Skip to main content

Tsautsayi - Hausa Novels

 

🔥 *TSAUTSAYI* 🔥

Chapter 1

Aunty Sauda Aunty Sauda, yarinyar take ta maimaitawa tun kafin ta kai ga shigowa cikin falon, Mommy dake zaune tana danna waya, ta ajiye wayar a gefe kawai ta zubawa yarinyar da ta shigo cikin falon da gudun ta ido, Allah ya shirye ki Baby yanzu dan Allah ban hana ki yiwa mutane irin wannan kiran ba, baki ta turo kai Mommy bafa ke na kira ba, gidan ku nace ai nasan bani kika kira din ba, baki ta tabe kamar zatai kuka, ta fara diddira kafa a kasa.


Ganin haka Saudat dake zaune a gefe tana kallon su, ta taso ta kama hannun ta, zo nan Baby na rabu da Mommy ita kullum tana cikin neman fada, zo nan ki fada min abinda kike son fada, kujerar da ta taso suka koma suka zauna, sannan ta kamo hannun Babyn to fada min menene, ba wannan Uncle din bane yazo kinga ma har ya kawo min chocolate, ta fada tana bude mata ledar dake hannun ta.

Wane Uncle ke nan, wannan kyakykyawan,
yanayin yanda tayi magana duka sai da suka dara, Mommy ta kalle ta, kai Baby yanzu ke har kin san ma kyau, eh mana wllh yana da kyau sosai, uhmm yama sunan sa ta fada tana cije baki, wai ita tunani, yauwa na tuna Uncle Abdul, tana fadin haka, Saudat ta hade rai, yauwa Aunty Sauda yace ma na kira ki, ke kuma sai kikace masa me, nace masa to, dama kuwa yanzu na baro ki a falo kina kallo.

         Tsaki taja, kije kice masa nayi bacci, baki ta rike kai Aunty Sauda wllh babu ruwana, Daddy na ya hana ni karya, Mommy ce ta kalle su, yauwa yarinyar kirki, kinga dai kina so ki koyawa yarinya karya, wai dan Allah Saudat me yake damun ki ne, nifa banga aibun yaron nan ba, yaro dashi, matashi, ga kudi ga kyau ga ilimi ga tarbiyya, gashi ya fito daga babban gida da babu family da zasu ki su so su hada zuri'a dashi.

         Babu fa abinda yaron nan ya rasa, amma kin zauna sai faman batawa kan ki lokaci kike shima kina bata masa, banda ma dai yaron nan yana son ki a samarin zamanin nan da kan su yake rawa har zasu tsaya suna da duk wadan nan abubuwan da na lisafo, su tsaya wata ya na ja musu aji.

       Hmm kar na zake da yawa na manta ni uwa ce, amma dai Ina mai baki shawara kiyi tunani, daga haka ma ta mike ta haye sama ta barsu a falon, jim ta dan yi a wajen kana kuma ta mike ta ware dan kwalin abayar dake jikin ta, ta yafa shi a kanta tayi hanyar waje ta bar Baby zaune ta baje uban sweet da chocolate din daya kawo mata dan gwana ce wajen son zaki.

    A zaune ta same shi akan motar sa yana kada mukullin motar a hannun sa, sai da ta kara hade fuska kafin ta isa wajen nasa, shi kuma yana hango tahowar ta ya diro daga kan motar ya tsaya yana jiran isowar tata.

          Kafin ta karaso ta kare masa kallo, gaskiya ne abinda kowa yake fada mata akan sa, tabbas bashi da makusa ta ko ina, gayen ya hadu, itama tasan tayi dace da miji idan har ta amince dashi, sai dai ita abinda suka kasa fahimta ko kadan bata so ta auri namijin da ya hada komai kyau ilimi kudi da wayewa.

 Tsautsayi Part (2)
Aisha Muhammad

            Dan ita yanda Allah ya halicce ta mace ce mai matukar kishi, idan tana son abu tofa ko kallon sa bata fiya son wani yayi ba, shiyasa ko kadan take ganin Abdulmalik din bai dace da irin tsarin namijin da take nema ba, tafi son idan zatayi aure ta auri wanda ma bai kai rabin rabin ta a kyau ba, yanda ko waje sukaje ana kallon su za'ace kai wannan yayi sa'ar mata, sabanin Abdul din da ta tabbata duk inda zasu shiga kafin a kalle ta ace yayi sa'a shi za'a fara kalla ace lallai tayi sa'ar miji, dan ko a hasken fata baza a taba hada hasken fatar ta data Abdul din ba, duk da itama tana cikin jerin farare amma dai nashi farin daban ne.

        Da wannan tunanin ta isa gaban sa ta tsaya bayan ta aika masa da sakon sallama, amsa mata yayi da kulawa yana bin ta da kallo, da alama dai yau akwai magana a wannan bakin naki, dan naga tunda kika taho kike kallo na abinda baki saba ba, kallon sa tayi wani shekeke,
yayi saurin kama kunnen sa, amin afuwa wasa nake, hakan ma ai wata girmamawa ce.

        Yaya mutanen gidan ya fada dan kawar da waccen maganar, lafiya ya aiki itama ta mayar masa, lafiya lau amma fa babu dadi, gashi idan na dawo gidan ma ba dadi, to babu wanda koda yar tara zan samu daga gare shi, idan fa na dawo na shige bangare na babu wanda zai ko leko inda nake idan ba yan aiki ba.

Shiru kawai ta masa tana kallon sa yana ta zuba har sai da taga ya kai aya sannan tace masa ai kai dinne babu wanda zai so ya kusanto inda kake fuska ya kyabe mata kamar wani karamin yaro, sabida mugun hali na ko,
aa ni bance ba, sabida dai surutun ka ai sai ka dami mutum yanzu fa kalli yanda kake ta magana babu ji babu gani, ni ai idan nace zan yi irin wannan sai kaina yayi ciwo.

Murmushi yayi, Allah sarki, kuma kinsan ni kaina ina mamakin yanda nake zagewa a gaban ki nayi ta surutu ko gajiya banayi, amma da zaki tambayi waye Abdul A na Allah da kinsha mamaki, amma na baki assignment, idan har kina tantama, kallon sa kawai tayi, ai abin bai kai ga haka ba.

sabida wato Saudat na fuskanci akwai wasu halaye na da baki fahimta ba kin fahimce su a bai bai wanda ya sanya har yanzu kika gagara amince min, bayan kafin na tunkare ki sai da na fara tunkarar mahaifin ki kuma ya nuna min babu matsala naje na nemi yardar ki, kuma a iya binciken da nayi akan ki, an tabbatar min da baki da wani saurayi balle nayi tunanin shine ya hana ki saurare ni.

Dan Allah ina nemam alfarmar ki sanar dani a matsayin da kika ajiye ni a cikin zuciyar ki, bawai na gaji bane aa wllh bazan taba gajiya ba koda kuwa zaki dauki shekaru masu yawa baki bani dama ba, nayi miki alkawarin zan cigaba da jira, bana ma fatan naga ranar da zan gaji da shiga lamarin ki, amma duk da haka ina mai kara rokon ki da ki daure badan ni ba ki tausaya min kice kin damu dani koda baki ce kina so na ba, hakan zai rage min fargabar da nake kwana kuma nake tashi da ita a kullum ta fargabar rasa ki.

Tsautsayi Part (3) Aisha Muhammad  Tunda ya fara magana kawai take kallon sa, tama rasa abinda zata ce masa wannan wane irin so ne, idan dai ba gizo idanun ta ke mata ba to hawaye take gani a cikin idanun sa, ikon Allah yau ita Saudah namiji yake zubar da hawaye akan ta, namijin ma irin Abdul wanda ko a cikin kawayen ta tasan wadan da zasu iya mutuwa akan sa, ita kuwa me zata cewa Allah banda ta gode masa, gaskiya idan har tayi sake ta bari wannan damar ta wuce ta to tayi babbar asara wacce zatai ta nadama har karshen rayuwar ta.  Bata san sanda tace masa, nima ina son ka Abdulmalik kawai dai akwai abubuwan da suke saka ni nake kokarin yin nesa da kai, bai san sanda wasu hawayen farin ciki masu sanyi suka zubo masa ba, Allah na gode maka daka nuna min wannan rana Allah Kai ne abin godiya ya Allah kamar yanda wannan baiwa taka ta faranta min ya Allah kaima ka faranta mata ranar lahira.  Ta amsa da ameen, nan ya shiga jero mata addu'oi kala kala ita kuma tana amsa masa da ameen, har sai da taga abin nashi bana kare bane kamar yana neman zaucewa sannan ta dakatar dashi, dan ita abin nashi yama dai na bata mamaki sai tsoro, dan tunda take bata taba ganin irin wannan so ba, ko a labarin litittafai, shine yau take gani a karan kanta.  Menene abinda kike tsoro daga gare ni da har ya saka kika gagara amince min tun da wuri Saudah, taji tambayar a bazata, shiru tayi na wani dan lokaci har sai da ya maimaita tambayar sannan tace zan fada maka amma kada kamin wata fahimta, kai ya jinjina mata.  Tana gama fada masa komai, mai zaiyi idan ba dariya ba sai da yayi mai isar sannan ya lura da yanda ta dauke wuta gaba daya, sai kuma ya shiga taitayin sa, tuba nake ranki ya dade, ba yin kaina bane, cikin masifa ta hayayyako masa to yin wane, dan kawai yau na sakar maka shine har zaka naimi raina ni, ni na isa, ya fada a fili a zuciyar sa kuwa, wata dariyar ce take cin sa, yanzu dan Allah kalli wannan yar yarinyar ce ta zage take masa fada harda wai na raina ta.  Idan ba haka ba mene, kaga tafiya ta kuma kar na kara ganin kafar ka a cikin gidan nan, Allah ya huci zuciyar ki, wllh ni ba maganar kice ta saka ni dariya ba, kawai ina mamakin yanda kika dade kina sona amma baki sani ba, wani kallo ta masa so ni din ta nuna kan ta, kwarai ma kuwa, wllh Saudah ko ki yarda ko karki yarda kin dade kina sona, tunda har kike tunanin idan wata ta kula ni ranki zai baci.  To ai kuwa kayi kus kure, ni kaga tafiya ta, ta fada tana kokarin juyawa, shan gaban ta yayi, haba tawan, ya bamu gama magana ba zaki tafi, kinga yi hakuri bazan kara fadar haka ba, ni koda ma bakya so na indai kin amince zaki aure ni to hakan ma nagode, idan anyi auren nayi alkawarin koya miki sona, kallon sa ta kuma yi da kuluwa da irin magan ganun sa, kaga ni kafafuna sun gaji zan shiga gida.

 Tsautsayi Part (4)
Aisha Muhammad

To ai ke ce baki iya saukar baki ba, kika bar ni a tsaye, amma dai duk da ni bako ne ai na kusa zama dan gida dan haka next  time idan nazo da kaina zan samawa kaina wajen zama, har kema na baki, yar dariya maganar sa ta bata, to naji kayi hakuri ni dai zan shiga gida, shikenan bazan takura miki ba nagode da lokaci, da kuma kyakykyawar karbar da na samu a yau.

Ina fata dawowa ta gaba mu yanke komai sai manya su shiga azo ayimagana, shiru ta masa, ta juya kawai tayi falo, hannu ya daga mata yana tsaye har yaga shigewar ta sannan ya shiga motar sa yabar gidan cike da farin ciki mara misaltuwa.

Itama a ranar kowa sai da ya fahimci tana cikin farin ciki, har Abban su daya dawo suna zaune a falon sa dukan su suna hira, sai da ya lura da irin fara'ar dake fuskar ta, yace wai ni kam Hajiya mai ya samu diyar nan taki ne naga gaba daya yau bakin ta yaki rufuwa menene sirrin ne, oho mata wllh nima sai da na tambaye ta, tace wai babu komai, Yaya Sadiq ne yace ku rabu da ita daga baya maji ai.

Ita dai dariya kawai tayi, daga haka ma ta musu sallama ta wuce dakin ta, tana shiga ta nufi gaban mudubi ta tsaya tana karewa kan ta kallo, so take taga sauyin da ake tacewa tayi a yau, dariya tayi, kuma fa gaskiya ne ita kanta tasan yau din kamar tana cikin farin ciki, dan abu kadan ke saka ta dariya wanda hakan ba dabi'ar ta bace, me ke nan, Abdul ta samu kanta da furtawa, kai tayi saurin girgizawa, aa no bama zai yiwu ba, tayaya ma.

Haka tayi ta sake sake a gaban mudubin har sai da wayar ta tayi kara sannan ta bar gaban mudubin ta tafi daukar wayar, number ce ke kiran nata, tsayawa tayi kawai tana kallon wayar ta kasa dagawa, tasan ma kiran Abdul ne, batayi saving number sa ba, amma yanda yake da nacin turo mata sako yasa ta gane number sa sosai.

Bata dauka ba har sai da ya kira sau biyu tana tsaye kawai tana kallon wayar, sai kuma sako ya shigo, zama tayi ta dauki wayar ta duba, sako ne mai dauke da roko akan ta daga wayar tasa, tana rike da wayar kuwa ya kara kira, sai da ta kusa yankewa sannan ta dauka ta kara a kunnen ta bata ce komai ba, sallama ya mata, ta amsa daga haka shiru ya biyo baya, shiya katse shirun ta hanyar fara sako mata hira irin wacce yake kyautata zaton zata birge ta.

Amma duk da haka bata wani sake masa ba har ya mata sallama, bayan ya sanar da ita zaiyi tafiya gobe, amma ba zai wuce sati daya ba, kuma yana dawo wa yake son azo ayi magana a saka musu rana dan ko kadan baya son a dauki lokaci, taji shi ne kawai amma bata amsa masa ba, ta dai yi masa addu'ar dawo wa lafiya, sannan suka yanke wayar.

Tsayawa kawai tayi rike da wayar a hannun ta, ta rasa me yake damun ta, gaba daya jin ta take kamar ba ita ba, tana jin wani iri, ko dan bata taba tsayawa da wani namiji ba har ta bashi irin wannan damar ne oho, dan mahaifin ta ya nuna mata a tsarin sa baya son ta fara kula samari har sai ta kammala karatun ta, kuma sai akai sa'a ra'ayin su yazo daya da diyar tasa.

Dan haka har ta kammala masters degree din ta bata taba kula saurayi ba da sunan soyayya sai dai abota, dan haka kai tsaye zata iya cewa indai son Abdul take to tabbas shine ya kasance first luv din ta, kuma ko da bata taba soyayya ba, tasan tabbas a yau ta kamu da son Abdul din mai tsanani wanda tana ji a ranta zata iya bashi damar da ya nema na yana dawowa ya turo iyayen sa ayi magana, amma kafin nan zata dukufa wajen neman zabin Allah

Tsautsayi Part (5)
Aisha Muhammad

Da wannan tunanin tayi bacci a ranar, tana tashi da sakon Abdul na barka da safiya ta fara cin karo, murmushi kawai tayi a duniya abinda tafi so shine a nuna an damu da ita, to kuma ta lura da dabi'un Abdul din suna nuni da mutum ne mai nunawa abinda yake so kulawa sosai, kota wannan tana ganin ta dace.

Da haka ta mike taje tayi alwala ta tada sallar asuba wacce ta makara bata samu tashi ba da asuba, daga nan kuma ta koma ta cigaba da bacci, ba ita ta tashi ba, sai bayan karfe goma na safe, tana tashi, wanka ta Fara yi sanna ta fita domin karyawa.

Wacece Saudah, Saudat Abdussalam shine cikakken sunan ta, su biyu iyayen su suka haifa a duniya, daga ita sai yayan ta, wanda take kira da Yaya Sadiq, daga kansu iyayen su suka tsayar da haihuwa kasancewar su rikakkun yan boko ne daga mahaifin su har mahaifiyar su, mahaifin su professor ne, yayin da mahaifiyar su kuma cikakkiyar medical doctor ce amma tayi retire shekara daya data wuce.

Sunyi yawon kasashe da dama, dan yanzu haka basu dade da dawowa Nigeria gaba daya daga Spain ba, mahaifin su prof Abdussalam ambassador Nigeria ne a Spain, yanzu ma retire yayi shine ya dawo mahaifar sa da zama gaba daya.

Yaya Sadiq shine dan su na fari, kuma bayan sun haife shi sun dauki lokaci mai tsaho basu kara haihuwa ba sai daga baya kuma suka haifi Saudah, sanda aka haife ta Sadiq yana da shekara goma, kowa ya dauki son duniya ba iyayen ba ba Sadiq din ba suka dora mata, hakan yasa Saudah ta taso cikin gata sosai.

A shekarar da Saudah ta kammala karatun ta na secondary a shekarar ne kuma Yaya Sadiq yayi aure, ya auri wata baturiya yar nan Spain din, amma musulma ce, shekarar su daya da yin aure Allah ya azurta su da samun karuwa a familyn, matar Yaya Sadiq Maimuna ta samu ciki, wai zo kaga murna a wajen familyn, haka suka dinga lelen ta har Allah ya sauke ta, ta haifo kyakykyawar diyar ta, wacce tayi zubin ruwa biyu ma'ana gaba daya mahaifin ta da mahaifiyar ta ta dauko kowa.

Allah cikin ikon sa tana haihuwa kafin ma a fito da ita Allah ya karbi abin sa, tace ga garin ku nan, fadin irin tashin hankalin da familyn suka shiga ma bata lokaci ne, haka dai suka dangana suka cigaba da kula da jaririyar, sosai yarinyar take samun kulawa tayi bul bul abinta, an mayar mata da sunan mahaifiyar ta, amma suna kiran ta da Baby.

Tsautsayi Part (6)
Aisha Muhammad

Gaba daya ma rainon ta yafi ga Saudah shiyasa tafi shakuwa da ita fiye da kowa, wannan kenan.

A bangaren Abdul kuwa yau ce ranar da zai dawo daga tafiya, sosai yake cikin farin ciki, sabida zai dawo ya hadu da sanyin idanun sa, wato Saudat wacce zuwa yanzu ba karamin dinkewa sukai ba, kai kace sunyi shekara, wanda gaba daya satin su daya ne da dai daitawa, amma Allah cikin ikon sa, a wadan nan yan kwanakin ita kanta Saudat har mamakin kanta take, yanda gaba daya ta gama macewa akan Abdul din.

Yana dawowa ko abinci bai yarda yaci a gida ba, ya garzayo ya taho gidan su Saudah, ai kuwa itama ta saka an shirya masa abinciccika na alfarma, iri iri, kai baka ce duka wannan shirin wai dan mutum daya bane, Mommy sai faman tsokanar ta take, wai ashe dai kanta na ja, tana fada mata tayi sauri ta cafke, dariya kawai take.

Yana kiran ta yace ya sauka, tasa aka kai kayan abincin nan duka garden, dama tun da safe ta saka ake ta faman kyalkyale garden din, dan a nan take son saukar shi, sosai tasa aka kayata wajen, sai da taje ta duba ta tabbatar komai yayi sannan ta tafi tayi wanka.

Shriyawa tayi cikin wani hadadden material kirar kasar Dubai tayi kyau sosai kai kace ruwa biyu ce, ita kanta data kalli kanta a mudubi sai da ta dara, dan tasan tayi babu karya, haka ma kowa na gidan sai da ya yaba irin kyan da tayi.

Tana cikin gyara mayafin ta, Baby ta shigo da gudu ta kawo mata rahoton isowar sa, sai da ta dan tsaya ta bata lokaci har sai da ya kira ta a waya, sannan ta fita, a garden din ta same shi har an masa iso, tun kafin ta karasa ya kafe ta da ido har tazo ta zauna bai daina kallon ta ba.

Hannun ta ta tafa dai dai fuskar sa, yayi firgigit ya kalle ta, lafiya, kai zan tambaya kalau, ka kafe ni da ido kamar zaka cinye ni, ai da zan iya dana sace ki dai kawai, amma ai idan kika bani dama cikin lasisi zan dauke ki na maida ke gida na, kinga sai nayi ta ganin ki a koda yaushe, har sai ka gaji, Allah ya kiyaye na gaji da kallon ki, har a bada.

Dariya tayi, to ni dai kaga zaka fara zancen naka baka ci komai ba, bayan kace min ko breakfast baka yi ba, ta fada tana kokarin fara bude kwanukan, aa kinga fa na fahimci wayo kike son min, to wllh naki wayon, ki tsaya kawai ki bani amsa ta, idan ba haka ba ma kawai na shiga yajin aikin cin abinci.

Barin abinda take tayi ta maida hankalin ta akan sa tana murmushi, da kuwa wani bai ganu ba, kalle ka fa wai a haka ma kana ci amma kamar baka ci inaga ka daina, kara bata rai yayi, kinga fa ni ba wasa nake ba, babu abinda zanci har sai kin fadan matsaya ta, dariya tayi kai dai wllh ka fiya rigima, matsayar ka mai kyau ce, a yau din nan na baka damar kaje ka gaida Abba, kuma nasan Abba na bashi da matsala, baza ka samu wata matsala daga wajen sa ba, kaga daga nan sai ka sanar dashi zaka turo iyayen ka.

Fadin irin farin cikin da Abdulmalik ya shiga ma bata lokaci ne, hakan kuwa aka yi, bai bar gidan ba har saida ya jira Abba ya dawo, taje ta masa iso, kuma Alhmdllh yaji dadin haduwar sa da Abban dan mutum ne mai saukin kai, a nan take ya bashi damar ya turo iyayen sa, dan basa bukatar yin wani bincike akan sa, sabida familyn sa ba boyayyu bane, sun hadu ma da Yaya Sadiq kuma Alhmdllh a wajen sa ma yaga alamar ya samu karbuwa.

Tsautsayi Part (7)
Aisha Muhammad

Dan haka baiyi kasa a gwuiwa ba, yana komawa gida ya samu mahaifiyar sa da maganar wato Hajiya Salma akan ta kira yan uwan mahaifin su ta musu magana sai suje a nema masa auren Saudah, sosai itama tayi farin ciki da autan nata ya nemi yin auren da kansa wanda dama ta dade tana masa magana akan yayan kawayen ta dama yan uwa wadan da suka nuna suna son shi, amma fur yaki amincewa.

