

"Wai Auntie Rafi'at kamar idona dangin mijin ki nake gani sun kawo Amarya, aikuwa indai haka ne, kin kaɗe daga ke har ganyenki wallahi."



Shiru kawai Rafi'at tayi bata kula surutun Sailuba ba.



Da dare wuraren ƙarfe Takwas su Sailuba suna zaune a palon Rafi'at suna taɓa fira. Yayin da ita kuma take daga cikin bedroom nata abin duniya ya ishe ta.



Sallamar su Jawaheer ne yasa su Badi'atu da Sailuba dama sauran matan dake Palon suka yi shiru da surutun da suke yi sannan suka amsa musu sallamar.

Ƙarisa shigowa matan wajen su biyar suka yi yayin da da Amaryar take tsakiyar su lulluɓe cikin mayafi kalar kayan jikin ta.
Gaba ɗayan su wuri suka samu suka zazzauna kana aka shiga gaishe gaishe tsakani, dama can Sailuba dasu Jummai sun san juna sosai.


Tashi Sailuba tayi tana faɗin "Bari dai na kira Auntie Rafi'at domin naga kamar bata san da shigowar ku ba."



Tayi maganar tana nufar hanyar bedroom na Rafi'at, gaba ɗaya suka bita da ido bayan sun amsa ma ta.




Ba'a ɗauki lokaci mai Yawa ba, sai gasu sun dawo tare, wannan karon Rafi'at sanye take cikin dogon hijjab blue color, dan haka, ba'a ce. ga kalar shigar jikinta ba.

Zama suka yi a 2sieter sannan Rafi'at ta gaisa dasu Jawaheer, dama can basu samu sun gaisa ba.

Sai kuma aka shiga bawa Rafi'at Amanar Amarya Hajarah.

Jinsu kawai take tana kuma bin su da kallo fuskar ta ɗauke da murmushin yaƙe can ƙasan zuciyarta kuwa

 "Humm hmm hmn...."


Har suka gama abin da ya kawo su suka ƙara gaba, Rafi'at bata ce musu ko ci kanku ba, sannan kuma ko fuskar Amaryar bata gani ba, har suka koma inda suka fito, tana zaune tana saƙa abinyi.

Can ma su Sailuba suka ma ta sallama ko wacce ta kama gabanta.




Ita kuwa ta ɓangaren Amarya Hajarah Babban abin da ya hana ta buɗe fuskar ta a gaban Rafi'at shi ne, ba tasan da wani ido zata kalla Rafi'at ba, sannan kuma ba tasan wani kalar kallo Rafi'at zata ma ta ba, kallon mayaudariya na miki alkhairi kin sakamin da Auren miji?, ko kuwa kallon nagode da kika Aura mijina?.

Tasan dai Auren ta da Abubakar Wanda yake matsayin miji a gareta, wani ikon Allah ne kawai domin kuwa cikin wata biyar komai ya faru tun daga rescue nata da suka yi, da kuma komawar ta Jigawa State wurin su Hajiya Zuwairiya da zaman ta a can.
Dama Auran ta da Abubakar da ya biyo baya komai a cikin watanni biyar kacal ya faru.





Rafi'at mata ga Abubakar Mai Kyau kuma uwar gidan sa, ganin da tayi kowa ya watse an barta, gashi har wuraren goma Abubakar bai shigo gidan ba, to koma ya shigo bata sani ba.

Yasa ta kwashi Yaranta gaba ɗaya da suka yi bacci a nan palon ta shige bedroom ɗinta dasu ta rufe ƙofa.



Washe gari ma tunda ta fito da asuba ta girka ma Yaranta abincin da zasu ci ta kwashe a kula ta koma bedroom ɗin ta, ta kuma rufo ƙofa bata kuma buɗewa ba har wuraren sha biyu na Rana, tana jiyo hayaniyar su Jawaheer sama sama da alama suna shirin komawa Jigawa State ne.

Amma ko fita bata yi ba, har tayi baccin da bata samu tayi ba, a daren jiya, ta tashi taga Yaran gaba ɗaya suma baccin wahala suke yi saman bed ɗin kusa da ita, amma banda Abdulmaleek da Yake can gefe Yana wasa da Teddy Bear abin shi.




A hankali ta sauko daga saman gadon tana ji cikin ta Yana ma ta ƙugin Yunwa domin kuwa Rabon ta da taci wani abu, tana ganin takai kwana biyu, tana shirin shiga bathroom taji muryar Abdulmaleek Yana kiran sunan ta, juyowa tayi tana kallon sa kana ta ɗaga masa kai alamar "Menene."




                   



___*💋 SARAUNIYAR KYAU 💋*_________ƚαƙυɳ ϝαɾƙσ__________________________________________________________💥👑𝑻𝒉𝒆 𝑮𝒍𝒂𝒎 𝐐𝐮𝐞𝐞𝐧👑💥____________________𝑩𝒚:𝑻𝒉𝒆 𝑵𝒂𝒊𝒏𝒂𝒓𝒉 𝑲𝒅____𝑲𝒉𝒂𝒅𝒆𝒆𝒋𝒂𝒓𝒕𝒉.  𝑺𝒂𝒃𝒊'𝒖.  𝒀𝒂𝒉𝒚𝒂𝒉🤙


☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆
💦𝑳𝒂𝒇𝒂𝒛𝒊 𝑾𝒓𝒊𝒕𝒕𝒆𝒓'𝒔 𝑨𝒔𝒔𝒐𝒄𝒊𝒂𝒕𝒊𝒐𝒏💦🤙

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆




Page *73&74*


Gimtse kyakyawar fuskar sa yaron ya yi sannan yace

"Momy melaca kika kulle mu a bedroom, bayan Daddy ya yi Mana cabuwar Auntie?."🤔.



Cike da maɗaukakin mamaki Rafi'at take kallon Yaron nata, tana mamakin kaifin tunani irin nasa.
Ashe duk wannan abin da ake ciki yana kula da komai duk da cewa cikin qwarancin sa na yara ya yi maganar amma ta fahimci komai.


Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta koma ta zauna a saman bed kana ta masa alama da hannunta naya ƙariso.


A je Teddy ɗin ya yi a gefe sannan ya ƙarisa wurin ta.

 Kallon sa tayi kana ta fara magana cikin ɗaure fuska

"Buddy Mine, faɗa min tsakanin ni da Daddyn ku waye kafi so?."


Da sauri Yaron ya kalleta jin abin da ta ce Duk da cewa shiɗin Yaro ne, amma ya fahimci wani abu daga cikin maganar ta, dariya ya yi sannan yace


"Momy ke can ai nafi con Daddyn a kanki." 🤪




Ɗiif wutar Rafi'at ya ɗauke na wani lokaci kana da kyar ta iya furta

"Saboda me kafi son Daddyn ku a kaina?."

Har Yanzu Yaron dariya yake sannan cikin qwaranci yace

"Caboda cima Daddy yana cona kuma baya min faɗa idan nayi wani kuch kuye cai dai ya min nasiha kuma ya bani chakuleti da yawa kuma yana kula dani cocai cocai."



Shiru Rafi'at tayi tana kallon Yaron a kullum kaifin basirar sa ƙara nin kuwa yake Yaron brain ɗin sa tana ja sosai.




Ajiyar zuciya ta kuma saukewa sannan ta ce
"Saboda haka ne kawai kafi son Daddyn ku a kaina ko?."


Girgiza ma ta kai ya yi alamar "Eh,"  murmushin mugunta tayi kana tana faɗin

"Yanzu idan ni ma na dena maka faɗa, sai dai nasiha kuma ina kula da kai sosai, ina baka chakuleti cikin basket da komai da komai zaka soni fi ye da Daddyn ku, kuma zaka dinga jin magana ta?."





Abun ka da ƙaramin Yaro yaji maganar chakuleti cikin basket, Aikuwa da sauri ya shiga girgiza ma ta kai alamar "Eh, ya amince.
Murmushi tayi nan dai ta ci gaba da janshi da fira, tuni ta manta da wata Yunwa.








**
Wuraren ƙarfe Takwas na Daren Ranar Rafi'at tana zaune a palon dake ɓangaren ta Yaranta zagaye da ita suna ma ta qwaran cin su na Yara tana biye musu.



Abubakar Ya yi sallama yana shiga ciki, da kyar ta iya amsa masa sallamar dan ma kawai tasan matsayin ta ne a Addini shiyasa.

Ƙarisa shigowa ya yi sannan ya sama wuri ya zauna kusa da ita, aikuwa da ganin sa Yaran gaba ɗaya suka dawo wurin sa cike da farin cikin ganin sa, shima dai nan ya shiga nuna musu Kalar ƙaunar da yake musu.





Sai faman satar kallon sa Rafi'at take yi ta ƙasan ido. Ƴan kwanakin da tayi bata gansa ba, sai taga kamar anƙara masa wani kyau na musamman fi ye da Wanda ta sansa dashi a baya.



Ajiyar zuciya ta sauke tana danne kishinta a kansa tuno wai a halin Yanzu ba ita kaɗai bace matar sa akwai wata a gefe.🤨




"Matar Mai Kyau ina ga da kin dena satar kallona, domin ni ɗin gaba ɗaya naki ne, gwara ki fito fili ki kalleni san ranki, dan bamai hanaki kinji tawan."😅



Duk wannan maganar Abubakar Mai Kyau ne yake antayo ma Rafi'at a lokacin da ya juyo da kallon sa a kanta.

Ɗan murmushi tayi ko banza taji daɗin abin da ya faɗa wato hakan na nufin ke nan mijinta har yanzu yana ƙaunar ta duk da bai taɓa fitowa fili ya faɗa ma ta ba, ta fahimci Abubakar shiɗin na musamman ne a cikin mutane, domin kuwa baya bayyana abu da baki sai dai ya yi shi a aikace.



"Kodai matar Mai Kyau tana azumin magana da mijin nata ne. Yana ta magana babu amsa."


Abubakar ya kuma faɗa cike da Zoyala, murmushi tayi kana ta ce

"A'a kawai dai matar Mai Kyau tayi kewar My Lawful ɗin ta ne obaaa."





"To gashi ya dawo sai matar mai kyau ta kwantar da hankalin ta domin kuwa Lawful ba inda zai ƙara tafiya Yabar matar mai kyau ita kaɗai."

Wannan karon murmushin da ya bayyana fararen haƙoranta tayi, wato dai su maza a kullum sun san takan mace ko. 😡




Ganin Yaran gaba ɗaya sunyi bacci ne, yasa ta miƙe ta ɗauka Nainarh tana faɗin

"Please My lawful taimaka min da Buddy ya cika nauyi wasu lokutan."



Tayi maganar a lokacin da take ƙoƙarin ɗaukar Nailah ita ma, da sauri Abubakar ya miƙe tsaye kana ya karɓa Nailah daga hannunta Yana faɗin


"Kudai mata akwai ku da kasa da. Yanzu idan kika yar da ita Nainarh wajen ɗaukar Nailah fa, wato saboda qwiuya zaki haɗasu duka, salon ki yarda ɗaya ko?."


Ya yi maganar ne shima Yana saɓa Nailah a kafaɗa sannan kuma ya ɗauki Abdulmaleek ya haɗa su ya nufa bedroom dasu.🤭.



Baki sake ta bisa da kallo tana murmushi, wato ya ma ta faɗa akan ɗaukar Yara biyu a haɗe, shikuma ya ɗauka ko?.🤓

Girgiza Kai tayi cike da nishaɗi kana tabi bayan sa ita ma kafaɗarta saɓe da Nainarh.






Shimfiɗe Yaran su kayi, Abdulmaleek bed nasa daban, haka su Nainarh da Nailah da suke ƙanana aka haɗasu a bed ɗaya da yake gadon Babba ne.



Lulluɓa musu blanket tayi gaba ɗaya kana ta rage gudun Air condition sannan ta juya zata bar bedroom ɗin, harta kai ƙofa taji yo muryar sa yana kiran sunanta.

Ɗan dakata wa tayi amma kuma bata juyo ba.

Murmushi ya yi daga inda yake tsaye kana Yace

"Please matar mai kyau, ki a je komai a gefe kizo ɓangarena akwai maganar da nakeso na muku da Ƴar uwar zaman ki H..."
Ya yi maganar ne domin a tunanin sa zuwa yanzu Rafi'at tasan wacece Abokiyar zaman da ya ƙara ma ta. 🤭🏃






Bata Jira ya kuma cewa komai ba, ta fice daga bedroom ɗin, kai tsaye bedroom nata ta wuce, zuciyarta tunani fall, wato dai farkon sunanta 'H', ne tunda taji ya faɗa hakan, da shigar ta ɗakin kasa zaune tayi bare tsaye, sai faman safa da marwa take yi, ta rasa mai zatayi tunani take akan taje ko kuwa karta je komai zai faru ya daɗe bai faru ba.






Ajiyar zuciya ta sauke abin da zuciyarta ta raya ma ta, shi zata aikata saboda haka ta yanke shawarar zuwa tayi.


Da sauri ta ƙarisa jikin Dressing mirror tana kallon kanta, murmushi tayi kana a fili ta ce

"Dan Allah dube ni Like a SARAUNIYAR KYAU, amma Abubakar ya rasa mai zai min sai kishi..."

Kasa ƙarisawa tayi saboda girman kalmar a wurin ta.





Mayafi ta ɗauka milk color shigen Arabian gown dake a jikinta, kana tayi rolling kanta dashi, sannan ta fito daga bedroom ɗin, kai tsaye part ɗin sa ta nufa zuciyarta na har bawa na Rashin dalili.






A hankali takai hannunta na dama ta tura ƙofar sannan ta shiga ciki bakinta ɗauke da sallama, sai dai kuma ba kowa a palon, dan haka ƙarisa shiga ciki tayi, sannan ta sama wuri ta zauna a saman 3sieter ta ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya tana karkaɗawa tana jiran ƙarisowar Ango da Amaryar sa.


Ta ɗan daɗe zaune a haka, sai kuma can taji alamar shigowar mutane wurin, bugun zuciyarta ne ya ƙaru a lokacin da suke ƙara matsowa wurin da take, da yake ta basu baya shiya sa har suka ƙariso wurin suka zauna fuskar Amaryar kamar yadda ta saba ganin ta lulluɓe da mayafi.



Taɓe baki tayi ƙasa ƙasa yadda ita kaɗai zataji ta ce
"Wannan kodai munafuka ce ita sai haka, idan ba tsaban munafunci ba, ta Aure min miji shi ne hadda wani rufe fuska?."



Taja tsaki ƙasa ƙasa ta gyara zamanta tana binsu da kallo.


Buɗe Taron Abubakar ya yi da addu'a sannan ya fara musu nasiha a kan zaman lafiya da sauran su, yana ta yi dai kuma har zuwa lokacin Amarya bata buɗe fuskar ta ba, a domin uwar gida ta gani.😏

Gyaɗa kai kawai Rafi'at take yi yayin da tarin nasihohin da Abubakar yake antayo musu kamar wani Babban Malami Suke shiga kunenta na dama su fita ana hagu.





Shiru Ya yi Bayan ya gama faɗar Abin da zai iya.

Jin Ya yi shiru da kwararo Ayoyi da hadisai Yasa Rafi'at tayi gyaran murya sannan ta kalla matar dake zaune suna fuskan tar juna da ita fuska rufe da mayafi ta ce.



"Umm gashi ƙanwar tawa naga kamar rowar fuskarta take min domin kuwa har yau kuma dai dai wannan lokaci ban samu na kalla kyakyawar fuskar ƙanwar tawa ba wata ƙila rowar kyakyawar fuskar take min ban sani ba."😐





Ta yi maganar ne cike da zoyala kamar ba ita ba.



Yayin da Abubakar Yaji maganar nata kamar ya ya ke nan dai har Yau Rafi'at bata san wacece ya Auro ba aikuwa akwai matsala.




Ta ɓangaren Amarya Hajarah kuwa murmushi tayi kana cikin nutsuwa irin na ta takai hannayenta duka biyun masu ɗauke da zanen jan lalle gunin burgewa tana Ya ye mayafin da ya Rufe ma ta fuska a hankali a hankali harta Ya ye shi tas duka kyawawan idanunta suka yi taho mu gama da kyawawan idanun Rafi'at .🏃.





Cak maganganun dake ƙoƙarin fitowa daga Bakin Rafi'at suka tsaya cak kamar Yadda Brain ɗin ta Ya tafi hutun Rabin lokaci.🙆





This is emotionality blackmail, da sauri takai hannu tana murza idanunta tana zargin kodai ba dai dai suke gani ba, tabbas idanunta dai dai suke, domin kuwa fuskar da ta gani da Farko ita ta kuma gani yanzu bayan ta murza idanunta, da'ace ta Yadda da tsafi ko sihiri tofa zata ce Hajarah dake zaune Yanzu a gabanta matsayin kishiya a gareta, Magic tayi ta Aura mijinta Abubakar sai dai kash. ☠️



Da wani irin sauri ta miƙe tsaye tana kallon Hajarah hannunta na rawa kamar yadda bakinta yake rawa ta nuna Hajarah tana faɗi cikin rarrabewar harshe.



"Ke,! Ke Hajar me ki-ka-zo anan?..."

Kasa ƙarisa maganar tayi saboda tsananin tashin hankali da ƙunar da zuciyarta take ma ta a lokacin ji take gwara ta harbe Hajarah ko kuma ta caccaka ma ta wuƙa a ciki ta mutu sai dai ta ƙare Rayuwar ta a matsayin PRISONER a Babban PRISON dake Lagos.






Batare da da Tunanin komai ba ta nufi glass center table dake a tsakiyar palon, iya ƙarfinta ta dage ta ɗauki wannan glass center table ta nufi Hajarah dashi zata buga ma ta.

Ai in 360 Hajarah tayi wani super sai gata a bayan Abubakar tana neman a gajin shi.





Kece wa Rafi'at tayi da wata kalar dariyar bosawa ba tunanin komai tabi bayanta tana ƙoƙarin buga ma ta, ai nanfa aka shiga zagaye palo domin kuwa duk yadda taso ta bugawa Hajarah wannan glass ɗin Abubakar ya hana faruwar haka, ita kuma taƙi haƙura gashi ya kasa kwace center table ɗin a hannunta, duk yadda yaso.


Gaba ɗaya sunbi sun hargitsa palon curtains duk sun faffaɗo hatta plasma tv bata gyale ba sai da ta ma ta raga raga, sai faman zagaye ƙaton palon suke yi duk tabi ta haɗa uban zufa, amma taƙi haƙura ta ɗauki ƙaddara tunda aikin gama ya riga da ya gama.


Da Allah ya ba Abubakar sa'a ya damƙe hannun ta da ƙarfin gaske, aikuwa ba shiri ta saki glass ɗin.

Sai kuma ta shaƙo Neck ɗin sa cikin kururuwa tana zage zage.

Duk Yadda yaso ya fin cike ta daga Riƙon da tayi masa kasawa ya yi, hakan ne Yasa ba tare da ya san lokacin ba yasa yatsun sa guda Biyar ya bata wani lafiyayen mari, wanda yasa sai da taga wulgawar wasu taurari a kanta domin kuwa ba kaɗan ba marin ya shige hannunta dake faman Rawa takai ta dafa fuskar ta dai dai sai tin da ya mara tana binsa da wani mugun kallo.



Sai a lokacin yaji Da ya sani marinta da Ya yi, domin kuwa Namiji mai duka ko Marin mace bai cika Namiji ba confirm that's Right.🤜🤛



Da sauri ya ƙarisa kusa da ita yana ƙoƙarin kamo fuskar ta da Shedan Yatsun hannun sa suka kwanta dama abun ka da farar fata take fuskar ta tayi jajir.




A mugun fusace taja baya tana binsa da wani matsiyacin kallo Sannan ta ce



 "Abubakar ke nan kayi min Abin da duk duniya babu Wanda ko da gi-gin wasa ya taɓa ƙoƙarin aikata hakan, ka mareni HHhH, mu bar wannan zancen Marin. Abubakar kayi min dafin da bazai taɓa goguwa a Brain ɗina ba, saboda tsaban cin amana ka rasa wacca zaka Auro min a matsayin kishiya sai Hajarah, toh wallahi tallahi kasani, ka siya wa gidan ka ticket na kallon YAƘIN DUNIYA NA UKU, a cikin gidan ka domin kuwa na Rantse da Allah mai girma sai na ɗauka fansar cin Amanar da kamin wallahi tallahi ka rubuta ka a je."




Tana maganar ne tun daga ƙasan zuciyarta kuma cikin kururuwa sannan kuma tana kuma tabbatar masa da Abin da take faɗa...☠️




Tofah Tun daga wannan Ranar wannan Daren wannan Lokacin salon zaman gidan Abubakar Mai Kyau Ya canza tsakanin sa da matarsa domin kuwa zama ake na ba Ruwan wannan da wancan, domin kuwa tuni Rafi'at ta koma Bakin aikinta suka ci gaba da gudanar da Rayuwa sati ɗayan Hajarah Yana ƙarewa ba tare da musu ba Rafi'at ta amshi girki.



To dai haka Rayuwar gidan ta ci gaba da gudana domin Rafi'at a kullum da Hanyar da take fitowa na takalar Hajarah da bala'i.



Sai dai kuma mugun wayo ne da Hajarah domin duk Hanyar da Rafi'at zata fito dashi na janta da fa ɗa ko wani Abun.


Bata taɓa yadda ta biye ma ta su bar Abin kunya, domin kuwa kyar Hajarah take kallonta ita da ta Karanci psychology ma'ana ilimin Tunani, ai ba abin da Rafi'at zata nuna ma ta domin tsaf take karantar tunanin ta.



Haka suka ci gaba da gungura Rayuwar daga ƙarshe da-dai Rafi'at taga ba sarki sai Allah, tuni ta zubar da makaman Yaƙinta.

Suka ci gaba da lula Rayuwar gidan, sai dai kuma na ciki fa Yana ciki eheee.







Tuni Yaran suka koma wajen Hajarah da zama gaba ɗaya domin kuwa mahaifiyar su Rafi'at bata cika zama ba, saboda yanayin aikinta hakan yasa ba wani kulawa ta uwa da take basu sosai.





Tuni Mai gidan da Jama'ar gidan suka miƙawa Hajarah kambun mulkin gidan gaba ɗaya, domin kuwa wata kalar soyayya mara misaltuwa Abubakar yake ma Hajarah, a saboda kyawawan halayenta a garesa daɗi da ƙari itaɗin ta musamman ce a cikin ma ta, ta kasance mai sa'a a cikin masu sa'a.





Komai Yana tafiya dai dai bisa tsari a gidan Mister Mai Kyau, Rayuwa ake na fahimtar juna da kuma ƙaunar juna.






Auren Abubakar da Hajarah nada watanni huɗu, ciki ya bayyana a jikin Hajarah, aikuwa kuzo kuga murna da Farin ciki wurin Abubakar, jinsa Yake Tamkar bai taɓa haihuwa ba, sai kanta wani kalar ƙauna mara misaltuwa Abubakar yake yiwa Hajarah da cikin jikinta.

Sai dai kuma duk da haka bai dena kulawa da matarsa Rafi'at ba, da kuma Yaran sa uku Abdulmaleek da kuma twin's Nainarh, Nailah.




Cikin Hajarah nada watanni biyar a duniya ciki ya bayyana a jikin Rafi'at Ita ma.

Ashe dama can tana da ciki bata faɗawa Abubakar ba, aikuwa koda ya gano haka saiya haɗasu gaba ɗaya yana kula dasu da cikin jikin su.


This novel Book 2 will be paid book fa,  a next post zan faɗi nawa ne payment ɗin_Karku damu sosai zan muku discount_-_😇


*For More Enquires*
08081129487
_-_💓The Nainarh KD💓_-_






       
___*💋 SARAUNIYAR KYAU 💋*_________ƚαƙυɳ ϝαɾƙσ__________________________________________________________💥👑𝑻𝒉𝒆 𝑮𝒍𝒂𝒎 𝐐𝐮𝐞𝐞𝐧👑💥____________________𝑩𝒚:𝑻𝒉𝒆 𝑵𝒂𝒊𝒏𝒂𝒓𝒉 𝑲𝒅____𝑲𝒉𝒂𝒅𝒆𝒆𝒋𝒂𝒓𝒕𝒉.  𝑺𝒂𝒃𝒊'𝒖.  𝒀𝒂𝒉𝒚𝒂𝒉🤙





Page *75&76*
_-_Still free page's muke_-_


______**

Rayuwa ta ci gaba da tafiya cike da tarin nasarori sannan kuma ta gefe guda Abubakar yana kula da matan sa duka da cikin jikin su, a lokacin da cikin jikin Hajarah yakai watanni bakwai shima na Rafi'at dai dai lokacin yakai watanni bakwai, ganin haka yasa Abubakar ya samo wata Dattijuwa tana kula dasu gaba ɗaya.





A Ranar wata lahadi da Yammaci Hajarah ta fara naƙuda sai dai kuma da yake haihuwar fari ne, batasan kan abin ba, shiru tayi bata faɗawa kowa ba, gashi kuma Abubakar baya ƙasar ya tafi ƙasar jamus a kan harkar kasuwancin sa.




Har gari ya waye ba wanda yasan Hajarah tana naƙuda, sai ita kaɗai wani Abin mamaki kuma a Ranar Rafi'at wuraren ƙarfe sha ɗaya na safe ta santalo jaririyarta da taimakon wannan Dattijuwar mata dake gidan, a lokacin Hajarah tana can ɓangaren ta ita ma tana fama da kanta domin kuwa naƙuda take yi sosai.




Ganin har wuraren sha biyu anyi Haihuwa a gidan har ma Ƴan uwan Rafi'at sun fara zuwa, amma Hajarah bata fito ba yasa Dattijuwar matar,
Hankalin ta ya gaza kwanciya hakan yasa ba shiri ta nufa ɓangaren Hajarah domin ganin ko lafiya, aikuwa tana zuwa ta tarar da Hajarah cikin wani hali na naƙuda wanda ba wacca zatasan Yanayin sai macen da ta taɓa ɗanɗanar haihuwa.




Aikuwa nan wannan Dattijuwar mata ta shiga bawa Hajarah taimakon da ya kamata, a taƙaice dai Hajarah ba ita ta hafe abin da ke cikin ta ba, sai Yammaci wuraren ƙarfe uku na Rana, sannan Ita ma ta santalo jaririyarta mace mai kama da ita Tamkar an tsaga kara, komai irin na ta ne sak, sai lokacin ta fara baccin wahala.




Zuwa dare gaba ɗaya dangi Ƴan uwa da Abokan arziƙi sunji haihuwar da a kayi ma Abubakar duka mata, hatta mutanen France sunji ta hanyar wayar tarho ko washe gari mutanen Jigawa State dana Adamawa dana Mai Duguri Kano gaba ɗaya sun hallara a gidan Abubakar cike da farin ciki, aikuwa nan aka shiga kula da masu jego.







A Ranar da suka cika kwanaki uku da Haihuwa Abubakar ya dura Nigeria aikuwa Ya yi kyakyawar gani a cikin gidan sa.
Gaba ɗaya matan da ya bari haihuwa yau ko gobe su ya tarar ko wacce da kyakyawar Ɗiyar da ta haifa masa, saboda tsananin farin ciki a lokacin rasa mai zayyi ya yi aikuwa ba tare da ɓata lokaci ba ya yi sujadar shukur yana miƙa godiyar sa ga Allah da ya nufe sa da ganin wannan rana.







A lokacin in banda dariya babu abin da su Sakeenah da su Zuwaira suke masa nan ya shiga ɗaukar jariran, idan ya ɗauki na Hajarah sai ya a je ya ɗauki na Rafi'at haka yake ta yi abin gunin burgewa.


Wani ƙarin ikon Allah kuma gaba ɗaya jariran biyu, mugun kama suke da juna tamkar mace ɗaya ce ta haife su, aikuwa nan mutane suka dingi magana a kan wannan abin mamaki.



Ranar suna kuwa ɗiyar Hajarah taci suna Zaynerb a Yayin da Ɗiyar Rafi'at taci suna Haleesat, wato dai har lokacin Abubakar bai manta da Haleesat Rashid Rayyan ba masoyin gaskiya ke nan, Allah sarki Rayuwa a lokacin har da yawa sun manta da ita.😞




Ba ƙaramin daɗin wannan sunan da Abubakar ya sakawa ɗiyarsa dangin Rafi'at suka ji ba, a lokacin wasu daga ciki har sai da suka yi kuka na tunawa da maragayya Haleesat Rashid Rayyan mutumiyar kirki.

Ita ma dai Hajarah sai lokacin take sanin wacece Haleesat Rashid Rayyan a wurin Abubakar.




Rayuwa ta ci gaba da antayewa yayin da Abubakar yake kula da matan sa duka domin kuwa ƙin bari ya yi su Hajiya Harirah su ɗauki Hajarah wankan gida, a lokacin sai dai Hajiya Harirah ce tazo ta zauna dasu tana kula da Hajarah, yayin da ita kuma Rafi'at wannan Dattijuwar mata da ta amsa haihuwar su take kula da ita.







---**

Wani Abun mamaki da ya taɓa faruwa Wanda gaba ɗaya Ahalin Alhaji Sameer Lamiɗo ba zasu taɓa mantawa dashi ba shi ne.



A wata Ranar Alhamis da safe lokacin Rafi'at da Hajarah suka cika watanni uku da Haihuwa, Ranar Abubakar bai fita Company ba.
Wuraren goma na safe suna zaune a palon gidan shida Rafi'at da Hajiya Harirah da kuma sauran Yaran gidan suna taɓa fira sama sama.





Sai ga Hajarah ta shigo tamkar an jefo ta, sai faman goge gumi take ga fuskar ta ɗauke da matsanancin Farin ciki saboda tsananin saurin da take yi har Ƴarta Zaynerb dake hannunta ta kusa faɗi ƙasa, ta taro ta.



_-_Mgnr Payment da nace. Tabbas Book 2 is paid fa_-_


_Duk Wanda Ya shirya ayi tafiyar da shi, kuma ya shirya Payment_






_-_Just Pay With This Details_



_-_-_-_-_-_
*The Phone Number*
*08081129487*
*The Acct Number*
*8081129487*
*The Bank Name*
*Palmpay Bank*
*The Acct Name*
*Khadeejarth Sabi'u Yahyah*

 



 

___*💋 SARAUNIYAR KYAU 💋*_________ƚαƙυɳ ϝαɾƙσ__________________________________________________________💥👑𝑻𝒉𝒆 𝑮𝒍𝒂𝒎 𝐐𝐮𝐞𝐞𝐧👑💥____________________𝑩𝒚:𝑻𝒉𝒆 𝑵𝒂𝒊𝒏𝒂𝒓𝒉 𝑲𝒅____𝑲𝒉𝒂𝒅𝒆𝒆𝒋𝒂𝒓𝒕𝒉.  𝑺𝒂𝒃𝒊'𝒖.  𝒀𝒂𝒉𝒚𝒂𝒉🤙


☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆
💦𝑳𝒂𝒇𝒂𝒛𝒊 𝑾𝒓𝒊𝒕𝒕𝒆𝒓'𝒔 𝑨𝒔𝒔𝒐𝒄𝒊𝒂𝒕𝒊𝒐𝒏💦🤙

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆







Page *77&78*



Qarisowa tayi sannan ta tsaya a tsakiyar palon tana faman sauke ajiyar zuciya game da haki, ganin yadda ta shigo a hargitse kamar wani ya biyo ta yasasu gaba ɗaya tashi suna tambayar abin da ke faruwa.




A hankali ta buɗe kyakyawan idanunta waɗanda saboda tsananin farin cikin da take ciki yasa suka kawo ruwa, ta kallesu dasu sannan ta fara magana.



"Ina cikin farin ciki wanda tunda nake a Rayuwata ban taɓa shiga ciki ba. Yau kuma a dai dai wannan lokaci na tuna WACECE NI, Yau bayan shafe tsawon shekaru ɗaya da wata biyar da kwanaki biyar da mintuna goma sha biyar da sakanni, a Yau ni 'Hajarah Haleed Mai Waje: na tuna Asalina na tuna Ahalina na tuna sunan State nawa, na tuna komai da komai duka...'



Tayi maganar ne a Yayin da wasu siraran Hawayen Farin ciki suka wanke ma ta fuska.



Gaba ɗayansu jama'ar dake a palon kabbara suka saka cike da tsantsan farin ciki, shikuwa Abubakar gaza jurewa ya yi har sai da ya yi sujadar shukur yana kuma miƙa godiyar sa ga Allah wato dai maganar bahaushe ce da yake cewa INDA RAI DA RABO ikon Allah, gashi dai daga ƙarshen ƙarshe, Hajarah zata kuma haɗuwa da Ahalinta a karo na biyu, Allah ke nan buwayi gagara misali.



Da gudu Rafi'at ta ƙarisa wurin Hajarah ta Rungumo ta gaba ɗayanta a jiki tana faɗin

"Na tayaki murna sosai sosai Abokiyar."


Da yake haka suke kiran juna, murmushi Hajarah tayi tana kuma damƙe hannun Rafi'at dake cikin nata Sannan ta ce

"Nagode sosai Abokiyar, Allah ya bar ƙauna."



Hajiya Harirah kuwa tun ɗazu fuskar ta ɗauke take da matsanancin Farin ciki, saboda haka sai ta kasa magana, kawai tana binsu da kallo, ƙari sowa wurin ta Hajarah tayi Bayanta miƙawa Abubakar Zaynerb kana ta Rungumo Hajiya Harirah faɗi take

"Hajiyar mu kita yani murna da farin ciki Yau ina cikin nishaɗi obaaaaa..."





Sai da gaba ɗaya suka sama nutsuwa suka zazzauna sannan kuma Abubakar ya ɗauki waya yana kiran gaba ɗaya dangi yana faɗa musu Abin farin cikin da suka wayi gari da shi.

Aikuwa nan aka dingi tayasu murna barinma dai su Zuwaira, Jawaheer, Jummai Sakeenah waɗanda suka ɗauki Hajarah matsayin Ƴar uwa ba matar ɗan uwansu ba, ai nan mutanen Jigawa State suka ce gasunan ƙarisowa Abujan ayi farin ciki tare dasu.






A Ranar gaba ɗaya Ahalin sun wuni ne cike da farin ciki mara misaltuwa.

Misalin ƙarfe bakwai na Yammaci mutanen Jigawa State tun daga kan Alhaji Sameer Lamiɗo Dr_Raheemah Hajiya Zuwairiya, Zuwaira, Jawaheer, Jummai hatta Sakeenah dake Aure a Adamawa State sai da ta hallara a garin Abuja gaba ɗayansu sun ƙariso.





Wuraren ƙarfe Takwas da Rabi na dare gaba ɗaya sun hallara a Babban palon gidan, suna fira cike da nishaɗi bayan komai ya lafa ne Alhaji Sameer Lamiɗo ya kalla Hajarah cike da kulawa Yake faɗin


"Ɗiyata Hajarah gaba ɗaya nida Ahalina muna tayaki murnar tuno Rayuwar ki da Ahalin ki da kikayi.."




Murmushi tayi cike da jindaɗi ta amsa da

"Ina godiya sosai Abbhee..."



"Tohm ni dai har Yanzu banji sunan State ɗin namu ba."


Cewar Jawaheer cike da zoyala, murmushi Hajarah take saboda farin cikin da take ciki ma haƙoranta sunƙi rufuwa gyara zama tayi kana ta fara magana kamar haka.



"Da Farko dai kamar Yadda kuka sani sunana Hajarah sunan mahaifina kuma Alhaji Haleed Mai Waje, ni ɗin cikakkiyar Ƴar Garin KADUNA STATE ce dake a nan AREWA cikin Nigeria Yankin Africa."🌍



"Alhamdullilah.
               
               Masha Allah..

                          Hakan akeso..."




Haka kawai gaba ɗaya mutanen da ke zazzaune a palon suke faɗa nan kuma aka ƙara tayata murna daga nan kuma Sabuwar fira ta ɓalle a tsakani daga ƙarshe sun yanke shawarar cewa gobe tun daga kan Alhaji Sameer Lamiɗo da matansa da kuma Zuwaira da Abubakar sai kuma ita Hajarah ɗin zasu wuce Kaduna Garin Gwamna domin haɗuwa da Ahalin Hajarah, daga haka kuma taron ya watse dama lokacin dare Ya yi sai kowa ya sama makwanci, dama kuma Hajarah ita keda girki sai kawai tabi mijinta tura karsa.🤭









*WASH£-GARI*




Wuraren ƙarfe goma sha ɗaya na safe gaba ɗayansu Ahalin tsaye suke a filin ajiye motoci na gidan. Yayin da waɗanda zasuyi tafiyar suna shirye tsaf, Yayin da kuma waɗanda ba da su za'a tafi ba, suka tsaya daga gefe suna musu ban kwana cike da Fatan Nasara.






Bayan sun gama ban kwana ɗin ne gaba ɗaya suka shiga motoci da yake motocin ba kalar na wannan zamanin bane, shiyasa sai da suka yi mota uku sannan gaba ɗaya suka shiga ciki.



*SAIDAI KUMA ME?.*

Wani Abun mamaki shi ne duk Yadda a kaso motar da Hajarah take ciki ta tashi Abu ya cutura.
Abu dai kamar wasa tun ana gwadawa cikin daɗin rai har aka koma gwada mota mota amma wani ikon Allah shi ne, duk motar da Hajarah ta shiga ciki ba zata tashi ba, amma kuma tana fita wannan mota zata tashi.




Abu fa kamar wasa anata abu ɗaya har wuraren ƙarfe ɗaya na rana ana kan abu ɗaya, sai daga ƙarshen ƙarshe ne, bayan Addu'o'i da suka dingiyi aka samu mota ta tashi.


Ajiyar zuciya ko wanen su yake saukewa gaba ɗaya sun haɗa uban zufa barin ma dai Hajarah da takeji kamar me?.


Sallama suka kuma yi da kowa sannan suka ɗauki hanya, Bayan gate man ya wangale musu gate.💃






_____*

Sun bar Garin Abuja wuraren ƙarfe ɗaya da rabi na Rana sannan suka fara wuce garuruwa sun wuce Minna ba daɗewa ke nan suna shirin shiga Garin Kaduna.



Jikin Hajarah ya fara wani irin rawa ta ko'ina haɗa zufa take ga wasu ƙuraje da suka fara fitowa daga ko'ina na jikinta, da yake su uku ne a Motar ita da Dr_raheemah da kuma Hajiya Harirah, da Farko basu lura da abin da ke faruwa da ita ba, sai da suka ji ta fara nishin wahala, aikuwa nan take suka ba driver umarnin tsayawa.

Gefan kwalta ya samu sannan ya tsayar da Motar da yake suna a gaba ne, shiyasa suma sauran motocin da ke bayansu suka sama wuri suka tsai tsaya,  sannan gaba ɗaya suka fiffito suna kallon Hajarah dake faman haɗa uban zufa ga wasu ƙuraje da suke feso mata tashi ɗaya, Abin gunin ban tausayi.😰





Da sauri Abubakar ya ƙarisa wurinta kana ya kamo hannunta cike da tausayawa ya kira sunan ta.

Kasa amsawa tayi saivma kallon sa da tayi cikin jin azaba ta ce

"Dan Allah mu koma gida, idan ba haka ba kuma mutuwa zanyi, zafi nakeji ta ko'ina a jikina jina nake kamar bani ba..."





Daga jin irin abin da take faɗa da kuma ganin yadda gaba ɗaya jikinta yake rawa ga wasu ƙuraje, Yasa Alhaji Sameer Lamiɗo Ya yi gyaran murya, gaba ɗaya suka juyo suna kallon sa, suna jira suji abin da zai ce.


"Ina ga mu juya gida kawai domin kuwa na lura wannan lamarin dasa hannun Jinnu a ciki, mu Fara komawa gida a ma ta magani sannan koma menene daga baya a yi."




Gaba ɗaya sun gamsu da maganar sa kuma sun fahimci abin da yake so ya fahimtar dasu, saboda haka ba tare da ɓata lokaci ba, gaba ɗaya suka shishshiga motocin su suka koma.



Su Rafi'at suna zazzaune a palon gidan suna taɓa fira tsakanin ta dasu Zuwaira suka ji dawowar motocin.

Mamaki ne ya kamasu ganin su Hajiya Zuwairiya sun shigo.



"To kodai har sun dawo ne?."

Jawaheer ta tambaya tana miƙewa tsaye kamar yadda suma sauran suka mimmiƙe suna binsu Hajarah da kallon neman ƙarin bayani.






Gaba ɗayansu zama suka yi a saman kujerun palon jiki a mugun sanyaye, ganin haka yasa suma su Jummai suka zazzauna sannan ne kuma suka lura da Hajarah da ƙurajen da suka fara fiffito mata a jiki.



"Ya Allah.! Menene kuma wannan?."


Sakeenah ta tambaya cikin waro ido tana ƙarisawa wurin da Hajarah take





Ajiyar zuciya Hajarah ta sauke idanunta sunyi jajur na ɓacin rai sannan a fili take faɗin


"Dama nasan haka zata faru, tabbas nasan ba zata taɓa bari na koma gida cikin sauƙi ba, ni na sa ni, kuma nasan komai, nasan ko ita wacece."






Gaba ɗaya mutanen dake palon suka zubo ma ta ido cike mamakin jin abin da take faɗa.

Abubakar da ya gaza jurewa sai da ya magantu.
"Wacece ita haka da kike faɗin kin san ba zata Bari ki koma gida lafiya ba?."


Ya tambayar idanun sa akanta, kamar yadda suma sauran jama'an palon suke ma ta kallon neman ƙarin bayani.



Numfashi kawai take fitarwa da sauri da sauri kana bayan wasu sakanni ta ɗago da kanta tana kallon jama'ar palon, kamar suma yadda ɗin ita suke kallo Sannan ta fara magana kamar haka.


"Alhaji Haleed Mai Waje shi ne cikakken sunan mahaifin mu.
Asalin sa Ɗan Garin Kaduna State ne.
Gaba da baya, su biyu a wurin iyayen su, shi da ƙanin sa Kamaludeen, sunan 'Mai Waje' kuma mutane ne suka saka masa.
A dalilin shiɗin ya kasance yana gudanar da harkokin kasuwancin sa ne a tsakanin ƙasashen waje.
Ya kasance cikakken Ɗan kasuwa kuma Mai Naira Wanda duniya take damawa dashi ta kowani ɓangare.
Matar sa ɗaya wacca ta kasance Baturiyar ƙasar Bulgaria ce, haifaffiyar Babban Birnin ƙasar wato 'Sofia'.
Tabar iyayen ta da Biyuninta a ƙasar su ta biyo sa.
Nigeria ne a dalilin son sa da take yi, kuma a kayi sa'a shima ɗin yana matuƙar ƙaunar ta.
Koda suka zo Nigeria a tare, batare da wani ɓata lokaci ba mahaifin sa ya ɗaura musu Aure, bayan ta karɓa Addinin Musulunci taci suna Haleematul Sa'adiya.
Yaran su huɗu a tare Hasheem shi ne na Farko, sai kuma wasu mata biyu da suka kasance twin's ne Mubashirah da kuma Munira, sai kuma Ni Auta Hajarah.

