Skip to main content

MAIRO

 

 

MAIRO COMPLETE

CHAPTER 1

AKWAI TYPING ERRORS AND OMISSIONS A CIKI SO DON'T MIND THE ERRORS JUST READ THE STORY


"Na rantse da Allah yau sai an biyani ni babu ruwana"

rik'e take da kunkuru tana marmaɗen ido da murguɗa baki jikinta sai rawa yake wai ita ga matsifaffeya.

yaron dake gabanta ya risina har k'asa yana bata hak'uri

"dan Allah Mairo ki yafe min wlh ba zan kara ba ni naga kinje wani gurin ne shiyasa na cika miki ban san ba kyaso ba"

sai a lokacin ta kalleshi cikin matsifa tace "saka nayi cewa nayi na cika min kai mai hegen salo yau ko saika busar dashi ko na maka hegen duka"


wata dattijuwa take wanki gefen kogin ta kalleta tace "ke Mairo wai miyasa baki jin magana ne yanzu miye laifin yaron nan dan ya cika miki tulu?"

harara ta watsa mata ta murguda mata baki "ke kuma tsohuwa ina ruwanki dake nake yi ne da zaki samun baki ko sashi nayi da zai cika min tulu wannan ai rainine"

"ke fa baki da kirki Mairo daga magan zaki wani taso min kamar wata warinki"

"mtsssss yau daman kin san ba warinki nake ba kika samin baki a magana dan neman tsokana"


daidai nan Almu ya iso da jakinsa da jalkunan ɗinba ruwa.

yana kallon Mairo yasan matsifa ce take ganin yadda take marmaɗen ido tana rawar jiki

murmushi kawai yayi ya gaida dattijuwar


"inna ina kwana?"


"lafiya kalau Almu an tashi lafiya?"


"Alhamdulillah inna"


kallon mairo yayi "ke lafiyarki kike wannan harare2?"


banza ta masa ta cigaba da karkada jiki.

inna ta taɓe baki


"ai haka take indai rashin kunya ne ta iya ga yar banzar matsifa"


juyowa mairo tayi kanta "wai ke ina ruwanki dani kinga ban hega saggarki ba ki fita tawa bana son shinshigi"


da marmaɗe2 ta ksrasa maganar tana murguda mata baki.

  mari Almu ya kai mata ya fizgota ya jefar

"ke wai miyasa rashin kunya yayi miki yawa kamar inna zaki tsaya kina faɗawa irin wannan maganar sa'arki ce?"

wani ihu mairo ta saki ta shiga murk'ususu cikin kasa tana jan gashin kanta

"wayyo na shiga uku ya kashe ni wayyo Allah ya kare ni wayyo gwaggo"


tsoro Almu yaji ganin yadda take ihu duk'awa yayi ya rikota "tashi mu gani?"

wani mugun cizo ta kai masa a hannu saida ya saki kara ya saketa da sauri.

inna ta rike baki "oh ni hajjo wannan wace irin masifaffiyar yarinya ce haka?"

Almu dai shiru yayi yana murzar hannun dan ba karamin cizo tayi masa ba,

ya dade a haka kamin ya nufi kogin ya shiga cika jalkunansa.

       ihunta ta cigaba dayi tana murje2 daga Almu har inna babu wadda ya sake bi ta kanta.

Almu na daf da cika kayansa halilu ya iso gurin yana ganin mairo yayi saurin ta data "ke lafiya miya faru?"

langaɓe masa tayi ta cigaba da kukan

nan ya kalli inna da Almu ya shiga tambayar su ba'asi "wai miya sameta ne haka?"

inna tace "babu kawai rashin kunya tayi min Almu ya ɗan zungureta shikenan fa ta faɗi ta shiga koke2"

cikin kuka Mairo ta ɗago "wlh karya suke itace ta fasa kuka tace masa na zageta shi kuma ya ɗaga ni sama ya jefar na kare"

tana kaiwa nan ta saki wata kara kamar wadda aka sokawa wuka.

rik'e baki inna tayi jin irin karyar da Mairo ta zagga

Halilu ya kalli Almu "haba Almu ya zaka mata haka kamar wata warinka ko namiji"

Almu yayi murmushi "haba dai Halilu sai kace bakasan halin Mairo ba wlh karya take"

Halilu yace  "wai minene mafarin wannan masifa?

inna tace "ɗiban ruwa tazo fa saita eje tulun ta tafi yawonta shine haruna ya dauka ya cika mata shine data dawo tace sai ya biyata shine ya zubar da ruwan daya zuba kuma duk da haka tace wai saiya busar tulun yadda yake shine ya shiga bata hak'uri taki hak'ura wai ita saita dake sai natibmata magana shine fa ta shiga fada min magagganu har Almu saida tayi masa rashin kunyar"

Halilu yace "daman shine kawai take yiwa wannan kuka?"

"shine kawai babu wani abun da akayi mata"

cewar inna.

kai halilu ya kaɗa ya Nufi ecen dogon yaro ya k'allo ya juyo gurin mairo cikin zafin nama ya watsa mata ita,

mairo najin saukar bulala ta tashi da gudu ta nufi gida tana uhu.


Story continues below





***   ***   ***


da ihu ta isa gida tana murxa gurin da Halilu ya buga mata bulalar.

da sauri gwaggo ta tare ta "lafiya Mairo miya sameki?"

rumgumeta tayi "wayyo gwaggo zasu kasheni gwaggo basa sona sun min taro suna ta duka na"

gwaggo ta dagota "su waye Mairo faɗa min uban wa ya taba ki cikin garin nan?"

cikin kuka ta shiga yima gwaggo k'arya data saba "tsohuwar gidansu hajara ce tace wa Almu wai na zageta shine shi kuma ya daga ni sama ya jefar gwaggo ya k'arya ni na bani mutuwa zanyi"

da sauri gwaggo ta zaunar da ita ta shiga duba ta tana matsifa "wannan wace irin k 'etace haka wlh duk suka karyaki sai munyi shari'ah dasu mugayen mutane azzalumai"

gwaggo na taɓa mata k'afa ta saki wani mahaukacin ihu "wayyo na shiga uku gwaggo nan gurin Halilu ya buga min ecce"

gwaggo tayo waje da ido "ecce kuma yaushe mi kika masa?"

"ban masa komai ba daga zuwansa suka fada masa k'arya shine ya dauko k'aton ecce ya buga min gwaggo basu sona na shiga uku"

tashi gwaggo tayi ta shiga ɗaki ta ɗauko mayafinta ta nufi kofa.


   

        '''

NOTE'''

*_Assalamu Alaikum ina bawa fans ɗina hak'uri bisa ga rashin ganin cigaban novel ɗina mai suna LAMARIN DUNIYA na k'are novel ɗin gaba ɗaya kamin na fara posting sai phone ɗina ya samu matsala kuma wadda nayi publishing a blog ɗina blog ɗin ya samu matsa. ta dalilin matsalar da phone ɗina ya samu amman ana kan gyara blog ɗin da zarar an kare zanyi muku C & P Insha Allah ko kuma na baku blog address ku karanta bayan haka dan Allah ina rokon duk mai novels ɗina ko wane iri ya turo min ta wannan number_*


*_taku har kullum Khadeeja Candy_*


© *Khadeeja Candy*

[11/5, 9:37 AM] Khadeeja Candy 🍧: *♡... MAIRO ...♡*


*BY*

 

    *_KHADEEJA CANDY_*


*2*


gwaggo na k'ok'arin fita halilu na k'ok'arin  shigowa sukaci karo nan taci kwalarsa ta k'asara shigowa dashi tana masifa "ashe baka da hankali halilu dan kana magu zaka sa ecce ka bugawa Mairo bancin bugun da Almu yayi mata wai mi ta tare maka ne?"

kai ya girgiza "haba gwaggo wai miyasa duk tazo tayi miki k'arya saiki yarda ya za'aiyi na buga mata ecce fisabilillahi?"

"ai halinka na sani ba sonta kake ba zaka iya mata komai"

kallon mairo yayi da tayi shiru tana kallonsu kamar wata munafuka yace "ke dukanki nayi?"

kai ta daga ta turo baki tana matsar kwallah.

"eh gurin da Almu ya karyani ka buga min ecce"

gwaggo ta kara ciyo kwalarsa "mugu yanzu abunda kake ya kamata kenan a gaban idonka ka bari Almu yayi mata wannan illar wai miyasa baka son yarinyar nan ne halilu?"

"ohhh gwaggo haba haba wane irin illa Almu zaiyi mata rashin kunya fa tayiwa tsohuwar mutane shine ya dan zingureta fa"

gwaggo tace "tho ina ruwansa ya zingureta haihuwarta yayi kuma karya kake karyata yayi"

"haba gwaggo yarinyar da aka karya zata iya kawo kanta gida har ta iya faɗa miki an karya ta ai saidai a kawo miki ita"

saki kwalarsa gwaggo tayi ta nufi Mairo ta shiga duba k'afar.

aiko nan mairo ta k'ara marairaicewa tana "wayyoh k'afata" gwaggo ta duba bata ga alamun kariya a k'afarta ba ko alamun jimuwa babu barre karaya ta data gwaggo tayi tsaye "tashi kiyi tafiya na gani"

nan ta lak'e kafar "wayyo bazan iya takata ba gwaggo ta riga ta karye"

cikin dabara halilu ya cire takalminsa ya jefa mata iya karfinsa aiko da gudu ta faɗa ɗaki tana ihu.

matsowa yayi kusa da gwaggo ya ɗauki takamin yana faɗin "yanzu wadda aka karya zata iya wannan gudun?"


shiru gwaggo tayi halilu yace "gwaggo wata rana saita saki kunya matukar duk abunda tazo ta faɗa miki kina yarda dashi tho ko zaki ɓata da kowa"

tsaki gwaggo taja "mtsss tho sai mi dan na ɓata da kowa akanta so kake na zuba ido ina kallon ana cin amanarta? ko kai ka taɓa ta saina taɓa ka bare wani can"

halilu bai kara cewa komai ba banda kan da ya girgiza ya fice ya barta tana masifarta.

saida Mairo taji fitarsa sannan ta fito tana kukan munafurci.

nan gwaggo tayi cikinta ta masifa "Allah mairo in kina zuwa kina min karya saina ɓata miki rai kuma na ɓata dake na fita harkarki"

    kwantowa tayi jikinta tana kukan shgwaɓa "tho ai ba karya nake ba Almu ya dakeni kuma Halilu ya zaggamin bulala"

tureta gwaggo tayi "amman ai cemin kikayi shiya buga miki ecce Almu kuma ya karyaki"

turo baki tayi

"eh karya nake amman dai sun dakeni dukansu"

"tho miyasa kika min karya kuma halilu yace ai tsohuwa kikayiwa rashin kunya"

"tho gwaggo ai itace ta samin baki a magana kuma tace min masifaffiya"

"amman ai kinsan na hanaki rashin kunya da karya ko ni daga yau babu ruwana dake"

kuka ta shiga rerawa "na daina gwaggo dan Allah kar kiyi fushi dani ba zan kara ba"

gwaggo bata so kuka mairo ko kaɗan janyota tayi jikinta "shi kenan bazanyi fushi dake ba amman ki daina kinji ba kyau kuma bana so"

"na daina daga yau ni ko kallon mutane bazan sakeyi ba"

gwaggo tayi dariya tace "rufe da ido zaki rika yawo kenan?"

"eh bazan sake kallon mutane ba bare suce nayi musu rashin kunya"

gwaggo ta shafa kanta "a'a kawai ki rika jin magana kibar rashin kunya yayi basai kim rufe idoba"

dariya mairo tayi "ai wasa nake miki gwaggo ya za'ayi na rufe ido kina son na fada rijiyane ko rame?"

dundu gwaggo ta kaimata a baya tana dariya "oh baki daina karyar ba kenan ko?"

"na daina Allah yanzu ko zanyi kaɗan zanyi"

gwaggo ta girgiza kai "a,a ki daina gaba ɗaya dai wai ina kika baro min tulu?"

"yana can kogi ni gaskiya gwaggo daga yau bazan kara zuwa ɗiban ruwa ba kullum ni nake zuwa kuma yar k'ank'anuwa dani shi halilu da yake k'ato bazai jeba sai ni shiyasa suke dukana sunga ni banida girma"

cike da shagwaɓa take maganar tana son yin kuka.

gwaggo ta shafa bayanta "shikenan bazaki sake zuwa ba halilu ne zai rik'a ɗebowa"

rumgumeta mairo tayi tana murna.


Story continues below





'''        * * *'''


_2:13pm..._

gwaggo ta kare dahuwar giɗar ta ta zuba a gwango.

ta kwalawa Mairo kira da sauri ta fito tana ɗaurin ɗankwali rabin fuskarta duk fodace da bata shafu ba.

"na'am gwaggo kin kare?"

saida ta kare lisafin sannan ta ɗago ta kalleta tace "ta ɗari biu da arba'ince"

ɓata fuska mairo tayi "gaskiya gwaggo saidai ace ta ɗari biu da talatin dai dan gaskiya zan ɗauki ɗaya

gwaggo tace "ɗauki ko nawa kike so mairo waya isa ya hanaki?"

murmushi tayi ta duka ta ɗauki turen tana faɗin "yau duka zan siyar"

"tho Allah bada sa'ah amman dai hodarki bata shafu ba mairo"

turo baki tayi "nidai gwaggo bana son haka bani na shafa ba nidai haka zanje"

hannu gwaggo ta ɗaga mata "jeki jeki Allah bada sa'ah inda yanzu kuma ban faɗa miki ba ki hauni da masifa"

batace komai ba ta ɗora turen samsn kai ta nufi kofa.

gwaggo ido ta sakar mata a ranta tana _Allah ya shirya minke mairo ya tsare_


© *Khadeeja Candy*

[11/5, 9:39 AM] Khadeeja Candy 🍧: *♡... MAIRO ...♡*


*BY*

 

    *_KHADEEJA CANDY_*


*3*


tafe Mairo take ɗauke da turenta na giɗa saman kai tana yan wakewakenta.

saida tayi nisa da tafiya sannan ta tuno da ɓanɓaramar da tayi jiya da sauri ta chaja hanya harda haɗawa da ɗan gudu tana waigen bayanta.

saida taga ta shanye kwana sannan hankalinta ya kwanta tafiya ta rik'ayi a hankali tana kwanɗalar giɗar tana ci.


kashe kunne tayi tayi gefen dashi tana son ta tabbatarda abunda kunnuwanta suke jiyo mata.

wak'ar india ce _ghajiniguzarish_ ke tashi cikin wani kiɗan taushi mai daɗi

taɓe baki tayi "tho wai wayasa wannan kiɗan mai ɗaɗi cikin ɗaji kodai buki ake?" magana take tana kallon giɗar dake hannunta kamar wata taɓaɓɓiya.

kara kasa kunne tayi har ta gano gefen da sautin ke tashi dariya tayi "Allah buki ne ake bari na leka na gani amman ba zan daɗe ba sai na dawo"

haka ta kunna kai daga wani ɓangare na hanyar ta rika tafiya tana bin inda taji sautin wakar na tashi harta iso wani guri mai kamada lambu.

tsayawa tayi tana kallon etacen dake gurin "lahhh ashe ma haka gurin yake ni kan ban taba zuwa ba sai yau"

rabon ido ta shigayi saida ta kare kallon gurin sannan ta cigaba da tafiya.

a hankali ta fara hango wasu mutane sanye da wani yadi kala ɗaya.

da sauri ta laɓe gefen ecce tana lekensu ,


duk kansu sanye suke da yadi kala ɗaya mai ja da kore (red and green) kana gani kasan fadawa ne in banda mutun biu dake zaune saman wani k'aton carpet na alfarma ɗayan sanye yake da riga da waddo na turawa ɗayan kuma sanye yake da riga doguwa mai kamada jalabiyar fakistan _golden color_ Mai kyau sai kyali take.

ya dora wani ɗan kyale saman wuyansa daya sauko har saman rigarsa.

gashin kansa ya kwanta lum kamar balarabe ya lankwashe kafafunsa wata rekoda na gefensa tana bada sauti shi kuma yana fuskarta ɗayan suna karta ko wannensu kuɗi yake azawa in aka cinye ya kara wasu.


        sosai abunda suke ya burge Mairo aje turen giɗar tayi tayi zaune tana kallonsu tana dariya amman baki rufe dan kar suji

ta daɗe a haka can dai taji bazata iya jurewa ba ta ɗauki turenta ta nufosu tana Murmushi.

"Assalamu alaikum"

sallama tayi musu tana k'ok'arin k'arisawa kusa dasu

   da sauri suka tare wadda ke zaune saman carpet ɗin wasu kuma suka nufota rik'e da takobi.

tsaye tayi tana kallonsu kamar hoto har suka karaso kusa da ita,

wani zarare cikinsu ya ɗaga takobi zai sara mata ɗayan yayi saurin  rikewa yana faɗin "Yarima yace a dakata"

da sauri ya janye takobin yayi baya.

ɗaya daga cikin fadawan ya fisgota da karfi har giɗar dake saman kanta ta watse ya nufi gurin yarima da ita.

yana tsaye yana kallonsu har suka iso da ita kallo ɗaya yayi mata ya gane bata cikin hayyacinta ganin yadda idonta suka k'afe kuma bata motsi.

    ido ya ɗan tsura mata sannan ya bada umarnin a zuba mata ruwa,


da sauri bafaden ya dauki ruwan gora ya watsa mata

sai a lokacin ta matsa alamar ta dawo hayyacinta zubewa tayi zaune ta ɗaga kai tana kallonsu

suma ita suke kallo har yarima saida ta kare kallonsu ɗaya bayan ɗaya sannan ta saki wata irin kara iya karfinta mai shiga cikin kwakwalwa faɗuwa yarima yayi zaune ya dafe kunnunwansa shida wadda ke kusa dashi.

mari daya daga cikin fadawan ya watsa mata saida ta faɗi can gefe ta fashe da kuka

     ɗagowa yarima yayi ya watsa masa wata mugunyar harara da sauri bafaden ya faɗi kasa "Allah ya huci zuciyarka Yarima banyi dan ranka ya bace ba"

kawarda kai yayi yana sauraren sautin kukanta dake tashi tare da sautin waka


Story continues below





ya daɗe a haka sannan ya ɗago cike da isa yace "kashe sautin nan" da sauri ya tashi ya nufi rikodar sa hannu ya kashe ya dawo ya risina gaban Yarima yana faɗin "Allah karawa Yarima martaba na kashe"

ba tare daya kalleshi ba yace

"jeki ka rarrasheta"

"am gama Yarima" tashi yayi da sauri ya nufi gurin Mairo.


tirgewa Mairo ta karayi tana kuka tana kiran gwaggo tana murza hannayenta da kafafunta cikin kasa,

yayita rarrashinta har ya gaji tak'i tayi shiru sai ma karawa take.

ganin tak'iyin shiru yasa Yarima yayi mata alamar tazo da hannun tashi tayi ta share hawayenta ta nufoshi tana murmushi kamar ba ita ba.

kallonta yake harta karaso kusa dashi tun kamin yayi mata magana ta zauna saman carpet ɗin kusa dashi.

       da sauri ɗaya daga cikin bafaden ya unkuro zai mata magana Yarima ya ɗaga masa hannu nan dukansu suka ja baya kowa ya shiga harkar gabansa.

kallonta yayi a natse cikin isa yace


"ya sunanki?"

washe masa hauru tayi

"Mairo"


"Mairo?"


"eh sunana Maryam amman Mairo ake cemin kaifa ya sunaka?"


bai amsa mata ba ya jefa mata wata tambayar "an garin kike?"

"eh kai amman dai ɗan birni ne ko?"

nan ma wata tambayar ya sake jefa mata batare daya amsa mata ba

"mi kikazo yi nan?"

"talla nake zan wuce sai naji kiɗi na ɗauka bukine ake shine nace bari nazo na gani saina koma shine na ganku sai na taɓe"

shiru ya ɗanyi yaɓa kallonta sannan yace

"tho miyasa kika fito?"

abunda ke gabansa ta ɗauka ta nuna masa "wasan da kuoe da wannan abun ya burgeni shiyasa na fito"

bai sake ce mata komai ba ya janyo wayarsa ya shiga danne2


sai a lokacin Mairo ta tuno da giɗarta

hannu ta ɗora saman kai ta fasa kuka

"wayyo na shiga uku giɗata"

wani mugun tsaki wadda ke kusa da Yarinan yaja yana hararta.

a hankali Yarima ya ɗago kai ya kalleta

"ina giɗar take?"

"nima ban saniba ɗazu dai kamin nayi bachi nasan tana saman kaina"

kallon rashin fahimta yayi mata "bachi kikayi?"

"eh ɗazu da suka nufoni da takobi ba sai naji bachi dana farka sai naganni nan kuma banga giɗar ba"

murmushi yayi dan ya gane suma take nufi da bachi.

ɗaya daga cikin fadawansa ya kira da sauri yazo gabansa ya risina cikin isa Yarima yace

"ina giɗar Yarinyar nan?"

"gata can kusa da ecce ta zubar"

"jeki ka ɗauko mata"

tashi yayi da sauri ya nufi gurin yana faɗin "am gama Yarima"

kallon Yarima tayi tana dariya "na gode"

kai kawai ya ɗaga mata

ta sakar masa murmushi tace

"kai baka fada min sunanka ba?"

yi yayi kamar bai jita ba ya mai yarda idonsa wani gefen

nan mairo ta ɓata fuska ta buro baki

"ni inna tambayeka saika kyaleni nima amsar da na baka ban yafe ba lafira saika biyani"

cikiciki take maganar amman hakan bai hanashi ji ba

dariya ce tazo masa da sauri ya mayarda ita murmushi ya kara kawarda fuskarsa.


*© Khadeeja Candy*

[11/5, 9:39 AM] Khadeeja Candy 🍧: *♡... MAIRO ...♡*


*BY*

 

    *_KHADEEJA CANDY_*


*4*


suna haka nafaden ya kawo mata turen giɗarta ya aje yana faɗin "gashi Yarima Allah ya kara maka daraja"

hannu ya ɗaga masa bafaɗen ya tashi.

kallonsa Mairo tayi "na gode"

banza yayi mata kamar bai jita ba sun daɗe a haka sannan ya juya ya kalleta yace "amsar da kika bani zan biyaki lahira?"

shru tayi tana kallonshi dan batayi zaton yaji ba can tace "eh mana tunda kai baka banu amsar tambaya ta ba"

shiru ya ɗanyi sannan yace "mi kike tambayeni?"

"ba nace ka faɗa min sunanka ba"

ya ɗan daɗe kamin ya bata amsa "sunana Yusuf Usaini"

dariya tayi harda sa hannun baki "lahhhh shiyasa kake da kyau daman masu suna Yusuf suna da kyau"

murmusawa ya ɗanyi ya ɗauki enabi yakai bakinshi.

yatsa ɗaya Mairo ta ɗaga masa "sauran tambaya ɗaya" 

kai ya ɗaga mata yana tsusar enabi kamar mai shan minti.

tsaki kawai na kusa dashi keja haushi ya isheshi

harara Mairo ta watsa masa ta kalli Yarima tace "amman dai ɗan bunni ne ko?"

murmushin gefe yayi ya ɗaga mata kai alamar 'eh' waje tayo da ido ta shiga shafa mishi riga "lahhh nikan daman nace dan bunni ne kai inason yan bunni kuma..."

"ke! mahaukaciya

bata karasa maganar ba na kusa dashi ya katsa mata tsawa saida ta razana

hmda sauri Yarima ya ɗaga mishi hannu yana kallon fuskar Mairo data k'ara rik'e masa riga tana kallon mutunen.

tsaki ya k'ara ja ya kalli Yarima "haba Yarima ya zaka..."

dakatar dashi Yarima yayi ba tare daya kalleshi ba yace "enough yahuza plz excuse us"

tashi yayi cike da bachin rai ya nufi wta bishiya ya zauna.


Story continues below





sai lokacin Mairo ta turo baki tayi kwafa "tho an taɓa shi zo kayi abunda zakayi mai k'aton kai"

murmushi Yarima yayi yace "baki tsoron ya dakeki?"

kai ta kaɗa "ni wlh bana tsoron duka nifa ko sheɗan bai kaini masifa ba"

faɗaɗa murmushinsa yayi "gaskiya ne tho tashi zaune"

tashi tayi zaune ta ɗauki ruwan dake gansa "insha ruwan bunni?"

kai ya ɗaga mata yana kakkaɓe rigarsa data bata da k'asar hannunta.

saida ta shanye ruwan kofin gaba ɗaya sannan ta dire kofin tana dariya tana faɗin "wlh na sha ruwan bunni"

"birni ake cewa ba bunni ba"

ya gyara mata

washe hakora tayi ta sake cewa "bunni"

murmushi yayi yace "waya shafa miki hoda?"

"nice na shafa ɗazu da zanje tallah"

ta karasa maganar tana gyaran ɗankwalinta.


can ta ɗauki abunda ke gabanshi ta kalleshi tace "minene kuke da wannan abun ɗazu naga kuna wasa dashi?"

saida ya ɗan daɗe sannan yace "chachace muke zakiyi?"

da sauri ta matso kisa dashi tace "eh zanyi dan Allah"

"tho mi zaki aza?"

"kamar ya mi ake azawa"

"duk abun mutum kr so yana azawa bakiga yadda muke yi ba ni kuɗi nake azawa"

kalle2 ta shigayi tana neman abunda zata aza can ta kalli giɗar ta da sauri ta ɗauko k'waya ɗaya ta aza "to ga giɗa nan na aza"

shafa kansa yayi yayi murmushi ya sa hannunsa aljihu ya ciro dalar amerika ɗaya ya aza.

bata fuska Mairo tayi ta turo baki "ni dai bana son wannan takardar da kuke da ita saida ka aza kuɗi ko wani abu mai daɗi"

ta karasa maganar tana lek'en lemun dake bayansa.

ido ya tsura mata yana mamakin wayonta wato shi ya aza (ɗora) kudin data sani ko abu mai daɗi ita kuma ta aza kwaya ɗaya ta giɗa

cikiciki yayi murmushi yace "ai kuɗi ne ba takarda bace in kika chaja kuɗi da yawa za a baki"

lak'e kafaɗa tayi "ban yarda ba kuɗi bane ai da na sansu saidai ka aza kuɗin k'warai"

"ba nida wayan can kuɗin da kika sani wannan ne kawai in kuma ba zakiyi ba shi kenan"

shiru tayi tana son masa musu shima shirun yayi yana kallonta.

da taga babu sarki sai Allah yasa ta kalleshi tace "na amince"

kai ya kaɗa mata ya ɗan daɗe sannan ya gyara zamansa suka fara.

yin kawai suke tana masa shirme dan bata iyaba ci kusan 10 yayi mata sai haushi take ji dak'er ta samu tayi masa ci biu koshi danya nuna mata yadda zatayi ne.

aiko murna kamar ta kasheta sai dariya take kwasa harda hawaye.

shidai kallonta kawai yana shakkun hankalinta.


da taga ya kara mata ci biu ta ɓata fuska tace

"nidai na daina kuma saika bana giɗata"

shiru yayi yana kallonta kamar ba zaiyi magana ba saida yaga ta fara turo masa baki sannan yace

"ni kuma kuɗina dana baki fa?"

ɗaukar kuɗin tayi ta kikkiresu tayi musu guntu guntu baiyi unkurin hanata ba saida ta k'are  ta watsar  ta kalleshi tace "ni bana sonsu"

"mi yasa kikayi haka bakisan ba kyau yaga kuɗi ba?"

"ai ba kuɗi bane takardace nidai bani giɗata"

banza yayi mata ya ɗauke kansa saida yagata soma yi masa kuka sannan ya ɗauki giɗar ya mik'a mata ta da sauri ta karɓa tasa a ture ta tashi ta karkaɗe jikinta ta ɗora turan saman kai tayi masa murmushi ta kama hanya.


har tayi nisa sai kuma tayi juyo ta nufoshi.

kaɗan kaɗan take tafiya tana turo baki har ta karaso kusa dashi ta sauke turen ta aje masa ta fashe da kuka.

kallon kawai yake tun tana kuka ba hawaye harta fara hawayen tana shureshuren kafafunta cikin k'asa sai kallonshi take,

shima ita yaƙke kallo yana tsusar baki kamar mai mai shan minti.

sunfi karfin minti 30 a haka ita taki tayi maganar sai kuka take shina yaki yayi mata magana fadawansa sai satar kallonsu suke yahuza ko yasa earphone a kunne dan kar haushi ya kasheshi.


saida yaji ta kara buɗe baki tana kiran Gwaggo sannan ya matsa ya rik'o fuskarta ya sakar mata manya idonsa yace "mi kike yiwa kuka?"

cikin kukan tace "ba kaine ba ka jani da wasa har lokacin komawa gida yayi ban siyar da giɗa ba kuma Gwaggo bazata bani kuɗin sawa asusu ba"

murmushi yayi yasa wani bafaden sa ya kira masa yahuza.

haka ya iso gurin yana hararar Mairo.

Yarima ya kalleshi yace "kuɗin nageriya nake so"

hannu yasa aljihu ya ciro yan dubu dubu ya aje masa gabansa.

nan ne yaga kuɗin da Mairo ta yaga kallon Yarima yayi yace "wayayi wannan aikin?"

kallon Mairo Yarima yayi bai bashi amsa ba hakan ya tabbatar masa da itace 'uhmmm' kawai yace ya watsa mata harara ya koma gurin zamansa.


Story continues below





Yarima ya kalli Mairo yace "ɗauki ko nawa kike so"

da sauri tasa hannu ta dauki dubu uku tana dariya tace "na gode"

kai ya ɗaga mata "sun isheki?"

"eh na gode amman dan Allah ka bani wacan abun"

juyawa yayi yana kallon apple ɗin data nuna masa.

hannu yakai ya dauki ɗaya ya mika mata tana karɓa takai baki "lahhh daman haka goribar bunni take?"

murmushin gefe yayi ya girgiza mata kai "ba goriba bace apple ne"

"minene apple?"

"tuffa"

"minene tufa?"

shiru yayi dan yanzu kam baisan mi zai ce mata ba.

kamin yayi mata wata magana ta sake rokonsa

"dan Allah karamin ɗaya na kaiwa Gwaggo"

kara ɗauko ɗaya yayi ya mika mata dariya tayi ta kara rok'onsa "na gode amman ɗan Allah kara min ɗaya na kaiwa k'awata jummalo (MANIRA Lol.) da Halilu hannu yasa ya sake ɗaukowa ya mika mata.

bata bar gurin ba saida ta lisafa masa mutum takwas ya bata sannan ta tashi ta ɗora ture tana dariya tayi masa godiya tare da sallama ta nufi hanyar fita gurin tana waigensa tana ɗago masa hannu shidai kallo kawai ya bita dashi da murmushi harta fice.


© *Khadeeja Candy*

[11/5, 9:39 AM] Khadeeja Candy 🍧: *♡... MAIRO ...♡*


*BY*

 

    *_KHADEEJA CANDY_*


*5*


tana tafe saman hanya tana cin apple ɗin tana ɗariya.

koda ta iso gida taci kusan guda 4 ɗayan ma da giɗa ta haɗashi ta ci a kofar gida ta tsaya ta karasa na biyar ɗin sannan ta shiga tana watsar hak'ora


Gwaggo na zaune k'ark'ashi ecce durumi taɓa jan carbi Mairo ta shigo

"fuwan (gafaran) kudai masu gida"

murmushi Gwaggo tayi jin yau abunda Mairo ta shigo dashi sabanin sallamar data saba.

kusa da ita Mairo ta zauna ta eje mata turen giɗar gabanta ta zuba mata ido.

Gwaggo saida ta kai karshen carbin ta shafa sannan ta kalli Mairo da fuskar damuwa tace "yanzu Mairo tun fitar da kikayi giɗa ɗaya kika siyar?"

ɗariya tayi ta ɗauki apple takai bakinta tace "ɗayar ma cinta nayi ba siyarwa ba"

kai Gwaggo ta girgiza "yayi miki kyau yanzu ai saiki ce na baki na sawa asusu ko na siyen wani abu"

fashewa tayi da dariya harda buga k'afa ta ɗauki apple ɗaya ta mikawa Gwaggo "Gwaggo karbi ki ci goribar bunni"

banza Gwaggo tayi mata ta kara hade fuska.

nan Mairo ta ciro  kuɗin dake lak'ame a k'ugunta ta ajewa Gwaggo

"nidai ga kuɗinki nan har ma sun ninka na giɗar"

buɗe baki Gwaggo tayi tayo waje da ido "Mairo ina kika samu wannan kuɗin mai yawa haka?"

"wani ɗan bunni ne ya bani harda wannan goribar shine ya bani kuma fa kuɗin da yawa ne nice na ɗebo kaɗan"

kallon tsoro Gwaggo tayi mata "ina kika haɗu dashi Mairo"

kwantayi tayi saman k'afafunta ta soma bata labari tun farkon fitarta.

       

Mairo na kaiwa karshe Gwaggo ta ɗora hanu bisa kai tana salati

"Hasbunallahu wa ni imal wakil innalillahi wa inna ilaihi raji'un Mairo mi ya kaike mi yasa bakisan ciyon kanki ba Mairo mun shiga uku da wannan 'ya mai ya kaiki shiga can?"


Tashi Mairo tayi zaune tana kallon Gwoggo gabanta soma faduwa.

“minene hala Gwaggo?”

“Mairo kinyi gamo miya kaiki Mairo”

baki Mairo ta saki “gamon me Gwaggo?”

kamin Gwaggo tayi magana sukaji sallamar Halilu da sauri Mairo ta shige cikin Gwaggo tana fad'in “Gwaggo karki fad'a masa”

koda ya karaso Mairo yake kallon ganin yadda ta ahige cikin Gwaggo dan yasan ruwa baya tsami banza gashi kuma Gwaggo na kuka.

“Lafiya Gwaggo miya faru kike kuka?”

da sauri Mairo tace “bata da lafiya ne shine take kuka”

risinawa yayi yana fad'in “Subhanallah mi yake damunki?”

Mairo tace “ciyon kai ne da ciki yake damunta ko Gwaggo?”

Kai Gwaggo ta girgiza Alamar 'ah ah' nan cikin Mairo ya duri ruwa hannu tasa ta toshe bakin Gwaggo tana fadin “dan Allah Gwaggo karki fada masa dan Allah”

tsawa Halilu ya katsa mata “jaye mata hannunki kona miki duka yanzu”

da sauri ta janye hannun idonta cike da hawaye.

hannu Gwaggo ya rike yana fadin “dan Allah Gwaggo ki fada min abunda ya faru”

cikin kuka ta soma fada masa abunda ya faru.

raku6ewa Mairo tayi gefe tana hawaye.


Halilu ya juyo yana harararta yace "ashe haukarki Mairo har takai kiyi wannan kasadar?"

Gwaggo tace "ni tsoro ma nake ji in basu shige mata ba"

Halilu yace "wane irin shige mata Gwaggo aini bako ta aljanu nake ba ya mutanen nan nake yan yankan kai ko yan iska tunda zamani yanzu ya chaja babu babba babu yaro inma aljanune ai da sauki"

sai a lokacin wannan tunanin ya zowa Gwaggo kallon Halilu tayi tace "kana da gaskiya Halilu tunda kaga harda goribar burni ya bata wata kila akwai abu a ciki"

Kallon apple ɗin dake saman ture Halilu ya kalla "ragowarce nan?"

"eh itace taci guda shida tace koma minene ai ta cinye shikenan"

da kuka ta karasa maganar.

Ayatul-kursiyu Halilu ya karanta sannan ya ɗauki sauran biu da suka rage ya jefar bayan gida ya juyo gurin ecce durumi ya kallo ya hau Mairo da duka.


Story continues below





ihu take tayi ko ina ana jinta babu wanda take kira sai Gwaggo tana faɗin kasheta zaiyi.

wannan karon kan Gwaggo ba tayi unkurin hanashi ba dan itama ta tsorata da lamarin Mairo

mak'ota ne suka shigo suka caceta koshi daker dan mugun rik'o Halilu yayi mata saida bulalar ta kwanta mata a jiki.

kowa tambayar yake dalilin dokan da akayi mata Halilu dai baice komai ba ya fice Gwaggo ce take cewa kuɗin tallah ta zubar kuma an sata aiki taki tayi

wasu dai basu yarda ba dan sunsan yadda Gwaggo take son Mairo duk abunda zaisa ayi mata wannan dukan ta kyale batayi magana ba ba karami bane.

haka suka fice kowa da abunda yake faɗa,


                 '''*   *   *'''

kuka kan Mairo ta shashi har ta gaji tun tana iya ɗaga murya har ta koma kiran baba.

tausayinta ne ya kama Gwaggo tana cikin ɗaki ta fito ta nufi ta tadata zaune tana kaɗe mata jiki "dan Allah Mairo ki rika jin magana ki gyara halinki ki daina wannan halin"

kai Mairo ta ɗaga mata tana shisshekar kuka kamar zuciyarta zata fito idonta sunyi mugun ja.

hannunta Gwaggo ta rik'a suka shiga banɗaki wannanka tayi mata sannan suka fito,

Mairo na shiga ɗaki ko kaya bata saba ta faɗa saman gado ta soma wahalallen bachi


_8:15pm..._

gwaggo ta tashe ta taci abinci.

da ciyon kai ta tashi saboda kukan da tasha gashi kuma tayi bachi hannunta Gwaggo ta riko suka fito.

saida ta wanke mata ido sannan ta nufo tabarma.

Halilu dai kallonsu kawai yake yan mamakin irin son da Gwaggo take yiwa Mairo

saida ta zauna sannan ta zaunar da ita saman cinanunta (cinyoyi) ta shiga bata abincin da hannunta.

kai Halilu ya girgaza yace "Gwaggo kinga irin wannan sagartar da kike nuna mata shi yasa take kara lalacewa tana rashin jin maganar nan"

tsaki Gwaggo taja ta watsa masa harara sai yanzu take jin haushin dukan da yayima Mairo.

bai sake ce mata komai ba harta kare bata abinci ta bata ruwa kamar wata jaririya ta zaunar da ita saman  tabarma tana k'ok'arin tashi Mairo ta rik'o hannunta tace "Gwaggo kin daina sona ko?"

dawowa tayi ta zauna tana shafa fuskarta tace "ina sonki Mairo inban so kiba wazan so  halinki ne bana so koshi kuma na rashin jin nan da kikene ina sonki Mairo"

saida ta kalli Halilu dake kallonta sannan ta sake kallon Gwaggo tace "tho miyasa kika bari Halilu ya dakeni ɗazin?"

"saboda abunda kikayi baki kyauta ba kuma inason ya zamo miki dalilin da zaisa bazaki sake irin abunda kikayi ba ko makamancinshi"

jikinta ta shiga nunawa Gwaggo da ko ina kwancin bulalane "amman Gwaggo ai kwarai dakeni dubi jikina kuma inata kiranki ki ceceni kika kyaleni"

"na daina Mairo daga yau babu wadda zai sake dukanki bazan bari ba kiyi hak'uri kinji"

kai ta ɗaga mata tana hawaye.

Gwaggo tace “amman fa ki rika jin magana kinji?”

“na daina daga yau bazan sake ba Gwaggo har na mutu”

tashi Halilu yayi ya nufi kofa yana faɗin “indai dukane tho yanxu kika fara shanshi har sai ranar da kikayi hankali” kukan shagwaɓa ta shigayi “Gwaggo ce ya kyaleni bana sonsa”

“a a ki daina cewa baki son sa amman dai dukakan bazan bari ya sake miki shi ba”

kai Mairo ta ɗaga mata tana share hawaye.


© *Khadeeja Candy*

[11/5, 9:39 AM] Khadeeja Candy 🍧: *♡... MAIRO ...♡*


*BY*

 

    *_KHADEEJA CANDY_*


*6*


tun daga lokacin Gwaggo bata sake bari Mairo ta fita ba.

tallar da take ɗora mata ma bata sake ba kullum tana gida ko fita zatayi saida tare da Gwaggo,


tun abun baya damun Mairo har ya fara damunta

tunani take ko ta saci hanya ta fita in kuma ta tuna da dukan da Halilu yayi mata saita tsorata duk da yake tasan Gwaggo tace mata ba zata sake bari ya dake taba.

tana zaune ta raffka uban tagumi tana tunanin karyar da zatayiwa Gwaggo da zata sa ta kyaleta ta barta fita,

can wata dabara tazo mata

tashi tayi ta koma kofar ɗakin gwaggo ta fasa kuka tana murgemurge

da sauri Gwaggo ta fito tana tamabayarta “lafiya Mairo mi nene?”

“ni gidansu Jummala nake son zuwa ba tada lafiya”

shiru Gwaggo tayi tana kallonta dan tasan rigimar ce ta tashi

“nidai babu ruwana kinsan halin Halilu in yanxu yazo bai ganki ba faɗa zaiyi”

“tho ai ba daɗewa zanyi ba kuma ai ba zaki faɗa masa ba”

Gwaggo bata sake cewa komai ba ta nufi tabarma ta zauna.

Mairo na ganin haka takara ɗaga murya tana ihu

cikin faɗa Gwaggo tace “tashi kije kuma duk kika daɗe babu ruwa daga can kuma karki biya ko ina”

tashi tayi tana dariya daman kukan kawai take ba hawaye.

“amman dai zan biya giɗan tsoho ko tunda kusa ne”

“nidai ba ruwana keda Halilu”

“eh na yarda”

da gudu ta fita gidan


Story continues below





bata tsaya ko'ina ba sai gidansu jummala wuni sukayi suna shiririta basu can basu nan.

sai da bayan magariba sannan ko wannensu ya nufi gida

da fargaba ta shiga gidan tana lek'e2

bakin k'ofar ɗakin Gwaggo ta hango Halilu zaune farin wata na haskashi.

faɗuwa gabanta yayi ɗan tasan ita yake jira zagi ta shiga zabga masa cikin ransa.

_hege mai katon kai mai kamada zabarmawa ni dai wlh ka takuramin Allah kasa ma ya mutu mai idon mage (mussa) mai kan ɓera_

ta daɗe gurin tsaye tana kallonsa wai ko zai tashi amman sai kara gyara zama yake.

kamar ta fasa kuka ta shiga kwalawa Gwaggo kira _Gwaggo Gwaggo Gwaggo a dawo_

ɗagowa Halilu yayi yana kallon k'ofa yace “to shigo mana aike ake jira”

k'in shigowa tayi ta cigaba da kwalawa Gwaggo kira “Gwaggo ke ki taho mana gani”

ta daɗe tana kiranta sannan ta fito sanye da hijab da alama sallah ta k'are,

har kofar gida tazo ta kama hannunta suka shigo.

tashi Halilu yayi yana k'ok'arin rikota Gwaggo ta tare “kyaleta Halilu ni na aiketa”

“Gwaggo ki daina goya mata baya tana k'ara lalacewa”

“tho mi nayi da zakace na goya mata baya bana son raini fa Halilu”

“wane irin aikene zaki mata tun da maraice sai dare zata dawo”

Mairo ta turo baki tana watsa mata harara “ai bada maraice bane da rana ne”

buge mata baki Gwaggo tayi “ke yiwa mutane shiru dake ake ne”

kai Halilu ya girgiza “yayi miki kyau ai kamaki zanyi saiki faɗi wadda ya aikeke”

kuka Mairo tasa “Gwaggo kinji ko dukana zaiyi”

“ba zai dakeki ba bani na aikeki ba”

“hmmm Gwaggo ina miki tsoron wata rana ki daina goyawa Mairo”

“wai miyasa ka rai nanine Halilu karya zan maka kenan na faɗa maka aikenta nayi”

taɓe baki yayi ya girgiza kai ya fice.


kwafa tayi da taga ya fice “kai mugu bakin azzalumi to zo ka dakeni ɗin”

sakin hannunta Gwaggo tayi ta shiga mata masifa “ban rabaki da rashin kunya ba kuma kinsan saida mukayi dake bazaki daɗe ba kikaje kika zauna har dare”

turo baki tayi “to ba shine daren yayi saurin yi ba kuma kinsan na daɗe ban fita ba kuma...”

bata karasa maganar ba Gwaggo ta katsa mata tsawa “ke dan Allah rufe min baki 'yar rashin ji kuma ki wuce kije kiyi sallah kici abinci”

da ture2 ta nufi ɗaki tana gunguni.


_Washe gari..._

tun safe Mairo tasa Gwaggo gaba tana rokonta tayi mata giɗar siyarwa,

sai faman rantsuwa take mata wai bazata sake yin abunda tayi ba.

sam Gwaggo kin yarda tayi duk da magiyar da tayi ta mata

Mairo na ganin haka ta sawa Gwaggo kuka ba k'akkautawa harda su shak'ewa tana murje murje cikin kasa duk ta bata kayan jikinta.

banza Gwaggo tayi da ita duk da bata son kukanta amman ta daure.

haka ta wuni tana kuka ta kuma yi sa ah Halilu bai dawo gidan ba tun fitar da yayi da safe. 

          saida ta gaji dan kanta ta shi ta dawo kusa da Gwaggo dake tukin tuwo ta zauna tana ajiyar numfashi,


    Gwaggo saida ta gama kwashe tuwon ta kai ɗaki sannan ta riko hannunta suka shiga banɗaki tayi mata wanka.

har suka fito bata daina ajiyar zuciya ba idanuwanta duk sun kunbura sunyi ja

saman gado Gwaggo ta zaunar da ita ta ɗauko doguwar rigar atamfa tasa mata,

ta kwantar da ita saman jikinta tana shafa bayanta

lafewa Mairo tayi in banda ajiyar zuciya babu abunda take sauke

sun daɗe a haka Gwaggo sai buga mata baya take tana son tayi bachi ita kuma taki tayi bachin sai faman sauke wahalallen numfashi take.

kai Gwaggo ta girgiza tace “ni kan Mairo kina bani mamaki ace bakida aiki sai kuka sai ja magana sai masifa haka kawai ki wahallarda kanki dubi yadda kika wuni kina kuka”

nan sabon kuka ya zo mata “to bake bace kika ki yarda kimin giɗa ba kuma na faɗa mki bazan sake ba”

da in'in niyar kuka take maganar tana numfashi da karfi kamar zuciyar zata fito


bubbuga bayanta Gwaggo ta shigayi tana faɗin “halinki nake tsoro Mairo karkije ki sake yin wani abun kuma kina ganin yadda Halilu ya sa miki ido jira kawai yake kiyi wani abun bama hHlilu kaɗai ba harda makota jiraye suke dake Mairo ke kuma gaki baki jin magana”

ɗagowa tayi idonta cike da hawaye tace “wlh Gwaggo na daina na faɗa miki bazan sake ba in kuma na sake Allah yasa na mutu”

rufe mata baki Gwaggo tayi “Subhanallahi Mairo miye haka karki sake faɗan irin wannan maganar kinji”

kai ta ɗaga mata “na daina Gwagho zaki doramin ko gobe zakimin giɗar?”

shiru Gwaggo tayi tana tunani dan tasan Halin Mairo in kuma bata dora mata ba wata sabuwar masifa ce.

kallonta tayi tace “kinmun Alkawari bazaki sake ba bazaki yi abunda zaisa a dake kiba?”

da sauri tace “eh nayi”

“shikenan zn dora miki”

“gobe ko Gwaggo?”

“eh Allah ya kaimu”

“amin”

rumgumeta tayi “na gode Gwaggo”

“Allah yayi miki Albarka”

“amin gwaggo zaki sayamin hancin ligidi?”

“eh  shi kike so?”

“eh”

“to bari na bada a siyo miki”

kwantar da ita Gwaggo tayi ta nufi kafit (wadurup ta da tsohuwar yayi) ta bude fanteka (kwala) ta ɗauko kuɗi ta sa hijabinta ta fice.


Story continues below





© *Khadeeja Candy*

[11/5, 9:39 AM] Khadeeja Candy 🍧: *♡... MAIRO ...♡*


*BY*

 

    *_KHADEEJA CANDY_*


*7*


_Washe gari..._

tun da asuba Mairo ta tashi tana yin sallah ta shiga karatun gajerun  surorin data iya inta kare ta sake maimaitawa har rana ta fito.


_8:14pm..._

Gwaggo na motsa kunu (koko) Halillu ya shigo gaishe ta har lokacin Mairo karatu take.

mamaki yayi sosai bayan sun gaisa da Gwaggo yace “yau yarki abun k'warai akeji?”

murmushi Gwaggo tayi “ai daman tana abun k'warai indai karatu ne ai kasan Mairo ba baya ba”

“a makarantan ba agida yaushe rabon da tayi irin wannan karatum tunfa da asuba nake jinyo ta ɗakina”

“to ai daman Mairo abunda take ai kuruciya ce data girma dainawa zatayi”

“ai da girmanta Gwaggo yanxu inta kara kaɗan ai aurarda ita za'ayi”


kuka Mairo ta fara wadda ba hawaye ta daina karantun “wlh Gwaggo bana son aure ba zanyi ba”

dariya Halilu yayi “au daman ba karatu kike ba kunnenki na kanmu ai daman nasan karatun munafirci ne”

kamar ta fasa kuka ta kalli Gwaggo “kice ya kyaleni ya tashi ya bar miki ɗakinki”

kofi Gwaggo ta janyo ta zubawa Halilu ta mika masa “karɓi ga kununka kosai na can gindin murhu a kwano”

dariya yayi bayan ya karɓa yace “dan tace ki koreni shine zaki koreni Gwaggo?”

“to naga fitina kake son jami muna zaman mu lafiya”

“ai ni gaskiya ce na faɗa kuma Mairo da kike gani aurene kawai zaiyi mata hankali ta daina abubuwan nan da take”

haɗashi da Allah Gwaggo ta shiga ganin Mairo nason yin kukan da gaske daker ta samu ya fita.

juyawa Mairo tayi zata cigaba da karatu Gwaggo ta shafa bayanta “taso haka yar Gwaggo ki karya (breakfast) ai kinyi karatun da yawa”

murmushi tayi “to gwaggo aI zaki mun giɗar ko?”

“sosai ma ai dole nayi miki bana miki alk'awari ba anjima kaɗan zanyi miki”

daɗi ne ya lumluɓe Mairo da sauri ta ɗauki kayan karatun ta aje gefe ta kwanto jikin Gwaggo ta soma bata kunun tana sha cike da jindaɗi.


_2:00pm....._

Mairo ta fita tallar giɗar k'inbi tayi hanyar da tabi ranar duk da zuciyarta na raya mata ta ɗan lek'a taga ko yana nan gashi har k'anshin goribar birni takeji tana tuna yadda take cinta.


haka dai ta daure ta nufi bakin kasuwa gurin data saba zama tana siyarda giɗar. wata yarinya na zaune a gurin tana ganin Mairo ta tashi da sauri ta koma gefe dan tasan halin Mairo indai matsifa ce saida ka barmata balle yau da fuskarta take a haɗe kamar anyi mata mutuwa.


koda la'asar tayi Mairo siyar da bakin rai ta nufo gida tana tureture baki kamar ta fasa kuka sai wata tafiya take kaɗan kaɗan.

haka ta ido gida ko sallama babu tun a bakin kofa tayi jifa da turen ta ta karaso idonta ciki da kwallah ta zauna kusa da Gwaggo dake Sallah,


tana sallamewa ta kalleta “lafiya Mairo waya taɓa ki?”

soshe soshe ta shiga yi tana tunano karyar da zatayi “ni..ni...ni....ɗan ta malele zan siya?”

shafa kanta Gwaggo tayi tana murmushi “haba Mairo sai kace wani abu harda su kwallah? ɗauki kuɗi kije ki siyo ki haɗa da kifi yadda zaki jidaɗin cinsa”

kai ta ɗaga “tho amman sai in zanje makaranta”

“tho inkin huta ki watsa ruwa sannan kije makaranta kinji”

kai ta ɗaga mata ta mika mata kuɗin giɗar.

“eyeee Mairo yau duka aka siyar gaske naji kin jefar da ture tun kofa”

murmushi Mairo tayi “yau nawa zaki ban?”

“hamsi zan baki ashiri kisa a susu talatin ki siye ɗan ta malele”

ta karasa maganar tare da mika mata 50 ɗin.,


da zumuɗi ta karɓa ta tashi ta nufi ɗaki da guɗu yau an sami abun sawa a susu mai tsoka.


    '''*** *** *** *** *** ***'''

     tun daga lokacin kullum sai Gwaggo tayiwa Mairo giɗa ita kuma bata fashin zuwa gurin siyarwa so ɗaya ta je gurinda aka bata goribar birni koda taje bata tararda kowa ba tsoro taji sosai babu abunda take rayawa a ranta sai aljani ne


Story continues below





“kai aljanine wannan mutunen da gaskiyar Gwaggo tunda gashi ban sake ganinshi ba kuma duk goriba karfine da ita amman tashi taushi ne da ita kuma na riga naci”

a fili take wannan maganar can ta tsaya tana tunani “inda ba aljani bane ai bazai zo cikin dajin nan ba har ya zauna kuma fa....”


bata karasa maganar ba ta watsa da gudu saboda motsin da taji cikin itacen dake gurin tana faɗin “karku biyoni na daina bazan sake zuwa ba wayyoh Gwaggo”

ihu take tayi da kuka tana gudu rabin giɗarta na zubewa,

har tabar gurin bata daina kuka ba dan gani take kamar sun biyota saida ta isa baki kasuwa sannan ta ɗan natsu ta soma numfasawa daidai,


tun daga lokacin bata kara tunanin zuwa gurin ba

duk ta ɗauko tallar giɗarta sai dai ta nufi bakin kasuwa inta siyar ta tayi ta shiririta ita da abokanin talla ko inta dawo ta biya gidansu jummala suyi gantalin da suka saba daman haka take so,


fagen neman magana da matsifa ba babba ba yaro kowa ta raina musamman inta ga ta girmeka ko kana tsoronta,

        Gwaggo in banda goya mata baya babu abunda take.

Halilu yayi faɗa harya gaji amman a banza kamar ma kara turata yake,


gashi Gwaggo ta hana ya daketa sai in ya faki idonta ko ya haɗu da ita can waje.

harta saba inta ganshi saita chanja hanya haka suka rika wasan ɓoya ita dashi.


*_3 months later....._*

yau da wuri Mairo ta siyarda giɗarta kuma yau bata jin wasa saboda dukan da Halilu yayi mata jiya dan yanzu har bakin kasuwa yake zuwa da ya tarar tana wasa ya fatattaketa da duka har gida,


duk yadda abokanin shashacinta sukaso ta tsaya kiyawa tayi dan tsan sai yazo gurin kuma Gwaggo tace mata da ta siyar ta dawo gida dan kar halilu ya daketa,

sallama tayi musu badan sunso ba dole suka kyaleta wasu kuma suka wuce gida dansu inba da Mairo ba basa jindaɗin wasa,


_Aysha adon gari ga Hajara adon gari ni Maryam adon gari inba ni ai ba gari Khadija Abubakar nake Candy kunji laqani gani tafe da'ayari yan mata a dandali_(MY UP COMING SONG INSHA ALLAH)

Mairo na tafe tana rera wak'a mak'ale da turenta na giɗa.


tunda kamin ta k'araso ta hango wata kafirar mota baqa mai shek'i fake kofar gidansu yara sun zagayeta sai shafa suke.


© *Khadeeja Candy*

[11/5, 9:39 AM] Khadeeja Candy 🍧: *♡... MAIRO ...♡*


*BY*

 

    *_KHADEEJA CANDY_*


*8*


da gudu Mairo ta karaso gurin ta shiga korar yaran duk da bata san mai motarba ɗan kawai ta ganta kofar gidansu ne kuma taga yara sun zagayeta suna shafa ita yar neman masifa,


shafa motar itama ta shigayi tana dariya tana kallon kanta ta madubin motar harda zira halshe tana lasa glass tana tale idanunta (fitar da ido)

tafi kafin minti 3 ahaka sai fana dariya take kamar wata taɓaɓɓiya,


yaran sai kallonta suke suna son su kwakwayeta suna tsaron tayi musu masifa tunda taɓa motar ma ta hana su.


can ta juyo ta kallesu ta hade rai taja tsaki “mtssss ku dan Allah ku ba mutane guri kauyawan banza kawai kowa ya bar mana k'ofar gidan mu ko naa muku hegen duka”

maganar take tana wani ɗageɗage da marmaɗen ido.

          duk ja yaran sukayi da baya dan sunsan halin Mairo indai masifa ce ba baya ba

yarinya ɗaya aka bari tana watsawa Mairo harara harda kai hannu ta shafa motar tana faɗin “an shafa kema ai yar kauyece da hegen kanki”

kai Mairo ta girgiza tana dariya “hee ni kike faɗawa wannan maganar  zaki ko ci ubanki yanzu”

ɗankwalinta ta cire ta k'ulle kuɗin giɗar dake hannunta ta ɗaura ɗan kwalin a k'ugunta (kwankwaso) tayi cikin yarinyar suka hau faɗa da juna,


kaye huɗu yarinyar tayiwa Mairo dan ta fita girma kuma k'arfi ba ɗaya ba gashi  daman can  Mairo ba wani k'arfi ne da itaba sai yar banzar masifa.

ɗukan k'warai Mairo tasha a hannun yarinyar tun tana iya jurewa har takai ga fasa kuka tana faɗin “azzaluma wlh sai naci ubanki hegiya-”

Mairo bata rufe baki ba yarinyar ta kai mata wani mugun shuri.

nan Mairo ta faɗi ta fashe da kuka

da gudu yarinyar tabar gurin gudun kar Gwaggo ta ji ta fito.


Story continues below

kuka Mairo tayi tayi tana kallon kofar gidan ganin babu wadda ya fito yasa dole ta tashi rik'e da ɗankwalinta a hannu kanta kuma duk k'asa ta shiga gida,

da kuka ta shiga gidan ta nufi gurin Gwaggo dake bakin murhu tana eza wuta.

da sauri ta ɗago ta rikata “lafiya Mairo Halilu ne ko?”

kai ta girgiza mata ta shiga faɗa mata abunda ya faru,

ɗankwalinta Gwaggo tasa tana share mata hawaye “haba Mairo miye na wani korar yara dansun taɓa mota kuma in banda fitina inake ina faɗa da wannan yariyar?”

turo baki Mairo tayi ta ɓata fuska kamar ta fasa kuka


“shigar mata kikayi ko Gwaggo?”


“a'a wani nan na shigarwa wata na bar Mairo dukan da ta miki ne ban jidaɗiba”


“kuma harda wani mugun shuri tayi mun ina jin zafi har yanzu”


“barta da Allah kijin”

kai ta ɗaga “Gwaggo motar wace kofar gida?”


“yan birni ne suka zo ganin gida”


kusa da ita Mairo ta matso “yan bunni Gwaggo gurin wa sukazo ina suke”


“sun tafi ganin sauran dangi”

“lahh daman Gwaggo kina da yan uwa yan bunni?”


“eh kema ai en'uwanki ne tun kima karama marabinsu da nan”

risinawa Mairo tayi zatayi magana sukaji Sallama.


Gwaggo ce ta amsa masa Mairo kan ido ta sakar masa kamar bata taɓa ganin mutane ba,


harya karaso tsakar gidan shi take kallon tana masa dariya shidai kallon kawai yake kamin ya kalli  Gwaggo yace “Sannu da aiki Gwaggo”

“yauwa sannu qasin kai kaɗai ka dawo?”

“eh ina gabansu ne suna hanya suma”

tabarmar dake shinfiɗe k'arkashin ecce ya nufa ana k'ok'arin zaunawa yayiwa Mairo magana

“ke baki eya gaida mutane ba?”

tasowa tayi da gudu tazo kisa dashi ta zauna.


“na eya ina wuni?”

“lafiya kalau ya sunaki?"

saida tayi dariya sannan tace “Mairo sunana Mairo”

murmushi yayi ya kalli Gwaggo “Gwaggo ni bansan wannan yarinyar ba yar gidan nan ce?”

daga can Gwaggo ta amsa mishi “eh gidan nan take ear uwarka ce ai yar wajen margayi ce”

“wane margayi?”

“malam tanimu wadda koda kukazo gaisuwarsa bakayi aureba ita kuma tana k'arama”

shiru yayi yana kallon Mairo data washe masa hak'ora,


“na ganeta Gwaggo daman ke kike rik'onta?”

sallamar dasu Abbah sukayine ya hana Gwaggo amsa masa tambayarsa.

“amin wa'alaikassalam alhaji harku dawo?”

“eh wlh kinga kara mu kama hanya da wuri tunda munga dangi”

momi ce ta amsa mata.

bayan sun xaune Gwaggo ta nufosu tana faɗin


“ai nikan ban yaba miku ba ace mutum shekara ds shekaru rabonsa da gida amman yazo ɗai rana ai kamata yayi ace kuzo ko sati ɗaya kuyi ko biu”


ɗariya sukayi Abbah yace “har yanzu dai Jamila baki chaja ba halinki nanan na masifa”


“yau ni wani haline dani daga faɗar gaskiya”

momi tace


“karki damu jamila insha Allahu zamuzo muyi sati anan yanzu bamuzo.da shirin kwana ba kuma kinga sauran yara suna makaranta sai anyi hutu tukuna”


taɓe baki Gwaggo tayi “nidai nawa idone ai rana bata karya”

dariya suka sake yi har Mairo sai a lokacin ta gaishesu.

duk suka amsa Abbah ya shafa kanta “Maryam am girma ko?”


“ashe zaka iya gane ta ai ɗaukar ka manta”

cewar Gwaggo


murmushi yayi yace “haba dai yar tawa zan manta ko yanzu da mukaje gurin tsoho saida mukayi maganarta”

mansura ta kalleta tana murmushi tace “oh Abbah itace yarinyar da ake magana”


momi tace “eh itace yar marainiya”

“Allah sarki Allah ya jikan mahaifa”

duk suka amsa da Amin.


sun ɗan juma suna fira daga bisani Gwaggo ta kawo musu abinci.

gudun masifar Gwaggo yasa dole suka ci badan sunso ba koshi kaɗan sukaci dan tuwon dawane ba wani sonshi suke sosai ba.


Story continues below


kuɗi Abbah ya ciro aljihunsa masu ɗan ɗama ya ajewa Gwaggo “gashi ayi wata lalurar”

“haba Alhaji bancin abin alkharin da aka kawo?”

“babu komai jamila a daici da hak'uri”

godiya sosai Gwaggo tayi masa momi da mansura sukayi mata sallama.

suna shirin fita Mairo ta laqe kafaɗa ta bata fuska ita saita bisu.


Gwaggo ce ta shiga lallasarta “haba Mairo wane irin binsu kuma bunni fa zasuje”

“eh ina son zuwa bunni nidai saina bisu”

“kinason ki daina ganina?”

“a a ai dawowa zanyi”

Abbah ne ya dafata “kiyi hakuri Mairo kinga Jamila bata so kije ki bari har wani lokacin inmun dawo sai muje dake kinji?”

kuka ta fasa “a a ni saina biku yanzu”

Qasin ya kalli Gwaggo yace “Gwaggo ki bari aje da ita tunda tana son zuwa”

faɗa Gwaggo ta soma “babu inda zataje ita kenan ina ganinta ina jindaɗi saiku ɗauke ta to baza taje ba”

juyowa Gwaggo tayi gurin Mairo ana lallasarta ba


aiko.kamar tana kara turata sai uhu take kaar wadda aka yiwa wani abu.

Abbah tsaye yayi yana lallaɓata shima

duk yadda Momi taso su tafi kiyawa yayi dan bayason barin Mairo tana kuka gashi Gwaggo ta hana aje da ita.


suna Halilu ya shigo aiko da gudu Mairo ta tashi tayi bayan Gwaggo tana kuka,

nan ya shiga tambayar abunda akayi mata momi ce ta faɗa masa,


nan ya hau Mairo da masifa “Allah in baki yiwa mutane  shiru ba saina miki shegen duka yar iskar yarinya”

kara buɗe baki Mairo tayi tana kuka kamar wata karamar yarinya,


Gwaggo ta kalli Halilu “kaga ko ana neman tayi shiru kaxo kana mata masifa ko”


“to Gwaggo in tana son xuwa ki barta taje mana in kuma ba zataje ba su su kama hanya kar dare yayi musu”


“to waya hanasu tafiya ai sune suka hure mata kunne tace saita bisu”


Qasin yace “a a Gwaggo karkiyi zargin kowa itace kawai dan kanta tace saita bimu”

momi dai haushine yasa ta fice ita da mansura suka bar Abbah da Qasin.


Halilu yace “ni wlh da kina yarda da kinbarta taje su da kansu zasu dawo da ita dan mugun halinta”


kin yarda Gwaggo tayi saida taga su Abbah zasu wuce gashi Mairo na kuka kamar ranta ya fita sannan ta amince.

aiko Mairo kamar ta zuba ruwa k'asa tasha da gudu ta nufi ɗaki ta shiga haɗa kayanta cikin bakko (ghana most go).


© *Khadeeja Candy*

[11/5, 9:39 AM] Khadeeja Candy 🍧: *♡... MAIRO ...♡*


*BY*

 

    *_KHADEEJA CANDY_*


*9*


bayan Amimcewar Gwaggo saida akaje gurin tsoho tare da Mairo aka faɗa masa shima kin amincewa yayi saida yaga abun na Mairo bana wasa bane sannan ya yarda sosai Abbah ya jidaɗi daman tun rasuwar kanensa yaso a bashi ita Gwaggo ta hana,


sai goshin magariba (kusan magariba) suka kama hanya

so huɗu ana tsayawa Mairo nayin amai jikinta sai rawa sanyi yake nan da nan zazzaɓi ya rifeta saida aka kashe ac ɗin motar,


*_9:37pm....._*

suka isa Sokoto koda Qasin yayi farkin Mairo na rungume jikin momi tana bachi.

saida kowa ya fita sannan momi ta tasheta

a firgice ta fito motar tana ɗaga kanta hankes ya cika mata ido,

gidan sama ne mai hawa ɗaya ko ina an manna gulof murza ido Mairo ta shigayi dan gani take kamar mafarki take.


bayan momi ta fito Qasin ya rufe motar shida Mansura suka nufi part ɗinsu daman Abbah tuni ya wuce nashi part ɗin,


Mairo na tsaye tana kalle2 momi ta rik'a hannunta zasu shiga ciki Mairo tayi tsaye tana kallon kofar farlon da alama tsoro take ji,


faɗuwa gaban momi yayi tana tsoron kar kuma tace bazata shiga ba.

“lafiya zomu shiga ciki mana”

shiru Mairo tayi ta lakkafe kafaɗa

saida Momi ta maimaita sannan tace “nan ne gidan?”

“eh nan ne zo mu shiga ciki”

tsaye tayi kamar bazata shiga ba

momi bata bi ta kanta ba taja hannunta suka cigaba da tafiya.

jiki a sanyaye Mairo ta shiga farlon tayiwa hannun momi mugun rik'o Usman na kwance saman doguwar kujera yana bachi siraj kuma na kallo,


Story continues below





shine ya taso ya tari momi da far'ah “sannu da zuwa momi”


“yauwa sannu siraj baka kwanta ba?”


kayan dake hannunta ya k'arɓa yana faɗin “eh ban kwanta ba wacece wannan momi?”


kallon Mairo momi tayi “qanwarka ce”


“daga can aka zo da ita?”


“eh bari na shiga ciki”


Up stairs momi ta nufa Mairo na rik'e da  hannun Momi,

suna shiga bedroom Momi ta faɗi zaune saman bed ita da Mairo,

har lokacin tana  rike da hannunta


bayan sun ɗan huta Momi ta nunawa Mairo tawel “jeki ki ɗauki ga tawul can ki ɗaura sai kiyi wanka kici abinci ki kwanta”

kai Mairo ta girgiza “a'a nidai Gwaggo wanke min kafafu kawai take in zan kwanta bata min wanka”

“to mu wanka muke in zamu kwanta tashi ki cire kayanki”

tashi Mairo tayi ta nufi gurin da Momi ta nuna mata.

itama Momi tashi tayi ta shiga cire kayanta


saida ta gama wanka sannan ta kira Mairo tayi mata

tare suka fito  Mairo bata tsaya jiran komai ba ta faɗa saman bed

Momi kuma ta nufi waduraf tasa kayan bachi ta ɗaura zane sama bayan tasa hijab ta kabbarta sallah.


koda Momi ta gama sallah Mairo tayi bachi.

tana cire hijab ɗinta ta nufi down stairs.

bata daɗe ba ta shigo ɗakin da plate din abinci a hankali ta shiga tada Mairo amman hakan bai hanata farkawa a firgice ba.

“k'arɓi ga abinci kici saiki kwanta”

kin k'arɓa tayi ta tsurawa Momi ido can kuma ta mayarda su gurin abinci.


sakwarace da miyar agutsi da namomi hannun tasa ta k'arɓa “ni bazan iya cinyewa duka ba”

“ci kibar saura”

kusa da ita Momi ta zauna tana amsa waya.


saukowa Mairo tayi kasa ta hau cin abinci

cikin yan mintuna ta kare ta tashi tana suɗar miyar dake plate ɗin duk ta ɓata gurin da miya kamar mai ɓararen baki.

nunawa Momi hannunta tayi “na kare ina zan wanke hannuna?”

toilet Momi ta nuna mata

tana gyaran ɗaurin tawul ta shiga toilet ɗin


koda ta fito Momi ta gyara gurin tana mopping

tsaye tayi har momi ta kare ta nuna mata gado “hau ki kwanta”

ba musu ta hau Momi taja zanen rufa ta lulluɓa mata.

ta kashe wutar ɗakin ta kunna ta bedside lamp ta nufi kofa,

Mairo na ganin zata fita ta tashi da sauri “ni kaɗai zaki bari nan?”

Momi daga gurin da take tsaye tace “tsoro kike jine?”

“eh bazan iya kwana ni kaɗai ba”

“babu abunda zai sameki ki kwantar warki kiji?”

“aa ni bazan yarda ba”

saukowa tayi ta nufo Momi.

Momi tace “to bari na kunna miki wutar saiki kwanta kamin nazo yanzu zan dawo jeki kwanta”

lake kafaɗa tayi “a a ni bazan yarda ba”

tsawa momi ta katsa mata “wuce kije ki wanta nace”

jiki na ràwa Mairo ta faɗa saman gado ta ɗanne fuskarta cikin katifa,

Momi na ganin haka ta taja kofa ta fice


kuka Mairo tayi tayi kaɗankaɗan kuma ta kasa ɗago kan dan tsoron kar taga wani abu har bachi ya ɗauketa.


*_washe gari....._*

tunda asuba Momi ta tada Mairo

a firgice ta farka jikinta sai rawa yake hannun momi ta rika suka shiga banɗaki tare sukayi alwala.

bayan sun fito Mairo ta nufi yar zakarta ta zazzage ta ɗauki wata atamfar kauye tasa tare da hijab ta fara sallah,


tana sallamewa komai bata tsaya yiba  ta koma bachi.

sai 8 da minta ta farka koshi dan siraj ya tada tane.

da murje murjen ido ta tashi tana mik'a idonta a lumshe tana soma kiran gwaggo.

“ke tashi momi na kiranki nace”

‘to’ tace tana turo baki kamar ta fasa kuka

shidai bai tsaya jiranta ba ya fice,


saida ta gama gunguninta sannan ta tashi ta nufi kowa duk jin take bata son gidan,

tana fitowa ta hango farlo down stairs.

wani irin ihu ta saki saboda juwa data gani tayi bayabaya tana kiran “na shiga uku wayyo Gwaggo na bani mutuwa zanyi”


Story continues below





duk kai suka ɗago sun Kallonta daga dining area siraj ne ya fara tambaya “lafiya?”

cikin kuka tace “na bani bazan iya saukowa ba na shiga uku Gwaggo”

duk fashewa sukayi da dariya banda siraj da yaja tsaki sai kuma Momi data hau mata faɗa “ke wai wane irin iskancine dake haka haka kawai zaki rika yiwa mutane uhu”

Qasin dake tsaye ya kalli Momi yana murmushi “tsorone taji momi kinsan yar kauye ce”

“to dan taji tsoro sai tayiwa mutane ihu iskancin da takeyi can kauye nan bazan ɗauke shiba”

tea cup ɗin dake hannunshi ya aje ya nufi up stairs.


hannunta ya riko ta rumgumeshi iya karfinta ta kulle ido gam sannan suka sauko.

har suka isa dining bata buɗe idon ba saida taji an zauner da ita sannan ta buɗe ido tana kare musu kallo,


da Qasin ta fara sannan Usman, Siraj sai kuma ta juyo gun Nura.

kofin tea Momi ta aje mata idonta cike da hawaye ta ɗauka ta kai baki

bata ajeba saida tasha rabin kofin Siraj da Nura da Usman sai dariyarta suke Qasin Murmushi yayi ya kalli agogon hannunsa yace “Momi ni bari na wuce gurin aiki”

“to Allah ya tsare”

“Amin”

saida ya kara kurɓa tea ɗin sannan ya fice.


Usman ya kalli Mairo yana driya yace “bakison bredin hala?”

banza ta masa har Momi ta kare cin abincinta da Usman suka tashi.

sannan ta ɗauki bredin tana hawaye ta rika somawa kamar turo da miya tana ci.


© *Khadeeja Candy*

[11/5, 9:39 AM] Khadeeja Candy 🍧: *♡... MAIRO ...♡*


*BY*

 

    *_KHADEEJA CANDY_*


*10*


Siraj dai sai kallonta yake can yaji bazai iya zurewa ba yace “wai mi kike yiwa kuka?”

cikin kukan tace

“ni gida nake so”

dariya yayi “gida?”

“eh”

“mi aka miki to?”

“bana son gidan nan bana son gida a sama kuma mumi faɗa take min”

fashewa sukayi da dariya Nura yace “hala baki taɓa ganin gidan sama ba?”

“eh nidai bana sansa”

tashi nura yayi yana faɗin “amman gaskiya kauyancinki yayi yawa”

k'ara turo baki tayi kuka nason fito mata fili Siraj dai kallonta kawai yake har ya kare cin abinci ya tashi,


Mairo tasowa tayi ta dawo kusa da doguwar kujera dake parlour ta zauna har lokacin hawaye take.

jin tafiyar momi yasa ta ɗago kai tana kallon up stairs “lafiya kike kuka?”

fuskar momi a haɗe take mata tambayar

“gida nake so gurin Gwaggo”

murmushi momi tayi “karya kike yi ai ke kika dage saikin biyomu jiya jiya muxo yau kice a kaiki gida babu yadda bayiba akan ki zauna kika ki”

hannayenta ta haɗe tana rokon momi

“na daina mumi bazan sake cewa a zo dani ba”

“uhmm tashi muje kicin kiyi wanke wanke”

lake kafaɗa tayi “ni ban iya wanke wanke ba”

kunneta momi ta kamo “ke bari kiji na faɗa miki iskancin da kike can kauye nan bazaki min shiba”

kuka Mairo tasa sai kiran Gwaggo take.


haka momi taja hannunta suka nufi kicin.

gurin wankewanke momi ta nuna mata ta “oya sa hannu ki wanke” kallon momi tayi idonta cike da hawaye tace “wlh ban iya wanke wanke ba”

“dukanki dai kikeso nayi kamar zakice baki iya wanke wanke ba kuma rikon kauye ba birnin ba koki wanke shi ko na miki dukan tsiya” momi na kaiwa nan ta juya tabar kicin ɗin,


haka Mairo ta hau wankewanke tana kuka

sama take wankewa dan har ga Allah bata iya ba tunda Gwaggo bata sata aikin komai inba sharaba koshi inta ga damane take yi.

haka ta wankesu samasama kofukan da akasha tea ma ɗaurayisu kawai tayi ta aje,

koda ta kare ta fashe tea cup ɗaya kuma duk ta ɓata gurin da ruwa ɗan kwalinta tasa ta goge ruwan ta jefashi bayan firjin.

jikinta a sanyaye ta nufo parlour tsaye tayi tana kallon momi dake zaune saman kujera.

ganin bata kula taba yasa ta karaso kusa da ita “na kare”

sai lokacin momi ta kalleta “to wuce kiyi wanka”

“ina?”

“inda kika ga na miki jiya”

lake kafaɗa tayi tayi baya baya “ni bazan hau sama ba gaskiya”

taɓe baki Momi tayi ta cigaba da kallon tv.


*****

ranar Mairo wuni tayi tana kuka saboda faɗan da momi tayi mata kuma ta hana mata abincin rana saboda takiyin wanka.


da magariba Mairo na gefen kujera zaune Momi ta nufi kofa da sauri Mairo ta tareta tana “ni ki bani abincina yunwa nake ji”

tureta momi tayi saida ta faɗi wani mahaukacin ihu ta saki momi saida ta rufe kunnuwanta ta hau shurenta.

“lafiya?”

Qasin na shigowa abunda ya fara tambaya kenan


momi ta nunata da yatsa “rainin wayo ne da ita so nake na gyara mata zama”

karasawa yayi ya tada ta “mi tayi momi?”

“iskancin da take can kauye ne take son tamun”

kallon Mairo yayi “mi kika mata?”

cikin kuka Mairo tace “ban mata komai ba muguwace azzaluma ƙk'atuwar banza kuma ban yafe miki b-”

da sauri Qasin ya rufe mata baki “ke karna sake ji ba mamanki bace”

kai ta girgiza tana hawaye “ni ban sonta ba mamana bace”

kwafa momi tayi “aiko kashinki ya bushe cikin gidan nan”

“wai minene mafarin wannan abun ne momi?”

momi tace “rantsuwa nayi duk batayi wanka ba bazan bata abinci ba”

kallon Mairo yayi “ke mi ya hana miki wanka maryam kin fi son ki zaina da k'azanta?”

“a a itace tace saina hau saman sama sannan nayi wanka ni kuma tsoro nake ji”

kallon momi yayi yana murmushi “kinji momi tsoro take ji kinsan ko ɗaxun saida aka saukarda ita”

“ba wani tsoro iskancine kawai”

“ba iskanci bane ko?”

ya tambayi Mairo kai ta ɗaga yace “bata hakuri sai kuje tayi miki wanka kuma karki kara rashin kunya kinji”

saida ta daɗe sannan ta kalli momi kasa2 tace “yi hakuri bazan sake ba”

da ita da dashi duk tsurawa momi ido sukayi sunajiran abunda zatace


saida ta watsa masu harara sannan ta fixgi hannun Mairo suka nufi up stairs.

kankame momi Mairo tayi ta rumtse ido nan momi ta sakar mata hannu “wuce da kanki”

kuka tasa nan momi ta katsa Mata tsawa dole ta rike karfen ta rika hawa da rumtsen ido har ta haye.

momi ce tayi mata wanka Mairo kan ana mata wanka tana tunanin yadda za ayi ta tsera ta gudu ta bar gida,

bayan sun fito momi ta wulgo mara kayanta ta sauka downstairs ta ɗebo mata abinci.