Tayi farinciki sosai duk da taso ace ya zaba daga cikin yaran da ta dade tana masa magana, dan tasan yanzu bazata taba tsira ba, sai sun zarge ta da gudun zuri'ar su, amma ita dai tana bayan abinda dan ta yake so, dan a yanzu bata da kowa da take kalla taji sanyi sama dashi.

Wacece Hajiya Salma, mata ce ga Alhaji abdurrazaq na Allah, shahararren dan kasuwa wanda ya mallaki kamfanoni da dama a fadin Nigeria, ya shahara sosai akan harkokin sa, idan har za'a jero masu kudin kasar nan dole ne sunan sa ya kasance a gaba gaba, abinda kawai Allah bai bashi ba shine yawan yaya, wanda kuma hakan ya kasance babban burin sa a rayuwa, hakan yasa yayi aure aure da dama, amma dai Allah bai bashi ba.

Yaran sa daya wanda suka haifa da uwar gidan sa, duk kannin aure auren da yayi basu taba samun haihuwa da matan ba, har saida, Allah ya hada shi da Hajiya Salma wacce ta kasance matar sa ta karshe, bayan ya auri Hajiya Salma babu dadewa Allah ya kuma bawa uwar gidan sa ciki, zo kaga murna a wajen sa.

Haka suka raini cikin cikin tattali, har Allah ya sauke ta lafiya ta samu diya mace, wanda a lokacin babban dan nashi mai suna mus'ab yana da shekara sha tara, anyi suna lafiya yarinya taci sunan ta Fatima suna kiran ta da Zarah, tunda Zarah ta fara wayo aka fuskanci tsananin muskilancin ta, gata bata da sabo ko kadan, karara take nuna wa mutane kyama da tsana ko waye kai idan har ka dauke iyayen ta da kuma dan uwan ta.

Matan baban ta kuwa ba'a ma maganar su, karara take nuna bata son su, haka dai suke hakurin zama da ita tunda idan ba dalili ba ba haduwa suke ba, ana haka babu dadewa Allah ya bawa Amarya Hajiya Salma ciki, murna sosai duka mutanen gidan sukai tare da addu'ar Allah ya sauke ta lafiya.

Cikin ta na shiga wata tara, ta haifo yaron ta kyakykyawa san kowa kin wanda ya rasa, murna a wajen Alhaji Abdurrazaq ba'a cewa komai, a lokacin Zarah tana da shekara tara, amma halayyar ta zaka ce takai shekara sha biyar, ranar suna yaro yaci sunan sa Abdulmalik.

Amma abin mamaki kowa ya dauka Zarah zata so Abdulmalik kasancewar sa dan uwan ta, sai dai abin ba haka bane dan tunda aka haife shi ko kallon inda yake Zarah bata taba yi ba, sosai abin yake bawa kowa mamaki mahaifiyar ta babu yanda bata yi ba, amma taki, idan tana mata fada sai ace ta kyale ta yarinya ce zata daina haka wani yaron yake baida son yara, haka dai ta rabu da ita amma ranta baya son abinda yarinyar take, dan ita wani lokacin yanayin halin yarinyar da miskilancin ta yana bata tsoro.

Haka dai rayuwa ta cigaba da tafiya, watarana Alhaji Abdurrazakaq ya bude wani kamfani a garin Kaduna za'ayi bikin bude shi, kowa yana ta dokin zuwa wannan biki, a ranar da za'ayi taron Allah ya saukarwa da Abdulmalik wani irin mugun zazzabi dashi ya kwana, ganin haka da gari ya waye, Alhaji yace babu inda Hajiya Salma zata yaro bashi da lafiya ta zauna ta kula da shi.

Tsautsayi Part (8)
Aisha Muhammad

Dama kuma a ranar Zarah zata zana junior waec dinta, dama baya son a barta daga ita sai yan aiki a gida, dan haka sai ta zauna za'a kira doctor yazo ya duba shi, ai ba kwana zasuyi ba a ranar zasu dawo, shine ma bazai yuwu ya taho a ranar ba, haka ta hakura ba dan taso ba, ta zauna suka shirya suka tafi bayan ta rako su bakin mota, dan a lokacin Zarah ta riga ta tafi makaranta, shi kuwa Abdul bama zai iya musu rakiyar ba.

Haka ranar ta wuni a gidan duk babu dadi ta kuma rasa abinda yake damun ta, dan jikin Abdul ma yayi sauki sosai tunda doctor yazo ya masa allurai, tayi waya dasu sun sauka lafiya, bayan tayi sallar la'asar ta kuma kiran su, sanar da ita anyi taro lafiya yanzu ma suke shirin juyowa, addu'a ta musu sannan ta kashe wayar ta nemi waje ta kwanta dan gaba daya bata jin dadi.

Tana kwanciya wani bacci mai dadi ya dauke ta, kamar a mafarki taji karar wayar ta, sanda ta tashi har ta katse, wayar ta duba taga Alhaji ne haka kawai taji gaban ta ya fadi, kiran ne ya kara shigowa, ta dauka ta kara wayar a kunnen ta, kafin ta masa sallama taji muryar sa kamar yana kuka, gaban ta ya kuma faduwa cikin kaduwa tace Alhaji lafiya, cike da dakiya tare da kokarin boye mata halin da yake ciki, yace mata Salma munyi rashi, innalillahi wa innalillahi raju'un ta furta, waye ya rasu Alhaji.

Salma su Mas'ud ne sukai hatsari yanzu aka kira ni gaba dayan su Allah ya musu rasuwa, bata san sanda ta yar da wayar hannun ta ba, ta yanke jiki ta fadi, ihun da Abdul ya kwala ne ya jawo hankalin masu aiki suka yo cikin dakin, harda Zarah wacce bata dade da dawowa ba, hankalin su a tashe suke tambayar Abdul abinda ya faru, ce musu yayi waya kawai yaga tana yi sai kuma ta saki wayar ta fadi.

Daya daga cikin masu aikin ce ta dauki wayar ta duba, sai taga har lokacin kiran bai yanke ba, karawa tayi a kunnen ta tace hello, Alhaji ne ya fara tambayar ta halin da Hajiya Salma ke ciki, ta fada masa, umarni ya basu kan su dauki wayar dake falon gidan su kira likita, sannan yake fada mata abinda yake faruwa, ita kanta yar aikin ba karamin kaduwa tayi ba.

Tana yanke kiran taja yan uwan ta yan aiki tace Alhaji yace suje su kira likita, suna fita ta fada musu abinda ya faru, gaba dayan su kuka suke, haka suka kira likita suka koma dakin, Abdul sai tambayar su yake mai yasa suke kuka, ita kuwa uwar miskilancin ko a jikin ta, ce masa sukai babu komai.

Bayan magariba aka kawo da gawarwakin zuwa lokacin gidan ya cika da yan uwa da abokan arziki, zuwa sannan itama Hajiya Salma ta farfado sai faman kuka take ana bata hakuri, sanda aka kawo gawawwakin ne gida ya kuma rudewa, sai koke koke ake, zuwa sannan ne har Abdul dake da kananan shekaru ya fahimci abinda yake faruwa, Salma ma tasha kuka, kowa sai da ya tausaya mata.

Haka washegari aka musu jana'iza aka mika su gidajen su na gaskiya, Allah kasa mu cika da imani, bayan an share makoki yan uwan Maman su da zasu tafi sun so Alhaji ya basu Zarah su tafi da ita amma fur yaki yace bazai raba kan yaran sa ba, babu abinda Hajiya Salma zata gagara mata, haka babu yanda zasuyi suka hakura suka barta, dan ma saukin ta sun tabbata Hajiya Salman bazata zalunci yarinyar ba, dan kowa yana yabawa halin kirki irin nata

Tsautsayi Part (9)
Aisha Muhammad

To bayan fa kowa ya watse ne suka fara wani irin zama da Zarah dan duka halayan ta sun ninka na da, rashin son mutane, har mahaifin nata yanzu ta daina sakewa da shi, tun suna ganin alhini ke samun ta har suka fara damuwa, rannan da suka ritsata a daki suka ce sai ta fada musu ko ana mata wani abu da bata so a gidan ne, sai ce musu tayi ita gaba daya zama dasu ne bata so, sabida suma ai basa son Maman ta da yayan ta.

Sabida Alhaji yafi son Hajiya Salma shine ya hana ta tafiya a ranar nan ya tura Maman ta da yayan ta suka je suka mutu, baki kawai Alhaji ya saki yana kallon yarinyar da tsoro a fuskar sa, yanda wannan yar yarinyar take zaro irin wadan nan maganganu, daga baya ransa ya fara baci ya fara mata fada, sosai yake mata fada irin wanda bai taba yiwa wani da nashi ba.

Har saida Hajiya Salma ta saka baki, da kyar ta samu ya fita daga dakin, ita ta zauna tana ta kokarin nusar da Zarah ba abinda take tunani bane, tayi hakuri lokacin su ne yayi, haka tayi ta mata nasiha, ita dai tana ta kuka, haka har ta gaji ta shi ta fita ta rufo mata kofar, daga nan basu kara mata magana ba, haka suka cigaba da rayuwa, wannan ke nan.

Bayan Abdul ya fita Hajiya Salma ta dauki waya ta kira kanin mahaifin su ta sanar dashi idan ya samu dama tana son ganin sa, ai kuwa washe gari da yamma yazo, bayani ta masa akan abinda Abdul din yazo dashi, shima yaji dadi sosai ya tambaye ta yarinyar yar gidan waye, nan ta sanar masa, yace ai tazo gidan sauki, ya sanshi sosai mutumin sa ne, insha Allah zaije ya samu duk wanda ya dace sai su saka rana a sanar dasu zasu zo, godiya ta masa sukai sallama ya tafi.

Kwana biyu da tafiyar sa, ya kira ya sanar da ita zasuje gidan su yarinyar nan gobe sai ta sanar da shi Abdul din ya fada musu dan suma su shirya, hakan kuwa akayi yana dawowa daga aiki Hajiya ta sanar dashi, baiyi kasa a gwuiwa ba ya kira Saudat ya sanar mata, itama tun kafin Abba ya dawo taje ta sanar da Mommy, addu'a Mommyn tayi tare da fatan Alkhairi.

Kamar yanda suka fada hakan ranar da suka fada suka zo, anyi musu shirye shirye sosai kai kace bikin ne ya fara gabatowa, tarba aka shirya musu ta ban mamaki, niko nace wani abin sai masu kudi, Abba ma ya sanar da yan uwan sa su hudu harda shi na biyar ke nan, suma sunzo mutum shida.

Bayan gaishe gaishe suka fara gabatar da abinda ya tara su, basu sami wata matsala ba, aka amince aka basu auren Saudat din kamar yanda suka zo tambaya, daga nan kuma sai suka shigo da maganar saka rana, dan a cewar su gaskiya su a familyn basu fiya son jan biki ba, sabida shine yake janyo azo a fara samun matsala daga baya.

Suma bangaren iyayen Saudat sunyi na'am da irin tsarin nasu, sukace ai babu damuwa tunda suma ta bangaren su ai a shirye suke tunda yarinyar nan ta riga da ta kammala karatun ta, babu abinda za'a jira, maganar ba karamin dadi tayiwa iyayen Abdul ba, sun tabbatar da tabbas yaron nasu yayi zabe a irin gidan da ya dace, dan a gaba daya mu'amalar su kasan ba kananan mutane bane.

Tsautsayi Part (10)
Aisha Muhammad

A nan take aka tsayar da rana nan da wata hudu idan Allah ya kaimu, a nan take daya daga cikin su wanda ya kasance kani ne ga marigayi wato mahaifin Abdul ya karbi account number Abban Saudah ya tura masa naira miliyan biyu a matsayin kudin aure dana saka rana, kamar yanda al'ada ta tanadar, daga nan sukai sallama, ba tare da sun taba komai daga cikin abubuwan da aka ajiye musu ba.

Mota aka saka aka bisu da kayayyakin da aka shirya musu, suka tafi kowa yana yabon kirki irin na dan uwan sa, suna yaba irin zaben da yaran nasu sukai, daga nan suma sauran yan uwan Alhaji Abdussalam suka masa sallama kowa ya kama gaban sa.

Bayan ya shiga ciki yake sanar da Mommy yanda komai ya kasance, tayi mamaki amma kuma hakan ya mata dadi, dan ta jima tana burin auren Saudat din, dan wannan ne karo na farko da zata aurar da diya mace kuma a cikin kasar ta, wanda zata gudanar da duk wata al'ada wacce bata samu gudanarwa ba a bikin Sadiq.

Saudat bata jiba har saida Abdul ya kira ta ya fara tsokanar ta da Amaryar sa, anan ne take ji, itama kasa boye farin cikin ta tayi, haka suka hadu suka dinga murna babu kunya, niko nace yaran zamani, a nan take suka fara shirye shirye, da kyar ranar suka rabu a waya.

Tana sauka kasa nan ma zancen suka je suka dasa ita da Mommy, abinka da yan boko babu wata kunya tsakanin uwa da diyar, a nan Mommyn take cewa sunyi magana da Abba karshen wata mai kamawa zasu tafi Italy da ita da Aunty kanwar ta Aunty Sadiya da kuma ita Saudat din dan ta zabi furnitures dinta da kanta.

Dan haka kafin lokacin ya kamata ta tambaye shi bedrooms dinta nawa sannan falo ma guda nawa ne dan su san abinda zasu siyo, sannan watan gaba kuma, Dubai zasuje tare da kawar ta Hajiya Lawuiza su siyo kayan kitchen sabida harkar ta ce tasan kansu sosai, can amma dai Mommy ba dani za'aje ba, dan zuwa lokacin nasan nima abubuwa sun fara min yawa, aa ai ba dole bane idan bazaki ba shike nan, eh wllh idan na zabi furniture dinma ya wadatar sauran kawai ku zaba min, ai nasan Mommy na ba baya bace wajen iya zabe.

Yanzu gaba daya iyalan biyu idan suka zauna basu da zance sai na bikin barin ma kuma iyayen gayyar kullum yazo ko sukai waya zancen kenan, dan yanzu haka har anci wata daya, a cikin wannan watan ne ma suke shirin tafiya Italy, ko yaya ta masa zancen tafiyar sai yayi ta korafi dan dai babu yanda zaiyi amma da bazai barta taje ba.

Cewa yake wai meyasa kawai bazata zaba ta waya ba, shifa baya son tana nisa, idan har akai auren nan bazata kara yin tafiya ba tare dashi ba, kuma shima duk inda zashi tare zasu na tafiya, ta kance masa to wajen aiki fa, sai yace ai shima badan kada a dinga kalle masa Mata ba ai da da ita zai dinga tafiya, amma kar ta samu damuwa idan akai auren sai ya dauki hutun wata guda ko kofar gida bazai leka ba.

Tsautsayi Part (11)
Aisha Muhammad

Kinga da Hajiya ma zata yarda ta dawo gidan mu sai a ware mata bangare, kinga dana huta zuwa wajen ta, amma wllh Hajiya ko zan mutu bazata yarda ba, to mu mu zauna a gidan nata mana sai kawai a ware mana bangare, cab bazata yarda ba, bata son mutane ne, a kawai dai wai zama da sirika ne bata so, sabida gudun fitina.

 Allah sarki ni kuwa ina tausayawa Hajiya, kasan zaman kadaici babu dadi, kaga kai ba zama kake ba, Allah baya barin wani dan wani yaji dadi, kaga da Alhaji yana nan da rai ai nasan zuwa yanzu dai yayi retire, ko Aunty Zarah duk da da tana da rai zuwa yanzu tayi aure amma da duk tsiya zata dinga yawan zuwa, kuma wata kila ma kaga ta bata yar ta ko kuma dan ta.

Murmushi kawai yayi, baki san wace Aunty Zarah ba da baki fadi haka ba, amma dai ba wannan ba, yanzu ke dai kawai sai kiyi kokari kina zuwa ki fara zuba mana yan bibbiyu, kinga sai mu bawa Hajiyan su dinga debe mata kewa, banza ta masa, yace ko bakya ji na, daya fahimce ta ai kuwa ya samu abinyi ya fara tsokanar ta, sai kashe wayar tayi ta rabu dashi.

Kwanci tashi babu wuya a wajen Allah, a yau ya kama saura shida biki, dukan wani shiryeye ya kankama daga ko wanne bangare, a bangaren Amarya da kawayen ta sun shirya parkage na ankon duka partyn da za'ayi, har sun gama rabawa kawaye duka kyauta ne, bangaren gidan su ma Mommy ba karamin shirin take ba ita da yan uwa da kawaye, zatayi Kamu, mother's Eve, gidan su angon ma Hajiya ta shirya nata mother's Eve din, shi kuma ango da abokan sa sun shirya gagarumar dinner, yayin da amarya zatayi Lady's night, a takaice dai ba karamin biki ake shiryawa ba ta ko wanne bangare, biki ne na dan gata da kuma yar gata, da zai ja magana a gaba daya fadin kasar kuma ya bar tarihi.

Saura sati uku biki aka kawo lefe, lefen daya dauki magana a gari da social media duk inda ka shiga kaga ana ta dora lefen, dan tsayawa fadin tsaruwar lefen ma bata lokaci ne, set biyar ne na akwati shake da kaya na alfarma, sai kuma set biyu shake da kaya da kuma mukullin dalleliyar mota wannan kuma wai kyauta ne daga sirikar ta, sai dai muce masha Allah, dan ko hassadin izahasada.

Takanas aka dauko mai gyaran jiki ta fara gyara Amarya a gida babu inda take zuwa, kowa a Family kokari yake yayi abida zai birge Saudat dan kowa yasan shalele ce a gidan su, dan Yaya Sadiq ma yayi rawar gani dan cewa yayi taje ta zabi duk wani kayan electronic shi zai siya mata, kuma masha Allah babu abinda ya gagara komai dai sai san barka.

A ranar da aka je jere ne dai aka dawo da magana, masoyan su na murna makiya kuma na kuka, dan duk da kasancewar suma familyn su masu kudi ne, amma da suka shiga gidan da akace wai shine za'a kai Saudat din, saida suka zama yan kauye, dan a bangaren girma wani irin mahaukacin girma ne dashi da ban mamaki.

Duk girma irin na gidan su idan aka saka shi a cikin wannan gidan zai zama kamar wani bangare ne kawai, a bangaren tsaruwa kuwa da kyau zata sauka wani kayataccen Hotel ne, duk uban kayan da suka mata kawai sai zaban bangare sukai suka jera mata dan kayan baza su cika gidan ba.

Tsautsayi Part (12)
Aisha Muhammad

Da suka dawo wasu daga cikin shakikan yan uwa sai da suka sami Mommy suke tambayar ta sun kuwa yi bincike sosai akan sana'ar yaron nan, da suka fada mata irin abinda suka gano, dariya tayi tace, dan gidan fa marigayi Alhaji Abdurrazaq na Allah ne, kun san dai irin shurar da mahaifin sa yayi kafin Allah ya masa rasuwa, kuma koda ya rasu ai harkokin sa basu durkushe ba, sai ma abinda yayi gaba.

Kuma shi Abdul din shine kadai ya gaji dukiyar yake cigaba da gudanar da ita, sannan gidan ma ai bashi ya gina ba, tun kafin ya fada mana muna da labarin mahaifin sa ne ya gina da niyyar zai koma ciki da iyalan sa, sai kuma Allah bai nufa ba, har ya rasu bai koma ba, matar sa kuma wato mahaifiyar Abdul din tace bazata koma ba, shi idan yayi aure ya zauna a ciki, to kunji fa.

Haba koda nace, amma fa gaskiya Rukayya yar ki tayi goshi, sai dai kuyi ta bin ta da addu:ar Allah ya zaunar su lafiya, ameen dai, Mommy tace tana ta washe hakora, da jin dadin yarta ta kere sa'a.

Da haka aka shiga biki gadan gadan, Ranar farko da Kamu aka fara, idan kaga Saudah a ranar kamar ka sace, haka akai kamu lafiya aka watse washe gari mother's Eve, gidan su ango kuwa basuyi nasu ba sai da aka daura aure da rana aka yi Mother's Eve na gidan ango, da daddare kuma bayan an kai Amarya akayi dinner.

Daga nan kuma Amarya da ango su kai sallama da kowa suka wuce gidan su, sai mu bisu da addu'ar Allah ya bada zaman lafiya.
Washe garin kai Amarya, kamar yanda Abdul ya alkawarta, ya dauki hutu, ranar babu inda ya fita a gida ya wuni, ko Hajiya ma kiran ta yayi a waya suka gaisa yace bazai fito ba a yau din, yama san gidan ta akwai baki, sai Allah ya kaimu gobe, Allah ya kaimu tace, sannan tace ya gaida mata da diyar ta.

Da yammacin ranar ne aka kira shi daga comparny su na Abuja, an samu gobara, dan haka dole ana bukatar sa a wajen, hankalin sa ya tashi sosai, Saudat ce ma tayi ta kwantar masa da hankali, haka dole babu yanda suka iya, a daren yayi booking flight na safe gobe dole zai tafi Abuja, wannan shine kana naka Allah na nashi.

Yana dawowa daga sallar asuba ya fara shiri dan jirgin su karfe bakwai na safe zai tashi, karfe shida da rabi ya gama duk shirin sa, Saudah ta rako shi bakin mota, rataye da jakar sa, sai faman shagwaba take zuba masa, wai wllh ita sai ta bishi, shi kuma sai biye mata yake yana ta lallashin ta.