Mun taso ne cikin Tarbiyar iyaye, saboda duk da cewa mahaifiyar mu ta kasance Baturiyar da ta Musulunta, hakan bai hana ta jajir cewa ba ita da mahaifin mu wurin bamu Tarbiya mai kyau da nagarta. Mun kasance a gidan mu.
Muna zaune ne tare da ƙanin mahaifin mu da matar sa, suma suna da Yara uku a tare.
Matar ƙanin mahaifin mu mai suna Asabe ta kasance ta tsani mahaifiyar mu fi ye da kima, wai saboda ta kasance TUBABBIYA ce, kuma duk da haka surukan su sunfi ƙaunar mahaifiyar mu a kanta, wannan ne Babban dalilin da Yasa ta tsani mahaifiyar mu, a kullum cikin muzguna ma ta take yi, duk da cewa a cikin gidan mu suke zaune, kuma da dukiyar mahaifin mu suke ci suke sha.
Amma hakan bai hana ta neman kai mahaifiyar mu ƙasa ba. Da duka ƙarfinta.
Sai dai kuma duk Abin da take yi cikin salo da dabara take yi domin kuwa kaf gidanmu dama Ahali baki ɗaya babu Wanda Yasan Burinta a kan mahaifiyar mu domin ta kasance mace mai ƙissa da kisisina, a cikin mutane nunawa take tafi kowa ƙaunar mahaifiyar mu, amma kuma cikin zuciyarta ba haka bane.

Kaf gidan ba Wanda Yasan Burinta akan mahaifiyar mu sai ni kaɗai, domin kuwa na kasance tun ina Yarinya ina da matuƙar kaifin basira sosai, Wanda wannan dalilin ne ma Yasa nake karantar psychology ma'ana ilimin Tunani.

Ita da ƙanin mahaifin mu suna da wani Yaro mai suna 'Sama'ila' Wanda ya kasance tun daga tasowar sa mutum ne shi mara imani ko kaɗan domin kuwa ya kashe mutum har lahira ba damuwar sa bane, domin kuwa koda ya kammala secondary school kai tsaye ya wuce ƙasar China ya Karanci Astrology Wato ilimin Bokanci.💀💀💀

Wanda a dalilin baƙin cikin hakan ƙanin mahaifin mu Kawu Kamaludeen zuciyar sa ta buga ya mutu.
Sai dai a maimakon mutuwar sa tasa Ɗan sa Sama'ila ya tuba ya koma ga Allah. A'a saima sabon salon abu da ya fito dashi. Domin tattarawa ya yi ya koma can kudu da zama.
Yayin da ƙannin sa biyu da mace dana miji da kuma mahaifiyar su suka ci gaba da zama a cikin gidan mu.
A lokacin ne kuma Asabe ta fito da nata sabon salon ita ma domin kuwa ta Yanke shawarar Auren mahaifin mu ta ko wani hali.
Nima a lokacin nazo gida hutu ne, sai na je ɓangaren nasu. Wajen ɗiyarta wacca ta kasance sa'ata ce shi ne fa naji abin da Yafi ƙarfina, a lokacin hankalina ya tashi sosai domin kuwa harji nayi tana faɗin, "Lallai zata iya kashe mahaifiyar mu har lahira indai ta nema kawo mata matsala."
"Lokacin ba ƙaramin tashi hankalina ya yi ba, sai dai kuma wani abun mamaki na kasa faɗa wa kowa abin da naji tana faɗa har hutuna ya ƙare na dawo Abuja domin kammala karatuna.



To a lokacin dana kammala karatuna ne a wajen dawowa ta daga wajen taro, na gamu da wannan Hatsarin da harna manta gaba ɗaya memory na akan Rayuwata da Ahalina..."😭





Hajarah ta na kawowa nan da maganar ta tayi shiru, Yayin da wasu zafafan hawaye suka wanke kyayawar fuskarta.


Shiru gaba ɗaya palon ya ɗauka tsawon mintuna goma, babu Wanda ya iya faɗar wani abu, saboda tsananin mamaki da al'ajabi, sai can ne Alhaji Sameer Lamiɗo ya nisa sannan yace



"Tabbas sosai mun tausaya miki fi ye da baya, da jin wannan labari naki mai cike da ƙalubale da chakwakiya game da rikitarwa, wannan yana nufin ke nan zargi na ya tabbata a kan cewa, da saka hannun Jinnu a wannan lamarin, to daga yau Insha Allah, zamu dage gaba ɗaya a haɗa ƙarfi da ƙarfe wurin ganin an nemo Ahalin ki, sun zo su ganki, tunda zuwan ki can bazai yiwu ba, kuma zamu ƙara dage wa wajen ganin an rabaki da waɗannan mutanen da suke a tare da ke Bi'iznillah.




***

Aikuwa Tun daga wancan ranar gaba ɗaya Ahalin Alhaji Sameer Lamiɗo suka ƙara zage damtse wajen kula da Hajarah fi ye da baya, kowa ƙaunar ta yake yi kamar me, hatta Rafi'at ba'a barta a baya ba, domin kuwa ba kaɗan ba labarin Hajarah ya taɓe ta. Ashe dai ko'ina da shegu😕
Ita babu abin da yafi ɗaga ma ta hankali sai ji da tayi wai musamman Sama'ila da yake Ɗan musulmi, ya ɗauki ƙafa wai yaje har can uwa duniya Ƙasar China dangin ifiritai, Karantar ilimin Bokanci ashe haka duniyar ta zama.😔



Zieey Jinjina mara adadi a gareki, ina godiya matuƙa da ƙaunar da kike yiwa wannan book, Allah ya barmu tare🥰                








Page*79&80*

_____*

Rayuwa ta ci gaba da tafiya Yayin da ta gefe guda Abubakar ya kammala binkciken sa akan Ahalin Hajarah sai dai kuma wani Abin haushin shi ne.
Wai gaba ɗaya dangin sun koma ƙasar waje da zama kuma bai san wata ƙasa suka koma ba.


To koda ya sama Hajarah da zancen ba ƙaramin tashi hankalinta ya yi ba faɗa kawai take
"Shikenan ita kuma da sake haɗuwa da Ahalin ta sai dai a darrusalam inda rabo, a lokacin shima hankalin Abubakar ba ƙaramin tashi ya yi ba, jin abin da take faɗa haka ya dingi kwantar ma ta da hankali, harya samu ta dawo normal."



Rayuwa ta ci gaba da lulawa ta ko wani ɓangare abin dai sai godiyar Allah, domin kuwa ta ɓangaren Ahalin Alhaji Sameer Lamiɗo sosai suka dage suna bawa Hajarah taimakon da ya kamata.


Zaynerb Ɗiyar Hajarah nada shekaru biyu a duniya.
Wata Ranar Alhamis da Yamma wuraren ƙarfe Bakwai na dare, Hajarah ta santalo jaririyarta mace ƙatuwa mai kama da ubanta sak wannan karon, babu abin da ta rage daga jikin Abubakar komai nashi ta ɗauko abu ɗaya ne kawai na Hajarah wanda ta ɗauko wato Manya Manyan dara daran kyawawan idanu.





Daya ke wannan karon Hajiya Zuwairiya ce ta karɓa haihuwar shi yasa sai da ta kammala ba Hajarah da Jaririyarta duk Abin da ya kamata, tayiwa jaririya wanka ta shirya ta, sannan ta fito palo wurin su Abubakar da Rafi'at wacca ita ma cikin jikinta haihuwa yau ko gobe, sai Sakeenah da Jawaheer da kuma Yusra matar Yusuf da suka zo.




Fuska ɗauke da matsanancin farin ciki ga kuma jaririya ɗauke a hannunta ta ƙariso sannan ta miƙawa Abubakar Jaririyar. Bayan ya karɓeta Hajiya Zuwairiya ta ce

"Ga jaririya an sama Ɗiya mace Masha Allah, gata kyakyawar gaske duk da dai ba fara bace."



Ai da jin haka yasa gaba ɗaya mutanen palon suka ƙariso wurin suna kallon jaririyar da aka kira da baƙa bayan kuma gaba ɗaya Ahalin su ta babu baƙaƙe.😜






A je jaririyar dake sanye cikin kayan sanyi na jaririrai tana Baccin ta gunin burgewa, Abubakar ya yi a saman 3sieter aikuwa nan suka shiga kallon ta Abin gunin burgewa.






Sakeenah ta ce "Ni dai tunda nake a Rayuwata ban taɓa ganin Jaririya wacca kyanta da komai nata ya burgeni ba kamar wannan kyakyawar furanga haka, da take a gaba na, sai dai kuma wani abu ɗaya, naga kalar fatar ta shi ba fari ba, haka zalika ba baƙi ba, sai wani shaining da yake yi kamar tauraruwa cikin taurari."





Jawaheer ta amshe zancen da cewa "Ke dai bari ai jina nake kamar wannan Jaririya ta zama tawa, gata Tabarakallah Masha Allah ga kuma Kalar fatarta Wanda a turance ake kira da one in Dollars, domin kuwa kafin ki sama fata Kalar wannan to da aiki gaskiya fa."


Yusra wacca take mata wurin Yusuf ta ce "Ai Auntie Jawaheer baki kai ni ƙaunar wannan Ɗiyar ba domin kuwa jinta nake can, can a cikin ƙasan zuciyata, ga kuma fatar ta wanda iya shi mutum ya gani sai ya mance hanyar garin sa, gidan sa dama sunan sa gaba ɗaya."🔥



Dariya suka yi gaba ɗayan su, Rafi'at wacca ta ƙurawa jaririyar ido tun ɗazu ta ce
"Ummm hmm kun san menene kuwa?."



Gaba ɗayansu suka haɗa baki wajen faɗin
"A'a.'

Dariya tayi sannan tana faɗin

"Wannan Jaririyar ko, ita ake yiwa laƙani da kinfi nurul'in, Dan Allah please ku taimaka ku tayani kallon wannan haɗaɗɗiyar fatar nata wanda in banda shaining babu abin da take yi, ga manya manyan dara daran kyawawan fararen idanunta masu ɗauke da launin £ye ball's wasu masu shaining su ba blue color ba, kuma su ba green color ba, sannan kuma baza'a kirasu purple color ba, abin dai sai Wanda ya gani wallahi."



Gaba ɗaya mutanen dake palon in banda dariya babu abin da suke yi.


Hajiya Zuwairiya ta ce "Ai ina faɗa muku wannan jikar tawa, sai an dinga haɗa mata da Addu'o'i domin kuwa wannan kyan nata ko, Humm hmmm."


Gaba ɗaya mutanen palon babu wanda bai magantu ba, sannan kuma bai susuce da wannan kyau kyawu irin na na wannan Jaririya ba, tana da kyau sosai, she is so cute and so sweet  so sexy and adorable, so and and so ka.!! abin ko humm Alƙalamin Nainarh Kd ya yi kaɗan wajen rubuta kyau da kyawu irin na wannan Jaririya.....ʝυʂƚ ιɱαɠιɳҽ...🥰





Abubakar da tun ɗazu ya yi shiru bai ce komai ba, amma idanun sa suna akan wannan kyakyawar furanya, ya sauke wata kyakyawar ajiyar zuciya na farin ciki sannan ya fara magana kamar haka..

"Kun san menene kuwa, jama'a?."



Dariya suka yi jin abin da yace kana suka haɗa baki wajen cewa "A'a a'a a'a...."


Yace

"Wannan kyakyawar furanya Insha  Allahu wata Rana za'a wayi gari ta zama SARAUNIYAR KYAU ta duniya Insha Allahu Burina ke nan a kanta.📷💃😎







<<<{Tofah masu karatu, kundai ji Burin Mister Mai Kyau, a kan wannan Ɗiya tasa da masoyiyar matarsa son sa Hajarah ta haifa masa, shin Burin zai cika, ko kuwa dai. Akwai Ƙalubale, kudai kawai ku biyo wannan Ƙayataccen labari mai suna *💋SARAUNIYAR KYAU 💋* domin jin irin abin da yake ciki, sannan da darasin da yake tafe dashi 💃💃}>>>






Gaba ɗaya mutanen dake palon suka ɗauki sowa na farin ciki Jawaheer faɗi take

"Ina bayanka Yaya ni ma dai Burina ke nan, akan wannan Ɗiyar tamu Ahaa muje zuwa *SARAUNIYAR KYAU*




Murmushin farin ciki Hajiya Zuwairiya tayi tana cewa
"To ai sai ku bar wannan Jaririya ta Huta, ga mahaifiyar ta can baku tambaya Lafiyar ta ba, kun tsaya a kan jaririyar ko?."




Dariya suka yi sannan Sakeenah ta miƙe tsaye da sauri tana cewa

"Ni Wallahi in banda Yanzu da kikayi maganar, ni harna manta da Hajarah mai jego, kyawun Jaririyar da ta haifa mana shiya saka hakan."



Tashi suka yi gaba ɗaya suka nufa bedroom ɗin da Hajarah take ciki

Kwance suka same ta tana kwasar baccin gajiya.
Zazzauna wa suka yi suma suka ci gaba da fira sama sama suna ko ɗa kyau irin na wannan Jaririya.


Zuwa can wuraren goma na dare Hajarah ta farka aikuwa tayi kyakyawan gani gaba ɗaya mutanen gidan zazzaune suna fira ga Ɗiyarta da mijinta a gefanta murmushi kawai take yi na farin ciki.



Ganin ta farka yasa Abubakar ya yi murmushi da yake yana kusa da ita ne, a gefan gadon, cikin ƙasa da murya, yadda ita kaɗai zataji abin da zai faɗa Yace

"Nagode miki sosai da kika Haifa min wannan kyakyawar furanya, kyakkyawar Tauraruwa wacca hasken ta yake haske wuri, nagode miki sosai kin san kuwa wani suna zan saka ma ta?."



Fuskar ta ɗauke da matsanancin farin ciki na yabon da godiyar da mijinta yake ma ta ta girgiza masa kai alamar "A'a,"
Murmushi ya yi sannan ya matsa da Bakin sa dai dai sai tin kunenta ya raɗa ma ta a kunne.


Dariya tayi ba shiri wanda sautin dariyar da tayi Yasa gaba ɗaya mutanen Ɗakin juyowa suna kallon ta domin kuwa babu wanda ya lura da tashin ta.







"Ah ah kunga masoyan zahiri, wato ana jegon mah ana taɓa love ne ko?, Aikuwa Abin naku ya ƙayatar dani sosai, na ɗauki course daga Yau."



Cewar Jawaheer cikin dariya, "Wato ma saka mana ido kikayi ko?."



Hajarah ta tambaya tana jefa ma ta hararar wasa, Jawaheer ta ce "A'a nadai gani ne kawa Aha." 🤣






Habba ai nan kuma wata sabuwar fira ta ɓalle a tsakanin su, gaba ɗaya cike da nishaɗi yi suke yi kamar babu gobe, har wuraren ƙarfe goma sha biyu na dare.


Sannan ne kuma suka fara shirin komawa bedrooms ɗin su domin kwanciya bacci, gaba ɗaya suka fiffita bayan sunyi wa mai jego da jaririyarta sallama.
Suka bar Abubakar da Hajiya Zuwairiya a cikin bedroom ɗin.




Miƙewa Abubakar ya yi kamar mai neman wani abu. Da sauri ya fakaici idon Hajiya Zuwairiya ya haye saman bed ɗin.
Cikin sauri Hajarah ta kalle sa ganin abin da ya yi kana cikin ƙasa da murya ta ce

"Menene haka kuma?, in ace kaima ɓangaren ka zaka wuce, sai kuma gobe ko?."


Dariya ya yi sannan shima cikin ƙasa da murya Yace

"Na fasa anan zan kwana, tare da mata ta da Ɗiyata domin kuwa wani kalar kewar su nakeji, tun kafin na tafi na barsu."


Shiru yayi kamar mai tunani, sai can ya kalle ta kamar yadda ita ma ta ƙura masa ido tana kallo, cikin sanyin murya yake faɗin

"Kin san menene kuwa?."


Bai jira ta amsa ba, ya ci gaba da cewa,
"Jina nake kamar bani ba, ina jina gaba ɗaya jikina a sake, sannan kuma kamar wani abu mara daɗi zai faru, gaba ɗaya a sanyaye nake wallahi."


Ƙura masa ido Hajarah tayi tana kallo Sannan ta sauke ajiyar zuciya tana faɗin

"Duk wannan wasi-wasin aikin sheɗan ne kawai, ka karanto Addu'o'i komai zayyi Normalcy Insha Allah." ta ci gaba da cewa

"Ka tsaya da kyau ka saurari bugun zuciyar ka ka nutsu zaka fahimci aikin sheɗan ne kawai?."


Murmushi ya yi kana Yace


"Ina son ki sosai sosai fi ye da yadda kike sona fa."


Dariya ita kuma tayi sannan ta basa amsa da

"Ni kuma ina ƙaunar mijina abin alfaharina a kullum da ko yaushe ina ƙaunarka obaa, fi ye da ƙaunar da Lailah da Majnun suke ma juna Tabbas."  Tayi maganar tana Rumgumo sa tightly.          

   

                      



                   
08081129487
Via WhatsApp
For more enquires
The Nainarh Kd




___*💋 SARAUNIYAR KYAU 💋*_________ƚαƙυɳ ϝαɾƙσ__________________________________________________________💥👑𝑻𝒉𝒆 𝑮𝒍𝒂𝒎 𝐐𝐮𝐞𝐞𝐧👑💥____________________𝑩𝒚:𝑻𝒉𝒆 𝑵𝒂𝒊𝒏𝒂𝒓𝒉 𝑲𝒅____𝑲𝒉𝒂𝒅𝒆𝒆𝒋𝒂𝒓𝒕𝒉.  𝑺𝒂𝒃𝒊'𝒖.  𝒀𝒂𝒉𝒚𝒂𝒉🤙






Idan kin shirya Payment, just pay with this details.

_-_-_-_-_-_
*The Phone Number*
*08081129487*
*The Acct Number*
*8081129487*
*The Bank Name*
*Palmpay Bank*
*The Acct Name*
*Khadeejarth Sabi'u Yahyah*



Page *81&82*





Ganin dai abin nasu bana ƙarewa bane. Yasa Hajiya Zuwairiya da tun hawar Abubakar saman bed ɗin, take ankare dashi, miƙewa tsaye tana faɗin
"Toh idan an gama rashin kunyar a gaba na, sai a tashi a tafi inda aka fito, domin zan kulle ɗakin."



Da sauri suka juyo suna kallon ta su biyun, aikuwa ta galla musu harara duka.

Ƙasa da kai Hajarah tayi cike da kunya, shikuwa Abubakar ko'a jikin sa ya sauko daga saman gadon idanun sa akan Hajarah harya fi ce daga bedroom ɗin, yana yiwa Hajiya Zuwairiya dariyar ƙeta.





Ajiyar zuciya Hajiya Zuwairiya ta sauke sannan ta kalla Hajarah tana qalla ma ta harara sai dai bata ce komai ba, taje ta kulle ɗakin, ta dawo ta koma can gefe saman wata doguwar stool mai faɗi ta kwanta, domin kuwa wani kalar bacci mara misaltuwa take ji kamar Ƴar maye, Aikuwa ko mintuna biyar batayi da kwanciya ba, bacci ya yi gaba da ita.






Ajiyar zuciyar ita ma dai Hajarah ta sauke sannan ta sauko daga saman mattress ɗin, ta shiga bathroom, ta ɗauki tsawon mintuna goma a ciki.

Jiyo kukan Jaririyarta da tayi ne, yada da sauri ta kammala abin da take yi sannan ta fito, ta ƙarisa saman gadon jariran ta ɗauka Ɗiyar ta ta tana ma ta wasa, daya ke Jaririyar taƙi karɓan Breast ɗin ta, tun ɗazu kuma ba'asan dalili ba, shi yasa ma batayi tunanin bata ba.




Sai da ta tabbatar da jaririyar ta ta tayi bacci, sannan ta kwantar da ita, kana ita ma ta koma ta kwanta saman bed, bayan tayi duka abin da take yi a al'adarta kafin ta kwanta, bata daɗe da kwanciyar ba, ita ma wani bacci mai ƙarfi Ya yi gaba da ita.






 
*WASH£-GARI*


Wuraren ƙarfe Bakwai na safiya, Sakeenah ta fito daga bedroom ɗin da ta sauka, jikin ta sanye cikin dogon hijjab blue color har ƙasa.
Hamma kawai take yi domin kuwa baccin bai isheta ba ta tashi, amma duk da haka sai da ta makara.



Tasha mamaki sosai ganin Palon ba kowa, bata kawo komai a Ranta ba, ta wuce kai tsaye tabi ta wani korido Wanda zai sadata ɓangaren Hajarah.






Knocking ƙofar bedroom ɗin tayi, amma shiru ba'a zo an buɗe ba.

Ƙara yi tayi nan ma shiru, ganin haka yasa ta ɗan tura ƙofar da hannunta, aikuwa sai ƙofar ta buɗe.



Sallama ɗauke a Bakinta ta shiga bedroom ɗin, amma sai taji ba'a amsa ma ta ba.
Ƙarisa shiga tayi aikuwa tayi kyakyawan gani can saman doguwar stool mai faɗi ta hango Hajiya Zuwairiya tana ta faman sauke snored bacci ya yi daɗi.


Dariya Sakeenah tayi tana faɗin "Ashe dai bani kaɗai na makara ba, tunda dai ga mai jego da Hajiya suna faman sauke numfashi bacci ya yi daɗi da alama."



Qarisa wa gadon da Hajarah take a kwance tayi, sannan ta kai hannu ta fara ɗan bubbuga gadon. Tana dai yi irin idan mutum yana so ya tashi wani daga bacci.



Amma ga mamakin ta sai taji shiru Hajarah bata farka ba, ɗan waro ido tayi waje, sai kuma a fili take faɗin


"Haba Sakeenah sai kace ba mace ba, don't be shy mana haba."


Tayi maganar tana kuma ƙoƙarin tashin Hajarah daga bacci.


Sai dai kuma har lokacin ko motsi Hajarah ba tayi ba zuwa, taƙin fa Sakeenah ta fara tsorata domin ko dama can akwai ta da mugun tsoro.



Hannu na rawa takai sai tin hancin Hajarah domin taji ko tana numfashi, sai dai kuma wani ƙarin tashin hankalin shi ne ko numfashi bata ji alamar tanayi ba, izuwa lokacin zufa kawai take haɗawa, ga jikinta dake faman rawa kamar mazari.
Fa sauri ta kai kunnen ta saitin hancin Hajarah, ko dai zata ji wani alamar amma kuma har lokacin shiru.



A mugun tsora ce ta fara ja da baya, sai kuma da gudun gaske tabar wurin, ta ƙarisa wurin da Hajiya Zuwairiya da take a kwance, ta fara bugunta cikin matsanancin kuka da tashin hankali take tashin ta, ganin ko motsi taƙi yi ne yasa ta ƙarisa wurin wani ɗan madaidaicin fridge a ɗakin ta buɗe, sannan ta ciro ruwa mai sanyi a ciki, kana ta dawo ta buɗe gorar ruwan ta watsawa Hajiya Zuwairiya a fuska.





A firgice Hajiya Zuwairiya ta tashi daga zaune tana karanto duk Addu'ar dake zuwa bakinta, sai da ta ɗan dawo nutsuwar ta sannan ta lura da Sakeenah dake faman rizgar kuka tamkar ranta zai fita.

"Ke, lafiyarki kuwa, Menene ya faru kike wannan kuka kamar anyi miki mutuwa?."

Hajiya Zuwairiya ta tambaye ta hankalin ta a ɗan tashe.




Sakeenah bata tsaya amsawa Hajiya tambayar da take ma ta ba, ta kamo hannunta ta ƙarisa da ita bakin gadon da Hajarah take kwance, sannan cikin kuka da wahalar fitar numfashi taƙe faɗin

"Hajiya Dan Allah ki duba Hajarah taƙi tashi fa, tun ɗazu, tsoro nakeji kar mu rasa ta."



Da jin haka yasa Hajiya Zuwairiya ta ƙarisa wuprin Hajarah ɗin nan ta shiga duba ta cikin sauri.

A hankali a hankali ta fara ja da baya babu abin da take karantawa a bakinta sai kalmar "Inna lil lahi."
Har ƙarshe saboda tsananin tashin hankali ta ma kasa magana, a matsayinta na cikakkiyar likita ta fahimci komai saboda haka kasa magana tayi.





Ganin Hajiya ta kasa magana ne, yasa Sakeenah ta fita da gudu daga bedroom ɗin saboda tsananin tashin hankali bata ma san inda take jefa ƙafafunta ba, a dai dai tsakiyar palon ta hango Abubakar da Jawaheer da kuma Rafi'at da Yusra suna magana.



Da gudun bala'i ta ƙarisa wurin tana kuka na fitar hankali, gaba ɗaya suka yo kanta suna tambayar ta ko lafiya, tama kasa magana, sai faman nuna musu bedroom na Hajarah take yi Yayin da wasu siraran Hawayen suke biyo idanunta suka wanke ma ta fuska.






Lura da inda take nuna musu ne, yasa gaba ɗaya suka nufa bedroom ɗin cikin tashin hankali ita ma ta mara musu baya.



Can gefe suka hango Hajiya Zuwairiya tana zaune kamar bata cikin hayyacinta saboda zaman Ƴan borin da tayi, Yayin da idanunta suke akan gadon da Hajarah take kwance saman shi.




Da sauri Abubakar ya ƙarisa wurin gadon ya fara kiran sunan Hajarah, amma ina rai Ya yi halinsa, gata dai Tamkar zata amsa masa, amma ina.




"Ta mutu, ta tafi shikenan ta tafi ta barmu, da Yaranta da jaririyar ta, ta tafi gidan ta na gaskiya, ba tare da ta cika Burinta na haɗuwa da Ahalin ta ba, shikenan kuma ta faru ta ƙare, Hajarah ta tafi ta Barmu a duniya, shikenan fa munyi Rashin mace ta gari, ga kirki, ga Haƙuri, Yah Allah bazan iya jurewa ba."



Duk wannan maganganun Hajiya Zuwairiya ce take yin su a Yayin da har lokacin idanunta suke akan gadon da Hajarah take kwance saman shi.





Tamkar Saukar Aradu haka zantukan Hajiya Zuwairiya suke shiga kunnen Abubakar Wanda ya tsaya cak da ƙoƙarin Tashin Hajarah da yake yi.


Zai iya cewa tunda Yake a duniya bai taɓa shiga matsanancin Tashin Hankali ba, irin na Ranar har Ranar kuwa da Haleesat Rashid Rayyan ta Rasu, komawa Ya yi Tamkar Statue a wurin gaba ɗaya zuciyar sa da gangar jikin sa sun tafi Hutun Rabin lokaci.



Yayin da gaba ɗaya mutanen palon suka ɗauki kalmar "Inna-lilahi-wa-inna-illahir-raji'un."


Suke faɗa cikin tashin hankali, amma banda Sakeenah wacca tuni ta sume a wurin.😭



A taƙaice dai faɗin irin tashin hankalin da wannan Ahali na Alhaji Sameer Lamiɗo suka tsinci kansu a ciki Tofah Tabbas Baki ko Alƙalami Ya yi kaɗan.  😓😥








Koda mutanen Jigawa dana Kano da sauran Ahali suka zo da Farin cikin na ganin mai jego da jaririyarta, suka sama wannan mummunar Labari na rasuwar Hajarah ga kyakyawar Jaririyarta da ta Bari.
Gaza jurewa da yawa daga cikin su suka yi domin sai da suka yi kuka.


Haka Rayuwar ta ci gaba da tafiya gaba ɗaya ɓangarorin babu daɗi sam, musamman ma ɓangaren Abubakar domin kuwa Rasuwar Hajarah ba ƙaramin taɓa Ya yi ba sosai sosai.






A Ranar da Hajarah ta cika sati biyu da Rasuwa Yusra matar Yusuf ta ɗauki Jaririyar Hajarah wacca taci suna 'AFEEFAH' /Tagari/

Ta koma Mai Duguri da ita da umarnin Abubakar domin kuwa da yardansa sannan kuma da amincewar sa Yusra ta ɗauki jaririyar domin ta ci gaba da kulawa da ita har zuwa wani lokaci, Wanda kuma wannan shawarar da ya Yanke, ba ƙaramin daɗi yayiwa gaba ɗaya Ahali ba.
Yayin da ita kuma Zaynerb ta koma Jigawa State hannun su Dr_Raheemah da zama.






Wanda Hakan ba ƙaramin haushi yaba Rafi'at ba, domin kuwa a cewarta ita Yafi kamata da ya bawa riƙon Zaynerb da kuma Jaririyar domin kuwa ta kusa haihuwa sai ta haɗa da Wanda zata haifa ta kula dasu duka, shiru kawai dai tayi ta shanye duka ɓacin Ranta.
Don karta kuma saka mijinta cikin wani hali bayan Wanda yake ciki.





Tofah haka suka ci gaba da gudanar da Rayuwar.
Tsakanin Rafi'at da Abubakar kuma zaman nasu dai abin babu yabo balle kuma wani abu wai shi Fallasa.




  - *-
  -
Hajarah nada wata Biyu da rasuwa, ranar wata Alhamis ita ma Rafi'at ta haifo Ɗiya mace, sai lokacin kuma Abubakar ya ɗan fara dawowa Nutsuwar sa.
Ranar suna Jaririya taci suna Lailah, zuwa lokacin Jaririyar da Hajarah ta Bari wacca Yusra take Riƙo duk da cewa madara take sha tayi ƙiba gata da kuma yi, ga wani kyau na musamman da ta ƙara.





Aikuwa a Ranar da Yusra taje da ita Abuja a hannun mahaifinta ta wuni yana bata wani kulawa na daban, duk cewa a duk ƙarshen wata Yana tafiya can Mai Dugurin domin ganin ta sannan ya wuce Jigawa State ma domin ganin Zaynerb.





___*💋 SARAUNIYAR KYAU 💋*_________ƚαƙυɳ ϝαɾƙσ__________________________________________________________💥👑𝑻𝒉𝒆 𝑮𝒍𝒂𝒎 𝐐𝐮𝐞𝐞𝐧👑💥____________________𝑩𝒚:𝑻𝒉𝒆 𝑵𝒂𝒊𝒏𝒂𝒓𝒉 𝑲𝒅____𝑲𝒉𝒂𝒅𝒆𝒆𝒋𝒂𝒓𝒕𝒉.  𝑺𝒂𝒃𝒊'𝒖.  𝒀𝒂𝒉𝒚𝒂𝒉

*



Page *83&84*


___**

Rayuwa ta ci gaba da tafiya da sauri sauri.
Yayin da dukiyar Abubakar Sameer Lamiɗo ta ci gaba haɓɓaka ta ko wani fanni dukiyar sa ƙara nin kuwa take yi sosai.


Wanda zuwa lokacin ya buɗe makarantar Islamiya da Masallatai da kuma Orphanage, da nin yar ladar ya dinga tafiya kai tsaye ga maragayya Hajarah matar sa.


 



Lailah Ɗiyar Rafi'at nada shekaru biyu a duniya Yayin da Haleesat take da shekaru huɗu twin's kuma Nailah da Nainarh suke da shekaru shida, shi kuma Abdulmaleek da Yake Babba Yake da shekaru Tara a duniya.



Zaynerb Ɗaya ga Maragayya Hajarah kuma take da shekaru huɗu a duniya ita ma.
Yayin da ƙanwar ta Afeefah dake can Mai Dugurin wurin Yusuf da matar sa da Yaran su da zama take da shekaru biyu kacal a duniya.



A lokacin ne kuma Rafi'at ta kuma Haihuwa ta haifa mace again Yarinya taci sunan mahaifiyar Rafi'at da ta Rasu ba jimawa wato Zinaru Yayin da Yayyinta suka saka mata xixi suna kiranta hakan.




A lokacin ne kuma Abubakar ba kunya ya amso Ɗiyarsa Afeefah a hannun Yusuf da matar sa, amma ita Zaynerb ya barta a Jigawa State a cewar sa ita ma zai karɓe ta amma sai bayan wani lokaci.





Rayuwa ta ci gaba da tafiya tana sauri sosai, Yayin da Abubakar Yake kula da Yarinyar sa Afeefah ko sauro baya bari ya taɓa ta, to a'ina ma sauro zai ganta.🤔




Afeefah ta taso Yarinya ce mai matuƙar kaifin basira da wayau, Sannan kuma sosai take ƙaunar Ƴan uwanta duka kamar yadda suma suke ƙaunar ta musamman ma dai Lailah, amma tsakanin ta da Momy Rafi'at kuwa sai dai kallo daga nesa, ko kuma gaisuwa amma in banda wannan, babu wani abu da yake shiga tsakanin su.


Dhekarunta uku a duniya aka saka su a school ita da Lailah Yayin da suke tafiya tare da sauran Yayyin su Haleesat da Nainarh Nailah sai kuma Abdulmaleek tsakanin ta da YaYarta Zaynerb kuwa duk da cewa ba'a tare suke ba, amma shaƙuwa ce ta musamman mai zaman kanta a tsakanin su, a dalilin kuwa duk a ƙarshen wata Abubakar yake haɗa kan Yaransa suje Jigawa State ziyara wani lokacin Momy Rafi'at tana binsu, amma wani lokacin saboda yanayin aikin ta haƙura take yi, Especially ma da mahaifinta ya gina ma ta asibiti nata na ƙashin kanta sai ya zama bata cika samun lokacin kanta ba.













_****______


Shekarun Afeefah Takwas a duniya Abubakar ya ɗauko Zaynerb daga Jigawa State, ya dawo da ita Abuja cikin Ƴan uwanta.
Rayuwa ta ci gaba da tafiya da yake Zaynerb yarinya ce mai masifar wayau da kaifin tunani shiyasa bata shiri ko kaɗan da Momy Rafi'at, domin kuwa ta fahimci ba ƙaunar su take ba, musamman ma idan ya kasance da mutane a wuri to nan ne fa zata dage ta dinga nuna musu ƙauna ta musamman, amma kuma suna kasancewa daga su sai ita, wahala take basu ba kaɗan ba, domin kuwa tasha ta zane Zaynerb ba sau ɗaya ba kuma ba biyu ba, amma kuma ita Afeefah ko tayi nin yar dukan ta kasawa take yi domin kuwa Zaynerb shiga tsakani take sai dai ita a dake ta amma bata bari ko ƙuda ya taɓa ma ta ƙanwa, wacca take shalele a wurin mahaifin su, Alhaji Abubakar Mai Kyau, sai dai kuma duk da ƙiyayyar da Momy Rafi'at take yi wa su Afeefah da Zaynerb bata taɓa nuna wa a gaban Yaranta ba, ko kuma mijinta cikin taku da tsare gida take abin ta.





A wata Ranar Jumma'a ne Ahalin Alhaji Sameer Lamiɗo suka tashi da wani mummunar Labari na Rasuwar Alhaji Sameer Lamiɗo ta farar ɗaya cikin dare, wuraren uku na dare ya rasu, Yayin da kafin gari ya waye ita ma matar sa Hajiya Harirah ta ce ga garin ku nan tabi mijinta.


A lokacin ba ƙaramin Tashin Hankali gaba ɗaya Ahalin Alhaji Sameer Lamiɗo suka shiga ba, musamman ma Abubakar domin kuwa zai iya cewa wannan ne mutuwa ta uku da aka taɓa masa waɗanda ba ƙaramin Tashin Hankali ya shiga ba.

A lokacin kuma sai mutuwar masoyiyar sa Haleesat Rashid Rayyan da kuma matar sa Hajarah Ya dawo masa sabo a zuciya.




Gaba ɗaya Ahalin basa cikin walwala sakamakon Rasuwar Alhaji Sameer Lamiɗo, hatta mutanen France, Lagos, Kano, Mai Duguri da Adamawa States dama su Abubakar dake Abuja suka taru a Jigawa State jikin ko wannensu a mugun sanyaye.






Alhaji Sameer Lamiɗo da matar sa Hajiya Harirah suna da watanni Biyar da Rasuwa zuwa lokacin tuni Dr_Raheemah da Hajiya Zuwairiya suka kammala taka ba.




A lokacin ne kuma suka gaza jurewa suka kasa zama a gidan dama Jigawa State gaba ɗaya.
Bayan Raba gadon Alhaji Sameer Lamiɗon. Mai matuqar Yawan gaske ne da akayi, Dr_raheemah ta tattare ya nata ya nata ta koma Kano da zama wajen Autan ta Sagir da iyalansa.

Yayin da ita kuma Hajiya Zuwairiya ta koma Mai Duguri wajen Yusuf da iyalansa.










____**__



Rayuwar ta ci gaba da tafiya ana gungura wa.
Yayin da a kullum dukiyar Alhaji Abubakar Mai Kyau ƙara bunƙasa take obaaaaa.



A lokacin ne kuma ya buɗe wurare da Yawa. banda waɗanda ya buɗe a baya, Ya buɗe wurare kamar su.


Mai kyau Chinese Restaurant.
Mai Kyau Indian Restaurant.
Mai Kyau Korean Restaurant.
Mai Kyau Spanish Restaurant. And Mai Kyau ethiopian Restaurant. Et.c.😘


Sannan kuma Ya buɗe Company na ƙera Takalma Wanda ya yi ma laƙani da.

'MAI KYAU ABBAN FEEFAH'
A Adamawa State, kana kuma ya buɗe wani Company shi kuma na ƙera Atamfofi, materials, laces a Borno State.



Kana ya buɗe wani company again na qera wayoyi shi kuma aka saka masa suna.

Mai Kyau
Bayan haka ya buɗe restaurant daban daban da kuma companies daban daban a kowani State na faɗin Nigeria, sannan kuma hatta ƙasashen waje akwai companies nasa da Yake ƙera kaya daban daban  kamar irin ƙasar.



Amsterdam, Romanian, Spain, Poland, Greece, Austria, Italy, Egypt, Sudan, Libya, Eritrea sai kuma Germany Wanda acan companies nasa sunkai uku sai kuma Malaysia. E.t.c.💫💫





______**

Rayuwa ta ci gaba da tafiya ta ko wani ɓangare cikin sauri sauri Yayin da zuwa wannan lokacin shekarun Afeefah goma a duniya Yayin da suke kai ɗaya da Lailah gasu suna masifar kama sosai Like a twin's.





A wata Ranar lahadi da safe misalin ƙarfe goma sha biyu.

Afeefah tana zaune a palon gidan ta ƙura karantun Alqur'ani a plasma tv, na palon tana sauraro sai faman karatu take yi, da yake lokacin ita da Lailah sun kammala primary school sun ma zama Jarabawar fita.



Sai faman karatun ta take Yayin da Lailah take zaune daga ƙasan carpet sai roƙon Afeefah ɗin take a kan ta kashe karatun ta kunna musu cartoon su kalla,  ita kuma Afeefah tayi ma ta kunnen uwar shegu.

Su biyu ne kacal a palon.

Daya ke shi Abdulmaleek Ya kammala secondary school Ya tafi ƙasar Russian  karatu.
Yayin da su kuma Nainarh da Nailah suke a Boarding school suna karatu.
Ita kuma Zaynerb da taƙi Boarding, a ranar tana saman Bene a Bedroom ɗin ta tana karatu.
Yayin da Momy Rafi'at aka ma ta kiran Emergency a hospital ɗin ta.
Shi kuma Daddyn su Alhaji Abubakar Mai Kyau kuma Ya fita company domin cike wasu Takardu, duk da cewar ba Ranar aiki Bane, da yake Yana shirin komawa ƙasar Jamus ne domin Ya qara bunƙasa Harkokin kasuwancin sa, na can.






Kallon Lailah dake faman sha re Hawaye tamkar an dake ta, Afeefah tayi tana dariya ta ce

"Allah sis kina Bani mamaki, ace ke kwata kwata bakya ƙaunar kiji an saka karatun Alqur'ani Mai Girma, a gida sai kace Ƴar maguzawa, to Indai kinaso na kashe karatun na kunna miki cartoon, sai kin Fara gogemun Ƙafata, amma idan kin yadda fa." 🌚




Da sauri Haleesat dake can Dining Room tana faman kai loma,  kallon Afeefah jin abin da take cewa, sai dai da yake ita ɗin miskilar gaske ce, ba tayi magana ba, sai ma dakata wa da cin abincin da tayi, tana kallon drama ɗin su domin ganin yadda zata kaya, shin Lailah zata Yarda ta goge ƙafar Afeefah ɗin, ko kuwa?."
Ita dai Haleesat iya sanin ta da Lailah muguwar Ƴar girman kai ce, ga ta da mugun tsafta, ga aji, ga Raini ga.!! umm ummm.🧐







Ajiyar zuciya Lailah ta sauke sannan cikin murya irin na Wanda ya sha kuka Ya ƙoshi ta ce

"Idan na goge miki ƙafar zaki bani remote control ɗin, na kunna cartoon ɗin?."




Murmushi Afeefah tayi wanda ya bayyana dimples ɗin ta duka biyun ga wushiryarta Mai Kyau, tana juya manyan dara daran kyawawan fararen idanunta ta amsa ma ta

"Yeah it's okay, idan zakiyi, to ga Remote sai na baki, ki kashe karatu ki kunna cartoon."




Da jin Haka Lailah tayi murmushin murna, sannan ta durƙusa dai dai saitin fararen ƙarfafun Afeefah dake sanye cikin farar safa.
Ta cire safar sannan takai hannu ta cire hular kanta, nan take dogon gashin kanta Wanda yasha kitson kalaba ƙanana ya zubo ma ta har gadon bayan ta.

Nan naɗe hular tayi, yadda zata ji daɗin goge ƙafar, sannan ta kamo ƙafar Afeefan ta ɗaura akan cinyarta, tana goge hawaye.
Yayin da Afeefah take dariyar murna, Lailah har takai Hannu ke nan zata fara goge ƙafar Afeefah ɗin, taji anyi sama da ita sannan an jefa ta saman 3sieter.



Da sauri gaba ɗayan su tun daga kan Haleesat dake zaune a Dining,nda Lailah da aka yi wurgi da ita saman 3sieter Like a Little kid, da kuma Afeefah wacca take saman 1sieter suka ɗago kansu a tare domin ganin mutumin da ya yi wannan aiki.





Momy Rafi'at ce tsaye sai Faman huci take yi, ga yarinyar ta xixi mai shekaru Takwas a duniya tsaye gefe.
Ashe tun lokacin da Afeefah taba Lailah zabi a kanta goge ma ta ƙafa sannan ta bata remote.
Momyn ta shigo ta tsaya ne domin ganin shin Lailah zata gogewa Afeefan ƙafar ko kuwa.





A mugun fusace Momy Rafi'at tayo kan Afeefah bata tsaya jiran komai ba, tasa Yatsun hannunta duka guda Biyar waɗanda Allah ya azurta ta dasu ta bawa Afeefah lafiyayen mari. Wanda sai da taga wuta tsaban azabar da ya ziyarci duka fuskar ta dama gangan jikinta.

Sannan ta fin ciko ta daga saman kujerar, nan ta shiga dukan ta kamar Allah ya aiko ta, tana dukanta tana Marin ta, ita kuwa Afeefah in banda kuka babu abin da take yi saboda tsananin azaba har muryar ta, ta dashe, da kyar ake iya jiyo kukan da take yi.



Lailah kuwa sai faman dariya take yi tana faɗin

"Ƙara ma ta, Momy ƙara ma ta."


Yayin da Haleesat dake Dining Room tayi shiru tana kallon ikon Allah cike da mamakin dukan da Momy take wa Afeefah, ita fa bata ga abin duka ba anan, sai dai bata ce komai ba, haka zalika bata miƙe ba a domin ta taimakawa Afeefah ɗin, sai dai ta ji babu daɗi a zuciyarta.




Da gudu Zaynerb ta fito daga bedroom ɗin ta jiyo kukan Ƴar uwanta da tayi, saboda tsananin saurin da take yi ga tashin hankalin da take ciki, yasa da uku uku take tsallake staircases ɗin, tana saukowa Down, Aikuwa garin saurin da take yi ƙafarta ɗaya ta gurɗe gaba ɗayanta tayo ƙasa tun daga saman bene har sai da ta yo Down.

Aikuwa tasha azaba sosai, ga Bayanta da ya riƙe dama abu ga mara ƙiba, amma duk da hakan bata dan dara ba.



Da a zamar ta ta miƙe tsaye, sannan ta ƙarisa tsakiyar palon inda Afeefah take kwance kamar gawa ga Momyn har Yanzu bata haƙura ba, sai Faman dukan ta da marinta harda hamɓarinta take yi.