*_washe gari....._*

tun asuba momi ta tada Mairo bayan sunyi sallah bata barta ta koma bachi ba suka nufi kicin.

tare suka haɗa komai na breakfast ranar momi batayi mata faɗa ba dan tare sukayi komai duk da ba wani iyawa tayi ba daman momi abunda bata so ta saka aiki kaki da kuma kuka.


*_8:30am....._*

suka kare hada komai momi ta nunawa Mairo gurin da zata jera.

ba musu ta rika jera abinci badan ranta yaso ba sai dan gudun matsifar momi aranta kan ɗebima momi albarka kawai take tana aiban ta'ta.

Mairo ce ta fara zama bayan ta jere breakfast ɗin sannan momi,

Usman da Nura dake zaune saman kukera suka nufo dining.

Siraj sai janta yake ita kuma ta wani haɗe fuska kamar ta fasa kuka .

momi da kanta ta zubawa Mairo breakfast su kuma suka shiga zubawa kansu.

Nura ya kalli Momi yace “yau yaya ba zai karya nanba ?”

momi tana k'ok'arin zuba ma kanta tace “zaizo mana ai kasan nan yake karyawa kila bai tashi bachi bane”


kamar daga sama sukaji an banko kofar parlour duk juyawa sukayi suna kallon Qasin daya shigo fuska a haɗe.

yana karasowa momi tace “lafiya?”

takardun dake hannunsa ya nunawa momi cikin zafin rai yace “kwangila ce Yarima yakai a kanfaninmu”

murmushi momi tayi “wow...-”

tare numfashinta yayi ya juyarda fuska “haba momi kamar bakisan Yarima ba he just want to ruin my life kuma deal ne between me and him saina gani tsakanin ni da shi who is going to be loser”

tashi momi tayi ta daga hannunta da niyar yi masa magana sai kuma ta kasa jefarda takardun yayi ya fice cike da bacin rai.


sanyi jikin momi yayi ta kasa kai komi bakinta Nura da Usman ne kawai suke cin abinci shima Siraj ya damu sai kallon momi yake,


tashi momi tayi ta nufi gurin daya watsarda takardun ta shiga haɗawa.

saida ta haɗesu guri ɗaya sannan ta kalli Siraj daya juyo yana kallonta tace “Siraj jeka kiran min yayanku”

kai kawai ya ɗaga mata ya tashi ya fice.

Mairo dai sai satar kallonsu take tana tsomen beredi,


guri momi ta samu ta zauna dafe da kai kamar mai mata ciyo.

tana haka Qasin da Siraj suka shigo dining Siraj ya nufa Qasin kuma ya nufota yana faɗin “gani momi”

kujera momi ta nuna masa har lokacin tana ɗafe da kai.

bayan ya zauna ta kalleshi tace “Qasin ka rika hakuri kasan da wadda kake zama Qasin ni bana tunanin saboda ɓata maka suna ko karyarda kai Yarima ya ɗauki kwangila ya baka”


kawar da kai yayi alamar bai jidaɗin maganar ba.

ganin haka yasa momi ta taso ta dawo kusa dashi ta zauna “Qasin ni a ganina kamar ma Yarima yana son ɗaukaka kanfaninku ne”

juyowa yayi ya kalleta “a a momi so yake ya karya ni kawai kuma bazan taɓa yarda da wannan kwagilar ba ba zai taɓa cinma burinsa a kaina ba”


kallon momi yayi yana nazarin kalamanta can ya lumshe ido ya sauke ajiyar zuciya ya sake buɗe idon yace “momi banida mafita sai wannan momi bana son Yarima yayi nasara a kaina momi ki duba min plz”

itama Momi ajiyar zuciya ta sauke tace “baka ganin mayarda kwangilar zai zame maka matsala?”


“zai iya zama kan dan lokacin da zai bada kwangilar tare da yan jarida yazo”

“to karka kuskura ka mayarda kwangilar zai zubar muku da mutuncin kanfani”

“momi ba nida wata mafita sai wannan”

“haba Qasin sai kace kai ba namiji ba kai bakasan yadda zaka sarrafashiba ka bashi kunya ka taka abunda ya taka Qasin ka zama gawurtaccen namiji ba rago ba”


Siraj da tunda ake maganar hankalinsa na gurin tasowa yayi yana faɗin “yes yaya kaima namijine ka ya k'eshi ks kara ɗags martabar kanfaninka kabi shawarar momi plz”


ajiyar zuciya Qasin ya sauke a karo na uku ya kalli momi “momi ba hannuna da nasa ya bani kwangilar ba PA ɗina yaba kuma banida tambas dan zai iya haɗa kai dashi ya cutar dani”

Siraj yace “ka chanja PA kawai”


“haba Siraj how many PA I have to change just because of him? PA 4 na chanja akanshi bazan sake chanja wani ba not anymore”

cikin faɗa yake maganar jijiyar wuyansa na tashi da sauri Usman da Nura suka juyo suna kallon su, Mairo kara sakin baki tayi tana kallonsu daman hankalinta yana gurin,


dafashi momi tayi “ga wata shawara Qasin”

kai ya ɗaga mata ba tare daya kalletaba ‘uhmm’

“mi zai hana ka karɓi kwangilar kayi da kanka?”


murmushi yayi mai cike da jin haushi “haba momi ai zubarda kai ne daɗi zaiji na k'arɓi kwangila da hannuna masa”

“ba faɗuwa kayi ba Qasin cigabane a gareka da kuma ɗaga darajar kanfaninku”

kai ya girgiza “momi ba zaki gane ba”


“kaine baxa ka gane ba Qasin idan kayi haka mutane zasu yaɓeka suce bakada girman kai sannan kodan kwangilar tayi ya kamata kayi haka kuma idan tayi kyau zaka jawowa kanka customers ayaba maka ka kara samun ɗaukaka”

Siraj yace “gaskiya ne yaya ka ɗauki shawarar momi”


ya daɗe zaune gurin kamin ya ɗago kai ya kalleta “shi kenan momi zanyi yadda kikace”


murmushin jidaɗi Momi tayi ta shafa kansa “Allah ya maka albarka ya shige maka gaba”

shida Siraj suka amsa da ‘amin’

tashi yayi ya nufi kofa yana sauke ajiyar zuciya,


Story continues below

da gudu Mairo ta taso ta nufo shi tana faɗin “dan Allah ka je dani yawo inson fita”

fuska a haɗe ya shafa kanta yace “ba yanzu ba” ɓata fuska tayi idonta suka cika da hawaye shirinta na guduwa ya rushe .

juya tayi  tana kallonsa har ya fice.


tashi momi tayi ta nufi up stairs tana faɗin “Maryam in kuka k'are ki haɗa kayan ki kai kicin ki wanke kuma ki share parlour nan ki goge”

kara ɓata fuska Mairo tayi abunda ta rsana kenan hawayen dake makale a idonta suka zubo.



© *Khadeeja Candy*

[11/5, 9:39 AM] Khadeeja Candy 🍧: *♡... MAIRO ...♡*


*BY*

 

    *_KHADEEJA CANDY_*


*12*


bachi Mairo take saman kujera ta wani turo baki sai numfashi take da k'arfi,


Momi na saukowa ta tadata “ke ke ke Maryam”

a firgice ta farka ta kara turo baki fuskartar momi ta rik'o “kinyi wanke2?”

kai ta ɗaga tana murza ido momi tace “tashi kije kiyi wanka”

tashi tayi kamar ta fasa kuka ta nufi up stairs zuciyarta cike da tsoro,

rik'e k'arfin tayi ta rumtse ido tana tafiya a hankali har ta haye.


        '''*  *  *'''

Momi na kicin tana girki taji uhun Mairo da sauri ta aje robar dake hannunta ta nufi up stairs.

tsakiyar ɗaki ta tararda Mairo sai juye2 take tana kuka jikinta ba kaya kikata momi tayi “ke lafiya miya faru?”

kasa magana tayi sai toilet take nunawa momi tana tuma,


da sauri momi ta nufi toilet ɗin,

kalle2 ta shiga ta rasa dalilin dayasa Mairo kuka hankalinta bai kai gurin shower da take kunne ba sai gab da zata fita sannan idonta suka kai gurin juyowa tayi ta nufi shower da niyar kashewa,

nan hannunta ya taɓo ruwan dake zuba da sauri tayi baya baya da yar k'ara saboda ta fasasshin ruwan da suka taɓa mata hannun,


ta daɗe tsaye cikin toilet ɗin tana duba hannunta,

sannan tasa hannun hagu ta kashe shower.

koda ta fito duk'e ta tararda Mairo sai faman kuka take tana kiran ta bani ta shiga uku ta data momi tayi tana faɗin “sannu Mairo ni wlh na manta da yadda shower take mantawa ma nayi na haɗa miki ruwan da kai na yi hakuri kinji”

kai ta ɗaga tana kuka tace “ni a kaini gida gurin Gwaggo”

hakuri momi tayi ta bata daker tayi hakuri momi ta haɗa mata wasu ruwan tayi mata wanka ranar har kanta saida momi ta wanke,


da suka fito momi ta rasa kayan da zata saka mata dan ita bata ga wasu kayan kwarai da zata sa mata ba haka dai momi ta ɗauko wata tsohuwar a tamfa tasa mata,

momi ta kalleta tace “hau gado ki kwanta”

da sauri ta nufi gadon ta faɗa rub da ciki,


momi na gab da wucewa Mairo ta ɗago da jajayen idanunta ta kalli momi “mumo ko zaki aikeni?”

juyowa momi tayi “aike kuma Maryam kamar ya?”

tashi tayi zaune “in siyo miki wani abu ko aike”

murmushi momi tayi tace “a a ni babu abunda za'asiyo min koma abu zan siya saidai na aiki direba ko yara su siyo”

komawa tayi ta kwanta tana zubarda hawaye.

kai kawai momi ta girgiza ta fice.


Mairo tunda ta kwanta take wahalallen bachi sai uku da rabi ta farka koshi dan momi ta tadata ne.

hannunta Momi ta riko ta suka nufi bathroom kin shiga tayi ta lak'e kafaɗa “ni bazan shiga ba”

“yi hakuri ni zan haɗa miki ruwan ba zakiji zafi ba”

daker momi ta lallaɓata ta yarda suka shiga,


brush momi tasa tayi tare da alwala sannan suka fito,

tsareta momi tayi saida tayi sallah sannan ta riko hannunta suka nufo downstairs.


zaune suka tararda Qasin yana cin abinci laptop na gefensa yana aikin danne2.

tsaki momi taja bayan ya jama Mairo kujera ta zauna,

ɗagowa yayi yana kallon Momi “lafiya dai momi?”

saida ta zauna sannan tace “hala baka ci abincin ba?”

sosa kai ya ɗanyi yayi murmushi “indomi ce ta ɗafa”

taɓe baki momi tayi “to Allah ya kyauta ya sawwake”

kasa amsawa yayi saima kallon Mairo da yayi yace “bakida lafiya ne hala?”

kin masa magana tayi saima faman cin abincinta da take tana sauke ajiyar zuciya,


Story continues below

momi ce ta kalleshi tace “k'onewa tayi da ruwan zafi shine take fushi”

“ayyah sorry kijin injin bata jimu ba?”

“bata jimuba zafin daine ya raɓeta”

kanta ya shafa “sannu kinji?”

kai ta ɗaga masa tana aika lomomi,


suna haka Usman ya fito ɗakinsa ya nufi kofa.

kiransa momi tayi “Usman”

“na'am Momi”

“dan Allah jeka ɗaki ka ɗauki ATM ɗina kaje nan Damary plaza ka siyo ma Maryam kayan sawa”

“owk momi”

da sauri ya nufi upstairs.


tashi Mairo tayi jikinta na rawa tace “zan bishi mumo ina zuwa”

momi kamar tasan plan ɗinta ta zauner da ita “a a ba yanzu ba ba kasuwa zaije kuma ba daɗewa zaiyi ba”


da kuka tace “thom”

ta sunkuyarda kanta tana hawaye.

Qasin ya shafa kanta yana murmushi “yi hakuri bari ranar da nake free sai muje yawo ko ki zaga gari?”


kai ta ɗaga mishi ba tare data kalleshi.

murmushi momi tayi ta kalli Qasin tace “Qasin ya akayi da batun kwangilar?”

“na karɓa ni da kaina zanyi kuma baza a samu matsala ba insha Allah”

daɗi sosai momi taji “Allah ya taimaka ya shige maka gaba”


tashi Qasin yayi ysns faɗin “Amin momi bari naje part ɗina nayi wani aiki”

kai kawai momi ta ɗaga mishi ya fice rik'e da laptop.


© *Khadeeja Candy*

[11/5, 9:39 AM] Khadeeja Candy 🍧: *♡... MAIRO ...♡*


*BY*

 

    *_KHADEEJA CANDY_*


*13*


da ɗare Usman ya kawoma Momi kayan (tufafi) data aikeshi ya siyo,

aiko murna gurin Mairo ba'a magana sai tsalle take tana wani shafar tufafin tana jefasu sama tana rawa.

duk wani bachin rai dake ranta ranar gushewa yayi sai faman godiya take yima momi.

tun abun naba Momi dariya har ya koma bata tsoro ganin irin murnar da take kamar zata haukace sai faman uhu take, tana daredare harda hawaye,


momi dai da taga ba kanta baro mata ɗakin tayi ta sauko k'asa,

nan ta tararda Qasin yana aikin rubuce2,

guri ta samu ta zauna suka soma fira.


Mairo na jin muryarsa ta kwaso tufafin ta nufo downstairs da gugu tana faɗin “Qasin kaga tufafina da-”

kasa karasa maganar tayi saboda wani mugun kaye da tasha saman tile aiko nan kuka ya chaja salo ta koma yin na gaske,


dariyace tazo ma Qasin haka ya matseta ya nufeta ya tadata tsaye yana bata hak'uri yana murza mata gurin data gimu.


momi kan faɗa ta hau yi mata “yarinya ba kai sai bak'ar hauka tun ɗazu take murnar tufafin nan kamar mahaukaciya kekan kauyenciki yayi yawa Maryam”

Qasin na dariya yace “haba momi koni ai murna zanyi inna samu sabon tufafi zuwa fa tayi ta gwada min ko?”

kai ta ɗaga masa tana kuka, handkerchief ɗinsa ya ciro yana share mata hawaye.

“ya isa haka jeki gwada tufafin mugani suna miki kyau”

da ininniyar kuka tace “thom”

ta nufi ɗaki.


       ''' *   *   *'''

tun daga lokacin Mairo bata k'ara saka tufafinta na kauye ba saidai wayanda momi ta siya mata,

kuma ba laifi Usaman ya iya zaɓi dan duk tufafin data saka saisun yi mata kyau sun k'arɓi jikin ta,

kyau ta ma ba laifi da farinta sai kara fitowa yake ga gashin kanta kullum sai momi ta gyara mata shi,


taci maikyau tasha maikyau tasa maikyau wasa wasa cikin wata 2 tayi bulbul kamar ba itaba,

aiki kan yanzu Mairo ta ɗan fara sabawa dan kullum tare da momi suke haɗa breakfast kuma duk wani karamin aiki ita momi take sawa tayi tun tana fushi har ta gaji ta daina sai in taje ɗaki ta rika kuka tana zagin momi da cire mata albarka,


Story continues below

zancen guduwa yanzu ta daina tunda taga momi bata bari a fita da ita kuma in zata fita bata zuwa da ita babu yadda batayi ba momi tak'i yarda duk wata dabara ta ta saita rushe ta daina ma yima momi zancen ta hakura,


*_3 months later....._*

yau da far'ah Mairo ta tashi saboda tayi markin Gwaggo,

koda Momi ta shigo ta tasheta zaune ta tararda ita harma tayi alwala tana sanye da hijab,

da mamaki momi ta shiga bathroom bayan ta ɗoro alwala ta fito ta nufi waduraf tana faɗin “Maryam ya akayi yau kika rigani tashi?”

carbi ta nunawa momi tana wani gyaran murya kamar wata babbar mace wai ita mai tasbihi ba a magana,


“hmm Maryam manya”

momi ke faɗar haka tana k'ok'arin ɗaura zane,

hijab tasa ta shimfiɗa carpet ta rik'a carbin tana salati har aka tada sallah sannan suka bi zan'in masallacin dake kusa dasu,

suna karewa bayan suyi yan addu'o'e suka nufi kicin.


*_8:45am_......*

Mairo ta shiga jera breakfast a dining sai tsaki take tana faɗin “mumo yau munyi rana”

tsayawa tayi tana kallon agogn dake manne gefen gurin tana tunani yadda momi ta koya mata,


ta daɗe a tsaye tana kallon agogon ganin bata tuna ba yasa ta shiga shirmen ta “kinga fa mumi har wannan mai laulaye tayi (8) da mai k'afa ɗaya (4) da mai kai sama (9) gaskiya munyi rana yau”

da dariya momi ta fito kincin ta nufo dining tana faɗin “waike Maryam yaushe zaki daina wannan shirmen naki ne? ke kullum ana koya miki abu amman kamar kara toshe miki k'wak'walwa ake”

turo baki tayi ta nufi kujerar data saba zama ta zauna,

momi bata sake cewa komai ba ta shiga zuba mata abincin harsu Usman da Nura da Siraj suka fito suka nufo dining,


bayan sun zauna kowannensu ya shiga zubama kansa,

har suka fara ci Mairo bata ci nata ba sai kunbure2 take tana harararsu duk da momi ce take son ta harara amman ba dama.

babu wadda ya tanka mata sai Siraj dake k'ok'arin zaunawa,

“waike lafiya kike hararar mutane?”

saida tayi kwafa sannan ta kalleshi tace “ina ruwanka dani”

tashi yayi da niyar ya doketa momi ta tareshi “ai tace maka ina ruwanka da ita bai isaba?”

“tho momi baki ganin yadda take hararar mutane”

“ba da kai take ba ni take son harara bata da dama saboda nace bata gane agogo”

komawa yayi ya zauna yana dariya “LOL yarinya aike kullum liki minandak'u ce kulli yaumin ɗifɗif”

kifa kanta tayi da dining tana kuka,


momi ta kalleshi da siffar masifa “wai Siraj mi yasa kake wasa da ita ne bafa tabashiyarka bace mahaifinta da naku uwa ɗaya uba ɗaya suke”

hannu ya ɗaga “tho momi kice ta daina wasa dani”

“ai kai ka soma wasa da ita gashi har sauran suna son yi”

jan zib yayi a bakinsa alamar bazai kara cewa komai ba,


© *Khadeeja Candy*

[11/5, 9:39 AM] Khadeeja Candy 🍧: *♡... MAIRO ...♡*


*BY*

 

    *_KHADEEJA CANDY_*


*14*


sai a lokacin Mairo ta ɗago kai ta soma cin abinci,


_GOOD MORNING EVERYONE_

yau da abunda Qasin ya shigo dashi kenan fuskarsa ɗauke da murmushi ya ware hannayensa hannunsa ɗaya rike da wasu file.

duk juyowa sukayi suna kallonsa rabon da suji muryar irin wannan ta farinciki daga gareshi harsun manta,

wani sanyi ne ya ziyarci zuciyar momi dan tasan duk yadda akwai abun farincikin daya faru,


yana karaso ya mika ma momi file ɗin yana faɗin “lafiya kuke kallona hakane?”

murmushi sukayi suka ci gaba da cin abincisu dan sun san ko minene dole a fasa kwai suji,


a rikice momi take karanta har tana tsalleke wasu saboda daɗi tana kare karantawa ta mike tsaye ta rumgumeshi idonta cike da hawaye

“ai daman na faɗa maka Qasin duk ka ɗauki hawarana bazaja taɓa jin kunya ba kuma ka gani”

rumgumeta yayi yana dariya “haka ne momi na”

ko wannensu kasa cin abincin yayi sai murna suke suna yaba masa suna rumgumarsa,


Story continues below





Mairo kan ido ta sakar musu kamar tana cin abincinta dan ita mahaukata ta ɗaukesu tunda bata gane abunda suke yiwa murna,


saida tayi tsaki sannan suka tuna da tana gurin

ɗagata momi tayi saboda murna ta tsayar da ita saman dining tana faɗin “me kike yiwa tsaki yata? yau ranar farinciki cefa”

“to ba duk kunata murna ba kuma kunk'i ku faɗa min dalili”

“ayyah to yi hakuri bari na faɗa miki yayanku ne yaci nasara akan kwangilar da aks bashi har mutumen ya yaba masa da kalamai masu daɗi”

“to minene kwangila?”

“sashi akayi yayi gini sai kuma yayi sa'ah shine muke murna”

fashewa tayi da dariya “hahaha nima Qasin nayi murna”

“to ai ba haka akeba uhu ake ana tuma”

aiko kamar jira take ta soma yin sama tana yin kasa saman dining,


juyawa momi tayi tana kallon Usman da yayi maganar “kasanfa bana son iskanci dan ba hankaline da ita ba”

juyowa tayi ta sauke Mairo tana faɗin “ke kuma kinsan na rabaki da kiran sa Qasin ko to daga yau karna sake ji”

bata fuska Mairo tayi ta soma kuka,


dafata Qasin yayi “haba momi miyasa zaki sata kuka yaufa ranar farinciki ce”

share mata hawaye ya shiga yi yana faɗin “yi hakuri yi shiru kinji?”

makkale kafaɗa tayi “ni bazanyi shiru ba”

“aiko in bakiyi shiru ba ba zanje dake yawo ba kindai san kinfi kowa son yawo ko kina so naje dake?”

kai ta ɗaga tana share hawaye.

Qasin yace “good to ysu zanje dake kodan farinciki danake”

da far'ah tace “yanzu ko?”

“a'a sai an jima inna shirya harda tufafi ma xan saiya miki kiyita tsalle”

wata irin dariya ta saki tana tunowa da momi yasa ta karasa ba ta rufe baki,


ɗagowa yayi yana murmushi ya kalli momi “thank you more. momi”

“ur welcome Qasin nafika farinciki”

“momi ai har a tv aka nuno dan da yan jarida yaje dan yayi zaton zan to zarta”

“kwata2 yau bamu kunna tv ba bamu gani ba”

“ai tun jiya ne da dare ai”

hannu momi ta daga “oh nidai Alhamdulillah ai tunda anyi nasara”


     ''' *   *   *'''

ranar wuni sukayi suna farinciki momi harda rabon kuɗi ta rikayi ko abincin rana ma kasa ci tayi saboda farinciki,


*_2:30pm......_*

Qasin ya shigo sanye da kananan kaya,

zaune ya tararda Mairo tasha doguwar rigar fakistan momi ta mata farkin ɗin kanta kamar wata balara sai ɗan gyale na abayar da take rike dashi,

ta wani hakinci kamar wata princess ga bakinta yasha mai yar girace kawai momi batayi mata ba,


tsayawa yayi yana kallonta kamin ya kai hannu yaja hannunta su taɓe “eyye yarinya haka momi ta gyara ki?”

da sauri ta tashi tsaye “eh daman kai nake jira tun ɗazu”

murmushi yayi “to yayi kyau bari naga momi sai muje kinji?”

kai ta ɗaga masa ya nufi stairs.


bai daɗe ba ya fito ba mairo ta mika masa hannu ya rika suka fice yana yaba kwaliyarta,

suna kaiwa parking space ya buɗe mata giɗan gaba ta zauna shi kuma ya shiga driver seat. yayima motar key suka fice,


wuni sukayi suna yawo duk gurinda suka ga wani abun kwadayi sai ya tsaya ya siya,

Qasin yasha dariya saboda Mairo take murna kamar wata taɓɓabiya.


*_4:52pm....._*

suka nufo gida Mairo sai surutu take masa shidai tun yana dariya harya koma murmushi,


daf ta zasu shiga gida ta tuno da Alkawarin da yayi mata na siya mata kaya,

aiko nan tasa mai kuka dole ya juya ya nufi Dubai mall. suna isa ta shiga k'ok'arin rigansa fita amman ta kasa dan bata san yadda ake buɗewa ba,


saida ya fita sannan ys buɗe mata kofar ta fito sai dariya take tana yaba kyaun gurin,

suna shiga ta nufi wani gurin saida ya riko hannunta suka nufi sashen yara,

sannan ya saketa ya ɗauki basket ya mika mata ya riko kunnenta “karki kuskura wuce ɗauko kala uku uku kawai zaki ɗauko kinji ni ai?”

kai kawai ta ɗaga mishi badan ta fahimci mi yake nufi ba dan hankalinta nacan gurin kayan data gani,


Story continues below





haka ta nufi kayan tana wani leko harshe kamar karya tana shafa kayan.

tafi karfin minti 20 tana duba kayan sannan ta ɗauko kala biyar ta nufoshi tana dariya “duba kaga suna da kyau sosai”

ɗaya bayan ɗaya ya rika dubasu “haba Maryam har huɗu keda nacewa uku?”

“nidai su nake so”

“a rage kinji?”

lake kafaɗa tayi “a a nidai duka”


bai sake cewa komai ba ya nuna mata gurin biyan kuɗi “ɗauki ki kai can”

da sauri ta ɗauki kayan ta rigashi isa,

ana cikin lissafi ta ɗauko wata riga ta ɗora “harda wannan inaso”

bakin baki Qasin yayi yana kallonta can dai yaji tsoron ta sake ɗauko wani abun ya nuna mata kofa “Maryam jeki gurin mota ki tsaya harna fito kinji?”

ba musu ta fice ta barshi,


tsaye tayi jikin motar tana wasa da hannayenta duk wadda zai shiga saita faɗa masa akwai kaya masu kyau a ciki,

wasu basa kulata wasu kuma suyi ta dariyarta,

tana haka Yarima yazo shiga cikin wasu tufafi na alfarma fadawansa na take masa baya,

nunashi Mairo tayi tana faɗin “kai ma kayi sa'ar zuwa nan kayan suna da kyau”

kwatakwata bai lura da itaba sai a lokacin ya juyo ya kalleta a ransa yana _wani sabon tsari suka samune nasa yara sunayiwa mutane welcome_

suna haɗa ido Mairo tayi waje da ido “lahhhh kaine”

kayanshi ta shiga shafawa tana ɗaga masa gira.

can ta shaa nata kayan tana juyi tana rawar kai “ni ka gani yanzu kaya masu kyau nake sawa”


shikan kallonta kawai yake yana tunanin gurin daya santa. dan jikinshi yana bashi ya santa,

saidai ta ɗan kwanta masa lumshe ido yayi yana tsusar hot pink lips ɗinsa faɗawansa dai sai kallonsa suke da k'warorin mutanen dake guri


bai buɗe idon ba sai da ya tuna da murmushi ya rika fuskarta “ya akyi kikayi kyau haka? waya kawoki nan?”

saida tayi dariya sannan tace “yaya kuma momi ce tamun kwaliya”

“wane yaya?”

kamin ta bashi amsa Qasin ya fito ya nufosu fuskarsa ɗauke da mamaki.


nunashi Mairo tayi “gama shi nan”

kai ya ɗaga mata yana wani shu'umin murmushi.

Qasin na karasowa Yarima ya mika masa hannu “thanks to yhu once again My Men for the contract”

kallon hannun kawai Qasin yayi fuskarsa babu yabo ba fallasa ba tare daya amsa ba yace “ur welcome the perfect one”

murmushin fuskar Yarima ne ya kara faɗaɗa,

Qasin bai saje kylashi ba buɗewa Mairo mota “ke shiga muje”

da sauri ta shiga tana ɗagawa Yarima hannutana sama byebye.


da wani irin karfi Qasin yaja motar har saida Mairo taji tsoro,

Yarima yayi tsaye yana kallon motar har suka bace masa.


© *Khadeeja Candy*

[11/5, 9:40 AM] Khadeeja Candy 🍧: *♡... MAIRO ...♡*


*BY*

 

    *_KHADEEJA CANDY_*


*15*


tunda suka shiga motar Mairo kasa magana tayi saboda tsoro saima rike bel ɗin motar da tayi,

shima bai tanka mata ba saida suka kusa isa gida sannan ya soma magana ba tareda ya kalleta ba “ina kika sanshi Maryam?”

shiru tayi kamar ba zata amsa ba saida ya sake maimai tawa sannan tace “can gida na sanshi harda kuɗi yake bani da goribar bunni ba na taba faɗa maka wani yaban goriban bunni ba?”

kai ya ɗaga mata “eh ina ya haɗu dake?”

“can gida”

“gida ina?”

daidai nan suka iso gida yana yin parking ta yinkura zata taji bazata iya buɗewa ta juyo ta kalleshe “buɗe min zan fita”

yana kallon kallon fulawoyin gidan yace “sai kin faɗa min gurin da kika sanshi?”

kamar ta fasa kuka tace “bana ce maka can gida ba”

sai a lokacin ya kalleta “to ai baki min bayani yadda zan gane ba”

ganin babu sarki sai Allah dole tasa ta faɗa masa tun farkon haɗuwarsu,


“to tun daga lokacin baki sake ganin shi ba sai yanzu?”

“eh nidai buɗe min na fita”

“to ya akayi ya ganeki?”

“nidai ba shine ya ganeni ba ni ban saniba”

bai sake ce mata komai ba ya buɗe motar ya fita,

ya zagayo gefenta ya buɗe mata ta fito da guɗu ta nufi parlour. bayan ya rufe motar ya rufa mata baya,


parlour suka tararda momi da gudu Mairo ta faɗa jikinta “kinga yaya ya simin mai kyau”

dubawa Momi ta shigayi tana yabawa “eyyye yar yayanta duk ke kadai?”

“eh ni kuma na zaɓo kuma mukaje yawo”

“amman gaskiya yana ji dake to injin kin masa godiya?”

“eh na masa ko yaya?”

kai ya ɗaga mata yana murmushi

“eh kinyi bama iyaka”

“naji je ɗaki ki aje”

“to”

tashi tayi tana dariya ta nufi ɗakin.


momi ta kalli Qasin tace “magana nake son muyi dakai Qasin mai muhimmanci”

agogonsa ya kalla “owk momi amman fa kamar lokacin Sallah yayi”

agogon ɗakin momi ta kalla “inaga ma an soma sallar wani gurin jeka masallaci kawai nima bari na tashi nayi sallah gobe mayi maganar”

‘to’

kawai yace ya tashi ya fice jiki yake baya son maganar duk da bashi da masaniya akan abunda zasu tautauna,


*_washe gari....._*

da safe Qasin bai lek'a part ɗin momi ba ya wuce gurin aiki,

bai shigo gidan ba sai dare part ɗinsa ya fara wucewa saida yayi wanka ya sauke gajiya sannan ya nufo part ɗinta,

zaune ya tararda momi tana hamma Mairo na kasan carpet tana bachi Usman da Nura ma duk bachi suke saman kujera,

ta dasu Qasin yayi yana faɗa “momi sai ki rika barinsu suna miki bachi saman kujera manya dasu kuma maza”

“ai nasha musu magana har na gaji”

masifa Qasin yayits musu da suka farka basu dai ce masa uffan ba daya kare suka tashi kowane ya nufi ɗakinsa,


tsaki yaja ya zauna yana faɗin “shi yasa Siraj yake burgeni wlh shi halinsa da ban yake”

momi tace “ai Siraj yasan kansa gadai wata nan da take son biye musu”

kallon Mairo yayi “gaskiya momi ya kamata asa maryam makaranta dan inaga Gwaggo ba k'arɓarta zatayi ba”

“eh ai inaso ma maka maganar daman jira nake naga yadda zaman zai kasance dan kar asata daga baya tace abata yarta amman kaga yanxu tunda bata tambaya ba ai sai a sakata”

“ina gafa Gwaggo fushi ne tayi kinga ai ko waya bata kira duk da son da take yiwa Maryam”

“fushi kan ai da gani”


momi na yunkurin tashi Qasin yace “momi wace magana ce kikace zamuyi jiya?”

da idon bachi momi ta kalleshi “bachi zanyi ba wani magana yanzu yau ma ko leko nan bakayi ba bakayi breakfast ba ka fita”

“eh kirana akayi shiyasa kuma tunda naje nake aiki sai da magriba na samu kaina”

“to nidai bachi zanyi kuma ko gobe bani da time dan gobe abbanku zai dawo”

tashi yayi yasa hannayensa aljihu yana faɗin “Allah kawoshi lafiya ni bari naje na kwanta”

“to saida safe ta damun maryam kamin ka wuce”

ɗaki momi ta nufa tana hamma,


a hankali Qasin ya shiga data ita ganin bata motsaba yasa shi girgiza ta. ciki magagin bachi ta rika faɗin “mumi kinga Siraj ko”

“ba Siraj bane nine tashi kije ɗaki ki kwanta”

sake komawa tayi bachi haka yasashi data ita tsaye yana girgizawa “ke momi tace kije ɗaki ki kwanta”

“aa barni ni nan zan kwanta”

girgizata ya rikayi da karfi daker ya samu ta buɗe ido aiko tana ganin shine ta kara zube masa, dole ya ɗauketa ya kaita ɗakin yayiwa momi saida safe ya fuce.


*_4:21pm....._*

momi na zaune ita da Siraj suna fira sukaji an buga k'ofa. kofar momi ta kalla tace “waye?”

shiru akayi ba amsa nan ta kalli Siraj “jeka duba”

tashi yayi ya nufi kofar yana buɗewa yaga Yarima tsaye cikin kananan kaya yasa hannayensa ciki aljihu sai kanshin turare yake fuskarsa na kallon wani gurin.

kasa masa magana Siraj yayi shima kin juyo fuskar yayi ya kalleshi,

juyowa Siraj yayi ya nufi ɗakinsa tambayarsa momi ta shiga “lafiya wanene?”

yana gaf da shiga ɗakin yace “gashi nan waje nima ban sanshi ba”

tashi momi tayi ta nufi kofar, yadda Siraj haka ita ta tararda shi tsaye murmushi momi tayi tace “Yarima ne yau a gidan?”

sai a lokacin ya juyo ya kalleta shima fuskarsa ɗauke da murmushin “nine Momi”

“kuma ka tsaya a waje”

“to ai ba amin iso bane”

kai momi ta girgiza “Yarima ai naga gidan ba bakonka bane gidan nan ai gidanku ne tunda kai ɗana ne”

momi na cewa haka ta juyo ta dawo cikin parlour.

kai ya ɗaga yana karewa bakin kofar kallo kamar sannan ya taka kafarsa ya shiga cike da takama,


yana zaunawa momi ta dire mishi drinks.

“yau Yarima an tuna damu? kodai wani abun ne ya kawoka?”

da kanshi ya shiga zuba drinks ɗin yana faɗin “ziyara ce na kawo muku momi”

momi tayi dariya “aiko ka kyauta ya aiki to ya kuma gida?”

saida ya kurɓa drinks ɗin kusan so uku sannan yace “Alhamdulillah”

kallon parlour yake ta ko ina kamar mai neman wani abu.

can ya kalli momi yace “gaskiya momi Siraj bashi da tarbiya”

ko kaɗan momi bata jidaɗin maganar ba amman haka ta haɗiye tayi murmushi “yayan zamanine sai hakuri kannen naka”

taɓe baki yayi ya juyarda fuskar wani gefe.

momi zatayi magana Mairo ta fito kicin rike da abu a hannu tana faɗin “mumi kinga ni duk na wanke shuwakar kuma ta fita” maganar take tana kallon kujerar da Yarima yake zaune dan bata gane ko wanene ba,

momi tace “thom naji jiki gani nan zuwa”


yana juyowa suka hada ido murmushi ya sakar mata.

waje Mairo tayo da ido ta buɗe baki ta nufoshi da gudu rike da shiwakar da sauri momi ta tashi tsaye kamin ta rikota ta rumgumeshi har cup ɗin dake hannunshi ya faɗi.  
fisgota momi tayi ta jefar k'asan carpet “lallai Maryam baki da hankali daga ganin mutun baki san inda ya fito ba ki wani rumgumeshi dubi yadda kika bata masa riga”
momi ta kalli yarima “dan Allah Yarima kayi hakuri hankaline bata da”
cikin kuka Mairo tace “nida hankalina niba mahaukaciya bace”
hannu momi ta ɗaga zata ɗaketa Yarima ya rik'e “no momi plz”
hannu yasa ya ɗago Mairo yana bata hakuri,

kuka Mairo tace yanzu ta fara daman mai nema a duhu balle an yada duk yadda yaso tayi shiru k'iyawa tayi.
fuskarta ya kama da hannayensa biu ya rik'e iya karfinsa ta kasa juya fuskarta shi kawai take kallo.
“yi shiru kinji in kina son na baki apple da abu mai daɗi”
kai ta ɗaga “to na daina”
“good girl”
handkerchief ya ciro ya share mata hawaye ya cire mata majina,

juyawa tayi tana hararar momi k'asak'asa ta gefe Yarima yayi murmushi ya rika hannunta ya “muje ki raka ni”
lakkame masa hannun tayi “ba kace zaka bani abun daɗi ba”
baice mata komai ba ya kalli momi yana murmushi yace “ni ban wuce momi in Qasin yazo ki gaishe shi”
fuska a sake momi ta amsa mishi “to zan faɗa miki mun gode a gaida gida”
kuɗi ya ciro masu ɗan dama ya aje mata sannan ya fice rike da hannun Mairo.

motarsa ya nufa harya buɗe rike yake da hannunta yana zaunawa ya kama ɗayan hannum ya rike “faɗa min miye dan gantakarki da gidan nan?”
turo masa baki tayi “to ni nasan mi kake nufi ne”
shiru yayi yana tunanin yadda zai mata ta gane “faɗa min momi mamar suwa ce?”
kai ta ɗaga sama “maman yaya da Siraj da Usman da Nura su kenan”
“good ke kuma ina mamanki?”
“mu bamuda mama sai dai Gwaggo tana can gida”
“yauwa to faɗa min ya akayi kika zo nan gidan?”
“da sukaje can suka zo dani nan gidan”
“to faɗa min Qasin yace miki wani abu da ya gamu tare?”
“a a baice komai ba”
banɗir ɗin 500 ya ciro ya dora mata saman hannu yana faɗin “karki faɗawa kowa munyi wannan maganar dake kinji”
da karfi tace “to bazan faɗa ba” tana wani kallon kuɗi tana dariya.
har kasa ta duka tana masa godiya,
kunnenta ya kamo yana faɗin “duk kika faɗawa wani saina ɓata dake kuma bazan sake miki komai ba”
ɗagowa tayi tana kallonsa “wlh ba zan faɗa ba ko za a kasheni”
murmushi yayi “yauwa jeki kar moni taga kin daɗe”
tashi tayi da gudu ta nufi cikin gida.


 
saida yaga shigewarta sannan yayi ma motarsa key.
kaura suka tashi yi da Qasin daya kunno kai cikin gidan shi kuma yana k'ok'arin fita da sauri Qasin ya bashi hanya dan yasan shi ba jaye mishi zaiyi ba, saida ya fita sannan Qasin ya karaso parking space a ransa yana mamakin abunda ya kawo Yarima yanzu,

da sallama ya shigo parlour momi ta amsa masa Mairo ta nufeshi da gudu tana nuna masa kuɗin “yaya ka gani Yarima ya bani duka kuma ni kadai”
kuɗin ya karɓa ya duba yana kokarin zaunawa yace “momi miya kawoshi yanzu kuma”
“jiyara ta kawoshi kuma yace a gaishe ka”
“a gaishe ni? yanzu fa kasa bari yayi na shigo saida na kauce masa”
momi tace “to ai kasan halin kayan ka”
Mairo ta riko hannunsa “yaya kuma harda mumi yaba kuɗi masu yawa”

 
lakatar mata hanci yayi “ke wai ba ance miki momi ake cewa ba ki daina cewa mumi”
turo baki tayi tana kallon momi “to kuma yaya momi tace mun banida hankali”
kamin Qasin yayi magana momi tace “ai ba kida hankaline Maryam”
kara ɓata fuska Mairo tayi “kaji ko?”
Qasin yayi dariya yace “haba momi Maryam fa nada hankalinta komai na hankali take dan Allah ki daina ce mata mahaukaci”
“Allah ni bana mata ɗaukar masu hankali kaga abunda tayiwa Yarima yanzu?”
“mi ta masa?”
“bata fa sanshi ba daga ganinshi ta tazo a guje ta rumgumeshi ga hannayenta ba kyau har cup ɗin hannunshi ya faɗi”
Qasin ya kalleta “amman ya dakeki ko?”
momi tace “bai mata komai ba dama zan daketa hanani yayi inajin yan k'aurai ne bisan kai harda fa kuɗi ya bata”
murmushi Qasin yayi ya shafa kan Mairo.
yace “ya santa ne shiyasa”
“ina ya santa?”
nan ya bata labari kamar yadda Mairo ta faɗa masa da kuma haduwar da sukayi Dubai Mall,
Momi tace “shiyasa kika rumgumeshi ni ai nayi mamaki yadda naga ya sakar mata fuska harda share mata hawaye”
uhum kawai Qasin yace yana kallon siraj dake saukowa downstairs.

Story continues below



“Maryam faɗa min mi Yarima yake ce miki daya rike miki hannu?”
wani irin ɓata fuska tati ta ɗago tana kallonshi “ni baice min komai ba kawai yace yace yace yana siyomin kayan daɗi kuma kuma yana in yana gaida momi”
taɓe baki yayi “aikin banza”
momi tace “kaga halin nan naks Siraj sam bana sonsa ai kodan girmanka da yayi yaci ake ka gaisheshi amman kaki”
“wlh momi matukar bai sauke wannan girman kan dake tare dashi ba to baza mu taɓa haɗa hanya ba”
cikinsa momi tayi da faɗa “bana fason shashanci Siraj bai girmeka miye abun girman kai a ciki mutun ya tako kafarsa har nan cikin parlour nan ka kasa yi masa magana kaifa da kanka ka buɗe masa kofa ina ruwanka da girman kansa”
murmushi yayi ya nufi kofa “Siraj”
kiran Qasin ne ya juyo dashi “na'am yaya”
“nasan bai fika da komai ba amman ka rika masa magana tunda momi bata so”
kai ɗaga masa ya fice.

 
candynovels.wordpress.com

© *Khadeeja Candy*
[11/5, 9:43 AM] Khadeeja Candy 🍧: *♡... MAIRO ...♡*

*BY*
 
    *_KHADEEJA CANDY_*

*17*

tsaki momi taja “da gaskiya Yarima da yace Siraj bashi tarbiya”
kallonta Qasin yayi “shi yace haka?”
“eh”
“shi Yarima har ya iya buɗe baki yace Siraj bashi da tarbiya”
momi tace “ai da gaskiyarsa ace murun ya shigo ka kasa masa mana dama fa na tambayeshi cemun yayi baisan ko wanene ba jifa”
“haba momi duk abunda Siraj ai baici ace gaban idonki ya furta bashi da tarbiya ba shi har ya isa yayi miki wannan maganar gaban idonki duk fa wadda ya aibanta maka abu kaiya aibanta babu wadda zai buɗe baki kaf duniyar nan yace yayan gidan nan basu da tarbiya”
cikin faɗa yake magana cike da jin zafin maganar.

 
momi tace “miye na wani tada jijiyar wuya akan wannan maganar”
tashi yayi tsaye yana faɗin “hmm iskancin Yarima yayi yawa sai yayi nadamar furta wannan kalamin”
tashi ita momi tayi tsaye “Qasin bance kayi rigima da shiba wannan maganar kuma ta wuce karka kuskura ka masa wani akan wannan maganar kaji na faɗa maka”
tana kawai nan ta nufi upstairs.

Mairo tayi war da ido ta rufe baki “tho momi tayi fushi kuma kaine”
murmushi yayi ya shafa kanta ya fice.

saida momi taji ficewarsa sannan ta fito tun kamin ta karasa saukowa Mairo tace “momi yaya yasa kinyi fushi ko?”
momi ta karasa saukowa tana faɗin “a a ni banyi fushi ba”
“to mi yasa kika masa faɗa kuma kika shige ɗaki saida ya fice kika fito?”
basarda maganar momi tayi “muje cikin mu karasa girki kar babanku ya dawo bamu kare ba”
da sauri ts nufi kicin momi ta rufa mata baya,

*_washe gari....._*
tara saura Qasin ya shigo part ɗin momi zaune ya tararda ita tana kallon aljazeera news saida yaɗan kalleta sannan ya zaina kusa da ita yana gaisheta,
juyowa tayi ta kalleshi fuskarsata ba yabo ba fallasa bayan ta amsa tace “ga abun breakfast ɗinka can inka kare zamuyi magana”
faduwa gabansa ya ɗanyi jin harsun karya basu jirashi ba,
su jiki a sanyaye ya kalli momi yace “ke har kun karya ne?”
“eh yau tea kawai nayi su Usman da Nura sunci nasu sun tafi makaranta”
“ke fa momi?”
“ni tun part ɗin babanku na karya nida Siraj maryam ce kawai bata tashi bachi ba”
bai sake cewa komai ba ya tashi ya nufi dining.

ruwan tea kawai ya zuɓo ya dawo kusa da momi ya zauna “momi wace magana ce?”
shiru momi tayi na ɗan wani lokacin kamin ta kalleshi tace “akan maganar matarka ne”
faduwa gabansa ya ɗanyi “momi wani abun ne?”
“a a ba wani sabon abu bane kawai dai na gaji da dafa maka abinci kana ci,
matarka na kwance tana yadda taga dama da aurenka ace kullum sai kazo nan kaci abinci kaci na rana kaci na dare banda na safe  tu na maka wannan lokacin da baka da aure yanzu kan bazan maka gaka ba”
Qasin jim ya ɗanyi sannan ya kalli momi yace “momi bata saba bane kota girka ba wani daɗi yake ba”
“to ta rika girka maka haka nan ko ruwa ne ta rika dafa maka kana sha daga yau dai bazan sake aje maka abinci ba kodai kayiwa kanka abun kunya kaci na kasuwa ko kuma ka cilasta mata ta girka maka”

 
Story continues below



“to momi a bamu maryam saita ri..-”
hannu momi ta ɗaga mishi “dan Allah karka soma na baka maryam ita da bata san zafin gikinta ba ko? kai da ka iya kare mata in anyi magana ka iya kareta ita yar masu kuɗi yar boko bata iya komai ba sai hutu ko to nadai faɗa maka kuma bazan bada maryam ba in yar aiki zaka ɗauko ya rage naka”
kansa na kasa har momi takai aya,
ko kaɗan bai jidaɗin maganar ba.
       “shikenan momi zan san abun yi shine kawai matsalar?”

kai ta ɗaga mishi tana kallon Mairo dake saukowa sanye da kayan bachi.
murmushi ya sakar mata “maryam kin tashi?”
“eh momi ina kwana yaya ina kwana”
“lafiya kalau kin tashi lafiya?”
kusa da momi ta zauna tana “kalau momi yau ba ayi kari ba?”
“anyi kinga naki can kan dining”
zata tashi Qasin yace “momi nafa nema wa Maryam makaranta”
sai lokacin momi ta ɗan sakar masa fuska “amman kuwa daka kyauta gaskiya a ina?”
“nan tudun wada Alex international school makarantar nada kyau kuma suna karatu sosai”
wani daɗi Mairo taji ta riko hannunshi “yaya da gaske?”
“da gaske mana ina miki karyane?”
“a a kuma zanje?”
“eh yau zamuje su tantanceki in aka shirya komai saiki fara zuwa”
tashi tayi ta shiga rawa tana taɓi da hannu momi tayi dariya “yau fa abun nema ya samu sai a dage ayi karatu in yaso sai a samu wadda zai rika miki lesin kina ɗan karawa”
Qasin ya tashi yana faɗin “nima haka nake sonyi yadda zatayi ssurin fahimta da kuma islamiya sai a nema mata ta na kusa kidai shirya mata kamin 11 sai muje ayi komai”
“to saika fito”
Mairo ta kalleshi “yanzu zamuje?”
“a a saikin karya kinci abinci”
“to bari nayi sauri”
da gudu ta nufi dining shi kuma ya fice yana murmushi,

'''   *    *    *   '''
tunda suka fita sai basu dawo ba sai dare Qasin na rike da hannunta suka shigo parlour.
Siraj ne ya taresu yana zolayar Mairo “eyye yar kauye an sata makaranta eyye aiko za a ga kauyanci kai”
murguda masa baki tayi “eh naji koma minene naji mai k'aton kai”
momi tayi dariya “a a maryam kan yar birni ce ko?”
nan Mairo ta nufeta “eh momi kuma karantar nada kyau kuma gidan sama ce har sun bani kayan makarata kuma momi wlh suna ta turanci harda yan yara”
Siraj yace “ke kan harki kare bazaki gani komai ba sai shinkafa”
ɓats fuska tayi “momi kin jishi ko?”
momi ta shafi fuskarta “ke kyaleshi xuwazuwa kema zaki iya ai da tambaya akan zama malami”
dariya tayi ta kwanta jikin momi tana rufe ido,

 
momi tana kallon Qasin tace “an kare komai ko?”
“eh anyi komai sunce monday zata iya fara zuwa ga uniform nan sun bata na biya kuɗin scul bos zata rika zuwa 7:30am tana ɗaukar ta in kuma suka tashi zata kawo ta”
“to Allah ya taimaka abbanku ma ya jidaɗi sosai”
murmushi yayi ya tashi “bari naga abbah naje na kwanta”
kai momi ta ɗaga mishi Mairo ta ɗago tana kallonsa “baza kaci abinci ba?”
kallon momi yayi dake kallonsa,
can ya ɗauke kai yace “bana jin yunwa”
ya sun kuyarda kai ya fice.

candynovels.wordpress.com

© *Khadeeja Candy*
[11/5, 9:43 AM] Khadeeja Candy 🍧: *♡... MAIRO ...♡*

*BY*
 
    *_KHADEEJA CANDY_*

*18*

 
wasawasa Mairo ta fara karatu a'na mata lesin a gida na makaranta ma Qasin ya sakata.
in kuma lokacin islamiya yayi momi ta tura bata samun zama inba weekend ba da dare ma Siraj ne yake tisa mata ko Usman,

*_2:30pm..._*
schools bus ta sauke Mairo.
da gudu ta shigo parlour tana faɗin “momi yau”
bata karasa magabar tayi shiru ganin Yarima zaune saman kujera.

ware mata hannaye yayi yana murmushi kaɗan kaɗan ta karaso tana kallon upstairs.
saida ya mata kiss a goshi sannan ya rumgumeta,

da sauri ta ɗago tana masa magana kamar mai raɗa “ina momi?”
schoolbag ɗinta ya shiga cirewa “bata nan nima ban tararda ita ba”
“tana ɗaki ko tana kicin”
kai girgiza mata “bata nan ta fita”
“a a bari dai na duba”
kicin ta nufa ta fara duba bata ga kowa ba nan ta nufi ɗakin momi nan ma bata nan haka ta fito ta nufoshi hannu a baki ta ɓata fuska,
hannu ya mika mata yana murmushi “zo nan bana faɗa miki bata nan ba”
ba musu tazo kusa dashi ta zauna hannu yasa ya cire mata takalmin makaranta da safa ya kara janta kimusa dashi ya riko mata fuska,
“pretty gal wani sirrin zanyi dake”
shiru tayi sannan tace “na minene?”
“bazaki faɗawa kowa ba?”
“wlh Allah ni bazan faɗa ba kofa wannan da kace karna faɗa har yanzu ban faɗawa kowa ba”
hannunsa yasa yana taɓa lips ɗinta “da gaske kodai kin faɗa?”
“wlh ban faɗa ba”
“yauwa haka nake so wannan ma karki faɗawa kowa kuma karki bari kowa ya gani kinji zan baki abun daɗi da kuɗi kinji”
“tho amman ka xaka kawo min kayan daɗi da gaske harda ice cream da madara kuma kaje dani yawo”
hannunsa yasa yana shafa gefen fuskarta “zan miki duk abunda kike so matukar zaki mun abunda na saki”
da sauri tace  “zanyi minene?”
“zan fada miki zaki daiyi ko?”
war tayi da ido “eh da gudu ma”
murmushi yayi ya shiga mata chakulkuli tana dariya saida tayi mai isarta ya jata jikinshi ya rumgumeta yana shafa bayanta,

Story continues below

 


“Maryam....”
kamar daga sama taji muryar Qasin da sauri ta ɗago tana ganinshi jikinta ya shiga rawa Yarima kuna bai fasa shafa bayanta da yake ba koma ɗagowa baiyi ya kalli Qasin ba saima haɗe fuska da yayi yana wani tsusar baki da yake na salon iskancin.

tsawa Qasin ya katsa mata “mi kike nan?”
tashi tayi tsaye cikin rawar murya tace “momi bata nan”
“bashi na tambayeki ba?”
razana tayi sosai tayi bayabaya tana son yin kuka zatayi magana Yarima ya tari numfashinta ba tare daya kalli gurin da Qasin yake ba “ba komai take ba miye matsalarka?”

kara haɗe fuska Qasin yayi yace “I thought da ita nake Magana”
tashi Yarima yayi tsaye yasa hannayensa Aljihu ya nufi Qasin cikin wata tafiya ta isa da tak'ama,

saida ya isa daf da fuskar Qasin ya sakar masa wani shu'umin murmushi yace “don’t put words into my mouth. I have got plenty to say”
wani kallo ya watsa masa tun daga samansa har kasa ya ɗauke kai ya fice.

wani kallo Qasin ya bishi dashi cike da jin haushi can ya juyo ya watsama Mairo wata muguwar harara,
aiko jikinta ya kara shiga rawa kamar mai jin sanyi.

cikin tsawa Qasin yace “baki san wanene Yarima ba ko miya tsayarda ke gurinshi?”

kasa masa magana tayi babu abunda zuciyarta take nuna mata saita shige cikin ɗaki ta kulle karya ɗaketa duk da bai taɓa dukanta ba amman haka zuciyarta take nunama ganin yadda yake harararta,

hankalinta bai kara tashi ba saida taga ya nufo gurinda take,
sakar masa ido tayi saida ya kisa kawowa kusa da ita ta watsa da gudu,
cikin zafin nama ya kaɗe mata k'afa ta faɗi.

gashinta ya riko ƴya tada ita tsaye “ina zaki ba tambayarki nake ba?”
fashewa tayi da kuka tana rokonsa “dan Allah kayi hakuri ka yafe min bazan kara ba wayyo Gwaggo momi”
saida ta kira momi ya tuna da ita da sauri yaja hannunta suka nufi kofa.
tana masa ihu ya buge mata baki yana mata alamar tayi shiru ba shiri ta rufe baki tana son mayarda kukan,

 
part ɗinsa ya nufa da ita wani emptyroom ya nufa da ita.
saida suka shiga sannan ya sake mata hannu ya kulle ɗakin ya zare bel ɗinsa ya buɗe mata ido “mi ya kaiki kwanta masa a jiki?”
baya tayi tana kuka ta kasa mace masa komai,
matsowa yayi yana faɗin “duk na sake ganin kin rumgumeshi saina miki shegen duka na rufeki cikin ɗakin nan babu wadda ya isa ya ceceki”

sai a lokacin ta soma magana “dan Allah yaya kayi hakuri bazan sake ba wayyo momi”
bel ɗin ya ɗaga sama kamar zai buga mata wani irin ihu ta saki tayi cikinshi ta rumgume mishi kafafu tana kuka,

“lafiya Qasin miya faru?”
mansura ce take masa tambayar tana jijjigar kofa.
nan Mairo ta koma kiranta “anty mansura zoki ceceni”
ɗagota “aya rufe min baki”
da sauri tasa hannu ta toshe baki tana ɗaga masa kai.
juyawa yayi ya buɗe kofar ya dawo parlour bel ɗin dake hannunshi mansura ta rika kallo kamin ta kunno kai cikin ɗakin tana duɓe duɓe,

bata ga komai ba sai Mairo take tsaye rufe da baki tana shawaye.
rikota mansura tayi suka fito gurin Qasin ta nufo tun kamin ta karaso ta jefa masa tambaya “mi kayi mata Qasin?”
ba tare daya kalleta ba yace “mi kike tunanin zanyi mata?”
“ka bani amsa ta kawai Qasin ya zaka saka ta cikin ɗaki harda zare bel zaka ɗaketa mi tayi maka?”
wani dogon tsaki yaja ya tashi fuska a haɗe ya fisgi hannun Mairo suka fice.

tunda suka fito Mairo take masa magiyar karya daketa,
yana shigowa parlour ya jefarda ita saman kujera yana kiran momi.
jin shiru yasa ya nufi upstairs. bai jima ba ya fito ya nufi kicin nan ma bai jima ba ya fito ya nufi gurin Mairo dake kuka,

 
da sauri ta tashi zaune tana share hawaye sai wani numfashi take kamar zai ɗauke,
“ina momi?”
“ta fita koda na dawo ban ganta ba Yarima kawai na isko”
cikin rawar muryar kuka take masa maganar,

Story continues below



ido ya tsura mata tayi kasa da kanta hawayen na zuba.

candynovels.wordpress.com

 
© *Khadeeja Candy*
[11/5, 9:43 AM] Khadeeja Candy 🍧: *♡... MAIRO ...♡*

*BY*
 
    *_KHADEEJA CANDY_*

*19*

ajiyar zuciya ya sauke ya ciro handkerchief ya kama fuskarta yana share mata hawayen “yi hakuri kinji bazan sake ba daina kuka”
kai ta ɗaga masa tana wani wahalallen numfashi,
kwantarda ita yayi saman kujera “wanta kiyi bachi?”
harta kwanta sai kuma ta ɗago ta kalleshi “yaya karka faɗawa momi kaji?”
kai ya ɗaga mata ya tashi ya fice.

takura kanta tayi saman kujera ta matse guri ɗaya kamar wadda aka cilasta tana matsar kwallah har bachi ya ɗauke ta,

 
'''   *   *   *   '''

*_2 hours letter..._*
can cikin bachi taji muryar momi da Siraj,
    da sauri ta tashi tana soshe2.
Momi na kallonta taja wani dogon tsaki “haba Maryam ace mutum kana girma kana cin k'asa kamar ki ace inkin dawo makaranta ba kisan ki cire uniform ba saidai ki samu guri ki kwanta dubi kiga har lokacin islamiya ya wuce kuma baki san ki saka uniform kije ba”

ɓata fuska tayi “to momi ba fita kikayi ba kika barni”
nan momi kasa ce mata komai tayi dan takaici in banda tsakin data sakeyi ta nufi kicin,

momi na shigewa Siraj yaja mata kunne “ba wani daman baki son makaranta yar kauye”
fashe masa tayi kuka ta tashi tana aika masa mugayen duduna tana son huce haushinta akansa.

tsawa momi ta katsa mata “wuce ki cire uniform ɗin nan kiyi wanka kila ma ko abinci baki ciba?”
kai ta ɗaga
Momi tace “Allah ya shiryaki maryam wuce kije kiyi wanka duk kika sake yin abunda kikayi yau saina miki shegen duka”
kamar ta fasa kuka ta nufi stairs Siraj na zolayarta,

 
ta kusan minti 30 toilet ɗin tana wasa ruwa saida taji motsin momi a bedroom sannan ta fara wanka,
koda ta fito momi na zaune saman kujera tana duba wasu matirial da atanfofi.
     kallonta kawai Mairo tayi ta nufi waduraf ta ɗauko wata atamfa red colour riga da saket tasa ko mai bata shafa ba ta janyo k'aton hijab ɗin momi tasa ta shimfiɗa carpet ta soma sallah,

momi na kalle da ita saida ta rama azahar sannan tayi la'asar.
bayan ta sallame ta cire hijab ɗin ta jefar saman bed ta nufi kusa da momi ta zauna,

    “momi kayan waye?”
kyaleta momi tayi saida ta kare danne2 wayar da take sannan ta kalleta “na siyarwane”
shafa kayan ta shigayi “wlh momi suna da kyau suma siyarwa zakiyi?”
momi bata amsa ba ta kama hannunta ta kira sunanta a natse “Maryam”
dariya tayi “na'am momi”
“magana zamuyi ki bani hankalinki kinji banason kisa wasa ki daina dariya kinji?”

wani haɗe fuska tayi saida tasa momi murmushi sai kace wani cartoon ta wani tada kafaɗu “thom ina jinki?”
a natse  momi ta soma mata magana yadda zata fahimta “maryam ki daina abunda kikeyi kinji ba kyau kinga kara girma kike ba ragewa ba ya kamata ki rika sanin ciyon kanki ki daina abunda kike”

“tho ni kuma momi mi nayi?”
ajiyar zuciya momi ta sauke “yanzu fa saida kika rama azahar sannan kikayi la'asar kina ganin kin kyauta?”
kai ta girgiza alamar a a momi tace “tho kingani wadda fa yake haɗa salloli azaba ake masa ba kyau ki daina kinji?”
nan ta ɗaga kai “kuma kinga in kika dawo makaranta maryam basai nace ki cire uniform ba ki rika cirewa duk abunda kika san aikin kine ki rikayi basai nace kiyi ba kinji? ki zama yarinyar kirki”
wata dariya ta rikayi tana kallon momi tana tsutsar leɓenta na kasa,
can dai ta kawarda fuska tace “tho momi na gane koma minene kike nufi”
shafata momi tayi “yauwa yata haka nake so kuma ki dage ki rika karatu ba wasa banda faɗa ko jan magana kinji?”
nan ma kan ta ɗaga ta tashi tsaye “nidai bari naje naci abincin yunwa nake ji”
bata ko tsaya jiran abunda momi za taceba ta fice.

 
Story continues below



tana saukowa downstairs Qasin na shigowa.
suna haɗa ido ta juya da sauri zata koma hannu yakai ya rikota “ya haka ina zaki?”
upstairs ta rika nunawa “ɗaki zan kwanta ne”
murmushi yayi yaja ta suka nufi kujera bayan ya zauna ya zaunarda ita “baki san ba kyau bachin maraice ba?”
“eh ni ban saniba”
“tho ba kyau ki daina karki sake bachi da maraice”
“tho na daina bazan sake ba”
idonta a kasa take amsa masa dan tsoron kallonsa take.
lura da hakan yasa ya sakar mata hannu yace “tsorona kike ko maryam?”
shiru tayi tana wasa da hannayenta fuskarta ya riko “faɗa min mana tsorona kike ne?”
ɓata fuska tayi ta soma magana “nidai bana son duka in mutun yana dukana tsoronsa nake sosai”

murmushi yayi “tho na daina bazan sake ba ai ban dakekiba”
“eh amman ai kaso ka dakeni dan dai anty mansura tazo ne ka kyaleni”
tana maganar tana wani langwashe langwashen kai da turo baki,

dariya yayi tace “ai ba mansura ce ta ceceki ba daman ba dukanki zanyi ba”
harara ta watsa mishi “kai wlh karya ne tho miyasa ka ɗaga dankon zaka buga min?”
“minene sanki?”
rufe ido tayi tace “wannan wadda kaso ka dakeni dashi”
“bel?”
kai ta ɗaga tana kara matse ido dariya yayi yace “ki yarda maryam bazan iya dukanki ba kawai dai horaki nayi”
kwanta masa tayi saman jiki tana dariya,

 
“wlh karya ne dukana kaso kayi”
kunnenta riko ya rika murɗawa “ni nake karya?”
dariya ta rikayi tana faɗin “na daina ba kaiba”
haka ya rika wasa da ita soma masa kuka sannan ya saketa ta nufi kicin shi kuma ya fice.

washe gari tunda safe Mairo ta shirya kanta duk abunda momi ta saba mata ita tayiwa kanta,
sosai momi ta jidaɗi da schoolbus ɗinsu tazo har bakin gate momi ta rakata ta buɗe mata motar ta shiga.
hannu ta rika ɗagoma momi har suka fice,

*_2:30pm..._*
ta shigo gidan da sallama ta shiga parlour momi ta amsa mata da fa'ah “wa'alaikissalam yar mama an dawo?”
kai ta ɗaga mata tana cire takalmin makaranta,

daga gurin da take zaune ta jefasu gurin da aka tana da dan ajeye takalmin tana faɗin “momi yau Yarima ya kai mana ziyara a makaranta”
Usman dake zaune kisa da momi yace “da gaske?”
“eh wlh harda chocolate ya raba mana”
momi tace “gurinki yaje ko makaranta gaba ɗaya”
“a a makaranta dai kofa jiya yaje kuma yazo gidan na-”
shiru tayi ta kasa karasawa sai rabon ido take. momi tace “jiya ya zo nan? bayan fitana ko?”
wata dariya tayi “ke momi na tuna mafarkine nayi ba gaske bane”
tashi tayi da sauri ta nufi upstairs “bari naje nayi sallah nayi shirin islamiya”
  tanayi tana waigo momi harta shige.
momi kan daɗine ya isheta tana gani ta fara samun kan Mairo.

© *Khadeeja Candy*
[11/5, 9:43 AM] Khadeeja Candy 🍧: *♡... MAIRO ...♡*

*BY*
 
    *_KHADEEJA CANDY_*

*20*

washe gari ma Mairo ita ta shirya ma kanta komai bayan ta saka safa ta riko schoolbag ɗinta ta nufo downstairs.

da dariya ta sarasa saukowa ta rumgume Qasin dake zaune saman kujera rike da laptop,
aje laptop ɗin yayi yana murmushi ya zaunar da ita saman kafafunsa “maryam har kin shirya?”
ɗagowa tayi tana murmushi “eh kuma ni na shirya kaina”
saukar da ita yayi jin motar makarantarsu ya karɓi jikar hannunta yasa mata,
da sauri momi ta fito kicin rike da kular abincinta tana faɗin “oya karɓi ga abincin ki naji motar ku”
da gudu ta karɓa ta nufi gurin da takalminta suke ta saka harta fice sai kuma ta dawo ta tsaya bakin kofa “momi ba zaki bani komai ba?”
“mi zan baki?”
shiru tayi tana bugun kofar parlour.
hannu Qasin yasa aljihu yana cirowa ya mika mata ɗari biyar,
wata dariya ta saki jikina na rawa ta karɓa tana masa godiya “na gode yaya” kai ya ɗaga mata ta fice da gudu.

ɓata fuska momi tayi tace “Qasin bana so karka sake ka ɗauki kuɗi har ɗari 500 ka bata”
hannu ya ɗaga “shi kenan na daina amman naga kamar bada yawa bane”
cikin faɗa momi tace “tho na dai faɗa maka bana so duk kyautar da ita karta wuce 100 zuwa k'asa”
tana kaiwa nan ta nufi kicin,
da sauri Qasin yace “owk momi yi hakuri ai ya wuce zo kiga wani abu?”
yi tayi kamar bata jishi ba shige kicin ɗin saida ta kare abunda take sannan ta fito.
har lokacin yana zaune ƴyana danne2 sa,
kujerar dake kusa dashi ta zauna “gani ya akayi?”
ɗagowa yayi ya kalleta “momi ɗan ruwan tea ma bazan samu ba?”
taɓe baki momi tayi “au daman jiran kake na ɗauko maka breakfast? inma shine dalilin zamanka nan tho tashi ka koma part ɗinka dan kasan munyi ba'ada dakai tun farko”
dariya yayi “a'a momi bashine ba abu zan nuna miki”
laptop ɗin ya ɗauko ya ɗora saman jikinta “kinga wani design ɗin wata kwangila da za'ah ba kanfaninmu”
duba momi ta shigayi tana faɗin “amman kan abun da girma sosai mi za a gina haka?”
“wani kanfani suke so a gina musu na sarrafa motoci _JAMES GLOBAL AUTOMOBILES_ sunan kanfanin shine na farko da zai kafa branch a Nigeria”
momi tace “aiko dasun kyauta muma mu ɗan samu cigaba kuma matasan mu su samu aiki”
“sosai ma momi kinga in aka ginashi mutun kusan ɗari biyar zasuyi aiki karkashin su kinga ai an ɗan rage kuma kanfanin sun iya motoci ana son motocinsu sosai sune zakiga J.G.A mutunin ɗan amerika ne”
momi tace “amman naji daɗi to kai zaka gina musu gurin ne?”
“tho haka ake tunani amman dai ba ni kaɗai bane mu uku aka kaimusu zasu zaɓa ne saisu bada kwangilar ga wadda suka yarda da aikinsa amman dai mutane da yawa ni suke cewa saboda kanfanin fitaccen kanfanine kuma muna aiki babu kissa ciki”
murmushi momi tayi “tho ai haka ake so Allah ya taimaka yasa ka samu”
“amin momi dan gaskiya zamu samu kuɗi masu yawa”
“to Allah ya yarda ya taimaka”
“amin”

Story continues below



tashi yayi rike da laptop ɗin yana kallon “bari naje can na karya”
kai momi ta ɗaga mishi “da yafi”
murmushi yayi ya fice.

*_7pm..._*
Mairo na zaune parlour kasan carpet ita da Siraj yana duba littafanta na makaranta sai zolayarta yake tana masa kuka yana sa ta karanta gurinda bata iyaba yayi mata dariya ita kuma ta buga masa fillo. suna haka sukaji an taɓa kofa duk juyawa sukayi suna kallon kofar,

cike da takama Yarima ya shigo ba tare da yayi sallama ba ya nufo gurinda suke,
wani irin haɗe fuska Siraj yayi kamar bai taɓa dariya ba,
wannan karon Mairo batayi unkurin tarboshi ba ido kawai ta sakar masa tana dariya.
da murmushi ya karaso kusa da ita tashi Siraj yayi tsaye da niyar tafiya tunowa da magagganun momi yasa ya kalli yarima yace “sannu da zuwa”

banza ya masa yana tsutsar lips ɗinsa.
juyawa Siraj yayi cike da bachin rai ya fice,
            hannu Mairo ya riko yana murmushi ya nufi kujera suka zauna tare.
     
kallonsa tayi tace “ba kaji Siraj yana mska magana ba?”
lakatar mata hanci yayi “na jishi bana jin amsa masa ne”
murmushi tayi gyaɗa masa kai,
wasa ya shigayi da hannayensa yana faɗin
“pretty gal ya maranta?”

“lafiya kalau”

“ina momi?”

“tana ɗaki na kirata?”

hannu yasa yana taɓa lips ɗinta “a a karki kirata”
saida ya ɗaga kansa ya kalli upstairs sannan ya kalleta yace “gurinki nazo kinsan munyi dake zan saki abu ko?”
kai ta ɗaga “eh kuma kace zaka bani kuɗi kuna kace zak-”
rufe mata baki yayi da sauri jin motse saukowar mutun downstairs,
saida yayi mata alama da tayi shiru sannan ya juya da murnushi yana kallon momi.
“Yarima yanzu ake tafe?”
“eh momi ya wunin gidan?”
taka kokarin zaunawa tace “lafiya kalau maryam baki ɗauko masa abun sha ba?”

war tayi da ido tace “lahh mantawa nayi bari na ɗauko”
tana sauka ya riko hannunta ya tashi tsaye “a a momi barshi kawai yanzu zan wuce”
“da wuri haka?”
“eh kinga an kira sallar isha kuma daman biyowa kawai nayi naga Maryam”
da ɗan mamaki momi tace “owk tho a gaida gida”
hannu yasa aljihu ya ciro dubu 20 ya aje mata “ayi hakuri da wannan momi”
murmushi momi tayi “Yarima kenan Allah dai ya amfana”
baice komai ba yaja hannun Maryam suka fice,

motarsa ya buɗe mata ta shiga bayan ya rufe ya zagayo shima ya shiga.
“ina zamu?”
tambayar data fara jefa masa kenan tana kallonshi,

baice mata komai ba yasa hannu baya ya ɗauko laptop ya ɗora mata saman jiki “kinga wannan abun?”
“eh”
“kin taɓa ganinta?”
“eh sunanta kwanfuta”
mirmushin jindaɗi yayi “good wa kika taɓa gani da irinta?”
“malamin makarantarmu da yaya”
“tho kinsan mi nake ao dake?”
kai ta girgiza “a a”
“ta yaya nake son ki ɗauko min”

da sauri tayi waje da ido ta rufe baki “kaikai nidai babu ruwana baya so fa ina taɓa mishi kaya”
“ke mayarwa zanyi kawai inason na arane na ɗanyi wani abu sai na baki ki mayar”
lake kafaɗa tayi “a a gaskiya saidai nace ya aro maka”
haɗe mata fuska yayi “a a karki kuskura kice masa haka bazai bayar ba kuma inma yaji dukanki zaiyi kuma nima na ɓata dake”

hannu yasa ya ɗauko wata leda dake bayan ya mika mata “kinga kayan daɗi nan na siyo miki kuma gobe zan karo miki wasu kullum zan rika siyo miki kuma na baki kuɗi amman fa sai in kin aikata abunda nace”

shiru tayi tana tunani kamar ta fasa kuka ta kalleshi tace “amman inna ɗauko cewa zaiyi mi zanyi da ita”
“no ai bazaki bari ya gani ba a boye zaki ɗauko karki yarda kowa ya gani koda kuda ne”
“tho inna ɗauko ina zan ɓoye?”
shiru yayi yana kallonta kamin yace

“ke bakisan gurin da zaki ɓoye ba?”

“eh duk gurinda zan ɓoye gani za ayi”

“tho ki kaɗa rijiya”
“kai rijiya?”

“eh koki jefar wani gurin innazo sai ki faɗamin na ɗauko”

“ba zai lalace ba?”

“ba zaiyi komai ba kinji”
kai ta ɗaga mishi sosai yaji daɗi ya shafa kanta “good pretty gal”
“amman mi zakayi da ita”
idonsa ya shiga susa kamar wadda abu ya faɗawa “am zan ɗan ɗauki wani abune a ciki na cofa sai na baki ki mayar kinga bazai gane ba ko?”
da mirmushi ya karasa maganar itama tayi masa murmishin karfin hali,
kuɗi ya ciro masu yawa ya mika mata “gashi ki siye duk abunda kike so amman kinsan bazaki faɗawa kowa munyi wannan maganar dake ba ko”
“eh bazan faɗa ba”
“good kuma tsakanin gobe sa jibi nake son ki ɗauko min ita”
kai ta ɗaga mishi,

daga nan ya mika hannu ya buɗe mata motar shima ya buɗe suka fito tare.
Qasin na tsaye bakin kofa yana kallonsu yana rumgume da hannayensa fuskarsa a haɗe,
faɗuwa gaban Mairo yayi da sauri ta juya ta riko hannun Yarima ta soma kuka “nidai bazan iya zuwa ba ga yaya can yana kallona”
mirmushi yayi yaja hannunta suka nufi kofar parlour.

har suka isa Yarima bai kalli gefen da Qasin yake ba,
ita kadaice ke masa kallon tsoro jikinta har wani ɓari yake, da kansa ya buɗe mata kofar data shiga yayi mata byebye yana murmushi hannu itama ta ɗago mishi sannan ya rufe kofar,

yana juyowa Qasin yace “ka bani kunya ka kuma zubar da girmaka momi bata taɓa yiwa yayanta gurɓatacciyar tarbiya ba kuma bana tunanin za'a samu matsala a maryam dan haka ta banbanta da sauran matan da kake gani.
maryam karamar yarinya ce in zakayi sama kayi kasa ba za ah aura maka itaba balle baka daman lalata mata rayuwa dan haka banga abunda zai haɗaku ba”
yana kaiwa nan ya juya ya shigewarsa parlour.

kasa tafiya Yarima yayi sosai maganganun suka ɓata masa rai sai wani busar da iskar baki yake,
_ɗan iskane ni Qasin na karshe har yanzu baka gama sanina ba zan nuna masa true color na_
a zuci yake wannan zancen yana wani kashe ido.

Mairo na zaune kusa da momi tana nuna mata kuɗin,
Qasin na shigowa ta tashi tsaye da sauri tana masa kallon tsoro gabanta sai faɗuwa yake ganin yadda ya haɗe fuska,

yana karasowa kusa da ita ya fisgota ya jefar kasan carpet ya cire bel ɗinsa ya watsa mata,
wani ihu mairo ta saki ta durkushe guri ɗaya,
da sauri momi ta tashi ta rik'e "lafiya Qasin miya faru?"
kallon momi yayi rai a bace yace "bata jin magana ne momi so nake nayi mata dukan da in taga Yarima ko kallonsa ba zata sake yiba"
bel ɗin momi ta karɓe "miya faru wani abu tayiwa Yarima?"
"ba wani abu tayi masa ba shi daine yake son yayi mata illah"
kallon mamaki momi tayi masa "wani abun yayi mata ne?"

"momi kinfi kowa sanin halin Yarima ba mutunin kirki bane taya zaki rika barinshi yana keɓanta da maryam?"
sai a lsokacin moni ta gane inda ya dosa kallon maryam "Ke Tashi Kije ɗaki"
tashi maryam tayi ta gudu ta nufi stairs tana kuka.

saida ta shige sannan momi ta kalli Qasin tace "mi yasa kake da zafin zuciya haka ne Qasin?"
"ba zafin zuciya bane momi ina tsoron abunda zaije ya dawo ne kinfi kowa sanin halin Yarima saboda mi zaki barta ta keɓanta dashi ba ɗan'uwanta bane ba wani nata bane hasalima bashida wata alaka da ita ta dalilin mi zai rika bata kuɗi haka masu yawa kuma ki zuba ido kina kallo keda kanki kika ce bakison ina bata kuɗi mai yawa saboda karta lalace to akanmi zaki barta da Yarima?"

cikin faɗa yake maganar har jijiyar wuyansa na tashi,
kai momi ta girgiza tace "bana tunanin haka Qasin nasan waye Yarima"
wani murmushin jin haishi Qasin yayi ya fice,

a hankali momi ta kai zaune saman kujera tana nazarin kalamansa.
sai a lokacin wani tunanin ya soma bijiro mata,
ta kusan awa biu a haka sannan ta tashi ta shiga ɗaki.