Da kyar ya samu ta hakura shima bisa alkawarin bazai wuce gobe ba, da ta dage ita gida zata tafi, amma yaki yace ai sai mutane su fara magana, dan yasan zuwa sannan wasu ma daga cikin bakin biki basu tafi ba, da kyar dai ya samu yasha kanta, bisa sharadin zai kira Abba ya roki alfarmar a kawo mata Baby, wanda ba karamin danbarwa aka sha ba, akan ta dage sai an bata Baby yayin da su Mommy kuma fur suka ki amincewa.

Tsautsayi Part (13)
Aisha Muhammad

To yanzu ma yasan sai yayi fama kafin su amince dan ko kadan basa son abinda zai sa Babyn tayi nisa dasu, yasan zasu ce menene amfanin yan aikin da suke gidan basu isa su taya ta zama ba, sannan ma kuma ai suma sun hado ta da yar aiki wacce tun tana karama sun shaku sosai duk basu isa ba.

Haka dai ya lallaba ta ya tafi kada yayi missing flight, amma duk da haka da kuka, bayan ya tafi haka ta koma cikin gidan tana ta faman sharar hawaye, saman ta ta wuce direct ta kulle kofar tayi ta faman kuka, har daga haka bacci ya sace ta.

Tana cikin baccin ne taji kamar ana nocking, dakyar ta iya mikewa dan wani ciwon kai ne taji ya ziyarce ta, zuwa tayi ta bude kofar, Baba Mairo ce mai aikin da aka hado ta da ita daga gida, fuska ta yamutsa, ya akai ne Baba Mairo, dama mai gidan ne ya kira ta wayar dake falo, yace wai ya kira baki dauka ba, tun dazu nace ma watakila kina bacci ne, shine yanzu ma ya kuma kira yace nazo na duba ki.

To naji, zan kira shi, daga haka ta juya ta tafi, ita kuma ta maida kofar ta rufe, wanka ta shiga tayi sannan ta dauro alwala dan taga karfe daya saura, tayi mamakin baccin da ta sha, sai da ta fito ta shirya sannan ta dauki wayar ta kira shi, tana shiga kuwa ya dauka kamar yana jira, dariya tayi, dama jiran kiran kake ne, shima dariyar yayi, sosai ma, duk kin bi kin daga min hankali.

Da na maka me, ban sani ba, tun fa dana sauka nake kiran wayar ki amma bakya picking, to bacci nayi, yayi kyau yaya kuka, ko kin daina, aa yana nan, dan Allah kalle ki ko kunya, eh din, to ya hanya, Alhmdllh, ya kuma ka tarar da abin, sai godiya, gaskiya fa amma akwai aiki sosai a wajen nan, dan haka gaskiya bazan samu dawowa gobe ba, a takaice ma dai sai yanda ta yuwu, ya fada cikin dakakkiyar murya wai dan kada ta samu damar masa rigima.

Amma duk da haka sai da tayi, inda ya samo kanta daya ce mata ya kira Abba ya masa bayani kuma ya amince za'a kawo mata Baby da yamma idan ta taso daga makaranta, inyaso daga nan shi zai yiwa driver magana sai ya dinga kaita makarantar.

Hakan daya fada mata shiya sa ta dan ware har suka shiga hira, saida taji buga kofa sannan sukai sallama ta tashi taje ta bude, daya daga cikin masu aikin gidan ne, ta russuna ta gaishe ta, sannan tace Hajiya kinyi baki, su waye, sunce wai kawayen ki ne, to kice musu ina zuwa, a kai musu abin tabawa, to Hajiya ta juya ta tafi.

Sallaya ta dauko ta shimfida, ta tada sallah, ta idar tayi addu'a sannan ta ninke abin sallar ta fita, a zazzaune ta same su, an cika musu gaban su da kayan motsa baki, kawayen tane na makaranta, suna ganin ta kuwa suka fara mata tsiya, wai duk amarcin ne ya hana ta sakkowa sai ta ja musu aji, ba'a gaya wa angon sune ba.

Kallon su kawai take har sai da ta samu waje ta zauna sannan ta kalle su, kun gama, to sallah zanyi a lokacin ko sai na bar sallar nazo na tare ku, daya daga cikin su tace to uwar bakar magana, saura kice zakiyiwa angon shima, wllh wannan tsalelen mijin naki ba dauka zaiyi ba, harara ta wurga mata, dan Allah manta ai ni babu ni babu hirar miji na da wata kawa balle har ta jiye min sirrin sa, sanda zan tarairayi abu na kina ina.

Tsautsayi Part (14)
Aisha Muhammad

Duka suka saka shewa irin ta kawaye, nan suka cigaba da hira da tsokane tsokane irin na kawaye, a nan suka wuni wanda hakan ba karamin dadi ya yiwa Saudat ba dan ya matukar debe mata kewa, sai da sukai sallar la'asar suka ci abinci wanda su suka fadi abinda suke so tasa masu aiki suka girka musu, sannan suka tafi, bayan ta basu tulin kayan kwalliya a cikin irin na kayan lefen ta, sannan ta hada musu da kudi wai su sha mai, da yake a cikin motar daya daga cikin su suka zo.

Basu dade da tafiya ba, tana zaune tana danna waya akayi nocking, tashi tayi da kanta taje ta bude, Baby ce ta shigo da gudun ta tana ihu, ta rungume ta, oyoyo Aunty Saudah, nayi missing din ki, irin sosai din nan fa, dariya tayi ta kama kumatun ta, nima nayi missing din ki Baby na, ba ke kika ki kice zaki dawo gida na ba.

Aa nifa cewa nayi kawai su Mommy ma duk su zo mu dawo tare, dariya tayi tana kara ganin kuruciyar Babyn, hannun ta ta kama to muje ciki ko, ta fada tana kokarin tura kofar, ai Malam Isa ne ya kawo ni, yana waje yace na fada miki zai shigo min da jaka ta, OK to kice masa ya shigo.

Daga nan ta leka tace wai ka shigo ta juya suka shiga cikin falon, Malam Isa ne ya turo kofar dakin dauke da sallama, Saudah ce kawai ta amsa masa, ita kuwa Baby ana can an fara zuba labari, karaso mana Malam Isa, shiga yayi cikin falon sosai yana jaye da katuwar trolley din Babyn wacce ke shake da kaya kamar wacce zata bar garin.

Tsakiyar falon ya isa inda suke zaune, sannan ya ajiye jakar daga gefe, ya russuna ya gaida ta, ta amsa masa da sakewa, sannan ya juya, to Hajiya ni zan koma, jakar ta dake gefen ta, ta jayo naira dubu uku ta dauko ta mika masa gashi Malam isa ka gaida gida, karba yayi yana ta zuba mata godiya.

Bayan tafiyar sa, Baby aka cigaba da zuba, yawancin labarin nata akan abubuwan da suka faru ne cikin kwana biyun da tabar gidan, da kuma labaran biki, ita dai Saudat kawai sauraron ta take wani abin tana ganewa wani kuma dai kawai tana biye mata ne.

Basu suka tashi a wajen ba har saida aka kira sallar magariba, sannan suka tashi suka hau sama domin gabatar da sallah, Baba Mairo ce ta hawowa da Baby jakar kayan ta, dakin dake kusa dana Saudat ta kai mata, wanda tana kyautata zaton a nan Babyn zata zauna.

Bayan sunyi sallah basu sakko ba sai da sukai sallar isha'i sannan suka sakko, Baby kitchen ta fara nufa wai ita yunwa take ji, oath tasa aka hada mata yaji madara, dan bata cin abinci da dare, haka ta saba shiyasa ma har ya zame mata jiki idan ma taci kwana zatai cikin ta a kumbure.

Bata baro kitchen din ba har saida aka gama aka bata sannan ta fito, ta tarar Aunty Saudah tana waya, ita da Abdul suke wayar, ai tana zuwa wajen dole wayar ta kare dan ta ishe su da kaudi, ce masa tayi kawai idan tazo kwanciya zata kira shi, cewa yayi ta bawa Babyn wayar su gaisa, mika mata tayi, ta karba suna gaisawa ta fara masa korafin wai ya mata wulankanci a wajen biki, dariya yayi kawai yace tayi hakuri, tace ina ita dai sai ta rama ko kuma ya siyo mata chocolate.

Tsautsayi Part (15)
Aisha Muhammad

Dariya yayi au chocolate kawai zata fanshe ni, eh tace, yace to zai siyo mata wadan da bata isa ta cinye ba, sai da Saudah taga abin na Baby bana kare bane, ta sa hannu ta karbe wayar ta masa sallama ta kashe, bata saurari korafin da take mata ba.

Ranar basu suka kwanta ba sai wajen sha daya na dare, dan har video call suka kira su Mommy suka yi ta hira har sai da Abba yace aje a kwanta haka dare yayi sannan sukayi sallama, suka kashe, tashi Saudah tayi ta kashe komai na falon sannan suka haye sama, dama yan aiki tuni suka musu sallama suka tafi bangaren su.

 Baba Mairo ce kawai dama dakin ta yake a cikin bangaren nasu, a kasan bene, to ita ma tuni tayi bacci, haka kawai Sauda taji tana jin tsoron kwana ita kadai duk da ta riga ta saba ko a gida babu wanda yake kwana da wani, amma yau din kawai sai tace Babyn tazo su kwana a dakin ta, haka sukayi addu'a suka kwanta, sai da Baby tayi bacci dama ita batayi ba tana chat da wayar ta, sannan ta kira Abdul sun dade suna waya daga baya kuma sukayi sallama kowannen su ya kwanta.

Ranar ta makara kasancewar bata saba kaiwa, dare haka bata yi bacci ba, hakan yasa bata ji sallar asuba ba, sai da gari ya fara haske sannan ta tashi,tana tashi toilet ta shiga ta dauro alwala ta fito ta tashi Baby dake kwance tana ta baccin ta, saida taga ta tashi sannan ta shimfida sallaya ta tada sallah.

Bayan ta idar tayi azkar dinta, ta mike ta fita, dan zuwa ta hado fresh milk din ta wacce ta riga da ta saba sha duk safiya tana gama azkar ita take fara sha sannan ta koma bacci kafin kuma ta tashi tayi breakfast, kuma da dumi take sha, gashi kitchen dinta na sama har yanzu ba'a hada mata gas din shi ba.

Tana tafe tana mitar sauka kasan, har ta fara sakkowa ta lura da wani abu akan makeken center carpet din dake malale a tsakiyar babban falon, ido ta kuma zurawa dan ta tabbatar da abinda idanun ta suke gani, sakkowa ta cigaba da yi, har ta sakko gaba daya, idan dai ba idanun ta karya suke mata ba, mushen wata rusheshiyar tinkiya ce a kwance a tsakiyar falon.

Baki ta rufe wanda take kokarin kwala kara, amma duk da haka sai da ta danyi ihu kadan, wanda ya fito da Baba Mairo da gudu daga dakin ta wanda ke cikin falon daga wani lungu, da gudu ta fito tana Hajiya lafiya, idon tane ya gane mata abinda yasa maganar tata makalewa, meye wannan Hajiya.

Ina zan sani Baba Mairo yanda kika ganshi haka nima na gani, kuma Hajiya jiya kin kulle kofar nan ko dai kin manta, jeki duba mana kofar falon nan a kulle take, tafiya tayi ta duba a kulle take sosai babu alamar an bude ta, wllh Hajiya a kulle take, haba dama ni nasan da hannu na na kulle ta.

Tsautsayi Part (16)
Aisha Muhammad

Mun shiga uku, to wannan abun daga ina, Allah masani, je ki kira mai gadi, sama ta koma kafin ta kira shi ta dakko hijabin ta ta saka, tana dawowa ta tarar da shi shima yana ta mamakin wannan abu, kuma da alama ta dai dai kirjin ta aka caka mata wuka dan ga wajen nan da jini.

Haka dai duka jiki a sanyaye tasa mai gadin ya fita da ita, ita kuma ta koma sama madarar da bata sha ba ke nan, a ranar wuni tayi da tunanin abin a ranta amma dai bata fadawa kowa ba, ko Baby data tashi bata mata maganar ba, dan tasan halin surutun Baby indai taji to kowa ma ya gama ji, ko da sukai waya da Abdul ma bata fada masa ba.

Da yamma bayan sunyi sallar la'asar suna zaune a falo ita da Baby laptop ce a hannun ta tana duba project dinta, Baby kuma tana zaune tana kallo, sukaji kararrawar kofa, tace Baby taje ta duba, tashi tayi tana kunkunin an dame ta, tace kyaji dashi amma wllh bazan tashi ba ke zaki je.

Bayan ta bude sai taga ta tsaya bata dawo ba kuma babu wanda ya shigo, murya ta daga tace Baby ke da waye ne, wata ce wai bakuwa ce, to ki matsa kice ta shigo mana, dawowa Babyn tayi ta cigaba da kallon ta, can kuma kamar bazata shigo ba sai taga an turo kofar an shigo.

Wata mata ce ta shigo yar gayu sosai kana ganin ta kaga isashshiyar mace mai ji da kudi ilimi da kuma wayewa, cikin takun ta wanda mai cike da isa da kuma gayu ta karaso cikin falon ta yiwa kanta mazauni a daya daga cikin luntsuma luntsuman kujerun falon, tana bin ko ina na cikin falon da kallo, wani irin kallo wanda kai tsaye zaka iya kiran sa da kallon wulakanci ko kuma raini.

Ita dai Saudat bin ta kawai take da kallo, sai da ta gama isar ta sannan ta juya ta kalli Saudah, sannu fa Amarya na shigo miki falo babu ko sallama, murmushin yake Saudat tayi, tace babu komai, ina wuni, dan tana tunanin duk yanda akai wannan matar tana daga cikin dangin Abdul, dan ko ba'a fada maka ba, ga kama nan karara a kan fuskar ta da Abdul din.

Lafiya ta amsa mata a yatsine, ya amarci, ita dai Saudat tayi shiru, Baby je ki ce a kawowa bakuwa ruwa, no no nagode ni ai ba bakuwa bace yar gida ce, ko kuma nace masu gidan, baki Saudat ta saki tana kallon ta, ta saki dariya ganin irin kallon da take mata.

Baki sanni ba ko, eh gaskiya ban gane ki ba, bai taba fada miki wacece ni ba, uhmm babu komai bari ni na fada miki, sunana Zarah Yayar mijin ki Abdul, ina fatan kin gane, eh sannu da zuwa, kiyi hakuri ban san ki bane, babu komai, mikewa Saudah tayi, bari na kawo miki wani abu.

Aa fa nagode tafiya ma zanyi, ina fatan zaki sanar dashi zuwa na, insha Allah mun gode ki gaida gida, ki gaida Hajiya, bata amsa mata ba ta juya tayi gaba, sai da taje bakin kofa, sai kuma ta juyo ta kalle ta tace ki fa tabbatar baki manta ba ki fada masa zuwana, ki kuma ce masa shima idan ya dawo zan kawo masa tashi ziyarar, to tace mata, ta juya ta fice.

Tsautsayi Part (17)
Aisha Muhammad

Ita dai Saudat tsayawa tayi a wajen kamar an dasa ta, tana mamakin wannan bakuwa tata mai ban mamaki, tana tsaye a wajen har sai da Baby ta kula da ita tace Aunty Saudah lafiya, sannan ta farga tace lafiya Baby, tun bayan tafiyar ta, taji gaba daya jikin ta kamar bata da lafiya, wani iri take jin ta.

Bayan sallar magariba ta kira Abdul bayan sun gaisa tace masa Abdul dama kana da wata Yayar amma baka taba fada min ba, wace Yayar kuma, ban sani ba, ke dan Allah da gaske nake ban gane ba, aa Yayar ka mana Zarah, daman kana da wata yayar me suna Zahra Kuma baka fada min ba, ke Dan Allah bana San wasa, wasa ko to da kanta tazo dazu ai, kuma wllh naga alamar taji haushi da nace ban santa ba.

Gaban sa ne ya fadi ya maimaita tazo, eh mana ya naga kana mamaki haka, akwai wani abu ne, aa babu, me tace miki, babu komai kawai dai mun gaisa ne, kuma da zata tafi tace na tabbatar na fada maka zuwan ta, sannan na fada maka kaima idan ka dawo akwai taka ziyarar ta musamman, sai da har muryar sa ta fara rawa yana mata magana.

Ke Saudah bana son zancen wasa, aa kamar ya wasa wai, wai ko dai akwai wani abu ne naji gaba daya ma ka wani rude, aa ba rudewa nayi ba, kawai dai ina mamaki ne, to meye abin mamaki kodai ba yayar ka bace, aa yaya tace baban mu daya, to amma dan Allah meyasa baka taba fada min kana da wata yayar ba, kinga Saudah yi hakuri zamuyi magana daga baya yanzu akwai abinda nake ne, idan na gama zan kira ki.

Daga nan bai kuma mata maganar ba, itama kuma bata masa ba, washe gari da asuba da ta tashi sallar asuba bataga Baby a kan gadon ba, sai ta dauka tana toilet, ta dan jira shiru bata ga ta fito ba, har ta gaji ta mike zuwa tayi ta kwankwasa kofar toilet din, shiru ba'a amsa ba, sai ta tura kofar ta shiga, bata ciki, tayi mamaki amma data tuna fitina irin ta Baby sai ta share, tace watakila ta sauka kasa yin wani abu.

Harta idar da sallah bata ga ta shigo ba, sai ta mike ta fita, dakin dake kallon nata ta fara lekawa bata ciki, fita tayi har dakin Abdul sai da ta leka dan tasan fitinar Baby zata iya shiga, amma bata ciki, daga nan kasa ta sauka, tana fara sauka ta hango ta akan carpet a kwance tana bacci, yanayin kwanciyar tata ne dai bai mata ba, dan haka ta karasa sauka da sauri ta isa wajen ta.

Kirji ta dafe ganin Babyn a kwance cikin jini male male, Bata iya taba ta ba, jikin ta yana ta rawa ta kwalawa Baba Mairo kira, da gudu ta fito jin irin kiran tasan bana lafiya bane, itama tana zuwa taga yanda Babyn ke kwance ba karamin tsorata tayi ba, mun shige su Hajiya meya same ta, nima haka nazo na ganta, Baba Mairo ce tayi karfin halin karasawa ta taba Babyn, abun mamaki tana tabata sai ta juya, zaro ido sukayi suka kalli juna, dan a tunanin su ma irin wannan jini da suka gani bata ma da rai.

Kiran sunan ta Saudah tayi, Baba Mairo ma ta kara mata da karfi tana dukan gefen cinyar ta, firgigit ta bude idon ta, tana turo baki tana mutsuka idon ta, wai ita an dame ta, Aunty Saudah menene, ke tashi dallah, idon ta ta bude sosai jin Aunty Saudah na mata tsawa, ai tana bude ido ta ganta cikin jini ta kwala ihu, Aunty Saudah ce ta kuma mata tsawar ki nutsu Baby.

Tsautsayi Part (18)
Aisha Muhammad

Amma ina bata saurare ta ba, kuka kawai take babu kakkautawa, Baba Mairo ce ta kamo hannun ta da kyar ta wuce da ita toilet din dakin ta ta wanke mata jiki Saudah ta kawo towel aka daura mata, sannan ta kama ta suka haye sama, har lokacin kuka take, Baba Mairo kuma ta shiga gyaran wajen.

Da kyar Saudah ta samu tasha kan ta ta hakura bayan ta mata dabarar ba jini bane zobo ne Baba Mairo ta dauko daga kitchen ta watsa mata, haka dai ranar daga Saudah har Baba Mairo suka wuni a gidan cikin rashin walwala, abin sai damun su yake, da dare yayi ma sun dade basu kwanta ba suna tunanin yau kuma dame zasu wayi gari, amma Saudat ta kudurce a ranta nidai gobe ma suka kuma tashi da wani tashin hankalin, to wllh ko dai Abdul ya dawo a goben ko kuma ta tafi gida.

A ranar da daddare basu wani dade suna hira ba suka tafi suka kwanta har Baba Mairo wacce dama ita bata fiya jure hirar dare ba, bayan sun kwanta Abdul ya kira Saudah, sun dade suna hira tana ta masa korafin ya fadi ranar da zai dawo yana ce mata ya kusa, da haka dai suka rabu tana fushi, daga nan bayan ta kashe wayar ta juya ta kwanta.

Can cikin bacci taji kamar ana buga mata kofa, a dan tsorace ta farka, mikewa tayi bayan ta tabbatar dakin nata ake bugawa, kamar me sanda ta isa bakin kofar, waye tace, nice Hajiya taji muryar Baba Mairo, hannu tasa ta bude kofar, Baba Mairon ce kuwa a tsaye a bakin kofar, amma kana ganin ta kasan bata cikin nutsuwar ta.

Aa Baba meya faru baki da lafiya ne, aa wllh Hajiya ni dai tsoro nake ji, da mamaki ta kalle ta, tsoro kuma tsoron me, wllh Hajiya tun bayan da muka tafi muka kwanta ina shiga daki sai na tuna ina so na gyara kaya na sai kawai na zauna na fara, tofa bayan na gama na kwanta kenan sai naji kamar motsi a falo, da sai na dauka ko kece kika fito yin wani abu, to daga baya sai motsin yayi yawa sai na tashi na fito, ina fitowa kuma babu kowa.

Har kitchen na duba amma babu kowa wutar falon ma a kashe take naje na duba kofa naga tana nan a rufe, na koma daki na kwanta na watsar, tofa bayan na koma har na fara bacci sai naji ana buga min kofa, na tashi nace waye sai naji muryar ki, hakan yasa na bude amma abin mamaki da na bude babu kowa, na koma na kwanta sai aka cigaba da bugawa, na kuma budewa babu kowa amma sai naga kamar gilmawar mutum sai na fito da niyyar nazo na fada miki, to wllh Hajiya ina tafiya ina ji ana bina har nazo nan.

Komawa tayi ta dauko room sliper tace muje, bin bayan ta Baba Mairo tayi amma tana dari dari dan ita tasan abinda taji, suna sauka suka nemi switch din kwan falon suka kunna, suna kunnawa juyowar da zasuyi sukaga mace a zaune a kan kujerar falon ta juya baya ta baza gashi a gadon bayan ta, jikin su ne ya fara rawa suka rike juna.