Tsuguna wa Zaynerb tayi a gaban Momyn tana bata haƙuri, amma ina Momy tayi nisa, bata jin kira da ta gata hakan ma bai isheta ba, sai ta ƙarisa wajen kayan wuta na Palon, ta ɗauko wayar wuta, sannan ta dawo ta haɗa da Zaynerb da Afeefah ɗin tana duka.
Gaba ɗaya tabi ta farfasa musu jiki da duka, ko gajiya ba tayi ga Zaynerb sai faman kuka da kururuwa take tana ka re Afeefah ita dukan yake samu.



Ganin dai Momyn nasu zatayi kisa ne, Yasa Haleesat tashi da sauri ta ƙarisa tsakiyar palon tana kare su, sannan kuma cikin tsawa da ɗaga murya take faɗin

"Momy.! Momy! Are going to crazy or what?, ki barsu haka mana zasu mutu fa, wai Menene ma abin duka anan ne, wannan zalunci ne fa."






Kallon Haleesat Momyn tayi ita ma cikin tsawa da huci ta ce.



"Ki barni Haleesat ki barni na daka wannan shegun, in banda tsaban Rashin mutunci har Afeefah ce zata ce Lailah ta goge ma ta ƙafa, ita har wacece hakan, Wacece ita iye, How Dare Her?, ki matsa ko kuma na haɗa dake, duka dasu na daka."


Ƙin matsawa Haleesat tayi sai ma ƙara rufe su tana ka resu da tayi.


Ganin haka yasa Momyn dage wa iya ƙarfinta, ta ɗauke Haleesat da mari mai zafi.


Da sauri Haleesat ta dafe kun cinta cike mamaki take kallon Momyn, gaza jurewa tayi da sauri tabar wurin ta haye sama da sassarfa.




Ita kuma Momyn ta ci gaba da dukan su Zaynerb da ko motsi ba sayi zuwa Lokacin. 😭


For More Enquires
08081129487
The Nainarh Kd




___*💋 SARAUNIYAR KYAU 💋*_________ƚαƙυɳ ϝαɾƙσ__________________________________________________________💥👑𝑻𝒉𝒆 𝑮𝒍𝒂𝒎 𝐐𝐮𝐞𝐞𝐧👑💥____________________𝑩𝒚:𝑻𝒉𝒆 𝑵𝒂𝒊𝒏𝒂𝒓𝒉 𝑲𝒅____𝑲𝒉𝒂𝒅𝒆𝒆𝒋𝒂𝒓𝒕𝒉.  𝑺𝒂𝒃𝒊'𝒖.  𝒀𝒂𝒉𝒚𝒂𝒉🤙


☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆
💦𝑳𝒂𝒇𝒂𝒛𝒊 𝑾𝒓𝒊𝒕𝒕𝒆𝒓'𝒔 𝑨𝒔𝒔𝒐𝒄𝒊𝒂𝒕𝒊𝒐𝒏💦🤙

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆

*




Page *85&86*


"Rafi'at. Rafi'at. Ke Rafi'at.!!"



Duk wannan kiran Alhaji Abubakar Mai Kyau ne Yake ƙwalawa Momy Rafi'at Yayin da yake ta kowa palon hankali tashe, ganin irin dukan mutuwar da take yi wa marayun Yaransa.



Aikuwa Yana ƙari sawa shima bai tsaya komai ba. Ya yasa kyawawan Yatsun hannun sa. Ya bata zazzafan maruka a kumatu, bai tsaya ba ya kuma ƙara ma ta, ya ƙara, ƙara ma ta, har sai da ya ma ta sau Biyar ta ko'ina, sannan ya dakata cikin huci da ɓacin rai yake kallon ta yana faɗin.



"Rafi'at akan wani dalili kika daki waɗannan marayun Yaran?, dama Haka mukayi dake zaki dinga duka min Yara Iyyyee?."


Ya yi ma ta Tambayar ne damma bayaso ya yanke Hukunci kai tsaye.


Tana huci ita ma take basa amsa da faɗin

"A kan na isa na taɓa su, nace saboda na isa dasu ne, kuma sunyi min laifi mai girma, shiyasa idan kuma akwai abin da zaka iya kayi kai tsaye ina jiran ka Malam Abubakar."



Tayi maganar cikin tsawa da kururuwa tamkar batasan wanene tsaye a gabanta ba.


"Okay haka kika ce ko?."


"Eh Abubakar Sameer Lamiɗo haka na faɗi kayi duk abin da kaga zaga iya."



Cikin Huci shima Yake faɗin

"It's okay a baya banso na yanke wannan tsatsaurar Hukuncin a kan ki ba, amma kuma tunda hakan kika zaɓa ki kwashi yaran ki, kije ni Abubakar Sameer Lamiɗo na sakeki, saki ɗaya ni Abubakar Sameer Lamiɗo na sakeki saki biyu..."😐




🔥🔥Kan Bala'i 😝 Taɓɓ, Tashin sense Wanda ba'a saka masa lokaci, Balle kuma Rana 🔥🔥 }






Cak... Momy Rafi'at ta tsaya galala tana kallon mijinta Abubakar wanda ya dan ƙara ma ta saki har biyu lokaci guda, gaba ɗaya wutarta ta tsaya cak, saboda tsananin tashin hankali, tama kasa magana, sam bata yi tunanin wannan tsatsaurar hukuncin Abubakar zai yanke a kanta ba, a tunanin ɗauke Yaransa zai yi daga gidan ya kaisu can wurin mahaifiyar sa ko kuma Ƴan uwansa.




Kallon Lailah da tayi tsuru tsuru da ita a saman 3sieter inda Momy Rafi'at ta jefa ta, Alhaji Abubakar Mai Kyau ya yi kana Ya daka ma ta wani uban tsawa Yana faɗin
"Tashi ki wuce wurin uwarki tun kafin na ya galgalaki a anan wurin... Wato ke ce mai cewa a ƙarawa Shalele ta ko?, zaku sani daga ke har uwan taki, sai nayi maganin ku."



Da gudu ta sauko daga saman 3sieter ɗin har tana tun tuɓe, ta ƙarisa wurin uwarta wacca ta zama Tamkar statue a wurin. 😹





Qari sawa wurin da Yaran nasa suke ko wacce a sume. Ya yi sannan ya kamo hannun Zaynerb ya ɗa ga ta ya saɓata a kafaɗa sannan Ita ma Afeefah da jini duk yabi ya ɓata rigar Ƴar kanti dake jikin ta.

Ko kallon wurin da Momy Rafi'at take bayyi ba, ya fi ce dasu kai tsaye parking lot ya nufi.




Da hango Mister Mai Kyau tafe, ga Yara jiki duk jini, driver Jacob ya tabbatar da babu lafiya.
Da saurin sa ya ƙarisa wajen da motocin gidan suke a fake, sannan ya buɗewa ogan nasa motar ya saka Zaynerb a back seat, sannan ita ma Afeefah ya sakata, kana shima ya shiga, ganin haka shima Jacob ɗin ya shiga sannan ya tayar da motar, da gudu suka bar gidan bayan gate man ya wangale musu gate.






Wani Emergency dake a nan kusa da yankin Jacob ya ƙarisa da su bisa umarnin Mister Mai Kyau.




Da sauri ya fito daga motar sannan ya fito da Zaynerb aka aurata bisa Stretcher sannan aka shiga ciki da ita. Yayin da ita ma Afeefah aka ɗaura ta bisa gadon ko numfashi bata yi, gaba ɗaya a kayi ciki da su domin basu a gajin gaggawa.
Yayin da Alhaji Abubakar ya yi ma Jacob umarni da ya koma can gida da motar.




Sannan ya shiga cikin emergency ɗin da yake Babban mutum ne kuma sananne a duniya, shiyasa ba tare da ɓata lokaci ba ko bincikan lamarin aka fara basu taimakon gaggawa.



Tuni Zaynerb ta dawo Hayyacinta sai dai kuma a dalilin faɗowar da tayi daga saman bene ta sama gocewar ƙashi a hannun ta na dama.



Sai dai kuma duk yadda aka so Afeefah ta dawo Hayyacinta Abu dai ya cutura, domin kuwa ba ƙaramin wahala ta sha ba. Wanda dalilin haka ne ma yasa ciwonta wanda ba'asan dashi ba tashi. 🙄





Fitowa daga cikin emergency room ɗin Dr. Ya yi Yayin da wasu Nurses ma ta biyu suke bin Bayansa.





Da sauri Alhaji Abubakar da Zaynerb wacca taƙi zama a room ɗin da aka bata, suka miƙe kana suka nufi Dr. suna tambayar sa halin da Afeefah din take ciki.




Cire Nose mask dake fuskar sa Dr. Ya yi kana cikin girmamawa ya fara magana.


"Mister Mai Kyau. Please ko zamu iya tattaunawa da kai a office nawa?, domin maganar ba zata yiwu a tsaye ba."




Ajiyar zuciya kawai Alhaji Abubakar Mai Kyau. Yake saukewa domin kuwa ya fahimci akwai matsala, kallon Zaynerb dake faman hawaye Ya yi kana cikin muryar kwantar da hankali Yace


"Zaynerb Ɗiyata, please koma ki zauna, ki jirani kinji Ƴar uwanki zata sama lafiya soon, amma fa sai kin daina kuka kinji tawan?."


Share hawaye tayi kana ta koma ta zauna, bata ce komai ba, amma ta yanke a ranta ko ba yanzu ba sai ta Rama musu Abin da Momy Rafi'at tayi musu, tana gani Daddyn da Dr. Sun nufa Hanyar office na Dr.
Ta miƙe da sauri ta ƙarisa ƙofar room ɗin tana leƙen ƙanwarta ta wacca aka saka mata oxygen ta baki kamar babu Rai a jikin ta.



Wani kuka ne mai ƙarfi ya kuma zuwa ma Zaynerb ganin irin Halin da ƴar uwan nata take a ciki. 😭






Wuri Alhaji Abubakar Mai Kyau. Ya samu ya zauna a ɗaya daga cikin kujerun da suke a office ɗin, sannan shima Dr. Ya zauna sannan bayan sun gaisa, suka yi shiru na wani lokaci, kana Dr. Ya katse shirun da office ɗin ya ɗauka, bayan ya yi gyaran murya sannan ya fara magana kamar haka.




"A gaskiya Mister Mai Kyau bazan ɓoye maka ba, domin kuwa halin da ɗiyar ka take ciki ya tsanan ta, fiye da kima, domin ko a dalilin dukan mutuwar da aka ma ta a bisa binkciken da muka gunadanar a kanta mun gano cewar, ciwon ta ne, ya tashi wanda hakan ne yasa zuciyarta da gangar jikin ta sukaƙi kaɓar duka taimakon da muke bata. Sann..."




Katse sa Alhaji Abubakar Ya yi Cike da Tashin Hankali Yake faɗin

"Ban fahimta ba, dama Afeefah tanada wani ciwo ne. Wanda mu bamu san dashi ba?. Please Dr. Yimin yayani yadda zan gane."🥺




Ajiyar zuciya Dr. Ya sauke sannan yana amsa masa da faɗin

"Dama Bai zama dole ku san tanada wannan ciwo ba, domin kuwa ba ko wani lokaci yake tashi ba, sai lokacin da aka ɓata ma ta rai, misali dai kamar ace.

Yanzu tana cikin Mood na farin ciki, sai kuma wani abu na baƙin ciki, ya same ta, shi ne wannan ciwo nata zai tashi, ko kuma tana cikin Mood na baƙin ciki, sai wani Abu na Baƙin ciki ya kuma samun ta a lokaci guda, tofa wannan ciwo nata yana iya tashi, ko dai still tana cikin Mood na farin ciki sai wani Abu na farin ciki Ya kuma nin kuwa akan wannan farin ciki da take ciki. Tofa ciwon ta nan ma zai iya tashi."




Zugum Alhaji Abubakar Mai Kyau Ya yi Yana sauraron Dr. Yayin da hankalin sa idan Ya yi dubu, tofa ya tashi domin kuwa shi tunda yake a tayuwar sa. Bai taɓa ji ko cin karo da makamancin wannan ciwo ba.

Sai da ya tattaro duka Nutsuwar sa sannan Ya fara faɗin

"Dr. Dama can ana iya samun mutane masu wannan ciwon ne, ko kuwa dai Yanzu ne, aka fara samu?."





Gyara zaman medical glass dake a idanun sa Dr. Ya yi tare da cewa

"Gaskiya dai a wannan zamanin da muke ciki, ba'a taɓa samun mutane masu kalar wannan ciwo nata ba.




"Okay, toh ciwon nata yana yanayi da na masu hawan jini ko ciwon zuciya ne ko kuwa dai akwai banbanci?."

Alhaji Abubakar Mai Kyau, ya kuma tambaya cike Fargaba.



"A'a sam ko kaɗan baya yanayi ko kama da ciwon zuciya ko Hawan jini."

Cewar Dr. Sannan Ya ci gaba da cewa "Sai dai kuma wannan ciwo nata yana kamance ceniya da ciwon 'tinnitus' sai dai kuma kai tsaye, ba za'a kira shi da tinnitus ba, saboda su masu fama da ciwon tinnitus. Yawancin su zaka ga mutanen da suka manyan ta ne, ko kuma waɗanda suke cikin damuwa obaaaaa.
Sannan Yawancin abin da yake yayar musu da wannan ciwo shi ne, kodai.

•Ringing.
•Buzzing.
•Roaring.
•Clicking.
•Hissing. E.t.c.
Amma ita Ɗiyar ka nata ciwon yana da Banbanci da wannan, domin kuwa ita ana bata kulawa, na musamman kuma idan aka dena Yawan ɓata ma ta rai, zata iya warkewa."



Ajiyar zuciya Alhaji Abubakar Mai Kyau. Ya sauke a karo na babu a dadi jin abin da, Dr. Yace sannan ya kuma tambayar


"Yanzu ita Afeefah nanda yaushe ne zata iya dawowa cikin hayyacinta?."


"Eh bazai wuce nan da gobe ba, idan kuma aka ci sa'a zuwa dare ma, zata iya dawowa cikin hayyacinta."




A taƙaice dai Afeefah ba ita ta sama dawowa hayyacinta ba sai washe gari wuraren goma na safe.




Aikuwa koda Alhaji Abubakar Mai Kyau ya tabbatar da ta sama lafiya gaba ɗaya ita da Ƴar uwanta Zaynerb.



Ranar da suka cika sati ɗaya a hospital. Ya kwashe su ya tattara gaba ɗaya yanasu yanasu yabar ƙasar dasu ta private gen. Nasa.




Aikuwa gaba ɗaya Ahali da dangi ba ƙaramin mamaki suka sha ba, lokacin da suka sama labarin ɗaukar Afeefah da Zaynerb da Alhaji Abubakar Ya yi yabar ƙasar dasu.
Gefe guda kuma ga sakin da dan ƙara wa Momy Rafi'at. Abu dai ba daɗinji, sai dai kuma basu sama labarin dukan da Momy Rafi'at tayi ma su Afeefah ba, abin da suka sani dai shi ne, Abubakar ya ɗauki Yaran sa biyu Ƴan lelen sa Yabar Nigeria dasu, ita kuma Momy Rafi'at ya ɗan ƙara ma ta saki har biyu na Rashin dalili, domin kuwa haka ita Momy Rafi'at ɗin ta faɗa musu.🤔






---------***


Mister Mai Kyau, Kai tsaye ƙasar Eritrea Ya wuce da su Afeefah, anan suka zauna a Babban birnin ƙasar wato Asmara suka Fara gudanar da Sabuwar Rayuwa mai cike ƴanci babu takurar Momy Rafi'at babu komai, sai dai kuma ba kaɗan ba, suka yi kewar ƴan uwansu, sai dai babu yadda suka iya, domin kuwa haka ƙaddara ta zaɓar musu.

Ba tare da wani ɓata lokaci ba, ya saka Afeefah a secondary school j.s.s.one Yayin da ita ma Zaynerb ta ci gaba da karatunta na secondary school ɗin.


Rayuwa ta ci gaba da tafiya musu cikin kwanciyar hankali Yayin da gefe guda Suke yawan yin waya dasu Nainarh da Nailah da suke Boarding school a Nigeria anan Lagos.
Yayin da Shima Abdulmaleek da yake karatu a Rasha suna yawan kai masa ziyara, sai dai kuma har lokacin Alhaji Abubakar Mai Kyau bai mayar da Momy Rafi'at ba, kuma ko sau ɗaya bai taɓa bari su Afeefah da Zaynerb ko kuma Nainarh da Nailah da Abdulmaleek su kirata a waya ba, ko kuma suyi waya dasu Lailah, ya hana faruwar hakan ta ko wani ɓangare.








Rayuwa ta ci gaba da lulawa cike da nasarori daban daban, shekarar su Afeefah biyu a ƙasar Eritrea, Mister Mai Kyau, mahaifin su ya kuma ɗaukar su, suka koma ƙasar Spain da zama, nan ma dai sai da suka kwashe tsawon shekara ɗaya, sannan ya ɗauke su ya kuma Barin ƙasar Spain dasu.
Zuwa lokacin Afeefah ta kammala j.s.s.three.




Kai tsaye ƙasar Germany {Jamus}. Ya wuce dasu, zuwa lokacin an mayar da Auren sa da Momy Rafi'at sakamakon takurawar da mahaifiyar sa da kuma Ahali suka dingi masa.

Sai da aka kuma ɗaura Auren, domin kuwa an shafe fin shekaru biyu da sakin, sai dai kuma yaƙi bari koda wasan wasa ita da yaranta, su tako ƙafa zuwa ƙasar da suke, domin kuwa a Nigeria suka tsaya ita da yaranta, kuma har lokacin bai bari su Afeefah su dinga waya dasu Lailah Ba.


 
08081129487
_-_💓The Nainarh Kd 💓_-_
       




___*💋 SARAUNIYAR KYAU 💋*_________ƚαƙυɳ ϝαɾƙσ__________________________________________________________💥👑𝑻𝒉𝒆 𝑮𝒍𝒂𝒎 𝐐𝐮𝐞𝐞𝐧👑💥____________________𝑩𝒚:𝑻𝒉𝒆 𝑵𝒂𝒊𝒏𝒂𝒓𝒉 𝑲𝒅____𝑲𝒉𝒂𝒅𝒆𝒆𝒋𝒂𝒓𝒕𝒉.  𝑺𝒂𝒃𝒊'𝒖.  𝒀𝒂𝒉𝒚𝒂𝒉🤙






Page *87&88*



****

Afeefah da Yayarta Zaynerb da kuma mahaifin su Alhaji Abubakar Sameer Lamiɗo ( Mister Mai Kyau.)



Sun ci gaba da tafiyar da rayuwar su, su uku kacal a ƙasar Jamus.
Rayuwa mai cike farin ciki da fahimtar juna.
Tunda suka bar Nigeria daga su har mahaifin su babu ɗayan su da ya kuma tako ƙafarsa izuwa Nigeria, ko da kuwa wani sha'anine ya tashi na Ahali.
Sai dai su gani ta Video call, sai dai kuma duk da haka su na Nigeria basu watsar dasu ba, domin kuwa duk ƙarshen shekara gaba ɗaya suke taruwa tun daga kan Ahalin Zuwaira da Jawaheer da Jummai dake Jigawa State da kuma Yusuf da ke zaune a Mai Duguri da kuma Sameen dake Lagos sai kuma Sakeenah dake Adamawa State har da ma Sagir dake zaune a Kano State.




Gaba ɗaaya suke taruwa da Familynsu suje ƙasar dasu Afeefah ɗin suke a can kuma suke haɗuwa da Yunus shima da Familynsa da suke zaune a ƙasar faransa.






Rayuwa ta ci gaba da tafiya sumuluqui ta ko wani ɓangare Yayin da tuni Zaynerb ta kammala secondary school nata anan ƙasar Jamus, kai tsaye ta wuce ƙasar NETH Babban Birnin ƙasar wato Amsterdam domin Karantar ilimin Halittar Furanni. 🥀





Yayin da Afeefah da mahaifinta Mister Mai Kyau, suka ci gaba da gunadanar da Rayuwa anan ƙasar Jamus.




Shekarun su uku a ƙasar Jamus, zuwa lokacin Afeefah ta kammala secondary school, izuwa lokacin ne kuma Mister Mai Kyau. Ya huce daga dogon fushin sa, suka fara shirin dawowa ƙasarmu ta haihuwa Abin alfaharin mu Nigeria.🇳🇬






A lokacin gaba ɗaya Dangi anyi Farin ciki da murnar dawowa Nigeria dasu Afeefah zasuyi, sai dai ba tare da Zaynerb ba, wacca take ƙasar Amsterdam.
Iya Shalelen Daddyn ta Afeefah ce da kuma Daddyn nata Mister Mai Kyau, zasu dawo Nigeria ɗin, duk da haka Ahalin Alhaji Sameer Lamiɗo, sunyi Farin ciki domin sun san ita ma Zaynerb ɗin, karatu ne ya kaita ƙasar Amsterdam ɗin. Tana kammalawa ita ma zata dawo ƙasarta Nigeria.💃





       



*GERMANY*




𝗕𝗮𝗯𝗯𝗮𝗻 𝗕𝗶𝗿𝗻𝗶𝗻 𝗞'𝗮𝘀𝗮𝗿 𝗚𝗲𝗿𝗺𝗮𝗻𝘆,𝗕𝗲𝗿𝗹𝗶𝗻.




Da gudu matashiyar budurwar wacca ba zata Haura shekaru goma sha shida da watanni ba a duniya ba.


Take Haura katafaren benen Gidan nasu, tana saukowa, doguwa ce sosai gata da coca cola shape Abin gunin ban sha'awa da Burgewa.🥰

Ga manya manyan dara daran kyawawan fararen idanunta, da suke sheƙi. Yanayin shape nasu Like a egg.

Ga ɗan ziririn hancin ta a wurin wanda Yake jinsa kamar biro, saboda tsaban siran taka da tsayi, gashi ɗan dai dai gunin burgewa.
Ga ja-ja-yen laɓɓanta ƙanana sirara dasu, sai faman sheƙi suke yi sannan suna motsi a hankali kamar tanaso ta furta wani abun. Yayin da Hakan yaba kyakyawar wushiryarta na ƙasa mai kyau, damar Bayyana.

WOW.💋
Ga eye brow nata gashin giranta wasu baƙaƙe masu kyau, ga shape nasu ya zauna ɗamass. Haka zalika ma eyelid da eyelashes nata gasu nan wasu masu kyau dasu. A hankali take lumtse kyakyawan idanunta tana buɗewa.
Beautiful face nata ɗauke da kyakyawar murmushi wanda yake bayyana duka dimples ɗin ta guda Biyu.
Sanye Take cikin silk Dresses gown doguwa sky purple color, gown ɗin ta zauna a jikinta ɗamas-mass, daga tsakiya wajen cikinta ta Tamke da wani belt black color, gown ɗin mai gajeren hannu ne, sai dai kuma duk da haka ba hannun vest bane da Rigar.

Kanta babu hula sai hakan yaba dogon gashin kanta mai tsayi da yawa na gaske. Wanda Yasha gyara in cute ponytail damar sauka ma ta har gadon baya.

Hannunta na hagu na daga cikin gown pocket ɗin rigar.
Yayin da ɗayan hannun nata na dama ke nan Wanda yatsun suka sha Jan lalle daga tsakiyar hannun kuma wani haɗaɗɗen Bracelet ne, shima sky purple and black color na zallar lu'u_lu'u, ta kama glass na staircases ɗin dashi tana saukowa.

Da gudunta ta ƙarisa saukowa daga saman staircases ɗin, kai tsaye ƙayataccen palon wanda ya gaji da haɗuwa ta ƙariso kana still cikin gudun ta ƙarisa wurin Daddyn ta dake hakimce saman wata haɗaɗɗiyar sofa 1sieter yana sipping coffee, Yayin da yake karanta magazine.

Ta Baya tayo hug nasa sannan cikin siririyar muryar ta mai zaƙi da daɗin sauraro Take faɗin
"Good morning My lovely Dad, today am so very happy, because today we are go back to Nigeria..."🥰



Murmushi Alhaji Abubakar Mai Kyau, Yayi kana Yace
"Okay saboda kina murnar komawa gida Nigeria shi ne zaki ɓallani ko?."



Dariya tayi tana ta zagayowa ta zauna a sofa mai fuskan tar sa wanda yake zaune akai kana ta basa amsa da faɗin

"Oh Dad kawai dai, ina cikin farin ciki ne, amma ina ni ina ɓalla My Daddy na?."


"Okay enjoy your glamorous day, My Shalele."

Cewar Mister Mai Kyau, sannan ya ci gaba da cewa
"Oyaaa ga breakfast nan a gaban ki, fara ci mu gani."


Kyaɓe Beauty face nata tayi cike da shagwaɓa take cewa
"Oh no Dad bana ci fa, kai dai kayi sauri ka kammala, domin kuwa na ƙosa na ganni a Naija, domin ganin su Auntie Haleesat na, da kuma su Auntie Nainarh da Nailah ta da sauran jama'an gida harda Lailah fa."☺️





Murmushin jindaɗi Alhaji Abubakar Mai Kyau, Ya yi a kullum yana kuma alfahari da Ɗiyarsa, a dalilin kyawawan halayen mahaifiyar ta da ta kwaso, wato dai har yau bata manta da Lailah ba wacca a dalilin ta komai Ya faru.

Haka dai suka ci gaba da fira a tsakanin Ƴa da uban, cike da fahimtar juna da ƙaunar juna irin na Ɗa da mahaifi. Abin nasu gunin burgewa.😘






Sai da ya kammala cin Breakfast ɗin nasa sannan bayan wani lokaci suka fito daga cikin ƙayataccen Gidan, gaba ɗaya su Biyun suka shiga motoci sannan suka Bar gidan izuwa filin jirgi tare da Rakiyar guard's.





Basu wani daɗe ba suka ƙarisa filin jirgin sama na ƙasa da ƙasa dake can ƙasar Jamus, suna isa ba tare da ɓata lokaci ba, suka shiga private gen. Na Mister Mai Kyau. kana Bayan shafe wasu mintoci Jirgin Ya ɗaga dasu can sararin samaniya. 🌨️ ✈️🛫












*ABUJA*,*NIGERIA*






Gaba ɗaya Ahalin gidan tsaye suke a ƙaton palo na gidan da alama wani ko wata suke jira.



Kallon tsadadden wrist watch dake ɗauke a tsintsiyar hannun ta tayi, kana cikin jan tsaki ta kalla gaba ɗaya mutanen dake tsai tsai ye a palon cikin harshen Turanci Ta ce

"Haba Momy kuzo mu tafi mana, suna fa ɓata mana time sosai, wannan ko Ƴa-ƴan sarki sai haka, saboda tsaban sun raina mu ne suka tsaya a bedroom, waima uban me suke jira ne, bayan sun san dai daga yau kuma yanzu ba ƙara dawowa gidan nan zamuyi ba.?"


Gaba ɗaya maganar da take yi tana yinsa ne cikin Harshen Turanci tana surkawa da Spanish sannan kuma cikin masifa.



Kallon ɗiyarta ta Hajiya Rafi'at tayi kana cikin kwantar da murya take faɗin

"Haba Nainarh ki ɗan ƙara jiransu mana, kin san fa, Yara ne, wata ƙila basu kammala shiryawa bane shiyasa."




Wani dogon tsaki taja kana cike da Bala'i Ta ce

"Oh my God, Momy a kullum ke kike ƙara goya wa Yaran nan baya, shiyasa suke abin da suka ga dama, fisabilillah Tun yaushe muke tsaye anan muna jiran Yaran nan, amma tsaban sun Raina mu shi ne sukaƙi fitowa, to Wallahi, Ba tsayawa zanyi jiran su ba, ni kunga Tafiya ta."



Tayi maganar tana jan ɗan ƙaramin akwatin ta Tayi waje.


Cike da tsantsan mamaki take bin ƴar uwan nata da kallo tsaban mamaki tama kasa magana, tasan cewa Nainarh masifaffiya ce, na nunawa a television, amma bata taɓa imagine rashin mutunci nata harya kai ta kalla tsaban idon mahaifiyarta ta ma ta masifa ba, da sauri Ita ma taja ɗan ƙaramin akwatin ta tabi bayan ƴar uwan nata cikin sauri sauri.





"Nainarh, Nainarh.! Nailah..."


Gaba ɗaya Twin's ɗin nata waɗanda suka fita suka barta tsaye take ƙwalawa kira, amma babu wacca ta juyo a cikin su, har suka fice daga palon.

Ajiyar zuciya ta sauke na ɓacin rai sannan ta koma ta zauna a saman sofa tana sauke Huci.



Ya mutsa Beauty face nata tayi sannan ta sauke kyawawan idanunta akan mahaifiyar tasu, sai da ta kyara after dress nata dake a hannunta kana ta ce


"Oh Momy! gaba ɗaya Yaranki sun Raina ki fa obaa, shiyasa na ƙosa 'BUDDY' ya dawo daga ƙasar Rasha domin ya koya musu sense, danna fahimci notukan kwakwalensu sun kwance gaba ɗaya."



Tayi maganar cikin harshen Jamus tana Yarfe hannu irin maganar ma wahalar fita take ma ta.



Cike da tsaban takaici Hajiya Rafi'at ta kalla Ɗiyarta ta mai kimanin shekaru goma sha huɗu a duniya, bakinta na furta.

"Kinga xixi idan baki rufe min wannan wawawran bakin naki ba, sai na huce gaba ɗaya takaicin da Yaran nawa suka cusa min akan ki fa."







___*💋 SARAUNIYAR KYAU 💋*_________ƚαƙυɳ ϝαɾƙσ__________________________________________________________💥👑𝑻𝒉𝒆 𝑮𝒍𝒂𝒎 𝐐𝐮𝐞𝐞𝐧👑💥____________________𝑩𝒚:𝑻𝒉𝒆 𝑵𝒂𝒊𝒏𝒂𝒓𝒉 𝑲𝒅____𝑲𝒉𝒂𝒅𝒆𝒆𝒋𝒂𝒓𝒕𝒉.  𝑺𝒂𝒃𝒊'𝒖.  𝒀𝒂𝒉𝒚𝒂𝒉🤙







Page *89&90*




Waro Manyan idanunta waje Tayi cike da Tashin Hankali Tana ƙara Ya mutsa Beauty face nata Ta ce.

"Amma fa gaskiya Momy akwai ki da kwafsi wasu lokutan amma idan ba haka ba. Nida nake Brush a kalla sau Biyar a Rana, shi ne zaki kirani da Mai wawawran Baki?, Haba Momy gaskiya kinyi ƙarya anan fa, eheee..."

Tayi maganar wannan karon cikin harshen Spanish Tana buɗewa mahaifiyar ta ta duka Bakinta alamar taga dai baya warin da ta faɗa. 🤭🏃




Tashi Hajiya Rafi'at tayi zata kaima ma ta duka.
Lura da hakan da xixi tayi ne Yasa ta kwasa da gudu, tana faɗin

"Ahhh lallai ma Momyn nan, kawai sai na bari ki dake ni. Bayan kuma gaskiya nake faɗa chabb."

Qwafa kawai Hajiya Rafi'at taja tana faɗin
"Au a haka zaki fita kai babu ko hula?, sannan kuma baki saka after dress ɗin ba."

Sai da takai bakin ƙofar palon sannan ta juyo ta kalla mahaifiyar tasu tana bata amsa da cewa
"Momy zufa akeyi bazan iya ba, Allah kuwa domin jina nake Like a Ruwan zafi saboda tsaban zufan da nakeji."





A hankali ta tura ƙofar bedroom ɗin ta shiga, batayi ko tunanin sallama ba.

"Sister Leesat, Sister Leesat..."

Sai faman kwalawa Yayarta ta kira take, amma taji shiru, ƙarisa shiga ainihin bedroom na ɗakin tayi, can saman bed ta hangota sai faman min shari take saukewa bacci ya yi daɗi.
Cike da tsananin mamaki ta tsaya tana kallon Yayarta ta.





Da sauri ta ƙarisa wajen gadon, daƙewa tayi iya ƙarfin ta ta ɗaka ma ta duka, a gadon baya, aikuwa a firgice ta tashi zaune tana ya mutsa fuska, sai dai bata ce komai ba.





Dariyar mugunta tayi kana cikin dariyar tana riƙe waist ta ce

"Ke Sis Leesat sarkin bacci, sai ki tashi tun ɗazu su Momy suke palo suna jiran mu, ko dai kin manta wurin da zamuje ne?."





Qara ya mutsa Beauty face nata tayi sannan cikin murya irin na wanda bai watsake ba ta ce.

"Kuje kawai domin ni babu inda zani tunda basu tuna damu ba tsayin shekaru ɗai-ɗai har shida sai yau."





"Ke Sis Leesat hala dai kinyi hauka ne?, ko kin manta da cewa muna barin Gidan nan ba sake dawowa zamuyi ba?."



Jin haka yasa Haleesat saukowa daga saman mattress ɗin tana faɗin


"Ina sane, kawai dai banyi tunanin yau ne zamu koma ba."

Tana faɗin haka tayi hanyar bathroom sannan ta shige ciki, fuskarta ta wanko sannan ta fito ta nufa wardrobe ta buɗe ta ciro wani ƙaramin scarf ta yafa, kana ta juyo tana kallon Lailah laɓɓanta na furta "Muje ko."




Kallon ta Lailah tayi tunda ga sama har ƙasa, sanye take cikin Arabian gown c.green mai adon flowers coffee color, sai kuma scarf da ta yafa a gefan kafaɗarta fuskar ta ko make-up babu.



"Oh kina nufin wai a haka zaki tafi ko mene?."


Ganin zata Raina ma ta wayo ne. Yasa Haleesat ta nufa hanyar fita tana faɗin "Idan kin gama sai ki zo mu tafi."

Da sauri ita ma Lailah ɗin tabi bayanta sannan suka fita a tare suka sauko Down can tsakiyar palon suka hango Momyn tsaye, ita kaɗai sai faman duba agogon dake daure a hannunta take yi.





.
Qari sawa wurin ta suka yi sannan gaba ɗaya ba tare da furta komai ba, suka fice daga palon.
Suka ƙarisa parking lot na gidan, gaba ɗaya suka shiga motoci hadda su Nainarh kana suka Bar gidan.





Wuraren ƙarfe diyu da Rabi na Rana, suka ƙarisa katafaren filin saukar jirgin sama dake a garin Abuja Mallakar Alhaji Abubakar Sameer Lamiɗo (Mister Mai Kyau).










*MAI KYAU INTERNATIONAL AIRPORT*








A hankali take taka ƙafafunta dake sanye cikin glitter stilettos shoe sky purple.
Yayin da take jinta cikin farin ciki mara misaltuwa, sai faman ƙarewa airport ɗin da yake mallakin mahaifinta kallo take yi, a zahiri zaka yi tunanin kyau da tsari da kuma yanayin yadda mutane suke gudanar da harkokin gaban su cikin tsari take kallo.





Amma kuma a baɗiri ba haka bane, kawai tana imagine ne zuwa yanzu ya Ƴan uwanta zasu kasance Especially ma, Abokiyar faɗarta Lailah da suka shafe tsawon shekaru ɗai-ɗai har shida, basu haɗu ko sunyi waya da juna ba. Tayi kewar Nigeria sosai, hadda ma mutanen cikin ta.





Juyawa tayi tana kallon mahaifin ta Abin ƙaunar ta kana ta ce
"Dad wai kuwa kana tunanin yadda su Lailah zasu kasance yanzu kuwa?, nasan dai dole ta ƙara tsayi da girma kamar yadda nima na ƙara ko?."😅








Murmushi Alhaji Abubakar Mai Kyau, Ya yi kana Yace

"Kina so kisan yadda gaba ɗaya Ƴan uwanki harda Lailah suka koma ko?."


Da sauri ta basa amsa da "E, mana sosai ma kuwa."




"Okay to kalla can wuraren."


A hankali a hankali ta mayar da kyawawan idanunta dake sanye cikin fancy Glass akan wurin da yake nuna ma ta.😎





Can ta hango wasu Family Uwa da Yaranta dukansu sanye cikin shiga kala ɗaya, sai dai kuma wata daga cikin su ita shigarta daban ne da nasu.



Ajiyar zuciya ta sauke Yayin da bugun zuciyarta yake ƙaruwa da kowani taku tayi tana ƙari sawa wurin da suke tsaye, suna kallon su kamar yadda ita ma su ɗin take kallo.




Cak taja ta tsaya a gaban su kamar yadda taga shima Daddyn ta ya tsaya Yana binsu da wani irin kallo. Wanda ta kasa fassara ko wani kala ne, kallon nayi kewar ku ko kuwa Mene?.





Ɗaya bayan ɗaya take binsu da kallo fuskarta dauke da ƙayataccen murmushi, kamar yadda suma nasu fuskokin suke ɗauke da murmushin farin ciki.




Kallon mahaifinta tayi tana murmushi tun kafin tayi wata magana ya jinjina ma ta kai alamar "Eh,"

Domin kuwa yasan kalar tambayar da zata masa Already.


Juyawa ta kuma yi tana kallon su gaba ɗaya wannan karon murmushin dake saman Beauty face nata yafi na baya.





A hankali ta buɗe bakinta sannan cikin wani kalar yanayi ta nuna Budurwar dake tsaye gabanta Ta ce

"Auntie Nainarh ko?."

Jinjina ma ta kai budurwar tayi alamar haka ne, aikuwa da gudu ta ƙarisa tayi hugging nata tightly, tana faɗin

"Oh Auntie Nainarh ta nayi kewar ki obaaa."






Dariya Nainarh tayi sannan tana bata amsa da cewa.
"Nima nayi kewar ki sosai sosai, My Dear."



Sakin Nainarh tayi kana ta juya ga budurwar dake tsaye gefan Nainarh fuskarta wada ce da murmushi ta ce


 "Auntie Nailah ko?."



Ita ma Nailah tana dariya ta ce "Ni ce Nailah ko baki gane ni bane?."



Ta tambaya tana ɗaga ma ta gira, da gudu ta ƙarisa ta rungumo Nailah ɗin tana dariya, sai da suka gaisa kamar dai yadda suka yi da Nainarh, sannan ta saki Nailah ta koma ga ɗayar budurwar wacca take sanye cikin Arabian gown tayi rolling da scarf.






Cak ta tsaya tana kallon budurwar kamar yadda ita ma ɗin, ita take kallo sai dai bata ce ma ta komai ba.




"Oh Auntie na bazaki tunamin sunan ki ba ko?."


Afeefah ta faɗa hakan cike da shgagwaɓa. Wanda ba ƙaramin kyau ya ƙara ma ta ba.






Dariya xixi dake gefanta tayi kana ta ce "Sunanta Sis Leesat fa."



Waro ido waje Afeefah tayi, aikuwa bata jira komai ba, ta Rungumo Haleesat tana faɗin



"Am so sorry My Auntie Haleesat, sam ban gane ki bane fa."






Bayan sun kammala da Haleesat nanma suka yi da Momy sai dai Afeefah batayi hugging ɗin Momyn ba, gaisheta kawai tayi sannan tayi gaba wajen xixi batare da, ta jira Momy ɗin ta amsa ba.

Wanda hakan ba ƙaramin taɓa zuciyar Yaranta Ya yi ba, kawai dai shiru suka yi.


Nan ma gaisawa suka yi da ƙanwar nata xixi cike da farin cikin ganin juna sannan kuma....




Cak Afeefah ta tsaya tana kallon kyakyawan matashiyar budurwar dake tsaye gabanta, wacca ba zata haura shekaru goma sha shida ba a duniya.




Kallon ta take kamar yadda ita ma take kallon ta, a kalla ba'a kasara ba, sun ɗauki tsawon mintuna uku suna kallon juna, suna tariyo komai da ya faru a shekaru shida da suka wuce tamkar Ranar Abin ya faru, tsakanin su.







Ita Afeefah a nata ɓangaren kallon da take yiwa Lailah bana komai bane Fa ce, kallon tsantsan kewar ta da begenta da tayi.


Yayin da ita kuma Lailah a nata ɓangaren take yiwa Afeefah kallon kin canza da yawa kin koma can kina Rayuwar ki, ko kewar mu bakiyi ba, kinyi kyau kin ƙara tsayi girma da komai da komai.





Gaza jurewa Lailah tayi da gudu ta ƙarisa ta rungumo Afeefah a chest ɗin ta tightly tana share qwallar da ya cika ma ta ido faɗi take


"Oh My Angel, Oh My Only One, wato baki damu da concern namu ba, shi yasa tunda kika tafi koda sau ɗaya Bakiyi tunanin kiran mu a waya ba, ko kuma kizo mu ganki ba ko?."



Duk tana maganar ne cikin harshen Turanci tana surkawa da Spanish sannan kuma tana haɗawa da Harshen Jamus domin kuwa duk a tunanin ta Afeefah bata iya Hausa ba yanzu.





Murmushin farin ciki kawai gaba ɗaya mutanen dake wurin suke yi barin ma dai Alhaji Abubakar Mai Kyau.




Murmushi Afeefah tayi bayan sun saki juna sannan ta buɗe baki zata yi magana. Domin kare kanta.


Da sauri Lailah takai fresh hand ɗin ta wanda yake sanye cikin handgloves white color, ta rufe wa Afeefah baki sannan ta ce

"Kar ma kice komai ba. Yanzu ba tukunna, sai a gida yanzu dai mu fara komawa gida sannan ki amsa tuhumomi kala kala."




Dariya suka yi gaba ɗaya sannan gaba ɗayan su suka shiga motoci suka bar airport ɗin tare da Rakiyar escort services.




Mota ɗaya Afeefah da Lailah suka shiga, sai kuma xixi. Yayin da Nainarh da Nailah da kuma Haleesat suka shiga mota guda, sai kuma ɗayar Motar Daddy Alhaji Abubakar Mai Kyau, da kuma Momy Rafi'at suka shiga. Motoci uku ke nan sai kuma motocin escort guda biyu.
Gaba da Bayan su ɗoɗar suke taka titin Abuja City suna fella gudu kamar ba gobe da jibi kai harda ma gata.🌚




___*💋 SARAUNIYAR KYAU 💋*_________ƚαƙυɳ ϝαɾƙσ__________________________________________________________💥👑𝑻𝒉𝒆 𝑮𝒍𝒂𝒎 𝐐𝐮𝐞𝐞𝐧👑💥____________________𝑩𝒚:𝑻𝒉𝒆 𝑵𝒂𝒊𝒏𝒂𝒓𝒉 𝑲𝒅____𝑲𝒉𝒂𝒅𝒆𝒆𝒋𝒂𝒓𝒕𝒉.  𝑺𝒂𝒃𝒊'𝒖.  𝒀𝒂𝒉𝒚𝒂𝒉🤙


☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆
💦𝑳𝒂𝒇𝒂𝒛𝒊 𝑾𝒓𝒊𝒕𝒕𝒆𝒓'𝒔 𝑨𝒔𝒔𝒐𝒄𝒊𝒂𝒕𝒊𝒐𝒏💦🤙

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆



Page *91&92*
_-_Still Free Page fa_-_🥰


**

A cikin mintuna kaɗan suka ƙariso Katafaren Gidan Alhaji Abubakar Mai Kyau. Wanda ya ɗauki tsayin shekaru yana gina abin shi, sai wannan Lokaci ne ya kammala.





Wangale musu haɗaɗɗen gate wanda shikaɗai ma Abin kallo ne a yankin securities suka yi, sannan slowly jerin motocin guda Biyar suka cin na Hancin su cikin ƙaton gidan. Wanda ya gaji da haɗuwa ta kowani ɓangare.



