Skip to main content

FULATA

 

FULATA 1/2

Na

Manu Fagge

***Wannan kagaggen labarine, sai dai kwatankwacin abinda yake faruwa yana faruwa a gaske, kuma ba mun rubuta wannan labari bane dan muzanta wata kabila ko wani jinsi ko wata hukuma, mun rubuta wannan labarin ne, dan nishadantarwa, ilimantarwa fadakarwa, jan hankali kan abubuwan dake faruwa cikin al'ummar mu.**

***** ***** *****

Durkushe take a kasan wata shanuwa yayin da ta tara kwarya ta kama hantsar shanuwar tana tatsar nono, bayan ta kammala aikace-aikacen ta na yau da kullum a rigursu, takan tashi daga rugarsu ta shiga Birni cikin kasuwanni tana saida Nono da Man Shanu, idan ta siyar takan siyo kayan abinci wani lokacin, ta kawowa mahaifiyar ta girka musu  suci, babu ranar da bata zuwa Birni sai dai idan bata da lafiya.

 FULATA yarinya ce Bafulatana kyakkyawa wacce  bata haura shekaru 18 ba, yarinya ce mai mutukar kirkiri da kyawawan halaye, yarinyace, ko cikin kasuwar birni ta shigo ko ina ana haba-haba da ita, wannan suna na FULATA ta samoshine daga wani abokin cinikinta da suke wasa a birni da yake yawan siyan madarar shanu a gurinta, yauda gobe tasa har suka saba

Amma duk da cewa yarinyace wacce babu ruwanta, sai sai a koda yaushe tana fuskantar matsala na yadda wasu mutanen ke jifanta da munan kalmomi, yau wani yace mata "yar masu garkuwa da mutane, gobe wani yace mata, jinin 'yan ta'adda, a koda yaushe tana fuskantar irin wadan nan maganganu daga wasu mutane, hakan na mutukar tayar mata da hankali har takai ga tayi kuka, wani lokacin masu siyan kayanta sai dai suganta tana hawaye, idan suka tambayeta dalili, sai tace babu komi a gidane aka bata mata rai.

Yauma kamar kullum fulata dauke take da kwaryar Nono ta ratso cikin kasuwa duk inda ta ratso wadanda suka santa sai kiran sunanta suke, daga manya har yara, ita kuma sai dai kawai tayi murmushi ta wuce, wani lokacin ta amsawa wadanda suke kusa da ita, tafiyarta take burinta kawai taje inda take ajiye kwaryar nononta. Bayan ta karasa bakin shagon rumfar Alhaji Na Anini, anan ta sauke kayanta, bayan an tayata saukewa, sannan ta gaida Alhaji Na Anini, sannan tabi rumfunan makotansa na kasuwa, suma ta gaidasu, anan duk mai bukatar Nono da manshanu ke fada mata ta kawo masa na adadin abinda yake bukata, sannan wadan suke nesa dasu kan aiko yaransu na kasuwa gunta dan siya masu Nono, domin Nonon shanun da take siyarwa anyi amannar cewa mai kyaune sosai babu algus a cikinsa, shiyasa mutane ke rubunin siya, Kankace me, zuwa sallar azahar Fulata ta saida Nonon shannunta, bayan tayi sallar azahar anan tabar kwarayen ta na nono tace zata shiga tsallaken  kasuwa ta sayo kayan masarufi, da za ayi amfani a gida Bayan ta  karasa, anan ta sayi shinkafa kwano daya da taliya leda uku, sai sabulu na wanka dana wanki kwara uku, sai takalmi silifas guda daya, sai omo Klin 90gram guda daya, sannan ta kara shiga tsakiyar kasuwa tasai dadawa, garin kuli, magi da gishiri, daduk dai wasu kayan bukatu, sannan zuwa la'asar ta dawo rumfar Alhaji Na Anini, ta dauki Kwarayen ta, sannan tayi sallama da makota mutan kasuwa, ta nufi inda zata hau mota ta nufi gida cikin farin ciki da annishuwa.

Da yake gefin la'asar ne bata samu wata matsalar cinkoso na masu rububin abin hawa ba, saboda 'yan kasuwa basu gama fitowa ba, anan ta samu mota Bus ta hau.