Tsautsayi Part (19)
Aisha Muhammad

Saudah ce tayi karfin halin cewa waye nan, shiru babu amsa, suna tsaye kamar an dasa su kuma sun kasa gudu, kawai basu ankara ba ta juyo da wani irin sauri, fuskar Saudah ce sak a fuskar matar amma idanun ta da bakin ta duk jini, ga kuma wuka a cikin ta a cake, ihu suka kwala suka juya a 360 wannan na ture wannan suka nufi sama, ita kuma ta bushe da wata irin mahaukaciyar dariya da suke jin karar ta kamar zata fasa dodon kunnen su.

Da gudu suka shiga daki suka buga kofa bam, karar rufe kofar ne ya tashi Baby dake bacci, ta mike tana tambayar Aunty Saudah lafiya, Baby mun shiga uku aljanu ne a gidan nan, Baba Mairo tace haba Hajiya kada ki tsorata ta mana, ai tuni ta diro daga gadon tazo ta kwakume ta.

Ai suna cikin wannan kaduwa sukaji wata irin iska mai matukar karfi kamar guguwa ta bude window dakin na waje, ga wata irin kara kamar tsawa tare da iska da haske kamarwalkiya yana shigowa cikin dakin, iskar kamar zata dauke su, hadewa sukayi waje daya suka rungume juna suna ta zabga salati har sai da sukaji iskar ta fara lafawa sannan wannan tsawar ma babu.

Saudah tace Baba Mairo jeki rufe mana window, ido Baba Mairo ta zaro tace haba yar nan rufa min asiri nida ban iya abin ku na birni ba ai sai na fada kasan dan Allah ke dai kije ki rufe, haka babu yanda zatai tayi karfin tashi ta nufi window dan tasan Baba Mairo kawai bazata je bane.

Tana zuwa ta zura hannu zata rufo kenan, saiga wannan fuskar matar da suka gani a falo ta leko ta window tana kyalkyala musu wannan mahaukaciyar dariyar, ai kan kace kwabo sun bar dakin kamar wasu walkiya, dakin dake kallon nata suka shige suka banko kofar, sannan suka tsaya suna haki.

Ai basu gama numfasawa ba sukaji ana nocking kofar dakin daga Saudah har Baby kuka suka barke dashi, Baba Mairo ce tayi karfin hali ta danne zuciyar ta bata koka ba, dan kada ta kara sagar musu da gwuiwa, amma fa itama idan ka kalli fuskar ta sai kayi dariya sabida tsananin tashin hankalin da zaka gani.

Can kuma sai sukaji ana magana, Saudah ki bude nice, Aunty Zarah ce, amma ina ai ko motsi basuyi ba, wannan dare dai sunga bakin dare dan yanda suka ga rana haka suka ga dare, har sai da aka fara kiraye kirayen sallah sannan sukaji gidan yayi shiru basu kara jin motsin komai ba, amma duk da haka babu wanda yayi yunkurin fita, har saida sukaga gari yayi haske sosai suna jin masu aiki suna ta buga kofa sunga ba'a bude ba zasu shigo su fara aiki, amma basu yi yinkurin budewa ba, sai a lokacin ma suka tashi a tare suka shiga bandakin dake cikin dakin sukayi alwala suka fito suka yi sallah.

Suna idarwa suka fita dakin Saudah suka koma ta dauki wayar ta kawai da mukullin mota suka fito, sai a lokacin suka bude kofar masu aikin har sun gaji da bugu sun koma bangaren su, a tunanin su makara sukayi.

Tsautsayi Part (20)
Aisha Muhammad

Sanda suka fito mai gadi ne kawai a zaune yana jin radio, da sauri ya taso yana gaishe da Saudah a takaice ta amsa masa, tayi wajen rumfar ajiye motoci tana ce masa ya bude mata get, Hajiya lafiya kuwa lafiya, kawai ka bude min get nace, kana ganin yanayin su kasan ba lau ba, amma kuma bashi da hurumin kara tambayar ta hakan yasa yace Allah ya huci zuciyar ki Hajiya, ya wuce ya tafi bude mata get din, ita kuma ta nufi motar da zata hau, su Baby da Baba Mairo suna biye da ita.

Sanda suka isa gida babu wanda ya tashi a gidan sai masu aiki da suke ta kai kawo a cikin gidan, ganin haka yasa kawai ta wuce dakin ta na gidan data bari, Baby ma dakin ta ta wuce Baba Mairo ce ta wuce bangaren yan aiki, suna zuwa dukan su bacci suka koma dan sun dauki bashin sa.

Daga cikin mutanen gidan babu wanda yasan da zuwan su dan haka koda suka tashi harkar gaban su suka shiga, sai da Abba da Yaya Sadiq suka shirya zasu fita akwai inda zai kai Abba kafin shi kuma ya wuce aiki, suna fita harabar gidan a wajen ajiye motoci suka ga motar Saudah a fake, Abba ne ya fara lura yace da Yaya Sadiq mai ya kawo motar Saudah gidan nan kuma, shima kallon motar yayi da mamaki, dan ko jiya da dare ya dawo amma babu motar a wajen.

Mai gadi Abba ya kwalawa kira, ya taso da gudu yazo, waye ya kawo motar nan, Hajiya karama ce tazo dazu ai da sassafe kana nufin Saudah, eh ita Alhaji, kallon juna sukayi da Yaya Sadiq muje cikin gidan Sadiq yace da mai gadin yaje.

Ciki suka koma suka tarar da Mommy tana zaune a falo da laptop a gaban ta, kallon su tayi, aa mantuwa kukayi ne, zama sukayi tukunna ita dai tana kallon su, yaushe Saudah tazo bansani ba, Saudah kuma, eh Saudah ga motar ta nan a waje kuma mai gadi ya tabbatar min da ita ce tazo tun dazu, aa to bari na duba dakin ta.

Mikewa tayi ta haye sama, can kuwa sai gasu ita da Saudan harma da Baby, idanun su fal bacci, kuma harda kayan bacci a jikin su, duka kallo suka bisu dashi har suka zo suka zauna, suka gaida Abba sannan Yaya Sadiq, Abba ne ya kalle ta, Saudah meya kawo ki gida da sassafe bayan ma kuma mijin ki baya gari, kuka ta fara wanda yasa gaban su duka faduwa, dan su a tunanin su matsala suka samu da Abdul din.

To kin saka mu a gaba kina ta faman kuka kiyi mana bayanin abinda yake faruwa mana, wllh Abba bazan koma wannan gidan ba, subhanallahi, haba Saudah yaya daga yin aure har zaki fara yaji kuma har kina rantsuwa baza ki koma ba, Abba bafa yaji nayi ba, Mommy ta cafe da cewa to me kika yi, yanzu Saudah wannan na koyar dake kenan, to Allah ya gani wannan ba tarbiyya ta bace, dan gani nan aure na da mahaifin ki ban taba yaji ba.

Baby ce tayi tsalam tace Mommy bafa yaji tayi ba aljanu ne suka koro mu daga gidan, dukan su kallon ta sukai, suka hada baki wajen fadin aljanun kuma eh aljanu Abba, ke Saudah fada mana yanda zamu gane.

Tsautsayi Part (21)
Aisha Muhammad

Nan ta shiga basu labarin duk irin abubuwan da suka dinga faruwa amma bata fada musu batun Aunty Zarah ba, sosai abin ya daure musu kai, amma sai suka ce wala'allah dadewar da gidan yayi ne babu kowa yasa shedanu suka sami wajen zama, sallamar ta Abba yayi yace idan ya fita zai kira Abdulmalik din ya sanar da shi.

Bayan fitar su Abba komawa sukayi wani baccin dan bacci ne sosai a idon su, zaune suka bar Mommy tana ta kakabin abin, har Baba Mairo sai da ta kira ta kuma ji daga bakin ta, su Abba kuwa suna fita ya dauki waya ya kira Abdulmalik bayan sun gaisa yake fada masa Saudah fa tana gida.

 Subhanallah, Abba meya faru, nan ya kwashe duk bayanin da ta musu ya fada masa, sosai hankalin sa ya tashi amma bai nunawa Abban haka ba, sai kawai yace masa insha Allah duk yanda ake ciki yau dinnan zai taho, Allah ya tsare Abban ya masa sukai sallama.

Saudat kuwa ba ita ta tashi ba sai sha biyu na rana, bayan tayi wanka ta sakko, ta sami Mommy a falo ita da Baby tana ta mata sharhi akan abinda ya farun, zama tayi ta gaida Mommy sannan tasa aka kawo mata abin kari, tana ci suna dan taba hira da Mommy, suna nan ma Abba ya dawo yake sanar dasu yanda sukayi da Abdul.

Kamar yanda kuwa ya fada karfe biyu na rana ya sauka, gidan Hajiya ya fara zuwa suka gaisa suka dan taba hira akan abinda ya kai shi Abujan amma bai mata zancen abinda yake faruwa a gidan nasa ba dan baya son ya daga mata hankali, sun dan jima suna hira sai da aka kira sallar la'asar sannan ya mata sallama akan idan yayi sallah zai wuce da ga nan.

Bayan yayi sallah wani abokin sa Salis ya kira, yace masa dan Allah yana son su hadu akwai inda yake so ya raka shi, yace masa ya same shi a gida, bayan yaje ya kira shi yace masa yazo, fitowa yayi yana ce masa ya shigo mana, gaban mota ya bude masa yace kaga Malam dan Allah shigo ba zama nazo yi ba, shigo mu tafi, ka fara baudadden halin naka ko, cewar Salis, eh naji ni dai shigo mu tafi.

Shiga yayi yaja motar, sai da suka fara tafiya sannan yace masa, kaga nifa wajen wannan islamic center Yayan kan nan zaka raka ni, to waye babu lafiya, wllh matsala ce dai kamar ta shaidanu a gida na, nayi tafiya ma bana nan zaman gidan ya gagare ta sai da ta koma gida, shine dole yau na taho, to yanzu ma ko gidan nasu banje ba, ina so ne sai an warware matsalar, to Allah ya warware mana, Ameen.

Suna zuwa kuwa sukai sa'a yana nan a wajen, kai tsaye office dinsa suka wuce, bayan sun gaisa ya masa bayanin duk abinda yake tafe da su, cewa yayi insha Allah babu komai, zamuyi iya bakin kokarin mu, da ikon Allah babu abinda zai kuma faruwa, yanzu zamuje gidan akwai aikin da za'ayi a cikin sa, sannan za'ayi sauka duka a yau din insha Allah, tunda kace baka so abin yaja lokaci zamu tafi da yara da yawa.

Godiya ya masa, daga nan ya fita ya hada kan duk wadan da zasu tafi dasu, sannan ya dawo, ya musu magana suka fita su suka shiga motar su sannan shima shi da Salis suka shiga tashi motar, yana tafiya suna bin bayan sa har suka isa gidan, yana shiga yace masa tabbas akwai shaidanu a gidna nan, amma da ikon Allah za'a kore su, to Allah ya bada sa'a cewar Abdul.

Tsautsayi Part (22)
Aisha Muhammad

Daga nan ya rarraba yaran sa waje waje a cikin gidan wadan da zasuyi sauka, shi kuma dashi da wasu suna falon a zaune suna gudanar da wasu addu'o, da Abdul da Salis ma barin gidan sukai akan idan sun gama zai kira Salis, daga nan gidan su Saudah suka wuce bayan sunje yasa mai gadi ya masa iso, dan yau din gaba daya wayar ta a kashe take.

Kafin mai gadi ya wuce sai ga motar Yaya Sadiq ta shigo gidan, tsayar da mai gadin yayi yace ya barshi, bayan yayi parking wajen su ya nufo, ya mika musu hannu suka gaggaisa, yace saukar yaushe, yace wllh dazun nan, sannu da zuwa, to ya akai baku shiga ba, aa yanzu da zan tura mai gadi ya sanar dasu sai kuma gaka, ayya to bisimillah, wucewa yayi suka bishi a baya.

Falon saukar, baki ya kai su sannan yace musu yana zuwa, ya wuce ciki, kafin kace kwabo an cika musu gaban su da kayan motsa baki kai kace dama an san da zuwan su, babu jimawa kuma Abba yayi sallama ya shigo, dukan su sauka sukai daga kan kujerar yace aa su koma su zauna idan ba haka ba bazai amsa gaisuwar su ba, haka dole suka koma suka zauna, sannan shima ya nemi waje ya zauna.

Bayan sun gaisa suka dan jajanta akan abinda ya farun Abba ya bashi hakuri akan tahowar Saudat din gida ba tare da sanin sa ba, yace haba babu komai wllh ai tayi dai dai ma akan ta zauna wani abu yazo ya faru fa, ai hakan shine dai dai, kuma insha Allah hakan bazata sake faruwa ba, dan yanzu haka ma bayan ya sauka kafin yazo nan sai da ya wuce ya nemo Malamai yanzu haka ma suna gidan suna sauka da wasu karatuttuka, dan haka zuwa bayan sallar isha'i zai zo sai su tafi da Saudat din.

To Masha Allah babu laifi Allah ya kaimu ya kuma kiyaye gaba, suka amsa da ameen, sannan ya mike yace bari ya kira musu Saudah ya juya ya fita suna masa godiya, bayan fitar sa sosai Salis ya shiga yabon halin Abban, yana cewa gaskiya mutumina kayi dacen siriki, wllh haka duk yan gidan suke suna da kirki.

Babu jimawa sukaji sallamar ta, duka hada baki sukai wajen amsa mata, ta shigo ta nemi waje ta zauna bayan sun gaisa Salis ya mike ya fita yana kara wayar sa a kunne wai shi a zuwan kiran sa akai, amma yayi hakan ne dan ya basu waje.

Bayan fitar sa ma kin yi masa magana tayi sai da yayi ta lallashin ta sannan ya samu ta sakko dan ita duk abinda ya faru laifin sa take gani.

Tsautsayi Part (23)
Aisha Muhammad

Lallashin ta yayi ta yi, har ya samu ya shawo kanta ta amince zata koma, yace yanzu zai tafi ta shirya bayan sallar isha'i zai zo sai su tafi.

Bayan sunyi sallar magariba suka koma gidan, shida Salis suna zuwa kuwa suka tarar sun gama, a cikin falon sukai jam'in sallar magariba, baya ni ya musu akan sunyi duk abinda ya kamata a gidan, insha Allah baza'a kuma samun wata matsala ba.

Godiya sosai Abdulmalik ya masa sannan ya sallame su suka raka su har bakin motar su, sannan suka koma suka shiga motar Abdul din zai maida Salis gida daga nan kuma ya wuce ya dauko matar sa.

A masallacin unguwar su Saudah yayi sallar isha'i dan ya gaji so yake kawai ya dauke ta su koma ya samu ya huta, tunda ya shigo garin baiyi hutun awa daya ba, sai zirga zirga da yake, ana idar da sallah, ya karasa kofar gidan su ya mata waya yace ta fito su tafi sauri yake basai ya shigo ba.

Jakar ta ta dauko da wayar ta, ta sauko ta sami Mommy a falo ita kadai su Abba basu dawo daga masallaci ba, Baby kuma tana dakin ta, sallama ta mata, ta sanar da ita yazo yana waje yana jiran ta, nasiha Mommyn ta mata, tare da jaddada mata ta kula da addu'a, tace insha Allah, zama tayi kuma, Mommy ta kalle ta meye haka, su Abba nake jira su dawo, dakuwa ta mata, sannu yar rainin hankali, ni zaki mayar wata yarinya.

      Naga har kin min sallama, sai faman zumudi kike, shine yanzu kuma dan wani munafurci wai ke ki nuna min baki damuba ko shine zaki wani zauna, kin tashi ko sai na bige ki, su Abban ai zan fada musu ko, mikewa tayi tana dariya kai Mommy yaushe nake wani zumudi, zuwa jibi ma zan shigo sai na dauki mota ta.

      Kar naga kafar ki a kwanan nan kin dinga fitar kenan daga yin aure, gobe zan sa driver ya kai miki indai mota ce, kai Mommy kora ta ma kike, eh na kore kin, wai zaki wuce ko kuwa, kin shanya bawan Allah a waje, tsayawa ta kuma yi sai da taga Mommyn ta mike tukunna ta fita da gudu tana dariya.

A bakin get ta same shi yayi parking, tana hango shi, ta gyara fuskar ta, taci magani wai ita irin jan ajin nan, ta bude motar ta shiga tana wani ciccin magani, kallon ta yayi, aa gimbiya yau ko sallama bazan samu bane, banza ta masa, yayi dariya ganin yanda ta tamke fuska, wai har yanzu fishin ne bai kare ba, nan ma shiru ta masa, yace ni dai dan Allah a min magana wannan fishin a adana shi sai munje gida, nayi alkawarin zanyi lallashi.

Da dai yaga bata da niyyar masa magana, sai ya fara Tsokanar ta kamar yanda ake yiwa yara yana kamo ta nan kamo ta nan, bata san sanda ta fara dariya ba, godiya ta kuma yiwa Allah daya bata mijin da ya san duk hanyar da zai bi yaga ya saka ta farinci, baya taba kosawa da wani hali nata, dama fushin na karya ne, ai ni nasan baza ki iya fushi da habibi ba ko ya fada da sigar tsokana.

Tsautsayi Part (25)
Aisha Muhammad

Tana wannan tunanin bata ankara ba taji yana horn ashe har sun iso gida, mai gadi ne yazo da gudu ya bude musu, suka shigo, bayan sunyi parking ya karaso bakin motar yana musu sannu da zuwa, sannan kuma yace yallabai kayi bakuwa, da mamaki ya kalle shi bakuwa kuma, eh tana ciki ma tana jiran ka.

Wace irin bakuwa ce haka da daddare kuma ka barta ta shigar min gida, kayi hakuri Alhaji, wllh dan tace min ita Yayar ka ce kuma tabbas naga kama shiyasa amma Alhaji dan Allah kayi hakuri, jikin sa ne yayi sanyi da yaji ya ambaci Yayar sa kuma wai suna kama, dan haka bai tsaya sauraren sa ba, ya fito ya rufe motar, yace yaje kawai, dan baya son ya cigaba da maganar Saudah dake waya da Mommy ta fahimci maganar.

Da sauri ya rufe motar yayi hanyar falo, Saudah tabi bayan sa tana tambayar saurin me yake yi, babu komai muje kawai, yana shiga falo wayam babu kowa, kalle kalle ya fara yana bin ko ina na cikin falon da kallo, Sauda data shigo a bayan sa tace me kake kallo haka, wayancewa yayi da sauri ya basar, aa babu komai, wllh yunwa nake ji, kiyi sauri ki dafa mana koda indomie ce.

Baki ta zumburo gaba, to ai sai ka bari na canza kaya ko, naji dan Allah kiyi sauri, sama ta haye tana yan kunkunai, tana hawa ya cigaba da bincike falon daga nan ya haura sama, dakin sa ya fara lekawa har toilet, haka ya fito ya dinga leka dakunan dake saman, yana haka ta fito ta same shi, wai meye kake nema ne haka, da sauri ya juyo kamar barawo, babu komai kawai ina lelleka daku nan ne nayi kewar su, murmushi tayi kawai tayi hanyar stairs ta barshi a wajen.

Shima sauka yayi ya fita wajen mai gadi yace kace nayi bakuwa, eh Alhaji, to ai ni banga kowa ba, aa tana ciki mana, yauwa ga Tabawa nan mai aiki ita tayi mata iso ma cikin falo, kira ya kwala mata, ta taho wajen su, bayan ta gaishe da Abdulmalik mai gadi ya tambaye ta, ba ita ta raka wata bakuwa ciki ba dazu, tace eh ita ta raka ta, daga nan ta shiga kitchen, amma data fito daga kitchen bata ganta ba, to amma da yake ta dade a kitchen din sai tayi tunanin ko ta kasa jiran nasu ne tayi tafiyar ta.

Kallon mai gadin yayi to amma kai baka ga fitar ta ba, eh wllh Alhaji banga fitar ta ba, walaAllah ko na dan kewaya ne lokacin data fita, daga haka bai tsaya jin wata magana ba kawai ya wuce ya barsu a wajen.

Yana shiga falo, yaji karar wayar sa daya bari akan center table, da sauri ya karasa ya dauka, yana dauka yaga sunan Aunty Zarah baro baro akan screen din ga kuma hoton fuskar ta tar akan screen din, jikin sa ne ya fara rawa wayar na neman faduwa a hannun sa, danna kashe kiran yayi, amma yaki kasuwa saima karar ringing din da take kara yawa, sai kuma hoton nata ya fara dariya, can kuma sai ya koma kuka, hawayen jini na zuba a idon ta.

Tsautsayi Part (26)
Aisha Muhammad

jifa yayi da wayar yana yarfe hannun sa wanda wannan hawayen nata na jini ya fara tabawa, hakan yayi dai dai da fitowar Saudah daga kitchen, da tray din data jero flate din indomie data dafa, da kuma juice da cups.

Itama saura kiris ta zubar da abinda ke hannun ta, dan ta tsorata da halin da ta ganshi a ciki, kan center table ta samu ta ajiye tray din, sannan ta isa wajen sa tana tambayar sa lafiya, ganin jini a hannun sa yasa tayi saurin kamo hannun nasa tana tambayar sa dame yaji ciwo.

Kasa bata amsa yayi kawai sai nuni da yake mata da wayar sa, inda wayar take a yashe taje ta dauka, duk screen din ya fashe, data danna ma kin kawowa tayi da alama dai wayar ta sami matsala, ajiyewa tayi ta dawo inda yake, ya akai wayar ta fashe kuma har ta ji maka irin wannan babban ciwon haka.