Gaba ɗayan su fitowa suka yi a tare lokacin da securities suka bubbuɗe musu murfin motocin sannan gaba ɗaya suka haɗu wuri ɗaya sai faman ƙarewa gidan kallo suke yi, domin kaf cikin su babu wacca ta taɓa zuwa koda kuwa duba Yanayin gini da tsarin gidan ne, asalin ma basu san da Gidan ba, sai kwana kwana nan.
Gidan ya gama tafiya dasu fi ye da tunanin mai tunani.









A hankali sannan kuma cikin nutsuwa suke tafiya har suka ƙarisa bakin ƙofar palon, sannan kuma wani daga cikin securities na gidan ya danna wasu Lambobi a jikin ƙofar palon, sai ga ƙofar Glass ɗin ta buɗe, gaba ɗayan su, ɗunguma suka yi suka shiga cikin haɗaɗɗen palon. Wanda tsayawa faɗin irin haɗuwar sa ma kawai sai an shafe page's fi ye da kima babu a dadi ba'asani ba.
Domin kuwa gaba ɗaya gidan bama iya palon ba kaɗai ba.
Abin kallo ne amma dai bari mu gani ko lissafo Yanayin tsarin gidan da komai da komai  zai yiwu ko kuwa.💫🌚





Da Farko dai Yanayin tsarin gidan shi ne.

Gidan Babban gida ne. Wanda Yanayin tsarin ginin gidan turawa ne dashi.
Kana shiga cikin gidan abin da zaka fara cin karo da shi a tsakiyar compound na gidan shi ne wani ƙayataccen fountain ma'ana marmaro. Wanda yake feshin ruwa fari kar kar Abin gunin ban sha'awa da burgewa.
Ga wasu flowers da aka ƙawata wurin dasu suka yi ma wannan fountain Zobe.





Daga can gefe daga ɓangaren hannun dama kuwa, wani haɗaɗɗen parking lot ne. Wanda a kalla ba'a kasara ba, sai ya cinye tsala tsalan motoci guda tara masu Rai da motsi.



Gaba ɗaya filin ƙaton gidan a ƙawace Yake da Grass carpet koraye ɓashau dasu, gasu gunin ban sha'awa da ƙayatarwa.




Daga can gefe kuwa ɓangaren hannun hagu wani Katafaren madaidaicin garden ne. Wanda aka zagaye shi da Net white color daga ciki kuwa, zasu wild Animals haɗe da dabbobin gida kyawawa dasu ana kiwa tasu a ciki ne, dabbobin ciki sun haɗa da.



•birds=tsuntsaye masu kyau da ban sha'awa, sai faman karkaɗa wings nasu suke gunin burgewa, da saka nishaɗi, ga mai kallo.🕊️🐦🦜



•dogs=sai kuma karnuka wasu sky Brown dasu irin na Turawa suma sai faman karkaɗa Tail nasu suke gunin burgewa da saka feeling better ga mai kallo .🐕


•squirrel=kurege ne, seagull=tsuntsun seagull ne, peacock=ɗawisu, ostrich=jimina. E.t.c.






Kai idan na tsaya lissafo kalar dabbobin ciki sai mu ƙare labari ba'a gama ba, saboda wajen da Gidan baki ɗaya an ƙawata su ne da gini na musamman wanda ba'a ko'ina ake samun kalar sa ba.




To daga Can gefe kuma na gidan, wani Katafaren swimming pool ne. Wanda Ruwan cikin sa yake sky blue gashi gare gare dashi harda wani madaidaicin Bene, a jiki Wanda Idan mutum ya kammala abin da zai yi a ciki zai kama su ya fito daga can jikin swimming pool ɗin, dai still harda wurin da mutum zai dan na idan yanaso Ruwan swimming ɗin Yayi dumi Idan kuma cold Yake so tohm.😎
Daga waje kuma bakin swimming pool ɗin, ga wasu haɗaɗɗun kujerun hutawa da aka ƙawata gefan swimming pool ɗin dasu.




*Again*
Daga wani ɓangare na gidan kuma still wani ƙayataccen Katafaren Garden ne, na hutawa. Wanda cikin sa aka ƙawata da bishiyu kamar na.
•Apple=tufa, Banana=Ayaba, grapes=innabi, pear=gwaiba, pineapple=abarba,
•gasunan dai Taura, kwakwa, magwaro da sauran su.





Can gefe kuma still a cikin garden ɗin wasu kujeru da seesaw na Lilo ne, a jere gunin burgewa.
Gaba ɗaya ƙasar wurin grass carpet ne garden ɗin ya haɗu obaa.



Kai masu karatu bafa zaku fahimci abin da nake nufi ba, saboda ginin gidan ya haɗu sosai, daga can gefe kuma filin wasan ni ne ƙato mai girman gaske.



Daga Asalin Gidan kuwa gini ne mai hawa uku, kana ƙari sawa Bakin ƙofar palon. Wanda yasha fenti fari mai shaining kalar wannan Farin mai ɗaukar Hankali da burgewa.



Daga ɓangaren dama wani haɗaɗden glass staircases ne. Wanda Idan mutum Ya Bishi kai tsaye zai sadaka da wani Arnen part na musamman. Wanda Yasha kayan duniya a hawa na Biyu. Wanda shi ne ɓangaren Abdulmaleek na musamman da aka gina masa.



Sai kuma ɓangaren hagu shima dai Glass staircases ne waɗanda Idan mutum yabi kai tsaye zai sadaka da Wani part shima a hawa na uku. Wanda shi kuma Yake a matsayin ɓangaren Alhaji Abubakar Mai Kyau.




Sai kuma Idan aka dawo ga tsakiyar ginin kuma, wajen bakin ƙofar palon ita kanta ƙofar ma Abin kallo ce, domin kuwa ta glass ce, irin wannan ɗin glass.  Wanda na ciki ne kawai zai hango na waje Yayin da shi kuma na waje bazai hango na ciki ba.




Sannan kuma ita kanta Door ɗin, sai an danna wasu special numbers sannan zata buɗe, kana kuma tana amfani da zanen Yatsa wato fingerprint.





Daga cikin palon kuwa aljannar duniya ke nan, palon ya haɗu fi ye da tunanin mai tunani, domin kuwa ƙaton palo ne, Wanda Yaji kayan mo re Rayuwa kala kala, ba abin da babu babu ne kawai babu a ciki.




Daga tsakiyar palon wasu Royal sofa's ne set Biyu, masu Launin sky Milk color Yayin da cushion ɗin su suke coffee and light orange and Ash color.




Komai na palon sky Milk and coffee color ne, hatta curtains ɗin palon sky Milk and coffee color ne.






Qofar palon yana daga Right hand sai ya kasance daga West and North na palon wasu haɗaɗɗun Arnayen staircases ne, wa'inda aka ƙerasu da zallar glass, domin kuwa hatta da handrail na staircases ɗin da kuma step's ɗin duk na glass ne.



Sai dai kuma staircases ɗin dake ɓangaren west Yamma wanda ya kasance twin's ne, ɗaya kai tsaye zai wuce da mutum izuwa part na Abdulmaleek da yake hawa na Biyu.



Yayin da shi kuma ɗayan kai tsaye zai wuce da kai part na Mister Mai Kyau, Alhaji Abubakar dake hawa na uku.



Sai kuma staircases wanda yake ta ɓangaren North Arewa shi kuma kai tsaye zai wuce da mutum hawa na ɗaya wanda shi kuma yake a matsayin part na Momy Rafi'at.




Bedrooms Huɗu ne Manya Manya daga ko wani part na Palon Yayin da akwai ƙaton kitchen wanda shima yasha kayan Mo re Rayuwar duniya ba'a magana, sai kuma Dining Room shima wanda yake wada ce da glass chairs guda goma sha biyu jere.






*Kai masu karatu ✍🏻 Alƙalamin Nainarh Kd fa, Ya yi kaɗan wajen rubuto da bayyano muku kyau da tsari irin na Gidan Mister Mai Kyau, sai dai kawai kuyi imagine yadda Gidan mutumin Da ya kasance kaf duniya da ƙasar an san da zaman sa, kuyi hasashen Yadda Living Home nasa wanda Iyalansa suke ciki, zai kasance ina architectures ne?,  ina ga ku zaku iya fahimtar yadda tsarin ginin gidan yake,☺️ Saboda Aikin kune Ni dai Nayi iyaka abin da zan iya a Bayani 🤓 saboda haka Nayi nan.*🏃🏃







**
Gaba ɗayan su zama su kayi a Royal sofa's dake zagaye da palon, nan suka shiga firan duniya a tsakanin Afeefah da ƴan uwanta domin kuwa Alhaji Abubakar Mai Kyau. Tuni Ya yi gaba part nasa domin Ya basu damar surutun yadda ya kamata.

Ita ma Momy Rafi'at tabi sa, saiya kasance iyakar Nainarh, Nailah, Haleesat, Lailah, xixi ne, a palon sai kuma Afeefah wacca suka sakata a tsakiya sai faman fira suke yi. Abun nasu gunin ban sha'awa da ƙayatarwa game da tsananin Burgewa.🥰






Lailah gaba ɗaya tabi ta nanu ƙewa Afeefah domin kuwa duk inda tayi ita ma tana nan, har dariya su Nailah Suke ma ta amma ita ba Ruwanta.




Xixi ce sarkin Iyayi da surutu, ta gyara zaman ta saman 1sieter sannan ta kalla Afeefah cikin Iyayi da Yanga irin na Young Lady mai ji da tashen balaga.


Tana Yarfe hannu Ta ce


"Oh Sis feeefat baki bamu labarin Abroad ba, kin san ba ko'ina Momy take Bari muje ba Especially, ma ƙasar France Wanda shi ne Burina nayi karatu a can idan na kammala secondary school da nakeyi."





Dariya Afeefah tayi Sannan tana amsa ma ta

"Menene kuma wani feefat?, Afeefah nake ba wani feefat nan. Ƙasar france kuma Labiba ma ta ce na gaisheki da kyau."



Dariyar murna ita ma xixi tayi kana cike da zaƙuwa ta ce
"Dan Allah Sis feefat da gaske kike, oh my God nayi kewar Labiba da ƙasar faransa obaa."




Ke baki ji ba ko?, nace wannan feefat yabar kan laɓɓanki, domin Afeefah nake kuma karki ƙara cemin wani Sis ehe. Iya Afeefah ma ya isa."




Cewar Afeefah ɗin cike da nata salon bala'in.


Ya mutsa Beauty face nata tayi cike da Yanga ta ce
"Oh Sis feefat..."


Sai kuma da sauri ta Rufe baki. "Oh na manta Sis Afeefah ni na ɗauka ma keɗin wayayyi yace. Ashe ba haka bane yanzu Menene aibin kiranki da Sis feefat?, naga shi ne normal suna na zamani ko?."



"Oho dai ke kika sani kuma?." cewar Afeefah tana dariya, dama da gangar tayi.








**
Da Dare misalin ƙarfe bakwai da Hamsin.

A hankali ta turo ƙofar bathroom ta fito sanye cikin bathrobe coffee color, jikin ta na ɗugar Ruwa.
Sam bata lura da mutum saman bed ba, don haka gaban mirror ta ƙarisa sannan ta janyo swivel chair ta zauna kana ta shafa lotion kaɗan, tayi light make-up sai dai bata saka powder ba.





Closet ta nufa ta ciro kalar tufafin da zaka saka, kana ta shirya cikin sleeping dress, dogon wando purple and vest ita ma purple color. sannan ta saka hula ita ma purple color, kana ta dawo ta nufa ƙofa zata fita Bayan ta saka hijjab sky purple iya gwiwar ta.






"Afeefah.!
            My only.."


Taji muryar Lailah tana kiran ta ɗan juyowa tayi, aikuwa ta hangota baje saman bed tana dariya ta ce

"Ina ne kuma zakije da wannan Daren haka?."


Murmushi Afeefah tayi tana faɗin"Oh Allah, Lailat ke ce yaushe kika shigo bedroom nawa ban sani ba?."



"Tun lokacin da kika shiga bathroom fa."



Lailah ta bata amsa, ɗan waro Manyan idanunta tayi sannan ta gyara tsayuwarta tana riƙe ƙofar bedroom ɗin ta ce

"Okay wato dai kin gannn.."


Tun kafin ta ƙarisa Lailah tayi saurin cewa

"A'a Wallahi. Rufe idanuna nayi, ni wacece haka, da zanka ƴar uwata?."



Tayi maganar tana dirowa daga saman mattress ɗin.



Ajiyar zuciya Afeefah ta sauke "Zo ki rakani wurin Daddy kinji?."



Dariya Lailah tayi sannan ta ce "Okay babu damuwa muje."




Fita suka yi a tare sannan suka nufa twin's staircases suka bi wanda zai sa dasu da part na Mister Mai Kyau.







"Ke Lailah.
Ke Lailah.! ina zakuje da Daren nan?."

Da sauri suka juyo jin muryar Momy Rafi'at tana magana, tsaye take daga tsakiyar palon sanye cikin sleeping dress kamar yadda ta saba tayi Rolling kanta da mayafi.





Washe baki Lailah tayi tana bawa mahaifiyar ta ta amsa da faɗin

"Momy Sister Afeefah zan raka wurin Daddyn za ta masa Good Night ne."



"Ba zakuje ba."


Momy Rafi'at ta faɗa hakan kai tsaye.



Gaba ɗaya da mamaki suka tsaya suna kallonta.


"Because of what, Momy kinga Halin naki ko?, akan me zaki ce baza muje ba, Bayan kuma na faɗa miki cewa Afeefah ce zata je tayima Daddy Good Night?."







Cewar Lailah ita ma kanta tsaye.
"Saboda na isa daku, nace baza kuje ba, idan kuma ban isa daku ba, ku shiga na gani."



Ita ma Momy Rafi'at ta faɗa a zafafe, Lailah zata kuma magana da sauri Afeefah ta Riƙo hannunta sannan suka sauko Downstairs.



Kallon Momy Rafi'at tayi cike da girmamawa ta ce

"Shikenan tunda kince ba zamuje ba. Please Idan kin shiga ki faɗawa Daddyn Shalelen sa tana zai gashe sa, kinji our Momy?."


Afeefah tana gama faɗin haka ta kuma jan hannun Lailah suka yi Hanyar bedroom.





Da masifa Momy Rafi'at take faɗin "Ke Afeefah, How dare you, wato har Ni ce zaki bani saƙo?, keɗin wacece?, har Yaushe kika girma?."




Juyowa Afeefah tayi ta ma ta murmushin Tura haushi sannan ta Rufo ƙofar  garamm. Kakeji.




Galala Momy Rafi'at ta bita da kallo saboda tsaban takaici tama kasa magana, qwafa taja sannan tayi gaba.






Jingina tayi da Bayan ƙofar tana sauke ajiyar zuciya na ɓacin rai.


"Please My only, wani lokacin fa sai kin dinga haƙuri da Halin Momyn domin akwai ta da shiga shara babu shanu."




Cewar Lailah Tana kwaɓe fuska, cike da Rashin enjoying na halin mahaifiyar tasu.

Murmushi Afeefah tayi tana faɗin "Babu komai wata ƙila shi Daddyn bacci Yake yi shi yasa ta faɗa, haka kuma nasan Halin Daddyn bayaso ana Tashin sa idan yana bacci."



Kallon bazaki fahimta ba, Lailah tayi ma ta kana ta nufa gefan bed ta zauna bata ce komai ba.



_-_Har Yanzu cikin free page's muke SARAUNIYAR KYAU_-_


___*💋 SARAUNIYAR KYAU 💋*_________ƚαƙυɳ ϝαɾƙσ__________________________________________________________💥👑𝑻𝒉𝒆 𝑮𝒍𝒂𝒎 𝐐𝐮𝐞𝐞𝐧👑💥____________________𝑩𝒚:𝑻𝒉𝒆 𝑵𝒂𝒊𝒏𝒂𝒓𝒉 𝑲𝒅____𝑲𝒉𝒂𝒅𝒆𝒆𝒋𝒂𝒓𝒕𝒉.  𝑺𝒂𝒃𝒊'𝒖.  𝒀𝒂𝒉𝒚𝒂𝒉🤙






Page *93&94*
_-_Free Page's Still_-_




"Yauwa dama fa akwai tambayar da nakeso nayi miki tun ɗazu."

Cewar Afeefah cikin murmushi ita ma tana zama kusa da Lailah ɗin.



"Okay Inajin ki Sister."



"Oh My Lailat, yanzu taya ya zanji daɗin magana dake bayan kuma kin ɗaure fuska faɗa min?."


Murmushi Lailah tayi tana faɗin"Tofa ."


Washe fuska tayi "Hakan Ya yi miki?."


Murmushin ita ma Afeefah tayi "Haba hakan yafi ae, nima zanfi enjoying na fira dake fuska sake ko?.

Dama tambayar ita ce, naji kun iya Harshen Jamus da kuma Spanish sosai sosai. Ta yaya aka yi kuka iya?, Please?."






Dariya Lailah tayi sannan ta ce "Ai bama iya harshen Jamus da Spanish muka iya ba, hadda ma yaren Eritrea mun iya, Labarin da tsayi fa."


"Okay Inajin ki ake."




Afeefah tayi maganar tana gyara zama fuskarta a washe.
Lailah ta ci gaba da cewa abin da ya faru, shi ne duk ƙasar da kukaje muma sai Momy ta nemo mana Malamin dazai dinga koya mana yaren da akeyi a ƙasar ace warta gwara muma mu'iya kar sai kun dawo Naija, ku baku iya Hausa sosai ba, muma kuma bamu iya Harshen da kukeji ba, wannan shi ne a taƙaice."


 Murmushin mamakin halin Momy Rafi'at kawai Afeefah take yi sannan a fili ta ce "Hakan ya yi fah gaskiya."












***
Washe gari ma haka suka tashi gidan a cike da Ƴan Uwa da Abokan arziƙi na nesa da kusa waɗanda suka zo domin ganin Afeefah da mahaifinta da suka dawo Nigeria Bayan shafe tsawon shekaru shida a Abroad.






Rayuwa ta ci gaba da tafiyar ma Afeefah tare da ƴn uwanta musamman ma Lailah da ba ƙaramin shaquwa ce ta fara shiga tsakanin su ba.




Yayin da a kullum cikin waya da Ƴar uwanta Zaynerb wacca take karatu a ƙasar Amsterdam suke yi babu dare ba rana.

Rayuwar ta ci gaba da lulawa cike farin ciki.
Watannin su Afeefah uku da dawowa Nigeria, tuni mahaifin su Mister Mai Kyau. Ya saka su a University ita da Lailah wacca Ita ma ta kammala secondary school nata, sun fara zuwa University tare. Yayin da suke karantar course ɗaya dukkansu wato karatun Likitanci ɓangaren na musamman surgery.







Sosai suka mayar da hankulansu akan karatun su, babu wasa. Yayin da tsakanin Afeefah da Momy Rafi'at babu wacca take shiga harkar wata, domin kuwa gaisuwa ce kawai take haɗasu, ita ma daga Afeefah ta gaisheta bata tsayawa saita amsa take warin wurin, sai dai idan taga Daddyn ta a wurin ne, tofa nan ne zata tsaya ta amsa daga haka kuma babu abin da yake ƙara shiga tsakanin su.





Wata Ranar Jumma'a wacca ta kasance watanni su Afeefah biyar da dawowa Nigeria.







Ranar suna zazzaune gaba ɗaya a palon gidan Yayin da Afeefah da Lailah suke karatu cikin wani ƙaton book irin na Likitoci daga can gefe kusa da Bene. sunyi kaca kaca da littafai a yayin suna karatun.



Sai kuma xixi dake hakim ce saman kujera tana kallon wani Nigeria Nollywood Drama, 'Recap Beyond The Veil, a plasma tv dake palon, can gefe kuma saman 3sieter Nainarh ce kwance tana chatting a wayarta. Yayin da Nailah take can kitchen tana Faman soya soye, dama ita ɗin akwai son kwaɗayi, ita kuma Haleesat sarkin bacci tana bedroom nata tana kwasar bacci.








Jin ana faman knocking na ƙofar palo ne babu tsayawa ko dakata wa ne, Yasa Nainarh ta kalla xixi dake faman ƙyakyata dariya tana cewa

"Ke xixi jeki buɗe ƙofar can, ƙarar ta yana  disturbing nawa da yawa."

Tashi xixi tayi tana faman ƙunƙuni ta nufa ƙofar, domin tasan ubanta zata ci idan bataje ta buɗe ba domin kuwa Nainarh babu wasa.



Buɗe ƙofar tayi cike da masifa ta hayayyaƙo zatayi ma koma waye a ƙofar, sai kuma bakin ya mutu, ganin wacca take tsaye gaban ƙofar janye da akwati.




Ware duka muryar ta tayi cike da tsananin mamaki Ta ce "Sister zaynerb ke ce?, kodai gizo kike min me kike yi a Nigeria, kodai har kin kammala karatun ne?."



Jin abinda take faɗa ne yasa ka daga Afeefah da Lailah wa'inda suke karatu harda Nainarh mai chatting dukkan su suka mimmiƙe tsaye a tare suka nufa ƙofar gudu gudu, Lailah na faɗin "Ke xixi banason hauka fa. Menene kuma zai kawo Sis Zaynerb Naija mutumiyar da take Amsterdam karatu?."







"Wallahi Siister zaynerb ce ai na santa a pictures, kuma ma idan baki yadda ba gata nan ki ganta, face to face." Cewar xixi tana basu hanya.




Gaba ɗaya da tsananin mamaki suke kallon kyakyawar budurwar dake tsaye bakin ƙofar palon gabanta akwatu wajen guda uku.




Saboda tsaban mamaki ma sun kasa magana sai kalloncta kawai da suke yi kamar sun sama tv, duk da cewa a lokacin basu san Zaynerb a fili ba, sai'a pictures amma sun gane ta.




"Auntie Zaynerb ɗina, kece kuwa me kike yi a Nigeria bayan kuma a ƙasar Amsterdam kike karatu, kodai kin sama hutu ne ki-ka-zo mana?."  Cewar Afeefah Tana kallon Zaynerb ɗin.





A maimakon Zaynerb ta bawa Afeefah amsar tambayoyin da take jero ma ta, a'a da gudu ta ƙarisa shigewa palon, sannan tayo hugging Afeefah ɗin tightly a chest nata, tana fashewa da matsanancin kuka kamar ranta zai fita, ganin haka yasa gaba ɗayan su jikin su ya yi sanyi laqwas.





A hankali Afeefah ta riƙo hannun Yayarta ta suka nufa cikin Palon. Bayan ta sake ta, ganin haka yasa Lailah da xixi suka ɗauko akwati nan Zaynerb da ta bari a wajen, suka shiga dasu cikin palon.



Gaba ɗaya zama suka yi akan Royal sofa's dake palon, sannan Lailah ta ce "Sis Zaynerb lafiya kuwa, naga kamar bakya cikin hayyacinki sosai..."

"To sarkin surutu sai ki bari ta huta ko, daga zuwa ko zama baki bari ta kammala yi ba, harkin sako ta gaba da tambayoyi haka?."

Cewar Nailah da take ƙari sawa palon hannunta riƙe da plate ciki shaƙare da kayan maƙulashe, ƙari sawa palon tayi Sannan ta miƙawa Zaynerb ɗin plate dake hannunta tana faɗin
"Gashi sister zaynerb fara cin abinci tukun na koma menene, daga baya a yi maganar."




Karɓa Zaynerb tayi sannan cikin muryar ta mai daɗin sauraro ta ce da Nailah ɗin
"Thanks to You."

Cikin Baturiyar Muryar ta, murmushi Nailah ta ma ta sannan ta koma ta zauna tana amsa ma ta da "Never mind enjoy."



Sai da Zaynerb ta kammala cin abinci da Nailah ta bata tas. Tasha Ruwa ta huta sannan ta kalla Ƴan uwanta duka da suka sakata gaba suna kallo kamar sun sama TV.



Ta ce
"Barkan ku dai ƴan uwa na."

"Kema barkan ki dai."


Suka haɗa haɗa baki wajen faɗin hakan, amma banda Afeefah wacca ta tsurawa Yayarta nata ido tana kallo.



A hankali ta buɗe bakinta ta ce "Auntie Zaynerb tawa, zuwa Yanzu nasan kin dawo nutsuwar ki please zaki iya faɗa mana abin da yake faruwa, kona samu na sama nutsuwa."



Ajiyar zuciya Zaynerb ta sauke tana tariyo duka abin da ya faru da ita tun daga ranar da ta taka ƙafafunta a ƙasar Amsterdam har izuwa rana mai kamar ta ranar da suke ciki.


Sannan ta kallesu gaba ɗaya kana cikin tsananin rawar murya gunin ban Tausayi take faɗin

"SOYAYYA CE. Sanadi Soyayya ce Sanadin duka Halin dana tsinci kaina, soyayya ta wahalar dani fi ye da tunanin mai tunani, soyayya tasa na tsana kaina, soyayya tasa na fita hayyacina, soyayya tasa a shekarar Farko na karatuna na tashi da c.o. Soyayya ce da kuma Namiji sun wahalar da zuciyata fi ye da kima. Dan Allah Ƴan uwana karku min tambayar dalili na dawowa, domin kuwa banason na ƙara tunawa dashi a rayuwata, saboda na tsane sa, na tsana duk wata alaqar da zata ƙara haɗani dashi. Ya Yaudareni da sunan soyayya Ya.. Ya..."


Kasa ƙari sawa tayi saboda kukan daya zo ma ta nanta shiga yi abin gunin ban tausayi, zafi zuciyarta take ma ta, ji take ba za ta iya jurewa ba, kwara ta mutu kawai ta huta.







Tsuru tsuru suka yi suna kallonta gaba ɗaya jikin su ya yi mugun sanyi ba kaɗan ba. Jin abin da Zaynerb take faɗi, sai aka rasa wanda zai rarrasheta, a cikin su, domin kuwa ba ƙaramin sanyi jikin su ya yi ba da wannan sarƙaƙaƙƙen labarin.




Lailah ce tayi ƙarfin halin cewa "Sis Zaynerb kinji kiyi shiru, ki dena kuka, domin kuwa babu amfani, ba dai kun rabu ba, to ni banga amfanin sakama rai damuwa ba, ina ce dai yanzu kin tsane sa, bakya ko son ganin sa ko?."



Da sauri Zaynerb ta ɗaga ma ta kai alamar hakane.



Sauke ajiyar zuciya xixi tayi sannan ta ce
"Sis zaynerb please zaki iya faɗa min sunan sa?, kuma musulmi ne ko kuma ba musulmi bane?."


"Amma dai xixi kinji kunya wallahi, yanzu ana so a lallaɓata ta manta dashi gaba ɗaya a cikin rayuwar ta, amma ke ta sunan saurayin da ya wahalar mana da ƙanwa kike ko?. Da bakin ki a gurin kamar na Angela ko?."


Cewar Nainarh cike da Bala'i.
Turo ƙaramin bakinta tayi cike da shagwaɓa ta ce.




"Allah sis Nainarh akwai ki da tsaban ƙarya, amma in banda haka, ta'ina kika ga ɗan ƙarami madaidaicin siririn bakina ja dashi ya miki kala dana Angela ne, in banda tsaban ƙarya da rashin kula da faɗin gaskiya irin na ki, haba dai Sis Nainarh a duba lamarin fa chabb, wai bakin Angela."




Tashi Nainarh tayi zata kaima ma ta mugun bugu, lura da hakan da xixi tayi ne. Yasa ta miƙe da gudu ta shige jikin Zaynerb tana faɗin "Please Sis Zaynerb ki ce ceni, zata kashe ma Daddyn mu Auta shikenan fa idan ta dakeni sai nayi ciwo, wayyo ni Zeenaru..."🤣😅




Biyo ta Nainarh tayi tana faɗin "Yau ko cikin, cikin Zaynerb zaki koma saina dake ki, badai baki da kunya ba?."

Qara shigewa jikin Zaynerb xixi tayi faɗi take "Please, please sis Zaynerb ki taimake ni zata dukeni fa."




Dariya kawai Zaynerb take yi na drama ɗin xixi da Nainarh, ta fahimci Yarinyar akwai tsokana, sai tsaban tsoro, ita kuma Nainarh babu haƙuri, riƙe girma.😕






Tun daga wannan ranar Rayuwa ta dawowa Afeefah sabuwa fil, don gata ga Yayarta Zaynerb wuri guda. Rayuwa suke cike da farin ciki da ƙaunar juna mara misaltuwa.




Watan Zaynerb ɗaya da dawowa Nigeria tuni ta koma school sai dai kuma ta canza course, domin kuwa koda mahaifin su Alhaji Abubakar Mai Kyau, Bayan Yaji dalilin ta na dawowa Nigeria Ya fahimce ta domin kuwa Yasan Menene so. To koda ya tambaye ta abin da zata karanta kai tsaye ta ce masa "LAW" take so ta karanta yanzu.

Aikuwa nan ba tare da wani ɓata lokaci ba, aka samar ma ta da Admission anan wata katafariyar University dake birnin tarayya, na Yaran Manya ta fara karatun ta cikin kwanciyar hankali ba tare da tunanin komai ba, domin kuwa makarantar ma da take yi na mata zalla ne, sannan kuma maganar soyayya ta a jeta a gefe






_-_Masu karatu nan gaba zamu san ainihin abin da da ya faru da Zaynerb a ƙasar Amsterdam Insha Allah, kudai kawai ku biyo wannan Ƙayataccen Labarin  *💋💋SARAUNIYAR KYAU💋💋* Much Love_-_😘






           

___*💋 SARAUNIYAR KYAU 💋*_________ƚαƙυɳ ϝαɾƙσ_________________________________________________💥👑𝑻𝒉𝒆 𝑮𝒍𝒂𝒎 𝐐𝐮𝐞𝐞𝐧👑💥____________________𝑩𝒚:𝑻𝒉𝒆 𝑵𝒂𝒊𝒏𝒂𝒓𝒉 𝑲𝒅_

Page *95&96*


_-_Uhum nayi maganar payment banga ana layi ba🥺. Kar fa ku manta Discount ɗin na sati ɗaya ne kacal 👌. Kwana ɗaya ya wuce, saura kwanaki shida kacal. Ku gaggauta biya fa, kafin Discount ya ƙare. 🥳🥳



***
Rayuwa ta ci gaba tafiya ta kowani ɓangare cikin nasara da kuma farin ciki sakanni suna tafiya Yayin da mintoci suke wuce wa, suma awanni suzo su wuce, haka ma kwanaki wucewa suke su suna bawa satikai damar suma suzo su wuce kamar ba'ayi ba Yayin da watanni suke tafiya suma shekaru suzo su wuce.




To haka ma Ahalin Alhaji Abubakar Sameer Lamiɗo _-_Mister Mai Kyau_-_ suka kasance Bayan shekaru biyu da dawowar Zaynerb Nigeria shima Abdulmaleek ya kammala karatun sa a ƙasar Rasha ya zama cikakken gynaecologist _-_Likitan mata_-_


         






*NAMADI-INT£RN@TIONAL-AIRPORT-ABUJA*




Tafiya yake cikin nutsuwa irin na sa. Tafiya kalar na Manyan Gayu masuji da Kyau ga hutu da jindaɗin duniya daɗi da kari kuma ga Naira.



Dogo ne shi sosai, kuma fari wanda farin sa yake haɗe da gauranyen ja, kyakyawa ne shi, first class domin kuwa duk wani qualities na kyau yana dasu, ga hutu da jindaɗi da yake ciki tsundum ta ko'ina.




Kyakyawar fuskar sa zagaye take da stubble beard. Wanda ba ƙaramin kyau madaidaicin stubble hair da ya tara a kyakyawar fuskar sa ta ƙara masa ba.


Yayin da sumar kansa mai tarin yawa gashi baƙi sidiq ya ma ta wani kalar gyara na musamman in stylishly sai shaining take.





Sanye yake cikin T-shirt black color mai gajeren hannu, wacca ta zazzago masa har kusan gwiwa, gefe da gefen Rigar Yanayin style na wurin sai Ya yi kamar a tsage.
Kalar wannan Riga dai wacca Manyan Gayu wa'inda suka san darajar Gayu da wanka suke sakawa, daga ƙasa ƙasan Rigar, gaba da baya Anyi wani Rubutu da farin kala cikin harshen farasanci, sai kuma trouser jeans pencil Black color wandon ba ƙaramin kamasa Ya yi ba, amma haka yake takawa ba ruwan sa, sai kuma wani farin Boots dake sanye cikin ƙafafunsa irin Takalmin nan wanda ake Ya yi sannan, kafin kaganshi a ƙafar wani tofa ƙaton aiki ne, saboda tsadan Takalmin sai wanda Ya isa ko kuma aka san da zaman sa ko uban sa a ƙasar sannan...



Ga Wani Arnen sunglasses da ya qwafa a kyakyawar fuskar sa. Ya Rufe fararen idanun sa dashi, masu shaining, ga diamond wristwatch dake ɗaure a tsintsiyar hannun sa na hagu, sai zuba shaining yake yi. Neck nasa kuwa sanye yake da wasu siraran sarƙoƙi wajen guda uku na zallar pearl, Yayin da Left ear nasa yake maƙale da wani ƙaramin earring na azurfa.
Ya haɗu sosai fi ye da tunanin duk wani mai tunani Abdulmaleek Abubakar Mai Kyau, ke nan kyakyawan matashin saurayi mai ji da ƙuruciya ga Naira. Maleek ya kasance mutum ne shi wanda a koda yaushe kyakyawar fuskar sa take wadace da ƙayataccen murmushi Mai bayyana dimples, sai dai kuma karkuji na ce fuskar sa koda yaushe tana wadace da ƙayataccen murmushi kuyi tunanin shiɗin mutum mai sauƙi ne. Eh yana da sauƙin kansa dai daishi sai dai bashi da haƙuri ko kaɗan ga zuciya akwai sa zafin zuciya kamar me.🙃


Gashi kuma ba mutum bane mai ɗaukar Raini sam ko kaɗan baya ɗaukar rashin respect, domin kuwa shi mutum ne mai masifar son a girmama sa.☺️






Tafiya Yake yi cikin Katafaren airport Wanda yake cike da mutane ta kowani part suna harkokin gaban su.
Janye yake da wata kyakyawar madaidaiciyar akwati. Yayin da gaba ɗaya mutanen wajen suka mayar da gaba ɗaya hankulan su akan sa, suna kallon kyau, iya kyau haɗuwa iya kar haɗuwa, kyakyawan saurayi gaba ɗaya mazan wurin ji suke ina ma, ina ma, ina ma ace sune wannan haɗaɗɗen Guy haka. Wanda takowani ɓangare ya gama haɗuwa ba ƙarya.😎



Yayin da su kuwa Ƴan matan wurin gaba ɗaya ji suke ina ma, ina ma, ina ma ace wannan haɗaɗɗen boyfriend ko kallon su ya yi da sunan soyayya, habba ji suke da sunfi kowa sa'a a duniya wannan haɗaɗɗen saurayi haka gashi kyau ga ƙiran gayu.🤓



_-_✍🏻(N)(a)(i)(n)(a)(r)(h) ((K)(d)📚📲_-_





Cikin harabar Airport ya fito cikin taku irin na cikakkun gayu, sannan ya fara tafiya yana ƙari sawa wurin Ahalin sa dake can tsaye sai faman waige waigen ta inda zai fito suke da alama basu gane sa ba.



Qari sawa wurin su Ya yi kana ya tsaya cak yana kallon su, kamar yadda suma shi suke kallo, murmushi Ya yi sannan yakai fresh hand nasa ya zare sunglasses dake manne da fuskar sa.

Qura masa ido Afeefah dake tsaye tana fuskantar sa ta yi tana kallo ita dai iya tunanin ta, hmmm bata gane ko waye wannan haɗaɗɗen matashin saurayi dake tsaye gabanta ba, ita dai a iya tunanin ta wani baturen ne, yazo Nigeria domin kuwa kalar fatar sa bata yi shiƙe dana ƴan Nigeria ba.







Ganin dai budurwar dake tsaye gaban sa, bata nuna wani Reacted ba, na ganin sa, da alama har yanzu bata gane ko shi waye ba yasa.



Ya fara magana cikin muryar sa mai daɗin sauraro
"Afeefah ce wannan a gaba na ko?."

Ya yi maganar yana nuna ta, Washe baki Afeefah tayi tana amsa masa da faɗin

"Eh, ita ce."

Murmushi Ya yi kana ya kuma matsawa kusa da Ɗayar budurwar dake tsaye kusa da Afeefah ɗin, ya nuna ta sannan Yace
"Lailah ce Ƴar rigimammamiya ce wannan da gani."


Ita ma washe baki tayi sannan ta amsa masa da
"Eh, Buddy ni ce wallahi."



Murmushin ya kuma kana ya nuna Ɗayar matashiyar budurwar dake kusa da Lailah ba tare da ya ƙarisa inda take ba Yace
"Zinaru ce wannan, wato wannan Yarinyar Ƴar gayu, da iyayi🤣😅
Kece ko amma ana kiran ki da xixi.


Ku kuma waɗannan Twin's masu kama da junan fa?, da kuka zubo min ido kuna kallo Nainarh da Na'ilah ko?."



Maleek ya kuma maganar bayan xixi ta basa amsa, Murmushi Nailah tayi kana ita ma cikin daddaɗar muryar ta ta ce "Buddy ke nan. Ashe baka manta da Ƴan ƙannin naka da halayen su ba."

Murmushi shima Ya yi kana Ya ce
"Ina sauran suke ne?."


Ya tambaya bayan sun gaisa da Momy Rafi'at da kuma mahaifin sa Alhaji Abubakar Mai Kyau, da suke tsaye gefe sai faman murmushi suke barin ma dai Momy Rafi'at hmmm.




Xixi ce ta basa amsa da faɗin "Sis Zaynerb tanada £xam a school wannan dalilin da ya hanata zuwa tar bar Babban Yayan mu, Yayin da ita kuma Sis Leesat ta tafi Birthday Party na wata Ƴar Yankin mu, ƙawarta."




"Okay aikuwa zasu haɗu na dani tunda sukaƙi zuwa tarba na kuwa."


Cewar Maleek cikin murmushi, ɗunguma suka yi gaba ɗaya kowa ya shishshiga mota suka bar Airport ɗin.





***
Watannin Maleek uku da dawowa Nigeria Ya fara zuwa aiki a katafaren Hospital na gani na faɗa da mahaifin sa Alhaji Abubakar Mai Kyau ya Gina masa na musamman a Birnin Tarayya Abujan.



_-_Sai dai kuma menene kuke ganin zai faru a tunanin ku?._-_




Maimakon Maleek ya mayar da hankalin sa ga aikin sa na cikakken gynaecologist Likitan mata, a'a sai ya saka wasa, domin kuwa yawon zuwa mashaya da kuma yawo da Ƴan mata a tsala tsalan motoci yana kashe musu kuɗaɗe, shiya saka gaba domin ko'a Rasha abin da ya koyo ke nan.




A Ranar da ya fara zuwa aikin ya shiga yima wata mata tiyata, yana tsakiya da Yimata tiyatar aka kirasa a waya domin kuwa bai kashe ba, shikuma bai tsaya tunanin komai ba, ya a je kayan tiyata a gefe ya ɗauki waya, aikuwa Sanadin wannan gangan cin nasa, wannan matar ta sheƙa barzahu.






A lokacin ba ƙaramin tashin hankali Alhaji Abubakar Mai Kyau. Ya shiga ba lokacin da ya sama wannan mummunar labari, sai dai kuma shi Maleek ko'a jikin sa.

Haka Rayuwar ta ci gaba da tafiya yana zuwa aiki sai dai kuma baya tsinana uban komai, domin kuwa duk da cewa ya iya aikin sosai, baya mayar da hankalin sa, Sanadin haka majinyata da yawa sunsha karɓar baƙar wahala a hannun sa, domin baya basu kulawar da ya kamata, sai dai tun daga matar Farko da ta Rasu bai kuma gigin da zaisa wani majinyaci ya mutu a hannun sa ba.



_-_



Sai wata Rana bisa tsautsayi da abin ya kasance, dama ance mutum baya wuce ƙaddarar sa. A Ranar wata budurwa yake yima tiyata, lokacin ma ba kiran sa aka yi a waya ba, kawai dai bisa tsautsayi ne, yana cikin tiyata aka sama wata Ƴar matsala, wannan matsala kuwa ba komai ya haddasa ba, sai wata ƴar na'ura da ya manta bai kunna ta ba, a lokacin dazai fara yima wannan budurwa tiyata, aikuwa Sanadin haka ita ma wannan budurwa ta rasa ranta.



A lokacin ba iyaka Alhaji Abubakar Mai Kyau, ba hatta shi kansa Maleek ba ƙaramin tashin hankali ya shiga ba, na abin da ya faru, gefe guda kuma ga Ahalin Yarinyar da suka ce sam ba zasu Yarda ba, dama tuntuni basuso a kai Yarinyar su hospital ɗin ba.

Ita ce ta takura saboda tana masifar son Maleek sai kuma wannan ƙaddararren al'amari ya kasance.
Ita budurwar mai suna IKRAM ta rasa ranta.




Aikuwa ba tare da wani ɓata lokaci ba, Ahalin Yarinyar nan suka danƙara Abdulmaleek da hospital nasa a kotu.



A wancan lokacin ba ƙaramin tashin Hankali gaba ɗaya Ahalin Mister Mai Kyau, suka shiga ba, na abin da yake faruwa.



A lokacin da kyar da suɗin goshi Alhaji Abubakar Mai Kyau. Ya samu aka bada belin Maleek da hospital nasa domin kuwa suma a Ahalin Yarinyar ba ƙananan mutane bane.






Watannin Maleek Biyu a gida Bayan bada belin sa baya zuwa ko'ina, sannan Alhaji Abubakar Mai Kyau. Ya mayar dashi a ɗaya daga cikin companies nasa dake Abuja ya saka shi a matsayin C.e.o na group of companies duk da cewa ba kasuwanci ya karanta ba.



Aikuwa ko watanni huɗu cikakku ba'a samu da fara aikin sa a companyn ba, aka sama Stock Market Crashed, gaba ɗaya shiyoyin company suka yi ƙasa company ya sama durƙushewa a kasuwanni.🥴


A lokacin ba ƙaramin asara akayi ba, a wannan company domin kuwa gaba ɗaya mutane sun janye shares nasu gaba ɗaya sunbi sun janye  hannun jarinsu na wannan company.



A lokacin faɗin irin tashin hankali da Mister Mai Kyau. Ya shiga ba'a magana, duk da cewa wannan company faɗuwarsa ba yana nufin durƙushewar dukiyar sa ba ne, koda kaɗan ba haka bane, sai dai kuma tattali yanada daɗi ko.


🔥_-_🔥
A mugun fusace Alhaji Abubakar Sameer Lamiɗo, Mister Mai Kyau. Ya fito daga company nasa na ƙera motoci mai suna 'MAI KYAU CARS FACTORY.'


Shiga motar sa Ya yi ko tsayawa jiran Jacob driver bai yi ba. Ya tasa Motar a mugun fusace. Wanda ba komai Ya Janyo fusatar da yake ciki ba, sai Labarin da ya samu akan abin da yake faruwa a company.




A lokacin ikon Allah ne kawai ya kai shi Gidan sa, aikuwa ko parking bai tsaya kammala gyarawa ba, ya turo murfin Motar da ƙafa, a mugun fusace ya fito kai tsaye ya nufa ƙofar palon, aikuwa yaci sa'a a buɗe take, aikuwa a mugun fusacen nan ko sallama babu ya kutsa kansa cikin palon.





Gaba ɗaya Yaran gidan suna zazzaune a katafaren palon gidan da mahaifiyar su.



Nainarh, Nailah, Haleesat, Zaynerb Afeefah, Lailah sai xixi gaba ɗaya suna zaune a saman kujeru Yayin da Shima Abdulmaleek Ya saka su a tsakiya, ga ƙaton board na wasan Chess _-_dara_-_ suna bugawa yana koya musu wasan kafta kutse.♟️♟️




Can gefe kuma Momy Rafi'at ce saman 3sieter tana sarrafa system.