Bayan ta hau an soma tafiya sai kwandasta yace "ke kudinki  dari takwas",  FULATA cikin raha tace, "Haba yayana kullum ina zuwa nan kuma dari biyar nake biya sai tayi tsamari nake bada dari shida, kayi hakuri ka karbi dari shidan"

Kwandas a fusace yace da ita "Barayin banza barayin hofi, duk kudin da kuke karba a hannun mutane ki gaza biyan dari takwas tirr"

Fulata dukar da kanta tayi cikin kwaryan nono dake kan cinyarta ta fashe da kuka me ciwo. Alamarin yayi mutukar fusata sauran fasinjoji yayin da suka rufeshi da fada kan rashin kyautawar da yayiwa Fulata, wasu harda masu zaginsa, dayi masa tofin Allah tsine amma shi ko a jikinsa yaci gaba da karbar kudinsa daga sauran fasinjojin da bai karba ba, daya daga cikin fasinjojin ya biyawa Fulata kudinta na mota dari takwas, domin ita ta kasa iya aiwatar da komi  saboda kunci.

Daf da magariba Fulata ta sauka a gurin da take, sauka bakin wani kauye, cikin sanyin jiki na bacin rai, sannan ta hau babur wanda zai kaita lungun sakonsu na rugarsu.

 FULATA. 3/4

Na

Manu Fagge

Bayan tafiyar kamar minti 15 akan babur, mai babur ya kawota rugarsu bayan magriba. Mahaifiyar Fulata na tsakiyar ruga tana tuka tuwo a wata 'yar karamar tukunya, ta hango 'yarta ta tafe tana kuka, itama cikin damuwa tabar aikin da takeyi ta nufo 'yarta ta, tana zuwa ta rage mata kayan da take dauke dashi, sannan ta jata zuwa Bukkarsu, sannan ta zaunar da ita tace " haba Shatu (Fulata), nasha fada miki ki daina sanyawa zuciyarki damuwa kan abinda wasu suke fada miki, nasan wannan kukan da kike wasu ne suka jefeki da magana mara dadi, idan wasu daga cikinmu sun kasance bata gari mu basu bane, Allah yana kallo, da akwai halin da zan dakatar dake da zuwa kai Nono talla a Birni da nayi, amma hakan bazai yiyuba, sai kin kai tallata muke samun damar siyan wadan nan abinci, bazai yiyu kullum muyi tashan Nono ba siga ba, kici gaba da hakuri, tare da danne zuciyarki, watarana sai labari".

 Haka mahaifiyar Fulata taci gaba da rarrshin nata, ta daina kuka, daga nan tace ta tashi tayi alwala tayi sallar Magriba.

Bayan Fulata tayi alwala tayi sallah, lokacin mahaifiyar tata ta gama kwashe musu tuwon dawa wanda yasha kanwa, hade da miyar tafasa, wacce suka tsinka a gefen rigar tasu suka sarrafa ta zuwa miya hade da man shanu. Sannan mahaifiyarta ta zubo mata nata tuwon tayi bisimilla taci ta amma duk a yanayi na damuwa. Bayan ta kammala ta dan shingide bisa gadon kara dan ta samu ta dan mike kafa na gajiya, sai ga yara a kalla su bakwai makotansu na ruga,sun shigo bukkarsu, suna zuwa suka dafe a jikin Fulata, suna fadin abasu tsarabar Birnin su. Da yake ko yaushe Fulata idan taje ta dawo, takan siyo musu biskit ko alawa mai tsinke.

   Fulata tace "to ku dagani na tashi na dauko muku" yaran suka tashi suna tsalle-tsalle tare da zumudin jiran a basu tsarabar birninsu.

Fulata ta kawo musu alawa mai tsinke, duk suka bare suna lasa, sannan suka fice suna tsalle, sai guda daya da ya tsaya da ya damu Fulata da surutu, yana fadin "Shatu yau she zakije dani Birni, naji ance akwai mutane da yawa sosai, inaso naga motaci"

Fulata tace dashi "Kabari sai Sallah duk zan debeku na kaiku wajen Abokaina na Birni. Sannan shima yaron ya fita ya wuce Bukkarsu yana tsalle ko wando babu a jikinsa

Bayan fitar su zuwa sallar Insha Fulata da mahaifiyar ta suka tashi sukai sallah, sannan filata ta kara komawa ta kwanta, amma sai gajiya da ciwon baya ya taso mata, da mahaifiyarta taga tana ta juyi sai tace "bayana ke min ciwo, saboda daukar kaya", nan take mahaifiyar Fulata ta tashi, ta dauko wani kullin magani, sannan ta dauko kwaryar danyen man shanu, ta kwaba, sannan ta shafawa Fulata maganin a bayanta zuwa wuya, daga nan kuma sai Fulata ta samu damar yin bacci.