Da kyar ya samu ya dai daita nutsuwar sa, sannan yace mata kada ki damu ba wani babban ciwo bane, bari naje sama akwai first aid box a daki na kada ki damu zan wanke, bari nazo na taimaka maka, ta fada tana kokarin kama shi, kallon ta yayi cikin dakiya, yace meye haka wai kin dauka kowa ma irin ki ne, mai shegen raki, wannan dan ciwon ni a waje na ba komai bane, kuma bari ki gani yanzun nan zanyi dressing abu na na sakko kamar bani ba.

Dariya tayi, kaji kuri kamar ban san labarin irin rakin ka ba, ka manta labarin da rannan abokin ka ya bani, dalla share shi, yanzu ai zaki tabbatar, to ai sai ka bari na bika na gani ko, aa wa zai jire mana abincin, ki zauna kawai, hmm ka dai ji dashi baka son nazo na ganka kana ihu, eh naji, ai idan dai kuka nayi zaki gani a ido na, to ai shike nan, amma wllh idan ka dade sai na hawo, naji ya fada yana hayewa sama.

Yana shiga dakin toilet ya wuce da sauri ya wanke jinin, sai da ya wanke hannun sa babu adadi amma duk da haka bai ji ya gamsu ba, har sannan ji yake kamar akwai sauran jinin a hannun sa, haka dai badan ya gamsu da hannun ba ya fito gudun kada Saudah ta ji shi shiru ta biyo bayan sa.

First aid din ya dauko ya samu plasta ya saka a wajen ya rufe wajen sabida kada taga babu ciwo a wajen, yana gama sakawa ya mike ya fita bayan ya maida akwatin, a zaune ya same ta tana dannan waya, hannu yasa ya warce wayar, ta juyo a dan tsorace, ganin shine yasa ta bata rai, bani waya ta, bazan bayar ba, wai ke bakya gajiya da dannan waya ne.

Eh to ina ruwan ka, da ruwa na mana, tunda yanzu a karkashi na kike, sannan ma kinga ai akwai agreement a tsakanin mu, dan haka daga yanzu idan ina gida bake babu dannan waya, ni kadai zaki bawa lokacin ki, kina ji na ko, ya fada yana kama kunnen sa alamar gargadi.

Ita dariya ma abin ya bata, tace to sannu ai dai naga agreement din namu na iya yau ne, kai dai kawai Malam kana so ne ka kadar da hankli na kada na gane kayi kuka, Allah ya kiyaye zo ki duba ido na, naki din kawai na rabu da kai sabida dai baka da lafiya, ni kalau nake kawai dai kinsan nafi karfin ki ne shine kika ji tsoro.

Tsautsayi Part (27)
Aisha Muhammad

Dariya tayi eh naji tsoron naji, zo ka zauna kaci abinci, yanzu ma nasan ya gama hucewa, naci ko kuma muci, aa wllh ni na koshi, kaga wannan juice din to shi kadai zan sha, ai wllh baki isa ba, ko dai kici da kan ki ko kuma na miki dura, irin wacce ake yiwa yara, kallon sa tayi, Allah ko, au kina shakka ne, aa maji ma gani.

Zama yayi yana yarinya zaki sani ne wllh naga alamar kin gama raina ni a gidan nan, inaga dai ya kamata mu raba raini, hmm kawai tace bata tanka masa ba, ya zauna ya janyo table din data dora abinci gaban sa.

Yana budewa sai kwano wayam, ga dai alamun abinci nan, amma an cinye, abun ne ya daure masa kai, da baiga alamun abinci ba sai yace dama yarinyar nan raina masa hankali tayi bata dafa komai ba, to amma ga alamun abinci nan kuma da alama ma yanzu aka cinye abincin, juyowa yayi yana kallon ta, ganin irin kallon daya ke mata, yasa ta maida hankalin ta kansa.

Lafiya, nuni ya mata da flate din abinci da ido, tana kalla ta mike zumbur, na shiga uku waya cinye abincin nan ina zaune, wllh tunda ka tashi ban motsa ko ina ba, ganin yanda ta gigice yasa ya kara tabbatar da ba ita ta cinye ba, dan dama bata da dalilin yin hakan, tabbas akwai matsala har yanzu a gidan nan.

Hankalin ta yayi matukar tashi ko zama ta kasa, hakan yasa ya mike ya riko hannun ta, haba Habibty meye na daga hankali ba kawai sai na sha tea ba, dama fa ba wata yunwa nake ji ba, ya fada dan ya kawar mata da wani tunani a ranta, amma ina hakan bai samu ba, tace haba Abdul taya hankali na bazai tashi ba, dama ai ba ta abincin ake ba, tashin hankali na shine ina abincin ya shige ina zaune a wajen nan.

Dariya yayi gyangyadi kikayi wani yazo ya juye, waye wanin eyye, haba Abdul ka daina kawo wasa kana kokarin batar min da hankali, nifa ba yarinya bace, tabbas da kace min an kori shaidanun da suke gidan kodai ka rufe min ne dan na dawo ko kuma basu koru ba, dan haka ni wllh bazan kwana a gidan nan ba.

Haba Saudatu na, meye hakan wai kike yi tsoron me kike ji bayan gani, ina mai tabbatar miki babu abinda zai same ki matsawar ina nan, wancan lokacin ma dan bana nan ne, kuma yanzu na miki alkawarin bazan kuma yin tafiya na barki ba.

Kaga nifa babu wani dadin baki da zaka min, kaine zaka iya ji da aljani, dariya yayi ya kamo hannun ta suka zauna akan kujera, ya dinga lallashin ta yana fada mata maganganun da zasu karfafa mata gwuiwa, duk da shima tashi gwuiwar a sanyaye take.

Tsautsayi Part (28)
Aisha Muhammad

Haka dai dakyar ya samu ta dan nutsu, sannan yaje da kansa ya hado musu tea tana biye dashi dan tace bazata kara zama ita kadai a gidan nan ba, shi dai sai dariya yake mata, yace kinga kuwa dole ki zauna ke kadai tunda dai mu kadai ne a gidan nan, idan zan tafi aiki ma bi na zakiyi, eh mana idan kuma kace bazan bika ba sai na tafi gida idan ka dawo sai na dawo.

Dariya yayi dama ana aure a haka, za'a fara daga kan mu, to idan zan shiga toilet ma bina zakiyi, sai na tafi wajen masu aiki, har tsakar dare, diddira kafa ta farayi tana kukan shagwaba, wllh bana so, sai ka sa na tafi gida ma a daren nan, aa yi hakuri ba za'ai haka ba wasa nake miki.

Haka ya hado musu tea suka zauna suka sha, yana dan jan ta da hira da wasa, har suka gama, yaje ya kulle kofar falo, suka haye sama, bayan sun kwanta babu dadewa Saudah tayi bacci, amma shi ya kasa baccin, dan dama duk wata raha da yake yi, yana yi ne kawai dan ya kwantar mata hankali amma zuciyar sa cike take da fargabar abubuwan da suke faruwa.

 Ya kai dare sosai kafin ya samu bacci barawo ya dauke shi, bai dade da yin baccin ba yayi wani mummunan mafarki kuma dai again da Aunty Zarah yayi mafarkin, a firgice ya farka, yana ta yanka zufa, zama yayi yayi shiru yana nazarin mafarkin, bai gano komai ba, hakan yasa kawai ya mike ya shiga toilet ya dauro alwala yazo ya tada sallah.

Haka ya kwana yana raya daren, koda zai tafi sallar asuba bai tashi Saudah ba, gudun kada ya tashe ta, ta tada rigima ta hana shi fita sallar a jam'i, dan haka ya kyale ta, sai da ya dawo sannan ya tashe ta.

Bayan ya gama azkar ya samu ya koma bacci, ai kuwa kasancewar bai samu bacci ba jiya, har sai da yaso makara, dan yaso ya fita kamar karfe tara, dan jiya daya dawo bai samu damar lekawa aiki ba, kuma akwai bukatar hakan, shiyasa yau yaso fita da wuri, amma bashi ya farka ba sai bayan karfe goma, shima dakyar ya yaki kansa ya mike.

Sanda ya tashi baiga Saudah ba, amma yaji motsin ruwa a toilet hakan yasa ya san tana toilet, komawa yayi ya kwanta yana jiran ta fito, shiru shiru bata fito ba, ya daga murya yace sweetheart dan Allah kiyi ki fito na makara, ta amsa masa da yanzu zan fito, ya jima a kwance yana jiran ta amma bata fito ba, yana shirin mikewa ya leka, yaji an turo kofa, kallon kofar yayi da mamakin waye ya shigo masa daki babu ko neman izini.

Ga mamakin sa sai yaga Saudah ta shigo cikin kwalliyar ta da alama ma ta dade da tashi har tayi wanka, ganin yana kallon ta ko sallamar da take masa bai amsa ba, tace dear har ka tashi, bai ce komai ba sai kallo da yake binta dashi kamar wani soko

Tsautsayi Part (29)
Aisha Muhammad

Karasowa tayi tana cewa dear irin wannan kallo haka nayi maka kyau ne, wayancewa yayi cikin inda inda yace mata sosai ma, kin tafi da nutsuwa ta ne, bari na kunna maka heater ko ba yanzu zakai wanka ba, aa barshi kawai bana so ki bata wannan kwalliyar taki, zo ki zauna kawai zanyi da kaina, ya fada yana kamo ta ya zaunar da ita a kan gadon, dan yaga tana kokarin yin hanyar toilet din.

Jikin kofar toilet din yaje sai kuma ya tsaya ya kasa kunne wai ko zaiji motsi daga ciki, dan tun bayan shigowar Saudah bai kara jin motsi a toilet din ba, amma shi yanzu akan Saudah ma kokwanto yake, shin ta cikin toilet din ce ta gasken ko kuma wannan data shigo, shiyasa ya zaunar da ita yana so yaje ya duba toilet din ne da kansa.

Sai da ya dinga jero addu'oi kafin ya tura kofar toilet din a hankali kamar wani barawo, leka kansa yayi ciki, babu kowa toilet dinma tsaf babu alamar anyi wanka a ciki, yana zaton Saudah ma a dakin ta tayi wanka, saida ya zaga da idanun sa kaf cikin toilet din amma babu kowa babu kuma komai.

Sai ya juyo yace, tashi ki raka ni dakin ki yau a can nake so nayi wanka, kallon sa tayi, me kuma naka toilet din yayi, babu komai, laifi ne idan nace zanyi wanka a toilet din ki, aa ba laifi bane muje, ta mike tayi gaba yabi bayan ta yana kara waiwayen toilet din.

Bayan yayi wanka ya fara shirin fita, nan fa ta saka darun ita fa kafar sa kafar ta, haka babu yanda ya iya yace ta shirya su fita tare, ya kai ta gidan Hajiyar sa ta gaishe ta, sai ya barta a can yaje office idan ya dawo sai ya biya su taho, ta amince ta shirya bayan sun yi breakfast suka fita.

Sosai Hajiya taji dadin ganin su, sai dai ta masa fadan fito da ita da yayi tun yanzu batayi ko wata ba, wllh Hajiya kin ganta nan ita ta matsa, to ai shike nan dai tunda gida kuka zo, shi bai zauna ba yace Hajiya zanje office na dawo wllh na ma makara, addu'a ta masa itama Saudah ta masa Allah ya kiyaye hanya ya juya ya fita.

Nan ta wuni Hajiya nata janta da hira dan ta sake, hidima sosai tasa masu aiki sukai ta mata, abinci kuwa anyi yafi a kirga, kamar ba cikin mutum daya ba, gaskiya ta yaba da kirkin Hajiyar, sosai take janta a jiki kamar ba sirikar ta ba.

Bashi ya dawo gidan ba sai bayan sallar magariba, lokacin suna dakin Hajiya sunyi sallah basu fito ba, zama yayi yasa mai aiki ta musu magana, shiga tayi ta fito tace gasu nan, ta wuce kitchen, babu jimawa kuwa Hajiya ta fito Saudah na biye a bayan ta.

Tsautsayi Part (30)
Aisha Muhammad

zama tayi akan kujera tana masa sannu da zuwa, itama Saudah waje ta samu wajen kafar Hajiya ta zauna daga kasa kan carpet ta masa sannu da zuwa, ya amsa yana cewa Hajiya a bani abinci naci mu wuce, wllh na gaji.

Kira ta kwalawa mai aikin ta, sannan ta tambaye shi me zai ci, ko meye ma Hajiya kawai ku bani, to a kawo maka tuwon alkama, eh wllh kuwa Hajiya da kin burge ni, dariya tayi ai nasan ka da tuwo musamman ma na alkama, mai aikin data zo tace ta kawo masa tuwon, bayan ta tambayi Saudah abinda za'a kawo mata, tace ita ta koshi, da Hajiyan ta matsa itama tace a kawo mata tuwon.

Babu jimawa mai aikin ta dawo dauke da babban tray a hannun ta da wata ma a bayan da wani tray din, suka zo suka ajiye dayar ta dauko ledar cin abinci ta shimfida dan sun san Abdul din tun yana gidan bai fiya son cin abinci a dining ba, hakan yasa suka kawo masa nan.

Bayan sun gama har sun fara shirin tafiya yaji ana kiran sallah, cewa yayi bari yaje yayi sallah tukunna itama tayi kafin ya dawo, idan sukaje gida kawai sai bacci, Hajiya tace ai kuwa kunyi dabara, nima bari na tashi nayi kada ku tafi ku barni da nauyi, sukayi dariya, ya fita itama Saudah ta mike domin zuwa gabatar da sallah.

Yana dawowa sukayiwa Hajiya sallama suka tafi bayan ta cika Saudah da kyaututtuka irin su turmin zani, da su turaruka, godiya Saudah tayi ta mata, Abdulmalik na taya ta, haka suka tafi a hanya sai yaba kirki irin na Hajyan take, yace Hajiya kenan ai haka take kadan ma kika gani, tana da son mutane, Allah sarki Allah ya kara girma, yace ameen.

Da haka har suka isa gida hirar Hajiya suke, suna isa bakin get yayi horn mai gadi yazo da gudu ya bude musu, bayan sun shigo mai gadin ya biyo su bakin mota, da takarda a hannun sa, bayan sun fito ya gaishe su sannan ya mikawa Abdulmalik takardar hannun sa, Alhaji gashi sako ne aka kawo a baka, karba yayi yana tambayar waye ya kawo.

Wllh ba na ce ba, wata mata ce dai, amma ta saka wannan abun da ake sakawa a fuska, fens mas ake cewa ko, dariya Saudah tayi, facemask ake cewa, to Hajiya wata kalmar ce ai sai ku din, kai to kuma bata ce maka injiwa ba, wllh Alhaji bata ce ba, naso ma na tambaye ta, amma sai tayi gaba da alama ma sauri take.

Daga nan Abdul bai tsaya kara jin wata magana ba yayi gaba, Saudah ma bin bayan sa tayi, kada yaje ya boye takardar dan ita tunda akayi maganar mace ce ta kawo hankalin ta ya tafi tunanin cewa budurwa ce ta aiko masa da sako, hakan yasa taji wani kishi ya kama ta, shiyasa ta bi bayan sa a fusace, suka bar mai gadi a tsaye a wajen.

Tsautsayi Part (31)
Aisha Muhammad

Yana shiga cikin falon itama tana shigowa, kujera ya nema ya zauna ya jefar da takardar akan center table, itama zama tayi a kufule tace wai me kake nufi ne daka ajiye takardar nan, wato kana nufin bazaka bude a gaba na ba ko, shine harda wani yasar da ita a zuwan baka damu da ita ba, kana so na manta da ita kafin ka bude ko.

Kallon ta yayi cikin kosawa yace me wai me kike nufi ne, nifa ban fahimce ki ba, akan me zan boye miki takardar da ban ma san wanda ya turo ba, oho na sani ko ka sani, so kake ka raina min hankali, haba dan Allah Saudah, so kike ki bata min rai ne, yanzu dan Allah a gaban ki fa aka bani takardar nan, kuma ma idan har nasan wacce ta kawo, me zai saka bazata min sakon ta waya ta ba sai ta sha wahalar kawo min har gida, bayan yanzu waya duk ta saukaka mana wannan.

Haba dan Allah ki dinga yin tunani akan abu kafin ki fade shi, sai a sannan jikin ta kuma yayi sanyi, itama taga rashin hankalin ta, cewa tayi kayi hakuri raina ne ya baci, aa nifa nama hakura, sai yanzu na gano bakin zaren, ashe duk wannan jan ajin da ake min na karya ne, ashe har haka ake kishi na.

Bata rai tayi, Allah ya kiyaye wannan ne kishi, eh mana au baki sani ba, to wllh zan iya dafa qur'ani cewa kin gama mutuwa akai na, kai amma gaskiya ni dan baiwa ne, duk irin cika bakin da aka dinga min, gashi ba'a je ko ina ba, har ana neman zaucewa akan kishi ba.

Filon kujera ta dauka ta jefe shi da shi, Allah bana so, wllh kai ka fiya sharri, bari kaga na bar maka falon, ni na hau sama sai ka hawo, hannun ta ya Kama ya mayar da ita ya zaunar, ai wllh baki isa ba sai mun bude takardar nan dake, idan sakon mace ne, da kaina zan nema miki ita ki mata duk hukuncin da kika ga dama, idan kuma akasin haka ne, to irin agreement din jiya zamu daura, kuma na sati guda.

Allah ya kiyaye ni na hakura da budewar kawai ka sake ni na tafi, Allah fa baki isa ba sai kin gani, da hannun sa daya ya rike ta sosai dan kada ta tashi, dayan hannun kuma ya dauko, envelope din ya shiga kokarin budewa.

Saida ya bude ya zaro takardar sannan bai bude ba ya mika mata, karbi ki bude da hannun ki kada kice nayi wata amajar, dariya tayi ta saka hannu ta karbi takardar dan tasan nacin Abdul, ai saika sakar min daya hannun na bude ko, sakin ta yayi yana fadin ai dai gaskiya na fada.

Bata tanka masa ba ta fara ware takardar, abinda suka gani gaba dayan su ya saka su cikin shock, rubutu ne akayi shi da wani abu kamar jini, an rubuta sunan Zarah da manyan baki, tashi yayi ya tsugunna ya dauki takardar ya shiga kitchen ya dauko laiter ya fita waje ta kofar baya, kona takardar yayi sannan ya dawo ciki.

Tsautsayi Part (32)
Aisha Muhammad

A zaune ya same ta yanda ya barta kamar mutum mutumi, sai da ya taba ta sannan ta dawo hayyacin ta, Abdul wa kake tunanin zai iya turo maka da irin wannan sakon, nima ban sani ba Saudah, a gaskiya babu wanda nake zargi, dan haka dan Allah ina so mu bar maganar nan haka, kawai mu cigaba da addu'a.
Insha Allah, Allah ya rufa asiri ya kara kiyayewa, ameen ya Allah, muje mu kwanta kawai dan wllh ko dadin kallo bazan ji ba yau, nima ai dama bacci nake ji, muje kawai, mikewa sikai suka haura sama.

Suna tura kofar bedroom dinsa wutar gidan ta dauke gaba daya, hasbunallah yace, me kuma ya faru cewar Saudat, oho nima ban sani ba, kunna fitilar wayar ki, bari naje na samu mai gadi, cab ni zaka bari ni kadai a cikin wannan duhun, baka san babu abinda na tsana kamar duhu ba, wllh yarinyar nan kin raina ni da yawa, ina miki magana zaki ce cab baza kiyi ba, to shine kuma raini, ai abinda kake fadan ne bazai yiwu ba.

Kinga wuce muje, idan kinga dama wannan ma kice baza ki ba, aa banda wannan ta fada tana bin bayan sa, suka sauka kasa yana haska musu da wayar sa, suna zuwa falo sai fitilar wayar tasa ma ta dauke, yayi yayi ya kunna wayar ma gaba daya ta mutu kuma taki kunnuwa, suka gwada ta Saudah ma taki yi.

A haka suna diririn neman hanya har suka isa bakin kofa sukai sukai su bude kofa kofa taki budewa, suna cikin al'ajabin abin, kawai sukaji wata murya ta kece da dariya, dariya mai karfi, Abdulmalik ke nan ina kake shirin zuwa, suka ji wannan muryar mai dariya tana fada ta tsaya da dariyar da take, nasan zakai mamakin sanin har yanzu ina nan a doron kasa, ko ba haka ba.

Gaba daya ilahirin jikin Saudat rawa yake, hawaye wani na bin wani, tabi ta kankame Abdul kamar zata shige cikin jikin sa, a ranta cewa take wannan wace irin masifa ce, yanzu ita wane Tsautsayi ne ya dawo da ita cikin wannan gidan, shima kansa Abdul din dauriya kawai yake, amma shi kansa a tsorace yake, dan dai kawai idan ya nuna gazawar sa to ita kuma Saudah tayi yaya ke nan.

Kana son kasan ko ni wacece, hmm ko baka so yau sai na nuna maka wacece ni, tunda tuntuni nake kokarin nuna maka amma kana rantse idon ka, haske ne ya mamaye ilahirin falon, mace suka gani a zaune akan kujera ta juya baya, irin matar da Saudah suka gani ita da Baba Mairo.

Ta barbaza gashi a bayan ta, juyowa tayi da kanta ba kuma tare da ta juyo da jikin ta ba, kamar yanda ake juya Babyn roba, shi kansa Abdulmalik zuwa lokacin jikin sa bari yake, wata zufar wahala na karyo masa, ita kuwa Saudah runtse idon ta tayi dan bata son ganewa idon ta abinda zai kasa fita a kwanyar ta.

Sanda ta gama juyowa sai da Abdul ya kusa sakin Saudah dake rike a jikin sa, dan shima ji yake kamar bazai iya daukar kan sa ba, idan ba idon sa ne yake masa gizo ba to tabbas Aunty Zarah yake gani a gaban sa, Aunty Zarah dai yayarsa, wacce ya tabbatar da mutuwar ta shekara da shekaru.