A mugun fusace Alhaji Abubakar Mai Kyau. Ya ƙariso wurin gaba ɗaya babu wanda ya lura dashi a wurin.




Watsawa Maleek takardun hannun sa Ya yi kana cikin tsananin matsanancin ɓacin Rai. Wanda gaba ɗaya Yaran sa kai hadda ma matar sa Momy Rafi'at basusan yana dashi ba, ya fara magana cikin kakkausar murya da zafafan kalmomi.



"Abdulmaleek, Maleek.. Abdulmaleek..."


Sai da ya kira sunan Maleek sau uku cikin kakausar murya sannan Ya ci gaba da cewa

"Na gaji da wannan shashashar ɗabi'ar taka, sai kace dabba wannan menene?, yanzu shima companyn baka barshi ba, sai da kasan yadda kayi ka durƙusar da companyn Bayan abubuwan da ka aikata a baya, kai yanzu ko kunya bakaji Sanadin ka mutane har Biyu sun mutu, kai baka tunanin yadda daraja da kimar Ahalin ka zai kasance ko, sai dai shashanci da rayuwar dabbobi daka sanya a gaba, kai ko tunanin gina Future naka bakayi?. To dama tayaya stupid kamar ka, zai damu da gina ci gaban sa. Bayan kuma ka shigo cikin ƙanƙanin ka mata ka rasa abin da zaka kowa musu sai wannan shashancin wasan dara.."


Gaba ɗaya Alhaji Abubakar Yana maganar ne, cikin tsananin ɓacin rai kalar wanda bai taɓa shiga ciki ba, bayama tauna maganganun da yake faɗi, kawai faɗa yake yi ba tare da tunanin abin da zai faru gaba ba.





Aikuwa shima Maleek cikin zafin zuciya ya miƙe tsaye Yana fuskan tar mahaifin nasu cikin huci da ɗaga murya....Yake Faɗin....




*Kamar yadda na faɗa muku Book 2 is paid, duba da yanzu nake rubuta labarin bawai na kammala bane. Kuɗin ya kasance 500 ne kacal, 👌 Sai dai Akwai Discount ga mutane da suka fara biya daga Yau zuwa nan da Rana ita yau, zasu sama Discount har Naira 200, a maimakon su biya 500, toh 300 kawai zasu bada, amma fa Kamar yadda na faɗa ga mutane da suka fara biya a wannan satin, sati ɗaya ne Discount ɗin, yana wuce Sati ɗaya sai dai ki biya Ɗari Biyar (500).😇 Ga waɗanda suka shirya Payment Now, zaku biya ta wannan details ɗin ne.....*






*The Phone Number*
*08081129487*
*The Acct Number*
*8081129487*
*The Bank Name*
*Palmpay Bank*
*The Acct Name*
*Khadeejarth Sabi'u Yahyah*


*Saiku turo evidence of payment ta wannan lamba (08081129487), sai na jiku mutane na.*🥳



~Karku bari a baku labari fa🤩~

~*SARAUNIYAR KYAU*~🔥🔥Takun Tsakiya_-_
*Iya kuɗin ki iya shagalin ki Hajiya*

   
                  
______





 
___*💋 SARAUNIYAR KYAU 💋*_________ƚαƙυɳ ϝαɾƙσ_


Writer
Khadeejarth Sabi'u Yahyah /+2348081129487/

Page *97&98*



"Daddy.!
    Daddy!!
Daddy!!!

Ka tsaya a'iya matsayinka na mahaifi a gareni, kar kayi yunƙurin shiga abin da bai shafe ka ba, domin kuwa wannan Rayuwa Ta ce dan haka ka barni nayi ta yadda naga dama, kuma da kake maganar sanadina mutane biyu suka rasa rayukansu, kai wani kalar mutum ne, da baisan tsautsayi ba. Sanadin tsautsayi komai ya faru, kullum cikin dana sani nake na zama na gynaecologist a matsayina na cikakken likitan mata wanda na kwashe tsawon shekaru ina karatu na kasa taimakon ta na kasa taimakon IKRAM, a kullum da ko yaushe cikin tuna kalamanta na ƙarshe a gareni nake, a lokacin faɗi take."  
''Dr. Ka taimaka ka cece rayuwata a gurin surgery nan ina tsoro na mutu Burina bai cika ba, please Dr. Save my life please pleased Dr. I'm beg you.''

''Kullum irin wannan maganar nata su suke min kuwa cikin kunne cikin dare su hanani bacci, da rana kuma su hana ni sukuni duka sanadin tsautsayi da kuma ƙaddara komai ya faru..."





Tunda Maleek ya fara magana babu abin da Alhaji Abubakar. Yake yi sai faman gyaɗa kai Maleek ɗin har yakai ƙarshen maganganun nasa sannan Yace.


"It's okay Wato ma haka zancen yake, wato dai har rogonka tayi ka ceci Rayuwar ta, amma saboda kaiɗin cikakken idiot ne, sai dai babu komai daga yau kaɗauka cewa ni Alhaji Abubakar Sameer Lamiɗo bani ba kai, ka ɗauka cewa baka taɓa mahaifi ba a
Duniya..."🥵



Katse sa Maleek Ya yi cikin tafi Raf-Raf sannan yana faɗin
"Wow, Amazing, please Mister Mai Kyau, da gaske kake, oh Lord so nice, it's amazingly fa. Yaudai wannan Ranar da nake jira tazo, bani babu wannan tsangwama da takurawa yanzu zanyi Rayuwata Normalcy irin na cikakkun mutane, oh my pride..."



Habba nan aka fara cacar baki tsakanin Alhaji Abubakar Mai Kyau da Ɗan nasa Maleek kowa cikin mugun zafin rai dana zuciya yake furta duk wani abu da yazo bakinsa.



Gaba ɗaya Yaran in banda kuka babu abin da suke yi ganin wannan tashin Hankalin da yake faruwa cikin gidan su.


Afeefah kuwa wacca kwata kwata ta tsana hashin hankali ko ya ya yake jikinta har wani rawa yake yi, na tashin hankali, Yayin da ita kuwa Momy Rafi'at baza'a iya faɗin ga irin yanayin halin da take ciki ba, amma dai kana kallon ta kasan ta fita hayyacinta. Yayin da ita kuma Zaynerb ta ƙarisa da gudu ta riƙe ƙafar mahaifin nasu tana basa haƙuri jin irin zafafan kalmomin da suke fitowa daga bakin sa.





Da ƙarfin gaske Maleek ya buga hannun sa saman glass center table dake tsakiyar palon, aikuwa nan jini ya fara tsatata kamar ambuɗe famfo bai damu da jinin dake zuba a hannun sa ba, saboda tsananin fusatar da yake ciki ya nufa staircases wanda kai tsaye zai sadashi da part nasa, ya fara taka steps cikin sauri sauri in twin's.

Gaba ɗaya suka bisa da kallon mamaki. Yayin da Alhaji Abubakar ya koma saman sofa ya zauna daɓasd, gaba ɗaya jikin su ya yi mugun sanyi an rasa mai magana.






     

*After some minutes*
    
    
    
Sai ga shi yana saukowa daga saman benen janye da akwati harya ƙarisa saukowa ko tsayawa bai yi ba, ya nufa ƙofar palon zai fita.🤕



Aikuwa da gudu ƙanin nasa su duka harda Momy Rafi'at suka bisa suna kiran sunan sa.


A guje Nainarh ta ƙarisa wurin sa ta riƙo akwatin hannun sa sannan cikin kuka take faɗin

"Buddy, ka taimaka karka tafi, please karabu da wannan unwarranted and unwanted tunanin, please Buddy na roƙeka karka tafi, ka duba Halin da Daddyn da Momyn dama mu ƙannin ka gaba ɗaya zamu shiga idan ka tafi pleased..."

Ganin Ya yi shiru baice komai bane yasa su duka suka ƙarisa wurin suka yi kamar yadda ita ma Nainarh tayi cikin kuka suke basa haƙuri, hadda Momy Rafi'at a kan karya tafi.

Abin dai babu daɗin faɗa gunin ban Tausayi gaba ɗaya suke _-_Lamarin it's heart touch obaaaaa_-_🔥





Kallon mahaifiyar su Maleek Ya yi sannan Yace

"Momy ki dena kuka kinji, ki dena zubar da hawayenki a kan wannan ƙaramin tashin hankalin, ba dai gida bane, to zan barmasa gidan sa."




Cikin kuka xixi ta katse shi da cewa "Haba Buddy ka taimaka ka tsaya, indai kana so Momy ta dena zubar da Hawayen ta..."



Haɗuwa suka yi gaba ɗaya suna basa haƙuri, sai dai duk da irin haƙurin da Suke basa, haka ya tsallake suna ji suna gani yasa ƙafa yabar gidan ko waywayensu bayyi ba, wayyo Allah.😭





Gaba ɗaya ranar cikin ɓaƙin ciki da wani kalar yanayi gunin ban tausayi suka wuni, jigum jigum a palon kaf cikin su babu wanda ya iya tashi tun tafiyar Maleek har yanzu da aka kwashe kusan awanni biyu da tafiyar sa.




Tun ɗazu wayar tarho dake tsakiyar palon take ƙara, sai dai saboda yanayin da suke ciki, an rasa wanda zai je domin ɗauka.

Lailah da ƙarar wayar ya isheta ta miƙe cike da masifa ta nufa wayar ta kara a kunne cike da Bala'i ta buɗe baki zata yi magana.


Kawai sai gani suka yi wayar tarhon dake hannunta ta faɗi ƙasa. Yayin da ita kuma ta zube ƙasan kamar wacca ta fita hayyacinta.


Da gudu gaba ɗaya suka mimmiƙe sukai kanta suna tambayar ta abin da aka faɗa ma ta, ganin yadda take faman Hawaye.




A hankali ta buɗe  bakinta cikin sarƙaƙƙiyar murya irin na wanda tasha kuka ta ƙoshi Ta ce


"Hajiya Zuwairiya ce Allah ya yi ma ta Rasuwa, shi ne aka kira aka faɗa yanzu."




Cak gaba ɗaya suka tsaya tamkar waɗanda wutan lantarki taja, saboda tsananin kiɗima da tashin hankalin da maganar ya ƙara musu akan wanda suke ciki.


Qarar faɗin mutum da suka ji a ta bayan su ne, yasa gaba ɗaya suka juya harda Alhaji Abubakar wanda ba'a gane yanayin da yake ciki ba.

Afeefah ce kwance ta faɗi a sume ashe ciwon ta ne ya tashi.🤧






*Tashin sense*

A taƙaicen taƙai tawa dai faɗi ko rubuta irin tashin hankalin da gaba ɗaya Ahalin Alhaji Sameer Lamiɗo suka shiga, bazai yiwu ba, saboda yanayin ba daɗi ko kaɗan, domin kuwa Afeefah ciwon tane ya tashi kuma yazo da matsala highly.






Domin kuwa sai da ta kwashe tsawon watanni huɗu a hospital na ƙasar Hindi tana jinya, kamar ba za ta Rayuwa ba, domin har an cire rai da ita.

Sannan aka samu ta dawo normal nata Sannan kuma Rayuwa ta ci gaba da tafiya babu daɗi domin kuwa duk irin neman da aka yiwa Maleek ƙasa, ƙasa ba'a ganshi ba, haka suka haƙura aka ci gaba da gunadanar da Rayuwar.





____*_💅

Nainarh Abubakar Mai Kyau.

Nainarh, ta kasance kyakyawar mace ce ita, son kowa ƙin mara sa'a, domin kuwa kyakyawa ce sosai, ita ɗin ta kasance mace ce mara haƙuri gashi bata ɗaukar raini ko kaɗan gata akwai son girma kamar me, gata tanada wani hali na riƙe abu arai ko ya ya yake, sai dai kuma duk da rashin mutuncinta tanason Ƴan uwanta sosai kamar yadda suma suke ƙaunar ta.


Yayin da ita kuma Biyuninta Nailah Abubakar Mai Kyau.
Nailah, ta kasance mace mai yawan sanyin hali da kuma maida abu ba abu ba, sannan kuma ita ma ɗin kyakyawar mace ce mai ji da ƙuruciya ga kyau da Naira.
Nailah ta kasance mace mai matuƙar tsoron tsiya, domin kuwa ko kyanwa tsoranta take yi, kamar mutuwar ta sannan ita ma ɗin macecce mai matuƙar ƙaunar Ƴan uwanta da Ahalinta.


Haleesat Abubakar Mai Kyau.
Haleesat, ita ma ta kasance miskilar gaske ce na bugawa a mujalla, domin kuwa komai miskilanci ka idan ka haɗu da ita, sai ka sara ma ta
To shigarta University ne ta rage miskilancin kaɗan, amma fah kaɗan ɗin. Sanadin haɗuwarta da Manyan mata masu fariya da dukiyar iyayen su, idonta ya kuma buɗewa sosai sosai. Sanadin shigarta University kuma a can tayi ƙawaye har uku domin kuwa a baya ko ƙawa ɗaya bata da ita.
Ƙawayen da tayi a University su ne, Zuree, Feenah sai kuma Jenny waɗanda Sanadin haɗuwarta dasu ne ma ta fara zuwa mashaya, amma fah a ɓoye, sannan kuma Haleesat ta kasance cikakkiyar kyakyawar mace ce ita ta nunawa a tv, gata ta iya ɗaukar wanka na manyan yara gata tana masifar kama da wannan shahararriyar Jarumar indian nan wannan kyakyawar  wato 'Krithi Shetty'.



Zaynerb Abubakar Mai Kyau.
Zaynerb, ta kasance cikakkiyar mace ce mai ji da kyau na musamman gata wayayyiyar mace ce ta nunawa sa'a, sannan akwai ta da shiga shara babu shanu wasu lokutan, domin kuwa akwai ta da surutu babu laifi sannan kuma tanada kirki dai dai ita, gata akwai wayau domin idonta a buɗe yake kar, gata tana masifar ƙaunar ƙanwar ta Afeefah, kamar Rayuwar ta domin kuwa Afeefah ita ce Raunin Zaynerb a komai, sai dai kuma ita ma tanada wani hali ɗaya shi ne, akwaita da mugun zuciya kamar me, sannan kuma bata iya so ba, domin idan zata so abu son gaba ɗaaya take masa, haka ma idan zataƙi abu tofa ƙin gaba ɗaya take masa, ita haka take a rayuwar ta, Zaynerb ta kasance suna masifar kama da wannan Turkish actress Cemre Baysel, Yanayin gashin nasu ma kala ɗaya suna kama obaaaaa, highly highly.🤩

Sannan, Kuma...!
*Afeefah Abubakar Mai Kyau.*
Afeefah *SARAUNIYAR KYAU* ke nan kyakyawa ce wacca idan aka ce kyau. Tofa ana zuwa kanta an rufe ƙofa. 💋


Afeefah ta kasance cikakkiyar mace mai son mutane kamar me, domin kuwa kowa nata ne, dukiyar mahaifin ta bai rufe ma ta ido ba sam ko kaɗan, gata akwai kirki kamar mene.
Afeefah ta kasance tana masifar ƙaunar Labari na *SOYAYYA* dama duk wani Abu daya shafi soyayya.
A lura da kyau Labarin soyayya nace Afeefah take ƙauna bawai soyayyar ba, domin kuwa bata taɓa soyayya ba, ita ɗin haka take, gata akwai ta da matuƙar kaifin basira da tunani sannan kuma Afeefah tana ƙaunar Ƴan uwanta sosai sosai obaaaaa.
Sannan kuma akwai ta da wani kyakyawan hali wanda shi ne kana ma ta Abu yanzu tofa yanzun zata manta, ita sam bata da riƙo ko kaɗan, sai dai kuma fah. A Lura kyau Afeefah ta kasance mace ce wacca tasan haƙin gayu obaaaaa.
Sannan duk da kirkinta bata ɗaukar raini ko kaɗan bata da girman kai amma fah akwai class highly highly. Sannan kuma ta kasance tana ƙaunar ayi surprisingly nata a komai. 💞



Lailah Abubakar Mai Kyau.
Lailah, ta kasance mace ce ita mai matuƙar tsafta da kyankyami kamar me, sannan kuma akwai ta da mugun rashin mutunci ba kaɗan ba, dan ma haɗuwarta da Afeefah ne ta raƙe wasu abubuwan.
Sannan kuma ita Lailah bata damu da harkar kowa ba, sai dai nata sannan kuma ita ba mace bace wacca ta iya gulma, sam bata iya gulma ko ƙarya ba, kai tsaye take harkar ta.
Amma fah akwai ɗan karan surutu, sannan kuma ita Lailah sam bata soyayya, ace warta ma soyayya ɓata lokaci ne kawai da shirme, amma fah a fahimtar ta ke nan.😂
Lailah tanason Afeefah sosai fi ye da son da take yi ma kanta. *_-_kunji masuyi Don Allah _-_*💫💫
Sannan Ita ma dai tana da kirkinta dai dai ita sai dai hali kawai irin na ɗan Adam.


Zinaru Abubakar Mai Kyau.
Xixi ke nan ƴar kwalisa da iya ado ga tsafta kamar me, gata ita ma akwai ɗan banzan iya yi da son asan da zamanta,  ta wani ɓangaren halinta yazo ɗaya dana Zaynerb wajen iya shiga shara babu shanu, gata faɗi ba'a tambayeki ba ke nan.
Akwai surutun tsiya sannan Ita ma irin Afeefah ce, ta wani fannin domin tanason mutane babu laifi sannan kuma Abin hannunta sam baya rufe ma ta ido eheee.🌝🌚



*Wannan ke nan, Kaɗan daga cikin Halayen Ƴaƴan Mister Mai Kyau...*💅






___***

To Haka dai Rayuwar nasu ta ci gaba da lulawa ba wani farin ciki gunin ban Tausayi ta kowani ɓangare watanni tara da barin Maleek Gida aka yi bikin Nainarh da Nailah.


Yayin da ita Nainarh ta Aura wani haifaffen ƙasar Eritrea. Wanda haɗuwar social media ce, harta kaisu ga Aure.
Duk da dai kafin Auren sai da aka sha fama da Momy Rafi'at domin taƙi yadda ne.
To daga baya haka ta haƙura aka yi ba yadda ta iya.
Yayin da ita ma Nailah ta Aura wani ɗan ƙasa Nigeria haifaffen Nasarawa State, mazaunin Lagos duk da Ita ma da farko Alhaji Abubakar Mai Kyau.
Yaso ya bada matsala, ace war sa bai amince da mijin da Nailah ɗin zata aura ba, saboda Yanayin sana'ar sa, amma daga baya haka komai ya wuce aka sha shagalin biki.






  - _-

Rayuwa ta ci gaba da gangarawa ta kowani ɓangare yau daɗi gobe babu, dama haka abin yake ba kullum ake cikin enjoying komai ba.

Shekarun Maleek Biyu da Barin Gida ba ko wai waye.
A lokacin ne kuma xixi ta kammala secondary school nata. Sannan ta ce ita a ƙasar france wurin Uncle Yunus take so ta ci gaba da karatunta, a can tare da Labiba ɗiyar sa wacca suke sa'anni ace war ta gaba ɗaya Gidan nasu babu daɗi tun Barin Buddy nasu.
To koda ta sama mahaifin su Alhaji Abubakar, da maganar da farko ƙin Yarda Ya yi saboda a tunanin sa Sanadin karatu a Abroad Babban ɗan sa Abdulmaleek Tarbiyar sa ta sama matsala.
Ita ma zaynerb kuma sanadin haka ta sama matsalar soyayya. Wanda nan gaba zamuji ainihin abin da ya faru da ita acan Amsterdam ɗin.






A lokacin ba ƙaramin wani hali xixi ta shiga ba, dalilin hana ta zuwa faransa domin ɗaura karatun ta na degree.
A lokacin har rashin Lafiyar ƙarya ta kwanta dan dai kawai a barta ta tafi, aikuwa daga baya Alhaji Abubakar Mai Kyau, da yaga babu sarki sai Allah, haka ya barta ta tattare ya nata ya nata ta koma faransa. Wajen Uncle Yunus ta fara sabuwar Rayuwa. Yayin da gefe guda ita da ɗiyar Uncle Yunus Labiba suka fara karatun anan wata hamshaƙiyar jami'a na ƙasar faransa.


Yayinda suke karantar course ɗaya.


Nigeria kuwa Rayuwar Ahalin Alhaji Abubakar Mai Kyau, ta ci gaba da tafiya salin alin. Yayin da aka kwashe tsawon shekaru uku hadda watanni da Maleek Yabar gida sai wannan karon ya dawo...💃💃




*Masu karatu idan nace zan ci gaba da tafiya cikin ainihin abin da ya faru a baya*.
To gaskiya ina ga har mu kammala wannan novel baza'a dawo cikin ainihin Labarin ba, saboda haka anyi min afuwa mu koma cikin ainihin Labari.
Yanzu dai kunji ainihin dalilin abin da Ya saka Maleek ya bar Gidan su tsawon shekaru uku da watanni sai wannan Lokaci ya dawo.
Kuma kunji dalilin da yasa Momy Rafi'at bata ƙaunar su Afeefah, saboda wai mahaifiyar su ta Aure mata miji.
Sannan kuma munji wani abu daga cikin ainihin dalilin da yasa Haleesat ta fara zuwa mashaya, wato Sanadin haɗuwarta dasu Zuree da Feenah da kuma Jenny.
Sannan again munji ainihin dalilin da Yasa Zaynerb ta dawo Nigeria.
Bayan kuma a Amsterdam ta fara karatu, wato dai Sanadin soyayya, kamar yadda nayi Alƙawari nan gaba zamu ji ainihin abin da ya faru da Zaynerb a can ƙasar NETH Babban Birnin ƙasar wato Amsterdam.
Haka ma Lailah munji wasu daga cikin silly. 😜 dalilanta da suka saka ta tsani soyayya, har ma da maza😕
Sannan kuma munji irin ciwon dake damun Jarumar mu.
To shin akwai maganin wannan ciwo nata ko kuma babu kudai kawai ku Biyo alƙalamin Nainarh Kd domin jin wannan ƙayataccen Novel Na musamman Wanda sai da a tsaya a Ta ce sannan kuma a tsaya aka zuba Basira wajen Taho muku dashi Labari mai Cike da sinqi sinqin chakwakiya_🤩_Cin Amana🤣_Yaudara😏_Zamba cikin Aminci🤕_Ban dariya obaaaaaaaaaa😆_Rikita Rikita🥴_____
Nishaɗantarwa🤪_Game da wa'azantarwa 😜_Buri💫_Fansa_makirci🤮_Hargitsi🤥_____
Game da Tsananin Zazzafar Soyayya Mai Ban sha'awa da Burgewa, da kuma tsindima mutum cikin Shauƙi ba tare da Da ya shirya ba. Labari Mai suna SARAUNIYAR KYAU 💋💋💋__THE GLAM QUEEN 👑💕🌹

 💓💓ƚԋҽ ϝαʂԋισɳ ʂԋσɯ.💓💓







*PR£S£NT*
                 *Ci gaban Labari*




*_-_Masu Karatu, Ina Fatan Dai Baku Manta Ta Wajajen Da Muka Tsaya Ba, To Yanzu Dai Zamu Ɗaura_-_*







*بسم الله الرحمن الرحيم*




Bayan sun shishshiga ƙayataccen palon, Gaba ɗayan su iyayen suka zazzauna saman Royal sofa's dake zagaye da ƙaton palon, Yayin da su kuma gaba ɗaya yaran suka zazzauna a ƙasa tsakiyar palon harda Maleek wanda kansa yake ƙasa cike da yasa nin komai da ya faru baya.




Yayin da ita kuma Afeefah wacca har zuwa lokacin bata farfaɗo ba, aka ɗaurata saman doguwar kujera 3sieter Yayin da Momy Rafi'at ta zauna kusa da ita tana ma ta firfita sama sama.


Gaba ɗaya palon shiru ya ɗauka tamkar babu wani hallita mai rai ciki, sai da aka shafe kusan mintuna goma, a haka sannan Uncle Yusuf da ya kasance mutum ne shi mai bala'in sauƙin kai da kuma ƙaunar peaceble.


Gyaran murya Ya yi sannan ya kuma buɗewa da addu'a bayan ya kammala suka shafa sannan ya kalla Maleek cike da kulawa ya fara magana kamar haka.





"Yanzu kai Maleek ka dawo gida Bayan ɗaukar tsawon shekaru baka nan, shin zaka iya faɗa mana duniyar da kaje ko kuma wurin da ka tafiya ko waiwaye babu?."




Gaba ɗaya mutanen palon ne suka mayar da hankulan su kan Maleek suna jira suji amsar da zai bawa Uncle Yusuf da ya yi masa tambayar.
Shikuwa Alhaji Abubakar, babu abin da yake sai faman sauke huci kurum yana kallon Ɗiyarsa dake kwance bata ko numfashi.



Shiru Maleek ya yi tsawon mintuna uku sannan ya yi gyaran murya yana gyara Yanayin zaman sa ya fara magana cikin murya wacca dai Yanayin ta sai as low.


"Da Farko dai Bayan na Bar Gidan nan kai tsaye Airport na wuce nabi jirgin ƙasar Rasha, to koda na isa Rasha Ban tsaya komai ba. Kai tsaye na fara aiki a Babban asibiti dake ƙasar tsawon shekara ɗaya, sannan kuma na fahimci wani abu, cewar shi baturen mutum kwata kwata bashi da alƙawari.
Wato abin dai da ya faru shi ne, ina gabatar da aiki cikin gaskiya a ƙasar cikin Babban asibitin ƙasar, sai wata Rana ɗaya daga cikin manyan likitocin asibitin da yake ba musulmi bane, shiyasa bama wani jituwa dashi, daɗi da kari kuma na fahimci baya da wani hali na KIRKI..."




Katse sa Alhaji Abubakar Ya yi cikin sauri
"Okay ke nan kai ɗin wani Halin kirki ne dakai. Yanzu kaine har zaka ce wani bashi da Halin kirki?."

Da sauri Uncle Yusuf ya katse Alhaji Abubakar cikin sanyin murya Yace
"Ina ga da kayi shiru mun gama jin abin da yake so ya faɗa mana."

Alhaji Abubakar bai tsaya sauraron maganar da Uncle Yusuf Yake ba, Ya kalla Maleek cikin daka tsawa yace "Yanzu me kake nufi?, kana nufin kace ka dawo Gidan nan ne, to a matsayin wane ke nan?, ni dai nasan bani da wani Yaro na miji duka Yarana mata ne,  kuma ina ƙaunar su duka."

Jin abin da mahaifin nasu yake faɗa ne yasa gaba ɗaya yaran nasa suka ɗago suna kallon sa, cike da tsananin tashin hankali.



Cike da nadama Maleek ya rarrafa kusa da mahaifin nasu ya kamo ƙafafunsa yana basa haƙuri kamar zayyi hauka cike da tsantsan nadama.
Yayin da shi kuma Alhaji Abubakar yake ture shi cikin tsananin fushi yana tuna duka abubuwan da suka faru baya tamkar yaune suke faruwa.






Maleek faɗi Yake yi "Please Daddy ka yafe min, wallahi na tuba, bazan kuma ba, domin nayi nadama highly."

Gaba ɗaya yaran kuka suke bama kamar Zaynerb da Nailah har wani shiɗewa suke yi saboda tsananin tashin hankali, tsoro suke karfa tarihi ya kuma maimaita kansa.





Ajiyar zuciya Alhaji Abubakar Mai Kyau, ya sauke a karo na babu a dadi yana kallon gaba ɗaya Yaran sa yadda suke kuka, shi uba ne dole yaji babu daɗi da ƙari ƙin yafewa Maleek da Ya yi bawai yana nufin baya ƙaunar sa bane ko kuma wani abun, kawai dai yanaso ya fahimci shin da gaske ya tuba ko kuwa.





Kallon Maleek dake hawaye kamar zararre, Uncle Yusuf Ya yi sannan ya masa umarni da ya koma ya zauna.




Komawa Maleek Ya yi kusa da ƙafafun mahaifin sa ya zauna dan Bala'i.🥵



Kallon gaba ɗaya mutanen palon Uncle Yusuf ya kuma yi sannan ya ƙara mayar da kallon sa, kan Alhaji Abubakar yana masa kallon nutsuwa, daga ƙarshe dai ya sauke idanun sa a kan Maleek.





Kiran sunan Abdulmaleek Ya yi har sau uku, yana amsawa sannan ya ci gaba da cewa.


"Yanzu dai mu a je maganar wurin da kaje gefe, a gaskiya gaba ɗaya Ahali ba muji daɗin barin Gida da kayi ba, a kan wani dalili wanda bai kai ya kawo ba, sannan kuma yanzu da ka dawo, ka dawo ka ci gaba da Rayuwa da Ahalin ka ne, ko kuwa dai akwai wani nufi a tare dakai?."





Uncle Yusuf Ya yi masa tambayar yana kallon Maleek ɗinda ya yi shiru kansa a ƙasa.





"Please Uncle ayi min haƙuri na duka abin da ya faru baya, sharrin shaiɗan ne sannan kuma na dawo gida ne saboda na ci gaba da Rayuwa cikin Ahalina kamar kowa."



 
Wani ƙayataccen murmushi Mister Mai Kyau. Ya yi amma fah na iya gefan fuska, domin kuwa idan ba ƙura masa ido kayi ba, to ba zaka fahimci Ya yi murmushin ba, daga yadda fuskar sa take a tsume, wani sanyi yaji cikin zuciyar sa jin abin da Maleek yake faɗa, a fili kuwa kallon Maleek dake kallon sa. Ya yi sannan yana faɗin


"Indai kanaso na manta komai da ya faru a baya, na bari ka dawo ka ci gaba da Rayuwa cikin mu. Tofa sai dai idan ka amince zaka fito da matar Aure. Idan kuma baka da budurwa ka zaɓa cikin Ƴan matan dangi, duk wacca tayi maka."



Duk wannan maganar Alhaji Abubakar ya yima Maleek ne cikin kakkausar murya da kuma bada zaɓi.




Murmushin enjoying da kalaman ɗan uwan nasa Uncle Yusuf Ya yi sannan Ya mayar da kallon sa a kan Maleek ɗin.


"Ka dai ji da kunnen ka, abin da mahaifin ka ya faɗa, saboda haka yanzu zaɓi ya rage naka."


Shima Uncle Yusuf Ya yi maganar cikin gimtse fuska alamar dai babu wasa cikin maganar.



Haka ma gaba ɗaya mutanen palon suka mayar da hankulan su kan sa hadda Momy Rafi'at da tun ganin Yaron nata bata ce komai ba.
Kai harda Afeefah wacca farfaɗowarta ke nan taji zancen Uncle Yusuf a sama, sannan kuma babu wanda ya lura ta farfaɗo domin kuwa bata nuna alama ba.






Ajiyar zuciya Maleek ya sauke yana tariyo gaba ɗaya girlfriend's da ya taɓayi kaf cikin su, baiga wacca suke tare yanzu ba, gaba ɗaya basa tare domin kuwa tunda daɗewa yabar kalar Rayuwar sa ta baya, shi dai yanzu iya tunanin sa baiga macen da zaice ya taɓa ma ta kallon so ba, ko kuma ya ma ta kallon wani abun ban da ƙawance, ɗagowa Ya yi Yana kallon gaba ɗaya mutanen palon, kamar yadda suma shi Suke kallo.

Murmushi Ya yi kaɗan kana ya buɗe muryar yadda gaba ɗaya zasuji yana faɗin

 


"Husnee ce wacca na zaɓa..." 💞💞




Gaba ɗaya palon dariya suka saka ganin yadda Husnee ta ɗago a firgice tana kallon sa hankali tashe.


Uncle Yusuf kuwa babu abin da yake faɗi sai

"Masha Allah dama haka ake so, lamari ya yi daɗi."

Nan kuma palon ya ɗauki hayaniyar murna da jindaɗi.



Sai da suka sama nutsuwa gaba ɗaya suka yi shiru sannan Uncle Yusuf ya kalla Husnee cikin maganar irin na manya yake tambayar ta

"Husnee  Ɗiyata kin amince zaki Aura Yayanki Abdulmaleek kamar yadda shima yace keya zaɓa?."


Kallon jama'ar palon Husnee tayi kamar yadda suma suka zubo ma ta na mujiya suna kallo.😅





Cikin gimtse kyakyawar fuskar ta take faɗin

"Uncle Yusuf a bani mintuna biyar zanje yanzun nan nayi shawara na dawo."




Tayi maganar fuska ba rahama, dariya suka saka baki ɗaya, sannan Uncle Yusuf yace cikin dariyar shima

"Kinji jeki Ɗiyata ki ɗauki iya a dadin lokacin da kike so domin duka naki ne."🥰


Miƙewa tayi sannan ta zagaya ta bayan kujeru ta wuce kai tsaye bedroom ɗin Lailah, ta wuce tana shiga ta rufe ƙofar harda murza key, sannan ta dawo ta ƙarisa can gaban madubi tana kallon kanta.

Cire mayafin da tayi rolling kanta dashi tayi kana ta daka tsalle tana faɗin

 "Yes, Yes, sai ni Husnee, wallahi sai ni Husnee, a gaskiya na cire tuta cikin ma ta niɗin ma mai sa'a ce cikin masu Nasara, inba hakan ba wannan Diamond boyfriend guda kamar Yaya Maleek Yace Yanaso Ya Aureni.
Haba duk inda aka ji maganar Aure ansan da akwai soyayya, Yasin sai ni Husnee, lallai dawowar Buddy Gida ba kowa Ya yi ma amfani ba sai ni, kai dole ma nayi waƙa, oh toni wata kalar waƙa ma, na iya?..."


Tayi maganar tana zama gefan bed cike da matsanancin nishaɗi highly highly,




Murmushi tayi sannan Ta ce "Yeah Wallahi na tuna."💃💃


Buɗe daddaɗar muryar ta Ta yi sannan ta fara Raira waƙa cike da enjoying Mood da take ciki rairawa take yi kamar haka.



"I'm coming home😌 I'm coming home. Tell the world, I'am coming home, 🙂 Let the rain Wash away..☔🌈 All.. the pain of yesterday😥😊 I know my kingdom awaits 💕💕 and... They've forgive my mistake"🤗💝 I'm coming home, I'm coming home Tell the world I'am coming home... { home is not a place it's feeling. }."






Murmushi tayi Bayan ta kai haka a waƙar nata sannan ta ɗauki mayafinta, wannan karon yafashi tayi saman kafaɗarta, sannan ta buɗe ƙofar ta fito bayan ta kuma gimtse kyakyawar fuskar ta.💝



Husnee ta kasance Ɗiyace ta uku wajen Hajiya Jawaheer.
Husnee, kyakyawar matashiyar budurwa ce wankan tarwatsa, doguwa ga hanci, ba zata Haura shekaru ashirin da ɗaya zuwa da biyu ba a duniya, sa'ar su Afeefah ce, ta kammala karatun degree nata anan Babbar University dake Jigawa State ta Karanci fannin Agriculture, Husnee akwai ta da san barkwanci kamar mene, gata akwai kirki da sauƙin kai, sai dai abin da ba'a rasa ba domin kuwa ɗan Adam ajizine. 😸






Komawa tayi ta zauna kusa da su Ƙarama da Mah'eesha saɓanin ɗazun da take kusa da Lailah da kuma Fateemah da Zakiyya.



Sai da ta sauke ajiyar zuciya sannan ta kalla Uncle Yusuf Ta ce
"Eh Uncle na amince nima."

Tayi maganar tana rufe fuska wai kunya.🤓


Gaba ɗaya fuskokin mutanen wurin idan ka kalla zaka fahimci bawai iya farin cikin dake bayyane a fuskar su bane, harda zuciyoyin su ma.

Murmushi Uncle Yusuf Ya yi sannan Yace

"hakan ake so. Yanzu sai a fara tunanin saka rana ko?."


Zuruf Husnee ta ce "Ah ai Uncle ina ga kawai tunda Already na kammala karatu na, a saka nan da one month kawai, kaga Lokacin Ya yi dai dai da lokacin da za'a kuma gasar SARAUNIYAR KYAU matakin ƙasa ko?."


Tayi maganar iya gaskiyar ta kuma har zuciyarta.





Fashewa da dariya gaba ɗaya mutanen palon, suka yi cike da nishaɗi.

Lailah da bata gani bata tanka ba, ta ce

"Oh oh ikon God sai Look. Wato yanzu ke Husnee ko kunya babu kike wannan zance gaban mu ko?."


Tayi maganar cikin dariya, muryar da basu yi tsammanin jinta bane, suka ji tana faɗin
"Oh ke kuma Lailah sarkin surutu zaki ba, My Aunty to be, kunya cikin society ko?."


Cewar Afeefah tana saukowa daga saman doguwar kujerar da aka kwantar da ita.


Murmushi Husnee tayi sannan ta ce "Batta kawai dai dai nake da ita nima ae, ko tayi tunanin zanji kunyar tane?."






Gaba ɗaya dariya suka kuma yi habba daga haka kuma fira ta kuma shiga tsakani cike da nishaɗi.
Shidai Maleek shiru ya yi yana kallon Ahalin nasa gaba ɗaya sun canza sosai. Jinsa yake tamkar wani sabo cikin su, sai yaji yau ya kuma yarda da wannan maganar da ake cewa 'Duk Wanda Yabar gida, Tofa Tabbas Gida Ya barsa'. Home is not a place it's feeling for All people.💞














*KANO*




Wannan karon da tsananin mamaki ya kuma kallon mahaifiyar tasa jin abin da take faɗi, shifa sam kansa ya ɗaure ya kasa fahimtar komai yadda ya kamata.



Murmushi tayi sannan ta ci gaba da cewa

"Umarni nake baka, akan kaje ka nema soyayyar Jiddarh saboda sai da hakan burina na tsawon shekaru fi ye da ashirin zai cika, idan kuma ba haka ba, zan san abin yi."



Murya na ɗan rawa Yace

"Ni nifa ina da wacca nakeso kuma zan Aura, sannan kuma da kike maganar na nema soyayyar jiddarh nifa matsayin ƙanwa na ɗauke ta sannan kuma..."



Katse sa tayi cikin tsananin ɓacin rai sannan cikin tsawa da ɗan ɗaga murya ta fara magana


"Heesham, indai ni ce mahaifiyar da ta haife ka ina baka umarni da kaje ka nema soyayyar wannan yarinya jiddarh, domin sai da hakan Burina zai cika."


Sai kuma ta ɗan sassauta murya tana tambayarsa da cewa


"Menene sunan ita yarinyar da kakeso ka Aura ɗin?."




Wannan karon cikin sanyin murya ya fara maganar domin kuwa mahaifiyar tasa a maimakon mamakin ta da ya faraji, tofa yanzu tsoro ta fara bashi, ganin yadda take maganar cikin kakkausar murya.


"Sunanta Bilkisu ne."



"Bilkisu. Bilkisu.."


Auntie ta maimaita tana ya mutsa fuskar ta, wacca ta ɓaci da Bleaching ta gode Allah.

"Ita ɗin Ƴar ina ce haka?".


"Katsina ne mahaifarta."



Ya bata amsa cikin sauri sauri, wata ɓoyayyar ajiyar zuciya ta sauke, jin ba wacca take tunanin ba ce, sannan ta ce

"Babu damuwa ita ma zaka iya Aurenta, amma fah Bayan ka Aura Ƴar uwarka Jiddarh. Zuwa lokacin Burina na tsayin shekaru ya cika sannan...."





Gyara zaman sa Ya yi saman swivel chair da yake kai sannan ya kira ta da sunan da sukafi kiranta dashi.




"Auntie."



Ta amsa sannan ya ci gaba da cewa


"Shin zan iya sannin wannan Burina naki da kike cewa har saina Aura Jiddarh shi ne zai cika?."





Murmushi tayi kalar na cikakkun wayayyun Mata tana kaɗa ido ta amsa masa da faɗin


"Oh no Heesham har yanzu kai yaro ne ba zaka fahimci komai ba, koda na faɗa maka."



"Kai, Auntie ni ne Yaron? nafa Haura Twenty five highly fa."


Cewar Heesham yana zare ido jin an kira shi da Yaro.







Still it's her cheek have clear smile, shiru tayi sannan ta kuma cewa

"Habba My first Born, just chill Boss, mana daga wasa to na yadda kai ɗin, ba yaro bane, Kocin ne."🥳


Tayi maganar tana ƴar dariya sannan ta ci gaba da cewa


"Wato Heesham misali kai ne kana da wata Riga wacca wannan Riga ta kasance tana da wani masifar kyau da tsada, kowa sonta yake kaima hakan, kana masifar ƙaunar ta, sai kuma ya kasance ita wannan Riga daga ka ɗaukota ka saka ta a jikinka zata dinga yi maka ƙaiƙayi ta ko wanne ɓangare na  jikin ka har sai ka cire ta, ka ƙona ta da wuta da fetur ta zama babu ɓurɓushinta sannan zata dena wahalar da kai shin idan kai ne ya zaka yi da wannan haɗaɗɗiyar Riga da kake masifar ƙauna?, shin zaka a jeta ne gefe ka dinga kallo kanajin daɗi, ko kuwa zaka ƙonata ne ka huta saboda bata da wani amfani?..."





Murmushi Heesham Ya yi Yana nazarin maganar ta, tabbas idan ya fahimta wato dai Hausa take masa cikin Hausa, sai dai kuma daga maganar ta bai fahimci komai ba, saima ɗaure masa kai da maganganun nata suka yi, ajiyar zuciya ya sauke yana kallon ta, sannan ya bata amsa da cewa


"Gaskiya idan ni ne mutum mai wannan Rigar tunda ina ƙaunar ta sosai, kawai zan saƙaleta ne na dunga kallon ta kullum tunda saka ta bazai Yiwu ba."





"Oh Heesham wannan maganar naka is not a efficacy, bazai yiwu ba, kawai kabar zancen nan, domin kuwa yafi ƙarfin tunanin ka."



Heesham zayyi magana yaji Alamar za'a shigo Bedroom ɗin, hakan ne Yasa sa fasa faɗar abin da zai ce, sannan ya mayar da kallon sa kan ƙofar.






A hankali ta tura ƙofar ɗakin ta shiga jikin ta sanye cikin Elegant Beauty Dress doguwar gown c.green color, wacca daga gaban gown ɗin Anyi ado da wasu stones sky green masu shaining, gown ɗin mara hannu ce, gashi ta matse ta gam gam, kanta babu hula sai gashinta Wanda Yasha gyara ta mishi style in braid.





"Oh Jiddarh lafiya kuwa naga kina faman dafe kan ki haka?."



Cewar Auntie a ɗan ruɗe, ƙari sawa wurin ta Jiddarh tayi sannan ta zauna kusa da ita, ta jingina kanta da Headboard na gadon da Auntie take zaune saman sa, tana faɗin


"Auntie kaina ciwo yake min kamar zai tsage gida biyar, haka nake ji."


"Oh sannu fah, kin sha magani kuwa?."


Auntie ta tambaya tana kamo ta jikin ta, ganin hankalin mahaifiyar tashi ya koma kan Jiddarh ne. Yasa shi tashi da sauri yabar bedroom ɗin, kai tsaye staircases ya nufa yana taka steps ya lalubo wata lamba kana ya dan na ma ta kira.





"Oh no Way gaskiya Auntie kema kin san bama shiri da magani ko kaɗan, kawai dai Yanayin hayaniyar dana shiga Yaune Ya ka womin Headache, amma nasan zuwa anjima zan dawo Normal nawa fa."

Cewar Jiddarh tana kyaɓe Beauty face nata. Domin ta tsani magani sama da komai.










*ABUJA*



*Wuraren Ƙarfe Biyar Da Rabi Na Yamma*





Gaba ɗayansu Ahalin Gidan suna tsai tsai ye a parking lot na gidan. Tun daga kan Daddy Mister Mai Kyau, da kuma Momy Rafi'at sai Nainarh, Nailah, Haleesat, Zaynerb, Afeefah, Lailah sai Deejarh sai kuma sauran baƙi.