*_washe gari..._*
Qasin na zaune garden ya wani aiki a computer yaji an dafashi,
a hankali ya ɗago suka haɗa ido da mairo da gefen fuskarsa ya kunbure,
murmishi ta ɗan sakar masa tace "yaya"
shima murmushin yayi mata yaja mata kujera ta zauna a kusa dashi "maryam kin tashi?"
"eh tun ɗazu"
"eh kaima kaci?"
kai ya ɗaga mata yana yana taɓa gurin daya kunɓurar mata "dukan da nayi miki jiya ne?"
taɓa gurin tayi "eh shine yaya karkayi fushi dani"
laptop ɗinsa ya matsar gefe ya kara matso da kujera kusa da ita "ba zanyi fushi dake ba maryam dukan jiya ma rai nane ya bace kiyi hakuri kinji?"

hawaye ne suka zuɓo mata "yaya ni banma ce ya bani kuɗi ba shine ya bani kuma bance ya sani mutarshi ba shine ya sani"
cikin kuka ta karasa maganar,

tausayinta Qasin yaji duk sai yaji ba daɗi hannunsa yasa yana share mata hawayen "ya isa daina kukan haka kinji bazan sake dukanki ba"
ɗagowa tayi ta kalleshi "kayi alk'awari?"
"eh nayi"
saida taja majina tace "malamin mu yace ba kyau saɓa alk'awari"

dariya yayi yace "maryam kwan wayo na yarda amman sai in kin min alkawari nima kin yarda"
"eh minene?"
ido ya tsura mata yayi shiru yana mata murmushi,

ganin haka yasa tace "yaya lafiya?"
ajiyar zuciya ya sauke yace "kalau kesan mi nake so dake?"
"a a saika faɗa"
"so nake karki sake kula Yarima duk abunda ya baki karki sake karɓa"
shiru tayi "koda kuɗi ne yaya"
"eh koma minene"
kai ta ɗaga mishi "tho bazan sake ba"
murmushi yayi ya rumgumeta yana faɗin "yauwa maryam ɗina"

"yaya mi yasa baka shiri da Yarima?"
daidai kunnensa tayi masa tambayar.
ɗagota yayi yana murmushi ya tashi ya rufe laptop ɗin ya mika mata "jeki ki kaimun ɗaki"
tashi tayi tsaye jikinta na rawa ta karɓi laptop ɗin tana kallonsa,
juyawa yayi ya nufi part ɗin momi ya barta nan tsaye.

Story continues below



laptop ɗin ta tsurawa ido tana shafawa maganganun Yarima suka rika mata yawo akai tunawa zuciyarta ta shiga mata zance biu akai akai takan kai duba gurin rijiyar dake gefen gurin sai faman haɗeye yawu take,
dukan da Qasin yayi matane ya faɗo mata rai nan da nan sai tsoro ya shigeta,
da sauri ta juya ta nufi part ɗinshi.

''' ***************** '''
*_6:15pm..._*
Qasin ya shigo part ɗin momi da sallama yana murmushi,
Nura da Usman suka amsa masa Maryam kuma ta tashi da gudu ta tarɓoshi "oyoyo yaya"
shafa kanta yayi "maryam oyoyo bita kikeyi?"
sakinshi tayi tana faɗin "eh kuma yaya iya"
zaunawa yayi yana sauke gajiya "yayi kyau haka nake so ina momi?"
"tana ɗaki bari na kirata"
da gudu ta nufi ɗakin tana kwalawa momi kira,

tare suka fito tana rike da hannun Mairo da murmushi ta zauna tana kallon Qasin "injin anyi nasara?"
dariya yayi yace "anyi momi saidai fa akwai yar matsala"
nan da nan yanayin fuskar momi ya chanja "wace irin matsala kuma?"
"wai sunce zasu min interview gobe bance wadda suka min yau"
"daman abun harda interview akeyi sai kace ɗaukar aiki"
ajiyar zuciya ya sauke "nima abunda yaban mamaki kenan momi kuma kinsan wani abu?"
"a a minene?"
"Yarima ne zai min interview ɗin kuma wai sai nazo da laptop ɗina sunga irin aikin da nayi"

lumshe ido momi tayi "oh ni har ka faɗarmun da gaba wannan tho ai ba wani abun ɗaga hankali bane sai kaje da ita ka nuna musu kuma duk abunda suka tambayeka ka basu amsa"
"momi bakiji mi nace ba Yarima fa zai mun"
"tho minene a ciki ai baka kirsa cikin aikinka ko kaɗan bana fargaba akan aikin da za'ayi maka"
"momi tsoron nake kar Yarima yayimin wani abun kinsan halinsa"
"karka taɓa saka wannan a ranka ka yarda da kanka Qasin karka bari damar nan ta wuce ka kaifa kmda kanka ka faɗa min kuɗine masu yawa"
kai ya ɗaga mata yana kallon maryam,

Usman yace "yaya ya akayi Yarima ya zama shine zaiyi maka interview ɗin"
Qasin yace "nima ban saniba amman dai kasan yana hulda da motocin kasashen waje kuma kasan tunda Illustrator ne inajin shiyasa"
"Allah dai ya baka nasara yaya"
duk suka amsa da 'amin'
sun ɗan jima suna fira saida aka kira sallar magriba sannan kowannensu ya tashi momi da maryam kuma suka nufi ɗaki dan sallah.

*_Monday @10:30am..._*
cikin nasara akayiwa Qasin interview duk yadda Yarima yaso ya samu matsala Allah bai yarda ba duk abubuwan da suka bukata saida ya nuna masu Yarima yayi mamaki sosai ganin laptop ɗin,
bayan fitarsa akayiwa mutun 3 duk basuji sun gamsu dasu ba kamar yadda sukaji da Qasin sun daɗe suna ttaunawa kamin su yanke hukunci sosai Yarima yaso a bawa wani ba Qasin ba amman suka ki yarda dan sun lura da gwarewarsa nesa ba kusa ba,

*_2 hours letter..._*
suka aika aka kira Qasin daya shigo suka sake yi masa wasu tambayoyi,
ya amsa musu fiye da yadda suke tunani nan suka kara jindaɗi Yarima suka bawa files ɗin cike da jin haushi ya mika masa,
Qasin na murmushi ya karɓa yayi sign fuskarsa a sake ya mikawaƳYarima files ɗin yana murmushi yace "thank you"
murmushi Yarima wadda bai kai zuci ba "ur welcome Men"
hannu suka rika mikawa Qasin sunna masa congrats,

'''**********************'''
cike da jindaɗi Qasin ya shigo gida kai tsaye part ɗin momi ya nufa tun daga sallamarsa ta gane haka bata masa magana ba saida ya zauna "an daiyi nasara ko?"
dariya yayi ya mika mata jakar dake hannunshi "anyi momi sun bani"
ba karamin daɗi momi taji ba saida ta gama duba laptop ɗin sannan tayi ma Allah godiya "Alhamdulillah Allah mun gode maka haka nake so Alhamdulillah Yarima yaje?"
"eh tare dashi akayi komai shima ya bani files ɗin nasa hannu"

"masha Allah Allah ya tayaka riko"
"amin momi kinga fa ko breakfast banyi ba"
maganar yake yana wani sosa kai,
taɓe baki momi tayi tace "zakaci albakacin wannan ranar zan baka na yau"
murmushi yayi "aiko momi da kin kyauta"
tashi yayi ya nufi dining yana faɗin "yau momi gidan sit ba kowa"
"to ai kasan yau monday wazai zauna nima anjima kaɗan fita zanyi"
"tho bari na daukeki dan nima fitar zanyi"
taahi momi tayi ta nufi upstairs,
"bari na shirya wani abin kamin ka kare"
"owk momi"

Story continues below



kujera yaja ya zauna ya hau cin abincin har wani sauri yake yana lumshe ido raban da yaci abinci mai daɗi haka har ya manta kullum cikin siyen takeaway yake gashi abinci inba na momi ba baya jindaɗinshi,

kusan plate biu yaci yasha zoɓon da momi ta haɗa ya tashi yana hamdallah,
part ɗinsa ya nufa bai daɗe ba ya fito ya sake nufo part ɗin momi bayan ya ɗan watsa ruwa ya chanja kaya, zaune ya tararda ita tana jiranshi,
"momi har kin shirya?"
"eh so nake nayi saurin dawowa kar maryam ta dawo gidan ba kowa"
agogon hannunsa ya duba "gashi ko sun kisa dan 12 ta kusa"
tashi momi tayi ya ɗaukar mata jekar dake gabanta suka fice.

*_2:34pm..._*
Mairo ta shigo gida kamar ta fasa kuka ta nufo parlour dan tun gate maigadi ya faɗa mata momi bata nan,
jefa tayi da jakarta tsakiyar parlour ta nufi upstairs,
tana shiga ta cire uniform ɗinta ta ɗauki tawul ta ɗaura ta shiga bathroom wanka tayi tare da alwala sannan ta fito sai wani tureturen baki take tana matsar kwallah,
wadurof ta nufa tana buɗewa taji an kira amsawa tayi duk da bata san mai kiran ba ta rufe wadurof ɗin da sauri ta nufi kofa.

candynovels.wordpress.com

© *Khadeeja Candy*
[11/5, 9:43 AM] Khadeeja Candy 🍧: *♡... MAIRO ...♡*

*BY*

*_KHADEEJA CANDY_*

*22*

da sauri ta sauko stairs tana rabon ido dan bata ga kowa ba har ta nufi kofa taji an rikota,
juyowa tayi da sauri suka haɗa ido da Yarima sosai ta razana ganin fuskarsa a haɗe gashi batayi tsamaninsa,
kokuwa ta shigayi dàshi tana son kwace kanta jikinta har wani rawa yake.
iya karfinsa yayi wurgi da ita saman kujera cikin jar fuska yace "mi yasa kika karya alkawarin?"
tashi tayi zaune tana kuka tace "yi hakuri dan Allah karka dakeni"
risinawa ya shafa gefen fuskarta "baki son na dake ki miyasa kika ki aikata abunda na saki? mi yasa maryam?"
shiru tayi tana kallonsa hawaye na mata zuba.
hannu yasa yana share mata wayarsa tayi ringing,
saida ta kusan katsewa sannan ya ɗauka banji mi akace masa ba saidai naji nace "Gret mun faɗi sai dai mu tari gaba... owk sai na ganka"
yana aje wayar ya tashi tsaye yana tafiya bayabaya fuskarsa ɗauki ke da murmushi saida ya kai kofa sannan ya juya ya fice,

ajiyar zuciya ta sauke ta kawanta saman kujera dafe da zuciya.
ta kusan minti 20 a haka sannan ta tashi ta nufi ɗaki,
cikin kankanen lokacin tayi shirin islamiya ta ɗauki littafanta ta nufo downstairs.

cike da tsoro ta sauko sai leke2 take har ta samu ta fita parlour,
har ta isa harabar gidan bata daina jin tsoro tana kisan isa gate motarsu momi ta kunno kai,
Qasin nayin parking mairo ta nufi momi ta rumgumeta idonta cike da hawaye.
murmushi momi tayi ta rumgumeta "maryam kin dawo?"
kamar tayi kuka tace "eh momi ki daina fita kina barina"
"tho na daina maryam jeki islamiyar karkiyi latti"
kin ɗagowa tayi saida taji an ja mata kunne sannan ta juyo da fuskar ta kalli Qasin,
murmushi ya sakar mata ya buɗe mata mota "shiga na kaiki"
ba musu ta shiga bayan ya rufe ya shiga mazaunin direba yayi ribas suka juya momi kuma ta nufi cikin gida.

tukin yake yana kallonta ita kuma kanta na kasa sai murza yatsunta take tana haɗiyar yawu,
A'hankali ya rage gudun da yake ganin haka yasa ta ɗago ta kalleshi suna haɗa ido yace "mi yake damunki maryam?"
shiru ta ɗanyi sannan tace "babu komai"
Qasin yace "kinsan ba kyau karya ko?"
kai ta ɗaga mishi
"tho faɗa min miya ke damunki?"
"nace maka babu komai"
"Yarima yazo?"
batace masa komai ba har yayi parking daidai gate ɗin makarantar saida ta buɗe motar zata fita sannan tace "eh yazo"
da sauri ta rufo motar ta nufi cikin makarantar,

saida ya daina hangota sannan yayima motar key da sakesake ya iso gida yana tuna yadda mairo ta rumgume momi,
har ya nufi part ɗinshi wani tunanin ya dawo dashi gurin maigadi ya soma masa tambayoyi bayan sun gaisa "Sadiqu bayan fitarmu waya shigo?"
"babu wadda ya shigo inba Yarima ba"
"ya jima nan?"
"a'a bai jimaba ya fita"
kai Qasin ya ɗaga mishi "owk na goɗe"
ya juyo ya nufi part ɗin momi,
da sallama ya shigo saidai bai samu mai amsa masa ba dan babu kowa parlour.
guri ya samu ya zauna yana sauke ajiyar zuciya sai kallon parlour yake ta ko ina kamar wani bako,
ya daɗe haka sannan ya tashi ya nufi part ɗinshi.

Story continues below



*_washe gari..._*
*7am* Qasin ya shigo part ɗin momi,
momi na kicin tana aiki taji shigowar mutum hakan yasa ta nufo parlour,
Qasin na ganinta yace "an tashi lafiya momi?"
"lafiya kalau"
"masha Allah maryam tqa tashi?"
da ɗan mamaki momi tace "eh tana ciki shirin makaranta take yi lafiya dai"
murmushi yayi ya nufi stairs "lafiya kalau momi abu zan bata"

a hankali ya tura kofar ya shiga tana zaune tana saka safa tana ganinshi ta saki murmushi "yaya ina kwana?"
"lafiya kalau maryam kin tashi lafiya?"
"lafiya kalau"
zaunawa yayi kusa da ita yana faɗin "shirin makaranta kikeyi?"
"eh"
"yayi kyau"
kafarta ɗaya rika yana saka mata safar "maryam jiya da Yarima yazo mi yayi miki?"
ɓata fuska tayi "nidai ba nace maka bai min komai ba bai min komai ba"
"tho miya yace miki?"
"nidai baice komai ba kawai yace gurin momi yazo kuma bata nan harda kuɗi ya bani amman ban karɓa ba sai yayi tafiyarsa"
tana maganar tana wani ɓalɓal da ido karya gano karya take.
daɗi Qasin yaji sosai da kanshi ya saka mata jikar makarantar yana murmushi yace "yauwa maryam daɗina dake jin magana kin kyauta da baki karɓi kuɗin nan ba"
rufe ido tayi ta fashe da dariya da gudu tabar ɗakin,

'''***********************'''
tafiya yake yana shewa (fito) hannayennsa na lakkame a bayansa.
duk gurin da yabi sai sun gaisheshi jiki na rawa amman ko kulasu ba yayi bare ya amsa gaisuwar sai wani rangashi yake har ya iso maidaidaicin parlour,

guri ya samu ya zauna bayan ya gaisheta ya ɗora kafa ɗaya saman ɗaya yana wani lumshe ido,
tsakin da yaji tayi ne ya sashi ɗago kai ya kalleta yana kalkatar dariya "haushi nake baki ko hajiya?"
taɓe baki tayi "Yusuf na gaji da maka magana na gaji da saka maka ido haba Yusuf sai kace wani yaro karami kullum ayita faɗar abu ɗaya ana maimai tawa"

rufe baki yayi kamar wani mai jin hamma "sorry hajiya komai ya kusa zuwa karshe na samu wadda nake so jira kawai nake ta karasa girma"
kallon rashin fahimta Haiyar tayi mishi "ban gane ba?"
murmushi yayi "na samu wadda nake so saidai karamace amman idona na kanta data girma zan ɗauke abunta"
maganar yake yana wani ɗaga hannu sama yana taɓe baki kamar wadda yasha wani abu,
kai Hajiya ta girgiza "Yusuf lafiyarka kuwa ban sanka da wannan halin ba"
dariya yayi yace "nayi miki kama da yan shaye2 ko kinfi kowa sanin bana shaye2"
"tho mi yasaka cikin wannan halin?"
"tsabar bakin ciki ne kawai"
"bakinciki kamar ya?"
kafaɗunsa ya ɗaga ya tashi tsaye yana faɗin "barshi kawai hajiya kona faɗa miki bashi da rana"
cikin rashin jindaɗi tace "Allah ya sauwake"
dariya yayi yace "amin bari naje ciki"
kofa ya nufa yana saida ya kusa fita sai kuma ya juyo ya kalleta yace "wlh hajiya bana shaye2 kuma ba wani abun na shaba karki saka wannan a ranki kinji dai na rantse wannan abun da nake tsabar bakincikine da kuma yunwa"
a jiyar zuciya ta sauke iya Tabbacci tana dashi akan Yarima baya shaye2 ko babu komai yakan yi mata irin haka wani lokacin saidai ba kamar na yau ba.
a kasale ta kalleshi tace "na yarda dakai Yusuf baka taɓa aikata irin wannan amman mi yasa ka bakinciki haka?"
yana rike da kofa yace "wani abin na sawa gaba kuma ban cima masara ba shiya ɓata min rai har na kasa cin abinci tun jiya amman karki damu yanzu zan koma daidai dan na hari gaba"
"Allah ya yaye maka ko minene Yusuf na yarda da kai"
murmushi ya sakar mata "good mother"
saida ta masa murmushin sannan ya fice.

*©Khadeeja Candy*

candynovels.wordpress.com
[11/5, 9:43 AM] Khadeeja Candy 🍧: *♡... MAIRO ...♡*

*BY*

*_KHADEEJA CANDY_*

*23*

yanzu hankalin mairo a kwance yake dan ta daina ganin Yarima ba tada wata matsala inba ta jarabawar da suke ba dan momi bata barinta ta zauna data dawo gida kullum ciki karatu take banda wadda ake mata a makaranta da kuma wanda Siraj yake tisa mata Qasin ma wani lokacin yakan mata,

'''*********'''
yau Mairo da far'ah ta tashi ita ta da shi kowa na gidan tare suka shiga kicin da momi aikin komai tare sukayi,
bayan sun kare ta shiga jerawa a dining tana wakewake momi na zuba mata abinci a kula tace "maryam yau far'ah me kike haka?"
fashewa tayi da dariya "oh momi kin manta yau muke kare jarabawa shikenan sai hutu"
momi ta rufe kular tana faɗin "o na ganoki shiyasa kika tashi tun safe haka tho Allah yasa a kara muku wata har 8"
da fuskar zolaya momibta karasa maganar
mairo ta marairaice fuskar "Allahumma a'a Allah karka amsa momi wlh bana son haka"
dariya momi tayi tace "tho na daina amman dai kinsan ta ɗaya zaki ɗauko mana ko?"
dariya tayi ta rufe ido "momi dan kinga ban iya ba ko?"
"a a kin iya maryam Allah dai ya bada sa ah"
"amin momi kin san kince in an mana hutu zaki kaini gurin Gwaggo ko?"
"eh anyi haka tho bari a muku hutun"
rumgume momi tayi cike da jindaɗi kamin ta sake ta ta ɗauki kular makarantar ta fice dan tuni motar makarantar ta iso,

Story continues below



*_2:37pm..._*
ta shigo gida uniform ɗinta duk ya bace da k'asa tafarta ma babu kyau gani,
tafiya ta rikayi laɓalaɓa har ta isa kofar parlour ta shiga leke.
cikin rashin sa'ah ta hango momi zaune ita da Siraj da sauri ta koma baya,
can kuma ta sake lekowa momi kamar wadda aka tsikara ta waigo suka haɗa ido.
"lafiya maryam kike laɓe?"
kara laɓewa tayi ta yadda fuskarta kawai ake gani tace "momi uniform ɗina duk yara sun lalashi"
"kamar ya? shigo mana"
"kasa suka samin kuma nidai banma yi qasan kasa ba sune suka samin"
"tho shigo"
"bazaki dakeni ba?"
"eh shigo"
daker ta shigo parlour tana wani kakkaɓen2 muna furci.

ɓata fuska Siraj yayi "yanzu maryam da girmanki zakiyi wasan kasa haka?"
harara ta watsa masa "ina ruwanka nida momi nake magana bada yara kananuba"
dariya Siraj yayi momi kuma tayi murmushi hakan yasa ts ɗan saki jiki ta matso kusa da momi "momi ni yarane suka ɓata uniform ɗin harda kular suka fasa marfin kawai suka barmin"
sai a lokacin momi ta lura da murfin kular dake hannunta,
Siraj yace "karya kike kedai kika fasa da kanki ai nasan halinki"
kamin mairo tayi magana momi ta tari numfashinsa "tho ai babu komai sai a siya mata wata aini tunda tana karatu komai zan iya yimata"
gwalu tayiwa Suraj tana daddalomai ido "yaee an bashi red card"
shikan inbanda dariya babu abunda yake ganin abun nata ba mai karewa bane yasa momi ta riko tace "kyaleshi haka jeki wanka kiyi sallah sai muci abinci"
saida ta kara masa gwalon sannan ta nufi stairs.

da dare mairo na zaune parlour ita da Qasin suna game Siraj ya shigo,
aiko daman neman tsokana yake haka yasha mur yace "ke tashi muje kiyi karatu"
juyowa tayi ta kalleshi tayi mai fari da ido "kai dan Allah ja can yaro ba sauran karatu mun kare jarabawa hune kawai zayi mana yaro"
dariyace ta suɓucewa Siraj Qasin ya kalleta yace "Siraj ɗin ne yaro?"
"eh yaro ne man baka ga ka girme shiba"
"tho ai shekara kaɗan na bashi"
"eh duk da haka dai yaro ne"
maganar take tana wani war da ido tana jujjuya baki,
fashewa Qasin yayi da dariya Siraj ma da dariyar ya nufi dining.

game ɗin Qasin ya kashe ya rika hannunta "tashi muje muci abinci"
ɓata fuska tayi ta taɓe baki "yaya bamu gama game ɗin ba fa kuma momi bata zoba barre muci abincin"
hancinta ya lakkata "momi yau ba nan zata ci abinci ba kisan abbah yana nan g(me kuma gobe zamuyi tunda ba makaranta tashi muje"
tashi tayi yana rike da hannunta suka nufo dining saida yaja mata kujera ta zauna sannan shima ya zauna ya soma zuba mata abincin"
Siraj dai kallonsu kawai yakeyana cin abincinsa yana murmushi saida suka fara cin abincin sannan yace "yaya kasan momi tace ka daina ci mata abinci fa"
harara Qasin ya watsa mishi "tho momi ka gani nan ne"
rufe baki mairo tayi tana dariya "lahh yaya Allah sai na faɗa mata"
dariya Siraj yayi Qasin ya haɗe fuska
"kaga bana son iskancin nan fa Siraj ina ruwanka"
Siraj yace "gaskiya ce ai ace mutum da matarsa amman kullum sai yazo gurin momi yaci abinci"
banza Qasin yayi mishi ya cigaba da cin abincinshi,
Mairo kan dariya kawai take tana kallon Qasin.

can ta dafe ciki ta koma kuka kamar ba ita ba "na bani cikina ciyo yake"
duk suka kalleta Qasin yace "ciki kodan kinyi dariya ne?"
"a a tun safe yake min ciyo kuma sosai"
Siraj yace "kinsha magani?"
"a-"
waje tayo da ido tunowa da bata son magani da sauri tace "eh na sha momi ta bani magani mai shegen ɗaci"
wani ya mutse fuska tayi kamar da gaske
Qasin yace "tho ci abincin sai kije ki kwanta"
kuka tasa masa
"ni bazan iya ciba Allah ciyo yake sosai"
"owk jeki ki kwanta"
tashi tayi da sauri tana yiwa Siraj ɗageɗage,
har ta kama hanya sai kuma ta dawo ta nunashi da yatsa ta maida baki gefe tace "kai kuma yaro kayi sauri ka cinyeshi duka"
juyawa tayi ta cigaba da tafiyarta tana wani rausaya kamar wata tsohuwar karuwa,
Siraj kai ya girgiza yana dariya,
murmushi Qasin yayi ya bita da kallon har shige.

*©Khadeeja Candy*

candynovels.wordpress.com
[11/5, 9:43 AM] Khadeeja Candy 🍧: *♡... MAIRO ...♡*

*BY*

*_KHADEEJA CANDY_*

*24*

*_washe gari..._*
9 da yan mintuna mairo ta nufo downstairs sanye da kayan bachi fuskarta babu annuri,
duk ɗagowa sukayi suna kallonta harta zauna momi nakai wainar kwai tace "maryam lafiyarki kuwa?"
kara ɓata fuska tayi "momi cikina ne yake ciyo sosai tun jiya"
Siraj ne ya gwaleta "dan Allah can ji kanta"
"kai yaro wlh ka kyaleni"
dariya yayi "Allah momi in bata daina cemun yaro ba dukan gwarai zanyi mata"
momi na mika mata cup ɗin tea tace "karma ka soma ka daketa bakai ka fara wasa da itaba"
gwalo mairo tayi mishi "ance yaro yaro yaro yaro yaro yaroooooo"
Usman yace "ba cikinki ke ciyo ba kenan?"
nan ta rike cikin ta langwashe "momi ni ko tea nan bazan iya shaba ciyo yake sosai"
momi tace "wani abun kika cine?"
"a a ni banci komai ba"
Qasin na kurɓa tea yace "bakince kinsha magani ba ko karya kike?"
soshe2 ta shigayi yana son kawarda maganar "uhm momi kinsan kince yaya bazai kara ci miki abinci ba ko jiya yaci kuma yau yana ci"
kallonshi momi tayi "tho yana iya da abunda yafi k'arfin wuta inji kishiyar k'onanna"
dariya yayi yace "Allah momi abinci inba naki ba bana jindaɗinshi"
momi zatayi magana Siraj yace "nidai duk ba wannan ba dan Allah momi karki barta taje ki hanata"

Story continues below



mairo da Qasin suka kalli momi mairo ce ta riga tambaya "minene momi wa za a hana?"
da fork Siraj ya nuna ta "ke mana ke za a hana"
"ina zataje?"
Qasin ya tambaya,
momi badan taso ba ta soma masa bayani "jiya ne bayan fitarka Yarima yazo wai yana son maryam ta rakashi wani taro da za ayi na buɗe wata kungiya ta taimakon yara"
ɓata fuska Qasin yayi ya taɓe baki "tho saboda mie sai ita zata rakashi miye haɗin ta ta kungiyar?"
Siraj ne ya karɓa mishi "wai shine zai kaddamar da abun kuma yana son yaje da yarinya da zatayi jawabi a maimakonsa jifa"
momi tace "tsarin ne yazo da haka dan haka aka tsara komai har ma abunda maryam zata faɗa a rubuce yake"
tsaki Qasin yaja "aikin banza maryam ce kawai yarinya ai yana da kanne mata da maza yaje dasu mana babu inda zata je"
momi tace "yafa riga ya bada abunda zata karanta har kayan da zata saka ya kawo"
tashi Qasin yayi tsaya yana faɗin "tho a mayar masa da kayansa momi dan Allah karki barta taje"
momi bata ce mishi komai ba sai maryam take kallo data ɓata fuska kamar ta fasa kuka,

tana ganin ya fice tace "momi nidai zanje inason nayi jawabi"
Usman da Nura dai kallonta kawai suke basu ce komai ba
kai momi ta ɗaga mata "ai zaki je inma kike kare zan baki takarɗar kiyita bita kamin assabar kin iya"
daɗi sosai mairo taji za a rika Microphone ayi jawabi.
baki sake Siraj yace "momi kina nufin barinta zakiyi taje duk magangganun nan da akayi"
shima banza momi tayi dashi mairo nata watsa masa harara harya kare cin abincin ya fice.

'''***'''
koda 12 tayi mairo na zaune ɗaki tana karanta takardar da taji motsi ta ɓoye dan kar Siraj ko Qasin ya shigo ya gani,
haik'an ta ɗauki abun ta rika tarewa a ɗaki duk abunda da bata gane ba ta tambayi momi,
islamiya ce kawai take tasa ta aje idan ta dawo ta cigaba,

a waya Yarima yake kiran momi tabawa mairo yana jin yadda take karantawa dan yasan zuwa gidan ba zai masa daɗiba kuma daman momi tayi dashi akan komai zasuyi ayi a waya karya zo gidan inba weekend ba ranar da zasu tafi,

kullum Qasin da Siraj cikin nanatawa momi suke akan karta barta taje. a fili momi nuna musu take bazata barta ba dan karsu dameta,
mairo har zumuɗi take taga assabar ɗin tayi duk wani ciyo da take ji daina faɗawa momi tayi dan karta hana ta zuwa,
cikin kwana biu mairo ta haddace abunda yake fefar kasancewar ba wani jawabi ne mai yawa ba,

*©Khadeeja Candy*

candynovels.wordpress.com
[11/5, 9:43 AM] Khadeeja Candy 🍧: *♡... MAIRO ...♡*

*BY*

*_KHADEEJA CANDY_*

*25*

*_Saturday morning..._*
_8:24am_ Qasin ya shigo part ɗin momi cikin kananan kaya,
parlour ya tararda su suna karyawa.
momi na ganinshi gabanta ya faɗi a haka ta ɗaure ta amsa gaisuwar da yayi mata "lafiya kalau ya naganka cikin shiri haka?"
yan duba agogon hannunsa yace "wlh meeting ne wai zamuyi da wasu kuma basu faɗa min ba sai jiya da maraice gashi anjima zasu wuce balle nayi cancle ɗinshi"
wani daɗine ya jiyarci zuciyar mairo da momi mairo kasa jurewa tayi saida tayi dariya,
cup ɗin tea momi ta aje mishi "xauna ka karya mana"
ɗaukar tea yayi a tsaye yana sha "bani da time ɗin tsayawa ina Siraj ne?"
"yaje birnin kebbi"
fuskar mamaki yayi birnin kabbi gurin mie?"
"nima ban saniba baba hajara ce ta aiko tana nemansa tun da 7 ya tafi"
iskar bakinsa ya busar "owk maryam tashi ki chanja kaya ki rakani"
da sauri momi ta kalleshi "gurin meeting ɗin zata rakaka?"
"eh momi ban yarda da barinta cikin gidan nan ba"
faɗa momi ta taso masa dashi "tho bazata ba in baka yarda da magana naba sai kayi abunda zakayi nifa na haifeka Qasin ba ni ka haifa ba"
kasa yayi da kansa yana sauke ajiyar zuciya,
duk sai yaji ba daɗi ganin yadda ranta ya bace haka ya juya jiki ba kwari ya fice.

*_9:41am..._*
motar Yarima tayi parking,
ya kusan minti uku ciki motar sannan ya fito ya nufi parlour.
da sallama ya shigo mairo ta amsa masa tana murmushi,

Story continues below



tsaye yayi yana kare mata kallo ganin yadda tayi masa mugun kyau doguwar rigace jikinta golden colour sai ɗan karamin bakin hijab da momi ta saka mata da da jan janbaki sosai tayi kyau,
a hankali ya karaso kusa da ita ya risina ya kai hannu ya taɓa gefen fuskarta yana haɗiye yawu,
murmushi ta sakar masa "ina kwana"
bai amsa mata ba
ya mayar mata da murmushin yana mata wani kallo,

jin an taɓa kofa ya sashi tashi ta sauri ya matsa baya yana kallon momi data nufo downstairs.
"Yarima ka iso?"
"eh momi naga har kin shiryata"
"eh kasan kace mun 9:30 zaka zo"
agogon hannunsa ya kalla "bari muje momi kar muyi african time"
"owk tho Allah ya kiyaye"
hannunta ya rika suka fice tana yiwa momi byebye.

murmushi momi ta bita dashi har ta fice ko kaɗan momi bata son tafiyarta dan dai babu yadda zatayine tunda tana ganin inta hana mairo zuwa bata kyautawa Yarima ba,

'''*************'''
Qasin ne tsaye tsakiyar ɗaki yana kai da kawo kana ganin yanayin fuskarsa kasan ransa a bache yake.

momi ma zaune take saman kujera dafe da kai lokaci lokaci takan kai dubanta gurin agogon dake parlour.
wannan karon *9:21pm* ya nuna hankalinta ne ya kara tashi,
da sauri ta janyo wayar dake hannunta tana kiran number Yarima duk sakamoko ɗaya ake bata kamar ɗazun wayar a kashe,
juyowa Qasin yayi ya kalleta "kinga ni ko momi saida nace miki karki barta taje kika ki yarda da magana na gashi yanxu abunda ake yiwa gudu"
numfashinsa momi ta tara "babu abunda zai samesu insha Allah kawai dai bana son sukai 10 ne"
magana take kamar abun bai dameta ba saɓanin cikin ranta dake cike da tashin hankali,
kai Qasin ya girgiza "hmm ace tun safe mutun ya fita har yanzu babu labarinsa"

da karfi Mairo ta turo kofar parlour ta shigo idonta zurun zurun.
duk juyowa sukayi suna kallonta babu wadda ya iya taɓuka komai harta karaso kusa dasu,
lumshe ido Qasin yayi yana sauke ajiyar zuciya.

da fata momi tayi tana kallon bayanta "ina Yarima?"
"yana can basan inda yake ba sawa yayi a kawoni"
magana take muryarta na rawa kana gani kasan tsoro take ji sai waiga bayanta take,

juyowa Qasin yayi da ita "maryam mi yasa kuka daɗe?"
shiru tayi tana haɗiyar yawu "ba ba babu komai"
tsawa Qasin ya katsa mata yana girgiza ta "faɗamin min gaskiya tun safe ku fita sai yanzu ki dawo kice mun babu komai faɗa min miya faru?"
matsawa tayi ta rike momi tana kuka "yace duk na faɗa sai ya kasheni"
sanyi jikin Qasin yayi momi kuma tsigar jikinta ta tashi,
a hankali momi ta rika zata zaunarda ita kin zama mairo tayi ta ɗan ɗaga rigarta cike da tsoro tace "momi kayana duk ya ɓata dubi jini na min zuba"
da sauri Qasin da Momi suka kalli jinin dake bin k'afarta.

*©Khadeeja Candy*

candynovels.wordpress.com
[11/5, 9:43 AM] Khadeeja Candy 🍧: *♡... MAIRO ...♡*

*BY*

*_KHADEEJA CANDY_*

*26*

waje Qasin yayi da ido cikin rawar murya yace "maryam..-"
da sauri ta kalleshi itama idon nata a tsaye.
zai rikata momi tayi saurin rika hannunta "muje ciki"
janta momi tayi suka nufi stairs jikinta babu karfin,
Qasin ma haka yake kallonsu jiki ba kwari har suka shige sannan ya faɗin zaune yana kallon gurin da jinin ya zuba,

sai kusan 10 da wani abu ya tashi ya nufi part ɗinshi tafiya yake kafafunsa na masa nauyi zuciyarsa sai bugawa take da karfi,
baiyi sallama ba ya shigo parlour.
har ya zauna bai lura da mansura dake zaune saman kujera ba
dafe kanshi yayi ya kulle idonsa gam yana cizon baki,
jin an dafashi yasashi ɗago kai ya kalleta.
tashi hankalinta yayi yanayin yadda taga idonsa yayi ja tasan ba lafiya ba,
tana shafa gefen fuskarsa tace "Qasin lafiya na ganka haka?"
janye mata hannun yayi "babu komai jeki kwanta"
"kamar ya naje na kwanta bayan kai hankalinka ba-"
cikin tsawa ya tari numfashinta "nace miki kije ki kwanta babu komai"
tashi tayi tana masa wani kallo kamin ta juya ta nufi ɗaki,

Story continues below



dafe kai yayi ya sake rumtse idon abunda ya faru ɗazu ne ya rika dawo masa,
jin yayi bashi da natsuwa yaji wani irin abu ya tsaya masa a zuciya da sauri ya tashi ya nufi firij yana buɗewa ya ɗauki gorar ruwa ya kafa a baki,
kaɗan yasha ya ɗire ta saman firij ɗin yana maida numfashin,
ya daɗe tsaye a gurin sannan ya juya ya nufi kofa.

part ɗin momi ya sake nufowa yadda yabar parlour haka ya tarardashi kai tsaye upstairs ya nufa,

tun kamin ya karasa hawa yayi tsaye jin shinshikar kukan momi wani abu yaji ya tsikareshi tun daga ɗan yatsan kafarsa har tsakiyar kansa karfen stairs ɗin ya rike da karfi ya matse hannunsa ciki yana dantsar hakora,

jin bazai iya jure tsayinba yasashi zaunawa a gurin,
lumashe ido yayi saida yaji abunda ke zuciyarsa ya ɗan kwanta sannan ya tashi ya nufi ɗakin momi,

a hankali yakai hannu ya tura kofar ɗakin.
tsaye yayi yana kallon mairo dake saman gado kwance tana bachi kamar gawa.
ɓachin ransa dake ransa ya karu saurin ɗauke idonsa yayi ya mayar gurin momi dake zaune kusa da ita hana sharar kwallah,
cikin dakisasshiyar murya yace "momi kuka kikeyi?"
ba tare data kalleshi ba ta girgiza masa kai alamar a'a,
kai ya ɗaga "itama naji kukanta ɗazu"
sai a lokacin momi tayi gyaran murya tace "eh ina tambayar tane ko yayi mata wanin abun ne shine nace zan daketa inbata faɗa ba shine take yiwa kuka"

saida ya ɗanyi jimmm sannan yace "mi tace momi?"
ita shirun ta ɗanyi kamin ta bashi amsa "ina jin menstruation ne Qasin dan banga wata alama data nuna yayi mata wani abun ba kuma ita bata faɗa ba"
sai a lokacin ta kalleshi

murmushi yayi "yes momi menstruation ne saida safe"
bai tsaya jiran mi zata ce ba yayi baya baya yaja mata kofa daman can bai karasa shiga cikin ɗakin ba,

cikin wani yanayi ya nufo downstairs yana tafe hawaye na masa zuba har sauko.
saman kujera ya zauna saida yaji hawayen sun tsaya masa sannan ya tashi a kasale ya nufi part ɗinshi,

*_washe gari..._*
Mairo na zaune saman gado tana wasa da kafafunta Qasin ya turo kofa ya shigo fuskarsa ɗauke da murmushi,
tana ɗago kai suka haɗa ido murmushin da ta gani a fuskarsa ya hanata jin tsoronsa tun kamin ya karaso tace "yaya ina kwana?"
saida ya risina kisa da ita sannan ya amsa mata murya kasakasa "lafiya kalau kin tashi lafiya?"
"lafiya kalau"
"ina momi?"
"tana kicin"
hannayenta ya riko "faɗa min maryam mi Yarima yayi miki?"
"ni bai min komai ba yaya"
shiru yayi ya soke kai

can ya ɗago kai ya kalleta "jinin dake miki zuba har yanzu yanayi ko ya daina?"
"a'a ya daina koda na tashi da safe bai min zuba ba"
da sauri ya lumshe ido bugun zuciyarsa ya karu.

"ba abunda kake zargi bane Qasin jikina bai bani haka ba kuma na bincike ta banga haka ba"
momi ce take maganar lokacin da ta karaso kusa dashi.
sakin hannunayen nata yayi suka tashi tsaye tare shida Mairo,

wani irin faɗuwa gabansa yayi lokacin da ya juyo suka haɗa ido da mansura dake tsaye bakin kofa rike da kofar ɗakin.
cikin rashin ta karasa shigowa tana faɗin "miya faru da maryam?"
da sauri momi ta tari numfashinta "babu abunda ya faru da ita gimuwa ne tayi da kuma ciyon kai"
karasowa tayi kusa da mairo "gimuwa a ina?"
nan mairo ta soma mata bayana "a a jiya ne da-"
tassssss Qasin ya wanke mata fuska da mari saida ta faɗi tun bata kai ko ina a zancen ba,
da sauri mansura ta kalleshi "Qasin mi-"
marin itama ya watsa mata saida tayi baya ta dafe kunci.

*©Khadeeja Candy*

candynovels.wordpress.com
[11/5, 9:43 AM] Khadeeja Candy 🍧: *♡... MAIRO ...♡*

*BY*

*_KHADEEJA CANDY_*

_dedicated this page to maama Hajiya Zainab Kano kakar yan biu 🙈 LOL_

Story continues below



*27*

da sauri momi ta riko Qasin da fuskarsa ke ɗauke da bachin rai tace "mi yake damunka Qasin mi suka maka?"
kallon kawai ya rikayi ba tare daya amsa mata ba,
sun minti 10 haka ɗakin tsit sai shehsekar kukan Mairo ke tashi.
mansura ce tayi karfin halin sake yin magana "momi mi yake damunsa ne tun jiya na kasa gane kansa?"
nan momi ta saki Qasin ta matsa kisa da mansura "abunda ya kawo ki kenan? daman nasan baki taɓa leko part ɗina ba sai a wata bukatar kanki ta taso"
kasa tayi da kanta har alokacin tana dafe da kuncinta hawaye na mata zuba,
"indai har abunda ya kawo ki kenan tho ki juya ki barmin ɗakinki ai mijinki ne kinfini sanin hanyoyin da zakibi ki fahimcin abunda yake damunsa"
kamar *HAWAINIYA* ta soma tafiya kanta a kasa har ta fice,

juyawa momi tayi ta nufi mairo ta tashe'ta tana share mata hawaye cikin sanyayyeyar murya momi ta soma magana da Qasin ba tare data kalleshi ba "bana son kowa yasan da maganar nan Qasin koda Siraj ne"
nan ma baice komai ba ya kaɗa kai ya fice,

mairo sai taga ya fice sannan ta kalli momi cikin muryar kuka tace "momi minayi masa?"
"baki masa komai ba maryam"
"amman momi ya mareni haka da zafi"
murmushi momi tayi "baya son idan manya na magana yara su saka baki"
shiru mairo tayi tana shafa gurin,
momi ta kwanto ta ita jikinta "maryam"
cikiciki ta amsa "na'am"
"duk wadda ya tambayeki mi akayi miki kice komai karki kuskura kice Yarima yace in kika faɗa sai ya kasheki ko kice ranar jini yayi miki zuba kinji?"
"tho momi"
"koda fa can ne kauye karki faɗawa kowa kinji?"
"tho bazan faɗa ba"
"yauwa Maryam ɗina yar albarka tashi muje muyi breakfast"
"tho"
da sauri ta tashi momi ta rika hannunta suka fice,

parlour suka tararda Qasin zaune saman tree-setter rike da cup din tea.
da kallo ya bisu yana kurɓa tea a hankali har suka zauna sannan ya tashi ya nufi kofa,
"yaya yau ba dakai za ah karya ba?"
Siraj ne yake masa maganar yana kokarin saka T-shirt ɗin dake hannunsa ya nufi dining.
kai kawai ya ɗaga masa ya fice,

haɗe gira yayi ya kalli momi "lafiyarsa kuwa?"
momi tace "lafiyarsa kalau saidai ko in wani gurin aka taɓoshi"
kafaɗunsa ya ɗaga alamar bai damu ba yaja kujera ya zauna yana tsokanar mairo,
"miya kunbura miki fuska haka yar kauye?"
turo baki tayi ta kalli momi "momi kingan shi ko?"
kai momi ta girgiza "oh Siraj dan Allah ka rabu da ita bana son fitinar nan dan Allah"
murmushi yayi ya noce kansa ya soma cin abincin.
lokaci lokacin ya kan ɗago dasun haɗa iɗo da mairo yayi mata gwalo ita kuma ta murguɗa masa baki,
daga ita har momi ba suyi wani cin abincin kirkiba suka tashi daman ita Siraj ya tsangwameta

*_2:55pm..._*
Qasin ya shigo part ɗin momi saida ya karewa kujerun parlour kallo sannan ya kalli momi dake tsaye dining yace "Yarima yazo?"
kallon mamaki momi tayi masa "Yarima? mi zaya maka?"
jijiyar kansa ce ta tashi jin yayi kamar ya ɓalɓalowa momi masifa amman ba dama dan mahaifiya ce. dole tasa ya tausasa harshensa "magana nake son miyi dashi momi na ɗauka ta shigo ne"
"tho bai zoba kuma in har akan maryam ne karka kuskura masa magana kaji na faɗa maka"
kallon rashin fahimta yayi mata "momi karfa ayi masa magana kikace"
kallonshi tayi ido cikin ido "eh nima mahaifiyarta ce ina tunanin ko ni kaɗai nayi magana dashi ya isa"
wani murmushin ban haushi Qasin yayi ya juya ya fice,

Gardem ya nufa yana tafe yana tunanin hali irin na momi,
wakewaken Mairo ne suka ɗago da hankalinsa yakai gareta
tana zaune karkarshin bushiyar mangoro rike da gwallon gwaiba tana ci,

sai a lokacin ya soma jin tausayinta nn d nn idansa suka cika da kwallah wata irin tsanar Yarima yaji ta taso masa a ɗayan ɓangaren kuma yana son ganin laifin momi,
ya daɗe yana kallonta zuciyarsa sai wani tunani take kawo masa saida ya fisgi kansa sannan ya samu karasa kusa da ita,

da sauri ta tashi tsaye ta jefarda gwaibar tana masa kallon tsoro.
risinowa yayi ya ɗan sakar mata murmushi "maryam..."
da sauri ta amsa "na'am yaya"
hannu yakai ya shafa gefen fuskarta kamin ya jata jikinshi ya rumgume,
_'ya lalata miki rayuwa Maryam ya cutar dani yayi miki taɓon ds zakiyi bakinciki nan gaba amman zan nuna masa kuskurensa sai yayi nadamar abunda ya aikata'_
a zuciyarsa yake wannan maganar yana cige da lips.

Story continues below



kalamanta ne suka dawo dashi daga tunanin da yake,
"wlh yaya kaci arziki yanzu na daina fitsara na shiryu da baka isa ka mareni na kyale kaba"
hannu yasa ya ciro handkerchief ya share hawaye da suka zubo masa ya ɗago yana murmushi yace "da gaske?"
"Allah wlh kai hmm"
gefen fuskarta ya lakata "ashe ke matsifaffiya'ce ko?"
dariya tayi ta rufe ido "a'a ni mai lafiya ce"
dariyar yayi shima "mai lafiya ai sunan wani ne"
wannan karon rumfumeshi tayi tana dariyar
"yaya zaka bimu kauye?"
"yaushe zaku je?"
"da anyi hutu ranar juma ah za ayi mana hutu"
saida ya sauke ajiyar zuciya sannan yace "zanje Allah ya kaimu"
rawa ta rika masa "yauwa yaya na gode ina sonka sosai"
murmushi kawai ya shafa bayanta,
can ta ɗago "bari naje nayi shirin islamiya kar momi tayi faɗa"
kai ya ɗaga mata ta masa byebye ta nufi cikin gida da sauri.

*©Khadeeja Candy*

candynovels.wordpress.com
[11/5, 9:43 AM] Khadeeja Candy 🍧: *♡... MAIRO ...♡*

*BY*

*_KHADEEJA CANDY_*

*28*

Mairo na zaune parlour gaban tv tana buga game Siraj ya shigo,
da far ah ya karaso kusa da ita yana ya zauna,
kallonshi tayi taja tsaki ta matsa nesa dashi tana harararsa.
hannu ya kai ya kashe game ɗin ya ja mata hanci,
tashi tayi tsaye ta ɗauki fillon kujera ta rika buga mishi iyakar karfinta.

rikota yayi ya fisge fillon yayi ya jefar ya shiga kokuwar zaunar da ita,
daker ta zauna koshi dan ya rike mata hannayene haka ta rika kokuwar kuncewa ganin bazata iya bane yasa dole ta hakura ta zauna kurum,

bakinsa ya ɗora daidai kunneta yace
"plz maryam magana nake son muyi dake ta fahimta ba faɗa"
banza tayi masa ta kara turo baki ta ɗauke fuska.
murmushi yayi "haba my sis plz"
"tho ka faɗa mana ai kunne ne yake ji kuma ka sakeni"
sakinta yayi ta zauna daidai tana fuskartarsa "maryam kinga yau aka muku hutu kuma momi tace kauye zata kaiki dan Allah in kukaje karki yarda a baro ki kice ke bazaki zauna ba"
wani kallo tayi masa ta ɗaga baki sama "saboda mie?"
"kinga can ba daɗi kuma ba abinci mai kyau irin wannan ba gurin bachi mai kyau ba daɗi kinsan ai kauye ba daɗine dashi ba"
"nikan inaso a haks zan zauna har hutun mu ya kare inason naga gwaggo da tsoho da kawayena da kowa da kowa"
"oh maryam bazaki gane ba yanxu fa in kikaje can bazaki sake ganinmu ba sai anyi hutu"
tashi tayi tsaye "eh naji nidai ka kyaleni"
kallo ya bita dashi har ta haye stairs tana masa gunguni.

*_6:30pm..._*
momi na zaune ita da Usman,Nura da Mairo Qasin ya shigo da sallama,
da gudu mairo ta rumgumeshi tana murna momi bata kulashi ba Nura da Usman ne suka rika kallonsa har ya zauna,
gefensa Mairo ta zauna tana rike da hannunsa "yaya mi yasa ka daina zuwa nan gurin momi?"
shiru yayi yana kallon fuskar momi data ki ta kalleshi,
nan mairo ta sake jefa masa wata tambayar "kuma yaya ka daina cin abinci nn?"
sai a lokacin ya kalleta yana murmushi yace "aiki ne ya mun yawa bani da time ɗin kaina shiyasa kika daina ganina"
kai ta girgirza tana dariya,

juyawa yayi ya kalli momi "momi an wuni lafiya?"
amsa mishi tayi still bata kalleshi ba "lafiya kalau Qasin ya aiki?"
"Alhamdulillah"

bai sake cewa komai ba in banda wasa da yake da yatsun mairo momi ma ko kallonsa batayi ba barre ta sake ce masa wani abu,
suna haka aka kira sallar magariba haka ya sashi tashi yana kallon momi "bari naje nayi sallah an kira magariba"
sai a lokacin ta kalleshi "ka shirya ranar assabar zamuje kauye"
kai ya ɗaga "owk momi har da mansura"
"a a daga ni sai kai sai maryam zamuje"
"owk Allah ya kaimu"
"amin"
kallon su Usman yayi "ku ba zakuyi sallar bane?"
tashi sukayi ko wane na sosa kai suka nufi kofa, nn ya juyo gurin mairo "kema je kiyi sallah"
"tho"
da sauri ta tashi ta nufi stairs saida ta shige sannan ya maso kusa da momi ya risina hakan yasa momi ta kalleahi cikin sanyayyiyar murya yace "momi fushi kike dani ko?"
"mi zai sa nayi fushi dakai Qasin mi kayi min?"
shiru yayi yana kallonta kamar mai tunanon abunda zaice,
tashi momi tayi "nikan bari na shiga ciki nayi sallah"
bata tsaya jiran mi zai ceba ta nufi stairs saida yaga shigewarta sannan ya tashi ya fice.

Story continues below



*_washe gari..._*
tun 7am Qasin ya shigo part ɗin momi ya tare a parlour murna gurin mairo ba a magana haka ya sake jikinshi kamar ba shiba momi dai sai kallonshi take.
tare sukayi breakfast sai kusan 10am ya koma part ɗinsa bai daɗe ba ya fito cikin shiri ya yabar gidan.

da dare ma nan ya ci abinci ya rika jan momi da fira tun tana shareshi har ta gaji ta sake jiki, saida dare ya raba sannan yayi mata sallama ya nufi part ɗinshi,

haka Qasin ya rikayi duk wani bachin rai dake ransa dannesa yayi ya barshi a ranshi saidai duk lokacin daya kalli mairo sai yaji ba daɗi,

da sallama ya shigo kaya nuki nuki a hannunsa banci wa yanda Siraj da Usman suka riko,
gaban momi suka ɗire kayan nn da nn mairo ta shiga budewa "momi kayan waye?"
ɗan kwalin dake kanta Siraj ya cire yaja mata gashi saida tayi uhu,
da sauri Qasin ya kalleshi "kai mi yasa kake son mata keta haka ne?"
mairo ta watsa masa harara "mugune shi mai katon kai ai gobe ba zaka gannin ba"
murmushi yayi ya kalli momi yace "dan Allah momi karki baro ta"
shafa kanta momi tayi "a a can zan barota sai taga gari sannan a dawo da ita"
gwalo tayi masa tana masa rawar kai,
dariya Qasin yayi yace "gobe mirna gurin Gwaggo ba a magana"
momi tace "lallaikan an kwana biu ba a ga mairo ba"
rufe baki Siraj yayi "momi mairo kike ce fa"
"eh ai haka suke ce mata can kauye"
aiko nan ya hau kiran suna nata yana fashewa da dariya tun bata kulaba har ta soma tsarguwa ta tsuke baki "tho sai miye dan kace Mairo ai sunane haka ake kirana"
gwalo yayi mata "ai ba mairo yake ba mero yar kauye"
fashewa duk sukayi da dariya haka yasa ta haɗe fuska kamar ta fasa ta turo baki,
nn Qasin ya sake fashewa da wata dariyar yace "Siraj shi yasa ta raina ka ka cika mata shinshigi da yawa"
"ba shinshigi bane Allah mero ne sunan"
da fata momi tayi "ke kyalesu tashi kije ki kwanta kinsan gobe sammako zamuyi"
tasgi tayi kamar ta fasa kuka ta nufi daki.

*©Khadeeja Candy*

candynovels.wordpress.com
[11/5, 9:43 AM] Khadeeja Candy 🍧: *♡... MAIRO ...♡*

*BY*

*_KHADEEJA CANDY_*

*29*

*_washe gari..._*
koda 8am tayi mairo tayi shirin tafiya kasa yin breakfast tayi saboda murna ruwan tea kawai tasha ta tare saman kujera tana kallon su momi dake karyawa,

can taja tsaki ta kalli agogon dake hannunta "mts momi duk kun ɓata min lokaci har 9tayi"
juyowa Siraj yayi ya kalleta "eyye yar kauye an waye yanzu kin iya agogo ko mero?"
kawarda fuska tayi ta masa banza momi ta tashi tana faɗin "bari naje na shirya muje na kaiki gurin Gwaggo ki huta da matsalar Siraj"
kallonta Siraj yayi "momi dan Allah karki baro mana Maryam wlh miss ɗinta zamuyi"
kallonta kawai Qasin yayi ya kara kurɓa tea dake gabansa ya tashi ya fice,

mairo ta kalli momi "nidai kije ki shirya momi kar ki daɗe"
Usman yayi dariya yace "yau Maryam har gudun mu akayi ne dan zakije kauye"
Siraj kamar mai tsira ya hau tsokanarta "kaji fa wai kauye babu ma daɗin faɗin"
taɓe baki mairo tayi ta kalli momi "momi kije dan Allah ki shirya muje"
stairs momi ta nufa tana faɗin "tho yar gidan Gwaggo"
itama tashi tayi tana rufawa momi baya tana hararar Siraj,

*✧*

sha ɗaya da yan mintuna suka kama hanya,
mairo na front-seat Qasin na driving momi kuma a gidan baya surutu kan mairo shi tasawa gaba inta ɗauko wannan ya ɗauko wannan momi dai saurarenta kawai take inta kai gana dariya ba ta tamata saɓanin Qasin da fuskarsa take haɗe hankalinsa ma a wani gurin yake,

hannu Mairo takai ta taɓoshi da sauri ya kalleta "ya maryam mi kikace ne?"
murmushi tayi masa "bance komai ba naga dai kayi shirune baka magana kuma ka ɓata fuska"
sakin fuskar yayi "ina tunanin wani business nawa ne"
"tho ka ka daina haɗe fuska"
murmushi yayi yace "na daina Auntie"
dariya tayi ta kwanta tana kallon t-t,
motocin dake wucewa ta rika lisafawa har bachi ya ɗauketa.

Story continues below



'''*************'''
tsayawar da motar tayi da karfine yasa ta farka a figice tana rabon ido,
rana ne zagaye dasu sai tsalle suke suna ambatar mairo.
da sauri ta fita motar tana uhu suka shiga rumgumar juna ita dasu suna tsalle² ta gina wasu matan aure suka rika lekenta,

tuni momi da Qasin suka kunna kai cikin gidan,
ita kan saida suka gama ɓata mata kaya da kasa sannan ta shiga cikin gidan. da gudun ta karasa ta rumgume Gwaggo dake zaune saman tabarma tare dasu momi, idon Gwaggo cike da hawaye ta soma ture mairo "ni ɗagani ai guduwa kikayi kika barni"
kara rumgume tayi "Gwaggo ni ba guduwa nayi ba ai daman nace miki zan dawo kuma ba gashi na dawo ba ni babu inda zanje"
momi tayi murmushi tace "haba aiko duk kika kori mairo baki mata adalci ba dan kullum zancenki take ita dai Gwaggo ta dai"
Qasin yace "Gwaggo yar matsifa ke kullum matsifarki karuwa take ba raguwa ba"
nn Gwggo ta dawo kansa "eh ai daman kaine ka hure mata kunne tunda kazo taki ta samu matsuwa sai ta biku"
dariya yayi "tho Gwaggo ba gata yanxu mun dawo da ita ba da nan fa da can duk ɗaya ne tunda duk abu ɗaya ne"
momi ta karɓa masa "duɓe ta ki gani na gyare miki ita ta zama yar zamani"
gaban Gwaggo mairo ta dawo tana jujjuyawa kamin ta fashe da dariya ta faɗa jikinta ta rumgumeta,

*_two hours letter..._*
"kingani ko Gwaggo mairo ta sami lafiya ai daman nasan cikin biu sai anyi ɗaya kodai a maidota dan mugun halinta ko kuma ta chanja hali"
Halilu ne ke maganar yana kai lomomin shinkafs da wake bakinsa,
taɓe bag Gwaggo tayi "ai daman ba wani mugun haline da ita ba kaine dai ka bi ka matsa mata"
halilu yayi dariya yace "Allah Gwaggo in zaki faɗi gaskiya kema kinsan mairo ta chanja jifa har take bari yaran na su taɓa ta inda ne ai basu isaba ballan tana ma ta dawo daga birni"
"gaskiya kan ya gashi yanzu har girma maryam tayi kuma tayi hankali"
maganar momi take tana kallon fuskar Gwaggo,

Gwaggo ta taɓe baki "ai dole tun Allah kaɗai yasan hawalar da kuke gwada mata ai duk abunda zai sa mairo ta zama haka ba karamin abu bane"
Halilu ya tashi yana faɗin "Gwaggo ai ba zasu dai yi mata abunda kike nufi ba"
momi tace "ai muna zuwa duk wani abu da tasan bana Gwarai bane zubarwa tayi kuma muka saka ta a makaranta"
juyowa Halilu yayi da far'ah "harda makaranta kuka saka ta momi gaske dai ta kara chanja wa tayi kyau yanzu"
dariya momi tayi "kaji Halilu shi boko har sawa yake mutun yayi kyau?"
"Allah kuwa momi kinga ai yanzu ta natsu kuma ta waye ba kamar daba daman burina kenan naga mairo a makaranta kuma cikin rayuwar jindaɗi"
harara Gwaggo ta watsa masa "kuma can da kake dukanta?"
"yau ai saboda bata jin maganane shiyasa kuma kinga dan ta dainane ake mata haka"
"hmm tho chanjawa tayi ne ai babu irin dukan da bata a hannunka ba"
dariya yayi ya aje kwanon dake hannunsa "ai ba zaki gane ba Gwaggo ni dai bari naje Qasin na jirana mu zaga gari"
momi ta kalleshi "kar kuyi nisa halilu yanzu zamu je gidan tsoho mu koma gida dan ba daɗewa zamuyi ba"
"tho momi bari na faɗa masa"
hannunsa ya ɗauraye bayan yasha ruwa ya kurkure baki ya fice.

*©Khadeeja Candy*

candynovels.wordpress.com
[11/5, 9:43 AM] Khadeeja Candy 🍧: *♡... MAIRO ...♡*

*BY*

*_KHADEEJA CANDY_*

*30*

momi ta kalli Gwaggo tace "wai halilu ya daina karantun da yaje ne"
"wane karatu?"
"ba nasan da yana zuwa can sokoto gurin karatu ba"
Gwaggo ta taɓe baki "karatu kan ai yasha kashi tunda babu kuɗin karasawa"
"ayyah haba nijan kasan yana karatu a da digiri yake ne ko mie?"
"karki tambayeni ni sanin nayi yadda abun yake ne can dai su suka sani"
dariya momi tayi tana gyara ɗaurin ɗan kwalinta,

abincin dake gaban momi Gwaggo ta kalla tace "kema bazaki ci abincin ba ko Qasin ma yace ba zai ciba ku yan birni baza kuci na kauye ba"
"a a aini kinfi kowa sanin ba haka nake ba tun kamin mu baro gida saida muka ci abinci kuma ni bama abincin ne a gaba na ba"
"ko a siyo miki wani abun ne kici?"
"a'a ai inason shinkafa da wake ni wata magana nake son muyi dake Gwaggo"
kara juyowa Gwaggo tayi tana fuskarta "wace magana ce hauwa?"
"cewa nayi wai mi zai hana ayi haɗin gida"
"haɗin gida kamar ya kiɓfito kiyi magana tunda ba kunyata kike jiba kuma ba bakuwarki nake ba"
dariya momi tayi ta matso kusa da Gwaggo "ina nufi auren gida a haɗa Maryam da Qasin"
faɗaɗa fuskar Gwaggo tayi da far'ah "masha Allahu hauwa kin kawo magana daman abunda aketa magana kena a gari wai mun bayarda mairo can birni dan kwaɗayi mamakon muyi mata aure ai kara lalacewa zatayi magagganu kalakala babu daɗin ji
shekaran jiya fa tsoho yake cewa shidai cewa zaiyi a maido da mairo ya huta har nace nidai ba zanyi magana ba indai ba garin kukazo"
dariya momi ta girgiza kai "ai koda man munce fushine kikeyi"
"ai babu yadda halilu bai yiba kan yaje ya ganota na hana amman gaskiya naji daɗin maganar nan kin kawo shawara tho amman kunyi magana da Alhaji?"
"da haɗin bakinsa nake wannan maganar saida muka tattauna komai dashi kuma ya aminci shi da kanshi yace in nazo nayi miki magana ke kuma kiyiwa tsoho magana kinga duk yadda kukayi in muka dawo sai muji"
"tho insha Allah haka za'ayi abu mai sauki"
sosai momi ta jidaɗi dan batayi zaton zata samu goyon bayan Gwaggo ba,
abincin taja ta fara ci suna fira da Gwaggo, daf da zata kare Qasin ya shigo tare halilu.
zaunawa yayi kusa da ita yana kallon agogon hannunasa yace "momi tashi muje gurin tsoho so nake muje gida da wuri mansura tace nayi baki"
banza momi ta masa saida ta gama cin abincin sannan ta tashi suka nufi gidan tsoho,

''' * * * '''
sai bayan la'asar suka dawo gidan Gwaggo har lokacin mairo bata dawo gida ba,
sosai momi taso ta ganin mairo kamin su wuce.
amman ba dama dan halilu yayi nemanta har ya gaji baiga inda ta shiga ba, haka yasa dole momi tayiwa Gwaggo sallama. godiya Gwaggo tayi ta musu ita da halilu suna ɗsgs musu hannu har suka daina hango su,
sannan suka koma cikin gida.
kuɗi halilu ya ciro aljigunsa ya mikawa Gwaggo "ga naki kason"
da far'ah ta karɓa "yayi ɗan albarka abun ya samu"
yana dariya yace "Qasin ne ya bani ɗazun da muka fita"
zaunawa Gwaggo tayi tana faɗin "ai yaron nan yana da albarka wlh shiyasa ni na jidaɗi sosai da haɗin auren na da za'ayi shida mairo"
faɗuwa gaban halilu yayi nn da nn yanayin fuskarsa ya chanja tsigar jikinshi ta tashi a kasali ya kalli Gwaggo yace "aure za a haɗa mairo da Qasin?"
"eh abunda muka tattins da hauwa kenan kuma alhaji ne ya aikota yace a faɗawa tsoho kuma ni wlh nafi kowa farinciki wannan abun da za ayi ksgs ms mun huta da tsegumin mutane-"
da karfi halilu ya haɗeye yawu duk sai yaji maganar ta cika masa kunne, ya juya jiki ba gwari ya nufi kofa, kallo Gwaggo ts bishi dashi baki sake har ya fice,
tsaki taja ta taɓe baki "ai daman kai bason mairo kake ba kafison ka rika gwada mata azaba kamar haihuwarta"

'''***************'''
cikin dare su momi suka shiga sokoto _Rahama Restaurant_ momi tasa Qasin ya biya sukayo takeaway sannan suka iso gida,
Qasin nayin parking ya nufi part ɗinsa, momi ma a gajiye ta nufi nata part ɗin,

*_washe gari..._*
sai kusan 10 momi ta kare haɗa breakfast saboda gajiyan tafiyar jiya gashi kuma mairo maitaimaka mata bata nan,
Nura ne ya taimaka mata gurin jera abincin a dining, Usman yayi dariya "ayyoh Allah momi har nayi miss ɗin mairo"
momi na shirin zaunawa tace "ai nice nayi miss ɗinta yanzu haka ita nake tunani aikin nan duk sai naga yayi min wata kala"
Qasin yayi murmushi "ai momi ko ita sai tayi miss ɗinki balle ma can da nan ai ba ɗaya ba"
Siraj ya kalli momi "Allah momi da ba dan wani abu ba dasai nace Allah ya kara ai saida nace karki barota kika ki ɗaukar shawara ta"
"ai dole na barota wata nawa bata ga gida ba sai yanzu bamabfa shi kaɗai ya kaini ba"
Siraj yace "tho miya kaiki momi?"
tana buɗe marfin filas tace "auren maryam naje nemawa Qasin..."
kamar daga ssma sukaji maganar da sauri Qasin ya tashi tsaye yana kallonta
Usman da Nura ma duk ita suke kallo Siraj baisan lokacin daya saki tea cup ɗin dake hannunshi ba.

"aure fa kika ce momi?"
Siraj ne yake maganar yana mata wani kallon rashin fahimta,
murmushi momi tayi "aure mana miye abun tada hankali a ciki?"
Qasin da tun ɗaxu ya kasa fahimtar ta yace "kamar ya momi nifa naji kin anbata?"
ɗago kai momi tayi ta kalleshi "eh kai na nemawa inason ka auri Maryam ne"
a hankali ya zauna yana kallonta "saboda mi momi nifa ban fahimta ba?"
"bari mu gama cin abinci sai muyi magana"
juyawa tayi gurin Siraj "zauna mana Siraj"
zaunawa yayi yana kallon wainar kwan dake gabansa momi ta sake haɗa masa wani tea ta mika masa,

Qasin kasa cin komai yayi shidai moni kawai yake kallo zuciyarsa cike da tambayoyi,
Siraj ma cin abinci kawai ba dan yana jidaɗinsa ba
wayarsa nayin ringing kamar mai jira yayi sauri tashi tsaye ya ciro ta a jihu ya kara a kunne ya fice,

momi saida ta kare cin abincin tsaf sannan ta tashi ta nufi stairs ko minti uku ba tayi ba Qasin ya rufa mata baya,
gefen gado ya samu ya zauna yana kallon momi dake tsaye gaban madubi yace "momi kefa nake saurare nama kasa fahimtar abun kike nufi?"
zaman kujerar mirrow momi ta zauna "kasan me nake nufi Qasin auren maryam nake so kayi"
"saboda mie momi?"
"saboda inason ka kara aure"
"ban gane na kara aure ba mansura fa momi?"
"mansura ba mata bace Qasin so nake ka auri matar da zaka san kayi aure kasan waye kai"
kai ya girgiza "momi ni ban shirya kara aure yanzu ba haba momi ni bazan iya zama da mata sama da ɗaya ba"
leme baki momi tayi
"soboda mi baka san macce hudu Allah ya halitta maka aure ba?"
"na sani momi amman gaskiya ni ban shirya kara aure yanzu ba"
momi tace "ban fahimceka ba Qasin baza iya ba kamar ya?"
shiru yayi ya maida dubansa wani gurin fuskarsa ɗauke da damuwa,
ido momi ta tsura masa tana jiran amsar da zai bata.
ganin bashida niyar magana yasa tace "ina saurarenka faɗamin dalilinka?"
juyowa yayi ya kalleta "momi da wane ido zan kalli mansura bama zata fahimta ba momi inma gwadanine kike dan Allah ki daina"
"mansura..." momi ta faɗa "itace ta faɗo maka a rai ko baka kada wata matsala sai ita. kar dai ranta ya bache kana gudun bachin ranta amman ita bata gudun naka"
kallon mamaki yayi mata "momi muna zaine lafiya da ita fa ba muda wata matsala"

a hankaɗe momi ta kalleshi "na faɗa maka mansura ba mace bace Qasin har yaushe zaka san waye kai ne tunda mansura tazo gidan nan bata taɓa girka maka na safe da rana da dare kaci ba saidai ka siye takeaway koka zo nan kaci, wata hidima ta dangi bata taɓa tashi ta wanke kafarta taje ba bata taba shiga familinmu ba wani daga familinmu bai taɓa zuwa gurinta tayi masa kyakyawar tarba ba bata taɓa tako kafarta tazo nan part ɗina da sunan tazo gaidani ba matarka bata son haihuwa duk wannan bai taɓa damunka ba bai taɓa bata maka rai ba?"
da karfi momi take masa faɗan saida ya rumtse ido,
"mi yasa son mansura ya rufe maka ido haka Qasin? miyasa baka ganin laifinta baka son bachin ranta wanyannan abubuwan dana lissafa nasan suna damunka amman ka ɓoye saboda kar ranta ya bachi thobin kai ka jure ni bazan iya jurewa ba umarnine nake baka ba neman shawara ba kuma mun riga mu yanke shawara da babanka maryam zaka aura"
kallonta yayi da raunanniyar fuska "momi naji amman fisabilillahi a rasa wadda za a ce na aura sai maryam"
"kamar ya sai maryam
maryam ba mutum bace?"
kamar ya fasa kuka yace "momi kankanuwar yarinya ai kowa ma yaji dariya zai mun"
"kwarai za'a maka dariya kan tunda ka auro dodo ko aljana kamar maryam kake cewa kankanuwar yarinya shekara goma sha?"
tashi yayi tsaye yana kallonta yace "momi am more than 30 now taya kike ganin zan auri yarinyar da bata kai shekara ashirin ba?"
"tho abun kunya kayi ko saɓawa addini kayi Annabi (S.A.W) ya auri nana Aysha tana da shekara 6 aka kaita gidansa tana yar shekara 9 auren duk kuma abunda Annabi ya aikata Sunna ce ba akanka aka fara ba barre a kare kanka dan haka ni maryam nake son ka aura"

lumshe ido yayi ya buɗe "amman momi kona sureta hankalina ba zai taɓa kwanciya da ita ba ba zan taɓa samun natsuwa ba"
momi tace "saboda mi Qasin baka son tane?"
ya daɗe kansa a kasa kamin ya bata amsa "inason ta momi ina sonta sosai amman-"
shiru yayi ya kasa karasawa,

Story continues below



tashi momi tayi tana murmushi tace "ka zamo min ɗa Qasin bana son ka bani kunya mun riga mun kate magana da babanka kuma na sanar a kauye amincewarsu kawai muke jira mansura zaɓinka ce Qasin kasan ko kaɗan bana son aurenta amman na hakura saboda ka samu farinciki dan na fahimci kana sonta sosai tho nima inson ka farantamin ka auri maryam"
baice mata komai ba ya sauke ajiyar zuciya ya fice.

*©Khadeeja Candy*

candynovels.wordpress.com
[11/5, 9:43 AM] Khadeeja Candy 🍧: *♡... MAIRO ...♡*

*BY*

*_KHADEEJA CANDY_*

*32*

*_K'auye..._*
taliya ɗaya ɗaya Mairo take ɗauka tana kaiwa baki tana kallon Halilu Da Shima Taliyar Yake Ci Tana Dariya,
"wai lafiyarki mairo mikike dariya haka?"
Gwaggo ta tambaya cikin dariyar Mairo tace "Halilu ne yake bani dariya"
ɗagowa yayi ya kalleta "dariyar mie nake baki mairo?"
nan ta ɓata fuska "ni dan Allah ku daina cemun mairo nan a birni fa maryam ake cewa yafi daɗi"
Gwaggo tayo dariya "lallai mairo yanzu fa an waye ko ɗan zuwan nan da kikayi tho ai nan k'auye duk mai suna maryam mairo ake ce masa"
"ni dai gaskiya ku daina cemun mairo haka fa jiya su hawwa damary suka rika cemun mairo duk naji haushi"
Gwaggo tace "lallai xuwa birni yayi miki daɗi mairo an fara chanjawa ga kiba ga fari ni har maganarki naji ta fara chanjawa"
"ai dole Gwaggo kullum fa da nama muke karya wa da rana ma muci da dare ma haka ga kwai ga madara ga komai na daɗi ai dole nayi kiba"
wani guntun tsaki Halilu yaja "Gwaggo sai kace marar ido yanxu dan Allah ina kibar da mairo tayi nan daman can ai tanada ɗan jikinta saida kice tayi fari da ɗan girma koshi ba sosai ba"
leme baki Gwaggo tayi "ai kai daman ba son kake a ambaci abun alkharin taba"
murmushi yayi ya ɗauke kai
Mairo ta watsa masa harara tace "aiko Halilu duk wadda ya gannin sai yace nayi kyau nayi fari nayi kiba"
Gwaggo tace "ke fita harkarsa ai shi haka yake baya kaunar a ambaceki da alkhari saidai abunds zaisa ya rika dukanki yana shuri kamar an aiko shi"
mairo tace "aiko Gwaggo kinga ɗana je can ba duka ba komai"
ta karasa maganar tana yiwa Halilu gwalo,
hartatarar ta yayi "dan Allah gafara can ai bazaki koma ba"
"ai wlh sai na koma da hutun mu ya kare zan koma birni na barka nan dan yaro"
kwafa yayi "gani kike kamar wasa nake ko tho bari ki gani bazaki koma ba kowa yayi miki tsaye"
ganin da gaske yake yasa Gwaggo ta kallonshi tace "kamar ya bazata koma ba?"
"babu komai kawai dai bazata koma ba"
"koma warta aiko yanzu ma take dan mai dalilice za'ayi sai in abunda ake son k'ullawa bai yiyu ba kuma bama fatar haka"
ɓata fuska Halilu yayi "tho karma ku soma Gwaggo wannan haɗin da kuke son yi ba zaifa haɗu ba"
Gwaggo ta leme baki "sannu baba ba zai yiyu ba tunda kai ka haifeta wai miyasa baka son mairo ne Halilu? mita tare maka?"
"Gwaggo ba wai bana son cigaban mairo bane ko kaɗan babu wannan a zuciyata hasalima nafi kowa son cigabanta amman Gwaggo ina son ki duba wannan lamarin da kuke son haɗawa kwata² bashi da wata ma'ana"
rike baki Gwaggo tayi "bashi da ma'ana kamar ya nifa ban gane inda ka dosa ba?"
matsowa yayi kusa da ita ya sassauta murya "dan Allah Gwaggo karki yarda da abun nan dasu momi suke son hadawa wata kila ma wata cutace zasuyi ya za ace kamar mairo Qasin ya aure ta haba Gwaggo ki duba fa"
Gwaggo tace "ban fa gane maka ba Halilu ka fito fili kamun bayani yadda zan fahimta mana mi kake nufi ne?"
"Gwaggo taya za ace kamar Qasin yace yana son mairo? mairo tashin yaushe ce kuma yar kauye yaushe mairo tayi wayewar da har zaice yana sonta shifa digirine dashi kuma mai kuɗi ɗan birni.
kuma fa har yana da mata haba Gwaggo ki duba fa"
"tho in banda abunka Halilu minene aciki Qasin ɗan'uwanta ne ka kuma san inda wani abun cutane babu yadda za ayi babansa da mamarsa su amince har suzo tambayar in an basu kuma fa muma abunda muke nemane ya samu tunda kafi kowa sanin abunda uan garinnan suke cewa anki ayiwa mairo aure an kaita birin minene² kananan maganganu anyi kara anyi ice tho yanxu dan an bashi aurenta ai ba wani abun bane tunda ko ba shiba dole ne ai ne ayi mata aure"
"th tunda har haka ne ai kinga kara ma a aura mata wani ɗin ko ɗan gujewa masu cewa dan kwaɗayi aka kaita birni kinga yanxu ai sai su kara cewa wani abun in aka haɗa auren"
Gwaggo tace "babu fa abunda zai sa mu fasa haɗa auren nan duk kuma uban da bai zagemu ba bai haihuba dan an zagemu zagin lake mana zaiyine maganar banza"
da tsaki Gwaggo ta karasa maganar cike da bachin rai.
Mairo ta aje kwanon abincin ta matsa kusa dasu tana musu kallon rashin fahimta tace "mi kuke yiwa faɗa Gwaggo?"
tashi halilu yayi tsaye fuskarsa babu yabo ba fallasa yace "aure za'ayi miki mairo Qasin za'a aura miki"
da sauri ta nuna kanta tana kallon Gwaggo "ni?"
"eh ke aure za ayi miki mairo ai kinsan kin kai munzalin aure ai"
kamar ta fasa kuka tace "ni wlh Gwaggo bana son aure ni yar k'ank'anuwa dani za'ayi mun aure ga yan mata nan a birni manya dasu ba ayi musu aure ba sai ni"
hannunta Gwaggo ta riko ta zaunar da ita kusa da ita "mairo nan kauye ne ba birni ba kuma kinga mutane sai gulma suke suna faɗin anki yi miki aure"
"tho ni ina ruwana dasu nidai ma bana son hutun na fasa a mayarda ni gurin momi"
halilu yace "momi itace ta kawo wannan shawarar tace a aura miki Qasin"
shiru mairo tayi tana tunani, Gwaggo tace "karki ji komai mairo alkharine ake nema miki ba sharri ba kinga ma sai kiyi ta zamanki can birni kina yin yadda kike so, ko bakyaso?"
kai ta ɗaga "ina so Gwaggo amman nidai ina jin tsoro"
idonta cike da hawaye ta ke maganar.
nan Gwaggo ta shiga tallaɓata tana kwantar mata da hankali
ido halilu ya tsura mata kamin ya sauke ajiyar zuciya ya fice.

Story continues below



'''*****'''
"dan Allah Momi ku nemawa Nura admission a A.B.U Zaria nidai ganibnake kamar can yafi"
Usaman ne ke maganar yana kallon Momi dake zaune saman tree-setter tana cin abinci,
Momi saida tasha ruwa sannan tace "ni bana ra'ayin A B U nan nafi son State University nan da aka buɗa ance ana karatu sosai kuma kaga nan garin ne hankalina yafi kwanciya iddan yayana suna kusa dani"
dariya yayi yace "momi ni da nake ɗan fodio fa?"
"eh tho ai duka ɗaya ne tun cikin sokoto take nidai bana son ayi nesa ne kawai irin gari haka ko wata kasa"
"amman momi ai kinga yaya ba nan yayi karatu ba shi har kasar ma ya bari"
kafin momi ta bashi amsa aka turo kofar parlour,
juyowa sukayi suna kallon Yarima daya shigo cikin wata bugaggiyar shadda sky blue.
ba tare da yayi sallama ba ya nufo gurinda suke zauna hannayensa sanye cikin aljihu yana tsosar baki kamar mai shan sweet.