Tsautsayi Part (33)
Aisha Muhammad

Jikin sa yana kyarma yana karanto duk wata addu'a daya taba sani a rayuwar sa, yama kasa furta ko kalma daya, tsawa ta daka masa, kai Abdul nasan kasan me nake nufi amma kana nuna kamar baka san komai ba, wllh bazan taba barin rayuwar ka ta huta ba har sai ka fito ka nunawa duniya waye kai, ka daina amfani da rigar mutanen kirki bayan ba haka kake ba.

Wllh Abdul bazan taba barin ka ba har sai na tabbatar da asirin ka ya tonu a idon duniya, sannan nima na maka hukunci dai dai da abinda ka min, idan ma kai bazaka fito ka fadi abinda kayi ba, to ni sai na tabbatar da na tona maka asiri, daga haka wutar gidan ta kuma daukewa.

Can kuma sai ta kawo, tana kawowar kuma sukaga bata nan, sannan gidan ma yayi shiru, a wajen duka suka sulale suka zube, Saudat kuwa tana zama ta saka kuka mai karfi, wllh Abdulmalik idan baka fadan dalilin faruwar wadan nan abubuwan ba bazan kuma kwana a gidan nan ba, kuma wllh ko me za'ayi bazan dawo ba sai ka sanar dani abinda ka aikata.

Tana fadar haka ta mike tayi sama, shima bin bayan ta yayi, amma bai bi ta dakin ta ba, sai ya fara shiga nashi dakin ya dauko mukullin gidan ya fito, kofar falon yaje ya sakawa mukulli gudun kada tace zata fita.

A daki ya same ta tana hada kayan ta a wata katuwar trolley, zuwa yayi ya rike hannun ta ya hana ci gaba da abinda take yi, haka tana tirjewa ya janyo hannun ta ya zaunar da ita a bakin gado, nan fa ya shiga lallashin ta da magiya da banbaki, amma fur taki saurarar sa, haka har ya gaji da yaga rigimar tata ba mai karewa bace ya tashi ya fita ya bar mata dakin ya koma dakin sa.

Ai kuwa yana fita ta janyo akwatin ta ta rufe, ta dauki wayar ta da mukullin motar sabuwa wacce aka sako mata a lefe dan tsohuwar motar tata tana gidan su, wancan zuwan da tayi da ita Mommy tace za'a kawo mata ba'a kawo ba.

Jan akwatin tayi ta sauka kasa, sai da taje bakin kofa tayi tayi ta bude kofar ta kasa, nan ta gane kulle kofar yayi dan kada ta fita shiyasa yayi tafiyar sa dakin sa dan yasan bazata iya fita ba, wata kwafa tayi, ta juya ta koma sama.

Dakin sa ta nufa kai tsaye, a kwance ta same shi yayi rigingine ya kurawa ceiling ido, kamar me son gano wani abu a jikin sa, har ta turo kofar ta shigo bai san ta shigo ba, saida ta mayar da kofar da karfi ta rufe ta, karar rufewar ce ta dawo da shi daga duniyar tunanin daya tafi.

Mikewa yayi zaune ya zuba mata ido, yana jiran yaji da wacce kuma tazo, tsayawa tayi a kansa kaga Malam ka tashi ka bude min kofa ko kuma ka bani mukullin na bude, yana jin abinda ta zo dashi ya koma ya kwanta ya juya mata baya, dan ya gaji da wannan fitinar da tazo masa da ita, ta bar shi ma da tashin hankalin daya ke ciki ya ishe shi.

Tsautsayi Part (34)
Aisha Muhammad

Tana ganin abinda yayi ranta ya kuma baci, wato ya ma maida ta mahaukaciya shine zai juya mata baya, nan fa tahau bala'i, amma ya mata banza bai tanka mata ba, har tayi ta gaji ta juya ta fita tana fadin ita zai mayar mahaukaciya to wllh Allah ya kaimu gobe idan har ta bar gidan nan ta barshi har abada, bazata kuma zama da shi ba, yana jinta ya mata shiru dan shirun nasa ma shi yafi alkhairi, idan ba haka ba sai azo ayi ba dai dai ba.

Ranar a gidan babu wanda ya runtsa, ita kuwa Saudah ma kwana tayi tana kuka, yau duk tsoron ma da take ji ta neme shi ta rasa, bacin rai yayi awon gaba dashi, tana idar da sallar asuba ta dawo falo tana jiran ya bude kofar ta fita.

Ai kuwa tana nan a zaune masu aiki suka fara nocking dan har lokacin shigowar su ma ya wuce, tana zaune taji sanda suka zo suka taba kofar suka ji ba'a bude ba suka koma, to yanzu ma sunga rana tayi ne yasa suka ce bari su buga.

Ba'a dade ba taji sakkowar sa, da alama dama idon sa biyu ba bacci yake ba, tana ganin shi ya sakko ta mike, har ya nufi wajen kofa ya dawo inda take, kafadun ta ya rike tayi kokarin kwacewa, ya rike ta gam, ki tsaya muyi magana mana, bazan tsaya ba kawai Malam ka sake ni, bazan sake ki ba sai kin tsaya kin saurare ni, shiru tayi ta daina kokarin kwace jikin ta da take.

Riketa ya kuma yi sosai, ya kura mata ido yana kallon tsakiyar kwayar idon ta, kasa jurewa irin kallon da yake mata tayi tai kasa da kanta, shi kuwa bai daina kallon ta ba har sai da ya tabbatar sakon sa ya kai inda yake so ya kai, gaba daya jikin ta yayi sanyi.

Sannan ya fara magana, haba Saudah haba sweetheart dina, meyasa bakya son abinda zai kwantar mana da hankali, ki duba fa ina gama hidimar biki wannan iftila'in ya faru da company na a Abuja, na kama hanya ma tafi ban huta daga hidimar biki ba, sannan ina can Abba ya min waya akan waccan matsala, na kamo hanya na taho ke shaida ce tunda na shigo garin nan ban huta, kina kallon dai duk irin abubuwan da nake facing.

To yanzu ina cikin wannan halin kike so kuma kema ta bangaren ki ki kara min wata damuwar, ya kike so nayi, ko kina son jini na yayi hawan da zan yanke jiki na fadi take na mutu ko kuma na kamu da wani mummunan ciwon, eyye, ya fada yana kokarin hada ido da ita, amma taki bashi damar hakan.

Sai kai da ta girgiza masa kai, to indai ba haka kike so ya faru dani ba to kiyi hakuri ki bari mu samu fahimtar juna, kinji ko, nan ma kai ta gyada masa, alamar to, sai kuma tace amma, sai kuma tayi shiru, amma me fadi kada ki damu, amma gaskiya sai ka wayar min da kai, akan abinda ya faru jiya, kada ki damu, dama gajen hakuri ki kayi, amma inada niyyar na zaunar dake na fada miki komai.

Tsautsayi Part (35)
Aisha Muhammad

To ka fada min, aa ba yanzu ba, sai kin kwantar da hankalin ki, kin samu kin ci wani abu tukunna kin nutsu sannan sai mu samu muyi magana, ni zata fara magana, ya dora yatsan sa akan leben sa yace shiii, bana son gardama kinji ko, kawai kice to, to tace masa sannan ya sake ta ya kama hannun ta yace muje mu bude kofar ko, kada suce yau wadan nan mutanen amarci ne ya hana su bude kofa.

Dariya tayi ta sunkuyar da kai, a haka suka karasa ya saka mukulli ya bude kofar sannan ya juya rike da hannun ta suka haura sama.

Sai bayan sunyi wanka, suka sakko sun tarar an gama shirya musu breakfast, suka zauna suka karya duk da gaba dayan su ba wani ci sukai ba, dan gaba daya basa jin taste din abincin, suna gamawa suka koma sama suka zauna, nan ya fara magana.

Wato Saudah a yau zan sanar dake wani sirri nawa wanda babu wanda duk duniya babu wanda ya taba sani, daga ni sai mahaliccina, alfarmar da nake nema a wajen ki, dan Allah kada jin abinda zan fada miki yasa ki guje ni, wllh zan iya rasa raina, zafin zai min yawa, dan haka kafin na sanar dake komai, ina son ki min alkawarin baza ki taba gudu na ba.

Kai ta girgiza masa dan yayi bala'in bata tausayi yanda duk taga ya fita hayyacin sa daga jiya zuwa yau, hannun sa da yake cikin nata ta rike sosai tace na maka alkawari Abdul duk rintsi ina tare da kai bazan taba gudun ka ba, shima hannun nata ya kuma rikewa gam, wani siririn hawaye ya silalo daga kwayar idon sa, kasa ya silalo ya zauna ya saka gwuiwowin sa a kasa, yace ban san da wane bakin zan miki godiya ba Saudat, sai dai ince Allah ya biya ki da gidan aljanna.

Take yaji kaso dari na damuwar sa ya ragu, dan dama babban tashin hankalin sa idan abin nan ya fito Saudah tace baza ta zauna da shi ba, itama zamowa tayi ta zauna a kasan idon ta na zubar da hawaye, amma tana share masa nashi hawayen.

Kada ka samu damuwa ka sanar da ni koma menene na maka alkawarin bazan taba barin ka ba, nan ya kara jin zuciyar sa tayi sanyi, ya share hawayen sa sannan ya gyara zama, itama gyara zaman ta tayi ta maida gaba daya hankalin ta gare shi.

Na taba baki labarin rasuwar mahaifiyar Aunty Zarah, a lokacin dukan mu muna da kananan shekaru, daga nan rikon ta ya dawo hannun Hajiya, duk da dai ba wani abu Hajiya take mata ba, tunda a lokacin ta kai tayiwa kanta komai, sai dai kula da tarbiyya wanda ko kadan bata bawa Hajiya damar hakan ba ko kadan.

Alhaji wato mahaifin mu babu irin fadan da nasiha wanda baya mata amma a banza, a haka har muka fara mallakar hankalin kan mu, Aunty Zarah tana nan a yanda take babu wani abu daya sauya a cikin halayyar ta sai ma abinda ya karu.

Tsautsayi Part (36)
Aisha Muhammad

Dai dai da yan aikin gidan mu basa kaunar yau ace tana gida, dan basa da sukuni, ga mugun saka aiki, ga kuma hantara, kai har dukan yan aiki tana yi, tasha korar su da bakin halin ta, Alhaji yayi fadan har ya gaji, rashin mutuncin da takewa Hajiya ne dai yayi sauki, dan nima a lokacin na kawo karfi tasan bazan bari ba, shiyasa ta kuma fita sosai a hanyar mahaifiya ta.

 Ita kadai take gudanar da rayuwar ta, bata da kawa ko daya, sannan ko dangin mahaifiyar ta bata mu'amala da su, da su suna zuwa amma da sukaga halin ta ba wanda zasu iya dauka bane sai suka tattara ta suka ajiye.

Bayan ta kammala karatun ta, ta fara aiki a companyn Alhaji na nan garin, tun a ranar ta ta farko a wajen aka fara samun matsala da ita da ma'aikata, sosai take diga rashin mutuncin ta a wajen, Alhaji yayi maganar yayi maganar taki ji, haka ya zuba mata idanu, a nan har nima na kammala nawa karatun na fara aiki tare dasu.

A lokacin ita ta kai matsayin mataimakiyar Alhajin mu, duk da bai so hakan ba, amma wani lokacin har ina mamakin yanda yake treating dinta kamar yana tsoron ta, har na taba samun Hajiya da maganar ta tsawatar min tace kuma kada ta kuma jin makamanciyar irin wannan maganar ta fito daga baki na.

Su kansu ma'aikatan wajen basu so hakan ba, amma ya suka iya, tunda ta kafa masifa a kai haka dole za'a karba ayi hakuri, ni kaina da nake kanin ta bana jin dadin aiki tare da ita, har na taba yiwa Alhaji magana akan ina so zan koma company sa na Kaduna, amma fur yaki yarda yace wai yafi sona anan kusa dashi, haka babu yanda na iya na hakura na zauna, muka cigaba da fuskantar rashin kirki da wulakanci na Aunty Zarah.

Ana haka wata rana Alhaji ya tara mu, yace yana so zai bar wata wasiyya ne, duk da ya riga da yayi ta a rubuce kuma ya bawa Lauyan sa, amma yaga dai ya kamata muma iyalin sa mu sani, kowa ya maida hankalin sa yana sauraron sa.

Ya nisa sannan yace, wato abinda nake so na fada shine, ina so zanyi ritaya nan ba da dadewa ba, kuma Abdulmalik shine wanda nake so ya gaje ni, badan wai dan nafi son shi bane ko wani abu, aa nayi hakan ne dan kasancewar shi da na miji, wanda a ko yaushe shi keda iko da kansa, sabanin mace da idan tayi aure dukkan nin wani iko nata ya koma kan mijin ta, sai yanda yayi da ita zai iya hana ta ma aikin gaba daya kuma dole tabi umarnin sa.

Sannan ma ko a mahanga ta addini, shi namiji a koda yaushe shine a saman mace, yau idan akace babu mahaifin sa a duniya, tofa har mahaifiyar sa shine zai zama yana kula da ita ba ita ce zata kula dashi ba, hakan nema Allah da ya raba gado ya bawa maza ninkin na mata, dan a karshe dai sune masu cigaba da kula dasu.

Dan haka ina fatan kowa zai karbi wannan hukuncin nawa ya kuma masa duba na fahimta, kada wani ya bari shaidan ya shiga zuciyar sa yayi tunanin nafi son wani ko kuma ina kin wani, idan akwai wanda yake da wata magana bisimillah muna sauraron sa.

Tsautsayi Part (37)
Aisha Muhammad

Babu wanda yace wani abu, yace kenan dai babu mai wata magana, to Alhmdllh, Allah ya kara hada kan mu, suka amsa da ameen kowa a wajen yayi mamaki da Aunty Zarah batayi wani korafi ba, nan yace sannan anjima bayan sallar la'asar, ina so ku shirya akwai inda nake so zamuje akwai abinda nake so zan nuna muku, sukace to, sannan ya salleme su.

Muna dawowa daga sallar la'asar muka tarar da Hajiya a falo ta shirya tana idar da sallah ta shirya dama Hajiya ba mace bace mai nauyi, muna shigowa Alhaji yace yauwa Hajiya har kin shirya, tace eh wllh Alhaji ai gara muje da wuri, kasan yanzu da wuri ake sallar magariba, hakane kai Abdulmalik shiga ka yiwa Zarah magana kace ta fito.

Hajiya ce tace, aa na shiga da na gama shiri na mata magana, tace mu tafi kawai bata jin dadi, Alhaji bai so haka ba, yayi shiru ko kadan baya son irin abinda Zarah takeyi, a ransa yace Allah ya shirya, dukan su sun san babu wani rashin lafiya, kawai bazata je dasu bane.

Haka dai Alhaji yayi gaba ransa a bace, yace Abdulmalik dauko mukullin mota ka same mu a waje, ka biya daki na akwai wani mukulli akan kujera ka dauko min, to nace masa suka fita, ni kuwa nayi bangaren Alhajin.

Bayan na dauko nazo na same su a tsaye jikin mota ta, na bude musu suka shiga, muka dauki hanya, bayan mun hau titi na juya na kalli Alhaji, nace Alhaji ina muka nufa, sunan wannan unguwar tamu ya fada min, bayan mun shiga ya fada min number gida, a dai dai kofar gidan nayi parking.

Sai da Alhaji ya fara fitowa sannan duk muka biyo bayan sa, mukulli ya ciro a aljihun sa ya mika min, karba nayi, yamin nuni dana bude gidan, mukullin na saka na bude gidan muka shiga, masha Allah dama tun daga get din gidan idan ka kalla kasan an zuba dukiya, ashe wani abun ma sai an shiga ciki.

Girman harabar gidan ma shi ya gama ruda mu, ba dai sai na tsaya lissafa miki girma ko tsaruwar gidan ba, tunda yanzu ma a cikin sa kike, kallon sa tayi, tace nan gidan, ya gyada mata kai, sannan ya cigaba.

Bayan mun gama shiga ko ina na gidan, muka dawo muka zauna a falon bangaren da zai kasance shine na Alhaji, wanda yanzu yake a matsayin nawa, abinda yasa kikaga bana zama a can, ni tunda ma bana da ra'ayin raba wajen zama da iyali na.

Yace to wannan gida da muka gani, nashi ne kuma ya gina shi ne idan ya bar aiki zamu dawo nan da zama, sosai mukai murna dan sosai gidan yafi gidan mu komai, haka muka tafi muna ta murna da labarin gidan.

Tsautsayi Part (38)
Aisha Muhammad

Bayan mun koma gida Alhaji yasa aka kira masa Aunty Zarah itama ya mata bayani kamar yanda ya mana, ta amsa masa amma babu alamar murna ko kadan a tare da ita, haka ta tashi ma gaba daya ta bar mana wajen, Alhaji ya kalle ta ya girgiza kai, yace Allah ka nuna min randa Zarah zata canza, duk muka amsa masa da ameen, daga nan muka cigaba da hirar mu.

Bayan sati daya da yin zuwan mu wannan gida, ina wajen aiki a ranar Aunty Zarah bata je aiki ba tana gida, ina tsaka da aiki waya ta tayi ringing, ina dubawa naga Aunty Zarah, nayi matukar mamaki dan rabon da ta kira ni na manta, ni na dauka ma yanzu bata da number ta.

Ina ta mamaki har ta katse, ta kara kira, ai tana kira nayi maza na amsa gudun tashin hankali, bayan na daga nayi tunanin zata min masifa akan ban daga kiran ta da wuri ba, sai abin mamaki bata ce komai ba, bayan na gaishe ta, ta amsa min, muryar nan tata a cunkushe kamar ko yaushe.

Can kamar bazatayi magana ba, sai naji tace kana ina ne, ina wajen aiki na bata amsa, to kazo yanzu ina jiran ka zaka kai ni wannan gidan da kwanaki kuka je da Alhaji, amma Aunty Zarah da kin bari, bata bari na karasa ba, ta katse ni cikin masifa, kaga Malam idan bazakaje bane kawai ka fada min, ba sai ka tsaya kana raina min hankali ba.

Raina ya baci sosai amma na danne dama ba yau ta fara min irin wannan karan tsayen ba, kawai ina raga mata ne sabida Hajiya a kullum bata da magana sai nabi yar uwa ta, wllh idan na sake na bata mata to kamar ita na batawa, kuma nasan Hajiya tana yin hakane kawai dan a zauna lafiya, kuma a kwantarwa da Alhaji hankali, dan indai za'a biyewa halin Aunty Zarah, tofa baza'a taba zama lafiya ba.

Kafin na ankara ma har ta kashe wayar, tsaki nayi, na danne zuciya ta na kira ta, kamar ma bazata dauka ba sai da na kira sau biyu, sannan ana biyun shima sai da ta kusa tsinkewa ta daga, bata ce komai ba, sai nine nace, kiyi hakuri zan zo yanzu insha Allah.

Bana gida ka same ni a red star restaurant, ok nace mata na kashe wayar, tashi nayi kawai na bar abinda nake yi na fita, gudun wani bacin ran, dan idan na dauki lokaci banje ba, zan iya yin zuwan banza na tarar ta tafi, kuma abin sai ya zama wani bala'in zata ce na shanya ta na mata wulakanci.

Ina zuwa wajen kuwa na hango ta a zaune kan irin kujerun nan na kaba daga waje wajen gurin ita kadai, ta na kallon mota ta amma taki tasowa, har sai da na bude motar na fito, sannan ta taso, tana tafe kamar bata son taka kasa, dama Allah ya halicce ta mace mai son nuna isa, da takama.

Tsautsayi Part (39)
Aisha Muhammad

Inda nake ta karaso bata ce min komai ba ta bude motar ta shiga abinta sai wani shan kanshi take, kai kawai na girgiza shima ba yanda zata gani ba, nima na bude motar na shiga na tada ita muka dauki hanya, da yake mukullin gidan yana hannu na na saka a cikin mukullai na.

Bayan mun isa na bude mana gidan muka shiga, muna shiga mai makon mu fara shiga falo, sai tace ita garden zan fara nuna mata, haka ta tasa ni a gaba ina tafe tana biye dani, har muka shiga garden din, muna shiga na samu irin kujerun nan na gini a gefen fool na zauna, ita kuma ta shiga zaga wajen.

Waya ta na dauko na shiga dannawa dan ta debe min kewa kada na gaji da zaman, dan yau na fuskanci halin nata ne ya motsa fiye da ko yaushe, shiyasa ta jawo ni wajen nan, tana son dole sai ta kure ni na kula ta, ni kuma naci alwashin insha Allah bazan biye mata ba, tayi duk abinda zatai, nasan dai babu yanda za'ai mukai dare a wajen.

Nayi nisa cikin danna waya ta, hankali na gaba daya yana wajen wayar, naji kamar motsi a baya na, kamar ance na juya, ina juyawa naga kamar a mafarki Aunty Zarah tayo kai na gadan gadan da wuka ta kusa caka min a gadon baya, Allah yasa na juyo, da sauri na kauce, ina kara kallon ta dan na tabbatar ba mafarki nake ba.

Kara yowa kai na tayi da gudu tana neman dole fa sai ta caka min wukar, ni kuma kamar an zare min laka haka nake jin jiki na kasa tabuka komai, sabida tsananin mamaki, a raina kawai mamaki ne ya kashe ni, yanzu dama tsanar da Aunty Zarah ta min har ta kai tayi kokarin kashe ni, innalillahi wainnailaihi raju'un, ya Allah kasa mafarki nake, Allah kasa na farka naga ba gaskiya bane.

Ina wannan tunanin ban ankara ba, ta caka min wukar a dai dai kahon zuci, Allah ya rufa asiri na saka hannu na na tare, wukar bata huda ni ba, amma fa ta shiga hannu na sosai ta yanka, take jini ya fara tsiyaya a hannu na, amma hakan bai saka ko kadan naga tausayi ko dana sani a fuskar ta ba.

Hakan yasa nima na shiga kokarin kare kai na, kokawa muka fara sosai, ina kokarin kwace wukar a hannun ta, kawai abin tsautsayi, na kwace wukar kenan ta kuma tahowa da gudu zata karba, tana tahowa wukar ta cake ta dai gefen zuciyar ta, take ta yanke jiki ta fadi, sai jini.