Suna yiwa su Mamy Zuwaira da kuma Mamy Jawaheer, da Sakeenah harda Jummai waɗannda a yau zasu koma Jigawa State. Yayin da sauran kuma sai zuwa gobe zasu wuce ta Kano sannan su wuce States nasu.




Sai faman waige waigen ta inda zata hangosa take amma bata hango kowa ba, tayi mamakin Rashin ganin sa cikin mutane.
Kamar ance ta ɗaga kanta wajajen part nasa, aikuwa ta hango sa tsaye yana leƙen su ta ƙaton glass window dake palon sa. Yana sanye cikin Black t-shirt and short white color hannun sa riƙe da coffee cup yana sipping a hankali.



Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta masa alama da hannunta cikin iska wai zasu Tafi fah, baizo Ya yi mata bye bye bah 👋.

Murmushi ya yi daga inda yake tsaye sannan shima Ya yi ma ta Bye bye daga inda yake tsaye.
Maƙe kafaɗa tayi wai a'a, sannan ta kuma yi masa alama da tafiso Yazo.
shima maƙe ma ta kafaɗar Ya yi sannan Ya koma saman Royal sofa nasa ya zauna kana ya ɗauki remote control ya danna curtains na wurin suka koma suka Rufe.





Murmushi Tayi sannan cike da nishaɗi ta shige cikin tsadaddiyar motar su cikin zuciyarta kuwa faɗi take

"Oh my God wallahi Yaya Maleek is so adorable highly, nidai wannan zuwa Gidan Uncle Mai kyau gaba ta kaini tunda na sama dami a kala."





Murmushi kawai Afeefah dake lura da Love drama tsakanin Buddy nasu da Husnee take yi cikin zuciyarta faɗi take

"Ah Yaya Maleek kaga ta kanka indai Husnee ce wallahi."




Sai da suka ga ficewar motocin kaf daga gate na gidan nasu sannan suka juya suka yi ciki. Bayan sun shiga ƙayataccen palon ga tsananin maɗaukakin mamakin su part na Maleek suka ga Daddy mahaifin su Mister Mai Kyau. Ya nufa.😸


Ganin haka shima Uncle Yusuf da sai gobe zai koma Mai duguri da iyalansa yabi bayan sa.


_+_🥴🥴Oh Oh Malam Mai Kyau Yada Sauri Hakan?..🥴🥴_-_





Gaba ɗaya murmushi suka yi harda Momy Rafi'at sannan Ita ma ta nufa staircases tana taka steps tana qwalawa Haleesat dake zaune saman 2sieter kira, tashi ita ma Haleesat tayi kana tabi Bayan Momyn nata.



Yayin da gaba ɗaya suka zazzauna saman Royal sofa's dake Palon suka dasa sabon fira tsakanin su.

Afeefah da kuma Auntie Yusra matar Uncle Yusuf da Yaranta waɗanda suka zo da kuma Auntie Suwaiba matar Uncle Sagir da Yaranta wa'inda suma sai gobe zasu wuce Kano tare da su Zaynerb.




A hankali Deejarh takai fresh hand nata cikin pocket na gown dake jikin ta ta ciro wata siririyar chain, bata zinare bace sannan kuma bata diamond bace, kawai dai normal chain ne, amma fah Kalar wannan chain ne wacca bata komai.


Murmushi tayi sannan ta kuma mayarwa cikin pocket gown nata.




Kallon Afeefah dake zaune gefanta tana latsa waya tayi, kana ta ce

"Balarabiyar India kin san Menene kuwa?, a'a sai kin faɗa."



Cewar Afeefah.
"Toki Rufe idon ki."


Deejarh ta faɗa lokacin da ta miƙe tsaye ta koma tana fuskan tar Afeefah ɗin. murmushin da ya bayyana dimples tayi sannan tana faɗin

"Oh My Deejarh, Menene zakimin Idan na Rufe?."



"Kedai kawai ki Rufe."


"Okay."


Jin haka Yasa Afeefah ta Rufe idanunta tana jiran taji abin da Deejarh zatayi gaba.


Dariya Deejarth tayi sannan tasa hannunta cikin gown pocket dake jikin ta, ta ciro wannan Ƴar siririyar chain mai ɗaukar ido Like a diamond, sannan ta ce



"Yanzu ki buɗe, a hankali ta buɗe manyan dara daran kyawawan idanunta, aikuwa taci karo da wannan haɗaɗɗiyar siririyar chain mai tsananin ɗaukar ido.
Dariya Deejarh tayi sannan ta miƙawa Afeefah ɗin chain ɗin tana faɗin

"Wannan ita ce kyauta na ta musamman a gareki."🤗




Fashewa gaba ɗaya mutanen palon suka yi da dariya, Zaynerb na faɗi


"A gaskiya anyi son kai wannan haɗaɗɗiyar chain a rasa wacca za'a ba sai Afeefah Bayan Wanda ta samu Wajen gasa."


Haseeya da take ɗiya wurin Uncle Sagir ta ce "Ah ta cancanta ne, shiyasa kika ga ta bata."



Ita kuwa Afeefah bakinta yaƙi rufuwa tsaban farin ciki, a Rayuwar ta tanaso ayi ma ta kyautar Abu, kamar dai sarƙa ko zobe kodai dangin waɗannan babu abin da take yi sai faman juya sarƙar a hannunta.


Kallon Deejarh tayi fuskarta ɗauke da matsanancin farin ciki ta ce
"Oh my Deejarh a gaskiya naji daɗin wannan special gift da kika bani highly."

Dariya ita ma Deejarh take yi sannan ta ams da,
"Haka nakeso Balarabiyar India kullum ki kasance ciki farin ciki sosai."


Komawa tayi ta zauna sannan ta ci gaba da cewa
"Nima kalar ta guda biyu nake da su, duka Babana ne ya bani da yake sana'ar sa ke nan siya da siyarwa na sarƙoƙi."



 "Aikuwa na gode highly, da kika zaɓeni matsayin wacca zaki bawa wannan haɗaɗɗiyar chain."





_-_Mgnr Payment Haba mutane na ya naji shiru ne😹
Wai iyakar soyayyar da kuke ma novel ɗin ke nan😏
Daga mgnr kuɗi sai ja baya😚





💃💃💃💃
Sannan kamar yadda na faɗa akwai discount in one week mutane da suka fara biya.
300
Kawai zasu biya madadin 500
Sai naji ku

_-_💓The Nainarh Kd 💓_-_
*The Phone Number*
*08081129487*
*The Acct Number*
*8081129487*
*The Bank Name*
*Palmpay Bank*
*The Acct Name*
*Khadeejarth Sabi'u Yahyah*


~Karku bari a baku labari fa🤩~

~*SARAUNIYAR KYAU*~🔥🔥Takun Tsakiya_-_
*Iya kuɗin ki iya shagalin ki Hajiya*






_-_💓The Nainarh Kd 💓_-_
*The Phone Number*
*08081129487*
*The Acct Number*
*8081129487*
*The Bank Name*
*Palmpay Bank*
*The Acct Name*
*Khadeejarth Sabi'u Yahyah*


~Karku bari a baku labari fa🤩~

~*SARAUNIYAR KYAU*~🔥🔥Takun Tsakiya_-_
*Iya kuɗin ki iya shagalin ki Hajiya*


*300 wa mutane ashirin na farko, kar a manta*


___*💋 SARAUNIYAR KYAU 💋*_________ƚαƙυɳ ϝαɾƙσ____________________________________💥👑𝑻𝒉𝒆 𝑮𝒍𝒂𝒎 𝐐𝐮𝐞𝐞𝐧👑💥____________________𝑩𝒚:𝑻𝒉𝒆 𝑵𝒂𝒊𝒏𝒂𝒓𝒉 𝑲𝒅__


Page *99&100*




*Wuraren ƙarfe Tara na Dare*


*Afeefah*


Zaune take saman doguwar softened stool. Yayin da Laptop nata yake saman Jinyarta tana karatu a ciki, da yake ita da Lailah sun kusa kammala karatun M.B.B.S. Nasu daga nan kuma su wuce ƙasar Poland, domin ɗaurawa da M.S. daga nan kuma Bayan sun kammala su koma China ko kuma Philippines su ci gaba da D.N.B Nasu daga nan kuma idan zuwa lokacin sunyi Aure Tom, idan kuma basu yi ba, su kuma ɗaurawa M.C.H.



Wannan ne ɗaya daga cikin Burikansu kuma suna Fatan ƙaddarar su ta kasance musu hakan. 👩‍❤️‍👩




A je laptop dake jinyarta tayi gefe sannan ta miƙe tsaye ta ƙarisa gaban Drawer, hannu tasa ta buɗe sannan ta ciro wannan secret box kana ta koma saman Royal Bed nata ta zauna tana buɗe kwalin, a hankali cikin nutsuwa irin na ta.


Sai da ta kammala warware wa tas sannan ta buɗe secret box da wani tsadadden haɗaɗɗen diamond wristwatch ta fara cin karo, ɗauki shi tayi ta riƙe a hannunta tana ƙare masa kallo. Yana da masifar tsada ga wani shaining na musamman da Yake yi, a jeshi tayi gefanta sannan ta kuma ciro wasu diamond chain and earings haɗe kuma da wani diamond ring mai matuƙar masifar tsadan gaske, murmushi tayi kana suma ta a je gefe ta kuma ciro wani check.



Ganin check na kuɗi ne yasa ta mayar cikin box ɗin batare da ta damu da Tasan ko nawa ne cikin check ɗin bah.😌




Ɗauko diamond Ring ɗin tayi tana juyasa a hannunta tana faman murmushin murna.
Shigowa bedroom ɗin Haleesat tayi waya maƙale a kunnenta tana amsawa, hango Afeefah gefan bed ne yasa ta ƙarisa sannan ta zauna kusa da ita tana amsa ci gaba da Wayar.




Ita kuwa Afeefah sai faman juya duka gift da ta samu take yi cike da farin ciki, kallon Haleesat tayi ganin ta kammala Wayar da take yi Ta ce cikin washe baki.

"Auntie Haleesat duba kiga duka fah na samu Wajen gasar."





Murmushi Haleesat Tayi sannan Ta ce
"Ina tayaki murna highly, da samun irin wannan gift Haka."



Tayi maganar ita ma lokacin da ta karɓq diamond wristwatch dake hannun Afeefah ɗin tana dubawa.



Da yake Haleesat ba wani surutu take ba. Yasa Afeefah kallonta cike da son janta da fira Ta ce

"Auntie Haleesat kina bani mamaki wasu Lokutan fah, sai naga ke ba surutu ba, sai tarin ƙawaye kamar mene."



"Tofa Menene ya kawo wannan maganar kuma?."

Cewar Haleesat still tana juya wannan haɗaɗɗen diamond wristwatch dake hannun ta.



Afeefah Ta ce "Naga Yanzu kika kammala Waya kuma cikin Harshen farasanci, nasan dai bada boyfriend ko kuma wani Namiji kike Wayar ba, tabbas da mace ce."





Dariya Haleesat tayi tana faɗin "Yeah kin ma tuna min wani abu wallahi. Ɗaukar wayarta dake saman Laps nata tayi sannan ta shiga ɓangaren gallery ta lalubo wasu pictures.
Nunawa Afeefah dake kallonta wayar tayi sannan Ta ce

"Please Afeefah wannan budurwar dake cikin pictures ɗin nan dawa take miki kama?, I'm so confused nah rasa gane koda waye take kama, sai dai tabbas akwai wanda take kama dashi fa."





Karɓar Wayar Afeefah tayi tana kallon picture ɗin. tsawon sakanni sannan ta kalla Haleesat wacca ta zuba ma ta ido tana kallo.
Ajiyar zuciya ta sauke sannan tana cewa
"Nidai Iya tunanina wannan budurwar dake cikin pictures nan, Bala'in kama suke da Ummyn Farhana wato Sunainah, wannan neighbor tamu ƙawarku."


Da sauri Haleesat ta karɓa Wayar tana ƙara duba picture ɗin a fili ta ce

"Kai wow, amma fah kema Afeefah ta musamman ce, tsawon Kwanaki ina so na gano dawa take min kama, sai Yau haba Biri Ya yi kama da mutum kamar tasu tayi Yawa highly highly."




Amma ita wannan ta cikin pictures ɗin wacece?, dan naga alamar kamar ba musulma bace, daɗi da ƙari kamar ba Ƴar Nigeria bace, lura da Yanayin shigarta da kuma launin fatarta tafi kamada turawan Yankin Asia." Cewar Afeefah.




Dariya Haleesat Tayi Ta ce "Afeefah You are so cute and talented kina da gaskiya sunanta 'HEART CHENG  JUNG' Ƴar Asalin ƙasar faransa ce amma anan Nigeria muka haɗu da ita, dalilin Wani Abu da ya taɓa faruwa dani, sannan kuma Ina matuƙar mamakin yadda ya kasance ita da Sunainah suna kama Like a twin's."



Afeefah ta ce "Ke kuwa Haleesat kamar ba Ƴar zamani b, kokin manta cewa Yanzu zamani ya sauya ana iya samun mutane Biyu ko sama da haka masu Bala'in kama da juna Like a twin's yanzu dai kamar doppelganger's kinga ae mutane Biyu ne waɗanda Yawancin su bama ƙasa ɗaya suke ba, amma kuma zaki samu suna matuƙar kama da juna."





Haleesat ta amsa da "Haka ne naji, kuma na gamsu da maganar ki, amma fah har Yanzu, am so very confused wannan Kamar tasu Ya ɓaci highly highly, wannan kama nasu sai dai Idan jini ɗaya ne kawai."



"To ina ga kawai muje mu sama ita Sunainah ɗin domin tambayar ta game da lamarin tunda har yanzu kina cikin confessing."


Cewar Afeefah, dariya Haleesat tayi  sannan
"Hakama Ya yi amma fah, dole sai mun dawo daga Kano State sannan ko?."


"Eh haka ma Ya yi  ae babu damuwa."


Cewar Afeefah tana dariya, domin kuwa Ita ma kamannin da wannan Baturiya mai suna HEART CHENG take yi da Ummyn Farhana ya ɗaure ma ta kai highly highly.




Tashi daga tsaye Haleesat tayi Bayanta mayar da diamond wristwatch ɗin saman bed ta a je sannan ta ce

"Barina koma bedroom nawa bacci nake ji highly highly yau."


Tayi maganar tana nufar ƙofa sannan ta fice daga Bedroom ɗin.





Dariya Afeefah tayi tana girgiza kai tare da faɗin

"Auntie Haleesat tawa ɗan wannan surutun harta fara jin bacci."




Mayar da abubuwan tayi cikin box ɗin kana Ita ma ta miƙe tsaye riƙe da box ɗin ta ficewa tayi daga bedroom ɗin, kai tsaye bedroom na Lailah ta nufa, kwankwasa ƙofar tayi daga ciki Lailah dake kwance saman mattress tayi ɗaiɗai cike da gajiya ta ce






"Oh my God kai koma waye Ya yi haƙuri sai gobe, domin kuwa a gajiye nake nasan ma bazai wuce Yasmin ɗiyar Uncle Yusuf ba, ok ko kuma Mah'eesha ɗiyar Uncle Sagir, so kawai koma wacece ta koma sama masauki dan bazan buɗe ba, a ƙaramin gajiya sama da wanda nake ciki.





Daiyake baƙin duka a sama zasu kwana ɓangaren baƙi na musamman.



Murmushi Afeefah tayi sannan ta ce "It's okay Tunda Haka ne, ki Huta da kyau dama wannan secret gift box nazo miki dashi domin kika abubuwan da suke ciki, amma Tunda kince Haka sai da safen good night."


___________________
*Maganar payment fa, Hajiya ta kiyi sauri har yanzu ana discount.300 ne kawai wa mutane ashirin na farko, mutane suna cika ashirin tofa sai dai ki biya 500*🙃

_-_💓The Nainarh Kd 💓_-_
*The Phone Number*
*08081129487*
*The Acct Number*
*8081129487*
*The Bank Name*
*Palmpay Bank*
*The Acct Name*
*Khadeejarth Sabi'u Yahyah*


~Karku bari a baku labari fa🤩~

~*SARAUNIYAR KYAU*~🔥🔥Takun Tsakiya_-_
*Iya kuɗin ki iya shagalin ki Hajiya*




______________________________________________
Wani irin hantsalowa daga saman bed Lailah Tayi tana faɗan

"Please My only one, feefah tsaya wallahi banyi tunanin ke ba ce, na ɗauka ko Yasmin ce ko kuma Haseeya da su Mah'eesha."





"Okay to ki sauke domin kuwa ni ce."



 

Cewar Afeefah Lokacin da tayi gaba, kai tsaye bedroom na Zaynerb ta nufa ta tura sannan ta shiga, sai dai kuma ba Zaynerb ciki da alama ta fita.

Dan Haka fitowa Afeefah tayi daga bedroom na Zaynerb ɗin, aikuwa suka buga karo da Lailah.

Yayin da Afeefah ta buge goshi ita kuma Lailah ta buge hancinta Garin buɗe ƙofar.
Gaba ɗaya suka yi baya da sauri Afeefah na faɗi cike shagwaɓa


"Ouch, My lovely Dad Lailah zata kashe maka shalele fah ka kawo ma ta ɗauki please." 🥺





Fashewa Lailah Tayi da dariya faɗi take "Kai Afeefah ki rage na gobe, ni ban san Yah yah mijinki zaiyi da wannan shagwaɓa naki ba."




'Okay to ki tsaya nanda lokaci kaɗan zaki gani."


Afeefah tayi maganar tana nufar hanyar bedroom na Deejarh.


Da sauri Lailah tabi Bayan ta tana faɗin


"Ke haba da gaske kike?. Tom kodai perfect perfume Guy ne, ko kuma mutumin waya da kika suburbuɗa masa ƙarya, da cewa sunan ki RISHITA ina ga da ɗaya daga cikin su za`ayi dashi Bamu sani ba."


Tayi maganar cikin Dariyar ƙetah.





Qin kulata Afeefah tayi sai ma tura ƙofar bedroom na Deejarh, tayi sannan ta shiga ciki, bakinta ɗauke da sallama ita ma Lailah tabi Bayan ta.



A hankali ta turo ƙofar bathroom ta fito chest nata ɗaure da Towel White color tana Raira waƙar Mawaƙi Sani Ahmad Cike da Nishaɗi takecyin waƙar, faɗi take

"Dalilin-so-kaji-dalilin-so-Nima kujerar-so.


Zauna-kujerar-so-kaidai-heyy,-soyayya_Ra'ayi, nii.!!"




Da sauri Tayi shiru ganin waɗanda suka shigo, sai kuma da gudu ta koma cikin bathroom ɗin tana faɗin


"Kai Balarabiyar India kun Bani kunya. Dan Allah ku fita na fara shiryawa."




Dariya Lailah tayi tana zama saman doguwar kujera dake cikin bedroom ɗin sannan ta ce

"Ae Yarinya idan zaki fito kawai ki fito, dukkanin mu ma ta ne anan, sannan kuma mun riga ki shan iskan duniya gaba ɗaya, so banga abin da zaki ɓoyemin ba, bayan kuma nima ɗin, ina dashi, Yarinya ki fito kawai ki ci gaba da Raira waƙarki ta Sani Ahmad domin kuwa akwai daɗi, wato KUJERAR SO."




Afeefah kuwa murmushi kawai tayi sannan ta ƙarisa wajen study chair dake bedroom ɗin, ta zauna tana faɗin
"Kinji Deejarh fito abin ki bari mu rufe ido kinji tawan."🤓





Kamar zatayi kuka Deejarh ta ce "Please Balarabiyar India ku koma kafin na shirya, ko kuma kiɗan miƙomin doguwar gown ta Bacci a cikin wardrobe nawa pleased."



Jin haka yasa Lailah miƙewa da sauri tana faɗin

"Bari na kawo miki kinji."


Tayi maganar tana nufar wardrobe sannan ta buɗe ta zaɓo wata sleeping dress black color mai taushi, sannan ta ƙarisa bakin ƙofar bathroom ɗin tana faɗin

"To gashi ki karɓa, da sauri ki saka tun kafin nayi fushi na mayar."




Jin haka yasa Deejarh zuciyarta guda ta ɗan turo ƙofar bathroom ɗin da ta Rufe, a hankali sannan ta zuro hannunta tana amsa wa da


"To Auntie Lailah ga hannuna ki bani kinji."



Ganin haka ita kuma Lailah ta mayar da sleeping gown ɗin Left hand ɗin ta sannan tasa right hand nata ta kamo Deejarh gaba ɗayan ta tayo waje da ita tana dariya.

Da gudu Deejarh ta haye saman bed ta ƙudun duna da bedsheet tana mayar da Numfashi ta ce
'Dan Allah Auntie Lailah ki Bani."




Murmushi nishaɗi Lailah tayi sannan ta miƙa ma ta sleeping gown ɗin tana faɗin

"Riƙe badan halinki ba."



Da sauri ta karɓa tana dariya sannan ta ce
"To ki Rufe idon ki sannan."




"Wannan ne kuma baki isa ba, Yarinya ni banga Abin ɓoyewa ba, bayan kuma duka muna dasu."



"It's okay wato dai bakiga Abin ɓoyewa ba ko, ke muguwa kin saka ƙaramar Yarinya gaba kina zalunta ko?."


Cewar Afeefah.



Kafin Lailah ta sama damar magana Deejarh mai baki, ta ce


"Tabɗi jan, Balarabiyar India, kinji ki da Wani zance. Yanzu ni ce ƙaramar Yarinyar, aikuwa bakiyi dai dai ba, domin kuwa a ƙauyen mu ae kamata tanada Yara biyu ko uku."




Zaro ido Lailah dake zama a doguwar kujerar da ta zauna da farko tayi sannan ta ce

"Haba sai kace wani Rayuwar Jahiliya ni dai ban Yarda ba gaskiya."




"Okay Tunda baki Yarda ba Wani Lokacin ki gwada zuwa ghetto Area, ko kuma wani ƙauye dake kusa, kiga Abin mamaki, domin kuwa zakiga mace wacca a shekaru ba za ta wuce twenty five ba, da Yara shida ko bakwai tana fama."





Cewar Deejarh iya gaskiyar ta.



Kallon Afeefah Lailah tayi tana cewa

"Wai Haka ne?."



Tayi tambayar da alamar Rashin Yarda Riƙe da Baki.

Murmushi Afeefah tayi sannan ta ce "Of course yes, da Yawa ana samun Hakan."





Daga faɗin Haka tayi shiru.


Ajiyar zuciya Lailah ta sauke sannan ta ƙariso wurin da Afeefah take zaune Ta ce

"To malama Feefah Yanzu sai mun roƙa za'aba mu secret gift box mu gani ko kuwa?."




Murmushi Afeefah tayi sannan ta miƙa ma ta duka box ɗin tana faɗin



"Gashin nan Miss Lailah ayi ta gani."


Da sauri Lailah ta karɓa box ɗin sannan ta koma saman doguwar kujerar ta zauna, tana buɗe secret gift box ɗin, da sauri Ita ma Deejarh da ta kammala sanya sleeping gown ɗin a jikin ta, ta ƙarisa wurin tana gani cike da farin ciki game da tsantsan nishaɗi da zaƙuwa. 😁







Qayataccen murmushi Mai kyau Afeefah mai kyau take ta faman saki ganin Yadda gaba ɗaya Lailah da Deejarh suka bi, suka shiga confused, na ganin wannan ƙayatattun diamond wristwatch da Diamond Ring, diamond chain and earings harda check na kuɗaɗe.


Ita dariya ma Lailah ta bata sai kace ba ɗiyar Mister Mai Kyau shahararren mai dukiya na ala tsine uwar mai ƙarya ba, koda yake ba ganin wa'innan abubuwan yasa ta wannan ruɗewar ba, harda na tayata murna, kuma taji daɗi mara misaltuwa da Hakan.





A hankali ta miƙe tsaye tana tafiya a hankali kamar mai tausayin ƙasa. Yayin da ƙafafunta suke nutsewa cikin carpet tattausa dake baje tsakiyar Room.







A hankali takai hannunta sannan in slow ta Ya ye curtains Milk color dake Rufe da Windows na room ɗin.




Buɗe glass windows ɗin tayi duka, Yayin da Yanayin yadda iskan garin yake kaɗa wa Ya yi dai dai da Yanayin nishaɗin da take jin kanta ciki, zuciyarta cike take da nishaɗi sosai sannan kuma bata Fatan wani abu yazo ya gifta tsakanin wannan Rayuwar farin ciki da nishaɗi da take ciki, ita da Ahalinta daɗi da ƙari daga ƙarshen ƙarshe dai ga Yaya Maleek nata ya dawo Gida.




Bayan shafe tsawon shekaru Bayanan.



Tasa ni cewa dukkan wani ɗan Adam Yana tare da ƙaddarar sa, koda kuwa yana ƙarshen duniya ne.




So ita tana fatan ta ta ƙaddarar ta kasance ma ta a Yayin da take cikin Ahalinta, bata Fatan wani abu yazo ya rabata da Ahalinta, Especially ma Daddynta, Auntie Zaynerb nata, Lailahnta, Deejarh da kowa da kowa.




Koda kuwa Aure ne tofah tafiso ta zauna kusa da Ahalinta gaba ɗaya cikin farin ciki da ƙaunar juna.


A Wani mugun tsora ce ta zaro fararen idanunta cikin ƴan sakannin da suka shuɗe tana cikin nishaɗi, amma kuma cikin ƴan wa'innan sakanni da bazasu wuce biyu zuwa uku ba, ta shiga matsanancin violence sosai, dalilin Haka kuwa shi ne.




Hango Auntyn ta Zaynerb kuma abar ƙaunarta cikin swimming pool tana iyo ciki ba tare da numfashi shi ba, to abin da ya faru shi ne, sai da Zaynerb ta cike mintuna biyar cikin ruwan ba tare da numfashi ba, sannan ta fito.


Tofah Wajen fitowan ne aka so a sama akasi, Allah ya kare, domin kuwa wajen riƙe Banister's na madaidaicin Benen da zata fito daga cikin swimming ɗin ne, zata riƙe bata riƙe da kyau ba, shiine fah.
Tayi baya zata koma cikin ruwan ta baya, sai Allah ya kiyaye ta riƙo Banister's ɗin da Left hand nata.🤯





Wata kalar ajiyar zuciya afeefah ta sauke, tana dafe saitin ƙahon zuciyarta. Yayin da idanunta kuwa har wasu qwallan farin ciki ne, suka taru sai faman haki take saukewa, duk da cewa ba ita bace ta kusa anta yawa cikin Ruwan.



Tana tunanin da'ace Zaynerb ta faɗa cikin ruwan, idan ba wani ikon Allah ba, da wuya a ciro ta da rai.

Saboda Yanayin yadda tayi bayan, gaba ɗayanta ba wani abu da zata iya.




Shiyasa ita bata damu da wani iyo cikin ruwa ba, ko kuma ta dama kanta da saita Iya tsawon mintoci cikin Ruwa ba batare da numfashi ba.



Tasan Allah shike karewa amma gaskiya hanyar lafiya a bita da shekara.




Koma wa tayi wurin su Lailah suka ci gaba da fira sama sama. Yawancin firan nasu akan Yanayin rayuwar poor people ne.



A taƙaice dai sai wuraren can cikin dare sannan Afeefah da Lailah suka koma bedrooms nasu bayan sun sha fira cike da farin ciki.








*Haleesat Mai Kyau*





Ɓangaren Haleesat kuwa, bayan fitarta daga bedroom na Afeefah, kai tsaye bedroom nata ta wuce, wanka ta fara yi sannan ta shirya cikin sleeping dress fanjama Riga doguwa fara mai taushi.





Sai da ta kammala duk wani al'adarta kafin kwanciya Bacci, sannan ta kwanta saman royal bed nata Yayin da ta zuba wa kyakyawar fuskar wanda ke rufe cikin face mask Souvenir Abin tunawanta ido tana kallo, tamkar ba zane take kallo ba.




Duk da cewa sau ɗaya tak ta taɓa ganin sa.

Tsayin rayuwar ta sannan a lokacin wata kalar ƙaunarsa ta shige ta duk da cewa bata ga fuskar sa ba.

Confirm tasan wasu zasu kirata da zararriya, ko kuma wacca ta sama taɓin hankali, amma ita ba zata damu ba, domin kuwa kyawawan idanun sa, kawai take tunawa a ganin ta yin soyayya ko kuma faɗawa soyayya, ba dole sai da wani dalili ba, domin kuwa yin soyayya ko faɗawa cikinta baya buƙatar wani dalili.





A hankali ta furta a saman laɓɓanta

"My souvenir Yaushe, a'ina wani lokacin na ƙosa sosai, da na ƙara ganin ka na ƙosa highly, Ranar da zanga beauty face naka tazo a Ranar ko'a gaban waye sai Nayi Rawa da juyi."



"Ina son ka daga kallon farko, ina son ka daga haɗuwar farko, hallaudai, I LOVE MY SOUVENIR. Please! sweet Dream Good Night, My love."🥰






Ta daɗe hakan cikin magana ita kaɗai da paper ɗin hannun ta, har can bacci Ya ɗauketa bata san lokaci ba.


_-_ To Miss Haleesat Mai Kyau Zararriyar Your Souvenir Good Night_-_💃💃

















"MY Feefah Baby.!"

"My feefah baby..."


 
"Umhm, My Baby."


"Kin san wani abu kuwa?."


"Umm umhm."

I Love So Very much, Thither I Love For the All My heart, please, Say me. You Love Me please My feefah?."


"umhm umm No Way."





Juyi kawai Take yi gaba ɗaya tabi ta haɗa uban gumi tamkar Babu a.c cikin bedroom ɗin, sai faman faɗin "Umhm um."

Take yi tana ƙara wa da kalmar "No Way."😉





A hankali ta buɗe kyawawan fararen idanunta, kai tsaye ta sauke su saman haɗaɗɗen ceiling.

Shiru tayi tana tariyo gaba ɗaya mafarkin da tayi.

Gaba ɗaya yasha banban da kalar wanda take yi kwana biyu, wancan tana yi ne akan Haleesat da wata mummunar Mata take so ta cutar.


Wannan kuma wanda tayi a yau, wai ita da wani haɗaɗɗen ƙasaitaccen matashin saurayi ne, wai Yake roƙonta akan ta soshi, sai dai kuma bata samu ta kalla fuskar sa ba ta farka.😇





Juya idanun ta tayi tana ƙarewa bedroom ɗin kallo, gaba ɗaya pillows ɗin sun zube ƙasa, kowanne da ɓangaren da Ya yi shi Kanshi bedsheet Tayi dai dai saman mattress ɗin a taƙaice dai, gaba ɗaya saman bed ɗin nata ya koma tamkar ansha bidiri saman sa.💃💃





Murmushi tayi ganin yadda bedroom ɗin ma gaba ɗaya ya koma, sannan ta miƙe tsaye, juya idanunta tayi kan clock, ƙarfe Biyar saura wasu mintoci.


Ajiyar zuciya ta sauke kana ta nufa bathroom Hannu tasa ta kama handle na door ɗin sannan ta buɗe ta shige ciki.



Sai da ta kwashe tsawon mintuna goma sha shida ciki, sannan ta fito zuwa lokacin an fara kiraye kirayen sallan asuba. Dan Haka Hijjab ta ɗauka sannan ta tayar da sallah.



Bayan ta iddar bata tashi daga saman sallaya ba, sai da ta kammala dukan wasu al'adunta bayan iddar da sallah.





Zuwa Lokacin shida da Rabi tayi Don Haka ɗan motsa jiki tayi irin su Lanqwasa can, dawo nan saqalo tana nan. Juya can, malƙwashe, Haka dai sai da ta shafe tsawon mintuna talatin tanayi sannan ta dakata.





Zama tayi gefan bed tana goge gumin da ta tara tsaban motsa jiki takai mintuna uku a Hakan sannan ta miƙe, kai tsaye ƙofa ta nufa sannan ta buɗe ta fita daga bedroom ɗin.




Bedroom na Zaynerb ta nufa aikuwa taci sa'a a buɗe yake, Don Haka kutsa kanta tayi ciki bakinta ɗauke da sallama.





Can saman doguwar stool ta hangota tana rubuta cikin wata ƴar ƙaramar jotter.
A hankali Zaynerb ta juyo tana amsa sallamar da Afeefah ɗin tayi fuskarta ɗauke da murmushi.



Qari sawa wurin tayi sannan ita ma ta zauna tana kallon ƴar uwan nata cike da farin ciki Ta ce


"Auntie Zaynerb, Menene kike Rubutawa cikin wannan jotter ɗin?."


Tayi maganar tana ƙoƙarin ɗaukar jotter ɗin, da sauri Zaynerb ta kai hannu ta riga ta ɗauka tana faɗin wannan sirri ne.





Murmushi mai bayyana dimples Afeefah tayi sannan ta ce

"Okay tunda Haka ne yanzu wani shiri kike yi wa zuwa Kano State da zamuyi zuwa anjima?."





Zaynerb ta ce

"Shiri dai shi ne muna zuwa bazan dawo ba, sai nanda two weeks."




Zaro ido Afeefah tayi waje cikin shiga violence Ta ce

"Amma dai wasa kike yi ko?, Yanzu idan Wani Abu Ya sameni fah, kinsan fah bazan iya zama wurin da baki ba ko?."





Dariya Zaynerb Tayi tana faɗin

"Lallai Afeefah na lura fah har Yanzu ɗaukar kanki kike matsayin ƙaramar Yarinya, wacca bata Haura shekaru huɗu ba."



"Eh mana ae Haka ne indai ina tare da ke, ko kuma Daddy tofa ɗaukar kaina nake tamkar wata ƙaramar Yarinya wacca bata wuce shekaru Biyu a duniya ba."💃




Afeefah tayi maganar tana dariya.



Kama Baki Zaynerb tayi tana dariya ta ce

"Afeefah lafiyar ki kuwa?, idan kikayi Aure fah?."


Afeefah Ta ce

"Wani Aure aeni indai kika ga nayi Aure, tofa sai dai idan shi mijin ya kasance zai barni na zauna anan gidan tare da Ahalina sannan Zanyi."🥸




"Tirƙashi ah lallai Afeefah kina ruwa tsundum highly ma kuwa."


Cewar Zaynerb tana dariyar silly tunani irin na ƙanwar nata.

Afeefah ta ce


"Allah da gaske nake yi.
"




"Tohm ni dai bazan taɓa Yarda ba."


Cewar Zaynerb.

Afeefah Ta ce

"Ae zaki gani nan da watanni nawa ne kwata kwata."






"Okay...👌

Kice ƙanwar tawa ta antaya soyayya, to da Yaushe Hakan ta faru ni ban sani ba kuwa?."


Zaynerb ta tambaya ah mamakance.


Afeefah..

"Oh Auntie Zaynerb tawa ni fa ba wani soyayya. Dana antaya, kawai dai na faɗa ra'ayi na ne."

Zaynab...



"Ni dai ban Yarda ba gaskiya sai an faɗa min gaskiyar lamarin, ah gaskiya."


Zaynerb ta faɗa cike da nishaɗi.


Ae fah nan suka Shiga compromise tsakanin Afeefah da Zaynerb, ita Afeefah ta tsaya akan cewa ba wani soyayya da ta faɗa yayin da ita kuma Zaynerb ta tsaya akan cewa lallai lallai fah Afeefah ta faɗa soyayya.






Shigowar Deejarh ne yasa firan nasu ta tsaya, kiran Afeefah tayi suka fita a tare zuwa kitchen.

Anan suka haɗu dasu Elina da Ummi wa'inda suma suka ƙariso kitchen ɗin, da yake a gidan suke kwana akwai part na musamman wanda suke ciki, daga backyard na gidan.



Nan suka shiga aikin haɗa breakfast da yake Gidan akwai baƙi waɗanda suka kwana, shiyasa breakfast ɗin da suke yi yafi na kullum.



Suna aikin suna taɓa fira tsananin su da yake Afeefah ta saba dasu sosai, dan ma Yawancin types na girke girken da ta iya a wurin sune.



"Nifa har Yanzu ban gane wannan kyakyawar Budurwar ba, nasan dai ba xixi bace kodai, ita ma cikin Dangi take ne?, amma fah kyakyawa ce highly Allah kuwa."




Duk wannan zanen Ummi ce take zubosu da yake ita ma ɗin gwana ce wurin iya surutu.




Murmushi Afeefah tayi wato dai shi ɗan Adam baya iya ganin Abu bayyi magana akai ba ko?.😇



Kallon Ummi Tayi sannan Ta ce "Sunanta Deejarh ƙanwar mu ce ita ma."


Tana maganar ne tana miƙa ma ta wasu onions da spinach dasu cabbage sannan Ta ce

"Please Ummi yayyanka wa'innan bazan iya ba, sun cika yaji da Yawa."


Karɓa Ummi tayi tana faɗin

"Aikuwa da ganin wannan onions ɗin Yaji zasu yi fah, ae wallahi kina ma ƙoƙari highly."



Murmushi kawai Afeefah tayi wanda ya zaman ma ta jiki koda, yaushe beauty face nata ɗauke take da ƙayataccen murmushi.


Sai dai ba tace komai ba, ita da tabata Albasa saboda karta isheta da surutu, domin kuwa tasan Ummi akwai surutu, sai dai kuma tana Bala'in burgeta ta wasu ɓangarorin domin Ummi nutsatsiyar budurwa ce, akwai ta da hankali sannan kuma bata irin wannan gossip da zaka samu da yawa daga cikin House maid Suke yi ba, ita dai barta da shegen surutu faɗi ba'a tambayeki ba ke nan.😸






Cikin ƙanƙanin lokaci ƙamshin haɗaɗɗun girke girken da suka kammala.
Ya gauraye Gidan gaba ɗaya ciki da waje sannan ya tashi gaba d`aya mutanen Gidan waɗanda basu tashi ba.🥰





Jere gaba ɗaya girke girken suka yi saman dinning tables waɗanda aka ƙara Yawansu saboda baƙin.





Tsayawa tayi tana ƙarewa gaba ɗaya girke girken da suke, jere saman dinning room ɗin kallo, sai faman steaming suke yi ga ƙamshi na musamman da yake tashi mai tayar da yunwa ko ba shiri.🥳





A hankali cike da enjoying Mood da Take ciki. Take kallon duka abincin breakfast ɗin gaba ɗaya babu abin da babu, komai akwai tun daga kan.




•Meat Balls and potato sauce 😇_____
•Peppered soup with chicken_
•Rolled stuffed moi-moi.   😋__________
•Healthy spinach mix.      
•Shredded chicken.       🍲____
•Savoury stuffed Yam balls.
•Fish Ball_&_Gas Meat_&_Special advice.
•Fried Yam with egg special 💢_
•Vegetable Fried Liver_&_Sphagetti salad __
•Mango fruit and pineapple juice 🧃🥤______
•Banana pancakes and potato crush 🥰_________
•Banana and strawberry Juice nd Yoghurt____
•Special gift Tea Wanda sai faman steam Yake ☕.



Da saura ma da ya wa waɗanda wasu ita kanta batasan sunayensu ba, sai dai su Elina da Ummi waɗanda suka ƙirƙiro wannan uban abubuwa Haka.




Kallon Elina da Ummi Tayi cikin murmushi ta ce
"Wannan uban girke girke da ababen shayashaye Haka aiko mutune talatin sunyi kaɗan su cinye fa."


Murmushi Ummi Tayi sannan ta ma ta nuni da Deejarh da take faman zaɓan abinci wanda ranta yake so tana sakawa cikin plates da suke saman wani special tray.




Dariya Afeefah tayi tana faɗin
"Ke, Deejarth lafiyar ki kuwa?, duk wannan uban abinci ina zaki kai su?."




Ɗagowa Deejarh tayi tana kallon Afeefah cikin washe fuska ta ce

"Duka ina son su ne, shiyasa zan kwashi rabona naje bedroom ɗina taci, saboda nan akwai baƙi."

Tayi maganar tana ɗaukar tray ɗin da ta cika sa dam shaƙare da abincicika kala kala.




"Amma dai daga nan sai hospital za'ayi dake ko?."

 Elina ta tambaya tana kallon ta, ƴar dariya Deejarh tayi sannan ta ce
"A'a tas zan cinye kuma na zauna qalau sai ma lafiya da zan ƙara sosai sosai.🥰





Dariyar wautar Deejarh kawai Afeefah take yi girgiza kai, kawai tayi sannan Ta ce

"Gaskiya Yaro Yaro ne, amma banda Abin Deejarh wannan uban abinci kamar wata mai juna huɗu haka, tohm Allah ya kyauta."


Tayi maganar a Yayin da ita ma ta ɗauki tray shaƙare da abincicika kala kala da ababen shayashaye ta nufa staircases Wanda Kai tsaye zai sadata da nangaren Maleek.






Zata fara taka steps na farko ke nan, ta hango fitowar Mah'fuz da Yasir suna saukowa suma daga ɓangaren Maleek ɗin, da yake su acan suka sauko, ko dama can Haka Abin Yake, a ɓangaren Maleek suke sauko indai aka zo Taro ko Wani Abu Cikin Gidan, da yake duka suda Maleek ɗin duk sa'annin junane watanni ne tsakanin su domin kuwa bae kae shekaru ba.






Washe baki Afeefah tayi tana faɗin "YaYa mah'fuz and YaYa Yasir, Good morning to you All, Fatan kun Tashi lafiya a cikin Gidan mu?."




Murmushi suka yi a tare sannan kuma a dai dai lokacin da suka ƙariso wurin da take rsaye riƙe da tray.


A Tare suka kuma faɗin
"Feefah Mai Kyau toya Garin SARAUNIYAR KYAU ta madinatul Abuja muna miƙo gaisuwa fah."




Har Lokacin fuskar Afeefah a washe take da ƙayataccen murmushi Ta ce

"Oh YaYa Yasir and YaYa Mah'fuz har Yanzu dai kuna nan da wannan Abu naku Tamkar wasu twin's, hmmm ae koda Yake idan mutum bae sani ba zai iya kiran ku da twin's ɗin, domin kuwa komai naku ɗaya ne, hatta magana idan zaku yi a tare ne."





"Ae dama twin's ɗin ne tun tuni sai dai kuma Hassan Yana Kano ne shi kuma Hussein Yana a Borno State."


cewar Yasir a taƙaice sannan kuma cikin murmushi.





"Okay.. 👌

Toh mai zai Hana ɗaya daga ciki ya koma State ɗin da ɗaya Yake ba, ae kunga daga nan kuma ba Mai ƙara tantama akan cewar kuɗin ba twin's bane."


 Cewar Afeefah a lokacin da tayi gaba ta fara taka steps na staircases ɗin.




Murmushi kawai suka yi a tare sannan suka nufi Dining domin bawa ciki haƙƙinsa.😋




Hango mutum tafe ne tasa Ummi tayi, off na Wayar dake hannunta sannan ta mayar cikin apron pocket dake jikinta.




Kallon su tayi Bayan sun zazzauna sannan cikin muryarta ta ce "Good morning everyone's please which kind of food did you needed for?."


Kallon juna suka yi a tare sannan kuma suka mayar da kallon su a kanta kana Yasir ya faɗa kalar wanda yake so yaci da sha, sannan tayi saving nashi bayan ta kammala ta ƙara kallon Mah'fuz sannan ta ce

"Yallaɓai uhum?."

Kallon ta mah'fuz Ya yi shima sannan Yace
"Menene kuma uhum?. Menene kalmar uhm take Nufi?."


Gyara tsayuwarta tayi ta ce
"Ina nufin wani kalar Abinci kakeso daga cikin nan domin nayi saving naka?."


