DAREN GOMA SHA HUD'Ucomplt
10/10/20, 1:12 AM - Anti qamshi🌷: *DAREN GOMA SHA HUD'U*🪔🪔
Written By Bintuu Seer
1
This is historical adventure story which occurred during the era of slave trade in one of the biggest and prestigious kingdom in middle east........
K'atoton jirgin ruwa ne irin gari gudan nan yana tafe a saman tekun atlantic ocean cikin tsakiyar daren goma sha hud'u,duniyar tamu gauraye take da hasken farin wata yana hasken ruwan teku,idan mai hange ya qure dubansa gabas da yamma, kudu da arewa babu abunda zaka hango sai ruwan tekun bahar maliya wanda baida iyaka,tamkar gbdy duniyar tamu ruwa ne sbd girman ruwan teku,jirgin ya fito ne daga nahiyarmu ta africa zuwa qasashen sahara.....
A cikin wannan jirgi kowa yana sabgogin gabansa tamkar ba a saman teku suke ba, yawancin fasinjojin wannan jirgi larabawa ne da turawa wanda suke zuwa qasashenmu na baqar fata kwasar al'umma su kaisu qasarsu su maishesu bayi, yanzun ma hknne don kuwa kusan dukkanin baqar fatar daka gani cikin wannan jirgi toh yana daya daga cikin kamammun bayin da suka kamo a qasashenmu na africa,wasu y'an mata na gano cure wuri guda daka gani dukkaninsu sun fito ne daga mabambamtan qasashe don kowacce cikinsu yanayin shigar jikinta ya bayyana hkn, wasu yan fillo na gano sanye cikin shigarsu ta saqi daga ganinsu fulanin ruga su biyar ne kowacce ba baya bace a fagen kyan halitta saida daga qarshen duk na rauna kyawun halittarsu lkcin da idanu na suka sauka bisa kan d'ayan cikinsu dake takure wuri guda ta sanya fuskarta tsakanin cinyoyinta nayi nasarar tozali da kyakykyawar fuskarta wannan yar fillo ne lkcin da wani bature dake gefensu yasa hannu ya dago dakanta ya busa mata hayaqin sigarin dayake busawa,lalle tsarki ya tabbata ga ubangijin daya qagi wannan kyakykyawar halitta, tana da dara dara idanu farare tas tamkar madara, bakinta dan mitsitsi ga le6enta pink tamkar ta sanya jan baki, hancinta dodar yake, kanta babu dankwali hkn ya bani daman ganin tsawon gashin kanta, gashin ra6e yake gida biyu rayi kalba, tsawon kalbar ta sauka har duwawunta ga gashin sai kyalli yake don baqine qirin irinna fulanin usul,billah Allah yyi ruwan tsallar madarar kyau a wurin, tsantsar kyau ne kawai daga rabbil izzati babu alqus.....
Jikinta rawa yake,haqoranta na had'uwa da juna ta qara qudundune jikinta a cikin wani kwali dake gefenta don dukkaninsu a yashe suke a qasan jirgin, babbar cikunsu ta matso kusa da ita tana ta6a jikinta tace" bimbii zazza6i kk,jikinki da zafi sosai" tana mata mgn ne da harshen fillanci,shiru ta mata batace komai ba, baturen dake kula dasu ne yazo wurin yana kallonsu sai kuma ya d'ora hannunsa a jikin bimbii yaji da zafi sosai yace"noo" watsa musu harara yyi yana huci don shi abunda ya tsana ya samu mara cikakken lfy a cikin bayinsa,gani yake tamkar asara zeyi kafin ya isa dasu wurin da saidawa,kuma ma ba kowa ne yake siyan bawa mara isashshiyar lfy ba, dafe kansa yyi ya koma ya zauna ya cigaba da busar sigarinsa, wani balarabe dake gefe guda shima tafe yake da nasa bayin ya kalli baturen yace" ita wannan bata da lfy ne" mgn yake masa cikin British English irinna na qasar birtaniyya, d'ago da kansa yyi ya kalli balaraben yace" ehh" tasowa balaraben yyi yazo wurin yana kallonsu sai yyi murmushi ya kalli baturen yace" idan kana so sai muyi musanye na baka bawa mai lfy ka bani ita" tuni baturen ya miqe ya kalli balaraben yana dariya yace" nunamin bayinka sai na za6a dakaina" murmushi balaraben yyi ya nuna masa tawagar bayinsa wadanda kusan dukkaninsu zaratan samari ne majiya qarfi saidai mafi yawancinsu qabilu ne" kallonsu ya dingayi har idanunsa suka sauka kan wani murd'add'en basamuden mutum mai ji da qarfi ya dafashi yace" muyi musanyan da wannan" hk balaraben yasa d'aya daga cikin masu kula masa da bayin ya kunce wannan mutumi ya damqawa wannan bature shi kuma ya taso qeyar bimbii ya kawo masa cikin jerin bayinsa, tana kuka sauran yan'uwanta suna kuka hk don dole suka rabu ita ta koma cikin jerin tawagar bayin wannan balarabe......
A jerin bayin nasa su biyar ne kawai mata kuma kowacce yarenta daban ba wanda yake jin yaren wani, sauran duk maza, tunda ta koma wannan tawagar ta koma tamkar kurma, basa iya mgn da junansu don basu jin yaren juna, zazza6in dake jikinta ya soma tsananta sai rawar d'ari take gashi babu abun rufa hk dai ta takure wuri d'aya, wani saurayi ne d'an qabilar igbo fari sol dashi ya matso kusa da ita ya cire rigar sanyin dake jikinsa ya rufa mata, jin a rufe ne yasa d'ago dakanta tayi tana kallonsa sai kuma ta komar da kanta kan guiwowinta, mgn yyiwa daya daga cikin masu kula dasu ya miqo masa ruwan sha a wata kwarya ya ta6ata ta d'ago da sauri ta matsa daga kusa dashi don su babban zunubi ne a rugansu namiji ya ta6a mace shiyasa tayi saurin matsawa,miqa mata kwaryan ruwan yyi ta miqa hannunta ta amsa ta soma sha sannan ta miqa masa cikin harshen fillanci tace ta gode.........................
*Wannan novel na siyarwa ne karki soma karanta free pages idan kinsan baki da halin siyan sauran pages wannan shawara ce........Ga wacce ta shirya siye zaki tura #300 ta wannan detail din
acct no: 0100790419
Bank:Union bank
Name: Alhaji shahida Nasir
Idan kin tura saiki turomin da screensht na payment naki ta wannan layin
07041195806
Alk'alamin Bintuu ne👌�
10/10/20, 1:12 AM - Anti qamshi🌷: *DAREN GOMA SHA HUD'U*🪔🪔
Written By Bintuu Seer
2
Kwanaki sun shud'e anyi dare dayawa duk sun shud'e amma sukam suna doron ruwan teku suna tfy rabonsu da doron qasa sun jima, duk cikin wad'annan bayi babu wanda yasan qasar da suka nufa abunda suka sani kawai an kamosu daga qasashensu an sakosu cikin jirgi a matsayin kamammun bayi,tunda bimbii ta soma zazza6i wannan saurayin d'an kabilar igbo shike kula da ita yana tausayin bimbii sosai sbd gsky tana da qarancin shekaru, sanyi na ratsa dukkanin sassan jikinsu amma saidai su takure wuri d'aya don babu abun rufa, shi kuwa wannan saurayin daga shi sai wata yar qaramar riga don ya cire rigan dake da kauri a jikinsa ya rufawa bimbii, jirgin nasu ne ya soma tangal tangal tamkar ze kifa kowa cikin wannan jirginsa cikinsa ya d'uri ruwa sbd tsoro, riqe hannun bimbii yyi qam don yaga gbdy ta rikice cikin ikon Allah jirgin ya koma yadda yake normal, kowa ya soma ajiyar zuciya, bimbii a hnkli ta janye hannunta, kallonsa tayi taga alamun shima dai yana jin sanyi amma ya gwammace ya rufa mata jacket dinsa, hannu tasa ta cire rigan daya rufa mata ta rufa masa, kallonta yyi yana qoqarin cire rigan tayi saurin dakatar dashi da hannunta cikin harshen fillanci tace" bana jin sanyi ka sanya kawai" be fahimci mai take fad'I ba amma ya fuskanci abunda takeson yyi, murmushi yyi mata yace"nagode" saurin dago da kanta tayi tana qare masa kallo don tabbas idan har ba kunnenta ne ya jiye mata ba daidai ba kamar hausa taji yyi,tana jin hausa itama 2kad'an don tana fita kasuwa tallan nono, tace" kana jin hausa ne" murmushi ya kuma mata a karo na biyu yace" ehh,amma ni igbo ne daga Abia nk" tace" me sunanka" yace" obinnah" yace"ke me sunanki" tace" bimbii" ya qara nanata sunan nata yace" daga ina kk" tace" ruganmu tana kudu da qauyen lamirde cikin garin gombe" kad'a mata kai yyi alamun ya gamsu, daga shi har ita babu wanda hausar tasa ke fita daidai duk tata suke a hausar amma hk suke dan mgn, bimbii bata da yawan zance amma saita samu kanta da sakewa dashi, cikin tsakiyar daren goma sha hudu jirginsu ya samu isa matattarar tsayawar jiragen ruwa wato Brandford port dake Amsterdam,tunda suka fito daga jirgin nan suke 2kalle kana ganinsu kaga k'auyawa, dole kam suyi k'auyanci don kaf nahiyarmu ta africa ba irin wannan port din, turawan dake kai kawo a wannan port kuwa kallonsu suke tamkar kashi sbd tsabar racism, dukkaninsu babu wanda ze iya fad'ar sunan qasar da suke amma yanayin kalar fatar mutanen qasar ya tabbatar musu qasa masu jan kunne ce wato lardin turawa suke, falmata d'aya da cikin yan'uwan bimbii da aka rabasu tun a jirgi ta saci jiki daga cikin tasu tawagar ta shigo cikin tawagar su bimbii, riqo hannun bimbii tayi tana kuka tace" bimbii zamu rabu gbdy kin ga zasu kuma shigar damu wani jirgin bamu san inda zasu kaimu ba, mudai tamu qaddarar kenan sun rabamu da danginmu sun shigo damu duniya,bimbii ki kula da kanki sannan ki saukar da kanki kiyi duk abunda suka sanyaki don basu da imani zasu iya kashe mutum" kuka suke sosai suna qanqame da juna har lkcin da baturan dake jagorantar tawagarsu ya ankara babu mace daya cikin yan matan nan, suna rumgume da juna suna kuka suka ji an finciko falmata batare da 6ata lkci ba ya sauke mata tagwayen mari a fuska sannan ya jata ya koma da ita cikin tawagarsu, had'esu turawan sukayi suka zargesu da igiya sannan suka tasa qeyarsu suka shige wani jirgin dasu,suna tfy suna waiwayen yar'uwarsu itako bimbii kuka take sosai tana kallonsu har suka shige jirgin,obinnah dake kusa da ita ne ya soma rarrashinta, itama tana cikin alhinin rabuwa da yan'uwanta wani daga cikin masu kula dasu yazo yace ta biyoshi, batasan meze mata ba ita dai kawai batare da gardama ba ta miqe tabi bayansa, obinnah dake gefenta yyi saurin miqewa ze rakata mutumin ya daka masa tsawa dole ya koma ya zauna ita kuwa tabi bayansa suka qarasa wurin wani tsohon jirgin ruwa dake gefen port din, nuna mata kofar jirgin yyi yace ta shiga, shiga tayi shima yabi bayanta, suna shiga gabanta ya yanke ya fad'I don lura tayi jirgin abandon one ne ba kowa cikinsa sai tarin shirgi, bata qarasa rikicewa ba saida taga ya soma zame wandon dake jikinsa, take jikinta ya soma rawa tamkar mazari ta soma ja da baya cike da tsantsar rudewa, murmushi yyi lkcin daya gama zame dukkanin tufafin dake jikinsa ya kalleta yaga yadda ta rufe idanunta ruf sai makyarkyata jikinta yake ta durqushe a wurin tare da daga hannayenta dukka ta soma masa mgn da harshen fillanci tace" ka yiwa Allah ka yiwa annabinsa ka kyaleni karka ketamin haddi niba kafira bace" cikin kuka take roqonsa duk fuskarta tayi 2sha6e da hawaye, shi kuwa tumuqin arne besan ma abunda take fad'I ba don ba jin yarenta yake ba, shima baqar fata ne amma yyi kala da irin mutanen kenya din nan baqine qirin tamkar gawayi asalin african man, matsowa kusa da ita tana ja da baya har takai qarshen jirgin yana biye da ita da murmushin qeta a fuskarsa, hannu yasa yana shirin kamota aka doko kofar jirgin, wannan asalin balaraben ne daya amsheta daga wurin baturen nan, kallon mutumin yyi ransa a mugun 6ace ya soma zaqinsa cikin harshen turanci yace" kai wawa ne so kk kamin asara, kasan dalilin dayasa na amsheta sbd daka ganinta kasan danyar budurwa ce kuma kudin virgins ko wurin saidawa daban yake, shine dan kai dan iskane kk neman mini asara daman all those africans are bunch of animals,bauta ita tafi dacewa daku" hk balaraben nan ya din ga masifa, shi kuwa sai qoqarin sanya wandonsa yake,bimbii kuwa na daga gefe sai ajiyar zuciya take, qeyarta dan balaraben ya tasa ya komar da ita cikin tawagar sauran bayin, obinnah na ganinta ya soma tmbyrta ko sun mata wani abunne ta kada masa kai alamar basu mata komai ba,suna nan yashe a gefen ruwa tamkar ba mutane ba sanyi sai busasu yake sai wurin asuba suka ga tsayawar wani jirgi, yana sauke fasinjojin cikinsa ya soma deban wasu fasinjojin, hk akazo aka tasa qeyarsu suka shige wannan jirgi,kwanansu biyu suna tfy kafin suka soma shiga lardin larabawa, jirginsu ya tsaya ne qasar KUWAIT..... Abdullah bin faisal International port, tun saukarsu daga jirgi wasu zungura zunguran motoci suka soma dibansu kai tsaye kasuwar cinikin bayi aka wuce dasu, yadda ake cin kasuwa saida tumakai ko dawakai hk ake cin kasuwar saida bayi, manya manya keji akeyi ake zuba bayin ciki, suma hk aka zubasu cikin keji, farashin bayin hawan hawa ne wani kudinsa yafi na wani, manya masu kudi da jinin sarauta da masu mulki sukan siye bayin dayawa sukaisu muhallinsu suna musu kowacce kalar bauta amma yawanci jinin sarauta basu daukan baqar fata sai larabawa kalar fatarsu, masu ma'aikatu da gonaki suke siyen baqar fata sukaisu suna musu aiki amma masu daukar boyi boyin gd ma sunyi son larabawa kalar fatarsu suna mugun kyamar baqar fata musumman na africa,bimbii an hadata keji daya ne da wasu yan'mata amma dukkaninsu larabawa ne sukansu kallonta suke suna mamakin wai daman a qasashen baqar fata ma akwai mata masu kyau kamar bimbii, gani sukayi gashin kanta yafi nasu tsawo gata duk cikinsu ta fisu kyau da cikakken diri irinna mata saidai kawai su nuna mata hasken fata, mutanen sai 2zirga suke suna siyen bayin da suka musu,kowanne bawa so yake a siyesa ko Allah zesa yyi dace da mutanen kwarai su masa riqon arziqi,wata balarabiya itama tazo duba bayi kallon daya zaka mata kasan ba daga gdn talauci take ba, balaraben dake dasu bimbii ne yyi saurin tararta ya kawota wurin kejin dasu bimbii suke wai ta duba koda wacce tayi mata, kallonsu take daya bayan daya tana duddubasu tamkar wacce zata siyi akuya, idanunta ne ya tsaya kan bimbii ta nuna bimbii da hannu tace" wannan baqar fata ce koh" balaraben yace" ehh,amma tana da cikakken lfy ba zaki samu mtsl da ita ba" sake kallon bimbii tayi tace masa ya fito da bimbii aikuwa ya bude kejin ya fito da bimbii, batare da bata lokaci ba tayi cinikinta ta biya suka bata certificates of ownership na bimbii har wurin motarta balaraben ya rakata ya budewa bimbii boot din mota ta shiga aka rufeta sannan matar ta shige gdn baya drivernta yaja motar suka wuce, bimbii na bayan boot din motar tamkar akuya tana rakube har suka iso gdnsu sannan aka budeta ta fito, gdn qaramin bungalor ne mai kyau da tsari ga furanni ta ko'ina kunsan larabawa da son hutawa, tsagaya matar ta somayi da bimbii tana nuna mata ayyukan da yake nata ciki har da baiwa wadannan furannin ruwa da kula dasu, duk aikin nata na wajene be danganci cikin bedroms,kitchen ko cikin parlourn ba don wannan aiki daya shafi cimmarsu ko kula da wurin kwanansu basu amincewa da baqi yyi musu ba suna da kyankyamin baqin mutum sosai duk wannan ayyukan na cikin gd balarabiya yar'uwarsu suke dauka, wani qaramin daki aka baiwa bimbii, kullum bimbii tunkan kowa ya tashi take tashi tayi dukkanin aikin da matar nan ta yanka mata, batasan sunan wannan balarabiya ba amma taji ma'aikatan gdn na kiranta ennah, tana da tsauri sosai batason wasa ko sakaci da aiki, tana yara biyu dukkaninsu maza ne amma kowanne da gdnsa basu zaune tare da ita, bawai iyali ne dasu ba amma kowa yana zaune shi kadai a gdnsa saidai duk weekend suzo su gaishe su yini sai dare suke tfy, ennah tana son wadannan yaran nata sosai da zayeed da maheer, maheer shine qarami atleast bazai gaza shekaru ashirin da uku ba sai zayeed mai shekaru ashirin da shida, yau weekend tun sanyin safiya bimbii ta gama aikinta, zuwan bimbii gdn yasa furanni dake gdn suka soma kyau da fitar da kyawawan furanni masu kala sannan tana yankesu tana saitasu tana cire ciyayin dake fitowa qasansu suna hanasu girma, kullum ennah na kallon yadda bimbii ke gyaran furannin ta windown dakinta, ita kanta ta yaba da aikin bimbii, kullum tana aikinta tana waqarta cikin harshen fillanci,tun tazo gdn bata taba shiga cikin wannan bungalor na masu gdn ba, ranar wata asabar maheer ya shigo gdn, tsayawa yyi yana kallon yadda bimbii ke gyaran furanni fuskarsa sam babu annuri don shi be ta6a tsammani ennah zata kawo musu baqar fata gd ba, qarasa yyi inda bimbii ke aikinta yasa hannu ya janyo mayafin dake rufe da gashin kanta ya janyo dogon gashin kanta, cike da tsoro ta dago a idanunta tana kallonshi tace" malam lfy me na mk" cikin harshen fillanci take masa mgn aikuwa ya watsa mata mari saida shatar hannunsa suka fito a fuskarta ya bala'i cikin harshen larabci wai uban waye ya kawo musu baqar fata gdnsu, muryarsa ennah taji tayi saurin fitowa ta qaraso wurin,kamashi tayi suka shige bungalor ita kuwa bimbii hawayene ya cika mata idanu kawai ganin yadda ake wulaqanta bil'adama toh shi baqar fata ba Allah ne ya halicceshi ba, itama bimbii indai a kalar fata ne tana da haske idan anan africa ne zamu iya kiranta da fara amma su kallo daya suke mata suke gane ba balarabiya bace duk da tsantsar kyawun halittarta.....
Washegari ennah ta kirata tace ta shirya zata koma gdn danta don ta bar mashi ita ta din ga masa hidima, gaban bimbii ne ya fad'i tayi shiru kawai don babu yadda ta iya a qasar da bata da kowa bata da komai sai Allah,ranar da yamma maheer yaxo ya tafi da ita gdnsa, gani tayi ai shi kadai yake zama a gdn nasa dake Najb ushakhair steet, gdn nasa qaramin flat ne mai kyau, kallonta yyi cike da tsana ya nuna mata rumfa da aka kewaye don shaqatawa yace"na miki alfarma ki din ga kwana anan idan kin tashi ki gyara furanni ki share duk gdnnan sannan ki din ga bawa kifi abinci ya nuna mata wani qarami fond dayake kiwon kifi,iya aikin daya nuna mata kaf ba wanda ze shigar da ita cikin flat dinsa, shigewa yyi ciki abinsa yabarta a wurin tare tabbatar mata da cewa daga yau aikinta xe fara, wata jemammiyar doguwar riga ce a jikinta da wani tattararren mayafi da take rufe kanta dashi, hk ta tsuguna ta soma cire matattun ciyayin dake qasan furannin tana tarawa a gefe, cike da kuzari da himma take aiwatar da aikinta babu kasala don ta qaddara she only want to survive amma tasan ita gd ko sake haduwa da danginta har abada don ta bar gd kuma nahiyarta da nisa bata ta6a sanya ran wataran zata tsinci kanta a qasarta ba hk dai take rayuwa cikin qangin bauta..........
*This book is seriously for sale dnt ever start reading the free pages if you know u can't afford the remaining pages,for those who want to purchase the continuation of the story these are the details for transaction*...... #300 naira for this acct...0100790419,alhaji shahida nasir,union bank.....send the screenshrt of ur payment through whatsapp....07041195806...for more information call....08080611486
Alkalamin bintuu ne.....
10/10/20, 1:12 AM - Anti qamshi🌷: *DAREN GOMA SHA HUD'U*🪔🪔
Written By Bintuu Seer
3
Ta gama nome busassun ciyayin dake farfajiyar gdn sannan sauyawa kifin dayake kiwo ruwa ta basu abinci sai gumi take ga yunwa dake neman kayar da ita, wannan rumfar gezevo din daya nuna mata a matsayin wurin kwananta ta nufa ta zauna tana ajiyar numfashi, gyangyadi ne ya soma daukarta ta batare data ankara ba taji saukar ruwa a tsakiyar kanta, bud'e idanunta tayi da sauri ta saukesu akan maheer yana tsaye akanta riqe da tiyon da ake baiwa furanni ruwa yana mata wanka da ruwan, kallon tsana yyi mata yace" daman bawa har yana da sukunin baccin yamma koh kin manta matsayinki ne" bata fahimtar larabcin dayake amma tana fahimtar tsantsar wulaqancinsa, miqewa tayi ya nuna mata wani karensa dake keji yace" ta fito dashi ta masa wanka" yanayin yadda yake mata alama da hannunsa yasa ta fahimci abunda yake nufi, miqa mata makullin kejin da karen yake yyi ta amsa ta nufi kejin da karen yake tana qoqarin bud'e kejin shi kuwa karen sai haushi yake kamar zeci babu tunkan ta bud'eshi aikuwa tana bud'eshi ya rarumota yana qoqarin cizonta ita kuwa sai ihu take tana neman taimako tana tureshi da iyakar k'arfinta, tun abunda ke faruwa maheer na tsaye daga gefe yana kallonsu yana murmushin mugunta, turmusheta karen yyi a qasa duk yaji mata ciwo da faratansa ita kuwa kuka take sosai tana ture karen ta matsawa duk ta cire takalman k'afarta tana jifan karen dashi,kamo rigarta yyi da haqoransa ya shirin cizonta maheer yyi masa mgn da harshen larabci sakinta yyi ya koma gefe yana haushi 2kad'an yana kallonta ita kuwa duk ta jigata hk ta miqe a razane ta soma qoqarin ficewa daga farfajiyar gdn da gudu ta fice waje don ta mugun tsorata da karen, kallonta maheer yyi sannan yyiwa karen nasa alama da idanu,wani irin tsalle karen yyi yasha gabanta ya gurnanin haushi, juyowa tayi da gudu ta koma ciki ta shige wannan rumfar gezevon, karen be biyota ba ya kyaleta ya tsaya wuri guda, maheer matsawa yyi wurin karen ya tsuguna yana shafashi don ya gama birgeshi yau din nan, kallon bimbii yyi dake raku6e tana kuka yace" matsa tashi ki fito kiyi masa wanka" bata ma ji abunda yake fad'i saida ya daka mata tsawa amma duk da hk taqi fitowa daga inda take kawai kallon karen nan take, nuna karen yyi inda take ba shiri ta fito jikinta sai rawa yake, kallonta yyi ya kalli karen sai ya bushe da dariyar mugunta ya nuna mata karen da hannu wai taje ta masa wanka, gaban mugun fad'uwa yake taje ta ciko ruwa a wani kwarmi tazo ta kama karen don taga maheer dab dasu, abun mamaki karen be kuma mata komai ba har ta gama masa wankan, tunda maheer ya shige building d'insa be kuma fitowa ba bare tasa ran ze bata abinci, yunwa takeji sosai ga dare yyi ba wurin kwanciya tana dai raku6e a wannan rumfar gezevon, tsirawa sararin samaniyya idanu tayi hawaye na zarya akan kumatunta, garin da hasken farin wata gashi kuma da yalwar taurari a sararin samaniyya tana takure wuri d'aya cikinta sai qugin yunwa yake,bata ta6a tsammanin a cikin larabawa akwai marasa imani da tausayi irin maheer ba, hk tayi kwanan zaune washegari babu k'arfi a jikinta sbd yunwa amma hk take ta faman 2aikace don tasan dole ne ma tayi ko kuma yana fitowa yaga ba tayi aikinta ba ya had'ata da karensa, maheer tashinsa kenan daga bacci ya kunna sigarinsa yana sha ya fito ya tsaya a barandar gaban building d'insa yana hangawa yaga abunda ba tayi ba ko wanda ya kamata ya qara mata, gani yyi tayi komai tunkan ya tashi ta gyara furanni ta basu ruwa sannan ta baiwa kifi abinci ta share farfajiyar wurin ta wanke masa qaramar motar hawansa tayi fes, komawa yyi ciki ya fito da wani farantin silver ya ajiye a wani wuri ya juye ragowar abincin dayaci ya rage jiya da dare sannan ya kirata ta taso tazo wurin dayake, nuna mata wannan abincin yyi yace ta dauka taje taci ta dawo da farantin wurin ta ajiye, tsugunawa tayi ta dauki farantin abincin ta wuce ta tafi ta soma ci duk da bata saba da cin irin cimmarsu ba amma hk take taci sbd yunwa, tana gamawa ta komar da farantin ta ajiye a wurin, toh tun daga wannan lkcin a wannan farantin yake zuba mata ragowar abincin idan yaci yage ya ajiye mata a wurin tamkar yadda ake zubawa kare ko sauran dabbobi abinci idan sun gani suzo suci hk itama idan taga ya zuba saita zo ta dauka ta tafi taci ta dawo da farantin ta ajiye a wurin wataran ma har abincin ya soma bushewa batasan ya zuba ba sai idan tazo ta duba ta gani ta dauka hkma kuma zataci ko yunwa ta kasheta a banza baida damuwa, yau hadari ne ya had'u sosai a garin ana sanya ran samun ruwan sama a kowanne lkci ita kuwa fargabar sakkowar ruwan take don tasan kwanan tsaye zatayi a wannan rumfar, cikin dare kuwa aka soma sheqa ruwa kamar da bakin kwarya tun ruwan yana feso mata har ya jiqa cikin rumfar gbdy, miqewa tayi ta tsaya a tsaye ta qanqame jikinta don sanyi ne ke shigarta sosai ga kuma ruwan dake fesowa cikin rumfar duk ya jiqa mata jiki,kayan dake jikinta duk ya jiqe shakaf kuma gashi su kadai gareta idan ma jiqewa sukayi hk zasu bushe a jikinta, wani lkcin idan sukayi datti sosai sai ta bari idan dare yyi dare saita tashi ta ciresu ta daura mayafinsu a jikinta ta wankesu ta shanya kafin asuba ta kwashesu ta maida jikinta, hk aketa sharara ruwa har da qanqara bimbii na tsaye qanqame da jikinta tana rawar sanyi sai gab da wayewar gari ruwan ya d'auke, ita kuwa bimbii ruwan daya jiqata ya sanya mata zazza6i sosai, tashi d'aya tana miqewa jiri ze d'ebeta ga tsananin ciwon kai, kuka take tana roqon Allah kar yasa zazza6in nan ya kayar da ita tana fargabar kar maheer ya fito ya tarar bata aiwatar da aikinta ba, jan jikinta ta somayi ta soma bawa furanni ruwa duk da ruwan saman da aka kwana ana sheqawa, jiri ne ya d'ebeta ta fad'i a wurin kanta yana wani irin sarawa, rarrabawa tayi ta koma gefe ta zauna tana maida numfashi tana son taji dama dama kafin ta kuma yunqurin miqewa, maheer ranar be fito da wuri ba sai yana building d'insa yana playing wani game, wanka ya shiga sannan ya shirya ya fito da niyya zuwa gaida mahaifiyarsa, abunda ya bashi mamaki shine yana fitowa ya tarar bimbii batayi ko d'aya daga cikin ayyukanta ba, makwancinta ya nufa ransa a mugun 6ace ya tarar ruwa ya cika wurin bata ciki, fitowa yyi ya duddubawa ya hangota jingine da wata qaramar bishiyar guiba dake qarshen gdn tana yashe a zaune tayi zaman dirshan, qarasowa yyi wurin batare da la'akari da yanayin da take ciki ba yasa hannunsa ya kamo gashin kanta ya watstsaketa da wasu lafiyayyun mari har uku sannan ya jefar da ita kanta ya bugu da bishiyar guiban sannan ya soma zazzage mata ruwan bala'i batare da digon tausayawa ga yanayinta daya ganta ciki ba ya umarceta data tashi ta kama aikinta, shiru ta masa taqi motsawa daga inda take bare yasa ran zatayi abunda ya umatceta, ranta yyi mugun 6aci take taji zuciyarta ta kangare koda kasheta zeyi ta sadaqar bata yin abunda yace, shi kuwa kallonta yake kawai da mugun mamaki don ya saba duk abunda yasata ba musu bare gardama zatayi amma yau dubi taurin kan da take gwada masa, hannu yasa ya cire belt din dake d'aure a k'ugunsa ya soma dukanta dashi tamkar Allah yyi masa wahayi, duk ya farfasa mata jiki amma be fasa dukanta ba ita kuma bata motsa daga inda take ba kuma ba tsillin hawaye ko qiris a idanunta, yana cikin dukan nata yayansa zayeed ya shigo gdn, wurin ya qarasa da sauri don shi kansa yasan zuciyar maheer idan har ransa ya 6aci zai iya aikata komai, jansa ya somayi yana qoqarin fizge belt d'in hannunsa shi kuma yana tirjewa, dakyar ya iya lalla6ashi ya shigar dashi cikin building d'insa yana cika yana batsewa yana kuma huci don ransa ya 6aci sosai gani yake bimbii bata chanchanci ta masa wannan taurin kan ba a matsayinta na qasqatacciyar baiwa kuma baqar fata shiyasa cikin zaqin dayake mata har yana ce mata gorilla family wai duk baqar fata dake africa daga family na gwagwggon biri suke she never deserve to behave like this cox she is nothing but gorilla family......zagi na uwa na uba hk ya dinga sauke mata kwando kwando yyi da larabci yyi da turanci, tun shigarsu ciki tana wurin bata motsa ba don batajin idan ta miqe tsaye k'afafunta zasu iya d'aukar gangar jikinta, sai lkcin taji saukar wasu hawaye masu d'umi a saman quncinta, kallon jikinta tayi taga yadda ya farfashe da duka sai kuma tayi murmushi wanda yafi kuka ciwo,zayeed ne ya fito ya kalleta shima cike yake da fushi amma yana kallonta ya fahimci bata da lafiya shima dai ba wani daraja bayi baqar fata ke dashi a idanunsa ba amma dai yaji tausayinta kad'an, samo mata magani yyi ya bata ta amsa da godiya shiko batare daya saurari abunda take fad'i ba ya fice daga gdn yyi tafiyarsa, maheer kuwa ranar bak'in ciki kamar ya kasheshi hk ya kwana cike da qunci, washegari kuwa ya fito da sanyin safiya yaga ko batayi aikin nata ba don qiris yake jira da ita ya mata dukan da zata kusa ziyartar lahira sai kuma yyi rashi sa'a don ta gama kowanne da cikin aikin nata duk da rashi jin dad'in jikinta da take amma ba kamar jiya ba don maganin da tasha yyi mata amfani yau taji dama dama ba kamar jiya shiyasa tun safe ta lalla6a ta gama komai ta koma gindin bishiyar guiwa ta zauna, cike da haushi ya koma ciki ya kwanta akan doguwar kujerar dake qaramin parlourn nasa yana fitar da hayaqin sigarin dayake busawa,hoton bimbii ne ke dawo masa lkcin dayake dukanta, idanunta qamas suke babu alamun kuka, zumbur yyi ya miqe ya kuma fita ya tsaya a barandar dake gaban building d'insa yana hangota zaune a gindin bishiyar guiba tana tsefe kalbar dake kanta tana sake kitsa wata,ita kuwa batasan ma ya fito ba tana tsifanta tana rera waqar da take idan ta fita kiwo cikin harshenta na fillanci,juyawa yyi ya koma ciki ya shiga kitchen d'insa ya soma preparing breakfast a cikin kowanne tunaninsa bimbii ce ke fad'o masa ya ayyana mugunta daya dace ya mata,yana gama girkinsa ya zuba a wani plate ya fito wajen inda yake ajiye mata abinci ya juye mata, ita kuwa bimbii daman tun jiya babu abunda taci kuma yanzun ma bakinta babu dandano ko kadan bama ta sha'awar cin komai sai koko da qosai wannan kuwa tasan samunsa wurinta saidai ko a mafarki amma ba'a gaske ba, bata ta6a sanya ran ze zuba mata abinci ganin yadda suka kwashe dashi jiya kawai tana biyowa ta wurin taga ya zuba mata abinci, wucewa tayi bata d'auki abinci ba, shi kuwa duk bayan sakan guda sai ya leqo yaga ko ta dauki abincin daya zuba mata, hk kawai ya samu kansa da son yaga taci abincin amma har dare ya fito yadda ya zuba abinci hk ze gansa, shiru yyi yana tunanin ko fushi tayi sbd abunda ya mata jiya don ya fahimci kamar tana da zucciya, ita kuwa bimbii ta mance ma da batun abinci kawai lalla6a jikinta take don batason ta kuma kwantawa rashin lfy sbd gudun wulaqancin maheer, qunci da tsantsar bauta duk sun sauya bimbii ta koma wata irin miskila bata da fara'a kullum fuskarta a tsuke babu annuri ko kad'an, duk sanda maheer ya fito ze tarar tayi aikinta ta koma gindin bishiya, yauma yana fitowa ya tarar ta gama aikinta, kiranta yyi ta taso tazo juyawa yyi ya shiga cikin building d'insa ita kuwa ta tsaya a inda take don tasan bata da damar shiga wurin, juyowa yyi yaga tana tsaye bata biyoshi ba, saida ya kuma kiranta sannan ta biyo bayansa ta shigo ciki gabanta yana tsananta fad'uwa don batasan me ze mata ba ya kirata cikin wurinsa, parlourn nasa qarami ne amma yana da kyau sosai kuma ya wadatu da kayan more rayuwa, kitchen d'insa babu abunda babu na kayan amfani, kallonta yyi ya soma nuna mata wasu ayyuka da zata din ga masa cikin building din nasa ciki har da girki, itako bimbii binsa kawai take da kallo cike da mamaki toh yaushe ya sauya ra'ayi har ya amince mata ta din ga ta6a abunda zeci har ma da yarje mata ta din ga shigowa bangarensa tana masa 2aikace,tsawan daya mata ne yasa ta dawo cikin hnklinta, saidai itakam bata iya girki irin nasu ba toh me yakeson ta dafa masa ko irin abincinmu na gargajiyar baqar fata, dayake yanzu tana jin larabci sama sama don Allah ya mata kwakwalwa mai kyau da kaifin basirah,cikin harshen nasa ta masa mgn tace"nikam ban iya girki irin naku ba sai irin namu na baqar fata idan kana so kuma sai na mk" harararta yyi ya wuce yabarta a wurin tare da kora mata warning cewa duk aikin daya yanka mata ta tabbatar bata gocewa kowanne ba, washegari tana gama aikin furanni da baiwa kifi abinci ta nufi wurin building nasa, danna masa alarm tayi saida aka dan jima yazo ya bud'e kofar sanye yake cikin kayan bacci da alamu alarm din data danna ne ya tashe shi daga bacci, bece mata komai ba ya matsa gefe ya bata hanya ta shiga, komar da k'ofar yyi ya rufe ya koma bedroom d'insa ya kwanta, ita kuwa ta shiga kitchen d'in nasa ta soma wanke masa kwanuka,gani tayi wasu abubuwan ma dake kitchen din duk sunyi qura, hk ta wanke komai ta fitar da abubuwan da suka lalace a fridge ta gyara komai ta goge floor din yyi tas, tuni wuri yadau haske da annuri, fitowa parlourn tayi ta goge electronics d'in dake parlourn ta kad'e kujeru ta gyarasu sannan ta share ko'ina ta goge, ba tayi gigin girka masa komai ba don itakam bata iya irin girkinsu, har ta gama aikin nata maheer yana baccinsa baida niyyar tashi, bud'e kofa tayi ta fice tunda ta gama aiki nata ta koma gindin bishiyar guiba inda ta saba zama, tunda ta shigo gdn maheer bata ta6a leqa koda k'ofar waje ba kullum tana ciki tana aikatuwa, tana wurin a zaune taga shigowar wata mota qirar mercedez ta shigo farfajiyar gdn, wasu samari ne su wajen biyar dukkaninsu larabawa ne amma suna sanye ne cikin qananan kaya, wurin building maheer suka nufa, shi kuwa tashinsa kenan ya fito parlourn nasa, tsayawa yyi kawai yana bin ko'ina da kallo tamkar ba parlourn nasa ba ganin yadda floor din ke kyalli da d'aukar idanu ga komai a shirye tsaf, shelves na littattafansa a gyare tsaf duk ta kad'e qurar wurin, yana shiga kitchen ya kuma yin turus sbd komai na kitchen tamkar an maidashi sabo hattar oven d'in dake manne da gas d'in girkinsa cikinsa sai sheqi yake, tunda yake masu aikin dake kula da building d'insa be ta6a samun wanda yyi masa wannan aiki mai kyau hk ba, murmushi yyi kawai be damu ba duk da yaga dinning din dake kitchen babu komai wato bata girka masa komai ba amma shi aikin nata kawai ya birgeshi don shi a rayuwarsa yana son tsafta, alarm din dayaji ana danna masa ne yasa ya fito daga kitchen ya nufi wurin k'ofa ya bud'e, friends dinsa ya gani, dariya yyi ya basu hanya suka shigo, duk suka kame akan kujerun dake parlourn shi kuwa ya shiga kitchen ya soma qoqarin had'a musu tea, su kuwa suna parlourn sun kunna waqar Ali bin wasid suna chashewa da ita abinsu,fitowa yyi ya fita, tsayawa yyi a baranda ya kira bimbii dake gindin bishiya, tahowa tayi tazo wurin tana kallonsa, juyawa yyi tabi bayansa, tana shigowa duk suka bita da kallo suna kallon maheer, daya daga cikinsu yace" mah a ina ka samo mai aiki baqar fata kana nufin ita take maka abinci,God forbid" bimbii tana tsaye daga gefensa, murmushi yyi ya kalle friends din nasa yyi yace" oh guys calm down, she is just my cleaner" d'ayan kuwa yana hakimce a kujera tunda suka fara mgn be furta komai ba kawai bin bimbii yake da kallo tun daga sama har qasa,tsayar da idanunsa yyi kan k'ugunta wanda sai mutum ya mugun qura mata idanu ze gano girmansa don doguwar zumbulin rigar dake sanye jikinta ta taimaka wurin asirtashi, sake dire idanunsa yyi kan na shanunta dake tsaye dodar sukam tsinin tsayuwarsu ya fito ta rigar kuma data taka kad'an suke girgixa don ba bra a jikinta, masu yanci suke da arziqin sanya bra,murmushi yyi kawai tare da lumshe idanu ya komar da kansa ya kwantar jikin kujera yasa hannu yana shafa kwantaccen sajen dake gefen fuskarsa,maheer kuwa kallon bimbii yyi yace ta biyoshi kitchen, bin bayansa tayi tana shiga ta tsaya a gefe shi kuma ya soma had'a breafast, duk abunda yake tana kallonsa.......
Littafin nan na siyarwa ne ki siya kiyi karatunki cikin yanci,idan kin shirya siye saiki tura naira#300 ta wannan acct no.0100790419,Alhaji shahida nasir,union bank, saiki turomin da screenshrt na payment dinki ta whatsapp 07041195806, idan kina buqatar wani bayanin kuma saiki kira wannan layin 08080611486
Alkalamin Bintuu ne....
10/10/20, 1:12 AM - Anti qamshi🌷: *DAREN GOMA SHA HUD'U*🪔🪔
Written By Bintuu Seer
4
Bayan ya gama komai akan idonta yace ta tafi, fitowa tayi daga kitchen d'in ta fito parlourn da niyyar fita, daya daga cikin friends nasa dake parlourn mai suna farid yasa hannu ya damqo hannunta yana murmushin qetai, qoqarin fixgewa take ta kasa maheer ya fito da cups na green tea a hannunsa, tsayawa yyi yana kallon farid da mamaki yace" ta maka wani abun ne koh" yace" No, but u said she is ur cleaner so i want her to clean my body" gbdy sauran abokan nasa suka bushe da dariya, shi kuwa farid murmushi kawai yyi, wani cikinsu mai suna jalil ya kalli farid yace" clean ur body as how,just make it clear" dariya yyi ya miqe ya soma 6alle ma6allan rigarsa ya cireta daga jikinsa ya kalli maheer yace" kace mata ina son tayimin wanka" maheer jin abun yyi wani banbarakwai ya kalleshi yace"wanka?" yace"yes,ko ba baiwa bace?" murmushi maheer yyi ya kalli 6angaren da bimbii ke tsaye don farid yyi blocking hanyar fitar, duk sauran abokan nasa suna daga zaune suna jiran maheer ya bawa bimbii umarnin yiwa farid wanka, shi kuma gashi baya son abokan nasa suyi zaton ko yana siding din bimbii ne don hk ya kalleta fuska a tamke yace" kije ki yiwa abokina wanka" kwalalo idanu waje tayi ta soma ja da baya tace" wanka zan yiwa wannan qatoton billah ban iya yiwa babba wanka ba" mgnr duk tana yine cikin harshenta na fillanci don bata gama kwarewa da larabcin ba, basu jin yaren nata amma yanayin yadda tayi ya tabbatar musu da gardama take baza tayi masa wankan ba, miqewa maheer yyi ya nufo inda take yace" yauma gardama zakiyimin" su kuwa sauran duk suna daga zaune suna dariyar qeta tare da qara zuga maheer wai lalle yyi sake baiwarsa bata bin umarninsa, kafin su ankara bimbii ta bud'e k'ofa ta fice da gudu, binta yyi da niyyar sakar mata kare ita kuwa Allah ya bata sa'a ta fice daga gdn gbdy, yana ganinta ta fita ya bita da gudu, ita kuwa tana fita ta miqe hanya tana ta gudu don wlh tsoro taji sosai gani take idan ta tsaya zasu iya keta mata rigar mutunci tunda har abun yakai ga hk, shi kuwa maheer gani yyi har ta masa nisa, komawa yyi gd ya kira masu tsaron hanyar data nufa kansu dakatar da ita baiwa ce take neman gudu, su kuwa sukace mata basu ganta ba, rikicewa yyi sosai lkcin da suka sanar dashi basu ganta ba, fita yyi da kansa yana ta zagayen neman bimbii amma ko mai kama da ita be gani ba, ita kuwa bimbii ba sanin gari tayi ba,tana cikin gudun tayi wata hanya data nufi outcast wato wajen gari,tsayawa tayi tana kalle kalle taga tabbas wurin da take wajen gari ne don ba mutane sosai, tana cikin waige waige ta jiyo qarar takun dawakai tana juyawa taga wasu mahaya dokuna ne su shida suna gwada tseren sukuwa sun nufo inda take gadan gadan tamkar basu ganin komai a gabansu, mugun firgita tayi ta soma qoqarin juyawa da gudu aikuwa tuni sun cimma inda take kafin kace kwabo daya daga cikinsu ya gwabjeta da gefen dokinsa, duk sukayi wucewarsu batare da sun tsaya ganin halin da take ciki ba don faduwa tayi a wurin, daga bayansu ashe akwai wasu dakarun mahaya dawakan dake take musu baya, shugaban wannan dakarun ne ya tsaya ya bada umarni a dauki bimbii dake kwance tamkar bata numfashi,su kuwa wadannan shidan da suka soma wucewa ya'yan sarakuna ne dake taqama da izzar jinin sarauta don kowannesu ya fito ne daga sananniyar masarauta me fada aji cikin daular larabawa, wannan wuri kuma filin tseren sukuwar dokunansu ne da suke fitowa duk qarshen mako don nishad'intar da kansu, hadimansu kuma na take musu baya tare da al'qalan dake fitar da gwanin daya cinye tseren cikinsu, suna isa madakata suka ja tunkan dawakansu suka tsaya, PRINCE AKBAR....shine ya samu nasarar cinye wasan tseren sukuwar dokin, sakkowa yyi da fuskarsa da babu yabo babu fallasa daga kan dokinsa, hadiminsa na hannun damansa ubaid ya kama masa dokinsa, sanye yake da wasu fararen kaya tamkar pakistan kansa sanye da rawani baki da fari, fari ne sol kallo daya zaka masa kasan cikakken balarabe, sajen daya zagaye fuskarsa baki ne ya taimaka wurin tona asirin kyan d'an sarkin,yanayin tafiyarsa da kallonsa kawai zai haska cikakkakiyar izzarsa, haqoransa a jere suke farare tas dasu duk wata halitta dake jikinsa fara ce idan ka cire gashin dake jikinsa da kuma kansa,gashin kansa dogo ne tamkar na mata har rawa yake idan ba rawani akansa,PRINCE AKBAR shi ya buge bimbii ta bashi haushi sosai daya ganta a hanyar sukuwar tseransu, ubaid ne ya matso kusa dashi yace" Your highness wannan alamunta ya nuna baiwa ce dake neman gudu" kallo d'aya yyiwa keken dokin da suka dauko bimbii yace" ku kaita cikin yan'uwanta bayi" abunda yace kenan ya wuce abinsa ya sake hawa dokinsa suka dau hanyar komawa gdn sarautar burham dake tsakiyar babban birnin kuwait........
*Masarautar Burham*🔱🔱
Ginin gdn sarautar burham shi kansa abun kallo ne don gini ne da kwararrun magina suka tsarashi cike da basira, gdn gari guda ne dauke da 6angarori daban daban tare da lambuka na shaqatawa da qoramai wanda ruwansu ke kwaranya, masarautar burham tsohuwar masarauta ce a qasar kuwait mai kafaffen tarihi, akwai arziki da tarin izzah ga jinin sarautar burham, sarki abdallah bin jabal shine mahaifi ga PRINCE AKBAR kuma shine riqe da sarautar wannan daular masarautar burham, sarki abdallah bin jabar mutum ne mai tsatstsauran ra'ayi irinna larabawan farko ga taurin kan bala'i shiyasa har yau suke kan tsoffi al'adunsu a wannan masarauta, suna da tarin bayi da hadimai,rukunin bayin dake wannan gdn sarauta ya kasu kashi uku kuma dukkaninsu da alamominsu, bayin farko sune na qasa qasa masu kula da share share da gyare gyare da yiwa dawakai wanka, sai na biyu masu kula da bangarorin iyalan wannan gd, kaso na uku kuma sune masu kula da lfy da kuma abincin iyalan wannan gd tare da tsaftace komai nasu, prince akbar shine daya d'a ga sarki abdallah bin jabal sai kuma ya'yan wasu sarakunan dake qasan masarautarsu da suka taso cikin wannan gdn sarauta kuma kowanne cikinsu da 6angarensa da hadimansa tare da gayyar bayi, 6angaren prince akbar yafi kowanne 6angare girma da fad'i, akwai bayi na musamman dake hidimtawa 6angaren nasa sai hadiminsa na hannun damansa ubaid, ubaid yafi kowa sanin halin prince akbar kuma yana mutuqar masa biyayya baya sa6awa umarninsa, gdn sarautar burham sun dau bayi tamkar ba rayuka ba don laifi qanqani bawa ze aikata sarki abdallah ya zartar da hukuncin kisa akansa shiyasa bayin gdn kowa yake taka tsantsan da kaffa kaffa, idan har baka daya daga cikin bayin dake hidimtawa 6angaren sarki ko sarauniyya ko ya'yan sarki to kuwa baka isa ka shiga 6angarensu ba, kowanne rukuni na bayi akwai wanda ke shugabantarsu, idan aka kawo sabbin bayi akwai wacce ke nuna musu ayyukansu suna kiranta ummul shukri, bata da wasa ko kadan gashi ta iya horar da bayi yadda ya kamata a hannunta ubaid ya damqa bimbii,akwai doka sosai a wannan gdn sarauta, kafin a za6i bayi su hidimtawa sarauniyya ko sarki ko ya'yan sarki sai an tabbar da asalin bayin da kuma himmarsu, bayi marasa asali yawancinsu basu aiki a bangaren iyalan gdn suna aiki ne kawai a cikin gdn sarautar,fadar sarki abdallah bin jabal an ginata ne da danyen gwal kowacce kusurwa a fadar daukar ido yake, tsarin wannan gd shine bawa ya tsaya iyakar matsayinsa idan kuwa ya nemi ya qetare kai tsaye hukunci mai tsauri ze hau kansa, kafin su dauki bawa ya soma aiki a wannan masarauta sai ummul shukri ta gwadasu ta kowacce siga shiyasa suke kiranta uwar bayi.........
10/10/20, 1:12 AM - Anti qamshi🌷: *DAREN GOMA SHA HUD'U*🪔🪔
Written By Bintuu Seer
5
*Love is the unsoluble equation to a great mathematician and also a heavy weapon to hold for a great legends and heroes*......🔱🔱
Tana farfad'owa ta ganta kwance bisa busassun ciyayi a yashe tsakiya wani d'aki mai yalwar teburan katako da tsoffin kwabobi, gefenta wasu y'an mata ne su uku kyawawa dasu jinsin larabawa saidai alamu sun nuna tamkar suma suna da tambarin bauta tattare dasu, suna ganin ta farfado suka matso kusa da ita suna mata sannu cikin harshensu na larabci, dayake tana d'an fuskantar larabcin 2kadan sai ta d'aga musu kai kawai ita dai sai qarewa d'akin kallo take tana tunanin yau kuma ina Allah ya jefota, hannun suwa kuma ta fado, d'ayar da taji suna kira da khulood ta miqe ta fita da sauri ba jimawa sai gata sun shigo da wata tsohuwar balarabiyya, tana tafe tana dogara sandarta, doguwar riga ce ruwa k'wai a jikinta ta yane kanta da mayafi amma hkn be hana gashin kanta dayake fari fat da furfura leqowa ba,wuyanta da wata katuwar sarqa,kunnuwanta kuma da wasu manya yan kunne sai yatsun hannunta kusan dukka da manya zobuna na azurfa, fuskarta a tamke ba alamun fara'a tana shigowa sauran y'an matan bayin nan suka rissinar da dakansu qasa alamar girmamawa ga uwar bayi ummul shukri, bimbii kuwa kallon tsohuwar kawai take,itako uwar bayi ummul shukri sandarta ta sanya ta d'ago da ha6ar bimbii tana qarewa fuskarta kallo musamman cikin idanunta don mafi yawan larabawa suna karantar sirri zucciyar mutum ne ta cikin k'wayar idaniyansa shiyasa uwar bayi ummul shukri ta qure bimbii da idanu tana karantar sirrin zucciyarta ta k'wayar idanunta, bimbii kuwa sai tayi sauri yin qasa da idanunta kamar yadda taga sauran yan matan bayin sun mata, tana ganin bimbii ta rissinar da idanunta qasa sai tayi wani d'an murmushi na gefen baki ta d'auke sandarta daga ha6arta ta kalli khulood tace" ki bata abinci" tana fadar hk ta dogara sandarta ta fice daga dakin bayin,khulood ta tashi da sauri ta fita don kawowa bimbii abinci itama israt ta tashi ta kawo mata ruwan sha cikin wani kofin tasa daidai lkcin khulood itama ta shigo da wani qaramin kwanon tasa da abinci a ciki,duk suka sanya mata a gaba, bimbii kuwa daman da yunwa ta tashi don hk batare da wani kunya ba ta wanke hannunta da ruwan da suka kawo mata, ta soma cin abincin duk da a ido ta raina yawan abinci suna kallonta ta gama cin abinci tasha ruwa tayi hamdala,khulood ta kalleta da murmushi tace ta tashi su fita ummul shukri na son ganinsu, ba musu ta miqe tabi bayansu suka dinga wuce kusurwowi har suka shiga kusurwar da ummul shukri take, zaune take bisa kujera tana riqe da sandarta suka durqusar da guiwowinsu dukka a gabanta tare da rissinar da kawunansu qasa suna jiran umarninta, itama yadda taga sunyi hk tayi, ummul shukri ta kalle bimbii ta soma mata mgn cikin harshen larabci tace" kin san inda kk yanzu?" girgixa kai bimbii tayi alamar aa, tace" kina gdn sarautar burham,kina cikin jerin maqasqatan bayin masarautar burham"nuna mata su khulood tayi da hannu tace"rukunin aiki iri d'aya zasu nuna miki naki aiki ciki" rissinar dakanta tayi alamar ta amsa yadda dai taga sunayi, sallamarsu tayi suka miqe suka fice, bimbii sai bin wannan gdn sarauta take da kallo don tsarin ginin masarautar ya birgeta sosai, gani tayi bayin gdn sai kai kawo suke,matan kusan dukkaninsu da mayafi a saman kansu,mazan kuma yawancinsu da rawani a kansu,ko'ina na gdn zagaye yake da furanni masu kwantar da zucciya, gdn kusurwa kusurwa ne, kowacce kusurwa an mata yanayi kamar kofar masallaci sanda sanda, israt da khulood na gaba, laila da bimbii na biye dasu,fita sukayi daga wannan 6angaren suka wuce wani wuri suka dauki kwanduna, lailah ta dauki kwando daya ta bawa bimbii ta amsa ta riqe suka sake ficewa daga wannan 6angaren sai tfy suke har suka fara fita daga inda gine gine suke suka soma shiga jeji jeji kuma fa duk a cikin gdn suke, bimbii dai sai binsu take, wani lambu mai cike da bishiyoyi na kayan marmari suka shiga, khulood ta hau bishiyar zaitun, israt tahau bishiyar tuffa suna tsinkowa suna jefo musu su kuma suna tattarawa suna zubawa a kwandunansu, saida suka cika kowanne kwando sannan su khulood da israt suka sakko kowacce ta dauki kwandonta ta dora a saman kanta suka fice daga lambun suka nufi cikin gd, suna cikin tfy wasu samari suma bayi ne suka tare musu hanya,abunda ya baiwa bimbii mamaki shine ashe kowacce cikinsu tana tafe da qaramar wuqarta a cikin jikinta sai gani tayi duk sun sauke kwandunansu sun sanya hannu cikin fatarinsu sun fito da qananan wuqaqensu sun tsatstsaya suna sauraron su ga me zasuyi musu su soma yankarsu, bimbii kuwa ta qame a tsaye da kwandonta a saman kanta cike da mamaki, su kuwa suna ganin yan matan sun fito da wuqa sai suka wuce abinsu saida suka ga sunyi nisa suka maida wuqaqensu cikin jikinsu suka sunkuya suka dau kwandunansu suka cigaba da tfy,su mazan larabawan wannan yankin Allah ya zuba musu son jikin mace ba wuya suke yiwa yan mata fyade shiyasa yan matansu ke yawo da wuqa sbd tsaro, bimbii dai tana ganin abun mamaki cikin wannan gd sbd ita daman tunda ta shigo qasar kuwait tana qunshe ne a wuri daya batasan al'adunsu ba sai yanzu da Allah ya jefota gdn sarautar burham, wani qaton kitchen suka shiga, kitchen bayi ne ciki keta hidima, shugabar bayin dake wannan babban kitchen din mai suna jahan ita ta amshi kwandunan nasu ta jujjuye kayan marmarin a cikin wasu manyan kwanduna dake kitchen din ta basu kwandunansu, duk bayin dake hidima cikin kitchen din sai bin bimbii suke da kallo tamkar sun ga wata sabuwar halitta,lallah ce taja hannun bimbii suka fice daga kitchen din,maida kwandunan sukayi suka koma wani 6angaren suka fito da wasu manyan barguna suka nufi wata qatuwar qorama dake dake tsakiyar gdn suka dauko wasu manyan abubuwan wanki da akayisu da katako suka soma dirzar wankin wannan manyar barguna sai yamma liqis suka kammala ayyukansu suka koma 6angarensu,su hud'u ne a dakin nasu,khulood,lailah, israt sai yanzu da aka kawo musu bimbii, dukkaninsu akan wannan busassun ciyayin suke kwana tamkar shine suka maida katifarsu saidai su shimfida mayafansu akan ciyayin su kwanta, ita bimbii ranar kam bacci tayi mai dadi don kuwa gani take ta samu cigaba tunda har ta samu damar kwanciya cikin daki ba'a rumfa ba kuma har ta samu albarkar kwanciya a ciyawa ba'a dandamalin k'asa ba wannan kadai cigaba ne a wurinta bata damu da tiqar aikin da suke ba don daman tasan ta ita baiwa ce kuma tana cikin qangin bauta,kwanan farin ciki tayi ga qawaye ta samu da basu nuna mata zangwama ko kadan sun dau kansu tamkar yan'uwa hk suke rayuwarsu tamkar jini daya kuma kusan dukkaninsu sun fito ne daga qasashe mabambanta saidai su duk daga qasashen larabawa suke masu makwabtaka da qasar kuwait ita kadai ce baqar fata daga africa, washegari da sanyin safiya duk suka tashi, tunkan su fita ummul shukri ta shigo ta kama tsintsiyar qafar bimbii ta sanya mata wata qaramar sarka irin wacce wasu matan ke sanyawa a qafa sbd ado su kuma wannan sarqar qafan itace alamar dake nuni da rukunin bayin da suke shiyasa taga suma su khulood kowacce da wannan sarqar a qafarta ita da ta dauka sbd ado suka sanya ashe shine tambarin rukunin bayin da suke,kallon qafar tayi taga sarqar ta mata kyau, miqewa tayi suka fice, ranar kwaryoyi suka dauka suka tafi tatsar nonon raqumi,kowacce saida ta cika kwaryarta da nonon sannan suka dauko suka taho kai tsaye wannan babban kitchen suka kai nonon aka juye a charkoki, daga nan suka wuce kowacce ta dauki tulunta suka tafi babbar qorama don debo ruwa, saida suka ciccika duk wasu abubuwan tara ruwa na 6angarori 2daban sai yamma liqis ranar ma suka koma 6angarensu, bayan sun gama cin abinci suna shirin kwanciya lailah ta fito da wata sabuwar wuqa yar qarama ta miqawa bimbii tace" ki riqe wannan kema sbd akwai hadari ki din ga yawo babu abun kare kai kin ga kema budurwa ce saiki sanya budurcinki cikin hadari" amsar wuqar bimbii tayi mata gdy sannan ta sanya wuqar qasan wurin kwananta......
***
6angaren maheer kuwa tunda bimbii ta gudu ya rasa kansa,shi kansa ya rasa abunda ke damunsa tun yana qoqarin 6oye damuwarsa har mutane suka soma fahimta, yau tun safe yana tsaye a barandar dake gaban building dinsa ya qurawa gindin bishiyar guiban da bimbii ke zama lkcin tana gdn,gani yake tamkar ze ganta zaune, har yayansa zayeed ya shigo gdn be sani yyi nisa cikin tunani saida ya dafashi tukun ya ankara da shigowarshi, zayeed kallo daya yyi masa yasan akwai abunda ke damunsa,ya lura da maheer tun sa'adda baiwarsa ta 6ace ya shiga damuwa ya kasa dawowa daidai har yanzu, dafa kafadarsa yyi ya soma masa mgn cikin taushin murya yace" maheer are you in love with that african lady" saurin dago dakai maheer yyi yana kallon yayan nasa da mamaki a shimfide a fuskarsa yace" what are you saying?" murmushi zayeed yyi yace" if not,why are worrying about her disappeared" kallonsa maheer yyi yace" cox she my slave" dariya zayeed yyi sai kuma yace" ok, i will bring another slave for you" haushi mgnr ta bashi ya tashi daga wurin ya shige cikin building nasa ransa a 6ace, zayeed kuwa bai bishi don yasanshi da shegiyar zuciyar tsiya ya cigaba da wasa da kare,maheer kuwa yana shiga ya kwanta a couch din dake parlourn nasa ya rufe idanunsa yana hango lkcin da bimbii ta 6acewa ganinsa bai ta6a zaton be zata dawo ba don shi la'akari yake ai bata da inda zataje dole ma ta dawo wurinsa saida yaga yau kusan kwana uku kenan ba bimbii ba alamun dawowarta, zuciyarsa tana tsananta bugawa idan yana tunani bimbii,gashi shi ko sunanta ma be sani ba, idan ya tashi baida aiki sai tunanin bimbii,tunda bimbii ta gudu bacci yake gagarar idanunsa,yauma dare yyi sosai ya fito ya tafi cikin rumfar gezevon da bimbii ke kwana ciki ya zauna ciki ya qurawa sama idanu yana kallon hasken farin wata tare da taurarin dake sararin samaniyya,a hnkli ya furta 'I lost my star,pls my black african lady come back to me" sai ga maheer uban marasa mutunci yana kuka da hawayensa,be ta6a sanin ashe son bimbii ya illata masa zuciya ba saida ta gudu tabarshi, dora kansa yyi akan cinyoyinsa yana kuka har sauti, ruwa aka soma kamar da bakin k'warya amma maheer na cikin wannan rumfar yana kuka da hawayensa, ji yake ya tsani friends din nan nasa da suka zama silar gudun bimbii shi kansa ji yake ya tsani kansa idan ya tuno rashin mutuncin daya din ga shukawa bimbii,sai yanzu ya fahimci lalle kowanne mutum yana da baiwa, wani baiwarsa a 6oye take Allah kadai shi yasan irin baiwar daya axirta kowanne bawa nashi dashi, duk irin yanayin da muka ga mutum karmu rainashi wataqila warakarmu tana tattare dashi,maheer ranar a rumfar ya kwana yadda ruwa ke jiqa bimbii hk ruwan saman ya jiqash amma shi duk ba wannan ne damuwarshi,zaman wurin kadai ya sanya masa nutsuwa don gani yake kamar zega bimbii, washegari ya nufi wurin dayake sanya mata abinci yyi zaman dirshan gaban plate din yana cin abinci daya zuba mata don dukda yasan bata nan amma kullum ranar duniya baya fashin zuba abinci a wannan plate gani yake kamar ze dawo yaga anci abincin, cikin mako guda maheer ya gama zaucewa da soyayyar bimbii,wata irin zafaffiyar soyayya yake yiwa bimbii wacce ke wahalar da ruhi da gangar jikinsa, soyayyar dake sanyashi kuka duk dare duniya,hmm, alhaki ai kamar dan kwuikuyo yake, bibiya yake.....
Masha'Allah, anan na kawo qarshen free pages na wannan littafi duk mai buqatar cigaban wannan qasaitaccen labari sai ya biya naira #300 kacal ta wannan acct no.0100790419,Alhaji shahida nasir,union bank, sai turon da screenshrt ta wannan layi through whatsapp....07041195806 ga mai buqatar qarin bayani saiki nemi wannan layi....08080611486...
Alkalamin Bintuu ne....
10/10/20, 1:12 AM - Anti qamshi🌷: *DAREN GOMA SHA HU'DU*🪔🪔
Written By Bintuu Seer
6
*One Goodbye is enough to melt a heart* he missed her like crazy...💕
Washegeri da sanyi safiya suka tashi kamar yadda suka saba saidai yau ayyukansu yana dayawa sbd yau itace ranar zagayowar haihuwar PRINCE AKBAR... Princess hindu ita ta shirya qasaitaccen birthday partyn wanda ze gudana a lambun sarauniyya mar'atussaliha, bayi da barorin wannan gd na sarauta sai kai komo suke wajen shirya inda taron ze gudana, su bimbii kuwa su aikinsu a wannan wuri shine su rissina d'iyan saraki suna bi takansu tamkar sun sami gada sbd tsa6ar izzah da daukar bawa ba a bakin koman komai ba, dukkanin wadannan ya'yan sarakuna sun hallara shima kansa prince akbar ya iso cikin wata alkyabba golden da rawaninsa ruwan k'wai sai irqa baqi daya dora a saman kansa, princess hindu ita ta iso a qarshe cikin wani keken doki yasha ado, bayinta na biye da ita, dage keken dokin sukayi ta sakko, takan bayi itama ta wuce har ta isa wurin zamanta dake kusa da prince akbar, bimbii kawai baiwa idanunta abinci take tana 2kalle don taga wata al'ada ce ta daban, princess hindu idan mgnr tsantsar kyawu ake toh tabbas zata iya cin gasar sarauniyyar kyau don bayan izzar da take taqama dashi na jinin sarauta ga kuma na kyawu da cikar asali, tasha ado na kwala kwalai,wata doguwar rigace a jikinta irinta d'iyan saraki kalar sararin samaniyya, 2ciye suka soma da 2shaye suna raha da barkwanci a tsakaninsu jinin sarauta, prince akbar yana daga zaune fuskar nan tashi dai ba yabo ba fallasa, wata baiwa na hango tsaye a bayansa amma ita sanye take da kaya masu kyau tamkar ba baiwa ba, kallon israt bimbii tayi tace" waccar ta dake bayan prince wacce ita?" tace"itace lenah babbar baiwa a 6angaren prince akbar, ita ke kula da duk wani ci da shanshi da kula da wurin kwanciyarsa kai har ma ta tayashi kwana ta raya masa dare idan yana da buqatar hkn" jinjina kai bimbii tayi tana cin tuffan dake hannunta tana qara kallon lenah, tana da kyau itama ko hassadun iza hassada ze furta hkn, bimbii ta kuma kallon israt tace" kince har da tayashi kwana idan da buqatar hkn toh kuma ai ba matarsa bace" dariya lailah tayi don tana bayansu tana jin hirar tasu tace" su al'adarsu shine d'an sarki da sarkin shi kansa idan sun ga baiwa ta musu sukam maidata ta zama kwarkwararsu amma da kyakykyawan sharad'i kar baiwar ta yadda ta fad'a soyayyarsu bare har ki nuna feeling dinki garesu sannan kuma ba haihuwa tsakaninku dasu don basu hada jini da bayi, hukuncin kisa shi yake tabbata ga duk baiwar data qetare wannan sharad'i ko kuma daurin rai da rai har qarshen rayuwarta, mafi yawan bayi suna son su kasance a wannan matsayi sbd tamkar an y'antasu ne kuma duk abunda suke so zasu samu,zakici maikyau ki saka mai kyau ki fita ki tafi duk inda kkso sbd kina da y'anci, zakiji dadin rayuwa idan kk samu kanki a wannan matsayi saidai karki sake ki karya sharadin nan" jinjina kai bimbii tayi tace" yoo idan bakai kai ba meye hadin zomo da kura ai ramin kura sai y'ayanta,bawa ai sai ya tsaya iyakar matsayinsa" murmushi israt tayi tace" kin ga ni kuma wlh kullum addu'ata Allah yasa shekara mai zuwa idan na shiga gasa na samu" harararta khulood tayi tace" waye ya fada miki rukunin bayin da muke ciki suna samun damar shiga gasar, rukunin bayi na biyu dana uku suke da damar shiga wannan gasa" bimbii tace" au kafin ma ka samu matsayin kasance baiwar prince din sai anyi gasa" sukace mata" ehh mn, sai an gwadaku kafin a fitar, duk shekara yake sauya baiwa" bimbii tace"tirqashi!" fitowar wasu jerin yan matan bayi ne ya janye hnklinsu daga hirar da suke,yan matan su sha biyu ne suka fito don nishadintar da wurin da waqoqi, sanye suke da skirt mai baza ta qasa da wata qaramar riga iyaka cibiya,rawa suka fara tare da girgixa jikinsu sannan zabiyar cikinsu ta soma rera wak'a mai dadi, wurin yyi shiru kowa na sauraron baitocin dake fita cikin wannan wak'e nata, baitoci ne da suka shafi rabuwar masoya, baitocin nata sun samu ta6a zuciyar masoya dayawa dake wannan wuri, bimbii sunkuyar dakanta tayi tana murza wani zobe dake yatsanta na tsakiya tana kuka da hawaye don ta tuna ranar da lamid'o ya bata wannan zobe da kuma rabuwarsu dashi ta qarshe itace ranar da wad'annan turawa suka kamasu lkcin sun dawo daga tallan nono suna sauri su koma gd don magriba ta kawo jiki Allah ya hadasu da wadannan turawan akan hanyarsu ta komawa rugarsu suka kamesu suka sanyasu cikin mota, kullum tunaninta shine wanne halin innanta yadikko zata shiga silar 6acewarta,wanne hali baffi da lamid'o zasu shiga silar 6acewa, tabbas tasan rayuka dayawa suna cikin wani hali dalilin 6acewarta, kuka take sosai saida su khulood suka rumgumota suna bata hkr, idanun gimbiya hindu ne ya tsaya akansu lkcin suna rumgume da bimbii suna bata hkr, nunawa babbar baiwarta su tayi da idanunta tace"wadan can bayin dake bayan bishiya me suke" kallon wurin zulham tayi tace"ranki ya jima suna rarrashin yar uwarsu ne" tace"aikin da suka zo yi wurin nan kenan, basu san murnar zagayowar babban prince muke ba shine suka ware kansu daga cikin yan'uwansu bayi suka koma gefe, toh kije ki tahomin dasu nan gabana naji me suke tattaunawa" cikin sauri zulham ta nufo wurinsu tace" gimbiya na son ganinsu gabanta" dukkaninsu gaban ya fadi suna tunanin ko laifi sukayi, itako bimbii ko d'ar bataji ba tunda dai tasan babu abunda tayi, hk ta sakosu a gaba ta kawosu gaban gimbiya hindu duk suka durqusar da guiwowinsu gabanta tare da rissinar dakansu qasa, lkcin ne idanun kowa dake wurin yazo kansu har shima prince akbar ya kallesu sau daya ya dauke kansa ya cigaba da shan ruwan inibin dake gabansa, daya bayan daya gimbiya hindu ke binsu da kallo ta tsaida idanunta kan bimbii tana qare mata kallo, tace" kece kk janye hnklinsu daga kan aikinsu koh" shiru bimbii tayi su kuwa su khulood sai suka sake rissinar dakansu suka hada baki sukace" mun tuba ranki ya dade" kallonsu tayi ta yatsine fuska tace" su tashi su bata wuri amma bimbii kuwa ta tsaya saita musu rawa da wak'a na abunda yasata kuka" kallon zulham tayi tace" ta sanar da mai gabatarwa ya gabatar da bimbii a matsayin mai rawa ta gaba" aikuwa hk akayi, duk wurin bimbii suke kallo itako gabanta sai faduwa yake, bata iya waqar larabci ko guda ba sai na harshenta na fillaci, kama hannunta zulham tayi ta fice da ita suka shiga wani wuri ta sauya mata kaya ta saka mata rigar nan iya ci6i da skirt mai baza ta qasa ta taje mata gashin kanta ya sakko mata har duwawu gashi da cikowa kuma baqin qirin dashi, bimbii kallon kanta tayi ta kalli zulham tace" hk zan fita gaban mutane kuma ni ban iya wak'a cikin harshen larabci ba" tamkar tana mgn da dutse don zulham aikinta kawai take ba sauraronta ba, tana shiryata ta kamo hannunta suka fito lkcin yan matan dake wak'e sun bar wurin bimbii ake jira, idanun kowa nakan bimbii sbd yadda kayan nan dake jikinta ya fito da asirin dirin dake tattare da ita sannan suna mamakin tsawo da cikar gashinta kasancewarta baqar fata amma ta zarta dayansu tsawon gashi da tsantsar diri irinna mata, itako bimbii tsayawa tayi a wurin ta kasa komai sai kallonta suke suna jiran suji ta fara rero baitoci, a hnkli ta soma juya qugunta tana girgixa tamkar macijiya wata irin rawa take wacce take sabuwa a wurinsu, basu ta6a ganin salon rawan ba, cikin zazzaqar muryarta me amsa amo ta soma rero baitocinta cikin harshenta na fillanci tana juya qugu cikin wani salo rawa irin nasu na d'iyan fillo,rawar ce ta dauko hnklin kowa kanta, prince akbar dago da kansa yyi yana kallonta tashi daya yaji rawar da take da kuma wak'en da take cikin harshen nata ya sanyashi nishadi sosai har wani lumshe idanu yake, hk suma sauran yaran sarakunan dake wurin musamman prince nasaar daya qurawa bimbii idanu yana kallon zubin tsarin halittarta, kunsan dai san larabawa da mugun qulaficin jikin mace, gimbiya hindu kuwa gbdy haushin kanta tayi na kuskuren sanya bimbii rawa, kishi sosai taji tanayi data ga yadda rawar da bimbii take ta dauke hnklin ya'yan sarakunan dake wurin, miqewa tayi zumbur ta buga teburin dake gabanta cike da tsantsar masifa ta dakawa bimbii tsawa kan tabar wurin, duk ya'yan sarakunan suka jiyo suna kallonta prince nasaar yace" no, ta cigaba rawan nata ya birgemu" tace" wlh idan bimbii ta cigaba ita zata bar wurin" dage kafa bimbii tayi alamar ta gama rawan ta taho kanta a qasa ta soma qetarawa ta gaban prince akbar ta wuce shi kuma yana satar kallonta ta gefen ido sai wanda ya lura sosai ne ze fahimci ita yake kallo,ita kuwa bimbii shigewa tayi taje ta sauya kayan dake jikinta ta mayar da nata na asali, har aka gama taron gimbiya hindu tacewa baiwarta zulham kar ta sake tabar bimbii ta kuma dawo wurin taron, bimbii ta gama sauya kaya zulham tace" ki wuce ki koma 6angarenku karki kuma dawowa wurin taron nan" bimbii kuwa dadi taji don daman kunya takeji ta koma wurin,kai tsaye 6angarensu ta koma tana jiran dawowar su lailah, sai dab da magriba su lailah suka dawo suna shigowa duk suka taho da gudu suka rumgumeta, israt tace" gsky kin iya rawa zaki koyami nima" murmushi bimbii tayi kawai,ranar basu yi bacci da wuri ba sai faman jarraba yadda bimbii ke rawa suke ita kuma sai dariya take musu, israt tafi kowa zaqewa don ita a rayuwa tana son rawa da wak'a,bimbii na koya musu irin rawarta suma suna koya mata irin nasu hk suka 6ata darensu sun qi kwantawa da wuri duk da kasancewar gobe ayyukansu yana dayawa, aikuwa suna kwanciya bacci mai nauyi yyi gaba dasu, washegari ummul shukri taga dukkaninsu babu wacce ta fito kan aikinta, dogaro sandarta tayi ta shigo dakin nasu ta tarar dasu sai sharar bacci suke ba wacce ta tashi a cikinsu, juyawa tayi ta fice ba tashesu ba, suna tsaka da sharar baccinsu sukaji saukar ruwan sanyi a jikinsu gbdy an musu wanka dashi kafin su gama sanin abun yi sun soma jin saukar dorina a jikinsu, miqewa sukayi da mugun gudu suka fita, ita kuwa ummul shukri tana tsaye da dorina a hannunta ranta yyi mugun 6ace don batason sakaci da aiki.....