 FULATA. 5/6

Na

Manu Fagge

Kashe gari da sassafe, Fulata ta tashi da sassafe ta daibowa mahaifiyar tata ruwa, sannan da yin wasu aikace aikace, sannan ta dauki Allo ta nufi wata makarantar Allo dake dan nesa dasu kusa da wani kauye har zuwa karfe tara da rabi na safe, sannan ta dawo gida, inda ta tarar da mahaifiyarta ta gama shirya mata kayan karin kumallo, bayan ta gama sannan ta dauki kayan tallarta zuwa Birni.

  Haka rayuwwr Fulata ta kasance, tana zuwa birni tallar Nono da man shanu, har takai wasu daga cikin 'yan matan rigarsu suma sun fara shiga kasuwar Birni tallar Nono, amma wasu abubuwan da suke fuskanta nacin zarafi sai dai su toshe kunnen su.

   Watarana ranar da Fulata bazata taba mantawa ba a tarhin rayuwarta, watarana da sanyin safiya a Rugar su Fulata, sun fito sun fara aikace-aikace da suka saba na yau da kullum, wasu na tatsar nonon shanu, wasu na shirin kora shanu izuwa kiwo, wasu na share-share, wasu na dumama abinda zasu karya dashi,  kawai sai sukaji wani irin rugugi da kugi wanda basu taba jin irinsa ba, kawai sai ganin jiragen yaki sukai suna ratsowa ta sararin samaniyar su, tare da sakin rokoki suna harbin duk ilahirin rugar nan, take wuta ta kama ko ina, mutuwa ta fara zirga-zirga tana daukar rayukan mai karar kwana, tuni guri ya hautsine da ihu da iffaace - ifface, Fulanin nan da dabbobinsu suka hau guje-guje, amma duk inda suka ratsa sai dai kaga saukar gurneti da harsashi na bundinga, sai dai kaga mutum ko dabba ta kama da wuta tana gudun neman ceto, sannan ta fadi a mace. Daga nankuma sai ga wasu  sojojin sun ratso ta kasa wasu akan manyan motocin yaki masu sulke, sukaci gaba dayiwa sauran Fulanin da suka rage dauki dai-dai. Ita kuwa Fulata, tarasa ina zatasa kanta ta yadda duk inda ta nufa tana ihu sai dai taga gawar 'yan uwanta naci da wuta, hango  mahaifiyar tayi itama ta fito daga bukkarta da gudu yayin da wuta keci a jikinta daga nan ta fadi kasa matacciya, da gudu ta nufi gawar, amma bata samu damar karasawa ba, yayin da ta hango wani yaro kwance yana kukan neman ceto a kasa, cikin azama da gaggawa, Fulata ta sabi yaron, ta jashi, ta samu wata kafa ta nausa dokar daji tana gudu, batasan inda ta nufa ba, tana gudu tana kuka, yayin da aka tarwatsa ilahirin rugarsu gaba ki daya.

Fulata gudu take batasan inda ta nufa ba, har takai ga tayi tuntube da wani dan itaciya, take ta kife  ta fadi kasa sumammiya, shima haka yaron ya fadi gefe daya can a sume.

   Wani Manomi da yadawo daga gona, saboda karar harbe-harbe da yake jiyowa daga nesa, hakan ya sa ya kasa karasawa gonar tasa, ya juyo gida akan amalankensa, cikin sauri da sassarfa dan gujewa abinda zai faru, kawai sai ya hango uwa mutane a kwance cikin duhun daji, da har ya gifta, amma wata zuciyar tasa ta tsaida shi, cikin azama ya karasa gurin, yaga mace ce budurwa tare da yaro a kwance cikin wani hali, mutu kwakwai rai kwakwai, baiyi wani dogon tunani ba, cikin gaggawa ya sabo macen ya dorata bisa kan Amalanke, sannan ya juya ya dauko yaron shima ya dorashi, sannan ya kada shanun dake jan Amalanken cikin azama da gaggawa ya nufi kauyensu.

©️ManuFagge