Lumshe kyawawan idanun sa Ya yi sannan yana faɗin
"Okay, wato dai yanzu wannan kalma ɗayan ce duk take nufin duk wannan bayanan da kika jeromin ko shikenan, amma fah Hakan Ya yi.👌



Murmushi tayi sannan ta ce "Yeah yanzu dai Yallaɓai zaɓa abin da kakeso domin na saka maka."



Shima murmushin ya saki kana Yace

 "£verything, All."

Zaro ido Ummi tayi waje, As Austere ta ce
"Menene amma dai wasa kake yi dai ko?."

 "A'a da gaske nake duka gaba ɗaya zakiyi saving nawa, domin kuwa duka nakejin ci."


Ummi ta ce
"A'a please Boss ka taimaka ka zaɓa wasu daga ciki domin kuwa bazaka iya cinye wa duka ba."

"Ah gwada mana a gani, ae sai an gwada akan san na qwarai ko?."



Shima mah'fuz ya faɗa, ae nan fa suka shiga compromise tsakanin su. Ita Ummi cewa take ya daure ya faɗa kalar nau'in abinci da yake so, domin tayi saving nashi.
Yayin da shi kuma mah'fuz ya dage kai da fata sai tayi saving nashi duka abincin wurin.🤣




Yasir da gaba ɗaya surutun nasu ya hanashi sukuni, da yake shiɗin ba, person ne mai son hayaniya highly ba ne.

Dakata wa Ya yi da kai loma Bakin sa sannan ya kalla Ummi Yana cewa

"Please Miss saka masa duka abin da kikaga dama, wannan bashi da ragadi ki dena Biye masa domin kuwa sai ku kwana anan kuna compromise tsakanin ku."




Murmushi Ummi tayi sannan ta ce "Nagode Yallaɓai domin kuwa duk surutuna naga alama so yake ya ƙure ni fa."

Tayi maganar tana ƙoƙarin saving na Mah'fuz ɗin.



"Kar ki sake kiyi saving nawa muddun ba, duka abincin bane kinji ko?."


Da sauri gaba ɗaya daga Ummi har Yasir da kuma Lailah wacca take shirin ƙari sawa Dining ɗin, taji maganar sa na ƙarshe a sama. Duk suka juya suna kallon sa.



Cike da tsananin mamaki Yasir ya tambaya.


"Saboda me ke nan?."


Kai tsaye mah'fuz ya basa amsa da cewa

"Saboda Haka nakeso kuma na zaɓa. Idan kuma ba Haka ba sai dai mu kwana anan."




Kallon Ummi wacca tayi raurau da ido tamkar zata fashe da kuka Yasir Ya yi sannan Yace


"Kinji Miss ki Rabu dashi, wannan ya zare fa da alama."

Cike da takaicin su duka Ummi ta kalla Yasir sannan ta ce dashi

"Sunana Ummu Sulaym, amma anfi kirana da Ummi, bawai Miss nake ba ehe. Menene Wani Miss sai kace kana kiran mage?."






Murmushi Lailah tayi a lokacin da ta zauna ta fahimci hau shin da mah'fuz ya cusa ma ta take zubarwa kan Yasir.

"Wata ƙila Ita ma Ummyn Yaya mah'fuz ɗin Ya yi ma ta kwarjinin da yake yi ma sauran girlfriend's ne, shiya sa ta kasa masa masifa ta ƙare akan Yasir."


Haka kawai Lailah take ayyana wa cikin zuciyarta tana dariyar wannan drama da Yaya mah'fuz ya tattara.
Ta fahimci komai sai dai zatayi shiru da bakinta domin ci gaba da ganin wannan sweet drama.







Sallama ɗauke saman laɓɓanta ta ƙarisa shiga cikin Katafaren Palon wanda Yasha kayan Mo re Rayuwar duniya daular duniya ke nan.



Can saman Royal sofa ta sangosa zaune ga System gabansa yana sarrafawa, yana sanye cikin t-shirt black color and trouser short black color.



Qari sawa tayi sannan ta ɗaura tray dake hanunta saman glass center table dake palon.
Sannan ta zauna a saman royal sofa 1sieter tana kallon Yayan nata cike da farin ciki. Yanzu dai daga ƙarshen ƙarshe ga YaYa Maleek nata ya dawo Gida.
zata ci gaba da kawo masa abinci kullum kamar dai baya.




Murmushi tayi sannan ta ce
"Yaya Maleek Good morning, Fatan dai kana Lafiya?." Tayi maganar cikin washe fuska.




A hankali ya ɗago da sexy eyes nasa yana kallonta kamar sakanni biyu sannan ya amsa da faɗin

"Bana Lafiya. Sai Yanzu kikaga damar zuwa ganina ko?, gaba ɗaya jiya inata saka ran shigowar ki, amma ba ki zo ganin Yaya Maleek naki ba, kowa Yazo banda ke hatta Nainarh da take fushi dani tazo munsha fira."



Kama Baki Afeefah tayi cikin dariya ta riƙe ear nata duka biyun sannan ta ce
"Please Yaya Maleek nawa afuwan wai dama fa, na bari ka huta ne zuwa ya fah."



Qayataccen murmushi Maleek ya saki sannan ya amsa ma ta da
"Afeefah ta ni ma da wasa nake yi, sauri ki saki kunen ki saboda kar suyi ciwo kinji ta gidana?."





Murmushi ita ma tayi tana faɗin

"Godiya nake Yayana."


Miƙewa tayi sannan ta ƙarisa wurin center table ta fara saving nasa, suna taɓa fira tsakanin su biyun.



Konawa tayi ta zauna bayan ta kammala saving nasa ta ce

"Yaya Maleek ae yau tare da kai zamuci breakfast namu domin kuwa nayi kewar cin abinci tare da kai highly."






"Okay.👌

Haka ma Ya yi dai dai ae, domin kuwa nima nayi kewar zama nayi fira da ƙanwata Afeefah sosai."

Cewar Maleek shima, gyara zama Afeefah tayi tana kallon sa sannan ta ce

"Wai Yaya Maleek shin zan iya sanin Abin da wannan Bature Ya yi maka a ƙasar Rasha ɗin?, domin kuwa Lailah ta Bani Labari sai dai kuma ta ce baka ƙarisa basu Labarin ba suma har aka tashi daga zaman."





Kallonta Maleek Ya yi sannan ya saki ɗan gajeren murmushi kana Yace

"Zan faɗa miki, amma ba yanzu ba."


Da sauri Afeefah ta ce "Saboda me?."


Yace saboda { Nainarh Kd 📲 } Tana maƙale tanaso taji abin da zan ce saboda taje ta rubuta cikin wannan shahararren Labari nata *💋SARAUNIYAR KYAU💋*



Dariya Afeefah ta amsa da "Ai babu damuwa ka faɗa kawai domin nasan a *SARAUNIYAR KYAU* *FAN'S CLUB* za ta yi update" 🤓


Ajiyar zuciya Maleek ya sauke sannan  ya magana kamar haka.

"Wato kinaso ki sani ko?."
Da sauri ta ce "Sosai ma kuwa."

Murmushi Ya yi sannan Yace

"A lokacin yaso ya ƙalamin wani sharri ne, saboda kawai bama shiri, sai kuma da taimakon Allah dana wani matashin saurayi likitan ƙasa da ƙasa na samu na fito daga cikin Ramin sharri da wannan bature yake so ya turani, sai kuma daga ƙarshe shi kuma wannan Bature ya faɗa ciki.
Dama Hausawa suka ce, Idan zaka haƙa Ramin mugunta tofa ka Gina shi dai dai ƙaurinka domin kuwa wata ƙil kai ɗin kai ne zaka faɗa ciki."




"A lokacin da Haka ta faru ko sati guda ban kuma yi a wannan hospital dama ƙasar ba gaba ɗaya, na tattara ya nawa ya nawa, ban dandara ba, na kuma komawa wata ƙasar turawan wato ƙasar Slovakia Babban Birnin ƙasar Bratislava nan ma a babban asibitin ƙasar nayi aiki, sai da na kwashe tsawon shekara ɗaya, sannan na bar ƙasar Slovakia na dawo ƙasar haihuwa ta Abin alfaharina ƙasata Nigeria, ina dawowa Nigeria ban tsaya tunanin komai ba sai...
Yarda za'a rage yawan cutu-ttuka irin na mata.
A lokacin akwai Manyan kuɗaɗ a tare dani saboda Haka ba tare da wani ɓata lokaci ba, na tatttaro gaba ɗaya ƴan uwana gynecologist waɗanda muka yi karatu tare dasu a can Rasha ƴan Nigeria mutanen Arewa har dama mutanen kudu da ko'ina duk waɗanda nasan na sansu kuma likitoci ne, na ɓangaren mata.
Sai da na tatttaro su gaba ɗaya sannan batare da da wani shan wahala ba, da yake kusan dukansu Ra'ayin mu yazo ɗaya gaba ɗayan mu...
Muka taru aka haɗa ƙarfi da ƙarfe muka fara gudanar da aikin mu a kowane ƙauye dake jahohin Nigeria, gaba ɗaya harkokin ayyukan namu akan ƙauyuka muka mayar dasu Abin dai shi ne...
Idan ƙauye ko gari ya kasance babu wasu asibitoci a ciki ko kuma akwai babu kayan aiki, mu kuma sai muje a ƙara buɗe Manyan asibitoci a garin ko kuma ƙauye ko kuma a kafa camp na bada taimakon gaggawa a kowani Layi ko kuma Yanki..
To dai da taimakon Allah wannan ƙungiya tamu da muka kafa mai suna *The Young Gynecologist* ta fara shahara a ƙasa harma da ƙasashen waje, domin kuwa abin namu ya ci gaba hatta likitocin ƙasashen waje suna iya zuwa ayi dasu, mu ma kuma har ƙasashen wajen muna zuwa wani Lokacin..
To abu dai ya ci gaba highly sosai, domin kuwa ko watanni bakwai ba'ayi da buɗe wannan ƙungiya ba, sai kuma mutane Manyan masu kuɗi na duniya suka fara bada tallafi harda masu saka hannun jari, daga ƙarshe ma gwamnati ta saka hannu ita ma aka ci gaba da gudanar da wannan shahararriyar ƙungiya mai suna *The Young Gynecologist* da ita."



"A takƙaicen taƙaitawa dai wannan shi ne kaɗan daga abin da ya faru. Bayan bari na Gida."

Maleek ya ƙarishe maganar yana zuba kakkauran Tea cikin mug sannan Yakai Baki ko jin zafi bayyi ba.

Shiru palon ya ɗauka Bayan kammala bawa Afeefah Labari da Maleek Ya yi, tsawon mintuna kusan goma sha ɗaya da sakanni.



Sannan Afeefah ta sauke nannauyar ajiyar zuciya kana ta kalla Yayan nata tana faɗin

"Buddy, to har Yanzu wannan ƙungiyar taku ta *The Young Gynecologist* tana aiki kuwa?."



Ƙayataccen murmushi Maleek ya saki sannan ya bata amsa da. "Sosai ma fi ye da baya domin kuwa yanzu akwai Resukanta a ƙasashe daban daban na faɗin duniya dan ba iyaka Nigeria muka tsaya ba harda ma gaba ɗaya duniyar mun zagaye.'






Murmushin jindaɗi Afeefah tayi sannan ta kuma cewa amma a lokacin da wannan matashin saurayi likitan ƙasa da ƙasa ya taimake ka daga sharrin da wannan Bature yaso ya saka ka, ya kaji?."






Da sauri Maleek ya kalleta jin tambayar da tayi masa, sai kuma yayi ɗan murmushi sannan Ya ce


"A lokacin ji nayi kamar na basa Auren ƙanwata, domin kuwa ya Burgeni fiye da tunanin duk wani mai tunani."





Zaro fararen idanunta waje Afeefah tayi tana kallon sa, jin amsar da ya bata, cikin ɗan shiga confused take faɗin



"Yaya Maleek amma dai, ha'a ina ce ba musulmi bane ko?."


"Waye ya faɗa miki ba musulmi bane, musulmi ne shi mana."




Ajiyar zuciya ta sauke na rashin dalili sannan ta sha re zancen likitan.

Nan dai suka ci gaba da fira cike da nishaɗi, sai can wuraren ƙarfe goma sannan Afeefah tabar ɓangaren Maleek bayan sun sha fira highly highly.








Kai tsaye bedroom ɗin ta ta wuce, tana shiga bata tsaya jiran komai ba, ta wuce bathroom tsawon mintuna Talatin ta kwashe ciki.



Sannan ta fito chest ɗin ta ɗaure da towel Pink color, ga wani ƙarami tana goge doguwar sumarta, wacca ta zubo ma ta gaba da baya.




Qari sawa tayi gaban Dress mirror sannan taja swivel chair ɗn ta zauna tana kallon kanta cikin mirror ɗin, murmushi tayi sannan a fili ta furta.


"Feefah Mai Kyau, shalelen Daddyn ta Mister mai kyau, da kuma Yayarta Zaynerb Mai Kyau, sai kuma YaYanta Maleek sannan kuma SARAUNIYAR KYAU ta garin Abuja.






Murmushin farin ciki ta kuma yi, sannan ta fara shafa tsadaddun lotion a jikin ta, bayan ta kammala miƙewa tayi ta ƙarisa can gefen bed, sannan ta ɗauko wani ƙaramin suitcase, kana ta dawo ta zauna akan swivel chair ɗin na Dress mirror sannan ta ɗaura saman mirror kana ta buɗe kid ɗin.



Ɓangarori Biyu ne da kid ɗin, ɓangare ɗaya make-up artist ne kamar su.


•Jagira-concealer-eye shadow-eye liner, gel liner-mascara-foundation-
•Highlighter-contour-Setting powder-finishing-powder-Lipstick, JamBaki and
•Lip glows-moisturizer, primer da kuma make-up setting spray-Blush-Brushes set
•Eye Lashes-Brow gel-Shimmer_Beauty blender spong {BBS}.




Yayin da ɓangare na biyu kuma kayan ado ne na mata ciki _-_jewelry_-_ kamar su.

•Ring-chain-earrings-stud-Necklace-Bracelet-wristwatch-Da sauransu domin kuwa gasunan dai sai wanda ta zaɓa.






Ajiyar zuciya Afeefah ta sauke tana kallon waɗannan uban tilin make-up artist and jewelry kamar Hauka, ita fah bata cika son waɗannan abubuwan ba. Tafi ganewa Normaly Natural beauty Nata bawai ayi ta shafe shafe ba.




Mayar da kid ɗin gefe guda tayi sannan ta zaɓa waɗanda zata iya amfani dasu, tabar waɗanda ba zata iya ba.




Cikin ɗan ƙanƙanin lokaci ta zauna ta tsara heavy light make-up a saman kyakyawar fuskar ta, wanda ba ƙaramin kyau tayi ba, sai ta fito sak Queen ɗin ta 💞👑💞




Miƙewa tayi bayan ta kammala yin kwalliyar sannan ta nufa closet ta zaɓa kalar tufafin da zata saka jikinta.


Nan ma sai da ta kwashe tsawon mintuna goma sannan ta shirya cikin Atamfa Dresses.



Doguwar gown na atamfa wacca aka ma ta ɗin kin fitted rigar tayi ma ta Bala'in kyau, musamman ma da ya kasance ɗin kin dai dai ita ne. Rigar ta zauna ma ta ɗamas.




Dawowa tayi gaban mirror sannan ta tsaya ta tsantsara ɗaurin ta na manyan Gayu. Sannan ta ɗauki earrings ta maƙale a kunnen ta, kana ta saka sarƙar tare da da Bracelet sannan ta ɗauki diamond ring ta saka a yatsarta na ƙarshe sai da ta kammala duka abin da ya kamata tayi, sannan ta ɗauki veil wanda yake Pink and sky purple color, ta riƙe a hannu daya ke gaba ɗaya shigar da tayi shigar Pink and sky purple color ne.
Hatta atamfar jikin ta launin sky purple and Pink color ne, kai komai da komai na jikin ta ma Haka ne, gashi tasha wankan diamond ta ko'ina diamond ke walwali a jikin ta gata Ita ma ɗin kanta Diamond ce guda.💓




Qari sawa tayi wajen doguwar softened stool dake bedroom ɗin, sannan ta ɗauki handbag nata Ita ma Launin Pink and sky purple color ce.







A taƙaice dai duka wankan jikin ta wankan Pink and sky purple color ne, domin kuwa Afeefah favorite color nata shi ne sky purple color, ita Haka take komai nata ya banbanta dana kowa.😇







Handbag ɗin ta riƙe a Left hand nata Yayin da veil nata shima da bata yafa ba. Yake Riƙe a right hand nata kallon agogon bedroom ɗin Tayi 12:00am ta gani fa.😺



Da sauri ta nufa ƙofar bedroom ɗin, tana faɗi a fili

"Shikenan kuma nasan ma kowa ya shirya ni kaɗai ake ta jira ma."





Fresh hand ɗin ta, ta saka sannan ta buɗe ƙofar bedroom ɗin, aikuwa tamkar ana jiran ta buɗe, nan suka shiga jera ma ta pictures wasu da camera Yayin da wasu kuma da wayoyin hannayensu Suke yi.



Da sauri takai tafin hannunta na dama Wanda Yasha Jan lalle, tana rufe fuskar ta saboda kar hasken Ya yi ma ta illa, sai hakan da tayi ya zama kamar style.


Aikuwa tamkar ta ce ku ci gaba na canza style ne. Haka suka ci gaba da jero ma ta Hotuna gaba ɗaya palon bakajin komai sai ƙaran flash flash jika ke

Tas!, tas Tattas tas tas.🤩




Haka kawai kake ji gaba ɗaya palon.


Afeefah dai da taga hotunan ba zasu ƙare ba, Yasa cikin sauri Ita ma ta shige cikin su tana dariya ta ce

"Kai Auntie Nainarh, Mah'eesha YaYa Yasir da YaYa mah'fuz harda ke Lailah Yasmin please ku dena Allah na gaji fa."


Tayi maganar cike da shagwaɓa.



Gaba ɗaya dariya suka fashe da ita cike da nishaɗi

"Okay Tunda Haka ne, gaba ɗaya kawai ku jeru ayi pictures ɗin na Ahali kawai."



Cewar Yasir cikin murmushi.


"Mene ae sai dai kuwa idan zaku bari acan Kano ayi, domin kuwa lokaci yaja sosai, duk Shalele ce ta janye mana lokaci."




Gaba ɗaya juyawa suka yi domin ganin mai maganar.



Uncle Yusuf ne tsaye shima cikin shirin sa na alfarma, gefan sa Mister Mai Kyau ne shi kuma kamar ko yaushe sanye cikin Business suit Maroon color.





Yasira ce da take ita ma ɗaya daga cikin Yaran Uncle Yusuf ɗin, ta kalla mahaifin nasu cike da shagwaɓa ita ma take cewa .

"Kai Abbhu ae hotuna fa, kawai zamay..."





Tun kafin ta ƙarisa Uncle Yusuf ya katse ta da faɗin

 
"Okay wato dai kece shagwaɓaɓɓiya ina faɗin lokaci Yaja shi ne zaki kawo wani checking nonsense ko?, shige muje ƴar jakar.🤫 Ko kuwa nayi jifa dake daga nan har mota kuwa."😂








Ya ƙarishe maganar yana ma ta nuni da Hanyar wajen.






Simimi simi Yasira tazo ta wuce ta gaban sa, sannan ta fita daga palon, suma sauran suka mara ma ta baya su Lailah suna ma ta dariya.🤣








Da sauri Afeefah ta kamo hannun Deejarh a lokacin da suke shirin fita daga ƙofar palon tana tambayar ta faɗin.


"Ke Deejarh, Wanene ya miki wannan make-up Haka, sannan kuma ya naga kunyi shiga kala ɗaya dasu Auntie Nainarh da Lailah harda ma Zaynerb da Haleesat faɗa min gaskiya kinji ko."




Dariya Deejarh tayi tana amsa ma ta da "Auntie Lailah ce tayi min wannan kwalliyar kuma ita ta bani kayan nan na saka mu kayi anko dukkanin mu."



Murmushi kawai Afeefah tayi tasan Halin Lailah tsaf indai ba wani Abu take nema wurin Deejarh ba. Tofa ba zata taɓa ɓata lokacin ta wajen yi ma ta kwalliya ba, amma dai ko miye zasu haɗu da Lailah ɗin sai taji koma menene.






Afeefah tana shirin magana ke nan ta lura da irin kallon da mah'fuz  yake ma Ummi da take Yima su Zaynerb Bye, bye.







Ajiyar zuciya ta sauke bayan ta ƙarisa kusa da shi, ɗan ɗigil-gile tayi sannan ta kai tsayi dai dai nasa kana cikin kunnen sa take raɗa masa.



"Wato dai Yaya mah'fuz ya kamu da love ko, amma fa karka damu indai Ummi ce, niɗin nan Feefah mai kyau, ɗiya wurin Mister mai kyau sannan kuma SARAUNIYAR KYAU ta garin Abuja zan shawo maka kan Ummi domin kuwa muna Bala'in shiri da ita sosai.😇






Qayataccen murmushin jindaɗin maganar ta mah'fuz ya saki, sannan ya kalle ta, tana shirin shiga tsadaddiyar mota bayan ta gama faɗa masa maganar.
Yace

"Kamar dai me da me kike so, faɗa inaji yanzu kiga aiki da cikawa."





Juyowa Afeefah tayi tana murmushi ta ce  dashi

"Ɗan ihsani da kuma wannan ring naka, da nace ka bani kaƙi, toh yanzu iya suma, sun isa kawai."




Tana faɗin hakan ta buɗe Motar ta shige ciki, ita ma Deejarh dake bayanta ta shiga motar tsaleliya da ita.





Ajiyar zuciya ya sauke yana kallon ring dake hannun sa. Wanda Afeefah ta nace masa ya bata, saboda ring ɗin ba maza ba mata duka ana sakawa. Wancan yaqi bata, amma kuma yau ba gobe ba, zai bata saboda Ummi .😎

Buɗe mota shima Ya yi sannan ya shiga ciki.







Gaba ɗayan su shishshiga tsadaddun motocin suka yi sannan as slowly motocin guda shida, suka fice daga gate na gidan, sannan bayan fitarsu gate man ya mayar da gate ɗin ya rufe.






A hanya Afeefah tana zaune a motar da ta shiga, gefanta Deejarth ce ita ma tana zaune tsit.



Ƙarar da wayarta tayi alamar shigowar message ne, yasa ta karɓa wayar daga hannun Deejarh da take game, sannan ta duba.


Message ɗin daga mah'fuz ne, kuɗaɗe ya turo ma ta 500K.
Murmushi tayi sannan ita ma kai tsaye batare da ɓata lokaci ba, ta turawa Ummi duka kuɗaɗen tare da message har kaloli byu daga ƙasa, sannan ta Mayar ma da Deejarh wayar, ita kuma ta ci gaba da kallon hanya cikin yanayin mai daɗi.





_-_
Da isar su katafaren filin sauka da Hawan Jirgin sama na Mister Mai Kyau, gaba ɗayan su suka fiffito daga tsala tsalan motocin su na alfarma.



Sannan suka fara tafiya izuwa wurin hawa jirgi, a tare tafiyar nasu ma kaɗai mutum ya gani, sai sun basa sha'awa da burgewa, balle kuma azo ga yanayin shigar alfarma dake jikin ko wannensu ma, Humm abin dai sai wanda ya gani gaskiya, domin kuwa gaba ɗaya hankulan kowa da kowa na Airport ɗin ne ya dawo kansu.

Kallon kowa yake cike da sha'awa, ga Deejarh ita ma da ta saje dasu kai idan ka ganta ba zaka ce, Yarinyar da ta zo daga ƙauye Bane, wacca ko sati biyu bata cika a Garin Abuja City ba.



Kai idan ka ganta zaka rantse Ɗiyar wani Ambassador ce, ko kuma wani minister ko ɗiyar wani ƙaton ƙusa a ƙasa.☺️



Ba tare da wani ja ko kuma ɓata lokaci ba, gaba ɗaya suka shishshiga cikin Jirgi.


Yayin da Mister mai kyau shi kuma zai bi ɗayan Jirgin nasa izuwa ƙasar Austria domin gudanar da harkokin kasuwancin sa.


Yayin da ita kuma Momy Rafi'at kai tsaye driver zai wuce da ita Katafaren Hospital nata, shi kuma Maleek da ya Rako su driver ya koma dashi Gida domin kuwa bare dashi za'ayi tafiyar Bah.





In Banda zare fararen idanunta tana ƙara ƙanƙame Afeefah sannan kuma tana bin cikin Jirgin da kallon tsoro, babu abin da Deejarh take yi, har suka zauna a first class ita da Afeefah.


Yayin da ita Afeefah take ɓangaren window ita kuma Deejarh take zaune kusa da ita.



Kallon ta Afeefah tayi cewa "Deejarh gyara na saka miki belt domin kuwa naga alamar baki iya ba."


_-_masu karatu shin kuwa ko kun san bakin surutun Deejarh ya mutu kuwa?_-_🤣😂😅








Dan haka ba tace komai ba, ta gyara sannan Afeefah ta gyara ma ta saka belt ɗin, kana ta koma ta zauna.

To abin dai haka yake domin kuwa koda Jirgi zai tashi ƙara ƙanƙame Afeefah Deejarh tayi, harda hawaye wai tsoro take ji, Lailah kuwa ita da Yasira da suke Bayan su sai Faman dariya suke ma ta.

A haka dai har Jirgin nasu ya ɗaga cikin gajimare yana yawa tawa dasu.🛬


         



___*💋 SARAUNIYAR KYAU 💋*_________ƚαƙυɳ ϝαɾƙσ__________________________________________________________💥👑𝑻𝒉𝒆 𝑮𝒍𝒂𝒎 𝐐𝐮𝐞𝐞𝐧👑💥____________________𝑩𝒚:𝑻𝒉𝒆 𝑵𝒂𝒊𝒏𝒂𝒓𝒉 𝑲𝒅____𝑲𝒉𝒂𝒅𝒆𝒆𝒋𝒂𝒓𝒕𝒉.  𝑺𝒂𝒃𝒊'𝒖.  𝒀𝒂𝒉𝒚𝒂𝒉🤙



_-_💓The Nainarh Kd 💓_-_
*The Phone Number*
*08081129487*
*The Acct Number*
*8081129487*
*The Bank Name*
*Palmpay Bank*
*The Acct Name*
*Khadeejarth Sabi'u Yahyah*



*Sister wannan ne ƙarshen Book 1 kiyi sauri kiyi Payment 300 only kafin lokaci ya ƙure fa🙄, ta waɗancan bayanan na sama 🖕🖕 zaki turo 300 kawai 🤗*




*Ƴar uwa kar fa ki tsaya har sai an baki labari, 🥳 Tohm 😇*






*£nd Of Takun Farko*


Page*101&105*

~Last Free Page's~😸

*And*

🔚σϝ ϝιɾʂƚ ɱιԃԃʅҽ🔚


Zaune take saman ɗaya daga cikin kujerun Dining da aka ƙawata kitchen ɗin dasu. Yayin da take cin breakfast ɗin ta wanda kaiwa da komowa a cikin gidan Bai Bari ta samu taci ba sai Yanzu.



Hannunta kuwa wayarta ne yayinda gaba ɗaya hankalinta yake akan wayar nata tana karanta littafin Mrs Aysib mai suna ZAN JIRA KA.



Message ne ya shigo wayar nata hakan ne yasa ta fita daga whatsApp da take ciki sannan ta buɗe, message da taga lambar Afeefah ne.


Waro ido tayi cike da mamaki tana tunanin anya kuwa ita ce, bawai mistake Afeefah tayi ba, idan ba haka ba mai zai sa Afeefah ta turo ma ta har 500k.

Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta buɗe message na farko da Afeefah ɗin ta haɗo ma ta dashi kamar haka.




"Hi, Ummi ga waɗannan kuɗaɗen nasan dai ba zaki rasa hidimar da zakiyi dasu ba, please bana son ki watsa min ƙasa a ido wurin cewa a'a, Afeefah ce."



Wani murmushin jindaɗi Ummi tayi a fili take faɗin

"Aikuwa Afeefah nagode sosai, kamar kuwa kin san kuɗi nake nema ruwa a jallo."



Cikin sauri ta lalubo lambar ƙanwar ta Ummu Salma, tana ɗagawa ba tare da Ummi ta jira tayi wata magana ba ta ce

"Ummu Salma, Allah ya Rufa mana asiri Yanzun nan wata budurwar da nake aiki a gidan su ta turomin da 500k, saboda haka yanzun nan ba anjima ba, ki turomin lambar account naki domin na taro miki kuɗaɗen saboda a samu ayi ma Ummu Shaheedah aikin ƙarin da ya fito ma ta kinji ummu Salma?.
Yanzun nan fa zaki turomin."



Ajiyar zuciya ta ɗayan ɓangaren wacca Ummi ta kira da Ummu Salma ta sauke sannan ta amsa da faɗin


"Toh Auntie Ummi amma please ba dai roƙonta kika yi ba koh?."






Ɗan murmushi Ummi tayi tana bawa ƙanwar nata amsa da cewa

"A'a ko ɗaya ban roƙeta ba, ha sali ma ko faɗa ma ta ina cikin matsalar kuɗi, banyi ba, kawai dai ina zaune naga anyi min alert na 500k, Yanzu dai ya jikin ita Ummu Shaheedah ɗin ne?."





Ummi ta tambaya domin kawar da wancan maganar.


Kallon ƙanwar tasu, dake kwance saman gado irin na marasa lafiya, Ummu Salma tayi ta ɓangaren ta sannan ta bata amsa da faɗin

"Lafiya Alhamdulillah Yanzu ma ta sama Bacci ne, kuma ita Oumm Sun tafi Gida, domin suyi wanka ita dasu Uzair da Usman Sai kuma Ummu Shahuda da tazo duba lafiyar Ummu Shaheedah ɗin."






"Okay,👌

Haka ake so yanzu Abin da nakeso dake, kiyi sauri ki turomin lambar account ɗin naki kinji ko?."


Cewar Ummi sannan ta kashe wayar bayan Ummu Salma ta amsa ma ta.


Ajiyar zuciya ta kuma saukewa tana tunanin Ahalinta da irin Halin da Suke ciki.
A gaskiya ba ƙaramin taimakon ta Afeefah tayi ba, wannan turo ma ta kuɗin da tayi. Sai taji ta kuma ba Afeefah wani muhimmanci a Rayuwa.

Buɗe ɗayan message ɗin da Afeefah ta haɗo ma ta dashi, tayi sannan ta fara karanta.


"Assalamu Alaikum, Ummi Ni ce feefah mai kyau, please kai tsaye maganar dama ita ce ki daure kiyi tunani akan Yaya mah'fuz ɗina, domin kuwa ƙaunar ki yake yi da gaskiya, shiyasa ma kika ga Yana miki wannan kallon ɗazun nan, please karki masa wani mummunar fahimta domin kuwa Yaya mah'fuz mutumin kirki ne shi, zai riƙe da amana Bayan Aure, saboda Haka ki daure kiyi tunani kafin nanda two days zamu dawo daga kano State, sai ki faɗamin abin da kika yanke, kinga ae sai ah haɗa bikin naku kawai dana Yaya Maleek shida Husnee.
Idan kina buƙatar lambar wayansa ba saikin nemeni ba, domin kuwa ga lambar nan ta ƙasa. Good Luck, Feefah Mai Kyau ce. Bye bye."😇






Ta karanta wannan message yafi sau goma, tana ƙarawa da dai ta gaji ne, ta tsaya dan kanta.


Murmushi tayi sannan a fili take faɗin "Afeefah ke nan ƴar Gidan Babanta. Yanzu haka ake rubuto kalaman huɗubar saurayi a garin ku Abuja?. Wannan saiki saka naji ya gundureni fa."






Murmushin ta kuma saki tuno drama ɗin ta dashi na Safe, a lokacin sai da Auntie Yusra matar uncle Yusuf da ta ƙariso wurin ta tarar da abin da ke faruwa, ta saka Baki sannan ya haqura Yaci abincin.



"Ikon Allah shi kuma irin na shi salon ƙaunar ke nan?, amma fah hakan ya tafi da Ummu Sulaym highly highly, ae Afeefah Mai Kyau, karki damu ranki, domin kuwa tuni mah'fuz Ya yi nisa cikin heart na Ummu Sulaym tun kallon Farko Ya sace heart ɗina." 👩‍❤️‍👨💃











*KANO STATE*





Misalin ƙarfe 2:00 na rana Jirgin su Ya yi Landing a babban Filin Saukar Jirgin sama na garin Kano.



Aikuwa batare da da ɓata lokaci ba, gaba ɗaya suka shishshiga motocin Gidan Uncle Sagir, da Yazo ɗaukarsu shida kansa.
Nan suka Bar Filin Saukar Jirgin suka nufi Katafaren Gidan Uncle Sagir dake nan New Life Kano State.






Da Isar su Katafaren Gidan na Uncle Sagir Sameer Lamiɗo. Nan securities da Suke tsaron ƙaton wagameman gate na gidan Suka buɗe musu gate ɗin cikin sauri.



A Jere sannan kuma a tare tsadaddun motocin guda Bakwai suka yi parking a wangameman Filin ajiye motoci dake Katafaren Gidan.



Sannan gaba ɗaya Suka fiffito a tare, to da yake tare da matar Gidan Suke shiyasa basu tsaya ɓata Lokaci ba.




Gaba ɗaya suka nufa cikin Ainihin Gidan, da Shigar su Katafaren daular duniya ƙaton palon Gidan Uncle Sagir. Wanda yasha ya gaji da shan kayan Mo re Rayuwa Ba'a magana, gaba ɗayan su zama su kayi saman Royal sofa's da aka ƙawata ƙaton palon dasu.




Yayin da mutanen gaba ɗaya waɗanda akazo dasu tun daga kan Mah'eesha, Haseeya, da kuma mahaifiyar su Auntie Suwaiba suka shiga kitchen domin Bawa masu aiki umarnin haɗa lunch Wanda Baƙi zasu ci. Yayinda mah'fuz shi da Yasir ɗan Uncle Yusuf kuwa ko tsayawa a Palon basu yi ba. Kai tsaye ɓangaren mazan Gidan suka wuce domin sauke gajiya.😘





Shima dai Uncle Yusuf da shigowar sa Gidan tuni ɓangaren da Amma wato Hajiya Raheemah take ya nufa tare da Uncle Sagir domin gaisheta da kuma duba lafiyar ta.



Sai ya kasance gaba ɗaya mutanen palon su Afeefah ne da kuma yaran Uncle Yusuf ma ta sai kuma Auntie Yusra matar sa da tabi Auntie Suwaiba kitchen domin tayata wasu ayyukan.





Tunda suka shigo wannan Katafaren Gidan har ƙuka ƙariso palon Suka zazzauna Deejarh tana maƙale da Afeefah. Yayin da take ƙarewa ƙaton palon wanda komai Ya yi zam zam  domin kuwa ba ƙaramin kuɗaɗe aka zuba ba, sai dai kuma ita haryanzu bai kai kyan Gidan Mister mai kyau ba, mahaifin su Afeefah ba a wurinta, domin kuwa shi wannan Gidan part's part's ne da yawa gare shi. Tundaga kan na yara ma ta da kuma na maza sai kuma na Amma sai kuma na Uncle Sagir sai wannan wanda Suke ciki da ya kasance na Auntie Suwaiba matar Uncle Sagir.
Yayin da shi kuma Gidan su Afeefah a haɗe ginin yake kuma a tsare yake.





Kallon Afeefah Deejarh tayi sannan ta raɗa Mata magana a kunne Muryar ta rawa.



Da sauri Afeefah ta kalle ta, amma bata ce komai ba, ita kuma Deejarh ta Ma ta alama da ido, wai zata fita, miƙefwa Afeefah tayi sannan ta kamo hannun Deejarh suka bar palon.



Sai da suka fita daga palon sannan Afeefah ta saki hannun Deejarh da ta riƙe, kallon ta tayi tana faɗin

"Da gaske kike yi wai?."



Tayi maganar tana ƙarewa Deejarh ɗin kallo, ko zataga alama.
Rau Rau Deejarh tayi da idanunta kamar zatayi kuka ta ce

"Allah Balarabiyar India haka kawai naji jikina kamar Ruwa yana tsiyaya. Nifa tsoro nake ji ƙilama saboda nahau Jirgine, shiyasa nake zubar da jini ta da yawa kuma."




Ta ƙarishe maganar tana shirin fashewa da kuka.



Ganin Haka yasa Afeefah ta kamo hannunta sannan suka nufa wani ɓangare daban ba wanda suka fito daga ciki ba.




Kwankwasa ƙofar palon da suka tsaya gaban sa, Afeefah tayi sannan kuma har lokacin hannunta yana cikin na Deejarh wacca gaba ɗaya ta gama tsurewa, saboda tsoron wani Abu kamar Ruwa da take ji yana ma ta Yawo a jiki. 😲








Wata kyakyawar Budurwa ce ta buɗe musu ƙofar palon, jikin ta sanye da kayan bacci, da alama daga Baccin ta farka.
Ganin Afeefah tsaye yasa budurwar sakin ihun murna sannan ta ƙarisa da sauri ta Rungumo Afeefah tana faɗin





"Feefah mai kyau kece, Yaushe ku ka zo, ah ah ina su Haseeya da Mah'eesha ɗin ne, waima ya ya banji ƙarar shigowar motocin ku ba, saida fah na faɗa wa Dad idan zai tafi Airport ɗauko ku yayi min magana shi ne yaƙi ko?."







Budurwar ta ƙarishe maganar cike da Rashin jindaɗin ɗaukosu Afeefah da bata sama Damar yi ba.




"Oh My Auntie Hameeda zaki ɓallani fah."



Afeefah tayi maganar cikin murmushi, ita ma Hameeda murmushi tayi sannan ta saki Afeefah daga Rungumar da tayi ma ta tana kallon Deejarh, cikin murmushi ta ce

"Feefah wannan kyakyawar fa, daga ina kuka samo ta?."





"Wai Deejarh bari zan faɗa miki, yanzu dai Bari mu shiga ciki."



 Afeefah tayi maganar tana kamo hannun Deejarh Sannan suka yi cikin palon.



Ita ma Hameeda ta mara musu baya, a tsakiyar palon suka tsaya.


Cire mayafin kanta Afeefah tayi sannan ta a je saman sofa, kallon Hameeda tayi tana cewa

"Please Auntie Hameeda Bari muyi amfani da bathroom na bedroom ɗin ki Abin is urgently."


"Okay babu damuwa ku Shiga ciki."


Hameeda ta bata amsa sannan Afeefah da Deejarh suka nufa wani bedroom dake cikin palon. Yayin da ita kuma Hameeda ta zauna saman 2sieter.






Suna Shiga bedroom ɗin sai da Afeefah ta mayar da ƙofar ta rufe, sannan ta juyo tana kallon Deejarh kana ta ce


"Oya cire doguwar gown dake jikin ki mu gani."


Da sauri Deejarh ta kalla Afeefah cikin mamaki ta ce

"Balarabiyar India in cire riga na fa kika ce, mai zakimin?."


"Oh Deejarh ina nufin ki cire muga jinin da kike zubar ne fa."

Cewar Afeefah.





Ae jin Afeefah ta ambaci jini kawai sai Deejarh ta fashe da kuka faɗi take
"Shikenan zan haihu, waiyo gwaggo na ki taimake ni zan haihu, daga zuwa Birni na shiga ukuna ni Deeje."



Ganin zata tara ma ta jama'a ne yasa Afeefah saurin kamota kai tsaye ta shiga bathroom da ita. Yayin da har zuwa lokacin Deejarh bata yi shiru ba.






"Ke deejarth kiyi shiru kiji abin da zan faɗa miki mana, kina kuka taya zakiji please my Deejarh wiping your tears okay."



Hannu takai ta sha re hawayen sannan tac e nayi.


Murmushi Afeefah tayi sannan ta ce ''Yauwa ina ce dai kin san wannan abun da ma ta suke yi duk ƙarshen wata ko?."





"A'a bansan shi ba. Menene shi haka?."



Deejarh ta tambaya. Afeefah ta bata amsa da cewa

"Wannan abun fah wanda idan mace takai shekaru goma sha huɗu ko fi ye da Haka ko kuma ƙasa da Hakan. Idan ta fara yi sai ace ta girma, wai bakisan shi ba?."





Da sauri Deejarh ta ce

"Nasan shi mana shi ne ma wanda Deluwa ta taɓayi a kasuwan garin mu, mutane suna ta kallon ta."






"Okay to shi ne fah yazo miki yanzu ae baki gane ba."

Afeefah ta faɗa hakan da son fahimtar da ita.



Zaro ido Deejarh tayi cike da tashin Hankali ta buɗe Baki ta ce

"Lah Balarabiyar India.!"


Shiru tayi tana zare ido domin kuwa bata san abin da zata ce ba.




Murmushi Afeefah tayi sannan ta ce "Yanzu dai kin fahimci komai ko?."



Da sauri Deejarh ta girgiza kai alamar e,




"Yauwa yanzu bari na fita na barki kiyi abin da zaki iya."


Afeefah tayi maganar sannan ta buɗe ƙofar bathroom ɗin ta fita.




Ganin haka yasa Deejarh cikin sauri sauri ta cire doguwar gown na atamfa dake jikin ta sannan tayi hanging nata Jikin ƙarfen shower curtain, sannan ta wanke duka inda jinin ya ɓata ta sannan tayi wanka gaba ɗaya bayan tayi na tsarki.




Knocking ɗin ƙofar bathroom ɗin da taji ana yi ne yasa tayi saurin ɗaukar orange towel dake saman bathtub ta ɗaura, sannan ta ƙarisa ta buɗe ƙofar Afeefah ce tsaye hannunta riqe da sanitary pads.


Miƙa ma ta tayi "Ga wannan ki saka ina fatan kinyi wankan tsarki?."


"Eh Nayi, amma Balarabiyar India a'ina kika sama wannan abin?."



"Oh wannan Hameeda ce ta bani ae, akwai matsala ne?."


Zaro ido Deejarh tayi tana furta "Shikenan kuma tasani ko?."🥺




Wata dariya ce ta kusa kwace wa Afeefah ganin yadda Deejarh ta zaro ido tana tambaya, danne wa tayi sannan ta bata amsa da faɗin

"Deejarh ni banma san abin da zan faɗa miki ba, ga wannan kawai."



Tayi maganar tana miƙa ma ta sanitary pad ɗin.



Karɓa tayi, har Afeefah ta juya zata fita, sai kuma ta juyo kallon ta tayi sannan ta ce
"Rigar ta ɓaci ne?."


Da sauri Deejarh ta ce "A'a bata ɓaci ba, amma dai dogon wandon ya ɓaci sosai, da kuma pant ɗin."


"Okay to a cikin wannan ledar na hannun ki akwai pant sai kiyi amfani dashi, sannan kuma idan kin fito."

Ta nuna ma ta wardrobe sannan ta ci gaba da cewa

"Ki buɗe ki ɗauki leggings wanda zai miki ki saka, kinji ko?."



"Toh Balarabiyar India na gode highly da kulawarki a gareni."


Murmushi Afeefah tayi sai dai bata ce komai ba, ta buɗe ƙofar bedroom ɗin ta fita.

Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta koma cikin bathroom ɗin.




"Yane feefah bai dai zo ma ta da ciro bah koh?."


Hameeda dake tsaye bakin ƙofar ta tambaya.
Afeefah ta ce "Eh bai zo ma ta da komai ba an goda Allah."





Komawa suka yi Palo sannan suka zauna, Hameeda saman 3sieter Yayin da Afeefah ta zauna saman 2, tana faɗin.




"Auntie Hameeda jiya fa, naga ɗaukar firan da kika yi da wannan budurwa da tayi rashin nasara wajen gasar SARAUNIYAR KYAU matakin jahar Kano na shekaran jiya."