*©Khadeeja Candy*

candynovels.wordpress.com
[11/5, 9:43 AM] Khadeeja Candy 🍧: *♡... MAIRO ...♡*

*BY*

*_KHADEEJA CANDY_*

*33*

Saida ya kusa kawowa kusa dasu sannan yayi sallama Momi ta amsa mishi da Usman,
kujerar dake kusa da Momi ya zauna yana yiwa Usman wani kallon raini ciki² Usman ya gaisheshi, ba tare daya amsa ba ya kalli Momi yace "sannu Momi an wuni lafiya?"
da far'ah Momi ta amsa masa "lafiya kalau Yarima kana nan?"
"no shekaran jiya na dawo dan naje Uk ne tun ranar da muka fita da Maryam"
"Allah sarki tho ya gida ya da kowa²?"
shiru ya ɗanyi kamin ya bata "Lafiya kalau kowa yake"
juyarda fuskarsa yayi gurin tv, Momi ta cigaba da cin abincinta Usman ya tashi ya fice,
daf da zata cinye ya juyo ya kalleta "Momi ina Maryam?"
"Maryam ta tafi Kauye kasan anyi hutu ta tafi ganin gida"
shiru yayi ya ɗan ɓata fuska "yau kwananta 6 tun ranar asabar taje sai kuma hutu ya kare"
gefen fuskarsa ya shafa "oh Momi nako yi mata tsaba na ɗauka tana nan"
"da yake baka cikin garin shiyasa baka sani ba"
tashi yayi tsaye yana murzar zabban hannunsa "ni zan wuce kuma Hajiya tace na faɗa miki tana son ganinki"
Momi ta kalleshi "lafiya dai ko?" wani murmushi yayi "yo ni momi ya za ayi na sani sai dai kinje zakiji"
"tho shikenan sai gobe zanzo insha Allahu ka gaisheta"
kai kawai ya ɗaga mata ya fice yana kallon upstairs,

*_7:12pm..._*
"Assalamu Alaikum"
a hankali momi ta ɗago kai ta kalleshi tare da amsawa ciki² "Amin wa'alaikassalam"
suku² ya nufi kujera ya zauna kansa a kasa yace "Momi an wuni lafiya?" momi fuska babu tabo ba fallasa tace "lafiya kalau ya iyali?"
saida ya haɗeye yawu sannan ya amsa mata "lafiya kalau Momi"
gyaran murya momi tayi tace "Qasin in baka aikin komai inason ka kaini gidansu Hajiya yanzu ta aiko tana nemana ɗazu naso na ɓari har gobe kuma dai hankalina bai kwantaba nafi son yanje naji koma minene"
"wace Hajiyar Momi?"
kallon mamaki momi tayi masa "Auntie Hasana mana"
"Yarima yazo nan ne?"
"eh shine ya faɗa min ai"
tashi yayi tsaye yana faɗin "bari na kiran Siraj sai ya kaiki akwai inda nake son zuwa"
haɗe fuska momi tayi cikin tsawa tace "babu wani gurin da zakaje Qasin kawai ka fito fili yace baka son zuwa gidan iya isa ba sai kayi min nuku² ba"
lumshe ido yayi ya dafa kai "oh Momi baki fahimceni ba-"
hannun Momi ta ɗaga mishi tana tari numfashinshi "na fahimceka Qasin na san abunda kake nufi amman karka amta wannan Yarima ɗan'uwanka ne kuma inason ka sani bazan taɓa yardar maka ba ka ɗauki kiyayyah ka ɗora masa babu wani dalili nayin haka koba ɗan uwanka bane ai ba abun kwaraine bane ballantana ɗan uwa mi yasa baka da tunanine in kaje gidansu Yarima faɗuwa kayi shi da yake tako kafarsa har nan gurina fa,
ya fika sanin muhimmancin yan'uwan taka Qasin ya fika iya siyasa dan ko kiyayyah ce Yarima bai taɓa fitowa fili ya nuna maka ba ballantana ni har a zuciyata nasan Yarima baya kiyayyah dakai"
komawa yayi ya zauna ya kama hannayen Momi ya rike cikin sanyayyiyar murya ya shiga mata magana "bana kishin Yarima ko kaɗan Momi bana kishinsa kawai dai halayensa ne banaso kuma momi bazan taɓa yarda na faɗa a gadar zaren da yake kullamin ba momi kinfi kowa sannin waye Yarima kinsan duk inda ya ganni ko yaga wani dags cikin familinmu sai ya musguna masa kodai ya faɗa masa gana mara daɗi ko kuma yayi masa wani abun na bachin rai ni kuma na tsani haka momi saboda babu abunda Yarima zai nuna min
sannan momi kin hana na rama momi kince Yarima ɗan'uwana ne nasani shiyasa ma nake ɗaga masa kafa amman momi kinsan Maryam ma yar'uwata ce ko kuma duk abunda ya sameta ya sameni bazan taɓa mantawa ba"
lumshe ido momi tayi ta sauke ajiyar zuciya a ranta tana _...ba zaka taɓa ganewa ba Qasin..._
can ta buɗe idon ta kalleshi tace "naji zaka iya tafiya"
"momi ki shirya na kaiki mana"
"a'a sai goben kafin ka fita"
"momi kar kimun rashin fahimta bana nuf-"
numfashinsa ta tara tare da tashi tsaye "a a Qasin na fahimtace ka karka damu gobe zaka kaini"
bata tsaya jiran mi zai ce mata ba ta nufi stairs,
Momi na shiga ta tararda wayarta saman madubi tana ringing da sauri ta karasa ta ɗauka Hajiya ta gani a screen kamin ta ɗanna picking ta kara a kunne,
_"Amin wa'alaikissalam Hajiya ya gida?"_
banji mi akace mata ba na daiji tace _"eh ina gida lafiya dai?"_
_"tho sakin iso"_
sauke wayar tayi gabanta na ɗan faɗuwa tana mamakin abunda yasa Hajiya take son ganinta haka.

Story continues below



*_© Khadeeja Candy_*
[11/5, 9:43 AM] Khadeeja Candy 🍧: *♡... MAIRO ...♡*

*BY*

*_KHADEEJA CANDY_*

*34*

*_9:35pm..._*
Hajiya ta iso gidan tun kamin ta fito mota momi ta fito ta tareta cike da far'ah, rumgume juna sukayi kowane na dariya suka shigo parlour,
momi bata barta ta zauna ba suka nufi bedroom drinks kala² momi ta jere mata da kayan ciye² bayan ta zauna suka ɗauko firar yaushe gamo,
can momi ta kalli Hajiya tace "nifa Hajiya ina mamakin zuwan nan naki haka kawai"
murmushi Hajiya tayi "ba zuwan haka kawai bane maman Nura ɗazu ai nayiwa Yusuf sako ya faɗa min kince sai gobe zaki zo shiyasa ni kuma na kasa hakura har goben nace bari nazo yau"
"nima ai na tashi zuwa ɗazun bayan magriba sai kuma nace bari dai na bari har goben lafiya dai ko?"
Hajiya ta dafa momi "lafiya kalau ɗanki ne yaga wata yarinya yace yana so"
farincikine ya bayayyana a fuskar momi duk da faɗuwar da gaban ta yake "masha Allahu ba dai Yarima ba?"
"shifa ai nima farinciki kasa ɓuyiwa yayi a gareni kuma yace nazo na tambaya masa shine fa nace tho ya kira min daya faɗa min kince sai gobe ni kuma na kasa hakuri"
momi tace "ai dole abunda aka ta jira shekara da shekaru nima ai na jidaɗi sosai"
Hajiya tace "yace yarinyar tana nan gidan ke kike rikonta yace mun sunanta maryam"
wani irin gaɗuwa gaban momi ya karayi shiru momi ta ɗanyi kamin ta haɗe yawu tace "maryam Hajiya?"
yanayn yadda tayi maganar yasa Hajiya ta kalleta "eh ita koda matsala ne?"
"a'a ba wata matsala kawai dai naga yarinyar karama ce dan bazata wuce 13 ba"
murmushi Hajiya tayi "kar wannan ya dameki ys faɗa min daman karamar yarinyace har yake cemin kiyonta yake sai ta girma tukuna tho shekaran jiya nida Mai Martaba muka sashi gaba muna masa faɗa mishine fa yake faɗa min shi babu yarinyar da yakeso inba ita ba sai kinga yadda mahaifinshi yayi murna"
momi jiki ba kwari tayi murmushi tace "ai dole kan abunda kowa yske mafarki nimaai nayi farinciki"
Hajiya tace "ina kika sani nima daɗin nake ji kamar me shine babbah yanzu kingaya kamata ace yanzu yayo aure kanensa na biu fa yanzu za ayiwa aure shi yasa ma ai abun ya damu mai martaba yasa yayi masa haka dan cewa yayi im bashi wadda yake so tho shi zai mema masa duk wadda yaga dama shine fa sai ya faɗa mana ita kaɗai kawai yake so dafa duk akayi magana sai yace shi bai samu wadda yake so ba kinga sai yanxu Allah yayi"
ajiyar zuciya Momi tace "kinsan komai yana da lokaci wata kila sai yanzu Allah ya kaddaro za ayi saida fs hajiya wani hanzari ba gudu ba"
kallonta Hajiya tayi "ina jinki minene?"
"its maryam ɗin yar kauye ce kuma ba tsyi wani karatu ba dan zuwannan ma da nayi da ita Qasin ya sata makaranta"
"kar wannan ya dameki duk ba matsala bace tho da dai har yace yana so ai duka ɗsys muke gurin Allah babu wadda yafi wani"
lumshe ido momi tayi ta buɗe ta kallii hajiya tace "shikenan zanje kauye sai nayi masa magana dan yarinyar ma tana can hutun na da akayi sai na kaita ganin gida"
"wai yar insce?"
"wlh kanwar su Qasin ce yar kanne mahaifinsu da mukaje kauye sai muka zo da ita......"
"tho yanzu dai kije kauyen ki nema masa"
cikin karfin hali momi tace "insha Allah haka za ayi"
hajiya tace "ki faɗawa mai gidanki dan ni cikin satin nan nake son aje inma ta kama har dani duk sai muje koda da Mai Martaba ne"
"a a ni ma ai ns isa na nema masa ba sai kunjeba inma dolene kuje ai sai na faɗa muku amman sai in babansu ya dawo dan yayi tafiya"
murmushin jindaɗi Hajiya tayi "ai ba matsala bace Allah ya dawo dashi lafiya ana nan anata harkokin business ɗin ko? ba hutu"
"eh ai shi koyaushe baya samum zama gida neman kuɗi kawai aka sawa gaba ba a nan ba a can zamansa gida kaɗsƙan ne kuma a koma"
"tho mai sa akan ai daman bai gaji zamaba musamman in akwai iyali"

haka momi tayi ta smsa mata firarda suke kamar marar lafiya sai kusan 11 da wani abu ta bar gidan,
daren momi kasa bachi tayi tana tunsnin yadda zata billowa lamarin, har a ranta Qasin take son maryam ta aura sai kuma yanzu dabo biu ziciyarta take mata akan maganar da hajiya tazo da ita dan Hajiya ba tada wani farinciki sai na yarima taya zata yarda Qasin ya aureta ga yarima in kuma ta yarda Yarima ya aureta rigima ce ba yar kaɗan,
kai ta dake ta zauna gefen gado _...oh ni mi yasa ban faɗawa hajiya anyiwa maryam miji ba..._ sai yanzu take jin haushin,
_...amman kuma in har taji Qasin ne ai zata iya cewa ya barwa Yarima kuma gashi har na rig na faɗa a kauye Qasin yana sonta yanzu kums si sai su ga ɓayi musu magana biu..._ busarda iskar bakinta tayi ta lumshe ido.

Story continues below



*_© Khadeeja Candy_*
[11/5, 9:43 AM] Khadeeja Candy 🍧: *♡... MAIRO ...♡*

*BY*

*_KHADEEJA CANDY_*

*35*

*_washe gari..._*
_10:47am_ Qasin ya shigo part ďin momi zauna ya tararda ita a dining area,
a kujerar daya saba zama ya zauna yana kallonta "momi ina kwana?"
a hankali ta kalleshi kana ganin fuskarsa kasam tana ďauke da damuwa "lafiya kalau ka tashi?"
"eh momi ke kaďai kike karyawa?"
"a a duk sun karya sun tafi makaranta ne kai ka daina karyawa nan ko?"
ďauke fuska yayi ya ďauko wani zancen "momi ya maganar tafiyar so nake na kaiki sannan na wuce dan yau zan wuni busy"
tea momi ta k'urɓa tace "ai tazo tun jiya"
kallon mamaki yayi mata "nan gidan laifiya dai ko?"
"lafiya kalau wata magana mukayi"
"tame momi?"
"sirrice"
"kamarbya momi nasan duk abunda zai sa Hajiya tazo gidanna ba karami bane dan Allah ki faɗa min minene kodai wani abun aka cene?"
momi bata ce masa komai ba ta tsura masa har tsargu ya tashi dan kanshi ya nufi kofa da tunane²
"Qasin..." murya kasa² momi ta kirashi da sairi ya juyo ya dawo "gani momi"
"ka faɗawa matar maganar aurenka?"
kasa yayi da kansa ya daɗe kamin ya bata amsa "a a momi ina tsoron abunda zai biyo baya ne kinsan ba fahimta zatayi ba"
ajiyar zuciya momi ta saike tace "yayi kyau zaka iya tafiya"
kallonta yayi kamar yace wani abu sai kuma ya juya ya fice,
dafe kai momi tayi tana nemawa kanta mafita sa kusan minti 30 haka sannan ta tashi ta nufi stairs,

''' * * * '''
kusan isha'i Siraj ya shigo part ďin momi ganin ba kowa parlour yasa kai tsaye ya wuce ďakinta, zaune ya tararda ita ta rafka uban tagumi tana kallon windo,
"lafiya momi?"
a sanyaye ta kalleshi da murmushin karfin hali "lafiya kalau Siraj ka shigo"
yana k'ok'arin zaunawa kusa da ita yace "momi gaskiya ba lafiya ba dan tunda safe naga damuwa a fuskarki akwai abunda yake damunki momi"
batace komai ba ta sauke ajiyar zuciya ganin haka yasa yace "barin kashi a ciki baya maganin yunwa momi babu kuma wadda ya dace ki fafawsa sirrinki irina hankalina bazai taɓa kwanciya ba momi matukar naki bai kwanta ba dan Allah ki faɗamin abunda ƴake damunki"
kallonshi tayi "kona faɗa maka Siraj ba magani zaka mun ba"
"naji nidai dan Allah ki faɗamin momi indai ba so kike nima na shiga damuwa ba"
momi ba dan taso ba ta fayyace masa komai,
Siraj ya daďe yana jinjina al'amarin kamin ya kalleta yace "yanzu momi mi kike gani shine fita?"
"nima ban saniba Siraj ita nake ta nema na kuma kasa samu"
Siraj yace "tho momi ga wata shawara..."
kallonshi momi tayi "ina jinka"
"momi mi zai hana kik'i yarda Qasin ko Yarima ya aureta"
"saboda mi?"
juyo yayi yadda zata fuskanceshi da kyau yace "kinga yanzu in kika bari Qasin ya aureta Yarima zai yita ganin laifinki shida mahaifiyarshi kuma otama zata taga kin mata cin fuska kinki bari Yarima ya aure kika bawa Qasin ya yaje ɗanki kimsan Hajiya bata tada wani Farinciki sai na Yarima tunda shi kaɗai ta haifa zata iya ɓatawala da kowa akansa kinga in kika mata haka ba zata taɓa mantawa dake ba kuma kinga zata ga baki tashi aurawa Qasin ita ba har saida Yarima ya ganeta yace yana so tunda baki riga kin faɗa mata kin nema masa ita ba kuma itama ba ganewa zata yiba sannan kinga shima yaya sai naga kamar bayason maryam sosai kuma kinga yana kaunar matarsa ko auren maryam yayi za suyita samun matsala,
in kuma kika yarda Yarima ya aureta nan ma baki tsira ba dan kinsan yaya bazai taɓa yarda ba kuma nima bazan yarda ki aura masa ita ba dan zai iya musguna mata kodam ganin daga falinmu take kuma kodan muji haushi zai iya yi mata hakan koda yana sonta dan kinsan halin Yarima ishesshen kanshine ko yanzu baki san dalilin da yasa yace sai ita kaɗai yake so ba tunda akwai yan mata da yawa a garinnna kuma suna sonsa dan babu wadda zaice yana so ta kishi kodan dukiyarsa balle ga mulki ga kyau amman ya nace shi sai maryam bakisan abunda yake shiryawa ba kuma kinga duk ya cuceta mudai ba kyalewa zamuyiba kauye kuma dake za suyi kuka dan haka ni abunda nake ganin mafita shine kawai ki bari can kauye ayi mata aurenta duk wadda suka ga damar haɗa shi da ita sai su aura mata"
gyara zama momi tayi tana nazarin kalamansa,
"ka kawo shawara Siraj amman kuma har yanzu da saura in har haka ta faru ita hajiya mi zan ce mata suma kauye dana riga nace Qasin na sonta ya zance musu har yanzu da sauran rina a kaba"
murmushi yayi "no momi kawai ki samu baba ku tattauna sai a warwar zancen auren Qasin ni da kaina zan kaiki kauye in yaso sai kice musu daman bakiyi shawara da Qasin ba kuma yanzu yaji bai amintaba kuma matarsa yar matsiface dan haka kina tsoron abunda zaije ya dawo dan haka a bar zancen aure kawai duk wadda suka dama su aura mata ita kuma hajiya in kika dawo saiki faɗa mata an riga anyiwa maryam miji alkawarine tun tana karama dan haka iyaye sunce bazasu tada ba koda tace ki kaita kauyen karki yarda kikaita dan zata iya zuwa ta rokesu ta nuna musu kuɗin koma shi Yarima da kanshi dan a yarda a aura mishi kuma kinga ko aura mishi ita akayi wahala zata sha dan kinga karamar yarinya ce sannan ba wani tsayawa zai kikayi yana bata hakkinta ba kuma zai iya ganinta tankar kaunarsa koma yarsa da ta masa abu ya daketa koma karki faɗa masu har sai an ɗaura aure, kawai momi wannan shine abunda nafa ya dace kiyi"
murmushin jindaďi momi tayi ta shafa kansa "ka kawo shawara Siraj haka zanyi Allah yayi maka Albarka"
shima murmushin yayi yace "amin momi shikenan damuwa ta wuce ko?"
kai momi ta ɗaga masa ya tashi tsaye yana faɗin "tho muje kici abinci dan nasan bakici abincin dare ba"
"jeka gani na zuwa"
"owk"
juyawa yayi ya fice cike da farinciki.

Story continues below



*_©Khadeeja Candy_*

candynovels.wordpress.com
[11/5, 9:43 AM] Khadeeja Candy 🍧: *♡... MAIRO ...♡*

*BY*

*_KHADEEJA CANDY_*

*36*

A waya Momi ta kira Abbah sukayi magana dan kasa hak'uri tayi ganin ta samu mafita sosai yaso ta bari har ya dawo suje tare amman tak'i dan yadda Hajiya ta matsa mata kullum cikin kiran wayarta take,
ranar alhamis tun da safe Siraj ya fitarda motar da zasu shiga suna karyawa suka kama hanya,

*_K'auye..._*
ajiyar zuciya Gwaggo ta sauke tace "wannan magana ai kamar anyi sara akan gaɓa ne"
Momi tayi mata kallon rashin fahimta "mi kike nufi wani abun ne?"
Gwaggo tace "akan maganar nan ne wai Halilu yanzu ya fito wai sonta yake bai tashi magana ba saida yaga anyi wannan maganar kiji mun rainin hankali"
Momi ta rik'e baki "yanzu Halilun ne yace haka?"
Gwaggo tace "ai kuma baki san wani abun haushi ba wlh tsoho yayi tsaye shi sai Halilu zai aurawa"
"amman tsoho yaji da Qasin ne ake son haɗa auren?"
"wlh yaji kinsan matsalar da aka samu? ya rigani zuwa yayi magana dan ni a yadda na yanke sai an ɗan kwana biu kusan zata koma sannan nsyi maganar kinga koma minene amsar in kukaje sai kuji aiko yana jin haka sai kawai yaje ya faɗawa tsoho wai shi sonta yake ni kuma da naji haka sai naje nima nace ga abunda kike ce aiko tsoho k'in yarda yayi ya dinga ganin laifi yace nice nake son juyarda abun haka ai da kunso shi zaku samu kuyiwa magana ba niba wai shi daman yana son ya haɗasu amman yana tsoho amman yanzu tunda har haka ta faru shikena ta kwana gidan sauki shi Halilu zai bawa babu yadda banyi ba amman yayi tsaye shi lallai sai Halilu balle nasan ya kwashi k'arya da gaskiya ya faɗa masa"
Momi tace "tho injin ita Maryam ɗin tana sonshi?"
"uhmmm aifa kinji inda matsalar take nan itakan tayi tsaye wlh bata sonshi yanxu haka in kikayi mata maganar kuka zatayi"
"dank'ari aiko akwai matsala tho ba'a faɗawa tsoho bata soba?"
"hmm ai sai kiyi abunda tsoho yake nema ai shine ya tsaya kai da fata wai ko bata so sai anyi shi daman ya yanke shawarar aurarda ita dan ya gaji da tsegunmi mutane"
Momi tace "amman kuma Gwaggo ai naga kamar shi Halilun bashi da wata matsala"
"aiko shine da matsa nifa na rik'ashi tun yana k'arami yanzu haka ganin da kike masa baya noma tho ɗsn k'auye in baiyi noma ba mi zaiyi sannan babu sana'ah babu aikin fari babu ma bak'i in kinmai magana yace shi karatu zai bazai iya rayuwar k'auye ba kuma karatun nan bai wani yi zurfi ba balle ace aiki kuma ance aikin nan fa ko a can birni wahala yake tho ina wani abun k'aurai tunda babu abun ci da mata"
Momi ta jinjina kai zatayi magana taji an rumgumeta da karfi,
dariya tayi jin Mairo ce tace "tun ɗazu mukazo ban ganki kiba kina can gurin yawo ko?"
dariya Mairo tayi ta k'ara rumgume Momi "a'a Momi tunda kukazo naga Siraj yaje dani yawo sai yanzu muka dawo Momi nayi mesage ɗinki"
"missed ake cewa yar boko"
Gwaggo tayi dariya tace "haka muke da ita abu kaɗan sai turanci ita yar boko"
Momi ta juyo da ita ta zauna daidai "ina kukaje yawo wato kings shigowa amman da kiks gs Siraj sai kiks shareni ko?"
"a'a Momi yawo fa mukaje da mota ko'ina sai kallonmu ake"
ta karasa maganar tana wani marmarɗen ido,
Gwaggo tace "kin samu abunda kikeso ko kiyiwa mutane kuri tho ina kika baroshi ko ya sake fitane?"
"a'a waya yake yi yanzu zai shigo"
kallon Momi tayi "Momi kinci abinci?"
da murmushi Momi tace "a'a Gwaggo ki bata bamu ba amarya"
nan da nan Mairo ta ɓata fuska kamar ta fasa kuka "Momi bana so ki daina"
Momi ta dafata "ai dole kiso kedai tashi ki ɗauko mana abincin"
matsawa tayi gefen ta takure kanta ta haɗe rai, Siraj na shigowa ta rushe da kuka.
da sauri ya karaso kusa da ita "lafiya mi akayi mata"
Momi tace "wai dan nace mata amarya shine take kuka"
"kamar ya auren za'ayi mata ne?"
"eh Halilu za'a aura mata wai ita kuma bata sonshi"
murmushi yayi ya shiga tallaɓata yana bata hak'uri, daker ya samu tayi shiru ta tashi ta nufi ɗaki,
gurinsu Momi ya nufo yana faɗin "wai yanxu daga yin magana har anjuyarda abun zuwa ga Halilu?"
kamin ya zauna Momi tace "a'a daman rigimar da aketayi kenan wai shi sonta yake...................."
nan Momi ta labarta masa komai,
Sosai Siraj yayi mamaki ya kalli Gwaggo yace "mi yasa bakison auren Gwaggo? Halilu bashida hallin k'waraine hala?"
Gwaggo tace "a' wlh yana dashi nina rik'ashi tun yana k'arami gaskiya bashi da wani mugun hali"
Siraj yace "tho mi yasa bakison ya auri Maryam ni aganina ba wani abu bane kinga shima ai ɗan'uwane kuma duk duniya bana ganin akwai wadda ya dace ya aureta sama da shi kefa kika reneshi Gwaggo ya tashi a hannunki yanzu dan yace yana son Maryam in kikak'i baki ganin xai iya shiga damuwa? ni aganina koda ahi baiyi magana ba kema ya kamata ki haɗasu ballantana har yayi gaskiya Gwaggo in kikak'i goya masa baya baki masa adalciba kuma kin nuna masa ke bake kka hafeshi ba"
shiru Gwaggo tayi tana nazarin maganar.
"amman fa Sirajo ita Mairo bata sonshi fa"
"karma ki kawo wannan Gwaggo Maryam k'aramar yarinyace bata san soba ko a birni ksmar Maryam za'a iya aura mata wadda akaga dama balle k'auye kune kuke k'ara sa tana cewa bata sonshi kawai kibar ma wannan zancen inta girma gidansa a babu zance k'i"
dariya Gwaggo tayi "kuma fa haka ne Sirajo da maganar ka Allah dai ya zaɓa mana abunda yafi zama alkhari"
duk sukace 'amin'
Siraj yace "amman dai Gwaggo ba zaku raba ta da karantunta ba ko?"
Gwaggo ta leme baki "karatu kan ai yasha kashi tunda in an mata aure ai tarewa zatayi kaga ko babu zancen karatu"
"amman gaskiya Gwaggo ku barta tayi makarantar ta koda anyi auren ne inta k'are sai ta cigaba da zamanta na aure"
ido Gwaggo ta nuna masa "kaga nawa ni yanzu kuma fa ako auren akayi nan zatayi ta zama dan bashida gurin ajeta sai yayi gina"
shiru Siraj yayi ya nuce kai bai sake magana ba,
can Momi tace "wai ins wadda taje ɗauko mana abinci?"
Gwaggo tace "aifa sai kiyi bafa zata ɗauko ba da nan fushine take dake"
Momi tayi dariya "in banda abinki Maryam daga faɗar gaskiya sai cibi ya zama k'ari"
Gwaggo ta tashi ta nufi ɗaki tana faɗin "bari na ɗauko miki indai wannan ce saiki shekara"
tashi Siraj yayi "ni bari naje bakin kasuwa kamin ki k'are cin abinci"
"kai ba zaka ciba?"
"kai Momi kinsan ni kan bazan iya cin abincin nan ba bari dai naje can ko zan samu abunda zanci"
kai Momi ta ɗaga mishi ya saka hannayensa aljihu ya fice.

Story continues below



*_©Khadeeja Candy_*

candynovels.wordpress.com
[11/5, 9:43 AM] Khadeeja Candy 🍧: *♡... MAIRO ...♡*

*BY*

*_KHADEEJA CANDY_*

*37*

kai tsaye Siraj bakin kasuwa ya nufa daman ɗazu da suka wuce ya hango gurinda Halilu yake zaune,
Halilu na hangoshi ya ɓata fuska aransa yana _babu wani magiya da zaka mun na barma ku ita wlh boko dai nima nayi dan haka baka fini wayeba_,
Siraj ya k'arasowa kusa dashi yayi masa sallama tare da mik'a masa hannu, ciki² ya karɓa ya juyarda fuska,
murmushi Siraj yayi ya zauna saman teburin da yake zaune yana faɗin "kai kaɗai kake zaune?"
"eh ina hutawane"
Siraj ya kalleshi "Halilu ka saki jikinka dani bana nufin cutarda kai ko cilas taka yin abunda baka tashi ba ni shawara nazo na baka kuma inason kayi nazari ka ɗauki shawarar karka kalleni a matsayen ɗan'uwan Qasin inason ka kalleni a matsayin ɗan'uwanka"
juyowa Halilu yayi ya kalleshi "wace shawarace?"
dafashi Siraj yayi yace "naji ance ka fito kana son Maryam ita kuma bata sonka kuma kaga yayana ma yana sonta banci shi kuma akwai wadda yake sonta can birni sannan naji ance baka kada sana'ah ba kama da gurin ajeta tho kuma yanzu naji tana zance sai ta bimu birni tho abunda nake so da kai shine kayi sauri ka matsa a ɗaura muku aure koda baka da gurin ajeta ɗin dan in kayi sake tho rasata zakayi kaga in ka aureta koda tace sai taje birrin kana iya kyaleta taje tayi karatunta amman fa da aurenka kaga kamin ta k'are kai kuma ka samu aiki kayi gidan ajeta ni zan iya taimaka maka ka cigaba da karatunka amman karka yarda wani sati yayi ba'a ɗaura maka aure da ita ba"
ido Halilu ya tsurawa Siraj yana son tantance abunda yake faɗa,
_ta yaya zai yi masa wannan shawarar bayan shi ɗan'uwan Qasin ne miyasa yake son shi ya aureta sama da Qasin can wata zuciyar tace amman kuma fa gaskiya ya faɗa min tunda banida gurin ajeta balle abun ciyarda ita kuma nasan yanzu Mairo bazata yarda ta zauna k'auyen nan ba tunda nama ji ta fara zancen sai ta bisu kuma gashi har yace zai taimaka min na k'arasa karatuna inhar da gaske yake kuma fa inna aureta na huta koda taje can birrin wani ya ganta yana so na dai riga na aureta......_
dafashi da Siraj yayi yasashi dawowa daga duniyar tunanin daya tafi,
Siraj yace "ka yarda da shawarata Halilu shine kawai mafita a gareka"
ajiyar zuciyar Halilu ya sauke yace "maganganunka abun dubawa ne Siraj saidai na kasa ganewa taya zaka goya mun baya na auri Mairo bayan yayanka ma yana sonta?"
murmushi Siraj yayi yace "shiyasa tun farko nace karka ɗaukeni a'matsayen ɗan'uwan Siraj ka ɗaukeni a'matsayin ɗan'uwanka Halilu bana nufi cuta a gareka nayi haka ne saboda shi Qasin yana da mata sannan kuma zuwan da Maryam tayi birni ne ya ganta yace yana so saɓanin kai da tun tana k'arama kake sonta ko ɗazu na faɗawa Gwaggo babu wadda ya dace da Maryam irinka,
Halilu nifa bance dole ka ɗauki shawarta ba kawai in tayi maka shikenan in kuma batayi maka ba duk ɗaya ne"
ya karasa maganar tare da tashi tsaye. Hannu halilu ya mik'a masa "na gode sosai Siraj zanyi tunani a kai"
"nima na gode da bani lokacinka da kayi Allah ya shige mana gaba"
nan sukayi sallama Siraj ya nufo gida,

''' * * * '''
bakin k'ofa ya tararda Mairo zaune rik'e da ɗan karenta tana zane a k'asa,
da murmushi ya fito motar ya nufota, saida ya kusa kawowa kusa da ita sannan ta ɗago ta kalleshi ta wani turo baki wai ita gamai fushi,
sai da ya zauna kusa da ita sannan yace "fushin mi kike Maryam?"
"wai Momi ce tace bazata je dani birni ba"
"tho ai hutunku bai k'areba kuma kinga aure za'ayi miki babu ma zancen komawa birni gaba ɗaya rayuwarki ta dawo nan kenan"
da sauri ta kalleshi "ni wlh ba zan zauna ba kuma ni bana son aure wlh bana son halilu"
da kuka ta k'arasa maganar,
saida Siraj ya duba yaga babu mai kallonsu sannan yace "in baki shawara?"
kai ta ɗaga mishi
yace "karki yarda a aura miki Halilu kinga ɗan k'auyene kuma duk wani abun daɗi da kikasan kinaci da kin aureshi kin daina cinsa kenan kuma kings babu ke babu karatu babu zuwa birni nan zakiyi ta zama kina daka da zuwa daji kina ɗebo kara shikenan kinyi bankwana da jindaɗi muma ba zaki sake ganinmu ba har Momi"
k'ara fashewa tayi da kuka da sauri ya rufe mata baki yana kallon k'ofa "shinnnnn kar sujiki kina son na baki wata shawara?"
nan ma kan ta ɗaga yace "koda an ɗaura miki aure da Halilu karki yarda ki zauna kice ke gurin mu kikeso kiyi ta musu kuka kice kesai an barki kinyi karatu in kikayi haka nasan za'a iya barinki ki bimu amman inba haka ba shikenan ba zaki k'ara jindaɗi ba kinji"
cikin muryar kuka tace "tho Gwaggo zanyiwa ko tsoho?"
"dukansu har Halilu kice indai yana sonki yabarki kije kiyi ta musu kuka kina murje² in kikaga sunk'i yarda sai kice ke sai kin kashe kanki...."
maganar yake yana wani kalle² kamar wani munafiki,
ita ko sai kai take ɗaga mishi, hannunta ya rik'o "Maryam kimin alk'awari komai akayi bazaki faɗa ni nace kiyi haka ba"
"nayi wlh bazan faɗa ba"
murmushi yayi "yauwa ai inma kika faɗa ɓatawa zanyi dake dan haka karki faɗawa kowa kinji share hawayenki"
hannu tasa tana share hawaye yana tayata saida ya goge mata fuska sannan ya rika hannunta suka shiga cikin gidan,

Story continues below



*_©Khadeeja Candy_*

candynovels.wordpress.com
[11/5, 9:43 AM] Khadeeja Candy 🍧: *♡... MAIRO ...♡*

*BY*

*_KHADEEJA CANDY_*

*38*

biye² Momi tayi dan duk inda wasu ɗangi suke na kusa saida takai Siraj,
da shine bai san dangi sosai ba sai kusan magariba suka dawo gidan Gwaggo danyi mata sallama, tana zaune tana tuki tuwo suka shigo Mairo na genta,
"Assalamu alaikum" Momi ce tayi sallamar Gwaggo ta amsa mata "amin wa'alaikumussalam ku wayannan sai yanzu?"
momi tace "tho ya muka iya Siraj ne ai ya tsayarda mu yanzu kan ai sai kama hanya"
"a'a zaku tsaya kuci abinci kan"
Siraj yace "a'a Gwaggo k'ara mu wuce kawai bason tuk'in nan na dare nake ba koma can ai munci abinci"
tashi Gwaggo tayi tana faɗin "kai ai da yayanka daman bason cin abincina kuke ba Allah dai ya kiyaye hanya"
dariya yayi ya ciro kuɗi aljihunshi ya mik'a mata "ga daishi a siye goro"
karɓa tayi tana godiya nan ya sake sa hannu ya ciro dubi kusan 5 ya mikawa Mairo, k'in karɓa tayi idonta suka ciko da kwallah "a'a nidai zan biku bama son nan"
hannun Momi ta rike ta fashe da kuka,
lallasarta Momi ta shigayi "haba Maryam ki bari har hutunku ya k'are sannan kinji kinga ko yanzu tsoho saida yayi ta mana masifa akanki kinga in mukaje dake faɗa zaiyi"
"nidai kije dani haka inaso Momi dan Allah karki bari"
risinawa Momi tayi ta dafata "tho ya isa daina kukan haka kinji ki tambaye Halilu in ya yarda sai na aiko a ɗaukeki amman fa sai inya yarda da zarar ya yarda kisa a bugamin waya kawai zam aiko mota aje dake?"
lak'e kafaɗa tayi "a'a nidai kije dani yanzu dan Allah Momi"
kuka ta ringa rusawa tana k'asa tana sama duk sai Momi taji ba daɗi babu irin lallaɓar da basuyi mata ba amman ta k'iyin shiru,
har bakin k'ofa ta biyosu tana jan gyalen Momi, nan Siraj ya shiga lallaɓata shida Gwaggo ganin abun nata na gaskene, k'in daina kukan tayi nan idanuwan Momi suka koma kwallah. daker ta samu tayi musu sallama suka kama hanya,

'''*****'''
cikin dare suka iso gida bayan Siraj yayi parking Momi ta fito rai ba daďi ta nufi part ďinta
palour ta tararda Qasin zaune yana kallon k'ofar data shigo, gyara zamansa yayi yana faďin "sannu da zuwa Momi"
wani irin haushinshi Momi taji ciki² ta amsa mishi "yauwa sannu"
saman kujera ta zauna tana sauke gajiya, Qasin ya kalleta yace "Momi yau ina kukaje haka tun safe naga kun fita kuma sai yanzu ka kuka dawo lafiya dai ko?"
"lafiya kalau k'auye mukaje"
Siraj ne ya bashi amsa yana k'ok'arin zaunawa kusa,
Qasin yadda yaji gabanshi ya faɗi yaji bazai iya k'ara tambayasu wani abu ba tashi yayi yasa hannayensa aljihu yace "sleep tight Momi saida safe" bai tsaya jiran amsarta ba ya nufi k'ofa,
saida ya fice Siraj ya kalli Momi yace "gaskiya Momi Maryam taban tausayi sosai banji daďin da muka barota ba"
wani guntun numfashi Momi taja tace "tho ya muka iya tunda haka suka zaɓa mata kuma kasan indai ba Halilu ya aminceba ba zasu bari muzo da ita ba"
"eh ai naga haka amman ya kamata a masa magana ya barta ta dawo nan kamin ya kammala shirye² kinga ta ɗan k'ara samu illimi"
"tho ai sai yaga dama tunda yanzu shi zai aureta"
taɓe baki yayi ya tashi yana faɗin "saida safe Momi"
"Allah ya tashemu lafiya nima ai bari na shiga ciki nayi sallah"
har zai fice Momi tace "amm.. Siraj gobe ma ka shirya muje gurin hajiya na mayar mata da amsa"
murmushi yayi yace "In'sha Allah" ya juya ya fice,

'''*** *** ***'''
*_3:47pm..._*
wani uban ta gumi Hajiya ta rafka wadda ya rufe mata fuska da kuma hanci,
cikin yanayin damuwa Momi tace "Hajiya babu yadda zanyi ne na buga na buga sukace ina su sam bazasu chanja zaɓin ds sukayi mata ba babu yadda banyi ba amman suka k'i aminta wai tun tana k'arama mahaifinta yayi wannan alk'awarin na haɗasu aure dan haka su bazasu tada ba"
saida Hajiya ta sauke ajiyar a'zuciya sannan ta kalli Momi tace "kin kuwa faɗa musu wanene yake sonta?"
"hmm Hajiya babu abunda ban faɗa musu ba inma baki yarda ba sai ki kira Siraj kiji komai dan tare mukaje ke in takaice miki labari magagganu babu daɗin ji nima ai kamar kar naje sai kin gani"
kai Hajiya ta girgiza "ni yanzu bansan yadda zan cewa Yarima ba ba fahimta zaiyi ba kuma yanzu yana iya cewa inba ita ba saidai ya fasa aure"
Momi tace "ni wlh dama zaki ɗauki shawarata a nema masa wata tunda yan'matan ne gasu nan kuma kyawawa"
Hajiya tace "ai inda matsalar take yace yana so ɗin"
dafata Momi tayi "ki yarda dani Hajiya In'sha Allah wannan sai yace yana so dan babu abunda akeso ga ‛ya mace wadda Allah bai bata ba babu wadda zai ganta yace baya sonta 'yar k'awata ce kawai ki bari mu haɗa shi da ita muga kuma abunda Allah zaiyi"
shiru Hajiya tayi kamin tace "tho yanxu mi kike ganin zance sa game da wannan yarinyar ta k'auye?"
"karki faɗa masa anyi mata miji dan inyaji haushin haka zai iya rufe mishi ido yak'i son wannan kawai ki bari inna kirata yaje ya ganta kinga in yace yana so sannan ki faɗa masa Maryam anyi mata miji kinga babu wani shan wahala nasan zai amince da wannan"
sosai Hajiya ta jidaɗin shawara daman mafita take ta nema,
da fira Momi ta jata sai kusan biyar ta baro gidan,

Story continues below



*_©Khadeeja Candy_*

candynovels.wordpress.com
[11/5, 9:43 AM] Khadeeja Candy 🍧: *♡... MAIRO ...♡*

*BY*

*_KHADEEJA CANDY_*

*39*

*_K'AUYE..._*
tun tafiyar Momi Mairo bata kara walwalah ba duk tabi ta takura kanta kullum cikin kuka take tana kiran Momi duk tabi ta rame dan bata cin abinci ga ɗan banzan ciyon kai da take fama dashi wadda ya sakar mata zazzaɓi sanaɗin kukan da take, Gwaggo babu irin rarrashin da batayi mata ba har ta gaji ta zura mata ido,
yau ma kamar kullum tana zaune saman ta barma tana rusa kukanta data saba Halilu ya shigo,
tana ganinshi ta juyarda fuska ta k'ara fashewa da kuka,
saman tabarmar ya zauna yana bata hakuri. maimako tayi shiru sai abun ya k'aru Gwaggo ta tabe baki tace "aifa sai kayi ai duk kasan matsalar yarinyar nan ka barta taje birni kak'i ka dai riga kasan halin Mairo tun ba yau ba ba daina kukan nan zatayi ba dubi yadda duk tabi ta rame dan Allah ko abincin kirki bata ci amman baka tausayinta shiyasa mani nake tsoron auren nan naku wlh kar kaje can kayi ta gallaza mata daman ka saba"
Ajiyar zuciya ya sauke ya dafe kanshi,
_ba nida wata mafita sai wannan inhar na barta taje birni tho na rasata kenan dole ne na ɗauki shawarar Siraj dan itace kawai mafita agareni_
kallon Gwaggo yayi dake ta masa masifa yace "shikenan zan barta taje birnin amman sai in an ďaura mana aure ta tafi da aurena inma karatun zatayi taje tayi in yaso daga baya sai ta tare"
kafin Gwaggo tayi magana Mairo tace "da gaske halilu?"
kai ya ɗaga mata yana murmushin da baikai zuci ba "da gaske Mairo tunda naga kina son zuwa birnin"
k'ara matsowa tayi kusa dashi "yanzu ka yarda gobe naje?"
"a a sai an ɗaura aure"
"tho a ɗaura mana ni na ƴyarda a ɗaura sai naje"
bakinta Gwaggo ta buge ta kalli Halalu tace "indai har da gaske kake tho kaje ka sanarda tsoho duk abunda yace shikenan"
kai ya ɗaga "In'sha Allah haka za'ayi anjima zan sameshi mu tattauna"
da sauri Mairo ta rumgimeshi tana masa godiya,
fisgeta Gwaggo tayi ta jefar tana mata faɗa wai bata da kunya, Halilu kan daɗi yaji dan gani yake yanzu Mairo na sonshi tunda ta daina kukan aurenshi sai na a barta taje birni,

'''*** *** *** *** ***'''
cikin satin nan aka saka ranar ɗaurin auren, murna gurin Mairo ba'ah magana ko yar kunyar nan da yan matan k'auye suke yi ita batayi ba,
duk wadda yagani sai yayi zaton son Halilu take itakan bata ma kulaba murnar zuwa birni take, a'waya aka sanarwa da su Momi dama duk wasu dangi da suke nesa,
duk wannan abun da ake Qasin bai saniba dan ya daina zuwa part ďin Momi indai ba wani abun zaiyi ba Momi kuma ta fita sabgasar,
ana gobe ɗaurin aure Abbah ya dawo dan Momi ta faɗa masa ranar laraba za'a ɗaura,
*_2:45pm..._*
Momi na shirye² kaima Abbah abinci Qasin ya shigo rike da wata leda a hannu,
saman kujera ya dire kayan yana faɗin "gashi inji Abbah yace na kawo miki"
ba tare data kalleshi ba tace "shaddodin ne?"
"eh sune"
"ok barsu harna tashi amm ka shirya gobe zamuje ɗauri aure k'auye"
haka yaji maganar kamar wadda aka jefowa abu daga sama da k'arfi ya haɗeye yawu ya kalleta yace "auren wa Momi waza'ayima aure?"
tsayawa Momi tayi ta kalleshi "Maryam za a ɗaurawa aure amman bada kai ba da ɗan'uwanta Halilu"
a hankali ya kai zaune saman kujera "Momi ban gane abunda kike nufi ba?"
kusa dashi Momi ta dawo ta zauna tace "Qasin na fahimci baka son Maryam kuma kana tsoron matarka dan haka nake ganin inna aura maka ita na cilas maka na kuma shiga tsakaninka da matarka shiyasa nace musu ka yanje zancen nemanta su kuma sukace koda kai ko ba da kai ba su daman aire zasuyi mata dan haka suka zaɓa mata Halilu a matsayen miji gobe ne ɗaurin aurensu na sani ko ba yau ba wata rana kai da kanka zaka nemi k'ara auren"
kai ya girgiza baki na rawa yace "wlh Momi ina sonta Momi na shirya bin umarninki kodan na faranta miki miyasa kika yi haka ba tare da kinyi shawara dani ba haba Momi"
"aikin gama ya riga ya gama Qasin sannan banida tabbacin kana sonta ko a'a bazan iya kai Maryam gurinda nasan zata cutu ba inason ka shirya gobe ka halarci ɗaurin aurenta"
kasa ce mata kamai yayi ya tashi idonsa cike da hawaye jiki ba gwari ya fice.
da dare Qasin kasa bachi yayi haka yasa ya dawo parlour,
_tunani fal a ransa jin yake bai kyautawa Momi ba da kuma zuciyarsa dan harga Allah yana son Mairo saidai natsuwace bayaji a tare da ita haka yasa sai kuma yaji daďin yadda Momi tayi dan yana ganin hakan kamar mafitane a gareshi tunda yanzu tayi aure ai dole ya daina sonta_ juyawa yayi daga kwancen da yake, ya lumshe ido.

Story continues below



*_WASHE GARI..._*
tun 6 na safe Qasin yabar gidan, kuma ya kama duk wayoyinsa ya kashe,
haka su Momi da Abbah suka Kama hanya ba dashi ba Siraj dai inbanda dariya babu abunda yake yana faɗin wai Qasin kishi yake.

*_©Khadeeja Candy_*

candynovels.wordpress.com
[11/5, 9:43 AM] Khadeeja Candy 🍧: *♡... MAIRO ...♡*

*BY*

*_KHADEEJA CANDY_*

*40*

*_K'ARFE 2:30PM..._*
aka ɗaura auren Mairo da Halilu babu laifi anyi taro saidai wasu yan'uwa na nesa basu samu halarta ba ango kan baki har kunne sai murna yake,
gudumuwa kan ya samu sosai musamman gurin Abbah.
ɓangaren Mairo ma farincikin ba baya ba dan ita zuwanta birni ne kawai a gabanta, da su Momi zasu dawo lak'ewa tayi sai ta biyosu daker aka samu aka lallaɓata bayan an aje ranar da Momi zata aiko a'je da ita.

'''*** *** *** ***'''
"miya hana ka zuwa ɗaurin auren nan Qasin?"
zaune yake saman kujera kansa a k'asa Momi kuma na tsaye kansa tana masa magana, a hankali ya ɗago kai ya kalleta yace "wani meeting ne mukayi da wasu chenis shiyasa na fita da wuri"
taɓe baki Momi tayi tace "tho Allah ya kyauta daman zancen karatun Nura ne inason ka nema masa admission a state University tun kamin lokaci ya k'ure"
"abun yana raina Momi nayi magana ai kuma In'sha Allah gobe zanje makarantar ma"
"Allah ya kaimu"
"Amin"
haka ya tashi ransa a jagule ya fice,

*_4 DAYS LETTER..._*
ruwan sama ake kamada bakin k'waya harda k'ank'anra,
Qasin na zaune parlour sanye da k'ananan, laptop na gabansa yana yan danne² sai cup ɗin drink dake gefen laptop ɗin. a hankali yaji ana shafashi ɗagowa yayi suka sakarwa juna murmushi "daman ba bachi kike ba?"
"a a idanuna huɗu baka jin sanyi dear kake zaune parlour?"
murmishi ya sake sakar mata "tho ya na iya so nake na k'are aikin nan kamin gobe dan-"
ihun daji yasashi kasa k'arasa maganar ya tashi da sauri ya nufi windo,
yana ɗaga labulen gabansa yayi wani dakan uku² ganin Mairo na gudu cikin ruwa tana son kama lema. kasa tantance abunda yake gani yayi mamaki ya rik'ayi yana tunanin abunɗa zai kawo Mairo gidan cikin wannan lokacin haka ya rik'a k'acce² wai ko idonsa ne suke masa gizo,
gani haka yasa Mansura ta karasa kusa dashi tana kallon windom tana ganin Mairo ta ɓata fuska ta taɓe baki "mts miye abun kallo gurin wannan mahaukaciyar ai daman ni nasan sonta kake"
juyowa yayi yana kallonta fuskarsa ɗauke da mamaki kwata² baya jin abunda take faɗi dan hankalinsa na can wani guri har ta k'are surutanta ta shige ko ɗaya kunnensa bai ɗauka ba,

*****
"gaskiya ni har yanzu sanyi nake ji sosai"
Mairo ce take maganar tana sanye da atamfa red colour da hijab tana saukowa downstairs,
Siraj dake zaune saman kujera ya kalleta yace "ai dole duk fa ruwan nan da akayi saman kaki suka k'are"
"tho ba lema naje kawowa ba sai suka jik'ani" "tho dan kinje kama lema sai akace ki tsaya cikin ruwa kiyi wanka?"
dariya tayi ta zauna saman kujera tana k'ank'anme jiki "kai kuma Siraj ba murna nake nazo birni ba saida fa nayi ta kuka sannan aka barni nazo"
rigar sanyin dake jikinsa ya cire ya mik'a mata yana faďin "ai naga duk kin rame k'arɓi wannan rigar ki saka"
saida ta k'arɓa sannan tace "kaifa?"
tashi yayi ya nufi stairs "bari na ɗauko wata"
kai ta ɗaga mishi ta shiga saka rigar,
takan mata yawa sosai saida kuma ta fitar mata da kyaunta sosai tana jan zip taji an buga k'ofa, da sauri ta nufi kofar tana buɗewa ta sako idanu "lahh Yarima"
"na'am pretty gal"
da murmushi ya amsa ya kai hannu ya shafa gefen fuskarta, sannan ya shigo.
hannunta ya rika suka nufi kujera Siraj na tsaye yana kallonsu da murmushi har suka zauna, sannan yace "ke Maryam tashi daga nan yanzu ba kamar da bane"
da sauri ta koma a ɗayar kujerar Yarima ya ɗago yana masa wani wulakantaccen kallo, can kuma ya ɗauke kai yana kallon Momi dake saukowa dwnstairs,
saida ta zauna sannan suka soma gaisawa "Yarima yau kaine a gidan namu da maraice haka?"
saida ya daɗe kamin ya bata amsa
"eh an faɗa min Maryam tazo ne"
mamaki ne fal a fuskar Momi "waya faɗa maka?"
"mutum..."
a takaice ya bata amsa yana kallon zoben hannunsa,
murmushi Momi tayi zatayi magana Siraj yace "Momi ya kamata yasan halin da Maryam take ciki yanzu Level ďinta ya chanja ba"
kallon Momi Yarima yayi alamar bai fahimci abunda Siraj ke faďi ba,
cike da tsoro Momi tace "Yarima...Marya...m fa yanzu ..matar..aurece.. satin da ya wuce aka ɗaura mata aure"
wani kyakkyawan murmushi ya saki wadda ya kara fitar da kyauwunsa yace "kidding me it's funny Momi"
Siraj yace "ba wasa ake maka ba yanzu Maryam igiya uku ce a kanta in kuma kana shakku kaje ka tambayi Hajiya ko kuma ita Maryam ɗin gata nan"
kallon Maryam yayi dake kallonshi tana dariya da rufe fuska, ya sake kallon Momi kai Momi da gyaɗa mishi tace "wlh an ɗaura mata aure Yarima kaji kuma na rantse"
tashi yayi tsaye ya wani yarfarda hannu "ohhh Momi inma gwadani ne kike tho ki daina bazai taɓa saɓuwa ba bindiga a ruwa bari kiji na faɗa miki tunda hajiya ta haifeni ban taɓa neman abu na rasaba wht ever I luff is my nd my only inason ki rubuta ki aje Maryam tawa ce no mttr wht dan haka in so kike ki gwadani k'ara ma ki daina in kuma so kike ki aura mata wani tho ki janye wannan tunanin..."
yana kaiwa nan ya karkaɗe rigarsa ya fice,
lumshe ido Siraj yayi yana _k'arya kake Maryan tawa ce duk wannan plan ɗin nawa ne tunda har yayana baya sonta tho mine mijina ba kaina she s my_ a zuciyar yake wannan zancen yana wani lafiyayyen murmushi
MAIRO CHAPTER 3

Kallon Siraj mummy tayi cike da tsoro tace "kaga abunda nake gudu ko?" cikin mamaki Siraj yace "bansan abunda yasa kike tsoron Yarima ba Momi kina gudun 6acin ransa sama dana kowa kuma fa dolene a fad'a masa gaskiya dan ita matar aurece yanzu kuma dolene ya d'aga mata k'afa"
ajiyar zuciya Momi ta sauke tace "Bashi nake nufi ba bakaga yadda ya fita ba rai a 6ace inafa gudun abunda zaije ya dawo"
kai Siraj ya girgiza "babu abunda zai faru ki kwantarda hankalinki babu abunda zai iya yi"
Momi ba dan ta gamsu ba tace "Allah yasa haka"
Siraj ya amsa da "amin"
nan Mairo ta kalli Momi tace "nifa duk ban gane abunda yake faruwa ba" k'arasowa Siraj yayi kusa da ita yace "ai bazaki ganeba maganar manya ce jeki upstairs"
lak'e kafad'a tayi "ni bazani ba kasan ďazun kace zaka siya min ice cream in an ďauke ruwa"
murmushi yayi "yanzu da sanyin nan zan siya miki ice cream Maryam gashi ma duk sanyi ya kamaki ki bari har gobe saina siya miki chocolate" kai ta girgixa tana masa kallon rashin yarda "a'a Ni bazan yarda ba saika siya min kuma ice cream nake s-"
Bata k'arasa ba Momi ta katsa mata tsawa "Ke dan Allah rufema mutane baki wuce kije ďaki"
razana Mairo tayi da sauri ta nufi upstairs
da kallo Siraj ya bita saida ta shige ďaki Sannan ya kalli Momi yace "Momi kin razana ta sosai ki daina mata tsawa haka yau² fa tazo gidan nan"
Tsaki Momi taja "mtwwss aikin banza in yau tazo gidan nn yau ta fara zuwane? ai tasan halina sarai danni bazan ďaukar mata abunda Gwaggo take mata ba kuma faďa ai yanzu ya dace ayi mata shi dan tasan ciyon kanta yanzu fa babbar macce take k'okarin zama tunda aure ne da ita"
dariya Siraj yayi "gaskiyarki Momi banga laifinki ba"
harara kawai Momi ta watsa mishi ta shige kitchen shi kuma ya fice yana dariya,

'''******'''
da dare Momi da Mairo na zaune parlor Qasin ya shigo,
Mairo na ganin shi ta tashi da sauri zata tare shi tana dariya "oyoyo yaya tun ɗazun na zo ban ganka ba"
Murmushi yayi ya ɗaga mata hannu alamar karta k'arso kusa dashi ya zauna a kujerar dake facing ɗin ta Momi yana faɗin "baki je part ɗina ba ai da kin ganni"
komawa tayi ta zauna tana faɗin "ai Momi ce ta hanani zuwa can kuma kasan yau anyi ruwa sosai"
kai ya ɗaga mata
"thom yayi kyau ya hanya dasu Gwaggo"?
"lafiya kalau suke duk sunce suna gaida ku"
"thom muna amsawa ina mijin ki?" dariya tayi ta shigar da kanta jikin Momi alamar kunya,
Kallon ta Siraj yayi yana dariya yace "ni wallahi abun nan ni har dariya yake bani wai kamar Maryam Ace anyi mata aure"
Kallon rainin wayo Momi tayi masa "au kama ce ma? ai Maryam ta isa aure koda a nan birni ballantana k'auye shekarar ta fa goma sha 13 fa yanzu musulunci ma ai da shekara 9 ya halitta ayi macce aure baka ga ta kusan kamo kafaɗa ta ba?"
Kai Siraj Ya jinjina yace "lailai Momi kema kina cikin masu ra'ayin yan da"
Momi tace "sosai ma aini da ace yaya mata Allah ya bani bazan bari suyi wani girma ba zan aurarsu dan bazan yarda mu haďa kafaďa dasu ba a'rasa gane uwar sai kace yayan yahudawa"
dariya Siraj yayi shida Mairo banda Qasin daya maida hankalinsa gurin tv,
sun daďe suna fira amma ko uffan bai ceba sai can ya kalli Momi yace "Momi me Maryam tazo yi?"
"cigaba zatayi da karatu"
Siraj ne ya bashi amsa
fuskar mamaki Qasin yayi yace "ba'a mata auren bane?"
murmishi Siraj yayi ya jefa masa tambaya ba tare daya amsa masa tasa tambayar ba "kamar ya ba'ayi mata auren ba?"

Qasin yace "tho ya za'a ďaukota a rabota da mijin azo nan da ita ace wani karatu zatayi sai in daman can ba'ayi mata auren ba"
Sai a lokacin Momi tasa baki "da izinin mijinta tazo nan"
gyara zama Qasin yayi yana murmushi mai ďauke da mamaki yace "nifa ban gane inda zancen nan ya dosa ba ya za'ace an ďauko yarinya daga k'auye a kawota birni tayi karatu kuma karama kamar Maryam"
Siraj ne ya tari numfashinsa "tho ai da yarda su Gwaggo tazo nan kuma shima mijin nata ya aminta ni banga wani abu a ciki ba"
kallon Mairo Qasin yayi ta wani marairaice jikin Momi kamar ba itaba kafaďunsa ya ďaga ya tashi tare da sa hannunsa aljihu ya fice,

Story continues below

Har ya isa part ďinsa tunani yake abunda yasa Momi take son yin haka sam zuciyarsa k'in yarda tayi da anyi mata aure,
_thom amman su Abbah sunje ďaurin aure kwanakin baya sai in ba nata bane in har kuma ba nata bane thom na wane_
Haka zuciyarsa ta rik'a masa sak'e² har ya shiga cikin parlour.
Zaune ya tararda Mansura ta wani sha kunu tana wani kunbure² murmushi yayi ya k'arasa kusa da ita yakai hannu ya shafa gefen fuskarta "my heart ya naga fuskarki haka?"
ture masa hannu tayi ta juyarda fuskarta, hannunta ya kama "wai mi yake damunki ne waya ta6a min zuciya?"
cikin fushi tace "ina kaje?"
"gurin Momi"
"mi kayi?"
"kamar ya mi nayi?"
cike da mamaki ya mayar mata da tambayar,
juyowa tayi ta kalleshi "gurin Maryam kaje Qasin"
fashewa yayi da dariya "kina bani mamaki Mansura bansan abunda yasa damun kanki akan Maryam ba yarinya da yanzu ta riga ta zama matar aure"
"thom mi tazo yi nan in har da gaske an ďaura mata auren?"
ta6e baki yayi "Momi tace karatu zata cigaba dayi kuma mijinta ya yarda"
shiru tayi alamar tunani ganin haka yasa ya janyota ta kwanto saman k'irginsa yana faďin "minene na wani tsayawa tunani dear baki yarda da mijinki bane?"
kallonshi kawai tayi ta zare hannunta daga nashi ta tashi ta shige bedroom,
da kallo ya bita harta shige sannan ya sauke ajiyar zuciya yana _"oh ni Qasin kuma yanxu wace rigimar ce Momi zata janyo min da Mansura"_
tsaki ya ďanja ya tashi ya sake nufo part ďin Momi,

tun kamin ya k'araso ya hango Mairo tsaye bak'in k'ofar tana kallon part ɗinsa,
shima ita yake kallo zuciyar na bugawa har ya k'araso fuska a ɗaure yace "min kike yi a nan?"
hannu tasa a baki tayi k'asa da kaita "Siraj nake jira Momi ta aike shi"
"shine zaki zo nan kiyama mutane tsaye da dare haka wuce ki shiga ciki"
da ɗan faɗa yayi mata maganar hakan yasa bata masa musu ba ta juya ta shiga shi kuma ya rufa mata baya,
tsaye tayi tsakiya parlor tana kallon shi har ya zauna "yaya....."
ciki² ta kira sunan shi yana kallonta tace "abinci zaka ci?"
Shiru yayi kamar ba zai amsa mata ba can kuma ya girgiza mata kai alamar a'a yace "ina Momi?"
da sauri ta bashi amsa "tana ɗaki bari na kirata" bata jira mi zaiceba ta nufi stairs da gudu,

_3 Minutes Later_
ta fito rike da hannun Momi k'asa Qasin yayi da kansa har suka sauko,
Zaunawa Momi tayi tana kallonshi "lafiya Qasin?"
ɗagowa yayi ya kalleta "Momi akan Maryam ne yanzu wannan abun da aka yi ba zai haifar da wata matsala ba?"
Kamin Momi tayi magana suka ji parking ɗin mota da sauri Mairo ta tashi ta nufi k'ofa dan a zaton ta Siraj ne,
juyowa tayi da sauri tana faɗin "Momi ga Yarima nan da wata mata"
da sauri Momi ta tashi tsaye "Yarima?" Momi ta tambaya nan Qasin ya tashi ya lek'a ta window cikin mamaki yace "Hajiya ce tare da Yarima miya kawo ta da dare haka?"
Kai Momi ta girgiza "daman nasan za'a rina" kallonta Qasin yayi "wani abun ne ya faru Momi?"
bata bashi amsa ba ta kalli Mairo tace "ke jeki ɗaki"
da gudu Mairo ta nufi upstairs.

*One heart One luff ❤*
*for my fan's*😍

*_©KHADEEJA CANDY_*
[11:27PM, 3/17/2017] Khadeeja Candy: ​*♡... MAIRO ...♡*

*BY*

*_KHADEEJA CANDY_*

Candynovel.wordpress.com

*42*

Da sallama Hajiya ta shigo parlor fuskantar ba yabo ba fallasa,
Momi da Qasin suka amsa mata guri ta samu ta zauna tana amsa gaisuwar da Qasin yake mata saida Hajiya ta gama gaisawa da Momi sannan Yarima ya shigo hannaye sa sanye cikin aljihu kansa a ɗage yana kallon ceiling,
kallo ɗaya Qasin yayi masa ya ɗauke kai dan yasan babu komai a tattare dashi sai rainin wayyo da wulakanci, zaunawa Yarima yayi yana ya mutsar fuska can ya kalli Momi yace "Momi ya dare? "
da far'ah ta amsa masa "lafiya kalau Yarima ya harkokin"
saida ya ɗan daɗe sannan ya amsa mata ciki² "Alhamdulillahi"
Murmushi Momi tayi ta kalli Hajiya tace "lafiya dai Hajiya na ganki da dare haka?"
Nisawa Hajiya tayi tace "lafiya kalau wata magana ce Yusuf yazo min da ita ɗazun shine nace bari na zo da kaina naji yadda abun yake"
da ɗan fargaba Momi tace "wani abun ne?"
Hajiya tace "ce mun yayi yaga yarinya da yake so a nan gidan wadda muka yi magana dake har nake ce masa kodai ba ita bace yace itace ni kuma nace bari na zo da kaina naji"
Momi saida tayi murmushi sannan tace "wai Maryam kike magana ta dawo ne dan zata cigaba da karatu ne kamin mijin nata ya ɗan kintsa"
da mamaki Hajiya tace "ya ďan kintsa kamar yaya nifa kwata² ban gane inda kika dosa ba Maman Nura yarinyar daman mijin bai shirya ba aka aura masa ita?"
Momi tace "Hajiya kinsan auren k'auye sai a han-"
bata k'arisaba Yarima ya katse ta "wait! wait!! wait!!! ni ban gane inda kuka dosa ba wai kuna nufin da gaske anyi mata aure?"
Momi ce ta riga bashi amsa "anyi mata aure Yarima ai kasan ba zanyi maka k'aryaba....... "
sai a lokacin yaji wani mummunan faɗuwar gaba tashi yayi tsaye yana kallon Hajiya yace "baki faɗa mata inason Maryam ba?"
ajiyar zuciya Hajiya ta sauke cikin sanyin jiki tace "na faɗa mata Yusuf na tambaya maka aurenta sai dai a lokacin ka riga kayi latti dan anyi mata engaged da wani har ma ansa ranar aure su ni kuma sai naji tsaron faɗa maka saboda gudun ɓacin ranka na yanke shawarar nema maka wata ba tare da ka sani ba"
tana kaiwa nan Yarima ya girgiza kai yana murmushin da za'a iya banbancewa shin na bak'in cikin ne ko kuwa na ɓacin ran da Hajiya ke magana,
rumtse ido yayi ya buɗe ya kalle su yace "Maryam bata isa aure ba ballantana na yarda da anyi mata auren da gaske, nima kaina raino ta zanyi har sai ta mallaki hankali kanta sannan na aure ta kuma ni babu ruwana da wani plan naku ko anyi mata aure ko bayi mata ba ni aurenta zanyi in'ma har anyi mata auren thom ku warware shi dan duk abunda nake so nawa ne ban taba son abunda ba nawa ba"
cikin wani irin ɓacin rai ya k'arasa maganar,
nan Qasin ya kalleshi a hankaɗe yace "su warware aure saboda kai ka haife su ko kuma dan kana wawa? But banga laifinka ba cox If you are shameless, you would do as you wish"
hannu Yarima ya ɗaga mishi yana wani izgilanlen murmushi "wait please Mr Pest stay where you are"
nan zuciyar Qasin ta kawo ya tashi tsaye tare da nuna shi da ɗan yatsa "you are fool Yarima Koda ba'a ɗaurama Maryam aure ba bazan taɓa bari ta aureka ba dan kai baka dace da zama mijin Maryam ba"
tsawa Momi ta katsa masa "ya isa haka Qasin! wace irin magana ce wannan Yarima bai dace da zama mijin Maryam ba sai kace wani mugun mutum ya kamata ka rik'a tauna magana kamin ka furta ta"
cike da ɓacin rai Momi ta k'arasa maganar,
nan Qasin ya sassauta murya ya kalli Momi yace "Momi karki ɓata ranki akan abunda na faɗa kinfi kowa sanin wanene Yarima wata k'ila ma mugun halinsa baya rasa nasaba da abunda yasa kika hana masa Maryam"
hannu Hajiya ta kai ta dafa kafaɗar Qasin "Qasin ɗana kake aiban tawa haka har kake ik'irarin hana masa matar daya buɗe baki ya furta yana son ya aura kuma kake faďa masa wayan nan kalaman a gaban idona mi yayi maka haka Qasin?"
taɓe baki Yarima yayi yace "kin ga ɗaya daga cikin abunda nake faɗa miki kenan ai Qasin yafi gaban haka"
matsowa Qasin yayi kusa da shi yana faɗin "banyi maka k'age ba Yarima, mummunan halinka a bayyane yake kai-"
"Qasin............"
da k'arfi Momi ta kira shi hakan yasa ya kasa k'arasa maganarsa,
K'ofa Momi ta nuna masa "wuce kabar parlor nan"
Hajiya ce ta tari numfashinta "ki barshi kawai ya faɗi son ransa damace ya samu sabodaYusuf yaga jininku yace yana so shine kake son wulakanta shi ko?"
kai Qasin ya girgiza "ba haka nake nufi ba Hajiya koke kikaji abunda Yarima ya aikatawa Maryam ba zaki yarda ya aure ta ba ya lalata mata rayuwa ya mayar da ita babbar mace"
Wani irin sanyi jikin Momi yayi da sauri tace "kabar wannan maganar Qasin karka kuskura aikata abunda zai zame maka matsala"
k'asa yayi da kansa ganin yadda ran Momi ya ɓace, tsaki Yarima yaja "mtssww aikin banza kara min mutum ai da ka faɗa ni duk a tafin hannu nake kallonku daga kai har Momi babu wani plan da zaku haďa da zaija kwakwalwata ni da kai kar tasan kar ne" har lokacin kan Qasin a kasa yake yana sauraren kalaman Yarima, gudun 6acin ran Momi yasa ya kasa ďagowa yace masa ko da uffan.
matsowa Hajiya tayi kusa da Qasin tace "me kuke nufi da wayannan kalaman Qasin me kake nufin Yusuf dashi me kake nufin ya aikata me kuke k'ok'arin yi haka? saboda ba Siraj bane ko shiyasa kake aibata shi har kake k'ok'arin yi masa k'age?"
nan Qasin ya ɗago kai ya kalleta a natse yace "shima ɗan uwana ne kamar Siraj Hajiya ba k'age nake masa ba shi kanshi ya sani na sani Momi ma gata a nan ta sani fyaďe yayi ma Maryam........"

tassssssssss!!!
Momi ta wanke fuskar Qasin da mari Hajiya kuma ta k'ura masa ido tana son tantance abunda ya faɗa,
fashewa Yarima yayi da dariya ya rik'a tafa hannayensa kamar wadda aka yima albishir,
matsowa yayi kusa da Qasin ya rik'a wuyar rigarsa da yatsu biu ya ɗan ja kamar mai wasa da yaro ya girgiza kai yana murmushi yace "ohhh brother why are you so stupid today? u knw wht da ace a film ne mukeyi a nan da ka zama super star cox it really works"
Sake masa wuyan rigar Yarima yayi ya ɗan matsa baya yana nuna shi da yatsa "bansan Wayyo ka iya nan ya tsaya ba i thought kai wani super hero ne ashe kai sakarene ai Kana da dama fel free 2 tll th wrld hw yuh hate mie ba sai kamin k'azafi ba"
Qasin cikin jan ido yace "in har nace bana sonka k'arya nake dan bansan ribar da zanci ba in'na tsaneka ba k'azafi nake maka ba Yarima abunda ka aikata ne na faɗa karka kuskura sake k'aryata ni"
wata dariyar Yarima ya sake yi ya shafa gashin kansa daya kwanta luf yace "I think ka manta wanene Yusuf bazan taɓa aikata abunda ka faɗa ba koda ga babbar mace ballantana ga k'aramar yarinya kamar Maryam pls tll mie nawa aka biya ka kayi min wannan k'azafin? nasan kai dan kwangila ne mai neman kuɗi ta kowace hanya kuma yima mutum irinna wannan k'azafin babbar hanyar samun kuɗine dan za'a baka million dollars go ahead tll mie waya saka wannan aikin?"
ya k'arasa maganar yana masa wani abu da hannu kamar mai wasa da maciji,
zauna Momi tayi dafe da kai dan bata jin akwai wani abun da zata iya cewa kota aikata dan Qasin ya riga ya chakuɗe komai iya ɓaci dai ranta ya gama yi,
Hajiya ma haka ta gama kamar yar kallo dan ta kasa furta komai gashi zuciyar ta tak'i yarda da abunda Qasin ya faɗa duk da tasan halin ɗan nata da yadda mutane ke yabonsa da mugun hali sai dai kuma ba ta taɓa jin anyi masa k'azafin zina ba,

qat.qat..qat... Yarima ya rik'ayi kamar mai kiran akuya yana faɗin "ina jinka faɗa min mana karkaji tsoro ni ba wani abun zai maka ba"
sai a lokacin Qasin yayi murmushi yace "wh d yuh thnk yuh are da har za biyani nayi maka k'azafi let mie tll yuh somethng yuh are nthng bt pest in trash ita da kanta Maryam ɗin ita ta faɗa"
waje Yarima yayi da ido kamar wadda yaji tsoro da gaske "OMG really?" sai kuma ya fashe da dariya ya shiga k'walama Mairo kiran da saida muryarsa ta cika falon,

amsawa tayi daga can cikin ɗakin sannan ta fito tayi tsaye bakin k'ofa tana kallonsu,
Suna haɗa ido da Yarima ta sakar masa Murmushi shima murmushin ya mayar mata ya mik'a mata hannu alamar tazo da gudu ta nufo downstairs tana dariya,
can idon ta suka kai ga fuskar Qasin ganin yadda yake harararta yasa data k'araso bata rik'a hannun Yarima ba ta rungume hannayen nata far'ar dake fuskantar ta gushe tayi k'asa da kanta,
mamaki ne ya cika Hajiya a ranta tana _...daman wannan ce yarinyar da Yusuf yake so k'arama..._
tashi Momi tayi tsaye ta nuna ma Mairo upstairs "ke wuce ɗakin..."
harta juya Yarima ya rik'ota "no Momi barta akwai abunda zan tambaye ta......"
hannu Qasin yasa ya buge hannun Yarima "ɗauke hannun ka daga jikinta"
dago hannun Yarima yayi ya kalla ya taɓe baki yace "are yuh jealous my friend kodai kai ma sonta kake shiyasa kuke wannan drama?"
wata mugunyar harara Qasin ya watsa masa "in sonta nake kai ka isa ka hanane da har zamu tsaya yin wata drama?"
dariya Yarima yayi ya ɗaga hannayensa sama "no ai ni ban isa na hana zuciyar ka faɗawa son yarinyar da ta kusa ta zama matar wani ba" cike da isa ya k'arasa maganar,
Qasin zai sake yin magana Hajiya ta kalli Mairo tace "ke Maryam faɗamin abunda Yarima yayi miki?"
ɗagowa Mairo tayi da kanta ta kalli Hajiya tace "ni bai min komai ba"
tsawa Qasin ya katsa mata "ke...! faɗi abunda Yarima yayi miki ranar daya fita dake bai dawo dake ba sai dare kika shigo jini na miki zuba da muka tambaye ki abunda ya faru kika ce yace duk kika faɗa sai ya kashe ki"
nan da nan tsoro ya bayyana a fuskar Mairo da k'arfi ta haɗeye yawu ta kalli Yarima idanuwanta kamar zasu zazzago.

*_©KHADEEJA CANDY_*
[11:27PM, 3/17/2017] Khadeeja Candy: ​*♡... MAIRO ...♡*

*BY*

*_KHADEEJA CANDY_*

Candynovel.wordpress.com

*43*

Murmushi Yarima yayi mata ya kaɗa mata kai alamar ta faɗa ganin haka yasa ta kalli Momi da Qasin sannan ta sake kallon Yarima cike da tsoro tace "bai min komai ba"
cikin tsawa Qasin yace duk baki faɗa ba saina miki shegen duka na kakkaryaki"
nan wani sabon tsoro ya sake shigar ta ta fashe da kuka tana faɗin "dan Allah yaya Qasin kayi hak'uri Wallahi yace duk na kuskura na fada sai ya kashe ni"
nan Qasin ya kaɗa kai ya kalli Hajiya yace "good yanzu kinji da bakinki ko?"
Kallon Yarima Hajiya tayi cike da mamaki da kuma sanyin jiki.
Murmushi yayi ya risina daidai tsaron Mairo ya soma mata magana a hankali "karki ji tsoro Maryam ki faɗa mishi duk abunda ya faru ranar kinji?"
lak'e kafaɗa tayi "a'a ba kace duk na faɗa ba zaka kashe ni"
Kai ya girgiza mata "no na fasa yanzu ma in kika faɗa harda chocolate zan siyasa miki na baki kuɗi"
shiru tayi alamar tunani can tace "da gaske ba zaka min komai ba?"
"bazan miki komai ba ai ni nace ki faɗa"
"thom rantse sauka rantse ba zaka min komai ba"
sai da ya yarda ya rantse mata sannan ta sake kallo shi tace "kadai san ba'a wasa da Allah ko ka dai riga ka rantse ba zaka min komai ba"
Sai da ya ɗaga mata kai sannan ta kalli Qasin murya k'asa² ta soma magana,

"Daman ranar da muka fita wani guri mukaje gurin buki daga can sai muka shiga mota zamuje wani gurin sai wasu suka cin mana da mota suka tsayar da mu duk fa suna ɗauke da bindigogi manya sun ɗauke wani mutum da sarka sai Yarima yaje yayi magana dasu har ya mari wadda aka ɗauren ya bugar masa baki ni kuma duk naji tsoro kwarai shine yace duk na faɗa sai ya kashe ni shine yace wani ya kawo ni gidan......"
kai Qasin ya girgiza "karya kike Maryam wannan ba shine kaɗai abunda ya faru ba"
rantsuwa ta shiga masa da kuka "wallahi yaya shine abunda ya faru ba karya nake ba kuma ka tambayi Yarima gashi nan"
matsowa yayi kusa da ita ya watsa mata mari da sauri ta nufi gurin Momi dafe da kuncin tana kuka,
Yarima ya kalle shi yace "ina tunani ta faɗa maka komai maye na wani dukanta kuma?"
yana nuna ta da yatsa yace "sai ta faɗamin dalilin zubar wannan jinin data shigo dashi"
"menstruation ne Qasin"
Momi ce ta bashi amsar tana share hawayen da suka zubo a fuskarta,
da sauri Qasin ya kalleta haka ya rik'a jin maganar tana masa yawo a k'wak'walwa nan da nan yaji jikin sa ba k'arfi gumi ya shiga karyo masa​

murmushi Yarima yayi ya rik'a wuyan rigar Qasin da hannu biu yana gyara masa kwalar rigar yace " ba haka ake takara ba Qasin da ace kai ɗan siyasa ne da ka faɗi zaɓe dan baka iya siyasa ba i really believed da ace kai lauya ne thom da kaji kunya a gaban kotuna da dama"
sake masa rigar yayi harya juya sai kuma ya juyo ya kalleshi yana tsotsar baki yace "u knw wht my frnd we are all in th sme game bt dffrnt roads wannan karon ka faɗi bt it is a deal btwn us last rubuta Ka aje I wsh yuh a very gud luk nxt time swt drm...."
da wani shu'umin murmushi ya k'arasa maganar ya sara masa sannan ya kalli Momi yace "ki kwana lafiya Momi"
yana kaiwa nan ya nufi k'ofa,
Kiran shi Momi ta shigayi idon ta sai zubar da k'wala suke, yi yayi kamar bai ji taba yayi ficewarsa.
nan Hajiya ta matso kusa da Qasin ta kalli k'wayar idonsa cikin sanyayyiyar murya tace "ko a mafarki ban taɓa tsammanin wannan ranar ba ban taɓa tunanin zaka iya yima ɗan'uwanka abunda kayi masa yanzu ba ina saka layin masu hankali da tunani duk abunda Yusuf yake faɗa a kanka ban taɓa yarda ba sai yau ka chanja rayuwa Qasin dan Yusuf ɗan'uwankane ba abokin gaba ba"
juyowa tayi gurin Momi idonta cike da k'wallah tace "kin ɓata wayonki da kike biyewa ɗanki kuka aikata abunda ban taɓa tunani ba"
dubawa tayi ta ɗauki jakarta harta fice Momi bata ce mata uffan ba sai hawaye take,

darker Qasin ya iya ɗaga kai ya kalli Momi "Momi dan Allah kibar kukan nan wallah-"
bai k'areba ta ɗaga mishi hannu tana hannun Mairo suka nufi upstairs.
Da ido ya bisu itama Mairo ta sako masa nata idon har suka shige,
Ajiyar zuciya ya sauke ya lumshe ido iya ɓacin rai ya san Momi tayi shi shi sam bai ɗauka abun haka yake ba kuma gashi har yanzu zuciyarsa tak'i yarda da abunda Mairo ta faɗa dan shi gani yake kamar biye wa ne tayi wata ajiyar zuciyar ya sake saukewa sannan ya buɗe idon ya nufi part ɗinsa jiki ba kwari,
duk wannan abun daya faru a idon Siraj ya faru dan yana tsaye a windon baya yan kallon su baby komai a I donsa sai kwallah dukawa yayi a gurin ya dafe kai,

sululu ya shiga parlor harya zauna bai lura da Mansura ba dan kwata² hankalinsa baya jikin shi "sai yanzu ka dawo ai daman nasan haka zai rik'a faruwa tunda ta dawo"
maganarta ce ta dawo dashi daga dogon tunanin daya tafi kallon ta yayi cike da jin haushi yace "gurin ta naje ko zaka hana ne?"
da sauri ta tashi tsaye "Qasin ni kake faɗawa wannan maganar?"
"an faɗa miki ke wace irin macce ce haka damuwa mijinki bata dameki ba sai kishi tirrr da halinki sai yanzu na soma yarda da wayansu kalamai da Momi take faɗa a kanki ba kida tunani wlh"
idon ta cike da hawaye tace
" *HAKA NAMIJI YAKE* banyi mamakin jin wannan kalmar daga bakinka ba daman nasan Momi ba sona take ba daman nasan-"
tassssssssss ya wanke mata fuska da mari yana nuna ta da yatsa yace "iskancinki ya tsaya kaina karki kuskura saka Momi a ciki dan ba sa'arki bace"
Baya² tayi tana kallon shi wani tsoro ne ya kamata wadda ko faɗa baya son mata yau gashi harda mari juyawa tayi da gudu ta shige ɗaki tana kuka,
faɗawa yayi zaune saman kujera ya lumshe ido "oh ya Rabbi" abunda ya furta kenan yana cizon baki,

'''*** * ** ***'''
cikin wani irin ɓacin Yarima ya isa gida yana sauke Hajiya ko motar bai fito ba ya nufi gidan sa,
cikin yan mintuna ya isa sakamakon gudun da yake ido a rufe yayi parking ya nufi k'ofar parlor da k'arfi ya tura k'ofar ya shiga yana wani irin numfashi da k'arfi.
zaunawa yayi yana murmushi mai cike da jin haushi yana kaɗa kai "lallai Qasin kana wasa ni zaka yima irin wannan siyasar hmmm yanzu ne ko zaka gane wanene ni dan saina aure ta"
wayarka ya ciro ya shiga danna neman number sannan ya danna callin bara daɗe tana ringing ba aka ɗauka "clock ka sameni gida gobe" haka kawai yace ya kashe wayar,
a hankali yaji an kai hannun ana taɓa shi tun daga k'eyar kansa har zuwa kirjinsa k'ara haɗe fuska yayi ya ɗaga idanuwansa sama yana faɗin "don't Zil am not in the mood......"