Littafin nan na kudi ne ki biya ki karanta cikin yanci ba satar faga ba, idan kin shirya siye ga transaction details nan, #300 ta wannan acct..0100790419,alhaji shahida nasir,union bank, saiki turomin da screenshrt na payment dinki ta whatsapp through wannan layin 07041195806, idan kuma da buqatar bayani ga layin kira nan 08080611486....
Alkalamin Bintuu ne...
10/10/20, 1:12 AM - Anti qamshi🌷: *DAREN GOMA SHA HUD'U*🪔🪔
Written By Bintuu Seer
7
*We are far apart from the thousand miles of journey only the destiny links us together*.......never,never leave me my luvv💕
Raba musu aiki ummul shukri tayi ranar kowacce tayi 6angaren da aikin nata yake,bimbii tsinko kayan marmari ne nata takai babban kitchen,israt da lailah kuma wanki ne nasu, khulood kuma tatso nonon raqumi, kowanne cikinsu yyi hanyarsa, bimbii zuwa tayi ta dauki kwando ta tafi lambu, tana shiga ta haye bishiya tana tsinko tuffa tana jefowa qasa tana yar waqarta cike da nishad'i, tana cillo na qarshe sai kawai gani tayi mutum ya chafe, prince nasaar ne fuskarsa dauke da murmushi yana kallonta, ita kuwa bimbii tsa6ar mamaki ne ya hanata sakkowa daga bishiyar saida ya mata alamar ta sakko da hannu sannan ta sakko,dole bimbii tayi mamakin ganinsa don ta karanci akwai izzah da cikakkiyar qasaita irinta sarauta ga jinin sarautar burham, tayi duba da yadda suka dauki bayi ba a bakin komai ba, idan har sunanka bawa kana dauke da tambarin bauta toh suna maka kallon qasqanci ne tare da nuna izzarsu akanka toh mamakinta shine me ya kawo wannan d'an sarki gareta, tashi guda tsoro da fargaba suka mata qawanya sai kallonshi take tamkar taga wani baqon mutum, tunawa tayi bata gaishe shi ba, saurin duqawa tayi akan guiwowinta tare da rissinar dakanta qasa yadda taga bayin wannan gida nayi, murmushinsa ya fad'ad'a ya tsuguna kusa da ita yana qarewa kyakykyawar fuskarta kallo, ita kuwa jikinta har rawa yake ta qosa tabar wurin, shima kansa ya fahimci hkn shiyasa ya miqe yace" me sunanki" cikin hard'ewar baki tace" bim...bii" yace" daga ina kk fito" tace" gombe" shikan besan ina ne gombe ba dama cewa tayi nigeria wataqila ya fahimci sunan qasa take nufi daga qasashen africa,murmushi yyi yace" koh na tayaki kwashe tuffan ne" saurin girgiza masa kai tayi jikinta na rawa ta soma tattara tuffan data tsinko tana zubawa cikin kwando tana gama ta soma qoqarin daukan kwandonta ta tafi, daukan kwandon yyi ya dora mata akanta yace" bimbii sai anjima" saurin kallonsa tayi tana mamakin jin yadda ya furta sunanta, sauri sauri take ta fice daga lambun shi kuwa yyi folding hannunsa a tsakiyar qirjinsa yana kallonta har ta fice daga lambu, sauri take tamkar zata kife tanayi tana waiwayen bayanta burinta kawai tabar wuraren lambun, ita batason ta shiga idanun wadannan y'an sarautan tana zaman zamanta lfy, kitchen ta wuce takai musu suka juye kayan marmarin suka bata kwandon ta mayar dashi ma'ajiyarsa sannan ta dauki tulu ta nufi qorama de6o ruwa, ranar hk ta yini da fargaba fal cikin ranta tana mamakin dogon zancen da wannan d'an sarki yyi mata, hk ta gama aikinta ta koma 6angarensu na bayi, tana shiga taga su israt ranar sun rigata dawowa, hannunta khulood ta kamo suka zauna dukkaninsu a qasa suka sanya abincinsu a tsakiya suna ci, bimbii gani tayi su uku ne kawai ba lailah ta kallesu tace" ina lailah take" khulood ta nuna ta masa wurin da lailah ke kwance tace" batajin dadi ne" saurin cire hannu bimbii tayi daga abincin ta nufi wurin da lailah ke kwance bisa busassun ciyayin da suka saba kwanciya ta dafata tace" lailah sannu koh" dagowa lailah tayi da kanta tana mata murmushin qarfin hali,hannunta tasa ta ta6a jikin laila tajishi zafi zau, miqewa tayi ta fita ta samu qaramin bowl ta ciko ruwan sanyi a ciki ta shigo dashi, mayafin kanta ta cire ta sakashi cikin ruwan tana matsewa tana sanya mata a jiki sbd jikin nata ya rage zafi, khulood da israt suma duk suka matso inda laila ke kwance, zazza6i ne sosai a jikin lailah, tashi d'aya kuma saita soma yunqurin amai ta fita ta dinga kwarara amai, khulood da israt suka fita da sauri don amsowa laila magani a dakin amsar magani, suna zuwa suka tarar k'ofar wurin a rufe sbd gsky dare yyi sosai, buga k'ofar suka dinga yi amma jahan yaqi bud'ewa don shine babban bawan dake kula da wurin maganin, hk suka gaji suka koma, bimbii na ganinsu ta taso da sauri tana tmbyrsu ko sun amso maganin, duk sukayi shiru tana ganin hk tasan basu amso ba, tace" sun kulle k'ofarsu koh" suka daga mata kai alamar ehh,duk sun zagaye lailah sunyi shiru suna kallonta tana numfashi a hnkli gumi sai keto mata yake,bimbii ta kallesu tace"toh yanzu meye abun yi" khulood tace" kawai muje mu haura katangar wurin mu sato maganin tunda na tabbata jahan na jinmu ya mana banxa sbd rashin imani" israt tace" hkma zamuyi" bimbii tace" toh kuma kar muje su kama mu" khulood tace" insha'Allah ba zasu kama mu ba, ta baya zamu duqa basa rufe kofar ciki a bud'e suke barinta" hk suka fito cikin wannan tsakiyar daren su uku suka soma la6a6awa cikin sand'a har suka qarasa gdn maganin,dayake sun saba da haura bishiya take suka haura katangar gdn magani suka soma tfy cikin sand'a, israt ce ta bud'e kofar a hnkli ta soma shiga bimbii na biye dasu, bincike suka somayi a wurin da magunguna ke jera har suka samo maganin zazza6i suka juya zasu fita, sai kawai jin muryar jahan sukayi yace" duk wanda ke cikin wurin nan ya tsaya karya fita" duk suka kalli juna cike da tsantsar tsoro, bimbii tayi saurin turasu waje tace" su suyi gaba zata biyo bayansu don tasan tabbas idan ya shigo be ga kowa ba kasancewar yaji motsin mutum a wurin ze ankarar da bayin dake tsaron wurin ne shiyasa ita ta tsaya tace su tafi, suna tfy suna waiwayen k'ofar suka sake haure katangar suka fice amma sai suka qi tfy suka tsaya jiran fitowar bimbii, bimbii kuwa tana ciki jahan ya bud'e kofar ya shigo, kallonta yake cike da mamaki yace" me ya kawoki nan wurin" tace" magani nazo amsarwa yar uwata tana fama da zafin zazza6i kuma nayi bugu ba'a bude ba" murmushin mugunta yace" shine kk shigo satar maganin, alamu sun nuna bakisan hukuncin sata a wannan masarautar bane koh" bimbii tace" toh kaimin aikin gafara" dariya yyi sosai yana qare mata kallo, yace" zan miki aikin gafara amma da kyakykyawan sharadi,kin amince" tace"fadi sharadin naka naji" dariya yyi a karo na biyu ya soma kusanto inda take ita kuma tana matsawa har ya cimma mata yace" sharadin nawa shine ki aminta dani wannan daren ki de6emin kewa" hannunsa yakai saman qirjinta, saurin buge masa hannu tayi tace" idan wannan ne sharadin naka toh bana buqatar gafararka gareni" dariyar mugunta yyi yana tauna asuwakin dake hannunsa, kallon qafarta yyi yaga sarqar kafan nan ya gane rukunin bayin da take, nuna mata kofar fita yyi yace" ga hanya nan zaki iya tafiya" a hnkli ta soma takawa tana kallonsa shi kuma yana mata dariyar qeta har ta fice ta haura ta katangar da suka hawo ta dire, ga mamakin sai ganin su khulood tayi a raku6e suna jiran fitowarta suna ganinta suka rumgumeta suna tmbyrta abunda ya faru, tace" babu komai,muyi saurin barin wurin nan kar wasu su ganmu" hk suka din ga la6a6awa suka koma 6angarensu, suka tarar da lailah sai murqususu take sbd zafin ciwo, cikin sauri suka hada maganin suka bata tasha, gumi sai keto mata yake a hk ta samu bacci, kallon bimbii khulood tayi tace"ki fada mn abunda ya faru a gdn magani, jahan ya ganki ne" daga mata kai tayi tana neman basar da zancen amma suka matsa dole ta sanar dasu yadda suka qare da jahan din, shiru taga sunyi tace" qalau dinku kuwa" israt tace" bimbii jahan mugun mutum ne besan arxiki ba cikin rayuwarsa tunda kkyi hk dashi toh wlh da abunda ze biyo baya gobe sbd basu daukan irin hk da sauqi cikin wannan masarautar" bimbii tayi murmushi tace" karku damu da wannan kudai ko mene ma ya biyo baya karku sake ku sanya kanku ciki" khulood tace" abunda bazai yuwu ba kenan, tunda har tare muka shiga toh koma meye ya biyo baya tare zamu tareshi" girgixa musu kai bimbii tayi tace" idan mukayi hk toh zamu 6ata biyu ne daya be kyaru ba, kun ga muna da mara lfy wa kk tsammanin ze kula da ita idan dukkaninmu muka tafi amsar hukunci, karku damu kudai kuyi yadda nace abun zezo mana da sauqi" shiru sukayi basu furta komai ba har suka kwanta bacci zuciyoyinsu cike da tunanin qarfin hali da tsantsar jarumta irinna bimbii, washegari da sanyi safiyya suka tashi, laila ma tadan ji dadin jikin nata, suna shirin fita kenan ummul shukri ta shigo 6angaren nasu ranta a mutuqar 6ace tana zuwa ta kalli bimbii tace" ke ki fita farfajiya ki amshi hukuncinki na shiga sata gdn magani" bimbii ta miqe ta fita batare data furta komai ba, wasu manya manya bayi ta gani su biyar riqe da wasu zabga zabgan bulalai, suna ganinta suka nuna mata kan wani itace dogo wai tahau ta kwanta ta juya bayanta, bata musu gardama ba tahau ta juya musu baya suka soma zabga mata wadannan manyan bulalan na hannun, lkcin ummul shukri ta fito riqe da sandarta tana kallon yadda suke hukunta bimbii, israt da khulood kuwa gani sukayi sam basu iya kyale bimbii ta amshi hukunci ita kadai ba suka dawo da gudu duk suka zo wurin suka durqushe da kafafunsu, ummul shukri ta tmbyeshi mene ya kawosu wurin sukace" muma mun zo amsar hukunci ne don tare muka shiga gdn maganin da ita" wata uwar tsawa uwar bayi ummul shukri ta daka musu tsawa tace" su 6ace su bata wuri,dole suna ji suna gani bimbii ta amshi hukuncinsu, bulala tamanin suka mata"duk jikinta ya farfashe jini ne kawai ke fita ya 6ata rigar dake jikinta amma abun mamaki ko digon hawaye basu gani ba a idanun bimbii, hk suka tasa qeyarta tana tangadi suka tafi da ita kurkun da ake kulle bayin da sukayi sata wai sai tayi sati biyu kafin ta fito, suna shiga da ita suka watsata cikin kurkun suka fito abinsu" tunda suka watsata bata dago da kanta ba sbd radadi da ciwo da jikin yake mata, tana kwance saman busassun ciyayin dake qasan wurin sai lkcin wasu hawaye masu d'umi suka soma sakko saman kuncinta, tabbas rashin yanci beyi ba, kafin dare ko'ina na jikinta ya suntume ya kumbura gashinta duk ya rufe mata fuska babu dankwali a kanta, idanunta sunyi jajir sun kumbura sbd tsa6ar kuka data tayi wannan dare,ga ciwo na cinta amma babu magani, Allah shi kadai shine gatanta don bata da wani gata kasancewarta qasqantacciyar baiwa mara galihu, 6angaren su israt da khulood kuwa ranar ko abinci kasa cinsa sukayi suna tunanin yar'uwarsu bimbii ga lailah kuma a kwance jiki ya kuma rikicewa, daren ranar ummul shukri ta shigo 6angaren nasu ta taddasu 2jugum, kallon yanayin lailah kawai tayi tasa hannu ta dago da ita tana qare mata kallo take ta hade fuska ta kalli tsakiyar idanun lailah tace" kina da juna biyu lailah, waye yyi miki ciki lailah" wannan kalma da uwar bayi ummul shukri ke furta ita ta razanar dasu israt dake gefe suka soma kuka, lailah kuwa duk da zafin zazza6in da take fama dashi kalaman ummul shukri sunyi masifar fadar mata da gaba, ta kalli uwar bayi ummul shukri tace" ciki? ciki ne dani" kafin ta rufe baki ummul shukri ta zabga mata mari har uku a fuska tace" kinsan hukuncin wannan abun kunya da kk aikata kuwa?" lailah kuwa kuka take sosai har da sheshsheqa tana roqon uwar bayi ummul shukri ta rufa mata asiri ta mata aikin gafara,ummul shukri bata kuma cewa komai ba ta miqe ta fita, tana fita su israt da khulood suka taho wurinta da gudu suna tmbyrta abunda ke faruwa da ita, lailah kuwa kuka kawai take tana tausayin kanta da rayuwarta,israt ta riqo hannunta tace" lailah me kk 6oye mn baki daukemu yan'uwa ba kenan" kuka take sosai ta kasa furta komai,khulood tayi shiru tana tunanin wani abu,a hnkli ta dago kanta cike da rudani da tsantsar fargaba hadi da tsoro ta kalli lailah suka hada idanu tace" lailah,lailah meyesa kkyi hk,lailah abunda nk tunani shine,kicemin aa lailah" sai kawai ta fashe da kuka ta soma jijjiga laila tana cewa tace mata aa, kallon khulood israt tayi cike da mamaki tace" akwai abunda kk 6oyemin,akwai abunda ya faru ban sani bane" miqewa tayi ta soma turesu tana kuka tana cewa baku yarda dani bane kuke 6oye min abu.......
Littafin nan na kudi ne ki biya kiyi karatu na yanci bana satar fage ba,naira dari uku kacal ta siya miki qarashen labarin DAREN GOMA SHA HUDU....zaki tura #300 ta wannan acct..0100790419,alhaji shahida nasir,union bank, sai turomin da screeshrt na payment naki ta whatsapp...07041195806, idan da buqata wani qarin bayani ga layin kira nan..08080611486
Alkalamin Bintuu ne....
10/10/20, 1:12 AM - Anti qamshi🌷: *DAREN GOMA SHA HUD'U*🪔🪔
Written By Bintuu Seer
8
*My luv to you is beyond words but looks into my eyes you will believe the real magic of your pure luv in it*........I give you my heart dear...💕
Janyo hannunta lailah tayi duk ta hadasu ta rumgume, kuka suke sosai sai can khulood tace" bazan ta6a gafartawa kaina ba lailah idan har wani mugun abu ya faru dake" rufe mata baki lailah tayi tace" ki daina fadar hk a rayuwa kowa da qaddararsa kuma babu wanda ya isa ya goce mata, qaddararmu shine mun zo lkcin da masu mulki da sarauta suke da qarfin izzah tare da murqushe wanda baida y'anci, dole mubi rayuwar yadda tazo mn" khulood tace" meye amfanin abunda kkyi lailah da kin bari mun amshi hukuncinmu a lkcin da duk hk bata faru dake ba" shiru lailah tayi tana tunanin abubuwan da suka faru kwanakin baya wanda shine silar shigarta wannan hali yanzu, khulood da lailah sun ta6a yunqurin guduwa kwanakin baya Allah bai basu sa'a ba aka kamasu don basu da shaidar fita,yawanci yantattun bayi suke da damar fita ko'ina su kuma bayi na qasa qasa saidai idan suna da shaida fita tare dasa hannun wani sananne cikin masarautan, bawan daya kamasu shine raqas babban bawa dake kula da babbar kofar fita daga masarautar,hukuncin bawan da aka kama da yunqurin gudu shine kisa ko kuma akaisa baqin kurkun qasa,kurkun qasa kurku ne da suka tanada a qarqashin qasa suke ajiye masu babban laifi tare da azabtar dasu, lkcin da raqas yaga su lailah da khulood na yunqurin gudu ya kamasu, ba kalar roqon da basu masa ba yyi kunnen uwar shegu dasu yace" wlh sai ya kaisu gaban hukuma sun amshi hukunci daidai da laifinsu amma daga qarshe sai ya nemi lailah ta amince ta kwana tare dashi shi kuma sai ya rufa musu asiri, lailah tayi qememe taqi amincewa da hkn, yace toh su tafi gobe su tsumayi sammaci, hk suka dawo 6angarensu cike da tsoron abunda ze biyo baya, lailah ba kanta take tausayawa ba khulood dake jin tausayi gani take idan bata amince da buqatar raqas ba toh fa daga ita har khulood basu tsira, lkcin da suka dawo israt ta tmbysu ina sukaje sai suka 6oye mata basu fada mata abunda sukayi ba, lailah koh saida ta bari bacci ya kwashe ta tashi ta fice ta tafi wurin raqas, shi kuwa yana ganinta yyi murmushi yace" kinyi tunani maikyau da kk dawo don kuwa da rayuwarku ta shiga garari" lailah bata ta6a tunanin samun shigar ciki ba akan wannan dare kawai, sai wurin asuba ta sato jiki ta dawo lkcin khulood na zaune don ta tashi bata ga lailah ba kuma tabbas zuciyarta ta bata lailah komawa tayi wurin raqas, tana zaune lailah ta shigo idanunta jajir ga dukkan kuka tasha, ganin khulood zaune ne yasa ta soma goge fuskarta, khulood ta zuba mata idanu tace" lailah ina kkje" shiru lailah ta mata itako khulood qara kallon lailah take sosai taga tfyrta ta sauya, miqewa tayi zumbur ta nufo inda lailah take tace" lailah komaqa kkyi wurinsa kk miqa masa budurcin naki" rufe mata baki lailah tayi tace" kiyi shiru kar israt taji hnklinta ya tashi, khulood bamu da wata mafita sai wannan tunda ya bamu za6i" khulood kasa mgn tayi sai durqushewa da tayi a wurin tana kuka sosai, wannan shine abunda ya faru dasu kwanakin baya, hk khulood sanar da israt abunda ya faru, dukkaninsu kuka suke sosai suna tausayawa lailah don ba makawa hukuncin jefewa ne ya rataya akanta,washegari dukkaninsu ba wacce hnklinta yake a kwance kowacce cikin fargaba da tashin hnkli take amma duk da hk saida suka tafi kurku don ganin halin da bimbii take ciki har da lailah, 2qiri bayin dake tsaron wurin suka hanasu ganinta hk suka koma bakin ayyukansu, bimbii kuwa yunwa qishin ruwa ga radadin ciwo duk sun galaibartar da ita, kwanan bimbii biyu prince nasaar yaga baya ganinta sbd yasan duk wurin zuwanta, sanya wani hadiminsa yyi bincike akanta, batare da wani 6ata lkci ba ya binciko masa inda bimbii take,dakansa yaje kurkun yasa a fito da ita, jiki na rawa suka fito da bimbii bata ma gane abunda ke faruwa, wata baiwarsa yasa mai suna salma ta tafi da bimbii ta kula da raunin dake jikinta, hk kuwa akayi salma ta tafi da bimbii wani 6angare na daban ta bata ruwa tayi wanka taci abinci ta bata wurin kwana,tunda bimbii tazo qasar sai ranar ta ta6a kwana a abu mai laushi, salma mace ce mai kirki hk ta din ga kula da bimbii tana shafa mata magani a raunin dake jikinta sbd kar ya bar mata ta6o ita mace ce,6angaren su khulood kuwa basu da masaniya kan sakin bimbii da akayi gashi kullum suna cikin tashin hnkli da tsammani don har yanzu uwar bayi ummul shukri bata kuma furta komai ba kan mgnr lailah, satin bimbii biyu ta murmure sosai don bata aikin fari bare na baqi kawai kula take samu saidai kewar qawayenta da take wato su lailah dukda kasancewar suna cikin gdn sarautan amma da akwai ta tazara sosai tsakanin 6angare zuwa 6angare, bimbii har yanzu batasan waye silar fitowarta daga kurku ba ita dai kawai ta samu kanta a hannun salma kuma itama salman bata fada mata wanda yasanya a fito da ita daga kurku ba, sati biyun na cika salma ta rakata zuwa 6angaresu, su israt kuwa tun safe suka tafi kurku suna zaton ranar za'a saketa amma har suka gama tsayuwarsu basu ga an bude kofar kurkun ba hk suka dawo jikinsu a sanyaye saidai mezai faru? suna dawowa daga ayyukansu ummul shukri ta shigo ta sanar da laila ta fito, duk suka biyo bayan laila suka fito, gabansu ne ya fadi lkcin da suka ga bayin dake aiki a kurkun qasa sun gane sune sbd kalar kayan dake jikinsu, suna ganin fitowarsu suka tmbyi ummul shukri wacce daga cikinsu ta nuna musu lailah,basu wani 6ata lkci ba suka tasa qeyar lailah suka tafi da ita,khulood da israt kuka suke sosai suna riqe lailah amma hk suka hankad'asu gefe suka wuce da ita,suna ji suna gani aka tafi da laila babu suka iya, toh suna cikin wannan jimamin ne suka ga shigowar bimbii, salma bata biyo bimbii ba tana kawota bakin 6angaren nasu ta juya, cike da mamaki duk suka miqe suna kallonta don kyau ma ta qara musu da gudu suka taho suka rumgumeta suna kuka, murmushi tayi musu ta duba bata ga lailah ba tace"ina lailah take, jikin nata da sauqi koh" gani tayi duk sun mata shiru, gabanta ne ya fadi don idan har ta tmbyi su lailah abu taga sunyi shiru sun sunkuyar da kawunansu toh amsar ce babu dadi, tace"wani abu ya faru ne" khulood tace" sun tafi da ita" tace" su waye" jan hannunta israt tayi suka koma suka zauna sannan suka zayyane mata abubuwan da suka faru, bimbii tayi shiru hawaye na fita daga idanunta,juya musu baya tayi ta kwanta bata kuma furta komai ba sbd zuciyarta quna take da tafasa, suna son tmbyrta abunda ya faru da ita amma sun fahimci sam bata mood nason mgn, bimbii kuwa wata irin tsanar wannan masarauta ce ta darsu cikin ranta,gani tayi abun yyi yawa su gbdy basu dauki rayuka a bakin komai ba,alwashi taci koda zata rasa ranta sai ta kubutar da lailah daga wannan hukunci na zalinci da suke son aiwatarwa akanta, washegari sunyi mamaki sosai da suka ga bimbii ta saki ranta ita kuma tayi hkne don ta sanyasu suma su saki ransu suyi ayyukansu yadda ya kamata kar suje suyi kuskure suma hukunci yahau kansu, yau bimbii ita daya ta dauki tulu ta tafi babbar qorama debo ruwa,tana zuwa ta tsuguna zata fara deban ruwanta ta hango wata tsuntsuwa mai kyau da daukar hnkli a jikin wata bishiya aikuwa sai ta ajiye tulunta ta soma lalla6awa da niyyar kama tsuntsuwar,tashi tsuntsuwar tayi ta sauya wuri, ita kuwa bimbii sai binta take wai ita zata kamata suna cikin hk har sukayi nisa da wurin qoramar data tabar tulun ruwanta, tsuntsuwar har bakin wani lambu takaita sannan ta tashi firrrrr ta6ar wurin,bimbii kallon tsuntsuwar take har ta qurewa ganinta, tsak tayi ta juya zata koma inda ta baro tulunta, hango yalwar bishiyoyi tayi a cikin wannan lambu kuma alamu sun nuna lambu yana cike da yalwar kayan marmari, kofar shiga lambu ta gani a bude, batare da wani tunani ba ta shiga lambun ta haye wata bishiyar tuffa tana tsinka tana ci, kishingida tayi abinta akan bishiyar tana cin tuffanta hnklinta kwance...
10/10/20, 1:12 AM - Anti qamshi🌷: *DAREN GOMA SHA HUD'U*🪔🪔
Written By Bintuu Seer
9
*Your love become my oxygen I can't live without you*......I'm infected with a serious virus on earth and you are the only doctor that can cure it......
Wani qasaitaccen k'amshi taji yana tashi ya had'e da ni'imatacciyar iskar dake kad'awa cikin wannan lambu, tashi tayi zaune ta leqa qasan bishiyar don ganin abunda ya haddasa wannan qamshi, abunda ta gani ne yyi mugun kad'a y'ay'an hancinta, PRINCE AKBAK!!.ne shida hadiminsa na hannun dama wato ubaid, tun shigowarsu suka ganta bisa bishiya abun yyi mugun basu mamaki, baiwa cikin lambu babban prince, ita kuwa bimbii tsabar tsorata kasa had'iye tuffan dake bakinta tayi ta sake baki tana kallonsu tamkar wata doluwa, prince akbar kuwa ko kallon bishiyar da take be sakeyi ba yyi gaba abinsa cikin qasaitaccen takunsa da yake bayyana tsantsar izzarsa da kuma isar matsayinsa, ubaid ya gama sanin halin babban prince, idan yana son bashi umarni da ido kawai idan ya kalleshi yana sanin me yake nufi take ze aiwatar, shi prince mgnr ce take masa mutuk'ar wahala tamkar d'an kurma hk yake sai tayi masifar kamawa yake bud'e bakinsa yyi mgn, wata irin tsawa ubaid ya doka mata wanda sauran qiris ya rage ta saki fitsari a wando ba shiri ta diro daga saman bishiya ta kife akan guiwowinta, kallonta ubaid yyi cike da qasqanci yace" wace ce ke? yanayinki kawai ya tabbatar min kedin qasqantacciyar baiwa ce amma ki rasa ina ya dace ki sauke raininki sai a lambun babban prince" kuka bimbii ta soma masa tace" don Allah kuyi hkr wallah ni bansan lambunsa bane" ubaid tsayawa yyi kawai yana kallonta don tabbas shi kansa ya yaba da k'arfin halinta, fuskarsa a murtuke yace" kije ki jira a waje" miqewa tayi sum sum tana d'an waiwayen baya musamman qaramar k'ofa dake cikin lambu da taga prince akbar ya shiga ya barsu a wurin,ubaid kuwa yana ganin ta fice yabi bayan prince cikin k'ofar shima sai gashi ya fito wani babban fili, prince ya hango yana gwada saitin harbin mashi, sauri yyi ya qarasa gefensa ya tsaya yana miqa masa masun dake hannunsa shi kuma yana amsa yana harbawa daidai saitin wata bishiya, bimbii kuwa tana wajen lambun tana jiran fitowar ubaid amma shiru shiru babu shi babu alamarsa har gari ya soma lumshewa,rana na dab da faduwa suka fito daga lambun tasha jira har ta gaji bacci ya dauketa a wurin, sai lkcin prince ya kalleta sosai tana baccinta a wurin, tsayar da idanunsa yyi sosai akanta abun har ya bawa ubaid mamaki don be ta6a ganin prince ya qurawa abu idanu hk ba, bud'e idanunta tayi a hnkli taga inuwar mutum tsaye akanta, k'afarsa kawai ta kalla tun kafin ta dago da kanta tasan mutum ne da hutu ya gama ratsashi,k'afarsa sanye take cikin wani farin takalmi half cover shoe, tunda take bata ta6a ganin mutum mai kyawun k'afa irin prince akbar ba, kafar nan tasa luwui luwui tamkar tumatir gata jajir da ita kamar ka matsa jini ya fito, jallabiya ce fara sol a jikinsa sai rawanin daya rufa a kafadarsa dayake ja da fari, gashin kansa baqin qirin ya sauka har kafadarsa yana rawa tamkar na mata,idanunsa tamkar yasa tozali gasu a lumshe kamar yanzu ya tashi daga bacci,sassayan k'amshinsa ne ya cika hancinta,dago da fuskarta tayi suka hada idanu take taji gabanta ya tsananta bugawa, yana ganin ta dago da idanunta yyi saurin dauke kansa akanta ya haye dokinsa shima dokin nasa fari, alamu sun nuna prince din yana qaunar farin abu, kallon ubaid kawai yyi shima ya haye dokinsa suka barta a wurin batare da sun ce mata komai ba, bin sawun dawakansu tayi da kallo har suka qurewa ganinta, tashi tayi tana karkad'e qasar dake jikinta ta soma tfy har ta isa inda ta ajiye tulunta yana nan inda tabarshi ta cika ruwanta ta dora aka ta nufi cikin gd,tunkan ta qarasa ta hango uwar bayi ummul shukri da tsumangiyanta a hannu, tana sauke ruwan ta rufeta da duka tace" tun safe ko aiki guda bakiyi cikin ayyukanki ba sai yanzu kk kawo sawun ruwa daya" shiru tayi batare data kawo wani uziri ba,ummul shukri bata amsar uxiri ko qaqa,fito mata tayi da wasu manyan barguna tace ta kwasa taje ta wankesu gashi dare ya soma shiga sosai don ma garin da hasken farin wata hk ta kwashi barguna ta nufi babbar qorama dasu ta soma tiqar wanki, tana cikin shanyawa ta gano inuwar mutum a bayanta, juyawa tayi da sauri idanunta ya gane mata prince nasaar, murmushi yyi mata da fararen haqoransa yace" wankin dare kuma baki tsoron mura" wani irin murmushi tayi tamkar kuka iyakarsa le6enta tare da rissinar da guiwowinta tana gaishe shi, tsugunawa yyi kusa da ita yace" ina buqatar kwarkwara kuma ke nkso" kalmar taji tayi mugun bugarta ta zaro manyan idanunta waje tare da dafe kirjinta tace" na shiga uku, wlh ni ban iya komai ba" dariya ta bashi yyi har jerarrun haqoransa suka bayyana yace" zaki koya ai, zaki zama baiwar dake kula dani kwanan nan" gabanta ke faduwa sosai tana kallonshi, babban abunda bimbii ke karewa a wannan yanayin data tsinci kanta aciki na bauta shine budurcinta bata qaunar abunda ze iya rabata da budurcinta, zama kwarkwara a gdn sarauta ai dole sai ka rabu da budurci kuma ga hadari na daukar ciki, itakam tafi qaunar ta cigaba da kasancewa a baiwa mara gata idan har budurcin bazai ta6u ba, sanya hannunsa yyi da niyyar riqo hannunta ta daka wani uban tsalle tayi gefe, abunda tayi yyi masifar daure masa kai,tunda yake ba baiwar data ta6a masa hk sai bimbii shi gani yake kamar taimakonta zeyi amma har ta gwada masa wannan cin fuskar a matsayinsa na jinin sarauta yace"bimbii wannan abunda kkyi kuskure ne babba kar ki kuma gwada hkn ga duk wani jinin sarauta" yyi mgnr fuskarsa a sake tamkar beji haushin abunda ta masa, shiru tayi ta sunkuyar dakanta qasa, wani dutse ya nuna mata yace" ta zauna ta tayashi hira" ji tayi kamar ta kurma ihu amma ba yadda ta iya hk ta zauna daga can gefe ta dosana duwawunta akan dutsen, Allah ya sota ta gama wankinta, murmushi yyi don yana lura da rashin sakewarta yace" bani labarin qasashenku na baqar fata tare da al'adunku" shiru tayi ba tace komai ba, shan kunu sannan ta sauka daga kan dutsen ta sauke guiwowinta a qasa tana roqonsa tace" don girman Allah ka rufamin asiri kabarni na koma bakin aiki na"murmushi yyi yace" wannan ce kawai buqatarki?" ta daga masa kai alamar ehh, yace" shikenan jeki saida safe" miqewa tayi da sauri tabar wurin tana qara dubawa don tabbatar da cewa babu wanda ya ganta tare da prince nasaar, shi kuwa yana daga zaune yana kallonta harta 6acewa hangensa, tana shiga 6angarensu taga su israt da khulood sai zaman jiranta suke suci abinci, suna ganinta kuwa suka tarota da murna suka tmbyta abunda ya sanya ta jima bata fada musu komai ba game da abunda ya faru da ita, suna gama cin abinci israt ta kalli bimbii da murmushi a fuskarta tace"albishirinki!" bimbii ta kalleta tace"goro" israt tace" babban prince ya fitar da ranar za6en sabuwar baiwa dake kula da 6angarensa, nida khulood muna son shiga gasar saidai bamu da chanchata sbd rukunin bayin da muke ciki basu shiga za6en" murmushi bimbii tayi tace" tab, amma kuna da karfin hali waye ya aikeni nikam bani so" khulood tace" wlh nima bawai don ina da sha'awar hkn nakeson shiga ba saidai hkn shine nake ganin ze taimakamin wurin jeton lailah daga wannan hukunci kinsan har an kaita kurkun qasa fa" bimbii tace" kamar ya kenan" khulood tace" idan kina wannan matsayi zaki samu dama sosai wurin neman alfarma wurin babban prince don shine na biyun sarki a wannan masarauta" shiru bimbii tayi sai kuma ta dago da kanta tace" kuna ganin hkn bazai ta6a budurcinku ba" dariya sukayi gbdynsu, israt tace" tab, ai nikam idan prince akbar ya buqaceni da gudu zan miqa wuya don burina ya cika" bimbii sakin baki tayi kurum tana kallon israt da mamaki shimfide kan fuskarta, khulood tace" kaf cikin bayin da suka ta6a kula da 6angaren prince babu wacce ya ta6a nema duk kuwa wacce yau babban prince ya amshi budurcinta dole ta burge kuma dole tayi alfahari dakanta don ta isa mace" bimbii kallon khulood take da tsantsar mamakin kalamanta,gyara zama tayi tana fuskantarsu tace" toh ya akayi kksan baya nemansu" murmushi sukayi israt tace"ai al'adar wannan masarauta shine babban prince dakansa yake za6en baiwar da zata kula dashi duk wacce ta samu nasara za'a sanar a wurin za6en amma matakin qarshe na za6en idan har prince ya samu baiwar a matsayin disvirgin wato ba danyar budurwa ba toh hukunci mai tsauri ze hau kan baiwar shiyasa duk wadanda suke shiga gasar sai sun yarda da kansu, abu na gaba kuma idan ya sameki a cikakkiyar budurwa toh washegarin ranar baiwar zata fito da zanin gadon daya 6aci zuwa babbar qorama ta wankesu dakanta cike da alfahari, hkn shine shaidar dake nuni prince shine ya fara saninta diya mace kuma zata cigaba da kasancewa a matsayin baiwarsa koda ya sake sabuwa kuma sarauniyya zata mata kyautar girma sbd ta faranta ran d'anta ta bashi babbar kyauta,toh shi prince akbar har yau duk bayin da yake za6e babu wacce ta taba fitowa da wannan shaida balle sarauniyya tayi mata kyauta sannan ba'a ta6a samun wacce hukuncin rashin budurci yahau kanta ba hkn na nuni da cewa prince akbar be ta6a kusantar ko daya daga cikin bayinsa ba, kinji dalilinmu" ajiyar zuciya bimbii tayi tana al'ajabin wannan al'ada tasu tamkar ta larabawan farko, khulood tace"idan kk kasance baiwar prince kin tsira kenan don babu dan iskan dazai nemi keta miki haddi kina matsayin baiwa ga prince akbar" shiru bimbii tayi tana tunani, tabbas idan hkne gwara ta shiga gasar don tana tunanin abunda prince nasaar yace da ita yau, wai zata zama kwarkwararsa, kallon khulood bimbii tayi tace" toh su kuma sauran princes din fa suna kwatar budurcin bayin nasu" khulood tace" sukam kowacce baiwa suka za6e washegari take fitowa wankin zanin gadon daya 6aci" shiru tayi sai kuma ta dago da kanta tace"tabbas nima idan zan samu dama zan shiga gasar prince akbar kodan lailah" rumgumeta sukayi suna dariya, saidai tunaninsu yanzu shine rashin cancanta musamman bimbii da take ba balarabiyar usul ba shikansa wannan naqasu ne gareta...........
No editing pls.
WANNAN PAGE SHINE QARSHEN FREE PAGE NA WANNAN LITTAFI MAI BUKATAR KASANCE DANI CIKIN CIGABAN SAIKI TURO DA DARI UKUNKI#300 TA WANNAN ACCT..0100790419,ALHAJI SHAHIDA NASIR,UNION BANK,SAIKI TURO DA SCREENSHRT NA PAYMENT DINKI TA WANNAN LAYI...07041195806.....IDAN DA BUKATAR QARIN BAYANI GA LAYIN KIRA NAN...08080611486....
Alkalamin Bintuu ne...
10/10/20, 1:12 AM - Anti qamshi🌷: *DAREN GOMA SHA HUD'U*🪔🪔
Written By Bintuu Seer
10
*Zinariyar mace mai ado da tagullah,jinjinar ban girma nk miki uwargida sarautar mata, kece uwar gd kuma kece amarya a gdn Dr. usman bukar*......a jima anayi sai uwar kissa mai ado da k'amshi dake nk......Hjy Hafsatu Usman Bukar��ina yinki irin totally din nan, wannan page naki ne kiyi yadda kkso dashi🌺
*When I feel boring staring at you comfort me,when I feel hopeless your words give hope,when I feel weak your smile give me strength*.......My luv to you is pure,pls accept me dear💕
Washegari suka tashi kamar yadda suka saba kullum kowacce tayi 6angaren da aikinta yake,6angaren lailah kuwa kai tsaye gdn hukunci aka wuce da ita inda alkali ya zartas da hukuncin kisa akanta amma sai ta haife cikin dake cikinta tukun, kurkun qasa suka kaita ta raini cikin nata a wurin, bimbii kullum tana cikin tunanin lailah ta rasa hanyar da zata iyabi ta taimaketa daga wannan hukuncin na zalinci amma kuma kalaman su khulood har yanzu suna yawo akanta wato idan ta kasance babbar baiwa ga prince akbar zata iya samu alfarmar ku6utar da lailah kenan daga wannan danyen hukunci, zama tayi bisa wani farin dutse tana tunanin hanyar daya dace tabi wurin samun cancantar shiga wannan gasa kuma gashi ranar gabatar da za6en yana kusantowa, miqewa tayi a hnkli ta dauki kwaryar data cika da nonon raqumi ta dora akanta ta wuce dashi babban kitchen,ranar dukkaninsu sun kammala aikin nasu da wuri suka dawo 6angarensu,israt ta zaunar da bimbii tana koya mata wasu baitoci cikin wata waqar larabci, tace" tunda kince baki iya ko baiti daya daga cikin waqoqinmu na larabci ba toh ki gwada wannan ko zata shiga da kalar rawarki" miqewa bimbii tayi ta soma rera baitocin waqar tana yar rawa sai dariya suke gbdynsu, israt ta miqe tace" ku tsaya ku ga yadda zanyi a gaban prince idan na samu shiga za6en nan" sexy dance ta soma irin nasu na larabawa tana kada cikinta da kirjinta ita suke kira raqas sharqi, dariya sosai suke mata bimbii tace" baki da dama israt kuma zaki iya irin wannan rawar a gabansa baza kiji kunya ba" tace" wacce kunya idan har xe za6en" khulood tace" amma fa bana bayin da suka shirya shiga wannan za6en suna dayawa" tsaki israt tayi tace" haushi suke bani ai" khulood tace"kayy israt a gaisheki da qoqari kice muma muna baki haushi kenan" dariya tayi tace" ku idan kune ai kamar nice na samu amma sauran bayin suna samu suna matsawa zasu soma sha mn qamshi dubi fa lenah yadda take yiwa su zainah kamar ba rukuni daya suke ba da" murmushi bimbii tayi kawai tace" toh yanxu meye abunyi kunsan dai banda rukunin a tsarin gasar" israt tace" satar jiki zamuyi kawai mu shiga" khulood tace" wacce irin shawara ce wannan kina tunanin bazasu gane rukuninmu bane" israt tace" nidai ranar tsinke wannan sarqar kafan zanyi na tafi wurin za6en" shiru bimbii tayi sai tace" gsky dole su gane mu" khulood tace"kawai mu gwada yin hkn" bimbii tace" toh Allah ya kaimu ranar" da wannan shawarar a zuciyoyinsu suka kwanta bacci kowacce tana mafarkin ta samu nasara a wannan za6e........
Yau itace ranar wannan za6e, kyawawan yan matan bayin sun jeru sahu sahu kowacce cikin sutura mai kyau a farfajiyar 6angaren prince akbar suna sauraron fitowarshi, bayin dake kula da wannan gasa kuwa sai kai kawo suke a wurin, y'ay'an sarakunan nan duk suna wurin sun hakimce, gimbiya hindu itama tayi ado sai walwali take da daukar idanu tana daga gefe a zaune itama,kofar fitowa prince kawai suke kallo suna tsammanin fitowarsa, ba jimawa kofar 6angaren nasa ta bud'e ya bayyana, sanye yake cikin wata doguwar farar jallabiya da farin rawani ya dora irqa baqi a saman rawanin sai baqar alkyabba, sajensa sai daukar ido yake sbd sheqi, gefensa ubaid ne yake take masa baya sai kuma babbar baiwarsa wacce ze musanya wato lenah,fuskarta babu annuri ko kadan sai hararar jerin yan matan take don ita tafi son kullum ta kasance da babban prince tana masa hidima,tsayawa yyi yana qarewa jerin y'an matan nan kallo, caraf idanunsa suka sauka kan bimbii dake ta faman rissinar dakanta qasa,duk cikin yan mata ita kadai ce mara hasken fata sosai,dauke idanunsa yyi akanta ya kalli ubaid yace" ku fara jarrabasu" batare da 6ata lkci ba aka soma jarrabasu,farko baiwa kowacce abun girki akayi ta canki abinci da prince yafi so ta girka ta kawo masa ya dandana, bimbii tana can baya don batason prince nasaar ya ganta shiyasa take ta sunkuyar dakanta, bimbii bata iya irin girkinsu ba tayi tsuru tsuru, kowacce sai aikinta take don ana tfy ne da lkci, ganin idanu yana zuwa kanta ne yasa ta soma aikin nata cike da tunanin abunda ya kamata tayi, tashi tayi taje ta tatso nonon raqumi ta dawa ta soma aiwatar da abunda ya kamata,chugui tayi na nonon ragumin sannan tayi green tea irin wanda ta koya a wurin maheer, daya bayan daya kowacce take miqewa taje gaban prince ta sunkuya ta riqe abunda ta girka shi kuma ya dandana yaji, bimbii itace ta qarshe cikin sanyin jiki ta qaraso don ita gani take kamar za'a mata dariya abunda ta girka, sunkuya tayi a gabansa ta riqe dan qaramin plate din data saka chuguin da small mug na green tea, sai da yadan dakata sbd ganinta da yyi mai duhun fata yana kyankyamin dandana abun nata sai kuma jan dai ya dauki small spoon din dake faranta ya debi green tea din nata ya dandana sau biyu yana dandanawa sannan ya dauki chugui kadan ya dora a saman le6ensa cike da shakku, kallon ubaid yyi tuni ya fahimci abunda yake nufi, ubaid ya kalli bimbii yace" prince yana son sanin da mene kk had'a wannan abun"ya nuna mata chugui din dake saman plate din hannunta, dago da idanunta tayi tace" da nonon raqumi na hada" komar da ita wurin nata akayi ta kuma hada chuguin yadda ta hada na farko, hk dai aka cigaba da jarrabawar har akazo fagen rawa shima bimbii ta birge kowa don komai nata fita yake daban,komai irin na al'adarta take hkn shine ya dauki hnkli kowa da prince shi kansa, prince nasaar dake gefe kuwa wani irin bala'in haushi yakeji, be ta6a tunanin zata iya shiga gasan nan ba, sauran yan matan dake wurin suma mugun haushin bimbii suka soma ji tun kafin a bayyana sakamako, gani sukayi komai nata ya dauki hnklin prince akbar saidai kafin a fadi sakamako rahoto ya shigo musu cewa bimbii tana cikin rukunin bayi ne na farko kuma suna da shakkun asalinta, prince yace" duk da hk su saki sakamakon a gaban kowa" batare da 6ata lkci ba aka bayyana bimbii a matsayin wacce ta lashe wannan za6e don prince ya yaba da salon dandanon abunda ta hada da kuma yanayin rawarta,israt wani irin tsalle tayi ta qanqame bimbii cike da farin ciki don sukam riqima ce kawai ta kawo su basu ta6a zato daya daga cikinsu zata samu nasara ba, musamman ma bimbii da take jinsin baqar fata,bimbii kuwa ta kasa dago idanunta sbd fuskoki daya aika mata da harara suke cike da hassada wasu kuma zallar qiyayyace kawai irinsu gimbiya hindu da ba shiri tabar wurin cike da mamaki babban prince fal ranta tayaya ze karye dokar gdn nan ya za6i baiwa mara cikakken asali kuma wani abun takaicin ma gata baqar fata a tarihin masarautar babu dan sarkin daya ta6a za6en baqar fata a matsayin babbar baiwa don yawancinsu basu da asali don ba jinin larabawa bane, bimbii kuwa saida aka gama za6en kafin aka gane rukuninsu amma tunda prince ya riga ya za6eta a matsayin babbar baiwa ta wuce wurin, 6angaren ummul shukri kuwa abun ya bata mata rai sosai na wannan za6en da prince yyi taya ze za6i babbar baiwarsa daga qasqantattun bayi rukunin farko wannan ai tamkar zub da qimar gdn ne, za6en bimbii a matsayin babbar baiwa ya kawo gutsiri tsoma sosai a wannan masarauta wanda hkn yakai kunne sarauniyya mar'atuusaliha ta kira ummul shukri don jin yadda akayi rukunin bayi na farko suka shiga za6en shiru ummul shukri tayi don tabbas tasan laifin kowa ze gani don su bimbii a qarqashin kulawarta suke itace tun farko tayi sake, ranar ummul shukri tasha fada a wurin sarauniya mar'atussaliha har takai da an dakatar da ita daga matsayinta na wasu kwanaki, hargitsi aka samu sosai cikin wannan gdn don mafi yawan jama'ar gdn na ganin rashin cancantar bimbii a wannan matsayi, 6angaren prince kuwa ko a jiknsa don halinsa kusan daya da mahaifinsa sarki Abdallah bin jabal akwai taurin kai da kafiya musamman akan abunda suka aminta akansa, babu wanda ya isa ya sanyashi sauyawa baiwa tunda har ya riga ya za6a, ummu sumayya ita ta wuce da bimbii wurin gyara aka gyarata kamar yadda ake yiwa duk baiwar data samu nasarar samun wannan matsayi, wani tamkamemen daki aka kaita a matsayin dakin kwananta sannan ummu sumayya ta soma sanar da bimbii abunda prince yakeso da kuma wanda baya so don mugunta sai tace mata prince baya son qamshi kuma yana son mace ta din ga yawan sanya baqaqen kaya, Allah sarki bimbii duk ta dauka hkne tace"toh" daren ranar bimbii zata soma ziyartar fadar prince,bimbii cike take da tsantsar fargaba da faduwar gaba sosai harta soma dana sanin shiga wannan gasar, maqiya da mahassada kuwa kawai jiran wayewar gari suke su ga ko bimbii zata fito wankin budurci bakin qorama.....
Littafin na kudi ne ki siya ki karanta cikin yanci ba satar fage ba, idan kin shirya siya ga trasaction detail nan, zaki tura #300 ta wannan acct..0100790419,alhaji shahida nasir,union bank,saiki turomin da screesht na payment ta whatsapp through wannan layi...07041195806, idan da neman qarin bayani ga layin kira nan..08080611486......
Alkalamin Bintuu ne.....
10/10/20, 1:12 AM - Anti qamshi🌷: *DAREN GOMA SHA HUD'U*🪔🪔
Written By Bintuu Seer
11
*In the middle of the night when the stars scattered at the sky the moon become shiny I keep thinking at you*.......Your voice are the sweetest thing I ever.......
Dare yyi sosai amma gdn akwai yalwar fitilu ta ko'ina suna haske kowacce kusurwa ko allura ce ta radio take za'a ganota sbd wadataccen haske daidai lkcin bimbii ta fito sanye da wata doguwar riga bak'a qirin hkm mayafin rigar tfy take a wani dogon corridor hannunta dauke da wani faranti na azurfa da qananan kofina da kuma wani jug mai kyan gaske a tsakiya, green tea ne aciki kuma wannan dogon corridorn shine zai sadata da babbar k'ofar inda prince akbar yake wato sashinsa,jikinta rawa yake sosai don duk a tsorace take sbd batasan meze faru ba, tana qarasowa bayin dake tsaron kofar suka bata hanya,kofar ta bude da kanta ita kuma ta danna kanta ciki kanta a sunkuye tamkar wata munafika, tana sanya kafafunta ciki wani sassayan qamshi tare da sanyi yyi mata maraba, qasan wurin tamkar glass yake sai daukar idanu yake da kyalli, dakin qaton gaske ne kuma kusurwa kusurwa yake,kowacce kusurwa tana da kofa kamar ta masallaci an kame wurin da curtains na alfarma ga kuma shimfida na manyan royal center carpets masu ado, curtains din da aka kame kowacce kusurwa zaka gansu sharara,komai na cikin wurin abun kallo ne, 6angare guda kuma wasu kujeru ne irin royal chairs din nan kalar golden, kusurwar tsakiya idanunta suka kalla inda ta gano kusurwar tafi kowacce girma an kameta da wani qasaitaccen curtains shara shara milk colour, wani gado ta gano a cikinta tafkeke yasha bedshit na wawayen kudade shima bedshit din milk colour, bimbii tsayawa tayi kalle kalle tamkar yar qauye cikin ranta tana mamaki wai nan duk wurin kwanan mutum guda ne, tunda ta shigo yana zaune a wata kujera yana karanta wani littafi na tarihi ko dago da kansa beyi ba sai yanzu, ita kuma sai lkcin idanunta suka sauka a 6angaren da yake take taji wata faduwar gaba ta tsaya qam a inda take batare data qaraso ciki ba, miqewa yyi ya soma takowa a hnkli har ya qaraso inda take fuskarsa babu yabo babu fallasa kamar dai yadda yake kullum, tsayawa yyi yana qarewa shigarta kallo ya tsayar da kwayar idanunta akan fuskarta ita kuwa sai tayi saurin yin qasa da guiwowinta a gabansa, bata ta6a tsammanin zeyi magana ba taji muryarsa cikin tsadadden larabcinsa yace" kije ki sauya wannan kayan dake jikinki" abunda ya fada mata kenan ya juya cike da takun qasaita ya koma inda yake zaune ya cigaba da abunda yake, ita kuwa bimbii miqewa tayi da sauri ta juya da niyyar ficewa daga dakin har tana hard'ewa ta rasa dalilinsa nacewa taje ta sauya kayan jikinta sai ta soma wani tunani nata na daba take hnklinta ya qara tashi cikin ya duri ruwa hk ta koma dakin da take, tana ta cika da mamakin ganin su israt da suka sato jiki suka zo wurinta suka tarar bata nan suka bararraje a saman gadonta suna baccinsu, motsin shigowarta ne da farkar dasu suka tashi suna binta da kallon mamaki, khulood tace" bimbii daga ina kk badai daga 6angaren prince kk ba cikin wannan kayan" kallon kanta tayi ta dago ta kallesu tace" me kayan yyi" israt ta sakko daga saman gado ta iso gabanta tace" waye ya fada miki prince yana son baqin abu komai nashi fari ne shiyasa bayinsa basu sanya duk abunda ya danganci baqi" shiru bimbii tayi sai lkcin ta gano manufarsa ta kuma fahimci mugunta ummu sumayya taso mata tace ta sanya baqin kaya, zama tayi a bakin gado ta zabga tagumi, israt ta sanya hannu ta cire mata tagumin da tayi tace" mene ya faru yar uwa" murmushi tayi tace" wlh nikam tsoro nk gbdy nayi dana sanin shiga wannan za6en" israt tace" me kkce? sake fada naji, yanzu bimbii baqin ciki kk mana don gashi dai silar cin za6en nan da kkyi har muma mun samu arzikin shigowa wannan wuri har da kwana akan gado mai taushi shine kk cewa kina dana sani, toh meye abun dana sani anan" kwantar dakanta tayi ta kafadar israt, khulood ta matso ta zauna kusa dasu ta dafa bimbii tace" tashi ki cire wannan kayan dake jikinki ki shirya cikin masu jan hnkli" harararta bimbii tayi suka bushe mata da dariya, hk suka sake shirya cikin wata milk colour din doguwar riga mai cike da kwalliya sannan israt ta mata 6arin turare har sai da tace" israt wlh ya isa hk" sannan suka qara taje mata gashi suka tufkeshi da wani band shima milk colour, suka sanya mata wani mai kyalli a le6en bakinta, le6en ya soma shiny, suna cikin shiryata lenah ita da wasu bayi su hudu suka bankado kofar dakin suka shigo ta soma binsu da wani matsiyacin kallo sai ta bushe da dariya suma sauran dake biye da ita suka bushe da dariya, tace" idan kun sauya mata baqin kaya ai baku isa ku sauya mata kalar fatar jikinta ba koh" israt tana shirin maida musu da martani bimbii ta riqeta, matsowa lenah tayi kusa da bimbii tana mata wani kallon wulaqanci tace" basu sanar dake babban prince bashi son baqin abu bane toh bawai baqin kaya ne kawai baya so ba har ma da baqar fata" khulood tazo iya wuya ta kallesu itama a wulaqance tace" dadin abun dai shiya za6eta kuma cikin gayyar fararen fatan yace ita ta dace ta hidimta masa wannan kadai abun alfahari ne" israt tace" idan ma ba naci da neman fada na wasu matan ba yace ya dena yayinki toh meye kuma na farkar jeji hk" kalaman nasu sun fusata lenah sosai amma sai ta dake tayi wani murmushin yaqe tace" toh muna nan muna jira muga ko iskar tusa zata hure wuta" dariya sauran bayin dake biye da ita sukayi suka juya suka fice abinsu,bimbii tayi tsuru tsuru da ita saida su khulood suka din ga binta da kalamai na qara qarfin guiwa,khulood tace" karki mance lailah tana nan tana jiran gudummawar mu gareta komai rintsi kiyi mn alqawarin ba zaki gjy ba" tashi tayi ta rumgumesu gbdy sannan suka mata rakiya har kofa ta fice ta doshi komawar 6angaren babban prince, tana shiga ta tarar dashi sanye da wasu kayan bacci farare qal, gashi kansa ya sauko masa har kafada yana zaune a wata kujera ta alfarma yana hada wasu takardu, shigowar ta ne yasa shi dago dakansa yana kallonta sannan ya dauke kansa ya cigaba da abunda yake, rasa abunyi tayi sai ta koma gefe ta sunkuya akan guiwowinta tana jiran umarninsa, kallonta yyi yace" wannan abun da kk kawo ni kkson na zuba dakaina" mgn yake yana abunda yake batare daya kalleta ba, tashi tayi da sauri ta matso wurin ta dauki qaramin jug din ta tsiyaya masa green tea din data kawo a daya daga cikin qananan cups din dake saman farantin ta rissinar dakanta tare da sanya hannu biyu ta miqa masa cup din, kallonta yyi sannan ya miqa hannunsa fari tas dashi ga yalwar gashi zarara ya amshi cup din daga hannunta ya komar dakansa ya kwantar jikin kujerar dayake yana sipping green tea din a hnkli tamkar bayason ya qare ita kanta na sunkuye cike da kunya irinta ta fulanin usul sbd ita tunda take bata ta6a ke6ewa da wani namiji irin hk ba, shiko prince akbar dayake mutum ne ma'abocin karantar yanayin jama'a yana biye da duk wani action dinta, sai jin muryarsa tayi yace"kinsan a tsari na hidimta mini zaki iya kwana dani da biyamin buqata koh, to meyesa kk shiga za6en duk da kinsan da hk ko kuma kin shiryawa hknne" tayi mutuk'ar mamakin jin wadannan kalmomi daga bakinsa, wani qasaitaccen murmushi yyi hkn ya kuma dulmiyata cikin tsagwaron ruwan mamakin wannan dan sarki da ta6a zaton yana mgn mai tsawo hk ba kuma kalmomin nasa sun sanya zuciyarta tsananin bugawa tana tsoron kar fa mai afkuwa ta afku akanta idan kuwa hk ta faru lamido bazai ta6a yafe mata ba har abada koda ta samu damar komawa gd, sai juyawa tayi bata ganshi a wurin ba dayake tana waiwaya ta gano shi saman royal bed nasa ya kwance ya saki curtains dinshi, alama ya mata data zo, wayyo Allah abunda ta furta kenan cikin zuciyarta dake tseren sukuwa sbd tsantsar bugawar da take, jiki a sanyaye ta nufi kusurwar da gadon nasa yake ta same shi kwance ya juya mata baya wannan alama ce dake nuni da prince din yana buqatar tausa, hk tahau gadon nasa cike da tsoro ta miqa hannunta dake rawa sosai ta dora a jikinsa dake fitar da wani tsadadden qamshi na musamman ta soma masa tausan cikin sanyin jiki, shi kuwa idanunsa a rufe suke tamkar besan me take ba hk ta cigaba da tausa a wannan jikin dan sarkin mai mutukar taushi da silbi tamkar jikin aljanu, tunda yaji bacci ya soma ziyartarsa yyi mata nuni data fice yana son bacci, take wani dadi ya ziyarci zuciyarta ta saukar da kafafunta qasa a hnkli ta fice da wurin ta sake masa curtainsa ta rage masa haske kamar yadda aka sanar da ita ta fice a millions tayi hanyar 6angaren da dakinta yake, tana shiga ta tarar dasu israt da khulood har sunyi nisa a bacci itama, rage kayan jikinta tayi ta nemi gefensu itama ta kwanta abinta take itama bacci yyi gaba da ita, khulood ce ta fara farkawa da asuba ta ganta kwance, israt ma ta tashi duk suna kallonta, baqin ciki ne ya cika zuciyoyinsu sbd ba hk suka so ba wato itama bimbii prince be amshi budurcinta ba kenan, kawai abunda suka qara yarda dashi a lkcin shine prince akbar yana tinqaho cikakkiyar izza mai k'arfi da take hanashi kusantar kowacce baiwa wato yana kyankyamin hada kyakykyawan jikinsa da bayi hkn suka aminta dashi, bimbii kuwa da farin ciki ta tashi tana musu albishir da Allah itama ya tsallakar da ita ta fito da budurcinta, harararta israt tayi tace" ke har wani murna kkyi sbd kin fito da budurcinki toh mu ba hk muka so ba" bimbii ta kalli israt tace" so kk daya keta min haddin budurci" khulood tace" tabbas da hk ta faru da mahassada da maqiya sun ji kunya saidai baqin ciki ya kashesu" dariya bimbii tayi ta miqe tace" wlh gwara da hkn bata faru ba don kuwa daga da hk ya faru lkcin ni kuma wata baqin ciki na zai soma" gbdy kalaman bimbii sun basu mamaki kawai kallonta suke cike da al'ajabi amma sai sukayi shiru, khulood ta kalli israt tace" ki tashi mu koma 6angarenmu kafin ummul shukri ta fahimci ba anan muka kwana ba" saurin miqewa sukayi bimbii ta rakasu har kofar shiga 6angaren nasu sannan ta dawo, baiwar gimbiya hindu zulham kuwa daman a 6angaren ta kwana don daukar rahoto aikuwa tun fitowar bimbii cikin dare daga 6angaren prince akan idanunta har fitowar da sukayi yanzu,murmushi tayi kawai wuce sum sum don isar da saqonnin ga gimbiya hindu, gari na wayewa kuwa bayi suka soma rige rigen fitowa bakin qorama suna jiran ganin bimbii ta fito wankin budurci, ita kuwa bimbii da wannan safiya ta shiga kitchen din da ake shiryawa prince abinci, bayin dake aiki a kitchen duk suka bita da kallon raini don haushinta sukeji, gaishe tayi fuskarta a sake amma cikinsu babu wacce ta amsa sai aikinsu suke, itama bata kuma tanka musu ba ta wuce cikin kitchen ta hada ruwan inibi ta sanya zuma ta dauko wani jug tamkar na zinare ta zuba ciki ta sanya qananan kofuna, duk suna kallon abunda take, bushewa sukayi da dariya, dayan da ake kira zulja ta kalli bimbii tace" yadda kk da duhun fata hk tunaninki yake mai kk dauki babban prince da zaki hada masa wannan shirmen ki kai masa hala baki iya girki bane" bimbii batace musu komai ba ta dauki faratin da jug da kofunan yake ta fice ta nufi 6angaren prince akbar, bata ganshi a ciki ba don hk ta qara gyara komai na 6angaren ta kuma sanya qamshi ta ko'ina ta gyara gadon nasa ta goge ko'ina don ummu sumayya ta fada mata aikin babbar baiwa mai hidima ga prince tana shirin fita ya shigo tare da hadiminsa ubaid, sunkuya tayi ta rissinar dakanta alamar gaisuwa, batare daya kalleta ba ya zauna abinshi ubaid na tsaye a bayansa, tana nan kan guiwowinta bata miqe shi kuwa yama mance da ita a wurin yana nunawa ubaid wasu maps, daga qarshe ya bawa ubaid maps din da batasan ko na meye ya fice dashi, sai lkcin ya kalli 6angaren da take durqushe ya kalli kuma abunda ta ajiye masa, itama sai lkcin ta tuna aikinta ta miqe da hanzari ta qarasa wurin nashi ta soma tsiyaya masa ruwan inibin a kofi, kallon ya kumayi ya kalli abunda take zuba masa yace" meye wannan?" ya nuna mata ruwan inibin da take tsiyaya masa cike da girmamawa ta sanar dashi ruwan inibi ne, yace" abunda kk iya kenan da safe" bata gane nufinsa ba tace" yana qara lfyr zuciya da faranta safiya ranka ya dade" shiru yyi be kuma mgn ba ta miqa masa ruwan inibin ya sanya hannu ya amsa ya ajiye a saman farantin, nuna mata yyi ta dauka ta fita dashi, shiru tayi kamar zatayi kuma hk ta dauka ta fita dashi ta koma kitchen, bayin dake kitchen din kuwa dariya suka soma mata har da tafa hannu,zulja tace" yanzu dai kinsan waye prince koh" fita tayi daga kitchen din don batasan me zata girka masa ba idan dai ba irin cimmarta ta rugarsu,idan kuwa tayi wannan ganganci tasan ba abune mai dadi ze biyo baya ba,kafin komai zancen rashin fitowarta wankin budurci ya karade ko'ina, wannan abu yasa sunan bimbii ya kuma fitowa cikin bayi kowa yasanta, dayawa abu yyi musu dadi musamman nasaar da shima ya sanya yar leqen asiri kuma ta kawo masa kyakykyawan labari daya sanya shi farin ciki,itama gimbiya hindu tayi dariya sosai ranta qal don hk prince akbar yake birgeta, sarauniya kuwa murmushi kawai tayi don tafi kowa sanin halin danta,ita kuwa bimbii sai yanzu take fahimtar yadda suka dauki za6en nata bada wasa ba sbd rashin qaunarsu ga baqar fata.......
Littafin nan na kudi ne idan kin shirya siye ga yadda zaki nan, zaki tura dari uku #300 ta wannan acct..0100790419,alhaji shahida nasir,union bank,saiki turomin da screesht na paymenta naki ta wannan layi kamar hk,07041195806, idan da buqatar qarin bayani ga layin kira..08080611486...
Alkalamin Bintuu ne....
10/10/20, 1:12 AM - Anti qamshi🌷: *DAREN GOMA SHA HUD'U*🪔🪔
Written By Bintuu Seer
12
*I'm waiting for you*.....
Da yamma ummu sumayya ta same bimbii ta qara karanta mata tsarin hidimarta ga babban prince, yau da dare ta fito sanye cikin wata doguwar riga kalar sararin samaniyya ta hada masa ginger tea ta sanya cikin qayatattun mazubi ta dauka ta nufi 6angaren nasa,zaune yake bisa wata kujera ya kwantar dakansa a jikin kujerar idanunsa a lumshe motsin shigowarta ne yasa ya bud'e idanunsa yana kallonta har ta qaraso wurin dayake ta ajiya abunda ke hannunta, sunkuyawa tayi ta soma tsiyaya masa ginger tea din sannan ta dago da kanta dauke da qaramin cup din tana miqa masa cike da alamun girmamawa, amsar cup din yyi ya ajiye sannan ya kalleta yace" ki koma ki qara sanin abunda nkso a wannan lkci" shiru tayi tana tunanin abunda ummu sumyya ta sanar da ita prince yake daidai wannan lkcin, kallon wata k'ofa tayi da sauri ta nufi kofar ta shiga, bece mata uffan ba ya cigaba duba wani littafi,ita kuwa bimbii tana shiga kofar taga qaton bathroom ne, cikin bathroom din ma akwai wata kusurwa da aka kame gefe gefenta da wasu shara sharan curtains farare sol, tsakiya kusurwar wani qaton kwarmin wanka ne, turarukan wanka ta gani ta ko'ina an jerasu ga fararen towels din wanka 2kala duk an ratayesu, kwarmin wankan ta cika dam da ruwan wanka sai turiri yake ta sanya turarukan wanka a ruwan da sauran sinadaran wanka don duk an koyar da ita yadda ake amfani dasu,tana gama hada komai ta fito ta tarar dashi sanye da wata rigar wanka fara sol yana jiran fitowarta, bude masa kofar bathroom din tayi ya shiga ciki ta rufe kofar ta koma ta tsaya tana jira, ba'a jima ba taji qarar qararrawa alamar dake sanar da ita prince yana buqatarta cikin bathroom, bud'e kofar bathroom din tayi ta shiga, yana cikin kwarmin wankan amma saman ruwan wankan duk kumfa ne iyakar kafadarsa kawai ake gani ya kwantar dakansa a wani qaramin matashi idanunsa a lumshe,qarasawa tayi wurin ta tsaya daidai saman kansa ta sanya hannu ta soma masa tausa a kafadunsa tana daddana masa jikinsa shi kuma idanunsa a lumshe yake yana jin dadin tausan, san can ya daga mata hannu alamar tausan ya isa, wucewa tayi ta nufi wani wuri ta dauko wasu sinadarai ta dawo wurin ta sunkuya ta soma wanke masa gashin kansa tana taje masa a hnkli sannan ta janyo wani qarami towel tana tsane masa gashin dashi shi kuwa yana riqe da qaramin cup na ginger tea dinsa yana sipping a hnkli, tana gamawa ya miqa mata qaramin cup din dake hannunsa ta juya ta fice daga dakin wanka ta koma kofa tana jiran fitowarsa, ta dade tsaye a wurin sannan taji qarar alarm tayi saurin bude dakin wankan ta shiga ta ganosa har ya gama wankan yana zaune a wata kujera dake kallon wani qaton madubi, wurin itama taje ta dauki comb ta soma taje masa gashin kan nasa sannan ta shafe gashin da mayuka gashin ya soma kyalli da sheqi, a hnkli kuma ta fara murza masa body cream a fatar jikinsa dake da yalwar gashi zarara ta ko'ina, shi kuwa yana kallonta ta jikin madubin, itakam ba madubin take kallo ba aikinta kawai take,tana kammalawa ta rissinar da kanta sannan ta juya ta fice tana sauraren fitowarsa, ba jimawa ya fito sanye da wasu kayan bacci farare masu taushi har da takalminsu sai qamshi yake mai jan hnkli, wajen wani qaramin stool ya nufa ya zauna a kujerar dake gaban stool din, matsawa tayi kusa dashi itama tana jiran umarninsa, ranar prince ya jima be kwanta ba yana karatunsa ita kuma tana zaune a gefensa, itako bimbii bacci ne fal idanunta batasan lkcin data soma gyangyadi ba, juyowa yyi yana kallonta kawai shidai tunda yake ganin bayi be ta6a ganin irin bimbii ba, motsinsa ne ya farkar da ita tayi zumbur ta miqe ta mutstsike idanunta tana satar kallonsa, tashi yyi ya tafi ya kwanta bisa royal bed nasa ya rufe idanunsa, bimbii kallonsa tayi ta turo baki gaba cikin zuciyarta tace hmm, Allah dai ya kyauta, bimbii tun tana tsammanin ze bata umarnin tfy har ta saduda don taga kamar bacci ma yake, can dai ta miqe a hnkli ta nufi kofar fita da niyyar ficewa taje ta kwanta, kofar taqi budewa, dawowa tayi wurin da take ta zauna cike da haushi, prince kuwa duk abunda take yana jinta amma idanunsa a rufe suke, ranar kwanan zaune tayi, washegari tun kafin ya tashi ta tashi nan ma bata isa ta fita ba har sai ta jira farkawarsa, tun kafin ya tashi ta soma goge goge ta qara qamshin dakin ta gyagygyara curtains din kowacce kusurwa, tunkan ya tashi saidai yana kwance be miqe ba kuma idanunsa suna rufe ita kuma sai tayi tsammanin be tashi bane, tana gama gyara wani curtains ta juyo sai kawai ganinsa tayi a zaune a bakin gadonsa ya dafe kansa da hannunsa, tahowa tayi ta sunkuya kusa dashi, dago da lumsassun idanunsa yyi ya kallonta ya qureta da idanu da idanu har saida ta tsargu tayi qasa dakanta, kasa dago dakanta tayi amma jikinta yana bata har yanzu ita yake kallo,nuna mata dakin wanka yyi yace" kije kiyi wanka" hk kawai yace da ita a taqaice yyi mgnr, bimbii miqewa tayi ta shige dakin wankan ranta a dagule don ba hk taso ba, tana shiga ta cire mayafin dake kanta ta soma taje dogon suman kanta sannan ta tayi wankan a gurguje, tsane jikinta tayi da wani towel sannan ta dauko kayan data cire ta maida jikinta ta fito ta sameshi a inda tabarshi, kallon daya ya mata yace"kije ki cire wannan kayan dake jikinki" wucewa tayi sum sum ta nufi kofar fita da niyyar ta fita taje dakinta ta sauya kayan, kofar taqi budewa, dawowa tayi ta sunkuya a gabansa tace" kofar taqi budewa" bece mata uffan ba bare tasa ran ze bata amsa ya miqe yabarta a wurin, abubuwan dake gabansa ya cigaba dayi batare daya kuma kallon 6angaren da take ba saida ya gama sannan ya juyo ya kalleta ya nuna mata wata kusurwa da hannu sannan ya juya ya shige wani wuri, kusurwar daya nuna mata ta shiga ta tarar da gbdy dakin kayan mata ne 2kala masu tsada da kyawun gaske, wata ash colour ta dauka ta sanya ta mata kyau sosa ita kanta sai qarewa kanta kallo take a jikin madubi, cikin ranta tace oh bimbii ashe zaki ganu hk, yana zaune ta fito sanye da wannan rigar kallonta yyi na wasu daqiqai sannan ya kawar dakansa, ranar yini tayi a 6angaren prince tana masa hidima batare da gjy ba, sai yamma ta fito da wasu barguna ta tafi bakin qorama wankesu, tana zuwa wurin ta hadu dasu khulood suka taho da gudu suka rumgumeta tana qarema suturar dake jikinta kallo, tana gama nata wankin ta shanya ta tayasu nasu don yana dayawa suka shanya, kamar ance ta waiga ta hango prince nasaar jikin bishiyar daya saba tsayawa ya zuba mata idanu hannunsa dukka a kirjinsa, sauri tayi ta dauke kanta tayi kamar bata ganshi ba, sun hada idanu kuma yasan sarai ta ganshi, saurin miqewa tayi zata tafi,israt ta riqo hannunta tace" ki jiramu" bimbii kuwa sauri take tabar wurin batasan su fahimci alaqar dake tsakaninta da prince nasaar amma hk ta fasa ta koma ta zauna bata kuma kallon inda yake ba, takowa yyi a hnkli ya qaraso inda suke, sai lkcin su israt suka ganshi sukayi saurin duqawa kan guiwowinsu tare da rissinar dakansu, shikam idanunsa nakan bimbii data tsuke fuska tamau,sukansu su israt mamakinta sukayi, murmushi prince nasaar yyi yace" nazo ne ina son kiyimin rakiya wani wuri" kallonshi tayi tace"wani aiki nake yanzu" yace" ki ajiye ki biyoni" be kuma cewa komai ba yyi gaba yabarsu a wurin, khulood ta kalli bimbii yace" daman prince nasaar ya sanki ne" israt tayi zagal tace" ba dole yasanta ba tana matsayin babbar baiwar prince akbar" khulood tace" hkne kuma fa" kallonsu tayi tace"ku jirani ina zuwa" bayan prince nasaar tabi suka nufi wani wuri nesa da farfajiyar gdn sarautan kusa da lambun prince akbar, kallonta yyi yace" don nace zaki zama kwarkwarata shine kk shiga za6en babbar baiwa ga prince akbar" shiru tayi kawai ya soma janta da zance har lkci yaja sosai ta kalli rana taga ta kusa faduwa ta kalleshi tace" kayi hkr lkcin aikina yyi" shiru yyi amma cikin zuciyarsa fal da kishi, yace" zaki iya tfy" juyawa tayi kamar zataji tuntu6e ta wuce cikin gdn, dakinta ta shige ta shirya tsaf ta wuce kitchen ta gyara kayan marmari ta sanya cikin qayatattun mazubi ta dauka ta wuce 6angaren prince dashi, bata same shi a ciki ba ta ajiya ta juya zata fita ya fito sanye da fararen kaya tas, binta yyi da kallo ita kuma tayi saurin yin qasa dakanta, qarasowa wurin nata yyi sosai ya kusanto ta ita dai tsaye take qam tana kallonsa,muryarsa taji yace" daga ina kk fito" tace" daga dakin da nk" tsakiyar idanunta yake kallo, ita bimbii ta rasa dalilin wannan kallo na babban prince, wuceta yyi ya koma ya zauna a wata kujera ta gabatar masa da kayan marmarin kadan yaci ya daga mata hannu,nuna mata kan bed nasa yyi yace taje ta jira a wurin, bimbii bata kawo komai ba taje tahau kan gadon tana jiransa, saida ya gama duk wani abunda zeyi shima ya nufi gadon ya hau yayi matashi da cinyarta yace" ki sanyani bacci" gaban bimbii ya soma bugawa kawai kallon prince akbar take daya dora kansa a jikinta, jikin rawa yake sosai ta kasa aiwatar da komai, shi kuma idanunsa na rufe yana sauraron ta sanyashi bacci...........