Murmushi Hameeda tayi ta ce

"Oho Juwairiya Jabir Bici, ae ina faɗa miki Afeefah Yarinyar ba ƙaramin tausayi ta bani ba, shiyasa ma saida Nasan Yadda nayi Dad yamin Hanya Nayi fira da ita cikin asibitin."



"Aikuwa abin dai akwai tausayi domin saida na kusa ma ta kuka a lokacin da naji labarin ta fa."

Cewar Afeefah, Hameeda ta ce "Ae shi ne ma Babban dalilin da yasa nayi fira da ita, domin ƙara wayar da kan mutane, yanzu kamar ita Juwairiya kaf Gidan su fa, wai YaYanta ne kawai yake mara ma ta Baya, ni banga amfanin mahaifiyar su ba Wallahi, menene amfanin uwan da ba za ta tsaya taji matsalar Yaranta ba, ae babu yanzu da Abin yazo da tsautsayi fa, duk da ba fata ake ba, ace ita Juwairiya ɗin wannan faɗin da tayi ta sama cardiology ko kuma wani ƙaton ciwon fah?.
Da sai dai uwan tayi kukan nadama only."





Ajiyar zuciya Afeefah ta sauke tana faɗin
"Please Auntie Hameeda idan kin san Gidan su, please Gobe zaki rakani, domin kuwa Haka kawai naji ina so naga Yarinyar face to face."



Murmushi Hameeda Tayi sannan ta amsa ma ta da cewa

"Sosai ma nasan Gidan su, dama nima gobe ina shirin zuwa duba ta, saboda Yanayin aikina bai bari naje duba ta ba kinga sai muje tare."





Hmmm wannan Aiki naki ma, ae kina ƙoƙari highly highly domin kuwa idan ni ce, wallah Bana iyawa."


Cewar Afeefah cikin kyaɓe fuska


"Kin ji ki feefah da wani zance, ae gwara aikin jarida akan wannan aikin da kike karanta na likitanci amma fa ganina?."





 Cewar Hameeda.

"Duk da haka aikin jarida kamar zai fi wahala fa."
Afeefah ta kuma faɗa, taɓe baki Hameeda tayi
"Kyaji dashi dai don nidai duk da haka nafi son aikina domin kuwa yana bani nishaɗi obaaa."


"Wani lokacin kuma ya na sakaki kuka ko?."

Afeefah ta kuma maganar.

"Ke feefah rabu dani haka kinji domin kuwa aikine a gabana, na tsaya fira dake zuwa anjima zan fita nida wata Abokiyar aikina Humaira, za muje wani company ne, da ake zargi ana safaran mata da ƙananan Yara a ciki."




Waro Manyan idanunta tayi tana kallon Hameeda da tayi maganar hankali kwance, buɗe baki tayi zatayi magana, sai ga Deejarh ta fito daga bedroom ɗin da take ciki.



Ajiyar zuciya Afeefah ta sauke bata ce komai ba, saima kallon Deejarh da tayi cikin murmushi ta ce

"My Deejarh kin gama ke nan?."


"Eh Balarabiyar India, na kammala."



"Okay yanzu ni wurin Amma zani zaki rakani ne, ko kuwa na tafi nika ɗai ke zaki tsaya anan?."

Afeefah ta Tambaya Deejarh ɗin tana kallon ta.




"Eh zan rakaki wurin Amma ɗin kawai."


Deejarh ta bata amsa. Miƙewa Afeefah tayi sannan ta kalla Hameeda tana cewa

"Auntie Hameeda bari muyi wajen Amma wata ƙila ma karki fita ba zaki gammu mun dawo ba."


Miƙewa tsaye ita ma Hameeda tayi tana faɗin

"Bari nima nabi ku wurin Amma ɗin domin kuwa yau kwata kwata bamu gaisa ba, saboda makaran da nayi."




Gaba ɗaya ɗunguma suka yi suka fita a tare, daga palon kai tsaye suka nufa Hanyar da zata sadasu da part na Amma.






Buɗe ƙofar palon Hameeda tayi sannan suka shiga ciki, aikuwa nan suka Hango ta sanye cikin shiga ta alfarma tana zaune saman tattausar carpet. Yayin da gabanta kuwa Littafai ne kala kala wasu na Addini wasu kuma na Likitoci.
Idanun ta cikin medical glass white color.
Ɗagowa tayi tana amsa sallamar da suka yi, sannan suka ƙariso kusa da ita, gaba ɗaya suma suka zazzauna a ƙasan carpet suna gaisheta, amsawa tayi tana ƙare musu kallo.





Ganin dai kamar yau tsufan nata ya motsa ne, yasa Hameeda faɗin
"Amma Afeefah ce fa, kodai baki gane ta bane?."

Murmushi Amma tayi sannan ta ce "Au au ohoo Afeefah ta Wajen Abubakari ke nan. Na gane ta mana sosai ma, sai dai kuma wannan ta kusa da ita."  Ta nuna Deejarh "Ita ce ban gane ba."




"Okay wai wannan sunanta Khadeejah fa, ita ma ɗiyar Uncle Mai Kyau ce fa, sai dai idan kece baki gane ta ba."


Cewar Hameeda tana kwashewa su Afeefah ido.


"Ke Hameeda ja'irar Yarinya, an faɗa miki niɗin na makance ne ko kuwa?,  wannan kyakyawar Yarinyar da ganinta ba ɗiyar Abubakar bace, ɗiyar Yarona Mai Kyau ne da gani."




Gaba ɗaya fashewa da dariya suka yi na jin abin da ta faɗa wato ba ɗiyar Abubakar bane, ɗiyar Mai Kyau ce. 🤣😂😅





"Kai Amma idan aka ce kin tsufa, sai kice a'a. Yanzu in banda rikicin tsufa, wanene Abubakar?, sannan kuma wanene Mai Kyau?, ae duk mutum ɗaya ko?."




Cewar Hameeda still fuskar ta ƙayataccen murmushi ce saman ta.


"Ae kyaji dashi ja'irar Yarinya ni dai nasan wannan Yarinya ɗiyar Yaro na Mai Kyau ce ehe."


Cewar Amma tana ci gaba da duba littafan gabanta.


Dariya Afeefah tayi tana faɗin "Kai Amma wato dai har Yanzu baki manta Baya ba, kina nan da wannan karance karance naki na littafan Addini da na ɓangaren ki ko wato Likitanci, to nima dai bari na gani ko akwai wanda zan iya karantawa a ciki."



Afeefah tayi maganar tana duba tilin littafan dake gaban Amma kamar wata professor.



Murmushi Hameeda tayi sannan ta miƙe tsaye ta nafa saman sofa ta kwanta a saman 3sieter tana faɗin

"Ae sai kiyi karatu da kyau da kyau ni dai nayi nan."🏃




Kallon Deejarh Afeefah tayi ganin kamar ba ita ba, duk ta nutsu, a Hankali ta kira sunan ta.

"Deejarh."





"Na'am Balarabiyar India."




Ita ma ta amsa, Murmushi tayi sannan ta ce
"Karfa kice zaki sakawa kanki damuwa, domin kuwa da haka aka fara gaba ɗaya, ba kanki fa rau ba."



Deejarth ta ce "Amma Balarabiyar India lokacin da kika fara yi, ya kikayi sannan kuma ya kikaji ne dan Allah?."


Deejarh tayi ma Afeefah tambayar tana dariya.



Sai da tayi tambayar kuma tayi saurin rufe baki, mana kallon Amma, dariya Afeefah tayi ta ce

"Ae indai Amma ce batama san kinayi ba, saboda haka saki jikin ki mutumiyar."


Washe baki Deejarh tayi jin abin da Afeefah ta ce sannan ta kuma cewa

"Ya kikaji ke a lokacin kuma kina ina ne?."




Wani murmushin tuno baya Afeefah tayi tana lumshe ido ta ce

"A Lokacin wai. Eh toh a Lokacin muna ƙasar Jamus ne, ni da Zaynerb da kuma Daddyn.
Ae deejarth ina faɗa miki bazan taɓa mantawa da lokacin ba, tsawon rayuwata, wato dai abin da ya faru shi ne.


Wata Ranar Monday na dawo daga school goye da Backpack ɗita, na fito daga cikin Bus na makarantar mu, wacca ta saukeni a ƙofar gate na gidan mu.
Kamar ance na kalla ƙasa, a lokacin kawai na tsinci kaina da durƙusawa ina kallon white socks dake ƙafafuna, aikuwa me zan gani?.👺
Nan fah naga wani abu kamar jini, kamar manja yana ɗigowa duk yabi ya ɓatamin safa ta, ina faɗa miki bansan Lokacin dana rintima a guje ba, ko tsayawa kula Baturen mai gadi, banyi ba, tunda Allah ya bani sa'a na shiga cikin gidan na dangana da Palo, aikuwa anan na sama Daddy yana duba wasu bayanai cikin laptop. Yayin da Zaynerb take daga can gefe tana Assignment cikin littafan ta na school.
Ae Tunda na shigo palon a guje ban tsaya komai ba. Nayi fatali da wannan laptop wacca Daddy yake aiki ciki. Ban tsaya bah, nanfa nan na shiga birgima ina faɗin shikenan kwanana ya ƙare zan mutu nima wajen Haihuwa tunda Jini yana fito min, shikenan nayi ciki a taimake ni.🙈
A lokacin Zaynerb da ta fahimci komai, in banda dariya babu abin da take min. Yayin da shi kuma Daddy kallona kawai Ya tsayi yi, saida kyar aka samu nayi shiru da kyar da ban baki, sannan ne fa, Daddy da Zaynerb suka min bayanin komai, domin kuwa violence highly highly da nake ciki bai bari na fahimci komai ba, duk da dai lokacin ba wani yawau ne dani ba sosai..."🤣



Tunda Afeefah ta fara zuba zance babu abin da Deejarh da Hameeda dake saman 3sieter suke yi banda dariya, Deejarh harda Birgima a ƙasa tana riƙe ciki saboda mugun dariya. Yayin da Hameeda kuwa sai da ta faɗo daga saman 3sieter da take kwance tsaban dariyar ƙeta.


Shiru Afeefah tayi tana kallon yadda suke dariya babu ƙaƙƙautawa, ita ma kawai saita fara dariyar cike da Nishaɗi.😅🤣😂



Su na cikin Haka sai ga Lailah, Zaynerb, Haleesat, Nainarh, Nailah, da gaba ɗaya Yaran Uncle Yusuf da kuma Haseeya da Mah'eesha Yaran Uncle sagir suma sun shishshigo gaba ɗayan su, gaisar da granny tasu suka fara yi.





Gaba ɗaya tsayawa suka yi suna kallon yadda su Hameeda suke ɓaɓɓaka dariya cike da kamar zararru, yayin da Amma ta zuba musu ido tana kallon ikon Allah.



"Ikon Allah sai Look, toh mu dugu ko kuwa mu tsaya?, domin naga kamar Babu Lafiya anan fa."
Cewar Yasira tana zare idanu.

Ido cike taf da qwalla saboda tsaban dariya Hameeda ta kalle su cikin ɗan dariya take faɗin

"Please ku tsaya, ku zazzauna."


"Ah taya ya zamu zauna bayan kuma kuna dariya sai kace waɗanda suka sama taɓin kwakwalwa. Ni tafiya ma zanyi dama nazo nayi ma Amma sallama ne."  cewar Nailah tana shirin fita.



Ganin Haka Yasa duk suka yi tsit Afeefah ta ce
"Please Auntie Nailah zoki zauna, ae mun gama dariyar, jin Haka yasa gaba ɗaya Ƴan matan suka zazzauna a tsakiyar palon, gaba ɗaya suka gagaisa da Amma ɗin tasu sannan.




Lailah ta ce
"Mu fah har Yanzu Bamu ji abin da Yasa kuke wannan dariyar da muka shigo muka samu kuna yi ba, sai kace waɗanda suka shaqa Laughing gas."




Hameeda da dariyar bai ishe ta ba take faɗin

"Kedai Lailah bari kawai. Wani Labari mukaji wanda ya sakamu nishaɗi."





Wannan kuma wani Labari ne haka, a gaskiya muma a bamu Musha, Zaynerb ta faɗa tana gyara zamanta saman tattausar carpet na Palon.




Hameeda ta ce
"Ae kinma san Labarin, sai dai kuwa idan kin manta."




"Mu dai bamu sani ba, saboda haka a bamu musha."


Wannan karon Yasira ta kuma maganar.

Satar kallon Amma Hameeda tayi sai taga hankalin ta baya kansu, saboda haka kallon su ita ma tayi cikin Dariya ta ce
"Dama kawai Afeefah ta bamu labarin first Period nata fa."





Aikuwa jin abin da ta faɗa gaba ɗaya suka gyara zama sunji gossip.

Yasmin ta ce
"Please Auntie Hameeda bamu Labarin daga ji Abin zai bada jitta highly higher highest ma."



Aikuwa nan bada ɓata lokaci ba, ita ma Hameeda da take sarkin surutu obaa, ta basu labarin da Afeefah ta basu wurin da tayi mistake Afeefah ta gyara ma ta, babu ko kunya.





Habba ae nan gaba ɗaya ƴan matan wurin suka kwashe da dariya. 😅🤣😂




Mah'eesha ta ce, Bayan sunyi shiru.

"Allah sarki Rayuwa, Auntie Hameeda da kika bada wannan Labari sai naji na tuna Baya, lokacin muna Boarding school nima haka nayi fama, first period nawa lokacin yazo min ana cikin tsakiyar Assembly, ae lokacin naci wuya ba kaɗan ba, abin ku da babu yawo sosai. Haka na dingi kuka, sai yanzu da naji wannan Labari sai naji na tuna Baya, sai naji dama ace baya zata dawo, habba ae kawai Abin Ba'a magana domin kuwa Rayuwar ƙuruciya tayi wallahi, Barin ma dai ace muku school Life, habba hummm." 🔥




Mah'eesha tayi maganar tana lumshe kyawawan idanun ta. Alamar dai tayi missing Baya highly highly.





Yasira ta chafe zancen da cewa
"Ke dai Mah'eesha Bari kawai. Abin cike yake da nishaɗi obaa."




Habba nanfa suka buɗe sabuwar fira tsakanin su.
Yayin da kowa sai ya bada Labarin shirmen da ya tafka a lokacin ƙuruciya, Especially ma Lokacin suna school kuma ace J.s.s.😘

Kowa bada labari yake a cikin su cike da Nishaɗi harda Haleesat da take miskilar gaske, ae ita ma tuni ta a je miskilanci a gefe aka shiga fira da bada Labari da ita. 😛







"Kun kammala kuwa?, nace kun kammala fitsarar taku Ja'iran Yaran zamani kawai, wato Babu kunya kunzo kun sakani, ni kakarku mahaifiyar ubannin ku a tsakiya, wato kowacce taji da farar fuska, sai kace zabiya, kuna bada Labarai koh?.
Wato ga marasa kunya har Gida, zakuci ƙaniyar ku domin kuwa da Babannin ku zan haɗaku duka."🙄





Gaba ɗaya tsit shiru suka yi suna jin Yadda kakartasu take ƙare musu tsiya.


Yayin da Lailah da Yasira da kuma Mah'eesha Waɗanda sune nan Ja'iran ciki sai faman tiƙa dariya suke yi.




"Eh dariya koh? Kuyi dariya da kyau, ke Lailah ɗiyar Abubakar kar kiga Sunanki Lailah, kiyi Tunanin zanji tsoron ki, dan kina Lailah, a'a Lailah kike ba dare bah."🌚
Ke kuma, ta nuna Deejarh wacca Tayi tsuru tsuru saboda yadda taji mararta ta ɗauki ƙugi.

Na dawo kanki wato kece wacca take al'adar ko kuwa ba ke ce ba, naga kinyi tsit kina kallona?."




Tayi maganar tana kallon Deejarh.

Cike da jin raɗaɗin ciwo Deejarh ta amsa da

"Eh Ni ce,"

Amma ta ci gaba da cewa abin da nakeso dake kije ki sama Ruwan zafi a gora ki ɗaura a saman cikin ki, sannan kuma ki dinga yawan shan ruwan zafi akai akai harki kammala kinji?."



Da toh kawai Deejarh ta amsa.



Miƙewa Afeefah tayi sannan ta kalla Deejarh ta ce

"Taho muje na rakaki domin ki fara tun Yanzu."

Aikuwa da sauri Deejarh ɗin ta miƙe sannan tabi bayan Afeefah suka fita.



A hanya kafin su ƙarisa ɓangaren Auntie Suwaiba ba, suna tafiya duk da ciwon da Deejarh take ji bai hanata kallon Afeefah ba, sannan ta ce

"Balarabiyar India wai dama fassarar sunan Lailah Yana Nufin Dare ne?. To ke, Kuma Menene fassarar Sunanki?."





Afeefah tana tafiya batare da ta juyo ba ta ce

"Eh Haka Lailah Yana Nufin Dare. Yayin da Afeefah kuma Yake Nufi 'TAGARI.''


"Aikuwa dai Sunan ya cancanta dake it's really deserved to you highly."

Cewar Deejarh cikin murmushi, Buɗe ƙofar palon Afeefah tayi Bayan sun ƙarisa sannan suka shiga ciki domin aiwatar da umarnin Amma ɗin.





**

Da Marece wuraren ƙarfe _-_05:00pm_-_ gaba ɗaya Ahalin Uncle Yusuf suka yi sallama da mutanen Gidan har dasu, Afeefah sannan suka tafi Airport domin komawa BORNO STATE.


Tare da Rakiyar wasu daga ƴan Gidan, Yayin da ita ma Nailah ta bisu Airport ɗin zatayi jiran awa ɗaya a Airport ɗin domin komawa Lagos Birnin da take Aure ita ma da yake akwai wata ƙawarta wacca take ma'aikaciya ce anan Airport ɗin.
Yayin da ita kuma Nainarh sai zuwa gobe idan Allah ya nufa zata bi Jirgi ita ma domin komawa ƙasar Auren ta wato Eritrea.









*ABUJA*
             *NIG£RIA*







Misalin Ƙarfe Tara Na Dare _-_09:00pm_-_



Zaune yake saman ɗaya daga cikin Royal sofa's waɗanda aka ƙawata qaton palon nashi dasu.



Hannu sa kuwa tsadaddiyar wayar sa ce yana latsawa, a zahiri zaka yi tunanin tsadaddiyar wayar hannun sa yake kallo.
Yayin da kuma cikin zuciyar sa tunani yake yi shin ya kira ta ne, ko kuwa dai ya barshi kawai.😀

Haka kawai yaji yana buƙatar jin daddaɗar muryarta cikin daren nan, ko da suna Yara yafi shiri da ita sama da kowa cikin Yaran Uncle's nasa da kuma Mamy's ɗin sa.



Shiga Contacts na wayar nasa ya yi sannan ya lalubo lambarta wanda Ya yi saving da, mí afortunado polola { My lucky girlfriend} daga yakai hannu zai danna call, sai kuma ya fasa, daga yakai hannu zai danna call sai kuma fasa, Haka ya shigayi yana maimaita wa, aikuwa cikin mistakenly ya danna kira.

Waro ido Ya yi waje ganin kira ya tafi harta fata ringing, ke nan dai babu damar katse wa tunda kiran ya rigatda ya tafi.


Ajiyar zuciya ya sauke ganin Tayi picking call ɗin, har tana rangaɗa sallama cikin daddaɗar muryar ta wacca duk ta karaɗe palon.






"Hello.! Hello Yaya Maleek are hearing me, shin kanajina kuwa?."


Ɗan Shiru Ya yi Yana kallon wayar domin kuwa baisan abin da zaice ba, sai da yaji ta ƙara magana sannan ya fara maganar shima.



"Ba'a koya miki Gaisuwa bane, kin wani ishe mutane da hello hey."



*Husnee*

Da sauri ta ciro wayar dake manne a kunnen ta domin ganin anya kuwa Yaya Maleek ɗin ne, aikuwa dai shi ne domin kuwa sunan da tayi saving lambar sa ne, wacca tayi saving da 'My Yaya Maleek' ✴️
Bayan ta karɓa wurin Lailah ne.

Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta ce "Good evening Yaya Maleek, Fatan kana Lafiya, ya gidan?."


Tayi maganar ƙasa ƙasa.
Daga ɓangaren sa kuwa ƙayataccen murmushi Ya yi sannan Ya ce
"Dama kawai na kira ki ne, domin ki rairamin waƙa."



Zumbur ta tashi zaune daga saman bed tana ƙara ƙanƙame wayar bakinta na furta.
"YaYa Maleek waƙa kuma?, toh ae ban iya ba, please ka canza wani abun amma banda waƙa pleased."



Ki shin giɗa Ya yi sannan ya bata amsa da cewa

"Eh mana kin iya, domin kuwa jiya ma da kika ce zakije tunani domin yanke hukunci nasan rawa da waƙa kawai kika je kika yi domin kuwa a Yadda gashin kanki yake zubowa yana rufe fuskar ki, da kuma Yadda mayafinki Yayi ƙasa da inci Biyar bisa baya, na tabbata rawa da waƙa kika yi, saboda Haka Malama Raira min waƙa ina jinki. Idan kuma bah Haka ba, bazan ƙara kiran ki ba, har Sai an ɗaura Aure, kuma Idan ke kika kirani bazan ɗauka ba, ko kuma na sakaki a Blacklist."🥵




Shiru Husnee tayi tana sauraron ikon Allah, sai da taji ya yi tsit alamar dai ita yake sauraro. Sannan ta sauke wata Nannauyar ajiyar zuciya, gyaran murya tayi, ta muka gyara zama, tana ƙara ƙanƙame wayar, sannan ta fara raira waƙa kamar Haka.







"Ya-masoyi-ina-jiranka-kazo-da-sauri-zuciya-tana-mini-ɗinlin-ɗinlin.."


Da sauri Maleek Yace
"Aikuwa bazan zo ba, saboda haka Malama canza wata, wannan batayi ba sam.



Turo Baki Husnee kamar zatayi kuka Ta ce
"Toh Yaya Maleek yanzu wanne kakeso nayi?."

Yana Lumshe kyawawan idanun sa Yace

"Koma wanne ne, kiyi."

Shiru tayi sannan ta fara Raira Wata waƙar kamar Haka.


"Eh-Zuciyata-kyauta-ka-riƙe-na-baka-babu-abin da-zaisa-na-naguje-na_barka.😅




"Aikuwa bazan Yarda ba, tunda waƙar Sani Ahmad kika Lauya, canza wata kawai ko kuma na gimtse kiran Yanzu nan."

Cewar Maleek yana murmushi, ita ma Husnee murmushi tayi ta ɓangaren ta wato dai Yaya Maleek yana buƙatar jin daddaɗar muryarta sosai ne, shi ne zai wani ce tayi waƙa ko?, aikuwa zataitayi har sai yace ya gaji daji. Nutsuwa ta kuma yi sannan ta fara.






"Ah_soyayya_dole_sai_kun_ɗanyi min_uzuri_Maleek_ne_shi ne_wanda_ni_Husnee_nake_son_aure_maleek_neh_maleek_neh_kaine_dai_kai_ɗaya_tun_a_dare_safiya_soyayya_kah_biya_ka_ƙaramin_lafiya_banajin_zance_na_kowa__ah_kanka_na_yadda_na_zama_gawa_na_ƙare_nazari_nah_ɗau_alƙawari_zancen_ayyiriri_aure_da_kai_zamuyi_bidiri_lissafina_haka_yake_soyayya_ta_haka_take_bana_ɗaukar_ta_da_sanyi_sanyi_nafi_sonta_da_zafi_zafi_highly_highly_.🤣😅😂





Fashewa Maleek Ya yi da dariyar da yake ta ƙoƙarin riƙewa yana faɗin

"Ah gaskiya wannan waƙa tayi daɗi sosai, duk da cewa ita ma waƙar Umar_M_Shareef ce Mai taken Ummitah kika Lauya, amma dai kinyi ƙoƙari highly highly sannan kuma..."



Ae Tun kafin Ya kuma cewa wani abu Husnee ta riga shi da cewa, "Ae Barima kaji Yanzu ƙasar India zan koma kaji salon su humm uhumm."

 Tayi gyaran murya sosai sannan ta fara.





"Munda_sona_hai_tu_kudi_main_crore_di.
Munda_sona_hai_tu_kudi_main_crore_di.
Tere_liye_maine_pehli_wali_chod_di.
Kahe_tujhe_Jawani_kar_shuru_kahani.
Tu_kar_mujhe_tang_sohneyahhh.

Sabko_na_kardi_tujhko_haan_kardi.
Main_jana_tere_sang_sohneyahhh......


Hmm_mere_jaisa_aashiq_hai_koi.
Banda_main_classic_hai_koi.
Main_jana_tere_sang_sohneyahhh


Mere_kad_kaath_sa_hai_koi_sir_phire.
Jaat_sa_hai_koi..
Tere_dad_se_lad_jaye_hai_koi.
Fir_pair_bhi_pad_jaye_hai_koi.


No_fat_fat_left_to_right_like_dhoom_chak.
Chak_dhoom_chakkkk
Chak_dhoom_chkkkkk." 😅🤣







Tunda ta fara Raira wannan waƙar na ƙasar India Maleek Ya yi tsit Yana sauraronta, har sai da Yaji Tayi shiru tana sauke ajiyar zuciya sannan Yace

"Kin gama kuwa?."



Washe baki Husnee tayi tamkar tana kusa dashi ta ce

"E, Yaya Maleek na gama ina fatan dai tayi daɗi?."🙄



"Hmmm ae ina faɗa miki banma fahimci komai ba, cikin waƙar nidai kawai naji ana tayi ana tayi."

Maleek Ya yi maganar yana murmushi.



Dariya Husnee Tayi sannan tana faɗin

"Kai Yaya Maleek waƙar film ɗin India ne fa, nah cikin wannan drama ɗin Wanda KARTIK_AARYAN, YaYi shida KRITI_SANON, ah kafcen su na $hehzahdah.
Tofah shi ne nayi maka waƙar magana suke akan banbancin soyayya da kuma kuɗi fa.🙄
Amma Yanzu bari na ƙirƙiro ta musamman nayi maka ta fara.



"Tahoo zoo garenii Yakai wannan masoyina, mai wahalar da zuciyata da bahamaƙiyar ƙauna, kazo ina jiran ka, kaji kuwa tahoo zoo garenii Yakai kyakyawan ƙayataccen saurayi Wanda Ya sace heart ɗita da masifar qaunar sahhh."🤭

 

😇😇😇




Shiru tayi tana sauke ajiyar zuciya na dogon numfashin da Taja sannan ta ce "YaYa Maleek, Yaya Maleek to yah kaji wannan tayi kuwa?."



Maleek dake faman tiqan dariya ƙasa ƙasa tunda ta fara Ya yi murmushi sannan yana faɗin

"It's Nice, 🙂 it's Very Amazing,😂 ae ina faɗa miki wannan waƙar taki ko Shakirah mawaƙiya ba zata gwada miki iya waƙa ba."


Ya yi maganar yana kuma ɓoye Dariyar sah.



Washe Baki Husnee tayi Sannan tana cewa
 
"YaYa Maleek ko kana so na ƙarayi maka wata kalar ce? Kaji salon iya saloh na burgewa da saka nishaɗi?."😘



Da sauri Maleek ya bata amsa da cewa

"A'a  Doctor a ɓangaren waƙa Husnee na gode sosai. Yanzu abin da nakeso dake ki kashe wayar sannan kiyi addu'a ki kwanta kinji?."


Husnee tana dariyar nishaɗi ta amsa masa da
"Toh amma Yaya Maleek idan na kashe kiran, gobe zaka kirani kuwa?."




"Eh," Ya bata amsa sannan tayi masa sallama kana ta kashe wayar ta.

Ajiyar zuciya Maleek ya sauke yana kallon wayar. Yayin da Fuskar sa take ɗauke da ƙayataccen murmushi na musamman cike yake da nishaɗi. Wanda shirmen Husnee ya jefasa ciki.


A fili ya furta

"Ina ƙaunar ki Husnee SARAUNIYATAH I Love You, For The All My Heart My Lucky Girlfriend..GN."👋💃











*KANO-STATE*







Misalin ƙarfe uku da rabi na ranar washe Garin zuwan su Afeefah Kano ita ma Nainarh tabi jirgin etritea domin komawa ƙasar Aurenta. Yayin da ta sama rakiyar Afeefah da Lailah da kuma Mah'eesha sai Deejarh.






Horn driver ya buga da ƙarfi ganin Mai gadi bai zo ba, da sauri gate man ɗin tare da da wasu securities suka wangale gate na gidan da sauri.



Sannan Driver ya cinna Hancin Motar cikin Katafaren Gidan na Uncle Sagir, sai da ya kammala parking a wurin da aka tanadar domin yin parking na motocin Gidan, sannan suka buɗe Motar suka fiffito a tare suka nufa ƙofar palon Gidan.




Afeefah tana shirin kai hannu ta buɗe ke nan saiga Hameeda ta fito daga ɓangaren su na yaran gidan mata.


Murmushi Afeefah tayi Hango Hameeda sannan tana cewa, Bayan Hameedar ta ƙariso wurin da suke tsaye

"Yauwa Auntie Hameeda dama fa ke nake nema, na ɗauka ma kina ɓangaren Auntie Suwaiba ne ae."





"A'a sauke kawai domin kuwa ina nan a ɓangaren mu yanzu ma da kika ganni Gidan su Juwairiya Jabir Bici nah nufa dama Allah, Allah nake na same ki kafin ki fito raka Auntie Nainarh sai kuma kafin na fito harkin tafi, Yanzu dai zance Ya ƙare sai mu ɗunguma muje Gidan kawai tunda kince zakije ko?."



Hameeda ta ƙare doguwar maganar tana saɓa backpack nata irin na ƴan Jarida masu neman Bayanai.





Murmushi Afeefah tayi sannan tana faɗin



"Okay muje kawai babu damuwa don a shirye nake."




Kallon Lailah da Mah'eesha da kuma Deejarh tayi sannan ta ce

"Bari muje wani guri mu dawo."


Cikin sauri har suna haɗa baki suka ce

"A'a ae koh ina ne muma zamuje domin Yawo muke ji highly."


 Lailah ta ƙara da cewa badai wannan Yarinyar da ta faɗi wajen gasar SARAUNIYAR KYAU na wannan Jahar Ba, aikuwa indai ita ce zani domin kuwa jiya da dare naga Labarin a Facebook."






Hameeda ta ce

"Ita ce badai Juwairiya Jabir Bici ba, ae wannan Labarin Ya zagaye duniya sosai."



Mah'eesha ta ce

"Ah gaskiya nima za biku saboda ina so na ganta ido da ido, domin kuwa sai da nayi Hawaye da jin labarinta."




Ita ma Deejarh ganin haka yasa ita ma da sauri ta ce.

"Nima zan biku."




"It's okay tunda na fahimci kowa ma so yake yi yaje, kawai kuzo mu tafi kawai tun kafin wasu su ƙaru, domin kuwa naji ita ma Haseeya tana cewa zataje."




Hameeda tayi maganar tana nufar hanyar parking, gaba ɗaya ɗunguma suka yi suma suka nufa parking lot ɗin, Afeefah na faɗin

"Aikuwa dai Haseeya ba zata sama damar zuwa ba tunda Auntie Raheemarh ta riƙeta da aiki."


Hameeda dake shirin buɗe mota ta ce
"Ke nan dai kun biya ta gidanta daga Airport ɗin ko, no wonder naji kun daɗe sosai, ashe akwai wurin da kuka biya ne."



Tayi maganar tana tayar da Motar sannan ta karya kwana ta nufa gate Lailah tana bata amsa da

"Ae dan ma Afeefah ce ta wani ce mu dawo Gida akwai wurin da take so taje, badan haka ba, ae dama har Gidan Yaya Shahid sai munje."




Mah'eesha ce wannan karon tayi magana Bayan gate man ya wangale musu gate sun fita ta ce

"Ae wallahi da sai dai kuje ku kaɗai domin kuwa ni babu inda zani, saboda wannan baƙar matar tasa ba tasan Menene mutunci ba sam."


Lailah ta kuma cewa
"Ae badan ita zamuje ba, saboda Yaya Shahid zamu je, kuma tunda naji kince Haka toh wallahi sai naje bari mu dawo daga nan inda zamu, sai naga ƙarshen rashin mutunci mu da muke siyan rigima da kuɗin mu ma."




Murmushi kawai Afeefah tayi sannan ta ce
"Ah gaskiya Dangin miji su nada matsala tasu ta musamman, wani lokacin zata iya Yiwuwa Mah'eesha kune baku biyo ma ta ta inda zata dinga muku kirki da mutun taku ba."



Hameeda dake ƙoƙarin karya kwanar da kai tsaye zai sa dasu da Street na Yankin da unguwan su Juwairiya Jabir Bici yake. Tayi murmushi tana faɗin


"Hehehh Afeefah ke nan bazaki fahimta bane kawai, domin kuwa wannan matar Yaya Shahid ɗin tafi ƙarfin duk tunanin ki Allah kuwa."


Afeefah mayar ma ta da martani ta hanyar faɗin

"Kune dai bazaku fahimta ba, domin kuwa mafi yawan samun rashin fahimta da ake yi tsakanin dangin miji ko kuma ƙannin sa da matar sa. Tofa mafi Yawa Laifin su waɗannan Dangin mijin ne fa, amma fa a Tunanina aha."😁






"Hahaha feefah mai kyau ke dai kawai tunda bazaki fahimci abin da ake so ah ganar dake ba, Bari kawai nayi shiru, duk Ranar da tsautsayi yakai ki zuwa Gidan zaki fahimta gaskiyar Mah'eesha ne."



"Toh Allah ya kaimu Gobe ni kuma zan biku zuwa Gidan domin nah ganewa ido na komai."


Cewar Afeefah daga haka kuma motar ta ɗauki shiru suka ci gaba da tafiya dama ita Deejarh ciwo sama sama da taji mararta tana yi ne yasa ko tsunduma Bakinta cikin firar tasu ba tayi ba.😌






   


"Dakata ina ga wannan ne, Gidan tsayawa driver na a daidaita ɗin Ya yi a ƙofar gate na wani makeken Gida, sannan suka fito.
Miƙa masa kuɗinsa tayi sannan ta juya tana kallon ɗayar Budurwar wacca suka zo tare tana faɗin.

"Mu shiga ciki ko."

Murmushi tayi sannan ta ce "Muje tohm."


Kwankwasa ƙaramar ƙofar gate ɗin tayi Sannan gate man ya buɗe Suka shiga ciki.




Sai da suka isa dai dai ƙofar palon Gidan sannan budurwar ta kalla ƴar uwan tafiyarta ta tana cewa

"Yanzu Humaira idan muka shiga mai zamuce ne?."




Murmushi Humaira tayi tana bata amsa da cewa

"Kawai zamu ce ne munzo ganin Juwairiya Jabir Bici domin mu tayata jaje, ko kuwa dai ke Jiddarh ba zaki iya faɗar Hakan ba ne?."




Ajiyar zuciya Jiddarh ta sauke tana shirin magana aka buɗe ƙofar palon saboda haka basu tsaya jiran komai bah
 suka shiga ciki.




Nuna musu kujera budurwar da ta buɗe ƙofar tayi, sannan bayan sun zauna ta ce

"Wurin Auntie Juwairiya ku ka zo ko?."


Tayi musu tambayar daga inda take miƙe.

Murmushi Jiddarh tayi sannan ta ce "Eh wurinta mukazo fatan dai tana nan?."



Murmushi ita ma budurwar tayi sannan ta ce

"Eh tana nan barima na kira muku ita kawai."


Tayi maganar tana nufar staircases.



Ya ye Niƙab ɗin da ta rufe kyakyawar fuskarta dashi, Jiddarh tayi tana faɗin

"Zufa wallahi sosai."


Dariya Humaira dake latsa wayarta tayi tana faɗin

"Ni dama ban san gulmar da ya saka kika wani sanya Niƙab ba sai kace wata ɓarauniya, ba sarauniya ba.🥰




"Kedai kawai Humaira Ba za ki fahimta bane, kawai saboda tsaro na sanya fa badan tsoro ba."

Ta ƙarishe maganar tana kallon kyakyawar budurwar da ta sauko palon da suke zaune ita da wannan budurwar da ta buɗe musu ƙofar.



"Sannun ku fatan kuna lafiya. Ya Hanya."



Budurwar tayi musu maganar a lokacin da take zama a kujerar dake fuskantar nasu. Yayin da ita ma ɗayar da alama ƙanwarta ce ta zauna kusa da ita.


Fuska washe Jiddarh ta amsa da cewa


"Lafiya qalau wallahi,bFatan kema Hakan, sannan kuma ya jiki, ya aka ji da al'amuran?."





Tayi maganar tana ƙarewa Budurwar kallo ta cikin Niƙab ɗin fuskarta, ta fahimci ba wata Babba bace cancan domin iya Lissafinta zasu iya zuwa sa'anni da ita.



"Jiki kam Alhamdulillah, Ina Godiya sosai da nuna kulawar ku a gareni."



Cewar Budurwar cike da fara'a.



"Aunty's please ga abin taɓawa fa, Bismillanku fa."


Budurwar tayi maganar tana musu nuni da saman center table na Palon.



"Mun gode sosai."


Cewar Jiddarh still bata cire Niƙab dake fuskarta ba.

Ƙarisawa Humaira tayi Sannan ta ɗauki Juice a cup daga saman tray dake kan center table ɗin, sannan ta koma ta zauna suna ɗan taɓa fira sama sama kai daga ganin Yanayin da suke kasan ba wani sabo ne a tsakanin su ba.





Knocking ɗin ƙofar palon da suka ji ne. Yasa budurwar da ta buɗewa su jiddarh ƙofar palon.
Nufar ƙofar tana faɗin
"Mudai Gidan nan muna shan baƙi sosai, gashi kuma Mamy bata nan."

Ta ƙari sa maganar a daidai lokacin da ta buɗe ƙofar tana kallon kyawawan Ƴan matan da suke tsai tsai ye bakin ƙofar su Biyar, mace ɗaya ta gane cikin su.



Da sauri ta matsa gefe domin basu Hanya tana faɗin

"Lah Auntie Hameeda kece?, barkan ku dai ku shigo Please."

Ƙari sa shiga palon suka yi gaba ɗaya sannan suka zazzauna.



Kallon su Humaira bayi babu shiri ta waro idanu tana faɗin
"Kaga wani katari Hameeda Sagir kece dai ko kuwa gizo ne?."


Murmushi Hameeda tayi bayan ta zauna a kujera 2sieter ita da Lailah. Yayin da Afeefah da Mah'eesha da kuma Deejarh suka zauna a 3sieter kusa da Jiddarh wacca har zuwa lokacin bata cire Niƙab dake fuskarta ba.


Da yake palon ƙatone kuma kujeru set Biyu ne, shiyasa ya wadace su duka.



Ta ce

"Ni ce mana Humaira kice dai kuma kunzo ganin Juwairiya Jabir Bici ce, me yasa bakizo da Jiddarh ba ne."


Tayi maganar tana kallon Jiddarh dake zaune da alama bata gane ko wacece zaune ba.



Murmushi Humaira tayi sannan ta nuna ma ta Jiddarh ta ce

"Ga Jiddarh ɗin, anan gulma ne kawai ya sakata rufe fuska da niƙab, hala dai baki gane ta bane?."




Da sauri Hameeda ta kalla Jiddarh tana washe Baki ta ce

"Ikon Allah kunga dai wani katari again wato ga sᴀʀᴀᴜɴɪʏᴀʀ ᴋʏᴀᴜ ta Abuja anan, sannan kuma ga sᴀʀᴀᴜɴɪʏᴀʀ ᴋʏᴀᴜ ta Kano State. kunga wani ikon Allah ko?."


Tayi maganar tana kallon Afeefah sannan tana ci gaba da faɗin

"Feefah Mai Kyau gafah Jiddarh SARAUNIYAR KYAU ta nan Kano State."


Sannan ta kalla Jiddarh still murmushi ɗauke saman kyakyawar fuskarta take cewa

"Lah Jiddarh kema dai ga Feefah mai kyau SARAUNIYAR KYAU ta madinatul Abuja City anan. saboda Haka What next?."🔥💃🔥



Da Wani irin mugun sauri zuciyarta na mugun luguden bugu, Juwairiya Jabir Bici ta ɗago dara daran idanunta tana kallon su gaba ɗaya.🙄

Yayin da ita ma Afeefah fuska ɗauke da ƙayataccen murmushi ta juya tana kallon budurwar dake zaune wacca Hameeda ta kira da Jiddarh SARAUNIYAR KYAU ta kano State.🥵


Yayin da Lokacin Ya yi daidai da ita ma Jiddarh ta cire wannan niƙab ɗin dake fuskarta, ta juyo tana kallon Kyakyawar Budurwar wacca ita ma Hameedah ta kira ta da ita ce SARAUNIYAR KYAU ta Madinatul Abuja.💥💃💥



     💫💫 Ⓦⓗⓐⓣ ⓝⓔⓧⓣ?💫💫




Menene zai faru gaba a tunanin ku?.
Akwai chakwakiyoyi fa a gaba domin bana ce chakwakiya ɗaya ba🔥🔥

Na farko dai
Shin Momy Rafi'at zata rabu da su Afeefah kuwa, ko dai still akwai abin da take shiryawa?😟
Na Biyu
Shin bakwa tunanin kashe Hajarah akayi bawai mutuwa tsakani da Allah tayi ba😓
Na Uku
Shin wanene ko wacece ta shirya sace Haleesat Rashid Rayyan da aka yi, Menene Kalmomin guda shida da aka rubuta a hannun Haleesat Rashid Rayyan suke nufi?😔
Na huɗu
Shin Juwairiya Jabir Bici zata haƙura ne da burin ta son Zama SARAUNIYAR KYAU ko kuwa ya ya zata kaya?🤔
Na Biyar
Wai shin ba za ku so sanin Labarin Soyayyar Zaynerb ba?, Wani kalar ƙalu bale ta fuska da ya janyo ma ta shiga shaya shaye?😰
Na shida
Shin ba za ku so sanin Wacece zata zama Miss Nigeria ba wai, Afeefah Mai Kyau ce ko kuwa dai Jiddarh Komai Naga ne?🤑
Na Bakwai
Shin wanene Bardia Wacece Budurwar da yake gani a video?🙄
Na Takwas
Wai shin wanene wannan Official ɗin ne?🤔
Na Tara
Wai Wacece Heart Cheng Jung ce wani kalar alaƙa ce tsakanin ta da Sunainah?🥺
Na Goma
Wai shin Auren Maleek da Husnee zai yiwu kuwa?…..
Wanene Likitan ƙasa da ƙasa da ya taimakawa Maleek a Rasha ne??????????🌀🌀🔥🔥


*You duk amsoshin waɗannan tambayoyin suna tafe cikin Takun Tsakiya wato SARAUNIYAR KYAU ba*

*Ke dai kawai ki hanzarta bi*
*With This Details.*

_-_-_-_-_-_
*The Phone Number*
*08081129487*
*The Acct Number*
*8081129487*
*The Bank Name*
*Palmpay Bank*
*The Acct Name*
*Khadeejarth Sabi'u Yahyah*


~Karku bari a baku labari fa🤩~

~*SARAUNIYAR KYAU*~🔥🔥Takun Tsakiya_-_
*Iya kuɗin ki iya shagalin ki Hajiya*




ALHAMDULILLAH END OF BOOK 1
______________________________________
DOMIN SAMUN CIGABAN LITTAFIN SARAUNIYAR KYAU BOOK 2, MUTUM ZAI BIYA 500 NE, VIP KUMA 1000, WANDA YA SHIRYA BIYA SAI YA TUNTUƁI NUMBER TA, 08081129487 KO CHAT TA HANYAR DANNA CHAT BUTTON 👇

KADA KU BARI ABAKU LABARI FAH 🔥