Nan fa hankali na yayi mugun tashi, na tsugunna na riko ta, jini yana ta fita ta bakin ta da hanci, gaba daya na rude nama rasa mafita, ni ba abun na kira, police ba, suna zuwa bani da fita za'ace na mata dabara ne na kawo ta nan na kashe ta, kema dai kinsan ko kece kika zo kika same su a wannan yanayin ko zan hadiyi kur'ani baza ki yarda bani na kashe ta ba, Allah ne kawai shaida ta.

Tana rike a hannu na sai faman kuka nake kamar mace, babu jimawa naga tayi wani yunkuri, wasu gudajin jini suka fita daga bakin ta, daga nan idon ta gaba daya ya rufe, na duba ta tsaf na tabbatar da ta mutu, innalillahi, fadin irin tashin hankalin dana shiga a lokacin ba zai yuwu ba.

Tsautsayi Part (40)
Aisha Muhammad

Ina cikin wannan tashin hankalin hawaye yaki tsayawa a ido na kamar mace, waya ta ta fara ringing, zo kiga yanda na firgita kamar mai kiran zai iya hango ni ta cikin wayar, kwantar da ita nayi a wajen naje na dauki wayar wacce na yasar da ita a can gefe.

Sanda naje kiran ya yanke, ina duba mai kiran naga Hajiya ce, gaba na ya bada wani dam, ina cikin tunanin na kira ko kuwa, kiran ya kuma shigowa, daurewa nayi na dauka, ina dagawa naji muryar Hajiya tana kuka, innalillahi na furta, a raina nace me kuma ya faru, ita kuma tana jin na daga tace, Abdulmalik kana ina maza kazo gida asthma Alhaji ce ta tashi.

Tashin hankali kan wani, ce mata nayi ta kira driver ya saka shi a mota su tafi asibiti, sai mu hadu acan, kada a bata lokaci, to tace min ta yanke wayar, kana jin muryar ta kasan cikin tashin hankali take, sabida dama indai asthma nan ta tashi tofa sai ma an fitar da rai dashi, kowa sai ya shiga tashin hankali, sabida irin halin da yake shiga.

Bayan na kashe wayar na juya na kalli gawar Aunty Zarah a kwance, gaba daya komai ya kwance min, nama rasa abin yi, cikin dan kan kanin lokaci komai yana neman lalace min, innalillahi Allah ka kawo min daukin ka.

Na dauki lokaci mai tsaho a wajen, na kasa koda motsi balle na san abinyi, gaba daya kamar an bubbuge min duk wata gaba ta jiki na, da kyar ina ta ambaton sunan Allah na samu na sami kwarin gwuiwar mikewa, na kalli Aunty Zarah dake kwance, kawai na juya da karfin gwuiwa nayi gaba.

Idan na tsaya anan ma babu abinda zan iya mata, tunda dai tata ta kare, kamata yayi naje na fuskanci ciwon mahaifin mu, kafin shima na rasa shi, wannan tunanin da nayi shi ya bani kwarin gwuiwar na mike na fita daga gidan na dauki hanyar asibin da gaba daya familyn mu anan suke ganin likita, nama san can za'a kai shi.

Ina gab da karasawa asibitin, naji waya ta na ringing, daukowa nayi na duba mai kiran, Hajiya ce, da sauri nayi picking, ina dauka naji ta tana kuka, ka kyauta Abdul, yanzu har mu iso asibitin nan baka zo ba, to ai shikenan tunda naga alama baka da bukatar ganawar ka ta karshe da mahaifin ka, ta faru ta kare, ya amsa kiran mahaliccin sa.

Wata tsawa naji an min a tsakiyar kai na, da kyar da taimakon Allah na samu na dawo cikin hayyaci na, wayar ma ban sani ba ni na kashe ko kuma itace ta gaji ta kashe, wani ikon Allah ne kawai ya kaini asibitin nan, addu'a kawai nake a raina Allah yasa kunne na bai jiyo min dai dai ba, dan gani nake bazan iya daukar wannan kaddarar ba.

Ina isa asibitin ana fito da gawar Alhaji za'a saka shi a ambulance a kai shi gida, ina fitowa daga mota nayi arba da wannan mugun gani, gaba daya wutar kai na sai ta dauke, daga nan ban kuma sanin inda kaina yake ba, sai kawai farkawa nayi na ganni a kan gado na, ga aboki na Salis a kusa dani a gefen gadon.

Ina farkawa abinda na fara tambayar sa Salis mafarki nake ko, ganin yayi shiru kawai ya sunkuyar da kai, na kara tabbatarwa gaskiya ne ba mafarki nake ba, Alhaji ya barmu, shike nan mun zama marayu, ko kuma nace na zama maraya, tunda ita Aunty Zarah, tama riga Alhajin, kuma wani karin tashin hankalin ma wai ni da kaina nayi sanadin Aunty Zarah, gara da Allah ya dauki ran Alhaji bai ga wannan tashin hankalin ba, ace dan cikin sa ya aikata kisan kai, kuma kisan kan ma akan yar uwar sa.

Tsautsayi Part (41)
Aisha Muhammad

Innalillahi wa innailaihi raju'un, Allah gare ka muke kuma gare ka zamu koma, yana kawo nan ya tsaya da labarin ya fashe da kuka wui wui kamar mace, ita kan ta Saudah sai da labarin ya saka ta kuka, daga ita har shi aka rasa mai lallashin wani, sai da suka yi mai Isar su, sannan ya cigaba.

Sanda na farka an riga an kai Alhaji gidan sa na gaskiya, Allah kasa mu cika da imani kuma mu tashi dashi, ameen, da kyar Salis ya samu yasha kai na bar abinda nake, dan kaina nake bugawa sosai a jikin allon gado, da gaske so nake nayiwa kaina illa, ko nima na mutu na huta da rikicin duniya.

A duk sanda na tuna da abinda na aikata da kuma gawar da na bari tana jiran nasan yanda zanyi da ita, ina jin kamar nima na kashe kai na na huta, da kyar Salis ya shawo kaina, sai da yayi ta mun fada sannan kuma daga baya ya koma nasiha.

Haba Abdulmalik kamar ba musulmi ba, akan ka aka fara yiwa wani mutuwa da bazaka dauki dangana ba, haba Abdulmalik ka godewa Allah mana, wasu fa tun suna kanana iyayen daga uwa har uba suke mutuwa su barsu, su taso cikin maraici da halin kaka ni kayi, to kai fa ka godewa Allah ka riga ka mallaki hankalin kan ka, sannan kuma a cikin duk wadan nan abubuwan dana lissafa babu wanda zaka fuskanta.

Sannan uwa uba kuma ga Hajiya wacce zata debe maka kewa sannan ta cigaba da dora ka akan hanya, kayi hakuri ka godewa Allah akan kaddarar daya dora maka, ban ki ta taka ba, Salis amma kai bazaka iya fahimtar halin da nake ciki ba.

Wane irin hali kake ciki wanda bazan iya fahimta ba Abdul, ka manta iyaye na gaba daya sun rasu, to ni ba da bane, da bazan ji irin radadin da ko wane da yake ji yayin daya rasa iyayen sa, a takaice ma na fika, tunda ni gaba daya suka rasu kuma a lokaci daya.

Hmmm kai dai kawai ka min addu'a Salis, amma ina cikin masifa, wacce babu mai fitar dani sai Allah, mikewa yayi kaga Abdul ni dai tafiya zanyi, tunda naga alamar bani da wani amfani, haba Salis me kuma ya kawo wannan maganar, eh mana ina baka hakuri amma kana kara shiga dawa, sai so kake kayi sabo ma, to ni ba dani ba.

Ni ai a tunani na kana farkawa abinda ya kamata ka farayi, shine kace a raka ka kabarin mahaifin ka, ka masa addu'a tunda baka samu damar raka shi ba, daga nan kuma kaje wajen mahaifiyar ka itama ka kwantar mata da hankali tunda duk tsiya ita ta fika rauni, a yanzu tana bukatar lallashi daga gare ka.

Tsautsayi Part (42)
Aisha Muhammad

Kai baza ka gane bane Salis, wllh yanzu duk ba wannan ne a gaba na ba, ido Salis ya zaro, baka da hankali Abdul, ko dai mutuwar nan ta fara taba maka kwakwalwa, idan ba wannan ne a gaban ka ba to meye a gaban ka.

Waccan gawar mana, gawa kuma ya fada da karfi, da sauri nayi kansa na rufe masa baki kada wani ya jiyo, dan wllh har ga Allah ban san sanda maganar ta fito fili ba, dan ni a zuciya nayi ta, ture ni yayi daga kansa, yace gawa fa naji kace Abdul, wani ka kashe.

Gefe na koma na zauna na kasa bashi amsa, kawai wasu zafafan hawaye suka fara zubo min, Abdulmalik ka min baya ni ka saka ni a duhu, me yake faruwa, kuka na ne ya kara karfi nace, Salis na shiga uku, yau tsautsayi ya kai ni ga aikata kisan kai, Salis yau ni Abdulmalik nine na kashe mutum da hannu na.

Da wadan nan hannayen nawa na kashe yar uwa ta, kaico na wllh a yau nafi bukatar mutuwa ta da cigaba da rayuwa ta, baki na ya rufe min, haba Abdul kayi shiru kada kayi sabo, ka nutsu ka min bayani, da tattaunawa ko wace matsala tana da solution, kayi hakuri kaji ka min bayani yanda zan fahimce ka.

Bani da wani zabi daya wuce na sanarwa da Salis halin da nake ci, koda kuwa hakan zai zama makasudin tonuwar asiri na, tunda ya riga ya fara jin wani abu daga ciki, rashin yi masa bayanin zai iya haifar masa, da wasi wasi da zargi kala kala a kai na.

Dan haka kawai na yanke hukuncin sanar dashi, bayan na gama masa bayani, yayi shiru har na wani lokaci, sai da nace masa, kayi shiru Salis, kai ma yanzu ka fuskanci halin da nake ciki ko, wllh yanzu karin fargaba ta, mutuwar Alhaji, idan maganar nan ta fito, mutane da dama zasu zargi na kashe Aunty Zarah ne sabida na gaje dukiyar Alhaji ni kadai.

Nisawa Salis yayi yace tabbas haka ne Abdul, naji tsautsayin daya same ka, kuma tabbas na yarda da duk abinda ka fada min gaskiya ne, sabida daga iyayen ka sai ni a sanin halin ka, tunda tun muna yara muka taso tare, sannan bani da wani aboki sama da kai, kuma kaima hakan take a wajen ka, dan haka zan iya sanin abinda zaka iya aikatawa, wannan ba halin ka bane, ba kuma tarbiyyar Hajiya bace, ace wai ka aikata kisan kai.

Wllh bazai taba yiwuwa ba, tsautsayi ne kawai ya fada maka, kuma wannan abun ba kai kadai ya fadawa ba har da ni, dan duk irin halin daka shiga nima na shige shi, dan haka yanzu zama za muyi kawai mu samo mafita, amma fitar da wannan maganar ba dabara bace, sabida wllh duk inda za'aje a dawo baka da fita Abdul, dole kowa zai ce kai ka kashe ta duk irin binciken da za'ayi baza'a taba gano gaskiya ba.

Tsautsayi Part (43)
Aisha Muhammad

Sabida tsautsayi ya riga da ya fada maka, dan haka mafita daya ce, mu binne wannan sirrin tsakanin ni da kai kawai, ko Hajiya bana so taji wannan maganar, tunda ni a nawa ganin har a wajen Allah bamuyi laifi ba, tunda babu yanda za'ayi ka tsaya ka karbi hukuncin abinda baka da laifi a cikin sa, hasali ma itace mai lefin, dan haka ni yanzu ma mafita tazo min a rai.

Da sauri na kalle shi, ta me fa, kasan me za'ayi, aa yanzu ka daure ka tashi, mu fita wajen zaman makokin nan, sabida ina so idan dare yayi zamu fita, kaga kuma idan ba'aga ka warware ba, za'a ce baka da lafiya kuma ina zaka da daddare, haka ne, ka tabbata babu matsala, ni wllh gani nake kamar idan na shiga mutane zasu gane abinda na aikata.

Dan Allah tashi ka zama namiji mana su mutanen suna gani har hanji ne, mikewa nayi, nace, amma dai ka bari nayi wanka na canja wadan nan kayan jikin nawa, dan ni kaina kyamar su nakeyi, bai ce komai ba, na shiga nayi wanka na fito, na shirya muka fita.

A can babban falo, muka tarar da mata, ana ta karbar gaisuwa, kowa yana gani na, aka shiga yi min sannu tare da gaisuwa, ina amsawa a can kasan makoshi, dan magana ma ko kadan bata min dadi, inda Hajiya take na karasa, na riko hannun ta, zanyi magana sai kuma na kasa, itama sai zuciyar ta ta kuma yin rauni, ta cigaba da kuka mai tsuma zuciya, nima kukan nake na kasa cewa komai.

Wai ni da nazo na lallashe ta sai kuma na bige da kuma saka ta kukan, Salis ne ya karaso ya kama ni, yana haba Abdul wai meye kake haka ne, yanzu kaji dadi da ka kara daga mata hankali kenan, fita yayi dani, itama yan uwan ta suka cigaba da bata baki.

A can waje muna zaune muna ta karbar gaisuwa, amma ni dai gangar jiki nace kawai a wajen gaba daya hankali na baya jiki na, idan ma aka min gaisuwa yawancin lokuta sai Salis ya tabo ni, wani lokacin kuma kawai ya amsa, kowa a wajen sai da ya tausaya min, ana ta cewa shakuwa ce, da yayi da mahaifin sa, kasancewar shi shi kadai ne namiji.

Har akai sallar magariba sannan wasu suka fara watsewa, mata ne dai na cikin gida suke nan makil, basu da niyyar tafiya, ana yin sallar isha'i kuwa kowa ya watse, sai yan uwa na kauye da suka zo kwana, su kuwa Salis ne ya tsaya ya tabbatar an kai kowa masauki, sannan yazo ya min magana, muka bi ta kofar baya muka fice daga falon, gudun tambayar matan nan na falo ina zamu.

Muna fita motar Salis muka shiga muka fice daga gidan, kafin mu isa gidan sai da muka fara biyawa ta gidan su Salis, a waje yayi parking ya bar ni a mota, ya shiga ciki, babu jimawa ya fito da wani buhu a hannun sa, yazo ya saka shi boot, sannan ya zagayo ya shiga muka tafi.

Tsautsayi Part (44)
Aisha Muhammad

Bayan mun isa gidan shi ya fito ya bude get din, muka shiga da motar ciki, inda gawar take na fara kai shi, bayan ya gani muka fito, ina tambayar shi abinda zai yi, bai bani amsa ba yayi gaba, wajen mota ya koma ya bude boot, ya dauko wannan buhun sannan ya dawo yayi cikin garden din, ciki ya nitsa sosai, sai da yaje can wajen karshe karshen sa.

Ni dai ina biye dashi kawai, sannan ya ajiye wannan buhun ya ciro abinda ke ciki, diga ce da fartanya, da kuma shebur, ya ajiye su duka, sannan ya dauki digar ya shiga haka wajen, sai a sannan na fahimci abinda yake nufi, nima fartanyar na dauka na shiga taya shi.

Nan da nan kuwa muka gama, ciki muka koma, muka dauko gawar, muka zo muka saka ta a cikin wannan ramin, sannan muka dauki wukar da jakar ta, duk muka hada muka rufe a wajen bayan mun cire wayar ta, sannan kuma, muka koma wajen famfon da ake bawa fulawa ruwa, muka sami wani bokiti a wajen, watakila wanda ake aikin bawa fulawowin ruwa ne, da yake akwai mai kula dasu, duk sati yake zuwa, har da tsintsiya mun samu a wajen, muka wanke wajen tass, muka gyara kamar babu abinda ya taba faruwa a wajen.

Bayan mun gama ma mun dade muna kara zagaye wajen, sai da muka tabbatar bamu bar ko wace irin shaida ba, sannan muka shiga mota muka tafi, bayan munje gida, ta can baya mukai parking, yana yin parking nayi sauri na fita na shige ta kofar bayan nan inda muka fita.

Shi kuma Salis sai ya koma ya shiga ta kofar main falo, ya tarar da matan harma da wasu daga cikin mazan, duk basuyi bacci ba, suna ta jejeto, yana shiga yace lafiya dai, daya daga cikin mazan yace, wllh kaga wai yarinyar nan ce Zarah tunda akai rasuwar nan ba'a ganta ba, kuma an kira wayar ta a kashe, munje dakin abokin ka mu sanar dashi ko yana da masaniya akan inda taje, bai bude kofar ba.

To shi dai Abdul bashi da lafiya ne, yanzu ma ni har naje gida ya kira ni yace na dawo bashi da lafiya.

kuma anje anyi report a wajen police, aa gaskiya, sabida ba'a farga da wuri ba, sai yanzu, sai dai idan Allah ya kaimu gobe, to Allah ya nuna mana, bari na duba shi, to ka masa sannu, idan kuma kaga ya kamata kuje asibiti, sai kayi magana a raka ku ko, to shike nan sai da safe.

Yana zuwa yacewa Abdulmalik, Abdul kaga kuwa Allah ya taimaka munyi dabarar, jefa wayar ta a cikin kogi, dan yanzu haka neman ta akeyi, ance gobe za'aje wajen police, ana zuwa kasan zasuyi tracing wayar ta, yanzu kuwa kaga inda muka kai wayar nan, koda an gano ta babu wani abu da za'a iya ganowa akai.

Hakane amma Salis kada ma mu kara tada maganar nan kasan ance bangwaye ma suna jin magana, yace hakane kuma, amma kaima ka saki ranka, ka zama namiji, ka daina duk wannan rabe raben, gobe idan an tashi da maganar, ka saki jikin ka, idan ta kama ma ka bisu aje police station din da kai.

Tsautsayi Part (45)
Aisha Muhammad

Saura kuma idan kaje ka dinga wani acting, har kasa police din su fara zargin ka, kaga dai yanzu idan dai ba kai kayi wani abun zargi ba, babu mai zargin ka, haka ne, insha Allah har addu'a zanyi akan hakan Allah ya bani kwarin gwuiwa, to ameen, daga haka muka kwanta, amma fa ni bacci ya gagare ni, idan ma ya dauke ni, to sai nayi wani mummunan mafarkin da zai saka ni na tashi.

Daga karshe ma kawai na mike nayi alwala na fara nafila, ina neman gafara Allah da kuma neman rufin asiri, sannan nayiwa mahaifi na addu'ar Allah ya haskaka masa kabarin sa, haka aka gama zaman makoki, kowa ya watse ana kan neman Aunty Zarah, amma dai har lokacin babu wani labari, kuma har kawo yau, Allah ya amsa addu'a ta, babu wanda ya taba sani, daga ni sai Allah sai kuma Salis, sai kuma ke da yau na sanar dake.

Kai ta rike tana jin jina ikon Allah, sannan ta kalle shi tace, ke nan yanzu kana nufin bata mutu ba kenan shine take zuwa mana ko kuwa fatalwa take mana, ke kin yarda da fatalwa, aa bana ceba, sai dai mu tambayi Malamai, amma kafin nan yana da kyau, ka fara sanarwa da Hajiya, nima nayi tunanin haka, ya dai kamata.

Amma a gaskiya daga yanzu har zuwa lokacin da za'a san mafita gaskiya mun daina kwana a gidan nan, sai ko hotel ne ka kama mana, haba hotel da mutuncin mu, wllh bazan iya kai matata hotel ba, sai dai mu nemi wani gidan a cikin gidaje na mu koma, to baka tunanin hakan zai iya jawo hankalin mutane su nemi jin ba'asin abinda yasa muka bar nan din.

Hakane, amma kinga mu bar maganar nan sai naje wajen Hajiya tukunna, itama muji abinda za tace akai tukunna, to amma yanzu ni a ina zaka barni, shirya mu tafi gidan Hajiyan, ba dai shike nan ba, eh naji shike nan din, idan ba gulma ba, naga jiya da masifa na cin ki, ke kadai ma kika kwana, eh wannan ai bana cikin hankali na, kyaji dashi dai, ni dai shirya mu tafi, ina da abinda nake so zanyi yau.

Mikewa tayi ta fara shiri, tana yi tana satar kallon sa, gaba daya tausayi ma yake bata, gashi duk irin tashin hankalin da yake ciki, baya fasa barkwanci musamman dan ya saka ta farin ciki, addu'a ta musu akan Allah ya kawo musu mafita, haka suka gama shiri suka fita, suka nufi gidan Hajiya.

Hajiya da ta gan mu tayi mamaki, sai kuma da ta fara fadan mun cika yawo, amma bayan mun karasa shigowa ganin yanayin fuskar mu, ta san ba lafiya ba, shiru tayi har muka sami waje muka zauna, bayan mun gaishe ta ni sai na mike na nufi dakin da ta saka aka kaini da muka zo nayi sallah.

Bayan na tashi, tace dashi, Abdulmalik amma dai ina fatan ba matsala kuka fara samu ba daga yin auren, dan dai kasan wannan ba tarbiyyar gidan nan bace, ta fada ranta a hade, aa ko daya Hajiya, wata dai matsalar ce daban ta kawo mu, to matsala kuma, to Allah ya kawo sauki, ina sauraron ka.

Aa Hajiya zai dai fi kyau mu shiga daga dakin ki, to abun har babba ne haka, to tashi muje, ta fada tana mikewa tayi hanyar bedroom din ta, shi ma yabi bayan ta.

Tsautsayi Part (46)
Aisha Muhammad

Bayan sun zauna sun nutsu, ya fara mata bayani har ya kai karshe tana sauraron sa bata ce uffan ba, sai da taji yayi shiru alamar ya gama, sannan ta numfasa tace, amma Abdulmalik ka bani mamaki da har zaka iya boye min irin wannan babban al'amari.