Littafin nan na kudi ne idan kina da buqatar siye ga yadda zakiyi, zaki tura #300 kacal ta wannan acct..0100790419,alhaji shahida nasir,saiki turon da screesht ta wannan layin na whatsapp.....07041195806.....idan da buqatar kira ga layin kira nan...08080611486
Alkalamin Bintuu ne....
10/10/20, 1:12 AM - Anti qamshi🌷: *DAREN GOMA SHA HUD'U*🪔🪔
Written By Bintuu Seer
13
*You black cutie skin is the glowing skin I ever seen dear*.........soft and shiny......💕
Hannunta takai zata d'ora akan sumarsa sai kuma ta janye hannun da sauri,shiru tayi tana tunani wata zuciyar ta qara jaddada mata matsayinta ba kowa ita face baiwa mai hidima ga wannan d'an sarki bata da y'anci masa gardama, cikin dokokin da ummu sumayya ta sanar da ita shine komai prince yakeso dole ta masa a matsayinta na baiwarsa, ba shiri ta komar da hannunta saman sumarsa ta cusa hannunta ciki tana barbaza masa gashin cikin yanayi na kwantar da hnkli, shidai prince idanunsa na rufe ya amsar saqonninta, cikin sanyin murya ta soma bashi labari na qasashen africa tare da yanayin al'adunmu, abunda yasa ta za6i hk sbd tana yawan ganinshi yana karanta littattafan tarihi wato mutum ne ma'abocin son tarihi, tana ta bashi labari yana jinta duk da idanunsa a rufe suke, gani tayi kamar yyi bacci ta gyara zaman lumtsatstsen pillownsa ta sauke kansa a hnkli daga jikinta ta mayar dashi kan pillown sannan ta fara yunqurin sauka daga kan gadon, caraff, taji ya riqo hannunta batare daya bude idanun nasa ba yace" ina zakije,ki taho ki cigaba da bani labari" dawowa tayi ta kuma zama tana ta bashi labarin bata kuma yunqurin guduwa ba, shi mamakin bimbii yake cikin ransa sbd duk bayin da yake yayi kowacce saita sanya duk wata hikima da dabararta na ganin ta jawo hnklinsa kanta ya kusanceta, itako bimbii yana karantarta bata ta6a gwada wannan hikimar ba kuma ba wata alama dake nuna bimbii tana da feeling akansa, dalilin dayasa duk ahekara yake sauya baiwa shine yawancin bayin nasa basa iyawa dole sai sun afka soyayyarsa har su fara nuna masa feeling dinsu a bayyane batare da sukansu sun ankara ba, shi kuma yana ganin hk yake sauyasu sbd yana guje musu fadawa tarkon mahaifinsa sarki abdallah bin jabal don baya daukan irin hk da wasa, idan har abu ya bayyana baiwa ta fara soyayya da jinin sarauta a wannan masarauta toh fa tsatstsauran hukunci ne yake hawa kanta batare ko digon tausayi ba, duk bayin da prince akbar yake sauyawa toh soyayyarsu suka fara nuna masa a bayyane shi kuma yake jiye musu wannan hukunci sai ya sauyasu kafin su zurfafa har abu ya fito fili, duk cikin masarautan babu wanda yasan wannan dalili nasa, bimbii kuwa be ta6a ganin alamun hk daga gareta ba duk da hk dai yana ganin kamar zuwa gaba itama zata bi sawun afkawa kogin sonshi,bimbii kam sai labaru take bashi amma yyi shiru bece ya isa ba, tun tana daure bacci dayake kawo mata farmaki har ta soma gyangyadi, shikam beyi bacci ba idanunsa ne kawai a lumshe, jin tayi shiru ne ya bude idanunsa sai ganinta yyi ta jingina bayanta da jikin gadon nasa sai baccinta take, fuskarta ya qurawa idanu sai lkcin ya gano tsantsar kyawun halitta irin na bimbii, tashi yyi zaune ya cire mata mayafin data rufe kanta dashi sbd taji dadin bacci, abunda ta tufke tulin gashin kanta ya cire gashin ya sauka mata a gadon baya, gyara mata kwanciya yyi ya kwanta da ita a gefensa sannan yaja musu bargo, bimbii kuwa duk wannan abu batasan ya faru ba kawai baccinta take hnkli kwance, haba ku kuwa ba dole bimbii ta lula duniyar bacci ba yadda ta samu kwanciya a wannan gadon na alfarma mai shegen taushi ga bargo duniyar kule gashi duk ta inda ta juya qasautaccen qamshi take shaqa mai cire damuwa da kwantar da hnkli,shikam yana kwance ne wuri guda yana kallon sama ya dora hannayensa akan cikinsa ita kuwa bimbii sai wani birgima take da gyara kwanciya har ta matsa kusa dashi sosai bata sani ba, kallonta kawai yyi ya dauke kansa, bimbii tana farkawa ta tsinci kanta a cikin bargo kuma alamu sun nuna kamar ba ita kadai bace a ciki, hannunta saka tana lalibe ba zato ta shafa fuskarsa da hannun nata, wani uban ihu ta saka tare da yaye bargon sai ganinta tayi a gadon prince akbar ashe tare ma suka kwana dashi, salati tayi ta soma shafa jikinta tamkar wata mahaukaciya shi kuwa yana jinta shiru kawai yyi amma abunda take ne yasanya shi yin murmushi, tashi yyi zaune aikuwa tana ganin ya tashi tayi wani irin tsalle ta dire qasa ta kife akan guiwowinta tace" don Allah kayi hkr wlh ban san lkcin da bacci ya daukeni bane na kwana mk a gado" kallonta yyi yace" hkn ya nuna baki san aikinki bane shiyasa kk bari bacci ya dauke ki" fashe masa tayi da kuka tace" don Allah kayi hkr wlh bazan sake ba" be sake mgn ba ya sakko daga gadon, miqewa tayi da sauri gudun kar ta kuma aikata wani laifin 2kwata ta mance babu mayafi akanta ta shige dakin wanka ta soma shirya masa ruwan wanka sannan ta fito shi kuma ya taso yazo ze shiga dakin wankan, tsayawa yyi ya dora mata mayafinta sannan ya shige abinsa, saurin gyara mayafin tayi, ba jimawa taji qarar qararrawa, saurin tura kofar bathroom din tayi ta tarar dashi cikin kwarmin wankan ruwan sai fitar da tururi yake ga kumfa ta rufe saman ruwan,tausa ta soma masa da hannunta da yake jin taushinsu sosai sannan ta wanke masa sumar kansa, tana gamawa ta fita saida ya kuma danna wannan alamar tukun ta kuma shigowa ta qarasa gyara masa gashi ta shafe gashin da mayuka, har da gyaran fuska ta masa ranar ta qara fito masa da sajen daya zagaye fuskarshi, shima kansa cikin ransa ya yaba da gyaran nata sannan ta fara murza masa cream kamar kar ta dena hk yakeji har ta gama, rissinar dakanta tayi sannan ta juya ta bude kofa ta fita tana jiran fitowarsa, ya jima kafin ya fito sanye da wasu pakistan kalar sararin samaniyya yyi kyau sosai sai fitar da qamshi yake sumarsa ko sai daukar idanu yake, zama yyi a wata kujera ya kalleta ya daga mata hannu alamar ta tafi, rissinar dakai tayi sannan ta juya ta nufi hanyar fita daga 6angaren shi kuma yabita da kallo har kofa ta bude ta fice, dakinta ta wuce tayi wanka ta shirya cikin wata jar doguwar riga tare da mayafinta, tayi kyau sosai don fatarta ta fara murjewa sbd yanayin cimmar da take samu tana ci ga kuma makwanci mai kyau, kitchen ta tafi tana shiga taji bayin kitchen din na qus qus ita dai bata tasu take ba ta, honey tea ta masa ta sanya ginger kadan ta dora a faranti na alfarma ta nufi 6angaren nasa, tana shiga ta tarar dashi yana rubutu batasan rubutun me yake ba dai ta ajiye masa honey tea din a gabansa, ajiye abun rubutun yyi ya dago da idanunsa yana kallonta saurin dauke kai tayi tare da rissinar da fuskarta sannan ta soma tsiyaya masa honey tea din a qaramin cup ta dago da fuskarta tana miqa masa cup din, abunda ya bata mamaki shine ba cup din da take miqa masa yake kallo ba ita yake kallo kuma wani irin kallo yake mata wanda ta kasa tantance ma'anarsa don bata saba ganin irin kallon cikin kwayar idanun jama'a ba, riqe cup din tayi ta sunkuyar dakanta qasa, hannunsa yasa ya amshi cup din ya soma sipping a hnkli tare da lumshe idanunsa, ajiye cp din yyi ya tashi ya tafi gaban manya manyan windows dake rufe da wasu kofofin glass ya tsaya tare da kalmashe hannayensa ta baya ya qurawa glasses din windown idanu, bimbii kallonsa tayi kawai ta fahimci kamar akwai abunda ke damunsa, cikin qarfin hali ya taho wurin dayake tsaye cikin sanyin murya tace" koh akwai abunda yarima yake buqata ne" bece mata komai ba kuma juyo ya kalleta ba, ganin hkne yasa ta koma ta dauki farantin ta fita dashi, tana fita ya juyo yana kallon kofar, komawa yyi ya zauna ya lumshe idanunsa yana fitar da wata zafaffiyar ajiyar zuciya, hk abu ya cigaba da tfy tun bimbii tana tsarguwa idan prince akbar ya qureta da idanu har ta saba da kallon nasa ta dau hkn ko shima duk yana daga cikin al'adarsu wato kallon qurilla, prince nasaar shima ya takurawa bimbii har ta soma shakkar zuwa qorama don baya gjy da zuwa wurin musamman sbd ita, bimbii yanzu wannan shegen tsoron nata ya soma raguwa ta soma zama jarumar mata, prince nasaar baya ta6a samun sakin fuska a wurin bimbii shi kuwa baya zuciya don har ga Allah son bimbii yake irin sosai din nan, sai ya shafe kusan awanni yana jiran fitowar bimbii bakin qorama wanki, israt da khulood kuwa saida bimbii ta samar musu da alfarma suka dawo 6angaren prince da bauta suka shiga jerin bayin dake aiki a kitchen, musamman bimbii tace su dawo dakinta da kwana hk suke kwana su uku kamar yadda suka saba,khulood ita ta din ga koyar da bimbii girke girke irin nasu na larabawa daban daban yanzu ta kware sosai a fagen girki, israt kuma ita take koya mata waqoqi iri daban daban, suna taimaka mata sosai, yau suka tashi cikin tsantsar rudani sbd samun labari da sukayi za'a jefe yan matan bayin da sukayi ciki, hanyar 6angaren prince bimbii tayi da gudu bayin dake tsaron kofar suka qi bude mata kofa suka sanar da ita prince baya buqatar ganin kowa, shi kuwa yana tare ne da hadiminsa ubaid suna tattaunawar sirri, bimbii kuwa hk ta din ga jira amma shiru babu alamun zasu bude mata kofar, juyawa tayi ta koma ta nufi bakin qorama, bata jima da zuwa wurin ba prince nasaar ya bayyana shima, tana ganinsa ta miqe kamar zataci tuntu6e ta nufi wurinsa shima abun ya bashi mamaki ya bita da kallo, kallonsa tayi ta sunkuya bisa guiwowinta a gabansa tace" don Allah ka taimakamin ka cetomin yar uwa tana cikin yan matan da za'a jefe yau" shiru yyi sai kuma ya kalleta da murmushi yace" wannan alfarma tana da wahalar gaske sbd sarki abdallah dakansa ne yasa hannu a jefesu babu wanda ya isa ya dakatar da hk duk cikin masarautan nan amma...." sai kuma yyi shiru tace" amma me?" yace" zan iya sanyawa a saceta akaita masarautarmu saidai wannan tamkar qunar bakin wake ne da tarar aradu da fadin kai don idan har aka samu mtsl toh gsky nikaina ina cikin mtsl amma karki damu zan iya yin komai sbd ke sbd na yarda da ingancin soyayyar da nk miki" kallonsa tayi da mugun mamaki ta nuna kanta tace" so kuma?" daga mata kai yyi alamar ehh, tace"don Allah ka dena fadar hk bani so" yace" baki sona kenan" tace" Aa, amma tsakanimu akwai bambanci mai karfi wanda yyi mn iyaka kayi hkr" murmushi yyi yace"bana mgn biyu kuma duk abunda nakeso babu makawa sai na same shi komai wuya ki fahimci hkn" bimbii sake baki tayi tana kallonshi tana waiwaye kar wani ya ganta tare da dan sarkin, takawa yyi ya wuce ya haye dokinsa yabarta a wurin,ranar ta makara sosai na zuwa 6angaren prince shi kuwa yana kallon kofa yaga shigowarta amma shiru sai yanzu taxo ta tarar ya bada umarni kar bayin dake tsaron kofarsa su barta ta shigo,qememe suka hanata shiga hk ta juya ta koma dakinsu ta tarar dasu israt sunyi jugum jugum ita ta zauna gefensu tayi shiru, tmbyrta israt tayi koda wani kyakykyawan labari, shiru tayi sannan ta zayyana musu yadda sukayi da prince nasaar, shiru sukayi don tabbas sun san wannan matakin yana da girma, kallon bimbii khulood tayi tace"kuma shi da kansa ya sanar dake ze miki wannan alfarma, gsky yaudararki yake don kuwa wannan abu mataki ne mai tsauri mai cike da kasada" duk abunda suke zantawa lenah na la6e tana jinsu, cikin sauri ta nufi 6angaren prince akbar jikinta har rawa yake, bata samu ganin prince ba sai ubaid ta samu ta zayyane masa abunda taji su bimbii na zantawa,batare da wani 6ata lkci ba ubaid ya shiga 6angaren prince ya tarar dashi a zaune, sunkuyawa yyi daidai kunnensa ya rada masa abunda lenah ta sanar dashi, shiru yyi sannan ya miqe dakansa ranar ya nufi 6angaren prince nasaar, cike da mamaki prince nasaar ya kalli babban prince don yasn ba qaramar mgn bace ta kawo shida kansa har 6angarensa, baiwarsa ce ta kawo musu green tea duk suka zauna a wasu kujeru suna fuskantar juna, prince akbar ya kalli prince nasaar yace" ina son ka janye kudirinka da kk dashi na shirin sace daya daga cikin bayin da aka zartas musu da hukuncin jefawa don ba zaka samu nasara ba kuma yin hkn tamkar hada masarautu biyu fada ne" cike da mamaki prince nasaar ya dago dakai yana kallon prince akbar, mamaki yake a ina yaji wannan sirrin dayasan duk duniya bimbii ce kawai ta sani toh ko ita ta sanar da babban prince wannan zancen, murmushi prince akbar yyi masa yace"ina baka shawara kar ka sake kayi wannan kuskuren don ba riba cikinsa kuma zaka sanya rayuka dayawa cikin qunci" har prince akbar ya gama jawabinsa be furta komai sai daga qarshe kawai yyi murmushin yaqe yace" zan so naji a ina prince yaji wannan labari na qanxon kurege duk da nasan cewa kai mutum mai taka tsantsan" murmushi prince akbar yyi tare da miqewa yace" ni zan wuce fata dai kayi aiki da hange don qaramar mgn kan iya zama babba" hk prince akbar yabar prince nasaar cike da tunani, washegari bimbii ta shiga kitchen ta shirya abun sha ta nufi 6angaren prince tana zuwa kofa ta bude mata ta shige, yana ganinta yyi saurin dauke kansa ya cigaba da abunda yake batare daya ba shigowar nata wani muhimmaci ba......
Littafin nan na kudi ne, idan kina da buqata zaki tura #300 ta wannan acct...0100790419,alhaji shahida nasir,union bank, saiki turon da screesht na payment naki ta whatsapp da wannan layi..07041195806....idan kuma da buqatar kira ga layin kira nan..08080611486
Alkalamin Bintuu ne......
10/10/20, 1:12 AM - Anti qamshi🌷: *DAREN GOMA SHA HUD'U*🪔🪔
Written By Bintuu Seer
14
*You break my heart*.......
Ita kanta jikinta yyi sanyi yanayin yadda taga yyi mata, qarasa tayi ta ajiye farantin dake hannunta tare da rissinar dakanta qasa, saida ya gama duk abunda yake sannan ya dago idanunsa yana kallonta ba zato taji muryarsa yace" jiya ina kkje" shiru tayi sai kuma tace" na tafi wanki qorama" tsayar da kwayar idonsa yyi akan fuskarta yace" sai kuma kk tsaya a ina" tsoro ne ya soma shigarta muryarta har rawa take tace" ba....bu...k..o.ina" tayi mgnr ne a daburce kuma cikin qinqina, murmushi yyi yana qare mata kallo ita kuma kanta na qasa, miqewa yyi ya nufi wurin windows din daya soma tsayawa hannayensa dukka yyi folding nasa a baya, batare daya juyo ba yace"me ya hadaki da prince nasaar" innalillahi wa'inna ilaihir rajuna.....abunda ta furta kenan kuma a bayyane sbd razana da tayi ta marairaice fuska kamar zatayi kuka gashi dai ba damar musawa sai ta sunkuya bisa guiwowinta tare da rissinar dakanta qasa alamar dake nuni data amsa laifinta, juyawa yyi ya koma ya zauna ta taso da sauri ta soma tsiyaya masa herbal tea din data hada masa, yace" kar ki sake sanya kanki cikin abunda be shafe ki ba" rissinar dakanta tayi tare da miqa masa cup na tea din sannan ta koma bayansa ta tsaya ta sanya hannunta a kafadarsa ta soma daddana masa jiki tana masa tausa, murmushi yyi sbd yasan abunda yasa tayi hkn sbd tasan tayi laifi ne, bece mata uffan ba ya cigaba da sipping tea nasa, daga mata hannu yyi alamar ya isa hk ta tafi, sum sum ta wuce ya bita da kallon wutsiyar ido, komawa tayi dakinta ta zauna tayi shiru gashi su khulood basu nan, tunanin abunda prince ya fada mata yanzu, gani tayi kamar yana da masaniya game da plan dinsu da prince nasaar shiyasa yake mata mgn cikin shagu6e, dafe kanta tayi kawai cike da tsantsar fargaba, shigowar wata baiwa ce ta sanyata dago da kanta, kallon bimbii baiwar tayi tace" prince nasaar yana da buqatar ganinki, kallon baiwar baiwar tayi sosai sannan ta miqe tabi bayanta, tfy sukayi mai tazara sannan suka shiga 6angaren prince nasaar, lambunsa ta wuce da bimbii sannan ta juya ta koma bakin aikinta, bimbii koh ta qarasa ciki, ganinsa tayi zauna akan wani farin dutse fuskarsa babu yabo ba fallasa, rissinar dakanta tayi alamar girmamawa ga prince din,yace" kece kk fadawa prince akbar plan din dana shirya na sace wannan baiwar" shiru bimbii tayi cike da mamaki sai kuma tace" Aa,bani bace" yace" amma kin sanar da wani koh" tace" ehh,munyi mgnr da yan'uwana amma tabbas nasan sukam basu sanar da kowa" yace"meyesa kk fadawa wani bayan na fada miki wannan mataki yana da tsauri kuma rashin nasara babban barazana ne" tace" an samu mtsl koh" shiru yyi yana nazarinta sai kuma yace" prince akbar yazo ya same ni akan wannan mgn kuma yace na dakata idan kuma ba hk ba za'a samu matsl" shiru bimbii tayi kamar zatayi kuka tace" babu komai" yace" zaki iya tfy" a hnkli kamar kazar da qwai ya fashewa a ciki ta juya ta soma tfy har ta fice daga lambun ta nufi sashinsu, tana shiga ta tarar su israt sun dawo, zama kusa dasu tace" bansan ya zamuyi ba an samu mtsl" dukkaninsu suka dago kai a razane don sunyi tunanin koh wurin aiwatar da plan din ne aka samu mtsl, bimbii ta kallesu sosai ta sanar dasu abunda ya faru, duk aukayi shiru suna tunanin waye kuwa ya sanar da prince wannan mgn, bimbii tace" ba abun mamaki bane don prince ya samu labari don yana da tsatstsauran tsaro da kuma tsananin taka tsantsan" israt tace" amma duk da hk alamu sun nuna akwai wadanda suke mn la6e" bimbii tayi shiru tana nazari kan mgnr israt, tace" toh yanzu meye mafita" duk sukayi shiru, suna cikin mgn sukaji sanarwa kowa ya fito wurin jifan bayi, dukka suka miqe a zabure suka fita, wani shararren fili ne me dauke da rairayi sosai nan aka fito da yan matan su ashirin da biyu wasu daga cikinsu sun haife cikin dake jikinsu wasu kuma basu haife ba, sai lkcin bimbii ta ta6a tozali da sarkin abdallah bin jabal dake zaune a wata kujera ta alfarma a can saman wata matattakala cikin wani tanti, farin balarabe ne tas yana da yalwar dogon farin gemu ga hancinsa dogo dodar amma ya manyanta sosai hannunsa riqe da sandar sarauta, sanye yake cikin wata alkyabba dark brown da jan rawani mai adon fari da ja, gefen hannunsa na dama prince akbar ne sanye yake shima cikin farar jallabiya da rawaninsa baqi da fari dayan 6angaren hagunsa kuma ragowar ya'yan sarakuna ne sai ministocinsa da y'an majalissar zartarwa, bayi kuma na tsaye cirko cirko daga qasa suna jiran ganin abunda za'a aiwatar kan wadannan yan matan, wasu manya manyan bayi majiya qarfi suka kukkunce yan mata suka soma haurawa dasu saman wani gini suka kuma daddaure a jikin wani qarfe, bimbii idanunta ne ya saukan akan lailah wacce hawaye ya gama 6atawa fuska tana daure ita jikin qarfen, fashewa bimbiii tayi da kuka suma su khulood duk kukan suke, sai yanzu bimbii ta tabbatar da zalinci a wannan masarauta tayi Allah tirrr da wannan al'ada tasu, prince akbar ne ya miqe dakansa ya nufi inda aka daure yan matan ya kallesu daya bayan daya sannan ya bada dama a soma jifansu, murmushi sarki abdallah bin jabal yyi lkcin da aka soma aikawa yan mata da saqonnin duwatsu, jifansu ake ta ko'ina, bimbii rufe idonta tayi qam tare da qanqame jikinta tamkar ita ake jifa, bayan an gama jefesu ne aka sakko da gawarwakinsu qasa abun gwanin tausayi, batare da bata lkci ba sarkin abdallah bin jabal ya tashi yyi jawabin gargadi ga duk wanda ya kuma aikata wannan abu sannan suka soma sakkowa daga matattakalan sai darewa ake ana basu hanya suka wuce zuwa fada, bimbii kafafunta kasa daukarta tayi ta zube bisa rairayin tana kukan zucci don tayi na filin har ta qoshi, rashin amfaninta kawai take gani tunda gashi ta kasa ceto rayuwar lailah, dakyar su khulood suka jata suka koma 6angarensu, bimbii tunda ta shiga dakin bata fito ba har dare sai da daren ta fito takaiwa prince dinner, tunda ta shiga ta ganshi zaune yana ta rubuce rubucensa ta ajiye masa dinner din wata kusurwa mai yalwar shimfidadden centre carpet da ado, kunsan mafi yawan larabawa sun fi son cin abinci a zaune bisa shimfida,tunda ta shigo ya lura sam babu annuri a fuskarta tayi mugun tsare gd, be kuma kallonta ba ya cigaba da gudanar da abunda yake, bayan ya gama ne tayi abunda ya kamata na al'adar wankansa ya fito cikin shigar bacci sannan ta tsaya har yaci abinci sannan ya bata umarnin tfy, tana komawa 6angaren nasu taga su khulood na jiranta don ta sanar dasu cikin dare zasu ruwan da aka watsa gawarwakin su lailah su mata kallon qarshe,dare nayi sosai suka saci jiki suka nufi wannan ruwa dayake nesa sosai daga wannan gd na sarauta amma duk cikin masarautan ne, gawarwakin na nan basu gama wucewa ba, tattare rigunansu sukayi suka soma shiga cikin ruwan suna lali6e ko Allah ze basu sa'ar gano gawar layla, khulood ce ta soma ganin gawar ta kirasu suka zo wurin da sauri, bimbii ta ta6a gawar, dago fuskarta tayi da sauri tace" kamar tana da sauran numfashi" israt ta dora kanta taji kamar alamun zuciyarta na buga a hnkli, kallonsu tayi tace" tabbas akwai alamun numfashi tattare da ita yanzu meye abunyi, shiru sukayi suna tunanin ina ya dace su dosa da gawar laylan tunda sunji kamar tana numfashi,jan gawar suka somayi suka kaita bakin wata bishiya, dukkaninsu sunayi suna 2kalle gudun kar wani ya gansu,bimbii tace" tana buqatar taimakonmu ina ya dace mu kaita inda ba za'a kamamu ba" suna kan shawara sukaji sawun dawakai sun nufo wurin da suke,take gabansu ya fara dokawa tara tara.......
Littafin na kudi ne gamai buqata za'a tura #300 kacal ta wannan acct...0100790419,alhaji shahida nasir,union bank, sai a tura screesht ta whatsapp ta wannan layin...07041195806.......
Alkalamin Bintuu ne...
10/10/20, 1:12 AM - Anti qamshi🌷: *DAREN GOMA SHA HUD'U*🪔🪔
Written By Bintuu Seer
15
*I never care about the difference betwee us*....my only concern is you to accept me as your companion💕
Wasu ne daga cikin dakarun dake tsaron gdn sarautar, suna kewayawa ne ta ko'ina cikin wannan masarauta don tabbatar da tsaro, tun kan su qaraso wurin da suke, khulood ta kallesu tace" muna cikin rikici fa idan suka ganmu"neman wurin 6uya suka somayi amma duk wurin babu wurin da zasu iya 6uya,israt ta kallesu a rikice tace" mu haye bishiya kawai" aikuwa kafin ta rufe baki sai ganinsu tayi sun rigata hayewa bishiyar dayake bishiyar tana da yalwar ganye kuma ga duhu, hkn yyi daidai da qarasowar dakarun wurin, ganin gawar layla da sukayi ne a gindin wannan bishiya yasa duk suka ja limzamin dawakansu suka tsaya, babban cikinsu ne ya fara sakkowa daga saman dokinsa sannan sauran ma duk suka sakko, duba gawar sukayi cike da mamaki don tabbas sun gane gawar na daga cikin gawarwakin yan matan da aka jefe yau, abunda ya basu mamaki shine wanda ya jawo gawar daga cikin kogi ya kawota wurin bishiyar nan, 2waige suka soma ko zasu gano wata alama dake nuna da wani a yankin wurin amma basu ga komai ba kuma basu ji motsin komai ba, babban cikin nasu ne ya gano alamar sawun kafar su bimbii dayake wurin rairayi ne, bin sawun ya somayi har ya gano daidai wurin da sawun kafar tasu ya tsaya, su bimbii kuwa dake maqale akan bishiya tuni cikinsu ya duri ruwa,israt kan rufe idanunta tayi kawai tana addu'ar Allah ya fisshesu ya rufa musu asiri kar su gano su,babban cikin nasu ya kalli sauran yace" su duba kan bishiya" israt tana jin hk ta saki fitsari a wando, bimbii da khulood kuwa sun sadaqar kawai mutuwarsu tazo,duk sunyi 2tsuro a maqale akan bishiya suka ga dakarun nan sun soma qoqarin hawowa bishiyar, daidai lkcin wani mahayin doki ya bayyana, takun sawun dokin nasa ne ya janye hnklinsu daga hawa bishiya duk suka juya suna kallonsa sanye yake da baqin kyalle ya rufe rabin fuskarsa, wucesu yyi da gudu bisa dokin nasa,hkn da suka gani ne ya janye hnklinsu suka haye dawakansu suka rufa masa baya,hknne yaba su bimbii damar sakkowa daga kan bishiya duk da hk zuciyarsu tana tsananta bugawa, sake ta6a gawar layla sukayi suka ji 2kwata ta dena numfashi alamar rai yyi halinsa, dukkaninsu kuka suke suna tfy suna waiwayen gawar layla babu halin su mata suttura hk suka bar wurin cike da taka tsantsan kar a gane takun sawunsu har Allah ya basu sa'ar komawa 6angarensu, suna shiga daki suka rufe da sakata suka hau gadonsu da gudu suka ja bargo suka rufa dashi zuciyarsu na cigaba da bugawa 2tara don gani suke kamar basu tsira ba, aikuwa basu jima ba sukaji ana buga musu kofa kamar za'a 6alla, bimbii ta rada musu kar ku sake koma waye ku bari a gane alamun tsoro ko rashin gsky a fuskokinku ku aro jarumta idan har kuna son tsira,raggo baya zama gwani damu mutu ragwaye gwara mun mutu jarumai, wadannan kalmomi su suka sanya wata sabuwar jarumta ta shigesu tashi guda, bude kofar sukayi fuskarsu da alamun nuna bacci, masu tsaron farfajiyar gdn ne suke bi daki daki na bayi don tabbatar da kowa yana cikin dakinsa a kwance, suna ganinsu suka wuce zuwa daki na gaba hk suka din ga zagaye cikin wannan dare, su bimbii kuwa rufe kofarsu suka sakeyi suna sauke ajiyar zuciya don da bayin sun zo kafin su dawo suka ga basu nan toh asirinsu ya gama tonuwa kenan sbd sai sun bincika su ga inda sukaje da wannan dare, komawa sukayi suka kwanta amma cikinsu babu wanda ya iya rintsawa don zuciyar har yanzu tana cike da fargabar abunda ze faru gobe,6angaren dakarun da suka bi bayan wannan mahayin dokin kuwa basu samu damar qarasawa wurinsa ba ma bare su iya kintata siffarsa sbd kwarewarsa wurin iya gudu da doki tashi daya ya 6ace musu suka rasa inda yyi babu irin duban da basu masa ba, dole suka koma wurin bishiyar nan suka ga ba gawar da suka bari a gindin bishiya, hkn ya basu mugun mamaki, kogin da aka watsa gawarwakin nan suka nufa suka tarar ruwa yyi gaba da kusan dukkan gawarwakin yan matan sai kadan kuma cikin kadan din da sukayi saura babu mai kama ma da wannan gawa da suka gani a bakin bishiya, so suke su gano asalin gawar sbd su bincika makusantan ta amma basu ga gawar ba, hk suka juya suka bar wurin amma sun sanar da dukkanin sauran dakaru masu tsaron masarautar su sanya idanu sosai kan kowanne lungu da saqo na masarautar, washegari su bimbii suka tashi suka shirya kowacce ta nufi wurin aikinta, sun 6oye duk wani tsoro nasu, bimbii sanye take cikin wata farar doguwar riga mai ado da kyalkyali, gashin kanta kuwa yasha gyara na musamman, kunnuwanta sanye da wasu manyan yan kunne masu kyau,hannunta kuma da wasu awarwaro, kitchen ta shiga ta hada abinci kala, bayin dake aiki a kitchen sai kallonta suke a yatsine, bimbii tana aiki ne cike da tsantsar takan tsan tsan, bata matsawa konan da can saita gama shirya komai sbd tsaro da kuma gudun kaidi da makirci na gdn sarauta, wani qaton basket ta dauka mai kyau ta soma sanya mazuban dake dauke da abincin a ciki ta dauka ta nufi 6angaren prince dashi, tana zuwa kofa ta bude ta danna kai ciki, yana zaune a wata royal chair yana rubuta wata wasiqa yana gama rubutun wasiqar ya dauki hatimin gdn sarautar burham ya danna a jikin wasiqar sannan ya rufe takardar ya sanyata cikin wani qaramin akwati, dago da kyakyawan idanunsa yyi yana qare mata kallo, ita kuwa tayi saurin yin qasa da kanta alamar girmamawa gareshi sannan ta wuce inda yake cin abinci ta soma jera masa abincin data shigo dashi shi kuwa rakata yyi da kallo kawai, bayam ta gama ne ta dawo wurin dayake tace"komai ya kammala" bece mata uffan ba ya tashi daga inda yake ya nufi wurin shimfidar alfarmar da abincin ke jera ya zauna, wurin itama taje ta soma zuzzuba masa abinci a qananan plate yana bin kowanne yana ci 2kadan, bayan ta gama bashi abinci ya koma ya kwanta akan gadonsa yace"tazo ta masa tausa" kwanciya yyi ruf da ciki ita kuma tana tausa masa baya, cikinsu babu mai mgn sai qarar awarwaron hannunta, muryarshi taji yace" ina sake ja miki kunne da ki guji sanya kanki a fitina idan kuma ba hk ba wataran zakiyi nadama mara amfani" saurin kallon fuskarsa tayi taga idanunsa a rufe suke yake wannan mgn, cike da jarumta ta 6oye tsoronta tace" zan cigaba da kiyayewa ranka ya dade" shiru yyi be kuma cewa komai ba ita kuma zuciyarta cike take da tunanin wannan mgnr ta prince, shi baya furta mgn kai tsaye saidai yyi shagu6e yabarka cikin tunani, tayi nisa cikin tunanin mgnrsa har ta dakata da tausan da take masa batare data ankara ba, shi kuwa yana ji ta dakata da tausan da take masa yasan tunanin abunda ya fada mata yanzu take, hannunsa yasa ta baya ya riqo hannayenta ya murzasu da karfi,saurin kallonsa tayi taga idanunsa a lumshe suke kuma yaqi sakin hannun nata, qoqarin janye hannun nata take a hnkli cikin dabara da hikima ya bude idanunsa ya saukesu akan fuskarta, yanayin yadda taga idanun nasa yasa tasha jinin jikinta tayi saurin sunkuyar dakanta qasa,ya jima yana mata wannan kallon qurullan da har yanzu ita ta kasa gane ma'anar kallon sai ta dauki hkn a matsayin al'adar prince akbar,yace" ki shirya zaki rakani wani wuri" rissinar dakanta tayi alamar amsa umarnin nasa,sakin hannunta yyi ya mata alama data tafi, sauka tayi daga kan tafkeken gadon nasa ta sake masa shara shara curtain din dake kame ta koma can wani gefe ta durqusa kan guiwowinta tana jiran fitowarsa, ya jima a kwance kuma ba bacci yake ba idanunsa biyu,babban hadiminsa ubaid ne ya shigo ta sanar dashi bazai samu ganin prince yanzu ba yana kwance,komawa yyi bakin kofa ya tsay yana jiran lkcin tashinsa, yana jinsu amma akwai abunda ke damunsa ne kuma yake tunani akai shiyasa yakeson kadaici, saida ya dade a kwance sannnan ya tashi ya shirya cikin wasu fararen kaya hatta rawanin kan nasa shims fari ne sol, ubaid ne ya shigo ya tsaya a wurin kujerar da prince yake ya rissinar dakansa sannan ya dago yace" komai ya tafi yadda ya kamata" ita tana tsaye daga gefe abunda taji ubaid ya fada kenan, prince ya daga masa hannun alamar shikenan, sake rissinar dakansa yyi sannan ya juya ya fita ya tsaya a bakin kofa yana jiran fitowar prince, daukar wani qaramin box yyi mai kalar ja ya miqa mata, sunkuyawa tayi ta amsa box din, bece mata komai ba ya miqe yyi hanyar waje shima tabi bayansa da sauri, a keken doki aka daukesu suka tafi wurin taron, sarki abdullah bin jabal ne dakansa ya shirya wannan qasaitaccen taro wadanda ya samu halarta wasu daga cikin manyan sarakuna na wannan nahiya, taro ne na cikarsa shekaru hamsin da tara akan mulki, masarautar burham kuma tana da shekaru dari uku da sittin da uku da kafuwa, wurin taron ya qayatu da shiri na alfarma ga kuma jini na sarauta masu ji da kansu da taqama da cikakkiyar izzah ta sarauta duk suna hakimce bisa kujeru na alfarma, ko'ina ka hanga hasken farar fata kk gani suna mgn da yaren alfarma wato harshen larabci, bimbii dai tana bayan prince akbar dayake wani babban jigo a taron, ubaid kuma yana daga gefensa na dama hk suka rakasa mazauninsa ya zauna, wurin bimbii taga bayi dayawa wadanda suke baqar fata maza da mata amma yawancinsu qasqantattun bayi ne, gimbiya hindu na daga gefe tare take itama da wasu ya'yan sarakuna,ganin bimbii a bayan prince yasa abun ya bata haushi ta kuma shirya yadda zata toxarta bimbii a taron kowa ya shaida, kade kade ne ya soma tashi a wurin irin nasu na larabawa, prince akbar kuwa duk sakan daya sai ya waiga yaga ko bimbii na nan, ubaid yana lura dashi yyi mamaki sosai na ganin yadda babban prince ya damu da lamarin bimbii, yana lura da yadda yake yawan kallon bimbii hkn tamkar wanin baqon hali ne cikin halayyar prince din don yadda ya sani prince akbar yana da cikakkiyar izzar da baya yiwa abu kallo biyu musamman mace, macen ma baiwarsa, baiwar ma wacce suke kira mara asali jinsin baqar fata, taro yyi taro sai shagali ake da kuma shan shayi irin nasu na al'adar larabawa, gimbiya hindu ce ta tashi ta nufi wurin sarki abdallah bin jabal tadan rissinar dakanta kusa dashi tace" Allah yaja zamaninka sarkin masu adalci baqinmu na da buqatar babbawar baiwa ga prince akbar ta fito ta nishadintar dasu da waqoqi masu dadi don kwararriya ce a wannan fannin" murmushi sarki abdallah yyi ya juya ya kalli badakaren dake bayansa yace" ya sanar ana buqatar babbar baiwar ga prince akbar ta fito ta nishadintar da taron da salonta" batare da 6ata lkci ba wannan badakaren ma'abocin babbar murya ya soma shela cikin muryarsa data karade wurin,prince akbar yana jin wannan sanarwa ransa yyi masifar 6aci sbd bimbii babbar baiwarsa ce dole saida izininshi zata aiwatar da wani abu amma ganin daya yyi babban bawan mahaifinsa ne yake wannan sanarwa yasan umarni ne daga wurin sarki abdallah dakansa,shiru yyi don ba yadda ya iya, bimbii ko gabanta ne ya yanke ya fadi tana tsoron fita gaban wadannan bunqasassu masu fama da izzar mulki, wasu bayi ne suka xo suka mata jagora ta tafi dakin sauya kaya, kayan da suka bata ta sanya wasu shara shara duk qaurun kafafunta a bude suke ga cikin nata shima a wangale dakyar suka janyota ta fito don dagewa tayi bata fita hk, prince akbar na daga idanu ya hango wannan shiga dake jikin bimbii take ransa ya qara 6aci ya daure fuskarsa tamau,prince nasaar na gefe yana karantar yanayin prince din har lkcin da bimbii ta hau stage, tsayawa tayi sai kalle kalle take kafin zaqaqqiyar muryarta ta soma rero wasu baitoci.....
Littafin nan na siyarwa ne, kan naira #300 kacal, zaki tura ta wannan acct...0100790419,alhaji shahida nasir,union bank, saiki turo da screesht na payment ta whatsapp ta wannan layi....07041195806....
Alkalamin Bintuu ne....
10/10/20, 1:12 AM - Anti qamshi🌷: *DAREN GOMA SHA HUD'U*🪔🪔
Written By Bintuu Seer
16
*The more I see you, my heart beat faster than I Imagine*.....so,you are my heart beat....💕
Idanun kowa a wurin yana kanta, lkcin ta soma rero baitocin dake cikin waqenta cikin karyayyen harshenta na diyan fillo dake fitar da luqqa na larabci mai dadin mutuqar dadin sauraro, waqa daya ta dauka cikin waqoqin larabcin da israt ta koya mata har da irin salon rawar waqar, rawan da ciki ake ana karkad'a k'ugu, toh abunku da masu ma'adanan kadawa gaba da baya tuni ta janye hnklin kowa na wurin da salon rawarta, k'ugunta take k'adawa cike da tsantsar k'warewa tana rero baitocinta da muryarta data gama kared'e wurin sbd zaqi, dayawa a wurin sun koma tamkar mutum mutumi sun zuba mata na mujiya, gimbiya hindu ranar ma hk ta din ga cika tana batsewa don ba hk taso ba, ita tunaninta bimbii waqar fillanci zatayi sbd ta toxarta ta a wurin a aibata harshenta tare da kalar fatarta, sai ga bimbii ta bata mamaki tayi waqenta cikin harshen larabci, juyi take sosai skirt din data saka mai batsa ne ta kasa yana hurawa, duk inda ake neman cika na mace toh bimbii ta qetare wurin, tana zuwa qarshen waqar ta sunkuya da qafa daya tare rissinar dakanta qasa ta musu hk da hannu�wurin ya dauki tafi sosai, shikanshi sarki abdallah murmushi yyi irin nasu na manya, prince akbar kuwa gbdy ransa a dagule yake ji yyi zaman wurin duk ya gundureshi, bimbii koh dawowa tayi bayansa ta tsaya bayan taje ta sauya kayan dake jikinta, prince nasaar shima takaicine ya ishe shi yadda yaga bimbii ta koma bayan prince akbar ta tsaya, wata baiwa ce wacce ke cikin bayin dake rarraba abun sha a wurin ta kawo ruwan inibi ta sunkuya tare da ajiyewa a gaban prince akbar sannan ta dauka ta tsiyaya masa a qaramin cup ta rissinar dakanta qasa tare da miqa masa cup din da hannu biyu, bimbii tayi sauri ta zagayo wurin ta zata amshi cup daga hannun baiwan nan, gani tayi baiwar taqi bata cup din sai miqawa prince take dakanta, kallon baiwar prince akbar yyi yace" ki bata itace keda haqqin bani abu naci" jiki a sanyaye baiwar ta miqawa bimbii cup din dake hannunta bimbii ta dan diga ruwan inibin a farcen dake babban yatsanta, duk suka tsaya suna mata kallon mamaki,yatsan nata ne yyi duhu sosai, juyawa tayi ta miqawa baiwar ruwan inibin data kawo tace" babban prince baya shan ruwa inibi" kallonta prince akbar yyi sannan ya kalli wannan baiwa dake tsaye sai kawai ya miqa mata hannu ta miqo masa cup din data tsiyaya ruwan inibi yakai bakinsa da niyyar sha, bimbii kuwa sai kallonshi take taga tabbas sha zeyi sai tayi saurin sanya hannunta ta amshi cup din daga hannunsa takai bakinta,gimbiya hindu dake kallonsu miqe tayi da sauri cike da tsan tsar mamaki, baiwa ta amshi abu daga hannu prince takai bakinta, hknne ya dauko hnklin mutane, prince akbar kuwa tsayawa yyi kawai yana kallon bimbii data shanye ruwan inibin dake cup din tas, kafin ta sauke cup din, ubaid ya dauketa da wasu kyawawan mari lafiyayyu guda uku,tana matsayin baiwa har ta samu yancin da zata amshi cup a hannun prince takai bakinta, wata irin fizga ubaid yakai mata ya durqusar da ita a qasa bisa guiwowinta, shi kuwa prince bece uffan ba kawai kallon bimbii yake, ita kuwa bimbii abunda yasa tayi hk shine tun tana rawa bisa stage idanunta yakai kan dan sarkin dulham wanda ake kira da prince amir shima ya bayyana a wannan taron, lkcin da baiwar takai masa nasa ta ajiye ta nufo wurin prince da dayan na hannunta ashe ita kanta baiwar bata ankara ba sa'adda prince amir ya musanya mata farantin da jug din da ruwan inibin da zata kaiwa prince akbar yake ya tura mata nashi wanda ta fara ajiyewa, ita kuma bimbii ganin hkn yasa tasan tabbas babu qamshin gsky kan lamarin, diga ruwan inibin da tayi a saman farcenta har yyi duhu shine ya tabbatar mata da akwai guba mai qarfi a cikin wannan abu don tun tana yarinya Allah yyi mata wannan baiwar, idan har akwai abu na cutarwa a abunda zataci idan ta sanya bisa farcenta tana ganewa, idan farcen nata yyi duhu toh abincin da akwai abun cutarwa a cikinsa,wannan dalili ne yasa ta hana prince shan ruwan inibi data ga kuma ya amsa ze sha shine ta amsa ta shanye ita,aikuwa tana wurin a durqushe kan guiwowinta idanunta suka soma gani dishi dishi, tsintsiyar hannunta tashi daya ta soma sauya launi zuwa kalar ja, basu ankara ba sai ganinta sukayi ta zube a wurin, zumbur prince ya miqe daga inda yake zauna ya nufo wurin da bimbii ke kwance ya tsuguna yakai hannunsa ze riqo tsintsiyar hannunta daya ga tayi jajir yana son tantance qarfin gubar dake jikinta, ubaid yyi saurin riqe masa hannu yace" ranka ya dade kar ka ta6a, guba ce mai qarfu zata iya shiga jikinka"sarki abdallah bin jabal kuwa dayake suna da dan tazara tsakaninsa da wurin da ya'yan sarakunan ke jera besan abunda ke faruwa ba saida hadiminsa ya matso kusa dashi ya rada masa abunda ke faruwa, saurin tashi yyi ransa a mutuqar 6ace, baiwar kuwa data kawo wannan ruwan inibi tashi daya jikinta ya soma rawa, ita dai har ga Allah tasan bata zuba komai a ruwan inibin ba toh waye ya mata hk, sarki abdallah bin jabal dakansa ya taso ya iso wurin yana kallon bimbii dake kwance ya kalli hannunta daya suntume tashi daya hkma wurin maqogwaronta, kallon hadimin dake bayansa kawai yyi shi kuma ya sunkuya da hanzari ze dauki bimbii ya fice da ita, prince yyi saurin dakatar dashi shi ya sunkuya da niyyar daukanta, tsawar da mahaifinsa sarki abdallah ya daka masa ne yasa shi janye hannunsa, akan idanunsa wannan hadimi ya sunkuya ya dauki bimbii ya fita da ita, ita kuwa wannan baiwa sarki abdallah ya bada umarnin tfy da ita dakin azabtarwa har saita bayyana wanda ya sanyata aikata wannan gangacin kan magajin masarautar burham, bimbii wani dogon daki aka kaita suna binciken irin gubar don bata magani, 6angaren wurin taro kuwa cigaba sukayi da taronsu batare da nuna kulawa ga abunda ya faru da bimbii ba sbd ita din baiwa ce, sarki abdallah yana da mugun ra'ayin riqau babu wanda ya isa yasa shi janye abunda yyi niyya shiyasa suka cigaba da gudanar da wannan taro tamkar babu abunda ya faru, prince kuwa kasa zama a wurin yyi ya sulale shi da hadiminsa ubaid suka bar wurin taron,suna fita ya kalli ubaid yace" kaje ka bincika inda suka kaita" rissinar dakai ubaid yyi alamar ya amsa umarni sannan yyiwa prince rakiya har 6angarensa sannan ya koma don binciko wurin da akai kai bimbii,prince kuwa ya kasa zaune ya kasa tsaye saikai komo yake da hannayensa a baya yana tunanin halin da bimbii ke ciki, zama yyi a wata kujera ya bude wani akwati ya fito da wata qaramar kwalba ta antidote na irin gubar dake jikin bimbii ya dora saman table din dake gabansa, bimbii kuwa gubar dake jikinta ba'a son ta jima a jikinta idan ta jima a jikin mutum tana illata dukkanin garkuwar jiki ne,sun bata magani amma har yanzu jikin nata beyi respond ga maganin ba, 6angaren prince kuwa ubaid ya kawo masa labaran dukkanin abunda ke faruwa da bimbii, cikin dare ya fice shima ya nufi sashin da bimbii, masu tsaron wurin suna ganin prince suka rissinar dakai tare da bashi hanya ya shige ciki, bimbii ya gani kwance bisa wani dogon gadon katako an lullu6a mata wani mayafi, hannun nata ya kalla da wuyanta yaga wurin ya qara yin jajir, batare daya sanya wata safar hannu ba ya kamo hannun nata yana kallo, kallon bayin dake kula da ita yyi yace su fita su bashi wuri, cikin sauri suka juya suka fice, handkchief dinsa fari sol yasa ya daure mata hannunta sannan ya fito da wannan qaramar kwalba ta antidote na wannan gubar ya bude bakinta ya tsiyaya mata ya jijjigata sosai har antidote din ya wuce zuwa maqogwaronta, qara riqo hannun nata yyi yana kallon wurin yaga ko mgnin zeyi respond har be ga wata alama data nuna jinkinta ya amshi mgnin ba, qura mata idanu yyi cike da sanyin ciki yasa hannunsa ya cire dukkanin awarwaron dake hannunta yasa a aljihunsa, gumi duk ya jiqa masa fuska sai qare mata kallo yake yana dana sanin gardaman daya mata da hkn be afku ba, 6angaren su israt da khulood kuwa sun sami labarin abunda ya faru da bimbii ranar dukkaninsu kasa bacci sukayi, sunyi kuka sunyi kuka har sun gaji, israt ta kalli khulood tace" shikenan mu kuma hk rayuwarmu zata cigaba da kasance kenan ,dubi abunda ya faru da layla yanzu kuma ga wata masifar ta kuma faruwa da bimbii duk a silar bauta" khulood ta kalleta tace" muma idan har muka cigaba da wanzuwa a wannan masarauta wlh qarshenmu bazai kyau ba, gwara mu cire tsoro kawai mu nemarwa kanmu hanyar gudu" kallonta israt tayi tace" abunda ya kamata kenan amma gwara musan halin da bimbii ke ciki tukun" khulood tace" hknne" prince akbar kuwa be bar dakin da bimbii take ba sai gab da asuba, saidai ya gargadi bayin dake tsaron wurin da wadanda suke aikin cikin wurin kar yaji kar ya gani, wato baya son wani ya fahimci a wurin ya kwana tare da bimbii, sukam mamaki ne ya cikasu na ganin duk girma da cikar izza na prince akbar yazo ya kwana tare da baiwarsa sannan ya nuna damuwa sosai kan halin da take ciki amma duk cikinsu babu wanda yasan ya bata antidote din nan, basu kawo komai ba saidai suna ganin yana nuna kulawar ne gareta don nuna halaccinsa ga sadaukarwar da tayi dominsa, sarki abdallah bin jabal kuwa baida masaniyya cewa prince yaje ganin wannan baiwa dakansa, wannan baiwa kuwa data kawo ruwan inibi tana nan ta azabtuwa amma har yanzu bata furta komai game da gubar da suke zargin ta zubawa prince a ruwan inibi............
Pls don Allah kuyimin afuwa kuyi hkr da wannan ba yawa...
Littafin nan na kudi ne kan naira dari uku kacal zaki samu damar karantashi, #300 ta wannan acct...0100790419,alhaji shahida nasir,union bank, saiki turon screenshrt na payment naki ta wannan layin...07041195806.....
Alkalamin Bintuu ne......
10/10/20, 1:12 AM - Anti qamshi🌷: *DAREN GOMA SHA HUD'U*🪔🪔
Written By Bintuu Seer
17
*Every second my heart beat just cox of you*........I really care about you💕
Washegarin ranar an tashi ne da ruwan sama sosai kamar da bakin k'warya shi kuwa yana tsaye a dogon corridorn dake gaban 6angarensa sanye da wata farar rigar iyaka guiwa da wando shima fari, takalmin qafarsa irin mai laushin nan ne half cover, kansa babu rawani hknne ya bawa gashin kansa damar sakko masa har kafarsa, iskar daminan dake kad'awa sai hura gashin nasa take yana rawa, hannunsa dukka suna hard'e a bayansa yana kallon iskar dake kad'a ganye bishiyu da furanni da kuma ruwan dake sauka, yanayin tsayuwarsa kawai ze tabbatar mk da yana tunanin wani abu ne, ubaid ne yazo ya tsaya a gefensa tare da rissinar dakansa qasa sannan yace"binciken ya nuna gubar an hadata ne da dafin wasu kunamai da bamu da irinsu a wannan yanki namu yawanci an fi samu irin kunaman a yankin masarautar dulham suna amfani da dafin kunaman wurin hada abuwawa dayawa ciki har da irin wannan gubar"shiru prince yyi batare daya juyo ya kalli ubaid ba sai can yace" na bata maganin kashe qarfin gubar" yana fadar hk ya juya ya soma takunsa cike da izza ya koma cikin 6angarensa, zama yyi akan wata kujera ya bud'e wani babban littafi mai dauke da tsohuwar kimiyya ta larabawa game da ilimin sanin 2kala dafin kunama da maciji yana wani nazari, lenah ce tsohuwar baiwarsa ta shigo hannunta riqe da wani faranti azurfa sai daukar idanu yake da qananan cups a saman faranti, tfy take tamkar zata karye sbd da rangwada na salon jan hnkli, le6enta jajir da jan baki ga gashin girarta tayi sama zara zara a gyare, wuyan qafarta da wata sarqa mai kwalliya, hancinta ma da dan kunne dan mitsitsi, ajiye masa farantin tayi ta risssinar dakanta qasa sannan ta sunkuya ta soma tsiyaya masa black ginger tea din data kawo masa, shi kuwa tamkar besan ta shigo ba ya cigaba da karatunsa, qara rissinar dakanta tayi ta miqa masa cup din dake hannunta tana murmushi, sai lkcin ya dago dakansa ya kalleta fuskarsa babu yabo babu fallasa ya sanya hannu ya amshi cup din ya ajiye a saman table din, daga mata hannun yyi alamar dake nuni da baya buqatar komai wannan lkci ya maida kansa ya cigaba da abunda yake, ubaid ne ya shiga kai tsaye ya wuce inda prince ke zaune tare da rissinar dakansa qasa ya ajiye masa wata farar takarda akan table din dake gabansa, a hknli yasa hannu ya dauki takarda ya soma karantawa, takardar tana dauke da sanya hannun mahaifinsa sarki abdallah yana umartarsa yyi shirin raka sarki najash bin akhir wato sarkin dake mulkin masarautar dulham tare da dansa prince amir da sauran tawagarsu da suka zo taya masarautar murnar cika shekaru dari uku da sittin da kafuwa,zasu rakasu bakin bodar da zata fitar dasu daga yankin masarautar burham don tabbatarwa sun fita daga yankin burham lfy, qara kallon takardar yyi sosai sannan ya ajiye ya kalli ubaid yace" kun bincika sosai babu wata alama dake nuni da sanya hannunsu a sanya guban nan" ubaid yace" babu alamar data nuna hkn" shiru prince akbar yyi sannan ya fito da hatiminsa yasa hannu a takardar sannan ya miqawa ubaid ya rissinar dakansa sannan ya amshi takardar ya fita, miqewa tsaye prince akbar yyi ya nufi wurin 2sharan curtains din dake sake sun rufe window ya tsaya yana kallon farfajiya waje hannunsa dukka a baya, 6angaren bimbii kuwa cikin izinin Allah sai gashi ta bud'e idanunta, le6enta ya bushe sai bin ko'ina na dakin take da kallo, lkcin herbalists din dake kula da ita ta shigo ta tarar ta bude idanu, matsowa tayi kusa da ita tana mata sannu, daga mata kai kawai tayi sannan ta mayar da idanunta ta rufe, sunyi mamakin bude idon nata sbd daren jiya maganin da suka bata sam be nuna ya dauki jikin nata, su basu san cewa prince ne ya bata antidote nasa ba kuma shine ya mata aiki don ya kashe qarfin gubar kaso sittin cikin dari,prince akbar kam beso wannan rakiya da mahaifin nasa yasashi yyi ba, yana cike da tausayin bimbii yana ganin idan ya tafi yabarta hk kwance cikin ciwo tamkar be kyautawa sadaukarwar da tayi. dominsa bane amma babu yadda ya iya hk ya soma shiri, daren ranar yaso yaje duba bimbii amma hkn be samu ba don tfyr dare zasuyi, cikin daren suka dauki hanya dukkaninsu bisa dawakansu tare da rakiyar manyan dakarin tsaro,kwanansu daya da yini guda suka isa boda dasu sarki najash, prince amir kuwa babu abunda daya hadashi da prince akbar ko a hanya, dalili kuwa shine sarki abdallah shine sanadiyyar mutuwar mahaifiyarsa, shekaru ashirin da suka gabata sarki abdallah yakai harin bazata yankin dulham inda ta qarfin tsiya yacisu a yaqi ya kwashe matansu ya maishesu bayi sannan ya kama mahaifiyar prince amir ya kawota masarautarsa ya maidata kwarkwararsa, qarshen ita kuma baqin cikin hkn yyi ajalinta, wannan shine yasanya har ranar yau gabar dake tsakanin masarautun tana nan saidai kowa cikinsu ta bayan fage yake neman durqusar da daya musamman ma masarautar dulham, sarki najash da dansa prince amir sun shirya zuwa wannan taron ne kawai don cimma manufarsu,prince amir ya rantse sai ya qunsawa sarki abdallah irin baqin cikin daya qunsa musu suma hknne yasa ya shirya poisoning din prince akbar dayake magajin masarautar burham sbd yasan mutuwar prince akbar itace hanya mafi sauqi ta ganin bayan sarki abdallah don duk wani buri nashi yana kan babban prince,rashin samun nasarar hknne yake cin ransa har yanzu, bimbii kuwa cikin hukuncin Allah sun samu sun zuqe ragowar guban dake jikinta, tana soma dawowa cikin hayyacinta suka ce ta koma bakin aikinta, hk ta dawo dakinta bata tarar dasu israt ba ta hau gado ta kwanta, khulood da israt kuwa suna bakin qorama suna shan wanki har kusan yamma sannan suka nufo dawowa, suna shiga tamkar gixo suka ga bimbii kwance bisa gado, cikin saurin suka qarasa bakin gadon suna kallonta tana bacci, zama sukayi kusa da ita israt na mata fifita ita kuma tana bacci, sai wurin yamma ta farka ta gansu zagaye da ita, murmushi tayi musu tare da hadasu ta rumgumesu suma suka qara rumgumeta suna jajanta mata abunda ya faru, cikin dauriyya ta sauka tayi wanka ta shirya ta nufi babban kitchen su khulood na biye da ita, tana shiga duk bayin dake cikin kitchen din suka bita da kallon mamaki don basu da masaniyyar samun sauqinta tunda ance gubar mutuwa tasha, ta6e baki sukayi, dayar cikinsu ta kalli bimbii tace"daman baki mutu ba don mun ji ance gubar mutuwa kk sha" israt tayi zagal tace" gata nan bata mutu ba don mutuwar ba yar aiken uban wani bace balle ya turata ta kashe" kallon israt sukayi gbdynsu sannan suka sheqe da dariya, dayar cikinsu tace"toh kema kawai ki maida fatarki kalar nata mn saiku saje" khuood tayi dariya tace" wasu idan ana mgnr siffa maikyau su daina sanya baki wlh don farar fatar ce kawai gadararsu amma ba qira da zubin zati irin na mata ba" shiru sukayi basu sake mgn ba suka cigaba da aikinsu, israt da khulood na daga gefen bimbii ta gama jera kayan marmari a farantai masu mutuqar kyawu ta nufi 6angaren prince batasan cewa yyi tfy ba, kan hanyarta ta hadu da lenah ta fito daga 6angaren prince, shigewa zatayi ta wuce abinta, lenah ta bita da kallon mamaki sai tayi saurin shan gabanta tana huce don haushi taji na ganin bimbii ta samu lfy sbd ita aka bawa aikin bimbii ta cigaba da hidimtawa prince kafin bimbii ta samu lfy, kallon rainin ta yiwa bimbii tace"uban me ya tashi kafadunki baki mutu ba" kai tsaye batare da wani shakku ba bimbii ta bata amsa tace" ubanki mn" wata irin zabura tayi ta nufo kan bimbii da niyyar bata mari taji an riqe hannunta, juyawa tayi a fusace sai tayi toxali da ummu sumayya tace" haba lenah meyesa kk hk ko kin mance dokar wannan 6angaren ne, kina son a sauya miki 6angaren aiki ne" shiru tayi sai huci take tana kallon bimbii sannan tayi gaba da sauri tabar wurin, ummu sumayya ta kalli bimbii tace"idan 6angaren prince kk nufa toh baya nan yyi tfy" turus bimbii tayi ta kasa gaba ta kasa baya, ita kuwa ummu sumayya ta wuce tabarta a wurin, babban abunda ya bawa bimbii mamaki shine wato su wadannan mutane basu dauki bawa mutum ba shiyasa dukka da abunda ya faru da ita tayi ne don kare prince matsayinta na baiwar dake kula da hidimarsa amma yaci ace ko sau daya yaje ya duba halin da take ciki, amma sbd kasancewarta baiwa be damu kota mutu kota rayu ba tfy ma yyi abinsa yabarta cikin mugun yanayi, neman wani tudu tayi ta zauna tana tunanin gd, mahaifinta da innanta yadda suke nuna mata gata tamkar zasu maidata ciki, idan kuwa bata da lfy sun shiga damuwa kenan amma nan kuwa wasu ma ftn mutuwa suke mata, shiru tayi tare da zabga tagumi, tunowa da tayi dasu khulood shine yasa ta murmushi, tabbas tasan a wannan qasa data samu kanta babu dangin iya bare na baba su khulood sun nuna mata so tsakani da Allah kuma sun fi kowa damuwa da ita da halin da take ciki, tabbas su khulood sun fi kowa sonta cikin wannan qasa..............
Littafin nan na kudi ne, idan kina da buqatar siya zaki tura #300 ta wannan.acct...0100790419, Alhaji shahida nasir,union bank, saiki turomin da screesht na payment ta wannan layin 07041195806.......
Alkalamin Bintuu ne.......
10/10/20, 1:12 AM - Anti qamshi🌷: *DAREN GOMA SHA HUD'U*🪔🪔
Written By Bintuu Seer
18
*I deeply fall in love*......the forbidden love In burham kingdom.....
Ta jima a wurin tana zaune sannan ta tashi ta qarasa 6angaren nasa, tana zuwa bayin dake tsaron kofar suka bata hanya ta shige, tana shiga ta saki wata ajiyar zuciya sbd qamshin sassayan qamshin daya ratsata hk kullum 6angaren nasa yake, mutum ne shi ma'abocin son qamshi, gani tayi komai a gyare yake babu buqatar ta gyara, bude dakin wankan tayi shima ta gansa a shirye komai a jere tsaf tun daga kan sinadaran wanka da 2towels duk anyi hanging nasu neat, fitowa tayi ta sassauke curtains din da suke a kame sannan ta juya ta fice, komawa tayi dakinsu sbd har yanzu lalla6a jikinta kawai take tana aiki mai tsayi zata soma hakki da fitar da numfashi 2sama, kwanciya tayi don qara bawa jikin nata hutu,tunawa tayi da wannan dan akwatin da prince ya bata, sauka tayi a hnkli daga gadon taje ta bude wata drawer ta fito da qaramin akwatin sai daukar idanu yake ta koma bakin gado ta zauna sannan ta fara qoqarin bude dan akwatin, tana budewa taci karo da wasu kyawawan awarwaro masu mutuqar kyau ko ba'a fada mata ba tasan gold ne, qurawa awarwaron idanu tayi tana kallonsu batasan lkcin da murmushi ya su6uce mata ba zira awarwaron a hannunta, tamkar an gwadata don chas suka mata daidai hannunta, sai kallon hannun nata take tamkar wata y'ar qauye, gani tayi kamar awarwaron sun fi qarfin matsayinta amma prince ya bata kyauta, sanya awarwaron gold ai sai jinin sarauta amma ba ita da take baiwa ba,shiko prince awarwaron data sanya ranar a hannunta ne suka birgeshi shiyasa yyi mata wannan kyautar,motsi ta jiyo alamun dake nuni da wani tunkaro dakin nata, saurin zame awarwaron tayi daga hannunta ta maidasu cikin akwatin tayi saurin tashi ta komar dashi cikin drawer din dayake ta dawo ta haye gado ta kwanta, israt da khulood ne suka shigo, zama sukayi kusa da ita suna sake mata sannu, murmushi ta musu kawai, wajejen yamma suka soma jin hayaniyar bayi a farfajiyan 6angaren prince akbar,bude kofa sukayi suma suka fita suka ga ashe prince ne ya dawo, gbdy bayin dake aiki a 6angaren nasa sun jeru sunyi 2sahu suna masa barka da dawowa lfy shi kuma yana daga tsaye a saman dogon corridorn 6angaren nasa,gefensa daman hadiminsa ubaid ne, kallon bayin yake daya bayan daya sannan ya juya ya soma takawa a hnkli da niyyar ya shige 6angarensa hkn yyi daidai da fitorwa su bimbii daga dakin nasu suka shiga sahun bayin, idanunsa ne suka sauka akanta amma sai yyi saurin shigewa 6angaren nasa duk da idanun nasa yana son qare mata kallo, ubaid ne yyiwa bayin mgn sannan ya sallamesu kowa ya koma bakin aikinsa, bimbii wucewa tayi babban kitchen ta hada masa abun sha na zaitun ta dauka ta nufi 6angaren nasa, tana zuwa kofar ta bude ta shiga, samunsa tayi kishingid'e a jikin wata kujera yana duba wasu maps, ganin shigowarta ne yasa yabar abunda yake ya dago dakansa ya zuba mata lumsassun idanunsa yana kallonta, kallon da prince din ke mata ne yasa ta tsarguwa sosai amma dai ta daure ta tako a hnkli ta rissinar dakanta sannan ta ajiye farantin dake hannunta, sunkuyawa tayi ta soma tsiyaya masa ruwan zaitun din a qaramin cup ta dauke tare da sunkuyar dakanta qasa tasa hannunta dukka ta miqa masa cup din, saida ya jima be amsa ba kawai ya qura mata idanu yana kallonta, dago da kanta tayi ta kalleshi idanunsu suka sarqe da juna, hannunsa ya miqa ya amshi cup din dake hannunta ya qara kwantar dakansa a jikin kujerar yana sipping ruwan zaitun din yana cigaba da kallonta, itace taji kunya ta sunkuyar dakanta qasa tana kallon floor, murmushi yyi yace" ya jikin naki" dago da kanta tayi suka sake hada idanu dashi sai kuma duk ta duburbuce sbd idanunsa dake neman kayar da ita, tace" d...a..sauqi" be kuma cewa komai ba ya miqe yabar wurin hkn ya ankarar da ita lkcin wankansa yyi, wucewa tayi saurin yi cikin dakin wankan ta soma hada ruwan wanka yadda ta saba sannan ta fito, ganinsa tayi sanye da wata rigar wanka fara qal yana zaune, tana fitowa ta rissinar dakanta a gabansa, bece mata komai ba ya miqe ya shige, ita kuma ta tsaya daga bakin kofa, tana nan tsaye taji alarm alamar dan sarkin na buqatarta cikin dakin wankan, shiga tayi da sauri ta tarar dashi a cikin kwarmin wanka cikin ruwan dake turiri, saman ruwan duk kumfa, hannunta tasa a kafadunsa ta soma masa tausa a hnkli, shi kuwa idanunsa a lumshe suke yana amsar saqon dake shiga jikinsa ta wata siga daban dashi kadai yabarwa kansa sani,daga mata hannu yyi tabar tausan ta soma masa wankin gashi tana gamawa ta fice ta kyaleshi yyi wankan, tadan jima sannan ta kuma jin alarm ta koma ciki, ruwa ta debo a wani qaramin bahun tazo gabansa ta ajiye ta kuma miqewa taje ta dauko sinadaran wankin qafa ta zuba a ruwan qaramin bahun, sannan ta riqo kafafunsa da suke sanye cikin takalmin wanka ta cire takalmin wankan ta sanya kafafun nasa cikin ruwa, kallon kafafun nasa take da suke jajir dasu tamkar tumatir ga laushi da santsi tamkar ta jarirai sai ka rantse baya taka qasa dasu, itakam bata ga abun wankewa a wadannan kafafu ba idan badai kawai izzah da hutu ba, riqo kafar tasa tayi tamkar wacce ta riqo gold cike da taka tsantsan ta soma wanke masa, duk abunda shi kuwa idanunsa a rufe ma suke tamkar mai bacci har ta gama masa wankin kafar, fita tayi tana jiran fitowarsa, ta jima da fita kafin ya fito sanye da wasu kaya masu kalar ruwan kwai, jikinsu tamkar na mage, gashin kansa kuwa walwali kawai yake da sheqi, takalmin kafarsa ma mai jikin mage, kai tsaye royal bed nasa ya haye ya kwanta, ita kuwa dayake ba wata cikakkiyar lafiyar jiki ne da ita ba tuni ta soma dan jin jiri sbd dan aikin da tayi, so kawai take ya bata izinin tfy taga yyi mata shiru hkn ya tabbatar mata bata gama aikinta ba so yake ta sanyashi yyi bacci, a hnkli ta qarasa kusurwar da royal bed nasa yake itama tahau gadon, yana jin ta hawo gadon ya dago da kansa ya daga mata hannu, alamar baya buqatar tausa, dadi taji har hkn ya bayyana a fuskarta ta soma qoqarin sauka da sauri, saurin riqo hannunta yyi ya kalli tsakiyar idanunta yace"kimin rawa ita nakeso" kallonsa tayi tamkar kuka, sakinta hannunta yyi ya tashi ya sauka daga kan gadon ya koma kan wata kujera,ita kuwa bimbii bata da karfin jiki tayaya zatayi rawa, tsayawa tayi sai kuma ta fara rawar 2kadan, shi kuma yabita da kallo tana cikin rawar kawai jiri ya debeta ta tafi luuuu, sai ganinsa tayi kawai ya tareta da hannu guda ta fada jikinsa, kallon fuskarsa take 2dishi shima yana kallonta, dagata yyi chak ya kwantar da ita kan royal bed dinsa shima ya kwanta daga gefenta,kunsan kowanne qabila suna da techniques nasu a gargajiyance, idanunta ya kalla kawai yasan jiri ne ya kwasheta, ba zato bimbii taji kyakykyawan bakin dan sarkin bisa nata, duk da halin da take ciki amma zuciyarta ta soma dokawa 2uku ta qwalalo manyan idanunta waje cike da razana..........kundai son halin bimbii taku😉....
Littafin nan na siyarwa ne, idan kina da buqata ki tura #300 ta wannan acct....0100790419,alhaji shahida nasir,union bank, saiki turomin da screesht na payment ta whasapp through wannan layin....07041195806......
Alkalamin Bintuu ne....