*_©KHADEEJA CANDY_*
[11:27PM, 3/17/2017] Khadeeja Candy: ​*♡... MAIRO ...♡*

*BY*

*_KHADEEJA CANDY_*

Candynovel.wordpress.com

*44*

Yi tayi kamar bata jishi ba ta cigaba da shafa shi,
Hannun ta ya fisgo da karfi ya yarfar ya tashi tsaye yace "nace miki am not in the mood bakida hankaline?"
Da sauri ta Kalleshi tsantsar ɓacin rai ta gani a tare dashi "Yarima mi yake damunka waya ɓata maka rai?"
Sama yayi da kansa "Zil miya kawo ki nan?"
"wannan wace irin magana ce ai kasan banada gurin zuwa sai nan wai wane irin ɓacin rai ne ya rufe maka ido haka Yarima Kaga yadda ka koma kuwa?"
Fuskarsa ya shafa yana yak'unar hanci "u are right Ni kaina nasan na chanja na daɗe banga ɓacin rai irin wannan ba ban taɓa sanin inason Maryam ba sai yau kuma kota halin yaya sai na aure ta koda sama da k'asa zasu haɗe"
cikin rashin fahimta tace "ban gane ba Yarima wata kake so ne?"
Murmushi yayi "yes wata kyakkyawar yarinya ce mai k'ananan shekaru kuma yar k'auyen"
Kai ta girgiza "kasan da ni kake faɗawa wannan maganar ko dai wani abun kasha?"
tana kare maganar ya wanke mata fuska da mari biu ya nuna ta da yatsa "karki kuskuren faɗa min kalmar da zata daɗamin ɓacin rai ɓace ki bani guri"
yanayin fuskanta naga ya chanja cikin ɓacin rai tace "babu inda zanje kawai ka fada min aure zaka yi ko me?"
gira ya ɗaga mata "yes aure zanyi tsoronki nake jine"
"tho ni kuma kayi yaya dani?"
"ai nasha faɗa miki Zil bazan taɓa iya aure ki ba maybe bazaki yarda ba har sai kinga matata a cikin gidan nan"
kwalla ne suka cika mata ido cikin muryar tausayi tace "amman ka ɓata min rayuwa Yarima ka raba ni da karatuna kasa na watsarda samarina"
murmusawa yayi ya taso yazo daf da ita ya ɗora hannayensa saman kafaɗarta yace "kina da matsala Zil mi yasa kike ɗora min wayannan laifukan koda yaushe ni ban lalata miki rayuwa ba kuɗine suka ja hanalinki kikaga zaki iya kum gwargwado na kyautata miki tunda na baki mota na kai ki makka na mallaka miki gida na cia miki account ɗin ki and what else do you need?"
Hannunsa ta rika hawaye nabin fuskanta tace "duk abunda ka zana yanzu ba sune a gabana ba aurenka nake so shine cikar burina"
Kai ya girgiza ya janye hannunsa "am so sorry Zil dear bazan iya yi miki wannan ba"
Cikin ɗaga murya tace "ba a haifi matar da zaka aura ba Yarima ba ayika dan ko wace mace ba sai ni kuskure ne kasa son wata a ciki zuciyar ka matukar ina raye"
Fashewa yayi da wata mahaukaciyar dariya yasa kafarsa ya kaɗe mata kafafu ta faɗi da karfi sai da kashinta ya amsa (yayi kara) sannan ya sake kai mata wani mugun shuri ba shiri ta saki ihu ya nuna ta da yatsa yace "ba'a faɗa min irin wannan maganar be careful next time ɓace min da gani"
da sauri tayi baya² ta shige ɗaki da kuka,
shi kuma ya zauna saman kujera yana cikama bakinsa iska
bai bar parlor ba sai kusan 3 dare bayan y gama sake² ya nufi bedroom,
zaune ya tararda Zil babu abunda take sai kuka tana rike da kunkurota kamar mai shirin haihuwa, yana kallonta yaja tsaki ya shiga toilet ya watsa ruwa ya fito
yana cikin saka kayan bachi yace "baci zanyi malama ko kiyi shiru koki fita kije gidan ubanki" ba shiri ta hade bakinta ta matse haka rage hasken wutar ɗakin yayi kwanciyarsa ya barta zaune.

*WASHE GARI..........*
8:34am Qasin ya shigo part ɗin Momi bai iya yin sallama ba saboda bugun gaban daya sami kansa dashi har ya isa dining room,
Nura da Usman suna zaune suna karyawa Momi kuma ta tisa abincin a gaba tana kallon wani guri
Mairo ce ta Kalleshi tace "yaya ina kwana?" da murmushi ya amsa mata "lafiya kalau Maryam an tashi lafiya?"
Kaita ɗaga mishi ta na dariya nan suma suka shiga gaida shi bayan ya amsa ya kalli Momi yace "Momi an tashi lafiya?"
ba tare data ɗago ba ta amsa mishi "lafiya kalau"
cikin sanyi jiki yace "dan Allah Momi kiyi hak'uri wallahi banyi-"
kasa k'arasa maganar yayi sakamakon ɗagowar da tayi ta ɗaga mishi hannu "karka kuskura fitar da kalma ko ɗaya daga bakin ka matuk'ar ni zaka furtawa ita kawai ka fita kabar parlor nan"
Nan da nan yanayinsa ya kara chanjawa bugun zuciyarsa ya karu kamar ya fasa kuka yace "dan Allah Momi karkiya fushi dani dan adam ne ni ajizi wallahi banyi hakan dan na ɓata miki rai ba dan Allah ki gafarce ni"
Momi fuska a ɗaure tace "bana fushi da kai tun har na iya amsa s
gaisuwarka kawai dai ka ɓace min da gani nace"
tsayar da cin abinci Usman yayi ya kalli ta yace "Momi lafiya?"
"babu ruwan ka kuma karka kuskura sa min baki a magana kaima inka kare ka tashi ka fice"
k'asa yayi da kansa shida Nura suna mamakin abunda yasa ran Momi ya ɓace haka,

tsaye Qasin yayi yana kallonta kamar ba dashi take maganar ba sai son yake yayi magana kuma ya kasa
ganin haka yasa Momi ta tashi ta bar mishi parlor,
Jinginawa yayi da ginin dake gurin ya dafe kai yana cizon baki ya daɗe a haka sannan shima ya juya ya fice,
Nura da Usman ma suna ganin ya fita suka tashi suma suka fice aka bar Mairo ita kaɗai sai cin abincin ta take tana yan wake²,

baifi 5 minutes da fitar su ba Siraj ya shigo fuskarsa babu yabo ba fallasa sallamar ma ciki² yayi ta Mairo ta amsa masa ta kaɗa kai "taf lallai ma kai wannan yaron sai yanzu kaga damar tashi har kowa ya gama breakfast? Kayi olo ma dan abincin ya k'are"
Murmushi ya ɗan yi "aini ba abinci zan ci ba"
gyara zama tayi "saboda me?"
shiru ya ɗanyi sannan yace "a zumi nakeyi"
taɓe baki tayi "thom kun zama ɗaya kai da Momi kenan"
"itama a zumin take ne?" ya tambaya saida ta girgiza kai sannan ta bashi amsa "a a bata dai ci abinci ba"
"miyasa?"
"Nima ban sani ba kila bata da lafiya dan tun jiya kuka take ko bachi bata yi ba"
da a sauri ya nufi upstairs jikinshi na rawa ya tura k'ofar ɗakin Momi,
da sallama ya shiga ta amsa masa da muryar kuka "wa'alaikassalam"
kusa da ita ya zauna yana faɗin" Momi kuka kike yi ne?"
bata iya ce masa a'a tunda yaga hawaye a idonta kawai sai kawarda fuska,
Hannun ta ya rik'a "dan Allah Momi kibar kukan nan Maryam tace tun jiya take kukan nan"
hannu tasa ta share hawayen tana faɗin "dole inyi kuka Siraj jiya Qasin a gaban Hajiya ya aibanta Yarima ɗan ta kwara ɗaya ɗan da tafi kowa sonsa ban taba ganin bacin ranta ba irin na na jiya wani abu bai taa haɗa ni da itaba sai jiya kuma nasan zata rika ɗaukar na hana ma ɗanta Maryam da nasan rikonta haka zai zamar min daban ɗauko ta ba tun farko"
Ajiyar zuciya Siraj ya sauke yace "har gobe Momi bazan basa faɗa miki ba Yarima bai dace da Maryam ba dan ba mutumin kwarai bane taya za a ɗauki karamar yarinya kamar Maryam a aura masa kada ki sake ɓata ranki akan wannan hukuncen da kika yi dan ni banga wata matsala ba"
Momi tace "akwai matsala Siraj dan yanzu ganin suke na hana Yarima auren Maryam na aura mata wani"
tashi yayi tsaye ya kalleta yace "Momi kina son Yarima sosai da badan wani abuba da nace kinfi sonshi sama da mu da muke yayanki"
Lumshe ido tayi ta sauke ajiyat zuciya shi kuma yasa hannayensa aljihu ya fice,

''' *** *** *** '''
duk inda yabi gaishe shi ake cikin girmamawa har ya isa parlor Hajiya zaune ya tararda ita tana cin apple wata baiwa na matsa mata kafafu Hajiya na ganinshi ta janye kafafun nata tayi mata alama data ta fice cikin sauri ta tashi ta gaida Yarima ta fice,
Karasowa yayi kusa da ita ya zauna ya ɗauki apple ɗin ya kai baki ganin bai yi mata magana ba yasa ta kalleshi yadda taga fuskarsa a ɗaure tasan akwai wata a kasa saida ta ɗanyi gyaran murya sannan tace "ɓacin ran jiya ne ko kuma na yau dn nasan Mai martaba yayi maka magana?"
ba tare da ya kalleta ba yace "saboda mi Mai martaba zaisa min baki a neman aure?"
"saboda bata dace da kaiba haba Yusuf koda basu wulakanta kaba ai kaima kasan bai dace ka auri wannan yarinyar ba ga yayan manyan mutane masu aji masu kyau wasu m har sun nuna suna sonka amman ka kai kank gunda za a wulakanta ka karama da ba ayi auren ba dan Mai martaba ya nuna baya so kamar yadda nima bana goyon baya"
kallonta yayi yana murmushi yace "nima zuciya tace take so ba ni ba kuma aure sai anyi shi no matter what dan haka kuso abunda ɗan ku yake so kawai"
fuskantar a haɗe ta kalleshi "saboda baka da zuciya ko shiyasa har yanzun kake son ta ina mamaki ka Yusuf kwata² ka chanja wai mi ka gani a jikin yarinyar nan ne.....?"
kamin ya bata amsa wayarsa tayi ringing ciro ta yayi ya danna picking ya kara a kunne,
banji mi akace masa ba murmushi kawai naga yayi yace "good job an samoshi kenan.........bani minti biyar"
da kallo Hajiya ta bishi har ya tashi tsaye sannan tace "waya kira ka a waya mi kake kokarin aikatawa?"
kallonta yayi fuskarsa ɗauke da far'ah ya rika hannunta yace "babu komai Ummi na ɗan ki ba zai aikata wani mummunan abu ba just trust him okey?"
bai jira cewarta ba ya sakarma hannun nata kiss ya fice yana murmushi.

*_©KHADEEJA CANDY_*
[11:27PM, 3/17/2017] Khadeeja Candy: ​*♡... MAIRO ...♡*

*BY*

*_KHADEEJA CANDY_*

Candynovel.wordpress.com

*45*

Haka Momi ta share kwana da kwanaki bata kula Qasin iyakarta dashi gaisuwa babu hanyar da bai biba na ganin ta dawo normal amman abun yaci tura dole tasa ya hakura ya kyaleta,

Wata ranar Asabar Momi na zaune parlor tana tunane² Siraj ya shigo guri ya samu kusa da ita ya zauna kasan carpet cike da ladabi ya kalleta yace "Momi wai miyasa yasa ba zaki ɗaga ma ya Qasin kafa ba Momi wadda fa kike abun nan danshi baima san kinayi ba dan me zaki rika fushi da ɗanki akan ɗan wata Momi"

Ajiyar zuciya Momi ta sauke irin nasu na manya sannan ta ɗan gyara zamata tace "bana daga cikin iyayen da suke fushi da y'ay'ayensu dan fushi iyaye yana tare da fushi Allah ko kaɗan ni bana fushi da Qasin kawai dai inason nuna masa kuskuren daya aikata babbane gaba karya sake aikata shi kuma wani gefen ma bana ganin laifinsa laifin kaina nake gani dana ɗauko Maryam riko har Yarima ya ganta ya nuna yana so kuma na hana shi ita wannan abun shine ya tsaya min a rai shiyasa yanxu na yanke shawarar ma yarda ita gurin Gwaggonta kusa da mijinta"

kallon rashin fahimta Siraj yayi mata "kina nufi ki ma yarda Maryam kauye kenan?"
"haka nake nufi kuma hakan shine kwanciyar hankali"
Amsar Da Momi ta bashi kenan a takaice

"amman Momi naga ai abunda na faru ya riga ya faru kuma kin riga kince yarinyar nan karatu zatayi mijinta yayi Na'am itama tana so Gwaggo ta amince dan me kuma yanzu zaki ce ki maida ta itama ai ba zata jidadi ba"

Motsa baki Momi tayi "ma yarda ita ya zama dole a gareni kodan suma na sama musu sukuni"
"ki sama musu sukuni su suwa?" Siraj ya tambaya

Momi saida ta nisa sannan tace "satin daya wuce Gwaggo ta kirani a wayar haruna tace mun wasu daga birni zunzo neman auren Maryam an faɗa musu tana da miji shine suka samu halilu sukace zasu bashi kuɗi mai yawa ya sake ta shi kuma ya k'i Aminta babu irin rarrashin da basu yi masa ba yak'i sun jera kwana da kwanaki suna zuwa har suka ce masa matukar bai rabu da itaba komai zai iya faruwa dashi"

keɓe baki Siraj yayi "ba kowa sai Yarima dan babu wadda zai aikata haka sai shi dan sheɗan kaɗa masa ganga yake yana rawa"

Momi tace "hakan yasa nake son maida ta kusa da mijin ta kar wani abun ya shiga kuma adawo ana ganin lafin juna"

"babu wani ganin laifi Momi kawai ki barta tayi karantunta shi kuma darasi yake son a koya masa"

kai Momi ta girgiza "a'a bana son wata fitina wacce na sha yanzu ta ishe ni kabar shi yayi duk abunda yake son aikatawa"

Da sauri ya kalleta fuskarsa da ayar tambaya "Momi wht are yhu tlkng abt abarshi ya kashe aure akan wani dalili na shi na banza?"

"abunda nayi ban kyauta masa ba Siraj na hana masa aurenta dan haka yanzu bazan hana shi rawar gaban hantsi ba na ganin ya kwatarwa zuciyarsa abunda take so"

Sai a lokacin idanuwan Momi suka kawo kwallah magana ta soma yi cikin muryarsu ta manya "kai Da yayanka kun kasa fahimta ta akan Yarima da mahaifiyarsa Siraj yau inason faɗa maka wani abu da baka san da shiba dan ina ganin har yanzu baka wayi dangantakar dake tsakaninmu ba..." lutse baki yayi ya tari numfashinta "na sani Momi bana nufin ɓata miki rai dan Allah karki zubar da hawayenki akan wannan maganar"

Momi ba tare da ta kalleshi ba tace "mu biyu kawai mahaifiyarmu ta haifa saida aka fara haihuwar Hajiya da shekara 6 sannan aka haife ni ina da shekara 15 mahaifiyarmu ta kwanta ciyon ajali a lokacin Hajiya tana gidan aure ni naje na kirata mukazo gaban gadon mahaifiyarmu muka zauna nan mahaifiyata ta rika hannuna tace nayi ma Hajiya biyayya na ɗauketa kamar uwa na guji ɓacin ranta duk kuma abunda zai sata farin ciki na tabbatar da na yi shi na sota kamar yadda nake son kaina sannan ta ɗauko hannun Hajiya ta ɗora saman hannuna tana faɗin ga kanwar ki nan ki riketa ki zamo mata uwa karkiyi mata abunda zai sata bakin ciki ki sota kamar yadda kike son kanki wannan itace wasiyar da mahaifiyarmu ta bar mana bayan rasuwarta Hajiya ta mayar dani gidan ta da zama wato gidan mahaifin Yarima tunda naje gidan bata taɓa koda hararata ba balle ta min tsawa bata taɓa ɓata min rai ba har ta aurardani ga mahaifinku lokaci ɗaya muka haihu da ita ita ta reni Qasin duk da irin son da take ma Yarima bai rufe mata ido ta nuna Qasin ba ɗanta bane karara take nunwa Yarima kiyayya ta karɓe abun hannunsa ta baiwa Qasin ko ta dake shi akan Qasin koda shine da gaskiyasa har kuka girma kuka kawo yanzu kuke ganin inayin abunda bai dace ba alhalin ni nasan abunda yake nan uwa ɗaya uba ɗaya ba wasa bane koda mahaifiyarmu bata mana wannan wasiyar ba......"

da kuka ta karasa maganar ta lumshe ido alamar tunawa da bacin cikin baya

Lakas jikin Siraj yayi sanyi a hankali ya sunkuyarda kansa cike da tausayi

Sun daɗe a haka parlor yayi tsit kamar ba kowa Momi dai in bada sharar hawaye babu abunda take,

Ganin hakan yasa dole Qasin ya ɗaga lalulen parlor ya shigo dan babu abunda ya tsana kamar zubar hawayen Momi.

*_©KHADEEJA CANDY_*
[11:27PM, 3/17/2017] Khadeeja Candy: ​*♡... MAIRO ...♡*

*BY*

*_KHADEEJA CANDY_*

Candynovel.wordpress.com

*46*

A kasan carpet shima ya zauna gefenta na dama yana faɗin "na fahimci dalilinki Momi ina neman yafiyarki akan abunda nayi"

"na yafe maka Allah ya yafe mana gaba ɗaya"
Shine abunda Momi ta furta suka amsa da amin

Sannan ta sake kallonsa tace "ka shirya gobe zamuje kauye"

Kai kawai ya ɗaga mata ya amsa da thom ya tashi ya fice

'''*** *** ***'''
Guraren biyar da rabi Mairo ta shigo ɗakin Momi kinik kinik da fuska kamar ta fasa kuka koda ta shigo ta tararda Momi na waya hakan yasa tayi kwance saman gado tana kallon fuskar Momi

Momi na sauke wayar ta kalleta "ke lafiya kike wani kumbure²?"

Tashi tayi zaune "Momi wai Siraj yace min wai kauye zaki maidani"

Shiru Momi ta ɗanyi kamin tace "Gwaggo ce tace a dawo dake amman...."

Mairo bata jira Momi ta karasa maganar ba ta faɗi kasan carpet ta shiga murje² tana kuka

Lallashinta Momi ta shigayi tana bata hakuri faifai taki yin shiru saima karawa take ganin haka yasa Momi ta tashi ta ɗauko wayar radio ta shiga duka ta dashi

Aiko nan ta soma kukan gwarai sai ihu take iya karfinta tana faɗin "na daina Momi dan Allah kiyi hakuri"

Momi bata saurara mata ba saida Siraj ya shigo ya karɓe bulalar ransa a ɓace yace "haba Momi ya zaki rika mata irin wannan dukan da wayar loba?"

Cikinsa Momi tayi da matsifa "an daketa ai kai ka jawo a daketa ɗin dan ance za mayar da ita kauye ta rika yima mutane kuka ba daga kauyen ta fito ba da rainin hankali tsaye ya tada ita yana faďin "amman Momi ai kinsan ta riga ta saba da nan ba jindaďin zama can zatayi ba"

Momi tace "ko taso ko karta so saina maidata inna kai ta karta zauna"

"tho amman Momi ai ba haka ya kamata kiyi mata ba lalla6ata ya kamats kiyi"

Kofa Momi ta nuna masa "kai fita ka bani guri"

Ba musu ya juya ya fice nan nan ta kalli Mairo ta nunata da yatsa "ke kuma in bakiyi min shiru ba yanzu saina dada miki wani dokan"

Da gudu ta tashi ta fice
Ranar Mairo wuni tayi kuka har dare Momi kan ido kawai ta samata

Washe gari ma daga inda ta tsaya da kukan ta tisa kamar wata karamar yarinya Momi dai bata bi ta kanta ba duk suna downstairs suna breakfast

Daf da zasu gama Siraj ya shigo bayan ya gaida Momi su Nura da Usman suka gaidashi yana kokarin zaunawa ya kalli kujerar Mairo yace "ina Maryam bata tashi bane?"

"ta tashi tana can ta tisa kukan daga inda ta tsaya ba shi kake son tayi ba?"

Momi ce ta bashi amsa tana ɗan hararasa
shi kuma yayi murmushi ya tashi ya nufi upstairs

Be dade sosai ba ya fito ɗakin Mairo na gaba yana bayanta murmushi shinfiɗe a fuskarta saidai ta ɗan kunbura saboda kukan da tayi

Kallon mamaki Momi ta ringa yi musu har suka kawo dining sannan ta kalli Siraj tace "me kace mata Siraj?"

Kallon Mairo yayi yana dariya "Momi kamar ya me nace mata me zan mata?"

"hmmm" Momi ta taɓe baki "ai kodan kai saina maida yarinyar dan kaima kanka sai ka hore mata kunne"

Fashewa yayi da dariya "hore mata kunne Momi akan mi mema akayi da har zaisa na hore mata kunne?"

Turo baki Mairo tayi "ke Momi kin cika matsala inda kuma kuka ga inayi kice kuma wani abu"

Tashi Momi tayi tana faɗin "kyaji dashi yau ne dai kawai kike garin nan anjima kaɗa kauye zakije"

A maimakon tayi kuka kota ɓata fuska sai kawai ta kalli Siraj ta fashe d dariya "naji Momi ai in a son kauyen"

Kallon Siraj Momi tayi shima ita yake kallo yana kokarin ɓuye murmushin dake son fito masa sai faman kware ido yake alamar marar gaskiya

Uffan Momi bata ce masa ba kwafa kawai tayi ta nufi upstairs

*@2:32pm*
Suka kama hanya Qasin ke driving Mairo na front seat Momi kuma na gidan baya

Akai² Mairo takan kalli Qasin tayi murmushi shi kuwa tuni ya tsargu daman ba son tafiyar yake ba duk yabi ya wani ɓata rai wannan karon tana kallonshi ya watsa mata harara

Taɓe baki Mairo tayi ta ɗan ja tsaki "mtw dan nan kalle ka zaka Harare ni"

Kasa² take maganar tana rama harar da yayi mata

Har yayi kamar yayi mata magana sai sai wata zuciyar ta hanashi wai a cewarsa matar aure ce

Bayan kamar minti 30 ta sake kallonshi wannan karon wsta magana ce tazo mata
"yaya wai mi yasa matarka bata dafa maka abunci saidai kaci na Momi koka siya kuma kullum ta rika bachi inna shiga part ɗinka ta rika hararata tana jan tsaki ni ko mi nayi mata oho"

Faduwa gabansa yayi sanin Momi na nan karta sa baki dan babu abunda ya tsana kamar maganar Mansura

Ta madubin gaba ya kalli Momi itama ta nan take kallonshi suna haɗa ido yayi sauri kawar da nashi idon
Bai iya cewa Mairo komai ba har suka isa

*☆ ☆ ☆*
Gwaggo tayi mamakin ganin su sosai dan sunyi mata tafiyar ba zata

Bayan sun ɗan huta Gwaggo ta kawo musu abinci Momi ce taja abincin tana ci daman shi Qasin al'adarsa ce duk akaje kauyen ba cin abinci yake ba sai dai ruwa ko k'walama Mairo kuma tuni ta nufi gidan tsoho

Bayan Momi ta kare ta sha ruwa ta wanke hannu tana hamdala

Murmushi Gwaggo tayi tace "nace Allah dai yasa lafiya naga kun mana zuwam rana tsaka kuma har da tufafin Mairo?"

"lafiya kalau gani nayi ya kamata a kawo ta taga gida tunda yanzu tana da aure kar a tauye ma mijin ta hakki"
Momi ta karasa tana gyatsa

Dariya Gwaggo tayi "a gaskiya kin kyauta ana son haka shekaran jiya ma halilu yake cewa shi wannan aure ya zame masa ala k'ak'ai matar daya aura tana gabas yana yamma amman an bi an takura shi"

Momi tayi murmushi "tho ya hutarda ranshi yanzu gata nan mun kawo sai ya gina ɗaki ya sakata ya huta"

Zunɗen baki Gwaggo tayi "ta ina zai iya gina ɗakin wannan ragon namiji ni wallahi sai yanzu nake jin haushi aura masa Mairo da akayi mutum ba sana ar komai sai zaman kashe wando"

Momi ta rike baki "to ai nema masa za'ayi ba za a kyale shi haka ba tunda yanzu har ya soma tasarma iyali"

Gwaggo ta taɓe baki "to wa zai nema masa shi ba zaije y nemaba si kace ba namiji ba ke nifa duk inda abun nan yakai ya kaimin na halilu kullum da anyi masa magana sai yace shi karatu yake son yi shidai ya cigaba da karatu koda uban me zaiyi karatun oho"

Sai a lokacin Qasin ya kalleta yayi dariya dan tunda suje maganar uffan baice ba har Gwaggo ta gama zaginsa da ɗebe masa albarka

'''*** *** *** '''
Sai kusan biyar na yamma su Momi suka kamo hanyar gida
har bakin mota Mairo ta rako su tana ɗaga musu hannu sosai Momi tayi mamakin ganin bata yi kuka ba saima murmushi da take kamar bata damu ba

Momi dai kallonta kawai take har suka ɓace

Juyowa Mairo tayi kamar kazar da kwai ya fashewa tana rike da hannun Gwaggo suka shiga gida

Koda suka zauna kwalla sun cika ma Mairo ido duk ta wani marairaice fuska cikin muryar tausayi ta kalli Gwaggo tace "Gwaggo kinga sun tafi sun barni"

Gwaggo ta janyota "tho ai in kika kwana biu sai ki je can kuma kinga ai kara kina zuwa ganin gida ko?"

"a a Gwaggo tace nan zata bar ni ba zan sake zuwa birni ba"

Yanayin fuskar Gwaggo naga ya chanja "tho me kika mata?"

Wannan karon har hawayen sun soma mata zuba "nima ban sani ba nidai haka kawai ta mayar dani kuma nata rokonta ta barni taki harda dukana tayi amman dai Siraj yace min kar nayi kuka gobe zai zo yaje dani"

Gwaggo ta shafa kanta "kedai faɗamin gaskiya yar Gwaggo kodai wani abun kikayi mata ne? "

ɗan kare ta ɗauka tana zanawa a kasa kanta na saman cinyoyin Gwaggo tace "wallahi ban mata komai ba ni duk ma na daina wannan rashin jin tunda naje can sai faman aiki da nake"

Gwaggo tace "tho me zai sa tayi miki haka ni daman zuwan nan naku ban yarda dashi ba dan ruwa baya tsami banza"

Cikin muryar kuka Mairo tace "kila dan taga suna da kuɗi ne sunga ina son zama gurin su dan ko wannan matar Qasin ɗin inna shiga gurinta sai ta rika hararana tana jamin tsaki shima yaya Qasin naga yana yimin bakin rai kuma ban masa komai ba Siraj ne kawai yake sake min fuska ina jindaɗi"

Shiru Gwaggo tayi alamar tunani kana ganin yanayin fuskarta kasan ranta ya ɓace.

*_©KHADEEJA CANDY_*
[11:27PM, 3/17/2017] Khadeeja Candy: ​*♡... MAIRO ...♡*

*BY*

*_KHADEEJA CANDY_*

Candynovel.wordpress.com

*_JINJINAR BAN GIRMA A GAREKI RUFAIDA OMAR_*😘👍🏻

*NA YABA DA SOYAYYARKI MARYAM ABDULKADIR (MAMAN AFFAN)*😍

*WANNAN SHAFIN NAKI NE DR. ZULAIHAT ISA (AUNTY NA)*😘

*47*

"Assalamu alaikum Assalamu alaikum Assalamu alaikum"
Halilu ne yake sallamar tun daga kan Gwaggo har Mairo aka rasa mai amsa masa.
Mairo dai in banda harara babu abunda take masa.
"wa'alaikassalam" saida ya kusa k'arasowa sannan Gwaggo ta amsa masa can k'asan mak'oshinta.
jiki ba k'wari ya zauna saman tabarmar ganin marhabar da Mairo take masa da harara ga kuma yanayin yadda Gwaggo ta amsa masa sallamar duk sai yasashi jin ba daɗi.
haka ya danne abunda ke zuciyarsa ya kalli Mairo da far'ah
"Yan birni saukar yaushe ?"
"D'azu ɗazun nan Hajiya ta kawota har ma take tambayarka"
Gwaggo ce ta bashi amsar bayan ta nisa
murmushi yayi
"Ayyah aiko ban jidaɗin da suka wuce ban samu ganinsu ba dan naso ganin Siraj sosai"
"Ai ba dashi aka zo ba da Ya Qasin aka zo kuma basu daɗe ba suka wuce"
Wannan karon Mairo ce ta amsa masa.
"Amman dai lafiya suka kawoki yanzu ko anfasa karatun ne ?".
Gwaggo ta taɓe baki "Toh ban sani ba amman dai sun kawota ne wai kar a tauye maka hakki"
Murmushin jindaɗi yayi "Aiko Hajiya ta kyauta kuma tayi abunda ya dace. daman jiya Tsohon yake cewa ya kamata a dawo da ita gida abar maganar karatun nan."
"Toh gata nan an kawo sai ta maka maganin da zatayi maka haka kawai ka ɓata rayuwarka kana son ɓata mata nata rayuwar." kallon Gwaggo yayi fuskarsa na nuna ɓacin ran dake zuciyar "Haba Gwaggo wannan wace irin magana ce haka.?"
Sake taɓe baki tayi a karo na biu "Eh mana toh in bashi ba miye na wani damuwa da a kawo ta alhalin ko ɗakin da zaka sakata baka ginaba gaka babu sana'ar yi barre aiki kai dai kamar ba namiji ba!"
a hankali ya sauke ajiyar zuciya "Gwaggo kada rashin aikina ya dame ki munyi magana da wani zanje neja zai nemin aiki kuma zai mayar dani makaranta yanzu haka ma na haɗa kuɗin mota nan da kwana biu zanje In'sha Allah"
cikin sanyayyiyar murya yake maganar cike da ladabi.
Gwaggo ta nisa "Toh Allah yasa ya kuma taimaka ai haka nake so jin"
Murmushin jindaɗi yayi ya amsa da 'amin' tare da tashi ya nufi k'ofar ɗakinsa.
daf da zai shiga Mairo ta tashi zaune ta kalleshi "Halilu zaka je dani ko ?"
juyowa yayi bakinsa ďauke da dariya
"A'a Mairo kinga nema zai kaini ba zama ba sai naga yadda abun zai kasance tukuna."
Gwaggo taja mata kunne "Wai mai yasa kike da shegen son yawo ne ?"
"Ni wallahi bana son zama a k'auyen nan."
cewar mairo tana wani yak'unar fuska kamar wacce taga wani abun k'azanta.
Murmushi. kawai halilu yayi ya shige ɗakinsa.
Gwaggo ma dariya tayi "Ai zama k'auye ya kamaki tun da nan kika tashi kuma nan kikayi aure. sai hak'uri"
ɓata fuska tayi ta sake komawa saman k'afafun Gwaggo kamar ta fasa kuka.

Washe gari k'iri k'iri Mairo tak'i ta ci dumame dak'er Gwaggo ta lallaɓata ta samu ta sha kunu da rana ma k'in cin abinci tayi haka ta wuni har dare wai ita ba zata ci tuwon dawa ba tuwon masara da Gwaggo ta tuk'a mata ma k'in cin tayi saida dare Halilu ya shigo mata da agashe mai tumatir da albasa.
da murna ta karɓa tayi zaman kirki taci tasha ruwa sannan ta kwanta.
Cikin kwana biu duk tabi ta chanja sai rama da take fama da ita na rashin cin abinci da kuma tunanin birni kullum cikin kuka. take da mafarkin ranar da Siraj zaizo yaje da ita,
Ranar wata laraba Gwaggo ta na zaune tsakar gida tana aiki Mairo ta fito daga cikin ɗaki ta zauna fuskarta a kunbure da a'lamar kuka tayi.
Kalllo ɗaya Gwaggo tayi mata ta ɗauke kai "Allah yayi miki saukin wannan halin rayuwa da kika saka kanki ciki Mairo wannan abu dame yayi kama daga zuwa birni shi kenan kin mayarda abu armun-azi'mun kin are kin yafe ke sai can ai toh k'ara da aka dawo dakw yanzu dan in kika kara jimawa k'ila koni bazaki so gani ba."
idonta ne suka k'ara cika da kwallah. da muryar kuka ta soma magana "Gwaggo nan fa babu daɗin zama kuma tunda na dawo babu halin na fita sai ace naje yawo Tsoho ya rik'a min faɗa ko k'awayene sun daina zuwa guna..."
Gwaggo ta rik'e baki "Oh ni yau kiji mani 'ya toh ba aurene dake yanzun ba yaya zamu saka miki ido kina yawo yanzu fa ba kamar da bane ke MATAR AURE ce yanzu"
fashewa tayi da kuka "har ga Allah ni bana son auren na dan kun mayardani k'ank'annu kuke min haka"
"Uhmmm. inma dan zuwanki birni ne yasa kike wannan abun gara tun wuri ki shafawa kanki lafiya ko babu komai dai kinga bason suke ki zauna a tare dasu ba."
cewar Gwaggo,
uffan Mairo bata sake cewa ba in banda kuka da ta shiga rusawa.
fitowa Halilu yayi daga cikin ɗakinsa ya nufo Gwaggo yana faɗin "Gwaggo ina ganin tafiya ta gobe ne in sha Allah"
wani irin faɗuwa gaban Mairo yayi zuciyar ta ta buga da k'arfi nan da nan hawayen dake mata zuba suka tsaya ta ɗaga kai tana kallon Halilu,
Gwaggo ta kalleshi "Gobe gobe Halilu ?"
"Eh kinsan nace miki ranar Alhamis za muje da naso ɗaga tafiyar toh wadanda zamuje tare ne suka k'i"
Gwaggo na dama garin dake gabanta tace "Shin wai yau wace ranace ni har Alhamis ɗin tazo ne ?"
Halilu yayi dariya "Eh mana Gwaggo gobe ne Alhamis fa ko kin manta yau Laraba kinsan shekanjiya ne matar Garba ha haihu yau kwana huɗu"
kai Gwaggo ta girgiza "Haka ne fa oh duniyar nan lokaci yana gudu dubi kaga haihuwar nan wai har an kwana huɗu Allah dai yasa mu cika da imani kwankinmu ne ke tafiya maganar nan yaushe muka yi ta amman wai har Alhamis ɗin tazo"
"Wallahi kuwa Gwaggo ai mai hankaline yasan wannan ga tsadar rayuwa saidai ace Alhamdulillahi"
yayi maganar yayin da yake k'ok'arin risinawa kusa da ita,
Gwaggo taja damun ta aje gefe ta sake kallon sa "Wai tafiyar nan dai babu wani abu ko nidai sai na rik'a ba daɗi karfa garin neman gira a rasa ido karka jefa kanka cikin wani halin daman dan neman abunyi, dama ace bakiyi nisa da muba ko nan kusa ai ka samu wani abun amman qce har neja"
Murmushi yayi "Babu komai Gwaggo sai alkhari kedai kiyi ta min addu'ah wannan abun da kikeji ba komai bane sai sabo in sha Allahu za ayi nasara."
Ajiyar zuciya ta sauke "Toh Allah yasa addu'ah ai kullum ciki yi muku ita nake Allah ya kaika lafiya ya tsare amman naso tafiyar nan ba yanzu ne da sai na karɓi a dashe na saina baka ka k'ara"
"Babu komai Gwaggo addu'ah kin ya fiye min komai inada yan kuɗin da zasu ishe ni kwana biu kuma kinga in naje ba zama zanyi ba aiki zamu rik'a yi"
"Toh Allah ya taimaka yasa ayi sa'ah ya tsare min kai ya raya ka ya cika maka burinka"
sosai ya jidaɗi addu'ah da Gwaggo tayi masa bayan ya amsa da 'amin' ya tashi tsaye yana faɗin "Bari na shiga gari na ɗanyi bankwana da wasu"
kai Gwaggo ta ɗaga masa "Toh aikan yafi Allah dai ya tsare."
tafiya ya somayi har yakai k'ofa Mairo ta kirashi
"Halilu..."
"Na'am"
juyowa yayi ya kalleta itama shi take kallo bakinta yayi mata nauyi ta kasa magana. ganin hakan yasa shi tambaya ta "Minene Mairo ko wani abun kike son a siyo miki ne ?"
kai ta girgiza alamar a'a "Toh minene faɗi naji ?"
cika idonta sukayi da kwallah "Halilu dan Allah karkaje neja ɗin nan kaji ko kuma kaje dani"
"Saboda mi ?" Gwaggo ta tambaya "Nidai bana son yaje bana so kawai"
cikin muryar tausayi ta bata amsar, hawayen dake idonta suka soma gudana.
dawowa Halilu yayi ya risina daidai gun da take zauna ya kalleta cikin muryar lallashi ya soma magana "Kar dai ace tafiya tace ta saki kuka ai ba daɗewa zanyi ba zan dawo dole naje dake dan haka kibar k'ararda hawayenki kinji ?"
"A'a nidai bana so kawai kar kaje bana son kaje ka bari har wani lokacin"
wannan karon muryarta na rawa tayi maganar.
iskan dake bakinsa ya busar sai zuciyar ta soma masa ba daɗi "Haba Mairo karfafa min gwuiwa ya kamata kiyi fa kinga nan ina zauna babu wani abunda zanyi amman can zan samu aikin yi nayi kuɗi na gina miki gida mai a birni da zaki zauna na rika baki kwai da daɗi kina ci amman kinga inna zauna nan haka zamuyi ta zama babu wani cigaba yanzu fa dana dawo birni zamu koma ko baki so ?"
"Ina so. mana"
Murmushi yayi "Yauwa toh ki zake ranki ki rik'a min addu'ah kinji ki daina kuka ?"
share hawayen tayi ta ɗaga mishi kai "Toh na daina amman dai in kaje karka daɗe"
"Ai bazan daɗe ba zan dawo na ɗaukeki"
Gwaggo daga gun da take tayi dariya tace "Oh Mairo kodai ya saki a jaka ne ya tafi dake ?"
fashewa tayi da dariya "Haba Gwaggo sai kace wata yar tsuntsuwa sai dai in Tsoho za asaka aje dashi"
wannan karon har Halilu saidai yayi dariya.
Gwaggo tasha mur "Wai Mairo mi yasa kika raina Tsoho ne naga dai ba sa'an ki bane ai ?"
"Amman dai kakana ne ko sai abarni dashi shima ai haka yake min"
"Toh shi kenan aiko zamu saka k'afar waddo ɗaya dake"
kai kawai Halilu ya kaɗa ya tashi ya fice.

Story continues below



*_©KHADEEJA CANDY_*
[11:27PM, 3/17/2017] Khadeeja Candy: *♡... MAIRO ...♡*

*BY*

*_KHADEEJA CANDY_*
Candynovel.wordpress.com

*48*

Tunda Halilu ya dawo, sallar A'suba ya shiga kintsa sauran kayansa.
daf da zai gama Gwaggo ta shigo masa da kari "Halilu ana nan nata shirin ?"
juyowa yayi bayan ya aje jakarsa gefe. "Eh wallahi har kin tashi Gwaggo ?"
"Eh tunda nayi sallah na shiga haɗa maka abun kari naji kace da wuri zaka wuce."
kunun data aje gaban shi ya buɗe ya shiga motsawa "Toh ai kara tafiyar safen Gwaggo tun kinga garin nesa ne kara muje da wuri"
Ajiyar zuciya kawai Gwaggo ta sauke ta tsora masa ido.
biu da ludayi yayi ya aje Gwaggo ta kalleshi "Ba dai ka k'oshi ba ?"
"Gwaggo bazan iya sha da yawa ba ki cikina a ɗaure yake wannan ma dan kar naje babu komai a ciki nane"
Gwaggo ta tura masa dumame "Toh kaci tuwon mana ai bakaje da yunwa ba dai"
"Bazan iya ci ba Gwaggo inna ji yunwa zan siye wani abun ko a hanya ne"
"Toh Allah ya sauwake ko ni haka nake in zanyi tafiya bana iya cin abincin kirki"
kuɗi dake ɗaure a gefen zaninta ta ciro ta mika masa "Ga wannan jiya na aro gun Faɗime ka ɗan k'ara"
kamar bazai k'arɓa sai kuma yasa hannun ya karba yana godiya "Allah ya saka da Alheri amman dama baki wahalar da kanki ba Gwaggo na faɗa miki inada yan kuɗin da zasu ishe ni." "Babu komai Halilu in banyi maka ba wa zaiyi maka Allah dai ya raya mani kai ya tsare ya baka abunda kake buk'ata."
"Amin Gwaggo Mairo bata tashi bane ?"
saida yayi tambayar kunya ta zo masa da sauri ya sunkuyarda kansa.
murmushi Gwaggo tayi "Bata tashi ba daman bana son ta tashi dan in taga tafiyar ka zata iya fasa min kuka"
shima murmushi yayi "Mairo manya ana girma na cin k'asa Allah dai ya shirya"
kamin Gwaggo tace Amin sukaji an buga gida.
da sauri ya tashi ya fita, bayan kamar minti ɗaya ya dawo ya ɗauki jakar yana faɗin "Ga abokan tafiyar nan sun zo zamu wuce..."
ganin idonta sun cika da kwallah yashi risinawa ya kalleta "Haba Gwaggo kar kimin haka mana dan Allah karkiyi kuka bafa rabuwa mukayi ba tafiyace kuma in sha Allahu zan dawo"
sam Gwaggo kasa hak'uri tayi saida kukan nata ya fito fili,
nan shima nashi idon suka cika da kwallah amman bai yarda ya bari ta gani ba kasancewar shi namiji. tsit ɗakin yayi in banda shashekar kukan Gwaggo babu abunda kake ji.
saida hawayen suka ɗan tsaya mata sannan ta kalleshi da jajayen ido "Allah ya tsare ka Halilu ya kaika lafiya"
dak'er ya iya amsawa da Amin ya tashi ya nufi k'ofa nan ma ya daɗe tsaye sannan ya fice.
. Sai takwas da yan mintuna Mairo ta tashi da murjar ido ta fito ɗakin ta ɗauki buta ta shiga banɗaki., bayan ta fito ta nemi guri ta zauna zata fara alwala.
Gwaggo ta kalleta "Yau Mairo anyi ranar sallah."
"Wallahi Gwaggo jikin ne yayi min nauyi kuma duhu dubun nan da nake gani saina ɗauka ko safiya bata waye bane."
Gwaggo ta ɗan kalli gajimare "Eh da yake yau an tashi da hadari kuma yayi bak'i sosai ina ganin ruwa ake a wani garin kusa."
taɓe baki kawai tayi ta cigaba da alwala bayan ta k'are ta shiga ɗaki ta saka Hijab ta shinfiɗa ɗan kwali ta soma Sallar, tana k'arewa, ta fito ɗakin da sauri ta shiga ɗakin Halilu.
fitowa tayi kinit kinit da fuska kamar ta fasa kuka ta nufo Gwaggo,
tun kamin ta k'araso Gwaggo ta tare ta "Toh karki fara mani kukan nan naki ni ban iyawa"
"Miyasa baki tashe niba da zai tafi kuma kika barshi ya tafi"
da rawar murya tayi maganar alamar tana son yin kuka.
"Shine a yace karna tashe ki na kyaleki baya son kukan nan naki" aiko kamar jira take Gwaggo ta kai aya ta fara sana'ar ta ta "Ni wallahi Gwaggo sai na miki kukan tunda kika ki tashi na" abunda ta dinga faɗa kenan tana murjar kafafunta akasa kamar wata k'aramar yarinya,

*BIRNI.........*
Koda Momi ta sauko downstairs ta nufo dining room ta tararda Siraj zaune yana haɗa ma kansa tea.
"Kai kaɗaine a dining ?"
juyowa yayi ya kalle ta "Eh sun wuce makaranta tun dazu wai suna da lakca k'arfe takwas good morning Momi"
"Morning too yau kayi saurin tashi tunda A'suba fa na ganka parlor nan nama ɗauka ko aikin ne naku ya taso."
ta faɗa yayinda take k'ok'arin zaunawa.
dariya yayi "Haba Momi aiki tunda asuba ?"
"Eh mana in an kawo patient irin wannan lokacin kuma ace duty ɗinka ne ai dole kaje ba ɗaga k'afa dole a tashi da wuri"
shafa kanshi yayi "Taf ai kan ba amin haka ko patient ne wasu likitocin saji dashi sai goma ko sha ɗaya nake shiga office."
"Hmm. kaidai Allah ya kawarda ɓacin rana ai inta kama dole kayi toh yanzu wai miya tashi ka tun da safe. ?"
"Wani mummannan mafarki nayi..."
Momi ta tsayarda zuba madarar da take. "Mummannan mafarki kuma har kasa gabana yayi dakan uku uku ?"
dariya yayi "Kai Momi kin cika tsoro bafa akanki nayi ba akan Abbah ba akan kowa na gidan nan ba."
"Toh akan wa faɗa min gaskiya Siraj ?"
"Momi ai ance in anyi mafarkin daba na k'warai ba ba'afaɗa"
"Toh miya rage a kariga ka faɗa."
saida ya ɗan cije baki sannan yace "Mafarkin nayi wai Maryam ta Auri wani mutum..."
Ajiyar zuciya Momi ta sauke ta lumshe ido,
bayan ta buɗe ta ɗanja tsaki "Mtsss Siraj ka iya tada hankalin bawa ni Wallahi na ɗauka ko wani abun ne"
"Wani abun ne mana Momi kai Allah dai ya tsare."
kallon mamaki Momi tayi mashi "Ya tsare. mi abunda Allah ya kaddaro ai babu mahani in Allah ya rubuta saita Auri wani ai sai ta Aura"
tea dake gabansa ya kurɓa "Eh haka ne amman dai kada Allah ya kaddaro ta Auri wani bayan..."
sai kuma yayi shiru ya kasa karasawa.
kai Momi ta girgiza "Allah yayi muku saukin wannan rayuwa kun ɗauki kiyayyah kun ɗorawa Yariman nan na san ai danshi ne kake wannan abun"
hannayensa ya ɗaga sama "A'a Momi karfa ki lakamin laifi kedai kika amfato sweet son ɗin nan naki baki ji a baki na ba."
Momi ta soma shan tea tana faɗin "Ai ko baka faɗa ba na san haka kake nufi."
Murmushi yayi ya tashi tare da cup ɗin tea ya ɗauki jaridar dake gefensa ya fice.

''' *** *** *** '''
Kishingiɗe yake tsakar parlorshi sanye da wando pencil da riga yellow, idoshi a lumshe yana tsutsar minti yana mayarda numfa a hankali,
"Yes enter..."
shine abunda ya furta bayan mai bugun k'ofar ya dade tsaye.
wani wassgegen mutum ne naga ya kunnu kai cikin ɗaki da gamammiyar fuska kamar an masa mutuwa.
nesa dashi ya tsaya yace "Oga nazo maka da Albishir mai daɗi"
saida ya kusan minti uku da yin maganar sannan ya amsa masa har lokacin idon shi a lumshe suke. "Wane irin Albishir kazo dashi ?"
cike da isa yayi mashi tambayar shi ko jiki na rawa ya bashi amsa,
"Halilu ya mutu..... "
_Halilu ya mutu.! Halilu ya mutu..!! Halilu ya mutu...!!!_
haka maganar ta rik'a yima Yarima yawo a kwakwalwa sai a lokacin ya buɗe ido ya kalli Mutumin "Nace maka duk yadda zakayi kayi na ganin ka raba tsakanin su amman banyi da kai ka kashe shi ba."
da sauri ya bashi amsa "Oga ba kashe shi nayi ba accident ya samu a hanyarsa ta zuwa Neja neman aiki" wani tsire baki Yarima yayi "Ya a'kayi kasan ya samu accident ?"
"Oga idun mu yana kansa fa tunda ka bamu aikin nan ko ina yarana nake sawa su kula dashi a motar da sukayi accident ɗinma harda yaron mu"
Wani irin kyakkyawan murmushi ya shinfiɗe fuskar Yarima wadda na tabbatar har a zuciyarsa yake.
tashi yayi tsaye ya k'arasa kusa da mutumin ya dafashi fuskarsa ɗauke da annashuwa "Kazo min da albishir mafi daɗi kuma goron mai tsokane jeki waje ka jirani amman ka tabbatar mutuwa yayi ba dogon suma ba."

Da gudu Qasin ya shigo part ɗin Momi kai tsaye upstairs ya nufa.
zaune ya tararda ita hawaye na mata zuba, jiki a sanyaye ya zauna "Momi yanzu Abbah ya kirani sai anyi rasuwa k'auye"
Kai ta daga masa "Eh Halilu ne Allah yayi masa cikawa..."
ta karasa maganar,
nan shima Qasin ya kawarda fuskarsa yace "Abbah yace na ɗaukeki muje kamin ya iso inya so sai yaje shida Siraj da Usman"
kai kawai ta iya ɗaga masa ya tashi ya fice.
Part ɗinta ya nufa a gaggauce ya shirya ya fito shida Mansura bayan ta shiga. mota ya shiga ya kira Momi suka kama hanya.

''' *** *** *** '''
Tunda Qasin ya doso unguwar soka soma hangen mutane,
ba karamin mamaki Qasin ya cika dashi ganin motocin Yarima.
yanayin parking ya kalli Momi "Momi ke kika faɗa masa anyi rasuwa ?"
Momi bata bashi amsa ba ta buɗe motar ta fice Mansura ta rufa mata baya.
_"inna illahi wa inna ilaihi raji'um_"
Shine abunda Gwaggo keta furtawa tana dafe da kai hawaye na mata zuba mutane sai hak'uri suke bata Mairo na ganin Momi ta nufe ta gudu tana kuka. rumgumeta Momi tayi suka faɗi zaune ko wanne su na kuka, ganin kukan da suke yasa Mansura ita ta soma kukan mutane dake shigowa suma auka fasa nasu aka sara mai bawa wani haku'uri,
haka gida ya kacame kowa sai yabon halinsa yake.,
guraren la'asar aka ɗauki gawarsa zuwa mak'abarta bayan anyi masa sallah.

Bayan an dawo mutane suka soma yima Gwaggo gaisuwa uffan bata iya cewa ba in banda zubar hawayen da take.
A lokacin su Abbah suka iso shida Siraj da Usman harda Nura. Ba karamin tashi hankalin Abbah yayi ba ganin yadda Gwaggo ta koma nan da nan shima hawayen suka soma masa zuba sai hak'uri yake ba Gwaggo dan yasan tafi kowa jin mutuwar,
"inba wadda ya saniba babu wadda zaice ba nice na haifi Halilu ba bai taɓa min musu ba bai taɓa kin mun biyayyah ba mutum ne da kowa ga yaba da halinsa duk abunda zai ɓata min rai yana gudunsa yana da burika dayawa aranshi na ya kautata min yayi rayuwar jindaɗi ashe Allah bai nufa ba aahe rayuwar yar kankanuwace ba mai tsoyo ba..." cikin kuka Gwaggo take wannan maganar a'na bata hak'uri.
_Gwaggo bata taɓa haihuwa ba hakan yasa lokacin da yayanta ya rasu ta ɗauko Halilu ta rikashi tun yana karami a hannunta ya tashi Mairo ma tunda aka haife aka kawo ata ita itace ta raine ta kasancewar ta tashi babu uba kuma mahaifiyarta gurin haihuwarta ta rasu_

Sai a lokacin Yarima ya shigo cikin gida da sunan gaisuwa har kasan tabarma ya zauna yana gaida Gwaggo "Sannun mu inna Allah ya jikan shi yayi masa rahama yasa ya huta."
duk suka amsa da Amin Abbah ya Kalleshi cike da jindaɗi abunda yayi "Allah yayi maka albarka Yarima ya biya ka"
"Babu komai Abbah ai yima kaine Hajiya ma tana nan zuwa gobe tace nayi muku gaisuwa kamin ta iso"
"Muna amsawa Allah ya kawota lafiya"
nan ya juyo ya kalli Qasin da fuskar da shi kadai zai iya fassara abunda ke rashi "Sannun mu Qasin Allah ya baku hak'uri..."
'Amin' ciki ciki Qasin ya amsa ya ɗauke kansa yana kallon k'ofa nan ya juyo kan Siraj yana yi mashi tashi gaisuwar.
Haka Siraj ya amsa gaisuwar yana jin kamar ya shak'o wuyanshi.
Hannu yasa Aljihu ya ciro kuɗin da zasu kai dubu ɗari biyar ya aje gaban Gwaggo yana faɗin "Ni zan wuce kuma za a shigo da abinci yanzu Allah ya baku hak'uri"
"Amin Yarima Allah yayi maka albarka ya taimake ka akan dukan k'uduri ka na Alheri.. "
Momi ce tayi mashi Addu'a idonta cike da kwallah,
Saida ya haɗe yawu sannan ya kalli Qasin "Ina Maryam ina son nayi mata gaisuwa ?"
haka Qasin yaji maganar kamar izgilanci uffan bai iya ce masa ba Siraj ne kawai ya iya cewa "Ai basai kayi mata ba tunda kayi mana ya wadatar..."
"A'a bari a kira masa ita yana da kyau ita ai yayi mata"
Momi ce ta tashi da sauri ta faɗan haka ta nufi ɗakin da Mairo take.
Daker Momi ta samu ta lallaɓata ta fito. da sauri Yarima ya karasa kusa da ita yana kallon fuskanta ya soma mata gaisuwar "Sannu Maryam Allah ya jikashi kinji Allah ya baki wani ya baki hak'uri..."
Kai kawai ta ɗaga mishi tana kuka, ya ɗan daɗe tsaye sannan yayi musu sallama ya fice.

Story continues below



*FEW HOURS LETTER..........*
Qasin ya tashi ya shiga ɗakin da Mairo take,
Zaune ya tararda ita rakuɓe gefe ɗaya tana shasshekar kuka guri ya samu nesa da ita ya zauna ya kafa mata ido.
Sai a lokacin ya lura da ramar da tayi wani irin tausayin ta ne ya mamaye masa k'ok'on zuciya _she's too young for that yarinyar nan tun tana k'arama ta tashi babu iyaye tayi rayuwar k'auye yanzu kuma mijin da aka aura miki ya rasu kai gaskiya kina cikin halin rayuwa Maryam_ a zuciyarsa yake wannan tunani yana ɗan motsa baki.
Can ya tashi ya k'arasa kusa da ita "Maryam..." a hankali ya kira sunanta.
ɗago kai tayi ta kalleshi da jajayen idonta "Kin ci abinci ?" ya tambaya
Kai ta girgiza masa alamar a'a "Toh miyasa ?" dak'er ta iya buɗe baki tace "Bana iya cine"
"Ai daurewa ake yi Maryam ke bakinsan komai na duniya ɗan hak'uri bane mi kike ao yanzu kici ?"
"Bana son komai bazan iya ciba"
"A'a ai zaki wuni haka ba tun ɗazun baki ci komai ba kuma yanzu ace ki kwanta haka faɗamin mi kike so ?"
Fashe masa tayi da kukan shagwaɓa "Nidai bana son komai kawai ka kyale ni"
"Bazan fa kyale kiba sai kin faɗa min abunda kike so kici ko kuma duk abunda na kawo miki ki ci"
"Qasin miye haka ne tace bata so ba zaka kyale taba"
Kamar daga sama yaji maganar Mansura dake tsaye bakin k'ofa. Juyowa yayi ya kalleta tare da jan tsaki "Mtss wai Mansura mi yake damunki ne ke ko ina sai kin nuna bak'in halinki ?"
"Babu wani bak'in hali sai gaskiya Yarinyar nan dai naga tak'aba take dan haka dole ne ka ɗaga mata k'afa"
Hannu ya ɗaga mata "Mansura yau yau fa akayi mutuwar nan ba jiya ba ko shekaran jiya dan haka kar k'wak'walwar ki ta yayo miki mummunan zato akaina kosan irin abunda kike yi dan ke ba yarinya bace"
Shiru tayi ta tsura masa ido dan tasan halinsa sarai zai iya yimata tatas in halin nashi ya motsa,
Kallon Mairo yayi "Ke mi kike son ki ci ?"
ganin faɗan da yayi ma Mansura kuma fuskarshi a haɗe yasa ta ɗan ji tsoro share hawayenta tayi murya k'asa k'asa tace "Shayi nake so"
kai ya ɗaga mata "Ok bari naje na nemo miki yanzu kinji ?"
ita kan ta ɗaga mishi tana kallon Mansura data wani mugun haɗe fuska,
hak Qasin ya tsara gefenta ya fice.

*©KHADEEJA CANDY*
[6:02PM, 3/23/2017] Khadeeja_ce👌: *♡... MAIRO ...♡*

*BY*

*_KHADEEJA CANDY_*
Candynovel.wordpress.com

*50.*

Koda Qasin ya dawo ya tararda Mairo waje ta ɗora kanta saman cinyar Momi da alama wata maganar suke.
K'arasawa yayi tare da sallama "Assalamu alaikum"
"Amin wa alaikassalam"
bayan Momi ta amsa mashi ya nemi guri kusa da ita ya zauna.
"Maryam tashi gashi ki ci" maganar yake yana k'okarin kwance ledar dake hannunashi.
"Minene ?" Momi ta tambaya
"Tea ne da bread da tace tana so shine na siyo mata na haɗo mata da indomie tun safe fa ba taci komai ba"
Ido Momi ta tsura mashi ba tare da yasan tana mishi kallon ba.
"Tashi mana Maryam ki ci kinji ?" ya sake maimaitawa ganin yadda tun ɗazu ko motsi ta kasayi sai kallon tea take,
Tashi tayi tana turo baki "Toh ai baka ɗauko kofi ba tunda ba a leda zan sha ba"
"Oh sorry na manta" da sauri ya tashi yaje ya ɗauko kofin da kwano ya dawo, saida ya zube tea da indomie sannan ya tura mata gabanta "Gashin nan duk zaki cinye karki raga"
Waje tayi da ido "ni ina zan iya cinye wannan duka ?"
"Naji amman dai kaɗan zaki raga"
Kai ta ɗaga mishi tana tummuk'ar biredin,
"Qasin..."
A hankali Momi ta kira shi juyowa yayi ya kalleta
"Na'am Momi"
"Matarka tana son zuwa gida kuma kaima nasan ba zaka rasa aikin da zakayi ba tunda gobe ma ranar aiki ce dan haka kaje kayi musu Sallama ku kama hanya"
Ajiyar zuciya ya sauke "Momi Mansura fa gaisuwa tazo kuma yau akayi rasuwar nan ya za'ace mu koma yanzu da dare ?"
"Toh ita ta nuna tana son komawa dan tamin magana da kanta kuma Abbah ku ma ɗazun yace ya kamata ka koma tunda ga mu. mun wadatar sai kaje ga aikin ka kai da Siraj kaga shi kana fita ya kama hanyar gida"
Shiru yayi kamar mai tunani can kuma ya kalleta "Shikenan Momi zan koma ɗin amman sai gobe da safe dan bana son tafiyar dare"
"A'a haka dai zaka jure ku tafi yanzu ya fi muku da safen nan tunda dare ba wani yi yayi sosai ba"
Nan ma shiru ya sakeyi sannan ya tashi ya nufi ɗakin Gwaggo. "Ya Qasin zakaje dani ?" daf da zai shiga ɗakin Mairo ta jefo mishi tambayar.
Juyowa yayi ya kalleta "Ina ? baga Momi nan ba gurin wa zaki can?"
"Gurinka mana"
"No ki bari in Momi ta tashi tafiya sai taje dake"
lak'e kafaďa tayi "A'a nidai kaje dani yanzu ita Momi in zata tafi cewa zatayi baza taje Daniels ba tafiyar ta zatayi ni dai kaje dani dan Allah"
Dafa kafaɗarta Momi tayi "Maryam yanzu fa babu ke ba fita kin shiga tak'aba kenan daga yau"
Kallon momi tayi "Minene tak'aba ?"
"Idan mijin mace ya rasu toh daga lokacin ta shiga tak'aba kenan bazata sake fita ba bazata sake shafa kwalli ba ko kwaliya ko saka turare kuma kullum zaki rik'a rufe jikinki ba a kitso sai dai tsoro huďu wasu ma suka ce tsoro biu akeyi har sai kinyi wata huɗu da kwana goma"
Tunda Momi ta kwararo mata bayanin ta tsaya tana saurare saida ta kai aya sannan ta fashe da kuka "Na shiga uku na bani nidai ba zan iya ba wallahi kuma fa bama nice maman shi haka kawai sai nayi duk wannan ?,
k'ila ma dan kar kije dani ne yasa kika ce haka dan Kinga ina son zama a gurinku"
"Mtsww"
Momi ta ɗan ja tsaki "Wai mi yasa ke baki da hankaline Maryam daga ana faɗa miki abunda ya wajaba akanki sai ki ɓarewa mutane baki ke kullum girma. kike kina cin k'asa"
Tashi tayi tsaye har lokacin tana kuka ta nufi ɗaki.
Kai kawai Momi ta girgiza Qasin kuma ya juya ya shiga ɗakin Gwaggo.
Sallama yayi ma Gwaggo da wasu Kawun nan sa da kuma Abbah sannan ya fito tare da Mansura.
Suna kawowa tsakar gida ya kalleta
"Ki je gurin Mota gani nan zuwa"
"Kai ina zaka ?"
"Kije dai nace miki ina zuwa" fuskarsa ba yabo ba fallasa ya bata amsar.
Kamar ta musa masa sai kuma wata zuciyar ta hanata haka ta kaɗa kai ta fice.
Shi kuma ya shiga ďakin da Mairo take.
Yayi kusan one hour ɗakin sannan ya fito ya nufi gurin Motar, buďewa yayi ya shiga bai ce da ita uffan ba ita bata ce dashi ba ko gefenshi bata kallaba har yayi ma Motar key suka kama hanya.
Saida dare ya raba sannan suka isa gida. yanayin parking ya kalli Mansura "Wai mi yake damunki ne tunda muka kamo hanya kike kukan nan ?"
Kawarda fuskarta ta k'arayi tana matsar kwallah "Ba komai"
"Ba komai kamar ya kukan daɗi ne kike kenan ko ?"
"Qasin mi yasa kake kula Maryam. ?" hannunshi ya ɗora saman sitarin Motar ya sauke ajiyar zuciya daman yasan za a rina dan duk abunda take bazai wuce kan Mairo ba.
"Ina kula Maryam ne saboda tana bukarta kulawa Mansura Maryam yarinya ce k'arama dole ne sai an kula da ita ba tada uwa ba uba sannan yanzu mijin da aka aura mata ya rasu Wallahi tausayi take bani sosai shiyasa kika ga ina kula ta bayan haka babu wani abu"
Juyowa tayi ta Kalleshi "Da gaske Qasin ?" fukar zolaya yayi bayan ya sakar mata murmushi
"Au Qasin yana miki k'arya ne daman ?"
kai ta girgiza "A'a baya min k'arya kuma bai taɓa min ba sai dai ina tsoron wannan karon kar zuciyarshi tasa shi yayi"
Murmushi yayi ya janyo hannunta ya ɗora daidai k'irjinsa yana kallon fuskarta "Kinji gun da zuciyar Qasin take ko ?"
Kai ta ďaga mishi
"Toh a karkashin ta ne son Mansura yake da kaɗan ya fara har ya ginu yayi katangar k'arfe da gambun dalma shin ta yaya kike ganin son wata zai iya shiga a innuwar da ke kaɗai kike da ita a zuciyar Qasin har ta iya haɗa kai da baki a a yaudare ki ?"
Kai ta ɗaga ta kalli kwayar idonshi "Zuciyata bata ta6a raya min cewa zaka yaudareni ba sai dai ina gudun kar ginin katangar k'arfen da nayi wata ta rusa"
"Babu mace da zata rusa ginin Gimbiya Mansura a fadar Qasin"
lumshe ido tayi tana faďin "Allah yasa"
Fuskarta ya riko yana murmushi "Don't doubt ke kadai ce kike da wannan masaukin a zuciyar angonki karki bari tsoro ya shiga ya fasa kwalbar amincin dake tsakanin mu okey ?"
Ya k'arasa maganar tare da manna mata kiss a goshi.
Sannan ya buɗe Motar ya fita ya zaga gefenta ya fito da ita suka nufi cikin gidan.

Story continues below



''' *** *** *** '''
Kwana biu Qasin ya jera kullum sai yaje gaisuwar.
Ranar da akayi addu'a uku ma saida yaje shida Usman da Nura Siraj ne kawai. bai samu damar zuwa ba saboda yanayin aikin shi.
Ranar Gwaggo taci kuka har sai da ta godema.
Allah Momi ma saida tayi kukan Abbah ne kawai ya iya jurewa ya bawa zuciyar shi hakuri.
kuɗi ya bata masu yawa bayan abincin da yasa Qasin yazo dashi,
Mairo ma tasha nata kukan dan abun biu ya zame mata gana son tabi Momi gana abunda ya faru sai duk idonta suka kumbura suka yi ja fuskarta kuma tayi wani fari alamar fek'ewa.
Sosai ta tsaya a zuciyar Qasin dan hawayene kawai bai zubar mata ba amman tausayinta ya mamayen mashi k'ok'on zuciya.
Shine yayi ta lallaɓata yana bata hak'uri har aka samu ta tsagaita kukan sannan suka yi musu sallama suka kama hanya.
A mota babu abunda Momi take sai yabon halin Halilu ita da Abbah. sun nema masa gafara.
"Gaskiya kan Maryam tayi rashin miji dan samun irin Halilu a K'auyen nan yana da wahala" Usman ne yayi maganar yana zaune gidan baya kusa da Momi. "Sosai ma mutum ne maison yayi rayuwar jindaɗi shiyasa ma kaga ya dage shi sai yayi karatu ya samu aiki yadda zai samu damar rik'eta suyi rayuwar jindaɗi ashe Allah bai nufa ba"
Abbah yace "Allah dai ya jik'an shi yayi niyar yin abubuwa da dama rai yayi halinsa haka rayuwar take kana naka Allah na nashi"
"Dakan sunyi zaman Aure da ta more dan yana sonta" cewar Momi
Duk firar da suke Qasin saurarensu kawai yake uffan baice ba har suka isa gida.

*WASHE GARI..........*
Guraren takwas da wani abu ya shigo part ɗin Momi.
Zaune ya tararda Siraj da Momi k'asan carpet har Abbah suna k'aryawa.
K'arasawa yayi fuskarshi ɗauke da murmushi ya nemi guri ya zauna "Abbah ina kwana Momi an tashi lafiya ?"
Abbah ne ya fara amsawa "Lafiya kalau ya gajiya ?"
Hannu ya kai ya ɗauki soyayyar plantain ya kai baki "Gajiya tabi lafiya"
nan ya dan saci kallon Momi tare da ɗaukar tea dake gaban ta ya ɗibi biredi dan yasan ba taya mashi zata yiba. ya soma ci.
harara Momi ta watsa mashi "Kai bana raba ka da zuwa nan kana karyawa ba ?"
Abbah ya kalle ta "Saboda mi ?"
"Ai yana da mata miyasa baza girka mashi ba sai ya rik'a zuwa min nan yana cin min abinci"
Murmushi Abbah yayi "Toh minene dan yazo yaci abincinki in baga Siraj nan yana ciba"
"Alhaji ba zaka gane bane samsam matarshi bata iya girki ba ko kuma nace bata iya girka mishi kullum cikin siyen take way yake ko kuma yazo nan yaci kamar ita zane tafi sauran matan dake kula da nasu mijin"
"Toh Allah ya sauwak'e"
"Amin gashi bata son haihuwa ko kaɗan ni halinta sam bana sonshi bata da halayya na gari Wallahi"
Tashi Abbah yayi yana faɗin "Wannan magana taku ce ta mata haihuwa ba Allah ne yake bayarwa in tazo ai ba a iya tsayarda ita."
yana kaiwa nan ya nufi k'ofar da zata kai shi part ɗinshi.
Sam Qasin bai nunawa Momi yaji zafin abunda tayi ba ko babu komai yasan gaskiya ta faɗa dan halin Mansura ne kuma shima kanshi abun yana damunshi dan dai babu yadda ya iya ne.
Kai ya ɗago ya kalli Siraj har ya ɗauke kanshi sai kuma ya sake kallon shi kamar wadda ya tuna da wani abu "Na fa manta ban faɗa maka ba Humaira tace tana gaida ka"
Tashi yayi tsaye yana jan tsaki "Wai ba nace ka daina karɓo min gaisuwar ta bane"
Murmushi yayi "Toh ai ni sak'o ta bani kuma har da cewa tayi karna manta fa"
Momi tayi dariya "Gaskiya Humaira tana da kirki kuma duk taga wani ɗan gidan nan sai tace tana gaida ka wai ko...."
"Wai ko mi ?"
Ya tari numfashinta "Momi karma ki soma ni yanzu babu wannan a gabana koma mace zanso ai ba zan so wannan yarinyar ba Allah ya kiyaye"
"Saboda mi ? aiko yarinyar bata da matsala. gata kyakyawa" Qasin ne yayi maganar.
Agogon hanunshi ya shiga gyarawa yana faɗin "Wai a'ce mace da ita kuma ba haushiya amman ta rasa abunda zata karanta sai Engineering ni ai haushi take bani"
"Toh minene a ciki ai dan ta nunawa duniya what ever man can do woman can do ne ba kaga cikin maza take gogyayyah ba amman Allah in yanzu kace kana sonta zata iya aje aikinta ta aureka" cewar Qasin.
Siraj ya tsire baki "Tace maka ?"
"A'a bata ce ba amman dai nasan indai tana sonka zata iya"
"Toh bana ina sonta ba taje tayi tayi. ni bana son yarinyar da tayi zufi a ilmin boko har ta iya gogyayyah da maza"
Momi ta taɓe baki "Ai daman kai baka taɓa ganin wace kake soba sai kace wadda Aljana ta aura"
Duk fashewa sukayi da dariya. Qasin yace "Momi babu wata Aljana tsabar iskancine kawai da samun guri"
Kanshi ya shafa "Oh Ya Qasin ai da ka bar shi as aljana ta aure ni basai na huta da faɗan nan na Momi ba nidai Kunga tafiya na karna ɓata lokaci"
yana kaiwa nan ya nufi k'ofa. da kallo Momi ta bishi har ya fice.

Story continues below



''' * * * * * * '''
"Gaskiya ya kamata kije gidan Momi ki kai mata ziyara"
Yarima ne yayi maganar yana kishinɗe ya ɗora k'afa ɗaya saman ɗaya yana cin anabi.
A hankali ta Kalleshi "Saboda mi ?"
"Ba komai naga dai k'anwarki ce kuma har gobe akwai zuminci a tsakaninku"
Lumshe ido tayi irin nasu na matan manyan Sarakai sannan ta buɗe ta sake kallon shi "Wato Yarima ba zaka bar maganar Yarinyar nan ba ko bazaka cireta a cikin rayuwarka ba wai mi take da shine yarinya yar k'auye"
"A haka nake son ta ada nayi niyar ajeta na raineta harta girma sannan na aureta amman yanzu na chanja shawara da kuruciyarta zan aure kodan na nunawa Qasin ni murucin kan dutse ne"
Ajiyar zuciya Hajiya ta sauke "Ko kaɗan Mahaifinka baya son auren nan nima kuma bana so duk kuma wadda yake sonka ba zai so auren nan ba haba Yusuf duk yayan saraika da attajirai da suke garin nan da wajen garin nan ace baka ga wace kake so ba sai wannan"
Kallonta yayi "Kar kiyi mamaki wannan shine ake kira so babu ruwan shi da kankanci ko mulki ko wulakanci ko sarauta barre dukiya a haka nake son ta kuma sai na aure wannan alk'awari ne"
Yanayin fuskarta naga ya chanja nan take ɓacin rai ya bayyana "Shikenan bazan hana ka aurenta ba tunda ka nace kai sai ita amman ka sani zaka aurota ne kawai tazo gidan nan a bautata dan ban rabata da baiwa ba bauta zata zo tayi mana" da kaukausar murya tayi mishi maganar
Wani irin kyakkyawa murmushi ne ya faɗaɗa fuskarshi dashi ya kai hannu ya shafa dogon hancinshi.

*© KHADEEJA CANDY*
[6:02PM, 3/23/2017] Khadeeja_ce👌: *♡... MAIRO ...♡*

*BY*

*_KHADEEJA CANDY_*
Candynovel.wordpress.com

_In dedication to YARIMA FAN'S_.👌
_Auntie na Dr Zulaihat Isa_
_Jidda Maman Al'amin_
_Besty Hauwa'u Zamau_
_Siddika love_
_Maryam Silver_
_and all YARIMA TEAM._😍

*51*

A kwana a tashi babu wuya. wasa wasa yau watan Halilu hudu kenan da rasuwa.
Mutuwa ta i'shi kowa Wa'azi ba k'aramin natsuwa Mairo ta. ta samu ba duk wani hali nata na banza ta zubar dashi.
Sosai taba Mutane mamaki bbu wadda yayi tunanin rayuwarta zata zama haka ta shanye raɗa dan kowa faɗan yake bazata taɓa tsaya tayi tak'aba yadda ya kamata ba dan ganin rawar kanta da take dashi.