Yanzu dama har kana da wanda zaka nema da matsalar ka sama dani, a gaskiya bazan boye maka ba, banji dadin abinda ka aikata ba, kuma ko dan gaba kada ka kara yin irin wannan kuskuren, insha Allah baza'a kara aikata hakan ba, kiyi hakuri ki gafarce mu, wllh ko a lokacin ma, dan munga kina cikin tashin hankali bai kamata mu kuma jefa ki a wani tashin hankalin ba.

Yanzu dai shike nan wannan ta wuce sai dai a kiyayi gaba, insha Allah Hajiya, nisawa tayi, sannan tace kira min Malam Saminu kaji yana gida, Malam Saminu Malamin Alhaji ne, kuma Malamin Allah, dan ko kadan baya daga cikin iri wadan nan Malam da wasu masu kudin suke ta'ammali dasu, suna musu duba, shi ko kadan ba haka yake ba, kuma Alhaji ya dauke shi, kamar uba ko kuma babban yayan shi, baya yin komai sai ya nemi shawarar shi.

Wayar sa ya ciro a aljihu ya nemi number ya kira, bugu biyu kuwa ya daga, bakin sa dauke da sallama, bayan sun gaisa, ya dan tsokani Abdulmalik dan ya dauke shi kamar jikan sa, yace Baba Hajiya ce tace na kira ka naji kana gida zan kawo ta, to ina fatan dai lafiya, aa lafiya kalau, akwai dai abinda zai kawo ta ne, idan tazo zaka ji, to shike nan sai tazo din, ina gida, ni yanzu ina nake zuwa, Allah ya kawo ku lafiya, daga nan sukai sallama ya kashe wayar.

Wajen Hajiya ya juyo, yace to yace yana nan zuwa zamuyi ko, dan ko bata fada ba yasan me take nufi, eh yanzu ma kuwa, bari na dauko mayafi na, ciki ta shiga babu jimawa ta fito, shima ya leka dakin da Saudah take, ya sanar da ita zasu fita da Hajiya, ta jira shi, Allah ya tsare ta musu, ya fito.

Bayan sunje ta yiwa Malam Saminu bayani shima Abdulmalik din ya kara masa karin bayani, shiru yayi na dan wani lokaci, sannan yace, wato Hajiya dake da Alhaji duka ina daukar ku ne a matsayin yaya na, wannan kuma jika na ne, sannan ku dukan ku a wajen Alhaji ba baki bane, balle ayi tunanin zaku iya bayyanar da wani sirri na Alhaji har wani yaji.

Kuma duk da haka, ba dan dalili ya kawo da ya kamata na muku wannan bayanin ba, sabida ku fahimce ni dakyau ba, da wllh har na bar duniya bazan taba fadawa wani wannan sirrin ba, duk da kasancewar ku abu daya da Alhaji, kuma ai kun gani, da ina da niyyar sanar muku, da tuni na fada, ko yanzun ma ban so hakan ba, amma ta kama ne, kuma nasan ko Alhaji yana raye, yanzu bazai damu ba, idan kuka san wannan sirrin.

Wannan wane sirri ne Malam, yanzu kuwa zan sanar daku, wato Allah ya hada mu da Alhaji ne tun kafin yayi auren sa na fari, kuma tunda na san shi, nasan shi mutum ne mai matukar son yaga ya tara zuri'a, sabida ya samu wanda zai gaje shi, amma Allah cikin ikon sa, koda yayi aure, sai Allah ya basu jinkirin samun karuwa.

Tsautsayi Part (47)
Aisha Muhammad

Tun abun yana damun sa shi kadai yana boyewa, har ta kai ya fito ya sanarwa da matar, itace ta bashi shawarar suje suga likita mana, ko akwai abinda za'a iya musu, ai kuwa nan da nan yayi na'am da wannan shawara, babu bata lokaci kuwa ya dauke ta sukaje wajen likita.

Bayan an musu duk wasu gwaje gwaje, aka tabbatar musu da matsalar daga wajen shi ne, bazai taba haihuwa ba, sai dai kuma wani ikon Allah, bayan sun baro asibiti sun dawo gida ya shiga damuwa sosai, ita marigayiya itace ta dinga kwantar masa da hankali, tace ita ta amince zata zauna dashi a haka, kuma indai daga bakin tane babu wanda zaiji, wai yana da wata matsala.

Hakan da tayi ya rage masa kaso mai yawa na damuwar shi, sai dai har lokacin yana jin daci da damuwar halin daya tsinci kan shi a ciki, duk da yanda yake son yaya amma wai ace bazai taba haihuwa ba, haka dai ya dauki dangana, suka cigaba da gudanar da rayuwar su.

Bayan tsahon lokaci basu haihu ba, sai ta fara fuskantar tsangwama da kyara a wajen yan uwan Alhaji, akan bata haihu, daga baya abun har ya kai ga mahaifiyar sa, itama ta fara matsa masa akan kawai ya kara aure, duk da kasancewar ita tasan da maganar matsalar shi, amma ta take, Allah dai ya jikan ta, tace wai ai gara ya kara aka sani ko za'a dace, shi kuma fur yaki amincewa dan yana ganin kamar bai yiwa matar sa adalci ba.

Daga baya da fitinar tayi yawa da kanta, ta same shi, tace ita wllh indai dan ita yaki amincewa da karin auren nan, to wllh ita ta amince, ada duk da haka yaki, sai da ta nuna masa ita fa yake janyowa bakin jini, sannan dai ya amince ya kara aure, amma dai ba'a dace ba, kuma yarinyar daya aura taki zama, tace wai ita bazata zauna da juya ba, wannan maganar tayiwa Alhaji ciwo.

Har sai da ya kasa jurewa ya sanarwa da matar sa, ita kanta abun ya mata ciwo sosai, hakan yasa tace dashi, Alhaji ina da wata shawara, tame fa, ya tambaye ta, mai zai hana muje gidan marayu mu dauko yaro, ko ya rage mana radadin rashin haihuwar nan, hmm to ai abinda bazaki gane ba, shine mu a wajen mu ne hakan zai rage mana wani abu, amma a wajen mutane a banza ne, sabida ai sun san ba haifar shi mukai ba.

Yana fadar haka, sai wani abu yazo ranta, tace Alhaji mai zai hana muyi wani abu, me kenan ya kalle ta, nayi cikin karya, har na tsahon wata tara, daga nan idan cikin ya isa haihuwa, sai muje gidan marayu, mu dauko jariri sabuwar haihuwa, idan muka tafi asibiti haihuwa, sai mu dawo da yaron mu, kaga har duniya ta tashi, babu wanda zai taba sani, kuma kaga daga sannan daga ni har kai, babu mai kuma mana kallon bama haihuwa, sai dai ace bamu haifa da yawa ba, kuma ma muna addu'a idan Allah yaso sai kaga wata rana ya bamu.

Shiru yayi na wani dan lokaci, can yace da ita, gaskiya abinda kika zo dashi abu ne mai girma dan haka ki bani lokaci sai nayu tunanin, kuma kafin nan ma zanje nayi shawara da Malam, to shike nan, Allah ya bada sa'a tace masa.

Kafin yazo ya same ni, sun fara yin magana da wani aminin sa, wanda a tsakanin su kowa baya boyewa dan uwan sa sirrin sa, kuma shima ya bashi aman na akan hakan, bayan yazo ya same ni da maganar, da naso na hana su yin karyar cikin, kawai nace musu suje su dauki yaro ba sai sunyi karya ba.

Amma daya nusar dani dalilin su nayin hakan, sai na amince musu, sabida suna so suyi karyar ne dan neman maslaha, har a wajen mahaifiyar sa, da a kullum take kara matsa masa lamba, nace suje suyi Allah ya bada sa'a, amma suji tsoron Allah kada daga baya Allah ya basu haihuwa, su wofintar da marayan Allah, yace insha Allah zasu kula.

Tsautsayi Part (48)
Aisha Muhammad

To wannan yaro da aka dauko, shine babban Yayan ku marigayi, ya fada yana kallon Abdulmalik, sunyi matukar mamaki dan basu taba kawowa ba, daga nan kuwa suka sami sauki a wajen mutane, kuma har kawo yau, idan banda ni da Alhaji da Aminin Alhaji, sai kuma ita marigayiya wato mahaifiyar Zarah, babu wanda ya taba sanin wannan sirrin sai kuma ku da kuka sani yanzu.

To bayan yaro yayi wayo, suna cigaba da rainon sa cikin kulawa, kamar dai su suka haife shi, amma har lokacin Alhaji hankalin sa yana kan ya samu nashi tsatson, dan yasan ko yaya za'aje a dawo wannan yaro dai ba jinin sa bane.

Bayan wasu shekaru, suna hira da Aminin sa Alhaji Tasi'u, yace masa, nifa Alhaji kwana biyun nan naga ka canja kamar akwai abinda yake damun ka, nisawa yayi, sannan yace, wllh Alhaji maganar matsalar nan ce dai ta rashin haihuwar nan, aa ba mun wuce wannan maganar ba, ina kuwa muka wuce tunda dai har yanzu ban samu ba.

Maganar wannan yaron fa, amma kaima wasa kake, yanzu kai ka ta ba ganin inda dan wani ya taba zama naka, wannan yaron fa mun dauke shine a matsayin kwaba, sabida takurar da mutane suke mana, amma har abada mu ai mun san ba jinin mu bane, kuma dai kasan hausawa na cewa kayan aro baya rufe katara.

Wannan gaskiya ne, to ai Alhaji kaine wani lokacin kana da kafiya, amma ai da yanzu wannan zancen sai tarihi, kamar yaya ina da kafiya, yanzu ka taba kawo min mafita akan wannan matsalar tawa naki, aa akan wannan dai ban taba ba, amma a baya nasha kawo maka, akan abubuwa da dama, amma kana saka kafa kana shurewa, wai kai mai tsoron Allah, ko ce maka akai mu bama tsoron sa.

Kabi ka makalewa wannan Malamin naka, da baya neman cigaban ka, kaga aa gaskiya kuma kar ka zagar min Malami, dan ni ina masa kallon uba ne ma, dan gaskiya ka gyara zancen ka, Allah ya baka hakuri ni ba wani abu nace ba, yanzu dai idan har ka shirya, to nima a shirye nake na kai ka inda za'a share maka hawaye.

Shiru yayi yana nazari, kaga ka bari zanyi tunani, zuwa gobe insha Allah zaka jini, to shike nan, ka dai yi tunani da kyau, dan kamar yanda ka fada ne kayan aro baya rufe katara, insha Allah, daga haka ma ya mike yace bari na wuce gida.

Bayan yaje gida ma kwana yayi yana nazarin maganar, daga bisani ma ya tashi ya fara nafila, ai kuwa da gari ya waye sai yaji, gaba daya ya kyamaci abun, sai yaji gaba daya ma hankalin sa ya karkata ga karo aure, dan haka koda Alhaji Tasi'u ya kira shi, sai ya sanar dashi, ya dakata tukunna ya dan bashi lokaci.

Bayan wannan ne Allah ya hada shi, da Hajiya Salma, wato Mahaifiyar ka, ya fada yana kallon Abdulmalik, gata nan a zaune, koda yazowa da marigayiya da maganar ta bashi goyen baya dari bisa dari, dan Allah yayi ta mace mai matukar hakuri da sanin ya kamata, bayan auren ta ne, itama yaji shiru, sai hankalin sa ya kara tashi, har ta kai tunanin sa ya fara karkata ga shawarar Alhaji Tasi'u, dan yana ganin idan dai ba wannan hanyar yabi ba, ba zai taba samun haihuwa ba.

Ai kuwa yana fita ya nufi gidan Alhaji Tasi'u, bayan sun gaisa ya sanar dashi abinda yake tafe dashi, dariya yayi yace dama nasan zaka dawo, to shike nan, yanzu ai sai ka saka mana ranar da zamuje ko, ai ni ko yau ma mu tafi mana, aa yau rana tayi, dan kauyen da nisa, sai dai mu bari gobe, ka fito kamar karfe tara, sai muje, yace Allah ya nuna mana.

Washe gari kuwa kamar yanda suka tsara karfe tara suka dauki hanya, bayan sun isa, sukayi bayanin abinda ke tafe dasu, boka yace babu damuwa, matar ka zata haihu, amma sharadin wannan aikin, duk aljanin da aka saka yayi aikin bazai taba barin jikin yaron ba, ko bayan ya mutu, zai iya cigaba da amfani da siffar sa.

Shi Alhaji da ya tsaya yana tunani, kawai Alhaji Tasi'u yace, sun amince, ai kuwa a take boka yayi wata irin kururuwa, sannan yace, wacce a cikin matan ka kake so a yiwa aikin, babu wani dogon nazari yace uwar gidan, boka ya kara yin wata kururuwar yana fadar wasu irin magan ganu, sannan kuma yayi shiru.

A cikin hannun sa daya dunkule ya bude sai ga wani kunshin magani, a cikin wani dan tsumma, ya mikawa, Alhaji, yace ya karba da hannun hagu, bayan ya karba, yace to gashi nan, duk randa yake dakin uwar gidan zai jika wannan maganin yasha ya bata itama ta sha, a ranar babu makawa zata dauki ciki.

Tsautsayi Part (49)
Aisha Muhammad

Alhaji zai tsaya godiya ya daka musu tsawa, yace maza su ajiye kudin su, su fita, Alhaji Tasi'u ne ya zaro wasu kudi masu yawa daga aljihun sa ya ajiye ya kama hannu Alhaji suka fita, sai bayan sun shiga mota, sannan Alhaji ya dawo cikin nutsuwar sa, Alhaji Tasi'u ya tuntsure da dariya yace haba Alhaji kar ka bada maza mana, duk kabi ka wani rude, numfasawa yayi, yace wllh Alhaji gaba daya wani iri nake ji kamar kada nayi amfani da maganin nan.

Kallon sa Alhaji Tasi'u yayi da bacin rai, yace amma ka bata min lokaci, to wllh babu ruwana, dan wannan mutumin da ka gani, baya bayar da magani a zubar masa, wllh mummunan mataki yake dauka akan mutum dan haka sai kayi kana sani, daga haka yaja motar suka bar wajen.

Bayan ya koma gida haka yayi ta juya abun a ransa, ya dai samu waje ya boye maganin, dama yau a dakin uwar gida yake, dan haka bayan sun gama cin abinci ya dauko maganin ya jika musu, suka sha, tace Alhaji yau kuma ka tuna da karbe karben maganin ne, shi dai yayi shiru, tace to Allah yasa mu dace, yace amin.

Bayan sati uku, ranar nan da safe Hajiya ta tashi da amai ga wani masifaffen zazzabi a jikin ta, gari na wayewa suka tafi asibiti, bayan an mata gwaje gwaje aka tabbatar musu da tana dauke da ciki na sati uku dai dai, take Alhaji ya tuno da wannan magani, sai kuma tsoro ya fara kama shi, na sharadin da bokan ya fada musu.

Hakan ne yasa har saida ta lura da kamar baiyi farin ciki ba, bayan sun koma gida take tambayar shi, sai yace mata baya jin dadi ne, bata yarda ba, amma dai tayi kokari ta watsar, shima kokarin yayi ya cire komai a ransa, gudun karta fahimci da akwai wata matsala.

Bayan an haifi Zarah kuma sai babu dadewa kema Allah ya baki cikin Abdulmalik, ya nunawa Alhaji yayi gajen hakuri ne, a lokacin murnar da Alhaji yayi ba kadan bace, yayi farin ciki fiye da na samun Zarah da yayi, dan wancan yasan abinda ya aikata akai, amma yayi kokarin boyewa, dan kada Hajiya ta fahimta, yasan ranta ba zai mata dadi ba
 Bayan rasuwar mahaifiyar Zarah ne Alhaji yazo ya same ni, bayan abubuwan da take aikatawa sun kara yawa, abun ba kadan ba yake damun sa, wanda har ta dalilin haka ya samu ciwon hawan jini, banda rashin kwanciyar hankali da yake fuskanta tun bayan haihuwar Zarah, sosai yayi nadamar abinda ya aikata.

Hakan yasa yazo ya same ni, ya mun bayanin duk abinda yake faruwa kamar yanda nima na muku yanzu, sosai nayi mamakin yanda ya iya zuwa ya aikata irin wannan ta'asa duk da na masa gargadi sosai, amma dai tunda ta riga ta faru, nasiha kawai na masa, sannan na bashi shawar yaje yayi ta istigifari, domin shi Allah gafururrahim ne.

Akan maganar Zarah kuwa addu'a nace yaje yayi ta mata har Allah ya raba ta da shaidanin da yake tare da ita, amma dai har Allah ya karbi rayuwar sa, lokaci zuwa lokaci ya kan zo min da maganar matsalar tata, na kan ce masa yaje yayi ta taya ta da addu'a muma muna mata, har Allah ya kawo karshen abun, tunda ko ruwan addu'a aka bata bazata sha ba, dan haka sai muyi ta taya ta da addu'a da bakin mu.

To a tunani na maganar da kuka zo min da ita, ina tunanin bazai wuce shaidanin dake tare da ita ne koda ta mutu ma bai rabu da ita ba, yake zuwa muku da siffar ta, tunda dai mu nan duka mun riga da mun san duk wanda ya mutu baya taba dawowa, kuma fatalwa ma dai ba gaskiya bace, sai dai shaidanu.

Dan haka ina ganin wannan ba zai zama wani matsala ba, abinda za'ayi, kawai shine, kuje ku cigaba da addu'a, sannan akwai wasu magunguna na tsari wanda yanzu zan rubuta maka kayan hadin ka siyo sai a hada muku ku dinga amfani dasu da kai da iyalin naka, sannan ku tabbatar kuna kula da azkar din ku, insha Allah babu abinda zai faru.

Tsautsayi Part (50)
Aisha Muhammad

Sannan game da abinda ka aikata kai Abdulmalik, babu laifi a cikin abinda ya faru, tunda kai kayi kokarin kare kan kane, sai dai abinda ka aikata ba dai dai ba, shine boye gawar ta daka yi, duk da kai kayi hakan ne dan bawa kan ka kariya, amma dai abinda yafi shine daka fito da maganar a lokacin, dan shi duk mai gaskiya yana tare da Allah, duk yanda kake ganin babu hanyar da za'a gano gaskiya, shi Allah yasan yanda zai yi dakai.

Kuma shi Allah ba azzalumin sarki bane, ba zai taba bari a zalunce ka ba, wllh ni kaina Malam daga baya nayi nadama, amma a lokacin na rasa mafita ne, amma wllh Malam yanzu a shirye nake da na bayyana abinda ya faru da kai kaina ga hukuma.

Aa ai shi Allah baya son haka, idan har Allah ya rufa maka asiri, to bai kyautu ka tonawa kan ka ba, dan haka a bar abin nan a yanda yake, kai dai kawai kaje kai ta istigfari, domin shi Allah gafururrahim ne, Allah ubangiji ya yafe mana baki daya, duka suka amsa da ameen daga nan sukai wa Malam sallama, bayan ya rubutawa Abdulmalik abubuwan da zai siyo.

Ya karba akan zai je ya kai Hajiya sannan sai yaje ya siyo ya kawo masa, bayan ya ajiye Hajiya ko gidan bai shiga ba ya juya ya tafi siyan kayan hada maganin, bayan ya kaima masa, yace ya dawo jibi ya karbi maganin, godiya ya masa sannan ya koma gidan Hajiya.

Bayan ya koma, Hajiya da kanta ta kira Saudah ta mata bayanin shaidanu ne suke jikin Zarah, to shine bayan ta mutu shaidanin suke amfani da siffar ta, suna zuwa musu, tayi mata bayani sosai yanda zata gamsu, kamar yanda Malam ya musu, sai dai bata fada mata, dalilin samuwar shaidanun ba, ta barta akan kawai daga Allah ne.

Abdulmalik ne yace, to abinda za'ai kawai sai su zauna anan gidan Hajiya har sai Malam ya gama hada musu maganin, sannan sai su koma, nan fa Saudah tayi tsalle ta dire, tace ai wllh babu ita babu wannan gida, sai dai ya nema musu wani gidan su koma, wannan kuma yasan yanda zai yi dashi.

Babu yanda basuyi da ita ba, amma tace itafa ba da ita ba, daga karshe Hajiya ce ta kawo shawarar su tafi wata kasar, a zuwan honey moon suka tafi, amma kafin nan su fara zama a gidan ta, har su kammala maganin su, sannan sai su tafi, idan yaso kafin su dawo, sai a nemi daya daga cikin gidajen su, a shirya musu shi, idan suka dawo, kawai sai a kawo wani dalilin ace sun koma can da zama.

Duka sun gamsu da shawarar da Hajiya ta kawo, dan haka suka zauna a nan gidan Hajiya har suka kammala maganin, zuwa lokacin dama ya gama shirya musu tafiyar su, zuwa kasar Paris, ana gobe zasu tafi, Saudah taje gida ta musu sallama, suma honey moon kawai tace musu zasu tafi, amma ta sanar dasu, idan sun dawo, zasu canza gida, sabida har yanzu akwai matsalar shedanu a wannan gidan.

Ance watakila hakan yana da alaka da dadewar da gidan yayi babu mutane, dan haka ita tace bazata cigaba da zama a ciki ba, suma duk sun gamsu da wannan hukunci, sai dare, sannan Abdulmalik yazo daukar ta, shima ya shigo ya musu sallama, yana tsokanar Baby wai ko zata bisu.

Washe gari jirgin su ya daga zuwa kasar Paris, sai muce Allah ya sauke su lafiya.

Alhamdulillah.
A nan muka kawo karshen wannan littafi namu mai suna Tsautsayi, ina fatan Allah ya yafe mana abinda muka rubuta ba dai dai ba, muna masu naiman gafarar duk wanda yaji wani bangare na labarin yayi kama da rayuwar sa, wannan kagaggen labari ne, bamuyi shi dan wani ko wata ba.

Bissalam.....