10/10/20, 1:12 AM - Anti qamshi🌷: *DAREN GOMA SHA HUD'U*🪔🪔
Written By Bintuu Seer
19
*Forbidden love*.....the beginnig of my story.....
Bakinsa na bisa nata ga dogon hancinsa daya dora saman nata ya qureta da idanun nasa masu sirrika 2kala yana kallon yadda duk ta gama rud'ewa, rufe idanunta tayi qam taqi budewa saidai bata fasa jin saukar numfashinsa ba kuma be dauke bakinsa daga kan nata ba, sun jima a hk sannan ya janye jiknsa a hnkli ya koma gefenta ya kwanta ya rufe idanunsa shima, bimbii na jin hk ta bude idanunta ta soma qoqarin sauka daga kan gadon, charaff, taji ya damqe hannun nata, kallon fusksrsa tayi taga idanunsa a lumshe suke tamkar mai bacci, maida idanunta tayi kan hannunta daya damqe da nasa, maido da qafafunta tayi ta sake hawa gadon duk da a tsorace take amma sai ta sanya qarfin hali, hannunta ta chusa cikin sumar kansa tana hargitsawa, bude idanunsa yyi ya sauke kan fuskarta, take gabanta ya yanke ya fad'I sbd kallonta yake cike da wani salo mai wuyar fassaruwa kuma gashi ya qura mata idanu, sauke numfashi yyi a hnkli sannan ya daga mata hannu alamar ta tafi, saurin sauka tayi daga gadon tamkar zataci tuntu6e ta nufi kofa, binta yyi da kallo har ta fice sannan ya mayar da idanunsa yyi ya rufe, bimbii kuwa har ta fice tana waiwayen 6angaren tamkar wacce tayi gamo da abun tsoro, bata wuce dakinsu ba sai ta tafi wani wuri mara hayaniyya ta zauna sai maida numfashi take, tuno moment nasu take da babban prince tamkar a mafarki ba gaske ba, shafa bakinta ta somayi, tace" anya kuwa prince yana cikin hayyacinsa yau" abunda ta furta kenan a bayyane, 2kwata ita bata kawo wai prince ya fara sonta bane don ita tana ganin hkn bamai yiwu bane ita a suwa kuma? idan har bimbii tasan meye so toh kallon da prince ke mata kawai ya isa ta fahimci dan sarkin ya afka finanniyar soyayyarta wanda shi kansa besan lkcin daya fara son bimbii ba har ya zurfafa hk,prince be iya furta kalmar so ba shiyasa yake qure bimbii da idanu, prince shi kansa da yaqi aminta cewa ya fara son baiwar tasa sai yanzu da soyayyar qasqantacciyar baiwar tasa ke neman hanasa sukuni ba dare ba rana, baya son kowa ya fahimci hkn sbd yasan wannan soyayyar dayake yiwa bimbii tamkar haramtacciyar soyayya ce a wannan masarautar ta burham, baya son sanya bimbii cikin fitina shiyasa yake iyakar qoqarinsa wurin ganin ya yakice wannan soyayyar daga zucciyarsa saidai abu ya gagara tamkar kullum qara masa wutar qaunar bimbii ake, miqewa tayi ta fara tfy, prince kuwa fitowa yyi wajen farfajiyar 6angaren nasa ya tsaya a saman corridor yana kallon haske farin wata, daidai lkcin ya hango tahowa bimbii tana tafe tamkar wata mara lfy, ita sam batasan yana hangenta ba, har ta shige dakinsu, hira ta tarar dasu khulood nayi ita ta shiga anayi da ita amma ana hirar tana skipping, israt ta kalleta tace" bimbii ko jikin ne" murmushi ta musu tace" aa" khulood tace" ki kwanta ki huta" ba musu ta tashi ta hau gadon ta kwanta, prince ko har ta shige yana kallonta sannan ya juya ya shige ciki abinsa, washegari,hk bimbii ta tashi sukuku komai cikin sanyin ciki take, shakkar zuwa 6angaren prince take amma dolenta ta hada masa herbal tea ta dauka ta nufi 6angaren nasa, tana shiga ta same shi a kwance ko tashi beyi ba, hkn ya bata mamaki sosai don prince akbar mutum ne mai tsari da kuma qa'ida, baya gota lkcin tashinsa hkma lkcin wanka da cin abincinsa duk a tsare suke, tunda ta soma masa hidima bata ta6a shigowa da safe ta same shi a kwance ba don ba'a shiga 6angaren nasa mutuqar be tashi daga bacci ba amma yau tayi mamaki da kofar shiga bangaren nasa ta bude mata, ajiye farantin hannunta tayi a saman table, juyawa tayi kamar zata fita sai kuma ta dawo ciki ta qarasa wurin royal bed din dayake kwance don qara tabbatarwa,yanayin yadda taga kwanciyarsa ne ya haska mata kamar baya jin dadi ne, a hnkli kamar wata mara gsky takai hannunta zata ta6a jikinsa taji koda zafi, bude idon daya yine ya sanya taja da baya a tsorace, miqewa yyi zaune a hnkli sannan ya miqa mata hannunsa, tsayawa tayi don bata gane nufinsa ba, saida taji yace" ba ta6ani kkson kiyi ba" a dan razane ta dafe qirji tace'wlh Allah so nk naji ko jikin naka da zafi don naga yanayin kwanciyar taka ne tamkar baka jin dadi kuma na lkcin tashinka ya wuce"har ta gama magana be dauke kansa daga kanta yana kallonta, murmushi yyi kawai sannan yace" eh, bani da lfy ko kina da maganin da zaki iya bani ne" shiru tayi ta kasa bashi amsa shima be jira jin komai daga gareta ba ya sauka daga gadon ya koma kan wata kujera, ranar dai kasa fahimtar prince tayi 2kwata, bata gama tsinkeyawa da lamarinsa ba sai da dare yyi, tausa yasanyata yaqi barinta taje ko'ina har bacci ya saceta tana daga saman gadon nasa, duvet dinsa ya rufa mata ya gyara mata kwanciya sannan shima yaja duvet din ya shiga, bimbii baccinta take shara kawai shi kuwa kasa baccin yyi sai juye juye yake har jikinsu ya hade, toh fa tun yana daurewa har ya bada kai, daga nan zance ya soma sauyawa, bimbii na cikin bacci ta soma tsintar kanta a wani irin yanayi da tunda uwata ta haifeta bata ta6a sanin makamancinsa ba, iyakar rudewa da tsantsar rikicewa hadi da tsoro suna suka soma walatoyi da ita, kuka ta soma sosai tana roqonsa da iyakar muryar da Allah ya hore mata amma prince yyi nisa baya jin kira zuciyarsa tayi rinkaye, duk wani abu na kwatar kai ranar tayi cixo ne, yakushi ne, babu abunda take kira sai don Allah kar ka yimin hk kaji qaina, banda kowa banda gata karka rabani da martaba ta, wlh na tuba nabi Allah na bika, innalillahi wa'inna ilairrir rajun.......wannan itace kalmar bimbii ta qarshe dana iya jiyowa, take nima alqalamin nawa ya su6uce daga hannuna don tabbas nasan mai afkuwa ta afku kenan..........
Manage this page pls.
10/10/20, 1:12 AM - Anti qamshi🌷: *DAREN GOMA SHA HUD'U*🪔🪔
Written By Bituu Seer
20
*You have a thousand reasons to blame me*....I'm sorry dear...💕💕
Prince sam ya kasa control kanshi saida ya samu isa babbar headquarter yyi 6arna sannan ya soma dawowa cikin hayyacinsa, fuskar bimbii ya kalla yaga tasha kuka har ta qoshi ta koma kukan zucci, duniyar juya mata take kawai ga wani radadi da zugi dake damunta, gefe yyi ya kwanta ya juya mata baya yana fitar da numfashi a hnkli sannan ya lumshe idanunsa, zuciyarsa a wannan yanayin cike take da tsantsar nadama da dana sanin abunda ya aikata, wani 6angaren na zuciyarsa ya soma tuna masa matsayin bimbii ba kowa bace face qasqantacciyar baiwarsa, kusantar ta da yyi alfarmar ce gareta da qarin daraja, duk bayinsa babban burinsu kenan su janye hnklinsa ya kusancesu amma basu ta6a birgeshi ba, ita bimbii kuwa hk kawai yaji Allah ya jarabceshi da qaunarta, bimbii ko tana daga gefe ita kuma ji take babu wanda ta tsana a duniya sama da prince akbar, miqewa tayi zaune a hnkli taja duvet ya rufe mata kirji sannan ta janyo doguwar rigarta ta saka ta saukar da qafafunta qasa, tashi take son tayi abu ya gagara sai cixe le6e take, sauka tayi dakyar ta koma qasan floor ta durqushe tare da sanya fuskarta a tsakanin cinyoyinta tana kuka mara sauti, tashi shima yyi ya sauka ya wuce dakin wanka ya jima kafin ya fito sanye da wasu fararen riga da wando, alamu sun nuna wanka yyi, kallon 6angaren da take durqushe yyi ya matsa kusa da ita sosai ya tsuguna gefenta, hannunsa yasa ya janye dogon gashinta daya zuba mata gaba ya maidashi baya, dago da kumburarrun idanunta tayi ta ture masa hannun, murmushi yyi yace" ki tashi ki shiga ki wanke jikinki" harararsa tayi tace" akwai alfarmar da nk nema a wurinka, don Allah ka sanya a maidani inda kk tsinto ni" kallonta yyi tamkar beji abunda take fada ba, tace" idan baka sanya an komai dani inda kk tsinto ni ba toh wataqila nice ajalinka don wlh saina dauki fansar abunda kayimin sbd bani da maqiyi sama dakai" kalamanta sun bashi mutuqar mamaki wanda suka sanya ya qura mata idanu,batare data ankara ba kawai taji ya rumgumota ta baya tayi tayi ta tureshi ta gagara,kwantar dakansa yyi a dokin wuyanta ya sanya bakinsa daidai kunnenta yace" kinsan me? ko yanzu kk bani guba da hannunki zan sha,ingarman namiji kamar akbar gwara ya mutu a hannun mace kamar ki" maganar cikin rada yake mata a kunnenta,yana gama mgnr ya sake ya koma ya zauna akan wata kujera ta alfarma mai ruwan zinare ya qureta da idanu, yace" ko ki shiga wanka ko na taso" bimbii na jin hkn tayi saurin afkawa dakin wankan,sama sama tayi wankan batare data wani gasa jikinta ba ta fito, kai tsaye wurin kofa tayi da niyyar ficewa, kofar taqi budewa,durqusa tayi a bakin taqi dawo ciki,shikam be kuma ce mata uffan ba ya dauki wani littafi yana dubawa,washegari da sanyin safiya bimbii ta janye zanin gadon ta fice dashi,cikin sanda ta soma satar hanyar zuwa qorama, tana zuwa ta soma wanke zanin gadon da sauri sauri don batason kowa ya ganta, hk ta gama ta shanya babu wanda ya ganta ta koma 6angarensu, tana shiga ta tarar har sun fice, dadi taji sosai don daman bata son su fuskanci komai game da abunda ya shiga tsakaninta da prince, shiga tayi ta gasa jikinta sosai da ruwan dumi sannan ta dawo ta kwanta, wannan abu daya faru da ita yasa walwalarta da annurinta sunyi hijira,abu kamar wasa prince ya dena ganin digon rahma a fuskar bimbii, yau tana gama hada masa abun sha ta sanya a mazubi mai kyau ta dauka ta nufi 6angaren nasa, baya nan yana lambunsa sai yamma ya dawo, tana shiga ta ganshi yana rubutu jan gefe tayi bashi wuri saida ya gama sannan ya dago da kanshi yana kallonta, qara tamke fuska tayi ta soma tsiyaya masa abun sha din, cup din ya amsa ya soma sha batare da wata shakka ba,gani yyi tana kallonsa, yace" da matsala ne" ...shiru tayi kawai ta juya ta fice abinta, dare na shiga ta fito a sace ta soma sanda ta nufi wurin wannan qaton kogin da aka yada gawarsu bimbii batare da wani tsoro ba ta afka cikin kogin kuma gashi bata iya ruwa ba.......
10/10/20, 1:12 AM - Anti qamshi🌷: *DAREN GOMA SHA HUD'U*🪔🪔
Written By Bintuu Seer
21
*If words were sufficient enough to ease out your sorrow and pain*.....I will keep talking never ever stop it even beyond after.....💕
Prince tunda ta kawo masa wannan abun sha yaga yanayin sai yaji gabansa na fad'uwa bayan fitar yasa ubaid ya bibiyar masa lamarin bimbii duk abunda ya gani baqo tattare da ita ya hanzarta sanar dashi, duk 2tsirgarta akan idanun ubaid take, lkcin daya ga fitowa da dare tana sand'a ta fice yyi saurin bin bayanta inda yaga ta nufa ne yasa ya juya da baya ya koma yaje mugun gudu ya sanar da prince akbar,ko rufe baki be bari yyi ba ya miqe da sauri ya fice ya haye dokinsa ya zabure shi da mugun gudu, ubaid ko tsaye yyi yana kallon prince da mutuqar mamaki yadda yaga ya dauki wannan baiwar tashi da muhimmanci hk,tashi guda kuma tsoro ya cikashi ya soma tunani kar abunda ya faru shekaru dari da talatin da suka gabata ya maimata kansa cikin masarautar burham, suma ji sukayi wurin iyaye da kakanni cewa shekaru dari da talatin da suka gabata lkcin zamanin sarki na biyar cikin wannan masarauta ta burham,d'ansa prince ansar ya ta6a fadawa soyayyar wata baiwa mai suna surayya yar qasar lebanon,tunda hkn ya bayyana sarki ashraf ya zartas da hukuncin kisa ga wannan baiwa batare da digon tausayi ba,baqin cikin mutuwar surayya shine yyi ajalin prince ansar sbd a lkcin ya fada mugun tarko na qaunar wannan baiwa tasa,ajiyar zuciya ubaid yyi yana fatan kar wannan tarihi ya maimata kansa cikin masarautarsu,prince akbar kuwa dayake yana bisa doki ne tuni ya kusa cimmata amma kafin ya qarasa har ta yarjewa kanta kawai ta afka cikin ruwan gwara ta mutu kawai da wannan tsautsariyar rayuwar da take a duniyar da bata da kowa, fad'awarta yyi daidai da qarasowar prince akbar wurin, sakkowa yyi daga dokin nasa ya qarasa bakin kogin da sauri batare da wani jira ba shima ya fad'a cikin ruwan, dayake gwani ne a ruwa da gudu yake suuuu cikin ruwan kogin yana lalibe kozai jiyota, miqa hannunsa kawai yake,gani yyi ruwan na janta sosai dayake ruwan mai tfy ne, tana daf da shigewa wani kwari ta qasan wata gada yyi saurin riqo hannunta ya janyota jikinsa, matseta yyi sosai a jikinsa ya soma suuuu da ita da mugun gudu suka soma tasowa saman ruwan kogin har suka kawo ga6a, daukanta yyi chak ya fito da ita bakin kogin ya kwantar da ita a qasa ya soma danna cikinta da hannunsa ta soma fitar da ruwan data sha, tari ta somayi sosai a hnkli ta soma bud'e idanunta, mamaki ne ya cikata lkcin da tayi tozali da kyakykyawar fuskarsa ya qura mata idanun nan nasa, binsa tayi da kallo kawai,yace" meyesa baki sanyamin guba a abun shan da kk bani ba kafin kizo kice zaki kashe kanki" batace masa uffan ba ta dauke kanta yace" ashe kina sona dayawa hk, kin gwammace ni kibarmin duniyar ke ki kashe kanki,toh idan kin tafi kin barni meye amfanin tawa rayuwar kenan" quresa tayi da idanu ko zata iya fahimta kalmomin dake fitowa daga bakinsa, qoqarin miqewa take ta kasa yasa hannunsa ya miqar da ita, tana zama ta ture hannunsa daga jikinta ya kuma dora hannunsa a cinyarta ta kuma sanya hannunta ta ture hannun nasa,murmushi yyi ya kwanta a wurin dayake rairayi ya janyo cinyar tata ya dora kansa, idanunsa suna sama yana kallon fuskarta, hannunta tasa tana qoqarin tureshi kansa daga saman cinyarta,hannayen nata ya riqe qam cikin nasa, tayi tayi ta kwace ta kasa,ganin hk ne yasa ta dauke kanta gefe guda,murmushi yyi ya miqe zaune ya matso da fuskarsa saitin nata kamar ze goga dogon hancinsa da nata ya fara mata mgn da rad'a yana fada wasu kalmomi da nikaina ban san me yake fada mata ba sbd mgn yake wanda ita kadai take iya jin abunda yake cewa, gani nayi ta kwalalo idanu waje tana kallonsa cike da mamaki, matsar da fuskarsa yyi tare da jan hancinta ya mayar dakansa saman cinyarta ya kwantar tare da folding hannayensa dukka a saman qirjinsa ya rufe idanunsa, kallonsa tayi tace" wani ze iya ganinka hk fa ka tashi" shiru ya mata yyi kamar beji me take fadi ba,saida ta kuma maimatawa ya bude idonsa yana kallon fuskarta yace" idan kina son na tashi ki gyaramin gashin kaina ya hargitse" kallon gashin nasa tayi taga sai digar ruwa yake dayake kuma gashin nasa dogo ne, tace" toh ka tashi zaune saina gyara mk" miqewa yyi zaune yayi folding kafafunsa ita kuma ta miqe tsaye kafin ya ankara ta arce da gudu tana daga masa hannu alamar bye bye, murmushi kawai yyi ya taho a hnkli yahau dokinsa yabi bayanta, hk suka qarasa 6angaren nasu saida ya tabbatar ta shige dakinsu sannan yasa ubaid ganin wurin,shi kuma ya wuce 6angarensa yyi saurin cire wannan kayan, israt da khulood kuwa har sunyi bacci don su da suka ga basu ganta ba sun dauko tana 6angaren prince ne, washegari, tun prince na jiran bimbii har ya hkr taqi zuwa 6angaren nasa ta wuce tabi su israt debo kayan marmari,tasan lkcin wankansa yyi amma ta share ta cigaba da huldar gabanta, shi kuwa prince sanye yake da wata rigar wanka fara sol, ya zauna yana jiran bimbii,lkci ya qure sosai amma bimbii bata zo ba, kwantar dakansa kawai yyi a jikin kujerar dayake zaune ya lumshe idanu, ita kuwa dawowarsu kenan ta kalli 6angaren prince, kamar zata shige abinta sai kuma ta dawo da baya ta wuce ciki, tana isa masu tsaron wurin suka bata hanya ta shige,tana shiga ta duba ko'ina bata ganshi ba tana shirin fice ta hangoshi tsaye wurin windows din nan ya harde hannunsa dukka a bayansa ya qurawa waje idanu tun dawowarsu dasu israt yake hangenta, yanzun ma yaji motsin shigowarta kawai juyowa ne beyi ba, matsawa tayi kusa dashi ta rissinar dakai,juyowa yyi yana kallonta fuskarsa babu yabo babu fallasa sannan ya qetarata ya wuce ya zauna ya dora kafarsa daya kan daya yana kallonta yace" na miki afuwan gocewa aikinki da kkyi yau amma idan kk sake maimata hkn toh zan dauki akan wadanda suke janyeki daga bakin aikin ki" gabanta ne ya fadi don ba qaramin tausayin su khulood takeyi baza ta6a yarda wani abu mara kyau ya same su silarta ba,durqusawa tayi akan guiwowinta gabansa tace" kayi hkr bazan sake ba amma kar ka cutar da yan uwana" kallonta yyi sai kuma ya dauke kanshi gefe guda yace" idan na dauki mataki akansu daman ai shine daidai tunda suke saki rashin jin mgn, sune silar dayasa kk tura kanki cikin rikici har da zuwa sace gawa a kogi" a mutuqar razane ta dago kanta tana kallonshi cike da mamakin yadda akayi babban prince yasan wannan sirrin nasu, harararta yadanyi daidai lkcin kuma ubaid ya shigo, rissinar dakansa yyi ya ajiyewa prince wani dogon akwati a gabansa, kallonta yyi yace" baki san aikinki bane koh kuma saina krt miki" wata irin zabura tayi da sauri ta miqe ta nufi cikin dakin wankan nan ta soma hada masa ruwan wanka cikin kwarmin wanka, shi kuwa prince da gangan ya mata hk yasan tana son su khulood sosai shiyass yake mata wannan barazanar, ita har yau batasan shine dakansa ya cecesu lkcin da suka tafi kogi ganin gawar layla ba,shine dakansa ya dauke hnklin bayin da suke shirin kamasu ya basu damar gudu shiyasa ya rufe fuskarsa da baqin kyalle, gani yyi taurin kan bimbii yyi yawa gata da kafiya kamar shi,dawowa da kallonsa yyi kan ubaid suka soma tattaunawa game da sabuwar takobin da mahaifinsa ya aiko masa dashi, bude masa akwatin ubaid yyi shi kuma ya fito da takobin sai sheqi take da walwali,murmushi yyi sosai sannan ya mayar da ita cikin akwatin,dagawa ubaid hannu yyi shi kuma ya sunkuyar dakanshi qasa sannan ya fice,komar da kallonsa yyi wurin dakin wankan yana jiran fitowarta, fitows tazo gabansa ta rissinar dakanta qasa alamar komai ya kammala, batayi saurin dagowa dakanta ba don tasan tunda bataji motsin miiqewarsa ba toh tabbas ita yake kallo,a zucci tace" haba mutum sai kallon tsiya kamar wani maye" tashi yyi yaxo ya wuceta ya shige dakin wankan, ranar dai kam ta jima tana masa tausa cikin dakin wankan kafin ya kammala wanka ya fito, kwanciya yyi kan gadonsa ya lumshe idanu,tasan sarai tausa yakeso kafin yyi bacci don shi baya iya bacci hk sai an masa dabara, bimbii kam ita yanzu kam tana tsayuwa ne tare da bata da yalwatacciyar tazara tsakaninta da royal bed na prince, tana mugun shakkar hawa gadon nan yanxu, jin taqi hayowa sai abun ya bashi dariya har ya murmusa sbd ya fahimci abunda take tsoro, daga mata hannu yyi tayi saurin sake masa curtains din data rufe kusurwar da gadonsa ke ciki ta wuce ta fice,shi kuma yabita da kallo yasan abunda tafi so kenan shiyasa ya bata umarnin tfy, washegari bimbii tayi masa rakiya wani taro da sarauniiya dakanta ta shirya a 6angarenta na yanta wasu bayi, prince baya taba sake bimbii ta 6acewa ganinsa duk inda tayi yana binta da kallo a sace, sarauniyya mar'atussaliha kuwa uwace wacce tasan halayyar dan nata ciki da waje, ta lura da kallon dayake bin bimbii dashi a sace, kiran bimbii tayi tazo gabanta ta rissinar dakai sannan ta maida dubanta kan kwayar idanun prince dake kallon bimbii nan take ta warware kanta komai tace" bimbii ta tafi, bimbii ta dawo inda take ta tsaya,sarauniyya mar'atussaliha ta kalli prince da murmushi a fuskarta sosai tace" idan na nemi alfarma a wurinka zakamin kai tsaye" kallonta mahaifiyar tasa yyi cike da mamaki yace" umarninki kawai nk jira na aiwatar" fadada murmushinta tayi tace" toh ina son ka bani wannan baiwar taka" saurin dago da idanunsa yyi yana kallonta, murmushi tayi masa sannan tace" kar damu saika maida tsohuwar baiwarka lenah ko ka sake za6en wata cikin bayi na" qaqalo murmushi yyi ya kalleta yace" meyesa kkson wannan baiwar kawai" itama murmushi tayi tace"kallonta kawai nayi naji ta kwantamin daka ganin tana da zuciya mai kyau" shiru yyi ssnnan ya dago dakansa yace" shikenan ranki ya dade na baki ita saidai......." sai kuma yyi shiru tace" kayi magana dana, fadi abunda kkson fada" murmushi yyi yace" aa, babu komai"ranar dai bimbii ta tattara ta koma 6angaren sarauniyya tabar 6angaren babban prince, wannan abu yyiwa mutane da dama dadi ban dasu israt da basu ji dadin hkn ba,itako bimbii abu yyi mata dadi sosai don hkn yafi nono fari a wurinta, wasu bayin har mamaki suke da suka ga bimbii na nuna farin ciki, lenah itama 6angaren abu yyi mata haske ta koma hidimtawa prince akbar, 6angaren prince kuwa abun babu kyau..........
Littafin nan na kudi ne, idan kina da buqata zaki tura #300 ta wannan acct...0100790419,alhaji shahida nasir,union bank, zaki turomin da screenshrt na payment dinki a whatsapp ta wannan layi...07041195806..
Alkalamin Bintuu ne.....
10/10/20, 1:12 AM - Anti qamshi🌷: *DAREN GOMA SHA HUD'U*🪔🪔
Written By Bintuu Seer
22
*Miss each movement spend with you* you are my medicine.......💕💕
Bangaren sarauniyya mar'atussaliha yana da girma sosai kuma suma bayin dake 6angaren nata wajensu yana da yalwa sosai,bimbii bata samu daki ita kadai ba yadda take a 6angaren prince,hadata akayi da wasu bayi su hudu ita ta zama ta biyar, neman wuri tayi daga can gefen dakin ta ajiye kayanta, yanayin bayin data hadu dasu anan ba kamar su khulood bane ta fahimci akwai tsugumi da baqin ciki a lamarinsu sbd tunda ta aka kawota dakin ba wacce ta mata kallon arziki,ummu nana ta sanar da ita aikinta shine baiwa furannin dake 6angaren gbdy ruwa safe da yamma sannan da tatso nonon raqumi, washegari da sanyin safiya bimbii ta tashi ta bawa furanni ruwa sannan ta dauki kwarya ta tafi tatso nonon raqumi anan suka hadu dasu khulood suna ganinta suka taho da gudu suka rumgumeta, israt tace" bimbii daman arzikinki muke ci jiya kina tfy lenah ta dawo dakin tayi mana korar wulaqanci muka koma dakin hadaka yanzu mu takwas ne a dakin da muke" murmushi bimbii tayi ta janyo hannun israt tace" karki damu komai na duniya dan hkr ne wani lkcin baka cimma kyakykyawar qaddararka kai tsaye har saika qetare'''' manyan qalubale na rayuwa" murmushi sukayi gbdy, khulood tace" wannan hk yake" sunkuyawa sukayi suka soma tsatsar nonon raqumi duk suka cika kwaryoyinsu sannan suka dora bisa kawunansu suna tafe suna hira har suka iso hanyar da zasu rabu su khulood suka wuce 6angarensu itama ta wuce nata 6angaren, prince akbar kuwa ranar kasa runtsawa yyi sai tunani yake dalilin dayasa sarauniyya ta nemi ya bata bimbii har yanzu ya kasa fahimtar manufarta saidai yana da tabbaci tana da manufa nayin hkn don mace ce mai mutuqar hange da fahimtar lamura kuma gata da tarin hikima, kiran ubaid yyi ya shigo ya rissinar dakai a gabansa cike da ladabi,dago dakansa yyi dake jingine bisa wata tattausan kujera ta alfarma ya kalli ubaid dakansa ke sunkuye, yace" kana da wata fahimta kan manufar sarauniyya na amsar wannan baiwa" shiru ubaid yyi na y'an daqiqai yana tunani sannan ya dago dakansa ya kalli babban prince yace" ranka ya dade bani da wata fahimta kan hkn saidai abunda ya bani mamaki shine me yasa sarauniyya ta kira bimbii har gabanta sannan tace ta tafi batare data furta komai ba sannan ta maida dubanta kan idaniyarka, abunda na fahima anan shine akwai wani sirri data gani cikin kwayar idanunka bisa al'muran wannan baiwa taka, ka gafarceni ranka ya dade da wannan hasashe nawa" shiru prince yyi domin amsar ubaid kadai ta haska masa manufar sarauniyya mar'atussaliha,wato ta fahimci sirrin zuciyar prince game da bimbii da take qasqantacciyar baiwarsa, kallon da prince ke yiwa bimbii kawai ya ankarar da sarauniyya cewa d'an nata yana da wani feeling kan wannan baiwa, abunda yasata aikata hkn shine tana gudun faruwar wani babban al'amari zuwa gaba mutuqar bimbii ta cigaba da kasancewa da prince, hkn da tayi na amshe bimbii daga wurinsa tana tunanin shine mafita, cikin kwana biyu kacal prince ya gama jigatuwa da kewar bimbii, hknne yasa ya buqaci ubaid ya kawo masa su israt yana son ganinsu, ubaid yaje ya taho dasu israt da jikinsu har rawa yake sbd tsorota da sukayi na jin wai babban prince nason ganinsu sai sukayi zaton ko wani laifin sukayi, suna shiga bangaren prince suka same shi a zaune kan wata kujerar mai ruwan zinare yana rubuta wata wasiqa,zubewa sukayi bisa guiwowinsu duk suka rissinar da kawunansu, saida ya dauki dogon lkci sannan ya dago da kansa ya kallesu, miqawa khulood wannan takarda yyi yace" gashi ina son ku miqa wannan takardar ga yar'uwarku, idan har kk bari wani yaji ko yaga wannan takarda toh hukunci mai tsauri na tanadar muku" qara sunkuyar dakai sukayi, khulood tasa hannu biyu ta amshi takardar da take nannad'e cikin wani siririn abu tamkar alqalami, yana miqa ya daga musu hannu suka miqe da sauri suka fice, ranar basu hadu da bimbii ba don hk da dare suka fita suka nufi bangaren sarauniyya, masu tsaron 6angaren sarauniyya ba kowanne bawa suke bari ya shiga 6angaren ba saidai idan a wurin kk aiki ko kuma kana hidimtawa daya daga cikin iyalan sarki,hk suka hana su khulood shiga 6angaren, qin tfy sukayi suka koma gefe suna ta tsaye ko zasu gano fitowar bimbii amma shiru, wani wuri suka samu suka tona rami suka binne takardar sbd basu son su koma 6angarensu da ita tsautsayi yasa wani ya gani, su kansu basu san meke rubuce cikin wasiqar ba, washegari da sanyin sfy suka fito suka nufi wurin da suka binne wasiqar suka tono wurin suka dauki wasiqar suka nufi 6angaren sarauniyya suka tsaya bakin kofa suna jiran fitowar bimbii, ita kuwa bimbii tana ciki ta bawa furanni ruwa tana gamawa ta dauki kwaryarta ta fito don tatso nonon raqumi, tana fitowa ta miqe hanya sai kawai ganinsu khulood tayi sun sha gabanta dukkaninsu a dan rikice, kallonsu tayi da mamaki tace"lfy kk kuwa" basu bata amsa ba sai 2waige suke kamar wasu marasa gsky saida suka tabbatar babu kowa wurin sannan israt ta sanya hannu cikin rigarta ta ciro saqon babban prince ta bawa bimbii, sannan suka sanar da ita gargadin daya musu,shiru bimbii tayi tana kallon wasiqar, khulood ta sake waigawa taga ba kowa ta matso kusa da bimbii tace" kiyi sauri ki 6oye ki tabbatar babu wanda yaga wannan saqo wurinki" sauri bimbii tayi ta chusa wasiqar cikin rigarta sannan ta rabu dasu khulood don su ranar qorama suka nufa, ranar bata samu lkcin kanta ba bare ta bud'a wasiqar taga abunda ta qunsa sai da dare data koma dakinsu ta saci jiki ta fito farfajiyar 6angaren ta nemi wurin da babu yalwar kilmawar bayi ta zauna gindin wata bishiyar dabino ta ciro wannan wasiqa ta bud'e, yyi rubutun ne da haruffan larabci, dayake itama tasan baqi hk ta soma karanta wasiqa, gabanta ne ya soma dokawa 2gudu lkcin data soma ganin kalmomin da prince yyi amfani dasu wurin rubutun wasiqar, ba wasu kalmomi bane sai tsantsar yabo da kuma mutunta darensu na farko, yyi mata gdy da kyautar budurcin da tayi masa sannan qarshen wasiqar kalmomi ne dake bayyana kewarta daya yyi cikin wadannan kwanaki sai kuma wasu zafafa kalmomi na soyayya daya soma furta mata karo na farko,bata qarashe karanta wasiqar ba tayi saurin rufe takardar jikinta na rawa ta dafe qirjinta dayake bugawa tamkar ze fashe sbd tsananin tsoro da razana da tayi, kallon takardar take tana tantaman anya prince ne dakansa ya rubuta wannan wasiqa, addu'a ta somayi cikin ranta Allah yasa su israt basu bud'a wannan wasiqar ba, duqunqune takardar tayi ta kutsirtsirata mitsi mitsi ta din ga tfy da nisa tana cillar da kowanne 6angare na takarda wuri daban daban sbd tsantsar tsaro, jiki a sanyaye ta koma dakin nasu ta tarar da abokan zaman dakin nata suna hirarsu ko kallonta ba wacce tayi itama bata sanya musu baki ba sbd akwai abu mafi girma dake dawainiyya da ruhi hade da gangar jikinta don hk bata da lkcinsu, samun wuri tayi ta kwanta, tana rufe idanunta kyakykyawar fuskar prince akbar zata soma mata gizo, miqewa tayi da sauri ta soma mutsitstsike idanunta,kunnuwanta taji tamkar muryarsa yana furta mata wadannan zafafan kalmomi da suka rudata suka gigita tunaninta baki daya,hannu tasa ta soma toshe kunnuwanta, duk bayin dake dakin suka soma kallonta suna tunanin ko ta samu matsalar kwakwalwa ne,6angaren prince kuwa ya rasa kansa sosai, be ta6a tunanin tarkon son wata diya mace zeyi masa irin wannan kamun ba amma sai gashi dare daya ya fada soyayyar qasqantacciya baiwa baqar fata da sun bambamta a komai, tun daga kan nahiya, asali,tushe har ma da kalar fata,riqe kansa yyi kawai ya rasa meke faruwa dashi, jin zuciyarsa yake tamkar zata zage sbd wani irin bugawa da take da qarfi, ga kewar bimbii dake azabtar da gangar jikinsa har ma da ruhinsa,miqewa yyi da sauri ya kira ubaid, kallon ubaid yyi yace" ina son ganin bimbii a wannan dare kasan duk yadda kayi ka kawo min ita" kallonsa ubaid yyi a nutse cike da girmamawa yace"an gama ranka ya dade" fita yyi da sauri, israt ya samu cikin sirri ya buqaci taje 6angaren sarauniyya ta fito da bimbii, sanar dashi tayi bata da damar shiga yankin sarauniya matsayinta na qasqantacciyar baiwa, wani qaramin gate pass ya ciro daga aljihunsa ya bata yace"ki nunawa bayin dake tsaron kofar wannan zasu bude miki kofa ki shiga" amsar gate pass din israt tayi ta tafi da sauri ta nufi yankin sarauniya tana zuwa ta nunawa masu tsaron kofa wannan gate pass suka bata hanya ta shige, bata sha wahala ba ta gane dakin da bimbii take, tana shiga dakin taga kusan dukkanin bayin dake dakin sunyi bacci sai bimbii kawai dake zaune ita kadai kamar wata mara gata, bimbii kamar ance ta kalli kofa taga israt tsaye tana kallonta,tasowa tayi da sauri tazo wurin israt, jan hannunta israt tayi suka fice daga dakin, israt ta kalleta tace" meke damunki hk bimbii yanayinki ya nuna kina tattare da damuwa" bimbii tayi shiru sai kuma ta kalli israt tace" babu komai" kallonta israt tayi kadan sannan ta kawar da waccar mgnr tace" babban hadimin babban prince ubaid shike son ganinki yanzu" dafe kirji bimbii tayi ta kalli israt tace" israt me kk zaton zemin" israt tace" gsky ban da sani kan hkn amma ga dukkanin alamu prince ne dakansa ke buqatar ganinki" take gaban bimbii ya yanke ya fadi, ta soma ja da baya, israt tsayawa tayi tana kallonta cike da mamaki,hannunta tasa ta riqo hannunta tace" akwai abunda ke faruwa ne tsakaninki da prince" girgixa kai tayi da sauri alamar aa, jan hannunta israt tayi suka soma tfy har suka fice daga yankin sarauniyya suka din ga wuce kusurwa kusurwa har suka qarasa inda ubaid ke jiransu, yana ganinsu yyi murmushi yace israt ta tafi sannan ya kalli bimbii yace" babban prince nada buqatar ganinki" juyawa yyi ita kuma ta soma bin bayansa cike da sanyin ciki kamar kaxar da kwai ya fashewa a ciki, gabanta kuma sai cigaba da faduwa yake har suka qarasa 6angaren prince, suna shiga suka tarar dashi zaune lenah na tsiyaya masa green tea, shigowarsu ne yasa shi dago da lumsassun idanunsa ya saukesu kan bimbii,lenah kuwa tana gama zuba masa tea din ta sunkuyar dakanta qasa sannan taja baya tana jira umarninsa,daga mata hannu yyi alamar ta tafi,rissinar dakanta ta sakeyi sannan ta juya da niyyar fita, mamki. tayi sosai na ganin bimbii tsaye a gefe,wata uwar harara ta aika mata sannan ta fita ranta a mugun 6ace, ubaid yana shigo da bimbii shima ya rissinar dakai,prince ya daga masa hannu ya fice, suna fita dukka ya rage sai bimbii kawai, yana daga zaune idanunsa na kanta ya kasa dauke kai,ita kuma ta kasa gaba ta kasa baya tana tsaye kawai wuri daya, sun dade a hk kanta na qasa ya taso a hnkli ya tako har inda take, matsowa yyi sosai tamkar zasu manne, ita kuwa take zuciyarta ta tsananta dokawa ta soma neman matsawa amma sai yyi saurin take mata kafa, zafi taji sosai ta dago dakanta tana kallonshi, dage mata gira daya yyi, cikin tsantsar dabara da hikima yyi mata jan bazata ta afko kirjinsa ya hannunsa duka ya mata daurin kazar kuku ta yadda bata da damar raba jikinta da nashi, kallonsa take cike da tsoro saita fara masa kuka, murmushi yyi ya dora fuskarsa saman nata ya rufe idanu itama ta rufe idanu suna sauraron bugawar zuciyoyinsu dake bugawa a tare kuma da qarfi, hannunsa ya dora kan kirjinta sannan ya kamo hannunta ya dora kan nashi qirjin, yace" wannan kawai ya tabbatar miki prince bazai iya rayuwa babu ke kusa dashi hkma kema bazaki rayuwa babu ni ba sbd bugawar zuciyarmu daya" shiru tayi tana jinsa amma taqi bude idanu gashi jikinta ya mutu murus bata da qarfin aiwatar da komai, sunkuyawa yyi yasa hannu ya cire mata wannan tsohon zoben dake yatsan hannunta na dama ya sanya mata wani na danyar azurfa daidai hannunta, jin jikinsa yake wani iri ya tabbatar idan har ya cigaba da kasance da bimbii toh ze sake tabargaza, janye jikinsa yyi a hnkli ya juya mata baya, daga mata hannu yyi ya bata izinin tfy batare daya juyo ya kalleta ba don baya son ta fahimci halin dayake ciki, juyawa tayi ta soma tafiya zata fita sai kuma ta jiyo ta dawo da baya, muryarta kawai yaji tace" idan za'a fara soyayya dole sai zuciyoyi biyu sun aminta da juna don cikin soyayya babu izzah bare nuna fin qarfi, idan daka shawarceni ko ka nemi amincewa ta zan fada mk cewa akwai wanda nkso, na bashi zuciyata tunkan yanzu kuma har gobe shi nk so, ka huta lfy" jin maganganunta yyi tamkar saukar ruwan dalma don prince mutum ne mai tsananin kishi musamman ga abunda yakeso, juyawa tayi zata tafi kawai taji ya damqo hannunta, idanunsa jajir dasu yace" soyayyata tana da tsada sosai nikaina na rasa yadda akayi qasqantacciyar baiwa kamarki ta samu zuciyata a araha da rahusa dare daya, toh ki sani duk wanda zaki so a baya na yake ko kin manta nina amshi budurcinki ba wani ba, ki sani soyayyarki itace babban kuskuren dana aikata ga dukkanin wani jini na sarautar burham, wannan irin soyayya ita ake kira haramtacciya a ilahirin wannan masarauta......ki amshi soyayyata ko karki amsa wannan za6in ya rage naki amma ina qara tuna miki ki kwana kullum cikin tuna matsayinki gareni ba kowa bace illah qasqantacciya baiwa mai mini hidima, ina da cikakken iko akanki" kallonsa bimbii tayi sannan tayi murmushi tace" idan da zaka zare kalmar so kabarni matsayin qasqantacciyar baiwa hkn shine farin ciki na" tana gama fadar hk ta juya ta fice daga sashin nasa tabarshi zaune ya dafe kansa dake juya masa, gani yake idan har bimbii taqi aminta da soyayyarshi zuciyarshi zata iya tarwatsewa........babbar baiwa ga sarauniya mar'atussaliha kuwa ummu nana tuni ta miqa zancen zuwan bimbii ga babban prince wurin sarauniya, shiru sauraniya tayi sannan ta dago dakanta ta kalli ummu nana dakanta ke sunkuye tace" ina son ganin azeez" jikin ummu nana har rawa yake ta fita don kiran azeez....azeez shine sarkin hukuncin dauri...............
Littafin nan na kudi ne, idan kina da buqata zaki tura #300 ta wannan acct....0100790419,alhaji shahida nasir,union bank....saiki tura screesht ta whatsapp a wannan layin 07041195806......
Alkalamin Bintuu ne.....
10/10/20, 1:12 AM - Anti qamshi🌷: *DAREN GOMA SHA HUD'U*🪔🪔
Written By Bintuu Seer
23
*Believe the power of love which make a king to be a servant and a servant to be the king*............I miss you like crazy......💕💕
Tana hakimce a wata kujerar ta alfarma cikin fadarta, ummu nana suka shigo tare da azeez sanye yake da baqaqen kaya,fuskar nan tasa babu yalwar fara'a duk suka rissinar dakansu a gabanta suna jiran umarninta, kallon fuskar azeez tayi yyi saurin dago da kansa,tace" ina son ka sace babbar baiwar prince dake hidima a 6angaren nan ka miqata babban kurku, bani son kowa yasan tana wannan kurku,sai a yad'a cewa tsohuwar baiwa ga prince ta gudu, wannan sirri ne tsakani na daku kawai bani son kowa ya samu wannan labari cikin wannan masarauta sbd wannan itace hanyar dazan ita ku6utar da prince daga fadawa fushin mahaifinsa sannan na dakatar da faruwar wani al'amari mai girma cikin wannan masarauta" gbdy suka sake rissinar da kawunansu alamar yin biyayyar ga umarnin sarauniya, daga musu hannu tayi suka juya suka fice daga fadar nata,dare nayi bimbii ta fito shan iskarta, batason zaman wannan daki sbd duk bayin dake suke zaune daki daya da ita basu kulata shiyssa duk dare take fita shan iska,tayi nesa sosai da farfajiyar 6angaren nasu ta nemi wani qaramin tudu ta zauna ta tsirawa wannan zobe da prince akbar ya bata idanu, motsi taji a bayanta tamkar motsin mutum, miqewa tayi da sauri cike da tsoro sbd wurin babu yalwar jama'a tana waigawa taji an toshe mata baki, tuni ta fadi a wurin suka dauketa suka sanyata cikin wani keken doki, hk suka din ga tfy har suka isa babban kurku, masu tsaron kofar basu san wacce bimbii sudai suna ganin azeez suka bude musu katuwar kofar kurkun suka shige da bimbii, sun samar mata da daki na qarshe a jerin dakunan dake kurkun, dakin tsagaye yake da manya qarafa masu kauri yadda babu wani mahalukin dazai iya 6allasu, kasan kurkun busassun ciyayi ne aka zuba,hk suka shigar da ita ciki suka watsata tamkar wata shara, har lkcin bimbii bata dawo cikin hayyacinta batasan abunda ke faruwa da rayuwarta ba saida sanyin asubahi ya soma ratsata ta bude idanunta a hnkli tana qarewa inda ta samu kanta kallo,wasu hawaye ne masu dumi suka soma ambaliya a fuskarta ta tashi zaune a hnkli tana cigaba da kallon inda ta kuma tsintar kanta, wahegari, bayin dake kwana tare da ita suka ga basu tashi da ita, basu kawo komai sai sukayi zaton tashi wuri tayi ta fice bakin aikiinta, jita jita ne ya soma yawo cikin wannan masarauta cewa daya daga cikin bayi dake hidima a 6angaren sarauniya ta samu nasarar gudu,su israt kuwa basu ta6a kawowa cewa bimbii ce ta tsere ba, ranar dai basu ganta, yamma nayi suka gama 2aikacensu suka koma dakin da suke suna shirin kwanciya suka ji ragowar bayin dake dakin suna hirar, israt ce ta juya da sauri ta kalli daya daga cikin bayin dake hira tace" don Allah wacce baiwa ce ta gudu" kallonta dayar tayi tace" tsohuwar babbar baiwar da prince yabarma sarauniya mn" daya daga cikinsu tace" ai kamar ma ina yawan ganinku tare da ita a bakin qorama" israt da khulood duk suka kalli juna a rikice, miqewa israt tayi da sauri tayi hanyar waje cike da rudani, khulood ma ta miqe da sauri tabi bayanta, saurin riqo hannu israt tayi da taga ta nufi 6angaren prince sbd ta lura bata cikin hnklinta, juyowa israt tayi a fusace ta fizge hannun daga riqon da khulood tayi mata sai kuma ta tsaya chak ta juyo ta kalli khulood tace" khulood wannan abu baki tunanin akwai sarqaqiya cikinsa sbd nasan bimbii ba zata ta6a tunanin gudu ba, anya babban prince baida hannu a wannan abu kuwa sbd na lura kamar ya takura mata dayawa" khuloo ta jata suka samu wani wuri suka zauna, kallonta israt tayi tace" nikam a yadda nk gani kamar akwai wani 6oyayyen al'amari tsakanin babban prince da kuma bimbii kamar hkn shine ze sata tayi yunqurin gudu" israt tayi ajiyar zuciya sannan tace" tabbas wannan hasashe naki hkne duk da bani da masaniya amma akwai abunda ke tsakanin prince da bimbii sbd ina yawan ganin damuwa tattare da ita, bani son matsa mata da tmby ne kawai" khulood tace" mu tayata da addu'a kawai kar su samu damar kamata" jinjina kai israt tayi alamun nuna gamsuwa da abunda khulood ta fada, 6angaren prince kuwa fitowarsa daga wanka kenan yana sanye da wasu kaya masu mutuqar taushi, zama yyi a wata kujera lenah ta matso ta soma tsiyaya mata ginger tea, daukan cup din tayi ta miqa masa da hannu biyu tare da rissinar dakanta qasa, amsar cup din yyi ya soma sipping a hnkli yana tunanin bimbii, zagayawa tayi ta bayanahi ta soma masa tausa a hnkli, ubaid ne ya shigo da sauri ya tsaye gaban prince tare da rissinar dakansa qasa, kallon ubaid yyi yasan yana tafe da wani labari mai muhimmanci sbd fuskarsa ta nuna hkn, dagawa lenah hannu yyi ta dakata da masa tausan ta sunkuyar dakanta qasa sannan sum sum ta wuce ta fice, ubaid ne ya matso da fuskarsa daidai kunnen prince ya rada masa wani abu, wata irin zabura prince yyi ya miqe tsaye tare da dire qaramin cup din dake hannunsa saman small table din dake gabansa, shi kansa ubaid cika yyi da mamakin yanayin da prince ya nuna,batare daya sake kallon inda ubaid yake ba yyi hanyar waje da sauri ya fice, ubaid ya rufa masa baya, hk suka isa 6angaren sarauniya mar'atussali, saida suka din qetare kusurwa kusurwa suka samu shiga cikin fadarta, ubaid yaja ya tsaya a kofa shi kuwa ko neman iso beyi ba ya afka ciki, bayi ne jere ta 6angaren dama da hagunta wasu cikinsu na mata fifita, ita kuma tayi ado na manya gwalagwalai tunda daga wuyanta har kunnuwanta da kuma hannayenta, batayi mamakin ganinsa ba don daman abunda take jira kenan guduwar bimbii yakai kunnensa, qarewa suturar dake jikinsa kallo take sbd gani tayi kayan bacci ne ma sanye jikinsa hkn ya kuma tabbatar mata da gskyr abunda ta gani cikin kwayar idanunsa, dagawa bayin dake tsatstsaye tayi hannu suka soma ficewa,zuba masa idanu tayi tana sauraron abunda ya kawoshi gareta,neman wurin yyi kan kyakykyawan turkish center carpet din dake malale ta cikin wata kusurwa ya harde kafafunsa, tasowa tayi itama a hnkli ta soma sakkowa daga tudun da kujerar alfarma da take zaune akai ta shiga wannan kusurwa ta zauna bisa wata lumshashshiya kujera mara tudu tana kallon prince, kallon shima yyi sannan ya soma mgn yace" ranki ya dade wani labari nakeji na guduwar baiwar dana bar miki shin wannan zance gskya ne" murmushi tayi sannan tace" tabbas hk abun yake saidai dakaran tsaro na nan suna bincike kan guduwar nata sbd an jima ba'a samu wani bawa da laifin gudu ba" shiru yyi batare daya kuma furta komai ba, tunani kawai yake abunda yasanya bimbii gudu tabarshi da dakon so, nutsawa cikin tunani yyi sai yake zaton ko furta mata kalmo so da yyine ya tsorata ta yasa ta gudu daga masarautar,dafashi sarauniyya tayi fuskarta dauke da murmushi tace" yakai wannan prince ka sanar da mahaifiyarka ma'anar wannan damuwa data bayyana qarara a fuskarka dalilin guduwar wannan qasqantacciyar baiwa" dago da idanunsa yyi da bbu komai cikinsu sai tsananin tashin hnkli ya qure mahaifiyar tasa da idanu, ita kanta ta tsorata dashi batayi tunanin soyayyar baiwar ta masa wannan illar ba, kunsan tsakanin uwa da d'a take wani tausayinsa ya shigeta, bece mata uffan ba ya miqe ta dago idanunta tana kallonsa har ya fice, ubaid na ganin fitowar tasa ya rufa masa baya don shi ko kallon inda ubaid ke tsaye beyi ba ya wuce abinsa, yana komawa 6angaren nasa ya janyo farin dokinsa ya haye ya zabureshi da mugun gudu shima ubaid yahau nasa ya rufa masa baya, ba ko'ina suka tosa ba sai filin sukuwar dokin da suka tsinci bimbii, tsayawa yyi yana kallon hanyoyin da suka rabu gida biyu, kallon hanyar da tayi damansa yyi batare da wata shakka ba ya dunfari hanyar bisa dokinsa mai tsalelen gudu,hk yyita zabga gudu bisa kan namijin dokinsa babban hadiminsa na take masa baya har suka soma shiga cikin gari, hknne yasa yaja linzamin dokinsa ya tsaya yana qarewa ko'ina kallo, juwaya kawai yyi dakan dokinsa ya koma baya, suna zuwa daidai inda ya ta6a bangaje bimbii da doki ya tsayar dakan dokin nasa sannan ya diro yana qarewa wurin kallo, ranar sai tsakar dare suka koma masarauta ya shige 6angarensa yace" kar abar kowa ya shigo masa baida buqatar ganin kowa" take masu tsaron kofar suka rufe kofar shiga 6angaren nasa, yana shiga ya nemi kan wata kujera ya zauna tare da jinginar dakansa cike da tsantsar damuwa da rudani, wata qaramar locker dake manne da table din dake gabansa yaja ya sanya hannu ya fito da wani qaramin akwati mai kyan gaske ya bude akwatin ya fito da wadannan awarwarayen daya ta6a ciresu daga hannun bimbii yana qare musu kallo tare da jujjuyasu a hannunsa, ranar dai prince kwanan zaune yyi don be bawa bacci lasisin saceshi......
10/10/20, 1:12 AM - Anti qamshi🌷: *A bitter sweet love affair with so much struggling and challenges* I'm waiting for you like crazy,pls come back to me my life.....💕💕
Sati biyu kenan da 6acewar bimbii daga masarautar burham dayawa sun mance da batunta idan aka dauke prince akbar da duk wayewar garin duniya sai ya fita neman bimbii ya gama zaga gari ya dawo babu labari, daga qarshe kawai ya soma bin duk wata kasuwa ta saida bayi, duk kasuwar daya shiga hk zaka ga masu cinikin bayi na binsa da gudu suna masa tallan bayi ko za'a samu irin wadanda yakeso, idan ya qarewa bayin kallo be ga wacce yake nema ba sai yyi gaba abinshi, babban hadiminsa ubaid na take masa baya domin idan zeyi irin wannan fitar ta sirri baya fitowa da sauran masu tsaron lfyrshi, ubaid shine na hannun damansa ya bashi daman sanin dukkanin sirrinshi sbd ya yarda dashi dari bisa dari dashi kadai yake fitowa, ubaid yana mutuqar tausayin prince yadda yaga ya zurfafa kan soyayyar wannan baiwa wanda tabbas yasan hkn na iya kawo fitina ba qarama ba cikin gdn sarautar burham, ranar ma hk suka koma gd babu wani kyakykyawan labari, bayan yyi wanka ya zauna ya zurfafa tunani kan wannan abu daya faru, nasarar gudu ga bawan dake masarautar burham ba abu ne mai sauqi ba sbd tsatstsauran matakan tsaro ta kowacce kofa,idan kuwa hkne taya bimbii har ta samu nasarar tserewa batare da kowa daga cikin dakarin dake tsaron kofa sun ankara ba,sunkuyar dakansa yyi yana tunani sosai don gani yake kamar da akwai lauje ciki nad'I cikin wannan abu, kiran ubaid yyi dake bakin kofa a dogare, shigowa yyi da sauri ya iso gabansa tare da rissinar dakansa qasa, dago idanunsa yyi da suke jaji dasu tamkar yyi kuka ya kalli ubaid yace" kaje kayimin bincike na musamman kan yadda abun ya faru" ko be nemi qarin haske ba yasan me prince ke nufi, rissinar dakansa yyi alamar amsar umarni, daga masa hannu prince yyi sannan ya fice don aiwatar da abunda aka umarce shi, yana ganin ya fita ya maida kansa ya kwantar jikin kujera dayake zaune,lenah ce ta shigo hannunta riqe da qaramin basket na kayan marmari taje kan table dake gabansa ta ajiye, ta fito da yar qaramar wuqa ta dauki tuffa daya tayi slicing dinta gida hudu tana daukan slice daya daga cikin yankan tana miqa masa idan yaci saita qara masa wani,slices biyu kawai yaci ya daga mata hannu alamar ya isa hk, daukan basket din tayi ta fita dashi sannan ta dawo taci uwar kwalliya tamkar wacce zata gasar sarauniyar kyau, sanye take cikin wata abaya fara sol ta rufe ko'ina na cikinta amma bakinta yadau jan janbaki sai daukar idanu yake abunku da farar fata, gashi ta tsayar da eye lashes na idanunta hkn yasa gashin idanun nata yyi duhu, kafarta bbu takalmi don daman ba'a shiga 6angaren nasa da takalmi, tunda ta shiga yake kallonta amma a zahiri gixo take masa sai yake mata kallo da bimbii, ita kuma ganin yana kallonta sai tayi zaton ta yaudaro hnklinsa kanta ne, murmushi tayi ta wuce kan royal bed nasa ta hau ta zauna tana jiran ya gama abunda yake ya hawo ita kuma ta soma mishi tausa daga nan ta qure basira da hikimarta ko Allah ze bata sa'a prince ya amshi budurcinta daren yau, prince kuwa ya jima yana 2karancensa sannan ya taso ya nufo gadon yahau, yanayin kwanciyar da yyi kawai ya nuna mata baya buqatar komai daga gareta, duk bayin dake masa hidima sun san alamomin mgnrsa koda be furta komai ba idan yyi wata alamar suna gane abunda yake nufi, idan yana son tausa ze kwanta ya juyo bayansa idan kuma ba hk ba toh tsakanin biyu za'ayi daya ko ki tafi ko kuma dai yana buqatar wani abun daban, itama yanzu tana ganin ya kwanta fuskarsa na kallon sama taja gefe sai kuma taga ya daga mata hannu, jikinta a mugun sanyaye ta sakko daga gadon ta sake masa curtains din dake kame gefe gefen kusurwar sannan ta juya a hnkli ta soma tfy har ta fice, 6angaren bimbii kuwa Izuwa yanzu ta gama jigatuwa, abinci sau guda kawai ake basu ga ciwo dake cinta a hnkli amma cikin masu tsaron wannan kurku babu wanda ya kalleta bare tasa ran zasu bata magani, qishirwa kawai ze iya kar mutum cikin wannan wuri don kusan kullum ma sai an fitar da fursunonin da suka mace a dakunansu, su kuwa masu tsaron wannan kurku zuciyarsu a bushe da rashin imani, hk zasu fito da gawarwakin mutanen da wahala ta kashesu su zubasu cikin keken doki aje a watsasu a babban kogi ruwa ya tafi dasu, dayake zuciyar tasu babu ko digon imani basu dauki ran mutum bakin komai ba, bimbii zazza6ine sosai yake wujijjigata kwana biyu amma babu yasan tanayi iyakarsu da furnoni shine duk safiyya su miqa musu abinci a wani qaramin akushi sai ruwa a wani cup na katako, hk zasu dauka suna ci tamkar mayu, bimbii tayi duhu ta lalace sai dogon hanci da manyan idanu da kuma dogon suman kanta daya hargitse ya sake fallasa tsantsar wahalar da take fuskanta, ruwan hawaye ya qare mata kawai kukan zucci take fama dashi da tafasar ruhi, burinta a yanzu shine mutuwa ta kawo mata ziyarar gaggawa, Allah kuma yasa qarshen wahalarta kenan, cikin dare ciwo ya tsananta mata sai murqususu take tana kakari sbd azaba ga gumi dake fama keto mata ta ko'ina, jan jikinta ta somayi har ta qarasa bakin kofa ta miqe zaune a hnkli tana buga kofar da hannunta ko zasu jiyota amma babu wanda ya jiyota har dan qarfin da yyi saura jikinta yyi qasa ta koma ta kwanta kawai, sai safiyya suka bude don ajiye mata abinci suka tarar da ita cikin wani irin yanayi na tsananin ciwo, fito da ita sukayi suka kaita wani babban daki da suka jibge masara lfy, daya daga cikin masu kula da marasa lfyn ana shigo da bimbii ta kalleta sannan ta koma tsaya bisa kanta, wasu yan 2kalle tayi kawai a jikin bimbii ta dago dakanta ta kalli wadanda suka shigo da ita tace" wannan sabuwa ce koh?" daga mata kai sukayi alamar ehh, tace"tana da aure ne?" duk suka kalli bimbii dake kwance a qasa gefe guda tana fama da ciwon dake dawainiyya da ita,dayan yace" gsky bamu sani ba ko tana da aure ko bata dashi" wani yace" ni ban san lkcin ma da aka kawota bare laifin data aikata" kallonta matar tayi tace" kina da shigar ciki shine ke wahal dake" bimbii na daga kwance a qasa ba lfy amma tana ji matar ta ambaci kalmar ciki tayi wani irin zabura ta miqe zaune ta kalleta tace" ciki?ciki kkce ina dashi?toh cikin uban wa?" tsabar rudewa yasata jero wadannan tmbyoyi tamkar wata zautacciya, matar bata kuma kallon inda take ba ta kalli wadanda suka shigo da ita cikin wurin tace" gsky bana jin tana da aure" cikin sauri suka juya suka fita, bimbii kuwa tana daga zaune ta dawo kamar wata mutum mutumi tunaninta ya tsaya chak, gbdy kwakwalwarta ta dakata da duty sbd tsabar dimaucewa da tayi, su kuwa wadanda da suka fita kai tsaye 6angaren azeez sukayi suka sanar dashi cewa an samu wata mai dauke da ciki cikin fursunoni mata amma basu tabbatar ko tana da aure ko bata da aure ba tinda su basu san lkcin da aka kawota ba ma,miqewa azeez yyi da hanzarinsa suka nufi wannan dakin da ake ajiye fursunoni marasa lfy, nuna masa inda bimbii ke zaune sukayi, qare bimbii kallo yyi tuni ya ganeta, mamaki ne sosai ya kamashi dalili kuwa yasan dai bimbii babbar baiwa ce ga prince akbar kuma kowa shaida ne prince akbar be ta6a kusantar kowacce daga cikin bayinsa sbd babu wacce har aka samu ta fito wankin budurci, idan kuwa hkne toh daga ina babbar baiwa guda ga dan sarki kuma jinin masarautar burham ta samo ciki,wannan lalle al'amari ne mai girman gaske don kowa tabbas kowanne cikakkiyar budurwa yake za6e kuma bayanshi babu mahalukin daya isa ya ratsa gonarshi ko ya kusanci baiwa ko karya kusanceta ita dai ta haramta ga kowa mutuqar ta taka wannan matsayi,yana gama wannan tunani ya juya ya fice batare daya furta uffan ba sbd duk wurin babu wanda yasan wacce bimbii ko kuma daga inda ta fito sbd abun sirri ne, shiyasa yana fita be tsaya ko'ina ba sai fadar sarauniya mar'atussaliha don sanar mata da wannan al'amari mai girman gaske, ummu nana ce tayi masa iso ya shiga yana shiga ya rissinar dakai gabanta yyi shiru yana shirin ta bashi umarnin yin mgn,ita kanta tayi mamakin ganin batare data nemi ganinshi ba hkn yasa ta soma tunanin ko wani ya fidda sirrinta ne, ummu nana ce ta sanar dashi sarauniyya ta bashi damar mgn, sai lkcin ya dago dakansa ya kalleta yace" ran wannan sarauniya ya dade nazo miki da wani babbar al'amari" kada masa kai tayi alamar tana sauraronsa, sake rissinar dakansa yyi yace" wannan baiwa da hukuncin daurinta yake kai tsaye daga fadarki an sameta da zaunannen ciki tare da ita" zumbur sarauniyya ta miqe tsaye tana nuna shi da yatsa a mutuqar fusace tace" wannan kuma qarya kk mutumin banza kawai, babbar baiwa ga babban prince a ina zata samu ciki, kowa ya shaida tun aka za6eta bata fito wankin budurci bare ace ya kusanceta koda ya kusanceta tayi ciki tabbas tana hukunci mai girma bare bai ma kusanceta toh idan kuwa a wani wurin ta samo ciki nayi rantsuwar da girman Allah saita gwammace mutuwarta da azabar da zata dandana don wannan tozarci ne ga jinin sarautar burham"...........
Littafin nan na kudi ne, idan kina da buqata zaki tura #300 ta wannan acct...0100790419,alhaji shahida nasir,union bank,saiki turon da screenshrt ta wannan layi ...07041195806......
Alkalamin Bintuu ne...
10/10/20, 1:12 AM - Anti qamshi🌷: *DAREN GOMA SHA HUD'U*🪔🪔
Written By Bintuu Seer
25
*My days of deepest sorrow and pain*........heart full of fear💕💕
Dukkaninsu kowa yyi shiru ya sunkuyar dakansa qasa, sarauniyya ta kuma kallon azeez cike da tsantsar 6acin rai tace" ka koma ka sanyata cikin dakin ukuba har sai ta bayyana wannan ciki dake jikinta na waye? amma kar kuyi sake wannan sirrin ya fita har wani yaji" rissinar dakai azeez yyi da sauri sannan yaja da baya ya fita, miqewa tayi ta soma zarya ta kasa zaune ta kasa tsaya tana mutuqar shakkar wannan zance yakai ga kunnen sarki abdallah bin jabal, ummu nana dake tsaye gefenta ta dago dakanta tace" ranki ya dade ki bani dama na dauki yarinyar nan kawai na damqata ga masu cinikin bayin dake tfy habasha su maisheta nahiyarta" saurin kallonta sarauniyya tayi sannan tayi shiru sai can ta dago dakanta tace" wannan shawarar ba mai amsuwa bace yanzu sai na gama binciken mamallakin cikin dake cikinta bana fatan ta kasance da wani abu mai kama da jininmu a tare da ita"kada kai ummu nana tayi alamar gamsuwa da mgnr sarauniya mar'atussaliha, azeez yana komawa yasa aka dauki bimbii batare da sun duba halin da take ciki ba yyi umarni a shigar da ita dakin azaba, batare da 6ata lkci ba suka shigar da ita wannan baqin daki suka dorata kan wata kujera aka daddaure mata hannuwa da kafafu, wata shafadediyar bulala suka soma tsula mata, saukar bulalar sau daya kawai ya dauke ganinta na wasu daqiqai kafin ta dawo hayyacinta sun sake zabga mata wata, azeez na gefe yana kallonta sannan yace" ki fadamin cikin dake jikinki na waye" kallonsa tayi da idanunta da suka kumbura sannan ta dauke kanta, kunsan bimbii idan ta sanya taurin kai ko za'a kasheta bata mgn, hk tayi musu shiru su kuwa basu fasa tsala mata wannan mugur bulala mai tfy da fatar jikin mutum ba, kallonta azeez yyi yace" wannan itace tmby ta qarshe dazan kuma miki wannan cikin dake jikinki na waye daga ina kk samo shi, idan baki bani amsa ba toh sai mu gwada miki azabarmu ta gaba" wuta taga sun kunna a wasu dindinan ginin qasa suka sanya wasu qarafa su jajir, kallonta yyi ya nuna mata wadannan qarafa yace" yanzu zaki ji saukar su a jikinki hkn yasa ki bude baki kiyi mgn"sunkuyar dakanta tayi qasa tana jiran su soma aiwatarwa ta rantse ko zasu kasheta basu sanin waye mamallakin cikin dake jikinta, 6angaren ubaid kuwa tunda prince akbar ya bashi umarnin bincike kan guduwar bimbii be dire binciken nasa ko'ina ba sai 6angaren sarauniya sbd hk kawai jikinsa yake bashi kamar dasa hannun sarauniya kan wannan lamarin qila hkne ma yasa ta amshi bimbii a matsayin baiwarta, duk yadda yyi saida yyi yasa israt da khulood suka koma 6angaren sarauniya da hidima sbd yana da alfarma shima a matsayinsa na babban hadimi ga babban prince be samu mtsl ba ummu nana ta karbesu ta hannun ummul shukri sam ita batasan dangantakarsu da bimbii ba, ubaid ya umarcesu su sanya idanu sosai kan dukkanin shige da ficen dake wakana a fadar sarauniyya mar'atussaliha, fitowar israt kenan daga babban kitchen taga shigowar azeez ummu nana tayi masa iso ya shiga don ganawa da sarauniyya, saurin ajiye kwandon tayi ta waiga hagu da damanta taga babu wanda ke ganinta ta lalla6a ta nufi wurin kofar shiga fadar sarauniyya ta tsaya da can nesa ta hango kuyangin bayin dake tsaye bakin kofar shiga fada, dakewa tayi ta qarasa wurin ta shiga cikin jerinsu tare da sunkuyar dakanta qasa, dayan dake qarshe ta wurin kofa tana ganin israt sai tayi zaton tana cikin masu zuwan rana waton bayin dake amsar dutynsu da rana, fita tayi daga jeri ta tafi sbd tana da uxiri mai qarfi, hkn yyiwa israt dadi sosai, wayancewa tayi ta mannu da kofa sosai tayi qasa kamar tana gyara doguwar rigar dake jikinta, karaff, ta jiyo sautin sarauniyya tana fadar wasu zantuttuka masu kama da al'mara,umarnin da saurauniya ta bawa azeez shine kalmar qarshe data iya jiyowa tayi saurin miqewa ta tsaya qam tare da sunkuyar dakanta qasa yadda taga bayin dake kofar sunyi, daidai lkcin taga fitowar azeez, tana tsaye duk ta qagu ta rasa yadda zata fice daga cikin jerin bayin don daman su uku ne kuma idan suka ga ta fita hk zasu zargi wani abu tattare da ita, tana nan tsaye har ummu nana ta fito kallonsu tayi tace" toh kuje yanzu wasu zasu zo" ita sam bata gane israt ba sbd daman su uku ne kuma ukun ta gansu, sauran suka kalli israt amma ganin da sukayi ummu nana batayi mgn game da israt din ba sai suka juya suka soma tfy daya bayan daya kamar yadda al'adar aikin ta nuna musu,israt kuwa qasa tayi da kanta har suka wuce sauran ita kadai saida ta tabbatar sun wuce kuma ummu nana ta koma ciki itama ta janye jiki ta wuce bata tsaya ko'ina ba sai 6angaren prince, hango ubaid tayi dogare a kofar shiga 6angaren prince, tun shigowarta ya ganota be bari ta qaraso ba ya janye jiki yabi ta wata kofa suka hadu, cikin saurin ta damqa masa takardar dake hannunta bata tsaya wata mgn dashi ba sbd tsaro ta juya ta koma bakin aikinta, shima sanya takardar yyi cikin aljihunsa yyi tfyrsa, saida ya samu wuri mafi sirri ya ciro takardar ya duba, abunda ya gani cikin takardar ne yasa shi sake kallon takardar batare da wani 6ata lkci ba ya nufi komawa 6angaren prince, yana shiga lenah ya gani ta sanar dashi prince bazai samu ganinshi ba yana kwance, kallonta yyi yace" kije dai ki fada masa mgnr tana da muhimmaci" kallonsa tayi tare da murmushi tace" ya kk mgn kamar wani baqo ga dokar wannan 6angare, ni kaina bani da daman iya masa ida baida buqatar hkn" shiru ubaid yyi yana sake duba yanayi yaga lkci na neman kwacewa yasan su waye hadiman babban kurku basu da tausayi bare imani tsaf zasu soma gana mata azaba kamar yadda sarauniya ta bada umarni, qara kallon lenah yyi yace" don Allah ki taimaka ki sanar dashi" haushin ya bata ta harareshi tayi juyawarta ta kyaleshi wurin,juyawa yyi da hanxari don yasan komai nacinsa be isa yaga prince yanzu ba, wurin wata bishiyar magarya ya tsaya ya ciro wani uzir ya hura da qarfi, sai ga wata kyakykyawar tsuntsuwa ta taso da gudu daga gabas ta nufo inda yake ta sauka a kafadarsa, saman wannan bishiyar magarya anan shekar wannan tsuntsuwa yake, sautin wannan uzir ne ke kiranta idan har ba tayi nisa ba,wannan tsuntsuwa ta prince akbar ce tana da tarin baiwa da fiqira daya banbanta ta da sauran tsuntsaye ba inda bata shiga a 6angaren prince akbar sannan duk inda ya aikata bata kuskuren isar da saqo, tasan ubaid sosai don shine kawai da prince ke kiranta da qarar uzir, daukanta ubaid yyi ya qulla mata saqon wata qaramar takarda a kafafunta sannan ya dagata sama ya kalli kudu da ita saitin 6angaren prince akbar ya saketa ta tashi firrrrrr, wannan tsuntsuwa bata tsaya ko'ina ba sai 6angaren prince akbar tasauka har tsakiyar gadon kwanansa daga gefensa, idanunsa na rufe hannunsa dafe da saitin zuciyarshi numfashinsa na sauka a hnkli, kansa ne ke tsananta ciwo,kukan wannan tsuntsuwa tasa yaji kusa dashi, bude idanunsa yyi a hnkli ya kalli gefen nasa ya hangota tana kada masa fika fikanta, tashi yyi zaune yana murmushi yasa hannunsa ya dauketa yana shafata, kafarta ya kalla yaga wata qaramar takarda a daure,hannunsa yasa ya cire takarda yana cirewa ta tashi firrrrr ta fice abinta don ta isar da saqonta, warware takardar yyi ya soma karantawa,be qarasa gama karanta abunda ke takardar ba ya sakko daga gadonsa da mugun sauri ya fice, ubaid kuwa na tsaye daga kofa yana ganin fitowarsa ya rufa masa baya, dokinsa ya hau ransa baqinqirin tamkar garwashin wuta, a wani irin sukawane ya dauki hanyar wannan babban kurku ubaid shima yana yana take masa baya, hk suka din ga qetawa ta cikin duwatsu da shuri har suka fara hango ganuwar kurkun, a cikin kurku kuwa azeez jira yake qarafan nan suyi jajir ya soma manna mata a jiki har saita magantu, ita kuwa fuskar nan nata tayi jajir saboda kwanciyar jini, idanunta sun kumbura har sun soma hadewa kamar zasu rufe, jikinta kuwa duk ya farfashe ko a hk suka kyaleta sai tayi jinya maikyan gaske, azeez tsugunawa yyi gabanta ya ciro daya daga cikin qarafan dake wutan yyi jajir tamkar zuga zugi yasa hannunsa yaye mata doguwar rigar dake jikinta yana shirin yin sama da ita ya manna mata qarfe a tsakanin cinyoyinta, tana ganin hk ta rufe idanunta rufe tana shirin taji saukar qarfe amma sai taji akasin hk don kunnenta ne ya jiyo mata sautim muryar da har yau bata mancewa, hancinta kuma ya jiyo mata qamshinsa,wata irin tsawa mai tsananin rikitarwa ya kwasawa azeez dake shirin sauke wannan jan qarfen wutan a tsakanin cinyoyin bimbii, hkn ne ya dakatar da azeez ya jiyo yyi ido hudu da prince, mamakine ya cikashi ya tsaya kawai yana kallon prince akbar, takowa yyi har tsakiyar dakin yasa hannu daya daya shaqo wuyan azeez take rawanin dake kime a kansa ya fadi qasa, duk da tsantsar jarimtar azeez amma kasa kwacewa yyi a hannun prince akbar, dagashi yyi sama da hannu daya, hannunshi daya harde a bayansa fuskar nan tasa tamau ya cillar dashi gefe guda take ya fadi kan wannan qarfen wutan dake yashe gefe yyi wata qara sbd zafin wannan qarfe daya janye fatar jikinsa sauran hadiman kurkun dake wannan daki kuwa duk sunyi 2tsuru suna kallon prince daya dawo musu tamkar wani namijin zaki, ita kanta bimbii duk da halin da take ciki be hanata mamakin yanayi na tsantsar fushi data ga prince ciki ba, qarasawa yyi inda take ya tsuguna 2kwata be dago da kansa ya kalleta ba sbd bayason ganin halin da fuskarta ke ciki, kunce mata hannayenta yyi da qafafunta ya dauketa chak ya juya ya fice da ita hk suka din ga bi ta wadannan dogayen corridorn sbd shi kanshi wannan kurku a jikin dutse aka ginashi, hk suka din ga ratsawa har suka fito wajen kurkun wurin da dawakansu ke daure ya fara dorata saman dokin sannan shima yahau suka zabiri dawakan nasu suka bar wurin da gudu, sosai suke gudu bisa dawakansa cikin jeji ubaid na biye da dokinsu har suka iso wani kyakykyawan kauye, kai tsaye kofar wani gida suka tsaya,prince ya rufe kusan rabin fuskarsa da rawanin dake kansa sbd baya son wani ya shaida shi don wannnan qauye shima mai suna jandun yana cikin yankin masarautarsu ne, wani tsoho ne ya fito sanye da wata akyabba da qaton rawani yana dogara sandarsa a rankwafe yake tfy sbd da tsufa, gemunsa fari ne gashi dogo sosai, dakatawa yyi yana kallonsu, prince dauke yake da bimbii a hannunsa, murmushi yyi wannan tsoho don sai yanzu ya gane prince daya kalli idanunsa sosai sbd fuskarsa rabi rufe take,nuna musu hanya yyi suka shige cikin gdn,ginin gdn dai gini ne irin nasu na larabawa na zamanin baya, ginin jajir irin na jar qasa, cikin wani daki suka shiga mai yalwa sosai ya nunawa princewa wata shimfida ya kwantar da bimbii data jima da shiga coma, wata dattijuwa ta shigo riqe da faranti da qananan cups ta ajiye gaban prince, itace naiha matar wannan tsoho, shi wannan tsoho ya fito ne daga yankin dilham, Allah yyi masa baiwa ta sanin magani sosai, prince akbar shine ya taba ceto rayuwar wannan dattijo mai suna abbas daga tarkon sarkin yankin dilham sarki najash ya bashi mafaka shi da matarsa cikin wannnan dan qauye.....