''' *** *** *** '''
"Ki shirya Ranar Monday za muje Asibiti" Maganar yae yana kallon cikinta ita kuma tana daga kwance kanta na saman cinyar shi.
Kalaminshi ne yasa tayi saurin tashi zaune tana rabon ido kamar marar gaskiya. can kuma ta sunkuyarda kai "A'a ni bana so ai ba sai munyi ma Allah shisshigi ba"
"Zuwan Asibiti a duba lafiyarki shine yima Allah shisshigi ?" Cike da mamaki yayi mata tambayar.
"Eh.... naga Haihuwar nan Allah ne yake bayarwa ko munje Asibiti babu abunda zasu mana idan Allah bai kawo lokacin haihuwar ba"
"Naji amman ai Allah bai hana a nemi lafiya ba ko ?"
Kallonshi tayi "Lafiya na kalau Qasin tun da ina haihu ba bana haihuwa lokacine kawai baiyi ba"
"Naji kina haihuwa tunda kin taɓa yin ɓari amman ai yanzu baki sani ba ko wani abun ne yasa kika kasa samun cikin yanzu ba"
"Babu wani abu kawai daga Allah ne".
"Mansura wai mi yasa duk lokacin da nayi miki maganar zuwa Asibiti nan kike jayewa ne bafa wani sabon abu zasu bankaɗo miki ba"
Kallonshi tayi fuskarta ɗauke da damuwa "Qasin mi yasa ka damu da haihuwa ne yanzu ada ba haka kake ba ?"
Hannunta ya rik'a "Ko a da na damu da haihuwa Mansura kawai dai ina taushe zuciya ta ne kowa yana aon ganin jininshi dan baka san ta raiba kuma kinga duk abokan da mukayi Auren nan tare dasu daga mai 'ya'ya biu uku sai wadda matarshi take ɗauke da ciki na hudu ko na biyar amman ni har yanzu shiru. gashi Momi ma tana son taga jinina tayi magana har ta gaji. kuma badan bakya haihuwa ba, tunda kin taɓa samun cikin can baya shiyasa nake son muje Asibitin nan muji ko wani abin ne"
Shiru tayi kamar mai tunanin abinda zata ce. can kuma ta kalleshi "Nifa ba zuwa Asibiti ne bana soba kawai dai... "
Knockings ɗin ta akayine yasa ta kasa k'arasa maganar.
"Bari na duba ana duga k'ofa" Da sauri ta tashi ta nufi k'ofar daman tana neman abinda zai katse maganar.
Wata kyakkyawar Budurwa ta gani tsaye sanye da gyale. bayan ta buɗe k'ofar.
"Sannu"
"Yauwa sannu"
"Sunana Zaliha"
"Allah sarki Saidai ban gane kiba ?"
Murmushi tayi "Haka ne bazaki sannin ba gurin mijinki nazo..."
Faduwa gaban Mansura yayi
"Mijina ?"
Ta nuna kanta
"Mi zaiyi miki mi kike nema a gareshi ?"
"Da zaki kira min shi da zaifi duk wayannan tambayoyin da zaki min"
Harara Mansura ta watsa mata
"Haka kawai zan kira miki mijina ba tare da nasan Wacece ke ba".
Da k'arfi tayi maganar kamar mai faɗa.
"Lafiya ?"
Qasin ya tambaya. juyowa tayi ta kalleshi "Wata ce take son ganinka"
Tashi yayi ya k'arasa bakin kofar.
Murmushi Zaliha ta fara aika mishi.
"Sannu Qasin"
"Yauwa sannu"
"Gurin ka nazo"
Da ɗan mamaki ya k'arasa buɗe k'ofar "Okey shigo ciki"
"Thank you"
Tace dashi yayin da take k'ok'arin ɗora kafarta saman k'aramin stairs ɗin dake gurin.
"Wait..."
Mansura ta tsayar da ita. ta kalli Qasin "Kamar ya ta shigo haka kawai baka ban san mata ba zaka ce ta shigo min ciki gida"
"Gidanki ko gidana! ?" Fuskarshi a haɗe yayi mata tambayar.
Baki sake Mansura ta kalli Zaliha. jin irin kalamin da Qasin ya furta a gabanta ko kuma ma nace akanta. Saida ta k'are mata kallo tun daga samanta har k'asa sannan ta sake kallonshi zatayi magana ya tari numfashinta "Bata hanya ta wuce"
Juyawa tayi jiki ba k'wari ta shige ɗakinta.
Kujera Qasin ya nuna mata "Zauna ko"
ba musu ta nufi kujerar ta zauna.
"No bana buk'atar komai i just want to talk to buk'atar h about something important"
Ganin ya nufi firjin yasa tace mishi haka. dawowa yayi ya zauna "Mi kike son muyi magana akai ?"
"Maganar sirri ce tsakanin ni da kai i hope idan mukayi ta a nan matarka ba zata jiba ?"
Ido ya tsura mata kamar mai son gano wani abu can kuma ya kawarda fuskarshi ya tashi tsaye "Muje waje" tashi itama tayi ta rufa mishi baya suka nufi Garden.
Bayan ya zauna itama ta zauna ta aje jikarta gefe ta kalleshi "Sunana Zaliha Lawal amman anfi kirana da Zil. nasan baka sanni ba ko kuma ma nace baka taɓa ganina ba toh ni buduwar Yarima ce. nazo ne mu tattauna wata magana da kai ina fatar zaka bani lokacink kuma kayima abinda nazo dashi kyakkyawar fahimta"
Tunda ta soma maganar gaban Qasin ya ɗan faɗi daman yasan ba zata wuce ɓan garen Yarima ba. abu ɗaya yake fargaba kar ace tazo mishi da wata rigimar ne.
A hankali Qasin ya gyara zaman shi "Mi kike son mu tattauna akai ?"
Wani motsi tayi da baki irin nasu na gogaggin mata sannan ta soma magana "Inason baka shawara ne a kan wata cousin ɗinka ce da Yarima ke so wacce ake kira Maryam ina son ka Aureta"
tashi Qasin yayi tsaye yayi mata wani kallo mai cike da tsana "You are not part of my family so baki da damar saka bakin akan abunda ya shafi rayuwata ko kuma ta gidanmu"
Tashi itama tayi tsaye tana wani murmushi "Of course I'm not part of your family or your life but mi kake tunanin zai samu Maryam idan tayi Aure a gidan da Uwar angon bata sonta haka ma Uban angon sannan sun k'uduri aniyar mayar da ita baiwa. angon ma ya shirya in har ya Aure ta ya gallaza mata dan kawai zuciyar ka ta munana. kuma nima naci Alwashi cutarda ita ?"
Wani kallo Qasin yayi mata alamun tambaya k'arara a fuskarashi "What are you talking about ?"
Wani taku tayi. tayi gaba ta ɗan bashi baya "Duk abubuwan nan dana lissafa maka zasu faru da ita ne kawai idan ta Auri Yarima. amman idan kai ta Aura ko wani toh zatayi rayuwar Aure mai kyau da kuma jindaɗi"
"Ban fa gane gun kika dosa ba ?"
"Qasin yau sauran kwana tara cif Maryam ta fita wanka kuma nasan tana fita Yarima zai fito neman Aurenta nasan kuma zaiyi nasara tunda ya ci alwashin sai ya aureta. babu wani namijin da zai iya takara dashi sai kai kaine kaɗai kake da damar da zaka tsallakarda Maryam daga ramen da take son faɗawa.
A iya binciken da nayi ko kuma nace wadda Yarima yayi naji yarinyar mairainiya kuma bata wuce 13, 14 to fifteen years ba.
kaga k'arama ce kuma gashi bata da iyaye marainiyace tana da buk'atar miji na gari irinka. kai kaɗaine kake da damar neman aurenta a aura maka ita ko dan zumuncin dake tsakanin ku.
Amman bayan kai babu wadda zai iya takara da Yarima kuma nasan muddin ya fito neman aurenta sai yayi nasara kodan darajar da yake da ita.
A halin yanzu Maryam bata san wadda take so ba ita dai burinta kawai tayi rayuwar birni data jindaɗi zuciyarta a buɗe take dan haka duk wadda ya tara zai samu kamar yadda Yarima ya faɗa".
Juyowa tayi ta kalleshi "Qasin Yarima bai dace da auren ko wace ya mace ba sai ni. dan haka karka kuskura ka yarda ya auri yar uwarka dan zan iya cutarda ita kuma iyayen shi ma haka ne burinsu"
Tunda ta soma maganar Qasin ya tattara hankalinshi ya mik'a mata.
koma yayi ya zauna jikinshi a sanyaye still yana kallonta.
"Ya akayi kika san dangantakar dake tsakanin mu da kuma wasu abubuwan da kika furta yanzu ?"
"Duk ta hanyar Yarima na sani har ma da wayanda baka dasu"
Ajiyar zuciya ya sauke ya rungume hannayenshi.
"Na gode da shawararki you can leave now"
Taku huɗu tayi ya kaita gurin kujerar ta ɗauki jakarta. ta rataya ta kalleshi fuskarta ɗauke da murmushi "I already done Mr Qasin yanzun zan fita thank you for your time and have a nice da"
Murmushi yayi mata as response ya bita da kallo har ta fice.
Sannan ya juya ya nufi parlour da tunanin kalamanta.
iya gaskiya yasan ta faɗa kuma duk abin da ta lissafa Yarima zai iya aikatasu saidai kuma yana da shankku akan lamarinta dan bashi da masani yar ko haɗin bakine da Yarima ya aiko ta dan ya cinma wani k'udiri nashi na daban.
_amman kuma mai zaisa yayi hakan duk fa abinda ta faɗa sirrishi ne na abin da yake da niyar aikatawa toh ta yaya zai so wani yaji ? lallai akwai wani abu a k'asa..._
Haka zuciyarshi tayi ta mishi sak'e sak'e har ya shiga bedroom.
Zaune ya tararda Mansura saman bed yana dannar waya fuskarta babu annuri.
Kusa da ita ya zauna ya mik'a hannu ya karɓe wayar.
"Miye haka ?"
Murmushi yayi "Oh Sweetie har kin ɗauki zafi ? wannan matar da kika gani abok..... "
Hannu ta ɗaga mishi "Bana buk'atar ka faɗa min ko wacece ita nasan tana da muhimmanci A gareka excuse me please" hannu tasa ta fisge wayar ta nufi parlor.
da kallo ya bita har ta fice sannan shima ya tashi ya nufi bedroom ɗinshi.

Story continues below



*BAYAN KWANA BIU..........*
'Jimmm jimmm jimmm'
Wayarshi dake saman bedside drawer tana ringing rufe wardrobe ɗin yayi bayan ya saka tufafinshi ya nufo dressing mirror ya ɗauki turare ya feshe jikinshi sannan ya nufi gurin da wayar take.
Murmushi naga yayi bayan ya duba screen ɗin yayi picking ya kara a kunne
"Hello Man"
"Kai ba wani Man ka wani shanya ni waje call ɗin ma kak'i picking sai yanga kake min"
Fashe yayi da dariya.
"Toh gidan bak'onka ne sai ka kirani zaka shigo.? wanka nake koda ka kira"
"Ku ji mun mutum toh nasan yadda kake da iyalinka sai kawai na faɗo maka cikin gida"
Dariya sosai Qasin yayi "Allah ya shirya ka Barrister"
"Amin wa yake kin shiriyar Allah nidai fito gani waje"
Har ya sauke wayar dariya yake.
Agogo shi ya ɗauka yasa sannan ya nufi parlor.
"Ai da karka shigo kama tsaya waje yafi" Faɗar Qasin bayan ya buɗe mishi k'ofar.
"Allah da baka zoba bazan shigo ba ai kasan halina mu bama taka doka specifically ta Mata da Miji"
Ruwa da Cup Qasin ya ɗauko mishi ya mik'a mishi
"Karɓi nidai kai kullum baka rabo da magana a bakinka"
"Kai tsaya ni bazan iya shan ruwa yanzu ba yunwa nake ji"
Kanshi ya shafa "Oh ka kawo kuka gidan Mutuwa nima wallahi ita nake ji yanzu ma wankan da nayi so nake na fita na samu ɗan abunda naci"
"Mtsss" yaja tsaki "Ni wallahi mantawa ma nayi nazo gidan ka dan dakai da marar mata duk ɗaya"
"Kai karfa ka wuce gurin kai miya hana ka yin auren tunda matarka ta fita kak'i ka k'ara amman kana son yi min rainin hankali ?"
"Ai ina bisa hanya Yaro banga wacce tayi min bane nidai yanzu muje waje muci abincin"
"A'a wane waje muje dai part ɗin Momi ganinka zaisa ta min alfarma nima naci"
"Oh kai kullum sai dai ka kai Mutum gurin Momi yaci abinci ba dai gurika ba"
"Toh yana iya" Qasin ya faɗa yana k'ok'arin tashi.
Shima tashi yayi yana faɗin "Toh Allah ya iya mana"
Tare suka fito suka nufi part ɗin Momi suna fira.
"Qasin wai da gaske ne naji ance kanfaninku yayima kanfanin Silver aiki ?"
"Eh ai tun da daɗewa ma har sun k'ara bamu wani"
Da karfi Barrister ha bugi kafaɗarshi yana dariya.
"Shege Mutume na kace kana cikin kaya"
"kai ni ba wannan ba" Qasin ya tsayar dashi.
"Wata magana nake son muyi dakai please"
Ya kalleshi "Kamar ta mi ?"
Saida ya nisa sannan yace "Kwana biu da suka wuce wata Mata ta shigo min gida tace min wai ita budurwar Yarima ce"
Barrister ya gyara tsayuwarshi "Kamar ya fa ?"
Nan Qasin ya kwashe duk abunda ya faru tsakanin su ya faɗa mishi.
Barrister ya girgiza kai "Toh kai yanzu ya kake ganin wannan lamarin ?"
"Ni gaskiya zuciyata ta kasa aminta da ita saidai kuma nasan duk abinda ta faɗa zai iya aikatawa mahifiyarshi ma nasan a halin yanzu bata son Auren"
"Wace shawara ka yanke ne yanzu mi kake ganin shine mafita ?"
"Toh ai mafitar nake nema shiyasa na faɗa maka ni kaina a kulle yake"
Matsowa Barrister yayi kusa dashi ya dafa shi "Shawarar da zan baka Qasin ba zata wuce shawarar da Yarinyar ta baka ba mafita kawai ka Auri Maryam in har dai kana gudun ta faɗa wani hali"
Ajiyar zuciya ya sauke "Nima ina wannan tunanin gaskiya dan Maryam yanzu tausayi take bani sosai but inda matsala take Yarinyar k'arama ce"
Murmushi Barrister yayi "Kai matsala ta da kai Qasin rashin ganewa sai kace ba ɗan boko ba ai k'aramar yarinya tafi daɗi auri dan bata san komai ba duk hanyar daka dorata nan zata bi kai yanzu ko auren Mansura bai isheka misali ba sai fa data gama digiri sannan ka aureta ba gashi nan tana juyaka ba sai kace masa girki ma sai taga dama zatayi kuma kaga kasha faɗamin Momi tana son ka k'ara aure tana son haihuwa kai ma kanka nasan kana son Haihuwar sannan yarinyar nan ita ce fa wacce Momi taso ka aura kak'i toh yanzu ba sai ka mata biyaya ba ko a ɓangaren Mansura saika huta da wasu abubuwan da bata maka da tsoron da kake mata" da fuskantar zolaya ya karasa maganar.
Qasin ya watsa mishi harara "Kai dan Allah gafara can wane irin tsoro ai kyale tane kawai nake ba wani tsoro fitina ce bana so"
Barrister ya fashe da dariya "Kai tsaya Malam munfa san komai"
Qasin ya nufi k'ofa yana faɗin "Toh idan ka gama sanin ka shigo"
Barrister ya rufa mishi baya "Aw dan na gama baka shawara shine zaka yi min wulakanci ko ai gobe ma rana ce"

'''***'''
_Gaskiya ne ina da buk'atar Aure kodan farantawa Momi rai da kuma kawarda wasu abubuwan da Mansura take min sai dai kuma gaskiya bana iya Auren Maryam tayi min k'arama auren da tayi ba tare ba bata taɓa zama gidan miji ba in kuma nace zanyi rayuwar Aure da ita zan sha wahala kai gaskiya bazan iya Auren ta sai dai kuma bazan bari Yarima ya Aureta ba_
kwance yake saman doguwar kujera yana wannan tunanin.
can wani ɓangare na zuciyarshi ya yayo mishi wani tunanin
_Toh yana zan hana Yarima Aurenta idan ba ni na Aureta ba. kuma gaskiya inya aureta zai iya cutarda ita dan banida tabbacin ko sonta yake da gaske in ma bada wata manufa ba miya kai Yarima son Maryam k'aramar yarinya yana babban Mutum gashi yana ji da kanshi amman yace yana son Maryam yar k'auye kuma k'aramar yarinya gaskiya da walakin goro baya tsami banza.... to ko dai na aureta ne..._
Kanshi ya dafe _oh Qasin Allah ka zaɓamin abinda yafi zama alkhari_.

Story continues below



"Dear..."
A hankali ya ɗago kai ya kalleta "Kanka ke ciyo ne ?" maganar take tana k'ok'arin zaunawa a kusa dashi.
"Ina kika je ?"
Fuska a haɗe yayi mata tambayar.
"Gida kasa yau ne bukin Asma'u"
"Wa kika tambaya da zaki tafi ?"
"Ban gane ba in zanje buki gidanmu sai na nemi izini? haba Qasin karka fara yimun abubuwan da baka saba yimun ba kwana nan naga kamar kana son chanja hali kuma gaskiya ba zai maka daɗi ba dan ni ba a mulki na i already educated nasan yadda abubuwan suke"
tana kaiwa nan ta tashi ta nufi ɗakinta.
Kai ya kaɗa "No wonder wuyanki yayi kauri shiyasa"
tashi yayi ya nufi kitchen zuciyarshi cike da abubuwa.

''' *** *** *** '''
Sannu sannu bata hana zuwa sai dai a daɗe ba ajeba komai yayi farko zaiyi k'arshe yau watan Halilu huɗu da kwana goma cikin k'abari.
Yau ce ranar da Mairo ta fita wanka.
Kwaliya tayi ta saka sabuwar atamfa. mutane sai shigo ake ana mata barka. wuni tayi fuskarta ba yabo ba fallasa. duk tabi ta zama wata irin farinciki take ko bakinciki sai ta gagara ganewa. wani yanayi ta samu kanta a ciki mai wuyar fassara.
nikan nace ai dole ko babba ma ya ya kasara ballantana ke yarinya.
Daf da za'a shiga sallar I'sha wani yaro ya shigo gidan da sallama. bayan Gwaggo ta amsa mishi ya gaisheta.
"Ina wuni Inna ?"
"Lafiya kalau Imrana ina ya mamaka ?"
"Lafiya kalau take wai ance ana sallama da Mairo a waje"
"Mairo kuma wanene ?"
"Wallahi nima ban sani ba yana dai nan waje cikin mota"
"A mota ?" Gwaggo ta daki gaba "Jeka kace ance wanene" juyawa yayi ya fita.
Be daɗe ba ya dawo "wai yace Yarima"
Murmushi Gwaggo tayi "Allah sarki bawan Allah yazo mata barka yaji ta fita wanka jeka kace tana zuwa"
Fita yaron yayi bayan yan mintuna ya sake dawowa ɗauke da manya ledodi ya dire mata "Wai gashi yace na shigo dasu gida"
Rike baki Gwaggo tayi "Oh wannan Yarima akwai shi da tausayi Allah dai ya sak mishi da alheri Allah yasa ya aureki Maryam an dan Auren irin wannan ake so inda zaki huta yar marainiyar Allah"
"Lafiya Gwaggo keda waye ne ?" Faɗar Mairo tana tsaye bakin k'ofa.
"Sallama akeyi dake a waje jeki ki saka hijabin ki Yarima ne"
"Yarima ? Mi yazo yi ?"
"Kila barkar fita wanka yazo miki kinga abin alherin daya kawo mana"
Kallon ledar Mairo tayi sannan ta juya ta shiga ɗakin ɗauko hijabin ta.

Tsaye ta tararda shi jingine jikin Mota ya rumgume hannayenshi yana kallon k'ofar gidan.
"Assalamu alaikum"
da murmushi ya amsa mata. "Wa'alaikissalam Maryam"
"Na'am ina wuni ?"
"Lafiya kalau kin fita wanka ko"
Kai ta ɗaga mishi "Eh yau ba"
Ido ya tsura mata "Naga kamar baki sake dani ba ko wani abin aka ce miki ne akaina ?"
"A'a ba ace min komai ba"
"Toh tunanin mijinki kikeyi ne ?"
Shiru tayi ta sunkuyarda kai
"Ki daina tunaninshi kinji ya riga ya tafi ba zai dawo ba"
Nan ma kan ta ɗaga mishi.
Can kuma ya sake kallonta "Zaki iya aurena Maryam kina sona ?"
"A'a ni bana son Aure yanzu"
"Saboda mi ? baki son kiji daɗine kiyi aure gidan da ba zaki yi aikin komai ba saidai ayi miki ? ki mallakin motar kanki kije makka kiyi rayuwa cikin jindaɗi ki saka mai kyau kici mai kyau"
Kai ta ɗaga ta Kalleshi "Ina so mana"
"Good toh ki daina cewa baki son aure kinji pretty kuma ki ce kina sona okey"
"Toh na daina"
Hannu yasa aljihu ya ciro kuɗi masu yawa ya mika mata "Karɓi wannan saina dawo kinji"
Waje tayi da ido
"Duka ?"
"Eh ko sun miki kaɗan ne a k'ara?"
"A'a sunyi dai yawa"
Murmushi kawai yayi yakai hannu ya ɗan shafa gefen fuskarta "I love you Maryam ki sake jikinki dani kinji ?"
Murmushi tayi itama "Toh na gode k'warai Allah ya biya ka"
Kai kawai ya ɗaga mata ta. ta juya ta shiga gida tana ɗaga mishi hannu.
Tsaye yayi yana kallonta har ta shige sannan shima ya shiga motar shi ya kama hanya.

'''**********'''

"Momi Aure fa nake son na kara"
Da sauri ta kalleshi "Aure fa kace Qasin ?"
"Eh Aure kan ko kar nayi ?"
Plate ɗin dake hannun ta ta aje saman dining ta nufo gurin da yake zaune.
"Da gaske Qasin"
"Allah da gaske Momi aure nake son na k'ara"
Murmushi Momi tayi "Aiko da ka kyautama kanka kuma ka cika min burina dan na daɗe ina jiran wannan ranar" Cike da jindaɗi tayi maganar.
"Alhamdulillahi ni Allah na gode maka Allah dai yasa da gaske kake Qasin ba wasa ba"
Dariya yayi "Allah da gaske ne Momi mutun na wasa da mahaifiyar shi ne"
"Amman ko naji daɗi Wallahi kuma matarka ta yarda ?"
Momi ta taɓe baki "A'a toh bana ce haka ba amman dai.... Hmmm ina ka samu matar ?"
Tashi yayi yana faɗin "In lokaci yayi Momi zaki ji"
"Toh Allah ya nuna mana Addu'a na ta karɓu" Ficewa yayi yana dariya.
Ranar Momi da farin ciki ta kwana tana tayi ma Allah godiya daman bata da wani buri a yanzu kamar taga Qasin yayi Aure.

Story continues below



*WASHE GARI..........*
Guraren bibda rabi na ran Qasin ya shigo part ɗin Momi da sauri.
"Lafiya ?" Momi ta tambaya ganin yana haki
"Kamar Yarima ne naga ya fita ko ?"
"Eh shine miya faru ?"
Faɗuwa gabanshi yayi ya karaso k'usa da ita ya zauna "Momi mi yazo yi ?"
"Zuwa kawai yayi ya gaishe kaga abin da ya kawo nan da kuɗi" Momi ta k'arasa maganar tare da nuna mishi kayan.
Manyan ledodi ne kusan guda bakwai da kuɗin da zasu kai dubu ɗari biu.
Momi ta sake kallonshi "Wai lafiya dai ?"
"Ba komai" Ajiyar zuciya ya sauke ya tashi ya fice.

Part ɗinshi ya dawo yana tunane tunane matuk' ar fa bai furta yana son Mairo ba har Yarima ya riga shi toh akwai matsala indan kuma ya bari Yarima ya aure ta ya cuce ta ganin ba shida wata mafita sai wannan yasa bayan sallar I'shi ya sake dawowa part ɗin Momi.
Zaune ya tararda ita tana kallon Tv Siraj kuma na zaune can gefe yana buga game.
Sallama yayi bayan sun amsa mishi ya samu guri ya zauna. "Momi magana nake son yi dake"
Juyowa tayi ta fuskance shi "Toh ina jinka"
Jimmm yayi kamar ba zai ce komai ba bakin shi yayi mishi nauyi zuciyarshi sai bugawa take da saurin.
Ganin shirun yayi yawa yasa Siraj ya kalleshi "Ko na baku guri ne ?"
"A'a zauna kawai ai yana da kyau kaima kaji" Kallon Momi Qasin ya sake yi "Momi... So nake.. Ki nema min Auren...... Maryam"
K'ara gyara zama Siraj yayi ya kalleshi baki sake.
"Wace Maryam ?"
Momi ta tambaya "Maryam mana ta k'auye"
Wata irin muguwar harara Momi ta watsa mishi "Kayi kaɗan Qasin baka isa ka sake sani cikin wata kunyar ba ou shine kace min aure zakayi daman dan kace kana son ta ne toh bazan nema maka auren ta kuma Wallahi karka kuskura sake sani matsala nida yayata daman nasan wannan tambayar da kamin ɗazun bata banz bace dan kasan Yarima zai iya cewa yana sonta shiyasa ka dawo yanzu kaima kace kana sonta kai gak ishesshe ko. to bazan nema maka aurenta ba innma dan tane kake da niyar yin aure toh ka fasa"
Haka Momi ta kunno mishi fanfon masifa ta inda take shiga bata nan take fita ba.
Shidai kanshi na Qasin ya lumshe ido yana saurarenta.
Uffan Siraj baice ba saima wani abu da yake da kai kamar wadda kanshi ke mishi ciyo tashi jiki a sanyaye ya fice.

*© KHADEEJA CANDY*
[6:02PM, 3/23/2017] Khadeeja_ce👌: *♡... MAIRO ...♡*

*BY*

*_KHADEEJA CANDY_*
Candynovel.wordpress.com

*52*

Saida Momi tayi ma Qasin tas. sannan ya tashi ya fice daga ɗakin ba tare da wata kalmar ta fita daga bakinshi ba.
Yasan dai duk abunda zai faɗa mata ba fahimta zatayi ba dan ba tsayawa zatayi ta saurare shi ba.

*WASHE GARI...*

Gurare tara da kwata Qasin ya samu Abbah ɗakin shi.
bayan sun gaisa ya nemi guri ya zauna ya noce kai Abbah na ganin haka yasan akwai magana a bakinshi.
"Lafiya Qasimu ?" Abbah ya tambaya yana kallon fuskarshi.
D'agowa yayi bayan ya sauke ajiyar zuciya "Abbah tunani nake yi akan Auren Maryam amman bazan yanke hukunci ba har sai naji abinda zaka ce"
Tashi Abbah yayi daga kishingiɗen da yake ya zauna "Wato tun rasuwar mijin. yarinyar nan ta soma bani tausayi.
kayi tunani mai kyau Qasimu ko babu komai daman ni inason Auren zumunci ballantana Maryam da take cikin wani hali abin tausayawa gaskiya kayi abu mai kyau kuma ina goyon bayanka ɗari bisa ɗari"
Daɗi sosai Qasin yaji ɗago kai yayi ya kalli Abbah "Nima Abbah tausayi take bani sosai hakan yasa na yanke shawarar aurenta n dawo da ita kodan zaman da take son yi tare damu"
"Gaskiya ne naji daɗin wannan shawarar da kayi Allah ya taimaka"
"Amin. amman fa Abbah kai nake so ka nema min Auren"
Ya faɗa yana ɗan sosa kai.
Abbah yayi dariya "Toh In'sha Allahu zan samu lokaci kamin naje Abuja saina je can k'auyen"
Godiya sosai Qasin yayi mishi sannan ya tashi ya fice.

Goma da mintuna ya kare shirin shi tsaf na fita office. laptop ɗinshi ya ɗauka tare keys ya nufi parking space.
"Yaya" Gudu Nura ya k'araso gurin yana faɗin "Yaya Momi na kiran ka"
Faɗuwa gabanshi yayi ajiyar zuciya ya sauke "je kace gani nan tafe"
Kai ya ɗaga mishi "Okey" ya juya ya bar gurin.
Saida ya buɗe Motar ya saka laptop ɗinshi sannan ya rufe ya nufi part ɗinta.
Bai tararda ita parlor ba hakan yasa ya nufi up stairs.
"Gani nan Qasin"
Juyowa yayi ya kalli dining inda yaji muryar Momi tare da nufar gurin.
Kujerar dake facing ɗin nata yaja ya zauna "Momi gani Nura yace kina nema na"
Shiru tayi har na wani lokacin sannan ta kalleshi ta soma magana "Qasin dan nace bazan nema maka auren Maryam ba shine kaje ka samu Abbah ka da maganar ?"
Ajiyar zuciya ya sauke "Momi toh naga babu yadda zanyi ne tunda babu wadda ya dace ya nema min auren nan sai ku ke kuma kince bazaki nema min ba baki ma bani goyon baya ba"
"Saboda mi zan goya maka baya Qasin kayi abin da gaba ba zamu jidaɗin shi ba"
"Saboda mi zai zamo abin rashin jindaɗi aciki ba cutar da ita zanyi ba Momi kuma naga kema fa kinason nayi nima kaina ina buk'atar auren nan toh minene abin rashin jindaɗi aciki"
"Qasin abunda nake son ka gane shine. Duk auren da akayi babu so toh yana da wahala auren ya ɗore ba son yarinyar nan kake ba kuma kaga matarka ba hali ne da ita ba zata iya cutar da ita kuma kaga yarinyar nan marainiyace ba Uwa a Uba bata da wani gata sai na Allah"
Murmushi yayi "Momi in dai har wannan ne matsalarki ko kuma abinda yake damunki toh ki kwantarda hankalinki In'sha Allahu hakan ba zai faru ba"
Momi ta ɗan motsa baki tayi mishi kallon manya "Amman mi yasa can baya baka nemi aurenta ba sai yanzu ? Alhalin saida na taya maka auren nata tun farko ?"
Agogon hannunshi ya duba ya tashi yana faɗin "Momi bari naje kar nayi latti" Bata ce mishi uffan ba shima bai jira mi zata ce ba ya fice.

Story continues below



*3:45 pm...*

Ya shigo gida ɗakin shi ya wuce bayan yayi wanka ya sake shiryawa ya nufo parlor.
Zaman doguwar kujera ya zauna ya kai hannu ya ɗauki remote ya chanja channel.
Murmushi yayi jin an shafa kanshi "Kin tashi ?"
"Waya ce maka bachi nake?"
"Ai nasan shi kike yi tun fa ɗazun na shigo na fa har nayi wanka banji motsinki ba"
Zagayowa tayi ta zauna kusa dashi. "Na barka ne ka ɗan huta tukuna tashi muje kaci abinci"
Cikinshi ya shafa "A k'oshe nake"
"Taf ai baka fara ba na dagargaje nayi maka girki kace kai a koshe kake"
"Toh ai kin riga kin saba min da cin abinci a waje ne"
"Ni gaskiya sai kaci"
Ta faɗa tana ɓata fuska.
Kumatunta ya rik'a "To miye sirrin ne nayi min girki yanzu bayan baki saba yimun hakan ba"
"Ban saniba nidai kawai ka tashi muje kaci plz" Tashi yayi rik'e da hannunta suka nufi dining.

*© KHADEEJA CANDY*
[6:17PM, 3/23/2017] Khadeeja_ce👌: *♡... MAIRO ...♡*

*BY*

*_KHADEEJA CANDY_*
Candynovel.wordpress.com

_INNALILLAHI WA'INA ILAIHI RAJI'UN._
_Yau ce Ranar da Mahaifina ya Cika shekara biu a cikin kabarinshi. Ya Allah ka haskaka mishi k'abarinshi ka faɗaɗa mishi ka yalwanta mishi ka haskaka mishi ka gafarta mishi ka sa Aljanna ce makomarshi ka zamo gatanshi ka isar mishi ka bishi da bishi da kyakkyawan halinshi._
_Hak'ik'a nayi Babban rashi Babban bango jigo na rayuwata kuma gata na farincikina Abin alfahari na mun shaku da dashi sosai sai gashi mutuwa tayi mana yankan k'auna a lokacin da bamuyi tsamani ba._
_Ya Allah ina rok'onka da kyawawan sunayenka. Ya Allah ka haɗa fuskata da ta Mahaifina a Aljanna Ya Allah ka gidana da nashi Aljanna domin shine mafi soyuwa a cikin rayuwa ta._
_nayi Babban rashi taɓonsa ba zai taɓa goguwa ba a cikina rayuwa ta har na koma ga Mahaliccina._
_Allah kayi mishi gata kamar yadda shima yayi mini._

_NA RASA GATA NA A DUNIYA WADDA BAYA SON KUKANA_😭😭😭😭😭😭

*53*

Saida Momi tayi ma Qasin tas. sannan ya tashi ya fice daga ɗakin ba tare da wata kalmar ta fita daga bakinshi ba.
Yasan dai duk abunda zai faɗa mata ba fahimta zatayi ba dan ba tsayawa zatayi ta saurare shi ba.

*WASHE GARI...*

Gurare tara da kwata Qasin ya samu Abbah ɗakin shi.
bayan sun gaisa ya nemi guri ya zauna ya noce kai Abbah na ganin haka yasan akwai magana a bakinshi.
"Lafiya Qasimu ?" Abbah ya tambaya yana kallon fuskarshi.
D'agowa yayi bayan ya sauke ajiyar zuciya "Abbah tunani nake yi akan Auren Maryam amman bazan yanke hukunci ba har sai naji abinda zaka ce"
Tashi Abbah yayi daga kishingiɗen da yake ya zauna "Wato tun rasuwar mijin. yarinyar nan ta soma bani tausayi.
kayi tunani mai kyau Qasimu ko babu komai daman ni inason Auren zumunci ballantana Maryam da take cikin wani hali abin tausayawa gaskiya kayi abu mai kyau kuma ina goyon bayanka ɗari bisa ɗari"
Daɗi sosai Qasin yaji ɗago kai yayi ya kalli Abbah "Nima Abbah tausayi take bani sosai hakan yasa na yanke shawarar aurenta n dawo da ita kodan zaman da take son yi tare damu"
"Gaskiya ne naji daɗin wannan shawarar da kayi Allah ya taimaka"
"Amin. amman fa Abbah kai nake so ka nema min Auren"
Ya faɗa yana ɗan sosa kai.
Abbah yayi dariya "Toh In'sha Allahu zan samu lokaci kamin naje Abuja saina je can k'auyen"
Godiya sosai Qasin yayi mishi sannan ya tashi ya fice.

Goma da mintuna ya kare shirin shi tsaf na fita office. laptop ɗinshi ya ɗauka tare keys ya nufi parking space.
"Yaya" Gudu Nura ya k'araso gurin yana faɗin "Yaya Momi na kiran ka"
Faɗuwa gabanshi yayi ajiyar zuciya ya sauke "je kace gani nan tafe"
Kai ya ɗaga mishi "Okey" ya juya ya bar gurin.
Saida ya buɗe Motar ya saka laptop ɗinshi sannan ya rufe ya nufi part ɗinta.
Bai tararda ita parlor ba hakan yasa ya nufi up stairs.
"Gani nan Qasin"
Juyowa yayi ya kalli dining inda yaji muryar Momi tare da nufar gurin.
Kujerar dake facing ɗin nata yaja ya zauna "Momi gani Nura yace kina nema na"
Shiru tayi har na wani lokacin sannan ta kalleshi ta soma magana "Qasin dan nace bazan nema maka auren Maryam ba shine kaje ka samu Abbah ka da maganar ?"
Ajiyar zuciya ya sauke "Momi toh naga babu yadda zanyi ne tunda babu wadda ya dace ya nema min auren nan sai ku ke kuma kince bazaki nema min ba baki ma bani goyon baya ba"
"Saboda mi zan goya maka baya Qasin kayi abin da gaba ba zamu jidaɗin shi ba"
"Saboda mi zai zamo abin rashin jindaɗi aciki ba cutar da ita zanyi ba Momi kuma naga kema fa kinason nayi nima kaina ina buk'atar auren nan toh minene abin rashin jindaɗi aciki"
"Qasin abunda nake son ka gane shine. Duk auren da akayi babu so toh yana da wahala auren ya ɗore ba son yarinyar nan kake ba kuma kaga matarka ba hali ne da ita ba zata iya cutar da ita kuma kaga yarinyar nan marainiyace ba Uwa a Uba bata da wani gata sai na Allah"
Murmushi yayi "Momi in dai har wannan ne matsalarki ko kuma abinda yake damunki toh ki kwantarda hankalinki In'sha Allahu hakan ba zai faru ba"
Momi ta ɗan motsa baki tayi mishi kallon manya "Amman mi yasa can baya baka nemi aurenta ba sai yanzu ? Alhalin saida na taya maka auren nata tun farko ?"
Agogon hannunshi ya duba ya tashi yana faɗin "Momi bari naje kar nayi latti" Bata ce mishi uffan ba shima bai jira mi zata ce ba ya fice.

Story continues below



*3:45 pm...*

Ya shigo gida ɗakin shi ya wuce bayan yayi wanka ya sake shiryawa ya nufo parlor.
Zaman doguwar kujera ya zauna ya kai hannu ya ɗauki remote ya chanja channel.
Murmushi yayi jin an shafa kanshi "Kin tashi ?"
"Waya ce maka bachi nake?"
"Ai nasan shi kike yi tun fa ɗazun na shigo na fa har nayi wanka banji motsinki ba"
Zagayowa tayi ta zauna kusa dashi. "Na barka ne ka ɗan huta tukuna tashi muje kaci abinci"
Cikinshi ya shafa "A k'oshe nake"
"Taf ai baka fara ba na dagargaje nayi maka girki kace kai a koshe kake"
"Toh ai kin riga kin saba min da cin abinci a waje ne"
"Ni gaskiya sai kaci"
Ta faɗa tana ɓata fuska.
Kumatunta ya rik'a "To miye sirrin ne nayi min girki yanzu bayan baki saba yimun hakan ba"
"Ban saniba nidai kawai ka tashi muje kaci plz" Tashi yayi rik'e da hannunta suka nufi dining.

*© KHADEEJA CANDY*
[9:17PM, 3/24/2017] Khadeeja_ce👌: *♡... MAIRO ...♡*

*BY*

*_KHADEEJA CANDY_*
Candynovel.wordpress.com

_Godiya ta musamman ga Balkisu Ammani Chuchu and Ashnur Pyar na gode sosai Allah ya bar Zumunci ya kara haɗa kan mu yan NAGARTA WRITTER'S ASSOCIATION_
_Special thanks to All My Fan's, Friends, and some of my co-Writer's i appreciate your prayers oll_

_No words can express how happy I am when I received your call and messages. u mean so much to me. thank you for being there always. (ROSE OKKAFO rosy lurv) 😘_

_In dedication to PERFECT WOMAN'S, and CLASSIC LADIES. u are very kind Mrs Tijjani thanks for the love_.

*NOTE*
_Nayi kuskure a page ďina na baya wadda nayi kamin wannan instead of nasa *53* saina sake mamaita *52* ya zama nayi *52* so biu kenan. Dan haka wannan zai zama *54* the second *52* ya zama *53* hop Kun fahimta ?_.

*54*

Kujera taja mishi ya zauna, Sannan ta shiga zuba mishi abincin.
mamaki yayi sosai ganin kalar abinci har huɗu gasu pizza da cake.
Haka ta sashi gaba ta rik'a tura Mishi abincin saida yaci yayi naket. sannan ta tashi ta ɗauko wani dan k'aramin box ta mik'a mishi tana murmushi.
Karɓa yayi yana "Minene ?"
"Open it"
"Okey"
Ya faɗa yana ɗaga gira. Arba yayi da wani agogon hannu golden color mai kyau.
D'agowa yayi ya kalleta
"Na waye ?"
"Na kane kaina siyo ma"
ta bashi amsa still tana murmushi.
"Wai duka wannan mi yake nufi ne Mansura nifa ban gane ba ?"
Hannayenta ta ware
"As how don't tell me you forget about today ?"
"Today is Wednesday so what is..."
"Today is our Anniversary"
Ta tari numfashi shi tana ɗan zaro ido.
Hannu yasa ya rufe bakinshi "Oh Allah ni Wallahi kwata kwata na manta"
Wani kallo tayi mishi mai ɗauke da mamaki "Did you hear yourself ?"
"Yes. Toh tunda mukayi auren nan babu wani abin farinciki daya faru da har zaisa na iya rik'e ranar zagayowar haihuwar mu! Mansura tun... "
Shiru yayi ganin irin kallon da take mishi.
Kanshi ya shafa zuwa fuskarashi ya lumshe ido. Haka yaji maganar daya furta mata kamar tuɓul da baka.
"What are you saying Qasin ?"
Idonta cike da hawaye tayi mashi tambayar.
Girgiza kai yayi yana haɗiyar yawu.
"I mean you... you know i..."
Gargada muryarshi ta dinga yi yana tunanin abinda zai furta mata. sai wani juye juye yake da kai. ya gagara haɗa ido da ita.
Tashi tayi hawaye na mata zuba ta nufi ɗakinta.
Da sauri ya rufa mata baya yana kiranta "Mansura Mansura saurara kiji mana"
Da gudu ta k'arasa ta bankaɗo k'ofar da k'arfi.
Yana isa ya mika hannu zai buɗe yaji tasa key. Ajiyar zuciya ya sauke ya janye hannunshi daga jikin k'ofar.
Ya daɗe tsaye a gurin sannan ya juya ya nufi hanyar fita.

'''***'''

1:28pm. Abbah ya isa k'auye. kai tsaye massalacin juma'ar garin ya wuce ganin sauran mintuna kaɗan a tada sallar.
Bayan an taso daga masallacin ya nufi gidan tsoho.
Kusan awarshi biu cikin gidan sannan ya fito ya nufi gidan Gwaggo.
Yanayin sallama ta tarɓeshi da far'ah "Ah ah ah lale marhaban da mutanen birni yanzu ake tafe ?"
Dariya Abbah yayi "Toh tafiyar ce ta kama haka tun safe nazo nazo Allah bai nufa ba amman dai nan nayi sallar juma'ah"
Tabarma Gwaggo ta shimfiɗa mashi "Bari na shinfiɗa maka a nan ɗakin nan zafi Wallahi"
Bayan ya zauna ta ɗauko mishi furau furau da maheci (hand fan) ta mik'a mishi. "Karɓi ko wannan ka ɗan zage zafi abinci kan yanzu na ɗora.
ya hanya dasu Hajiya ?"
Abbah saida yasha ruwan sannan ya amsa mata
"Lafiya kalau kowa yake duk kuma suna gaisheki"
"Tob madallah yau lafiya akayi mana zuwa ba zata kuma kai kaɗai ?"
Abbah yayi murmushi.
"Lafiya kalau wani muhimmin abune ya kawo ni Maryam ?"
"Na aike ta nan mak'ota ta karɓo min surfe ince dai kasan ta fita wanka tun kwanaki ko ?"
"Eh na sani ai munso muzo yanayin aikin ne bai barmu ba ta fita lafiya dai ko ?"
"Ta fita lafiya kalau Alhamdulillahi mabi ɗa na nan sai tasowa suke har da abokanin margayi"
Da dariya ta k'arasa maganar. Abbah ya gyara zama shi "Masha Allahu toh ai nima yana ɗaya daga cikin abinda ya kawo ni"
"Na me ba ?" Gwaggo ta tambaya.
"Na neman auren Maryam"
Gwaggo ta k'ara matsowa "Toh ko wanine yace yana son ta ?"
"Eh ɗanki ne yake son in an bashi ita yayi ta biu"
"Qasin kake magana ?"
Gwaggo ta faɗa tana zaro ido.
"Eh shi fa kuma nayi magana da tsoho yace ya bashi yanzu sauran muji bakin yarinya"
Hannu Gwaggo ta ɗaga sama "Alhamdulillahi Allah na gode maka daka nuna min wannan rana amman na jindaɗi wannan lamari Allah ya tabbatar"
Abbah ma daɗi yaji "Ni nafiki jindaɗi dan tun zamanta na farko mukaso ayi abun Allah bai nufa ba"
Fuskarshi shinfiɗe da murmushi yayi maganar.
"Daman ni kullum fatana Allah ya zaɓa mata miji na gari inda zata jidaɗi. kuma Kaga ko shekaran jiya saida tayi maganar birnin nan tana son zama gurinku sosai. Allah dai ya yarda mude mun aminta ba wata matsa Wallahi" Faɗar Gwaggo.
"Haka ne amman yanzu sai munji ta bakinta idan tana sonshi tunda yanzu ba kamar baya bane kuma Annabi (S. A. W) yace a nemi izinin mace kamin a aurar da ita toh kinga ba mu sani ba ko akwai wadda take so"
"A'a babu wani wadda take so Mairo ma wani so ta sanine tun can baya ma da tana da yar hayaniyarta ballantana yanzu da ta koma shushushu ai babu wani abu tunda dai har yace yana son ta"
Abbah ya girgiza kai "A'a baza fa ayi haka ba sai naji rayinta tukuna yanzu dai aika a kiramin ita"
"Oh toh tunda ka matsa bari na aika a kirata" Tashi tayi tana faɗin "Bari na ɗauko mayafina na aiki haruna".

Story continues below



_PROUD OF YOU Miss S-S_😘

*© KHADEEJA CANDY*
[2:41PM, 3/27/2017] Khadeeja_ce👌: *♡... MAIRO ...♡*

*BY*

*_KHADEEJA CANDY_*
Candynovel.wordpress.com

*55*

Da far'ah Mairo ta shigo cike da ladabi ta k'araso kusa da Abbah ta risina.
"Abbah ina wuni?"
Da murmushi Abbah ya amsa "Lafiya kalau Maryam barka da fita wanka"
"Yauwa Abbah yanzu ka zo? Yasu Momi?"
"Lafiya kalau suke suna gaishe ki kuma suna miki barka da fita wanka"
"Ina amsawa Abbah ina Siraj?"
"Yana can gida am.. Maryam" Ta ɗaga kai ta amsa "Na'am Abbah"
"Jeki waje kice ma direba ya baki jika tana nan cikin Mota ki kawo"
"Toh Abbah" Tashi tayi ta fita.
Bayan yan mintuna ta shigo rik'e da *BABBAR JAKA* ta aje mishi gabanshi
"Abbah gashi"
Abbah yasa hannu aljihu ya ciro kuɗi masu ɗan dama ya ɗora saman jakar.
"Am...Maryam wannan kuɗin da kayan da kika gani na neman aurekin ne Qasin ya aiko yana son idan an Amince mishi kizo a matarshi ta biu"
Da sauri ta nuna kanta "Abbah ni?" Ta tambaya tana zaro ido. Abbah ya gyara zamanshi "Eh kefa Maryam amman fa ba cilas bane shima ya saka kanshi cikin manema ne idan kin aminta shi kenan sai ayi yar gida indan kuma baki ra'ayinshi toh mu duk wanda kika kawo zamuyi maraba dashi".
Nan da nan idonta suka kawo ruwa "Abbah bana son aure yanzu ni bana son aure dan Allah Abbah kar kumin aure yanzu kaji?"
Mamakine ya bayyana a fuskar Abbah "Baki son aure kamar yaya Maryam ai duk ɗan aure bazai k'i aure ba"
Gwaggo tace "Ita fa fun abinda ya faru naga tsoro ya kamata duk tabi ta chanja"
"Karki kuskura kisa abinda ya faru da Halilu cikin ranki har ya iya zama wani dalili na tsorata ki haka Allah yake lamarinsa babu yadda bawa zaiyi sai godiya da kuma hak'uri" Faɗar Abbah.
Kwanta tayi jikin Gwaggo tana kukan da baza'ace ba shagwaɓa bace.
Nisawa Abbah yayi ya kalli Gwaggo "Ina ganin lokaci ya kamata mu bata tayi tunani sannan muni daga bakinta"
Gwaggo ta lasa baki "Toh ba nak'i zancen kaba amman dai ita Mairo har wani tunani tasan ta tsaya tayi ita dai tsoro ne kawai take ji kuma nasan In'sha Allahu zata daina"
"A'a mu barta dai har nan da zuwa sati tukuna"
Kai Gwaggo ta gyaɗa "Toh Allah ya kaimu ya saukwake"
Abbah ya amsa da 'Amin' Nan ta kalli Mairo "Tashi ki shiga ɗaki ni bari na duba abincin can ina ga ruwan ya tafasa"
Tashi tayi ta nufi ɗaki Gwaggo kuma ta nufi gurin girkinta.
Sai bayan La'asar Abbah ya baro garin daf da magriba ya iso gida.

Bayan Sallar Isha'i Qasin ya shigo part ɗin Momi.
Siraj kawai ya tararda zaune yana danne danne waya. Saida ya zauna sannan ya ɗago kai ya kalleshi "Yaya" "Na'am Siraj chatting kake ne"
"Eh Wallahi na ɗan kwana biu ban hau bane ya naga fuskar ka kamar ɗauke da damuwa?"
Ajiyar zuciya ya sauke "Ina Momi?"
"Tana part ɗin Abbah"
"Bata faɗa maka yadda Abbah yayi da Maryam ba?"
Dakan uku-uku gabanshi yayi nan ya aje wayar gefe ya fuskanci shi sosai "Bata faɗa min Wallahi miya faru?"
Saida ya sauke sauke wata ajiyar zuciyar sannan ya soma magana "Abbah yace ana faɗa mata kuka ta dinga yi tana faɗin ita bata son aure kowa yayi na'am da maganar yanzu matsalar daga gurinta take"
Shiru Siraj yayi ya tsorama Qasin ido "Wai yaya da gaske son ta kake?"
Qasin ya kalleshi "Hakan nake tunani"
"Tunani kake ma kenan"
Kawarda fuska yayi kamar baya son maganar.
"Toh yanzu ya zakayi?"
"Nima ban saniba banaan miye mafita ba"
Siraj ya busarda iskan bakinshi tare da sauke ajiyar zuciya "Idai har kana sonta toh kaje ka lallaɓata koda a waya ne. Maryam ba tada matsala tana da sauk'in kai. Kuna kasan ba wani wayau ne da ita sosai ba kana lallaɓa zaka shawo kanta wannan shine kawai nake ganin mafita"
Jimm Qasin yayi kamar mai tunani. can kuma ya jinjina kai "Ina ganin haka zanyi ka kawo shawara zan samu lokaci inje In'sha Allah"
Tashi Siraj yayi yana faɗin "Good luck" Ya nufi k'ofar fita.
"Thank you very much" Daf da zai fice Qasin yayi mishi godiyar yana murmushi.

Saida dare ya raba sannan ya tashi ya nufi part ɗin shi.
A hankalin ya tura k'ofar parlor ya shiga.
Da sauri Mansura ta tashi tsaye tana sanye da kayan bachi "Qasin ina kaje?"
K'arasowa yayi kusa da ita ya dafa kafaɗanta "Miyasa kika tambaya my dear?"
"Dubi fa agogo ka gani Qasin ɗaya saura"
Ta faɗa fuskarta ɗauke da damuwa.
Saida ya kalli agogon sannan ya shafa gefen fuskarta
"Ai ni bansan dare yayi ba ina can gurin fira"
"Fira?"
"Eh aure fa zan k'ara"
Wani tsire baki tayi "Taf ai Wallahi ko baka isa ba baza ka fara ba"
"Saboda mi?"
"Saboda Qasin dan Mansura kawai akayi shi. duk matar da tace zata saka sonka cikin ranta toh zata wahalarda kanta ne kawai"
Gira ya ɗaga mata "Allah ko?"
"Baka yarda ba kenan nidai yanxu faɗamin ina kaje?"
"Ina tunatar dake a koyaushe Mansura nifa nake auren ki bake kike aurena ba dan haka inda naje inda zanje duk bai shafeki ba kedai yanzu muje mu kwanta"
Bai jira abinda zata ce ba ya duka ya tallabeta kamar yar baby ya nufi bedroom ɗinshi da ita.

Story continues below



'''*** *** '''
*K'auye...*

"Alhamdulillahi yanzu kan cikina ya cika sosai" Mairo ta faɗa tana gyatsa.
Murmushi Gwaggo tayi "Haba ko kefa yanzu ba sai kiji k'arfi-k'afi ba haka nakeso kullum naga cinki kin k'oshi"
"Ai yanzu ina cin abinci ba laifi"
"Eh ai bance baki ciba amman dai yau kinfi ci da yawa dan rabon da kici abinci haka har na manta"
Mairo zatayi magana wani yaro yayi sallar.
"Assalamu alaikum wai ance ana salama da Mairo"
Mairo ta mere baki.
"Taf lallai ma jeka kace bata nan wani irin sallama yanzu da rana tsaka"
Gwaggo ta kalleta "A'a ba ayi haka ba baki san ko waye ba maza ba a musu wulakanci"
"Kofa wanene ni baza niba yanzu da rana ake fira"
"Saifa kinje ai bakinsan uzurinsa ba" ta kalli yaron "Kai jeka kace tana zuwa"
Juyawa yaron yayi ya fice bayan ya amsa da toh.
Gwaggo ta kalli Mairo "Tashi ɗauki mayafinki kije nace gaki nan zuwa"
Tashi tayi tana turo baki "Amman dai ni gaskiya Gwaggo bana son irin abun nan da kike min ni gaskiya wani karon ba zani ba"
Kai Gwaggo ta ɗaga mata "Eh naji yanzu dai jeki" kamar ta fasa kuka ta ɗauki hijabinta da kwanon da taci abinci ta fice.

Fitowa yayi daga cikin motar. yana sanye da wando pencil black color da blue t-shirt. Jingine yayi jikin motar yana kallon k'ofar gidan.
Da ture-turen baki ta fito suna haɗa ido ya jefeta da wani kyakkyawan murmushi.
Murmushi ita ta mayar mishi cike da fa'ah ta k'araso gurin da yake.
"Lahhh Yaya Qasin daman kaine?"
Murmushi ya sake mata as respond.
"Amman shine baka shiga ba kace ana nemana?"
Kai ya ɗaga mata still yana murmushi.
"Toh mu shiga ciki mana nida Gwaggo duk mun ɗauka ma wani ne Wallahi"
Sai a lokacin yayi magana.
"A'a bazan shiga ciki ba"
"Saboda gurin ki nazo ba ba gurin Gwaggo ba"
"Ni?" ta nuna kanta.
"Eh kefa nazo taɗi ne dan kar wasu su fini zuga su kwace min ke"
K'asa tayi da kanta tana guntse murmushi daya zoma.
Wata irin kunya ce ta baibayeta rungume jikinta tayi kamar mai jin sanye.
Fuskarta Qasin ya lek'a "Toh duk salon k'iyayyar ce kodai baki jindaɗi zuwan nawa bane. daman Abbab yace kince baki sona"
Da sauri ta kalle tana zaro ido "Lahhh ni Wallahi ban ce ba"
"Abbah yace lokacin da akayi miki maganar kuka kika rigayi"
"Eh ba kai nake yima kukan ba ni bana son aure ne kawai" Cike da shagwaɓa tayi maganar tana son yin kuka.
"Maryam...?"
Amsawa tayi ba tare data kalleshi ba.
"Na'am"
"Bakisan Aure sunnan Annabi bace kike cewa bakiso karatunki bai kaiki gurinda Annabi (S. A. W) yake cewa Aure Sunna tace duk wadda yak'i Sunna ta toh baya tare dani. shifa da kanshi yace kuyi Aure ku haifafa dan inyi alfahari da yawanku Ranar Alk'iyama.
Maryam mi yasa baki son Aure? Bakison ki zauna tare dani da Momi. Maryam ina sonki bazan cutar dake ba bazan miki wani abuba please ki yarda dani"
Kallonshi tayi fuskarta na nuna abinda yake zuciyarta k'arara.
"Yaya nifa ba ce bana sonka ba ni ba sonka ne bana yiba Auren ne bana so tsoro nake ji"
"Toh ki daina jin tsoro dan Halilu ya rasu baya nufin nima zan rasu kinji dan Allah ki amince da maganar Aurena Maryam kinji?"
Kai ta ɗaga mishi tana lank'wasar yatsun hannunta.
Ya ɗan daɗe yana fira da ita yana kwantar mata da hankali saida yaga ta soma gajiya da tsayuwar sannan yasa hannayenshi aljihu yace "Nikan bari na wuce kar tsayinki ya k'are ki faɗar min"
Dariya tayi "Toh mu shiga ciki sai mu zauna"
"A'a ni ba zan shiga ba yanzu zan wuce kice dai ina gaidata"
"Da gaske ba zaka shiga ba?"
"Allah bazan shiga ba wannan zuwan naki ne bana kowa ba"
Hannu yasa Aljihu ya ciro kuɗi masu ɗan dama ya mika mata.
Hannu biu tasa ta k'arɓa "Ahh Yaya duka?"
Nan ya sake mik'a mata wasu "Wannan naki ne wannan kuma na Gwaggo kice ina gaida"
Farin ciki ne wanwar a zuciyarta "Na gode Yaya Allah ya saka da Alheri" Murmushi yayi mata yana mamakin hali irin na Mairo watau har yanzu bata daina halinta na son kuɗi ba.
Buɗe Motarshi yayi ya shiga "Na tafi Maryam kiyi min Addu'a"
"Allah ya kiyaya ya tsare na gode sosai"
"Kada ki damu amman fa zanyi kiwarki"
Rufe ido tayi ta nufi gida da gudu.
In banda kallo babu abinda ya bita dashi yana murmushi har ta shige. Haka kawai sai yaji tayi mugun burgeshi.
Ya daɗe yana kallon k'ofar gidan sannan ya tada motar ya kama hanya.

Story continues below



Faɗawa Mairo tayi jikin Gwaggo tana dariya ta nuna mata kuɗin.
"Ahh Mairo ina kika samo wanene yazo?"
Da dariya tace "Yaya Qasin ne Wallahi"
"Wane Qasin dai?"
"Na birni mana na Momi"
"Wai Qasimu kike magana?"
"Eh nayi-nayi dashi yace shi ba zai shigo ba wai guna yazo saidai nace yana gaishe ki"
"Gurin ki kuma?"
"Eh wai shi fira yazo"
"Au" Gwaggo tayi dariya "Sai yanzu na gane hausarki toh Allah yasa ki k'arɓa mashi da ga dukan alamu dai yana sonki kece dai baki sonshi"
"A'a Gwaggo nifa bance bana sonshi ba kune da kuda Abbah kuka ce amman ni bance bana sonshi ba"
"Ah toh kina sonshi kenan yanzu fa amincewarki kawai muke jira da kowa yayi na'am da Auren nan kice kawai ake jira kin amine ko?"
Murmushi tayi ta duk'unk'une kanta cikin hijab ta shige jikin Gwaggo.

*** *** ***

Cikin satin zuwan Qasin uku k'auye duk zuwan da yake bai taɓa yarda ya shiga cikin gidan ba.
Saidai yace yana gaida Gwaggo ko ya aika mata da kuɗi ko siyayyah.
A yan kwanakin nan da yayi yana zuwa sai duk yaji ya hak'u da ita. Ita idan tana tare dashi sai ta riga jinta cikin wani yanayi na daman.
Idan zai tafi har jin take kamar ta bishi har dai zuwanshi na ukun nan daya ɗauketa suka tafi zaga gari.

*Saturday Morning*

Duk zazzaune suke part ɗin Momi suna fira. Kasancewar yau weekend.
Sallamar da Abbah yayi tasa duk suka kalli k'ofa tare da amsawa. Kusa da Momi ya zauna yana amsa gaisuwar da suke mishi.
Nan suka sake dasa wata sabuwar firar yan siyasa. Sai kusan sha biu na rana Qasin ya kalli agogo yace "Bari na tashi akwai inda nake son zuwa"
Abbah ya kalleshi "Qasin baka tambaye ya akayi akan maganar Maryam ba kasan jiya sati ɗaya kenan"
Murmushi yayi "Abbah tsoro nake ji"
"Tsoro sai kace ba Namiji ba" Momi ta faɗa
"A'a bafa irin wannan tsoron nake nufi ba na kar naji mummunan amsa nake nufi"
"Toh ba zakaji ba dan ta aminci jiya da yamma Baba Saminu ya kira yace min yarinya tace ta amince"
Wani kalar murmushi ne yazo ma Qasin ya kasa ɓoye farin ciki shi sai dariya yake haka kawai yaji wani irin jindaɗi ya mamaye shi bakinshi har kunne ya kalli Abbah "Amman na jindaɗi Wallahi Allah ya tabbatar da alheri banyi tunanin zata amince ba"
Usman ya kalleshi yana dariya "Ashe yaya kana sonta"
Harara ya watsa mishi ya kawarda kai.
Siraj ya dafa shi yana murmushi "Congratulations Bros Allah ya saka albarka a ciki"
Duk suka amsa da 'Amin' suna dariya.
Siraj ya ciro wata takarda cikin aljihu shi ya mik'awa Abbah yana faɗin "Abbah nafa samu transfer"
"Transfer?" Duk suka kalleshi da mamaki.
Abbah ya karɓa yana tambaya "Zuwa ina kuma?"
"Abuja suka mayarda ni Abbah"
Qasin ya kalleshi fuskarshi da ɗan damuwa "Amman dai gaskiya ban jindaɗi ba anya zaka iya zama can kuwa?"
"Zan iya mana ai transfer tazo a daidai dan daman na gaji da garin nan"
Abbah yace "Toh Allah yasa haka shine mafi alheri"
"Amin Abbah nima haka nake rok'o"
Momi dai uffan bata ceba saidai tunda ya faɗi maganar yanayin ta ya chanja.
Har suka gama tattauna akan maganar transfer bata ce k'ala ba saima tashi da tayi ta bar gurin.

*© KHADEEJA CANDY*
[10:45AM, 3/28/2017] Khadeeja_ce👌: *♡... MAIRO ...♡*

*BY*

*_KHADEEJA CANDY_*
Candynovel.wordpress.com

_In Dedication To All Members of MUSHA KARATU._

*56*

Tashi Siraj yayi bayan kowa ya watse ya nufi ɗakin Momi.
Tunda ya tura k'ofar ɗakin gabanshi ya soma faɗuwa ganin har lokacin fuskarta na ɗauke da alamun damuwa. Cikin sanyi jiki ya k'arasa kusa da ita ya zauna gefen gadon.
"Momi baki ji daɗin transfer ɗin tawa bane?"
Momi kamar tana jiran shi ta juyo ta fuskance shi "Taya zan jindaɗi transfer ka Siraj. akan mi zaka nemi ayi maka transfer.? nasani kaine ka nema".
Shiru yayi sm baya son ya k'aryata ta dan bata faɗi k'arya ba saidai kuma baya son ta gane da gaske shi ne ya nemi a yi mishi transfer ɗin
"Momi bafa ni kaɗai akayi ma ba.
akwai wasu guraren da ake buk'atar likitocin shiyasa. Kuma Momi cigabana ne naje asibitin Abuja aiki"
"Ba cigban ka bane bana so Siraj kawai dai bana son kayi nisa da nine.
bana da wadda nake shawara dashi irinka bana sakewa da kowa kamar yadda nake sakewa da kai Siraj"
"Momi baga yaya Qasin ba koda bana nan kinga shi yana nan kuma bafa wata k'asar zanje ba ina nan cikin arewa duk lokaci-lokaci zan rik'a zuwa ina ganinki i promise you"
Bata ce mishi komai ba sai idonta suka cika da k'wallah.
Ganin tana son yin kuka yasa ya tashi da sauri ya bar mata ɗakin.

*Bayan wasu kwanaki...*

Momi na zaune saman dining suna breakfast ita da Siraj da Usman dan Nura tuni ya wuce makaranta.
A gaggauce Usman ya k'are ya tashi "Momi na tafi amana Addu'a muna da exam mai zafi"
"Ai Addu'a kullum cikin yi muku ita ake Allah ya bada sa'ah ya tsare"
"Amin Momi"
Ya kalli Siraj "Yaya na wuce"
"Toh Allah ya bada sa'ah"
"Amin thanks"
Saida ya kai bakin k'ofa Momi ta kira shi "Usman"
Juyowa yayi "Na'am Momi"
"Ka kira min Qasin kamin ka wuce"
"Ok toh"
Bayan ya fice Momi tayi ma Siraj kallon natsuwa tace "Ya kamata ka fitarda matar aure Siraj, zai rage maka wasu abubuwan"
'Bata fuska yayi "Wai Momi mi yasa kike damuwa da maganar aure nane?"
"Ina son kayi auren ne Siraj banga dalilin da zaisa kayi ta zama babu aure ba"
"Zanyi Momi har yanzu ban samu wace tayi min bane"
"Kullum haka kake faɗa wai miyasa kake wasa da lokacin kane?. Mutuwa da lokaci wasu abubuwa ne da in har suka riga suka wuce ba zasu sake dawowa ba karasa su kenan"
Baice mata uffan ba ya juya ya kalli k'ofa tare da amsa Sallamar da Qasin yayi.
"Amin wa'alaikassalam"
Kujera yaja ya zauna yana yima Momi gaisuwa "Momi ina kwana?"
"Siraj"
"Na'am yaya ina kwana?"
"Lafiya kalau"
Kofi yaja ya shiga haɗama kanshi tea yana faɗin "Usman yace kina son ganina"
"Eh Jiya da dare Abbah ku ya kirani yace na faɗa maka inka shirya inya zo wannan week ɗin sai kuje k'auye ayi maganar ɗaurin aure dan yana son yaje Spain a duba lafiya shi kuma baya son ayi ɗaurin auren bada shi ba"
Saida ya kurɓa ruwan tea ɗin sannan ya kalleta
"Nika a shirye nake ko shekaranjiya da naje Gwaggo take cewa wai yaushe za'a ɗaura auren nan ne ta huta.
itama Maryam ɗin tana so dan tayi min magana. tana son ta dawo nan da zama"
"Gyara maganar ka ta dawo gidanka da zama dai nikan ba gidana ba wannan karon zaman aure zata zoyi ba, zaman gidana naba"
Murmushi yayi "Amman Momi ai dole nan zata fara zama"
Siraj ya kalleshi "Amman dai ba anan zata zata tare ba ko?"
"A'a sabon gidana zan zauna dasu gaba ɗaya"
"Ok nifa nina ganin Monday nan zan wuce dan sun matsa min"
Ajiyar zuciya Momi ta sauke "In dan ka tafiyarka Qasin ya tare da matan shi.
shi kenan kun barni da kaɗaice da kewa daman Usman da Nura ba zama suke yi"
Idonta cike da k'wallah tayi maganar.
"Haba Momi miye na wannan maganar? Sai kace wa yanda suka rabu har abada.
Shi kenan in na koma Abuja Qasin ya tare gidan sai mu kyale ki kula zamuyi dake wace tafi wanda mike miki yanzu"
"Uhmmm" Kawai Momi tace ta tashi ta nufi ɗakinta.
Dafe kai Siraj yayi ya zauke ajiyar zuciya. Can kuma ya tashi ya fice.

******

Cikin shigar alfarma yake yana zaune driver seat sai kamshin turare yake.
Ba k'arya koni na yaba da kyau da yayi yau. driving yake hankalinshi kwace yana shan sauti har ya isa.
Gurin da ya saba parking yayi wato k'ark'ashin ice bedi.
"Kai zo nan" Ya kira wani yaro da yazo wuce wa"
Da gudu yaron yazo ya duk'a har k'asa ya gaishe shi. Bai amsa ba yace "Jeki can gidan kace ana kiran Maryam"
Tashi yaron yayi da sauri ya shiga gidan.
Bai daɗe ba ya fito yana faɗin "Wai ance gata nan zuwa"
Kai kawai ya ɗaga mishi ya ciro 1k ya mika mishi. da sauri yaron ya karɓa yana godiya ya auna da gudu.
Fitowa yayi ya jingina jikin Motar yana bin hanyar da yaron yabi d kallon.
3 minutes later ta fito sanye da dogon hijab.
Tsaye tayi tana kallon shi kamar mai mamaki ko kuma jin tsoro.
Ganin ya kalleta yasa ta k'arasa kusa da shi tana ɗan murmushi "Ina wuni?"
Murmushi shima ya mayar mata "Lafiya kalau ya gida?"
"Lafiya kalau"
Ido ya sakar mata still yana murmushi "Kin min kyau yau kamar na sace ki na gudu"
Dariya tasa mishi "Ai ba zaka iya sace niba"
Murmushi yayi "Allah ko hmmm baki sanni ba jina kike.
ai sace ki abune mai sauki"
"Koma ka sace ni ka kaini ina ai ni bana satuwa"
"Na kaiki birni mana inda kike son zama ciki mai kyau ki sha mai daɗi"
Dariya ta sakeyi "Ai nima na kusa zuwa birni"
"Da gaske? Gidan Momi zaki zauna?"
"Eh da an ɗaura mana aure da Qasin zan tare can har a bada sai dai nazo nan ganin gidan"
Nan da nan murmushin dake fuskarshi ya gushe da sauri ya riko hannunta "Maryam kake min wasa kinsan bama irin wannan wasan ko? Faɗa min mikike nufi Qasin zaki aura?"
"Eh Wallahi shi zan aura"
"Yaushe yace yana sonki?"
"Tun da daɗewa ya aiko Abbah ya tambaya mishi aurena kuma akace an bashi"
Ya haɗe rai kamar bai taɓa dariya ba fuskarshi kuma kamar bak'in hadari.
Hannunta dake ciki nashi ya matse iya k'arfinshi "Mi yasa baki faɗa musu baki sonashi ba?"
Kamar ta fasa kuka ta shiga k'ok'arin kwatar hannun tace "Ai ina sonshi sake min hannu da zafi"
Wani wawan mari ya watsa mata da hannun hagu kuma gefen da zobbansa suke.
Ba itaba kashi saida hannunshi yayi zugi balle ita da aka mara a fuska.
Aiko nan da nan sai jini gefen fuskarta yayi kumburi ijiyarta ta rine da ja sakamakon ɗan yatsanshi daya shigar mata ido.
Wata irin mahaukaciyar k'ara ta saki tana kallon jinin daya zubo har a hijab ɗinta. Tureta yayi da karfi ta faɗi.
Aiko da gudu ta tashi tana kuka ta nufi gida.

Tana shigewa gida shima ya buɗe Motar shi ya shiga.
Driving ya rik'ayi da gudun tsiya. ya rike sitarin Motar da k'arfi. Ya haɗe rai kamar bai taɓa dariya ba sai faman buɗan hannta yake.
         Cikin yan mintuna ya isa gida. Kamin a buɗe mishi gate ya danna horn baji ba gani kamar zai tada gidan.
Da gudun mai gadin ya buɗe. Wani mahaukacin parking yayi ya fito ya nufi parlor Hajiya.
Da k'arfi ya banko k'ofar parlor ya shigo Hajiya na zauna ita da k'awarta suna fira yanayin yadda taga fuskarshi tasan ba lafiya da sauri ta tashi tsaye.
“Lafiya Yusuf?"
hak'oranshi ya haɗe ya ɗantse gam sannan ya bata amsa.
“Ba lafiya ba lafiya ba"
      Hajiya tasan sarai zai iya faɗar komai a gaban k'awarta.
duk da yake aminiyarta ce amman kuma ɗa da uwa sai Allah, hakan yasa ta rik'a hannunshi suka nufi ɗaki.
          K'ok'arin zaunar dashi ta shiga amman yak'i saima fisge hannunshi da yayi daga rik'on da tayi mishi.
Kallonshi tayi fuskarta ɗauke da damuwa da kuma mamakin abinda ya ɓata mishi rai har haka.
“Wai miya faru ne Yusuf waya ɓata maka rai haka ne?"
   “Kune ku kuka ɓata min rai tun yaushe yake bibiyarku akan kuje ku nema min aure Maryam amman kuka k'i toh gashi nan yanzu Qasin zai Aure ta"
Shiru Hajiya tayi kamar wadda ruwa ya canye.
can ta sauke ajiyar zuciya tace “Alhamdulillahi Allah ya karɓa Addu'a ta"
Da sauri ya kalleta “Kinji mi nace kuwa?"
Faɗa Hajiya ta rufe shi dashi.
    “Naji Yusuf naji wai kai har yaushe zaka san ciyon kanka ne yaushe zaka san abinda ya dace dakai da wadda bai dace ba.
Ina mamakinka Yusuf Namiji kamar ka mai ilmin da wayewa da arziki da mulki da isa da Sarauta da kamala.
          ta ko ina Allah yayi maka baiwa amman ka lashi takobin kai sai ka Auri yarinyar da bata san A ba bari B yarinyar k'auye, k'azama, yar k'aramin gida,  kuma k'aramar yarinya.
Kai ko kunya baja ji aganka da ita a matsayin mata?
   a family nan taya zaka nuna ta ko gun abokanka ma ai abin kunya ne.
Auren nan ni mahaifiyarka bana so haka mahaifinka shima baya so.
   toh akan mi zaka nace sai ita daga gamon tsintsiya da ragga.
Toh bazaka Aure ta dan bata dace da kai ba daman na daɗi ina rikon kada Allah ya haɗa Auren nan"
     Kai ya gyaɗa mata “Fine Addu'arki ta k'arɓu na rasata. Ku kuma kin rasa suruka har a bada!"
    “Mi kake nufi?"
Juyowa yayi ya fuskance ta.
    “Bazan Auri wace nake soba saboda na rasata. Dan haka bazan taɓa Auren wace kuke soba sai dai na Mutu banyi Aure ba"
Yana kaiwa nan bai jira abinda zata ceba ya kaɓa rigarshi ya fice.
   Faɗuwa Hajiya tayi zaune saman gado tafe da kai tana faɗin.
        “Innalillahi wa inna-ilaihi raji'un ya Allah ka shirya min wannan bawa naka ka sassauta mishi wannan Zuciya"

          **********

Abbah ne ya fara shiga tare da kawunshi Momi na baya ita da Qasin.
Gwaggo ta fito daga ɗaki tana amsa sallamar.
“Amin wa'alaikumussalam ah'ah marhaban da manyan bak'i harda kawu"
Komawa tayi cikin ɗakin ta ɗauko sabuwar tabarma ta shinfiɗa musu.
“Bissimillah Kawu ga tabarma ku zauna"
Ta kalli Momi “Ah Hajiya sannu da zuwa Qasin mu?"
Ya amsa yana k'ok'arin zaunawa
     “Na'am Gwaggo ina wuni?"
     “Lafiya kalau ya hanya aikan kumsha rana wannan k'walele"
   “Gaskiya kan ana rana kwanakin nan gari kamar zai kama"
Faɗar Kawu.
Abbah yace “Har dai nan arewa gaskiya ana buga zafi sosai"
    “Zafin bana kan ai saidai hamdalla"
Momi ta faɗa tana firfita da gefen mayafinta.
Tashi Gwaggo tayi ta ɗauko musu fura tare da bulbulo ruwan tulo mai sanyi ta aje musu,
   Abbah ya ɗauka ya mik'awa Kawu saida ya sha sannan duk suka sha.
Aka ɗauko sabuwar firar yaushe gamo.
   
_2:02pm..._
Momi na k'are Addu'a sallame sallah Gwaggo ta kawo mata wake da shinkafa.
“Ga naki Abincin kici su kuma ga nasu can in sun dawo"
Murmushi Momi tayi “Sannu Gwaggon yara ba'a gajiya?"
  “Gajiya da mi kin jiki da wata magana"
    Momi ta k'arayin murmushi a karo na biu “Toh Allah ya biya.
   wai nika Gwaggo nace banga Maryam ba tunda nazo"
  Gwaggo tayi dariya.
“Maryam yar gidanki ai yanzu ta daina zama nan tunda abin nan na faru ta koma gidan Hindatu". _(k'aunar Gwaggo)_
  “Wani abin ne ya faru?"
Cike da son sani Momi tayi mata tambayar.
       Gwaggo ta gyara zama.
   “Wallahi rannan ina zauna tsakar gida na faɗa miki ta shigo min da baki duk jini,
Fuska kuma a kumbure sai kuka take wai Yarima ne ya fasa mata baki"
Momi ta zaro ido “Yarima kuma mi tayi mishi?"
   “Bata mishi komai ba kawai dai tace dan ta faɗa mishi Qasimu zai Aure ta shine fa yaji haushi ya mareta"
     “Daman yana zuwa nan ne?"
  “Eh can ba'a sara ba yakan zo ni abin ya ban mamaki nace ba ɗan'uwanki bane?"
   “Dan'uwa nane baisan da maganar Auren bane Shiyasa"
  “Ayyah aiko tun lokacin sai duk tabi ta tsorata ta ringa ganin kamar dawowa zaiyi yayi mata wani abin,
Shiyasa sai ta koma can gidan Hindatu da zama"
   Momi zata sake magana su Abbah suka yi sallama.
Haɗa baki suka yi ita da Gwaggo gurin amsawa.
Bayan sun zauna Momi ta labarta musu abinda yake faruwa.
       Mamaki ne ya cika Abbah “Amman mi yasa Yarima yayi haka sai kace marar tunani"
   Momi ta nisa tace  “Yarima kayan Allah kasan Halin shi da zuciya"
   “Toh miye abin zuciya a ciki harda bugu?"
  Gwaggo ta tari numfashin Abbah “Shiyasa ma duk muka k'agu muga anyi bikin nan ta ɗaga daga gunmu zuwa gidan mijinta"
Sai a lokacin Qasin yasa baki.
     “Haka ne kan kuma dan Allah inason da an ɗaura Auren nan na zuce da ita"
   Harara Momi ta watsa mishi “Wannan wane irin abune haka ina ka taɓa jin anyi haka?"
  Kawu yace “Toh ai ba wani abin bane tunda ba budurwace ba kuma ai can zata zauna"
      Abbah ya karɓa mishi “Nima dai haka na gani indai an ɗaura Aure ai ba wata matsa"
“A'a gaskiya bazan yarda ba shikenan
daga ɗaura Aure sai yaje da mata sai dai ka aiko da Mota aje da ita gaskiya muda dangi mu kai ta ɗakinta"
  “Ki daiyi hak'uri ya wuce da matarshi kawai" cewar Abbah
   “A'a ban yarda ba gaskiya"
“Shikenan Gwaggo na amince da an ɗaura Aure zan aiko a tafi da ita da duk mai son zuwa"
    Gwaggo tayi murmushi “Yauwa toh kaga haka yafi Tsoho yasa muku ranar ne?"
   “Eh ansa Ranar Jumma'a mai zuwa yace kuma yace sadaki dubu ashirin"
     Gwaggo ta rik'e baki
     “Dubu ashirin haba dai shiko Tsoho ai ya cika sai kace budurwa"
Murmushi Abbah yayi “Babu komai ai tunda yace yana so"
   “Toh Allah yasa alkhari a ciki"
  Abbah ya amsa da    “Amin kuma mun faɗa mishi bam son komai komai ni zanyi Amaryar kawai za'a kai mana"
    Gwaggo saboda jindaɗi ta sara ina zata saka kanta godiya tayi musu sosai da Addu'ar Alkhari.
Abbah yace
      “Ai babu komai itama ya tace koba Qasin ta Aura ba zan iya mata haka"
   Gwaggo tayi murmushi
    “Ai nasanka alhaji ba daga nan ba indai wannan ne tun muna yara"
   Duk dariya sukasa aka tada labarin k'uruciya.