Littafin nan na kudi ne, idan kina da buqata zaki sanya #300 ta wannan acct...0100790419,alhaji shahida nasir,union bank sai turomin da screesht na payment ta wannan layi..07041195806 da ita nk whatsapp...
Alkalamin Bintuu ne....
10/10/20, 1:12 AM - Anti qamshi🌷: *DAREN GOMA SHA HUD'U*🪔🪔
Written By Bintuu Seer
26
*I'm here to hold you tight dear,if you feel like cry do it on my shoulder*.......I' m here for you my love💕💕
Tunkan su mishi bayanin komai, matarshi naiha ta sake shigowa dakin dauke da wani qaramin bowl mai dan fadi da ruwa a ciki ta wuce inda bimbii ke kwance, sunkuyawa tayi kusa da bimbii ta soma sanya wasu ganye cikin ruwan bowl din nan tana fito da ganyen ta matse tana daddanna mata a jiki musamman wuraren dake da rauni, saida ta gama sannan ta fito da wani garin magani tana shafe mata dukkanin jikinta dashi, su kuwa su prince akbar basu iya hangen abunda take mata har ta gama, ubaid tuni daman ya fice yana farfajiyar tsakar gdn yana jiran fitowar princce akbar, dattijo abbas shima miqewa yyi shi da prince suka nufi wurin da bimbii ke kwance, kallonta kawai abbas yyi yace" amma tana da ciki sbd alamun hkn ya bayyana tattare da ita" shi kansa prince gabansa yyi mugun faduwa na jin wannan zance, dago idanunsa yyi ya qura mata idanu, kallonsa abbas yyi yace" dole tana buqatar hutu da cikakken kulawa" murmushi prince yyi kawai, dattijo abbas ya juya ya fita shi kuma ya nemi gefenta ya zauna tare da riqo hannunta dukka yana kallon zoben azurfan daya sanya mata har yanzu yana nan bata cireshi ba, ganin hawaye yyi na fita daga idanunta dukda kasancewar idanun nata a rufe suke tana bacci, qura mata idanu yyi sosai sai kuma ya kwantar dakansa gefenta ya dauki hannun nata ya cusa cikin gashin kansa yadda take masa kenan idan tana son sanya shi bacci, ji yyi duk duniya babu wacce yake tsananin tausayi irin bimbii sai ya soma ganin laifinsa na rashi bawa abunda yafi so fiye da komai cikakken kulawan daya dace, shigowar naiha ne yasa ya dago dakansa da sauri yaja gefe amma still hannunsa na riqe da nata, murmushi naiha tayi tace" ina son gyarata ne" kallonta prince yyi sai ya maida kansa ya kalli bimbii daidai lkcin bimbii ta bude idanunta a hnkli ta saukesu bisa fuskarsa, hannunta ta kalla ta gansa cikin nasa sai ta dago idanunta ta zuba ma fuskarshi idanu shima ita yake kallo duk sun qure juna da idanu, naiha dake tsaye gefe binsu kawai take da kallo tana karantar saqon idaniyansu, murmushi tayi kawai don tabbas yanayin kallon dake kwayar idon kowanne cikinsu ya bata tabbacin dukkaninsu sunyi nitso cikin kogin soyayya hade da kewar junansu, juyawa tayi ta fice ta basu wuri, bimbii rufe idanunta tayi tana kuka, matsawa yyi kusa da inda take kwance yasa hannu yana share mata hawayen dake fita daga idanunta, cikin sanyin murya yace" kiyi hkr ki yafe min kinji" shiru tayi amma still idanunta na rufe yace" don Allah ki bude idanunki ki kalleni qila ki yadda da abunda zan fada miki" qin bude idanunta tayi yyi, hannunsa yasa ya soma tattaro dogon gashin kanta dake baje yasa wani dogon kyalle ya daure mata wuri daya, duk da hk bata bude idanunta ba, hannunsa yakai kan kirjinta tana jin saukar hannunsa wurin tayi saurin bude idanunta tana son ture hannunsa daga wurin amma jikinta ba qarfi tana cikin zafin ciwo, shima da gangan yyi hkn sbd ta bude idanu ta kalleshi aikuwa yyi nasarar sarqe idanunsa da nata, ta jima tana kallonsa sannan ta juyar dakanta, naiha ce ta shigo prince ya miqe ya fice, a farfajiyar tsakar gdn ya tarar da dattijo abbas yana hada wasu magunguna suna hira da ubaid,suna ganin fitowarsa ubaid yyi saurin tashi daga inda yake ya tsaya qam, dattijo abbas ya fito da wata qaramar kwalbar magani ya miqawa babban prince yace" ranka ya dade gashi ka riqe wannan yana maganin duk wani zugin ciwo" hannu yasa ya amshi mgnin ya daga masa hannu alamar ya gode, rakasu yyi suka fita waje suka haye dawakansu suka zaburesu suka dauki hanyar barin wannan qauye, 6angaren sarainiyya kuwa wannan mummunan labari yakai kunnenta, kwatanta rudewar da tayi ba'a mgn, tasan tabbas tunda hk ta faru dole sarki abdallah bin jabal ya samu labari, sarki abdallah bin jabal kuwa ya samu labarin zuwan prince akbar babban kurku abunda ya daure masa kai shine wai prince ya fitar da wata baiwa da aka sameta da ciki, toh meye hadin babban prince da baiwa kuma? miqewa yyi tsaye ya bada umarnin ayi masa bincike kan wacce wannan baiwa kuma wanne laifi tayi aka kaita wannan wuri,batare wani 6ata lkci ba bincike ya kammala, cikin binciken sun tabbatar masa wannan baiwa dai tsohuwar babbar baiwar prince akbar ce kuma hadima a 6angaren sarauniyya amma basu gano laifin da tayi aka kaita wannan wuri ba saidai ta tafi wurin ne bisa umarnin sarauniyya mar'atussaliha, sarki abdallah bin jabal ya dago fuskarsa da tayi ja sbd tsantsar 6acin rai yace" babbar baiwa ga prince kuma take dauke da ciki?toh cikin waye?" miqewa yyi kawai ya shige cikin gd, sarauniya kuwa tana 6angarenta sai faman zirya take don tabbas ta rasa mafita, saqon kiran sarki ne ya tarar da ita, sanye take daman da wata doguwar riga da mayafi ta fito ummu nana ta mata rakiya har kofar shiga 6angaren sarki tana shiga ta tarar dashi zaune a wata kujera, neman qasan carpet tayi ta zauna tare da sunkuyar dakanta qasa, be mata mgn ba sai ya dauki lkci sannan yace" meye laifin baiwar da kk bada umarnin a kaita babban kurku?" dago dakanta tayi ta kalleshi tace" ranka ya dade wannan baiwa a 6angare na take kuma an sameta da laifin ciki" yace" kurkun qasa shine kurkun da ake miqa duk baiwar da aka samu da ciki amma ita wannan meyesa aka kaita babban kurku?" shiru sarauniyya tayi saida ya daka mata tsawa tukunna yace" ina mgn kin min shiru, cikin waye a jikin wannan baiwa?" sarauniyya jikinta har rawa yake ta daga idanunta ta kalli sarki abdallah da idanunsa kawai sun tabbatar mata da rashin wargi, tace" nima binciken da nk kenan" girgixa kansa yyi ya daga mata hannu ta miqe jiki a mugun sanyaye ta fita, tuni sarki abdallah ya bada umarni cikin wannan daren yake son su nemo duk inda prince akbar yakai wannan baiwa su kaita kurkun qasa kafin washegari, isowar prince akbar kenan shi da ubaid labarin abunda ke faruwa ya taddasu, wannan zance na cikin jikin bimbii gbdy ya zama wani zance dake masifar tashe cikin wannan gdn sarauta, duk inda taron bayi suka hadu toh wannan zance suke gutsurawa junansu cikin hk har zancen yakai kunnen su israt, wannan abun sun jishi tamkar al'amara, mafi yawan mutane cewa suke bimbii a wani wurin tayo cikinta don tabbas ba wanda ya shaida ta fito wankin budurci, gimbiya hindu har ma da prince nasaar dukkaninsu sun aminta cewa cikin jikin bimbii bana prince akbar bane,prince yasan sarai halin mahaifin nasa bazai tanka masa ba har sai ya samo inda bimbii inda take, kiran ubaid yyi yace" komawa zamuyi qauye jandu don tabbas yankin burham ne kuma zasu iya gano inda bimbii take" ubaid yace" ranka ya dade yanzu duk wani motsinka dama duk wanda ke wannan 6angare yana kan idanun masarauta, yanzu hk gbdy saman 6angaren nan zagaye yake da dakarin sama masu masu" shiru prince yyi amma hnklinshi ba'a kwance yake ba, 6angaren bimbii kuwa tana samun duk wata kulawa daga wurin wadannan dattijai sun dauketa kamar wata diyarsu don daman basu ta6a samun magaji ba, bimbii ta samu ingantattun magunguna bacci mai dadi yyi gaba da ita, wadanda aka sanya binciko inda bimbii take kuwa tuni suka yiwa kauyen jandu tsinke cikin shigar bad da kama ta yadda babu wanda ze ganesu suka soma kewaye cikin qauyen bawai sun tabbatar wannan qauyen bimbii take ba, sun shiga qauyuka da dama bincike suke sbd ance prince yyi gabas ne lkcin daya dauki wannan baiwa kuma bisa doki yake, prince baya shiga cikin gari bisa doki kuma idan har gabas yyi toh tabbas wani qauyen ya kaita dake maqobtaka da masarautar burham,cikin masu farautar bimbii har da mutanen prince nasaar, suma burinsu su riga dakarun sarki abdallah bin jabal samo inda bimbii take ya basu umarni mutuqar sun ganta su dauketa su miqata qasar spain ta jirgin ruwa,cikin izinin ubangiji mutanen prince nasaar suka riga isa inda bimbii take suka dauketa suka qarasa da ita port suka sanyata cikin jirgin ruwa saidai kafin wannan jirgi ya tashi har dakarin sarki abdallah bin jabbal sun bayyana a wurin,bayin prince nasaar kuwa suna ganin hk suka sulale suka bar port din don basu so wadancan dakaru su shaida fuskokinsu, su kuwa dakarin babban burinsu su chafke bimbii kuma cikin ikon Allah sukayi nasarar kamata, 6angaren masarautar burham kuwa sarki abdallah bin jabal ya sanya taro na musamman wanda ze gudana a filin kofar fadarsa, washegari filin wurin ya cika maqil da jama'a, sarki abdallah bin jabal yana can saman matattakala bisa kujera ta alfarma gefensa kuma prince akbar ne sai sauran princes din da ragowar masu fada aji cikin wannan masarauta ta burham, ta can daya gefe kuma sarauniya mar'atussaliha ce tasha kaya na alfarma ita da yan fadanta duk suna zazzaune a kujerun girma idan suka hanga qasa matattakar al'umma ne birjik kowa na sauraro, wurin tsaro ne ta ko'ina,sarki abdallah bin jabal dakansa ya miqe ya soma jawabi, jawabinsa na farko shine yace" yau ranar farin ciki ce hade da baqin ciki dukka,yau itace ranar da masarautar burham zata qulla yarjejeniyar aure tsakaninta da masarautar abu ansar, wannan yarjejeniya ta aure zan qulla tane tsakanin da prince akbar da princess mariyatul qifdiya" prince akbar dake gefe sunkuyar dakansa yyi, zuciyarsa cike da mamakin wannan abu, prince nasaar kuwa sai wani murmushi yake, fuskokin kowa wurin dauke take da annuri musamman sarauniya mar'atussaliha, sarki abdallah ya tsuke fuska sannan ya koma ya zauna prince andal ya miqe ya dora bisa jawabin sarki abdallah yace" sannan yau din kuma wannan masarauta ta zartas da hukuncin kisa kan wata tsohuwar baiwa dan sarki da aka samu da ciki wanda kowa yasan girman wannan laifi cikin wannan masarauta ta burham" sai lkcin prince akbar yyi hanxarin dago da fuskarsa inda ya hango manyan dakaru majiya qarfin sun fara hawo da bimbii kan matattakalar, tsayar da ita akayi gbdy duk sun daddaureta, sarki abdallah ya bada umarni sarkin kisa ya sare kan bimbii...........
Littafin nan na kudi ne, idan kina da buqata zaki tura #300 ta wannan acct...0100790419,alhaji shahida nasir, union bank, saiki turomin da screesht ta whatsapp ta wannan layi....07041195806.....
Alkalamin Bintuu ne....
10/10/20, 1:12 AM - Anti qamshi🌷: *DAREN GOMA SHA HUD'U*🪔🪔
Written By Bintuu Seer
27
*My heart is paining*....I can't stop the tears💕💕
Sarkin kisa ra'iz wani gabjejen qaton mutum ne mai yalwar girman jiki da fad'I ga wani jibgegen rawani akansa, hannunsa rige da wata takobi tsirararta ya soma haurawa matattakalar inda bimbii ke daure, bimbii gbdy ta jigatu bakinta sai fitar da jini yake ga gashin kanta daya hargitse ya rufe mata fuska, jira kawai take su gaggauta fille mata kai ko zata huta da wannan mawuyacin halin da take ciki, ra'iz ya qarasa hawa wurin ya daga takobinsa sama da niyyar fille kan bimbii yaji an daka masa wata razananniyar tsawa, dakatawa yyi ya waiga sai ganin prince akbar yyi tsaye a bayansa, sauke takobin yyi qasa, hkn yyi daidai da miqewar sarauniya daga kujerarta ta dakawa prince tsawa akan ya hanzarta barin wurin, sarki abdallah kuwa yana daga zaune yana kallon abunda ke faruwa,murmushi sarki abdallah yyi ya kalli prince nasaar dake gefensa yace" ka sanar da sarkin kisa yana bisa umarni ne kar ya tsaya 6ata lkci" miqewa prince nasaar yyi shima jikinsa a mutuqar sanyaye ya daga murya sosai yace" sarkin kisa ya harzarta aiwatar da umarni batare da 6ata lkci ba" wannan zance na shiga kunnen sarkin kisa ra'iz ya kuma daga takobinsa da niyyar cika umarnin sarki abdallah bin jabal, cikin tsananin zafin nama prince akbar ya chafe takobin nasa yyi wulli da ita gefen daman bimbii tuni takobin ta tsinke daurin da akayi mata ta 6angaren dama, qara chafe takobin yyi ya kuma cillata gefen hagunta tuni daurin ya warware dukka ya riqeta yyi gefe da ita, wurin yyi tsit sbd kowa ya cika tsantsar mamakin wannan abu da prince keyi bisa umarnin mahaifinsa, sarki abdallah bin jabal miqewa yyi cike da mamaki shima amma sai ya 6oye hkn a fuskarshi ya kalli shugaban dakarin dake tsaye a wurinl yace" su kama prince maxa su miqashi kurku tare da azabtar dashi pita kuma wannan baiwa su kawo masa kanta yanzu gabanshi"wannan umarni da sarki abdallah bin jabal ya bayar yyi masifar gigita sarauniya mar'atussaliha saidai ko kusa bata da damar mgn musamman a wannan yanayi da ran sarki abdallah ke tafasa,batare da wani 6ata lkci ba dakarun dake wurin duk suka zare makamansu sukayi kan prince akbar, shi kuwa yana tsaye yana ganin hk kawai yaja bimbii zuwa bayansa, kallo daya zaka masa kasan ya shirya tararsu, suna qarasowa suka afkan kansa da hannu guda kawai yake 6arar dasu dayan hannun nashi riqe da bimbii, cike da azama da mugun zafin nama yake uwar watsi dasu tamkar wani gawurtaccen zaki ta tsakiyarsu yake bi idan ya watsar dasu sun zube qasa, wuri gbdy ya hautsine da artabu tsakanin dakarin sarki abdallah bin jabal da prince akbar shi daya kawai ya gagaresu, ba kashesu yakeyi ba kawai raunata su yakeyi ya wuce burinsa kawai ya samu doki ya haye su bar wurin amma ina abu ya gagare sbd dakarin nan kamar qaruwa suke, gumurxu sosai ake bugawa a wannan wuri, bimbii bata ta6a sanin prince namijin gaske bane a filin fama sai yau ta tabbatar da hkn, gwaninta kawai yake nuna ta tsantsar jarumta duk yawansu ko kwarzane babu wanda yyi masa kuma a hkn yake kare bimbii daga harinsu, fararen kayan dake jikinsa gbdy sun 6aci da jini, fada yake cikin tsananin zafin nama da gocciya tamkar wani hatsabibi, yadda prince akbar ke fada da nuna bajinta be kasance ya basu mamaki ba don duk wanda ya kwana ya hantse a masarautar burham yasan wane ne prince akbar a filin fama shiyasa shi kansa sarki abdallah bin jabal ke mugun alfahari dashi, ganin hk ne yasa sarki abdallah bin jabal miqawa hadiminsa uxair hannu ya miqa masa wani mashi mai tsinin gaske, daga mashin yyi dakansa yyi saitin prince akbar, shi kuwa yana cikin fada da wadannan dakaru batare daya ankara ba kawai yaji harbin mashi a bayansa, mashin yana dauke da guba sosai, daga kansa yyi ya hango mahaifinsa riqe da wani mashin yana saitinsa, batare daya zare mashin dake jikinshi ba yyi kukan kura yyi watsi da dakarin dake gabansa yaja hannun bimbii da gudu suka hau kan wani doki, dakyar yahau dokin cike da dauriya sbd wannan harbin mashin, suna bisa dokin wani harbin ya kuma samunsa, hk ya cije yaja dokin da mugun gudu suka bar wurin a guje, sarki abdallah ya bada umarnin su bisu, yana kan dokin amma qarfinsa ya soma qarewa sbd harbin mashin dake jikinsa, zuciyarsa ce kawai ke tfy dasu bisa dokin, hannu yasa ya cire mashin dake tsire a bayansa, bimbii juyowa tayi tana kallonshi taga halin dayake ciki amma duk da hk yana qara daurewa yana jan dokin, gudu suke amma dakarin sarki abdallah na biye dasu, wata hanya suka miqa cikin jeji suna gudu saida suka je qarshen hanyar suka tarar ba hanya sai wani qatoton rami mai zurfi da fadi, qasan ramin qananan bishiyoyi ne tare ruwa dake kwaranya tamkar qorama, dokin nasu yaja ya tsaya gaban wannan qaton rami mai tsayin gaske, sauka sukayi daga kan dokin duk suka tsaya sukayi cirko cirko, gashi tabbas wadannan dakaru sun kusa cimmusu, bimbii a wannan lkci ta dena tausayin kanta prince take tausayawa yanayin yadda ta ganshi, matsowa kusa dashi tayi ta riqeshi ya durgusa a wurin yasa hannu ya zare dayan mashin dake cake a gefen cikinsa, tabbas shi kansa lkcin yasan abu ne mawuyaci ya rayu domin wannan mashi na mahaifinsa yana da gubar gaske, saidai babban burinsa shine ya tsirar da bimbii ita da abunda ke cikinta, sautin sawun dawakai suka jiyo hkn ya tabbatar musu dakarin dake biye dasu ne, dago dakansa yyi ya kalli bimbii yace" ki gafarce ni don Allah ki yafemin" riqo hannunta yyi yace" ina son ki rayu komai wuya sannan kar ki mance dani cikin rayuwarki, kin ji, ina sonki dayawa na sadaukar miki da rayuwata gbdynta" kuka bimbii take sosai tana rufe masa baki da hannunta tace" bani son ka sadaukarmin da rayuwarka na fison mu rayu tare ko mu mutu tare, bazan rayu babu kai ba, wlh bazan iya ba" kuka sosai take ta kwantar dakansa a kirjinta, daidai lkcin dakarin sarki abdallah bin jabal suka qaraso wurin, batare da 6ata lkci ba suka sakko daga kan dawakansu suka nufo wurin, prince yana ganin hk yasan tabbas wlh kashe bimbii zasuyi, miqewa yyi duk da jirin dake dibansa. yana ja da baya, bimbii kuwa tana bayansa tana kuka, gani yyi wasu daga cikinsu na bisa dawakai sun saita bimbii da mashi, ita kanta bimbii bata ankara ba sai ji tayi kawai prince yasa hannu cikin azama ya hankadata cikin wannan dogon rami, su kansu dakarin dake wurin basuyi zaton hk ba, ihu take har ta fada qasan wannan rami cikin ruwan dake kwaranya,shi kuwa prince tsayawa yyi yana kallonsu sai kuma kawai ya sunkuya ya dauki takobinsa ya afka musu tamkar ba rauni a jikinsa, prince nasaar daya biyo bayansu yana qarasowa yaga wannan artabu tsakanin dakarin nan da prince, murmushi yyi yasa hannu ya ciro kibiyoyi ya soma masa dashi, burin daman kawai ya kashe shi, aikuwa kibiyoyin suka same shi dukka a gadon baya, sakin takobin dake hannunsa yyi kawai ya durqushe a wurin yyi zaman ruku'u, daga wata kibiyar yyi da niyyar qara masa yaji an riqe ta baya, juyawa yyi a fusace yaci karo da gimbiya hindu bisa doki ta rufe rabin fuskarta da baqin kyalle, tace" waye yace ka kashe shi" sauke hannunsa yyi ya maida kibiyoyin, shi kuwa prince hannunsa kawai yake miqawa saitin ramin da bimbii ta fada har numfashin shi ya tsaya chak, gimbiya hindu ta sakko daga kan dokinta ta nufo inda yake ta soma jijjigashi tana hawaye sosai, kamar daga sama suka soma suka ganin wani irin hayaqi yana gauraye ko'ina cikin dajin, zumbur gimbiya hindu ta miqe tana waiwaye hkma sauran dakarun dake wurin, prince nasaar shima 2kalle ya somayi basu ga kowa ba, wasa wasa wannan hayaqin ya cika wurin sosai ko tafin hannunsu basu iya gani, a hnkli kuma hayaqin ya soma washewa suka kai dubansu wurin da prince yake kwance suka ga wayam, abun yyi mugun daure musu kai da basu mamaki basu ji motsin komai ba kuma basu ga kowa ba amma sun nemi gangar jikin prince akbar sama ko qasa sun rasa, ba kowa ne da wannan aikin ba sai ubaid babban hadimi ga prince,shine ya sanya wannan hayaqin sannan kuma ya lalla6a ya dauke prince batare da sun ankara ba, nesa da wurin sosai ya ajiye dokinsa, hk ya dauki prince ya haye dokinsa yabar wurin, prince nasaar yasa dakarun duk su bazama cikin wannan jeji don nemo gawar prince akbar don miqata ga sarki abdallah bin jabal, batare da 6ata lkci ba suka watsu cikin wannan jeji suna neman prince akbar, shi kuwa ubaid be tsaya ba saida ya tabbatar ya fice daga yankin masarautar burham, wani kogon dutse ya shige da prince anan ya tarar da dattijo abbas, ajiye prince yyi dattijo abbas ya matso kusa da inda prince akbar ke kwance yakai hannunsa ya dora saitin zuciyarshi yaji babu alamun numfashi tattare dashi, kansa ya dora wurin sai lkcin ya jiyo bugawar zuciyar tasa a hnkli, dago da kansa yyi,ubaid yace"meke faruwa dashi ya mutu ne" girgixa kansa yyi yace" da sauran numfashi a tare dashi" ajiyar zuciya ubaid yyi yana kallon fuskar prince da kwance, dattijo abbas ya fito da wasu magunguna daga jakar dake rataye a kafadarsa, wuraren harbin mashin ya soma zubawa garin maganin, 6angaren sarki abdallah kuwa jira kawai su dawo masa da kan bimbii da kuma dansa prince akbar,shi yana son ya hukunta prince dakansa bisa laifin daya yyi, sai dare suka koma ga sarki abdallah ba bimbii ba prince akbar, hkn ba qaramin 6ata masa rai yyi ba yasa a rufe dukkanin dakarin, sarauniya mar'atussaliha kuwa kuka sosai take ta kasa cin abinci ba yadda ummu nana batayi da ita ba kawai ita danta take son gani, gimbiya hindu ita ta labarta masa abunda ya faru, miqewa tayi tsaye da sauri ta fice ta nufi 6angaren sarki abdallah bin jabal, tana shiga ta zube a gabansa tana kuka sosai tana roqonsa don girman Allah yasa a nemo mata danta, kallonta kawai yyi ya tashi yabarta a wurin, durgushewa tayi tana kuka kamar ranta ze fita, prince akbar shi kadai ne dansu yanzu gashi silar wannan baiwa ta rasa danta gudan jininta.........
Littafin nan na kudi ne, idan kin idan kina da buqatar karantawa zaki tura #300 ta wannan acct.....0100790419,alhaji shahida nasir,union bank,saiki turomin da screesht ta whatsapp da wannan layin 07041195806......
Alkalamin Bintuu ne.....
10/10/20, 1:12 AM - Anti qamshi🌷: *DAREN GOMA SHA HUD'U*🪔🪔
Written By Bintuu Seer
28
*You are the only one I can hear*.....You are the only one I can feel cox you are are the reason of my living💕💕
Bimbii kuwa tunda ta fada wannan dogon rami bata kuma sanin inda kanta yake, dulmiyewa tayi cikin wannan ruwan dake kwaranya tamkar na 6ul6ula, ruwan zuba yake shaaaa daga jikin wani dutse gashi fari tas dashi, karfin ruwan ne ya janyeta ta fada wani qaton ruwa wanda yyi iyakar yankin burham da yankin dilham, wannan ruwa shi ya raba tsakanin yankunan guda biyu,qananan jiragen ruwa da manyan kwale kwale masu safarar bayin zuwa yankunan qasashen larabawa 2daban suna ratsawa ta wannan dogon kogi, igiyar ruwa ce tayi tfy mai nisan gaske da ita takaita ga6ar wannan kogi cikin izinin ubangiji wani mutuqin kwale kwale mai suna abeed ya hangi gangar jikinta a yashe gefen wannan kogi igiyar ruwa ta watso ta ga6a, cikin sauri ya nufi wurin don tabbatarwa kansa yana zuwa kuwa ya ganta kwance babu alamun ruhi tattare da gangar jikinta, sunkuyawa yyi yakai hannunsa daidai wurin bugawar numfashinta yaji shiru, duk da hk be hkr ba yasa hannu ya dinga dannan cikinta ruwa ya soma fita mata ta hanci ta baki har saidai ruwan data sha ya fita, jikinta yyi sanyi tamkar qanqara hkn ya tabbatar masa cewa ta jima a cikin ruwa, yatsunsa biyu ya kuma pointing kan qahon zuccinta sai lkcin yaji dif dif alamun akwai sauran ruhi tattare da gangar jikin nata, daukanta yyi yasata cikin kwale kwalensa ya shige ya soma tuqa kwale kwalen nasa har suka fita asalin ga6ar da yake da 2hadar jama'a, duk wanda ya gansa sai yyi zaton baiwarsa ce ta kasa har jaje ake masa hk ya samu ya wuce da bimbii, abeed mutumin dilham ne kuma masunci ne yana zaune shi da iyalinsa a wani qaramin gdn katako kusa da wannan kogi, matar shi daya da d'ansa daya dan kimanin shekaru ashirin sunan shi farhan, matar shi saudat ta tausaya mutuqa da taga halin da bimbii ke ciki, hk suka din ga bata taimakon daya dace kasancewarsu masunta, saudat ta dumamawa bimbii jikinta sosai yadda jikin nata ya dauki dumi sosai, kallon daya ta yiwa bimbii ta fahimci tana dauke da juna biyu, hk suka cigaba da bata duk wani taimako kusan sati guda kenan amma bimbii bata ta6a koda motsi ba bare su sanya mata ran samun lfy, dansu farham a lkcin yana high schl ne ajin qarshe, ba wasu mawadata bane talakawa ne saidai sun fi qarfin cikinsu, bimbii saida tayi sati uku chur tana kwance tamkar mutum mutumi amma basu gjy da kula da ita ba, yau da dare saudat tana kasa mata jiki kawai taga yatsun qafarta sun motsa, murza idanunta tayi ta kuma kallon kafarta taga tabbas motsi take da yatsun qafarta, kwalawa danta farhan kira tayi suka shigo cikin dakin da gudu shi da abeed, nuna musu yatsun kafar bimbii tayi su ga tana motsasu, murna sosai suka somayi tamkar wata jininsu,washegari, da sanyin safiyya saudat ta shigo dakin da bimbii ke kwance sai ganinta tayi idanunta bude tana 2kalle dasu, matsowa tayi da gudu ta zauna kusa da ita ta riqo hannayenta tana mata sannu, ita kuwa kawai binta take da idanu tamkar wata kurma,6angaren prince akbar kuwa shikam be dauki wani tsawon lkci ba, kwanan shi biyar kwance abbas yana bashi magungunan da suka tsuge dafin mashin daya soke shi, a kwana na biyar ya bude idanunsa, ubaid da abbas ba qaramin dadi sukaji ba na ganin prince ya farka, suna dai cikin wannan kogon dutsen dashi sbd sarki abdallah bin jabal har yau be hkr da nemansu ba, prince akbar ya zamto wanted ga masarautar burham,mtslr shine har yanzu suna cikin yankin masarautar burham basu da hnyr da zasu iya ficewa daga yankin masarautar burham sbd nemansu ake ruwa a jallo, prince akbar ya farfado kuma yana cigaba da amsar magani wurin dattijo abbas saidai tunda ya farfado har yau be tankawa kowa ba, da tunanin bimbii ya farka ita kawai yakeson gani a halin da yake ciki, d'an sarki mai cikakken izzah wanda ya saba kwana bisa tattausa yau shine ya samu kansa cikin wannan kogon dutse amma shi duk ba wannan ne ya dame shi ba,babbar damuwarsa shine shin bimbii tana raye ko tana mace, idan har bimbii bata raye toh shikam be ga amfanin tasa rayuwar ba sbd itace mahadin ruhinsa itace bugawar numfashinsa, wadannan irin tunani su suka zame masa sana'a, ubaid ya fara damuwa da yanayin da yake ganin prince ciki sai yake ganin kodai ya samu wata mtslr ne, dattijo abbas yace ya kyale prince ya kadaice da zuciyarshi, prince akbar ko gama samun sauqi beyi ba ya fito daga wannan kogo, ubaid ya kalleshi ya rissinar dakansa qasa yace" ranka ya dade dakarin masarauta sun bazu ko'ina nemanka kawai suke idan kayi wani wuri yanzu zasu iya ganinka" kallon prince yyi sannan ya dauke kansa ya juya sai can yace" gudu yana ga raggo ne amma namiji baya gudu a fagen fama koda hkn na nufin ajalinsa" yana gama fadar hk ya kama dokin dake daure yahau ya sakar masa linzami yabar wurin, kai tsaye wurin ramin daya tura bimbii ya nufa, yana qarasawa wurin ya sauka daga kan dokin ya nufi wurin ramin ya leqa qasan ramin ya tabbatar da tsayinsa batare da wani shakka ba ya soma shirin afkawa cikin dogon ramin shima ya isa duniyar da bimbii take, murya da yaji bayansa ne yasa shi juyawa, ubaid ne yace" ranka ya dade kafin ka aikata hkn ya kamata kasan halin da sarauniya take ciki tun ranar daka bar masarauta ta kwanta babu lfy kuma jikinta ya tsananta tana da burin sake ganinka kar ka kashe kanka batare daka gana da mahaifiyarka ba" kalaman ubaid sunyi tasiri mutuqa sun sanya ya soma begen ganin mahaifiyarsa duk da laifinta gare shi amma uwa ai uwa ce" jiki a sanyaye ya koma ya haye dokinsa kawai bisa mamakin ubaid sai kawai gani yyi babban prince ya dauki hanyar masarautar burham, tun daga nesa dakarin dake tsaron kofa suka hango shi batare da wani 6ata lkci ba suka bude masa kofar wannan gdn sarauta ya shige da dokinsa, duk wanda yaga prince sai ya cika da mamaki, tuni wannan albishir yakai kunnen sarauniya sannan yakai ga sarki abdallah bin jabal, umarni ya bayar a rufe kowacce kofa ta wannan masarauta sannan ya sake bada umarni a kama prince a miqashi kurkun qasa, prince yana sauka daga dokinsa yaga dakarin tsaron wannan gd sun tsagayeshi ta ko'ina dukkaninsu riqe da makamai, sarauniya bata da masaniyyar wannan umarni da sarki abdallah ya bayar saida ummu nana ta shigo ta shaida mata, prince kuwa fuskar nan tashi tamkar hadari ya kalli wadannan dakaru yace" duk wanda yakeson uwarsa ta haifi wani ya cigaba da tsayuwa anan" dukda sun san jarimtarshi amma basu kauce ba don suna mtuqar shakkar mahaifinsa sarki abdallah bin jabal, prince wata qaramar wuqa ya ciro daga jikin dokin dake gabansa ya nufi shiga cikinsu, kai tsaye yaji muryar mahaifiyarsa daga bayanshi tace" idan har nina haifeka kar ka kuma aikata wannan abu,bani son ka kuma zare takobinka bisa umarnin mahaifinka kabi umarnin shi" juyawa yyi a hnkli ya hango an turota a wheel chair, sauke wuqar dake hannunsa yyi ya qarasa inda take a hnkli ya tsuguna gabanta ya dora kansa bisa cinyarta ya rufe idanunsa, hawaye take sosai tasa hannunta tana shafa kansa, daidai lkcin sarki abdallah bin jabal shi da tawagarsa suka qaraso wurin, fuskarshi babu digon afuwa, dago dakai prince akbar yyi ya juya sukayi ido hudu da mahaifin nasa, dauke kai sarki abdallah yyi ya kalli dakarun dake wurin yace" ku miqashi kurku" kafin ya rufe baki sun matso wurin da prince yake suka kama shi, saurin cire musu hannu yyi daga jikinshi ya kalli mahaifin nasa yace" zan tafi dakai na" wucewa yyi gaba suka bishi a baya, sarauniya ta fashe da kuka ta kalli sarki abdallah tace" don Allah kayi masa aikin gafara" be kalleta ba bare ta sanya ran ze bata amsa ya juya abunshi yan fadansa suka take masa baya, ummu nana ta tura wheel chair din da sarauniya ke kai ta koma da ita 6angarenta tana kuka, ita kanta tasan sarki abdallah ba qaramin kafiya ne dashi da taurin kai ba shima kuma dan nasa hk yake ai gado ba karambani bane, bude masa kofar kurku sukayi ya shige ya zauna abinsa suka maida kofa suka rufe, bimbii kuwa tana samun kulawa yadda ya kamata daga wurin saudat da danta farhan saidai babban tashin hnklin shine bimbii tayi losing memory nata, 2kwata bata iya tuna komai ta manta duk abunda ya faru da ita ta mance ita wace ce,komai koya mata ake hatta mgn da yadda ake cin abinci dama komai, farhan yana mutuqar qoqari wurin kula da bimbii da koya mata abubuwa, shidai abu guda ne ya tsole masa idanu game da bimbii shine wannan jikin dake jikinta ya tsani yaji ance bimbii tana da ciki, sudai sun tsinci bimbii basu san ko tana da aure bane ko bata da aure sudai kawai sun ganta da ciki kuma gashi tayi losing memory nata bata iya tuna komai bare su nemi ta sanar dasu wace ce ita, yau da gobe jikinta ya warware saidai komai nata cikin sanyi take yinsa, bata son mgn shiru shiru, farhan shi kullum mamaki yake wai bimbii yar qarama da ita amma tana da ciki don shi gani yake ya girmi bimbii, tun bimbii bata mgn har ya dage ya soma sanyata mgn, hk yake shiriricewa kullum gabanta yana bata labarai na ban dariya, ya maida bimbii tamkar wata qawarshi itama saita dauke shi aboki kuma dan'uwanta don ita duk zatonta saudat itace ta haifeta, farhan kuma qaninta ne saidai ita mamakinta meyesa ita bata kaisu hasken fata ba, tana yawan yiwa farhan wannan tmbya shi kuma sai ya shashatar da zancen, a kwana a tashi cikin bimbii kullum qara girma yake, tmbyr saudat tayi wai meyesa cikinta ke girma hk, murmushi kawai saudat tayi tace" kar ki damu wataran zaki haifa mn baby ne" shiru tayi bata kuma cewa komai ba,hk rayuwa ta cigaba da tfy, shaquwa sosai ta shiga tsakanin bimbii da farhan sun zama tamkar abokai,wata rana sun je bakin teku kallon ruwa, farhan ya kalli bimbii yace" ki bani wannan zoben na hannunki yana min kyau" kallon zoben bimbii tayi wanda ita bata ce ga yadda akayi zoben ya shiga hannunta ba tace" zoben nan yana min kyau a hannu bani cireshi don ma kaji" dariya yyi yace" toh shikenan ai" prince akbar kuwa tunda sarki abdallah ya sanya shi cikin kurku ya dauke masa kai, kuma yace ayi treating nasa equal da sauran prisoners, babban damuwa prince bimbii ce, shi kansa yana mamakin irin son da yake yiwa bimbii, duk daren duniya sai yyi mafarkinta, hali yake ciki na quncin zuciya da damuwa, tun yana daurewa har abu ya soma cin qarfinsa sai wayar gari akayi prince na aman jini, sarauniya kam kullum tana hanyar wannan kurku kuma kusan duk ranar duniya saita neman wa prince gafara wurin mahaifinsa amma ya kafe kai da fata sai prince ya gane kurensa kafin ya fito dashi kuma sai ya fito duniya ya qaryata soyayyarsa ga wannan baiwa sannan ya nesanta kansa da cikin dake jikinta idan yyi hk kawai shine ze iya yafe masa, wannan abu kuwa shine abu mafi tsauri ga prince akbar, bazai ta6a qaryata soyayyar bimbii ba hkma cikin dake jikinta duk kuwa da cewa besan ko tana raye ko bata raye ba........
Littafin nan na kudi ne, idan kina da buqatar karantawa zaki tura #300 ta wannan acct...0100790419,alhaji shahida nasir,union bank, saiki turomin da screesht na payment ta whatsapp ta wannan layi...07041195806....
Alkalamin Bintuu ne......
10/10/20, 1:12 AM - Anti qamshi🌷: *DAREN GOMA SHA HUD'U*🪔🪔
Written By Bintuu Seer
29
*Only one person fill my heart*.....You are the reason of my breathing,I love you so much dear💕💕
Yau bimbii na kwance ita kadai a daki sbd tun safe take jin jikinta wani iri babu dadi amma tana ta daurewa batason ummu farhan ta gane halin da take ciki, ummu farhan ce ta shigo dakin hannunsa riqe da wani qaramin cup da zuma a ciki, bimbii na ganinta tayi saurin miqewa zaune, murmushi ummu farhan tayi ta miqa mata qaramin cup din dake hannunta tace" ki shanye zuma ce tana cike da sirrika na magunguna 2kala musamman wurin mace mai juna biyu" murmushi bimbii tayi tasa hannu ta amshi cup din ta soma shan zumar har ta shanye, da dare lkcin cin abincin dare duk suna zazzaune kan wata qatuwar darduma duk sun harde kafafunsu suna cin abinci, farhan ya kalli mahaifinsa abeed yace" abu itama andal akaita mkrt mn" dago dakai abeed yyi ya kalli 6angaren da bimbii ke zaune yace" andal wai kina son mkrt" murmushi bimbii tayi tace" ehh abu ina so" kallonta farhan yyi ya kalli cikinta daya dan turo sosai ya ta6e baki ya cigaba da cin abincinsa, ummu farhan ta kalli abeed tace" amma dai ba yanzu ba saita haihu tukunna" farhan ya dago ya kalli bimbii yace" nikam ban ta6a ganin yarinya qarama kamar ki da ciki ba" iyayen nasa ne sukayi saurin kallonshi tare da harararsa sai yyi saurin sunkuyar dakansa qasa, shima kawai zancen ne ya kubce masa sbd ya tsani ganin wannan ciki a jikin bimbii da suke kira da andal, bimbii kuwa tsuru tayi tana son tuna wani abu amma kwakwalwarta ta toshe duk wata kafa ta tuna mata abunda ya faru da ita a baya, ummu farhan ce ta dafata da murmushi a saman fuskarta tace" andal ko bacci kkji ne" daga mata kai tayi alamar ehh, kamo hannunta tayi suka miqe suka nufi dakin kwanan bimbii, gyara mata wurin kwanciya tayi tace" ki kwanta saida safe" kallonta bimbii tayi tace" Allah ya bamu alheri" murmushi tayi ta sunkuya ta shafa kan bimbii tace" ameen summa ameen"bimbii cikin dare ta tashi zaune, bayanta taji ya riqe qam ga wani irin ciwo da mararta take mata duk ta hada gumi, hk ta din ga fama har asuba tayi ta soma jin motsin abeed da farhan zasu fita masallaci, tana cikin wannan hali ummu farhan ta shigo dakin, cikin sauri ta qarasa wurin da bimbii ke durqushe riqe da mararta, tace" andal mene ke damunki,kiyimin mgn" bimbii ba bakin mgn sai idanu kawai take bin ummu farhan dashi, ummu farhan kam tasan ba haihuwa bane sbd cikin nata bekai mizanin haihuwa ba saidai idan wani ciwon ne daban, ruwan zaitun da zuma ta bata ta sha, suna cikin hk su abeed suka dawo, farhan ne ya shigo dakin ya tarar da abunda ke faruwa, shigowa yyi cikin dakin a rude yana kiran suna bimbii, tana jinsa amma ba bakin amsawa, juyawa yyi ya fita da sauri ya sanarwa mahaifinsa, abeed ya shigo shima cikin dakin, farhan ya kalli mahaifinsa yace" ina ganin kawai mu wuce da ita asibiti" kada kai abeed yyi alamar hk za'ayi, cikin wannan safiyya farhan da abeed suka fita, suna fita suka tarar da wani tsoho yana jan keken dokinsa, alfarma abeed ya roqeshi kan ya amince ya fitar dasu bakin babban hanya ko zasu samu abun hawa zuwa asibiti,wannan majanyin keken doki kuwa ya amince suka fito da bimbii suka sanyata ciki tare ummu farhan mai keken dokin yaja suka tafi, sunyi tfy mai nisan gaske kafin suka isa bakin hanyar motoci ke wucewa, dakatawa sukayi har su abeed suka qaraso sannan suka tsayar da wata mota suka shige, daidai king faisal specialist hospital motar tasu ta tsaya suka fito dukkaninsu har da bimbii, suna shiga hospital din wadanda ke yawo da gadon daukar marasa lfy suka dauki bimbii suka shige da ita,wata nurse ta wuce da gudu zuwa office din doctorn dake kula da wannan 6angare ta sanar masa an kawo wata patient mai juna biyu dake buqatar taimakon gaggawa, doctorn be dago kai ya kalleta ba saida ya gama danne dannensa a laptop din dake gabansa sannan ya dago dakansa yace" kije gani nan zuwa" juyawa tayi ta fita sbd idan da sabo duk sun saba da halin DR.MAHEER mugun dan I dnt care akan patients, hknlinsa kwance ya miqe ya fita daga office din nasa, farhan da abeed na ganin fitowarsa suka nufo shi da sauri, be sauraresu ba yyi wucewarsa cikin dakin da bimbii ke kwance,qarasawa yyi bakin gadon da take yana kallon ruwan drift din dake shiga jikinta sannan ya maida dubansa ga saman fuskarta......wani irin bugawa gabansa yyi da karfi ya qurawa fuskar bimbii idanu, tabbas shidai yasan bazai ta6a mance wannan fuskar ba cikin rayuwarsa, fuskar da kullum take masa gixo ba dare babu rana, mamaki yyi mutuqa na ganin ciki a jikinta, juyawa yyi ya kalli nurse din dake gefensa ya nuna cikin dake jikin bimbii yace" meye wannan a jikinta" nurse din kallonsa tayi cike da mamaki sai kuma ta kalli cikin bimbii dayake nunawa da hannu tace" tana da ciki ne doctorn" cikin tsantsar rudewa yace" what!" nurse din sai abun ya soma bata tsoro ta soma kallon Dr.maheer da tarin mamakin wannan action din nasa, yace" waye ya kawota" tace" wadanda suka kawota suna waje" juyawa yyi da sauri ya fita yana fita farhan yyi saurin shan gabansa yace" yy jikin nata" tsayawa yyi yana qarewa farhan kallo tun daga sama har qasa sannan yace" kaine ka kawota?" cikin sauri yace" ehh, nine" Dr.maheer yace" kai waye nata?" kai tsaye yace" mata ta ce" wani irin kallo maheer ya masa sai kuma ya juyar dakai yana wani irin murmushi mai ciwo, cike da axama ya juya ya chakumi kwalar rigar farhan da idanunsa da suka kala sukayi jazir, ummu farhan da abeed dake gefensu sukayi saurin qarasowa wurin suna mamakin abunda ya hada Dr.maheer da farhan, maheer da idanunsa suka juye sbd tsantsar bala'en kishi ya kalli kwayar idanun farhan yace" kasan wacce ita a wuri na kk fadamin wannan iskancin nk" farhan da idanunsa suka firfito sbd tsaurin shaqar da maheer ya masa yace" kaima kasan wacce ita a wuri na" hknne yasa maheer yyi jifa dashi gefe daya, yace" wlh,wlh bazan kyaleka ba saika fuskanci hukunci" wucewa yyi a mugun fusace ya wuce office dinsa yasa key, nurses din dake tsatstsaye da sauran ma'aikatan asibitin kowa ya cika da mamakin wannan abu, Dr.maheer kuwa kifa kansa yyi kawai a saman table din dake gabansa ya fashe da kuka tamkar wani qaramin yaro, meyesa bimbii tayi masa hk, meyesa bimbii ta bawa waninsa dama har ya ratsa gonar da ba tashi ba, shikam ko a ido ya raina shekarun farhan amma wai wannan danyen yaron bimbii ta baiwa kanta yyi mata wannan danyen aiki, tsananin so tare da tsantsar qiyayyar bimbii su sukayi tarayya cikin zuciyarsa, shi kansa ya rasa wanne ne yafi rinjaye, miqewa yyi a hnkli ya dauki handkerchief dinsa ya goge hawayen fuskarsa sannan ya dauki farar rigarsa ta likitoci yasa ya bude office dinsa ya fita, dakin da bimbii take ya shiga ya tarar da nurses sun zagayeta don bleeding take sosai, suna ganin shigowarsa suka bashi wuri, kai tsaye ya soma gudanar da aikinsa akanta batare daya kuma kallon fuskarta ba, cikin izinin Allah ya samu nasarar tsaida jinin dake zuba sannan ya mata allurar bacci mai nauyi, yana gama aikinsa ya fito daga dakin ko kallon inda su farhan suke beyi ba saida abeed ya miqe da sauri yasha gabansa yace" kayi hkr abunda yaro na ya mk don Allah ka dubamin diyata dakyau" kallon mamaki maheer ya masa sai kuma yyi murmushi yace" ka ta6a ganin inda mutum yyi wasa da rayuwarshi?" dukkaninsu kallonsa sukayi don basu fuskanci me yake nufi da hk ba, be sake kallonsu ba ya koma office dinsa, farhan dogarewa yyi daidai bakin dakin da bimbii take har lkcin da nurse ta basu damar shiga su ganta, cikin sauri duk suka miqe suka shige dakin, samunta sukayi tana bacci, farhan ya zauna gefenta yana kallon fuskarta yana hararar cikin dake jikinta don gani yake duk wannan cikin ne ke wahal da ita,ummu farhan riqo hannun bimbii tayi tana mata addu'ar samun lfy, ranar Dr.maheer a asibiti ya kwana ya kasa tfy gida, bini bini ze leqa dakin da bimbii ke kwance, idanunsa kuwa sunyi jajir sbd kukan daya sha, kishi ne kawai ke wahal dashi mutuqar ya bude idanu yaga bimbii dauke da jikin waninsa sai zuciyarsa tayi daci,6angaren masarautar burham kuwa har yanzu sarki abdallah bin jabal na nan kan bakansa, wannan abu dake faruwa shine ya bawa prince nasaar damar samun shiga sosai wurin sarki abdallah, prince nasaar ya samu cikakken iko da fada aji cikin wannan masarauta ta burham, hkn shine ya bashi damar fito da abunda ya jima a qasan ruhinsa wato daukar fansa kan sarki abdallah bin jabal, prince nasaar da ne ga sarki hamxa mai sarautar birnin al' bait, sarki abdallah bin jabal shine silar rusa wannan kyakykawan birni ya dawo dashi qarqashin mulkinsa, qarfi da shahara da masarautar burham ke dashi idanun duniya yasa batare da wani jayayya ba sarki hamxa ya miqa wuya ga sarki abdallah bin jabal inda birninsa ya dawo qarqashin inuwar masarautar burham, sarki abdallah dakansa ya nemi sarki hamxa ya bashi riqon prince nasaar tun yana qarami sbd yana son masarautarsa ta qulla zumunta ta musamman da masarautar al'bait, wannan shahara da daukaka da masarautar burham ta samu ya mugun tsolewa masarautu da dama idanu burinsu su durqusar da wannan izzah ta sarki abdallah bin jabal, prince nasaar babban burinsa shine masarautar burham ta dawo qarqashin izzah da sarautar birnin mahaifinsa, wannan kudiri nasa yasa shi cigaba son cigaba da kasancewa cikin wannan masarauta yana aikawa da sirrin wannan masarauta birnin al'bait saidai har wayau masarautarsu batayi tsayin da zata iya hada kafada da masarautar burham ba, prince akbar ya kasance babbar garkuwa ga wannan masarauta ta burham sbd tsantsar jarimtarsa hadi da sharp intelligency nasa, rufe prince akbar da sarki abdallah yyi ya baiwa tarin maqiyansa na ruguza masarautar burham ne batare daya fahimci hkn ba,prince nasaar ya samu yarda da amincewar sarki abdallah sosai, prince akbar yasa bimbii cikin qalbinsa, zuciya da gangar jikinsa bimbii suke buqata, yau tsawon watanni hudu kenan yana rufe amma bimbii bata ta6a 6acewa cikin tunaninsa ba,yau da dare yana zaune ya kalmashe kafafunsa ya jingina da jikin qarfen kurkun, idanunsa a lumshe suke yana tuna duk wani kyakykyawan memory nasa da bimbii,muryar mahaifiyarsa yaji tana masa mgn tace" ina son kayi yadda mahaifinka keso ka mance da wannan baiwar, cikin jikinta ba nk bane daman ai, ka furta hkn gaban kowa, mahaifinka yana yin hkne duk don ya kare muhibba da daraja na wannan masarauta, ina son ka bashi hadin kai" shiru prince akbar yyi sai kuma ya bude idanunsa ya kalli mahaifiyarsa dake hawaye tana kallonsa yace" ranki ya dade idan har na furta hkn nayi qarya, cikin dake jikin wannan baiwa nawa ne bana wani bane sbd me zan qaryata hkn,kar ki damu dani ko halin da nk ciki a yanzu koda na fita daga nan ba lalle rayuwa tayi tsawo ba nima, nafi son nima na tafi na bar wannan duniya mai cike da rudani" kuka sosai sarauniya take tace" kafi fifita soyayyar mace fiye da soyayyar mahaifiyarka yarima" kallonta yyi sosai yace" soyayyarki ta daban ce cikin ruhina baki da mahadi nan duniya ranki ya dade" murmushi tayi hade da kuka a hade ta zauna dakanta take bashi abinci a baki cike da qauna,hmmm,uwa uwace Allah kabarmu da iyayenmu ka bamu ikon faranta musu, soyayyar uwa soyayya ce da babu alqus so ne na haqiqatan, idan mutanen duniya dukka sun gujeka uwarka tana nan tare dakai.............
Littafin nan na kudi ne, idan kina da buqatar karantawa zaki tura #300 ta wannan acct...0100790419,alhaji shahida nasir, saiki turon da screesht ta wannan layi a whatsapp...07041195806......
Alkalamin Bintuu ne......
10/10/20, 1:12 AM - Anti qamshi🌷: *DAREN GOMA SHA HUD'U*🪔🪔
Written By Bintuu Seer
30
*Without you in my life there is no happiness*.....how long can I wait for you my love💕💕
Cikin dare ta farka ta bude idanu ta ganta kwance bisa gadon asibiti, dakin babu kowa sai ita kadai, qoqarin miqewa take zaune taji duk jikinta yyi tsami tamkar wacce ta shekara tana jinya, ciza le6enta tayi ta miqe zaune dakyar, kofar dakin taga an turo ta waiga da sauri ta gano ummu farhan, tana ganinta zaune ta qaraso da yalwar fara'a a fuskarta tana mata sannu da jiki,daga kai kawai bimbii tayi,kamar yadda ta saba mata cup ta dauka ta zuba mata zuma a ciki ta bata ta shanye, shigowar Dr.maheer cikin dakin ne yasa su kallon kofa, tsayawa yyi chak yana qarewa bimbii kallo da take zaune riqe da cup a hannunta sannan ya soma takowa a hnkli ya qaraso wurin gadon da take, kallon dayake mata ne yasa ta dago da kanta ta kalleshi suka hada idanu, sam ita bata gane shi ba amma mamakinta shine meye yasa hk kawai shi wannan mutum ze tsareta da idanu hk, Dr.maheer kuwa tsabar mamakin bimbii ne ya qamar dashi a wurin ganin yadda ta nuna 2kwata bata ma gane shi ba, kallonta yyi sosai ya nuna mata cikin dake jikinta yace" wannan meye a jikinki" ummu farhan kallon maheer tayi galala sai kuma ta mayar da dubanta kan bimbii data sunkuyar dakanta tana kallon cikin dake jikinta, yace" daman hk kk ban sani ba, sai yanzu na fahimci abunda yasa ki gudu wato sbd baki samun abunda kk buqata koh" dukkaninsu kallon maheer suke da tarin mamaki musamman bimbii da ko kusa bata fuskanci inda zancen Dr.maheer yasa gaba ba, kallon ummu farhan bimbii tayi ta nuna maheer da hannu tace" ummu wannan waye shi" murmushi ummu farhan tayi tace" shine likitan daya duba ki" murmushi bimbii tayi tace" toh meye yake fada hk" dafata ummu farhan tayi tace" ki bar wannan mgn zamuyi anjima" wannan abu ba qaramin fusata Dr.maheer yyi ba yace" kin manta dani koh sbd kin samu tsinannen daya la'anta rayuwarki,uhumm" miqewa ummu farhan tayi cike da fushi tace" ya isheka hk mn, baka ganin halin da yarinya ke ciki ne kk takura mata da wasu zantuttuka nk" bimbii ta kalleta tace" ummu wai meye ke faruwa ne dani" daidai lkcin abeed da maheer suka shigo suka tarar da abunda ke faruwa, farhan ya kalli Dr.maheer yace" wai kai waye ne kk takura mn" murmushi Dr.maheer yyi ya fizgo hannu bimbii ya cire mata drift din dake hannunta tunda ya riga ya qare sannan ya dago dakansa ya kalli farhan yace" nine mamallakinta gbdy" abeed ya kalli Dr.maheer yana son mgn kuma sai yyi shiru can dai ya dago dakansa yace" doctor ita wannan da kk gani tana da matslr lose of memory bazata gane abunda kk fada ba yanzu" saurin kallon bimbii maheer yyi cike da mamaki, farhan kuwa haushi ne ya cika shi, ita kuwa bimbii kallon kowa take a wurin galalau tamkar wata sakarya sbd bata fuskanci abunda yake faruwa ba, juyawa abeed yyi ya fice daga dakin Dr.maheer yabi bayansa, office din Dr.maheer suka shiga ya nuna masa wurin zama ya zauna, 2tiryan abeed ya labartawa Dr.maheer yanayin daya tsinci bimbii, shiru yyi ya kasa mgn, dago dakansa yyi yace" kaima bakasan waye da cikin jikinta ba kenan" kada kai abeed yyi alamar ehh, gbdy kansa ya kulle ya rasa abunda ke masa dadi, miqewa yyi ya fice daga office din shima abeed ya miqe yabi bayansa, batare da wani 6ata lkci ba Dr.maheer ya nufi neurologists dept ya samu Dr.waaz suka tattauna, washegari aka sanya bimbii cikin wani na'urar don't bincika mtslr dake faruwa da kwakwalwarta, abunda suka gani kawai shine ta samu temporary lose of memory amma with time insha'Allah all past events ze din ga dawo mata cikin brain nata, cikinta dake jikinta kuma yana da watanni shida da kwanaki, lkcin daya ga result din shiru yyi sbd shi sai yanzu ne yarda tayi losing memory, kwananta uku sukayi discharge nata amma 2qiri Dr.maheer ya nunawa abeed wlh bimbii wurinshi zata koma tunda ita din property dinsa ce yana da certificate na mallakarta, farhan da umminsa suka doge kan basu san wannan zance ba, Dr.maheer yace" idan kunki bani ita da arziki toh hukuma zata bani ita" abeed mutum ne mara son hargitsi tashi daya ya damqawa Dr.maheer bimbii, farhan baqin ciki kamar ze kashe shi, ranar qin yiwa kowa mgn yyi, bimbii kam bata san abunda ke faruwa ba sai wayar gari tayi ta nemi wannan iyali ta rasa sun tafi sun barta a asibitin ko sallama abeed be bari sun mata ba sbd kar hnklinta ya tashi ko kuma taqi amincewa, Dr.maheer ya shigo dakin dakansa ya sanar mata tfyrsu sannan ya shaida mata duk abunda ya faru, yace" yanzu gida na zaki koma da zama" wani irin kallo ta masa mai kama da harara sai kuma ta fashe da kuka tace" kai wanne irin mutum ne hk kawai zaka rabani da dan'uwana da iyayena" murmushi yyi yace" su waye iyayen nk? uhum, ko ban furta miki ba kina kallon launin fatarki da nasu kinsan basu ne iyayenki ba ai suma tsintarki sukayi da cikin da basu san daga inda kk samo shi ba,kona arziqi kona tsiya nafi gani ma dai na tsiyan ne" qura masa idanu tayi kawai tana sauraron baqaqen maganganun dake fita daga bakinsa kan cikin dake jikinta da ita kanta batasan a ina ta same shi ba, murmushin rainin hnkli ya mata daya ga tana kallonshi ya noqe kafadarsa tare da ta6e baki, badan ta so ba hk ta tashi tabi bayan Dr.maheer suka fita daga dakin suka fice compound na hospital din sai 2waige take ko zata gano ummu farhan ko farhan amma bata ga ko masu kama dasu ba, bude mata mota Dr.maheer yyi ta doge taqi shiga saida ya matso da niyyar daukanta ya cusata ciki tayi saurin shiga motar,farhan kuwa yana la6e daidai gate din fita daga hospital din yana kallon fitowarsu, hawayen dayake 6oyewa suka soma sauka kan quncinsa yana kallo har suka fice daga hospital din, tana ta 2kalle ta jikin glass din motars, har suka qaraso wani wurin inda ta hango tarin mahaya dawakai suna wucewa, wannan abun yaso tuna mata da wani abu amma ta kasa tunawa dole ta hkr, suna shiga farfajiyar gdn yyi parking yar motar shi gefe sannan ya fita ya bude mata ta fito, sai kallon gdn take har suka shiga building din maheer,two bedroom flat ne don hk ya bata daki daya, zama tayi a dan qaramin parlourn nasa sai qarewa ko'ina kallo take, shi kuwa ya shige bedroom nasa sai can ya fito sanye da three quater baqi da wata shirt ya shiga kitchen dakansa ya hada mata black tea da honey meast ya kawo gabanta ya ajiye, sannan ya tafi ya gyara mata bedroom din nata, ni kuwa nace lalle yaushe maheer ya zama bawan baqar fata,dakyar bimbii ta yarda tasha black tea, nuna mata dakinta yyi ta tashi ta shiga, dakin madaidaci mai kyau, ita gabanta har yanzu be bar faduwa ba sbd ta lura tunda ta shigo wannan gd bata ga matar gdn ba, tashi tayi da sauri ta sanya key ta rufe kofar sannan ta koma ta kwanta, maheer kuwa yazo ya buga ya buga taqi budewa so yake ta fito tayi dinner amma qirmishishi taqi bude kofar kuma tana jinsa sarai hk ya hkr ya koma yyi dinner dinsa shi kadai, bimbii kuwa kwanciya tayi ta matsantawa kanta da tunani don tana son tuna abubuwa amma kwakwalwarta tamkar ta toshe hk har kanta ya soma sara mata, hk bimbii ta cigaba da rayuwa a gdn maheer shi kuwa yana qoqari wurin bata kulawa yana ture damuwarsa kan cikin dake jikinta, ennah mahaifiyar maheer har yanzu batasan maheer ya gano baiwarsa ba don be sanar da ita ba hkma yayansa, masarautar burham kuwa tsantsar makirci ne yake kai kawo a cikinta, sarki abdallah yaqi sakin prince akbar duk kuwa da iyakar qoqarin neman afuwa da sarauniya keyi a madadinsa kullum ba dare ba rana amma sarki abdallah bin jabal shegen taurin kai ne dashi tamkar na kafiran farko, sarki abdallah yana zaune a dakin ganawar sirri shi da prince nasaar suna tattauna kan yadda zasu buda harkar kasuwanci tsakanin masarautar burham da manyan qasashe na turai, sarki abdallah bin jabal yana daya daga cikin manyan merchants na duniya dake fita da danyen gold a kasuwar duniya, shiyasa ya tara arxiki na ban mamaki, prince nasaar ya fito da wani qaramin akwati ya ajiye a gabansa yace" takardar yarjejrniyar kasuwanci ne tsakanin wannan masarauta da qasar japan" saurin daukan qaramin akwatin sarki abdallah bin jabal yyi ya bude, wata farar takarda ya gani a ciki kai tsaya yasa hannunsa ya fito da takardar ya soma warwarewa, prince nasaar yana kallonsa har ya gama warware farar takardar, hannunsa ne daya riqe takarda ya soma rawa sosai sbd qarfin gubar dake tattare da wannan takardar, dago idanunsa yyi yana kallon yana son yin mgn amma ya kasa,shi kuwa prince nasaar sai zabga murmushin qeta yake yana kallon sarki abdallah dake jan jiki,abunda ya shirya ya tafi daidai, mirqinewa sarki abdallah yyi daga kujerar dayake yana qoqarin nuna prince nasaar da hannu, prince nassar ficewa yyi daga 6angaren yana fita ya tura babbar hadimar sarki abdallah ciki kan sarki na buqatar ganinta tana shiga ta tarar da sarki abdallah cikin wannan yanayin, da gudu ta fito tana sanar da masu tsaron lfyrsa, arresting dinta sukayi kan itace tayi poisoning dinsa, wannan lbri tuni yakai kunnen sarauniyya mar'atussaliha, a gigice ta iso 6angaren ta tarar da gubar ta soma shiga jikinsa sosai,prince nasaar kuwa batare da wani bincike ba yasa takobinsa ya cire kan wannan hadima kan ita tayi poisoning din sarki, sarki abdallah kuwa ba bakin mgn balle ya furta abunda ke bakinsa yana son yin mgn amma ya kasa sai kallon nasaar yake, miqewa sarauniya tayi ta umarci kowa ya fita aka barta daga ita sai uxair sai kuma sarki, prince nasaar yaso ya tsaya amma sarauniya ta nuna shima ya fita dole ya juya ya fice,kallon uxair sarauniya tayi tace" ina son ka haxarta kai tsaye kaje a fito da prince mahaifinsa na son ganinsa" rissinar dakai uxair yyi alamar ya amsa umarninta sannan ya fita, kallon qaramin akwatin dake gefen sarki abdallah tayi ta qurawa akwatin idanu, prince nasaar kuwa tuni ya sanar da prince amir cewa aiki ya kammala, zaki ya kwanta dama wato sarki abdallah kenan, zaki ya kwanta dama shi kuwa dan zaki yana rufe, wannan itace kyakykywan dama da zasu iya amfani da ita wurin murqushe wannan masarauta ta burham, dayake a shirye suke tsaf tuni suka zagaye wannan masarauta da dakarunsu masu qarfin kayan yaqi, prince nasaar dakansa yasa a cinnawa wannan gdn kurku da prince akbar ke ciki wuta sbd so yake ya 6atar da tarihin sarki abdallah bin jabal da dukkanin ahlinsa, sarki najash wato mahaifin prince amir ya riga ya alqawarta ma sarki hamxa idan har ya taimaka musu suka ga bayan masarautar burham toh zasu samu cikakken dama wurin gauraya da manyan qasashen duniya musamman qasashen jar fata wurin kasuwanci, suna ganin kamar masarauta burham ita ta babbanke komai sbd tana da qarfi, su" 2kwata ba'a damawa dasu a kasuwar duniya........
Littafin nan na kudi ne, idan kina da buqatar karatun littafin zaki tura #300 ta wannan acct...0100790419, alhaji shahida nasir,union bank,saiki turon da screenshrt na payment dinki a whatsapp ta wannan layin...07041195806......
Alkalamin Bintuu ne......
10/10/20, 1:12 AM - Anti qamshi🌷: *DAREN GOMA SHA HUD'U*🪔🪔
Written By Bintuu Seer
31
*I miss you like crazy*....I will keep up waiting until the end of my last breath💕💕
Idanunsa na lumshe ya jingina da jikin qarfen kurkun yaji ana bude wurin dayake, dago idanunsa yyi sukayi idanu hudu da uxair babban hadimin mahaifinsa, kallon prince yyi ya rissinar dakai sannan ya qara bude masa kofar fita yace" yakai wannan dan sarki mahaifinka na son ganawa dakai" shiru prince akbar yyi sannan ya miqe suka fito, fitarsu kenan suka ga wuta ta kama wannan gdn kurku sai kururuwar mutane ake jiyo daga cikin wannan kurku, cike da mamaki prince ya kalli uxair yace" wannan ne dalilin dayasa kk fito dani sbd ku kashe bayin Allah marasa gata" girgixa masa kai uxair yyi yace" yakai wannan dan sarki wannan sharrin abokan gaba ne yanzu hk sun sanyawa mahaifinka guba yana cikin wani hali sannan gbdy masarauta a zagaye take da dakarunsu kowanne lkci zasu iya cimmu a yaqi" kallon prince yyi yace" yakai wannan hadimi ma'abocin kwarjini ina son ka dakata anan ka bada taimako wurin kashe wannan wuta" batare daya jira amsar uxair ba yyi wani irin tsalle ya haye dokin daya gani gabansa ya sakar masa linzami yyi hanyar da zata sadashi da masarautar burham, tun tahowarsa bisa doki kwararrun maharba mashi suke saitinsa, suna la6e ne bisa kan manyan tsaunika saitinsa kawai suke da mashi, abunku da jarimin gaske jikinsa ne kawai ya bashi tamkar akwai masu harinsa, cikin tsantsar hikima da zafin nama ya juya kan dokin dayake kai suka bar kan miqaqqiyar hanya suka fada cikin jeji, su kuwa maharan suna ganin hk suka tabbatar ya fahimci ana harinsa ne yasa yyi musu hk, dayake jejin na da duhu da sarqaqiya tuni ya soma shiga wannan sarqaqiya har ya samu damar 6ace masu ya fice daga wannan jeji, saidai tun daga nesa ya hango qatuwar kofar masarautar burham a rufe, wasu manya dakaru sun zagaye kofar ta waje suna son fasa kofar su afka ciki, qara gudun dokin yyi ya tunkari wannan rundunar mayaqan, ba jira kawai ya janyo wani bisa doki yyi wulli dashi ya amshe takobin hannunsa ya daga takobin sama tsirararta kafi kace kwabo kawai ya soma shayar da wannan takobi dake hannunsa jinin abokan gaba, wata irin bajinta yake nunawa tamkar wani ifiritin aljani hk yake fada ba gjywa, dakarin masarautar burham dake saman qanuwar masarautar suna hangen artabun dake wakana tsakanin wadannan dakaru da babban prince, fada yake cike da sadaukarwa batare da shakkar mutuwa ba domin zuciyarsa ta bushe qamas baya tsoron mutuwa ko kadan, daga idon da zeyi ne ya hango prince amir dakansa ya saitinshi da mashi, yana harbo mashin ya damqo wani daga cikin mutanensu ya tare mashin dashi,gbdy jikinsa ya 6aci da jini sai lkcin masu tsaron babbar kofar shiga masarautar burham suka wangale kofar dakarin sarki abdallah suka soma fitowa sanye da shigar yaqi saidai lkcin prince akbar shi kadai kawai ya riga yaci qarfin yaqin, abun mamaki prince nasaar na cikin dakarin masarautar burham domin har yanzu babu wanda ya fahimci fuska biyu ne dashi, tsayawa yyi yana kallon yadda prince yyi musu 6arna, tsoronshi daya kar suyi failing plan dinsu sbd idan har aka samu mtsl tabbas daga shi har mahaifinsa suna cikin mtsl don sun san masarautar burham saita dauki fansa akansu, shiga cikin wannan filin artabu ya somayi sai yyi kamar yana yaqar dayan 6angaren, prince akbar kuwa yana tsaka da fatattakar wannan dakaru ya hango fitowar dakarin mahaifinsa sanye da shigar yaqi, juyawa yyi ya cigaba da 6arar da maxa abinsa, prince nasaar cikin hk ya samu qarasowa kusa da prince akbar, prince ya ganshi amma ya dauka a 6angarensu yake don hk ya juya ya cigaba da fadansa, ba zato kawai yaji saukar takobin prince nasaar a qirjinsa, juyawa yyi yana kallon prince nasaar da mamaki yaga ya sake daga takobinsa da niyyar yanke kansa cikin zafin nama ya bige dokin da prince nasaar yake kai ya fadi qasa yasa sawun dokinsa ya takeshi ya wuce abinsa, takobin daya sara masa bata samu damar ratsa shi sosai ba don hk ya cigaba da wasa da jinin abokan gaba, cikin qanqanin lkci suka musu kyakykywar 6arna, tsirarun dakarinsu sarki najash suka soma ja da baya suna neman gudu, prince amir kuwa ya dade da arcewa tunda yaga 6arnar da ake musu daman shi ba wani jarimi bane a filin fama barshi dai da iya hada tuggu, lkcin da prince yaga abokan gaba sun soma arcewa sai yaja gefe ya sauke takobinsa qasa sai digar da jini take ya nufi wurin da abokan gaban suka kafe tutarsu ya tugeta ya jefar, salute kawai dakarin masarautar burham suke masa cike da girmawa, hk suka soma shiga cikin babbar kofar masarautar burham cike da murnar samun nasara akan abokan gaba, tun daga kofa yan mata ne jere sunyi ado suna rera waqar yabo da jinjina ga jarimai mazan fama wadanda suka sadaukar da rayuwarsu sbd kare mutunci masarautarsu, suna rera waqar ne cikin harshen larabci hannunsu dauke da furanni suna watsa musu suna daga musu hannu alamar barkansu da dawowa lfy, prince kuwa fuskar nan tashi tamkar hadari sai bin dokinshi suke suna zuba masa fure suna masa baitoci da jinjinar ban girma bisa namijin jarumtarsa, cikin waqar tasu suna danganta shi da zaki dan zaki, jarimtar gadonsa ce ba haure ba, hk dai suka din ga binsa da baitocin yabo har ya isa cikin gdn sarautar burham, nan ma ya samu tarar girma ga dukkanin bayi da masu tsaron wannan gida hk suka raka shi da baitoci, sarauniya na 6angaren sarki abdallah wannan lbr na isowar danta ya taddata, ummu nana ta sanar da ita prince akbar shine yyi uwar watsi da maqiya ya kuma cire musu tuta, wannan kyakykywan labari yasanya xuciyar sarauniya tayi haske duk da alhinin da take ciki na ganin sarki abdallah bin jabal kwance rai a hannun Allah, tana zaune gefen sarki abdallah prince ya nemi iso take ta bashi damar shigowa, cikin sauri ta tashi ta rumgume shi tana kuka sai kuma ta soma duba jikinsa ko ya samu rauni, murmushi yyi ya riqe mata hannunta suka qarasa inda sarki abdallah bin jabal ke kwance, kallon mahaifin nasa yyi sosai yana nazarin symptoms na poison din dake jikinshi, hannu yasa cikin aljihunsa ya fito da wata qaramar kwalba ta antidote din daya ta6a baiwa bimbii ya bude bakin mahaifin nasa ya tsiyaya masa, wannan antidote shima dattijo abbas ne ya ta6a bashi lkcin daya ceto rayuwarsa a hannun sarki najash, antidote din yana kashe qarfin kowanne irin guba, sarauniya ta kalleshi tace"ka gafarci mahaifinka bisa kuskurensa gare ka yakai wannan jarimin dan sarki" riqo hannayenta yyi yace" komai laifinsa gare ni mahaifina ne shi dole ranki ya dade" murmushi tayi kawai,prince ya jima a 6angaren mahaifinsa suna tattaunawa da sarauniya kafin ya dawo 6angarensa, komai na 6angaren nasa yana nan yadda yake sannan bayin dake hidimtawa 6angaren kowa yana kan aikinsa,lenah itace daman mai kula da makwancin prince 6ata wasa da aikinta, ubaid yana shima yana kan aikinsa, prince yana shiga ya bada izini baya buqatar ganawa da kowa, lenah ce kawai ta samu damar shiga ciki, batare da 6ata lkci ba tayi masa gyaran fuska ta wanke masa qafa, ta rage masa tsawon suman kansa data sauko masa har baya tamkar gashin mata ta maida shi ya dawo kafadarsa,tuni sumar tasa ta soma walwali da sheqi tana daukar idanu, duk abunda take gani yake kamar bimbii ce take masa hidima,6angaren gidan maheer kuwa bimbii bata masa aikin fari bare na baqi komai shine yakeyi dakansa, idan ya dafa abinci tunkan yaci ze kawo mata nata ya zauna ya sata gaba har sai taci sannan zeci nashi, wani lkci idan ya zauna yana kallonta sai ya qurawa cikin jikinta idanu ya tunanin uban waye da wannan ciki, ji yake tamkar idan ya hadu da wanda yyi cikin nan ze iya kashe shi sbd baqin kishin dayake ji idan ya kalli cikin amma a hk dole yake daurewa yake hidimta mata sbd qarfin so daya rinjayi qarfin qiyayya, kullum idan ya shirya fita aiki sai ya ajiye mata komai kusa da ita tamkar wacce bata iya motsi sannan baya fita sai ya tabbatar ya rufe duk wata kofar fita ta gdn, gani yake kamar idan yabar kofa bude bimbii zata sake guduwa ta fice daga rayuwarsa ta barshi da dawainiyya da dakon soyayyarta, idan ya dawo sai ya dubata ya tabbatar ita da abunda ke cikinta suna cikin qoshin lfy, fatar jikinta tuni ta murje tayi kyau da santsi sbd cima da take samu mai kyau da gina jiki,duk bala'I bata bari maheer ya matso kusa da ita tuni zata matsa nesa dashi, wannan abu yana masa ciwo amma Allah ya dorata akansa yadda komai takeso shi yake tamkar wani bawanta,ranar wata laraba ennah mahaifiyarsa ta kawo masa ziyarar bazata, lkcin data ga bimbii abun ya mugun bata mamaki da daure mata kai musamman data ganta da ciki, kallon Dr.maheer tayi tace" a ina ka samota" sosa qeya ya somayi yace" a asibitinmu mn" wata uwar harara ta doka masa tace" shine baka fadamin ba yaushe ka soma 6oyemin abu" murmushi yyi yace" sorrryy" cikin wasa ya furta hkn ya soma riqe mata hannu, fizgewa tayi cikin fushi ta kalleshi tace" wannan cikin dake jikinta na uban waye?! ko kana nufin kacemin a hk ga gano ka kuma amince ta dawo gdnka sbd kai daqiqi ne" kalaman mahaifiyar tashi sun masa tsauri sosai tuni ya tamke fuska, sam shi be saba ganin ennah na masa fada ba ta shagwa6a shi dayawa, batare data kula da hade ran daya yyi ba ta dokawa bimbii tsawa tace" ke cikin uban waye a jikinki" bimbii kuwa jikinta rawa yake ta tsorata da matar kawai kallonta take ta kasa mgn, ennah ta nunawa bimbii hanyar fita tace" ina son ki fita ki kama gabanki ko waiwaye wannan gdn kar ki kuma yi" saurin kallonta maheer yyi yace" what are talking, did you mean ta tafi ta barni kenan" murmushi yyi yace" idan ta tafi nima zan bita mu tafi tare cox she is my life" galala ennah tayi tana kallon abun mamaki..............
Littafin nan na kudi ne, idan kina da buqatar karantawa zaki tura #300 ta wannan acct...0100790419, alhaji shahida nasir,union bank, saiki turon da screenshrt ta whatsapp through wannan layin....07041195806.......
Alkalamin Bintuu ne......
10/10/20, 1:12 AM - Anti qamshi🌷: *DAREN GOMA SHA HUD'U*🪔🪔
Written By Bintuu Seer
32
*Come back to me my love*......I can't hold back my tears, I can't forget your beautiful face,I'm missing everything about you my sweetheart💕💕
Ennah ta daka masa wata rikitacciyar tsawa tace" are you in your right sense? kai makaho ne baka ga abunda ke tare da ita bane, maheer mai ke faruwa dakai ne, just cox of this stupid slave you are exchanging word with your mother" bimbii kuwa jikinta na rawa sbd tsorata da tayi ta soma qoqarin fita ta gudu, charaff, maheer ya riqe mata hannu, kallon ennah yyi yace" I just want to marry her" wata irin zabura ennah tayi tana masa wani irin kallo irin wanda ake yiwa masu ta6in kwakwalwa, tunani ta somayi anya maheer be samu matsl a brain nasa ba kuwa, murmushi tayi kawai ta juya ta fice daga gdn gbdy ta shige mota driver nata yaja suka nufi gd, tun a mota zuciyarta ke kai kawo da tunani barkatai game da bimbii,tana isa gd ta kira faisal tayi masa bayanin kan abunda ya faru, shiru yyi sai can yace" kinsan rigimar maheer amma ina ganin kawai abunda yafi ki dauki yarinyar ki mayar da ita kasuwar saida bayi inda kk siyota ki musanyo da wata amma kar ki kuma kawo mn baqar fata" murmushi tayi tace" hkn ya kamata nayi kam" maheer kuwa dakyar ya rarrashi bimbii yyi ta bata hkr kan kar ta damu babu inda zata mutuqar yana raye, washegari, ya shiga kitchen ya hada breakfast ya kawo mata har dakinta, tana daga kwance tana faman tunani taga ya bude kofa ya shigo, saurin miqewa zaune tayi tana kallonsa, wani qaramin stool ya jawo ya ajiye mata honey tea din daya kawo mata da wani abu kamar samosa a small plate, yace" ga breakfast ki tashi kici sai kiyi wanka ki kwanta ni zan tafi hospital" daga masa kai kawai tayi ya juya ya fita daga dakin, qaramin briefcase dinsa ya dauka ya fice wajen building din ya hau qaramar motarsa ya nufi hospital, bimbii kuwa a hnkli ta sanya hannu ta dauki cup na tea din tana sipping cike da sanyin ciki ga cikinta sai motsi yake mata, hannunta ta dora kan cikin nata tana shafawa, hawaye ya soma sauka saman kumatunta ba komai ne yasata kuka ba sai rashin sanin waye da wannan cikin dake cikinta wanda akanshi kowa sai tsangwamarta yake, gani take kawai ita tamkar rayuwa take mara alqibla don batasan komai game da rayuwarta ba, sautin qarar bude kofan da taji ne yasata kallon kofar shigowa dakinta, shiru bata ga kowa ya shigo ba, tashi tayi da sauri ta nufi kofar ta dan bude don leqawa aikuwa idanunta ya nuna mata ennah, faisal ne yasa wani key ya bude kofofin shigowa building din gbdy don maheer ya rufe ko'ina, qoqarin rufe kofarta take ta sanya key faisal yyi saurin turowa, kallonta suka tsaya yi cike da mamaki wato har ma daki ne da ita na musamman cikin building din maheer,ennah tace" ki fito mu tafi" kallonsu ta tsaya yi saida faisal yyi mata tsawa sannan ta fito, hk suka tasata a gaba har bakin motarsu, cikin sauri driver ya bude mata butt ba musu ta shiga ya rufe butt din, ennah da faisal suka shige bayan mota suka zauna drivern yaja suka fice daga gdn, kai tsaye kasuwar saida bayi suka wuce da ita, yawanci masu cinikin bayin sun qi siyenta sbd basu son mai ciki sun fi son suna siyen bawa su siyar dashi amma ita idan sun siyeta saidai suyita wahala da ita masu siye basu son mai ciki, ennah da taga kowa yaqi siyen bimbii sai kawai ta kalli wani daga cikin masu saida bayin tace" toh gata na baka ita kyauta" washe baki balaraben mutumin ya somayi yana dariya cike da jin dadi ya mata gdy sosai, ennah ta siya wani bawan suka shige motarsu suka tafi, bimbii kuwa balaraben ya sanya gefe cikin bayin da basu da kasuwa don be sanya cikin kejin siyar da bayi ba kar masu siye su qi qarasowa wurinsa idan suka hangi mai ciki cikin bayinsa, wasu manyan hadimai ne daga masarautar abu ansar suka shigo wannan kasuwa don siyen bayi, masu cinikin bayi kuwa suna ganinsu suka soma zuwa wurinsu da gudu suna nuna musu bayinsu don tun daga ganinsu sun san daga gdn sarauta suke kuma sun san sarakai bayi dayawa suke siye basu siyen dai dai, su kuwa wadanda manyan hadiman gdn sarauta sai wani shan qamshi suke suna tfy suna kalle kallen kejin da bayi ke ciki, tsayawa sukayi wurin kejin wannan balarabe da bimbii ke wurinsa, kallonsa sukayi suka ce suna son siyen dukka bayin dake wurinsa, jikinsa na rawa ya shiga rumfarsa ya soma rubuta musu certificate na mallakar bayin da suka siya ya fito ya miqa musu, har zasu wuce dayan ya kalli bayin dake gefe yace" wadannan bana saidawa bane" da gudu balaraben yace" suma na saidawa ne ranka ya dade" yace" toh meyesa baka hada dasu ba" shafa dogon gemunsa yyi yace" su wadannan suna da yar matsala ne shiyasa" nuna bimbii yyi da yatsa yace" waccer ita ciki gare ta sauran kuma basu da cikakken lfy" murmushi daya daga cikin hadiman yyi yace" bamu son marasa lfy amma ita mai cikin tana da cikakken lfy ne?" cikin sauri balaraben yace" ita tana da cikakken lfy kawai cikin ne mtslrta" yace" ka hada mn da ita" da gudu ya shiga cikin rumfarsa ya rubuta musu certificate na mallakar bimbii ya kawo musu, hk suka din ga bi keji keji suna siyen bayi suka hada bayi dayawa suka kwashesu cikin wata doguwar mota suka nufi masarautar abu ansar, sarki abu ansar aminin sarki abdallah bin jabal ne sosai kuma shima masarautarsa tana da qarfi sosai, yana da ya'ya mata guda biyu, gimbiya khamriyya da gimbiya mariyatul kifdiyya wacce itace akayi yarjejeniyyar aure tsakaninta da prince akbar, dukkanin wadannan gimbiyoyi kyawawa ne na gaban kwatance, gimbiya mariyatul qifdiya itace qarama, sarki abu ansar ya dora buri sosai kan wadannan yara nasa yana mutuqar son su baya son 6acin ransu ko kadan, lkcin da manyan hadiman wannan masarauta ta abu ansar suka iso da bayi, tuni uwar bayi ramlatul asuwat tayi jawabi ga wadannan sabbi bayi ta sanar dasu duk wasu dokoki na wannan gd, tana gamawa ta rarrabasu 6angarori daban daban na wannan gdn sarauta tare da basu ayyuka daya dace da kowanne, kallon bimbii tayi ta ganta da ciki tace" ke zan kai ki turakar jira sbd anan baki da aiki amma can qila wani ya buqaci mai yaron ciki" kallonta bimbii kawai take don ita bata fuskanci ina ne turakar jira ba, turakar jira wuri ne da ake ajiye mata masu kyawun jiki da siffa mai kyau dake iya daukar hnklin maza sbd da tarar manyan baqi, idan aka kai mace wannan wuri bata da aiki saidai gyaran jikinta da kula dakanta da kwalliya da sutura mai kyau, toh idan akayi wasu manyan baqi a wannan masarauta akan zo turakar jira a za6i mata a kai musu don su debe musu kewa, suyi musu tausa su kwana dasu idan suna buqata, duk macen dake turakar jira toh amfaninta kenan a wannan masarauta, batare da wani 6ata lkci ba ramlatul aswat ta miqa bimbii hannun suwaiba wacce itace mai kula da matan dake turakar jira, suwaibah kallon bimbii tayi da murmushi a fuskarta tace" tabbas zaki samu wurin zama a wannan turaka sbd kina da siffa mai kyawun gaske duk da kasancewarki baqar fata" ita dai bimbii bata fahimci kwata kwata me suwaiba take nufi har ta kira wata baiwa tace" kije ki gyara wannan sabuwa ce tana buqatar a koya mata dabarun jan hnkli da kula da jiki,amma yanxu ki shiga da ita ki soma gyarata tukunna" kama hannun bimbii tayi suka shige ciki, dogon gashin bimbii ta soma wankewa tayi masa tas sannan ta hada sinadaran wanka ta kalli bimbii dake tsaye tamkar wawuya tace" ki shiga kiyi wanka da wadannan sinadarai" ba musu bimbii ta shige dakin wanka, tana wanka tana ganin datti sosai na fita sbd wadannan sinadaran wanka basu barin datti a fata, tana fitowa wannan baiwa mai suna rabi'at ta zaunar da ita ta soma shafeta da kayan gyara, tuni fatarta ta soma sheqi da daukar idanu tamkar ba baiwa ba, gashin kanta shima ya kwanta har tsakiyar gadon bayanta, sai kyalli yake,ita dai bimbii sai kallon ikon Allah take gani tayi sai gyarata ake tamkar wata amarya, kayan mai kyau rabi'at ta bata ta sanya ta nannade mata gashnta yyi tudu tamkar a cuci sannan ta yafeta da wani mayafi mai shara shara, turare kuwa an mata 6arinshi, maida ita tayi dakin da suwaiba take, tana ganinta tayi murmushi tace"masha'Allah" basu sanya bimbii cikin jerin masu tarar baqi ba sai ta kware sosai wurin iya hillata da kissa da sauran dabaru na janye hnklin maza kafin su sanyata cikin jerin matan dake tarar manyan baqi, daki na musamman aka kaita inda ta ga dukkanin mata dake dakin sunyi ado na kece raini suna zazzaune, wata hamshaqiyar mace zaune tana koyar dasu salon tfy da rausaya da iya juya jiki har ma da yadda zasuyi taku a gaban namiji, tashin kowacce take cikinsu daya bayan daya suna gwada yadda zasuyi taku da karkada jikinsu don su janye hnkli, bimbii sakwato tayi tana ganin abubuwan mamaki, lalle kuwa cikin akwai salon rayuwa 2kala sai wanda idanunka suka iya gani da wanda kunnuwanka ya ta6a ji, ita dai bimbii gata ta shigo duniya tana diban darasi 2iri mai amfani da mara amfani, yau dai ga bimbii Allah ya jefota masarautar abu ansar kuma a turakar jira,6angaren masarautar burham kuwa jikin sarki abdallah bin jabal dai toh har yanzu dai cigaban kadan aka samu da taimakon wannan antidote da prince akbar ya bashi yanxu yana iya motsa jikinsa, prince tunda yake be ta6a tsintar kansa cikin halin rayuwa irin wannan ba, ga mahaifinsa babu lfy ga bimbii besan tana raye ko a mace ba, yau shi kadai yana tsaye bakin wannan glass window din dayake tsayuwa hannunsa dukka a bayansa, sanye yake da wasu fararen pakistan, gashin kansa yyi luf luf don yana shan gyara, fuskarsa ta dan fada hkn ya baiwa dogon hancinsa damar fitowa dodar tamkar biro,sajensa kwance gefen fuskarsa, kallon waje yake tamkar mai tuna wani abu hannunsa na dama riqe da wadannan awarwarayen na bimbii, lenah ce ta shigo hannunta riqe da wani qaramin faranti mai kyan gaske ta ajiye saman wani table, takowa tayi a hnkli wurin dayake tsaye ta tsaya a bayansa tare da rissinar dakanta qasa tace" ranka ya dade ka kwantar da hnklinka insha'Allah jikin sarki mai daraja zeyi sauqi bada jimawa ba" shiru ya mata kuma be jiyo ya kalleta ba, idanunta ne yakai kan hannunsa na dama inda ta ga yana riqe da wasu awarwaraye, mamaki sosai ya cikata take tunanin ko wannan awarwaron wacce prince yake riqe dashi, cigaba tayi da tsayuwa har ya juyo ya wuceta ya koma kan wata kujera ya zauna ya janyo alqalami da farar takarda yana rubutu, tahowa tayi wurin ta soma tsiyaya masa herbal tea din data kawo masa, hannun biyu tasa tare da rissinar dakanta qasa tana miqa masa cup din, dago da kansa yyi ya kalleta sannab yasa hannu ya amshi cup din ya ajiye ya daga mata hannu, hkn yasa ta dauki farantin data kawo ta juya ta nufi hanyar fita jikinta a sanyaye, ubaid ne ya shigo ciki da sauri ya tsaya tare da rissinar dakansa qasa yace" ranka ya dade muna da baqi daga masarautar abu ansar" .....
Littafin nan na kudi ne, idan kina da buqata zaki tura #300 ta wannan acct..0100790419,alhaji shahida nasir,union bank,idan kin tura saiki turomin da screenshrt na payment dinki ta whatsapp a wannan layin...07041195806....
Alkalamin Bintuu ne....
10/10/20, 1:12 AM - Anti qamshi🌷: *DAREN GOMA SHA HUD'U*🪔🪔
Written By Bintuu Seer
33
*I still love you, I still miss you*.........I just want to see you back,pls come back I'm still waiting for you💕💕
Baqi ne daga masarautar abu ansar sun iso ne bisa wakilcin ammar bin jabir don duba jikin sarki abdallah bin jabal,sun samu tarar girma sosai cikin masarautar burham, sarki abdallah kam yanzu jikin nasa babu laifi tunda yana iya miqewa zaune saidai baya iya furta komai,masarautu da dama sun ji dadin wannan cuta da sarki abdallah bin jabal ya kwanta, 6angaren da sarki abdallah ke jinya kuwa ko quda be isa ya ratsa ta wurin ba sbd tsatstsauran matakan tsaro, iyalanshi kawai keda damar shiga su duba shi shiyasa har yanzu babu wanda ze iya bada tabbacin ya jikin sarki abdallah yake ana samun cigaba ko ba'a samu game da lalurar data tadda shi, yau da dare sarki abdallah bin jabal ya daga idanu ya kalli prince akbar dake zaune gefensa yana son furta masa wata kalma amma babu bakin mgn, miqa hannunsa yyi yana buqatar a bashi takarda da alqalamin rubutu, prince ne ya dauki alqalamin da takarda ya miqa masa don ya fahimci abunda yake nufi, amsar takardar yyi ya soma rubutu a hnkli,yana gamawa ya ajiye alqalamin ya miqawa prince akbar farar takarda, amsar takardar yyi yana duba abunda ta qunsa, umartar prince akbar yyi kan yabi wadannan baqi da suka zo daga masarautar abu ansar don ganawa da sarki abu ansar da kuma yarsa gimbiya mariyatul qifdiya, saurin dago idanunsa yyi yana kallon mahaifin nasa cike da mamaki, sarauniya dake zaune gefe ta amshi wannan takarda dake hannun prince akbar ta duba, saurin dago idanunta tayi ta kalli sarki abdallah bin jabal tace" ranka ya dade, yanzu lfyrka itace mafarin farko a gare mu ba batun aure ba don Allah ka kyale wannan mgn har Allah ya tashi kafadunka,tayaya prince ze tafi nesa hk alhalin kaima da kanka kana buqatarshi kusa dakai" kau da kansa yyi gefe alamar hkn dai yakeson ayi, kun dai san taurin kai irin na sarki abdallah sam a tsarinshi baya zance biyu, washegari prince akbar tare da rakiyar babban hadiminsa ubaid da kuma wadannan manya baqi da suka zo suka dugumxuma suka nufi masarautar abu ansar, tun kan su isa sarki abu ansar yasan da zuwan prince akbar don hk ya shirya liyafar girma don tarar wannan dan sarki ma'abocin daraja da qarfin izzah,sun qawata wannan masarauta da kayan ado, jan carpet aka shimfida dogo inda takan wannan carpet prince ya taka har ya samu isa cikin fadar sarki abu ansar, yana zaune bisa kujerar mulkinsa fuskarsa da yalwataccen murmushi dakansa ya miqe ya riqo hannayen prince akbar ya zaunar dashi a kujerar da aka tanada domin shi,sarki abu ansar yyiwa prince akbar dayake tamkar surikinsa barka da ziyartar wannnan masarauta, bayan wannan jawabi na sarki abu ansar sai liyafar da aka shiryawa prince akbar ta soma gudana, gimbiya mariyatul qifdiya kuwa tunda ta samu lbrin zuwan prince take ta murna har farin cikin nata ya kasa 6oyuwa, gimbiya khamriyya tayi ruwa tayi maqarbiya wurin kimtsa tilon qanwarta tata sbd ta fahimci mariyatul qifdiya bata da masoyin data mallakawa ruhinta kamar prince akbar, gimbiya mariyatul qifdiya tayi kwalliya na ruwan zinare hannu,wuya har ma da qafa, sanye take cikin wata lafiyayyen jar doguwar riga da mayafinta data yane kanta dashi,riga ce irin wacce yaran sarakai da manyan attajirai ke iya sakawa,gbdy ta zaqu ta gana da masoyinta prince akbar, shi kuwa babban prince ana qare wannan liyafa sarki abu ansar yasa aka kaisa royal louge na wannan masarautar,6angare ne na musamman suka tanada sbd baqi jinin sarauta, wurin yyi kyau sosai don an qawata wurin tun daga farfajiyar 6angaren idanun mutum zasu soma lumewa kan kyakyawan furanni masu mutuqar daukar hnkli tare da kukan tsuntsaye ta ko'ina,babban hadimin sarki abu ansar jamal tare da wasu hadiman suka yiwa prince akbar rakiya zuwa wannan royal louge, ubaid na biye da prince akbar har ya shiga cikin wurin shi kuma ubaid da sauran wadannan hadimai suka tsatstsaya a bakin kofa don tsaronsa, prince na shiga ya samu komai tsaftsaf, zama yyi bakin wani gado na alfarma yyi shiru, 6angaren turakar jira kuwa inda bimbii take lbrin isowar wannan dan sarki ya iso ga suwaibah don hk ta tashi ta shiga inda yan mata suke don za6o mai cikakken dirin halitta da kaifin basirah ta kasance da wannan dan sarki don hidimta masa, yan matan duk suna zazzaune kowacce tayi ado na a kalleta, kallonsu take daya bayan daya, idanunta ne ya sauka kan bimbii, tace" ke tashi na ganki" miqewa bimbii tayi a hnkli ta tsaya suwaibah na qare mata kallo tun daga sama har qasa, kallon buqasassun hips dinta tayi daya fito sosai ga albarkatun fulaninta tsaye qam tamkar danyar budurwa duk da cikin dake cikinta, kowacce a cikin yan matan burinta a za6eta don tarar wannan dan sarki amma sai suwaiba ta nuna bimbii tace" maxa ki biyo baya na" mamaki ne ya cika kowa wurin sbd kowa yasan ba'a tarar jinin sarauta da baiwar da ba virgin ba wato danyar budurwa toh don me shugaba zata za6i bimbii wacce take da yaron ciki,suwaiba kuwa sam bata duba hk ba abunda kawai tayi la'akari dashi shine bimbii tafi dukkaninsu cikar dirin halitta ta cikakkun matan girma burin kowanne da namiji duk da kasancewarta baqar fata kuma mai yaron ciki, kai tsaye dakin gyara ta wuce da ita ta shiryata dakanta cikin wasu sexy dress masu mutuqar janye hnkli ta taje mata gashin kanta ya saukar mata har tsakiyar gadon bayanta sannan ta dauko wata abaya fara sol ta sanya mata ya rufe wannan shiga dake jikinta,gashin idanunta kuwa shima yasha gyara yyi baqi qirin hasken kwayar idanunta kawai ake iya gani ga lips nata yasha pink lipatick sai glowing yake, murmushi suwaiba tayi yadda taga bimbii tayi masifar kyau na gasken gaske, hamshaqiya ramlatu ce ta shigo ta kalli bimbii sai kuma ta kalli suwaibah tace" shugaba wannan wa zata tara hk" murmushi suwaiba tayi tace" zata tari dan sarki prince akbar na gimbiya mariyatul qifdiya ma'abocin cikakkiyar izzah" hamshaqiya ramlatu tayi saurin kallon suwaiba cike da mamaki tace" amma baki gani wannan ba budurwa bace sannan cikin darasin jan hnkli da ake koyar dasu sam bata da fahimta gashi tana dauke da yaron ciki shugaba karki saba doka kinsan cikakkiyar izzah irin ta jinin masarautar burham tayaya zaki tari wannan dan sarkinsu da baiwar daba budurwa ba qarewa ma tana dauke da juna biyu wannan tamkar gangaci ne kk shirin aikatawa" dafata suwaibah tayi tace" sam babu gangaci cikin wannan hikima tawa baki da sani cewa prince akbar shine masoyi kuma miji ga gimbiya mariyatul qifdiya,itace ta umarceni kar na sake na tura virgin din baiwa ga masoyinta" shiru hamshaqiya ramlatu tayi tana tunani, tabbas ba komai ne yasa gimbiya mariyatu tayi hk ba sai tsantsar kishi irin nata bata son suwaiba ta tura danyar budurwa ga prince akbar don tasan idan ma yana da tunanin mace ta debe masa kewa yaga an tura masa baiwa mai yaron ciki tasan babu ta yadda za'ayi ya sauke buqatarsa kan wannan baiwa sbd yana da cikakkiyar izzah bazai ta6a kusantar macen da take a bude ba, kuma dakyar ne be koreta ba, ita kuma gimbiya mariyatu hk take so sbd tana da kishi akansa sosai, lkcin da gimbiya mariyatul qifdiya ta nemi ganin suwaiba ta sanar da ita buqatarta, murmushi suwaibah tayi tace" ranki ya dade kar damu don yanzu hkma ina da wata baiwa cikin yan matana dake dauke da yaron ciki kuma gata bata da wata dabara na janye hnklin namiji ita zan tura masa"wannan batu na suwaibah ba qaramin sanya gimbiya mariyatu qifdiya farin ciki yyi ba har saida ta yiwa suwaiba kyautar zoben gwal,bayan an gama shirya bimbii suka fito suwaiba ta kama hannun bimbii ta sanyata cikin keken doki wasu hadimai hudu suka soma jan keken dokin suka wuce da ita royal louge don tarar wannan dan sarki, suna isa ta sakko daga keken dokin fuskarta rufe da mayafi, babbar baiwar dake kula da wannan 6angare mai suna aslamiyya ita ta miqawa bimbii wani kyakykyawan kwando dan qarami mai dauke da kayan marmari ta nufi hnyr shiga cikin wannan 6angare, masu tsaron dake kula da wurin suka bata hanya cikinsu har da ubaid, sam be ganeta ba domin fuskarta a rufe take da mayafi ya bata hanya ta shige,tfy take a hnkli bawai da niyyar yanga ba ko jan hnkli ba saidai kawai ita daman hk Allah ya mata wannan baiwa, idan tana tfy tamkar tarwada duk wasu ma'adanai na jikinta juyawa suke suna tsole idon masu budadden ido suna musu kwalele,cikin wannan irin salon tfy ta samu shiga wannan louge, tsarin wurin yyi mata kyau sosai, bata bude mayafin data rufe fuskarta dashi ba amma tana ganin komai a hk, prince kuwa yana zaune bisa wata kujera fitowarsa kenan daga wanka don be aminta wata baiwa ta taimaka masa wurin wanka ba koh a gida babbar baiwar kadai keda wannan yancin bare a masarautar daba tashi ba, aslamiyya ita ta fara shiga wurinsa kafin bimbii ta iso ta hada masa ruwan wanka a kwarmin wanka ta sanya sinadaran wanka tana gama wannan aiki ya daga mata hannu alamar ta tafi baya buqatar komai bayan hk, yana daga zaune yaji motsin shigowa amma be waiga ba har ta tako inda yake zaune ta tsaya a bayansa,ta bude fuskarta ta dora kyawawan hannayenta wanda ke sanye da awarwaraye masu kyan gaske ta dora bisa kafadarsa ta soma masa tausa...........
Littafin nan na kudi ne, idan kina da buqatar krtw saiki tura #300 ta wannan acct...0100790419,alhaji shahida nasir,union bank, idan kin tura saiki turo da screenhrt na payment dinki ta whatsapp a wannan layin...07041195806........
Alkalamin Bintuu ne.......
10/10/20, 1:12 AM - Anti qamshi🌷: *DAREN GOMA SHA HUD'U*🪔🪔
Written By Bintuu Seer
34
*My heart is bursting,my heart is beating more and more*......the time I set eyes on you I was totally confused💕💕
A hnkli take masa tausan tamkar tana tausayin jikinsa, yanayin yadda take masa tausan yasa shi lumshe idanunsa yana tuna wacce take masa irin wannan tausan wato bimbii, ji yake tamkar itace ke masa tausan sbd exactly yadda take masa hk wannan baiwar take masa, so yake ya dago da kansa yaga wannan baiwa saidai izzah irin tasu ta jinin sarauta na yawo a jikinsa, daga mata hannu yyi alamar tausan ya isa hk, gabansa ta dawo ta tsaya tare da rissinar dakanta qasa sannan ta dago dakanta ta dauki tuffa daga cikin qaramin kwandon data shiga dashi na kayan marmari ta sanya wata kyakykyawar qaramar wuqa ta yanka tuffan ta sake rissinar dakanta tana miqa masa slice na tuffan,shi kuwa babbar prince yana tozali da fuskarta numfashinsa ya dauke na wasu sakanni kafin ya dawo hnklinsa, zuciyarsa bugawa ta somayi da qarfi tamkar zata fasa kirjinsa ta fito ya qureta da idanu ko qiftawa baya yi cike da tsantsar mamaki, ita kuwa bimbii kanta na sunkuye tana riqe da tuffan da take miqa masa jin shirun yyi yawa ne yasa ta dago dakanta tana kallonshi, kallon daya qureta dashi ne yasa taji gabanta ya fadi, miqewa yyi a hnkli yasa hannunsa ya dago da ha6arta yana kallon cikin qwayar idonta cike da tarin rudani, gani yake tamkar gixo take masa ko kuma mafarki yake, ita kuwa bimbii rawa jikinta ya soma tamkar mazari sbd daman taji tattaunawar shugaba suwaiba da hamshaqiya ramlatu kan zuwanta tarar wannan dan sarki matsayinta na mai yaron ciki sai take gani kamar ganin cikin dake jikinta ne yasa wannan dan sarki yi mata hk, sauke hannunsa yyi yana cigaba da kallonta, gani yyi a tsorace take dashi hkn ya nuna tamkar bata gane shi bane,gabansa ne yaji ya yanke ya fadi, maida kallonsa yyi kan qaramin cikinta daya turo sosai ya jima yana kallon cikin sannab ya dago da jajayen idanunsa da tashi daya suka sauya launi, idanunsa ne suka sake bata tsoro tayi saurin ja da baya, a hnkli ya soma takawa har ya isa inda take tsaye ya matsa jikinta sosai tamkar ze hade jikinsu, ita kuwa bimbii ji take tamkar ta saki fitsari a wando sbd tsabar tsorata da tayi dashi, cikin wata irin murya mai cike da rudani yace" me kk nufi? baki gane ni ba?" mgn ta soma cike da qinqina tamkar me koyon mgn tace" ni...baiwa..c..e, shu..ga..ba ce ta turon gareka" be kuma furta komai ba saida kallonta dayake tun daga sama har qasa, ja yyi da baya ya koma kujerar dayake ya zauna ya kwantar dakansa jikin kujerar ya rufe idanunsa sbd dokawa da zuciyarshi take 2akai,ita kuma tayi saurin qarasowa gabansa ta durqushe qasa bisa guiwowinta, batare daya bude idanunsa ya kalleta ba yace" me sunanki?" cikin sauri ta amsa masa tace" suna na andal" bude idanunsa yyi ya kalleta sosai sai kuma ya rufe saida ya jima sannan ya sake mgn yace" waye da cikin jikinki?" cikin tsantsar rudu ta dago da fuskarta tana kallonshi taga idanunsa na rufe sai ta sunkuya ta kalli cikin dake tare da ita, cikin sanyin murya tace" nima ban sani ba kawai ganin cikin nayi a jikina" cikin sauri ya bude idanunsa yana kallonta yace" me kkce?" shiru tayi bata sake mgn ba don yanayin yadda yyi yasa taji tsoron sake maimaita abunda ta fada, tashi yyi zaune sosai ya zuba mata idanu sai kuma ya miqe abinsa ya qarasa hadadden gadon dake can gefe ya kwanta sannan ya dago ya kalleta yaga tana inda yabarta bata da niyyar tashi yace" hk shugabar ta koyar dake aikinki" saurin tashi tayi ta qaraso wurin gadon ta tsaya batare data hau kan gadon ba, murmushin yaqe yyi wanda a zahiri ji yake tamkar ya rushe da kuka, ga zuciyarsa ta gaza dena bugawa da qarfi kawai dauriyya yake yace" ina buqatar ki sanya ni bacci" shiru tayi sai kuma ta hau gadon cikin sanyin jiki yana ganin tahau yyi matashi da cinyarta ji yake tamkar ya rumgumeta a jikinsa ko bugawar da zuciyarsa keyi ze ragu, saidai kawai ya daure, ita kuwa sakoko tayi tana kallon gashi kansa,ba zato taji.muryarsa yace" idan ina jin bacci sai an bani labarai masu dadi nk bacci,ki bani labarinki sai nayi bacci sbd kin min kama da wata wacce na sani" kallonshi take da mamaki sai kuma ta kalli gyararren sumar kansa dake kwance a saman kafadarsa, ji tayi gbdy ya birgeta, cikin sanyin murya ta soma bashi lbrinta iyakar wanda ta sani har da lbrin gidansu farhan da zaman a gdn maheer har kawo wannan lkci, kwance yake a saman cinyarta idanunsa a sama yana kallonta ya harde hannayensa saman qirjinsa ya qura mata idanu a hnkli yace" kuma baki da buqatar sanin me wannan cikin na jikinki" yasa hannu saman cikin nata yana dannawa a hnkli, shiru tayi sai kuma tace" in Allah yaso wataran zan tuna lbr na" murmushi yyi yace" kiyi qoqarin tunawa sbd qila mai cikin yana jiran abinshi" shiru tayi tana mamakin wannan dan sarki daya sake yake mgn da ita hk kuma ya bada interest nasa yana sauraren lbrinta, cikinsu babu wanda ya sake mgn, shi babban prince duk cikin lbrin data bashi babu wanda ya 6ata masa rai yaji bala'in kishinsa irin maheer, be sanshi ba amma yaji tsanarsa sosai cikin ranshi, lumshe idanusa yyi yana jinsa tamkar wani sabon mutum yau gashi ga rayuwarsa suna numfashi a muhalli guda abu kamar cikin mafarki, ita kuwa bimbii hannunta na cikin sumar kansa tana son sanyashi bacci, tunda ya rufe idanunsa be kuma budewa ba, idanun nasa na rufe ya daga mata hannu alamar ta tafi, ji tayi sam batasan sauka sbd qamshin dake fita daga jikinsa yana mata dadi sosai amma dole ta sauka ta nufi hanyar fita, tana fita yyi saurin tashi zaune yana kallon hanyar data bi, zumbur yyi ya miqe ya soma zirya, bimbii kuwa tana fita ubaid ya bita da kallo,saidai be samu nasarar ganin fuskarta ba amma ya hangi cikin dake jikinta, hknne ya bashi tabbaci dalilin dayasa babban prince ya koreta kenan, wani hadimi ne ya sanar dashi prince na son ganinshi ya shiga da sauri,batare da bata lkci ba prince ya bashi umarnin abunda ze aikata.....
**
6angaren maheer kuwa hauka tuburan ya gwada musu lkcin daya dawo gida ya tarar ba bimbii ba alamunta cikin gdn, a guje ya fito tamkar mahaukaci yahau motarsa yyi gdn ennah, tana zaune tana krt wata jarida taji shigowarsa ya afko ciki kamar an jefo shi kallonta yyi yace" ina kk kaita ina kk kaimin ita?" kallonshi tayi cike da rashin fahimta tace" me kk fada" kallonta yyi a tsorace yace" ban ganta ba ina kk kaita nasa kece kk dauke min ita" miqewa tayi tana kallonsa tace" au taji gargadin da na mata kenan ta nemi hanyarta hkn yyi kyau" kallonta ya tsaya yi yace" ina take?" tace" wannan kai zan tmby" kallonshi tayi kawai sai taga yana hawaye yace" do you want me to live?" kallonshi ta tsaya tanayi cike da mamaki don batayi zaton abun nashi yyi tsananin hk ba tace" what do you mean maheer" wani murmushi yyi ya kuma kallonta batare data ankara ba yyi saurin daukar qaramar wuqar yanka lemo dake gefenta ya soma ja da baya yace" I told you my life is useless without her, do you know how much I suffered when I lost her? a rikice take kallon wuqar dake hannunsa tace" no, maheer dnt do this u are a muslim" murmushi yyi be sake cewa komai ba ya chaka wuqar a qirjinsa, wani irin ihu ta kurma a guje tayi kansa tana kiran sunan shi, shi kuwa sulalewa yyi qasa cikin jini...........
pls manage it pls....
Littafin nan na kudi ne, idan kina da buqatar krtw zaki tura #300 ta wannan acct...0100790419,alhaji shahida nasir, union bank saiki turo da screenshrt na payment naki a whatsapp ta wannan layi...07041195806....
Alkalamin Bintuu ne......
10/10/20, 1:12 AM - Anti qamshi🌷: *DAREN GOMA SHA HUD'U*🪔🪔
Written By Bintuu Seer
35
*To me you are the princess*........you are my queen,you build a perfect kingdom in my heart.....so, you are the star💕💕
Bimbii na komawa turakar jira kuwa yan mata wannan turaka suka soma tuntsira mata dariya don su tunaninsu babban prince ya koreta ne, wata daga cikinsu mai suna veesha tayi saurin miqewa tayi wani irin juyi da rausaya tana karkada jikinta cike da salo, sauran yan mata suka dauki tafi da shewa, murmushi veesha tayi tace" ku duba fa ku gani da mata irinmu wadanda suka kware wurin iya sarrafa jiki da kissar dauke hnkli kowanne taurarren namiji amma wai duk a wuce mu dauki wannan mai tutsetsen cikin,hhhh" zeena tace" kedai yi shiru kawai ai daman sanya idanu nayi naga yadda abun ze kaya, ke kin ga haduwar wannan dan sarkin kuwa, tayaya ne ma ze sauke buqatarsa kan ragowar wani ga danyun yan mata irinmu masu cikakken budurci ga kuma salon hillata" tafawa sukayi suna sheqa dariya ita kuwa bimbii tana zaune gefe tayi tsuru tana kallonsu, ganin suna watsa mata baqar mgn yasa ta miqe ta wuce dakin kwananta,2kwata kasa rintsawa tayi burinta kawai ta sake shaqar qamshin jikin babban prince,miqewa tayi ta soma shinshina jikin kayanta ko ya kama qamshin nasa, hk ta din yi tamkar wacce ta samu aiki, shigowa wasu yan mata biyu da suke kwana daki daya ne yasa tayi saurin komawa ta kwanta amma a zahiri hoton fuskarsa ne yake mata gixo, hannu tasa ta daki kanta dashi tace" na shiga uku me nake yi hk" zuciyarta ta gargadeta kan ita fa qanqantacciyar baiwa ta tsaya matsayinta kar ta sake takai kanta inda Allah be kaita ba, hk dai ta din ga fama tana qoqarin manta fuskarshi dake mata yawo har ta samu bacci ya soma daukarta,washegari, suwaiba taje ta sanar da gimbiya mariyatul qifdiya wannan kyakykyawan lbri hkn yyi mutuqar sanyayawa gimbiya mariyatu zuciya, musamman aka shiryata cikin wasu kayan na alfarma don ganawa da masoyinta rabin rayuwarta, babban prince yana tare da sarki abu ansar a dakin ganawar sirrinsa, sarki abu ansar ya kalli prince akbar yace" tabbas maqiya sunyi amfani da baquwar guba ne wacce take sabuwa qirqira da har yau masana basu gano laqonta wurin cutar da mahaifinka sai zan tura ka ga wani bawan Allah tsohon masani ne kuma bayahude daya jima yana qirqirar gubobi masu tsananin cutarwa ga lfyr bil'adam, yasan sirrin kowacce irin guba, wannan bayahude yana rayuwa ne a wani tsibiri can arewacin spain da ake kira oldest Inland na tabbata wannan bayahude bazai rasa sani game da abunda ze daqusar da wannan guba dake jikin mahaifinka ba" shiru prince akbar yyi sai kuma ya dago ya kalli sarki abu ansar yace" yakai wannan sarki ma'abocin sani tabbas da yarda wannan raina ke hannunsa bazan koma ga mahaifina ba har sai da mgnin matsalarsa" murmushi sarki abu ansar yyi yace" madallah da d'a nagari kuma kyakykyawan jarimi a fagen fama" rissinar dakai prince yyi alamar girmamawa ga sarki abu ansar" hannun prince akbar sarki abu ansar ya riqe suka fito, babbar hadima ga sarauniya ita ta yiwa babban prince jagora har wani babban lambu mai cike da kyawawan furanni da tsuntsaye masu dadin kuka, wata kyawawan kujeru aka tana don zaman shi, bayan fitar ta bada jimawa ya soma jiyo wani sassayyan qamshi mai kwantar da hnkli, daga kansa yyi yana kallon 6angaren da qamshin ke tahowa, gimbiya mariyatul qifdiya ce sanye da wata doguwar riga mai ruwan kwai, tayi ado na awarwaron zinare ga sarqa ga abun wuya, tasha kyau na ban mamaki, kallo daya za'a mata a fahimci diyar girma ce kuma jinin sarauta, tfy take dai dai cike da qasaita da kuma izzah har ta qaraso wurin dayake daya daga cikin hadiman dake take mata baya ta gyara mata zaman kujerar dake gefensa ta zauna, juyawa hadiman sukayi suka fice daga lambun ya rage daga ita sai babban prince, duk sunyi shiru don kowanne cikinsu yana taqama da izzah da kuma qasaita gdn sarautar daya fito, gimbiya khamriyya da kanta ta jaddadawa gimbiya mariyatu akanta 6oye soyayyarta ga prince akbar ta martaba izzar gdn sarautar abu ansar, ta bari shi ya soma sauke izzarsa gareta ya fallasa mata sirrin zuciyarshi, prince sau daya ya kalleta duk da kuwa tsantsar kyawunta irin na larabawan usul,sun jima a hk babu mai niyyar mgn cikinsu, gimbiya mariyatu kam taji ana ambatar cikakken izzah irin na wannan dan sarki amma bata ta6a zaton yakai hk ba, miqewa taga yyi ya soma takunsa mai cike da qasaita ya fice daga wannan lambu yabarta zaune tamkar an dasata, kuka ta fashe dashi tana dana sanin daukar shawarar yayarta kan ta nuna masa cikar izzarta gashi nan ya fita ya barta da izzar nata, shi kuwa prince akbar duk duniya mace daya ce zata iya gwada masa izza tasha kuma ita din ba kowan kowa bace face qasqantacciyar baiwa amma ita Allah ya dora bisa kansa ko durqusawa gabanta ze iya yi sbd ta gama da qarfin izzarsa, hadimansa na ganin fitowarsa suka take masa baya, ubaid na daga hannun damansa, bimbii ta tashi da kasala ranar sai bin jiki take babu abunda takeson ji sai qamshin jikin prince, fitowa tayi tana kwashe shanya tana zubawa cikin wani kwandon saqi, tana shiga 6angarensu ta hango dukkanin yan matan dake turakar jira sun fito farfajiya wurin sunyi jeri tana shigowa duk suka bita da kallo,ramlatul aswat ta gani tare da suwaiba sai kuma wasu qattan bayi, kallonta ramlatul aswat tayi a wulaqance cikin fada tace" ke daman gudandiyar baiwa ce daga gdn yasser bin walid amma har kk shigo wannan masarauta ta abu ansar" wani hadimi dayake cikin hadiman da suka siyo bimbii yace" tabbas bamu san gudaddiyar baiwa bace daga gdn yasser da bamu siyenta" ramlatul aswat ta galla masa harara sannan ta kalli bimbii take sauraronsu don bata gane abunda suke fada ba, turata cikin hadiman gdn yasseer bin walid ramlatul aswat tayi tace" ka baiwarku nan amma ku bawa nana hkr kar wannan zance yakai kunnen sarauniyya" hadiman gdn yasser suka ja bimbii suka fita da ita har suka fice daga masarautar abu ansar da ita, yasser bin walid shararren attajiri ne mai qarfin arziqi da yalwar bayi, sarakuna suna ganin darajarsa sosai sbd qarfin arziqinsa, yasser bin walid abokin kasuwancin prince akbar ne kuma shine ya tura ubaid wurinsa kan ya masa wannan alfarmar batare da bata lkci ba ya aika hadimansa gdn sarautar burham don aiwatar da wannan aiki, yasser ya damqa bimbii ga ubaid sai lkcin ubaid yaga bimbii shi kansa ya cika da mamakin ganinta, kamar yadda prince ya umarci ubaid hk ya aiwatar yasa bimbii cikin wani babban jirgin ruwa mai zuwa spain tare da wata amintacciyar hadima mai suna sumayya da yasser ya hadasu da ita don kula da lfyr bimbii har su isa qasar spain, sumayya mace ce mai mutuqar jarimta tamkar na maxa gata da hikima hk ta din ga kula da bimbii har jirginsu ya isa qasar spain suka wuce masaukinsu, ubaid ya isa ya sanar da babban prince jirginsu bimbii ya tashi zuwa spain, suma da yamma tawaga guda sarki abu ansar yasa suka yi masa rakiya har ya shiga jirgin ruwa tare da ubaid, sauran hadimansa kuwa suka koma ga masarautar burham suka sanar da tfyr babban prince spain don ganawa da tsohon bayahude abram dake oldest Inland, bimbii tunda jirginsu ya tsaya a port na tsayawa jiragen ruwa dake qasar spain ta fito sai kalle kalle take, gani tayi ta dena ganin masu rawani sai turawa nasarar asarar duniya, qasar spain ta mata kyau ko'ina hasken fitilu dayake da dare suka qarasa, sun sauka ne a wani orchard house mai kyau, qaramin gini ne irin na turawa amma ya tsaru sosai, ko'ina ta gefe bishiyoyin fruit ne da shuke shuke, tsarin wurin kawai akwai kwanciyar hnkli, bimbii ranar bacci tayi mai rai da lfy sbd peaceful environment din data samu kanta ciki, cikin kwana uku ubaid da babban prince suka iso qasar spain, suma a wannan orchard house suka sauka sbd tsarin wurin yana yiwa prince dadi idan ya shiga spain a wannan wuri yake rayuwarsa, nesa kadan da wannan orchard house teku ne,bimbii dai kam batasan dalilin zuwanta wannan waje ba ita dai kawai gata nan ne batasan ina rayuwarta ta dosa ba,da dare sumayya ta sanar da ita wanda ya siyeta ya iso yana buqatar takai masa abun sha, ba musu bimbii ta tashi ta hada lemon zaitun da zuma ta zuba a kyakykawan mazubi ta din ga qetare corridor har ta isa bakin dakin da prince yake,ta6a kofar tayi taji ta a bude tayi sallama ta shiga, bedroom ne mai girman gaske, komai na wannan bedroom fari ne da dark blue, everything is so cool, qamshin da take maita ta soma shaqa, prince kuwa yana kwance a tafkeken gadon dake dakin yana duba wani littafi yaji ta turo kofa, ita bata lura dashi ba kawai kallon dakin take sai data waiga wurin da wannan tafkeken gadon yake ta hango shi kwance ya tsareta da idanu,gabanta ne ya yanke ya fadi ta tsira masa idanu cike da tarin mamaki da al'ajabin ganinsa a wannan wuri, shafa idanunta ta somayi tana son tabbatarwa wannan dan sarkin ne kuwa.....
***
6angaren maheer kuwa tuni ennah ta kira faisal suka nufi hospital dashi, hnklinta duk a tashe sbd tana da masifar son yaranta,maheer yyiwa kansa rauni sosai, bayan hk likitoci sun tabbatar musu jininsa yahau dayawa a kowanne irin lkci zuciyarsa zata iya bugawa, ennah kuka take sosai sai lkcin take nadamar dauke masa bimbii da tayi har kasuwar saida bayin data kai bimbii ta koma amma wannan balaraba ya fada mata shi wlh ya saida ita dole hk ta dawo hospital din da maheer ke kwance cike da tarin dana sani, zama tayi ta tsura masa idanu, shi kuwa yana kwance duk an sanya masa oxygen a hanci da bakinsa, numfashinsa na fita a hnkli, tunani take wai wanne irin so kuwa maheer yake yiwa wannan baiwa hk, she can't imagine this kind of sacrifices until she witnessed it on her son......
Littafin nan na kudi ne, idan kina da buqatar krtw saiki tura #300 ta wannan acct..0100790419,alhaji shahida nasir,union bank, saiki turo da screenshrt na payment nk ta whatsapp ta wannan layi..07041195806.....
Alkalamin Bintuu ne.....
10/10/20, 1:12 AM - Anti qamshi🌷: *DAREN GOMA SHA HUD'U*🪔🪔
Written By Bintuu Seer
36
*I LOVE YOU*💕💕I MISS YOU💕💕
Duk abunda take idonsa na kanta yana qare mata kallo, dauke kansa yyi daga kallonta ya cigaba da karanta littafin dake hannunsa, hknne itama ya bata damar takawa a hnkli ta qarasa wurin qaramin stool din dake gefen gadon dayake kwance ta ajiye farantin hannunta ta dauki cup ta soma tsiyaya masa drink, daukan cup din tayi ta matsa daidai wurin dayake kwance ta rissinar dakanta qasa tare da miqa masa cup din dake hannunta, daga idanunsa yyi kawai yana kallonta, tashi yyi zaune ya ajiye littafin dake hannunsa ya amshi cup din dake hannunta ya soma sipping drink na zaitun din, miqa mata cup din yyi ta mayar dashi kan faranti ta ajiye sai kuma ta dauki farantin da niyyar ficewa dashi don ta soma gjy da wannan kallon qurallah da wannan dan sarki ke binta dashi, rissinar dakanta tayi alamun girmamawa sannan ta juya da niyyar fita saidai taku daya zuwa biyu tayi taji charaff an damqe mata hannu, kafin ta dawo cikin tunaninta ya rumgumeta ta baya hannunsa nakan qugunta ya dora kansa akan dokin wuyanta yana sauke numfashi a hnkli, ita kuwa bimbii mutuwar tsaye tayi zuciyarta na wani irin tsere da mugun speed, saukar numfashinsa kawai take iya ji, jikinta sai rawa yake kamar mazari, shi kansa yaji rawar da jikinta yake yi, murmushi yyi ya janye hannunsa daga qugunta ya juyo da ita suna fuskantar juna, tsirawa juna ido sukayi, bece mata uffan ba amma tana iya karantar saqonsa da cikin kwayar idonsa, zallar madarar sonta kawai take hange cikin kwayar idonsa shi kuwa babu abunda yake gani cikin idonta sai tarin tsoro da rudu, hannunsa yakai wurin idanunta yyi kamar ze tsole mata idanu tayi saurin blinking eyes nata, janye jikinta ta soma qoqarin yi amma ta kasa don namijin gaske ne yake riqe da ita, raurau tayi da idanunta da niyyar fashe masa da kuka, rufe idanunsa yyi don baya son ganin hawayenta kuma baida niyyar fasa abunda yyi niyya, matsar da fuskarsa yyi sosai ya hade da nata ya dora dogon hancinsa kan nata, bimbii kuwa qirjinta kamar ze faso sbd tsoro, bata gama sallamawa da lamarinsa ba saida taji ya hade bakinsu wuri guda,numfashinta ne ya soma fizga shi kuwa gently yake kissing nata dukkaninsu idanunsa a lumshe kowanne cikinsu zuciyarsa na bugawa da qarfi, a hnkli ya tsare bakinsa daga cikin nata amma be dauke fuskarsa dake manne da nata ba kuma be bude idanunsa ba, itama idanunta na rufe, saida suka jima a hk sannan ya janyota ta fada qirjinsa yasa hannunsa around her, kuka take masa, idanunsa shima sunyi jajir he wish to be with her this night but he can't until she gain her memory back, bimbii tana kuka tana qara manna fuskarta a qirjinsa tana shaqar qamshinsa sbd abunda take so kenan, ya jima yana rumgume da ita yana shinshinar qamshin da gashinta ke fitarwa yana tunanin abunda ze iya raba shi da ita, mahaifinsa ne ya shigo cikin tunaninsa take yaji gabansa ya yake ya fadi, idan har ya rasa bimbii baya jin rayuwarsa zata dore sbd kowanne sashi na jikinsa qaunarta ne hatta jinin dake circulating a cikin jikinsa, sonta shine bugawar zuciyarsa, hannunsa yasa ya dago da fuskarta data jiqe da ruwan hawaye ya tsura mata idanu, qasa tayi da kanta don kallon nasa na sanya mata mutuwar jiki, hannu yasa a aljihu ya fito da wani farin handkchiep nasa yasa hannu ya dago da ha6arta ya soma goge mata hawayen da yyi spoiling beautiful face dinta, gani tayi ya durgusa a gabanta ya dora kansa kan cikin dake jikinta yana jin motsin abunda dake cikin, hannu tasa ta tureshi yyi saurin miqewa yyi yana murmushi ya kanne mata ido daya tare da dage mata kafada kamar wani qaramin yaro, komawa yyi ya kwanta abinsa ya daga mata hannu alamar ya sallameta, kamar jira take tayi hanyar kofa da sauri kamar zata ci tuntu6e ta murda handle na kofar ta fice, murmushi yyi kawai daya ga ta fita ya lumshe idanunsa, ita kuwa bimbii tana fita tasa gudu ta qarasa dakin da take tana sauke numfashi tare da kallon kofa tamkar wacce tayi gamo, sumayya dake bayanta riqe da cup na black tea tace" mene ya tsorataki hk na ganki duk a rikice" inda inda ta somayi kamar wata munafika don gani take kamar sumayya tasan abunda ya faru da ita, sumayya na ganin hk ta wuce tare da basar da tmbyr data mata, zuma ta sanya a black tea din dake cikin cup din hannunta ta miqa mata, amsar cup din tayi tana shan tea din a hnkli har ta shanye, bathroom ta shiga tayi wanka da warm water sannan ta fito ta sanya wasu kayan bacci masu taushi tabi lfyr gado, mood nasu na dazu kawai take tunawa ya kasa 6ace mata a cikin brain nata, hannunta tasa ta shafa lips dinta daya sha kissing, yanayinsa take tunawa da cool love nasa mai tsayawa a rai, mafi yawan soyayyarsa a kwayar idonsa take be cika yawan mgn ba, murmushi ne ya su6uce mata ta rufe fuskarta da small pillow din dake gefenta, da wannan tunanin bacci 6arawo yyi gaba da ita, washegari, bata samu ganin prince ba sbd da sassafe suka fice shi da ubaid suka nufi oldest Inland, cikin nasara suka gane inda wannan tsohon bayahude yake, abram yana rayuwa ne shi daya a wani gdn katako, suna tsayawa da mota ubaid yyi saurin budewa babban prince kofar mota ya fito, hk suka taka suka qarasa wannan gdn katakon, ubaid yasa hannu ya buga kofar katakon a hnkli, saida aka dauki time abram ya bude kofar ya tsaya yana kallonsu, tsoho ne sosai, gashin gemunsa dogo kuma fari sol, sanye yake da wata hula iyakarta tsakiyar kansa irin wacce jews ke sanyawa, kansa duk saiqo, kallonsu yake da mamaki kuma yaqi basu hanya su shiga ciki yace" arab men to my house, what's are you up to...?" ubaid yace" this is not abram house" they are speaking with pure british english, yana ji sun ambaci sunan shi ya basu hanya suka shiga ciki, ko'ina cikin gdn kwalabe ne dauke da chemical samples, ta gefe guda kuma shelter ne na manya tsoffi littattafan manya scientists da suka shude, yanayin tsarin gdn kawai ya tabbatar musu gd ne na masana kimiyya da binciken qurulla, coffee ya kawo musu yana turiri suka soma sipping sannan prince ya soma masa bayanin abunda ya kawosu gare shi, shiru yyi na wasu daqiqai sai kuma yace" ina son ganin mahaifin nk don na duba yanayin gubar dake circulating a jikinsa" gdy sosai babban prince yyi masa bai ta6a tsammanin wannan bayahude zeyi saurin amincewa dasu ba cox most of jews basu da trust ga larabawa.......
Pls don Allah kuyi manage da wannan page din, bani jin dadi ne naso yau nayi muku dogo typing amma jiki da jini sai gdyr Allah.....
10/10/20, 1:12 AM - Anti qamshi🌷: *DAREN GOMA SHA HUD'U*🪔🪔
Written By Bintuu Seer
37
*Your love is a special chemistry and also the most concentrated pure love to my heart*.......I love everything about you💕💕
Sun shirya komawa masarautar burham da abram don ya duba sarki abdallah bin jabal dakansa ya fahimci irin gubar dake jikinsa,6angaren bimbii kuwa tana zaune ita da sumayya suna hira taji mararta tayi wani irin murdewa, skipping tayi ta runtse idanunta tare da riqe mararta, cikin sauri sumayya ta matso kusa da ita ta riqeta tana mata sannu, abu kamar wasa ciwo ya soma cigaba, fita sumayya tayi da hanzari ta nufi wurin ubaid ta sanar dashi abunda yake faruwa, shiga yyi ya sanar da prince, cikin hanzari ya fito suka nufi dakin da bimbii take, ubaid ya tsaya a bakin kofa,prince da sumayya suka shiga ciki, saurin qarasawa yyi inda take durqushe riqe da mararta ya tsuguna ya riqo hannunta, sumayya na gefenta itama, kallon prince tayi tace" kamar haihuwa ce ta matso mata" saurin dago da kansa yyi yana kallon sumayya bece komai ba yyi saurin miqewa tsaye ya fita, ubaid yyiwa mgn sannan ya dawo ciki, gbdy gumi sai tsatstsafo masa yake tamkar shine yake labour din, a telephone ubaid ya kira gdn sarautan even kan suna buqatar royal doctor, bada jimawa ba even house suka turo musu da wata likita, baturiya ce ta shigo itama atleast bazata gaza shekaru hamsin ba, shigowa tayi da gudu da qaramin briefcase a hannunta, ubaid na ganin shigowarta yyi mata jagora har dakin da bimbii take ta shiga, prince na ganinta yyi saurin miqewa ya bata wuri, bude briefcase dinta tayi ta fito da handgloves ta saka cikin azama take gudanar da abubuwa, sumayya na taimaka mata prince kuwa, kasa cigaba yyi da kallon yadda bimbii ke shan azabar naquda yyi saurin ficewa daga dakin,ita kuwa bimbii wani irin ninshi take sbd ciwon da takeji bata ta6a jin irinsa ba tunda uwata ta haife sai yau, bayan ciwon naquda ga kuma wani azababben ciwon kai tamkar kanta ze rabe biyu,ita dai gbdy ta sadaqar da rayuwa sbd ta soma jiyo qamshin lahira,Dr.Margaret pushing nata take sosai, itama tana numfasawa da qarfi, prince yana bakin kofa ya harde hannayensa dukka a baya yana jiyo sautin ninshinta, idanunsa ya kada yyi ja shi kadai yasan me yakeji but still he looks very smart, cikin izinin Allah sai ga kan jariri ya fito, hannun doctorn tasa ta ciro jaririn ta miqawa sumayya dake gefe, jaririn kuwa ya charke musu da kuka, prince da ubaid kukan jaririn kawai suka jiyo,murmushi ubaid shi kuwa prince kawai so yake yaji yaya lfyr uwar jaririn, yana son shiga dakin amma yana daurewa, bimbii kuwa tasha wuya ba kadan ba gashi kanta be dena ciwo ba, hknne yasa doctorn tayi mata allurar bacci sbd ta huta, sumayya ce ta fita cike da farin ciki ta yiwa babban prince albishir bimbii ta sauka ta samu yaro namiji, sai lkcin ya shiga dakin wurin gadon da take kwance ya nufa yana kallonta tana bacci, kallo daya ya yiwa fuskarta yasan ta jigata ba kadan ba, doctorn da kanta ta dauki jaririn ta miqa masa tana murmushi, hannu yasa ya amshi jaririn ya tsira masa idanu, yaron fari ne qal gashi dogo masha'Allah, yanayin ga6o6in jaririn ya kalla yasan komai nasa ne, murmushi yyi sosai har fararen haqoransa suka bayyana, bimbii baccinta yyi tsayi sosai har kusan yamma bata farka ba, hkn ne ya tashi hnklin prince ita kuma doctorn sai kwantar masa da hnkli take sai dare ta tashi a razane, tana kallon inda take, fuskar da bazata ta6a mancewa da ita bane ta gani kusa da ita, kallonshi take sosai shima ya qura mata idanu, fashewa tayi da kuka ta dora kanta saman kafadan shi, kallonta yake cike da mamaki, ita kuwa all that past events da suka faru take tunawa ta sake dago da fuskarta tasa hannunta tana shafa face dinshi sannan ta sakko da hannunta daidai wurin da mahaifinsa ya harbe shi da mashi, hannunta ya riqe dukka ya janyota jikinsa ya kwantar da ita tana kuka a hnkli, yace" ki dena kuka baki ganin yanzu kin zama ummi" ya nuna mata babyn dake kwance a gefenta, saurin janye jikinta tayi ta komar dakanta ta kwanta ta rufe idanunta tana son tuna komai da komai ne, prince matsawa yyi kusa da ita yaja duvet ya rufeta, sunkuyawa yyi ya mata peck a kumatu, shiru tayi bata bude idanunta har saida taga ya fita daga dakin ta bude idanunta tana kallon babyn data haifa tana qura masa idanu,kuka take sosai tana tausayawa rayuwarta, tunani take yanzu idan qaddara ta kuma daukarta ta mayar da ita nahiyarta me zata fadawa su baffa da innah, tayi ciki har ta haife kenan bada igiyar aure ba, sosai ta kuma fashewa da kuka, sumayya ce ta shigo dakin ta ganta tana kuka tayi saurin qarasawa wurinta ta zauna kusa da ita tana rarrashinta da kalmomi masu kwantar da zuciya, prince komawa yyi side dinsa ya zauna ya dafe kansa, babban tashin hnklinsa mahaifinsa ne ya rasa ina ze dosa da wannan rayuwar, zuciyarsa fal take da tsantsar tausayin bimbii da babynsa dake tare da ita, har gobe yasan shine silar faruwar komai, tashi yyi da sauri ya koma dakin da bimbii take ya tarar da ita zaune fuskar nan nata babu alamar annuri, hannunsa yasa da niyyar kama mata hannu tayi saurin matsawa gefe ta dago da fuskarta tana kallonshi tace" kaga na haife muku jininku dake tare dani don Allah ku mai dani nahiyata na koma wurin iyayena na gaji da wannan rayuwar mara madafa" durqusawa tayi a gabansa ta daga hannunta alamar roqo tana kuka tace" don Allah ku maida ni nahiyata kar ka komar dani wannan masarautar na mahaifinka" shiru yyi komai ya daqule masa ya kalleta da jajayen idanunsa yace" kina son ki tafi ki barni kenan baki da damuwa, duk tsawon wannan lkcin dana dauka ina jiranki ki dawo gare ni kk dawo batare da kin iya shaida fuskata ba hk na kuma hkr har memory nk ya dawo kk gane ni amma abunda zaki iya fadamin kenan sbd baki dauki soyayyar da nk miki da daraja ba" kallonshi tayi tace" ranka ya dade ba wannan zaka duba ba, wannan son da kk fada tun farko na fada mk ze haifar da mtsl gashi silarta ne har rayuwarka ta shiga garari, mahaifinka dakansa ya harbeka da mashi duk silar wannan soyayya da kk fada don Allah kayi hkr ka taimake ni na koma qasata" wata uwar tsawa ya daka mata wacce ta sanyata shiga taitayinta, ubaid da sumayya dake waje su kansu sun razana da wannan tsawar da prince yyiwa bimbii, yace" kiyi yadda kkso" juyawa yyi ya fice ransa a 6ace sosai, bimbii fashewa tayi da kuka ita dai ta gaji da wannan rayuwar qasarta take son komawa don muguntar larabawan nan ya tsorata ta dayawa, basu dauki kisa a bakin komai ba, laifi qanqani sai su kashe rai batare da shakku ba, fushi sosai prince yyi da ita kusan kwana uku be sake shigowa inda take ba saidai sumayya ta dauki babyn takai masa duk safiyya da maraici, idan ya tuna abunda take fada wai ya maidata qasarta sai gabansa ya yanke ya fadi, tunani yake kar fa ya wayi gari ya rasa bimbii ta gudu tabar shi da dakon sonta, shi gani yake kamar bimbii ba sonshi take ba shine kawai Allah ya jarabta da soyayyarta, qanqame babyn dake hannunsa yyi yana kallonshi, idanunsa yyi ja tausayin kansa yake sosai, rana zafi inuwa quna, ta 6angaren mahaifinsa babu sassauci gata itama tana son ta gudu tabar shi, bimbii kam sai duk taji babu dadi fushin dayake da ita, tana zaune sumayya ta shigo ta sameta, kallonta tayi tace" kije ki bawa prince hkr sbd ranshi ya 6aci sosai dake tana mugun kafiya da zuciya bazai ta6a kallonki ba kar ki bari ya juya miki baya kece kadai macen da Allah ya dora akanshi" shiru tayi kawai tana sauraron sumayya, sai kuma tace"tohm" sumayya tace" ki same shi da dare a bakin teku nan yake zuwa duk dare" kallonta bimbii tayi tace" shikenan"da dare ubaid dakansa yyi mata rakiya har wajen teku, garin da hasken farin wata sosai, tunkan ta qarasa ta hango inuwarsa yana tsaye hannunsa dukka a baya ya qurawa ruwan teku ido, alamu sun nuna tunani yake mai zurfi, a hnkli ta qarasa inda yake ta tsaya a bayansa, shima ya hangi inuwarta kawai juyowa ne beyi ya kalleta ba, ita kuwa shiru tayi ta rasa abun fada, ta jima tana tsaye a wurin, juyowa yyi ya wuce ta da niyyar komawa gd, tana ganin hk tayi saurin qarasa kusa dashi ta sanya hannunta cikin nashi, tsayawa yyi chak ya juyo yana kallonta, cire hannunsa yyi daga cikin nata yyi gaba abinsa, da gudu ta kuma binsa ta rumgumesa ta baya ta qanqamesa da dukka hannayensa tana masa kuka tana bashi hkr, shiru yyi sannan ya juyo ya riqeta sosai a jikinsa duk sukayi shiru,hannunsu ta sarqe dana juna suka soma tfy a hnkli kanta na kafadarsa hannunsu na sarqe har suka qarasa bakin teku suka nemi rairayin suka zauna suna kallon ruwan teku, shiru sukayi saidai zuciyoyinsu na amsar saqonnin juna, muryarsa a hnkli cike da sanyi yace" har yanzu kina son ki tafi ki barni koh?" yanayin yadda yyi mgnr ta fahimci akwai rauni tattare da muryar nasa, dago da idanunta tayi tana kallonshi, daga hannunta tayi ta cusa a gashin kansa tana wargaza masa sumar kanshi, shikam binta kawai yake da kallo, cikin sanyin murya tace" bazan barka ba komai wuya zan kasance tare dakai" tsayar da idanunsa yyi kan fuskarta sai kuma yyi murmushi, nuna mata bakinsa yyi yace" kimin abunda zan so anan" sosai ta gane abunda yake nufi tayi saurin rufe ido ta 6oye fuskarta a saman shoulder dinsa cike da kunya irin nasu na fulani, shi kuwa dariya ta bashi yadan murmusa yace" kina son akbar?" sosai tmbyr tasa ta qara bata kunya, ta6e baki yyi kafin ta ankara sai ji tayi ta kwantar da ita a wurin rairayin shima ya kwanta ya dora kansa a saman qirjinta, dukka kansu na sama suna kallon hasken farin wata da taurarin dake watse a sararin samaniyya,hannunta ya kamo ya hade da nashi, ita kuma tana wasa da sajen fuskarsa da dayan hannunta, wannan yanayin da suke ciki ya kore musu duk wata damuwa ji suke tamkar su kadai ne a duniyar, tmbyrsa take abubuwan da suka faru dashi duk ya fada mata amma sai ya 6oye mata sanya shi a kurku da mahaifinsa yyi gudun kar ya qara mata karayar zucci, har dare ya shiga sosai basu sani ba suna nan kwance wurin, hadarin da suka gani ne yasa suka miqe suka soma tfy suna manne da juna suka nufi orchard house din da suke, kafin su isa ruwa ya tsuge sosai, hnklin prince ya tashi sosai sbd gani yyi bimbii ba wani kwarin jiki ne da ita ba ga danyen jego kar ruwan saman ya sanya mata zazza6i, itama dan qaramin hannunta ta daga wai zata kare masa ruwa amma tsayinta ya gaza kaiwa saman kansa sai dage take, dariya yyi, kallonsu tayi don ita wallah bata saba ganinsa yana dariya ba saidai murmushi,rawanin dake kafadarsa ya cire ya rufa mata amma duk da hk saida ruwa ya jiqasu, tfy suke kamar masu tausayin qasa a hk suka qarasa, dakyar ta iya kwace hannunta a cikin nashi ta shige dakin da take shima ya nufi dakin dayake, washegari, sun tashi ne da shirin komawa gd, bimbii dai gabanta faduwa yake idan taji an ambaci sunan masarautar burham, dukkaninsu suka shiga cikin jirgin ruwa tare da abram, bimbii fuskarta a rufe take kuma batare suke da prince ba tamkar ba tfyrsu daya ba sbd tsaro, sumayya tana rumgume da baby dayake cikin yalwatattun kayan sanyi, abram yana zaune kusa da ubaid, tmbyrshi yyi alaqarsu dasu bimbii, batare shakku ba ubaid ya soma bawa abram lbrin soyayyar dake tsakanin bimbii da prince mai cike da sarqaqiya da tarin qalubale, sosai wannan tsohon bayahude ya tausaya don lbrin nasu ya ta6a masa zuciya,hk har suka qarasa yankin masarautar burham, tunkan jirginsu ya iso dakarun masarautar burham suka iso don tararshi, lkcin da jirginsu ya iso fasinjojin jirgin suka soma fitowa, kamar yadda prince ya shirya tuni sumayya ta wuce da bimbii ta wani 6angare daban babu wanda zeyi tunanin tare suke da prince, bimbii fuskarta na rufe cikin niqab, sumayya tana da wayo shiyasa yaseer ya hadosu da ita, yadda prince ya umarceta ta wuce da bimbii qasarban wani asirtaccen gd ne da babban prince ke zuwa shan iska yana nesa ne sosai da masarautar burham,bimbii cike take da tunani kar wannan sarki mara imani ya ganota cikin yankinsa ya turo a kasheta ita da jaririnta,tuni tsoro da fargaba suka mata dirar mikiya...
Littafin nan na kudi ne, idan kina da buqatar krtw zaki tura #300 ta wannan acct..0100790419,alhaji shahida nasir,union bank, saiki tura screenshrt na payment ta whatsapp a wannan layin..07041195806...
Alkalamin Bintuu ne.....