Story continues below



    Saida yamma liss suka baro garin bayan sunyi biye biyen gidajen dangi.
  A lokoja road Qasin ya sauke kawu sannan ya nufo hanyar nasu gida.
    Part ɗin Momi yayi parking su Abbah na fita shima ya fita ya nufi part ɗin shi cike da farin cikin da baisan dalilinsa ba.
        Yana shiga ya faɗa bath room ya watsa ruwa ya fito ya shiga sallar I'sha, dan Magariba tun a hanya sukayi Momi ce kawai zatayi ramako.
   Bayan ya sallame sallar yana cikin Addu'a Mansura tazo ta zauna saman sallayar tana mashi murmushi.
    Saida ya shafa Addu'ar sannan ya mayar mata da murmushin.
  “Dear na ya akayi?"
“Lafiya kalau dear ina kuka je tun safe?"
Kumatunta ya rik'a ya girgiza “In da kika aike mu"
   “Please nidai faɗa min tun safe fa kuka fita kuma harda Momi da Abbah?"
Janyota yayi ta kwanto jikinshi.
   “Zan faɗa miki amman ba yanzu ba sai nan da kwana biyu mi kika dafa min?"
    “Ni ban dafa komai ba kai nake jira kawo muje muyi takeaway"
   “Hum toh tashi ki shirya muje"
Tashi tayi ta nufi ɗaki ido ya sakar mata harta shige sannan ya sauke ajiyar zuciya.

          _WASHE GARI..._

@9:21am ya shigo part ɗin Momi. Ita kaɗai ya tarar parlor tana zaune tana kallon tv.
Saman mujera ya zauna yana gaishe ta.
“Momi ina kwana?"
  “Lafiya kalau ya gajiya?"
   “Gajiya tabi tafiya Usman yace kina nema na"
“Eh hka ne"
Momi saida ta gyara zama sannan ta kira sunan shi.
“Qasin"
“Na'am Momi"
“Nace ka faɗawa matarka zaka k'ara Aure?"
“A'a Momi ban faɗa mata ba ina dai da niyar faɗa mata ɗin"
  “To ka sanar da ita da wuri dan hak'inta tane ta sani karka ɓoye mata komai"
“Insha Allah Momi zan faɗa mata akwai kayan da nayi oda ina jiran su iso ne"
   “Toh Allah ya taimaka daman shine kawai"
  “Amin Momi na gode bari n wuce office"
Kai Momi ta ɗaga mishi “Adawo lafiya"
Tashi yayi ya fice.

            ***************
   Manyan akwatuna ne ya shigo dasu guda uku light green masu kyau da ɗaukar hankali.
     Tsakiyar parlor ya aje su haka ya bisu ɗaya bayan ɗaya ya buɗe su sannan ya zauna saman kujera yana k'walama Mansura kira.
   Sai da yayi kusan minti biyar dayi mata kiran sannan ta fito ta nufo downstairs.
         “Dear lafiya kake min wannan kiran?"
“Lafiya kalau alkhari ne ya samu"
  Ya bata amsa yana murmushi. “Wannan lefen waye?"
Ta tambaya yayi da ta k'araso kuda da kayan.
     “Ba lefe bane kaya ne danayi miki oda tun dag Dubai sai yanzu suka iso"
Zaro ido tayi “Oh my god" da sauri ta duk'a tana duba kayan.
Bata iya tsayawa ta duba da hankali ba saboda jindaɗi d gudu ta taso ta rungume Qasin.
    “Oh dear you mean so much to me bansan da bakin da zanyi maka godiya ba"
     “You don't have to"
Hannu yasa aljihu ya ciro cak ya mika mata.
   Da hannu biu ta karɓa tana ɗan mamaki.
“One million Qasin for what?"
   “Just for you"
Dariya tayi mai alamar rashin gamsuwa “Qasin i don't understand please kamin kwari-kwari na minene?"
   Janta yayi ya kwanto saman jikinshi bakinshi dai-dai kunne ta yace “Na faɗan kishiya ne AURE ZAN K'ARA!".
Da k'arfi ta ɗago harta buge mishi haɓa.
  “No-no Qasin bamu saba irin wannan wasan da kai ba Please faɗa min kodai wata ksangilar kuka samu ne?"
  Murmushi yayi “Babu wata kwangila sweetheart naki ne wannan Wallahi da gaske Aure zan k'ara"
Tashi tayi tsaye da sauri taja baya kamar wace taga abin tsoro.
   “Kishiya fa kace Qasin kasan abinda kake faɗa?"
    “Da gaske nake mana gani nayi bai kyau na ɓoye miki ba"
Daga gun da take tsaye ta risina k'asan kuiwoyinta tana kuka.
“Qasin mi nayi maka dan Allah ka yafe min in har wani abin nayi maka ban saniba Wallahi zan gyara duk halayena.
zan chanja rayuwa dan Allah ka janye maganar Aure in har da gaske ne"
_Ashe kinsan baki da halin kwarai_ a rashi yake wannan maganar a fili kuma yace “Mansura babu wani dalili da zaisa na k'ara Aure kawai dai kinsan shi Aure sunna ce ta Manzo Rahama kuma ya umarce mu da yinta"
  Hannu tasa ta yaga cak ɗin ta watsa mishi.
     “Aikin banza ni koda na tashi cikin dukiya na tashi dan haka kuɗinka ba sha'awa suke bani ba kuma wannan kayan daka ɗebo ka kawo ka kwashi abinka ka k'ara gaba dan ni koda ka Auro ni gidanmu ba tsirara kaga ina yawo ba.
Da kake maganar Sunnan ai ba Aure ne kawai Sunnan Manzo ba miyasa baka dabbak'a sauran Sunnonin ba sai wannan,
Indai Aure ka Auro uku rana ɗaya kaga mun zama hudu kenan duk a karkashina zasu zauna Wallahi dan na gaba yayi gaba na baya sai kallar dangi.
   Ni zaka wulakanta? Wato ance mogiyar ganga za'a yada kotenta ko?
toh kaje ka Auro yar Sarkin masar ko yar Sarkin Aljannu k'arshe kenan Wallahi wahala duk akan zata k'are
Kuma kai da farin ciki kun raba hanya"
Tana kaiwa nan tasa k'afa tayi shuri ta akwatin takalma.
   Ido kawai Qasin ya sama ta tunda ta soma maganar har ya shige ɗakin ta daman yasan za'a rina.
        Tana shiga ɗakinta ta faɗa zaune saman gado tana ciyon lips.
  Sam zuciyarta tak'i yarda da abinda ta gani ko kuma nace abinda Qasin ya faɗa mata.
_Taya zai k'ara Aure bayan ban taɓa mafarkin Kishiya ba shima kuma bai taɓa min maganar taba koda wasa kai ba gaskiya bane inajin gwadani ne kawai yake son yi. ta ina ma zai iya zama da mata biyu shi da baya son rigima?_
Ajiyar zuciya ta sauke _Kai amman nayi wauta danayi mishi wannan cin mutuncin amman kuma k'ara danayi mishi kodan gaba kar yayi tunanin k'arin Aure da gaske_
    Duk a zuciyarta take wannan tunanin tana faman sauke ajiyar zuciya.

Story continues below



         _9pm_
Bayan Sallar Isha'i Qasin ya shiga ɗakin Mansura.
Kwance ya tararda tana kuka da sauti marar k'ara.
A hankalin ya zauna saman gadon ya kai hannu yana shafa bayanta.
“Dear kuka kike ne"
  Cikin muryar kuka tayi magana.
“Dear please faɗa min gaskiya zuciya tak'i aminta da da abinda ka faɗa min sai dai kuma jiki yana bani kamar haka ne"
  “Wallahi da gaske Aure zanyi kinji kuma na runtse"
  “Saboda mi?"
“Saboda yana Sunnah"
Kanta ta dafe.
  “Inna lillahi wa innnna ilaihi raji'un Qasin wane irin abune ya same ka haka?"
“Babu abinda ya sameni"
“Wace yar iskarce zaka Aura?"
  “Kin santa ai MARYAM CE!"
“Wace Maryam ɗin?"
Ta tambaya cike da son sani"
“Maryam tamu mana ta k'auye"
Tashi tayi tsaye ta nuna mishi hanya
“Tashi ka fice min ɗaki ai daman nasan k'arshen tika-tika-tik kuma ta tsuniyar gizo bata wuce ta k'ok'i.
   nasan zamanta gidan nan bana banza bane ni zayi ma munafurci. daman ras nake kallon ku kuma ga fili ga mai doki.
   Aure ko muje zuwa mahaukaci ya hau kura.
Sai kayi nadamar Auren nan dan haka gara ma tun wuri ka janye k'udirinka"
   “Bazan janye kudirina ba Mansura sai dai kiyi hakuri dan na riga na nema kuma an bani"
   Dariya tasa mishi
  “Ai dole a baka kan dangin matsiyata anga kuɗi ai koda asiri za'a janyo hankalinka ballantana kuma gashi..."
  Tassssssssss ya wanke mata fuska da mari.
Ya nunata da yatsa
    “Ki tsayarda kalamanki dan naga kina k'ok'arin wuce hankalinki kar garin neman gira ki rasa ido"
   Yana kaiwa nan ya juya ya fice.
Faɗawa tayi saman gadon ta fashe da matsanaucin kuka.

       Gabah ta shigayi dashi  duk yadda yaso ya lallasheta k'in bashi haɗin kai tayi sai ma bullo mashi da wasu sabbin mugayen halaye nata data yi.
  A haka ya hak'ura yasa mata ido,
Bata tabbatar da gaske Auren zaiyi ba saida taji ta jishi a waya yana faɗawa wasu abokaninshi.
   Dawowa tayi ɗakinta bayan ta gama laɓen ta dinga safa da marwa.
   “Kan Uba wai da gaske Auren zaiyi kenan duk abin nan da nake mishi ba zai daina ba ko hmmm Wallahi sai ya gane shayi ruwane dan saina gasa mishi giɗa a hannu wannan ai kunyata ni zaiyi duk ɗakin mu ace ni kaɗai mijina zai yima kishiya,
Duk kicihim Momi ne bakar munafuka ita ce take kitsa mishi komai tunda da can ai bai yi tunanin k'arin Auren ba sai yanzu gaskiya ba zan iya juyewa ba naga Qasin da wata ba ni ba dole ne na nemi mafita"
   Ita kaɗai take maganganunta tana rawar kai kamar wata taɓaɓɓiya.

     Nan ta buɗe mishi sabon shafin iya shege,
  Tun abin baya damunshi har ya soma sosa mishi rai.
  Ana sauran kwana biyu ɗaurin Auren shi ya samu Momi yana koka mata akan sabbin halayen da Mansura ta tsiro dasu marasa kyau.
   Momi batayi mamaki ba dan daman tasan ba kirki ne da ita ba,
  “Hak'uri zakayi Qasin daman nasan sai tayi haka koma nace abinda yafi haka tunda daman can ba halin k'waraine da ita ba"
  Qasin ya sauke ajiyar zuciya.
“Allah ni Momi har naji son Auren ya shiga raina"
Momi tace “Toh ai dole ansan kan kishi kumallon mata ne amman wani lokacin mu muke jawa kanmu.
Sai kaji mace da ance za'ayi mata kishiya shi kenan fa ta dingi tada hankalin miji kenan kuma hakan ba zai sa ya daina neman Auren ba saima k'ara chusa kanshi da zaiyi,
  Mata da yawa baza gane in ance mijinki zaiyi Aure ai sai ki ɗinga yi mishi biyyah da nuna mishi so da goyon baya koda a zuciyarki baki son.
sai kiga yaji tausayi wata k'ilama ya fasa Auren ko in yayi yaji bazai iya zalumtarki ba kuma ba zai yarda wacan ta raina ki.
Kuma duk abinda wacan zata faɗa ba zai yarda ba koda gaskiya dan bai gani a zahiri ba,
Amman irin wannan kishin ai ni a ganina k'uruciyace kawai da rashin wayewa"
  Qasin yayi Murmushi.
   “Toh ai Momi ba duk matane suke gane wannan ba"
“Lallai kan sai mai hankali da hangen nesa ko nace mai wayau kai dai yanzu kasa hak'uri zai wuce In'sha Allah dama taga anyi Auren zata saki ai yanzu dan tana cikin zafin ne"
    “Allah yasa"
“Amin ka ci abinci?"
    “A'a"
“Toh ga tuwo can kan dining"
Tashi yayi ya nufi dining.
    Plate yaja ya zuba abincin son ranshi.
Ci yayi saida yayi nass sannan ya sha ruwa ya tashi yana hamdala tare da gyatsa. Rabon da yaci abinci ya k'oshi irin haka har ya manta.

Story continues below



   '''**********'''
*_RANAR JUMMA'AH..._*

Tun da safe Qasin ya shirya cikin farar shadda yayi ma jikinshi wanka turare.
D'akin Mansura ya nufo yana taɓa k'ofar ya jita kulle. Kiranta ya shigayi.
“Mansura Mansura buɗe zamuyi magana"
  Ya ɗan daɗe tsaye gurin wai ko zata buɗe amman sam ko motsinta bai jiba bare alamun buɗewar.
    Ganin hakan yasa ya nufo parlor ɗin Momi tsokanarshi Usman da Nura suka ringayi suna ce mishi Yaya Ango.
Sai da ya taka musu burki sannan suka saurara mishi Siraj sai bace komai ban in banda murmushin da yake.
Sai kusan 10 Abbah ya fito suka kama hanya tare da wata tawagar ta yan'uwa da abokanin arziki.

     K'arfe biu da rabi aka ɗaura Auren Qasin da Maryam bisa ga sadaki naira dubu ashirin.
  Ango kan baki har kunne sai gaisawa yake da mutane suna mashi barka, Daga nan suka kwasa sukayi gidan Gwaggo.
Siraj dai tun gurin ɗaurin Auren ya kama hanyar gida bai yarda yazo gidan Gwaggo ba wai a cewar shi yana da wani aikin a asibiti.
    Gwaggo tasha adonta da sabuwar atamba baki a washe sai farinciki take.
   Kayan abincin dake both Abbah yasa aka shigo dasu takeaway da Momi tayi kuma aka rabawa yan ɗaurin Auren.

Mansura wai mi yake damunki kin min waya nazo kuma nazo kink'i yi magana sai kuka kike miya farune"

  Kasa mata magana tayi har saida tayi kukan mai isarta sannan ta tashi ta shiga bathroom ta wanke fuskarta.

       Bayan ta fito ta zauna gefen gadon tana murzar hanci

“K'awata mijina aure zaiyi!"

   “Aure?" ta daki k'irji tare da zaro ido.

“Saboda mi? mikayi mashi?"

    “Wallahi ban mishi komai ba kawai dai ya nace shi sai yayi kinsan mahaifiyar shi bata sona ina ganin itace ta kitsa komi"

   “Subhanalllahi mi yake damun Qasin haka baki buɗa mashi wuta ba?"

“Babu abinda banyi mishi ba amman kamar k'ara zuwa shi nake sai da yayi yau fa aka ɗaura mashi Aure"

   “Amman Mansura kinyi wauta Miyasa baki faɗa tun da wuri ba?"

        “Kunyar faɗa nake ji ace duk ɗakin mu ni kadai mijina yayi ma kishiya kuma bai faɗa min da wuri ba sai ana sauran kwana kaɗan a ɗaura Aure"

   “Taf amman Qasin ya iya cin mutunci wacece matar?"

   “Wata yar'uwarshi ce yar k'auye k'aramar yarinya kuma k'azama"

   Tsananin mamaki ta cika dashi “Yar k'auye Qasin ɗin ne zai Auro miki yar k'auy?"

“Hasbunallahu wani'imar wakin toh yanzu miye abinyi?"

  “Nima ban sani ba shiyasa na kiraki da son nayi na haɗa kayana na bar mishi gidan kawai"

  “A'a karki kuskura yin haka ai in kikayi haka kin k'ara bashi dama kenan kiyi zamanki zanje na samu Mommy zan faɗa mata komai"

Kai ta ɗaga mata.

       “Toh Rahila dan Allah kuyi wani abu bana son ganin Qasin da ko wace mace kuma kinga zanji kunya ace yayi min kishiya"

     “In'sha Allahu zamu san abinyi ki kwantar da hankalinki kawai"

  Maganar Rahira take tana buga kafaɗunta. Ita kuma ta fashe da sabon kuka.


*****

Saida yamma suka ɗauko hanya koda suka iso gida dare ya soma yi.

D'akinshi ya wuce ya watsa ruwa ya fito ya shirya cikin k'ananan kaya ya sake ɗaukar keys ɗin motar shi ya fice.

    Bayan kamar mintu arba'in ya shigo rik'e da ledodi ya nufi ɗakin Mansura,

   Yana shigowa ta tashi tsaye da sauri idonta sunyi kumburi sunyi ja “Ba nace karka sake shigo min ɗaki ba?"

K'arasowa yayi ya aje ledar ya rungume “Mansura kina wahalarda kanki nifa ba cutarki zanyi ba banyi Auren nan dan na wulakanta kiba"

   Rigarshi ta rik'e da k'arfi “Qasin da gaske an ɗaura maka Aure yau? Da gaske Aure kayi?"

   Saida ya sauke ajiyar zuciya sannan yace “Anyi Mansura yau na zama mijin macce biu"

Rushewa tayi da kuka ta sulale k'asa zata faɗi.

     Da sauri ya ɗauketa ya ɗora saman gado yana lallaɓata.

   Wani irin shure-shure ta shigayi tana murzar gadon kamar mahaukaciya. Tun yana iya bata hak'uri har ya gaji ya taso ya baro mata ɗakin.


     

   _Washe gari..._

Tun da safe Qasin ya tura mota da direba k'auye.

Bai koma part ɗin shi ba ya nufi part ɗin Momi. Kitchen ya tararda ita ita da wasu suna aikace-aikace,

  “Momi good morning har kin tashi?"

  Murmushi Momi tayi “Ai dole na tashi tunda Amarya za'a kawo mana Abbah kan tunda safe ya aika Usman da mota wai yaje ya ɗauko ta"

    Qasin ya rik'e baki “Oh aiko za'asha bam-bam dan nima na aiki Hafizu da Mota"

  “Da safen nan?"

“Eh yanzu-yanzu bari na kira shi nace ya dawo"

  “A toh kirashi gaskiya tun baiyi nisa ba"

  Da sauri ya fitarda wayarshi ya shiga danna kira.


Story continues below


***


               Saida ya gama breakfast sannan ya dawo part ɗin shi,

Bedroom ɗin shi ya shiga yayi wanka ya shirya cikin shadda brown color. Da takalmi bak'ak'e ya ɗauki hula itama the same color da shadda yasa ya feshe jikinshi da turare ya nufo ɗakin Mansura.

  D'aukar numfashi ya tararda tanayi idanunta a kafe tana matsar yatsunta.

Da gudu ya k'arasa yana kiran sunanta,

   “Inna lillahi wa innnna ilaihi raji'un Mansura"

  D'aukarta yayi da sauri ya fice daga ɗakin. A Motashi. yasa ta ya nufi asibiti.

Yana isa aka cewa da ita emergency safa da marwa ya ringayi a bakin kofar ya ciro wayar shi ya sanar da Momi da yan gidansu.

  Cikin yan mintuna suka iso cike da tashin hankali bayan isowarsu da minti talatin Momi ta iso ita da wasu k'awayenta.

  Da sauri ya tareta “Momi kin iso?"

  “Eh ya jikin nata?"

“Da sauk'i alura akayi mata bachi take yanzu"

   Kujera Momi ta nufa ta zauna tana gaisawa da yan'uwan Mansura.

  Wata sister Mansura ta kalli Momi tace “Ance ɗanki yayi Aure"

Momi ta kalleta dan tasan gatsa mata magana ne tayi

    “Eh jiya aka ɗaura Aure Amaryar ma tana kan hanya"

  Momi ta mayar mata da amsa tana ɗan hararar ta.

    Shiru tayi bata sake cewa komai ba har na wani lokaci

Can Momi ta tashi tana faɗin “Tunda abun da sauk'i ni bari naje gida kar su iso su tararda gidan ba kowa"

   Kai Qasin ya ɗaga mata “Okey Momi"

Sallama Momi tayi musu sannan ta fice.

   Har gun Mota Qasin ya rakata daf da zata shiga mota tace mishi “Sai fa kayi hak'uri da yan'uwan nan nata dan tama ta kishi suke dan haka karka kula su"

     “In'sha Allahu Momi ni miye nawa ma na biye mata"

  Shiga tayi motar ya rufe mata direba yaja suka fice.


_4:30pm_

Suka iso da far'ah Momi ta fito tana taron su.

Gwaggo ta fito Mota tana k' arewa gidan kallon “Oh Allah mai haɗin zumunta ban taɓa zuwa gidan nan ba sai yau daman haka gidan naku yake aljannar duniya"

    Himdatu tace “Shi yasa Mairo take son zama nan ashe da gaskiyarta tasan daɗin da take ji"

   Momi tayi murmushi

“Wai nikan zaku shigo ne ko sai kun gama kallon gida?"

  Hannu Momi ta kai ta riko hannun Mairo dake sun-sun da kai ta nufi kofar parlor “Nidai naja yata in kunga dama saiku shigo"

   Dariya sukayi sannan suka kunno kai cikin gidan.

    Abinci kala-kala Momi ta jera musu k'asan carpet nan suka baje hazarsu sai da aka kira Magariba sannan suka tashi,

     Sai bayan sallar I'sha Abbah ya shigo suka gaisa nan ne Gwaggo take tambayar Qasin'

   “Wai nikan nace ina Angon ne tunda muka zo ban ganshi ba?"

Momi tace “Wallahi yana can asibiti aina kira shi na faɗa mishi yace likitan ne yace ya tsaya ya zo da matarshi dan taji sauki"

    “Daman bata da lafiya ne?"

   Gwaggo tq tambaya

  “Lafiyar kalau kishi ne kawai ya motsa ta ɗinga ɗaukar numfashi shine  ya kaita asibiti amman dai yanzu ance sun da sauk'i zata ma iya dawowa gida"

“Oh daman kishi ne da ita har haka?"

   “Kishi ma kuwa ai sai dai ace Allah ya sauwak'e kawai"

Abbah ne ya kawarda maganar ta ya tado wani labarin.


***        ***      ****

Sai kusan sha ɗayan dare suka dawo bayan mahaifiyarta ta haɗata da yan'uwanta biyu wai su kula da ita.

  Da kanshi ya kaita ɗakin shi ya haɗa ruwan wanka sukayi wankan tare,

  Bayan sun fito ya saka mata kayan bachi sannan shima ya saka ya kwanta kan gado rumgume da ita yana aika mata da sak'onni.


    _Washe gari_

  Sai goma da rabi ya shigo part ɗin Momi duk zaune ya tararda su suna kallo.

  Haka ya samu kanshi da jin kunyarsu ɗaya bayan ɗaya ya bisu yana gaisarwa.

   “Momi ba kuje kuka duba mata na bafa"

   Yana k'ok'arin zaunawa yayi maganar.

  Momi tace “D'azun naso muje sai kuma nace k'ila baku tashi daga bachi ba"

   “A'a mun tashi tun ɗazun take tambayarki"

Gwaggo dai kallonshi take tana mamakin yadda yake ta matarshi ko Mairo bai tambaya ba.

  Momi ta tashi tana faɗin “Ku tashi muje mu duba ta"

Duk tashi sukayi suka Momi na gaba suna baya suka nufi part ɗin.

   Suna fita shi kuma ya tashi ya hau sama.

“Maryam... " ɗakin Momi ya shiga yana kwala mata kira

Jin motsin ruwa a bathroom ya tabbatar mishi da wanka take. 

  Zaunawa yayi yna kallon gown ɗin dake gefen shi da alama ita zata saka.

   Bayan kamar minti biyar ta ɗaura tawul ta saka hijab ta fito.

tana ganinshi ta ɗanyi murmushi “lahh Yaya"

Bai amsa ba ya tsareta da ido har ta ɗauki rigar ta koma toilet ta saka sannan ta fito,

    Tsaye tayi bakin kofar toilet ɗin tana kallonshi still tana murmushi.

Sai a lokacin shima yayi murmushi ya mika mata hannu alamar tazo, k'arasa tayi saidai bata mik'a mishi hannu ba,

  Fuskarta ya shafa “Ya kika kwana?"

   “Lafiya kalau"

“Kin karya?"

“Eh tun ɗazun"

    “Toh yayi kyau ni ina nawa?"

  Dariya tasa mishi ta juya ta nufi kofar fita.

Tashi shima yayi ya rufa mata baya suka sauko downstairs tare.

    Ganin ta nufi kitchen yasa yayi saurin dakatar da ita

“Ke ni wasa nake miki dawo naci abinci"

  Juyowa tayi “Da gaske"

  “Eh nayi brackfast tun ɗazu wasa bake miki"

    Dawowa tayi ta zauna saman kujera tana murmushi'

   Murmushi ya mayar mata sannan ya fice gabanshi na faɗuwa.


***

       Da gudu suka shigo parlor suna dariya

“Lafiya?"

Mansura ta tambaya

Rahila ta zauna kusa da ita tana faɗin “Kice yar aiki aka kawo miki ba kishiya ba daman akan wannan ce kike tada hankalin?"

“Itace ina kika ganta?"

  “Gata can Garden ai ki kwantar hankalinki k'awata indai wannan ce sai mun lalata Auren sannan mu haɗa da kirsar k'asa"

“Dan Allah ki taimaka min"

    “Karki damu ba dai wannan Maryam ɗince ba yarinyar da Yarima yake so Wallahi saina lalata Auren nan"

  Kvanwarta ta dafa ta “Ni kuma shawarar da zan baki karki kuskura ki sake su kwana ɗaki ɗaya kuma daga yau kullum ita wanke-wanken ki da shara da moping idan tayi miki kallo biyu ki kasheta mari sannan ki riga chusa kanki gurin mijinki dan nasan har gobe Qasin yana sonki"
Shiru tayi  tana ɗan murmushi kamar mai tunani.
_THE JOURNEY IS BEGIN..._👌🏿

CHAPTER 4

Kuka Mairo take sosai kanta na saman ciyar Gwaggo sai yanzu take jin ba daɗi kamar kar su Gwaggo su tafi.
“Kiyi hak'uri Mairo ai Aure haka ya gada"
Da kuka Gwaggo tayi mata maganar tana buga bayanta,
Momi ta mik'a hannu ta rik'ota “Yi hak'uri kinji Maryam ai ba nisa zatayi miki ba duk lokacin da kika so ganin su ai sai a kaiki kuma suma akai-akai zasu rik'a zuwa"
K'ara rushewa tayi da kuka ta kwanta jikin Momi,
Gwaggo ta share hawayen ta ta kalli Momi “Ga Amana nan mun baki ki rik'e ki kula da ita in kikaga tayi ba dai-dai ba ki ɗorata a hanya"
Momi ta ɗaga kai “In'sha Allahu zan rik'eta Amana"
“Toh Allah ya tayaki rik'o ya bata ikon yi miki biyayyah"
“Amin Gwaggon yara"
Momi ta faɗa tana ɗan dariya.
   “Bari naje na dubo girkin can karya kone"
Momi na tashi Gwaggo ta janyo hannun Mairo.
   “Mairo ki rike hajiya Uwa kinji kinga dama can Uwar ki ce barre yanzu dan haka ban saɓa mata ko ta baki umarni ki k'i bi kiji?"
  Kai ta ɗaga mata idonta a kumbure
   “Kuma bari kiji na faɗa miki duk kikaga Qasimu yayi miki wani abu da baki so ko matarshi toh ki faɗa mata dan naga sunan wannan matar kuma karki saurara mata duk tayi miki can mutunci Ki mata Idan kuma ta nemi zaman lafiya toh ku zauna da tayi miki wani abu Ki fada ma maman shi in kikaga bata ɗauki matakiba ki bugo min waya"
   Nan ma kan ta ɗaga
“Kuma ki bi mijinki sau da k'afa banda rashin kunya duk huɗubar da nayi miki karki zubar da ita"
   “Toh Gwaggo amman dai zaku k'ara zuwa ko?"
  “Zuwa ai dolene Mairo dole ne na rik'a zuwa ina ganin yadda zamanku zai kasance dan naga wannan matar tashi ba kirkirne da itaba koda yake naga kowa gidan shi daban (Part)  dan jiya ya kaimu munga gidan"
   Kwantawa tayi jikin Gwaggo tana shan majina

***
      Kwance take saman jikinshi suna kallo,
  “Dear"
   “Na'am"
“Amman dai ba zaka raba mana gida da ita ba ko?"
Cike da mamaki ya kalleta “Miya kawo wannan maganar kuma keda baki son maganar ta?"
  “Ba komai kawai dai naga hakan zai sa na ɗan rage abinda nake ji a kanta"
   “Toh Allah yasa ni daman banida niyar raba muku gida"
    “Toh Allah ya haɗa kan mu"
   Da mamaki yace “Amin dear Allah ya cigaba da shirya min ke"
Ya faɗa yana shafa saman kanta.
         Sun daɗe a haka sannan ya tashi ya shiga bathroom.
Wanka yayi ya shirya cikin k'ananan kaya ita kuma har lokacin tana kwance.
Kiss ya mana mata ya fito ya nufi part ɗin Momi,
Koda ya shigo ya tararda su Gwaggo parlor driving na saka musu kayansu both
   Saida ya gaida su sannan ya zauna kusa da Momi yana kalln Mairo “Mi akayi mata?"
   “Ba mata komai ba wai dan zasu tafi take kuka"
   Murmushi kawai yayi bai sake cewa komai ba har aka k'are saka kayan.
   Sallamar k'warai Qasin da Momi sukayi musu daman Abbah tuni yayi musu tashi sallamar dan tun washe garin zuwansu ya wuce Abuja.
   Har motar su ta tashi Mairo bata daina kuka ba daker Momi ta lallaɓata tayi shiru.
   “Haba ko ke fa amman tun ɗazu kukan nan ne kawai kike kinsan kuka fa baya da kyau"
    “Toh Momi ba na daina ba"
   “Yauwa toh nima ba gashi na jindaɗi ba Allah yayi miki albarka"
  “Amin Momi"
  Qasin ya ɗan murmusa “Maryam tashi kije kiyi wanka mai ɗinki na nan zuwa ta auna ki"
  Da sauri ta tashi ta nufi upstairs.
Momi ta k'ara mata “Kuma kici abinci"
Daga can ta amsa da “Toh"
   Tashi yayi yana faɗin “Nima bari na lek'a office"
    “Ok sai ka dawo"
Hannayenshi yasa aljihu ya fice.
    
      Sai goman dare ya dawo gidan.
Kai tsaye part ɗin Momi ya nufo hannun shi rik'e da bak'ar leda.
    A parlor ya tararda Mairo zaune sqman doguwar kujera idonta na akan tv.
“Ke aljana dare ne ranar kallon ki ko?"
Da sauri ta kalli k'ofar
   “Yaya har ka tsorata ni Wallahi"
  Zaunawa yayi kusa da ita “Allah ko?"
Murmushi tayi “Eh mana ina wuni"
   “lafiya kalau mai ɗinkin tazo?"
“Eh tazo Yaya ashe ko'ina aunawa take"
  “Eh mana saboda kar ɗinkin ya matseki ko yayi miki yawa"
Yayi maganar yana k'ok'arin bude ledar
  Cinyar kaza ɗaya ya ɗauka ya mika mata ledar da gorar yagot
  “K'arɓi ki ci dan nasan baki ci abinci ba kuka kika wuni kinayi ai yau sai kinyi mafarki su"
   Dariya tayi “A'a ba zanyi mafarki su ai sun riga sun tafi"
  “Ko sun tafi sai kinyi mafarkinsu"
.  “A'a Allah ba zanyi ba"
   “Toh mu k'ulla in kikayi mafarki su saina miki horo"
   “Eh na yarda amman ni kuma in banyi mafarki su sai na maka horo ka yarda?"
  “Eh na yarda yarinya gobe zaki yabawa aya zak'inta"
   Dariya tasa mishi “Kai dai zaka yabawa aya zak'inta zaka ji jiki"
    Dariya yayi sosai harda kwantawa a kujerar “Lallai yarinya nime zanji jiki? Zaki dai ji jiki idan ranar jin jikin tazo"
   Hannu ya kai kan ledar da sauri ta tashi tare da ledar “A'a Yaya ka ci naka fa wannan nida Momi zamuci"
    “Ai Momi bachi take kuma yayi miki yawa ba zaki iya cinyewa ba"
  “Wallahi idonta biu tana ɗakinta"
  Tashi tsaye yayi da sauri “Da gaske Momi ba tayi bachi ba?"
Gira ta ɗaga mishi as respond tana murmushi.
   Da sauri ya fice yana kallon stairs.

Story continues below



       _Washe gari_
   Tunda akayi sallar A'suba Mairo ta dawo parlor ta zauna sai rabon ido take can kuma ta tashi ta kunna tv.
   7 da yar mintuna Momi ta sauko k'asa da sauri Mairo ta risina ta gaisheta “Momi ina kwana"
Momi tayi murmushi “Lafiya kalau an dasa dag inda aka tsaya kan kallo ko?"
   “A'a Momi daman wannan film ɗin nake so kuma sun k'are"
“Toh muje kitchen a hada breakfast"
Remote ɗin dake hannunta ta aje suka nufi kicin ɗin tare.
   Aikin kawai suke amman hankalinta na wani guri da taji motsi sai taje ta lek'a.
Kacar taga sun gama aikin ta ɗauko ta kawo saman dining,
    “Momi naje na kira Yaya Qasin?"
Momi ta aje kula tare da kallonta “A'a ai kinsan ba nan yake breakfast ba"
  Ta marairaice fuska “Dan Allah Momi daga yau bazai k'ara ba wani abu zan faɗa mishi"
    “Indai wani abun zaki faɗa mishi jeki amman breakfast kan ba nan ba"
    "Toh"
Da gudu ta juya Momi ta kwala mata “Maryam zo ki ɗauki ɗan kwali"
“Toh bari nazo"
Momi ta girgiza kai “Oh Allah ya shirya"
   Da gudu ta faɗo parlor Mansura bata lura da Qasin dake tsaye jikin windo ba ta nufi k'ofar ɗakin shi.
“Ke..."
Da sauri ta juyo suna haha ido ta gaidashi
“Ina kwana?"
   “Lafiya kalau an tashi lafiya"
  Ido ta ɗan sakar mishi sanye yake da gundun wando mai kamar na bachi jikinshi babu riga.
   Kasa tayi da kanta ta juya ta nufi k'ofar fita.
Gudu yayi ya kamota “Ina zaki?"
   “Yaya jikinka babu tufafi"
   Kallon jikin nashi yayi sannan yaja suka zauna saman kujera.
    “Miya kawo ki nan?"
Fuskar zolaya tayi mishi tana dariya “Banyi mafarki su ba"
   Hancinta yaja yana murmushi “Oh kedai faɗamin gaskiya  Dan nasan fa sai kinyi mafarki su"
  “Banyi ba ai na faɗa maka sai kaji jiki"
  Dariya yayi ya rumgume ta Yana faďin “Wai ke baza kibar cewa sai naji Jilin nan ba ko?"
Wani yarrr taji kamar an tsoketa da alura. Duk tsigar jikinta ta tashi.da sauri ta ɗago tana kallon fuskarshi,
  Bai kula taba ya sake maida ita cikin faffaɗan k'irjinshi ya rumgume ta tsam-tsam.

      Can zuciyashi ta yayo mishi Mansura dake bachi.
ba zai iya da matsifar taba duk da yasan ba haramun ya aikata ba amman yasan in yanzu ta tashi daga bachi ta gani ba k'aramar drama ra'ayiba.
D'agota yayi “Momi ta haɗa breakfast?"
  “Eh tare mukayi amman tace karka zo wai ba nan kake breakfast ba" Ta bashi amsa idonta a kulle gam.
  Murmushi yayi “Toh jeki gani nan zuwa"
Saida ta sauka saman jikinshi sannan ta buɗe idon ta fice.
      Koda ta dawo ta tararda Momi na break ita Usman da Nura kujera taja ta zauna tana murmushi.
   Batayi minti biyar da zaman ba ya shigo sanye da doguwar jallabiya, a kujerar da ya saba zama ya zauna bayan sun gaisa da Momi.
  “Mi zakayi?" Momi ta tambaye shi ganin ya janyo plate
   “Breakfast Maryam tace nazo naci abinci"
Momi ta watsama Mairo harara.
Da sauri Mairo ta kalleshi “Lahhh" ganin babu alamun wasa a fuskarshi yasa tayi shiru ba tace komai ba.
   Sai suka magama cin abinci sannan ta kalleshi “Yaya ni naci yanzu mi zakayi min?"
  Momi tace “Ke kikaci mi?"
Da sauri ya tari numfashinta “Wai abinci take nufi jeko kiyi wanka kamin na tashi sai na faɗa miki"
   Tashi tayi har ta juya sai kuma ta juyo “Wai Momi ina Siraj?"
   “Yana Abuja Asabar ɗin da za kuzo ya tafi da safe yanzu can yake aiki"
    Bata sake cewa wani abuba ta nufi ɗaki.

Bayan su Usman ta tashi Momi ta kalli Qasin a natse tace “Yanzu matsayinka ya canja nauyi biu ne a kanka ko wace dolene ka bata hak'inta ban zalumci shi aure sai anyi hak'uri tun a Mansura ka gani balle Maryam da ba wani wayau ne da ita ba.
Amanace aka baka bana son naji wani saɓani a tsakaninku"
   Sai da ya nisa sannan yace “In'sha Allahu Momi babu abinda zai faru zan rike ta amana zanyi adalci a tsakanin su"
  “Toh Allah ya taimaka ya baka iko kuma bana son tayi zama mai tsayo agurina dan haka kasa himma gurin shirye-shiryenka ku tare"
    “Ai ni banida wani shiri Momi inba kayanta dake gurin ɗinki ba sai kuma kayan ɗakin da Abbah yayi mata oda ne basu iso ba amman nasan cikin watan nan komai zai kamala In'sha Allah"
“Toh Allah ya taimakamin haka nake so Allah Baku hak'urin zama"
Amsaba yayi da “Amin” Ya Tasha ya fice.
Wanka Mairo tayi ta shirya cikin bak'ar abaya.
Sai lek'e-lek'e take har bayan Azahar bata ga Qasin ba ganin Momi na bachi yasa ta nufi part ɗin shi,
    Sallama ta ɗingayi tun daga bakin k'ofar har takai tsakiyar parlor.
   Mansura ta fito kicin “Ke Uban mi kika zoyi part ɗina"
   “Ubaki!" Kai tsaye Mairo ta bata amsa Tana wani turo baki.
Mansura ta daki k'irji “Kan uba ke ni zaki zaga?"
      “Aini ban zage ki ba ke kikace uban mi nazo ni kuma nace ubanki kuma ni bama gurinki nazo ba Yaya nake nama"
    “Aini ban zage ki ba ke kikace uban mi nazo ni kuma nace ubanki kuma ni bama gurinki nazo ba Yaya nake nema"
   K'ofar ɗakin shi Mansura ta nuna mata “Shiga yana nan ciki"
Juyawa tayi ta nufi k'ofar ɗakin.
    Tana shiga Mansura ta rufa mata baya, tana shiga ta cakumo wuyanta “Uban kike zagi?"
Nan Mairo ta marairaice fuska “Ba ubanki ba ba keba dan Allah kiyi hak'uri"
Mansura  bata saurara mata ba ta watsa mata mari.
  Uhu Mairo tasa mata ta fashe da kuka Mansura bata saurara mata ba ta danneta a kasa tana dukan ta har sai da ta fasa mata baki,
     Da gudu Mairo ta baro part ɗin ta nufo part ɗin Momi tana kuka bakin k'ofar parlor ta faɗi tana murje-murje.
   “Wayyo na bani na lalace ta kashe ni wayyo Gwaggo Momi wayyo Allah wayyo Babana"
  Da gudu Momi ta fito tana tambayar ba'asi,
Zaro ido tayi tana faɗin “Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un miya fasa miki baki haka Maryam"
Cikin kuka ta nuna part ɗin Qasin “Mansura ce ta dake ni"
Momi ta rik'a ta “Mi kikayi mata?"
     “Ban mata komai ba wai dan naje neman Yaya Qasin shine tace na shiga ciki yana ɗaki dana shiga sai ta rufeni da duka Momi na shiga uku kasheni zatayi"
    Kai Momi ta girgiza cike da ɓacin rai ta rik'a Hannunta suka suka shiga ciki,
Bathroom Momi ta shiga da ita ta wanke mata bakin da fuska sannan suka fito.
   Waya Momi ta ciro ta danna ma Qasin kira.
    
Yana isowa Momi ta nuna mishi fuskar Mairo tana masifa,
  “Dubi fuskar yarinyar nan kalli yadda matarka tayi mata duka"
   “Duka kuma?" Ya tambaya “Mi kika mata?"
“Ban mata komai ba wai dan naje neman ka"
    Zaunawa yayi saman kujera “Ke kuma Maryam miye na zuwa nemana in banda abinki"
  Momi ta tari numfashi shi “Miya kai wannan wace irin magana ce ko babu Aure tsakanin ku ai zata iya zuwq part ɗinka balle yanzu da take Matarka,
  Yadda fa kake Auren Mansura haka kake aurenta kuma duk hak'in da kasan yana kanka na Mansura haka na Maryam yake kanka.
   Kawai ka takawa matarka birki karta sake dakar min, ya dan amanace agurina ba zan sa mata ido tana dukanta ba tunda ba haihuwarta tayi ba"
    Tunda Momi take mashi faɗan idonshi na kan fuskar Mairo da ta ɗan kumbura.
  Hannu yakai ya taɓa kumatunta. Nan ta saki uhu ta fashe da kuka,
  Momi tace “Kagani ko zafi take ji taji mata ciyo sosai"
   Ajiyar zuciya ya sauke “Tashi muje pharmacy"
  Tashi tayi tana kukan da ban raba shi dana munafurci ba ta shiga ɗaki ta ɗauko mayafi suka fice.
      A pharmacy dak'er ta tsaya aka sa mata maganin sai ihu take tana kiran Abban ta,
     Bayan sun dawo ya kawota part ɗin Momi tare da maganin da aka bata. Da zai fice saida Momi ta k'ara jaddadamishi “Kafa jawa matarka kunne karta sake dukanta dan itama haihuwarta akayi kamar kowa ba sassak'ota akayi ba"
  "In'sha Allahu Momi zanyi mata magana ayi hak'uri"
Kawarda fuska Momi tayi shi kuma yasa kai ya fice.

        Tun daga yanayin shigowarta ta fahimci yana cikin damuwa dan ko Sallamar shi kamar a kasale yayi ta.
Bayan ta amsa ya zauna kusa da ita. “Sannu da zuwa"
  “Yauwa sannu Mansura mi yasa kika daki Maryam mi tayi miki?"
Taɓe baki tayi “Oh an daki yar'gol ko shine kabi ka haɗe rai toh an dake ta ɗin ko zama mata zakayi?"
   Wani kallo yayi mata mai cike da jin haushi. “Bazan rama mata yanzun ba amman duk kika sake dukanta zan rama mata dan ita mutunce kamar ke kuma abokiyar zamanki ce ba yar aiki ko ya ba dan haka karki sake sa mata hannu"
  Yana kaiwa nan ya tashi ya nufi bedroom ɗinshi. Tintsirewa tayi da dariya ta taɓa hannu “Lallai Qasin ni zaka faɗawa haka saboda kayi yar tsakin Amarya? Wato anci moriyar ganga za'a yada korenta ko toh baka isaba wallahi dan kowa yaci tuwo dani miya ya sha kuma indai dukane sai na mata shi sai dai in bata shigo part ɗin nan ba"
Haka ta dinga faɗa ita ka ɗai cikin parlor

Washe gari Mairo k'in cin abinci tayi duk yadda Momi ta lallaɓata k'in ci tayi ita la dole ga mai ciyo a baki.
   Saida Qasin ya shigo ya sata a gaba sannan ta ɗanci ko shi bawani abin kirkiba.

    Haka sukayi ta lallaɓata shida Momi har suka samu ta warke.

   _Ranar Assabar..._
Duk da yake yau ba rabar aiki bace bai hana Qasin fita tun da safe ba,
     Momi ma sha biu na bugawa tasa Mairo tayi wanka saida ta fito sannan itama ta shiga. Koda ta fito Mairo ta ɗanɗasa kwaliyarta ta shirya cikin koriyar atamfa ta cika janbaki a bakinta yayi mata yawur.
   Murmushin jindaɗi Momi tayi daman haka take son ganinta kullum, Hijab Momi ta ɗauko tasa tana faɗin “Karkije ko ina saina dawo kinji na faɗa miki ko?"
  “Eh naji amman karki dade Momi"
  “Bazan daɗe ba danayi gaisuwar zan dawo"
  “Toh Allah ya tsare"
“Amin"
     Har bakin k'ofa Mairo ta rako ta saida ta shiga mota sannan ta dawo parlor.
   Batayi minti 8 da fita ba taji tsayawar mota da sauri ta lek'a ta windo, Qasin ta tsinkaya ya fita daga motarshi ya nufi part ɗin shi.
    Da gudu ta fito ta nufi part ɗin ita. Zauna ta tararda shi yana shan ruwa gora.
  “Yaya sannu da zuwa"
  Saida ya kare mata kallo sannan ya amsa.
  “Yauwa sannu zo nan" Ya mik'a mata hannu.
Ba musu ta mik'a mishi nata hannun ya rik'a ta ya zaunar kusa dashi “Wa yayi miki wannan kwaliyarta?"
  Murmushi tayi “Ni nayi nayi kyau ko?"
   “Sosai ma kamar ba keba"
   Dariyar jindaɗi tayi.
Bakinta ya sakarma ido daga bisani yakai nashi bakin cikin nata.
  Sai da ya tsotse janbakin tas sannan ya yanje bakinshi yana lumshe ido. Tofarda yawu tayi tasa hannu tana goge baki,
“Wai kai Yaya nace ka daina min haka bana so k'azanta nake ji amman kullum sai kayi gashi nan duk ka goge min janbaki"
   Kamar ta rusa kuka tayi maganar tana buga k'afarta a kasa.
    Murmushi yayi “Toh yi hak'uri bari na ɗauko miki janbakin matata ki shafa kina so?"
    “Eh amman babu ruwana in tayi maka faɗa"
   “Ai bata nan ta tafi kasuwa ta siyo abun bak'i zatayi"
   “Toh ɗauko min"
  Tashi yayi rike da gorar ruwan ya nufi ɗakinshi kayan dake jikinshi ya rage ya koma daga shi sai rigar shan iska sannan ya fito ya nufi ɗakin Mansura.

Story continues below



   Kale-kalenta ya kai idonta kan cake ɗin dake gefen kujera.
Ta sauri ta tashi ta nufi gurin daman tun dazu take jin k'anshi.
   D'aya ta fara ɗandanawa da taji yayi mata daɗi sai ta hau cin abinci tana lasar hannu,
  Qasin na fitowa ya hango aikin da take daga can ya katsa mata tsawa “Ke waya kaiki bak'ifa zatayi ta siyo musu cake ɗin shine kika zauna kika ci? Aiko mai rabaki da ita yau sai Allah"
   Ragowar dake hannunta ta aje “Toh ni bana ɗauka naka nabe"
  “Nawa zan aje nan ban bakai miki naki ba bak'i fa tayi ta siyo musu kuma yanzu kar ta iskomu da munje mun tsiy..."
jin tsahawar motarta  yasa yayi shiru.
Da sauri Mairo ta tashi tsaye “Itace ko?"
  “Itace kuma ni babu ruwana ke da ita can"
  Tana tashi ta niyar guduwa Mansura ta turo k'ofar parlor ta shigo.
   Da sauri Qasin ya k'arasa saukowa ya tareta “Kin dawo?"
   Bata amsa mishi ba ta watsama Mairo harara “Mi kikazo nan?"
Duk bata ga aika-aikan da tayi mata ba sai da ta kusa kaiwa kusa da ita.
  “Kan Uba uban wa ya aikeki taɓa min cake?"
   Gabanta Qasin yaci ya rik'ota “Yi hak'uri Mansura bata san naki bane bari na siyo miki wani yanzu"
    Janbakin dake hannun shi ta kalla “Waya ɗauko min jan baki mi zakayi dashi?"
    Matsowa Mairo tayi kusa da ita ta turo bakinta tana nuna mata.
   “Shine ya tsotse min janbakina shine yace bari ya ɗauko min naki na shafa amman na fasa shafawan gida zani"
    Baki Qasin ya saki ya juyo ya kalli Mairo,
“Ke miyasa karya bata miki wahala ne?"
   Sake juyowa yayi ya kalli Mansura “K'arya fa take"
  Uffan ba tace mishi ba ta mika mishi hannu “Bani cake ɗin"
    Yana duk'awa ya ɗauko mata nan ta cire takalmin ta mai tsini ta saita kan Mairo ta k'wala mata shi.
    Wata mahaukaciyar k'ara Mairo ta saki. Jini ya malalo mata daga saman kai,
   K'arasa jefa mat takalmin Mansura tayi tana faɗin “Gobe in kikaga na sake ganin na aje abu ki ɗauka ciki wai har kike faɗamin janbakinki ya tsotse ke tsohuwar karuwa ko?"
    Da gudu Mairo ta bar parlor dafe da kai.
    Jefeta Qasin yayi ya cake ɗin ya wanke mata fuska da mari hudu masu kyau. Da sauri ta dafe kunci tayi baya-baya tana kallonshi “Qasin saboda na fasa mata kai ka mareni"
   K'ara mata na biyar yayi “In bakida hankali sai kiyi shi saboda taci miki cake ɗin banza zaki daketa ki safa mata kai haka aina fada miki duk kika sake sa mata hannu sai na samiki"
    “Lallai Qasin kai butulu ne yaushe aka ɗaura maka Auren da ita da har kake fifitata a kaina? Koda yake halinku ne maza haka kuka gada"
      Cikin kuka take mishi maganar.
  “Ke in banda rashin hankali mi zakiji a jikin Maryam in kika daketa?"
    “Abinda kasan a naji shi zanji mai abin kunya yasa k'aramar yarinya a gaba yana kiss"
    “Toh haramun nayi har abinda yafi kiss sai nayi mata tunda matata ce"
    “Bazan iya zama da kai ba Qasin sun riga sun shiga tsakanin mu yaushe kayi Auren nan amman gashi har ka fara canja min bazan iya zama da kai ba har sai ka zaɓa koni ko ita"
    Tsaki yaja ya fice ya bar mata parlor.

_A ɓangaren Mairo_
Da gudu Mairo ta shigo parlor tana kiran sunan Momi.
   “Lafiya Maryam?"
Jin muryar Yarima yasa ta juyo da fukar jini ta kalleshi. Baya-baya tayi tana cigaba da kukan.
  Da sauri ya rik'ota “Ke Maryam ba wani abin zanyi miki ba miya sameki haka?"
  Cikin kuka ta bashi amsa “Matar Yaya Qasin ce ta fasa min kai"
    Baiyi wata-wata ba yasa hannu ya ɗauketa yana faɗin “Muje na kaiki asibiti"
  Tirjiya ta shiga mishi tana k'ok'arin k'wace kanta.
   Sauketa yayi “Trust me Maryam bazan miki komai ba asibiti zan kaiki"
    Ganin bata da mafita yasa ta kyale shi kodan zogin da take ji yaja hannunta suka fice.

        Koda Qasin ya shigo bai tararda ita ba duk saida ya bikaca gidan amman babu ta babu labarinta,
    Fitowa yayi ya nufi gurin mai gadinsu yana tambaya shi ko yaga Mairo.
    “Eh ranka ya daɗe naganta a motar Yarima sun fita"
   “What!?" Da k'arfi Qasin ya tambaya
  “Yaushe Yarima ya shigo?"
   “Bai daɗe da shigowa ba sai kuma naga ya fito tare da ita da gudu ma ya fita"
  Kai Qasin ya ɗaga mishi ya nufi part ɗin shi.
     D'akinshi ya nufa yana jin kukan Mansura. bai ta kanta ba ya ɗauko keys ɗin matar shi ya fito.
   Yana kawowa parking space ya tararda Momi ta fito daga mota.
   Yanayin yadda ta ganshi yasa ta tambaya “Lafiya dai?"
  Shiru yayi yana kallonta ya kasa bata amsa, “Qasin da kai nake magana lafiya na ganka haka?"
   Kanshi ya sosa “Momi Maryam ce tayi faɗa da Mansura shine ita kuma ta fasa mata kai kuma nazo yanzu ban ganta ba ance Yarima ya fita da ita shine zan bi bayan shi"
   Momi ta zaro ido “Wa aka fasama kai?"
   “Maryam"
Wani irin Momi tayi kamar ta fasa kuka “Ta mutu ne?"
  “A'a Momi kaɗan fa ne ma aka fasa mata kan"
   Motar Momi ta rufe ta nufi cikin gida idonta da k'wallah.
    Rufa mata baya yayi tana kwantar mata da hankali,
   Saman kujera Momi ta zauna dafe da kai.
  Nan shima ya zauna “Dan Allah Momi ki kwantar da hankalinki bafa wani mugun ciyo bane taji kawai.."
  Hannu ta ɗaga mishi “ɗan Allah ka rufe min baki ka naji da wane da raunin da kukayi mata ko da surutunka"
   Shiru yayi yana shafa kanshi. duk abin duniya ya ishe shi ya rasa da wanne zaiji ɗayan ɓangaren zuciyashi yana gurin Yarima da tafi mishi da Mairo.
nan kuma yasan Momi ba saurara mishi zatayi ba.
    
   ***
    Pharmacy mafi kusa ya nufa da ita k'in yarda tayi a dubata saida Yarima ya rumgume ta.
   Da kuka  akayi treatment ɗinta sannan ya suka bata wasu maganin nika ya sata mota suka ɗauko hanyar gida.
   bataana isa yayi horn kamin a buɗe mishi ya mik'a hannu ya riko hannunta yana sauke ajiyar zuciya
   “Ina sonki Maryam ina sonki"
D'ago kai tayi tana kalloshi har aka buɗe mishi gate ɗin ya kunna kai cikin gidan.
    Bayan yayi parking ya fito ya nufi parlor Momi still yana rik'e da hannunta,

Daga Momi har Qasin tashi sukayi Suna kallonshi. nan Mairo ta shiga k'ok'arin kwace hannunta. Iya k'arfinshi yasa ya rik'e hannun gam. Ko motsin kirki ta gagara yi.
   Cikin wani irin zafin nama Qasin ya k'araso kusa dashi ya ɗaga hannu zai mareshi. Da sauri Yarima yasa ɗayan hannunshi ya rik'e mashi hannu yana mishi wani kallo.
   “Kayi kaɗan kasa wulakantaccen hannunka a fuska ta"
  Damk'e hannu Qasin yayi da k'arfi kamar mai dambe ya kai mishi naushi dai-dai k'ahon zuciya.
  Zaro ido Momi tayi ta ɗora hannu aka “Qasin mi kake k'ok'arin aikatawa haka?"
  Baiyi wata-wata ba ya sake aika mishi wani bugun.
Ba shiri ya saki hannun Mairo ya faɗi durk'ushe dafe da zuciyar. Ture Qasin Momi tayi idonta cike da k'wallah “Wai baka da hankali ne Qasin so kake ka kashe shi fice ka bar parlor nan"
   Hannu Mairo ya fisga sukabar parlor tare.
         
Part ɗin shi ya nuf har lokacin yana rik'e da hannunta.
    Bai sake ta ba sai da ya sata cikin ɗakin shi sannan ya jefar da ita saman kujera ya zaro belt ɗin shi ya hau dukanta.
     Mairo bata san zafin duka ba sai yau tunda Gwaggo bata taɓa sa mata hannu ba kuma bata bari kowa yasa mata.
   Ihu ta dinga yi tana kuka baji ba gani tun tana iya ɗaga murya har muryata ta dakushe.
  Saida yayi mata dakan da shi kanshi ya gamsu ta daku sannan ya jefar da belt ɗin yana faɗin “Daga yau duk kika kuskura kika sake bari wani namiji ya rik'a miki hannu sai na karya ki"
Yana kaiwa nan ya juya ya fice.

      Saida yayi kusan minti 30 da fita sannan ta samu ta rarrafa ta fito.
    Tana kawowa parlor Momi ta zube k'asa ta rushe da sabon kuka. Da sauri Momi ta k'arasa ta rik'o “Inna lillahi wainna ilaihi raji'un dukanki yayi Maryam?"
   Kai ta ɗaga mata tana wani irin kuka. Dak'er Momi ta lallaɓata tayi shiru sannan taja hannunta tana matsifa suka shiga ɗakinta.
   Sai da Momi ta shiga ta haɗa mata ruwan ɗumi sannan ta shigar da ita bathroom ɗin ta gasa mata jiki. Bayan ta k'are ta sake haɗa mata wasu ruwan wankan ta fito.
     Mairo wanka take tana kuka har tayi ta gama. Koda ta fito ta tararda doguwar rigar atamfa aje saman gado. D'auka tayi ta saka ta hau tsakiyar gadon ta kwanta tana sauraren ciyonkai da ya kawo mata ziyara.

***
    Bayan Sallar Isha'i Qasin ya shigo side ɗin Momi k'asa-k'asa ta amsa mishi sallamar da yayi muryarta na ɗauke da damuwa.
Kusa da ita ya zauna tana kallonta tare da sauke ajiyar zuciya,
    “Momi kiyi hak'uri Zuciyata ce ta rufe shiyasa"
Kallonshi Momi tayi “Amman kuma dan zuciyarka ta rufe saika aikata abinda in badan Allah ya gyara ba da zai iya kaimu ga dana sani? Daker Yarima yabar parlor, saboda mugun Bugun da kayi mishi duk kuma haka bai maka ba sai da kasa Maryam gaba ka dinga dukanta kamar an aiko ka"
      “Momi Yarima dai ko kashe shi nayi inada hujja tunda shi ya kawo kanshi har cikin gidan nan ya kuma ɗaukar min mata ya fita da ita Maryam kuma inba duka nayi mata ba ba zata samu  natsuwa ba"
    Kai Momi ta girgiza “Ko kaɗan Qasin duka baya gyara sai dai ya ɓata faɗa ya kamata kayi mata ba duka ba bazan yarda ba,
   Ba kuma zansa muku ido ba kai ka daketa matar ka ta daketa ba jaka bace dan haka karka sake sa mata hannu"
    Bak'ar ledar dake gefen hannun shi ya mik'a mata yana faɗin “Naji Momi ayi hak'uri bazan sake ba ga wannan maganin a bata tasha"
  Saida Momi ta sauke ajiyar zuciya sannan ta k'arɓi ledar tana faɗin “Ka turo min Mansura zanyi magana da ita"
    “Bata nan Momi nima koda na dawo ban tararda itaba daman da zan fita naga tana haɗa kayan ta"
    “Fushi tayi kenan akan wani dalili?"
  Kafaɗunsa ya ɗaga “Oho mata nidai bazan je bikonta yanzun ba tunda bani nace taje ba kuma ba wani abin akayi mata ba"
     Taɓe baki Momi tayi “Toh Allah ya kyauta"
Saida ya amsa da “Amin" sannan ya tashi ya nufi dining.
   Momi kuma ta nufi ɗakinta.

Story continues below



        Zaune Momi ta tararda Mairo tana cin kankanar dake gabanta da ɗai-ɗai. Ruwan goran dake gabanta Momi ta ɗauka ta k'ara zubawa a kofi sannan ta kankare maganin ta mik'a mata.
   “K'arɓi kisha jikinki zai ɗanyi sauki kamin gobe"
   Ba musu ta karɓa ta sha. ta cigaba da cin kankanar.
   A hankali Momi ta shafa kanta “Maryam dan Allah ki rik'a jin magana kinji in nace kiyi abu ki rik'ayi ki ɗinga karatun ta natsu
Kinga har makaranta nayi maganar zan saki amman sai naga natsuwarki tukuna"
   Da sauri ta kalli Momi “Na daina Momi ina son makarantan ina ne? Bazan sake ba"
   Murmushi Momi tayi “Toh sai dai naga natsuwarki tukuna dan karatu natsuwa yake so balle ba subject ɗaya za'ayi muku ba kinga za'a koya Miki yadda zaki iya saka tufafi, da tafiya, da iya magana, da dafa abinci, da zaman gidan Aure, da rubuta da karantawa,
   Har sana o'i duk ciki za'a koya muku kuma kuɗi da yawa ake kashe dan haka nafi son sai kin natsu dan bana son kuɗina suje a banza"
    Shiru Mairo tayi kamar mai tunani.
   Momi ta cigaba
       “Makarantar ba nisa nan ne gurin Abdullahi Fodio Road sunan makarantar gyara da kanki nima a radio naji ta na ɗauki number malamar na kirata mukayi magana kuma Fitar da nayi ɗazun gurin gaisuwa ma saida na biya naga makarantar,
  Dan Allah ki natsu kinji ki daina duk wani abu da kikasan baya da kyau"
   Kai kawai ta ɗaga mata taja fillo ta kwanta Momi taja zane ta rufe mata jiki tana faɗin “Ina tafar dai kinyi sallar I'sha ko?"
  Nan ma kai ta ɗaga tasa hannu a baki.

Washe gari Mairo a ɗaki tayi breakfast su Momi ne kawai sukayi a dining room.
   Nan na Momi take tabartawa Qasin maganar makarantar. Bai yi unk'urin hana taba duk da wani ɓangare na zuciyarshi baya so fatan alheri kawai yayi mata ya tashi ya fice.

    Wasan ɓoya Mairo ta dinga yi da Qasin sam bata yarda ya ganta duk gun da tasan zai iya ganin ta daina zama.
Sai da Momi tayi mta faɗa sannan gaisuwa ta dinga shiga tsakanin su kuma daga gaisuwar bata wuce ba data gaisheshi ya amsa zata tashi ta bashi guri,
    Hakan kuma sai ya soma damuwar Qasin ganin bata sakewa dashi.

   Saida Momi ta tabbatar da taji sauki sosai sannan ta ɗauke ta da kanta ta kaita makaranta akayi mata komai da ake buk'ata. Daman suna da school bus ga mai buk'ata. Kuɗin bus ɗin Momi ta biya wadda za'a rik'a zuwa ɗaukarta kullum da k'arfe 10am a dawo da ita 5pm.
     Maida hankali tayi sosai gurin karatun gashi Momi kullum cikin jaddadamata take kar tasa tayi hasarar kuɗinta
    Wata irin natsuwa ce ta sauko mata tunda ta fara zuwa makarantar kwata-kwata ta cire wasa gefe ta aje ta tattara hankalinta gurin ɗaya ta kama karantunta
   
       A makarantar darussa aka dingayi musu kala-kala tun Mairo na ganin abinda kamar lalata tarbiyane yana bata haushi har ta daina sannu-sannu abin ya fara shiga ranta.

*****
      Ranar wata Jumma'a da misalin karfe goma sha ɗaya na dare Qasin ya shigo parlor Momi.
    Mairo na ganin shi tayi saurin tashi daman ita ka ɗai ce parlor ta gaishe shi bayan ya amsa ta aje remote ɗin dae hannunta ta juya da niyar tafiya.
   Da sauri ya riko hannunta “Ina zaki Maryam?"
   Ba tare data juyo ba ta amsa mishi “D'aki kwantawa zanyi"
     “Baki tashi yin bachi ba sai da kika ganin wai miyasa kike wahalar da nine Maryam bayan kuma kin kore min mata"
   Sai a lokacin ta kalleshi “Nikan ban korar maka mata ba ita dai taga dama tayi tafiyar ta"
   “Amman dai ai saboda ke ta tafi ko?"
  “Amman kuma ni bance ta tafi ba ganin damarta ne"
    Wani dogon numfashi yaja “Fine tunda kin iya jayayya"
   B'ata fuska ta ɗanyi “Ni ba jayayya nake ba ai jayayya ba kyau kawai ina faɗan gaskiya ne"
    Taɓe baki yayi yaja hannunta. Saida suka kai bakin k'ofa sannan ta fisge hannun ganin zai fita da ita “Ina zamu?"
   “Part ɗina mana"
“Na maka mi?"
“In mukaje zaki gani"
Yana sake rik'a hanunta ta fisge.
  D'aure fuska yayi “Kinsan bana son musu ko ba dai canye ki zanyi ba ba kuma dukanki zanyi"
  Shiru tayi ta ɗanyi k'asa da kanta.
Bai bari ta tsaya tunani ba ya sake jan hanunnata a karo na uku suka nufi Part ɗin.
   
       Sama  gadon shi ya zaunar da ita.
Ita kuma gaban sai faɗuwa yake bedside drawer ya buɗe ya ɗauko wani dan karamin box Red color ya ya kalleta yace “Rumtse idonki"
   “Kamin mi?"
“Ai dai bazan cutar dake ba ko Please close your eyes"
   Rumtse idon tayi gam tana haɗiyar yawu.
Wani daddaɗan K'anshi ne ya daki hancinta hakan yasa ta buɗe idon a hankali.
    Arba tayi da wata kyakkyawar sark'ar gold “Yaya kamar zinari na wanene?"
  Ta tambaya idonta a zare zuciyar na bugawa da sauri.
   “Gold ne ba kama bace kuma ke na siya ma ko baki so"
   Da sauri tasa hannu biu ta karɓa ta kuma durkusa k'asa “Inaso yaya na gode sosai Allah ya bika Jazakallahu khar"
   Murmushi yayi ya ɗan tsosa bakinshi “Ur welcome dear" Ya tado da ita yasa bakinshi cikin nata.
   Batayi k'ok'arin hana shiba har saida ya gaji dan kanshi ya zare bakin daga nata.
Tashi tayi da sauri “Bari naje na nuna ma Momi"
  Kunkurumta ya rik'e “A'a Momi yanzu ai tayi bachi kuma kinsan bata son a tashe ta"
    Kai ta ɗaga mishi tana murmushi mai fitar da sauti har cikin zuciyar ta take jindaɗin.
    Laptop ɗin shi ya janyo “Zauna na nuna miki wani abu" kusa dashi ta zauna tana ciki da jindaɗi.
    Kunna laptop ɗin yayi ya shiga nuna mata wasu pictures ɗin da bata san lokacin ya ɗauke suba.
       Dariya ta dingayi ganin wasu bachi ma take “Lahhh Yaya yaushe ka ɗauka?”
   “Kina bachi na ɗauka ba kece kike tsayawa kallo a parlor ba"
     Murmushi tayi ta k'asa da kanta kamar wace taji kunya.
    Nan ya shiga nuna mata nashi hotunan da yayi a k'asashe waje. Ganin ta fara jin bachi yasa ya janyota ya kwantar da ita saman jikinshi.
    Aiko nan da nan bachi ya buget. Qasin kamar mai jira ya rufe laptop ɗin, bai ko bari bachi nata ya nina sosai ba, ya kwantar da ita kan gadon ya rabata da rigar jikinta ya shiga shafa ta yana aika mata kiss ta ko'ina.
   Wasa yayi da ita sosai sai da yaji ya gamsu sannan ya tashi a wahale ya shiga bathroom. Wanka yayi ya fito ya saka kayan bachi sannan ya nufo ta ya mayar mata da rigar,
   Itakan sai bachi take abinda bata masan yayi ba. ɗaukar ta yayi kamar baby tare da sark'ar ya kawota part ɗin Momi ya kwantar saman doguwar kujera ya aje mata sak'ar aje.
      Ya daɗe tsaye yana kallonta sannan manna mata kiss a goshi, ya kashe wutar parlor tare da Tv yaja mata k'ofa.

***
   Asubar farin Momi ta tashi ta daman haka take mata kullum saboda zuwa makaranta tunda har Asabar da Lahadi zuwa suke basu da ranar hutu.
    Cikin magagin bachi ta motsa tana faɗin “Yaya duk sunyi kyau"
   Momi ta jijjigata da k'arfi “Ke tashi kiyi wanka kiyi sallah wane yaya kuma?"
    Muk'a ta shiga k'ok'arin yi sannan ta tashi, sark'ar dake gefenta ta faɗo. Bata kula ba ta wuce ɗaki tana murza ido da mamakin ganinta parlor Momi ita da bachi ya ɗauke a part ɗin Qasin.
   D'aukar sak'ar Momi tayi ta rufa mata baya bayan ta k'are mata kallo,  Sai da tayi sallah ta shirya sannan Momi ta tambayeta ina ta samo sark'a.
   Dariya tayi “Ashe da gaske ne ni na ɗauka duk mafarki nake Yaya ya bani jiya da dare"
    Momi tayi murmushi “Aiko ya kyauta tunda daman bakida sak'ar zinari kuma ya siya miki mai tsada ina fatar dai kin mashi godiya dan godiya tana ɗaya daga cikin abin da take saka Namiji jindaɗi idan yayi miki kyauta koda kusa kyautar bata kai ta kawo ba"
        Kular abincinta ta ɗauka tana faɗin “Nayi mishi Momi bari naje ga motar makarantar mu can ta iso"
    “Toh Allah ya tsare ya kiyaye"
    “Amin Momi sai na dawo"
    Kai Momi ta daga mata tana murmushi, iya natsuwa yanzu kan tasan Mairo ta samu saidai wayou ne ba tada tabbaci ko tayi amman da tasan ko minene dai sannu-sannu bata hana zuwa sai dai a daɗe ba'aje ba.

 
'''**'''
    
Bayan Sallar Azahar Qasin ya shigo part ɗin Momi, sun ɗan daɗe suna fira anan ne take mashi zance sark'ar daya ba Maryam tana godiya.
     Dariya yayi “Haba Momi dan naba Maryam sark'a sai kuma kimin godiya?"
    “Eh mana ai idan kayima Maryam abu kamar ni kayima tunda Maryam yata ce"
     “Amman dai Momi bata ce miki wani abuba ko?"
   “Kamar na mi kasan ai yanzu ta rage yawan zubar nan wani abun kace tace ne?"
  Kai ya girgiza “A'a"

     “Wai Qasin ya maganar tarewarku ne?" Yana unk'urin tashi tayi mishi maganar hakan yasa ya koma ya zauna yana faɗin “Momi toh ai ke nake jira"
    Momi tace “Jiya Abbah ka yayi maganar daya kirani a waya har nake ce mishi akwai kayan da ba'ahada ba yace zai turo kuɗi ayi komai,
   K'auye ma ance tambaya kawai suke Gwaggo ku sai fama  matsifa take"
     “Nima dai Momi shi nagani yanzu dai babu wani abinda ake jira"
   “Idan ya turo kuɗin zan siya mata duk abunda ake bukata sai asa ranar tarewar taku"
   Murmushi yayi “Hakan yayi Momi Allah ya taimaka"
   “Amin amman dai kasan dole ne kaje bikon Mansura ko da baka tare daga kai sai ita ba ka kyale ta can"
   “Momi ai Mansura bata gari"
   “Bata gari kuma?" Momi ta tambaya.
   “Eh wai taje raka yayarta a indiya duba lafiya"
   “Da gaske?"
“Allah kuwa nima a bakin Sadiq naji kinsan yana Auren k'anwarta kuma dana kira wayar yak'i shiga"
   “Amman da izinin waye taje kai kasan da tafiyar ne?"
  “A'a sai bayan ma taje ne nake ji"
  Momi ta rik'e baki “Amman dai gaskiya daga ita har iyayenta basa da tunani Allah ya kyauta"
    “Amin ai sai ta gane kuskurenta bari naje nayi sallah naji kiran La'asar"
   Maganar yake yana kallon agogon hannun shi, Momi tace “Nima ai bari na tashi naje nayi sallar"
   Tashi yayi ya fice, ya bar Momi tana mamakin hali irin na Mansura.

'''** ** ** **'''
Da murmushi Momi ta sauko downstairs tana kallon kujerar da Yarima yake zaune,
   “Masha Allah Yarima har an iso?"
   Ba tare daya kalleta yace “Eh miyasa kike nema na?"
   Ruwa Momi ta ɗauko mishi da cup ta dire mishi sannan ta zauna a ɗayan kujerar tana faɗin “Ya gida ya kowa da kowa"
    Ya daɗe yana kallon zoben hannun shi sannan ya amsa mata “Lafiya kalau"
   Momi tayi gyaran murya cikin fuskar manya ta soma magana “Wata alfarma nake nema a gurinka Yarima"
   Sai a lokacin ya kalleta “Allah yasa zan iya"
    “Zaka iya dan bata gagareka ba kuma kana da ikon aiwatarda ita"
    Shiru yayi yana murza yatsunshi, yasan Momi da wayo kuma gashi she's look so serious akan ko minene.
    Sai da ya busar da iskar bakinshi ya ɗora k'afarshi ɗaya saman ɗaya sannan ya kalleta kamar mai karantar abu a fukarta.

Ya daɗe yana kallonta sannan ya ɗauke kanshi “Ina jinki"
   Momi saida ta sauke ajiyar zuciya sannan tace “Aure nake son kayi Yarima"
    Nan ya sake kallonta yana ɗan murmurewa.
    “Yes dole kice nayi Aure tunda kinga burin ɗanki ya cika ko banyi tunani zaki iya sakani a gaba ba kiyi min irin wannan maganar"
     “Yarima shekaranjiya Hajiya ta kirani ta faɗamin kace kai  ba zakiyi Aure toh akan wane dalili? Kaine kaɗai ɗan data haifa kaine farin cikin ta miyasa baka tunanin kyautata mata kayi mata abinda zai sata farin ciki"
    Taɓe baki yayi “Inayi abinda nasan zan iyane kawai dan kinsan ko Allah baya kallafawa rayuwa har sai abinda rayuwar take iyawa da kanta so idan kina da wata maganar kiyi"
   “Bani da wata maganar wannan ce kawai kuma a tunani na isa nace kayi kayi shiyasa na rik'e ka dan wannan matsalar ce kawai take damun mahaifiyarka da kuma duk wani masoyinka"
   Tashi yayi tsaye yasa hannayenshi aljihu.
   “Ko zanyi Aure ba yanzu ba so maganar Aure ta daina damunku have a wonderful day"
Yana kaiwa nan bai tsaya jiran abinda zata ce ba yasa kai ya fice.
   Ko kaɗan Momi bata jindaɗi yadda yayi mata ba duk da yake tasan kaɗan ne daga halinshi babu wadda ya isa ya sashi abinda bai tashi ba.

    As usually biyar dai-dai motar makarantar *KOYI DA KANKI* (gidan sisto😉) ta sauketa k'ofar gida.
   Tana shigowa kayanta karatunta kawai ta aje ta nufi  bathroom, wanka tayi ta shirya cikin wani farin material sannan ta nufo dining room,
    Saida ta cika cikinta sannan ta tashi tana hamdala, ta dawo saman kujeara ta zauna tana shafar ciki.
   Sallamar Momi ce tasa ta ɗago kai ta kalli k'ofa “Wa'alaikissalam Momi sannu da zuwa"
   “Yauwa sannu kin dawo?"
  “Eh tin ɗazu har naci abinci nayi wanka Momi ina kikaje?"
   Upstairs Momi ta nufa tana faɗin “Gidanki wasu kaya na kai"
   'Dauke kai tayi ta cigaba da kallon tana cikama bakinta iska.
        Daga can cikin ɗakin Momi ta kwalama Mairo kira,
  Tashi tayi tare da amsawa “Na'am Momi"
   Shiga tayi cikin ɗakin tana faɗin “Momi gani"
   “Zo ga kaya nan ki buɗe"
   Duk'awa tayi gaban sait ɗin akwatunan ta shiga buɗewa “Momi na waye ne tun ɗazun na gansu?"
    “Naki ne shine lefen da mijinki yayi miki"
'Dauke hannayenta tayi tayi k'asa da kanta.
   Murmushi Momi tayi tace “Ranar Asabar mai zuwa za ayi walima In'sha Allah kuma za' kaiki ɗakin mijinki kuma ki shirya gobe mai dilka zata zo ta fara gyaraki"
   B'ata rai ta ɗanyi kamar bata jindaɗi ba. Ta tashi jiki a kasale ta bar ɗakin,
   Shiru Momi tayi kamar mai tunani can kuma ta shiga duba kayan da kanta.

  Tun daga lokacin Mairo bata sake walwalah ba,  Momi kuma bata bi ta kanta ba ta cigaba da shirye-shiryenta da take mata hankalin Momi bai kwanta ba sai taga komai na gidan ya kammala.
   Kullum mai dilka sai tazo tayi mata Momi ta ɗaukar mata hutu a makaranta cikim yan kwamakin Mairo ta zama wata irin mace abar sha'awa, jikinta yayi kutil-kutil sai sheki take tayi wani assirtattaccen fari,

   Ranar da akayi mata dilkar k'arshe ne take tambayar Momi ko su Gwaggo zasu zo,  
  Momi tace “Bana tunani zasu zo dan bn fada musu ba kinga ai ko mun nan mun isa tunda akwai yan'uwan nan ko a nan bayan kin tare zan faɗa musu sai suzo so ganki kinji?"
  Kai kawai ta ɗaga mata ta tashi idonta cike da hawaye ta fice.
    Washe gari Jumma'a tunda safe mai kitso da lalle tazo aka hau aikin gyara ta,  wunin ranar komai bata sa abakinta ba har akayi aka k'are,
   Kallon ɗaya Momi tayi mata ta fahimci tana cikin wani yanayi mai wuyar fassara.
Bayan Sallar Isha'i Momi tasa Mairo gaba tana faɗa mata wasu abubuwan da ya kamata ace ta sani da kuma jan kunneta akan abubuwan da tasan tana yi masara kyau.
   