10/10/20, 1:12 AM - Anti qamshi🌷: *DAREN GOMA SHA HUD'U*🪔🪔
Written By Bintuu Seer
38
*I want to be with you even beyond for ever*......you are my destiny💕💕
Sun isa masarautar burham inda kai tsaye wasu hadimai suka wuce da abram inda akayi masa masauki,prince kuwa wucewa yyi 6angaren mahaifinsa ya same shi yadda dai yabar shi, sarauniyya na zaune gefensa, sarki abdallah yana daga kwance idanunsa na kallon prince akbar, tabbas prince yana cike da tausayin mahaifinsa bisa halin dayake ciki, baya iya mgn har yanzu kawai saidai yana bin komai da idanu tamkar ba sarki abdallah bin jabal ma'abocin cikar izzah da qarfin mulki ba, prince ya labarta masa yadda abubuwa suka kasance tsakaninsa da sarki abu ansar da kuma haduwarsa da abram, batare daya iya cewa komai ba sai kawai murmushi daya bayyana a saman fuskarsa, hkn ya nuna yaji dadin bayanin da prince yyi masa, sarauniya ta kalli prince tace" tashi kaje ka huta don kana buqatar hutu" miqewa yyi ya rissinar dakansa alamar girmamawa sannan ya juya ya fice daga turakar mahaifin nasa, 6angarensa ya wuce ubaid na take masa baya, suna shiga suka tadda bayin dake 6angaren sun jeru sunyi layi don tarbar babban prince, suna ganin shigowarsu duk suka rissinar dakansu har ya shigesu ya wuce 6angarensa, ubaid ne ya dawo ya tsaya a saman corridorn dake 6angaren ya sanar dasu babban prince ya dawo lfy kuma yana kowa fatan alheri sannan ya umarcesu kowa ya koma bakin aikinsa,yana zaune sanye da wata farar riga ta shiga wanka lenah ta shigo, sanye take da wata doguwar jar riga, hannunta yasha tsiraran awarwaro ya cika mata hannu,bisa al'adarta qafarta daure da sarqar qafa, qarasowa tayi inda yake ta tsaye tare da rissinar dakanta qasa alamar girmamawa sannan ta dago dakanta ta wuce da sauri ta shige dakin wanka ta hada masa ruwan wanka mai dumi a cikin kwarmin wanka tasa sinadaran wanka sannan ta fito ta sake rissinar dakanta qasa tayi gefe ta tsaya, wuce ta yyi ya shige dakin wankan, washegari, tun safe abram da prince suka bayyana a turakar sarki abdallah bin jabal, abram kallon sarki abdallah kawai yyi yaga yanayin yadda jikin nasa yyi, dago idanu yyi ya kalli sarauniya mar'atussaliha dake tsaye gefe yace" ina buqatar ku bani lkcin nan da kwana uku nayi bincike akan gubar" tace" an baka amma ka tabbata kayi bincike maikyau don mu nan bamu son kuskure" sunkuyar dakansa yyi alamar girmamawa ga wannan sarauniya sannan ya fita, sarauniya ta kalli babban prince tace" kana ganin akwai alamun nasara tattare da wannan bayahude, kasan fa mutane abun tsoro ne bani yarda da kowa ya duba mahaifinka sai cikakken amitacce sbd muna da maqiya dayawa masu neman ganin bayan wannan masarauta" murmushi babban prince yyi yace" ranka ya dade wannan bayahude baida wani niyya mara kyau ki duba kwayar idanunsa zaki tabbatar da hkn" murmushi tayi ta shafa kansa cike da qauna tace" madallah da wannan jarumin d'a nawa mai tsananin kaifin basira tabbas ina alfahari dakai" murmushi shima yyi ya miqe tare da rissinar dakansa ya fice, komawa yyi 6angarensa yana son ziyartar qasarban don duba lfyr bimbii da gudan jininsa saidai yana shakkar hkn don ko qaqa baya son wani ya gano bimbii na raye har ta haife cikin dake jikinta sbd tsaro, ubaid ya buqaci gani ya shigo da sauri ya iso wurinsa tare da rissinar dakansa qasa yana sauraron umarni,kallonsa babban prince yyi yace" meye tunaninka da ziyarar da nkson kaiwa qasarban" shiru ubaid yyi yana tunani sannan ya dago dakansa yace" yakai ma'abocin hikima tabbas har yanzu duk wani motsinmu akan idanun masarauta yake kuma ko yaya ka fita ziyartar wani wuri a yanzu zasu iya tunanin wani abu wanda hkn zesa su sanya masu binciken sirri su soma gudanar da bincike" jinjina kai yyi alamar gamsuwa, ubaid yace" duk wani kulawa tana samu ita da gudan jinin burham dake tare da ita, kuma nasa cikakken tsaro daya dace" kallonsa prince yyi yace" madallah da wannan amintaccen hadimi" rissinar dakai ubaid yyi saida prince ya daga masa hannu ya ja da baya sannan ya juya ya fice, jinginar dakansa yyi a kujerar dayake zaune yana tunanin qalubalen dazai fuskanta zuwa gaba kan wannan batu don masarautar burham na da tsauri sosai bisa jagoranci mahaifinsa sarki abdallah bin jabal, yana daga cikin tsaurin wannan masarauta basu amfani da maganin bature komai a gargajiyance suke yinsa suna kan al'adun iyaye da kakanni wato larabawan farko, bimbii tana qarqashin kulawar sumayya tana bata cikakken kulawar data dace, gudan jinin burham kuwa yana cike da kuzari sam be dauko bimbii a komai ba yyi gadon larabawa ne, yau suna kwance cikin dare yaro ya soma kuka sosai yaqi yin shiru, daukansa bimbii tayi tana ta jijjigashi ko zeyi shiru amma yaqi yin shiru kuma yaqi karbar nono yasha, kukan shi sumayya taji tayi hanzarin shigowa dakin a rikice tana tmbyr bimbii abunda ya same shi, bimbii tace" nima gani nayi ya fara kuka yaqi yin shiru" hannu tasa ta amshi jaririn tana kallonshi, jikinsa taji yyi zafi alamun sun nuna zazzafi ne a jikinsa, ruwan dumi ta hada ta sanya shi ciki sannan ta bashi mgnin zazzafi, saida ta jima dashi cikin ruwan dumi sannan ta fito dashi ta goge shi ta sanya masa kaya masu taushi,hkn data masa yasa ya tsagaita da kukan har bacci yyi gaba dashi, washegari, kwana ukun da abram ya diba ya cika, sai yamma abram ya iso akayi masa iso ga sarauniya ita kuma ta wuce dashi turakar da sarki abdallah ke kwance, anan suka tarar da babban prince yana tare da mahaifinsa suna sauraron qarasowar abram, batare da 6ata lkci ba abram ya fito da wasu tsinkaye masu kaifin gske ya ajiye gefe, tare da wani farin ruwa, dago dakan sarki abdallah yyi ya bashi wannan ruwan dake cikin wani gora yasha sosai sannan ya sanya wannan tsinken daya a bakinsa ya fito masa da wani abu kamar dan wuya ya ajiye a cikin wani qoqo hk ya cigaba dayi har ya gama, wata qaramar kwalbar ya fito da ita da wani ruwan magani a ciki ya sake bashi yasha sannan ya goga masa wani mai mai kyalli a dukka sasssan jikinsa, prince da sarauniya kuwa suna daga gefe suna kallon abunda wannan bayahude yake, miqewa yyi ya kalli sarauniya tare da rissinar dakansa qasa yace" ranki ya dade na gama sai mu saurara mu ga yadda jikin nasa ze amshi mgnin, gubar dake jikinsa baquwar guba ce wacce ta fito daga nahiya mai nisa wato nahiyar baqar fata, nayi nasarar gano antidote dinta ne sbd na ta6a krt yanayin wannan guba, idan har jikin nasa yyi maraba da wannan antidote toh daga gobe alamar hkn ze soma bayyana" murmushi sarauniya tayi tace" idan har nasara ta tabbata lfyrsa ta dawo kana da kyakykyawar kyauta ta musamman idan kuma muka ga akasin nasarar tabbas fushi na ze tabbata akan ka" murmushi abram yyi ya sake rissinar dakai sannan yaja da baya ya fice,dukkanin wanda ke wannan masarauta kawai tsumaye yake yaji ya lfyr sarki abdallah bin jabal har tsawon kwana daya da yini jikin sarki abdallah be nuna wata alamar na sauyi ba, cikin izinin ubangiji a washegari sai gashi ya soma miqewa zaune dakansa, wannan cigaban da aka samu a lfyr sarki ba qaramin farin ciki yasanya sarauniyya ba, saidai sarki abdallah da batun auren babban prince da gimbiya qifdiya ya bude baki,hkn yasa prince yyi shiru, cikin kwanaki uku jikin sarki abdallah ya warware ya dawo yadda yake tun farko, sarki abdallah bin jabal yyi farin ciki da wannan lfy daya samu tuni yasa aka kira masa wannan bayahude wato abram har fadarsa, abram na shiga wannan fada ta sarki abdallah bin jabal da aka ginata da danyen gwal ya zube gaban sarki yyi gaisuwa, murmushi sarki abdallah yyi yace" yakai wannan masani ma'abocin kimiyya da tarin sani tabbas nayi farin ciki da wannan ingantaccen magani nk don hk ka fadamin buqatarka gareni kowacce iri ce nayi maka alqawarin cika maka ita batare da wani 6ata lkci ba,zan faranta ranka kamar yadda ka faranta min" fadar sarki abdallah tayi shiru kowa na sauraron jawabin dake fita daga bakin sarki kuma suna sauraron suji buqatar wannan bayahude ga sarki abdallah, prince na tsaye gefen mahaifinsa shima yana sauraro, abram dago dakansa yyi ya kalli sarki abdallah sosai yace" yakai wannan sarki ma'abocin qarfin mulki da magana daya ina da buqata mai qarfi a gareka duk da ina da cikakken sani kan halayyarka ta cika alqawari da tsayawa kan mgn daya amma duk da hkn ina da shakka bansan ko zaka iya cikamin wannan buqata tawa ba don tana da qarfi" wannan zance na abram ya sanyawa kowa tunani shin wanne bayahude kuwa wacce buqata ce dashi hk dayake wannan batu, jikin sarki abdallah yyi sanyi da jin wannan batu na abram don shi tunaninsa wannan bayahude buqatarsa bata wuce dukiya, shi kuwa dukiya kowacce iri yakeso ze iya mallaka mishi batare da yasan yyi wani abu ba don yana da qarfin arziqi, prince shima a nashi 6angare mamakin abram yake yana tmbyr kansa shin wanne bayahude wacce buqata yake da ita a wannan masarauta tasu da har yake fadin tana da qarfi, kallonsa sarki abdallah yyi yace" ka fadi buqatar taka naji kai tsaye" shiru abram yyi yana shakkar fadin wannan buqata tashi kar wannan sarki yasa a masa kisan gilla, daka masa tsawa uxair yyi yace" yakai wannan bayahude ba'a yiwa sarki shiru ka hanxarta fadar buqatarka don sarkinmu ma'abocin alqawari ne da mgn daya kowa ya shaida" ajiyar zuciya abram yyi ya numfasa sosai sannan ya dago dakansa ya kalli sarki abdallah bin jabal dake hakimce a wata kujera ta alfarma mai ruwan zinare yasha alkyabba baqa da rawani mai baqi da fari, duk da sarki abdallah ya cika masa idanu amma hkn ya bude yace" yakai wannan sarki buqatar da nk nema gare ka itace ka yarje auren prince akbar da tsohuwar baiwarsa daka yankewa hukunci kisa sannan kayi aikin gafara a garesu tare da sanya musu albarka su da gudan jininka da yanzu hk wannan baiwa ta zama silar zuwansa duniya".....fadar yanayin rudani da daya bayyana a fuskokin al'ummar dake wannan fada yafi gaban kwatance, prince akbar kuwa mutuwar tsaye yyi, sarki abdallah bin jabal kuwa qurawa abram idanu yyi da fuskarsa da babu alamun annuri, jin zciyarsa yake kamar zata tsago ta fito sbd tsananin 6acin rai, fadar tayi tsit tamkar mutuwa ta gifta, prince gabansa mugun faduwa yake duk da tarin jarumtarsa yana masifar shakkar mahaifinsa, wannan yanayi da abram ya gani ne yasa tsoro da tarin rudani hade da firgici ya bayyana a fuskarsa,jikinsa rawa ya somayi sosai, miqewa sarki abdallah yyi yayi ya soma takawa a hnkli masu tsarinsa suka take masa baya yabar cikin wannan fada batare daya furta komai ba,sarkin hukunci yaba dakarun dake fadar umarni su kama abram su wuce dashi dakin horo don koyar dashi darasin harshe.......
Littafin nan na kudi ne, idan kina da buqatar krtw zaki tura #300 a wannan acct...0100790419,alhaji shahida nasir,saiki tura screenahrt na payment naki ta whatsapp ta wannan layi......07041195806..........
Alkalamin Bintuu ne......
10/10/20, 1:12 AM - Anti qamshi🌷: *DAREN GOMA SHA HUD'U*🪔🪔
Written By Bintuu Seer
39
*I feel a lot about you darling*........My blood circulate in your blood,yeah, our love has an identity, I adore you💕💕
Qaramin kurku suka kai shi kafin sarki ya yanke masa hukunci dakansa, prince kuwa zuciyarsa a hargitse ya koma 6angarensa, ubaid ya kira yace" ka samu amintacciyar baiwa ka tura ta qasarban don isar da wannan saqo ga sumayya" miqa masa wata farar takarda yyi, rissinar dakansa yyi ya amshi takardar sannan yaja da baya ya juya ya fita, wurin qorama ya wuce ya tsaya can nesa ya hango su israt da khulood suna wanki, kamar ance israt ta juya ta hango shi tsaye ga dukkan alamu su yake son gani, shikam ubaid yana ganin sun ganshi a wayance ya soke musu wata takarda a jikin wata bishiya yyi saurin barin wurin, khulood na ganin hk tayi saurin tashi da niyyar zuwa wurin israt ta dakatar da ita suka cigaba da wankinsu suka basar sai bayin dake wanki wurin suka watse sannan israt cikin dabara taje wurin bishiyar ta zare takarda suka wuce abinsu, wurin da babu koma suka samu suka warware takardar, dayan takardar itace wacce zasu kai ga sumayya dayan kuma takardar shaidar fita ce da sanya hannun ummu nana don basu basu mai sanya hannun babban prince ba kar a zargi wani abu sai ubaid ya samu ummu nana ta sanya hannu itama kanta bata fahimci komai ba don ubaid kamar qani yake a wurinta shiyasa ta bashi sa hannunta batare da wani tunani ba, israt ta kalli khulood tace"kece zakije koh sbd shaidar fitan mutum guda ne wannan" murmushi khulood tayi tace" kece zaki iya wannan aiki sbd kin fini qarfin hali da dabara" wucewa sukayi babban kitchen suka dauki kwandunan debo kayan marmari suka nufi lambu basu jima ba suka dawo kawunansu dauke da kwanduna cike da tuffa suka kai musu babban kitchen, cikin dabara israt ta saci jiki ta nufi babban kofar fita daga masarauta, ganin bayi tayi jere masu shaidar fita suna nunawa ana basu hanyar su fita, layin yyi tsawo dayawa haka take ta Allah Allah a iso kanta har masu tsaron kofa suka iso kanta ta nuna musu shaidar fita suka bata hanya ta wuce, cikin izinin Allah tana fita saqon sarki abdallah ya iso ga masu tsaron dukkan kofofin masarauta su rufe kofar shiga da fita, batare da sun sake barin kowa ya fita ba suka hade kofa suka rufe ruf,israt kuwa qarar rufe kofan da taji ne yasa ta juyawa, farin ciki tayi da Allah ya bata damar fitowa lfy, tfy take sosai tana qetarawa ta siraran hanyoyi da suka ratsa ta gefen gidajen jama'a kunsan yanayin ginin larabawa yadda yake hk har ta qarasa qasarban, rufe kanta tayi sosai har da gefen fuskarta, tsayawa tayi tana hangen kofar shiga wurin ta ganta da qaton kwado, kofar shiga wurin be nuna mata akwai wani mahaluki sake rayuwa a cikin wurin ba, hkn ya ankarar da ita lalle karta qarasa kofar shiga wurin ta shiga wurin ta wani wurin, 2kalle take ta babu kowa don wurin bayan gari ne sosai,tsalle tayi ta haye katangar shiga wurin ta dire ciki, ko'ina yyi qura har ta soma jin tsoro anya kuwa da wani abu mai numfashi a cikin wannan gd,shiga dai take tana danna kai cikin gdn dayake da zurfi, tuntu6e tayi da wani dutse ta fadi ta riqe kafarta, sumayya kuwa tana nesa kadan da wurin ta jiyo motsin mutum, miqewa tayi da hanzari ta isa inda israt take ta bayanta sai ji tayi an saka mata wuqa a wuya, bude idanu israt tayi tana kallon sumayya tace" kiyi hkr ki sake ne don nidin isar da saqo nazo yi" sauke wuqan sumayya tayi, israt ta kalli sumayya sosai ta ganta yadda ubaid ya kwatanta kamanninta cikin takarda, ciro takardar tayi daga jikinta ta miqa mata,saurin warware takardar sumayya ta ga sanya hannun babban prince sannan ta soma krt abunda ke ciki, tana gama krtw tayi ciki da sauri, israt tabi bayanta don tana son sake ganin bimbii, kai tsaye suka shiga inda bimbii take, bimbii na dago dakanta taga israt tsaye da gudu ta taho suka rumgume juna cike da farin ciki, sumayya kuwa saurin kama hannun bimbii tayi, jaririn na hannunta shiga dasu wani wuri, wata kusurwa suka shiga ta janye center carpet din dake shimfide wurin sai ga kofa ta bayyana ta bude kofar tayi da hannunta suka hangi matattakala data shiga qasan wurin, takawa suke a hnkli sumayya na haska musu hanya da wata qatuwar fitila har suka qarasa qasan wurin, cikin qasan wurin yana da fadi sosai, rumbii tara dukiya ne sbd ta kowanne gefe diamond ne a jere sai kyalli yake da daukar idanu, dukkaninsu sake baki sukayi suna kallon wannan tarin arziqi tamkar ba za'a mutu ba,zaunar da bimbii sumayya tayi israt ta zauna kusa da ita, fita sumayya ta sakeyi taje tayi clearing komai wanda ze nuna akwai mutane a gdn sannan ta dawo ta shiga ta maida kofar wurin ta rufe kamar yadda yake a baya, befi awanni uku da faruwar hkn ba, dakarun sarki abdallah suka shigo wannan gd don bincike, sumayya kasa kunne tayi ta jinsu suna bincika kowanne lungu da saqo na wannan gd don suna tunanin nan prince ya kawo bimbii, har suka gama bincikensu ba bimbii babu alamarta, har zasu juya su tafi wani daga cikinsu ya hangi mayafin mace a saman gado, nuna ma sauran yyi suka dawo, daukan mayafin sukayi suna qara kallon ko'ina, binciken qurulla suka cigaba dayin cikin gdn har kusurwar da dakin qasan nan yake suka shiga suka gama bincikensu basu ga komai ba hk suka koma suka sanar da masarauta,sarauniya mar'atussaliha kuwa lkcin data ji wannan abu daya faru ba qaramin tashi hnklinta yyi ba bata ta6a tsammanin wannan baiwa na raye ba har kuma wai ta haife cikin jikinta, tsoron da take yanzu kar sarki abdallah bin jabal ya kuma fishi da prince sam bata fatan hk, tashi tayi cikin sauri ta nufi turakar sarki ta nemi iso, uxair ya shiga ya fito ya sanar da ita sarki bazai ganta ba, dole ta hkr ta koma 6angarenta cike da rudani,sarki abdallah bin jabal be sake fitowa ba sai washegari ya nufi fadarsa, umarni yyi kan a kawo masa abram, batare da 6ata lkci dakarun tsaron fadar suka gabatar da abram gaban sarki abdallah bin jabal, prince shima yana fadar beyi shakkar zuwa ba, yana tsaye daga gefe kansa a sunkuye har lkcin da aka gabatar da abram gaban sarki, abram kallo daya zaka masa kasan ya jigatu abunka da jar fata tuni jigatuwa da wahala ta bayyana a tare dashi, fada tayi tsit kowa na jiran yaji hukuncin da sarki abdallah ze yankewa wannan bayahude tare dansa, daga kai sarki abdallah yyi ya kalli abram yace" kamar yadda na mk alqawari na amshi buqatarka zan cika mk sbd bana alqawari na saba wannan itace nasarar da kayi saidai da kyakykyawan sharadi, shine na amince zan aurawa d'ana baiwa mara asali dalilin alqawarin dana dauka saidai aure ne dazai wakana batare da masarautarmu ta gayyaci kowa ba kuma ba za'ayi wani sha'ani ba"prince dake gefe yyi saurin dago dakansa cike da mamaki yana kallon mahaifin nasa, don be ta6a zaton mahaifin nasa ze amshi wannan buqata ta abram ba, shiru yyi yana tunani anya sarki abdallah be shirya wani tuggu ba kuwa shi yasa yyi hkn,kallon prince sarkin yyi yace" ina son daren yau ka gabatar da wannan baiwa da kk 6oye da ita ga ahlinka" rissinar dakai prince yyi alamar biyayya da amsar umarni,sarki yyi umarni da dakarin nan su saki abram, daga nan zaman fada ya watse, prince ya qarasa 6angarensa cike da tunani kan manufar sarki abdallah kan wannan batu gani yake kamar da wata a qasa kar fa sarki ya shirya masa shigo shigo ne ya samu damar damqe bimbii da dansa dake tare da ita ya aikasu lahira, zuciyarsa ta kasa nutsuwa har yanxu, lbrin wannan hukunci da sarki abdallah ya yanke tuni ya isa ga sarauniya itama dai mamaki abun ya bata, gimbiya hindu kuwa da bata jima da dawowa daga habasha ba baqin ciki da takaici ne ya cikata itama batayi zaton har yanzu bimbii na raye ba don akan idon kowa bimbii ta afka wannan dogon rami........
Littafin nan na kudi ne, idan kina da buqatar krtw zaki tura #300 ta wannan acct...0100790419, alhaji shahida nasir,union bank, saiki tura screensht na payment dinki a whatsapp ta wannan layi...07041195806....
Alkalamin Bintuu ne....
10/10/20, 1:12 AM - Anti qamshi🌷: *DAREN GOMA SHA HUD'U*🪔🪔
Written By Bintuu Seer
40
*I give you my heart,I give you my blood,I give you my soul*............I sacrifice everything to you my beloved💕💕
Prince dakansa ya nufi qasarban ya taho da bimbii, ranar duk inda ka zauna cikin bayi tsegumin wannan zancen suke wai tsohuwar baiwar babban prince ta dawo tare da sabon jariri, mafi yawan masu tsegumin basu aminta cewa wannan d'an na babban prince bane, sarauniyya mar'atussaliha dakanta ta bada umarnin a shiga da bimbii 6angarenta, bimbii kam zuciyar cike take da tsoro musamman yadda taga fuskar wadanda suka tare ta, ummu nana da wasu kuyangi biyu suka kama hannun bimbii suka shige da ita,ummu nana ta amshi jarrin dake hannun sumayya ta wuce dashi ciki, wanka aka yiwa jarrin aka sanya masa kaya na alfarma sannan ta fito dashi ta wuce dashi ga sarauniyya, tana shiga ta sunkuya ta miqa mata jaririn, miqa hannu tayi ta amshi jaririn, qurawa jaririn idanu tayi tana kallon ikon Allah don wannan jariri babu ta inda ya baro kakansa sarki abdallah hatta idanunsa na kakansa ne, kasa dena kallon jaririn tayi tana qara jaddada mulkin ubangiji wato dai zakaran da Allah ya nufa da chara ko ana muzu ana shaho sai yyi, yaro dai kakansa ya dauko, miqewa tayi dakanta hannunta biyu riqe da jaririn ta nufi 6angaren sarki abdallah ummu nana da sauran kuyaginta na take mata baya, uxair ne ya shiga ya nema mata iso sarki abdallah ya bata damar shigowa ta shigo, yana zaune a wata kujera ta sarauta tunda ta shigo yake kallonta, rissinar dakanta tayi a gabansa sannan ta miqa masa jaririn dake hannunta, qin miqa hannunsa yyi ya amshi jaririn ya daga mata hannu alamar ya sallameta, shiru tayi tana kallonsa sanin halin taurin kai da kafiya irin nasa yasa taja da baya jikinta a sanyaye ta juya ta fita, komawa tayi sashinta ta tarar itama bimbii ta shirya tsaf, itakam sarauniya ta zubar da makaman yaqinta tunda ta dora idanunta kan jaririn nan, bayin gdn gbdy sun saka idanu har sun gaji amma basu samu damar ganin bimbii ba bare jaririn dake tare da ita,shi kansa prince ganin bimbii ya gagare shi,kamar yadda sarki abdallah ya alqawarta hkne ya faru, safiyar alhamis al'ummar fadar masarautar burham suka shaida daurin auren bimbii da prince akbar, wurin wannan daurin aure tamkar wurin makoki babu mai annuri ko walwala, a dai daura, sarki abdallah ya tabbarwa al'ummar duniya shi sarki ne mai mgn guda da tsayawa kan alqawari, wannan rana baqa take qirin ga sarki abdallah da dukkanin wani jini na sarautar burham idan muka dauke babban prince da ranar take fara qal a wurinsa, a tarihin masarautar burham yarima akbar shine d'an sarki na farko daya karya tsaurarriyar dokar wannan masarauta ya auri baiwarsa, wannan aure ya zamto tamkar faruwar mugun abu ga jinin sarautar burham, dayake abun duniya baya 6uya kafin giftawar ido wannan aure tsakanin d'an sarki da baiwa ya karad'a sauran masarautun larabawa, sarakai dayawa idan suka ji wai duk qarfin mulki da izzah irin ta sarautar burham magajin masarautar ya bige da auren qasqantacciyar baiwa kuma baqar fata, hkn yasa sarki abdallah ya dena halartar taron sarakuna na nahiyar larabawa sbd wannan abun kunya da d'ansa ya janyo masarautarsa,bimbii har yanzu tana 6angaren sarauniyya daren yau za'a miqata 6angaren prince akbar, sun shirya sosai albarkacin hada jini dasu da tayi, prince yasa matakan tsaron sirri masu sanya idanu kan duk wani motsi na masarautar burham kan iyalinsa,keken doki na musamman aka kawo don daukar bimbii zuwa 6angaren babban prince, dakarun tsaro da yan matan bayi kewaye suke da wannan keken dokin, fuskarta rufe take da jan mayafin kayan dake jikinta, ta wata siririyar dake saman gada suka bi,hanya ce da dawakai ke ratsawa zuwa 6angarori daban daban na gdn, tfy suke zabiyoyi dake biye da keken dokin na rero waqoqi na masoya masu dadi har suka kai tsakiyar hanyar, suna tsakiyar wannan siririyar hanya sai gani sukayi kawai an tsagayesu, wasu mutane ne sanye da baqaqen kaya, fuskokinsu ma a rufe suke batare da wani 6ata lkci ba suka soma fada da dakarun dake janye da keken dokin da amarya ke ciki, sunyi masifar iya fada kafi kwabo sun soma kwantar da dakarun, burinsu kawai su qarasa wurin wannan keken doki su dauke amarya da jaririn dake tare da ita, ihu kawai kkji, jini duk ya 6ata keken dokin, yan matan bayin nan qoqarin fito da amarya suke su gudu da ita kafin wadannan mutane su qaraso, tuni suka gane nufin kafin suyi wani yunquri wani cikin mutanen ya yarfa musu wani sai ga wasu kananan allurai masu guba sun fita sun sossoki jikinsu suka zube a wurin, sai da suka gama da kowa suka bude keken dokin suka janyota waje wani daga cikinsu yasa hannu ya wafce jarrin dake hannunta, jin jikin jaririn yyi wani iri, saurin bud'e kyakykyawan farin towel din da jaririn yake ciki yyi,tirrqashi! kunsan me ya gani qatuwar teddie, kallon juna sukayi cike da tsantsar mamaki, aikuwa tamkar hadin baki su duka suka sanya hannu suka yaye mayafin da armarya ke rufe dashi sukaci karo da wata baiwa itama duk a tsorace take, batare da wata wata ba babban cikinsu ya daga takobi ze fille kan wannan baiwa a fusace,wani mahayi fuskarsa rufe da baqin kyalle ya bayyana bisa farin doki tunkan ya qaraso yake harbinsu da kwari da baka har ya qaraso wurin, hkn yasa hnklinsu gbdy ya tafi ga wannan mahayin doki suka gyara riqon takubban dake hannunsu hkn ya bawa wannan baiwa daman barin wajen don tsira da rayuwarta, wani irin fada suke gwabzawa tsakaninsu da wannan mahayin dokin burinsu kawai suyi masa illah saidai salon fadansa yyi masifar basu mamaki sbd fada yake irin na cikakkun jarumai masana sirrin takobi, gashi da zafin nama da iya gociya, suna ganin hk sukayi wani irin alkafira suka fada qasan gada su dukka, sauka yyi a hnkli daga saman dokinsa yana kallon irin 6arnar rayukan da sukayi sbd kawai son zuciya, shikam taurun kai wannan sarki na bashi mamaki besan sai yaushe ne ze ajiya wannan kiyayyar da taurin kai ba, qara jinjina kaifin basira na prince yyi daman yasan hkn na iya faruwa shiyasa ya bawa sumayya kayan da bayi ke sanyawa yace ta bawa bimbii ta saka ta fito da ita a sace ya tura mata wannan baiwa ta zama a madadin bimbii, saida sumayya ta bari an gama shirya bimbii daga ita sai ita tayi saurin sanyata ta cire wannan kayan dake jikinta sannan ta shigo da wannan baiwa ta cire kayan jikinta sukayi musaye, ita baiwa ta zauna a madadin bimbii ta rufe fuskarta da mayafi, sumayya sanya jaririn cikin kwando bimbii ta fita dashi batare da kowa ya ankara ba ta nufa inda sumayya ta fada mata don daman tasan ko'ina cikin gdn, sai qasa take da fuskarta kar wani ya ganeta hk har ta samu ta fice daga 6angaren sarauniya ta nufi daidai gdn magani wurin da sumayya ta fada mata ta hangi inuwar mutum tana waigawa ta hangi ubaid ta qarasa, batare da wata doguwar mgn ba ya samu ya qarasa da ita 6angaren prince akbar ta shige, wannan shine zahirin abunda ya faru a 6angaren sarauniyya, lkcin da bimbii ta shiga ta tarar da prince tsaye yana sauraron qarasowarta don ya aminta da hikimar hadiman dayasa wannan aiki yasan dakyar ne a samu kuskure, yana ganin bimbii ta shigo yyi murmushi tare da bude mata hannayensa, tsayawa tayi don kunyarsa take ji, murmushi yyi ya qaraso ya amshi yaron dake hannunta ya rumgume shi a qirjinsa itama ya janyota ya rumgumeta suka qarasa bakin gado suka zauna hannunsa yasa ya dago da fuskarsa data 6oye a saman kafadarsa yace" kin zama sarauniyata nafi kowa farin ciki da hkn kefa?" shiru tayi masa ta qara 6oye fuskarta a kafadarsa, juyawa yyi ya kwantar da babyn dake hannunsa a saman gadon ya dawo ya zauna ya sake janyota jikinta suna fuskantar juna, numfashinsu na haduwa, bakinsa ya matso dashi daidai da dan mitsitsin bakinta ya dora saman nata a hnkli kuma ya soma kissing nata cikin wani salo mai saurin rikita lissafi, bimbii kam idanunta na lumshe, sun yi nisa cikin wannan yanayi suka ji qarar kukan babynsu yana wani irin kakari, a rude suka saki juna suka juya don ganin me ya same shi................
Littafin nan na kudi ne, idan kina da buqatar krtw zaki tura #300 ta wannan acct...0100790419,alhaji shahida nasir,union bank,saiki tura screenshrt na payment ta whatsapp ta wannan layi...07041195806.....
Alkalamin Bintuu ne......
10/10/20, 1:12 AM - Anti qamshi🌷: *DAREN GOMA SHA HUD'U*🪔🪔
Written By Bintuu Seer
41
*Your love is the most precious gift to me*.......You are my weakness coz i love you so much💕💕
Jikin jaririn yyi jajir yyi 2rud'u tashi daya, sai kuka yake da wata irin shaquwa numfashinsa na sarqewa, prince daukansa yyi yana kallonsa sosai yana son gane meye ya faru da babyn, hnklinsu gbdy yyi masifar tashi,bimbii kuka take sosai babban prince idanunsa sunyi jajir shima,miqawa bimbii babyn yyi ta koma bakin gado ta zauna rumgume da jaririn a qirjinta, prince fita yyi ya tarar ubaid har lkcin be dawo ba don shine ya tafi tserar da baiwar nan data shiga keken doki a matsayin bimbii, takawa ya somayi a hnkli masu tsaron lfyrsa suka biyo bayansa yyi saurin dakatar dasu yyi nesa kadan da 6angarensa yasa hannu ya ciro usir din kiran yar tsuntsuwarsa ya hura sau uku, batare da wani 6ata lkci ba wannan yar tsuntsuwa ta bayyana ta sauka a kafadarsa, hannu yasa ya sakko da ita daga kafadarsa ya daura mata wata qaramar takarda a qafarta sannan ya dagata ya saketa tayi kudu, tsuntsuwar nan bata tsayawa ko'ina ba sai wani gd na jar qasa wata tsohuwar balarabiya na zaune a wata kujera ta katako wannan tsuntsuwa ta sauka bisa kafadarta, murmushi tsohuwar tayi don tana ganin wannan tsuntsuwa tasan saqon babban prince ne ya taddata, cire saqon takardar tayi daga qafar tsuntsuwan ita kuma ta kad'a fiffikenta ta tashi tayi tfyrt, wannan tsuhuwa mai suna deenah likita ce ta gargajiya kuma ungowar zoman ta musamman dake amsar duk wata haihuwa ta jinin sarautar burham, miqewa tayi ta shige cikin wani daki bata jima ba ta fito rataye da wata jaka ta sake jan mayafinta ta dora bisa kanta ta fita ta nufi gdn sarautar burham ta kofar yamma ta shiga kamar yadda prince ya sanar da ita, dayake tasan gdn sosai kai tsaye 6angarensa ta wuce, dakatar da ita masu tsaron kofa sukayi saida aka mata iso ta shiga, prince na ganinta yyi saurin miqewa tsaye, qarasawa tayi inda yake ta rissinar dakanta sannan ta dago ta miqa hannu ta amshi jaririn dake rumgume a qirjinsa, kallon jaririn tayi sosai taga ya sauke wata ajiyar zuciya sai kuma numfashinsa ya dagata chak tamkar anyi ruwa an dauke, dago kanta tayi suka hada idanu da babban prince ta soma girgixa masa kai alamar saidai hkr,saurin sunkuyar dakansa yyi qasa, bimbii ta matso wurin da sauri tana kallon deenah tace" mene ya same shi?" shiru taga duk sun mata, hkn yasa ta kuma shiga rud'u ta fara kiciniyar amshe jaririnta daga hannun deenah a rikice, saurin riqeta prince yyi ya kwantar dakanta a saman kafadarsa yana mata mgn a hnkli wanda ba kowa ke iya jin abunda yake fadi ba, kuka sosai ta fashe dashi sai sheshsheqa take tamkar ranta ze fita, shima idanunta sun kada sunyi jajir kukan zucci yake bana hawaye ba, deenah kallonsu tayi cike da tausayawa ta wuce jiki a sanyaye ta dauki wani farin towel ta lullu6e jaririn har fuskarshi,cikin daren wannan baqin lbr yakai ga sarauniyya mar'atussaliha ya kuma karade lunqu da saqo na wannan gd, sarauniyya rasuwar jaririn ya bugeta sosai fiye da tunanin mutum, ummu nana kuwa tuni ta lalla6a ta sanar da uxair cewa aiki yyi kyau ta 6angarenta, uxair shine ya bawa ummu nana wani ruwan guba a wata yar qaramar kwalba ta zuba cikin ruwan da zata yiwa jaririn wanka, da farko tayi masa gardama saida ya sanar da ita wannan umarni ne kai tsaye daga sarki abdallah shine ta amince ta aikata hkn, gubar tana fara aiki a bayan awanni ashirin da hudu,hknne yasa ba'a saurin fahimtar gubar a cikin jiki shiyasa suma sukayi amfani da ita ga jaririn sbd tsabar rashin imani, sarauniya sam bata da masaniya kan wannan cin amana na ummu nana amma sarki abdallah ya sani kuma yyi farin ciki da wannan lbri na mutuwar jikan nasa,washegari, fuskar kowa ta nuna alhini musamman ubaid da sumayya, israt da khulood wannan lbri sun jishi tamkar sukar mashi, hk aka yiwa wannan jariri sutura, lkcin da aka nufi maqabartar da ake binne jinin sarautar burham da gawar wannan jariri 2qiri sarki abdallah bin jabal ya dakatar da hkn yace a binne jaririn a maqabartar da ake binne bayi,wannan abu yyi masifar 6atawa sarauniyya mar'atussaliha rai ba shiri ta nufi 6angarensa saidai uxair ya sanar mata sarki yace bashi bidar ganin kowa, prince kuwa takaici da baqin ciki sun masa qawanya tabbas halin mahaifinsa hali ne na Allah tirrr, yana da baqar zuciya tamkar ta kafiran farko, 6oye 6acin ransa yyi hk aka binne jaririn a maqabartar binne bayi, prince be sanar da bimbii komai ba game da abunda ya faru kawai dai tunda ya shigo be kalli inda take ba yyi saurin shigewa wata kusurwa ya sake curtains, zama yyi ya dafe kansa ranar duk qarfin hali irin na babban prince saida ya zubda hawayen baqin ciki da qunar zucci, idanunsa sun kada sunyi jajir, jijiyoyin kansa sunyi 2rud'u har lkcin mahaifinsa be masa ta'aziyya ba sannan ya biyo shi da wannan abu, bimbii fita tayi ta nufi 6angaren su israt, tana tfy bayi na rissina mata tare da mata ta'aziyya wata girmamawa da take gani na daban ga dukkanin bayin dake 6angaren har da wadanda da suke mata kyashi da hassada,su israt na hangota suka nufota da sauri duk suka rissinar dakansu a gabanta tare da mata ta'aziyya amsawa tayi ta sanya hannu ta dago da kansu tana murmushin qarfin hali tace" mene hk kkyi?bani so kar ku sake, yan'uwa muke har gobe" murmushi suka mata, israt da bakinta baya shiru ta kalli bimbii data ga ta lula duniyar tunani tayi gyaran murya tace" sai kin cigaba da hkr tare da taka tsantsan don sharrin dake wannan gida yana da hadarin gaske tabbas kasancewarki mata ga babban prince ya zamto rubutaccen al'amari ne da babu wanda ya isa ya sauya amma har yanzu kina da tarin maqiya,kar abinda sarki yyi yau ya dame ki wataran hkn ze zama lbri" saurin kallonta bimbii tayi tace" me yyi yau din" shiru israt tayi don batayi tsammanin bimbii batasan abunda ya faru ba da batayi wannan azar6a6in ba,juyawa tayi ta kalli khulood duk sukayi shiru suka sunkuyar dakansu qasa,bimbii tace" ku fadamin abun daya faru kar ku 6oyemin komai idan har kun dauke ni a matsayin yar'uwa" dago dakai khulood tayi tace" tabbas abunda sarki abdallah ya aikata ga gudan jininsa yasha gaban kwatance da dukkanin wani zato, ya hana a binne jininsa a inda ake binne jinin wannan gd yyi umarni da a binne shi a inda ake binne bayin wannan gd, wannan abu yyiwa babban prince zafi sosai" shiru bimbii tayi kamar mai tunanin wani abu sai kuma ta tashi da sauri ta soma tfy suka bi bayanta saida suka rakata har kofar shiga 6angaren babban prince kafin suka dakata ta shige, tana shiga ta nufi wannan kusurwa da taga ya shiga ta tarar dashi yana zaune ya kwantar dakansa a jikin wani matashi, idanunsa a rufe, yaji motsin shigowarta amma be bude idanunsa ba, matsawa tayi a hnkli ta zauna kusa dashi ta dauke matashin daya jingina kansa dashi ta kwantar dakansa a jikinta ta cusa hannunta cikin gashinsa, qin bude idanunsa yyi sbd baya son taga rauninsa don ya zubda hawaye sosai hkn yasa idanunsa sukai jajir, muryarta yaji a hnkli tace" inda ake binne jinin sarauta da inda ake binne bayi wannan bashi bane burinmu kawai ya kasance mai ceto a garemu, fatanmu ya zamto ya tadda kyakykyawan rabo wurin wanda ya bamu kuma ya amshe abinshi, prince dina dai dana sani jarumin gaske ne ban ta6a ganin karayarsa sai yau" bude jajayen idanunsa yyi ya sauke su a fuskarta, kallon idanunsa tayi taga yadda suka juye sukayi jajir, murmushi ta masa shi kuma ya qurama fuskarta ido, dariya tayi tace" tashi lkcin wanka yyi" besan lkcin da murmushi ya su6uce masa shima ya miqe zaune, komawa tayi bayansa ta rumgumeshi ta baya tana rada masa wasu zantuka na sirrinsu a kunnensa wanda yasa shi murmushi, janye hannunta yyi daga jikinsa ya koma ya kwantar dakansa a matashin dayake tun farko, kallonshi tayi ya noqe kafada, murmushi tayi ta matso kusa dashi sosai ta dora fuskarta akan tashi suna jin bugun numfashin juna, a hnkli ta dora bakinta saman nashi ba zato ba tsammani yaji ta soma bashi nata darasin wanda ya shagaltar dashi sosai ya mantar dashi dukkanin tarin damuwarsa,tsarki ya tabbata ga Allah wanda ya qaddaro soyayyar wadannan masoya kuma ya basu qarfin zuciyar fuskartar qaddararsu, a wannan lkci tarihi ya maimata kansa, bimbii ita ta fara wasan shi kuma ya wuce gona da iri, tsohon darasin nan dai shi prince ya biya mata tun bata ganewa har ta soma fuskanta, wannan karon babu tirjiya ta bada kai bori yahau, prince kam qara qanqame bimbii yyi tamkar wani ze gudu masa da ita, bayan kwana uku prince da wannan rasuwa bimbii ta tare a 6angarenta, qaton gini ne har yafi 6angaren prince girma tare da yalwar bayi masu hidimtawa 6angaren nata, sumayya itace prince yasa ta kasance ta hannu damanta, israt da khulood kuwa bimbii
t
a
10/10/20, 1:12 AM - Anti qamshi🌷: *DAREN GOMA SHA HUD'U*🪔🪔
Written By Bintuu Seer
42
*You are my princess*......I love only one woman, I give you my soul pls give me your heart💕💕
Israt da khulood kuwa bimbii ta y'antasu sun fita daga sawun bayi sun zama masu y'anci, prince yasa mugun tsaro a 6amgaren nata sannan sumayya idonta nakan duk wani motsi na bayin dake hidimtawa 6angaren, sumayya ita ke kula da duk wani abun sha ko ci na nata, bimbii dai itace mata, babbar baiwa kuma masoyiya ga prince akbar, bata bari wata baiwa ta zama babbar baiwa ga prince dinta ba, gbdy ta babbanke komai tamkar ba bimbii da kk sani ba don kuwa idanunta ya bud'e da wayo da dabara taga babu sarki sai Allah, kunsan ance duniya mkrt ce,bimbii dai tayi karatun rayuwa da wayonka da hikimar ma yaka qare cikin rayuwa,6angaren abram kam prince ya hada masa sha tara ta arxiqi ya koma spain, abram na da wani babban matsayi a wurin prince akbar duk da kasancewarsa bayahude bazai ta6a mancewa dashi ba don ya bada kyakykyawar gudummawa wurin samar da farin cikinsa, sarki abu ansar ya samu lbrin abubuwan da suka wakana kuma tabbas ranshi yyi mutuqar 6aci hknne yasa ya rubutowa sarki abdallah bin jabal rubutacciyar wasiqa mai qunshe da zafafan kalmomi, wannan wasiqa tayi masifar qonawa sarki abdallah rai don cikin wasiqar har sarki abu ansar yana aibata masarautar burham cewar sun gur6ata jinin masarautarsu ta zama garmai na bayi baqar fata, wannan kalami shi tunzura sarki abdallah sosai har ya rantse sai ya dauki ran bimbii tunkan ta 6ata jinin sarautar burham, sarki abu ansar kuwa tuni ya tsinke wannan yarjejeniya na hada yarsa aure da prince yace yarsa tafi qarfin tayi kishi da qasqantacciyar baiwa mara asali, sarki abdallah ya dakatar dakansa da halartar taron manyan sarakuna saidai ya tura prince ya wakilce shi sbd yana jin kunyar hada ido da sauran sarakunan larabawa bisa kuskuren da masarautarsa ta tafka na hada jini da baqar fata, yau da dare tana tafe bayinta na biye da ita har suka isa 6angaren prince, duk suka dakata a kofa ta wuce ta shige ciki, sanye take da farar doguwar riga mai adon duwatsu, gashin kanta a tufke yasha gyara sai zabga qamshi take tana shiga ta ganshi sanye da wata farar riga ta shiga wanka yana zaune hannunsa riqe da awarwaron nan nata, dago da kansa yyi yana kallonta tana tahowa wurinsa hannunta riqe da qaramin faranti, riqar data sanya ta fito da sirrin dirinta sosai hkn ya bawa ma'adanan jikinta damar watayawa, zuba mata idanu yyi sosai musamman boobs nata dake tsatstsaye tamkar wani maye,kashe masa idanu tayi da murmushi a fuskarta, besan me lkcin data qaraso wurin dayake zaune saida ta hure masa idanu ya dawo cikin sense nashi,hannunsa ta kama ya miqe suka shiga dakin wanka, ruwa ta hada masa mai dumi cikin kwarmin ta sanya sinadaran wanka ya shiga, tana tsaye tana masa tausa saida ya daga mata hannu sannan ta dakata, juyawa tayi da niyyar fita ta bashi damar qarasa wankan,hannunsa yasa ya riqota ta dawo tana zaton ko yana da buqatar wani abu ne taji yace" baki qarasa min wanka ba zaki fita" noqe kafada tayi ta dan turo baki gaba tace" nidai ban iya yiwa babba wanka ba" bece mata uffan ba yyi saida murmushin da yyi aikuwa bata ankara ba yyi wuf ya jata cikin kwarmin wankan, zaro idanunta tayi waje tana facalfacal da ruwa tana son fita shi kuwa yasa karfi ya danne mata qafafu, kokawa ta kaure tsakaninsu, sai ture shi take idanunta a rufe taqi budewa, shikam dariya ta bashi sosai ya zuba mata idanu yana murmushi yace" a hk zamu kwana idan baki bude idanunki kin fara aikin ki ba amma idan baki iyawa ni barin miki saiki koya" aikuwa tana jin hk tayi saurin bude idanunta suka hada idanu, kallonshi take shi kuwa ya qara fito da jikinsa ta kalla sosai, kauda kanta tayi cike da kunya, matsowa yyi kusa da ita yaja mazargin doguwar rigar dake jikinta ya soma warwareta, saida ya cire tuffan dake tare da ita duk da tsilliyar da take, wankan ya soma qoqrin fara mata tayi saurin dakatar dashi ita ta soma masa, hkn yafi komai masa dadi har da lumshe idanu, tana yi yana satar fage ya rage zafi da abubuwan dake tsole idonsa, bata hana shi ba ta kyaleshi, hk suka gama wankan nan kusan dai kawai soyewa akayi cikin bathroom, wani lkcin idan ta kalli fatarta ta kalli nashi saita ga duhun fatarta ta bayyana sosai don shikam fari ne sol ga kuma hutu daya zauna a jikinsa, hannunsu na sarqe da juna suka fito cikin fararen kayan bacci iri daya masu taushi sai qamshi suke, gashinta na baje a tsakiyar gadon bayanta, zama tayi a bakin gado shima ya zauna kusa ya kamata suka kwanta saman gadon, shi prince gbdy ya sakalce baya iya bacci idan be kwanta a jikinta ba hk take fama dashi kullum, yadda uwa take ririta jariri kafin yyi bacci hk take masa idan tana son yyi bacci ya kyaleta ta huta da fitinarsa, rayuwa suke mai cike da farin ciki,koda sunyi fada toh ba jimawa zasu jone kamar basu ba, cikin watanni uku alamomin juna biyu ya bayyana ga bimbii, tayi bulbul, komai na jikinta ya qara cikowa, ita kanta idan ta tuna matsayin a baya ta kuma duba gatan data da tsinci kanta yanzu silar mijinta saita qara yiwa Allah godiya, prince yana fahimtar bimbii nada ciki ya shirya musu tfyr bazata, ya sanar da mahaifinsa tfyr amma be sanar dashi har da iyalinsa ze tafi ba, cikin daren asabar jirginsu yahau saman teku inda suka nufin yankin turai wato qasar birtaniyya, bimbii na zaune gefensa tana kallon ruwan teku hkn na tuna mata wasu muhimman abubuwan da suka faru cikin rayuwarta tayi nisa cikin tunani taji ya riqo hannunta, juyowa tayi tana kallon kyakykyawar fuskarsa da tunda take bata ta6a mafarkin Allah ze hadata da miji mai kyau irin prince ba amma gashi qaddarar aurensa ta fito da ita duniya sun hadu,wai yau ita bimbiin inna da baffi ita ke auran dan sarki balarabe daga nahiyar larabawa,murde mata hannu yyi hkn yasa tayi yar qara cike da shagwa6a yace" me kk tunani hk" murmushi tayi ta daga hannunta tana shafa sajen daya zagaye fuskarshi ta dora yatsanta sama lip dinshi dayake jajir kamar yasa lipstick tace" har yau ban ga wanda yafi ka kyau ba" qanqance idanunsa yyi yana kallonta cike da salo tamkar mai jin bacci, beyi mgn ba don wani lkcin hk yake koda ta masa mgn idan beyi niyyar tankawa ba saidai ya bata amsa da action dinsa ko kuma ta gane amsar mgnrta cikin kwayar idanunsa, yanzun ma idanunsa ta kalla sai kawai tayi murmushi ta juyar dakanta ta cigaba da kallon ruwa, kwantar dakansa yyi a shoulder dinta ya lumshe idanunsa, kowa ya kallesu sai yyi sha'awar yanayin soyayyarsu,sunyi kwanaki saman teku kafin jirginsu ya isa birnin london, musamman aka turo hadimai daga masarautar ingila su tare shi kasancewar dan sarki daga masarautar larabawa mai qarfi kuma official visit ya kawo, kai tsaye royal louge aka wuce dasu, washegari, prince akbar bin abdallah ya gana da sarauniyar ingila Queen Elizabeth I, kwanan prince uku a qasar london ya soma shirin komawa gd, rigima sosai bimbii tasa data ga shirin komawa yake babu ita, saida yyi lallashi yyi lallashi kafin ya shawo kanta ta hkr zata zauna, gdn da bimbii take gd ne mai kyan gaske, tana da yalwar hadimai wadanda kusan dukkaninsu turawa ne, saida bimbii ba turanci, sake baki tayi lkcin data ji prince ya juye harshe yana fitar da zallar tsagwaron turanci tamkar ba balarabe ba, prince a birnin london yyi karatunsa tun daga elementary sannan ya wuce Oxford, saidai idan sun koma masarauta basu amfani da al'adar kowa sai zallar al'adarsu na iyaye da kakanni, suna ji suka rabu ya koma kuwait ita kuma ta zauna a birnin london tana rainon cikin dake tare da ita, prince ya daukar mata malamai wadanda kusan dukkaninsu turawa ne suna mata special lesson, sumayya daga baya daya koma gd ya turota ta zauna da bimbii, komai mata ake, jikinta ya soma sabawa da hutu, sarki abdallah sai bayan tfyrsu ya gane tare suka tafi hkn ba qaramin 6ata ransa yyi ba gani yake ashe har akwai abunda prince xe 6oye masa, lkcin da prince ya koma sosai sarki abdallah ya dauki dumi dashi, dakyar ya sakko da taimakon sarauniyya, ita kadai ce tasan bimbii nada ciki ta fahimci hknne yasa prince ya dauketa daga masarauta, prince kam be yarda da kowa ba tunda yasan duk ba son bimbii suke ba gani yake za'a cutar da ita da abunda ke tare da ita, maganin kar ayi kar a soma shiyasa batare da shawarci kowa ba ya yanke wannan shawarar bazai dawo da bimbii masarautar burham ba har sai ta haife abunda yake cikinta kuma sai ta sauya 2kwata daga yadda suka santa, so yake ta dawo a babbar giwa yadda inuwarta kawai zata tsorata maqiya..............
Littafin nan na kudi ne, idan kina da buqata krtw zaki tura #300 ta wannan acct...0100790419,alhaji shahida nasir,union bank,saiki turo da screenshrt na payment a whatsapp ta wannan layi...07041195806......
Alkalamin Bintuu ne.....
10/10/20, 1:12 AM - Anti qamshi🌷: *DAREN GOMA SHA HUD'U*🪔🪔
Written By Bintuu Seer
43
*My dream is only you dear*......I just want to spent my life time with you my sweet woman...only you sweetheart💕💕
5mounths later
Cikinta yyi girma sosai tayi wani d'an lukutin kyau,fatar jikinta sai kyalli da sheqi tana glowing, hutu ya zauna ga bakinta ya fara fitar da inglishi yadda ya kamata, dayake masu abun dakansu ke koyar da ita harshenta ya karye da turancin cikin sauri gata dama da yaren fillo da larabci a bakinta sai turancin nata yake fita tamkar wata haifaffiyar ingila, duk wanda ya kalli bimbii a yanzu yasan yyi gamo da matar manya, bata aiki fari bare na baqi komai mata ake hutun har yaso ya mata yawa, yadda take sha'awar qafar prince dinta da take luwai luwai kamar tumatir hk nata qafar ta koma itama, prince kuwa kawai fama yake da kewar bimbii gashi babu damar yakai mata ziyara don sarki abdallah ya jibga masa duk wani nauyi nasa komai shike gudanarwa bashi da lkcin kansa sai na masarauta, saidai saqon shi yana tarar da ita 2akai kuma suna mgn ta telephone don lkcin babu wayar tafi da gdnka, yauma tana zaune kan cushion tana shan bornvita sumayya ta shigo ta rissina gabanta ta sanar da ita telephone din dake bedroom na yana ringing, tashi tayi dakyar ta nufi bedroom din ta zauna bakin gado ta janyo qaramin stool din da telephone din ke kai ta daga ta sanya a kunnenta, sweet voice nashi taji yana mgn cike da sanyi, shiru tayi bata tanka masa ba, shima sai yyi shiru, duk sukayi shiru suna sauraron bugun numfashinsu ta cikin telephone din, cikin wata maraitacciyar murya yace" can't you talk to me?" tura baki tayi gaba kamar tana gabansa ta sauke numfashi cikin sanyin murya tace" I really miss you, can't you come back to me?" numfashinsa yaja sannan yace" I miss everything about you baby" kwantar dakanta tayi tace" toh yaushe zaka zo" tayi mgnr ne cikin harshen larabci, murmushi yyi har tana iya jiyo sautinsa yace" yaushe kk son nazo me kk shirya na tara ta keda kkmin rowa abun ma" tace" kullum mafarkin ka nk, ina son ganinka" dariya yyi yace" yy lfyr babyna, ina son kina bashi kulawa na musamman" tace" he just want to see you" yace" I guess this woman miss me so much" dariya tayi suka soma hirarsu irin ta masoyan da sukayi nesa da juna suke kuma begen haduwa, sun jima suna hira har saceta saida yaji tayi bacci sannan ya ajiye kan telephone din, prince be leqa ingila ba saida cikinta ya cika wata na tara yyima qasar dirar mikiya,lkcin daya ganta kasa mgn yyi ya tsaya kawai yana kallonta don ta koma masa wata daban tamkar ba bimbiin daya sani ba, sai kuma ya soma takawa a hnkli ya qarasa wurinta ya dagata chak ko kunyar hadiman dake wurin beyi ba ya wuce da ita ciki, su kuwa hadiman dayake turawa ne hkn ba wani baqon abu bane a wurinsu hk suka cigaba da ayyukansu, prince be direta ko'ina ba sai saman royal bed din dake side din dayake, gbdy ta kasa gane masa daga zuwa kuma babu wani zance sai na biyan fashi da qarayi,ranar bimbii ta gane kurenta tun tana bashi hadin kai har ta soma kuka tana ture shi, shi kuwa ina ai sai daya fanshe kafin hnklinshi ya kwanta, janta yyi ya qanqameta yana bata hkr yace" kin qara kyau sosai fa my princess" dauke kanta tayi wai ita tayi fushi ya jiyo da kanta ta ture hannunsa, sai shima ya juya baya abinsa ya kyaleta, tana ganin hk ta matsa ta rumgumesa ta baya, juyowa yyi yana murmushi ya shafa qaton cikinta yace" wannan cikin yafi na baya girma" shiru ta masa tana kallon gashin kansa daya sake tsayi kamar na mata, hannunta ta dora akansa tana jan gashin nasa, ranar ta kasance wani farin dare ga wadannan masoya da suka jima rabonsu da juna, bimbii kamar jiran zuwan mijinta take kwana uku da zuwansa da sanyin safiyar litinin ta soma naquda, batare da 6ata lkci ba aka turo musu royal doctor, wannan haihuwar bata jima rana labour ba sai ga kan jariri ya fito, likitan tasa hannu ta fito da jaririn yana kuka, cigaban da tayi da labour ne ya dawo da hnklin likita kanta, sumayya na tsaye daga gefe tare da wata midwife itama jar fata, midwife din ce ta amshi dayan jaririn ita kuma likitan ta matsa wurin bimbii ta cigaba da taimaka mata har kan wani jaririn ya kuma fitowa shima suka fito dashi amma bimbii bata dena naquda ba sai ga kan na uku shima ya biyo baya, prince dake tsaye gefe matsowa yyi kusa sosai don be fita daga room din ba a gabansa bimbii ta haifo wadannan zaratan mazaje guda uku, kwatanta farin cikinsa a wannan lkcin ba'a mgn jikinsa har tsuma yake ya miqa hannu yana son amsar na qarshen, likitan ta janye hannu saida suka yanke musu ci6i suka gyarasu sannan ta miqa mishi dayan, dukkaninsu fuskokinsu dauke take da tsantsar farin ciki suna taya prince murnar samun wannan kyauta daga Allah, bimbii kam takanta take kawai burinta kawai ta kwanta ta huta, sumayya ce ta kamata suka shiga bathroom ta hada mata ruwan dumi, midwife din nan tayi mata wanka irin nasu na likitocin turawa mai cike da taka tsantsan, tana fitowa daga wanka taga dakin a gyara tsaf, har suma yaran an musu wanka an shiryasu cikin kayan sanyi dayake yanayin qasar akwai sanyi sosai, prince na fita hadiman gdn sai taya shi murna suke, murmushi da farin ciki ya kasa barin fuskarshi, ji yake tamkar a mafarki wai shine aka haifawa yara har uku dukkaninsu maza masu kama dashi, an dakatar da dukkanin hadiman gdn shiga 6angaren da bimbii take ita da yaranta, sumayya itace kawai hadimar dake kai kawo a wannan 6angaren sbd tsaro sai kuma likitan yara da prince ya dauko don duba lfyr jariran nan yan gaban goshi, abunku da jinin sarauta basu son zuwa asibiti qwararrun likitoci ke basu home treatment, bimbii tamkar ba mai jego ba hnklinta kwance cike da qoshin lfy ga soyayyar miji ta samu,zero tension hk take, kulawa take samu fiye da tunanin mutum wurin prince da dukkanin hadiman take gdn,ubaid kam tamkar shi aka yiwa haihuwa sbd farin cikin daya nuna, dakin guda aka cika da kayan babies da dukkanin abun buqatarsu, bimbii tana zaune ita kadai kawai hawaye ya soma sauka mata a kumatu, bakomai ta tuna ba sai iyayenta da danginta zata so ace sun ga yadda Allah ya qaddara mata nata rayuwar tasan sai sun fi kowa farin ciki, bata sani ba kawai taji hnkchf nasa a saman fuskarta yana share mata hawaye yace" meye abun kuka ga kyauta Allah yyi miki" nuna mata inda babies din ke kwance yyi kowanne a gadonsa irin na kwantar da jarirai,lbrin wannan haihuwa na bimbii tuni ya samu isa masarautar burham, sarauniya mar'atussaliha har sujudun shukr tayi na nuna farin ciki da godiya Allah, 6angaren sarki abdallah haihuwar tazo masa a bazata musamman dayaji cewa har yara uku dai wannan baiwa ta kuma haifa kuma dikkaninsu maxa, hkn ya tabbata baiwa ta zama uwa a wannan masarauta don ta haifi magada,baxan iya kwatanta muku baqin cikin dake qunshe a zuciyar sarki abdallah ba, hk ya din ga sauke fushinsa akan bayi yana aikasu kurku koma ya yanke musu hukuncin kisa, sati daya da isar saqon haihuwar sarki abdallah ya soma ciwo 2sama abu kamar wasa dare daya ya gamu da bugun zuciya sakamakon baqin ciki da takaici daya masa yawa,wannan shine silar dayasa sarauniya ta aikawa prince saqo ya dawo gd mahaifinsa babu lfy, shi kadai yyi niyyar komawa masarauta amma sarauniya tace dole ya taho da bimbii da yaran don su gansu, ba don ya so ba suka soma shirin komawa, ranar alhamis jirginsu ya hau saman ruwa suka nufi komawa nahiyarsu, safiyar laraba suka isa yankin burham, hadimai ne ta ko'ina suka zo tararsu, hk suka qarasa gdn sarautar burham kai tsaye prince yyi umarni sumayya ta wuce da bimbii 6angarenta, hkn shine ya kawo tarnaqi cikin gdn don 6angaren sarauniya yakamata a wuce da maijego da yaranta amma mirtsitsi prince ya take wannan al'adar yaqi bari a wuce da bimbii da jariranta sashin sarauniya, wannan abu ya hasala sarauniya sosai kuma ga ummu nana sai qara rura wutar lamarin take tana sake tunzura sarauniya mar'atussali, yanzu kam sarauniya ta soma zargin bimbii kan tana son mallake komai na gdn sarautar burham tunda gashi ta haifi yara uku kuma ta mallake zuciyar ubansu,wannan dalilin ne yasa ita ta koma bayan mijinta,babban prince tsoro yake kar maqiya su sake masa yankan baya shiyasa ya rufe idanunsa yyi hkn kuma yasa tsauri sosai a 6angaren bimbii, tsaurin dake 6angaren nata ma babu a nashi 6angaren, ita kanta bimbiin jariran nata na mata qamshin dan goma............
Littafin nan na kudi ne,idan kina da buqatar krtw biya #300 ta wannan acct...0100790419,alhaji shahida nasir,union bank,ki tura screenshrt na payment naki ta wannan layin....0704119580
Alkalamin Bintuu ne....
10/10/20, 1:12 AM - Anti qamshi🌷: *DAREN GOMA SHA HUD'U*🪔🪔
Written By Bintuu Seer
44
*If God destinied no one can say no*...........💕💕
Ammar,adeel,areef,sunayen babies din kenan, shagali akayi d'an gaske ita kanta sarauniya tayi rawar gani a sunan yaran duk da 6acin ran dake qunshe a cikin zuciyarta, wannan shagalin suna daya gudana a masarautar burham shine yasa y'an jaridu watsa lbrin haihuwar a kafafen yad'a labarai inda hkn ya fallasa asalin mafarin soyayyar prince akbar da bimbii ga y'an jaridu, wannan lbri jaridar OMAN ita ta soma wallafashi inda sauran jaridu da kafafen yada labarai na qasaahen larabawa suka dauki lbrin da zafi zafi, abunda ya qarawa lbrin armashi shine kasancewar bimbii baqar fata wacce itace baqar fata ta farko data ta6a hada jini da jinin sarautar larabawa kuma a masarauta mai qarfi, sannan yanayin challenges da soyayyar tasu ta fuskanta yasa tuni lbrin nasu ya zamto controversial a nahiyar larabawa, hkn shine ya janyo hnklin kafafen yada labarai na duniya suka soma buga wannan labari, wannan ya kasance wata daukaka babba ga bimbii don sunanta ya soma shahara yana fita a duniya, gdn tv na NYA su suka soma aika katin gayyata ga princess bimbii mata a gdn prince akbar saidai bata samu damar amsa gayyatarsu ba, musamman kungiya ta yan jaridu daga newyork sukayo tattaki har masarautar burham don ganawa da wadannan masoya, abunda yasa yan jarida suka daukaki lbrin sbd yadda suka ga jama'a sun karbe shi, first black woman as a princess in arab kingdom,just a wonderful, prince da princess sun amince sun zanta da wadannan yan jarida, suna musu tmbyoyi suna basu amsa cike da barkwanci, you ppl will imagine how bimbii speak fluent english during the conference, abun ya qayatar ya bada citta, bimbii kuka tayi sosai lkcin data hada idanu da tawagar yan jarida wai duk ita suke so ta musu mgn, bata ta6a zaton cikin rayuwa Allah ze mata irin wannan daukakan ba, sarauniya mar'atussaliha kuwa yau da dare ta kira wasu yan mata biyu daga cikin kuyanginta su mata rakiya tana son taka qafafunta ta zaga wannan gd,tana tafe suna binta a baya har suka yanko wani wurin da babu yalwar zirga zirgar bayi, hango ummu nana tayi suna mgn da uxair irin mgnr qus qus din nan can nesa daga inda suke, ummu nana sam batasan sarauniya ta fito zagayen shan iska ba, mamaki tayi sosai,sauya hanya sarauniya tayi suka bi ta baya, tun daga lkcin sai sarauniya ta soma sanya idanu kan shige da ficen ummu nana har ta sanya wata baiwa mai suna jalila ta bibiyi mata lamarin ummu nana, jalila ta zamto tana saka idanunta sosai kan ummu nana har kunnenta ya jiyo mata wani babban sirri, jiki na rawa ta isa ga sarauniyya ta zayyana mata abunda taji ummu nana na fada ita da uxair, ba wani zance bane sai na poisoning jaririn bimbii na farko da sukayi cikin ruwan wanka, shiru sarauniya mar'atussaliha tayi sai lkcin ta fahimci abunda ya hana prince akbar kawo yaransa 6angarenta wataqila shi yana zargin da sanin mahaifiyarsa aka cutar mata da yaro,wannan tunanin sarauniya duk abu ya dameta zuciyarta tayi baqi tunanin irin hukuncin daya kamata ta dauka kan ummu nana take na wannan cin amana data mata.
10/10/20, 1:12 AM - Anti qamshi🌷: 45*****
NIGERIA QASARMU TA GADO....waiwayen baya..
Rugar lamido tana cikin jihar gombe ne, ruga ce ta fulani kuma babbar ruga ce sosai wanda cigaba ya soma qarasawa wurin,malam abba shine mahaifin bimbii wadda suke kira baffi sai mahaifiyarta halima ita kuma suna kiranta da inno, bimbii asalin sunanta khadijah sai yayarta mai suna hauwa'u wacce tana aure a gdn uban rugarsu wato hardo, sai kuma lamido wanda yake dan qanin mahaifinta amma ya taso a gdnsu ne, lamido yaso bimbii tun tana zanin goyonta,lkcin data fara wayyo shaquwa sosai ta shiga tsakaninsu bacci kadai ke rabasu, wani lkcin hk take binsa kiwo yana kiwo tana masa waqa, lkcin data fara zama budurwa ta sai ta dena binshi kiwo saidai tabi yan matan ruga su tafi tallan nono, bimbii tayi tashen farin jini wanda hkn yasa lamido yyi saurin furta mata so don kar garin kallon ruwa kwado yyi masa qafa, yasha wahala kafin ta yarda dashi duk kuwa da shaquwar dake tsakaninsu, wata rana hamma isuhu wato wan inna dake zaune a birni yazo yaga lamido ya nemi baffi yabar lamido ya bishi birni yyi ya sanya shi krtun boko, sam baffi yaqi amincewa da wannan zance don ganin boko yake tamkar kafirci ko ficewa daga addini, wannan yasa hamma isuhu ya koma birni batare da lamido ya bishi sai da aka sake daukar dogon lkci ya sake zuwa ruga nan ma ya sake roqar alfarma wannan karo be ambaci karatun boko ba sai yace ya samar masa wani aiki a birni, dakyar da taimakon inno baffi ya kyale lamido yabi hamma isuhu birni, suna zuwa birni kuwa lamido ya nuna yana da sha'awa a karatun nasara, hamma isuhu kuwa beyi shawara da kowa ba ya miqa lamido mkrtr boko, lamido baya jimawa bezo ruga ba sbd bimbiinsa amma duk da hk be nunawa baffi ya shiga mkrtr boko ba, zuwan sa na qarshe ne ya bata wannan tsohon zoben kan tayi alqawarin bata barinsa komai rintsi ta riqe amanar soyayyarsa tayi masa wannan alqawari itama ta bashi nata zoben wanda har kwanan gobe yana hannunsa be cire ba, be jima da komawa birni ba wannan qaddarar ta 6acewar bimbii ta afku, ranar talata qungun yan mata fillon daga rugar lamido cikin har da bimbi suka shiga kasuwar jalla tallan nono, wurin qarfe shida kowaccensu ta saida nononta suka hawo akori kura ta saukesu a bakin qaramin kogi wanda sai sun tsallakeshi zasu dauki hanyar shiga rugar lamido, kwale kwale suka hau sannan suka soma ratsawa ta cikin gonaki sai sauri suke don magriba ta qarato, kunsan ance qaddara ta riga fata suna dab da shiga rugarsu kowacce dauke da kwaryar nononta akanta motar turawa masu kwasar bayi tasha gabansu, tsayawa sukayi suna kallon motar cike da fargaba har lkcin da wadannan turawa suka fito sanye suke da hula malafa, wani daga cikin turawan fuskarsa dauke da baqin tabarau ya ba blacks din dake tare dasu dama kan su kama yan matan fillon su sanyasu cikin mota, yan matan fillon na ganin hk wasu daga cikinsu suka yada kwaryoyin nonon dake kansu suka fada cikin gonaki da gudu suna 6uya a dogayen tsiron masara, sunyi nasarar chafke wasu shida daga cikinsu har da bimbii sauran kuma Allah ya basu sa'ar tserewa sune suka kai wannan lbri cikin ruga, hnklin iyayen wadannan yan mata ya tashi mutuqa musamman da suka ga kwanaki sun soma ja babu labarin ganinsu, baffi da inno da hauwa'u kwatanta tashin hnklin da suka shiga ma 6ata lkci ne, lamido kam yana birni bashi da lbrin 6acewar bimbii saida ya dawo yaji wannan mummunan lbri wanda takaisa da kwantawa cuta, saida ya shafe makonni a kwance kafin Allah ya bashi lfy ya rumgumi qaddara, wannan shine silar fitowar bimbii duniya,bari mu dawo kan lbrinmu,,,,
Inno tana saida da qosai da safe yau kamar kullum da safe ta fito tsakar gd ta kunna murhu ta dora kaskon suya ta soma zubi, wani yaro mai suna iro ne ya shigo yace" inno ki sawa adda jamila na sittin a kaskon farko" tace" toh" janyo tsohuwar jaridar dake gefenta tayi ta buda zata yago shafin ta zuba qosai ciki idanunta yyi tozali da hoton wata mace mai kama da diyarta sak, qurawa hoton jaridar idanu tayi taga matar tana riqe da hannun wani kyakykyawan balarabe, sosai take kallon hoton zuciyarta na wani irin dokawa, hannunta sai karkarwa yake ta miqe da sauri har tayi kamar zata 6arar da qullin qosan ta soma kwalawa baffi kira a rikice, yana cikin rumbu ya jiyo wannan kira da take masa tamkar bana lfy ba ya fito a dan firgice, tana ganinta ta nufo inda yake hannunta riqe da jaridar ta kalleshi muryarta na rawa tace" malam dubamin wannan hoton dake wannan jarida ka gani" amsar jaridar yyi yana kallon hoton bimbii da yan jarida suka daukesu hannunta sarqe cikin na prince, fuskarta dauke da murmushi , sosai ya gano tsantsar kamanni wannan mace da diyarsa data 6ace amma zuciyarsa bata kawo wannan itace bimbiinsu ba sbd karma su yaudari kansu, dago idanu yyi ya kalli inna yace" naga kamar suna yanayi da diyarki" tace" yanayi kawai toh wallah wannan diyata ce" murmushi baffi yyi yace" lalle kam, ki dawo cikin hnklinki wannan balarabiya ce ba bafulata na ba" mayar dakanta tayi tana sake kallon jaridar shi kuwa baffi ya wuce ya nufi wurin turken shanunsa yana tsatsar nono, inna shigewa tayi daki ta cusa wannan jaridar qasar adaka tana son lamido yazo ya krt mata abunda ke rubuce cikin wannan jarida..............
Littafin nan na kudi ne, idan kina da buqatar krtw zaki tura #300 ta wannan acct..0100790419,alhaji shahida nasir,union bank saiki tura screenshrt a whatsapp ta wannan layi...07041195806......
Alkalamin Bintuu ne....