Kamar yadda Momi tace washe garin Jumma'a  wato Assabar akayi Walima. Ba laifi anyi taro dik da ba wasu mutane sosai Momi ta gayyato ba yan'uwan da suke garine kawai sai abokaninta da kuma wasu daga cikin abokanin Mairo yan makarantar su,

Story continues below



K'arfe 9 motocin ɗaukar amarya suka zo, huɗuba sosai Momi tayi mata itako tana ta aikin kuka.
  Daker aka fitar da ita daga gidan aka sata mota. Har aka zaunar da ita saman gadonta kuka take kamar ranta zai fita.
       Mutane da suka kaita suka rik'a bata hak'uri har suka gaji suka kyaleta, basu fi awa ɗaya da zama ba ango ya shigo shida abokaninshi nan sukayi musu tasu huɗubar suka sannan sukayi musu sallama.
     Har bakin k'ofa Qasin ya raka abokaninshi sai zolayarshi suke shi dai in banda murmushi babu abinda yake,
   
Yadda ya barta haka ya dawo ya sameta tana aikin kuka.
Kusa da ita ya zauna ya kai hannu a hankali ya yaye mahafin data rufa da shi.  Nan ta ɗago kai ta kalleshi da jajayen idanunta dake cike da kwallah.
    Hannu yakai ya taɓa gefen fuskarta “Mi kike yima kuka haka Maryam?"
  Daker ta iya tsayarda kuka tayi mishi magana “Yaya wani yanayi nake jin kai wadda ban taɓa jin kaina a ciki ba"
   'Daya hannun shi yasa ya shafe mata hawaye ya kwantar da ita saman jikinshi yana buga bayanta alamar rarrashi.
   Sai da ya tabbatar da kuka ta ɗan tsaya mata sannan ya ɗago kanta yace “Tashi muje muyi Sallah kinji?"
  Kai ta ɗaga mishi ya rik'o hannunta bayan ya cire babbar rigarshi suka nufi bathroom.
  Tare sukayi alwalar ya sake rik'o hannunta suka fito. Da kanshi ya shinfiɗa musu carpet ya buɗe akwatinti ya ɗauko mata hijab tasa sannan ya kabbarta sallar.
       Raka'ah biu sukayi suka sallame saida suka yima Allah godiya sannan sukayi ma Annabi sallati bayan sun k'are ya juyo ya rik'a kanta ya karanta Addu'ar da Annabi Rahama (S. A. W) ya koyar da mu, har lokacin hawaye take.
  Tashi yayi ya ɗauko Plate da cups. Ya dawo kusa da ita ya zauna ya buɗe ledar kazar dake saman drawer ya zuba a plate kofunan kuma ya cikasu da juice.
  Daker ya lallaɓata taci koshi kaɗan ta hau saman gadon ta kwanta,
     Bayan ya k'are ya ɗauke plate ɗin ya chanja kayan jikinshi zuwa na bachi sannan ya hau shima ya kwanta bayanta.

_Washe gari_
    Tara da rabi Momi ta aiko musu da breakfast saida ya ɗora kulolin dining sannan ya shiga ya tashe ta tayi brush sannan suka nufo dining tare.
    Shida kanshi ya zuba mata abinci sannan ya zuba kanshi yaja kujera ya zauna,
  Suka soma kalace.
Daf da zasu gama cin abincin wayar shi tayi ringing.  Hakan yasa shi tashi tsaye ya ciro wayar a aljihu yana duba mai kiran.
  Ya daɗe yana kallon wayar sannan ya ɗora ta saman dining ya cigaba da cin abincin ba tare da yayi picking ba,
    Mairo kamar ta mishi maganar sai kuma wata zuciyar ta hana ta tashi tayi tana goge baki.
  “Har kin k'oshi?"
Kai ta ɗaga mishi tana ɗan murmushi. Ta nufi ɗaki,

  Da rana Momi ta aiko wata daga cikin 'ya' yan k'awayinta suka kawo masu abincin rana ita kadai suka tararda sai mak'otanta dn Qasin ya fita lokacin,

Sun daɗe suna taya ta fira. Nan duk ta sake dasu ta jindaɗi.
    Saida sukayi mata kwaliya suna gyara mata gidan sannan suka fice.
Da dare direba Momi ta aiko ya kawo musu tuwo da drinks haɗin gida.
   Haka Momi tayi ta musu kuma kullum sai ta kirata a waya ta tambaya ko da wani abun tace mata babu,
   Ranar da tacika sati ɗaya da dare Qasin ya shigo musu da kuloli. Tashi tayi ta tarbo shi ta karɓi kulolin takai dining ta aje tana faɗin “Yau kai aka aiko"
  “Naje can ne shine tace na wuto dasu kuma ta bani sak'o na faɗa miki"
  Nufi shi tayi tana faɗin “Minene mi tace?"
  Kumatunta ya rik'a ya manna mata kiss “Bazan faɗa ba sai nayi waka munci abinci tukuna"
   Dariya tayi “Toh je kayi ina jira"
    Matsowa yayi kus da ita ta yadda zasu iya shak'ar numfashin junansu ciki kashe murya yace “Ni kaɗai zanyi?"
   Matsawa tayi baya ta ɗan mashi fuskar shanu “Toh kai da wa zakayi?"
   Kafaɗunsa ya ɗaga “Nidai baki ji nace kizo muyi ba ai ko?"
   Gira ta ɗaga mishi “Good boy je kayi wankan ka"
   Kanta ya shafa yana dariya “Oh i like you baby"
  Dariya itama tayi ta cigaba da kallonshi har ya shige ɗaki.

***
Bayan sun gama cin abincin ya rik'o hannunta suka dawo saman kujeara suka zauna.
   “Yaya dan Allah fada min minene Momi tace tun ɗazu sai jamin rai kake"
     Janyota yayi ta kwanta saman kirjinshi “Kamin na faɗa miki abinda Momi tace ina son fada miki wani abun"
     “Toh ina jinka"
Shiru ya ɗanyi sannan ya shiga shafata “Ban da gobe idan Allah ya kaimu Mansura zata zo ta gyara ɗakinta so bana son ki kula ta koda ta tsokaneki kinji?"
   Faɗuwa gabanta yayi ta dan daɗe kamin tayi magana “Ba Momi tace min taje k'asar waje ba kota dawo ne?"
   “Ta dawo ita ta aiko gurin Momi tace zata zo ta gyara ɗakinta dan ni na faɗa mata ba zan je bikonta ba tunda bani ne nace taje gida ba"
   Taɓe baki tayi “Yau ni ina ruwana da ita tazo tayi duk abinda zatayi nidai faɗa min abinda Momi tace"
   Sai da ya shafa kanta sannan yaja hannunta yasa a bakinshi ya ɗan cijeta,
   “Cewa tayi na cije miki ɗan yatsa"
   Kukan shagwaɓa tayi mishi “Allah sai na rama Momi ba zata ce ka cijeni ba"
    Dariya yayi yaja mata kunne “Ke cewa tayi na faɗa miki daga gobe ki fara girki da kanki"
    Kallonshi tayi “Wasa dai kake?"
   “Allah ba wasa nake ba haka tace in kuma baki yarda ba na kira miki ita a waya yanzu kiji"
   “Ai Momi ba zata ce haka ba gaskiya dani ruwan tea kawai na iya dafawa"
    “Tace komai kika iya kiyi babu ruwana nidai na faɗa miki sak'onta"
  “Toh naji Yaya dan Allah zaka kaini gurin Momi gobe?"
  “Yaushe kika zo gidan da har zaki fara fita?"
  “Itace tace a kawo ni ɗazun a waya baka jiba?"
   “A'a k'arya kike batace koma tace bazan kaiki ba"
   “Toh kai da kake fita fa?"
  “Namiji ai bai gaji zama ba"
“Nidai gaskiya ka kaini ko na maka kuka"
  “Tashi ki shirya na kaiki gurin Gwaggo"
Dariya tasa mishi “Wasa kake min nasa ni ai"
  Hancinta yaja “Au ashe kina da wayo"
   Ita kuma tayi dariya ta kwantar da kanta.

Story continues below



         Da safe shi y haɗa musu breakfast sai da ya kammala komai sannan ya yaje ya tashe ta,
  Tare suka wanke baki sannan ya tallabota kamar yar baby suka nufo dining. Sai da ya k'osar da ita sannan shima yaci.
     K'in tashi tayi daga gurin ta marairaice mishi fuska, “Minene wai baby na?"
  “Gun da ka ɗauko ni zaka mayar dani"
“Au daga na miki alfarma na ɗauko na kawoki sai kuma kice sai na maida ki"
  “Eh ai bance ka ɗauko niba"
  Dariya yayi yasa hannu ya lak'atar mata hanci “I love you Maryam"
   Murmushi tayi ta rik'e mishi hannu “Yaya Qasin... " sai kuma tayi shiru.
    Risinawa yayi daidai kunne ya busa mata iska “Faɗi maganar Yayanki yana jinki"
  Ido ta sakar mishi tana murmushi.
Can kuma ta ɗauke ido ta tashi yana rike da hannunta suka koma saman kujera.
    “Faɗi maganar ki baby na"
   "Momi nake son ka kira min a waya ko kuma ka kaini"
“Zan dai kira miki ita a waya amman zuwa can kan ba yanzu ba kin yarda"
  “Eh kira min ita"
Wayar shi ya ciro ya danna kiran yana faɗin “yanzu kuwa yar gidan Momi"
  Bata daɗe tana rawa ringing ba Momi ta ɗauka sai da ya gaisa da ita sannan ya mik'awa Mairo, tana karɓa ta tashi ta nufi ɗakinta da gudu,
Da ido ya bita har ta shige sannan yayi murmushi.

    Saman gado ta zauna tana yima Momi ina kwana “Momi an tashi lafiya?"
  “Lafiya kalau Maryam ya gidan?"
“Lafiya kalau ina Usman da Nura?"
  “Suna nan kalau ko jiya sai da sukayi maganar ki"
  “Momi kice ina gaida su"
  “Toh zasu ji lafiya dai ko?"
  “Lafiya kalau Momi wai jiya Yaya Qasin yake faɗa min Mansura zata dawo"
“Eh haka ne toh mi akayi?"
  Shiru tayi, Momi tace “Maryam kaki saka tsoro a cikin ranki karki kuskura mayar da kanki ballagaza a gaban kishiryar yanzu fa kin tashi daga matsayin da kike na da kin koma *BABBAR MACE* kada ki shashanta kanki ki wulakanta kanki kin gadai mijinki yana sonki,
   Kuma zaman Aure ya kaiki karki biye mata ki kyautata mishi dab haka ne zai k'ara mishi sonki karma ki shiga sabgarta ban kuma idan tayi miki abu karki rama ba.
yadda take mace haka kike matsayinta da naki duk ɗaya ne dan haka karki soma min wani complain indai akan Mansura ne kuma bari kiji na faɗa miki karki yarda ki nuna mata kina tsoro ta dan ba'a nunawa kishiya haka"
   Ajiyar zuciya ta sauke cikin sanyi murya tace “Toh Momi zanyi"
    “Wai Maryam miye anfanin makarantar da nasaki waike ba zaki waye ba kima kamar sauran mata? Yaushe zaki fara ɗaukar darasin da ake koya miki a makarantar?"
  “Daman Momi ni ba wani abin zance zanji ne kawai inda gaske ne zata dawo"
“Toh yanzu ai kinji zata dawo kae naji kin mayarda kanki wata kalar mace ki rik'e k'imarki Allah ya haɗa kanku ya baku zama Lafiya"
   “Amin Momi na gode a gaida gida"
“Gida zaiji ki fara girkinki yau dan bazan sake aiko muku abinci ba"
   “Toh Momi"
Dariya ta dingayi har Momi ta karshe wayar.
   Sannan ta tashi ta koma parlor, kusa dashi ta zauna ta mik'a mishi wayar “Gashi nan na gode"
Karɓa yayi “Toh kun gama sirrin?"
“Eh mun gama sai gobe kuma"
    “Da wayar wa?"
Tashi tayi taja mishi kunne biu “Da kunnen ka" ta watsa da gudu ɗaki.

       ***
Jalof ta girka da rana da dare kuma tayi mishi Tuwo da miyar akusi,
    Sosai Qasin ya jindaɗi ya kuma ci abincin sosai yana sa mata albarka. Da safe ma da dumamen tuwon ya karya.
   Sai goma na safe ya shirya ya fita,
Saida ta gama gyara gidan ko ina gwanin shawa'awa sannan ta shiga tayi wanka ta shirya cikin koriyar atamfa. Ta nufo parlor.
    Tana k'ok'arin zama taji an buga k'ofa basa zaman tayi ta nufi k'ofar tana tambayar waje ne,
   “Khadeeja'tu ce mak'ociyarki"
  Da far'ah ta buɗe mata “Ah Khadeeja sannu da zuwa"
  “Yauwa sannu Amarya ina dai fatar angonki baya ciki?"
“Shigo baya nan ya fita"
   Shigowa tayi ta zauna Mairo ta ɗauko mata drinks,
        Sannan ta zauna tana tambayarta ya gida,
  “Gida lafiya Amarya kin gyara gida sai k'anshi yake"
  Murmushi Mairo tayi “Kai Khadeeja'tu kullum baki rasa magana a bakinki"
   Dariya tayi suka cigaba ta ɗauko mat wani zancen.
  Suna cikin fira Qasin ya shigo.
       Da sauri Khadeeja'tu ta tashi suna haɗa ido ta sakar mishi murmushi ta gaishe shi sannan ta fice,
  Mairo kuma ta nufoshi tana faɗin “Har ka dawo?"
   Tsaye yayi yana kallonta fuskarshi ɗauke da murmushi “Kinyi min kyau baby na"
  Ita ma murmushin tayi “Na gode dear"
  “Haka kawai zaki ce?"
   Murmushi ta sakeyi dan tasan mi yake nufi ta hau saman Kujera ta kamo tsawon shi ta sakar ma kumatunshi kiss.
    Rumgume yayi ya ɗauketa suka nufi ɗaki, saman gado ya sauke ta ya bude drawer ya ɗauki wasu k'ananan documents sannan ya rik'o hannun ta suka nufo parlor,
    Dai-dai bakin k'ofar parlor ya tsayar da ita yana shafa gefen wuyanta “Yau mi zaki dafa?"
   “Mi kake so?"
“Dambu ai kin iya ko?"
Wani fari tayi mishi da ido wadda ita kanta batsan tayi ba “Sosai ma"
   “Toh shi nake so"
“Zan yi maka"
Murmushi yayi zai sake magana yaji horn.
  Juyawa yayi daga shi har ita suna kallon motocin da suka kunno kai gidan,
   Ko ba'a faɗa ba yasan Mansura ce da muk'arrabanta. Juyowa yayi ya kalli Mairo “Baby na bari naje office na jirana but please karki kula su kinji ba zan daɗe ba yanzu zan dawo alright?"
    Murmushi “Okay Allah ya tsare"
  Murmushi yayi mata as respond, har ya juya sai tayi saurin kamo hannun shi ta sakar mishi kiss.
    Daɗi yaji ya shima ya sakarma goshinta kiss, har ya shiga mota murmushi suke sarkarwa juna. Bayan yayi mata key ya ɗago mata hannu har ya fice bai kalli gurin da Mansura take ba.
    Yana ficewa Mairo ta juya ta shige parlor,

  Duk abinda suke Mansura na tsaye tana kallonsu ita da k'awayenta da kuma Sisters ɗin biu. 'Daya daga cikin k' awayen ta tabe baki ta kalleta “Amman Wallahi Qasin ya iya cin mutun da Auro miki wannan yarinyar a matsayen kishiya"
    Nan suma sauran suka hau saka nasu baki suna zugata,
    Sun daɗe tsaye a gurin suna cak-cakar ta sannan suka nufi cikin parlor.
    Basu sallama hakan yasa Mairo bata bi ta kansu ta cigaba da kallonta, “Kee baki ga mutane bane hala?"
   Nan ma banza tayi dasu. 'Dayar ta kalleta tana wata dariya “Wayyo ni Allah wai wannan ce Kishiyar ki?"
   Sai a lokacin Mairo ta kalleta “Eh nice ya ranki?"
   Duk tintsirewa sukayi da dariya Mansura tace “Ita kin ganta kamar k' aruwa ko?"
   “Lallai kuwa k'amar karuwa baki ga har da mishi kiss ba daman dai taba inba haka ba duk yaushe akayi Aure da har zata sake jiki tana irin wannan karuwancin?"
Faɗar sister Mansura.
    Tashi Mairo tayi tsaye ta ɗanja baya ta taɓe baki
“Daɗin abinda dai karuwancin mijina nayi ma kuma duk mace da kika ta zama karuwa a gaban mijinta toh ta isa ne"
   Mansura ta rike baki “Lalala ke yar k'auye yaushe kika zo da har zaki tsaya faɗa min magana Wallahi in kikayi wasa saina miki shegen duka naga uban da zai rama miki"
   Ba k'aramin ɓaci ran Mairo yayi ba cikin zafin rai tace “Yar k'auyen da kike rainawa tafi ki dajara a gurin mijinki da nice Wallahi bazan dawo matukar baje bikona ba dan hakan ya nuna mijina bai damu dani ba ko kuma baya sona"
   Tana kaiwa nan ta juya ta nufi kofar ɗakinta, da k'arfi Mansura ta fisgota ta watsa mata mari. Jefar ita tayi saman kujeara da niyar dukanta. Da sauri wata friend ɗinta fa rik'eta “Haba dai ke kuwa daga zuwan mu zaki daketa ai wannan tsakanin ku ne daga ke sai ita kiyi mata yadda kike so ke k'aramar yarinya kamar wannan ta isa ta raina miki wayo har ta faɗa miki magana haka kawai ki bari sai kin zauna saiki gyara mata nata zaman"
  Sakinta tayi tana faɗin “Ai da kin barni naci uban Shegiya"
   Mairo na tashi ta nufi ɗaki ta sauri tana kuka.

MAIRO CHAPTER 5 KARSHE

Sai da Mairo ta tabbatar da sun gama gyare-gayarensu su tafi, sannan ta fito ta shiga kitchen.
Tana kare girkin ta kama ɗakin,
Sai goma dare Qasin ya dawo gidan kai tsaye ɗakinta ya nufa “Baby na kinga ni sai yanzu aiki ne ya rik'e ni"
Fuskarta shagwaɓa tayi “Amman kuma har dare kadai ko dan matar ka ta dawo ne?"
Kusa da ita ya zauna “Oh karki kawo wannan a ranki yanzu dai muje ki haɗa min ruwa nayi wanka sai mici abinci ko?"
Hannunta ya rik'a suka fice tare.
Bayan yayi wanka ya saka kayan bachi suka dawo parlor suka ci abinci sai dare-dare suke, ba k'aramin bachi ran Mansura yayi ba ganin ko ɗakinta bai leko ba.
Sun daɗe suna fira parlor saida dare ya tsala sannan suka nufi gurin bachi,
_Washe gari_ guraren 8 Mairo ta fito ɗakinta zaune ta tararda Mansura tana kallon k'ofar ɗakinta bata kula taba ta nufi kincin.
Aiko tana shiga Mansura ta rufa mata baya, a bakin kofa ta tsaya ta katsa mata tsawa “Ke uban mi zakiyi a kitchen ɗin?"
Juyowa Mairo tayi tana hararata “Uban ki zanyi kinsan ai yafi daɗi ci wai ke Mansura mi kike ɗaukar kanki ne?"
“Ke ni zaki faɗama wannan maganar? Ke nan fa gidana ne kuma Wallahi in baki bi a hankaliba sai na miki ɗan ba zan duka"
Taɓa hannu Mairo tayi “Amman naga ai da kunya ki kira kanki matar gida matar da bata san darajar mijinta mijin kullum cikin kuka yake da ita ke bari kiji na faɗa miki yanda nan gidan yake gidan mijinki haka nima yake gidan miji n babu banbanci dan haka ki fita idona kona gyara miki zama"
Hannu Mansura ta kai zata mare ta da sauri Mairo ta rike “Kinyi na ɗaya bazaki kara na biu ba kinyi kaɗan ki sake sakamin hannu a fuska ko wacan karon da kikayi na kyaleki saboda mijina ne"
Jefar da hannun nata tayi ta juya ta cigaba da aikinta.
Tsaye Mansura tayi tana mamaki da kuma jin tsoro dan gani take kamar ba Mairo ba,
    Ruwan zafi Mairo ta ɗora sannan ta shiga feraye ɗankali. Har lokacin Mansura na tsaye tana kallonta,
  Can ta matsa kusa da ita ta kai mata wani mugun shuri, tashi Mairo tay daga zaune ta dake ta wankeata fuska da mari biu ta janyo muciya ta buga mata ita a kafaɗa,
  Da sauri tayi baya ta dafe kunci tana zaro ido “Maryam ni kika yima haka?"
   Wani ya tsine hanci tayi “Kaɗan kenan daga abubuwan dana tanadar miki saibna gyara miki zama acikin gidan nan kuma ki fice ki bari guri ko yanzu na chaja miki halinta"
   Kai ta gyaɗa “Ke wai gidan ubanki ne nan Wallahi zan halakaki"
   “A'a ba gidan ubana bane amman inajin ke gidan naki uban ne ko ki fice ki bani guri ko Wallahi na miki wanka da ruwan zafi nan"
  Tsaye tayi tana kallonta cike da tsoro saida taga ta nufi ruwan zafin sannan ta juya da sauri ta fice.
'Dakinta da dawo ta zauna tana mamakin Mairo tabbas aljanune da ita haka zuciyar ke nasa mata dan daga ganin faɗan nan bana banza bane iskokinta ne ke son tasowa, haka ta dinga tunane-tunanenta tana naman hanyar da zata biyo mata.
    
Tana ficewa Mairo tayi k'wafa ta buga tsale “Yauwa yanzu kin fara gane karatun kenan ai nima yar issakar kaina ce"
  Cigaba tayi da girkinta tana mai jindaɗin abinda tayi har ta gama sannan ta shiga tayi wanka ta shiga tada Qasin,
   “Yaya tashi abincin yayi"
  Janyo ta yayi ya rumgume “Toh bbyna"
  Ya daɗe rumgume da ita sannan ya tashi ya shiga bathroom,
Bayan ya gama abinda zaiyi ya fito suka nufi dining, suna cikin karyawa ne Mansura ta fito daga & ɗakinta dan muryar su taji ya tabbatar mata da suna dining.
  Har ta zauna Mairo harararta take. Plate taja da cup zata zuba ta bude kular k'wai zata zuba,
   Nan Mairo ta tashi tsaye “Ke mi zakiyi?"
  Banza ta mata ta cigaba da zubawan,
Kular k'wan Mairo ya janyo da k'arfi “Ai baki isa ba Wallahi indai zakice sai dai ki girka ni mijina kawai nake iya girkama abinda duk wata k'atanyar banza tayi kaɗan Wallahi"
   Kallo Mairo Qasin yayi kamar yayi magana sai kuma yayi shiru ya cigaba da cin abincin,
   Mansura ta Taɓe baki “Ni ba biye miki zanyi ba dan na fahimcin baki da hankali ba ki kuma da tarbiya"
   Nan Qasin ya saka baki “Ke ya isheki haka ke idan na Maganar tarbiya har kina da bakin magana?"
  Mamaki ne ya cika Mansura “Qasin ni kake faɗama haka saboda kayi sabuwar Amarya kan uba" ta faɗa tana gyaɗa kai.
  Filas ɗin ruwan zafi Mairo ta buɗe tana faɗin “Yanzu zakiga rashin hankalin nawa"
   A fuska ta watsa mata su kamin ta ankara ta k'ara watsa mata su har so uku, cikin hanzari Qasin ya rik'e yana “Maryam lafiyarki?"
   Ita kuma ta faɗi tana ihu da murzar jiki.
   “Wayyo Allah na shiga uku ta kashe ni wayyo Allah"
Nan ya saki Mairo ya nufe yana kiran sunanta, rik'a ta yayi ya tada ita ya nufi mota da ita.
Tsaye Mairo tayi tana kallonsu har suka fice sannan ta cikama bakinta iskan dan tasan tayi ɓaran-ɓarama.


Asibiti ya nufa da ita bayan an bata gado, ya kira a gidan su ya sanar.
Cikin yan mintuna mahaifiyarta ta iso tare da k'anenta biu, tambayarshi suka rik'ayi yadda abin ya faru bai faɗa musu gaskiya sai kawai yace ruwan zafi ne ta ɗauko sai ya watsar mata a fuska da jiki.
   Sai da ka kira sallar Azahar sannan ya baro asibitin ya nufo gidan Momi, a masallacin dake kusa dasu ya tsaya yayi sallah sannan ya shiga ciki.
   Tun daga yanayin Sallamar shi Momi ta gane akwai abinda yake faruwa bayan sun gaisa ta soma tambayarshi, “Ya akayi yau naga kamar ranka a ɓace?"
  Saida ya sauke ajiyar zuciya sannan yace “Momi Maryam ce ta watsama Mansura ruwan zafi"
   “Subhanalllahi garin yaya?"
Nan ya kwashe abunda ya faru ya faɗa mata.
  Baki Momi ta rik'e “Da gaske Maryam ce tayi?"
  “Itace Momi kuma ni irin masifar nan ce nake gudu kar wata rana suje suyi abinda yafi haka kuma"
   “Ai maganin biri karen baguzawa abinda Maryam tayi Batayi dai-dai ba amman kuma hakan zai sa Mansura ta ɗan saurara mata"
  Qasin ya gyaɗa kai “Ko kuma tace saita rama ba"
   “Abinda nake so dakai indan taji sauk'i sai ka tarasu guri ɗaya kaja musu kunne"
  “Toh Momi zanyi haka In'sha Allahu"
  Sai da yaci abinci sannan ya bar gidan.

  Mairo na zaune parlor ya shigo da sallama amsa mishi tayi tana kallon cikin idonshi, k'in yarda yayi ya haɗa ido da ita tana mishi sannu da zuwa ya amsa ya wuce dakinshi,
   Da ido ta bishi har ya shige sannan ta zauna saman kujera tana sauke ajiyar zuciya. Duk sai raji ba daɗi. Ta kusan minti 30 a haka sannan ta tashi ta nufi ɗakin nashi.
   “Assalamu alaikum" a sanyaye tayi sallama shi kuma ya amsa mata yana daga kishingiɗe tana dannar wayar shi,
   Juyawa tayi zata koma nan ya ɗaga kai ya kirata “Maryam"
  “Na'am" Juyowa tayi ta k'araso kusa da gadon shi idonta cike da hawaye.
   Nan ya unk'ura ya tashi zaune “Mi akay?"
  “Ba komai"
“Ba komai kike kuka?"
“Naga kana fushi danine"
  “Kan mi zanyi fushi dake ni bana fushi dake amman abinda kikayi ban jidaɗi kuma baki kyauta ba"
  “Amman ita ta kyauta data fasa min kai ko?"
Cike da shagwaɓa tayi maganar.
  Murmushi yayi mata ya janyo ta ya zaunar saman k'afafunshi,
  “Toh ramuwace kikayi kenan?"
  “A'a nidai bance ba"
“Amman nasan nufi kenan naji yanzu kin rama ai shi kenan ko dan Allah karki sake kinji ku zauna lafiya nine za jindaɗi in kika min haka karki sake kulata"
   Kai ta ɗaga mishi “Bazan sake ba amman sai idan ita bata min ba"
   “Ba zata miki ba zanja mata kunne itama"
  “Naji tashi muje kaci abinci"
   Tashi yayi badan yana jin yunwa ba sai dan yana gudun yace baya ci tace mishi fushi yake da ita.
   Zamansu su cigaba dayi na ma'aurata wani abu bi sake shiga tsakanin su,

***      ***      ***    ***
Mansura kin yarda tayi ta dawo gidan bayan an sallame ta daga asibiti danginta sai masifa suke ita kuma tace sai da ya zaɓa ko ita ko ita ko kuma ya raba musu gurin zama shi kuma yace ba zaiyi ko ɗaya ba Momi tace mishi ya samu musu ido idan ta gaji ita zata nemi dawowa,
    

*BAYAN WATA UKU*
     Rufe yake da ido Mairo na gudu yana binta suna yar link'wa. Saman kujeara ta hau tayi tsaye tana taɓa bayan shi juyowa yayi cikin hanzari ya rike yana faɗin “Na kama" ita kuma ta fashe da dariya suka faɗi k'asa,
  Wata razzanann ihu ta saki lokacin da kuiwar  hannushi ta daketa a mara by mistake.
    Da sauri ya buɗe idon yana tambayar ba'asi. kasa magana tayi sai kuka take tana rike ciki, nan ya shiga duba cikin. Jikin da yaganine ya katse mishi hanzari,
     da sauri ya ɗaga ta amman ta kasa tsaye sai kuka take tana kiran Abban ta saman kujera ya zaunar da ita ya nufi ɗaki, riga yasa ya ɗauko keys ya dawo parlor a guje ya ɗauke ta ya nufi mota da ita.

Story continues below

           Asibiti mafi kusa ya nufa da ita yana isa ka wuce da ita Emergency,
  Shi kuma ya kasa zaune ya kasa tsaye sai safa da marwa yake a bakin kofar. Can Momi ta faɗo mishi a rai da sauri ya taɓa aljihu shi da niyar ɗaukar waya yaji babu komai dan ba'a cikin shiri ya fito ba,
    juyawa yayi da sauri ya koma gurin da aka tana da dan parking din Motocin Asibitin da na mutane ya shiga tashi motar ya ɗauki hanyar gidan Momi.


     Hankali a tashi ya shigo yana kiranta.
  Da sauri ta fito daga kitchen “Gani nan Qasin lafiya"
  “Momi Maryam ce na kai Asibiti yanzu"
“Lafiya miya sameta?"
Kasa faɗa mata ainihim abu  yayi sai kawai yace “Ruwa suka zuba a kasa shine tana takawa sai ta faɗi jini ya dinga mata zuba"
  “Inna lillahi wainna ilaihi raji'un wace Asibitin ka kaita?"
"Momi saka hijab ɗinki muje a Special Rahama hospital na kaita yanzu suka shiga da ita Emergency"
  Kitchen ɗin Momi ta koma ta kashe gas ta ɗauko Hijab ɗinta suka fice.
       Gudu ya rik'ayi sosai cikin yan mintuna suka iso Asibitin direct Emergency ya nufa.
Koda ya isa har likitan ya fito daga ciki yana tsaye waje yana magana da wata Nurse. Qasin yace “Yauwa gama likitan daya karɓe ta can"
   Gurin shi suka nufa ko k'arasawa basu yi kusa dashi ba Momi ta shiga tambayarshi “Likita ya jikin wadda aka kawo?"
    Kallon Momi yayi ya ɗan murmushi “Kune iyayenta? yanzu nake tambayar wadda ya kawota"
  “Mune muka kawota ya jikin nata?" Qasin ya tambaya
  “Da sauki bachi take yanzu muje office ɗina akwai maganar da nake sonyi da kai"
   Shine a gaba suna biye har ya isa office ɗin gurin zama ya nuna musu bayan ya zauna ya ɗauko wata takarda yayi rubuce-rubuce ya mika mishi “Wannan maganin za'a siyo mata kuma ina son sanin abinda ya faru da ita har ya janyo zubar jinin nan nata?"
   K'arya da yayi ma Momi ita yayi ma likitan yana noce-noce da kai.
   Likitan yace “Toh kunci sa'a da cikin bai zube gaba daya ba amman dai yayi zuba dan haka kawanakin haihuwar ta zai karu kamin ta haihu"
   Bakin Qasin sake yana kallon likitan dan bai fahimci inda ya dosa ba,
   Momi cikin rashin fahimta tace “Dr mi kake nufi ciki ne da ita ko mi?"
   “Eh tana da ciki baku sani bane? 3 months amman yanzu ya koma 2 saboda zubar da yayi"
  “Dr da gaske?"
“Ya no doubt zaka iya zuwa wani Asibitin ka bincika idan baka yarda ba"
  Baki Qasin ya rufe ya lashe ido yana sauke wani nauyayen ajiyar zuciya. Can ya tashi tsaye ya yaba likitan baya ya rumgume hannayenshi yana murmushi,
  Momi kuma ta ɗaga hannu sama tayi yima Allah godiya. Likitan dai sai kallonsu yake yana murmushi. Momi ce tayi ma likitan godiya shi kuma ya ɗauki takardar maganin suka fice.


         A hankalin ta fara motsa hannunta har ta buɗe idonta,
   Qasin ta fara yin karo dashi yana zaune kusa da ita yana murmushin da duk wadda ya gani yasan daga zuciyashi yake. Hannu yakai ha shafa kanta “Babyna kin tashi?“
Kuka ta rik'a k'ok'arin k'ak'arowa “Ina Momi?"
  “Tazo ta duba ki sai kuma tace bari taje ta girka miki abinci"
  Shiru tayi bata sake cewa komai ba. Nan yaja yatsanta yana murzawa “Maryam albishirinki?"
  Kallonshi tayi “Mi akayi?"
  “Mi zaki ban idan na faɗa miki?"
Kuka tasa mishi “Nidai kawai ka faɗa min"
  Ido ya sakar mata yana murmushi har sai da tayi kukan da gaske sannan ya shiga share mata hawaye yana faɗin “Likita yace kina ɗauke da juna biu kina da ciki"
  Tashi tayi zaune “K'arya ne"
Qasin ya ɗan sha kunu ya lak'aci kuncinta “Toh wa yake yin k'aryar?"
  “Likita mana"
“Toh bari na kirashi kiji daman ai yace idan kika tashi na kirashi"
  Bai jira cewarta ba ya tashi ya fice.


     Bayan wasu yan mintuna ya shigo tare da likitan suna dariya,
   “Sannu ko ya jikin naki yanzu?"
“Da sauki"
Qasin ya zauna kusa da ita “Likita wai har yanzu bata yarda tana da ciki ba"
   Dariya yayi “Saboda mi ni har yanzu mamaki kuke bani ace wai bakusan tana ɗauke da ciki ba har na tsawon lokaci haka"
   “Toh bata wata alama na masu ciki balle na gane tunda bata amai bata rashin lafiya ba wani"
  “Eh ai ba duk cikine yake saka amai ba wani sai ciki ya tsofa wani sai yakai tsakiya wani tun yana farkon shiga kai wani ma har ta haihu ita abin yazo mata da sauki ne shiyasa amman ko tofar da yawun nan batayi ne ko kwaɗayi? Kuma baka lura da lokutan period ɗinta ba?"
    “Bata tofar da yawu gaskiya sai dai kwaɗayi da maganar period kuma ni duk ban ɗauka cikin ne ba"
  Murmushi likitan yayi ya shiga duba “Akwai wani abin da kike ji yanzu?"
Kai ta girgiza “Babu wai da gaske ciki ne?"
  “Ciki ne mana nan da wasu watanin saiki haifo mana baby boy ko girl koma biu ko uku"
   Shiru tayi kamar mai tunani ta ɗora hannu saman cikin, nan Dr ya shiga faɗa ma Qasin wasu abubuwan daya dace tayi ko kar tayi da kuma wa yanda zata ci,  ya dade yana mishi bayani sannan ya fice.


Story continues below

   ***, *** ***
Kwananta biu Asibitin aka sallame ta bayan likitan yasa ya buɗe mata file ɗin awo,
   Momi k'in yarda tayi su koma gida sai wai abubuwa zasu mata yawa tun shi namiji ne ba zama yake ba k'ara ta ɗan kwana biu gurinta sannan.
   Qasin ba dan yana so ba sai dan ganin ta nace akan hakan dole tasa ya sai kyali ta dawo gurin Momi da zama, ta kusan wata biu gurin Momi baya aikin komai sai dai taci tasha sai bachi da kuma kallo Momi ta dinga shagwaɓata kamar gareta farau ciki.
   Sai da Qasin yayi kamar yanayi sannan Momi ta samu wata yar tsohuwa ta haɗa su wai ta rik'a kama mata aiki, da kuma lurarda ita wasu abubuwan da ya kamata ta sani.
     Aɓangaren Mansura tunda labarin ya sameta ta shiga damuwa da nadama kullum cikin kuka take tana dana sanin abinda tayi,
      
****   ****    ****
   Wani yanayi Qasin ya sami kanshi wadda bai taɓa mafarkin samun haka ba wai yau gashi shida matarshi suna rainon ciki,
  Kula yake da cikin sosai yana Shagwaɓata da tarairaiyarta hakan yasa abu kaɗan sai tasa mishi kuka shi kuma duk yabi ya rikece. Cikinta na wata shida yasa ta shirya shi da ita suka je k'auye gaida Gwaggo,
    Aiko kamar ta haɗeye Mairo dan murna dan rabonta da ita tun tana Amarya ga kuma cikin da taga jikinta dan Qasin hana Momi yayi ta faɗa, aiko murna gurin Gwaggo ba'a magana ta rasa inda zata saka Mairo. Duk inda dangi suke na kusa sai da Gwaggo ta kai ta duk da ita Mairo ba hakan taso ba wai ita kunya take ji,
     Kwananta biu can ran na uku Qasin ya zo ya ɗauke ta abubuwan su na k'auye Gwaggo ta haɗa mata bayan tayi mata tsabar daddawa da miyar kuka, da guro. Da kayayyakin k'walama na k'auye.

***         *****     ****    ****

Ganin babu Sarki sai Allah yasa dole Mansura ta nemi dawowa gidanta,
  Bai hana taba amman kuma bai bari ta dawo gidan ba dan ganin yake wata fitinar ce zata sake haddasuwa idan ta dawo tunda yasan halinta da kishi kuma Mairo da ciki komai zai iya faru hakan yasa ya ware mata ɗaya daga cikin gidajenshi ta tare can duk da ba hakan yaso ba dan wasu ganin suke raba mata kesa yara su tashi ba haɗin kai ko kuma su rik'a k'iyayyar junansu,
   
   Wasa-wasa cikinta ya tasarma wata na takwas. Sam Qasin baya yarda tayi wasa da awo dan yasan muhimmancin zuwa awo ga mace mai ciki yana hana faruwar wasu abubuwan yana kuma taimakawa mace ta sami saukin haihuwa.
     kullum Qasin cikin zolayar yake wai yan biu zata haifa duk da likita ya tabbatar musu da ɗa ɗayane a cikinta,
   Itan babu abinda ta tsana irin wannan maganar dan ɗan ɗaya ma tunanin take yadda zata haifoshi.



***          ****        *****     ******
  Duk zaune suke k'asan carpet suna kallon Tv. Ita kuma sai faman nishi take tana cin gauta,
Hannu yakai ya shafa cikinta “Wannan cikin Akwaishi da ciye-ciye koda yake daman ance yan biu haka suke"
  B'ata fuska tayi “Ka fara ko nace maka nidai bana so"
  “Toh ko baki so idan Allah ya nufa sai kin haifa baki ga cikin kullum k'ara girma yake ba?"
   “Ai Dr yace ɗa ɗaya ne"
  “Toh likita Allah ne? Abinda Allah yaga dama yake sanar dasu kuma so nawa akayi haka kinga an haifi ba abinda suka ce ba? Kedai kawai kice Allah ya sauke ki lafiya"
   “Amin amman nidai ɗaya zan haifa"
Murmushi kawai yayi ya cigaba da kallon yana shafa cikinta.
   Kwantowa tayi saman jikinshi “Yaya" a hankali ta kira sunan shi
  “Na'am K'anwata"
“Ya maganar tafiyarka tana nan?"
   “Tana nan amman idan kin barni ba kince bakison naje ba?"
“Toh baza ni ba"
“Toh kayan da naga kasa a boot ɗazun fa?"
  Murmushi yayi “Wanine ya rok'eni tufafi shine na saka a mota idan zan fita sai na biya na kai mishi"
  “Amman kuma ka saka a jakar da kake tafiya da ita?"
  “Eh har jakar zan bashi"
  “Da gaske?"
“Eh mana ba kince kar naje ba amman fa abubuwa zasu wuce ni da yawa kinga tunda kika zamu cikin nan duk wani abun da zai kaini nesa bana zuwa wannan ma dan naga yana da muhimmanci ne dan kuɗi zamu samu ba kaɗan ba kuma kinga zamu haɗu da wasu turawa ne idan sun mana interview munci sai su saman hannu mu fara wata kwangila a South Africa"
  “A'a nidai bana so ka bari har wani lokacin ai duk gun da arzikinka yake sai ka ci"
   Kwantar da ita ya ya k'arayi “Ai a zani ba tunda kince bakiso amman dai da kin Amince da yafi"
  “A'a ban Amince ba"
“Ok My Queen"
   Dariya tayi shima yayi murmushi ya rumgume ta,
       Sun daɗe parlor sai da yaga ta fara jin bachi sannan ya tashi suka shiga Bedroom.

Story continues below

       
      *WASHE GARI*
Tun da sukayi sallar A'suba suka sake komawa bachi. Mairo bata farka ba sai 9 da rabi. Ta daɗe zaune saman gadon sannan ta sauko tana wani abu da jiki kamar wadda ke mata ciyo,
   Sai da ta shiga bathroom tayi fitsari sannan ta nufi parlor sanye da doguwar rigar bachi kanta ba ɗankwali,
    Murmushi ya rik'a sakar mata har ta k'arasa kusa dashi tana kallon dining room. “Baba Ladi bata k'are haɗa breakfast ɗin bane?"
    “Ta kare mana acici ke nake jira ki tashi muci"
Sai a lokacin ta kalleshi “Good morning"
Ta faɗa tana shafa kanshi tana murmushi
Kiss yayi mata a cikin “Morning my babies how was your night?"
  Dariya tayi taja mishi kunne. Nan ya tashi tsaye yana faɗin “Muje nayi miki brush muci abinci"
   Hannunta yaja suka koma ɗakin.

*11:5am* Suka gama breakfast cikin dabara Qasin ya zare jiki ya shiga ɗakin shi yayi wanka, yana fitowa ya tararda Mairo zaune saman gadonshi tana kallon k'ofar bathroom ɗin.
    Murmushi ya sakar mata “My babies"
  “Ina zaka je?"
Zaunawa yayi kusa da ita yana tsane jikinshi da tawul “Bana faɗa miki tun shekaranjiya ba ina da ɗaurin Aure?"
  “Eh amman ai K'arfe biu kace za'ayi"
   “Inason na biya gurin Momi ne kamin lokacin yayi dan kusa da sune"
   “Da gaske?"
Fuskarta ya rik'a ya goga mata hancin shi “A'a da k'arya"
Murmushi tayi “Na shirya ka kaini gurin Momi sai ka wuce? Tun da kace zaja biya"
      Shiru yayi har na wani lokacin sannan yace “Eh jeki shirya"
  Da dariya ta tashi ta fice.

       Tare suka tafi gidan Momi yana yin parking yayi saurin riganta shiga parlor, koda ta shiga bata tararda kowa ba kujera ta samu ta zauna taba kiran Momi.
    Kitchen Momi ta fito tare da Qasin tana murmushi “Oyoyo Maryam yau gidan mu?"
  “Eh Momi ina kwana?"
  Zaunawa tayi tana faɗin “Wuni dai ko ai sha biu ta wuce yanzu ya gidan?"
“Lafiya kalau ina su Usman?"
   “Yana makaranta jiya ko Siraj ya turo mana hoton matar da zai Aura"
    Mairo tace “Eh muma ya turo mana Momi kyakkyawa da ita fara"
  “Eh yace yana nan zuwa a shirya zuwa gaida iyayenta"
     Qasin yace “Wai Momi yar Abuja ce?"
  “Eh yace acan take ita da iyayenta"
   "amman yayi dacen mata gaskiya" fadar Mairo.
  Momi tace "Ai ko ita tayi dacen miji dan ɗaya nima ba baya ba"
  Duk dariya sukayi Qasin ya shafa kanshi “Nikan bari naje ina son biyawa wani guri"
Momi ta kalleshi “Ok Allah ya tsare"
   "Amin"
Da ido Mairo ta bishi har ya fice. Sannan taji ya kira ta,
    “Na'am" amsawa tayi ta tashi ta nufi k'ofar, tsaye tayi bakin k'ofar tana faɗin “Gani"
  Hannu yasa ya janyota ya rufe k'ofar.
   “Baki ce Allah ya tsare ba"
  “Toh Allah ya tsare duk abinda aka ci ka kawo min"
  Dariya yayi “Toh an gama Hajiya ta"
   Nan ya matso kusa da ita sosai yasa bakinshi cikin nata ya soma kissing.
        Sun daɗe haka sannan ya cire bakinshi yana sauke ajiyar zuciya ya ɗora goshinshi saman nata ya lumshe ido,
   Can ya ɗauke kanshi yana murmushi “Sai na dawo biebes na I LOVE YOU"
“I love you too Allah ya tsare"
Murmushi yayi mata as respond ya nufi gurin motarshi,
   Har ya fice hannu take ɗaga mishi yaba dago mata. Saida Mai gadin ta rufe gate sannan ta juya ta koma cikin parlor.
 
      shigowanta yasa Momi ta kalleta tana murmushi “Allah ya saukeki lafiya Maryam wannan ciki sai kace yan biu"
  “Haka yaya yake cewa shiyasa ko wani aikin kirki bana iyawa" ta faɗa tana k'ok'arin zaunawa,
  “Ai dole yanzu ma ba dan kar Ladi tace an barta ita ka ɗai ba da sai kiyi zamanki har ya dawo"
   “Ai sai ya dawo zamuje"
  “A'a yace da maraice yayi na turaki gida kar na bari dare yayi"
  Kallon Momi tayi “Momi ba ɗaurin Auren zaije ba?"
   Murmushi Momi tayi
  “Yaje kaduna amman yace kar a faɗa miki sai ya tafi"
   Nan da nan gashin jikinta ya tashi idonta suka cika da kwallah kan kace kwabo har hawaye sun fara mata zuba,
    Momi tace “Toh ai ba dade wa zaiyi ba kwana biu zaiyi ya dawo"
     Kuka ta sama Momi sosai “Niko Wallahi ba zan koma ba sai ranar daya dawo ko shekara zaiyi"
    “Toh gaki ga guri ai indai zamane ita Ladi anjima sai Nura yaje ya faɗa mata taje gida har ki dawo daga nan sai ya biyo miki da kayanki"
   Duk da hakan ta daɗe tana kuka Sannan ta share hawayen ta cire hijab ɗinta,
    Momi ta tashi ta ɗauko mata fruits.
 
  ***    ****   *****
Tunda ya tafi kullum cikin kiranta yake kirn safe daban na rana daban na dare ma daban.
      Ranar da zai dawo Mairo ta tashi da wani irin matsanaicin ciyon kai da zazzaɓi wuni tayi kwance breakfast ma dak'er tayi bata fito ɗakin ba saida Momi ta kare shirya ma Qasin komai da tasan zai buk'ata dan ya faɗa mata nan zai sauka,
   Abinci kusan kala uku Momi ta shirya mishi sannan taje tayi wanka. Mairo ma wankan tayi ta shirya cikin wani les Sky Blue bata yi makeup ba powder kawai ta shafa sai mai a leɓe ta dawo parlor ta zauna. Fuskarta babu walwala,

   Zaune tayi a parlor har kusan biyar na yamma. akai-akai take duba wayarta dake saman hannun kujera kamar mai jiran kira gaban sai faɗuwa yake, Guraren biyar da rabi ta samu kanta ciki wani yanayi kamar ta fasa kuka. Sai juye-juye take tana sauke ajiyar zuciya.
  “Amman yaya ya daɗe bai iso ba ko bai taso da wuri bane" a fili ta furta tana kallon k'ofar ɗakin Momi,
   Wata zuciyar na nuna mata ta kira shi sai kuma taji ba zata iyaba.
   Tana haka taji Parking ɗin mota da k'arfi ta zabura tana kallon k'ofa bugun gabanta ya k'aru,
     Usman ne ya shigo hawaye na mashi zuba, suna haɗa ido yayi saurin sadda kanshi yana share hawayen.
    Zaro ido Mairo tayi nata idon suka cika da k'wallah “Lafiya Usman miya faru?" ta tambaya muryar ta na rawa.
      “Ba komai ina Momi?"
   Kasa bashi amsa tayi ta k'ura mishi ido tana son karantar abinda yake ɓoye mata,
     Fitowar Momi ce tasa ta daga kai tana kallon upstairs. Hawayen da ta gani a fuskar Usman su ta sake gani shinfiɗe a fuskar Momi,
     Rawa jikinta ya shigayi ta fara wani wahalallen numfashi, kamar haɗin baki wayarta tayi ringing.
    Da sauri ta kalli wayar tana haɗe yawu,
     Cikin hanzari Usman ya kai hannu ya ɗauke wayar ya kashe.
       K'ara zaro ido Mairo tayi hawaye suka shiga mata zuba kamar an koro su, Momi na da fata ta saki wata irin razananniyar kara ta faɗi zaune dafe da ciki.

 

Da sauri Momi ta kamata wani irin rik'o Mairo tayi ma Momi da k'arfi tana wasu zafafan hawaye “Momi ya rasu ko? Yaya ya rasu?"
    “Ba rasuwa yayi accident ya samu a hanyar shi ta dawowa"
  Usman ne ya bata amsa dan Momi in banda kuka babu abinda take.
    Kai ta girgiza “A'a nasani ɓoye min ne kuke ya rasu na shiga uku na bani na lalace"
  Bakinta Momi ta tushe tana girgiza mata kai,
  Sun dade a haka kowane su sai kuka yake Usman ne yayi k'arfin halin yace “Momi kuka bayayi addu'a zakiyi bari naje Asibitin na gani"
   Momi na k'ok'arin tashi Mairo ta rigata “Zan bika Usman"
  “A'a Maryam ki zauna gida har na dawo" Momi ce take maganar cikin kuka,
  “A'a Momi dan Allah ki barni naje koda gawarshi ce na gani babu wani abinda zaku ɓoye min na riga naji komai dan Allah Momi karki hana ni"
   Shiru Momi tayi kamar mai tunani sannan ta nufi upstairs ta ɗauko hijab ɗinta dana Mairo ta fito. Momi da kanta tasa mata hijab ɗin sannan ta sama kanta suka fice.

   Suna isa Asibitin suka nufi gurin da wata Nurse ta nuna musu, tsaye sukayi bakin k'ofar cirko-cirko kowanne fuskarsa da hawaye in banda Usman da yake k'ok'arin danne kuka,
   Likitoci uku ne akan shi suna aiki bashi taimakon gaggawa. Sunyi awa uku a ɗakin suna abu ɗaya dak'er suka sami numfashinshi ya tsaya dai-dai yadda ake buk'ata, sannan suka cigaba da duba sassan jikinshi,  Ko a hakan ma sun daɗe sannan suka fito.
    Da sauri Momi ta tare su “Dr yana da rai yuwa?"
   Ido Dr ya sakar mata sannan ya kalli Usman ya sake kallonta ba tare da yayi magana ba. Momi cikin kuka tace “Dr ka faɗa mana kawai ni uwar shi ce wannan k'anen shine wacan kuma matarshi ka faɗa mana kawai"
  Ajiyar zuciya ya sauke yace “Mama ki kwantar da hankalinki bai mutu ba ya daiji mummunan rauni ne babu kariya aciki amman dai awazonshi sun samu matsala wadda ya haddasa murdewar jiyojinshi"
   Kuka Mairo tasa “Dr kawai kace mana ya mutu"
Nan ya kalleta “Bai mutu ba nan da wasu awanin zai farka har magana zaku iya yi dashi amman ba zai iya tashi ba ko cin abinci ya haɗe har sai an mishi aiki"
  Usman ya faɗi zaune dafe da kai yana “Inna lillahi wainna ilaihi raji'un"
    Momi ma durkuashewa tayi tana kuka, Mairo kan hawayen tsaya mata sukayi k'ofar ɗakin kawai take kallo,
_ni kuma na kasa ganewa shin farincikin ance yana raye ne ya hana mata kuka ko kuwa dan ance ya samu matsala ne bakin cikin ya hanata kuka_.?

   A hankalin ta jingina jikinta jikin ginar dake bayanta ta sulale k'asa zaune ta rafka tagumi,
  Daker Usman ya lallaɓa Momi ta tashi daga inda take ta zauna saman kujera,
Nan ya zauna kusa da ita yana bata hak'uri.
  Kiran sallar I'sha ice tasa kowanne su ya tuna da bai yi magariba. Da sauri Usman ya tashi “Momi bari naje nayi Sallah"
Kiran shi tayi ya juyo tace ya bata wayarshi ba musu ya mik'a mata ya fice,
   Wata number tasa ana ɗauka ta fda mata wasu abubuwa da za'a dauko mata. Bayan ta ashe wayar ta kalli Mairo tace “Zaki wani abu?"
  Kallonta kawai Mairo tayi ta kauda kai ba tare data bata amsa ba,

   Zirga-zirga yan'uwan da abokin arziki da suke kusa suka rik'ayi Asibitin duk da likita bai ba kowa damar shiga ba, sai dai su yima Momi da Mairo sannu su tafi.
   Guraren 3 da rabi likitan ya sake shiga ɗakin bayan wasu yan mintuna ya fito ya kora Usman dake zaune saman kujera a hankali dan a zaton shi su Momi sunyi bachi ganin duk sun zaburo yasa ya ɗaga musu hannu “No kuyi zamanku shi kawai nake buk'atar yazo"
  Da sauri Usman ya tashi ya nufe shi. Shi kuma ya k'arasa buɗe mishi kofar suka shiga tare.
        Maida k'ofar Dr yayi ya rufe sannan ya kalli Usman yace “Ya farka baya buk'atar hayaniya shiyasa na kiraka kai ka ɗai dan nasan su zasu iya sa mishi kuka har wani abu ya faru"
   Usman ya rike shi “Da gaske Dr"
  “Gashi can zaka iya zuwa ka ganshi sai dai ba zai iya magana ba sai nan da awa biu"
   Cikin sauri ya k'arasa gaban dagon yana kallon Qasin shima shi yake kallo kowanne idonshi cike da hawaye.
    A hankalin Usman ya kira sunanshi cikin muryar kuka “Yaya" nan Dr ya tari numfashi shi “Na fada maka baya son hayaniya ciyinshi zai iya karuwa idan ka tada mishi hankali dn haka ina son ka zauna dashi ne kawai har lokacin da zaiyi magana kar kuma ka barsu su shiga har sai na bada izini"
   Kai kawai Usman ya ɗaga mushi yaja kujera ya zauna,
    Shi kuma Dr ya juya ya fice.
     Momi na ganin ya fito ta tareshi “Dr ko ya mutu ne?"
  Murmushi ya ɗanyi “A'a bai mutu ba ɗanki fa shida wata matsala idan ba wannan matsalar dana faɗa miki ba"
   “Toh yanzu Dr babu wani abu da zaku iyaye ku shawo kan wannan matsalar?"
  "Za'a iya mana za'a iya yi mishi aiki sai dai aikin da hatsari sosai kuma Dr ɗaya ne ya k'ware sosai akan wannan matsalar duk Nijeriya shine Dr Siraj kuma yanzu an mayar da shi Abuja da aiki sai idan transfer za'ayi muku kuje can Abuja ko kuma na ku fitar dashi waje gaba ɗaya gun da k'wararrun suka da yawa dan a ganina fitar dashi wajen yafi"
    Rufe baki Momi tayi hawaye suka zubo mata, hak'uri Dr ya bata sannan yasa kai ya fice.

Story continues below

***

Sai da awa biyu ta cika cif sannan Qasin ya lumshe ido ya haɗeye yawu har lokacin Usman kallonshi yake yana hawaye,
    A wahale ya soma magana “Ina Momi"
  B'ari jikin Usman ya shigayi cikin rawar murya ya bashi amsa, “Tana waje Yaya ya jikin naka?"
   “Maryam tayi kuka ko?"
   “A'a batayi ba"
“Karkamin karya Usman"
  “Tayi yaya ita da Momi duk sunyi"
   Har lokacin idonshi a rufe yake yana maganar duk da turo k'ofar da Momi tayi ta shigo baisa ya buɗe ido ba sai hawaye kawai suke mashi zuba,
   Cikin muryar kuka Momi ta kira sunan shi “Qasin... "
   Ya dade kamin yayi magana “Momi kibar kukan nan bana son kina kukan nan koda na mutu"
   “Bazan iya ba Qasin bazan iya juye ganin halin da kake ciki ba banyi kuka ba kaima kanka ai kukan kake"
   A hankalin ya buɗe ido ya kalleta “Momi ina kukane saboda ni kadai nasan abinda nake ji sannan ina tunanin yadda rayuwarku zata kasan idan bani"
    Cikin kuka Momi tace “Ba zaka mutu ka bar muba Qasin kada Allah ya nuna min san wannan ranar ina raye"
   “Ina Mansura ina Maryam?"
   “Mansura tana can kwance tun da labarin ya sameta ta faɗi ana mata k'arin ruwa Maryam kuma tana nan waje zaune"
  Usman ne ya bashi amsa
   Ya ɗan daɗe kamin yace “Kira min ita" da sauri Momi ta juya sai da Usman yayi kamar ya dakatar da ita akan abinda Dr yace sai kuma yaji ba zai iya ba,
   Da sauri-sauri gudu-gudu Mairo ta shigo ɗakin ta k'araso kusa da gadon shi “Sannu Yaya sannu" Abinda ta ringa furtawa kenan tana wani yawo da ido kamar firgitacciya.
  Cikinta ya k'urawa ido sannan ya kalleta ya sakar mata murmushin k'arfin hali tare da kiran sunanta “Maryam"
Da sauri ta amsa "Na'am Yaya Allah ya baka sauki tashi kafaɗarka" Hannu takai tana taɓa shi,
   “Amin amman dan Allah kubar kukan bana son kuna min kuka koda na mutu"
  Kai ta girgiza “A'a bazaka mutu ba Yaya baza mutu ba idan ka mutu nima mutuwar zanyi"
   “Ba zaki mutu ba nine dai zan mutu ke zaki rayune keda abinda kika haifa cikin jindaɗi"
   "Taya kake tunanin zamu yi rayuwar jindaɗi nida abinda na haifa idan baka raye kunci ne kawai zai mamaye mu dan Allah ka dai na wannan maganar bazaka mutu ba"
  “Mutuwa wajibi ce Maryam dole ne sai mun mutu shiyasa ake son a rik'a tuna ta a kowane lokaci"
   Rushewa Mairo tayi da kuka  mai k'arfi ta rike gadon da yake kwance. Hakan ya haddasa shigowar likitocin da sauri.
     Faɗa sosai ɗayan likitan yayi ma Usman sannan duk suka sawo su waje,
   Kuka sosai Mairo keyi wadda har saida ya haddasa mata ciyo a kasan mararta,
 
***  
    Ana sauke Sallar A'suba Siraj ya diro cikin Asibitin, Momi na ganin shi ta tsaye da sauri tana kallon shi har ya iso. Fuskarshi cike da tashin hankali yace “Momi ya jikin nashi?"
    “Yana ciki bazan ce maka ba sauki ba tunda yana magana amman yana cikin mawuyacin hali"
   Kai Siraj ya ɗaga wadda hakan yasa ya hango Mairo dake kwance saman carpet dafe da ciki idonshi cike daf da hawaye,
     Da sauri ya share hawayen ya kara matsowa kusa da Momi ta yadda Mairo bazataji Abinda yake faɗa ba yace “Momi mi yasa kika sanar da ita miyasa kuka zo da ita har a Asibiti ba a sanar da mace mai ciki irin wannan tashin hankali"
    "Nima ba a son raina ta sani ba" Haka kawai Momi tace mishi ta cigaba da kukanta.
   Hannayenshi yasa aljihu ya sake ajiyar zuciya sannan ya nufi k'ofar ɗakin,
        Tsaye yayi yana kallonshi bayan ya maida k'ofar ya rufe kamin ya k'arasa kusa dashi ya kira sunanshi "Yaya ya jikin naka?"
Daker ya masa mishi “Alhamdulillahi Siraj ka iso?"
    “Eh mi kake ji yanzu?"
   Bai bashi amsa ba sai kawai yace “Siraj Please ka kula da Momi sosai da kuma Abinda Mairo zata haifa nasan zasu iya shiga wani hali idan ba kowa kusa dasu musamman Momi"
   Kallon rashin fahimta Siraj yayi mishi “Mi kake magana akai ne
?"
    “Siraj bana jin zan tashi daga ciyon nan  inajin ajalina yana kusa dani"
   “Waya baka tabbacin ba zaka tashi ba?"
   “Babu nine naji a jikina"
  "Zafin ciyone kuma In'sha Allahu zaka warka"
    “Nidai inason ka kula da Momi Siraj karka barta ta shiga damuwa"
   Siraj zai sake yin magana yaji an turo k'ofar ɗakin, hakan yasa shi juyawa yana kallon Mansura da wata mata ke rike da ita, daga jiya zuwa yau kawai tayi wata irin rama idonta yayi bak'i kamar ba ita ba,
   Har kusa da gadon matar ta kawota, ita kuma ta fashe da kuka tana kallon Qasin “Ina ni Allah ya ɗorawa wannan ba kai ba ina son ka Qasin sosai"
    Cikin sanyin murya yace “Na sani Mansura shiyasa naso nayi rayuwa ta jindaɗi tare da ke naso naga jininki"
     Durkushewa tayi gaban gadon tana kuka “Hakika na cutar dakai Qasin duk wani hakki da yake akaina naka banayi kana son haihuwa amman na dinga shan magani akan kar ka ɓata min rai ka kyale ni har mahaifa ta lalace ta yadda bazan iya haihuwar ba yanzu"
    “Ba amfanin yin wannan maganar a yanzu ni dai Abinda nake so dake shine kada ki cutar da abinda Maryam zata haifa dan Allah"
    “Duk abinda Maryam zata gaifa Qasin jininka ne bazan taɓa cutar dashi ba zan nuna mishi so kamar ɗan ciki na zamu bashi kyakkyawar tarbiya ba zamu sake faɗa nida Maryam ba zamu zauna a gida ɗaya zan rike kamar k'anwata nayi maka alkawari"
   “Ba tashi zanyi ba Mansura dan haka babu anfanin yin wannan maganar kawai dai inason ki kula da abinda Maryam zata haifa kamar naki"
    Kai ta girgiza tana wani irin hawaye “Bazan iya rayuwa ba kai ba Qasin ka sani"
   “Na sani amman daga yanzu zaki soma"
   Cikin kuka mai k'arfi tace “A'a Qasin ba zaka mutu ka barni ba ba zamu rabu da juna ba"
      Nan Siraj ya kalli matar ake rike da ita itama tana kukan yace “Fitar da ita waje Please yana cikin zafin ciyo yanzu"
   Ba musu ta kamata tana kukan suka fice.
      Tashi shima yayi ya fice yan nashi hawaye,
   Jinginawa yayibjikin k'ofar yana kallon Mairo dake kwance dafe da ciki bayan ya fito,
    Can ya k'arasa kusa da ita yana kllonta rabon daya sata a idonshi tun ba'a ɗaura mata Aure da Qasin ba dan duk zuwan da yake yi sai dai yace yana gaisheta amman bai taɓa yarda sun haɗu ba koda sau ɗaya,
   Tana kallonshi ta fashe da kuka “Siraj Yaya" Abinda ya furta kenan tana rike da mararta. Nan ya kalli Momi yace “Ko nakuda take ne?"
   “A'a ba watan haihuwar ta bane cikinta wata takwas ne"
   Nurses Siraj ya kwalama kira cikin hanzari suka iso ya nuna musu ita,
    Bayan sun ɗauke ta yaje ya kira wata Dr mace dan ta kula da ita.
    Baifi minti biyar zuwa shida da barin gurin ba Yarima ya iso, kana ganin shi shima zakasan hankalinshi a tashe yake. Kallo kawai yayi ma su Momi a atsayin gaisuwa dan yadda ya gansu cirko-cirko bai iya yi musu magana ba sai kawai ya tura k'ofar ɗakin ya shiga,
   “Sannu friend Allah ya baka lafiya" Abinda yake faɗa kenan yana k'ok'arin k'arasawa kusa dashi.
    “Yarima..." A hankalin Qasin ya kira suna shi. Amsawa yayi tare da jan kujera ya zauna “Na'am ya jikin naka?"
   “Wata alfarma nake rik'o a gareka"
  “Alfarma kuma Qasin kamar ta me?"
   Ya dade kamin yace “Nasan ka tsaneni Yarima amman ina rokonka dan Allah kada k'iyayyar da kake min ta shafi Maryam ko abinda zata haifa Please"
   Murmushi Yarima yayi idonshi cike da hawaye yace “I hate you no more Qasin banyi maka tsanar da har zai iyasa na cutar da iyalinka ba kuma duk wannan ma abaya ne na maka alkawari babu abunda zai sake shiga tsakanin mu"
   “Yes babu kan tunda zan mutu zan tafiyata na bar duniyar"
   Kafadarshi Yarima ya dafa “Zaka tashi Qasin zamu sake zama abokai kamar lokacin da muna k'anana"
   “Bazan tashi ba Yarima i feel it" Idonshi cike da hawaye yayi maganar,
    Hannu Yarima yasa ya toshe bakinshi ya lumshe ido. Suna haka Siraj ya shigo wata Nurse na bayanshi rike da akwatin magani,
  Tun daga bakin kofa yace ma Yarima “Ka tashi ka fice yana cikin zafin ciyo yanzu baya buk'atar kowa kusa dashi"
     Sai da ya buɗe ido ya sake kallon Qasin sannan ya tashi ya fice.

       Sirinji Siraj ya ɗauka ya shiga ɗura mishi allura, yana faɗin “Ya kamata ka samu bachi yanzu"
   “Karka min alurar nan Siraj"
    “Dole ne ayi maka ita Yaya kana buk'atar hutu"
  “Baka tsoron idan kayi min wannan alurar nayi ta bachin da bazan farka ba"
   Tsayawa Siraj yayi cak. Sannan ya lankwashe alurar har ta sokar mishi hannu, da sauri Nurse ɗin ta aje abinda ke hannunta ta rik'e hannun shi tana faɗin “Calm down Dr"
  Bai kulata ba ya shiga faɗa da Qasin idonshi cike da kwallah “Irin wa yannan kalaman naka ne suka haddasa matar nakuda ba lokacin haihuwar taba wadda hakan kan iya haddasa mutuwar abinda zata haifa ko kuma ita kanta, miyasa kake irin haka ne Yaya?"
   “Siraj ba ko wane bawa bane idan zai mutu yake samun irin damar dana samu ta aiwatarda wasu abubuwan da halshen bakina ba"
    Gufanawa Siraj yayi gaban gadon kamar mai rokon gafara yana kuka “Dan Allah kabar irin wannan maganar Yaya i don't want to lose you"
   “Of course you haka to" A wahale yake maganar,
  “Taya kake tunanin ɗan'uwanka zai rayu idan ba kai a kusa dashi?"
   “Ka dawo da aikinka a nan Siraj dan idan ka cigaba da zama Abuja abin zai yima Momi yawa"
   Gefen rigarshi Siraj yasa ya share hawayenshi ya tashi ya fice.

   ***     ***     ***
Two hours Mairo tayi tana nak'uda cikin ikon Allah Allah ya kawo mata sauki ta santalo kyakkyawan ɗanta,
   Nan wasu Nurses suka hau gyara ta ita kuma Dr ta shiga cigaba da yi mata abubuwan da akeyi ma macce bayan cire ɗa.
   Saida suka gyara shi tsaf sannan wata Nurse ɗin ta fita karɓa kayan jariri,
    Bayan sun saka mishi kayan suka naɗeshi cikin tawul suka fito dashi suka mik'ama Momi dake kuka tare da dariya.
    Mansura ce ta riga kowa karɓar shi ta manna mishi kiss a goshi sannan ta nufi hanyar da zata kai gurin da ɗakin Qasin yake,
    A hankalin ta tura k'ofar ɗakin ta shiga Momi na bayanta kowanne fuskarsa da hawaye. Kusa da gadon ta tsaya tana nuna mishi jaririn “Maryam ta sauka Qasin mun samu ɗa"
     Yana kallon yaron ya lumshe ido hawaye suka gangaro mishi suka shiga cikin kunnen shi sai numfashinshi ya fara rawa.


Taimakon gaggawa likitocin suka shiga bashi cikin taimakon Allah numfashin nashi ya dawo dai-dai,
   Su Momi na tsaye waje cirko-cirko likitocin suka fito. Jiki na rawa Momi ta shiga tambayar ɗayan likitan “Yana da rai kuwa?"
  Sai da ya sauke ajiyar zuciya sannan yace “Yana da rai amman abinda kukayi kasada ne babban dan ba'a nunawa marar lafiya abinda zai tada mishi hankali irin haka"
   "Alhamdulillahi" Mansura ce tayi godiyar tana share hawaye, Doc yace “Daga yanzu kada wadda ya sake shiga ɗakin sai da izinin Dr"
Kai Momi ta gyaɗa dai-dai lokacin Siraj ya iso yana faɗin “Ance numfashinshi ya ɗauke?"
   “Eh amman ya dawo yanzu komai na tafiya dai-dai" Dr ne ya bashi amsa
   
Kanshi ya shafa yayi ma Allah godiya Dr ya kalleshi yace “Dr Siraj kayi mishi tiyatar yanzu kaiwa dan akwai jijiyar da take taushe mashi numfashi kaga idan akayi komai zai zama dai-dai"
   Siraj ya nisa yace “Nima haka nake tunani dan idan ace sai ya warke za'ayi toh kamar wani sabon ciyon ne kuma"
   “Good haka nake nufi kuma kaga idan zai warke zai warke gaba ɗaya ne ba sai yayi jinya biu ba"
   “Haka za'ayi amman sai naga tafiyar numfashinshi tukuna sai naga yadda abin yayi"
    “Okey haka yayi amman karka sake bari wani ya shiga ɗakin koda Momi ce" Ya faɗa yana murmushi.
     Kai Siraj ya kaɗa mishi yana kallon Momi sannan ya nufi ɗakin,

Saida Siraj ya ɗauki awa biu yana ganin tafiyar numfashinshi sannan yasa aka shirya mishi komai ya shiga ɗakin tiyata dashi,
   
Awarshi hudu ɗakin tiyarta har da yan muntuna sannan ya fito tare da wasu manyan likitoci, saida ya shiga wani ɗakin ya cire kayan daya fito dasu daga ɗakin tiyatar sannan ya nufo gurin su Momi.
     A fuskarashi Momi ta karanci abinda ke bakinshi, da murmushi ya k'arasa yana kallon Momi da ita murmushin take idonta da hawaye.
   “Anyi nasara Momi babu sauran kuka sai dai ayi adduu Allah ya bashi sauki"
  Godema Allah Momi ta dinga ita da Mansura da sauran yan uwa da suke gurin,
  Murmushi Siraj yayi ya nufi k'ofar ɗakin da aka chanja ma Qasin, a nan ya tararda Yarima tsaye hannayenshi sanye cikin aljihu,
          Uffan Siraj bai ce mishi ba sai ma kauda kai da kuma yayi, murmusawa Yarima yayi ya mik'a mishi hannu yana faɗin “Congratulations Siraj"
Hannun nashi Siraj ya kalla sannan ya kalleshi “Banyi zato wannan daga gareka ba so tell me minene sirrin?"
    Murmushi Yarima ya sakeyi yace “Babu komai Siraj kuma bana so ka sake daukata cikin makiyan Qasin no more"
    Fuskarshi Siraj ya k'urawa ido nan Yarima ya k'araso kusa dashi ya dafashi “Siraj abinda ya samu Qasin ya karantar dani abubuwa da yawa just look at him da ace mutuwa yayi da yayi kyakkyawar cikawa kowa yana kuka da rashin shi ni kaina ban taba jiya n abinda naji game Qasin ba irin wadda na daga jiya zuwa yau,
  Siraj Qasin yana da farin jini gurin kowa ba kuma komai ya jawo mishi wannan ba face kyakkyawar mu'amala da kowa"
   Sukuku Siraj yayi yana kallonshi kamin yace “Yarima kaine da kanka kake wannan maganar?"
   “Nine Siraj ina nadamar abinda nayi ma Qasin da ace ya mutu da bansa ya duniya da mutane zasu kalleni ba bansan abinda zan fadawa ubangijina ba"
    Ajiyar zuciya Siraj ya sauke yace “Idan har da gaske kayi nadama ba afurincika kawai za'a gani ba a aikace za'a gani Yarima zanfi kowa jindaɗi idan ka zubarda duk wani mummunan hali nake ka chanja rayuwarka ka maida kanka ba kowa ba,
  Mulki fa ba ya dawwama kamar yadda sarauta bata dawwwama dole ne ka barsu ko su barka shin idan da tunani mutuwa miya zau kawo girman kai da ɗagawa baka fi kowa ba a gurin Allah kuma babu wadda ya fika sai wadda yafi wani tsoron Allah,
idan har da gaske ne toh zanfi kowa farin ciki da haka"
   Yarima yace “Inason ka zubarda duk wani kallo da kake mi na marar kyau hali ko kuma wadda zai iya cutar da kai ina son mu koma normal bida Qasin"
    Murmushi Siraj yayi “Nima zanso haka sai dai har yanzu gani nake kamar ba Yariman dana sani bane"
   Murmushi kawai yayi ya juya yasa hannun shi aljihu ya nufi kofar da zata fitar dashi daga gurin gaba ɗaya,
Da ido Siraj ya bishi har ya fice,

Kai tsaye gida ya nufa gurin hajiya,
     Parlor ya sameta kishingiɗe ita da bak'inta suna fira, tana ganin shi ta zaune yana kallon shi.
  'Daya bayan ɗaya ga bisu duk sai da ya gaishe su, sannan ya nufi cikin ɗakin,
Ba Hajiya ba har ba har su saida sukayi mamakin abinda yau Yarima yayi musu abinda bai tanaɓa.
     Tashi Hajiya tayi ta tufa mishi baya zuciyarta cike da tambayoyi ta shiga ɗakin,
Yana ganinta ya sakar mata murmushi "Hajiya ta?"
“Na'am Yusuf"
Sai ta zauna sannan tace “Ka chanja Yarima fiye da yadda nake tsammani ka fara zama yadda nake mafarkin zaka zama"
  “Yafiyarki nake nema nasan na ɓata miki da yawa"
   Kai ta girgiza mishi tana murmushi “So nawa kake so nace na yafe maka Yusuf? Na faɗa maka nida Mai Martaba tuni muka yafe maka babu sauran ɓacin ranka cikin ranmu"
   Dukawa yayi har k'asa yace “Hajiya ina neman wata alfarma agareku?"
  “Ka faɗi ko minene zanyi maka shi Yarima"
  “So nake ku zaɓa min matar Aure keda Mai Martaba"
Wani irin daɗi Momi taji sai kawai idonta suka cika da kwallah.
  “Na gode Yusuf Allah yayi maka albarka zamu zaɓa maka matar data dace da kai In'sha Allahu"
   Tashi yayi tsaye ya rumgume ta ya lumshe ido.

     *Wannan kenan*

  ***
Ranar da Mairo ta cika sati ɗaya da haihuwa yaro yaci suna Yusuf sunan Yarima akayi mishi lak'ani da little Yarima sosai Yarima ya jindaɗi karku so ganin irin kayan da yayima jariri da uwar shi,
  Aɓangaren su Momi basai na faɗa muku irin kayan barka da ta zuba ita da mutanenta ba dan kusan hausawa sunce abu namu.....
  Su Gwaggo kan bana cewa komai dan nasu farin cikin baya faɗuwa,

   ***   ***   ***  
Ciyo ne yake zuwa nan take amman Lafiya sannu-sannu take Shiga haka Qasin ya cigaba da jinya yana samu kyakkyawar kulawa daga ɓangaren mtanshin da kuma Momi, Yarima da Hajiya ma ba baya ba kusan kullum sai yajs Asibitin har ya samu sauki aka sallame shi,
    Ranar daya dawo gida Mansura da Mairo kamar su zuba ruwa k'asa su sha dan murnar, anan gasa ta shiga tsakaninsu kowace ta rik'a k'ok'arin ganin ta kyautata mishi kuma suka haɗa kansu kamar babu abinda ya taɓa shiga tsakanin su,
      Bayan wata hudu da sallamar Qasin daga Asibiti aka ɗaura Auren Yarima da Amaryar da Hajiya ta zaɓa mishi yar wani tsohon kwannan katsina,
    An zubarda nera tsayawa faɗa muku irin shagulgulan da akayi a biki ɓata lokacine, manyan mutane suka halarci bikin ta ko ina.

***
     Bikin shi da wata biu akayi na na Siraj da Amaryar shi a Abuja akayi komai can ne Mansura ta ziyarci wata Asibiti mai zaman kanta dan a duba mata lafiyar mahaifarta.
     Duk wani bincike da ya dace saida likitocin sukayi sannan suka tabbatar mata da bazata iya ɗaukar ciki ba dan mahaifarta ta lalace sosai ta yadda bazata iya rikon ciki ba,
Bakin ciki Mansura tayi sosai tayi dana Sanin abinda tayi.

***

Little Yarima nada shekara da wata biyar Mairo ga sake samu ciki. Murna gurin Momi da Qasin ba'a magana, Qasin kamar ya haɗe ta dan farin ciki.
    Cikin jindaɗi ta kwanciyar hankali tayi fa rainon cikinta har ya girma ta haifo yan biu duk mata, aiko lokacin ne Qasin yace bata ga komai ba indai so da kauna ne yanzu na fara nuna mata shi.
   Mairo tayi sani fari tayi bulbul gwanin shawa'awa Mansura ma ba bayab dan duk wani bacin rai nata aje shi tayi gefe suka rika juna ita da mairo kamar ba kiyashi ba ba zaka gansu kace wani abu ya taba shiga tsakanin su ba,

Aɓangaren Yarima ma ba shida wata matsala shida matarshi farin ciki ne da jindaɗi kawai a gidan duk wani hali nashi marar kyau ya zubar suka koma shi da Qasin kamar AMINNAN JUNA, Momi tafi kowa farin cikin ganin halin da su Qasin da Yarima suke yanzu,
  Ita da hajiya suka koma kamar yadda suke da komai normal.
Suka shiga wata sabuwar rayuwa mai cike da jindaɗi.

TAMMAT BIHAMDILLAH!
Oh Allah hope for your mercy. Do not leave me for myself. Correct all of my affairs for me.
Anan na kawo karshen wannan littafin mai suna MAIRO kurakuran dake ciki Allah ka yafe min yar karamar faɗakarwa dake ciki Allah yasa mu anfana da ita, duk da ba a nan naso na tsayawa amman ku kuka hanani kashe Qasin 🤷🏿‍♀.

Compiled By Hausa Novels Online (Telegram)