10/10/20, 1:12 AM - Anti qamshi🌷: *DAREN GOMA SHA HUD'U*🪔🪔
Written By Bintuu Seer
46
*LOVE IS SWEET,LOVE IS BITTER*💕💕
angaren maheer kuwa jikin nasa babu laifi har sun koma gd amma ba gdnsa ba gdn ennah, 2kwata rayuwarsa ta sauya ya koma wani irin miskili 2shiru baya shiga sabgar kowa, duk lkcin kuwa daya samu ke6ewa shi kadai sai yyi ta zubda da hawaye shi kansa besan wani irin mugun so yake yiwa bimbii ba,tabbas soyayya tayi masa mummunan kamu, idan ya rufe idanu fuskarta kawai yake gani, likita yace a dena barinsa ya ke6e shi daya sbd wannan tunanin dayake yawan yi kan iya haddasa masa bugawar zuciya farat daya tayi ajalinsa hknne yasa ennah fitowa ta taddashi a parlour shi kadai, wurin tv ta nufa ta kunna masa tashar NYA sbd kallon labaran ya debe masa kewa, kitchen ta shiga ta yanka masa fruit a wani bowl ta fito ta jawo wani stool gabansa ta ajiye masa bowl din fruit din ta koma ta zauna ta sanya siririn medical glass nata tana duba wasu documents, maheer yana shan fruit din a hnkli yana kallon labaran da ake a tasha NYA daidai lkcin suka hasko prince akbar sanye yake da alkyabba golden da farar jallabiya ciki sai rawani fari sol, sajen nan nasa yasha gyara fuskarsa dauke da murmushi, 2kalan hotunansa suka cigaba nunawa suna bada lbrin aurensa da kuma kyautar yan uku daya samu daga princess dinsa wacce take baqar fata daga daga africa, hkn shine yasa ennah dago dakanta ta kalli maheer da dukka attention nasa yana kan labaran tace" yanzu duk isa da qasaitar prince akbar a baqar fata ya qare yana jinin sarautar burham,one in history" kallonta maheer yyi yace"ra'ayinsa kenan kuma ai yana sonta ne shi so ba ruwansa da kalar fata" shiru tayi ba tace komai ba ta maida kanta ta cigaba da bin document din dake hannunta shima ya cigaba da kallonsa daidai lkcin suka fara nuna hotunan bimbii da prince, dukkanin hotunan nasu yana bayyana tsantsar soyayyar dake tsakaninsu koda daga yanayin kallon dake kwayar idanunsa suna jifan junansu, ya daga cup din ruwa kenan ze sha idanunsa suka sauka kan hotunan take glass cup din dake hannunsa ya fadi qasa ya tsaida idanunsa akan screen din tv baya ko blinking sai kawai zuciyarsa dake bugawa da qarfi tamkar zata tarwatse,qarar fashewar cup din ne yasa ennah dago dakanta tana kallonshi, gani tayi ya qure tv da idanu sai ta maida kallonta kan tvn, abunda ta gani ne itama yasa ta saurin watsar da takardun dake hannunta ta miqe da sauri ta wuce ta kashe tvn, juyowa ta matso inda yake ta dafashi kawai sai gani tayi ya fadi kan kujerar cikin sauri ta soma girgixa shi baya koh motsi, fashewa tayi da kuka gbdy ta rude ta cigaba da jijjigashi tana kiran sunan shi amma inaaa, tashi ta janyo telephone ta dannawa faisal kira yana dauka yaji kukanta tana tace" kazo gd maheer ya mutu" kalmomin data iya fada kenan ta kife kan telephone din ta koma wurin da maheer yake tana jijjigashi kamar wata mahaukaciya duk ta fice daga hayyacinta don ba qaramin son yara ne da ita ba, ba jimawa faisal ya shigo ya tarar da halin da dan'uwansa ke ciki shima hnklinsa ya tashi sosai hk suka fito dashi suka saka shi cikin mota suka nufi hospital, cikin hanzari aka wuce dashi emergency sbd ya shiga coma sosai, sai dare likitoci sukayi samu zuciyarsa ta soma bugawa a hnkli, likitan daya fito ya fara fada sosai yana cewa meyesa suka bari hk ya faru yace tabbas yaci karo da abunda ya tada hnklinsa ne shine silar bugawar da zuciyarsa tayi yanzu dai yana cikin wani hali wanda saidai kawai addu'a amma abun yyi tsanani, wadannan kalamai su suka qara daga hnklin ennah ta kifa kan a jikin faisal tana kuka kamar ranta ze fita,gani take kamar mutuwa maheer zeyi gashi dai su biyu kawai Allah ya bata kundai san larabawa da shegen son y'ay'an tsiya, faisal mai dan qarfin halin rarrashin mahaifiyar tasu shima dai kaeai shanye kukan nasa yake, tace" tabbas rashin sani yafi dare duhu idan da nasan yariyar nan itace muguwar qaddarar maheer mezai sanya na siyeta da kudi na, gashi yanzu tana son kashemin yaro" hk dai tayi ta maganganu faisal na rarrashinta,6angaren masarautar burham kam gimbiya mariyatul qifdiya ta sato jiki ta taho masarautar burham burinta kawai ta sake tozali da prince akbar bazata iya jure rashinsa ba, sarauniya ta mata tarar girma sosai, sarki abdallah yana kwance har yau jikin nasa qara tsanani yake sbd tarin damuwa dake addabarsa, kullum cikin tunanin hanyar dazai bi ya yakice bimbii daga masarautarsa yake duk kuwa da halin rashin lfyr dayake jiki,lkcin da lbrin zuwan gimbiya mariyatul qifdiya ya kawo gare shi be bata lkci ba yyi umarni a rubuta wasiqa a aika masarautar abu ansar kamar yadda shima ya aiko masa da zafafan kalmomi hk shima ya aika masa batare da sanin sarauniya don itakam bazata so hk ba sbd mariyatu ta sanar mata mahaifinta besan ta taho ba, lkcin da sarki abu ansar ya krt wasiqar nan ransa yyi masifar 6aci don cikin wasiqar sarki abdallah ya fada masa jinin sarautar burham suna da cikakkiyar izzah da basu bibiya saidai a bibiyesu hknne yasa yarsa tayi tattaki har gdn sarautar burham don samun soyayya mafi girma, wannan batu ya 6atawa sarki abu ansari rai yyi Allah wadai da abun da diyarsa ta aikata, sanyawa yyi aka kira masa gimbiya khamriyya ya soma mata fada kan dalilin dayasa ta kyale gimbiya mariyatu ta aikata wannan abun kunya don ta zubar masa da mutunci da tozarta izzar masarautar abu ansar, sunkuyar dakai gimbiya khamriyya tayi tace" Allah ja zamanin sarki mai daraja tabbas mariyatu tana qaunar yarima akbar dayawa wannan shine dalilin dayasa ta kasa jure hukuncin daka yanke ta nufi masarautar burham batare da sanin kowa ba, ina roqon alfarma a gareka sarki mai daraja kar ka sauke fushinka akanta bisa wannan laifi data aikata mafi muni" shiru yyi ya juyar dakansa tare da daga mata hannu ta miqe jiki a sanyaye ta fice.........
Manage this page pls.
Littafin nan na kudi ne, idan kina da buqatar krtw toh ki biya #300 ta wannan acct...0100790419,Alhaji shahida nasir,union bank, saiki turon da screenshrt na payment ta whatspp ta wannan layi....07041195806...
Alkalamin Bintuu ne......
10/10/20, 1:12 AM - Anti qamshi🌷: 47*****
Cikin hadiman da suka rako mariyatul qifdiya masarautar burham har da ramlatul aswat,sarauniya dakanta ta shirya rana da kuma lkcin da prince akbar ze gana da mariyatu don musamman wurin shi tazo, sarki abdallah yana halin jin jiki amma hk yasa akayi masa kiran prince, yana shiga ya tadda mahaifin nasa a kwance, dago dakai sarki abdallah yyi ya kalli prince, muryarsa a hnkli mai nuni da yana jin jiki yace" alfarma ta qarshe da nk nema wurinka shine auren gimbiya mariyatul qifdiya,tun farko itace daidai dakai itace ta dace dakai ta fito daga gdn izzah tamkar yadda kaima ka fito sannan yarenku daya kalar fatarku daya da itace ta haifamin jikoki dana fi kowa farin ciki saidai kash yaran sun fito ne daga jinin qasqanci wanda har qasa ta rufe idona bani ta6ar amsarsu a matsayin masu gadon sarautar burham, wannan shine kuskuren daka tafka cikin rayuwarka kuma da sannu zakayi nadama" shiru babban prince yyi yana sauraron mahaifin nasa, atishawa yyi har sau uku sannan uxair ya taimaka masa ya koma ya kwanta daidai zuciyarsa cike daci duk lkcin daya tuna da auren qasqantacciyar baiwa baqar fata da d'ansa yyi gashi har ta fara yad'o cikin zuri'arsu wannan abu ya sanya zuciyarsa ta shiga qunci,tashi prince yyi duk jikinsa a sanyaye ya fita, ubaid ne ya rufa masa baya suka wuce 6angaren sarauniya, prince ya shiga ya gana da ita take umartarsa daya shirya da dare don ganawa da gimbiya mariyatul qifdiya batare jan wani zance ba ya amsa mata da toh, hk itama ya fito daga wurinta ya nufi yankinsa, yana shiga ya wuce lambunsa, ranar be koma 6angarensa da wuri ba yana cikin lambunsa, bimbi kuwa tayi jiran nasa har ta gaji sai ta koma yankinta, tun jiya ta sami lbrin zuwan gimbiya mariyatu daga bakin sumayya sosai zuciyarta ta harba cike tsoro ga wani kishi daya taso mata ya cika qirjinta, miqewa tayi ta nufi babban kitchen duk ta inda ta ratsa bayi ke sunkuyawa suna kwasar gaisuwa cike da girmamawa sumayya na biye da ita har suka qarasa babban kitchen, honey mist ta hada masa ta juye ciki qasaitatttun mazubi ta dora akan faranti ta dauka ta fito suna tafe har 6angaren prince,shiga ciki tayi a hnkli ta wuce ta ajiye farantin hannunta kan wani table ta duba ta hango shi kwance a saman royal bed nasa, curtains din kusurwar duk a sake,takawa tayi ta nufi wurin ta daga shara sharan milky curtains daya rufe kusurwar da gadon ke ciki, hawa tayi gadon ta kalleshi sosai taga idanunsa a lumshe kamar bacci yake, sauka ta soma qoqarinyi kar ta tashe shi, hannu yasa ya riqota ta juyo tana kallonshi yace" ina kuma zakije" murmushi tayi ta matsa kusa dashi, folding hands nasa yyi a qirji batare daya tashi ba ya qureta da idanu ita har ta saba da wannan maitar kallon nashi,cire hannunsa tayi daga saman qirjinsa ta kwantar dakanta a saman qirjin nasa tayi bottoning rigan bacci dake jikinsa tana wasa da qashin chest nashi, hannu yasa yaja dogon gashin kanta tayi saurin dago idanu ta kalleshi yace" kina sona dayawa kuwa kamar yadda nk sonki" kunya taji amma sai ta daure ta matso da fuskarta kusa da nashi tace"kana shakku ne?" murmushi yyi ya nuna mata pinkyred lips nashi yace" prove it here" hararar shi tayi cikin wasa tana yar dariya, dora lips nata tayi kan nashi ya wani lumshe ido yana jiran yaji tayi kissing nashi sai jinta yyi ta kama lips din nasa tadan ciza yyi saurin bude idanu ya wani marairace fuska kamar ze mata kuka, bude baki yyi da shirin yin mgn ta toshe masa bakin da nata, rikito da ita yyi jikinsa sosai ya soma nuna mata yadda abun yake don shine malaminta daman, kwantar dakanta yyi a chest nata ya rufe idanu, can ya soma mgn a hnkli yace" kiyi hkr dani kuma ki fahimce ni sosai, mahaifina ya umarceni dana cika alqawarin daya daukarwa gdn ansar kan batun auren gimbiya mariyatu" bimbii jin gabanta tayi ya yanke ya fadi duk wani annurin dake fuskarta ya 6ace lkci daya don tana da kishi, shiru tayi bata furta komai ba hknne yasa shi dago idanu ya kalleta, sakin fuskarta tayi har da dan murmushi tace" baka da mtsl Allah ya taimaka yasa alheri" qura mata ido yyi yana son gano gskyr abinda ke qunshe cikin zuciyarta shin ta amshi zancen da hannu biyu, saurin miqewa tayi ta sauke kansa dake jikinta a hnkli tace" bari na fita ina son motsa qafafu na" shiru yyi ya bita da kallo sai kuma yace" ki shiryani ina son naje mu gana da ita din" wani irin malolon baqin ciki ne ya chaketa tuni idanunta sukayi jajir amma sai ta juya ta kalleshi da murmushi tace" ok, toh muje ka shirya" miqewa yyi ya bita a baya har dakin da kayansa ke jere ta za6o masa wata jallabiya fara sol da rawani mai ja da fari ta sanya masa yyi kyau sosai ta feshe shi da turaruka masu sanyin qamshi, murmushi tayi wanda bekai zucci ba tace" ka qara kyau sosai" shiru yyi yana kallon kwayar idonta wanda shi zallar kishinsa kawai ya hango kwance a kwayar idonta amma ita a hkn wai basaja take, murmushi yyi ya manna mata peck kumatu, tsayawa tayi tana kallonsa wani lkcin tana rasa gane kan babban prince, shi kuma a nashi 6angaren yana so yaga bimbii ta nuna wani alama dake nuna tana son shi dayawa kamar yadda shima yake sonta yanzu daya ga kishin shi tsantsa cikin kwayar idonta sai abun yyi masa dadi,6oye kishin nata data take qoqarin yine yasa shi murmushi, prince natural love yake mata baya hada soyayyarta dana wata mace coz itace first love nashi kuma har yau be ta6a son wata mace bayanta ba, wuceta yyi cikin takunsa na birgewa ya fita, ubaid ya take masa baya har lambun sarauniya, anan ya tadda gimbiya har ta riga shi zuwa lambun, yana shiga ta dago dakanta tana kallon shi, batare daya kalleta ba ya zauna gefenta, murmushi tayi tace" barka da wannan lkci ma'abocin haiba" shiru yyi bece mata komai ba, tace" nazo don isar da saqon ruhi ne" nan ma dai ya mata shiru, batayi qasa a quiwa ba kuma batayi zuciya ba ta fara fallasa masa sirrin zuciyarta, shi mamaki ne ya cika shi yadda yaga tayi kuma ya fahimci feeling nata coz shima victim ne, karon farko ya kalleta cikin murya mai cike da izzah yace" nagode" ita sam bata gane mai yake nufi ba taga ya soma takawa a hnkli ya fita daga lambun ta bishi da idanu dayake so makaho ne batayi fushi ba,bimbii kam zuciyarta na suya ta koma yankinta,saida ta leqa dakin yaranta da amitacciyar hadima halimatu ke rainonsu sannan ta cike cikin wurinta, dagawa sumayya hannu tayi alamar tana son kadaici, fita sumayya tayi ita kuma ta kwanta a qaton gadonta tana wani tunani, ita dai tasan ba kowan kowa bace face baiwa kuma wacce ta fito daga nahiyar baqar fata qaddara ta qaddaro aurenta da babban prince batare da son ahlinsa ba yanzu yaya zata iya kishi da yar sarki, gani take kamar tayi dage daman can dan sarki ai da yar sarki ya dace ba irinta ba, kuka ta fashe dashi sosai idanunta yyi luwu luwu, kanta ya soma ciwo, maheer yana bude idanu sunan bimbii yake kira kamar wanda ya zautu ya dukan qirjinsa, yace" why,why? me na miki da zafi hk da kk za6i ki hukunta zuciyata ta wannan siga,I hate you, I hate you" sai sambatu yake har saida likita yyi masa allurar bacci tukun,ennah ta zuba masa idanu kawai tana mamakin wannan abu, bangare guda kuma mamaki take da kuma shakku gani take kamar ba bimbii bace ta gani a tv da prince akbar, gani take tayaya hk zata faru wannan qasqantacciyar baiwa ta auri prince guda abu kamar al'mara.....
***
Inno bata sake yiwa baffi wannan batu na yarinyar data gani a jarida ba amma kullum saita fito da wannan jarida tana kallo, duk wanda ta nunawa jarida tace wannan diyarta ce bimbii sai ayi ta mata dariya, dayake lamido yana birni burinta Allah ya dawo da lamido daga birni lfy ta nuna masa jaridar ko shi ze iya shaidata tunda kowa ya maida ita abun dariya hatta hauwa'u murmushi tayi lkcin data nuna mata hoton jaridar tace" haba inno ki cire damuwa a ranki kibar damun kanki tayaya wannan zata zama bimbii wannan fa balarabiya ce saidai kawai kama kuma kowa dama yana da mai kama dashi cikin duniya" shiru inno tayi ta miqe ta shige daki ta sake adana wannan jarida don ita a haqiqanin gsky ta aminta wannan diyarta ce, bayan sati biyu kuwa Allah ya kawo lamido,sosai inno tayi murnar ganinsa ya gama krtunsa ya soma koyarwa a polytechnic, fura ta kawo masa a wata qaramar kwarya ta shimfida masa tabarbar kafa a tsakar gdn ya zauna ya soma shan furarsa, baffi ne ya shigo ya gansa, cikin farin ciki yace" madallah da mutan birni" dariya lamido yyi ya gaida baffi cike da girmamawa, hk suka soma hira da baffi har aka kira sallar la'asar suka tashi suka nufi masallaci, bayan sun dawo ne baffi ya tsaya kofar gd yana sauraron radionsa shiko lamido ya cikin gd, yana shiga ya tadda inno zaune tana jiran shigowarsa tana ganinsa ta miqe ta shiga daki ta fito da wannan jarida ta miqa masa tace" dubamin wannan hoto ka gani kuma ka karantomin abunda ke rubuce jiki" amsar jaridar yyi yana yar dariya ya bude jaridar,gabansa yyi mugun bugawa lkcin da idanunsa suka sauka kan fuskar bimbii dake murmushi, numfashinsa ya tsaya na wucin gadi ya qurawa hoton idanu........
Littafin nan na kudi ne, idan kina da buqatar krtw zaki tura #300 ta wannan acct..0100790419,alhaji shahida nasir,union bank, saiki tura screenshrt na payment naki ta whatsapp ta wannan layi....07041195806....
Alkalamin Bintuu ne��
10/10/20, 1:12 AM - Anti qamshi🌷: *DAREN GOMA SHA HUD'U*🪔🪔
Written By Bintuu Seer
48
*My world is empty without you dear*.........pure love and natural💕💕
Tashi guda idanunsa suka sauya launi,sunansa dayaji inno ta kira ne yasa shi dawowa hayyacinsa ya dago dakansa a hnkli yana kallonta, kallonsa take sosai tana fahimtar sauyawarsa murya a hnkli tace" me aka rubuta a jikin jaridar" jirin ya soma ji yana dibarsa cikin dabara yyi saurin neman saman turmi ya zauna yq kalli inno yace" shi wannan wani dan sarki ne a nahiyar larabawa wannan kuma mai kama da khadija matarsa ce" saurin kallonsa inno sai kuma ta amshi jaridar tana kuma kallon jaridar tace" kace shi wannan balaraben dan sarki ne kuma ita wannan matarsa ce?" daga mata kai, tace" amma ita wannan din tayi kama sosai da qanwarka khadija shiyasa na ajiye jaridar nace zan nuna mk yanzu daka ce wannan din dan sarki ne daga nahiyar larabawa kuma wannan din matarsa ce nasan ta bakin malam ne ba qanwarka bace wannan yanayin su ne dai daya, ina khadija ina auren dan sarki kuma jinsin larabawa" lamido shiru dai kawai yyi shima zuciyarsa taqi amincewa wannan macen bimbii ce, kallon inno yyi da sauri yace" ina sauran shafikan jaridar suke ina son krt cikakken labarin ne kodan albarkacin wannan mai kama da qanwata" inno tace" kayy,ashha wallah iya wannan shafin dake dauke da hoton kawai na cire na zuba qosai a sauran shafikan" miqa hannu yyi ya kuma amsar wannan shafin yana qara kallon hoton,zuciyarsa na kuma dokawa amma har yanzu yaqi barin zuciyarsa ta aminta wannan bimbii ce taya ma hk zata faru, dayake jaridar ba cikakkiya bace babu cikakken labarinsu saidai kawai highlights, inno komawa tayi gindin murhu tana hura wutar da zata dora tuwon dare don magriba ta soma kunno kai, ninke jaridar yyi ya cusata cikin aljihun wandonsa ya miqe yace" inno ni zan wuce gdn yadikko" dago dakai tayi tana kallonsa tace" haba mn baka tsayawa kaci tuwon dare kafin ka tafi can din" murmushi yyi yace" karki damu zan shigo bayan isha'I" tace" toh shikenan saika shigo din ka gaida mutan gdn" yace" zasu ji" fita yyi duk jikinsa wani irin tunanin hoton wannan mace dake wan ga jarida yake kamarsu da bimbii har ta 6aci saidai kawai wannan tana da hasken fata fiye da bimbii" duk da wannan tunanin dayake still zuciyarsa na gauraye da shakku da kuma tarin rudani kan wannan abu hk, tafe yake yana zancen zucci har ya qarasa gdn mahaifiyarsa yadikko, qiris ya rage yaci karo da dattijo wato mahaifinsa, fitowarsa kenan daga cikin gd hannunsa riqe da buta zeyi alwala don ana gab da kiran sallar magriba, sauri yin qasa yyi ya gaida mahaifin nasa, kallonsa dattijo yyi sosai don yanyinsa ya tabbatar masa kamar ba daidai yake ba amma be masa mgn kan hkn ba sai ya amsa gaisuwar kawai ya tsuguna ya soma alwala, miqewa lamido yyi shima ya shige cikin gd don dauko buta ya gabatar da nasa alwalan, tare da dattijo suka tafi wuce masallaci, ranar komai cikin sanyi yake don zuciyarsa ta kasa dena kawo masa tunani 2kala..........
***
Washegari bimbii ta shirya ita da yaranta sunyi masifar kyau da kwalliya kalar birgewa, israt, khulood da sumayya dukkaninsu suna riqe da ammar,adeel da areef tare da rakiyar wasu bayin nata suka take mata baya zuwa yankin sarauniya don ranar sarauniya take gudanar da biki na musamman kan title din da masarauta tayi mata na *UMMU BURHAM* bimbii ta shirya tsaf don halartar wannan qasaitaccen taro da aka shirya wanda ya qunshi manya jiqaqqun mutane dake taqama da izzar sarautar masarautar burham har ma da baqi na musamman mariyatul qifdiya na daya daga ciki,
duk ta inda suka qetare cikin wannan gd bayi zubewa qasa suke suna miqa gaisuwa gareta sai ta wuce suke miqewa,kunsan dai salon takunta mai yanayi da na qasaita a hk ta qarasa yankin sarauniya tare da tawagarta, suna zuwa wajen babban hall din taron, bayin dake tsaron kofa sukayi saurin wangale musu kofa suka taka cikin qasaitacce dakin taron, jinin izza kowa na zaune kan mazaunin alfarma bimbii ta shiga bayi uku na take mata baya dukkaninsu riqe da babies a cikin fararen towels sauren bayin nata kuma sun dakata daga kofa, tunda bimbii ta shiga wurin kowa yyi tsit tamkar sarki dakansa ne ya shigo,prince dake daga kujerun sama kusa da mahaifiyarsa sanye yake cikin wasu fararen kaya rawaninsa ma fari qal hatta takalmin kafarsa mai kafar half cover fari ne, qure bimbii yyi da idanu sbd wani kyau da haiba data qara masa ita yake gani ta haske dukkanin wurin don shikam idanunsa basu gane masa macen data darata kyau ba, ita kanta sarauniya bimbii ta birgeta tuni taji tana alfahari da ita cikin taron, ita kuwa gimbiya mariyatul qifdiya ta kasa dauke idanunta kan bimbii kawai kallonta take har bayinta suka gyara mata wurin zama ta zauna, gimbiya hindu kuwa mamaki bimbii take yadda taga tayi tamkar daman can tayi gadon sarauta ne komai nata cike da izzah tamkar ba jinin bayi ba, ramlatul aswat kuwa dake tare da gimbiya mariyatu? qamewa tayi a tsaye sbd tsantsar mamakin bimbii a wannan masarauta kuma a matsayi mai girma na matar babban prince, ita dai tasan bimbii a matsayin baiwar data tura turakar jira daga baya kuma hadiman gdn yaseer bin walid suka tafi da ita kan gudajjiyar baiwa ce, toh meke faruwa ne? tmbyr data yiwa kanta kenan ta qara kallon 6angaren da bimbii ke hakimce cike da mamaki da daurewar kai, bimbii ita kanta tasan akwai tarin yan adawanta a wannan wuri hknne yasa ita take nuna cikar izza yadda ya kamata sbd ta basu abun fada, aikuwa kam ta raba musu abun fada, a hk taro ya soma amitattun hadiman dake wurin suka soma raba abubuwan sha cikin hadiman dake dawainiyya a wannan wuri har da lenah tsohuwar baiwa ga babban prince, daukan abun sha tayi a wani faranti na alfarma ta haura tudun da prince ke zaune a wata qasaitacciya kujera ta ajiye farantin a saman hadadden table din dake gabansa tana shirin tsiyaya masa ruwan inibin a qaramin cup yyi saurin daga mata hannu alamar ta ajiye taje, daidai lkcin suka hada idanu da gimbiyarsa ya kashe mata ido tare da mata inkiya ta qaraso tayi aikinta don itace komai nasa, tuni ta ankara da abunda yake nufi, qoqarin miqewa tayi sumayya tayi saurin gyara mata mayafinta, tashin nata sai ya kuma janyo idanu kanta, bata damu da idanun dake kanta ba ta soma takawa taku irin na qasaita da cikar izza koda ta fitar da prince dinta kunya har ta soma hawa steps ta wuce inda prince ke hakimce, tunkan ta qaraso yake murmushi har ta qarasa, rissinar dakai tayi a gabansa sannan ta sunkuyawa ta soma tsiyaya masa ruwan inibi a cup din ta sanya hannu biyu tare da rissinar dakanta qasa ta miqa masa cup din hannu ya miqa ya hada cup din da hannunta ya riqe tayi saurin janye hannunta sbd kar su wuce gona da iri a gaban suruka, ita tasan wani abu wai kunyar idon suruka sukam basu san shi ba, sake riqo hannunta yyi yana gyara mata mayafi, bimbii ji tayi tamkar ta nutse a wurin don kunya sbd prince ya gama bata kunya, jikinta ya bata kowa kallonsu yake, bata ankara ba taji ya miqe ya matso kusa da inda take ya manna mata light kiss a goshinta sannan ya koma ya zauna, yadda yaga ta rissinar dakanta yasan kunya taji shikam ko a jikinsa, toh meye don ya nunawa duniya abunda mutuqar so da qauna, dakyar bimbii ta iya sauka daga step din, sumayya dake tsaye ta take mata baya ta koma mazauninta, wasu dake wurin tuni sukaji soyayyar nasu ta birgesu suka soma tafawa a hnkli kuma sai dukka wurin ya dauki tafi, murmushi sosai sarauniya mar'atussaliha tayi sbd ba prince kadai bimbii ta fidda kunya ba har da ita kanta bimbii ta fiddata kunya ta nuna izza yadda ya kamata irinta ta jinin sarautar burham,fuskarta ta cika da annuri, idanunta ne yakai kan ummu nana ta saci jiki ta fita, da ido ta yiwa wata baiwa alama tayi hanzari bin bayan ummu nana,hk taron nan ya gudana wasu zucciyoyi fal da farin ciki wasu kuma suna cike da baqin ciki, gimbiya mariyatul qifdiya tayi dana sanin halartar wannan taro, jin zuciyarta take tamkar zata fashe ga wani azababben kishi dake taso mata tamkar zeyi ajalinta, bayan kammala taron ne ta wuce masaukinta kanta har wani juyawa yake, a gabanta mutumin da take yiwa haukar so yyi kissing wata mace cike da farin ciki da annushuwa wanda ita bata ta6a ganin hk tattare dashi ba, ashe prince ze iya yin hk ga mace amma ita magana ma dakyar yake mata dukda kasancewarta jinin sarauta amma sai gashi ita bata samu hk daga gare shi sai wata qasqantacciyar baiwa mara asali da tushe, tana ciki ramlatul aswat ta shigo ta durgusa gabanta tace" ranki ya dade wato nikam akwai abunda ya bani mamaki a wannan masarauta" kallonta gimbiya mariyatul qifdiya tayi fuskarta ba annuri ko kada tace" kiyimin mgn kai tsaye" sake rissinar dakai ramlatul aswat tayi tace"game da wannan uwar izzar dana gani yau a matsayin mata ga wannar dan sarki ba wata bace wannan face qasqantacciyar baiwa wacce na tura turakar jira" saurin tashi zaune gimbiya mariyatu tayi tana kallon ramlatul aswat tace" kina nufin kice baiwar masarautar abu ansar ce ita" tace" tabbas babu qarya cikin zance na itace wacce suwaiba ta za6a ta tura ga wannan dan sarki lkcin daya kai ziyara masarautar abu ansar" cike da tsagwaron mamaki gimbiya mariyatu ke kallon ramlatul aswat, kai tsaye ramlatul aswat ta labarta mata yadda akayi bimbii tabar masarautar abu ansar, shiru mariyatul qifdiya tayi tana auna lamarin don gano bakin zaren, kallon ramlatul aswat tayi da sauri tace" ina son kiyimin cikakken bincike kan al'amarin wannan mace" kada kai tayi alamar amsar umarni, daga mata hannu tayi ta miqe cikin sauri ta fita ita kuma ta dulmiya cikin kogin tunanin......
Littafin nan na kudi ne, idan kina da buqatar krtw ki tura #300 ta wannan acct..0100790419, alhaji shahida nasir,union bank, saiki turon da screenshrt na payment naki ta wannan layi...07041195806.....Idan da buqatar kira ga layin kira
08036598141
Alkalamin Bintuu ne��
10/10/20, 1:12 AM - Anti qamshi🌷: *DAREN GOMA SHA HUD'U*🪔🪔
Written By Bintuu Seer
49
*I love you without knowing how,when*.....what I really know is that I love you so much💕💕
Murmushi tayi batare data jira ramlatul aswat ta kawo mata sakamakon binciken data tayi kan bimbii ba ta hanzarta rubuta saqon takarda zuwa ga prince akbar ta aika daya daga cikin manyan hadimanta kan ya hanzarta isar da saqon takardar ga babban prince, batare da 6ata lkci ba wannan hadimi ya samu isar da wannan takarda ta hannu ubaid tabi kafin ta qarasa ga prince akbar, zaune yake bisa kujera yana shan ruwan inibi ubaid ya shiga masa da saqon takardar ya sanar dashi saqo ne daga gimbiya mariyatu, hannu ya miqa ya amshi takardar ya warware ya soma krtw kamar hk.....zuwa gareka yakai wannan dan sarki ma'abocin cikar izzah, tabbas nayi mutuqar mamaki da wannan mace ma'abociyar qasqanci ta zamto za6i gareka matsayinka na jinin girma, wannan mace dake tare dakai ba kowan kowa bace face qasqantacciyar baiwa wacce take a turakar jira take taron duk wanda aka turata ta tara, ko kasan kafin kai ta tari tarin baqinmu da wannan jikin nata dake rudarka dashi dai ta nishadintar da was....saurin dakatawa yyi da karanta wasiqar sbd wani irin abu daya taso masa tuni idanunsa suka sauya launi suka koma jajir yyi saurin jifa da takardan, ubaid dake tsaye gefe guda kansa a sunkuye yyi saurin dago da kansa yana kallonsa, bakomai ya gani tare dashi ba sai tsantsar 6acin rai daya jima be ga irinsa a fuskarsa ba, daga masa hannu prince yyi yaja da baya kafin nan ya juya ya fice cike da mamaki, daidai lkcin bimbii ta qaraso zata shiga 6angaren hannunta riqe da wani faranti na azurfa,ubaid na ganinta yyi saurin rissinar dakai qasa alamar girmamawa sauran bayin dake tsaye a bakin kofar suma duk suka sunkuyar da kawunansu ta taka a hnkli ta shige ciki, tana shiga ta hango 6arnar da yyi duk yyi watsi da abubuwan saman table din dake gabansa, yana zaune inda yake ya riqe kansa da hannu biyu, sauri tayi ta nufi wurin ta ajiye abunda ke hannunta kan wani stool ta matsa kusa dashi, tsugunawa tayi ta dora hannunta saman kanshi tana shafa sumar kansa yana jinta yaqi dago dakansa ya kalleta domin zuciyarsa tafasa take da muggan kalaman da gimbiya mariyatu ta fada kan macen dayafi so kuma yake tsananin kishi a duniya, ita kuwa bimbii batasan abunda ke faruwa ba ita dai taga ransa a 6ace, kwantar da murya tayi cikin sanyi tace" Allah ya huci zuciyarka sadauki na" dago da jajayen idanunsa yyi wanda ita kanta saida suka bata tsoro ta bishi da kallo har ya miqe ya wuceta ya fice abin shi, abun ya bata mamaki sosai tuni gabanta ya soma faduwa ta fara addu'ar Allah yasa dai lfy, shikam yana fita kai tsaye ya wuce lambunsa batare da rakiyar kowa ba, tunani ne 2kala ke kai kawo cikin zuciyarsa, tabbas yana son bimbii shiyasa yake jin kishinta sosai har qasan ransa, itama bata bar 6angaren nasa hk ta cigaba da jiran dawowarsa har bacci ya soma janyeta ta soma gyangyadi, dare ya soma shiga sosai amma shiru ba prince yaqi shigowa, shi kuwa yana cikin lambunsa zaune saman wani dutse ya kallon taurare, garin da hasken farin wata sosai yacce ko allura ce ta fadi za'a hangeta sbd muna cikin daren goma sha hudu wata ya raba, ita kuwa tana gyangyadi tayi firgit ta farka kamar wacce aka tsikara tana kallon ko'ina, saman tafkeken royal bed nasa ta kuma kallo taga baya nan alamu sun tabbatar mata be dawo ba, miqewa tayi daga inda take ta soma bi kusurwa kusurwa ta bude curtains daya rufe kusurwar ta gani ko yana ciki ta gama duba ko'ina bata ganshi ba, jan qafa tayi ta fita ta tarar da ubaid a kofa shima duk fuskarsa ta cika da damuwa, kallonshi tayi tace" ko kana da sani kan abunda ke faruwa" shiru yyi ya rissinar dakai yace" ranki ya dade bani da sani akan komai abunda na sani kawai shine gimbiya mariyatu ta aiko da saqon takarda, wannan saqo shine silar 6acin ran prince" tana jin hk ta koma ciki da sauri domin kuwa tabbas ta hangi farar takarda a qasa tana son dubawa taga ko itace takardan da saqon ke ciki, tana shiga ta sunkuya ta dauki takardar ta soma karantawa, komawa tayi ta zauna ji6is lkcin data gama krtw wasiqar duk jikinta yyi mugun sanyi ga wata faduwar gaba dake zuwa mata, miqewa tayi a hnkli ta fice daga 6angaren ta nufi yankinta,bata jima da tfy ba prince shima ya koma 6angaren nasa, washegari, kamar yadda ta saba taci ado cikin wata doguwar riga mai kalar golden tasha awarwaraye da sarqa masu kyawun gaske sai sheqa qamshi take ta fito ta nufi dakin yaranta, tana shiga ta tarar an musu wanka suna baccinsu, peck tabi ta musu a goshi kafin ta fita ta nufi 6angaren mahaifinsu, tana shiga ta tarar da leenah tsohuwar baiwarsa ita ke masa tausa yana daga zaune idanunsa a lumshe, abun ya 6ata mamaki sannab yyi masifar 6ata mata rai, wato hkn ya nuna bashi da buqatarta kenan shine yasa a turo masa da baiwa domin ita dai tasan ita ke masa komai kuma aikin ta ne wannan baiwa take yanzu, leenah tana ganin shigowarta taqi ta dakata da tausan ta cigaba da masa tausan cike da salo, hkn ya kuma qona mata rai batasan lkcin data daka mata wata uwar tsawa ba ta nuna mata kofa fita da hannu, tsawar ce tasa shi bude idanu ya sauke akanta, leenah tsayawa tayi tana kallon prince, tsawar da bimbii ta kuma mata ne a karo na biyu yasa prince ya daga mata hannu kan ta fice ta basu wuri, jikinta har 6ari yake ta kama hanya ta fice, tana fita bimbii ta qaraso wurin dayake batace masa uffan ba ta soma masa tausan har saida ya daga mata hannu sannan ta wuce ta shige dakin wanka ta hada masa ruwan wanka hadi da sinadaran wanka ta fito, daga ita har shi babu wanda yyiwa wani mgn, shine ma ta 6angare guda yake satar kallonta don yaga sam fuskarta ba annuri kamar yadda ya saba gani, har ta gama masa komai suka fito beyi mgn ba itama batayi mgn ba, wasu kaya masu kama da pakistan masu ruwan kwai ta za6a masa yasa ta feshe shi da turarukan sunfi kala shida, tana gama abunda ya kamata ta juya da niyyar fita daga 6angaren abinta don zuciyarta har lkcin tana cikin qunci, fahimtar nufin da yyi ne yasa yyi sauri riqo hannunta ya juyo da ita suna fuskantar juna, duk sukayi shiru sai ita da kuka ke neman kwace mata, dora tsinin hancinsa yyi kan nata yyi saurin toshe bakinta da nashi sautin kukan nata be fito ba, ba zato taji yajata sun afka kan tafkeken bed nasa, ko kalma daya beyi amfani da ita ba wurin bata hkr kawai da salon soyayyarsa yyi amfani wurin isar da saqonshi na ban hkr da neman afuwa kan abunda yyi, duk da yyi nasarar kashe mata jiki da salonshi amma hk tayi qarfin tattaro dukkanin qarfinta ta ture shi daga jikinta, murmushi yyi yasa qafa ya danneta yadda ba zata iya motsawa ba, tayi tayi ta kwace ta kasa tadan soma dukan broad chest nasa cike da shagwaba har da hawayenta, murmushi ya kumayi a karo na biyu yasa hannunsa mai yalwar 2tsaran gashi ya jawota jikinsa ya matseta, tayi dan qara tana qoqarin ture shi, kafin ta ankara yyi qasa da ita ya mata rumfa, lkcin duk jikinta ya mutu murus ta tsare shi da manyan idanunta shima ita yake kallo, dayake gwani a fagen lovayya tuni ya soma harbinta da wasu kibiyoyi wadanda suke fita daga idanunsa, saurin rufe idanu tayi don bata iya cigaba da kallon cikin kwayar idanunsa, dariya yyi har jerarrun fararen haqoransa suka bayyana, kwantar dakansa yyi a jikinta ya la6e har da wani lumshe idanu yana sauke wani nannauyan numfashi, bude idanunta tayi ta soma shafa kansa tamkar wani baby tana wasa da dogon gashinsa dake kwance saman kafadansa, cikin wani irin voice yace" ina sonki dayawa, kishinki yana dawainiyya dani don Allah ki kula dani ki soni ko ko kwatan yadda nk sonki ne, ke mace ta farko da kk ta6a birgeni kece mace ta farko dana mallakawa kaina da komai nawa, just love me the way I love you pls &pls" kallon tsakiyar idanunsa tayi taga har shiny yake tamkar ze mata kuka, tunawa tayi waye akbar, namijin fama wanda besan tsoro ba, daya tamkar da dubu a fage fama shine nan yake mata wannan magiya tabbas babu abun gdy sai Allah wanda ya halicci soyayya kuma ya rayar damu a cikin alfarmarta, zagaye wuyansa tayi da hannayenta ta hade fuskarsu wuri guda har suna iya jin numfashin juna tace" kana da shakku ne kan mace da tsawon lkci take dakon soyayyarka cikin ruhi da gangar jiki, macen da bata ta6a sanin waninka ba saikai daya tilo domin kaine sirrinta, macen da jininta ya gauraya da nk, nikam yadda na baka kaina hk na damqa maka ragamar rayuwata fata ne kar ka juyamin baya har gaban abada don zuciyata bata iya son wani cikin duniya idan bakai ba" kalamanta sunyi mutuqar tasiri akansa ya sake matseta sosai a jikinsa ya kamo hannunta ya dora kan zuciyarsa tana jin bugawar numfashinta sosai, rumgume juna sukayi cike da farin ciki wannan yanayi yasa suka dulmiya wata duniya ta daban......
**
6angaren gimbiya mariyatul qifdiya kuwa tayi mutuqar dana sanin saqon data tura ga babban prince sbd ramlatul aswat ta kawo mata binciken da tayi kan bimbii, cikin binciken kuwa taji ashe jikin dake cikin bimbii a lkcin na babban prince ne, wannan abu taji shi kamar al'mara, cikin wasiqar data yiwa prince ta sanar dashi mgnr cikin dake jikin bimbii a lkcin da take turakar jira wai na wani ne cikin bayinta tayi hkn ne don ta tozarta bimbii ta shafa mata baqin fenti a idanun prince, sai dai yanzu take ganin tsantsar shirmenta data fahimci ashe wai prince shine mamallakin cikin dake jikin bimbii tun lkcin,prince akbar kuwa daman bekai ga qarasa karanta wasiqar nata ba ya jefar da takardar shiyasa be ga wannan rubutu nata ba dake nuni da tsagwaron rashin sani daya fi dare duhu, wata dariya tayi mai tattare da tsantsar baqin ciki mara misaltuwa, tana jin tsananin tsanar bimbii cikin ranta wato kenan babban prince ne ya amshi budurcinta bata sani ba, wannan abu shi yafi komai dungunxuma tunaninta, yanzu data san cikakken lbrn bimbii sai taji tafi tsananta da kishi da ita fiye da kafin tasan wacce ita,6angaren sarauniya kuwa tuni tasa an damqe ummu nana batare da sanin kowa ba aka turata kurku, ta sauya sabuwar babbar hadima, komai yanzu cikin taka tsantsan take yinsa don abunda ummu nana tayi mata yasa ta soma sanya rashin yarda ga dukkanin bayinta,sarki abdallah kam jiya iya yau jikin nasa don ya kasa kwantar da hnklinsa ya rumgumi hukuncin Allah gani yake yana da mafita kullum, duk wanda yyi damarar ja da ikon Allah sai muce ga fili gamai doki.........
Littafin nan na kudi ne, idan kina da buqatar krtw zaki tura #300 ta wannan acct..0100790419,alhaji shahida nasir,union bank,saiki tura screenshrt na payment nk ta a whatsapp ta wannan layi...07041195806,
Alkalamin Bintuu ne��������
10/10/20, 1:12 AM - Anti qamshi🌷: *DAREN GOMA SHA HUD'U*🪔🪔
Written By Bintuu Seer
50
*I always confess to your love dear*.....I gave you my heart, I just want you to stay behind me everyday cox u are my woman💕💕only me!
6angaren maheer zamu iya cewa jikin nasa babu laifi, yana kwance a gadon asibitin likitan dake duba shi ya shigo dayake kamar friends suke don tare sukayi medical college, jan kujera yyi dake kusa da gadon maheer yyi ya zauna yana kallon maheer dake qoqarin tashi zaune, taimaka masa yyi ya tashi ya koma shima ya zauna, kallonshi yyi sosai cike da tausayawa yace" ya kk jin jikin nk yanzu" murmushi yyi yace" jikin da sauqi" murmushi doctorn yyi sannan yyi gyaran murya yace" matsayinka na likita ko ban fada mk ba nasan kasan condition din da lfyrka ke ciki, don Allah doctor ka manta da yarinyar nan kamar yadda itama ta mance dakai tayi aurenta just forget everthing about her and let her go, free yourself frm worries, stop torturing yourself cox of woman u are capable to live alone without anyone support,pls man ka tausayawa mahaifiyarka da masoyanka,wannan itace alfarmar da nk nema a wurinka doctor" murmushi maheer ya dago dakansa yana kallon doctorn yace" kar damu doctorn zanyi iyakar qoqarina na mance da shafinta cikin rayuwata kamar yadda itama tayi" fadada murmushi doctorn yyi yace" sound good! keep praying by God grace u will succeed" duk sukayi murmushi, miqewa likitan yyi ya miqa masa hannu sukayi shaking hands sannan ya juya ya fita, komawa yyi ya jingina da pillow ya qurawa wani 6angare na dakin ido, tsanar bimbii ne kawai yakeji ya cika masa zucciya,gani yake idan da Allah zesa ya hadu da ita sai ya shaqeta ta mutu har lahira kowa ya huta sbd wani irin tsanarta yakeji cikin ransa, duk da wannan feeling din dake naso a sararin zucciyarsa qasan ransa soyayyarta ne fal, gsky bimbii tabar masa babban ta6o da har yabar duniya bazai sashe ba, yaci alwashin mantawa rufe babinta ya lalla6a ya cigaba da rayuwarsa cikin walwala, washegari akayi discharge nasu, ennah sai lalla6ashi take komai yake so shi take masa, fitittikewa mata yyi kan shi gdnsa ze wuce ba yarda ta iya dashi hk suka masa rakiya har gdn nashi ita da faisal, masu aiki har uku ta daukar masa sbd tsabar gata, maheer hali a qoqon rai rashin mutuncin nasa har yanzu yana nan amma kashi hamsin ciki dari ya ragu, masu aikin nasa duk maza ne komai masa suke, wani lkcin idan ya zauna shi kadai tunanin bimbii sai ya soma bijiro masa amma yyi ta yaqi da zuciyarsa don kam shima kansa yasan ta masa nisa, toh mudai muna masa ftn alheri Allah ya qara masa dangana........
***
Mariyatul qifdiya ba shiri ta soma haramar komawa gd, zuciyarta cike da damuwa 2iri, damuwarta na farko shine ta tabbatar bata da gurbi ko kadan a wurin babban prince sannan gashi tana masifar shakkar tunkarar mahaifinta kan kunyata shi da tayi a idon duniya,hk dai sukayi shiri tfy, sarauniya ta hadata da dakaru su rakata har boader ita da tawagarta, cikin sanyin safiya suka dauki hanyar komawa masarautar abu ansar,cikin hukuncin ubangiji suka isa lfy, saidai tunda ta koma ko kadan bata ga fuska a wurin mahaifinta ba har tsawon kwana uku, yayarta gimbiya khamriyya ita ta bata shawara kan ta fuskanci mahaifin nasu da batu na neman gafara don yyi fushi mai tsanani da ita, batare da wata gardama ba ta tunkari mahaifin nata, tabbas ta nuna tayi nadama kuma tayi masa alqawarin zata manta da yarima akbar ta rumgumi duk wanda ya za6a mata, hkn shine ya sanyaya ransa ya sakko daga fushin dayake da ita, yyi mata nasiha sosai kan tsautsayin dake tattare da bijirewa umarnin mahaifa, Allah ya bamu ikon rabuwa da iyayenmu lfy ya kuma bamu qarfin guiwan yi musu biyayya, 6angaren masarautar burham kuwa babban prince shine yake gudanar da dukkanin abubuwan daya kamata sarki abdallah ya gudanar sbd shine daman magajin masarautar, ammar, adeel, areef tubarkallah masha'Allah sun fara wayyo sosai ga wani irin girman jiki da suka taso dashi abunka da ya'yan hutu kuma jinin girma, bimbii kam bata da wata mtsl daya wuce ta ziyarci nahiyarta don ta gana da danginta da iyayenta su ganta ta gansu, bimbii kan qaddara ta fito da ita duniya ta tako arziqi, bata ta6a fadawa prince cewa tana son zuwa africa ba shima kuma be ta6a tmbyr kan hkn ba saidai ya shirya tsaf don bata mamaki, yau da dare aka kai masa ya'yansa 6angarensa ya shirya ya nufi yankin mahaifinsa dasu, gbdy yaran basu dauki komai na bimbii ba, hk suka fito larabawa ziryan tamkar ba ruwa biyu ba, areef kan idan ka gansa kaga kakansa kamar har ta 6aci, lkcin da sarauniya, prince da bimbii suka shiga dasu wurinsa kawai da kallo yabi yaran idanunsa suka saukan kan areef da shi kansa ya gano kamanninsa da yaron ko prince dayake dansa beyi kama dashi hk ba, saurin dauke kansa yyi gefe, idan ya tuna baiwa ce ta haifi yaran sai baqin ciki ya tokare shi, hmm, niko nace lalle kam wallah bimbii yanzu ta zarce ajin ka kirata baiwa ka gyara tunaninka tsoho,atoh, bimbii na daga bayan prince riqe da adeel, be ganota ba saida prince yyi gefe ya hangeta tayi saurin rissinar dakanta cike da faduwar gaba don wallah har yanzu tana masifar shakkar wan ga tsoho daya kusa zama ajalinta, tsayar da idonsa yyi akanta yana mamaki sauyawarta gbdy tamkar ba wannan baiwa daya sani ba wacce ta kawo masa fitina a masarauta, bimbii uwar tsoro kamar farar kura, jikinta sai rawa yake sauran qiris adeel ya su6uce daga hannunta, hnklin kowa yakai kanta, murmushi prince yyi don ya fahimci tsoron mahaifin nasa take, hannu yasa ya amshi adeel din daga hannunta, take mata qafa yyi tayi saurin dago dakanta tana kallonshi ya kashe mata idanu, sarki abdallah yana kallonsu, tashi yyi zaune ya miqa hannunsa ga sarauniya dake riqe da ammar ya amshi yaron, duk suka kalleshi cike da mamaki, matsawa prince yyi kusa dashi ya miqa masa areef, kallon areef yyi ya saki murmushi yace" Allah ya rayaku yasa kar kuyi za6i irin na mahaifinku" shiru kowa yyi suka sunkuyar dakansu qasa, ya jima yana kallon yaran sannan ya dauke ido a kansu ya maida kan bimbii, kallon sarauniya yyi yace" ku fita ina son mgn da uwar yaran" gaban prince yyi masifar faduwa ya kalli mahaifin nasa, bimbii kuwa saurin riqo hannun prince tayi cike da tsoro, da ido ya mata alama kan karta damu babu komai, janye hannunsa yyi ya juya ya fita itama sarauniya tabi bayansa ya rage daga bimbii sai sarki abdallah, nuna mata kujera yyi da hannunsa ta zauna jiki a sanyaye, tana sauraron abunda wannan tsoho ze fada mata,duk da batasan abunda ze fada ba amma tana da tabbacin ba alheri bane ze fito daga bakinsa musamman yadda taga ya tamke fuska kamar wanda yaga mutuwarsa.........
Littafin nan na kudi ne, idan kina da buqatar krtw tura #300 ta wannan acct..0100790419,alhaji shahida nasir,union bank, saiki tura screen shrt na payment naki a whatsapp ta wannan layi...07041195806.......
Alkalamin Bintuu ne��
10/10/20, 1:12 AM - Anti qamshi🌷: *DAREN GOMA SHA HUD'U*🪔🪔
Written By Bintuu Seer
51
*You will always be mine even if we are miles apart*........your love is a blessed to me,huuuu lovvey💕💕
Cikin wata irin murya wacce ta amsa amo sosai a kunnenta yace" shakka babu kina da jarumtar zucci shiyasa kkyi nasarar karya tarihin wannan masarauta mai tushe da cikar asali, qasqastacciyar baiwa kamar ki bata chanchaci hada zuri'a da jinin wannan masarauta ba amma ke qarfin zucciyarki yasa kinyi nasarar hkn,tabbas kin samu lambar yabo a wurina don ina son mutum mai kafiya da kuma dauriya kan cikar burinsa kamar yadda nima nk, wannan yasa nk miki ftn alheri amma hkn ba yana nufin na amsheki bane,aa,ni mutum ne mai mgn daya bana sauyawa shiyasa bazan ta6a aminta dake ba, ki cigaba da gwada hikimarki sbd duk ranar dana samu nasara akan ki ina mai miki albishir da rayuwar qunci mai cike da nadama don har yau alqawarin kisanki yana nan babu sauyi kuma ya'yan nan nk dole sai sun dandani rayuwar bauta kamar yadda uwarsu take baiwa mara cikakken asali" tarin daya sarqeshi ya dakatar dashi da fadin wadannan baqaqen kalaman gareta, tarin ya cigaba dayi sosai hkn ne ya janyo hnklin su prince dake waje suka shigo suka nufi inda yake da sauri suna masa sannu, ita kuwa tana nan zaune ko motsi ta kasayi kawai kalaman sarki abdallah ne ke yawo a cikin kwanyar kanta, ruwan yasha kafin tarin nasa ya tsagaita kallon prince yyi yace" ka dauki iyalanka ka ficemin dasu daga nan bani son ganinsu" sakinsa prince yyi duk jikinsa yyi sanyi ya juya ya nufi inda take ya riqo hannunta ya rumgumeta ta gefensa suka fice daga dakin ya bisu da kallon takaici, suna komawa 6angarensa ya zaunar da ita a saman kujera ya tsuguna a gabanta ya soma fada mata kalmomi masu sanyi na kwantar da hnkli cike da hikima da dabara don yadda ya ganta jikinta duk a sanyaye yasan tabbas mahaifinsa ya fada mata son ranshi, murmushi tayi ta riqo hannunsa tace" ina tare da namijin duniya irin akbar ai bani da sauran damuwa idan ma da ita toh yar kadan ce" dago idanunsa yyi yana mata wani kallon mai sigogi da dama yace" meye mtslr taki kince yar kadan ce" murmushi tayi tadan marairaice fuska tace" ba wata mtsl bace kawai so nk na ziyarci nahiyar dana fito da kuma qasata" murmushi yyi yasa hannu ya kama dan mitsitsin bakinta yace" kin gaji dani kenan" dariya tayi sosai shi kuma ya wani hade rai wai shi yyi fushi tace" ashe mutum na gajiya da rayuwarsa" tsira mata idanu yyi sai kuma yyi murmushi ya dora kansa akan cinyarta ita kuma ta soma wasa da gashinsa don sumarsa tana daya daga abunda dake birgeta dashi, kwana uku da faruwar hkn, cikin dare suna kwance ubaid ya aiko wannan kyakykyawar tsuntsuwa don isar da saqon gaggawa wurin prince, yana kwance jikin gimbiyar tasa yaga shigowar wannan tsuntsuwa hkn ya tabbatar masa babu lfy, tashi yyi zaune da sauri yasa hannu ya cire saqon takardar dake kafar wannan tsuntsuwa, itama bimbii ta tashi tare da jan blanket ta rufe jikinta tana kallonshi yana krt takardar aikuwa yana gama krt saqon ya zabura ya miqe da sauri, tace" lfy,mai ya faru" batare daya bata amsa ba taga ya sanya sleeping dress nasa yyi hanyar fita, sakkowa tayi ta nemi gown dinta ta sanya tabi bayansa itama, suna fita suka ga ubaid tsaye duk da dare yyi sosai yana jiran fitowar prince suka garzaya 6angaren sarki abdallah, bakin kofar shiga turakar gbdy an sanya tsaro mai tsanani ba'a barin kowa ya shiga amma su tuni aka basu hanya suka shiga, ubaid kuma yaja ya tsaya a waje, sarauniya ce ita da uxair sai kuma wani consultant doctorn wanda musamman prince ya dauko shi don duba lfyr mahaifin nasa amma sarki abdallah yyi qememe yaqi amincewa wannan likitan ya duba lfyrshi sbd shi baya son likitan bature ya duba lfyrshi yafi son na gargajiya, sarauniya ita dakanta ta kuma kiran wannan likita da wannan dare yazo ya duba lfyr sarki don cikin wannan dare tashi daya mutuwar 6arin jiki ta same shi gashi ya shiga coma sosai tamkar bazai rayu ba, dayake abu na manyan mutane kafin kwabo likitocin bature dana gargajiya sunfi goma akansa suna qoqarin ceto rayuwarsa, daga qarshe ya soma aman jini, gashin kansa ya fara sa6ulewa tamkar wanda a kwarawa tafasasshen ruwan zafi, duk wanda yaga halin da sarki abdallah ya shiga wannan lkci sai ya zubda kwallah, hmm, duniyar kenan, kudai duba qarfin izzah irinta wannan bawan Allah amma gashi yau ya samu kansa cikin wani irin yanayi shi bai mutu ba shi bai rayu ba, dabararsa da iyawarsa sun kasa samar masa da lfy gashi ga ikon Allah, ranar hnklin kowa cikin wannan gd a tashe yake musamman prince wanda har hawaye ya zubar lkcin daya ga halin da mahaifin nasa ke ciki, asubar fari likitocin suka fito daga dakin duk suka nufo kansu, Dr.zaid ya kallesu ya soma girgiza musu kai alamar saidai kawai hkr wanda yafisu sonshi ya amshi abinsa, sarki abdallah dai rai yyi halinsa ftnmu Allah ya gafarta masa kurakuransa, wannan mutuwa ta doki iyalansa sun ji mutuwa sosai, sarauniya mar'atussaliha har suma tayi, mutuwar wannan hamshaqin sarki tuni ta zagaya kowacce kafar watsa labarai dake wannan qasa ta kuwait sai bada sanarwar mutuwar suke suna taya masarautar burham alhini, ba'a binne shi ranar ba sai washegari lkcin baqi daga sassa 2daban na duniya tun daga jinsin turawa, chinese,japanese, blacks, hk dai jirage suke ta shigowa wannan qasa ta kuwait cike da manyan mutane don samun damar halatarta jana'izar wannan hamshaqin sarki ma'abocin qarfin izzah da nuna isa da qasaita, ranar kam kowa cikin wannan qasar yasan wani jigo ya kwanta dama sbd yadda dandazon al'umma ke 6ul6ulowa daga 6angarori da dama na duniya, wannan shi ya qara tabbatar da qarfin sarki abdallah domin gsky yana da connection sosai da manya qasashen duniya, duk wannan connection din nasa be masa iyaka da mutuwa ba, idan lkci yyi dole a amsa kira.........
Hk bimbii tayi ta fama da babban prince tana kwantar masa da hnkli domin mutuwar mahaifin nasa ta ta6a shi sosai, cikin izinin ubangiji ya soma dawowa hayyacinsa da taimakonta, bayan wata uku da wannan mutuwar, yarima akbar ya shirya tfyr bimbii zuwa africa don ziyartar mahaifarta, ita kanta batasan da hkn ba sai yau yake sanar mata, wata irin rumguma tayi masa ta soma bashi kiss ta ko'ina tana masa addu'oin alheri, murmushi yyi kawai yace" naso na biki don nima ina son ziyarta nahiyar africa amma yanzu nauyi yyi min yawa saidai zuwa gaba idan Allah yakaimu" murmushi tayi kawai tace" idan ka bini wazai kula da masarauta tunda har yanzu ba'a fidda sabon sarki ba kaine ke gudanar da komai" lakace mata kumatu yyi yace" sauran idan kinje ki manta dani" dariya tayi tace" ai ban isa ba" washegari juma'a bimbii ta tashi da shiri cike da farin ciki, tawaga guda prince ya hada mata cikin tawagar nata har da wani black yoruba ne dan nijeria daga embassy na nigeria dake qasar prince ya dauko shi don yyi masu jagora, lkcin da yyi masu rakiya yaga zata shiga jirgi riqo hannunta yyi da sauri, kallon idanunsa tayi taga sunyi ja, gani yake kamar idan ta tafi qasarta bazata dawo gareshi, kamar ta fahimci tunaninsa tayi saurin yin laqe tayi kissing nashi a goshi tace" zan dawo gareka insha'Allah cikin kwanakin daka bani" murmushi yyi ya amshi ammar dake hannunta ya mishi peck a kumatu hk yabi duk yyi musu peck sannan ya miqawa hadiman dake riqe dasu, cikin tawagar yan rakiyan har da israt da khulood sai sumayya wacce prince yaba alhakin kula masa da iyali babu mishkila, yana kallo suka shige jirgi har jirgin ya soma tfy akan ruwa, tun daga lkcin ya soma jin kewar bimbii he wish daya kasance tare da ita cikin wannan tfy.........
Littafin nan na kudi ne,idan kina da buqata saiki tura #300 ta wannan acct..0100790419,alhaji shahida nasir,union bank, saiki tura screenshrt nk via whatsapp ta wannan layin..07041195806.....
Alkalamin Bintuu ne��
10/10/20, 1:12 AM - Anti qamshi🌷: *DAREN GOMA SHA HUD'U*🪔🪔
Written By Bintuu Seer
52
*GAISUWA DA DUMBIN FATAN ALHERI GA MASOYA NA 6OYE DANA FILI UBANGIJI ALLAH YABAR ZUMUNCI*
*I feel like I have been punished*.......I miss your touch,I miss your presence, I miss your smile,I miss you love,I miss you like crazy! 💕💕
Da yammacin talata jirginsu ya tsaya a babban port na tsayawar jiragen ruwa dake birnin ikko wato lagos, that yoruba man mr.oluwola shine yyi musu jagora wani hadadden gd na shegun nairori dake victoria Inland, israt da khulood basu zaci akwai beautiful environment a qasashen africa hk ba coz sudai yadda suke gani yunwa da tsantsar talauci ya qare a qasashen baqar fata, victoria lnland kowa ya sani matattara ce ta isassu kuma bunkasassun masu hatimin nasara, ita kanta bimbii bata zaci akwai wuri mai kyau da tsaruwa a qasarta irin hk ba sbd ita dai kam bata ta6a ziyarar wuri makamancin nan ba don matsayinta bai kai nan ba, kwanan su biyu a lagos suka hau flight ya saukesu a garin gombe tun lkcin gombe na cikin maiduguri, bimbii bata gama tsinkewa da lamarin ba saida taga wasu fitinannu hadaddun motoci masu numfashi dai dai har shida sun zo daukarsu, itakam har tsoro abun ya bata, hmm, nikam nace toh ai daman tuwon girma dole miyarsa da tsoka, hk motocin suka kwashesu zuwa fadar mai martaba shehun borno, ranar kam bimbi saida tayi kuka bakomai ne yasa ta kuka ba kawai tarbar girma da kuma karimci data gani a wannan gdn sarauta, sun samu tarar girma wanda yafi qarfin na kwatanta muku shi da bakin alqalami na, daga nan aka wuce dasu royal louge na masarautar borno nan suka sauka, su israt kam nasu ido don basu jin yaren fulanci bare kanuri, larabci nan dai shine yarensu, kwanansu biyu shehun borno ya shirya musu shiga rugar lamido dake cikin gombe, lkcin da tawagarsu tahau hanyar shiga wannan ruga bimbii tayi mamaki sosai don yadda ta zata ba hk ta gani ba, rugarsu daba hanyar shiga mai kyau amma yanzu tfy motocinsu keyi kan hadaddiyar kwalta baqa qirin alamu sun nuna ba'a jima da shimfida kwaltar ba wanda silar zuwansu shehun borno dakansa yyiwa gomnan jihar mgn akayi wannan kwaltar don fita kunya, akan kwalta suka din ga tfy har motocinsu suka tsaya a kofar gdn malam abba wato gdnsu bimbii, duk da sauye sauye na cigaba da aka samu hkn be hanata kasa gane gdnsu ba, sun samu rakiyar jami'an tsaro sosai da masarautar borno ta basu don kare lfyrsu, baffi da lamido na zaune kan tabarmar dake saman dandamalin kofar gdn suka hango wannan tawaga ta motoci, jerin gwanon motocin shine ya janyo hnklin jama'a suna kallon motocin cike da mamaki ina zasu tsaya, baffi ya kalli lamido yace" wadannan motocin kuma daga ina ko gomnan jihar ne ya shigo mn" lamido da idanunsa na kan motocin yana son ganin inda zasu tsaya yace" tab, ni motocin har tsoro suka ban, gsky wannan tawaga ta gomna ce" shiru sukayi suna kallon motocin dake daukar idanu ga mamakinsu suka ga sun soma tsayawa a kofar gdn, hadimanta ne sukayi saurin fitowa suka bude mata kofar mota, lamido da baffi idanunsu duka na ga wannan mota suna son ganin wanda ze fito, qafar mace suka fara gano fara sol da ita don kuwa qafar bimbii tasha hutu yadda ya kamata, sanye take da wani heel din takalmi mai igiya, fitowarta ne sanye cikin farar doguwar riga da mayafinta ya sanya yawun bakinsu kafewa suka qura mata idanu babu ko qiftawa, fuskarta dauketa take da tsantsar farin ciki dawowarta gd, tana ganin mahaifinta ta saki ihu ta qarasa da gudu ta qanqame shi da tsantsar murna da farin ciki, baffi kam ji yake kamar mafarki yake ya zama kamar wani mutum mutumi, kawai kallonta yake, lamido kuwa daskarewa yyi don ya kasa motsin kirki kawai kallonta suke,a hnkli baffi ya furta sunanta yace" khadijah! khadijah ke nk gani da gaske ba'a mafarki ba" murmushi tayi tace" baffi ba mafarki kk ba nice da gaske, na dawo gareku" hawayen farin ciki ne kawai ya soma sauka a fuskar mahaifin nata yana kallonta,goge masa hawaye tayi da hsnnunta tace" baffi na dawo" kallon lamida tayi daya kafeta da idanu tayi murmushi tace" hamma lamido na sameku lfy" kasa mgn yyi sai kallonta kawai yake, baffi ya kalli tawagar dake tare da ita sai ya rige hannunta suka shiga cikin gd, sumayya,israt,khulood na biye da ita hannunsu riqe da yan uku sanye cikin kayan alfarma, inno na kwashe shanye juyawar daza tayi don miqa kayan shanyan cikin daki idanunta suka sauka kansu, gabanta yyi wani irin bugawa tuni kayan dake hannunta suka watse ta quresu da idanu bakinta sai motsi yake amma ta kasa mgn, bimbii ta ruga da gudu ta rumgumeta qam kawai sai kuka ya kubce mata, inno ta riqeta qam tamkar zata gudu tace" khadijah! kece da gaske nk gani gabana" qara qanqameta tayi tace" nice inno,nice kk gani" fashewa tayi da kuka har da majina tace" Allah na gode mk daka nunamin wannan rana,Allah na gode mk,Allah na gode mk" take kuka yaci qarfinsu gbdy saida baffi yyi gyaran murya tukun yace" kukan ya isa hk tana tare da baqi" a hnkli inno ta maida kallonta kan kyawawan yan matan larabawan dake tsatstsaye hannu kowacce cikinsu riqe da jariri suna kallonsu, mamaki ne sosai ya bayyana akan fusksrta ta juya ta kalli bimbii tace" wadannan larabawan ma tare kk dasu" murmushi bimbii tayi tace" eh tare muke" tashi tayi da sauri ta shiga daki ta fito da qatuwar tabarmar kafa ta shimfida musu suka zazzauna, suna gaida ita cikin harshen larabci, itakam shiru tayi kawai tana son jin yadda diyarta ta samu rakiyar wadannan larabawa, lamido na tsaye can gefe yyi nisa cikin tunani yanzu kam ya tabbatar bimbii itace jikin wannan jarida daya gani, tsoro tare da rudani tuni sun dade da masa qawanya don kallon farko kawai daya mata yasan bimbii ta masa nisa, sallamar yaddiko da hauwa'u tare da wasu matan ne yasa suka waiga, hauwa'u kasa qarasowa tayi lkcin da idanunta ya sauka kan qanwarta ta, abu kamar al'mara bimbii ta koma balarabiya, miqewa bimbii tayi ta qarasa ta rumgumeta suka fara kuka hk dai suka qaraso ciki suka nemi wurin zama, batare da wani 6ata lkci ba bimbii ta soma gabatar musu da mutanen dake tare da ita, kowa yyi shiru suna sauraronta har lkcin data soma musu bayanin komai ta kuma gabatar musu da jikokinsu, Allahu akbar! Allahu akbar!! kalmar dake amsa kuwwa kenan a wannan wuri, lalle godiya ta tabbata da wanda yyi rayuwa da qaddarar dake cikinta, maxan sune masu qarfin hali amma kaf matan dake wurin kuka suke, hk kowa ya din ga amsar yaran yana yabawa da kyawunsu, inno zubawa yaran idanu tayi hawaye na fita daga idonta,Allah abun godiya ita ko cikin mafarki bata ta6a irin wannan mafarkin ba, yau dai ga qaddara ta kawo mata jikoki larabawa, itace wai yarta ta auri dan sarki kuma balarabe yaren fiyayyen halitta,tsawon rayuwarta bata ta6a farin ciki irin na yau ba, tuni gdn ya soma cika da jama'a, dangi da abokan arziqi suna shigowa taya murna, rugar nan ta dauka bimbii yar gdn malam abba tayi gamo da arziqi, bimbii ta tako arziqi abunda mutane ke fadi kenan, yadikko ta kalli inno tace" ki gode Allah ke kam kinyi farar haihuwa irin haihuwa da akeso" lamido tuni ya sallama shima yasanya yan uku albarka amma a zahiri shi kadai yasan me yake ji a zucciyarsa saidai dole ya yarda da qaddara kuma ya rumguma,satinsu biyu suka soma shirin komawa don prince ya aiko da saqo kan su hanzarta komawa gd, bimbii sam batason komawa batason sake barin gd, saida baffi yyi da gaske tukun ta soma shirinta,inno kuka take gani take idan bimbii ta tafi bazata kuma ganinta ba saida bimbii ta din ga kwantar mata da hnkli tukunna, ranar asabar tayi sallama da yan'uwa da abokan arziqi suka dauki hanya sai birnin ikko, daga nan kuma jirginsu yahau saman teku, kwanan biyar a saman ruwa jirginsu ya isa qasar kuwait, tunkan su iso tawagar zuwa tararsu take jiransu, 6angaren prince kam satin ukun nan da ba bimbii kusa dashi ji yake tamkar shekara,yyi kewarta mutuqa ga begen yaransa dake qunshe cikin zuciyarsa shiyasa ya musu aike don qara tunatar dasu, bimbii ta koma masarautar burham, ranar prince rasa inda ze cusa ransa yyi sbd farin ciki, itama tayi kewarsa sosai hk suka rumgume juna, watanta daya da dawowa majalisar nadin sabon sarki ta fitar da sunan prince a matsayin sabon sarki, ranar nadi bimbii taga shagali da wasu kalar 6oyayyun al'adun larabawa daya birgeta sosai, bimbii ta zama sarauniya a qasar larabawa cikin ikon Allah, cikin shekara daya sauyi sosai ya samu cikin wannan masarauta, tozarci da daukar bawa a matsayin wani abu wulaqatacce tuni yakau cikin gdn sarautar burham, bimbii ta taka muhimmiyar rawa wurin kawo sauye sauye mai tarin yawa a masarautar burham, bimbii itace sarauniya ta farko a wannan masarauta da sunanta ya fita sosai cikin qasar kuwait, ta zamto wata tauraruwa dake haske alqarya, a shekarar alif dari tara da sitti da biyar ne bimbii tayi wata hira da yan jaridu tayi kushe sosai kan yadda mahukunta na duniya suka zuba idanu kan cinikin bayi, wannan furuci nata shine ya janyo cece kuce wanda hkn ya jawo hnklin masu fashin baqi da kuma masu fafutikar kare haqqin dan adam suka fara tofa albarkancin bakinsu kan furucin nata, ana cikin hk majalisar dinkin duniya ta kafa dokar cinikin bayi a dukkkanin qasashen duniya, tabbas masarautar burham suna alfahari da bimbii, cikin wani taron yan jaridu da suka taba kai mata ziyara nan taga farhan shima ya zama shararren dan jarida, sosai tayi farin cikin sake haduwa da wannan mutane da suka nuna mata halarci cikin rayuwa........
*BURHAM KINGDOM AFTER 25YEARS*⚜�
⚜�
Wasu kyawawan samari na gani masu kalar larabawan usul, yarima ammar yana da tsayin gashi irin na mahaifinsa saidai na lura sosai prince ammar akwai cikar izzah da qasaita har ma yaso ya zarta mahaifinsa, princes adeel,prince areef kuwa hali suka gado irin na kakansu shegen kafiya da nuna mulki, sai kuma qannesu biyu prince abdallah da prince abdul jalal,sai kuma mace daya gimbiya afiya, bimbii ta cika gdn burham zuri'arta, sarauniya mar'atuusaliha tana tsananin son jikokin nata kamar me kunsan dai larabawa da shegen shagwa6a yara tana nuna yaran gata, bimbii da king dinta kam har yau soyayyarsu tamkar sabuwa basa gjy da juna, ita gani take kamar ma kullum sonta hawa yake a zuciyar king din nata, kusan dukkanin yaran nata a london sukayi krtunsu sai idan sun gama suke dawowa masarauta, lkcin da bimbii ta halarci wani taro na campaign against breast cancer ne ta hadu da maheer, yana cikin manyan likitocin da suke cikin wannan campaig, maheer ya manyanta shima, sun gaisa cike girmama juna, maheer yyi aure ya auri wata baturiya yar qasar german, ganinta bimbii a zahiri yaso fama masa da tsohon ta6o duk da kasancewa girma ya shigesu yanzu amma son bimbii har yau yana nan qasan zuciyarsa kawai dai ba yadda ya iya ne don kuwa Allah ya zartas da hukuncinsa, king tattalin bimbii yake kamar kwai, israt da khulood har da sumayya duk sunyi aure cikin daidaito don bimbii ta nuna musu halacci, ubaid shima yyi aurensa kuma har yau shine na hannun daman king akbar................END.
ALHAMDULILLAH!
Anan na kawo karshen wannan littafi nawa mai suna..... *DAREN GOMA SHA HUD'U*....saqon dana isar daidai cikinsa ALLAH ya amfanar damu dashi wanda na kuskure kuma ALLAH ya gafarta mana....
Masoya ina qara godiya da jinjina gareku na hkr da kkyi dani har na sauke wannan littafi, ina ftn sake kasancewa daku a sabbin littattafai na masu fitowa nan gaba, addu'oinku da kuma fatan alherin da kk bina dashi kodayaushe shine jigon dayasa bintuu ta zama kainuwa dashen ALLAH a duniyar marubuta ku cigaba da mini fatan alheri da addu' oin alheri, ubanhiji yabar qauna....son so jama'ata!�anan zan dire alkalamina sai kun jini a littafi na gaba.
Alkalamin Bintuuu ne.....